Tabarmar Kashi Book 2 Page 42

  TABARMAR KASHI_*


Book 02 Page 42





"Nifa bakiyimin komai ba kibar ma maganar don Allah, banason bacin ran fauziyya gaskiya,a kan ranta ya baci komai ma zan iya aikatawa,yar uwata ce bani da kamarta,farincikinta shine nawa, zama lafiya da ita shine zama lafiya da ni" shuru tayi tana juya maganar a ranta,tabbas akwai qamshin gaskiya akan abinda zuciyarta keta raya mata. Tun faruwar wannan mu' amalar tsakaninta dashi sai aka dan samu sassauci kadan,ya daina fushin da ya dauka gadan gadan da ita,yaci gaba da bata kufin cefane shima, amma kuma har yanzu abubuwa da yawa bata canza zani ba, fauziyya taci gaba da juya akalar gidan tamkar yadda mahaifiya ke juya akalar gidan danta. Hatta da abinci a yanzun suna cin duk abinda fauziyya ta zabi a girka ne. A haka aka yiwa mahmud albashin farko,sun kuma hada masa da wani kudi da suke bawa sabon ma'aikacinsu,don haka a sannan ya shirya tashinsu daga gidan, zuwa babban gidan da Kamfani ya bashi.


Batasan hawa ba batasan sauka ba,sai siyayya da taga suna ta fita ita dashi. Ko sau daya bata nuna tasan abinda yake gudana ba,idan ma fauziyyan tayi ne saboda ta quntata mata ko ta bata haushi, saidai qasan ranta bacin rai ne danqar irin wanda fauziyya ke burin ganin ta cusa mata,ko a fuska a lokacin wani irin ramewa majin tayi,saboda dukka wani kwanciyar hankali da • nutsuwar gidan miji ta rasata, dukkan hankalin mahmud ya karkata ga buqatunta da faranta mata,kai idan kaga yadda abun yake zaka dauka kishiya ce fauziyya a wajenta,kishiyar ma irin wadda tayi dukkan me yiwuwa wajen raba tsakanin miji da abokiyar zamanta.


Da wani dare mahmud ya aika toufeeq ya kirayi shifa din, a lokacin tana zaune saman abun sallah,don yanzu babu abinda yake bata nutsuwar ruhi da sanyin zuciya sai sallah da azkar. Ta iso ta riskesu a falo sunata sabgoginsu,fauziyyan ta wani murje a lokacin saboda tarin supplement da take dirkawa kanta na qarin qiba da kuma qara haske,wanda har sun wuce qa'ida,hips da boobs dukka sun fito sosai.


Guri ta samu ta zauna a nutse tace


"Gani" dubanta mahmud yayi,a idanunsa yaga ramewa da kuma canzawar da tayi, qasan zuciyarsa yana jin wani iri babu dadi, saidai baki ya gaza furta komai, hakanan wani abu yana tasowa yana danne dan qaramin tausayin da yakejin yana masa tasiri.


"Nidai bansan me yake damunki ba, gaba daya kin tsangwami kanki?,lokacin da ya kamata ki tsaya mu fuskanci rayuwa, Allah amshi addu'ar da kiketa yi mana" wani kallo tayi masa sai ta kauda kanta,batason tace komai saboda bata son fauziyya ko kadan taga alamun karaya a tattare da ita,ta tabbatar abinda taketa son gani kenan,saboda yadda ta matsa qaimi kawai ya isa bayar da amsa ga maji


