Kurkukun Kaddara Book 2 Page 5

_~*BossLadiesWriters*~_

_*KURKUKUN ƘADDARA*_

 

_The Prisoners E5_

*Daga alƙalamin Hafsat Bature*


~Middle step~

 

_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty._

*ANEELERH*

Kwance ta ke asaman katafaren gadon ta da ke acikin haÉ—aÉ—É—en bedroom É—inta da ke a sabon gidan su na Abuja mallakin Uncle É—an Iya É—aya daga Cikin Æ™annan Abie É—inta mazaunin garin Abuja, Attajirin mai kuÉ—i ne mai yiwa Æ´an siyasa hidima, Tun bayan da Abie ya samu Æ™arin matsayi a wurin aikin shi aka yi mashi transfer zuwa ministry of finance da ke anan Abuja, a Æ™alla yau watan su bakwai da barin jihar jos, ba Æ™aramin canjin rayuwa su ka samu ba a gidan É—an Iya, mutunne mai son jama’a ga iya mu’amala da kyautatawa mutane, kusan halin shi É—aya da matar shi Aishatu wadda ake da Aunty Ummi.

“Aunty Aneelerh! Auntyna! Where are u? i’m back” can cikin bacci ta dinga jin ana Æ™wala mata kira, Sautin muryar matashiyar budurwa.

Nauyin bacci ya hana ta buɗe idanuwanta sai ma ƙara ƙudundune kanta da ta ke yi acikin lallausar bargonta, faɗowa cikin ɗakin ta yi Tabarakallahu Zankaɗeɗiyar budurwa jawur da ita, Jikinta na sanye da egyptian gown launin shuɗi, Ta yi rolling veil akanta, Light make up ne akan fuskarta daga ganinta ba ƙaramar wayayyi bace a jin farko, Takalman ƙafarta high hills ne launi ɗaya da Mayafinta white colour, hannunta na dama na asanya da Tsadadden agogo silver colour. Ƙamshin turaren Jikin ta mai matuƙar sanyaya zuciya, wayar da ke a ruƙe a hannunta ƙirar i phone 15 pro ce.

Agogon bangon da ke a É—akin ta kalla Æ™arfe 9 Na safe, Da sauri ta wurga Æ™wayar idanuwanta kan Aneelerh dake kwance saman gado, girgiza kai ta É—anyi fuskarta É—auke da Æ™ayataccen murmushi tace”Auntyna kenan bakya gajiya da bacci, sam kin canza mini ba kamar yarda na sanki ba, Gaskiya zanyi magana da Daddy ya hanzarta sama maki aiki ki fara Ni bana son inga mutun yana zaman kashe buje” da zolaya ta yi maganar a yayin da take Æ™arasa shigewa Cikin bedroom É—in, Cikin sanÉ—a take tafiya tana tunkarar A.c remote da ke ajiye saman bedside drawer, É—aukar shi ta yi saboda mugunta ta Æ™ure mata sanyin A.c, Jikin Aneelerh tuni ya fara kakarwa Sosai ta ke Æ™ara nannaÉ—e kanta Cikin bargo, Dariya sosai *FATIMA ZAHRA* ta sa ki a yayin da ta ke kallonta, Kasa jurewa Aneelerh saboda sanyin ya addabe ta, A gigice ta sanya hannu ta yaye bargon ta jefar dashi kafin ta yi yunÆ™urin buÉ—e ido da sauri Zahra ta rage sanyin a.c ta ajiye remove É—in saman drawer, ta ruÆ™e qugu tana binta da kallo.

Sleeping dress ne a jikinta Riga da wando Milk colour, Gashin kanta a hargitse, Tunkan ta buÉ—e ido ta soma surfa masifa tana faÉ—in”junaid bana hana ka Æ™ara min sanyin a.c ba? Saboda ka raina min wayau ko?wlh idan ka bari na damÆ™i hannun ka sai ka gane ba ka da wayau, Sullu6iyo kawai……” Bata Æ™arasa maganar ba ta soma Jin sautin dariyar Zahra, hakan yasa ta yi saurin ware idanuwanta tare da wurga su kan fuskarta.

Gwalo ta yi mata tare da É—aga mata gira tace”Ba junaid bane yayar shi ce mai irin halin shi, ” Harara Aneelerh ta shiga watsa mata kamar Æ™wayar idon zata faÉ—o kasa.

