Cuta ta Dau Cuta 8
*_Typing_*
*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_
_ _
_Shafi na takwas_
INA ƳAN KASUWA MASU SON ƘAWATA KASUWANCINSU TA HANYAN GRAPHIC DESIGN, DA MASU SHIRIN BIKI, KO SUNA, DA MASU SHIRIN WALIMAR SAUƘA, DA MASU SHIRIN YIN BIRTHDAY, KAI HARMA DA MASU ANNIVERSARY
MAZA KU GARZAYO “UMMUH FARUQ GRAPHIC DESIGN “TA TANADAR MUKU DA HAƊAƊƊUN DESIGN MASU ƘAYATAR DA MAI KALLONSU.
KAMA DAGA
*FLYER
*3D MOCKUP LOGO
*2D MOCKUP LOGO
*NORMAL LOGO
*IMAGE LOGO
*BANA
*STICKERS
*ADVERT VIDEO
*PROFESSIONAL INVITATION
*INVITATIONS CARD
*BIRTHDAY VIDEOS
*POSTER
*CERTIFICATE.AND MORE……
CONTACT ME ON
09035390383
___________
……..Cikin ƙarfin hali ta ƙarasa duka aikin da ya kamata tayi taja jikinta da ƙyar zuwa falo ta kwanta. Sosai kanta ke mata ciwo saboda kukan da tasha. Barci ya ɗan fara figarta sama-sama ya shigo gidan. Ciki-ciki yay sallama batare da ya kalli inda take ba. Har ya wuceta sai kuma ya dawo da baya yana kallonta. Gabansa ne ya faɗi ganin yanda idanunta sukai tulu-tulu alamar taci kuka, ga jijiyoyin kanta da sukai ruɗu-ruɗu suma.
“Yanzu ke akan wannan ɗan abunne kika zauna kikai kuka har idanunki suka kumbura haka?”.
Idanun ta buɗe a hankali ta sauke kansa, maimakon amsa masa sai ma ga wasu hawayen na zaryar sakkowa. Da sauri ya kauda kansa yana jan ƙaramin tsaki zai bar wajen ta riƙo hannunsa caraf. Cak ya tsaya, sai dai bai juyo ya kalleta ba. Ƙasa ta zamo daga kujerar ta durƙushe tare da sake fashewa da sabon kuka hannunta biyu riƙe da nasa.
“Dan ALLAH kayi haƙuri ka yafemin, nasan nayi kuskure amma in sha ALLAHU bazan sake ba, kada kayi fushi dani mijina na tuba”.
Idanunsa ya lumshe yana jan ajiyar zuciya, kamar bazai kulata ba sai kuma ya juyo gaba ɗayansa. Idanu ya zuba mata na tsawon mintuna biyu. Ita dai tama durƙushe tana kuka mai ban tausayi. Kamata yay ya miƙar, batare da yayi magana ba ya zaunar da ita a kujera shima ya zauna. Nan ɗin ma baice komai ba ya dai zuba mata ido tana cigaba da kukan har tsawon wani lokaci kafin ya ɗan tsuke fuska da faɗin, “Amma kin san bana son kuka ko! To na gaji daji haka nan”.
Da sauri ta shiga goge hawayenta, dan tasan tunda ya faɗi hakan to ya huce kuma kenan. Cikin dasashiyyar muryarta ta ce, “Nagode mijina.”
Bai tanka mataba nan ma, bata kuma damu ba ta sake cewa, “A kawo abinci? Abinda kafi so na dafa maka”.
“Ba yanzu ba, bani ruwa kawai”. Ya amsa mata cikin sauƙaƙa murya yanzu kam.
