Tabarmar Kashi book 2 page 71

 "HUGUMA*



_TABARMAR KASHI*




Book 02 Page 71


Tare suka shirya shi da ita, ta saka doguwar rigar abaya wanda yanzun sune suturarta saboda girman cikinta,shi kuma ya Sanya kaftan abaya sassauga suka fice.


"Ina muka nufa?"


"Pizza zanci" ta fada tana tande baki. Dole ta bashi dariya sosai


"Wadan nan babies,wanne irin kwadayayya suka maida ke?"


"Ask them" ta fada kawai tana nuna masa tsinin cikinta wayarta na hannunta tana qoqarin kunnata.

Gurin saida pizza me kyau tsafta da inganci va kaita cikin nasarawa GRA


"A nan fa zamuci" ta fada tana neman gurin zama


"Oh god" ya fada a hankali, mamaki yana sake kasheki, da gaske ake cewa dole ka sake yin karatu na musamman akan mace idan tana da juna biyu, wawayen maza sai suyita cusgunawa matansu a irin wanan yanayin su dauka kome iskanci ke sawa suyi. Tunda yake da ita bai-taba gani ta zauna cin abinci cikin mutane da yawa bama bare waje sai yanzu. 


Hakanan yaja tasa kujerar shima ya

) zauna,ya jira waitress ya bata order.

Dukan pizza din ya tura mata,yana kallon yadda take ci hannu baka hannu qwarya


..Hmmm.


...i love you"


"Baby iam finished"


"Alright" ya fadi yana miqewa


"Moha…...i wanna discuss something with you please mana" ta fadi tana narke murya tare da tara hawaye a idanunta. Tare suka waiwaya suka kalleta shi da sãahar din, kasa ci gaba da kallonta tayi saboda wani irin kallo da taga tana jifan toufeeq din dashi, ta dauke kanta gefe tana gogarin hadiye wani mugun kishi da ya taso mata, bata taba zaton tana da kishi irin wannan ba sai yanzu.


Mamakin zallar garfin hali ko gegashewar zuciya zaice irin ta ameesha ke kai kawo a ran toufeeq, bai taba zaton har gaban abada zata iya tararsa da zancan ban haguri bama bare batun ya koma sonta har akai ga zancan ta koma tana amsa sunan MATARSA. ransa yaji wani wani irin baci, duk sansa ya kalli fuskarta sai va tuna zunubinta,sai yaga komai muraran shimfide saman fuskarta muraran kamar a lokacin kunnuwanta suke jive masa abinda yaji din.


Karo na biyu säahar ta gaza jurar kallon da tayi imani har yanzu ameesha na jinfan toufeeq din nata dashi,sai ta waiyawa tana mata wani qasgantaccen kallo


"Da kamun kai da cikakkiyar nutsuwa akasan diya mace, bin d'a namiji ba nata bane, ki tagaita kallonki a kansa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa he's mine ever and ever"


Kalaman sun taba ameesha sosai, dole ta waiwayo ta zubawa säahar idanu,kallon fuskar säahar din taketa gudun yi din batasan me yasa a duk sanda ta kalleta ba sai taji kamar ita nata ajin baiki ba, duk sanda ta dubeta sai taji kamar har abada toufeeq bazai iva sake kallon kowacce diya mace yaji ta burgeshi ba, duk sanda ta kalleta tana jin cewa tsananin rabo da kuma tausayi ya mallaka mata toufeeq a baya,duk sanda ta kalli qualities din da sãahar din ta hada sai taji kamar ta rasa toufeeq har abada,mafi munin tunin da batason tunashi wanann ne kuma ya sanya taqi giving up,wata yudararriyar zuciyar tana gaya maya cewa ZAKIYI NASARA,SHI ME TAUSAYI NE.


Taku biyu yayi ya kamota cikin jikinsa qasan ransa yanajin farinciki yana ratsashi, har yanzun classy säahar din nan tasa tana nan babu abinda ya canzata,me tsananin kamun kai da jin takaicin yadda mata da yawa suka zama was marasa aji da sanin ciwon kansu


"Yes‚iam your's,lam all yours,let's go" ya fadi yana dauka mata wayarta tana jingine a jikinsa suna takawa a nutse.


Zallar kishin da ya gani cikin idanunta bai taba ganin irinsa ba kaman yau,mota ya bude mata ta shiga,ya kunna mata Ac ya kuma daura mata seatbelt ya dage dukkan glasses din


"Ina zuwa, kada ki fito" ya fada yana rufe mata qofofin sannnan ya juya yana barin wajen.