Zahra tana dariya tace”Iya hararar ne kawai idan mutun ya isa ya sanya hannu ya dake ni, kai da ka zo baÆ™unta gidan mutane ka ishe su da baccin lalaci…..” bata samu damar Æ™arasa maganarta ba, Aneelerh ta rarumi pillow a zafafe da duro daga saman gadonta, zaro ido zahra ta yi kafin ta juya da gudu ta nufi Æ™ofa cikin rashin sa’a Æ™afarta ta jirkice ta fasa Æ™ara zata kife Æ™asa da sauri Aneelerh ta janyota zuwa jikinta, sosai ta Æ™anÆ™ameta sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi ta firgita sosai.

“Rasa kunya 6eran tanka, Yanzu ga ki a hannuna, mai Æ™watarki yau sai Allah” Kokoyi su ka soma Yi kamar Æ™ananun yara, Zahra sai Æ™walawa Umminta kira ta ke yi tana faÉ—in tazo ta cece ta daga hannun Aunty aneelerh zata kashe mata Æ´arta, Aneeleh na dariya tace”Nima ai ina da uwar sai in kirata tazo taga idon mara kunya” ta ambaci hakan tare da Æ™walawa Maminta kira.

Sun shaƙe junansu sai nishi su ke yi gyalen Zahta tuni ya jima da zamewa saman tiles, gashin kanta baƙi wulik anyi mata kitson kalaba ya sauko har kafaɗarta.

“Aunty Aneelerh Am sorry wlh na miÆ™a wuya, zan maki biyayya na tufa bazan Æ™ara ba” Azabar zafin da taji ne yasa ta furta mata hakan donta Æ™yale ta.

Sakinta Aneelerh ta yi don itama ta gaji da kokawar Sai haki ta ke yi, A nan ƙasa suka zauna saman floor suna kallon juna.

“ÆŠauko mun ruwa mai sanyi in sha” harara zahra ta É—an jefa mata”Baki da hannu ne”? Zaro ido Aneelerh ta yi tare da cewa”bugun da nayi maki bai ishe ki ba” Jin haka yasa zahra yin saurin miÆ™ewa hannunta É—aya dafe da qugunta, Binta da kallo Aneelerh tayi fuskarta É—auke da murmushi fucewa tayi daga Cikin É—akin, after some minutes ta dawo hannunta É—auke da glass É—in ruwa me sanyi, ta miÆ™a ma Aneelerh hannu tasa ta kar6a tare da kafa ruwan abakinta Kur6a uku tayi mashi ya Æ™are, Janye shi tayi daga bakinta tadan kalli zahra da ke tsaye tana gatsina mata hanci.

“Ki gama yi mini rashin kunyar ina nan ina jiran ki, in dai ni ce za ki zo roÆ™ona in faÉ—a maki Æ™iyamil lailin da za ki yi don ki mallaki Zuciyar matashin saurayin nan da ki ka Æ™wallafa rai akan shi, meye ma sunan shi? tai tambayar tana kallon Zahra, Dariya ta saki tare da kai hannu ta kar6i glass cup din hannun aneelerh, Cikin kwarkwasa ta Juya ta nufi Æ™ofar fita daga É—akin tana faÉ—in”Heart beat of Obinna” Murmushi Aneelerh tasaki tare da cewa”Ehem shi nake nufi, zakiyi bayani ne” bayan fitar zahra miÆ™ewa Aneelerh ta yi tare da juyawa har ta kusa shiga toilet Muryar zahra ta katse ta”Bafa tafiya nayi ba, taimakon nan dai da aka saba aunty Aneelerh, ” Juyawa aneelerh ta yi tare da kallonta, Fuskarta É—auke da murmushi.

Harara ta jefa mata”Æ´ar wahala wanka zan shiga idan na fito zamu tattauna” Zahra tace”idan ma shekara za ki yi zan zauna in jira ki” ta6e mata baki Aneelerh ta yi a yayin da ta ke shigewa cikin toilet taja Æ™ofa ta datse.