"Nan da kwanaki uku zamu koma sabon gida,a baya na miki alqawarin sabbin kayan furniture da komai da komai,to yanzu yanayi ya sanya ba zasu samu ba,saboda nauyi da ya gara yimin yawa,an siya bawai ba'a siya ba, amma kayan furniture za'a sakawa fauziyya tunda itace garama, kuma ba mai zama bace, idan ta samu miji aurar da ita zanyi,kayan kitchen kuma na ajjiye mata su kada auren ya taso bani da komai a lokacin, idan Allah ya hore miki nan gaba sai a canza miki wasu,zan saka azo a kwashe wadan nan ayi musu gyara" qas tayi da kanta,har cikin zuciyarta takejin wani irin bacin rai,bawai na furniture din da yace za'a yiwa kwaskwarima ba,a'ah…...na yadda kullum kwanan duniya yake qara qasqantar da martabarta a idanun fauziyya yake kuma sake wulagantata. Ta tabbatar idanun fauziyya a kanta suke taga action dinta,don haka ta daga fuskarta da murmushi


"Banda abinka ai basai ka tsaya yimin bayani ba, Allah ya hore ya bada yadda za'a yi‚ba komai" har ransa yaji dadi duk da cikin jikinsa yakejin bai kyauta ba, sai ya jawo wata leda


"Gashi ganwarki tace ki fara dauka"


"A'ah ta dauka ba wani abu;idan ta gama zaba moha ya kawomin" ta fada tana miqewa


"Laaa maji ai ba wani abun bane,komai iri daya aka siyo, bambancin kala ne kawai" fauziyya ta fadi,wadda bata son maiin ta wuce ba tare data sake ganin wannan ba. Sabbin atamfofi ya siya musu masu tsada da zasu dinka na tarewa a sabon gida,waiwayawa maji tayi ta kalleta


"Bani da zabin kala fauziyya,ko kin manta likkafani da kala qwaya daya yazo?, kuma shine tufafinki kuma tufafina na qarshe?" Turus tayi tana bin maji da kallo,tasan cewa magana ce ta gaya mata a fakaice,sai bata sake cewa komai ba har ta wuce zuwa dakinta.


Saman abun sallarta ta koma ta zauna tana nazarin abun zuciyarta na soyewa,ta gaji da zubda hawayenta,zuwa yanzu zuciyarta ta fara soyewa,sai taci gaba da ambaton sunan Allah sannu a hankali har ta samu sassauci.


Cikin wannan yanayin suka koma sabon

gidan,wanda duk yaga dakin fauziyyan zai dauka shine dakin maji,ya zuba mata komai sabo,hakanan kayan yara ma suna gurinta da komai nasu


"'Itace uwarsu ai ita zata kula dasu" abinda Mahmud ya fada kenan. Maji ta jishi kawai, amma ta barwa ranta koda zata sallamawa fauziyya komai banda yaranta da ita daya ta raini cikinsu ta kuma haife abinta. Tsayayyar macace da ita kanta fauziyyan tasan cewa nasararta dukka akan yayanta take,amma majin ta shallake hankalinta,duk yadda taso a maida mata maji kamar mahmud don taci duniyarta da tsinke ta gaza samun hakan. Hakanan yaran, kusan tunda suka koma gidan majin ta sake janye yaranta jikinta da kyau,ta kuma sakasu cikin dukkan wasu addu'o'i na tsari na sha da shafawa.


Kwatsam Allah ya fiddawa fauziyya miji,a ranar har kukan farinciki maji tayi cikin daki, saboda tana ganin Allah ya kawo mata qarshen baqinciki da damuwarta. Da farko fauziyya taso taqi auren YA'AQOUB AJI, saboda yana da mata,sannan arziqinsa baikai yadda ta tsarawa mijin da takeson aura b,amma daga bisani yaci galaba a kanta bayan itama yaci galabar fidda matarsa daga gidan tun kafin takai ga shiga gidan.


Mahaukatan kudi mahmud ya kashe wa auren fauziyya,duk abinda ta nuna tace tana so shi zai saya mata,a lokacin hatta hidimar yara data gida data makarantarsu sai data tabu,ya tsaida wasu abubuwan da yawa saboda ya cika muradin fauziyya yayi mata aure kece raini. Sam maji bata damu ba,saboda tasan aski ya riga yazo gaban goshi,akayi biki aka tattarata aka migata gidanta.


