TAYI MIN KANKANTA 15

 



*Marasa lafiyanmu Allah kabasu lafiya,masu ciki Allah ka saukesu lafiya,Allah kazaunar da kowa agidan auranta lafiya,Ameen*


*15*



Da asuba,da kanshi ya tasheta yabata jallabiyarsa tasa tayi rolling da rawaninsa tayi sallah,sannan ta koma bacci bayan ta cire masa rigar tasa,


Bata farka ba se tara na safe,tuni hammad yayi wankansa ya kimtsa,jin motsin da yayine yasa yazo ya sameta a zaune ta farka,rigarta take ƙoƙarin sawa amma zafin da gun ƴunar jiya ke mata yasa ta kasa sawa sabida rigar bata kai jallabiyar daya bata faɗi ba.


Da sauri ya ƙaraso gurinta,ɗago ido tayi ta kalleshi sannan ta sunkuyar da kai,


Zama yayi kusa da ita har jikinsu na gogar juna,waigowa tayi asanyaye ta kalleshi shima ita yake kallo,hannu yasa ya zagayota dashi ya kamo rigar yasa mata,sunkuyar da kai tayi ta runtse ido sabida zafin da taji,a hankali yace"sorry,"gyaɗa kai tayi sannan ta miƙe,ta fice daga ɗakin,yabi bayanta da kallo,yana haɗiye wani miyau.


Se da ta fice ne kuma kunyar ta faɗo mata,to tacewa mummy agurin wa ta kwana,kasa ƙarasawa cikin falon tayi ta tsaya tana wasi-wasi.


Hammad ne ya fito zashi gaida iyayen nasa,anan yaci karo da ita tsaye tana tunani,ƙarasowa yayi inda take,yace"ke lafiyarki ƙalau kuwa,tsayuwar me kikeyi anan?"

A raunane ta É—ago idonta ta dibeshi tana hawaye tace"kunya nakeji suji na kwana agurinka"


Murmushi yayi sannan yace "sabida kin kwana da kwarto ko?"


Da sauri ta girgiza kanta tana faÉ—in "Allah ya tsaremin miji da zama kwarto,ni mijina ba kwarto bane,aniyarka ta bika"sam ita ta mance ma matsayinsa agunta take wannan batun.


Be kulata ba hannu yasa yaja hannunta suka nufi falon,itako tirjewa take tana kuka tana "wallahi bazaa ganmu atare ba,nide kasakeni ka tafi kai kaÉ—ai"a haka suka shigo falon,inda mutanen gidan ke zaune a dinning  suna karyawa,É“urarin da zahra kewa Hammad É—inne ya dawo da hankalinsu kansu,

Shiko Hammad be saketa ba seda suka shigo falon,ay tana ganinta gaban su mummy,da sauri ta É“oye abayanshi,duk yadda Hammad ya kauce itama da gudu zata koma gurin,sosai abun yaba su daddy dariya,a hankali daddy yace "rakata É—aki mana muhammad,ka tsaida ita anan"


Murmushi yayi sannan yaja hannunta zuwa É—akin nasu se É“oyewa take agefensa.


Seda ya kaita sannan ya dawo gun mahaifan nasa,tsugunawa yayi ya gaishesu sannan yaja kujera ya zauna,


"Angama shirya komai na gidan da zaku zauna,anjima mummynka zasu kaita gidan,ka kwantar da hankalinka"daddy ya faÉ—i yana murmushi.


Sosai kunya ta kama Hammad,ya sosa ƙeya yana murmushi yace"daddy ay ko anan ɗinma zamu iya zama"


"kuci gaba da mana rashin kunya a cikin gida ko?"daddy ya buƙata.


Shuru Muhammad yayi  dan se yanzu yagano ma manufar daddyn.


Haka yayi break fast duk a tsarge,yana gamawa ya miƙe ya bar falon.


Shiryawa yayi ya fice zuwa gun amininsa Jameel,kasancewar yana hutu be koma bakin aykiba.


Surayya ce tasamu zahra a ɗaki tayi wanka ta kimtsa cikin wata atamfa ja da milk me golden tayi kyau matuƙa.

Tana shiga ta fara mata tsiya,"kaga amaryar yaya,me bin angonta É—aki"duka zahra takai mata tana faÉ—in"zanko haÉ—aki dashi,bari muhaÉ—u"


"ayya yarinya kwantar da hankalinki yau zaa kaiki gidanshi seku dena satar hanya"ta ƙarasa maganar tana tuntsira dariya,


Zahra de ba baka se kunne,seda su mummy sika bar falon sannan taje tayi breakfast É—inta.


Da magriba su mummy da ƙawayenta guda biyu suka kai zahra gidan auranta daya gaji da haɗuwa,se kuka take wurjanjan ita bazata zauna ba,


Surayya aka baro agurinta azuwan in Hammad yazo yasa direba yakawota gida.


Hammad ko suna can shida jameel yana ƙara kwantar mai da hankali,akan auran nasa da zahra,tare da bashi tabbacin insha Allahu zasi ga ƴarfillonsa,


Sai da ishai daddy ya kirashi awaya ya shaida masa tun É—azu ankai masa matarsa gida.


Jameel ne yasa shi yayi wanka ya kimtsa awata sabuwar shadda ta jameel ɗin,sannan,suka fito domin yamasa rakiya,kaji da madara suka siya sannan suka ƙaraso gidan.

Jameel besan me yasa ba amma lokaci zuwa lokaci gabansa na yawan faɗuwa,a haka suka ƙaraso gidan.


Muje zuwa


No comments