Daga gefen gadonta Zahra ta zauna tana jiran fitowarta, almost 15 mins Aneelerh ta buÉ—e Æ™ofar toilet ta fito jikinta sanye da rigar wanka fara Æ™yal, ganin yadda zahra ta tsare ta da ido yasa ta murguÉ—a mata baki “Tubarkallah” Dariya Zahra ta sa ki kafin ta tsagaita da yin dariyar tace”Masha Allah Iyayen mu sun Iya haihuwa” girgiza kai Aneelerh ta É—anyi”Allah ya shiryeki Zahra, Yanzu dai ta shi ki fuce zan sanya sutura, Ki jira Ni a palour ” maÆ™e mata kafaÉ—a zarah tayi”Nifa ba Æ™aramar yarinya bace da zaki kore ni, Menene aciki don kin sanya kaya agabana, sai kace wani gardin Æ™ato Nima fa macace kamar ke komai ki ke dashi ina da…..” Kafin ta Æ™arasa maganar Aneelerh ta nufeta da gudu Zarah ta bar Cikin É—akin tana dariya.

Kaitsaye ta nufi Cikin Hadadden palourn gidan mai girman gaske. Tun kan ta ƙarasa ta hango mami da ummi zaune saman sofa suna fira, kowaccen su na sanye da atampha riga da zane ba ƙaramin kyau su ka yi ba.

“Gani nan tafe” kamar daga sama suka ji miryarta.

Atare suka É—ago suna kallonta, mami tace”yaushe kika dawo gidan”?

“Ban jima da shigowa ba, Na shiga É—akin Aunty Aneelerh ne, Na same ta kwance Tana bacci,” Tai maganar a yayin da ta ke zama saman sofa mai mazaunin mutun É—aya.

“Nasan kin kwaso gajiya, Tun asuba sai yanzu aka kammala aikin decoration É—in, Kin ci abinci kuwa”? cikin Kulawa mami ta yi mata maganar, Fuskarta É—auke da murmushi tace”mun aikatu Mami, Uban aiki kamar zamu shekara muna Yi, kinsan hidima idan akace maki ta HamshaÆ™an attajiran masu kuÉ—ine komai dagaske ake yin shi basu Æ™aramar harka, Mami zanso Kije Gidan nan zaki sha mamaki wlh, HaÉ—aÉ—É—iyar Daular arziÆ™i ce….” tun kan Zahra ta rufe baki Ummi tace”Ae Obie estate Aljannar Duniya ce Mai zaman kanta, Idan fa ki ka shiga gidan Sai ki rasa gane Awace Æ™asa kike, tsabar kayan alatun da ke a cikinsa, Yasin in mutun mai Æ™aramin Imani na rayuwa acikin tuni zai daina Sallah…..” Dariya mami ta saki Yayin da take sauraron su, daga uwar har É—iyar gwanaye ne wurin Iya bada Labari.

“Aunty duk yadda zan kwatanta maki HaÉ—uwar Kayan alatun dake acikin Estate É—insu Ba zaki Fahimta ba, Gani da ido yafi abaka Labari, Obinna family duniyace mai zaman Kanta, Ranar dana ta6a zura Æ™afa ta cikin gidan wlh Sai da gabana ya faÉ—i, nace Anya ko Mutane suna tunanin duniya? Yo abu kamar baza a mutu ba, wannan ae sai mutun ya manta cewa da tur6aya aka halicce shi” Dariya sosai Mami ta ke yi tana kallon Aunty Ummi da ke kora mata jawabi, Zahra ta É—aura da cewa”Ni wlh Naso Daddy ya sama mun Ko aikatau ne agidan su, tun ranar da naji Salary din masu aikin gidan da dollar ake biyan su, Ci da sha da suturarsu duka A kyauta ake yi masu, ai duk wanda Ya haÉ—a alaÆ™a Da É—an familyn Obinna kakar shi ta yanke saÆ™a, Shi da talauci sun raba Jaha….” in serious matter za’a ta ke magana, Ummi taci gaba da cewa”Shiyasa naso mahaifin ki ya kutsa ki cikin danginsu tun da dama É—an bangar siyasa ne, Ni ko wannan Yaron ne *DR JAZZ* kisamu ki aure shi, ko mun samu muma mu dangawali arziÆ™i” ta Æ™arasa maganar tana dariya, tur6une fuska zahra tayi Jin abunda Ummi tace”haba ummi, dr Jazz fa meye haka, Ni da na ke harin bugun zuciyar Family É—in gaba É—aya, Taya zaki haÉ—a ni da yaron da har yau ba’asan waye ubanshi ba acikin family É—in” da mamaki akan fuskar Mami tace”kamar ya ba’asan Ubanshi ba”? Zahra tace”É—aya daga Cikin ma’aikatan gidan su ce tazo dashi aikatau, Matar ma farar fata ce, ba ki ga yaron ba kyakkyawa ga son mutane, ni bazan Iya auran mara asali ba, Ta ya Ummi zatai min fatan auranshi? Ga gwarazan samari a family din kyawawan gaske masu kama da kakansu Obinna….” tana magana tana turo baki.

