TUMFAFIYA 40
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/21, 6:28 AM] +234 803 800 7509: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH
,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
4️⃣0️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,
Washegari an kare buki a zatona su gwaggo zasu kara kwana
garin don naji suna fadin suna son shiga kasuwa su danyi sayayya don haka
al,adan mata yake idan anje wuri buki bayan an hada buki zasu dan shiga kasuwa
su yawata su sai abubuwan amdanin mata a garin.
Amma ina shiga don
gaidasu da kwana sai na samu suna hada kayan su wai zasu koma gida a ranan cikin
mamaki nake fadin gwaggo ba kunce kuna son shiga kasuwa ba ?
Bar wanan zancen
bari dai mu tafi gida asirin mu rufe gwaggo shafa ta fada do munfi dasawa da ita dama ban daddaraba na
sake fadin kasuwa fa kun fasa zuwane
gwaggo ?
Maganan kasuwa akai
tunda abu ya zama kamar kora mun hwada mata cewa gobene zamu komawa gida amma
matan nan tace a,a mu tafi yau don a rage tunda an gama buki.
Duk da nayi masu
gwai da hakan ya faru dama ance inda kwadai da wullakanci ai su suna ganin
wurin cine sun kwaso jiki zuwa mata karan buki ga irin abinda tayi masu nasan
ma wani maganan basu fadi a gabanane.
To nima ko yau zan
tafi zan biku mu koma gida bari naje na hada kayana na fada ina juyawa sai naji
gwaggo Ai tace ke mukan baki bin mu a dauka mun kitsa maki wani zancena kuma ?
Ki dai jirasu ranan
da sunka gama sai ku taho tare awo don walle cewa za ayi wani shirine kuma
munka hada ki bimu dauri ki taho da shirin haka kega ba wanda zaiyi zaton wani
abuna yanzu matar baffa ta fada.
Waka zaton wani
abuna tunda tace gida zata yau itama mi da baku barin ta tahiyata gida tunda
ankare bukin ga gwaggo shafa ta fada a hasale.
A,a shafa walle
hakan na iya jawo wani tsegumi kuma wadda naga kan matan ga na rawa tana iya
kiran office ta kulla muna sheri kesan shiko namijina ba tsayawa bincika zaiyi
ba yahaye.
To ya hau din mana
ni dai in tace gida zatana walle ban hanata tunda ta tashi mi da baku son
gaskiyana wai wanga buki hwa an kareshi mi zata tsayayi nanan ga ?
Shafa an ba hakana
bane in munyi hakan bamu kyauta ba gaskiya tunda dai ba tare da ita munka taho
ba shigowan mommy dake magana sama sama yasa sukai shiru a lokacin.
Tana gaba wata mace
na bayanta dauke da bukitan robobi na bukin ta shigo tana fadin kinga Ai ga
kayan bukin ku nan takai zaune ta fara masu bayani.
Suka don kitihi sai
godiya suke mata suna yabawa banda gwaggo shafa data fake da shirin kayanta a
lokacin saida taji mommy din ta gama lissafi bata amci su mama ba da ummah ta
dago tana fadin.
Ina na kishiyotin
ki sai tayi wani kwalkwal da idanu tace ai basuzo min buki ba kinga ke nan ko
ban basu ba banyi laifi ba ko ?
A,a wagga maganan
ba gaskiya bana yadda kinka bada na kowa haka zaki bayar akai masu nasu din
basu taho ba mugashi mun taho ba har ita hjy salma da yarta ttataho ?
Gara ita ina iya
badawa akai mata din hjy salma bata taba nuna min komai ba koda kuwa tana dani
a zuciyar ta wani kallo nayiwa mommy din dayasa ta farga da sakin layin da take
shirin yi a lokacin.
Yarki hwa bin mu
zatayi tace gwaggo Ai ta fada wace zahra wai mommy din ta fada ita hwa shina
muka magana kinka shigo ai.
Munkace ai ba tare
munkazo da ita ba ta bari dauri ta biku in kun tashi zaifi sauki tunda tahiyan
mu ba gudana ba.