Zaram ta miƙe baiwar ALLAH har tana cin tuntuɓe, ALLAH dai ya taimaka bata faɗi ba. Yanda bai motsa ba haka bai tanka mata ba, sai binta da kallo da yay harta fice. Bayansa ya kai jikin kujerar a hankali ya kwantar yana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanunsa, tabbas yana son Khadijah, duk da kuwa faɗa ne ya fara haɗasu, ya kuma fara jin sonta ne akan bigiren sha’awa, dan a lokacin daya yaga mata hijjabi a wancan lokacin yay tozali da cikakken halittar ta yaji wani abu da bai taɓa jiba akan mace ba ya tsarga masa, bayan an musu sulhu hararar da take masa da murguɗen baki a duk sanda suka haɗu ya dasa masa soyayyarta, dan duk da yaji sha’awarta a waccan ranar bai taɓa sama ransa wani mummunan al’amari a kanta ba. Tabbas son Khadijah yake, ya kuma yanke shawarar su gudo suyi aure ganin iyayensu sunƙi fahimtarsu. To a yau kuma ga Hajiya Kainaat a rana tsaka. A wata gaɓa da shi kansa yasan yana buƙatar kuɗi, dan kuwa bashi da wani buri a mataki na biyu bayan samun Khadijah da yaso sai mallakar dukiya. Sun baro iyayensu sun gudo nan sunyi aure, yasan dolene watarana su buƙaci waiwayar gida, komawa da tarin dukiya a wani matsayi shine abu mafi muhimmanci da iyayensu zasu kalla suyi saurin amsarsu. Wasu sukance idan aka samu akasi a irin auremsu da an haihu aka koma ga iyaye sukan amsheka dan waɗan nan ƴaƴan, sai dai kuma kash shifa magana ta gaskiya baya buƙatar haihuwa a yanzu, yo ALLAH na tuba shekararsa nawa ne ma kwata-kwata da zai yarda ya haihu a yanzu duk ya tsofe. Ita kanta Khadijah ya barta ta fara haihuwa ai sai tazo ta koma wata babarsa ne, shiyyasa ma yake zuba mata ƙwaya a duk sanda ta samu ciki batare data fargaba ta sha a lemo cikin ya zube. Da ga ƙarshe daya fahimci ba daina ɗaukar cikin zatai ba sai kawai ya saka likitan ya saka mata robar hana ɗaukar ciki tana tsaka da magagin ɓarinta na ƙarshe, sai bayan wani lokaci idan aikinta ya ƙare zai bi wata hanyar a sake saka mata wata batare data sani ba, dan ko zai yarda ta haihu gaskiya sai nan da shekara goma sha biyar haka sun gama more rayuwarsu. Amma yanzu baya buƙatar takura, ƴaƴa takurane kawai da salon tsofar da mutane, gashi ka zama wahalalle dan dole ka nemo suci ka biya musu kuɗin makaranta idan basu da lafiya kaine, kai abunfa ba sauƙi. To amma yanzu ga babbar dama ta samu, wato samuwar dukiya, dan duk da Kainaat ƙyaƙyawar mace ce fara tass shi baiji zai iya sonta ba, yo dakaɗan fa Ummansa ta girmeta, dan Ummansa ta sanar masa tana da shekara goma sha biyu akai mata aure kasancewarsu fulani, ta tare tana da shekara sha uku, ta haifesa tanada shekara goma sha biyar, yanzu shekararsa ashirin da huɗu, Ummansa nada shekara talatin da tara, matarnan zata iya kaiwa talatin da biyar, shekara huɗu Ummansa ta bata fa kawai. Taɓɗi babbar magana, yo ai koda take da ƙaramin jiki duk wanda ya kalleta yasan ba yarinya bace ba wlhy, amma kuma bazai bari damar nan ta kuɓce masa ba, dan a yanda ya fahimceta zata iya bashi dukiya mai yawa akan son shin da take, sannan in har ya mallaketa wannan companyn kansa da akace nata ne da tsohon mijinta ya gina mata zai iya mallakesa batare data farga ba….”
Wani irin murmushi ya kufce masa har haƙoransa na bayyana. Idanu sosai Khadijah da tun ɗazun ke faɗa masa ga ruwa ta kawo bai jiba ta sake zuba masa. Mamaki na ƙara baibaye mata zuciya, dan yanayin nashi na sake tabbatar mata akwai abinda yake ɓoye matan tabbas. Amma tana jin tsoron cigaba da masa bore, dan haka haƙuri da shanyewa ta zubama sarautar ALLAH ido kawai ya kamata gareta a yanzu.
“Ga ruwan”.
Ta sake maimaitawa a hankali. Idanunsa ya buɗe a kanta, a take ya haɗiye murmushin da yake yi batare da yace komai ba ya amsa. Sosai ya sha ruwan har hakan ya bata mamaki, yana kammalawa ya miƙe ya shige bedroom. Kwance ya kai a can ma ya sake zurfafa a tunani, da ga baya kuma yama miƙe ya shiga kaiwa da komowa tare da ƙulla abubuwa da yawa akan Kainaat da dukiyarta…..
__________★
“Wai kina nufin har kin zauna da shi Kainaat? Anya bakiyi gaggawa ba kuwa?”.