Ummi tace”Saboda nasan baza ki Iya samun wanda kike so ba, Haukan banza ki ke yi a kan shi, ke kin sani Ruwa ba sa’an kwando bane, Babban Goro sai magogin Æ™arfe, Wutsiyar raÆ™umi tayi nesa da Æ™asa, In banda haÉ—ama irin ta zahra taya zaki nace wa mutumin da yafi Æ™arfin ki nesa ba kusa ba? Shiyasa nace Æ™wara Dr Jazz É—in shine dai dai da ke,” É—aure fuska Zahra tayi jin abunda Umminta take faÉ—i, ta haÉ—e rai sosai, Muryarta a Æ™ule tace”Mami kinga ni ko? Ita fa mahaifiyata ce amma bata min fatan naci ka burina, Kullum sai dai tayi discouraging É—ina, meyasa ta ke yi min haka ne”? a bun ka ga me saurin kuka tuni idonta sun ciko tab da Æ™walla.

Fuskar mami É—auke da matashin murmushi ta soma magana a tsanake”kwantar da hankalin ki zahra, Ai duk kyan takalmi Æ™afa ce ke taka shi, kuma idan Allah ya Æ™addara cewa shi Yaron wanda kikeso Mijin ki ne duk min muÆ™amin shi duk mun izzar shi da kyanshi wlh da kanshi zai nemo ki a duk inda ki ke, Ai shi so bashi a matsayin mutun, mai kuÉ—i ko talaka Zahra kuma ta haÉ—a komai da duk wani É—a namiji zaiso zama da ita a matsayin matarshi,…” Tunda mamin Aneelerh ta soma magana zahra ta washe baki tana zabga uban murmushi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Aljanna, Tsabar murna batasan sa’adda ta sauko daga saman sofa É—in da ta ke zaune ba, ta dawo Æ™asa saman carpet, Ta kafe mami ido tana kallonta kamar wadda ta samu Tashar Bolly wood, Hakan ba Æ™aramin dariya yaso ba Ummi ba, Ganin yadda zarah ta ke sakin murmushi jin ana yabanta.

“Mami ni ba ina kushe Zahra bane, Just bana so ta Æ™wallafa rai akan abunda ita kanta tasan bazata ta6a mallakarshi ba, Yakamata ta runÆ™a tuna matsayinta, Mahaifinta fa É—an bangar siyasa ne ba wani shege ba, Ta ya ya ta ke tunanin zata Mallakin HamshaÆ™in mutun kamar *OWAIS SHARAFUDEEN OBINNA*!? Bazan iya lissafi ma matan da su ka yi hauka akanshi ba, Daga cikin hada ÆŠiyar Chancellor na Æ™asar Germany bayan ita akwai Ƴar sarkin saudi arab, Ga É—iyar shugaban Æ™asar America…..” Lamarin ya É—aure wa mami kai, Baki asake ta ke kallon Ummi sai da ta kai Æ™arshen maganar tukunna tace”Ni ko zanso In ga wanene wannan Namijin hurul ainin, Farin Jini sai kace É—an gwal yo wannan koda lu’u lu’u aka Æ™era fatar Jikin shi sai haka,” Dariya su ka saki gaba É—ayan su.

“Saboda Farin Jinin da Allah ya yi mashi kakan shi Ya toshe duk wata Æ™ofa da za’a Iya ganin shi, Zaiyi wuya ki samu hoton shi a social media, shahararre ne sosai babu inda ba asan shi ba, Da zarar kin ambaci sunan shi awuri sai an girgiza” Ummi ce ta kora mata jawabi, Al’ajabi Ya kama Mami”Na Æ™osa Inji tarihin Family É—insu, Najima Ina jin zancensu abakin mutune da kuma labaransu a gidan radio, Nasan fuskokin Ya’yanshi a tv sai dai bansan Komai dangane da su ba”

Gyara zama Ummi ta yi”Jinin Nasara shi ne sunan da akeyiwa family É—insu laÆ™abi da shi saboda wadatar ArziÆ™in da Allah yayi masu, Suna É—aya daga cikin Most richest family in the world, shahararru ne na bugawa A jarida, shi Obinna da ki ka ji ana faÉ—i Kakan su ne tsohon É—an siyasa ne wanda yai gwagwarmaya ya ruÆ™e muÆ™amai da dama tun daga Æ™asa Nigeria har zuwa Æ™asashen waje, Allah ya yi su da farin Jini, matan shi biyu a yadda naji labari, amma dukansu basa araye yanzu, shi kaÉ—ai ne ya rage, Æ´a’Æ´an shi bakwai kaf É—insu suna ruÆ™e da manyan muÆ™amai, su ke ruÆ™e da Æ™asar nan, Manyan Æ´a’Æ´an shi Æ´an Uku ne sune first born É—in shi” numsafawa Ummi tayi kafin ta soma zayyana mata sunayen su kamar haka.