A washegari sai da maji tayi azumin godiya ga

Allah,a ranar gidanta ya fara zamar mata gidanta,hatta da iskar gidan sai da ta jita daban da wadda ta saba shaqa. Cikin lokaci kadan abubuwa suka fara komawa saiti,saidai hausawa sukance ba'a taba bari a kwashe duka,haka yake,don duk da da tayi nasarar daidaita al'amura masu tarin yawa,amma har yanzu fauziyya na baki da zuciyar mahmud,a qalla a rana sai yayi zancanta ya kusa sau goma,kira kuwa sai da maji ta gaji tayi masa magana


"Kai yayanta ne kuma namiji, bai kamata ace kana vawan kiranta haka ba saboda tsira da mutuncinka, ina laifi a rana sau daya?" Shine aka samu sassauci ta fannin kira, amma banda haka babu abinda ya canza zani.



* BAYAN SHEKARA BIYU_*


Ana murna bago ya tafi ashe bago yana bayan gari,shekarar fauziyya biyu da aurenta da diyarta daya

HASEENA MEENAL arziqin Mahmud ya fara dawowa yadda ya kamata. A take shaidan yayi mata kururuwa,taji sam zaman gidan YA'AQOUB bai dace da ita ba, hakan kamar ta tauyi rayuwarta ne,ta kuma barwa wata dan uwanta tana cin arziqin da daga ita har mahaifiyarta basu cishi ba,duk da babu abinda Mahmud ya rageta. dashi,komai ya samu tana ciki kuma taba da kaso a ciki.


Dare daya ta shiga ta fita da yawan gidan malamanta ta tilastawa ya'aqoub ya rubuta mata takardar saki uku a jare,don bata tunanin har abada zata dawo,don yanzu ba wannan ravuwar bane a gabanta. Manya manyan zawaran dake tashe a media ake damawa dasu ta fannin kasuwanci su suke rudarta, rayuwar 'yanci da business,fita qasashen qetare a duk sanda suka so,gidan kansu da manyan motocin hawa da sutturu na alfarma vanzu sune babban burinta, sai kuma diyarta meenal wadda Allah ya jarabta da mugun sonta,irin soyayyar da bata taba yiwa wata halitta irinta ba.

Tanason ta tara mata dukiyar da ba zata taba sanin meye talauci ba har garshen tata rayuwar.


Ranar data isa gidan Mahmud da takardar shaidar saki a ranar baiwar Allah shifa na cikin farinciki,karon farko tun bayan karayar arziqinsa ya sake siyan mota,a lokacin yace ta dinga hawa tana hidimar gida,kai yara makaranta da daukosu,da sauran abinda ba'a rasa ba,idan ta kama kuma shima zai karba ya hau ya fita sabgoginsa,kafin ya samu damar siya mata tata.

Sallamar fauziyya kadai a gidan janye da meenal da faggon kaya ya sanya maji cikin matsanancin faduwar gaba,tana fadin cewa sakinta yayi maji ta samu ta daddafa kuiera ta zauna a kai cikin zucivarta tana ian


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" yadda takeji cikin ranta da jikinta a sannan tamkar ita aka saka ba fauziyya ba.


Zaman dai bai sauya zani ba,saima canza salo da fauziyyan tayi, cikin salon wata hikima da iya taku take tatsar kudi daga hannun Mahmud, adadin kudin da ko ita maji wadda ita tasha wahalar kusan komai kawo yanzu bata samesu ba daga jikinsa. Tunda majin ta qyalla idanu ta fuskanci mugun shiru fauziyya ta yi, wanda ya ninka na baya,saboda ayanzun ta samu makiran qawaye gwanaye iya bin malaman tsubbu, sai ta hana kanta sakat da addu'a ba dare ba rana,wanann ya sakawa majin qarfin zuciya da ruhi,duk wani kalar iskanci da fauziyya tayi mata awancan zaman wanna karon ko daya bata dauka ba,wanann ya kawo gagarumin sabani tsakaninta da mahmud, saboda muddin kanason kaga tashin hankalinsa ka taba fauziyya da 'yar lelenta meenal.

