Tabarmar Kashi book 2 page 55

 *HUGUMA*





*_TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 55




Tom



Bai taba dauka fada mata hakan zai zama babbar matsala a tsakaninsu ba,ya sanya tausayinta da na mahaifiyarta shine gaba da komai, tausayinta ya sanya masa soyayyarsa a ransa, musamman da ya fuskanci mahaifiyarta dake kwance tana fama da jinya mutuniyar kirki ce qwarai. Irin mutanen nan da sam rayuwa bata damesu ba,basu da wani buri me zurfi a cikinta. Kusan tafi kowa farinciki da wanzuwar taoufeeq cikin rayuwar d'iyarta, bawai saboda dukiya ko kuma wani abu daya mallaka ba, a'ah tsantsar nutsuwa hankali da hangen nesa da ta hanga muraran tattare dashi,dukiyar mahaifinsa ko wadatarsu bata sanya masa girman kai ko jin cewa shi din wani bane,tayi imani ameesha din zatayi aure hannun da za'a datajtata, za'a mutuntata,inda koda bata raye ba zatayi kukan maraici ba.


To ita rayuwa a duk yadda kaga Allah ya ajiye bawa,tofa yafi cancanta da wannan matsayinne, saboda shine Allamul ghuyub wato (masanin gaibu). AMEESHA na daya daga cikin matan da zuciyarsu ke cike da dimbin burika na rayuwa saboda kyawun fuskar da Allah ya azurtasu dashi. To amma me? yanayin talauci da matsi na rayuwa da kuma yanayin environment da suke ciki dukkan alamu sun nuna babu inda wadannan burika nata zasu shura,saidai duk da hakan akwai was baqin halaye da idan kayi tsinkaye zaka iya fahimta a tattare da ita.


Yadda ameesha din bata da saurayi duk da kyau da take dashi da kuma yadda matasan unguwar ke sonta ya gara kafa ameesha a zuciyar toufeeq,a nasa tunanin tsananin kamun kai ne da kuma darajta kai,abinda bai sani ba shine,ita din ta raina ajin dukkan mazan da suke zuwa mata da kalmar soyayya,tana ganin tafi qarfin ajinsu,ko a ranar da taje karban tallafin sai da mahaifiyarta tayi da ayar sannan taje din, da kuma tsananin rabon haduwarsu da toufeeq.


Shigowar toufeeq cikin rayuwarta sai ya sanya ta fara jin kanta yana budewa,idanunta suka fara budewa,ta fara shanshanowa tare da hango cikar wadan nan burikan da talauci ya yiwa dukan mutuwa suka kwanta magashiyyan,sai ta fara farfado dasu, musamman da ya kasance toufeeq din me sakakken hannu ne, mutum ne me tarin kyauta. Cikin lokaci qalilan tafi qarfin sutura da cima,ta samu tsadajjiyar wayar hannu wadda tayi sanadin haduwarta da 'yammata irinta da suka dauki rayuwar duniya da fadi,'ya'yan da sai da taimakon Allah da huwacewarsa ake samun abicin da za'a ci cikin gidajen iyayensu,amma idan sukayi wanka suka riqe wayoyinsu zakayi tsananin 'ya'yan wani commissioner dinne. lya wayar hannunsu kawai tafi jarin ubansu kauri.


To bare kuma ameesh da a sannan abinci a gidansu baya yankewa, toufeeq ya fahimci yanayin rayuwar da suke ciki, ya kuma dauki nauyin komai hatta da jiyyar mahaifiyarta. Mutuniyar kirki ko yaushe addu'a take Allah vasa ameesha ta kasance tasa ce ta har abada,ko yaushe fada takewa ameesha ta riqeshi hannu bibbiyu.