“SENATE PRESIDENT LATEEF OBINNA, bayan shi akwai CHIEF OF ARMY STAFF SIR MUBARAK OBINNA, cikon Na ukun su shine HIS EXCELLENCY ABDUL RAZAK Obinna Gomnan Jihar Lagos, waÉ—annan sune yan ukun shi, bayan su akwai Æ™annan su maza HIS EXCELLENCY DEEN OBINNA Gomnan Jihar kaduna state, mai bi mashi PRIME MINISTER HATEEM OBINNA Shugaban Æ™asar Canada Shi ne ya ke auran Gimbiya mujeedat Æ´ar Sarkin Dubai…..” Tun da Ummi ta soma bata labarin Mami ta baza kunne tana sauraronta, ga dukkan alamu al’ajabi ya kamata duba da yadda ta saki baki tana kallonta

“Bayan Hateem sai mai bi mashi SHARAFUDEEN OBINNA Current president na Æ™asar Nigeria, Adalin shugaba hawan shi mulki da wata biyar kacal ba a Æ™ara jin É—uriyar Ƴan ta’adda ba” Fuskarta É—auke da murmushi ta yi maganar”Kada ki ji Ina yabon shi ya cancanta ne, matan shi biyu Uwar gidan shi É—iyar Sarkin Yarbawan Jihar lagos ce, Ta biyun kuma Æ´ar gidan Alhaji wada ce, Ƙanwar former Gomna na Jiharku Jos” Murmusawa mami ta yi fuskarta da alamun mamaki tace”Wai Alhaji Ubaid ki ke nufi surukin tajudden? Dama Æ™anwarshi ke auran Sharafuddeen”? Dariya ummi tayi”haba dai kada ki ce min ba ki da masaniya,” watsa hannu mami tayi”taya za’ae in sani? Ni da ba shisshige masu na ke yi ba, In banda ma abun ki ae bani da alaÆ™a dasu da ya wuce Æ™awancen Benazir da Aneelerh, Makaranta ce ta haÉ—a kuma Yanzu sun rabu, amma duk da haka Na yi mamaki,”

Ummi tace”Auran su shekara goma sha É—aya kenan A lissafi na, kada ki yi tunanin ina sanya masu ido ne, Kinsan in mutun nada ArziÆ™i da É—aukaka a kyauta ake bin diddigin shi….” ta Æ™arasa maganar tana dariya Mamin ma dariyar ta ke yi.

“Nasan zakiyi mamaki Idan na faÉ—a maki cewa Duk irin wadatar ArziÆ™in dake gare su da É—aukakarsu Basu da yawa family É—insu, Jikokin Obinna Goma sha Biyar” A É—an ruÉ—e mami tace”kai! Wai dagaske”? Jinjina kai mami tayi”Æ™warai kuwa, Saratu Obinna ce kaÉ—ai ta ke da Æ´a’Æ´a Uku, twins zaid da zain sai autarsu Faryat Obinna, Na manta ma ban faÉ—a maki ita a jerin Æ´a’Æ´an shi ba, Saratu obinna Itace Autarsu, tana ruÆ™e da muÆ™amin Minister of health Mijinta Pravin Obinna É—an Æ™asar india ne silar zuwanta karatun likitanci india Allah ya haÉ—a ta dashi…..” Ummi bata Æ™arasa maganar ba, Zahra tai saurin cewa”Cin ArziÆ™i ya kawo shi, tsabar son banza mami ya canza sunan ubanshi ya maidashi na Obinna, Sai ki rasa gane É—a ne ko suruki a gidan” tun da suka fara magana sai Yanzu ta tsoma masu baki hannunta ruÆ™e da wayarta da alama chatting ta ke yi.