Yarinyar Allah ya zuba mata rashin ji na tsiya,zuwansu ba dadewa amma ta fashe duk wani kayan ado da alatu na falon gidan.


Lokaci galilan kuma ta fiddo dabi' ar tara mata qawaye a gidan,sabbin qawaye irinta,wadanda suka bawa duniya amana da dukkan qauna,suka kuma riqeta da kyau,wasu 'yammata ne wasu kuma zawarawa ne kamarta,cikinsu kuma akwai MANSURA wadda tafi kowa zagewa tare da rawar kai.


Da farko falonta ake zuwa a baje,fauziyya ta shiga kitchen cikin taqamarta da jin izza harda yin gayyata ta bare duk abinda takeso tayi musu abincin wadata da alfarma,su bata ko ina a kuma fice abata guri a barta da aiki. Idanunta maji ta rufe, cikin tsayayyar nan tata da dakewa randa suka cika sati guda suna mata tayi musu tasss daga fauziyyan har qawayen,kai fauziyya ta jinjina


"Zakiyi nadama" kamar yadda ta furta kuwa daren ranar majin bata samu cikakken bacci ba,saboda mugun tashin hankalin data haddasa tsakaninta da mahmud,ya gaggaya mata maganganu masu zafi da gori wanda tunda sukayi aure bai taba gaya mata irinsu ba. Ta kwana tana kuka tana kuma gayawa Allah,da safe kuma tayi qoqarin ta tashi kamar komai bai faru ba, abu daya ta sani, ko zasu dawwama suna rikici da Mahmud, ba zata. dauki wasu bagin halayen cin fuska na fauziyya ba,ba ita kadai bama,ace har gawayenta suna da power din shiga mata kitchen suyi yadda sukeso?, bazai yiwu ba, inda ita daya ce zata iya kau da kai, saboda kau da kai da haquri ta sani su kadai ne suka kawota warhaka gidan.


Ba'a jima da gama wannan ba tana zaune da wani yammaci tana gyarawa su toufeeq farce fauziyya ta shigo,tanata baza qamshi hade da taunar chewing gum, tunda taji hayaniyar tarkacen qawayenta na banza marasa da'a ta hada kan yaranta cikin falonta suka zauna a nan


"Key zaki bani" a nutse ta daga kai ta kalleta


"Key na me fa?"


"Na motar yaya na,zan fita unguwa,wani ma yayi rawa bare dan makadi, a bani na mori arziqin dan uwana ko kuma rai ya baci" bacin rai ne ya tasowa maji,yadda take mata magana a tsaitsaye saman kanta,sai ya maida dubanta ga aikin da takeyi


"Bazan bayar ba,rai kuma ya dade bai baci ba,idan kuma kina da qarfin qwata saiki danne ni ki karba"

"Abu me sauqi, kamar qofar dakin naki baqona ne" ta furta tana takawa zuwa hanyar bedroom dinta. Tsam maji ta mige ta kuma daka mata tsawa


"Ke fauziyya!, dakata,kikayi kuskuren shigamin daki wallahi saikin gane sakarya ce ke,ina da kaidi da kuma tuggun da yafi naki ninkin baninkin,saidai kawai banbanci na dake ni din ba jahila bace,nasan sakamakon dake iya biyo bayan aiwatar da sharri tuggu da kuma makirci" tsaiwa tai tana duban idanun maji,ta rasa meye a tattare da matar da har yanzu ta kasa juyuwa a gareta kamar yadda take juya yayanta? ita kadai ce yanzu matsalarta

[02/10, 2:56 pm] Mimah Yusuf: *HUGUMA*


No comments