Tabarmar Kashi book 2 page 57

 "HUGUMA*






•_TABARMAR KASHI_*



Book 02 Page 57


Zuciyarsa ta sake jin amanna data koma

din, saboda gananun maganganu da yaji sun fara yawo akan shi dinma kada Allah yasa ba irin halin mahaifinsa na auri saki yake dashi ba.


Sanda ta koma din duniya ta samu,don haka ta kwantar da kai sosai, duk wani biyayya kulawa da tattali tana bakin qoqarinta, duk da cikinta yayi nauyi amma bata fasa duk wani abu da tasan yana so din ba. Wani lokaci tausayinta kan lullubeshi qwarai,ya sanya hannu suyi duk wasu ayyuka tare, tayi wani mugun laushi, ta sauya kwata kwata daga ameesha din da ya sani. Tun yana mamaki yana d'ari d'ari har ya saki jikinsa, ya kuma barwa ransa rasuwar mahaifiyarta ne ya kawo hakan, tunda ya san ciwon mahaifiya,shi da ba rasuwa ma tayi ba.


Biyayyarta da canzawarta ya sanya shima yake tuquru wajen kyautata mata, ya sakar mata komai da take da bugata. Wannan ya sanya ta sake ninka biyayyarta,kyautatawa da kulawa da nuna zallar soyayya me zurfi data sake sanyashi sakankacewa da ita,ya kuma sakar mata zuciyarsa,ita kuma hakan ya bude mata gofofi da dama na abubuwa masu yawa.


Cikin wata na goma ta sauka ta haifi fadeela, yarinyar da tazo da wani irin farinjini da tarin alkhairai masu yawa ga mahaifinta harma da mahaifiyar tata.

Suna na kece raini ameesha tayi kanta ya fashe sosai, toufeea ya fasa mata kai ya sanya taji ta kere sa'a cikin mata.


Hankali kwance ta fara rainon fadeela saboda masu aiki biyu da toufeeq ya dauko mata saboda yarinyar. Wani irin raino takeyi mata kamar ba diyarta ba,a lokacin ya siya mata mota irin wadda takeso saboda dadin zama,a sannan ko watanni biyu fadeela batayi ba ameesha tana iya fita ta barta hannun masu aiki ba zata dawo ba sai yamma awa daya ko biyu kafin toufeeq ya dawo,zata shirya ta shiga sabgoginta cikin gidan sannan ta dauki yarinyar, tun bata gama mallakar hankalin kanta ba ta saba da rashin uwa a kusa. Kusan baba ramatu ce ta zame mata kamar kaka kuma uwa,ta jima tana wanann dabi'ar kafin toufeeq ya ankara. Ya nuna mata bacin ransa qwarai, amma saita kwantar da kai ta bashi haguri tare d algawari ba zata sake ba,don a sanann ko zaginta zaiyi bata tada kai bare ta nuna masa ta damu, bata gaunar duk wani abu da zai hadasu, saboda kudade

sosai take karba daga hannunsa, bai kuma taba cewa

a'ah ko don me ba?,shi a ganinsa muddin zaka samu

kulawa daga wajen mace da biyayya meye ba zaka iya

kashe mata ba?,meye ba zaka iyayi mata ba?. Abu daya ne har a sannan ya gaza canzata akai shine bugatar aure, baisan abinda ke faruwa ba da ita sam,amma ya aza hakan akan yanayin halittar ne wanda yasha banban da rasa neeesa ba kusa ba. Damuwar kawai shi tun asali ba meson auren mata biyu bane, hakan ya samo asali da yadda yaga mahaifinsa na yawan aurar mata yana kuma

saki tun bayan rabuwarsa da mahaifiyarsu.



Kyautatawar bogi da biyayyarsa ya sanya yakejin

haquri da mace idan tana da wani nagasu ba aibu

bane, dama duk dan adam tara yake bai cika goma

ba,duk kuwa da yana shan dan karen wahala amma yana goqari tare da neman sani akan hanyoyin da zai

magance matsalar a tsakaninsu a samu daidaito.




•_SHEKARA UKU_*



Shekara uku da haihuwar fadeelan,a wata rana

cikin ranakun sa'a a wajen toufeeq ya samu fiye da

yadda yake samu daga gurin ameesha. Sunyi sallama

dashi sallama me kyau,cike da aminci da qauna, zaiyi

tafiya zuwa Canada.


Har bakin mota ta rakoshi tana koke koken zatayi

kewarsa, vana dauke da fadeela akafadarsa,yayi

murmushi yayi kissing goshin yarinyar yana jin qaunar

yarinyar har gasan zuciyarsa sannan ya miga mata ita

hadi da kamo hannunta va rige cikin nasa a tausashe


"nayi alqawarin ina gama abinda naje yi zan dawo gida immediately, zan iso tare da dream car dinki" wani dan garamin ihu tare da tsalle ta saki ta kuma

rungumeshi, yayi mata suprise, bata taba zaton zai siya mata motar ba,ta dai fada ne kawai


"Thank you, thank you so much"


"You deserved it" ya fada a tausashe yana kissing

goshinta itama. Ita ta bude masa motar ya shiga sannan ta rufe masa sukayi gaba tana gurin a tsaye.