“To ke ina ruwanki zahra? Na rasa meya tsone maki ido da mutumin nan, ya fa riga daya zama É—an gida, yafi Æ™arfin a kira shi da suruki sai da É—a” Ta6e baki zahra tai”Haba Ummi haka ake surukuntaka, mutun ya tare a gidan surukai don kawai yana auran yar shi, nifa Pravin sam baya burgeni mutun kamar É—an ta’adda” mami sai kallonta take yi, ta fahinci bata Æ™aunar mutumin.

Ummi na ƙoƙarin buɗe baki don ta yi magana Muryar Baby Junaid ta katse masu firar tasu.

Mommy! I’m back! I really missed u, Na maki tsaraba” Gaba É—aya suka É—ago suna kallon shi, shigowar shi kenan Cikin Falon Jikin shi sanye da suit Na yara Black colour, Madarar kyau, Ya Æ™ara girma ayanzu yana acikin shekara ta biyar a duniya. hannun shi na aruÆ™e da Farar leda ta shopping, ba shi kaÉ—ai ya shigo palourn ba, Yana atare da Mahboob Ƙanin Zahra, Kamar su sak kamar tagwaye shi da ita, Crazy Jeans ne a jikin shi, daga sama Ya sanya farar t shirt, Sumar kanshi kwance luf tasha gyara, MiÆ™ewa zahra tayi da gudu ta nufi baby junaid tana ware mashi hannu don yazo ta rungume shi, tunkan ta Æ™araso ya girgiza mata kai Yana faÉ—in”Na mommy ne wlh, Wayo kike so ki min dan In É—an maki tsarabata” Dariya suka saki, Zahra tace”matsalata dakai kenan, Komai Mommy mommy, idan da kara nima ai uwarka ce, Zonan dallah” ta ambaci hakan tare da janyo shi zuwa jikinta.

Ummi tana murmushi tace”Kada ka yarda Junaid, Aunty zahra wayau zata maka don ka É—an mata tsarabarka, ” É—aure fuska zahra tayi”Ummi kada kisa ya raina ni fa” Ummi tace”Æ™arya nayi ne? Yaro yayiwa babarsa tsaraba ke kuma Uwar wayau kina son cinye mashi abu” gatsina mata hanci zahra tayi tare da Wuce Bedroom É—in Aneeleh É—auke da Junaid a hannunta, Ya É—aure mata fuska duk don kada tace zata Ci mashi tsarabar shi.

“Sannu da dawowa,” Mami ce tayi maganar tana kallon mahboob dake zaune saman Sofa, Fuskarshi É—auke da murmushi Ya ce”Yawwa mami fatan na same ku lafiya,” Suka amsa mashi da lafiyalou

“Har an kammala registration É—in”? Ummi ce ta yi mashi maganar, É—aga mata kai yai alamar eh Saura zuwa school Ya rage mashi On monday zai fara zuwa, Uniform É—inshi suna acikin mota nabarsu, wlh nagaji Ummi yunwa nake ji kamar in ci Æ´an hancin Cikina” yai maganar Yana yamutsa fuska,

Ummi tace”nayi zaton Kun biya restaurant Cin abinci” É—an zaro ido yai kafin yace”Tab, Ga abinci agidanmu sai in kwasa in tafi restaurant cin abinci saboda almubazzaranci, ” dariya mami ta saki, Mahboob Ya iya tattalin kuÉ—in shi, Ya tsani almuzarranci arayuwarshi. Yasan ciwon kuÉ—in shi.

“Tsokanar ka na ke yi don nasan halinka, Da shegen maÆ™o, Fatana Allah yasa ba ka bar mana yaro da yunwa ba” ta6e la66ansa yai”Tun da muka baro school É—in ya fara yi min kukan yunwa, don dole na tsaya a wata plaza na siya mashi snack, shine fa daya ci ya rage saura nace ya bani inci yace mommyn shi zai ma tsaraba, ni da na sayi abu da kuÉ—ina amma ya hanani ci, SauÆ™in ma wurin jatumarshi zanje ta biyani Æ´an canji na,” tuntsirewa Mami tayi da dariya, ita kanta Ummin murmushi ne akan fuskarta, Lamarin mahboob sai addu’a, Babu mutunci indai akan kuÉ—ine
“Kai yanzu saboda rashin ta ido, Sai ka je wurin Aneelerh ka ce ta biya kuÉ—in daka siyama yaronta snacks? ÆŠanka ne fa” Hura hanci yai tare da cewa”Kusan fa dubu É—aya na kashe mashi, haba ummi, kinsan fa yadda nake wahalar neman kuÉ—i, Daddy fa ko sisi baya bani sai in yaga dama kema kuma haka” Baki asake Mami ke kallon shi Ummi tace”indai mahboob ne kaÉ—an kika gani, ae baida mutunci indai akan kuÉ—in shi ne, Mara Kunya tashi ka bamu wuri, kuÉ—inka kuma Ka zo da anjima ka kar6a ni zan biya ka,” har ya yunÆ™ura zai miÆ™ewa, Idon shi ya sauka akan Ana mai aikinsu Aneelerh, Fitowa tayi daga Kitchen hannunta ruÆ™e da tray an jera kayan breakfast É—insu, hankalinta kwance take tafiya jikinta na sanye da Skirt pensil baÆ™i yabi shape din Jikinta, Daga sama ta sanya Riga launin green, Ƙura mata ido yai yana kallonta, Idon su mami akanshi ganin yadda yake binta da ido.