Tanason tace masa ina zaije? yazo kawai su tafi amma ta kasa,minti daya biyu har biyar shuru, take zucivarta ta fara raya mata qila ma ya shanya ne kawai vana wajen tsohuwar matarsa suna soyewa.


Wannan tunanin ya kumbura zuciyarta,sai kawai ta fashe da kuka,take mararta tayi wani mugun motsawa da matsanancin civo.


Ransa fes yake dawowa ga motar,ya tabbatar yau vau kawo garshen case din ameesha,yayi imani daga rana irin ta yau ba zata sake marmarin hada hanya da shi ba indai da zuciya a qirjinta. Zasu biya su dauko fadeela da yanzun maji keson qwaceta itama, tuntuni yakeson ta dawo gida säahar ke hanashi daukota


"Zaka iya kallon idon maji kace kazo daukar 'yarka?"


"B wani madam, kema fa nasan kaara kawai kikey" murmushi kadai takeyi bata taba yarda ta amsashi ba.

Yana bude motar sautin kukanta ya sauka a kunnensa


"Subhanallah" ya fadi da sauri yana dagota saboda vadda ta zauna din ya tabbatar ta takure da yawa


*Ka daina tabani, marata kamar zata tsinke,babu dadi, ka koma wajen tsohuwar matarka ka gyaleni naii da ciwona" bai sake ce mata komai ba sai kawai ya tayar da motar, cikin wani mugun speed ya fice da motar daga harabar asibitin.


Kafin sukai asibitin ciwon ya sake tsananta.

Luckily suka tarar da Dr raheema na shirin fita daga duty, dubawar farko taga haihuwa ce, kuma gadan gadan tazo don takai 4cm.


Ya rude gaba daya saboda yadda yaga tana juyi a tana riqe komai da qarfinta na gaske sai ya daga masa hankali. Ya rasa waye zaima fara kira?,sai kawai ya kira maji.


Hankalinta yadan daga, saboda burinta a duniya na garshe taga tulin jikoki daga jikin diyoyinta guda biyu,tunda ita Allah bai gaddareta da samun tarin 


'ya'ya masu yawa ba, ta daure zuciyarta cikin nutsuwa tace


"Ma sha Allah, Allah ya raba lafiya,Kun dauko kayan haihuwar ne?"


"Daga gurin pizza nagudar ta tashi"


"Ashsha wanne irin sakarci ne haka Muhammad? ka dinga yawo ya yarinyar mutane da tsohon ciki?,waye yace maka ana fita anyhow da tsohon ciki?" Kai kawai ya girgizawa,maji ba zata fahimta,yanzun inda bai fito da ita ba da yanzun tana gida suna dambarwa


"Ka yiwa baaba ramatu magana,gani nan isowa nima" katse wayar yayi kawai ya kira baaba ramatu din. Maama maji ta kira, amma saboda kara irin tata,duk kuwa da cewa säahar din auta ce, autar ma da ake fatan ganin abinda zata haifa amma cikin alkunya tace


"Haba maji, kina gurin ai ba sai nazo ba" sosai maii keiin dadin yadda dr girema da maama ke bata girma da damqa mata säahar halak malak, saidai duk da haka ta roqi tazo din a haka suka rabu.


Cikin abinda bai wuce mintuna talatin ba sai gasu a asibitin. Maji, anty farheen, anty sumaira, raihanatu wadda tazo musu hutu ne(cousin din adam da su dr girema suka turata karatu,bayan dawowarta sun laluba ainihin dangin mahaifinta sun maidata hannunsu, sun kuma yi mata kaykkyawan rigo,sun barwa momee itane dama saboda ta dage zata rigeta da amana, suka barta suna ganin kamar 'yar 'yaruwarta ce ba zata cutar da ita ba yanzun haka shirin bikinta akeyi) sai fadeela data kasa ta tsare itakam vau zatayi 'yan ganne. Kwatsam saiga afifa ita dake da danyen jego ta saka sajjad din a gaba sai da suka taho. Sosai maji ta dinga fada,tace ya dauketa su koma amma ya bawa majin haquri, tayi algawarin bestie dinta tana sauka zasu koma,tunda ance takai kusan 7cm ma. Yadda ta marairaice yasa ta bawa maji tausayi,sai ta qyaleta kawai suka zauna kowa yana fatan samun labari me dadi. Oga toufeeq kuwa basusan ina ya shiga bama,don basu sake ganin fuskarsa ba ma.



• Zafafabiyar

No comments