“Humm Nadwa kenan, to miye amfanin jinkirin? Karfa ki manta kwana goma sha biyu ya ragen na gama iddata, kuma a washe gari nake son a ɗaura aure.”
“To ni yanzu babu abinda zance tunda kin riga kin yanke hukunci, sai dai zan baki shawara gaskiya kiyi ƙoƙari bayan an ɗaura auremku ki tasashi gaba kuje ga iyayensa, kinga dai gara ita matarsa duk da gudowa sukai iyayensa sun san da ita, ke kuwa fa? Sannan yanda nake ganin idanun yaron nan a tsakar ka wlhy gara kisan tushensa koda ta ƙwaɓe kina da madafa”.
Dariya sosai Kainaat keyi, Sai da tai mai isarta Nadwa na kallonta kamar ta samu tv kafin ta tsagaita. “Oh oh! ALLAH Nadwa kinada kayan haushi dana dariya. Yanzu ni banda abinki wannan ɗan yaron ne har zai iya sakani a wani tarko kike tunani? Sannan kuma idan baki mantaba bari na tuna miki, auren kisan wuta zanyi domin na koma gidan Abaan, bawai zama zanje yi da yaron nan ba. To niko har wace matsala ce zan hanga da zata sakani damuwa da wani sanin iyayensa da tushensa. Please karki hargitsa mini lissafi. Ke dai kawai ki tayani da fatan alheri, sannan ki samo min wanda nace miki ɗin dan ina son da ga gobe a fara bibiyarmin duk wani motsinsa”.
Kaɗa kai kawai Nadwa tai da faɗin, “Okay shike nan. ALLAH yasa ayi lafiya a kuma rabu lafiya. Amma ya kamata kuma shima Abaan ki fara tabbatar da har yanzu kina a zuciyarsa, kar kiyi jifan gaffiyar ɓaidu. Dan yanzu haka yanda nake jin labari tunda kuka rabu yabar ƙasar har yanzu bai sake waiwayowa ba, amma akwai bikin buɗe katafaren companyn nan nasa na shinkafa da ake saka ran zai zo nan da wata uku da wasu satittika”.
“Nadwa kenan ai duk nasan wannan. Hasalima duk wani tsare-tsaren buɗe Companyn nan nice na tsarashi a satin da tsinanninyar uwarsa zata saka shi ya sakan. Na kuma tabbatar dama duk inda yake sai ya dawo anyi bikin buɗe Companyn da shi, saboda muhimmancisa a wajensa. Wannan shine dalilin da yasa ma nake son ina gama Idda washe gari a ɗaura min aure da yaron nan dan sati biyu ko wata ɗaya nake son nayi da shi, kin ga zan sake wata iddar na gama kusan dai-dai da lokacin buɗe Companyn….”
“Aiko bazai gamu ba kafin sannan lissafa kuma kiga”.
“Hakan na matsala bane ai, fatan ba dai nayi auren na fito ba, duk sanda zai zo ƙasar ya san dai yana da damar maida aurenmu hakan ya wadatar dani”.
“To ALLAH ya fidda a’i daga rogo”.
“Suɓul kuwa zata fita gyara zama kisha kallo.”
“A kallo kam mune a gaba ai. Sai dai a shirya tsaff dan irin yaran nan fa shap shooters ne wlhy zuwa ɗaya sukema yaƙin ƙasa da ƙasa su dawo da ganima. Karki saki jiki cewar kunata neman haihuwa ke da Abaan tun bayan haihuwar farko da kikai yaron ya rasu yanzu ciki bazai shiga ba”.
Cikin ɗage gira Kainaat ta ce, “Uhhyimm! Sai akace miki kuma zan ma bashi kaina ne? Ai bana jin zan iya mallakama wani namiji jikina bayan Abaan Nadwa, dan Abaan da kike gani babban gwarzon mayaƙi ne da bayi da kwatankwaci a filin yaƙin nan…”
“A wajenki ba”. Nadwa ta faɗa tana dariya.
Dariyar itama Kainaat keyi, ta bata amsa da, “Muje a hakan a wajena ɗin”.
Haka suka cigaba da hirarsu cikin nishaɗi da tsara zaman Kainaat a gidan Dafeeq da yanda al’amura zasu kasance. Duk da dai batun cikin nan da Nadwa tayi ya tsayama Kainaat a zuciya matuƙa….