Sanda ya isa airport sai ya samu anyi cancelling

tashin wannan jirgin, sunata bawa mutane irinsa haquri wadanda basu duba sagon da suka tura musu ta email

ba akan hakan tun yau din da sassafe, ransa ya baci da wannan al'amarin da sai a qasata Nigeria kawai yake faruwa.haka suka juyo suka bar airport din. Har zai koma gida sai kawai ya fasa ya wuce sabgoginsa,a can din magriba ta kusa cimmasa,sai ga kiran hajiya qarama


"Ya akayi number dinka na Nigeria ya shiga? kai da yanzu warhaka ya kamata ace kana canada?" Dan garamin tsaki ya ja yana mata bayani


"To Allah yasa hakane yafi alkhairi, yauwa idan zai yuwu don Allah ka dawo yanzun, ina bugatar takardun nan da na baka ajiya,nan da awa daya alhaji kutama zaizo ya karba, ana bugatarsu urgently" ta fada da alamun gaggawa a muryarta



"Alright, na gama abinda nakeyi nima,gani nan"


"Yauwa,sai ka garaso, koda zaka rigani isa ka jirani please,don ina asibiti yanzu duba hajiya barratu"


•"Ba damuwa" yace da ita sannan ya aje wayar.


A hanya ya tsaya ya ya duba musu kayayyaki a wani shopping mall na ciye ciye da yasan ameesha da fadeela sunfi so, kowa ya siya masa nasa. Yana tafe yana imagining murnar da zasuyi da bai samu flight ba,yanason yaga kulawa qwarai da soyayyya daga fuskar matarsa,shi yasa ma yaso mata suprise bai gaya mata bai samu flight din ba.


Suna gab da karya kwanar shiga gidan haka kawai gabansa yaji ya fara faduwa. Ya lumshe ido yana kiran sunan Allah, me yake faruwa haka dashi?, Ya tambayi kana. A haka suka garasa cikin gidan shi da jibril ne ya dauki ledojin ya buda motar ya wuce kai tsaye sashensa. Harabar gidan ba kowa kasancewar magariba ta kawo kai.


Qofar a rufe take, sai ya sanya key dinsa ya bude ya tura ya shiga ya fara takawa a hankali zuwa ciki. Parlor din babu kowa shuru kakeji,ya danji mamaki ya kamashi,sai yaci gaba da kutsawa zuwa hanyar da zata sadashi da stairs yana kyautata zaton sun haura sama ne ita da fadeela din.


Wani mahaukacin bugawa zuciyarsa tayi yaji qwaqwalwarsa na neman tsayawa cak daga aiki. Fadeela ce kwance saman saman sassanyan marbles din dake shinfide a gurin, qafafunta na saman stairs na garshe, kanga kuma daya langabe na a qasa,sassalkar sumarsa ta baje sosai a gasa,yayin da kakkauran jini ya soma bata gurin.


Wani irin mummunar rawa jikinsa ya fara yi yanajin kamar numfashinsa zai bar iikinsa sanda va dagata yaga jikinta ya saki gaba daya kamar babu ruhi a tattare da ita. Bakinsa rawa yakeyi yanason kiran sunanta amma ya kasa yanason ya kira ameesha nan ma komai yaqi fitowa daga bakinsa,sai kawai ya saketa ya haura saman da mugun gudu da zummar nemo ameeshan yaji me ya samu diyarsa, saboda komai ya kwance daga kansa tunanin fara zuwa asibiti ma ya fita a kansa,so yake yaji meye ya sameta.


A hankali va janye hannunsa daga marigin gofar dakin sakamakon sautin darivar ameesha da yaji cakude da sautin muryar wani namijin


"Ya isa haka please mana, kai wai baka gajiya ne?"


"Ta yaya zan gaji? bayan har yanzu kawai dandanamin zuma kike a baki, kinqi barina na shiga ainihin inda abin yake?, kina rudani kawai da jikinki, kina barina akan hanya navita fama"


"Au, hakanma baiyi maka ba?,an gaya maka taba jikina din ma abune mai saugi? to ko mijin aurena sai randa nayi ra'ayi naji jima ina cikin yanayi matuqa nake sallama masa, kaima ka godewa Allah daka samu wannan damar,gaka yau har cikin dakin mijina,zaka kwana kana murzata" Dariya ya saki


"In sha Allahu vau sai na cimma gaci" dan tsaki taja


"To watagila idan naii abun yayimin yadda nakeso"


"Kina son muyita wahala ne na baki shawara ki kashe auren nan kawai kizo muyi aure ki huta da debar masa dukiya da kadan da kadan, kizo inda zan bude miki bakin lalitata kivita diba har sai kin gaji" dan shuru tayi sannan tace


"Ba zaka gane ba, kayi suna a rayuwa ma wani abune,yau ace ni matar dan MT JARMA ne ma wani babban alfarma ne, tabbas kana da kudi irin kudin da nakeso, amma matsalar sunanka baiyi fice kamar nasu ba,sannan kuma inason guy din sosai,yana da kyau ya iya soyayya garshe ne"