Tsawa Ummi ta daka mashi a firgice ya waiwayo yana kallonta, fuskarta a É—aure tace”Uban me kake kallo”? Yamutsa fuska yai”Kayan abincin dake a hannunta nake kallo ba wani abu ba,” yai maganar tare da wuce ya nufi dining table É—in, da Ana take jera masu kayan breakfast, Kujera yaja ya zauna Yana faÉ—in”Ya ki ke”? Murmushi ta sakar mashi”lafiyalou, na gan ka É—azu da safe zaku fita da baby junaid” 6ata fuska yai”shine baki min magana ba mun gaisa”?

Hankalinsu mami gaba É—aya akanshi, Ummi tace”Oh Ni Æ´ar ubansu, Yaro ya zama mayen mata, In banda haÉ—ama irinta Mahboob ina zai kai Ana”? Mami tace”tashen balaga ne kawai, nan da wani lokaci zai dawo hayyacin shi,” dariya suka saki, Kafin suka miÆ™e zuwa Dining É—in domin suyi breakfast..

Lokacin da Zahra ta shigo ɗakin Aneelerh ɗauke da baby junaid, A zaune ta same ta gefen gado hannunta ruƙe da hoton su, wanda su ka yi aranar birthday ɗin Angel, tun da ta fito daga wanka, ta shirya kanta Cikin riga da skirt, kanta na ɗaure da mayafi, jin motsin shigowar Zahra yasa tayi saurin ɗaura hoton hannunta saman drawer, idanuwanta acike suke tab da ƙwalla.

“Aunty Aneelerh Ga Baby Junaid É—inmu Ya dawo” cikin sanyin murya zahra tayi maganar don ta fahimci yanayin da Aneelerh take aciki, taÆ™i É—agowa su haÉ—a ido, saboda ba ta san zahra taga hawayenta.

Sauke Junaid ta yi Æ™asa, da gudu ya nufi Aneelerh ya haye saman Jikinta hannun shi ruÆ™e da ledar tsarabarta”Mommy ba ki yi missing É—ina ba”? a hankali ta É—ago ta kalle shi, wani irin farin ciki ya ratsa zuciyarta, duk halin da zata shiga idan tayi tozali da fuskarshi sai ta ji sanyi aranta, ÆŠaukarshi tayi tare da É—aura shi saman laps É—inta sosai ta rungume abunta”Momy ga tsaraba ki ci” Zahra na atsaye tana kallon fuskar Aneelerh, tsananin tausayinta ta ke ji.

“Thank U my baby Boy, Nayi kewarka kamar zan zauce, Ya school É—in? Surutu ya soma yi mata yana zayyana mata kyawun makarantarsu, yana magana ya buÉ—e ledar tsabar ya curo guntun donut daya ajiye mata abaki Ya tura mata, taunar shi ta soma yi tana murmushi, daga gefen su Zahra ta zauna still idonta akan fuskar Aneelerh, Sai kakkauce mata take yi duk don kada su haÉ—a ido

“Mommy uniform É—ina suna acikin motar bro, hada sandals É—ina, kuma ya ce in faÉ—a maki ba zai Æ™ara kaini school ba saboda fetur tsada yake yi, wai sai dai ke kina kai ni” dariya Aneelerh tasaki jin abunda yace”kwantar da hankalin ka, nima ai ina da mota, kuma zan fara zuwa aiki, Kamar yadda nake É—awainiyar kai Angel makaranta lokacin da tana araye, inje in É—auko ta kaima haka zan dinga yi maka….” zahra ce ta katse ta da cewa”nima ina da mota, kuma ashirye nake da in dinga É—awainiyar kaishi,” sai da tayi wannan maganar Aneelerh ta É—ago tare da kallonta, Hawayen da take 6oye mata ne suke soma gangarowa saman kuncinta.

