TUMFAFIYA 38
Ayi hakkuri da wanan din busy nake kwana biyun nan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[2/18, 10:38 AM] +234 816 362 6370: 🌱TUMFAFIYA UWAR
KWANKWANMAI ,,,,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA BAKI FITA A WURIN BANZA ,,,,,,,
🌱TUMFAFIYA SIRIN KI SAI ALLAH
,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
3️⃣8️⃣
ONLINE PAID NOVEL YARUWA KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA
DARI BIYAR NE DON KIRA 08036959257 KO BIYA KI AIKA 2254380105 ZAINAB IDRIS
MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN WAYA MUN GODE UBANGIJI YA BAKI IKON BIYA
AMIN,,,,,,,
Zaune suke shida malam musa a rumfar shan iska yayin da
Shattu ke daga can gefe daya tana aikin tsuntar shimkafa a cikin tire ta mayar
da hankalinta ga abinda takeyi din a lokacin.
Magana dattijon
keyi saidai yaron bai motsa ba a lokacin ma,ana zuciyan shi nawani tunane a
lokacin bai tare da dattijon a zahiri.
Ikon Allah yarona tunane kakeyi haka kai nisa
har bakaji me nake fadi ba yana dan buga alkalamin dake hannun shi saman allo
iccen da yake rubutu.
Hakan ya dawo dashi
daga tunanen yana sauke ajiyan zuciya lokaci guda dattijon yake fadin kada ka
halaka kanka da tunane dana insha Allah zaka sadu da mahaifinka da yardan
ubangiji.
Zama ya gyara ya
dan murmusa a fuskanshi yana sam baba ba wanan nake tunane ba a halin yanzu
kakata dana bari a gida cikin damuwa don da sunan kwana daya.
Yanzun gashi ina batun
shiga sati na biyu ban koma gida ba zuwa yanzu nasan tana can ta shiga damuwa
don zata dauka cewa na mutu ko nayi hatsari ko kuma ansaceni ne abu dai
makamancin hakan yasameni ne a tafiyana.
Nayi hakan ne kuma
don nasan idan na fadi inda zanzo ba zasu taba barina nazo nan din ba ni kadai
haka.
Haka zalika babu
ranan da zasu kawoni gareshi har yasan ina raye ni bukatana a wurin mahaifina
shine yasan ina raye a duniya ya dauke kamar ko wani da a gareshi koda bai bani
komai nasa ba.
A rayuwana a hakan
na fara fuskantar kalubulanta a wajen mutane don har wasu na tantama a kaina
yanzu haka din wanan ne dalilun fitowana daga gida nazo nan neman mahaifin
nawa.
Gaskiyane don ko
baka fada ba nasan za a zo wanan wurin zuwa gaba don duk lokacin daka daukowa
kanka zancen aure ko wani mukami wanan zance shi makiya zasu rike a makami
gareka.
Dukko da sunsan
cewa kai din ba shege bane amma haka bai hana a jefaka da wanan kalman mai zafi
a zuciyar ka.
Sai dai barin gida
da kayi ba tare da fadawa kowa inda zakaba a wana zamanin gaskiya kayi kuskure sosai a nan don
hankalinsu zaiyi matukar tashi ga rashin sanin inda ka shiga yanzu.
Don haka kayi
kokarin kira ka sanar masu cewa kana nan kuma ga abinda kazo yi a nan din kadai
riga da kazo din duk mai wani korafi kan hakan yanzu ka shiga gaban shi kuma.
Ahmed din yace baba
nagode insha Allahu zanyi yarda kace min din nayi zan kira in sheda masu ga
inda na tafi su kwantar da hankalinsu a kaina.
Gaskiyane kayi
kokarin yin hakan idan ka samu daman hakan kuma gaskiya suyi kokari wajen baka
tarbiya irin haka mai amfani a gareka nan gaba zakayi alfahari da hakan in sha
Allahu.