Ina ma motar zai
isheku da ita ina ku biyar ne a ina zata zauna din sai naji gwaggo shafa tace
matsa mata zamuyi har nawa salma take da bai daukan mu.
Kai shafa na gaya
maki ki barta a nan tunda nan munka taho munka sameta balle ba inda zata tafi
gaskiyane bata so shine nayi mata fada take wanan fushin.
Wai ki duba dan
gidan Tahir manir mai kudin gaske a garin nan shi yazo yace yana son zahra amma
yarinyar nan taki bashi hankalin ta tafi ganewa tsamayen samarin ta na zamfara
dake hure mata kunne.
Wallahi haram koh
hwada maki Zahra na kula samari yayi karya yarinyar da kullun tana gida kulle
kamar macen aure har fadan haka mukeyi ko buki ake a cikin dangi baki ganin
Zahra.
Eh kwarai inda
wanan kan zahra haka take kamar me tsoron mutane bata fa zuwa ko ina ita gwaggo
Ai ta fada nidai ina jinsu.
Wai kuna wanan
maganan kamar baku san dan yau ba kuna ina da take kula wani fakirin yaro a
gusau saida Alh tayi mata iyaka dashi don Allah kuyi shiru don ku baku san
komai ba.
Wani irin malolon
bakin ciki na hade a makogorona don
ganin irin sherin da mommy ke kokarin azamin don haka bansan lokacin da nace
Allah shine shadata kan kazafin da ake kokarin dora min wanda banji bangani ba.
Zahra ashe haka
kike sululun boni cuta zalla nice zan maki kazafin ko wa abinda na sani shina
fada yanzu yaro kuma in bakya son shi shike nan gari da yawa maye bayacin kansa
ai .
A,a kada ki dakata
tata ai don ita har yanzu yarinya ce yo ke kuwa ana son ki da arzikine ai yan
mata nawa ke zaman jiranshi koke albarkacin hjy dake tare da uwarshine ai.
Wanan matar da suka
shigo tare da mommy don dakin ta dauko abin bukin data kawowa su gwaggo ke
wanan maganan .
In bataso ai sai a
barta din wani bai auren matar wani haka wata bata haihuwan dan wani sai da
busurun ta gwaggo shafa ta fada sai naga mommy din ta mike tanacewa wanan matar
su tafi ta sallami mutanen Abuja.
Ni walle ban
yarda da wanga cin fuska a,a za,a tura yarinya wurin maza kamar maamah aka
hwadama haka har yaushe maamah takena ?
To gaskiyan Allah
bamu zuwa da ita gida don in munyi hakan kamar mun nunawa hjy karima wani abune
gwaggo Ai ke fadi ke mama hakuri zakiyi har randa kunka koma abuja kega daga
can sai ki dawo gida.
Don ko yaya fada
zaiyi in yajiya mun taho dake gida kesan mazan ga wadda suke in suna borin aure
gaba daya lissahinsu karewa yakai.
Tsayawan ki da kun
koma Abuja ki tahowanki gida ni dama kada mu barki anan ta canza maki huska
nakawa don yanzu tsoro matan ga ka bani mace ko yan uwanta basu mata shedan
kwarai ai kega akwai matsala.
Ina kallo suka
tafi tunda na juya na koma cikin gida ban sake fitowa ba ina kuryan dakin hjyn
su mommy din har bayan la,asar saidai in tashi inyi sallah in koma in kwanta.
Mahaifiyar maryam
ce ta shigo dakin jin muryan ta da nayi na mike ina gaida ita don dan zaman mu
dasu na fahinci muryan matar.
Ta gama daukan
abinda zata dauka a cikin kayan su ta juya zata fita sai kuma ta juyo gareni
tana fadin waiko kinci abinci zahra ?
Tun dazun idan na
shigo kwance nake samun ki daga falon tsohuwar tace yanzu nake zancen yar nan a
raina ashe kema kin kula da hakan.