To koda umma batace mata ta riqeshin ba itama ba zata soma sakinsa ba,ina taga ta sakin toufeeq din?, mutumin da ya fara matso mata da burikanta kusa kusa da ita ya kuma fara cika mata su?. Ai bata ma gama sanin waye toufeeg din a zahirance ba sai bayan haduwarta da hadaddun qawayen data maye gurbin rayuwarta dasu,ta sake sanin waye mahaifin toufeeq, a nan suka hure mata kunne akan ta qara yawan buqatunta tana sake samun abubuwan rayuwa masu tarin yawana jikinsa,su saka sanya ta fara raina hidimar da yake mata,saboda suna gaya mata


"A arzigin ubansa,wannan hidimar da yakeyi miki tayi matuqar yin kadan" yana mata kwarjini sosai,tana kuma kunyar ta tambaya kanta tsaye,sai ta fara shigo da qarairayi tana karbar kudade a hannunsa. Bai taba hanata ba,duk da sannu a hankali ya fara fahimtar wasu kudaden da take karba setup ne kawai,yana yi matan, saboda kawai a lokacin bugatunta basa hawa kansa,kuma basufi qarfin samunsa ba.


Sanda ya gabatar da zancan aurensa ga Dr jarma hankalin hajiya garama yayi mugun tashi,ko kusa ko alama bata taba tsammanin zaiyi zancan aure a lokacin ba, babban abinda ya Sanya take sake ingiza Dr jarma akan yabar toufeeq ya nema na kansa kada ya sangarce ya shagala da dukiyar sa ba,ba komai bane sai don taja lokaci zuwa sanda HASEENA zata sake tasawa,ta zama mutum, kuma a nata lissafin sanda haseena zata gama nata karatun zuwa lokacin ya zama wani me fada aji,yayi irin kudin da take buqata daga mijin diyarta, tunda toufeeg din yana da wani irin nasibi da albarkar hannu.


Kiransa tayi tayi masa fada sosai bayan ta gama binciken wace ameesha?,diyar wacece?. Fadan da tayi masa ta bullo masa ta bayan gida ne


"A matsayin da mahaifinka yake dashi, da baiwar da Allah yayi maka,ai abun kunya ne ace kaje ka nemo aure a wannan gidan"


"Arzigin kaykkyawar nasaba shine arziqi bana dukiya ba,so ni banga abun damuwa ba mommy, please cool down" ya fada da I don't care manner dinsa.


Duk hanyar da zatabi don ta ruguza abun bai yiwu ba saboda rabo da Allah ya tsaga a tsakani,tana ji tana gani akayi auren, saidai kuma ta barwa ranta lallai  saita ruguza abun ko ba dade ko ba jima, don ba zata bari ma haseena ta zauna da kowacce mace da sunan kishiya ba.


Tun lokacin shagalin bikin ameeshan ta fidda tsarukan biki na kere sa'a da kuma kashe kudade,yayi wasu wasu kuma yace bashi da kudi bazai iya ba.

Maganar data sosa ran ameesha, zugar tawagar qawaye kuma suka sake azata akai suna fadin


"Anya zaki qulla abun arziqi da mutumin nan?, ki dubi dukiya irin ta mahaifinsa amma ya dinga ambatar babu?, ina babu taga gurbin zama a family dinsu ma gaba daya?.


Washegarin ranar da Ameesha ta tare bayan sunyi first night dinsu,tana langabe a jikinsa saboda hannu da tasha a hannunsa tace dashi


"Mota nakeso a matsayin tukuicina na first night" gyara zamansa yayi


"A yanzun bani da kudin siyan wata sabuwar motar, motocina guda biyu,duk sanda kk fara fita kidauki guda daya aro kafin na samu sukunin siya miki". Tashi tayi ta zauna sosai tana kallonsa


"Nikam mamaki yake kamani idan kana cewa

BABU.kasan me wannan kalmar ke nufi? duk tarin dukiyar da Allah ya mallaka muku kai da mahaifinka?" Murmushi yayi ya girgiza kai, zuciyarsa na girgiza sosai da yadda ta iya buda baki kanta tsaye ta fadi abinda ya fahimci ya jima a zuiciyarta,yau ta amayar dashi da alama ta gaji da boyonsa

"Bana lissafi da abinda ba gumina bane ya tarashi ba,sanann ban isa nayi rabon gadon mutumin dake rayuwa lafiya lau cikin iyalinsa ba,duk abinda naga ya kamaci nayi miki zanyi miki gwargwadon wadatata ba wadatar mahaifina ba,nayi miki alqawarin ko sau daya ba zakiyi kukan rashin ci sha ko suttura ko kuma kudin da zaki biya bugatunki ba tare da almubazzaranci ba".