"Bansan baki da wayo ba sai yau, don ya fini kyau ni mummuna ne a kansa ai ba wani abu bane, kuma da kike maganar so soyayya, da soyayyarsa da dukiya wanne kika fi so?" Ya tambaya seriously


"KUDI malam sune fa gare magana" gyalgyalewa yayi da dariya


"Yauwa,aini na sani, shi kansa da bashi da komai ba zakiii sonsa ba na san halinki fa....ki bani kanki a yau kawai na miki algawarin million goma yanzun nan zakiji alert idan kin yarda"


"Amazing!" Ta fada da matuqar farinciki da zumudi fal muryarta

"Na yard…" Kamar an hankadashi da baya haka

yaji, bai iya tsaiwa yaji ragowar kalmar daga bakinta ba yaji kamar na daka tsawar sunan


"FADEELA!" tsakiyar kwanyarsa. Da wani mugun gudu da sassarfa ya dinga hada matakala bibbiyu uku uku yana sauka,yana isa yasa hannu ya kwashi fadeelan ya fita da gudu. Jibril na hangoshi ya tabbatar babu lafiya, bai bari ya iso ba ya wangle masa gofa,suna shiga ya figi motar da mugun gudu tare da searching na asibitin da zasuje a kansa ba tare da ya tambayi ogan L nasa ba,hankalinsa a mugun tashe sakamakon ganin hawaye saman fuskar mai gidan nasa,mutumin da ya sani sama da shekaru, bai taba ganin karaya ko girgiza saman fuskarsa ba komai girman tashin hankali, lallai abinda ya sameshi ba qarami bane, duk da kowa yasan tsananin qaunar da yakewa fadeela din wanda bata boyuwa.


Har sukaje asibitin aka karbeta tare da qogarin dawo da ita cikin hayyacinta ameeshan batasan abinda akeyi ba. Sai da likitoci suka gama komai suka masa bayanin idan ta farka za'a yi mata X-ray saboda tabbatar da lafiyar qwaqwalwarta akan buguwar da tayi,yana dakin gaban gadon fadeela din a zaune sannan uwar ta iso a birkice tana kuka.


"Me ya sameta?" Ta jefa masa tambayar da sai da yaji kamar ya Sanya wuga ya yanka maqogaronta banda zuciyar musulunci dake qirjinsa, da sunayen Allah daya dinga kira wadanda suka taimaka waien daidaita shi, banda haka ya tabbatar a yadda qirjinsa yayi nauyi shima iwar haka ba shakka yana kwance saman gado ana jinyarsa


"Fita!!" Ya fada a tsawace muryarsa na wani irin sargewa da matsanancin bacin rai,fitar saurin muryarta ba abinda yake tuna masa sai gazantacciyar hirarsu da kwartonta


"Kayi haquri don Allah, ba laifi ko sakacina bane,na gama mata wanka na shiryata kenan,na hau sama nayi wanka nima kafin na shirya na fito na sauko naga babu ita,sai jini wajen stairs, masu aiki suke gayamin ka fita da ita" ta fada cikin gunjin kuka,gabanta kuma yana faduwa da matsanancin toro da firgicin zaiyiwu yaga ANAS ko Kuma wani abu da yayi kama da haka Zaki fita daga nan ko sai na wulaqantaki?, maci amana me tozarta sunnar ma'aiki banason na sake ganin fuskarki daga yau a gaban ido na, muddin kika sake kika qara nunan fuskarki sai nasa bindiga na harbeki,ki tafi na sakeki saki daya" ya furta cikin matugar danne zuciyarsa ya furta saki dayan, amma zuciyarsa tafi amanna da ya qarasa guntule igiyar guda dayan da a yanzu tayi saura a tsakaninsu.


Sosai ta gigice da jin sakin da ya rattabo matan,ta bude baki cikin rawar murya ta fara roqarsa yace


"Ki yiwa kanki suttura ki fita tun ban tattaka ki a nan wajen ba,kije ki auri me kudin da ya fini,ki tara dukiyar da duk kikeson tarawar wannan damuwarki ne, abu daya zan gaya miki,daga yau ki cire a ranki a duniya kin taba haihuwar wata diya fadeela har abada" zata ci gaba da rogonsa yace


"Duk kalma daya idan kika qafa furtamin a bakin aurenki take, get out from here idiot!!!" Dole taja qafafunta ta fice, yasa hannu ya lullube fuskarsa zuciyarsa na bashi yanxun haka akwai janaba a jikinta na wancan kwarton nata.


Bincike akan fadeela ya kammala,ya kuma tabbatar data samu ciwo cikin qwaqwalwarta wanda shine sila na haduwarta da lalurar EPILEPSY. randa ciwon ya fara motsa mata yayi mugun birkicewar da bai taba yi ba,saboda shi dai bai tana ganin ciwon a gaban idanunsa ba daga wajen wani sai yau akan diyarsa mafi soyuwa a wajensa.



Zafafa biyar

No comments