Bana cin abincin ne
na fada haba dai yata tashi kici koda kadan ne ko kisha tea ga kayan tea nan ai
kinsan inda maryam ta ajesu dacewa yarta da muke tare.
Idan zansha zan
diba mama nagode na fada ba komai keko ai an zama daya yanzun kuma nadai kulane
cewa duk na shigo dakin nan tun safe kina nan kwance su maryam kuma suna can
gidan da uwayen su basu dawo ba.
Bansan irin karima
ba bata da lokacin kula yarinyar nan yaya zakazo da mutum gari ka dinga
barinshi shi kadai ai dole yarinya ta shiga damuwa.
Hjy ai kinsan halin
karima wurin hutsanci tun jiya nake jin tana complain kan yarinyar nan abu ne
ba daman kayi magana yanzu ta hauka da sababi kuma.
Azuciyana nace
Abba ashe ya kwaso muna bakar ashanace kona gari kowa bai maganan dadi a kanta
wanan wata irin mace ce wai na tambayi kaina ?
Jikin nasa ya
danyi dama sosai zuwa safe hakan yasa ya fito har jam,in asuba ya samu yaje
saidai bai dade ba ya dawo dakin shi ya shiga yana karatun kur,ani ko zai rage
jin abinda yake ji a lokacin.
Suratul Yusuf yake
karantawa a lokacin a cikin daga murya har wa yanda ke gidan suna iya jiwoshi
kadan kadan daga inda tsohon nan yake ya kada kanshi yai murmushi jin yadda
yaron matashin yake karatun nasa.
Bayan shattu ta
gama abin karyawa ta hada ta kai mashi har dakin yayi mata godiya ta fito ya
tashi zaici ko malam musa ya tambayeta yana kallonta yaji amsan da za ta bashi.
Eh to yana dai
zaune yana tulawa nadai aje masa na fito saidai naga kamar yaji sauki sosai yau
din ta bashi amsa.
Sai zuwa karfe tara na safe rana ya haska ko
ina ya fito daga dakin inda ya samu malam musa a zaune a dan rumfarshi yana
rubutu a allon shi da bakin tawadiya.
Sannu da hutawa
Ahmed din ya fada lokacin daya kawo kusa da dan rumfar malam musa din ya dago
kai yana fadin yarona anfito ya karfin jikin naka.
Da sauki baba
Alhamdullahi sai ya kai zaune malam musa din na fadin masha Allahu na dauka yau
zakaje asibiti amma tunda kaji sauki Alhamdullahi.
Ya jawo wani tasa
da ruwan tawada yasa shi baki ya tara wanke rubutun da yayi din ga mamakin
Ahmed sai yaga tsohon ya miko mashi ruwan rubutun yana fadin yi bissimillah ka
kurbe wanan tsarine da kariya daga ko wani irin abin tsoro ga bawa.
Baiyi mussu ba ya
karba ya kafa kai ya kwankwade ya daureye tasa
ya kube ya aje a gefen malam musa din sai dan shiru ya biyo baya kafin
can Ahmed din yace baba dama naso fadama ranan laraba insha Allahu zan koma
gida.
Cikin bazata da
tarin mamaki a fuskanshi malam musa din ya dago kai ya kalli bakon saurayin
nasa yana fadin yarona wani abu akai ma
da bai maka dadi ba ko yanayin muhalin namune bai maka ba ?
Kai Ahmed din ya
kada yana kokarin kakaro murmushi a fuskanshi kafin ya iya fadin wallahi ko
daya baba baku min komai banda Allah ya saka da alheri banda abinda zance a
kanku yanzu kuma.
In bashi ba yaushe
zaka kawo maganan gida yanzu kai da ka baro wuri mai nisa kazo nan neman
magaifin ka ana tsaka da nema kuma kace kai ka tashi gida zaka.
Komawa gidan a
yanzu ai baida amfani a gareka ba tare da kasan waye mahaifinka ba har in kana
ganin cewa neman da muke masa bai maka bane sai mukai cigiya gurin magabata
dama haka shine tsarina na gaba.