Nayi mamakin
yadda mommy ta bata rai ga rashin zuwana wurin dinner har bata iya boye min
bakin cikin hakan ba duk da har gwaggo shafa ta fada mata gaskiyane ban fitan
dare don ina da matsalan hakan idan na fita din.
Batayi magana ba
sai fuskan data canza min hakan bai dameni ba don ba haduwa mukeyi ba sai
lokaci lokaci don haka canza fuskan bai wani damuna ba.
Ranan da aka daura
auren kuma suka aza wani bidi,a wai wankin ango wanda ba kowane keyinsa ba sai
dai yan son bidi,a irinsu.
Za a hadu maza da
mata yaro da babba yan uwa da abokan arziki afito da ango da amaryan shi a
dinga zuba kudi ace ana neman wanan ko waccan tazo ta sayi bakin angon da sauran su.
Inda yan gidan amarya
suma zasuyi nasu bajinta su bada kudin ga ango daga mahaifan amarya din da
sauransu dai.
Wanan kan naje
wurin don karfe duhu akace za a fara amma basu fara ba sai karfe biyar aka aza
bidian wuri ya dauki cida da mutane.
Don muyiwa mommy
kara duk dana kula data raina da kuran gwaggonni din da matan ubanan namu
dasuka zo mata karan sai ta sharesu basu ganin ta sai nice zan fito na nema
masu abinci da ruwa ko wani lokaci .
Allah ya taimakeni
na samu wanan matar da tun farko na sayeta take min komai yanzun ma din itace
min tsaye da dawainiyar su gwaggo din don ita hjy karima batayi hikimar yin
hakan ba a ranta.
Mun fito munyi
barin kudi tare dasu maryam dasu gwaggo lokaci guda ba kunya saiga hjy karima
dama ta manta da zancen su gwaggo din tazo tana washe baki a wurin mu tana
fadin wai mun fitar da ita kunya sosai mun kara mata girma da kima a idon
mutane ai.
Ko ta manta da
maryam na wurin ne saidata wucene maryam ke fadin andaiyi hasara wallahi dafa
su mummy na take wanan zancen wai.
Yan uwanta ke nan
tayi adawa dasu inaga kishiyoyinta ina ganin daddy ku baisan auren ta biyar ba
dashine na shida kuma bata zama da kishiya duk inda taje sai ta watsa matan
gidan ta koma ita kadai karshe in mijin ya tsiyace ta gudu ta barshi bakunya ko
tsoron Allah.
Irin wanan halin ne
ke hadata fada da yan uwa don su basu son abinda takeyi din sai mama Rufaida da
tasu yazo daya ko ina suna tare dasu a manne.
Koke dazun ai naji
su maman mu na fadin wai zata fara nuna maki halinta don jiya taso kije wurin
dinner nan don tasan akwai diyan manya taci kasuwa dake ta hakan .
Sai kuma tayi
rashin sa,a bakije ba shine suke ta zaginki wai zatayi maganin ki ai sam mun
manta gwaggo shafa tana tare damu take wanan zuban haka .
Saiji mukayi tana
fadin dama ai daga ganin wanan matar da barikanci a idanunta ni wallahi kar
nake kallon ta in ma iya shegene ai gidan tazo don tsab maimuna zatayi maganin
ta.
Ke kuma nasan
zuwan dole kikayi shiyasa banji komai ba koda maimuna ke fadin wai munafunci
aka kulla da zuwanki wurinta hutu don ai mata bakin ciki ita da yaranta.
Ni kuma nasan
idonta hjy salmace ba zaki taba zuwa ko ina ba idan ba tare da ita ba wanan
zuwan ma nasan yayane ya saka kizo don tayi mai dadin baki.
Aifa da haka zata
sayeku kaf daga karshe sai duk kun raina kanku da ita don bata da kyau idan
halinta ya motsa kin ganta nan ni bakiga ko gaisuwa bamayi da ita ba .
Nidai shiru nayi
ina saurarenta sai gwaggo shafane ma ta biye mata take bata amsa a karshe wuri
na samu na zauna suma suka biyomu suka zauna din.
