TAYI MIN KANKANTA 6

 *Zahra Surbajo*





*6*



"ƴarfillo!!!!!!!!!"ya ambata da ƙarfi sanda ya farka a gadon asibiti yana laluben ta,faɗowa yayi daga kan gadon yana ihun kiran sunan ta.


Da sauri sojojin dake kula dasu suka zo suka riƙeshi,dambe yake iya ƙarfinshi yana kiranta,"ƴarfillo kina ina,ki zo nan kusa dani,kar kimin nisa,don Allah kiyi magana injiki,kitaimakeni kiyi magana mana,nace kiyi haƙuri,ko baki yarda dani bane,nace zan kula dake,zan ɗaga darajarki fiye da ta kowacce mace me gata"sambatun da Hammad yake kenan sanda ya farka a asibiti.allurar bacci aka masa ko zaa samu sauƙin sambatun.


A can sansanin Æ´an gudun hijira ko masu kawo sadakar abincine suka zo dan haka kowa da gudu yaje ya hau layi,banda Zahra wacce cinyoyinta ke mata mugun ciwo,zaune take ta kife kanta akan guiwowinta tana kuka,


Haka aka gama rabon abincin ita bata samuba,se hanne ce ta sammata nata.shima daƙyar ta iya ci sabida bakinta ɗaci yake mata.


Haka suka kwashe tsawon kwanaki uku,Zahra zuwa lokacin bata iya ko tafiya sede rarrafe,ga wani ruwa data rasa ko na menene dake bin cinyoyinta.tayi kukan tayi kukan har ta gaji.gashi ba suturar arziÆ™i ke garesu ba haka take zaune Æ™uda na bin ta.hanne  kanta yanzu ta gujeta sabida warin da zahran take.


Duk sanda zaa kawo abinci zahra bata samu sabida ƙyamarta da akeyi,hakan ne yasa take fita daga sansanin da rarrafen taje,bakin titi tayi bara dan ta samo abinda zata ci.cikin ikon Allah kuma tana samowar seta koma gefe taci ta ɓoye sauran.


Acikin sati biyu duk wanda yaga Batulun inna bazece ita bace,gaba É—aya ta sauya,tazama abar tausayi.


Acan kaduna ko,lamarin na hammad ba sauƙi,dan gaba ɗaya kwakwalwarsa tasamu matsala,a birkice yake,arana seya kira ƴarfillo yafi so dubu,kuma yana dukan duk wanda yazo kusa dashi.


Hakanne yasa aka nemo iyayenshi sukazo aka basu shi domin suje su nema masa lafiya.


Allah sarki,a É—aÉ—É—aure aka sashi a mota sabida dukan da yakeyi,shima seda aka masa allurar bacci sannan akai nasarar fita dashi.


Alhaji Nasir Abubakar shine mahaifin Hammad,me hamshaƙin me kuɗine,wanda sunanshi ya kewaye ko ina a ƙasar nan harma da ƙasashen ƙetare.ƴaƴanshi biyu Hammad da Surayya,se matarsa hajiya maryam,dukansu asalinsu ƴan gombe ne.



Alhaji ba abinda yakeso a duniya sama da ɗansa Hammad,duk wani buri nasa na duniya akan Hammad ya ɗorashi,lokacin daya ga halin da ɗan nasa yashiga kuka yake da idonsa kamar ƙaramin yaro.dan shi dama a dole yabar Hammad ya shiga aykin soja,dan kawai ya nuna yana sone.


 Hammad matashine É—an kimanin shekara 30 da haihuwa,bayan kammala karatunsa na secondry,mahaifinshi  oxford university ya tura shi inda ya karanci gynocology,wato likitan mata,inda yasamu sakamako me kyau bayan kammala karatun.

Lokacin daya dawo gida nigeria,seya samu ƙasar na cikin yanayi na fama da rashin tsaro,ana kashe mitane basuji ba basu gani ba,wannan dalili ne yasa Hammad da Amininsa jameel suka faɗa aykin soja,wanda mahaifin hammad yasaki ƴan mazan kuɗi aka basu manyan muƙamai,bayan sun samu horo na musamman asansanin sojoji dake NDA kaduna. sunason taimakawa ƙasarsu da dukkan ƙarfinsu.



Wannan kenan.


Muje zuwa


No comments