A,a baba ba sai
kaje ba don na gano mahaifina da kaina wanan fitan da mukayi da dan bayaro jiya
kuma har nayi magana dashi a jiyan don hakane nake sin komawa gidan ma.
Tsaye Shattu take
tana sauraren su tun soma maganan su da taji malam din na fadin ko sun mashi ba
daidai bane a nan din yasata dan tsarguwa.
Sai kuma taji
saurayin na fadin ai ya samu ganin mahaifinshi ya gano ko waye shi din haka a
cikin ruwan sanyi anya ba dai fadi yayi ba don ya kwantar masu da hankalinsu
kada su zargi komai ga tafiyan shi ?
Dana kace ka sadu
da mahaifinka a garin nan yace kwarai baba don hakanema nake son komaw gida
yanzu don na fahinci yabarni da gangan bawai wani matsala aka samu ba.
Azoto da talauci ko
rashin lafiya ko rashin zarahi yasa ya kasa waiwayana amma yanzun na fahinci
cewa hakan ra,ayinshine kawai ya wofintar dani haka cikin duniya.
Subbahanallahi duk
meyasa kake wanan tunanen ko zato akan abinda baka tabbatar dashi ba gareshi
kada ka manta cewa koma yaya yake shine dai mahaifin ka daya kawo ka duniya.
Wani malolon bakin
ciki Ahmed din ya hade kafin yace duk nasan da hakan baba nasan kuma abinda
yasa nace haka baba.
Don baya cikin
yanayin rashi ko damuwa saima falalan da ko irin mu goma ya watsar zai iya
neman mu cikin duniyan nan.
Amma babu tunanena
a zuciyan shi yadda naga rayuwan shi na tafiya ya samu wasu diyan yanzu ya
manta da zancena ga baki daya.
Murmushi malam musa
din ya sauke a fuskan shi kafin yace kana ganin haka daine baka san meke
zuciyarshi ba game dakai ai don haka karka yanke hukunci akan abinda baka sani
ba ko kayi zato.
Waima waye
mahaifin naka dake masa wanan hukuncin hakane don har yanzu ban fahinci inda
zancen ka ya dosa ba ta yaya kayi ka ganoshi kuma ina ka ganshi har kasan shine
din .
Zuwan da wata mace
tayi gidan suka tsaya gaisawa da malam din yasa Ahmed din tashi ya bar dattijon
a wurin ba tare da dattijon ya farga da hakan ba .
Dakinshi ya shiga
ya soma hada kayan shi a cikin fushi da bacin rai ya mike ya dago sai kuma ya fita waje ya rasa me zaiyi a
lokacin don haka ya nufi inda garken gidan yake yaja ya tsaya yana kallon su.
Idon shi ya sauka
kan akuyan nan me zubin uwar garke sai yaga kamar akuyan na hawaye lokacin dan
kara kura mata ido yayi sisai.
Tabbas hawayen
takeyi ba karya idonshi yai mashi ba hawayen take sakewa a idonta to hawayen
meye ya tabayi kanshi tare da nufar inda take kiwo din.
Yana zuwa kusa da ita tayo kanshi tana
zagayenshi tana dan tuma kafin ta wani ja baya ta dawo ta kwanta a gaban shi
tana cigaba da tuka tare da dan rufe idanunta.
Tsugunawa ya samu
kanshi a gabata yayi yakai hannunshi saman bayanta yana dan shafata a hankali
yana fadin .
Allah kadai yasan
dalilin hakan a garemu nasan akwai wani sirin dake boye ga hakan koma maye
ubangiji Allah ya mayar muna dashi alheri a tsakanin mu.,
Haka yai ta shafan
akuya yana jin wani iri a
zuciyarshi wanda shi kadai zai iya
fassara irin abinda yake ji a rayuwan shi lokacin sai can ya kalli akuyan yace.
Uwargarke kokece ko
bake bace in Allah ya kaimu gobe in sha Allahu zan koma gida sai kuma in Allah
ya sadamu da alheri sa ke nan.
No comments