Muna nan zaune a
wurin saiga wata tazo wai nazo don Allah yayanta keson magana dani yi nayi
kamar badani take ba don hankalina yana gun wayana banko kallon bidirin da
akeyi a wurin.
Maryam ce ta dan taboni nadago kai take fada
min abinda budurwan tazo dashi dan murmushi nayi ina fadin ayyah don Allah ki
fada mai tare da iyayyena nake zaune ai.
To ki ban number
wayan ki saiya kiraki nace bana haka ni keko tashi mana kije kiji gwaggo sha ta
fadi Allah ya taimakeni budurwan bata jimu ba nace ba inda zani numban dai aka
bata ta tafi.
Ganin samari zasu
rakura min kuma ga magariba yayi yasa nace su tashi mu tafi maryam tace ina
zaku samu mota a nan.
Nace kada ku damu
zamu samu a daidata sai mu shiga hakan mukayi muka samu masu adaidaita muka
shiga sai zuwa gidan don da ankai unguwar zan gane kwanan gidansu.
Dan bayaro ne yayi
sallama kofan gidan malam musa yace ace anawa saurayin gidan nan bako sallama
yaron na shiga ya samesu a zaune tare malam musa ya fadi sakon dan bayaron .
Da fillanci saidai
ba wai irin filancin nan da kowa ya iya irinsa bane wanan zakace wani yare na
daban yakeyi ba filanci ba.
Shi malam musa din
yacewa yaron yaje yace yana zuwa bayan fitan yarone malam musan ke fadin kayi
hankali da yaran garin nan kasan mu fulani akwai mu da zuciya sosai.
Kasan yadda zaka
taka da kowa ka samu ka rabu lafiya dasu har ka bar garin nan kada ka yarda ka
jefa kanka cikin wani kungiya tasu nan din.
Nagode baba ya
fada yana mikewa ya saka takalman shi ya fice daga gidan tsaye ya samu dan
bayaro ya bada baya ya tokare hannun shi a jikin iccen mangoron dake kofan
gidan ya kuwa wani waje idanu yana kallo gami da tunane.
Kamar yadda addini
ya koyar ga musulmai suyiwa dan uwa sallama don falalan ladan dake cikin hakan
shima dai sallaman yayiwa saurayin jin hakan ya juyo yana karbawa.
Suka mikawa juna
hannu suka gaisa kadin dan bayaro ya fara bayani da fadin wallahi Allah ka
ganeni nazo maka a bazata so nake ka rakani cikin mambilla naje na sayo yadi ai
min irin dinkin nan naka kafin ka koma dan kayan yana matukar karban jikin ka
sosai.
Kowa a karkaran nan
yana maganan hakan kaidin ka iya kwalliya na birgewa sosai wallahi sai muje
tare ka tayani zabben yadi mu bada dinki daga nan ma sai mu dan yawata kaga
garin sosai.
Dan shirun mamaki
Ahmed din yayi kafin wata shawara tazo mai yace to dan bayaro barin koma ciki
in sanar da babana cewa zamu fita tare dakai idan ya yarda da hakan ai sai in
rakaka ba wani matsala bane hakan.
To amma fitan ma
sai baffan ka ya sani sai kace wani mace can yace haka na saba dashi tun a gida
bana zuwa wuri ba tare dana fadawa iyayyena don haka sukai min tarbiya.
Koda wurin mace zaka
dan bayaron ya tambayeshi cikin zollaya yana dan murmushi yace ai ban isa fara
zuwa wurin mace bani yanzu saidai nan gaba kila.
Daga haka ya juya
ya koma cikin gidan shi kuma dan bayaron ya bishi da kallon mamaki a fuskanshi
don shi yanzu zancen kara mata na biyu yakeyi sanan wanan din kato dashi yace
mai wai bai isa zuwa gun mace bama shi.