_________★
Da ƙyar aka iya tara-tara wajen kamashi, wani dattijo maƙwafcinsu ya cire babbar rigarsa aka sakamasa. Gudun da yaci yasa numfashinsa gaba ɗaya ya koma fita da ƙyar, da ga ƙarshe ma ganin yana neman shiɗe musu dole akai gaggawar wucewa asibiti mafi kusa da shi, dan ya matuƙar birkice musu tamkar mai Asthma. An amshesu da gaggawa aka saka masa oxgyn kafin likita ya tsaya a kansa. Da ga ƙarshe dole akai masa allurar barci mai nauyin gaske dan doctor ya tabbatar da in har aka barsa ido biyu brain ɗinsa na gab da susucewa. Zuciyarsa kuwa bugunta ya wuce musali alamar yana cikin matsanancin tsoro ko tashin hankali.
Bayan likita ya tabbatar musu su kwantar da hankalinsu sun ɗan samu nutsuwa, sai a lokacin suka samu tattaunawa akan batun wannan tashin hankali haka. An yanke shawarar barin wasu anan asibitin, wasu kuma suka nufi gidan JJ ɗin domin bincika abinda ke faruwa.
Sun sami gidan kaca-kaca tamkar anyi yaƙi a cikinsa musamman ma falon. Dan komai an birkitashi da ga mazauninsa zuwa wani waje daban. Ba mamaki kawai ba harda birkicewar tunani ya samesu. Musamman ma Baba da yasan a jiya sune na ƙarshen barin gidan, kuma sun bar komai tsaff da shi tamkar an zana. Amma yanzu gaba ɗaya ya koma kamar ɗakin ajiye shara. Ruɗani na biyu shine rashin ganin Alimah da basuyi ba, hakan na nufin itama tabar gidanne kokuwa yaya ne?. Suna tsaka da dube-dube sukaji kamar ana kuka, da sauri Yaya Mujee ya nufi inda yake jiyo sautin kukan. Can bayan ɗakunan ne, fitowa sukai su duka zuwa inda kukan ke fitowa, tun daga nesa suka hangota a wani ɗan lungu takure.
“Subahanallahi! Alimah kece anan?”. Yaya Mujee ya faɗa har yanayi kamar zaici tuntuɓe sai da Yaya Inusa ya ruƙosa. Su duka inda take suka isa suna kiran sunanta, sai dai babu alamar zata ɗago. Kusan mintuna uku suna faman lallashi da lallaɓata amma taƙi tako motsa sai ƙarama ƙarfin kukanta take.
“To ko dai za’a kira iyayenta ne?”.
Cewar Baba yana kallon ƴaƴan nashi. Yaya Inusa ne ya amsa masa da, “To gaskiya kam Baba hakan zaifi nake ga. Dan al’amarin naga ba ƙarami bane ba”.
Waya Baba ya zaro da shirin kiran mahaifin Alimah, tamkar wadda aka zabura sai gata tai wani irin ɗagowa gashinta dake wargaje yayi bulahh fuskarta ta bayyana. A kusan tare Baba, Yaya Mujee, yaya Inusa suka zabura jikunansu na rawa. Dariya ta kwashe da shi tare da miƙewa tsaye gaba ɗayanta. Ai kafin ma kace takk ƙafa mi naci ban baki ba. Tuni tsakanin Baba da su Yaya Mujee an fara gudun wuce sa’a. Kowa burinsa ya kai ga ƙofa. Babu mai tunawa da girman na gaba da shi ko ƙanƙanta. Faɗuwar Baba biyu kafin suje gate, amma babu wanda yako waigo domin taimakonsa tsakanin Mujee da Inusa. Sai shi ke taƙarƙarawa ya tashi har dai ALLAH ya taimakesu suke fice.
Tofa, ƴan anguwa da dama ke’a ɗari-ɗari tun daga fitowar JJ yanzu fa sun sake tabbatar da babu lafiya. Tuni aka fara ƴar rere ƴaƴa da mata kasancewar mazan duk sun fice wajen nema. Ga shi sabuwar anguwa ce dama. Bakajin komai sai ihun mata da kukan yara. Ga shi su Baba sunƙi tsayawa, dan suma kansu sun rarrabu kowa yayi titi. Duk wanda kuma ya samu abin hawa baya neman ɗan uwansa yake afkawa kawai……….✍️
_To gaskiya akwai matsala. Uncle JJ anya kuwa ba sarauniyar aljanu ka kwaso mana ba a family _.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu _*
No comments