Hakan da ya fadi baiyi mata sam,tun a satin ta fara fushi dashi akan ya gaza siya mata mota,bata kuma sake bari ya tabata ba,har sai bayan wata guda da ya kawo mata motar har farfajiyar gidan. Ba kunya ba tsoron Allah ta ware,ta dinga murna tana waya da qawayenta tana labarta musu zuwan motar,ranar kyautatawa sabuwa tare da wani sakin jiki na musamman, tun a sannan jikinsa ya fara sanyi, tunani kala daban daban ya shiga kai kawo a ransa.


Watansu uku kacal ta soma ciwo wanda aka tabbatar musu da shigar ciki na watanni biyu, abinda bai taba kawowa ba,don kuka ameesha ta dinga yi,da yabi ba'asi babu kunya tace dashi


"Nifa ban shirya haihuwa yanzu ba,haba.....kamar wata akuya,aure wata uku kawai? ,bana tunani cikin friends dina da akayi aurenmu tare akwai wadda ke da ciki, sai kuma ni?duka duka ma sau nawa mukayi tarayya?, uku ne fa kawai" Kansa kawai ya kawar ransa yana baci zuciyarsa na masa suya Sosai,dazun kafin su fito ya raba rigima tsakaninta da hajiya qarama,ci mata mutunci tayi sosai abinda ya hanashi daukan mataki rashin lafiyarta,gashi yanzun ta sake dasa masa wani bacin ran


"Me kikeso yanzu kice?" Ita kanta kafin ta furta sai dataji shakka,saboda tasan halinsa sarai,idan ransa ya baci ko va baude bashi da dadin sha' ani,ciki ciki tace


"Kawai, kawai aje a zubar dashi, a sakamin implants,kamar nan da next two years sai a cire kafin na samu ciki na haihu aqalla munyi 4 to 3yrs" wani wawan birki yaja tsakiyar titi,saura kadan ya daki motar dake gabansu


"Ni inaso, kuma ina gaunarsa ko da dan qadangare zaki haifa,sannan ina miki rantsuwa da ubangijin da ya busamin numfashi, duk ranar da kika sake yimin magana makamanciyar wannan sai kin gane ni toufeeq asalin tataccen mara mutunci ne" daga haka bai qara ba ya tashi motar ya figeta da mugun gudu,har tana yin gaba kamar zata daki gaban motar.


Har suka isa gida bai sake kallon koda koda gefen da take ba,duk da kikan da taketa yi har da sheshsheqa.

Suna isa gidan ya fita a motar abinsa ya barta. Cikin watanni uku kacal tayi masa abubuwa masu tarin yawa,abu daya zuwa biyu yasa yake shanye komai,darajar so da zuciyarsa ke mata zalla mara algus kuma fisabilillahi, sai kuma mahaifiyarta da a kullum yaje gaidata ko yayi mata aike take bashi tausayi,bakinta baya gajiya da gode masa da sanya masa albarka tare da bashi amanar ameesha,don a koda yaushe takance bata dauke tsammani da mutuwar ta ba.


Yadda ya watsar da ita itama data gama kukan baqinciki kan yadda cikin zai kawo mata cikas akan sabuwar rayuwar morewa da more arziqin mazajen da suka aura da cikin zai kawo mata, taga baibi ta kanta ba kwana daya biyu har zata nema sulhu sai ta fasa,zugar qawaye da tarin shawarwari batakai marasa kan gado sukayi mata caaa a saman kai,sai itama ta watsar dashi taci gaba da rayuwarta. 

Shawara daya ce tasu da bata zauna mata a kai ba,na tayi amfani da qwayar zubda ciki ta cire cikin kawai. Ita kanta tasan aikata hakan babban ganganci ne da kuma kuskure me tarin yawa a gareta,tunda tafi kowa sanin waye toufeeg din.




Zafafabiyar

🔥🔥🔥🔥🔥🔥

No comments