Sosai malam musa
din yayi mamaki amma sai ya kara yabawa da tarbiyan yaron da yayi dabaran fada
mai kafin ya bishi dan mutum yanzu ba abin yarda bane gara kasan komai a kan
wanda duk kake tare dashi a zamanin nan don boyon baya da amfani ga dan uwa
yanzu.
Allah ya tsare a
dawo lafiya dattijon yai mashi hakama Shattu dake madafa tana shirin dora masu
abincin rana tayi mai Allah ya tsare a dawo lafiya.
Ya fito ya samu
dan bayaron suka fice daga unguwar sai binsu ake da kallo don ganin danbayon
tare da bakon fuska da yanayin shigarshi ya nuna ba daga nahiyar su yake bashi.
Akwai dan tazara
da inda gidajen su yake da cikin gari don haka suna tafiya dan bayon yana masa
bayanin komai ba abinda tafi tsaya mai a rai kamar ganin wasu kabila da yayi a
cikinsu.
Gasu dai fulanine
su amma kuma ba musulmai ba nan dan bayaron yake mai bayanin cewa a cikin su
akwai musulmai da kafirai da masu zuwa coci.
Sun isa kasuwan
garin ba zaka kira garin da birni ba haka kuma ba zakace dashi kauye ba garine
mai abubuwan mamaki ga ni,iman ubangiji a wurin don ko tsaunukan dake zagaye da
garin lub suke da korayen ganyayaki.
Shanuko shi zai
iya fadin a nan asalin shanun duniya suka fito ga farare ga jajaye ga masu fari
da baki ko wani kuma zaka gani garkene tafe sai inda idon ka ya tsayama da
kallo.
Basu sha wuya ba
samun yadin dan bambamcin kudin yadin kadan ne suka yanka mai yadin ne yayi
masu kwatancen tellan da zasu kaiwa dinki yaimasu irin wanda sukeso din yayi
kyau .
Don haka dan
bayaron yabi dasu inda zasu kai ga tellan da akai masu kwatance din wuri ne mai
kyau da aka gyara ga telolinan a shaguna zazaune suna aikinsu.
Ya fadi sunan
wanda suke nema din aka nuna masu shi suka karasa shagon nasa tun kan su isa
danbayo ya fara fadin aradu wajen nan sai sunci kudin dinki sosai kai malam da
ganin yadda aka gyara shagon nan kasan sai wanda ya isane ke kawo dinki wurin
nan.
Sallama sukayi
shagon suna tambayan Isa tella aka nuna masu shi ya juyo yana fadin wake nema
na idon shi ya sauka a kan masu neman nasa sai ya sake murmushi yana fadin.
Ah a a malam Yasir
saukan yaushe haka kasan banda labari nazo amsan tsarabata kaga ko shekarab
jiya mun hadu da mummuni amma bai fada min ka dawo ba.
Sam shi Ahmed din
bai san dashi ake zancen ba sai da ya dan waiga yaga dai shi matashin tellan ke
kallo a lokacin .
Hannu ya mika masu
suka gaisa a nan ya dan kallesu tsab ya gane cewa ba wanda yake zato bane ashe
a cikin yaresu na mambilla yake fadin wallahi nayi zaton Yasir ne dan gidan Alh
dan gaske.
A,a wanan kan
bakone shi daga wajajen sokoto yake dan bayaro ya bashi amsa yace ikon Allah
malam wallahi kana da kama da yaran gidan dan gaske sosai don har kamar ya
baci.
Tellan ya fada da
hausa danshi da gani ya dan taba barin gari yasan ta kan duniya sosai a, a
bashi bana Ahmed din ya fada ya fara
yiwa tellan bayanin abinda ya kawosu din yace ya gane a wurin cinikin dinkin ne
dan bayaron ya tsure don jin kudin da tellan ya tsaga mashi ya bayar.
Kaiko dai ina
laifin kace muna dari biyar shikanshi Ahmed dinn murmushi yayi don jin abinda
abokin tafiyanshi din ya fada a lokacin.