“Haba Aunty Aneeleeh i know it’s hard to let go of the past, but worrying about it won’t change anything wlh bamu jin daÉ—i idan muna ganinki cikin damuwa” zahra na rufe baki Baby junaid yace”sai da na mata faÉ—a ta daina kuka, ta Æ™i jin maganana, mommy bata jin magana zanje na faÉ—a wa mami kina kuka” yai maganar yana Æ™oÆ™arin sauka daga saman jikinta da sauri ta Æ™anÆ™ame shi”na daina babyna, tun da baka so, ba sai ka faÉ—a ma mami ba kaji ko” amsa mata yai da toh amma idan ki ka Æ™ara saina faÉ—a mata” murmushi Aneelerh ta saki idonta akan zahra dake kallonta.

“Idan ina kallon hotunansu ina tuna irin rayuwar farin cikin da mu ka yi, Shiyasa ni ke zubda hawaye na, Allah na gani bazan Iya mantawa dasu acikin rayuwata ba, waÉ—annan mutanan uku masu mahimmanci sun kafa tarihi acikin zuciyata, nayi imanin har in koma ga mahaliccina bazan ta6a samun wanda zai maye min gurbinsu ba, Nafi damuwa da Angel wlh ina son yarinyar nan naji takaicin rashinta naso ace sun rayu tare da É—an uwanta junaid, Angel abun tausayice ta rayu ba tare da mahaifiyarta ba, Na rasa wata irin zuciya ce a Æ™irjin benazir……” sosai Aneelerh ta fashe da kuka, Jikin zahra duk yai sanyi, zagayo da hannunta tayi saman bayan Aneelerh ta kwanto da kanta saman kafaÉ—arta”I feel ur pain Aunty Aneelerh, da inada halin da zan iya yaye maki damuwarki da nayi sai dai babu, abu É—ayane nayi maki alÆ™awari zan tayaki addu’a, ni a tunanina bai kamata ace anyi shiru da maganar nan ba, idan har ba a yaÉ—a labarinsu taya za’asan in suna araye? Yakamata atada zancen labarin 6acewarsu a social media, inaso labarin ya zama sabo tamkar a yau ya faru in dai har mu ka yi hakan in sha Allah indai suna araye zasu bayyana ne…….” tunda zahra ta soma magana Aneelerh ta natsu tana sauraronta, ga dukkan alamu ta gamsu da zancenta

Da sauri ta É—ago da kanta daga saman kafaÉ—ar zahra muryarta adisashe tace”Zahra kina ganin idan muka yi hakan za’a dace” fuskar zahra É—auke da murmushi tace Æ™warai kuwa in sha Allah zamuyi nasara, Kibar komai a hannuna Idan Daddy ya dawo zamu yi magana dashi, tunda kinga shi mutunne na jama’a zai tsara mana yadda za’a watsa labarin 6acewarsu, so nake duniya ta É—auka,” lumshe ido Aneelerh tayi har cikin ranta take jin Æ™warin gwiwa.

“Samu Ƴar uwa kamarki zaiyi wuya Zahra, shiyasa nakeson ki ina matuÆ™ar Æ™aunarki, ke ta dabance kina da kaifin basira, Ni ban ta6a tunanin tada zancen 6acewarsu tajuddeen ba sai da ki ka bani shawara, Allah ya Biya maki buÆ™atunki na alkhairi”

“Ameen auntyna, ko dan saboda farin Cikin ki zanyi Æ™oÆ™ari inga an watsa labaransu tare da hotunansu, “farin ciki ya cika Aneelerh, sosai ta rungume zahra, Baby Junaid yayi lamo saman Æ™irjinta, sai faman lumshe ido ya ke yi bacci ne ke shirin É—aukarshi

“Excuse ma’am” muryar Ana ce ta katse su, atare suka É—ago suna kallonta, tana daga tsaye bakin Æ™ofar É—akin, a mutunce suka gaisa kafin ta sanar dasu cewa Breakfast yana jiransu a dining’ amsa mata su ka yi da toh, kusan atare suka miÆ™e, Aneeleh na É—auke da babyn junaid”

 

*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*

 

First bank

 

3196407426,

 

*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*

No comments