Jin yadda dan
bayaron keson badasu yasa yace kai mune dubu da dari biyu yasa hannu ya ciro
kudi yabawa tellan yace yaushe zamuzo mu karba.
Ikon Allah halin ma
iri dayane wallahi tellan ya fada koshi yasir baya son dogon jayayya sosai haka
yake min idan yazo ya samu muna ciniki da wani a nan.
Murmushi kawai
yayi ya kara fadin yaushe zamu zo karba tellan ya dan tsaya yana tunane kafin
yace kuzo ranan jumma,a da karfe hudu in sha Allahu zaku samu na hada don ma
kaidin ne don da sai bayan sati biyu kuzo ku karba din.
Sukayi sallama
dashi yana jin suna maganan shi a shagon ta kamarsu da wancan da suka kira da
yasir yasa kai ya tafi yana jin wani abu a zuciyar shi game da hakan.
Sayayya dan
bayaron ya danyi shi kuma bread da kayan tea ya sayo masu sai kayan miya daya
rikowa shattu masu yawan gaske.
Har sun kamo hanya
sai dan bayoron yake fadin barin bi dakai ta cikin gari don kaga garin mu da
kyau kasan garin mu ba kauye bane Allah ya albarkaci garin nan da arziki mai
yawa sosai ga kiwo ga noma da mutanen mu keyi duk da bamu da wajen noma sosai
amma haka mutanen wanan yankin namu ke kokari.
Madaran shannu daga
ko ina har kasan waje ana zuwa a dauka nan
suna tafiya dashi kasashe da dama shiyasa mu nan da kiwo muka dagora
sosai a nan.
Kaga ikon Allah
ashe rabo ke kiran mu ga dangaske gari ko bamu samu komai ba masha kallo a
gidan nasa ai kaga inda daulan duniya ta yanke saka a nan.
Shi din mai kudine
sosai suke kuma da sauratan garin nan a yadda naji ana fada a gari cewa kaf
karkaran nan daga chedi wuro garba chedi gembo duk babu wanda yai arzikin shi a
kasan nan.
Baffa na ban
tarihin shi cewa a baya an turashi cikin duniya saida aka tashi tsaya rana
tsaka sai gashi ya dawo gida kwantsam ba zato ba tsamanin hakan .
Acewar mutane shidin
ya gaji arziki ta uwa ta uba duk ko wani bangare nasa suna da manyan garakan
shanu a nahiyar nan .
Yanzun ko ya hada da
ilimin zamani sai abin nasa ya kara bunkasa sosai don yanzun ma a Abuja yake da
zama saidai yana yawan zuwa gida sosai idan yazo kuma yanawa mutane alheri
sosai shiyasa kaga mutane suna ta tururuwa a gidan shi yanzu.
Lalaima wanan
mutumin ya riku a kasa yadda danbayarin nan yake fadin dukiyan shi in dai ba
abin fulani ba ace dukiya a daji suke aida yanzu sunan shi ya karba kasa ke nan
.
Amma ba a gane
hakan garesu don dukiyan a dawa suke sai wanda ya ganewa idon shi zai gano
hakan su dai a kirga yawan shanun mutum daya tara ace wani yana da Nagge dari
kaza ko wani ya tara nagge kaza shine alfaharinsu ba yawan kudin bane ya damesu
.
Shiyasa hukuma
sarakuna ko yan doka suke son yin sharia da bafalatin daji da mafi yawan
yaransu na yanzu ke dauko masu magana zakaga sai an ware wasu garke an sayar
kafin sharia ya mutu.
Wanda sam ba a san
bafilatanin da da daukan magana ba haka don ko yaushe su a daji aka sansu da
zama sai lalura ke kawosu cikingari a da can baya
Haka yan asibiti
sunfi son bafilatanin daji ya kawo masu mara lafiya yanzu ne koda flagyl zasu
bashi zasuce dashi dubu goma bajin zafin hakan zai fidda ya bayarne.
Fulani akwai arziki
a garesu sosai saidai abin sirine a gareau ba kowa ke gane hakan ba garesu.
No comments