Tabarmar Kashi Book 2 Page 23

 


Book 02 Page 23






*****Tsaye take cikin kitchen din tana qoqarin rufe lunch bag din fadeela dake dauke da tarkacen kavan beak dinta na makaranta. Sanye take da wata lafiyayyar tattausar abaya sagar dubai, da aka sagata da zare da kuma yadi me tsananin kyau da tsada. Maroon color ce wadda aka yiwa ado da bagi da kuma zaiba a jiki. Daga ciki kuma wani lallausan cotton lace ne maras nauyi wanda aka yiwa dinkin riga me dogon hannu da straight skirt. Daurin kanta ya zauna das sakamakon yadda ta yiwa gashin kanta gammo daga baya ta kuma daura dankwalinta ya zauna mata dass da samfurin daurin dankwalin nan da ake kira zahra buhari. Wani irin tattausan gamshi take fitarwa,wanda ya zame mata al'ada ya kuma kama suturunta da kyau. Turaren wuta na kaya me asalin tsada wanda take samu takanas daga masu abun wato garin mahaifinta BORNO. Wani irin sassanyan kyau tayi a safiyar kyau me ratsa idanu da shiga zuciya,ba tun yau ba shigar laffaya na daya daga cikin shigar dake matuqar qara mata kyau da matuqar da kwarjini, takan koma kamar balarabiya tare da fita a ainihin yarenta na SHUWA-ARAB.


Dai dai lokacin da dukka motocinsa da suke fita zuwa kamfani suka gama komai, fitowarta kadai suke jira, harda toufeeq din dake zaune cikin motar. Sanye yake da wasu kurtas charcoal color da suka dace da farar fatarsa,hankalinsa duka suna kan system din dake cinyarsa yana shigar da wasu bayanai akan meeting din da sukayi a daren jiya shida board members na sabon kamfaninsa da zai fara aiki wata me kamawa, dai dai lokacin da yake sanya ran ya kammala da kamfanin MT JARMA. Ta cikin eye glasses dinsa ya daga agogon hannunsa daya kwanta luf cikin gargasar data zama tamkar rumfa wa fatarsa vana duba lokaci. A galla sunyi zaman jiran mintuna goma kenan zuwa sha biyar,baya cikin tsarinsa bata lokaci da saba lokacin zuwa aiki,gashi tana son zama silar haka a ranar farko. Qaramin tsaki yaja yana ajiye system din, sannan ya buda gofar side dinsa a hankali yana zura gafafunsa waje. Da sauri elyas ya matso,sai ya daga masa hannu,ya fahimci me yake nufi don haka ya koma da baya yaci gaba da tsaiwa a gurbinsa.


Har ya sako daya qafar ya hangi tahowarsu,fuskokinsu gaba daya cike da wani irin walwala da annuri ita da fadeelan, tana riqe da lunch box din fadeelan,ta kuma rataya school bag din nata still a daya kafadar, daya hannun kuma na riqe da hannun yarinyar. Sak suka fito a 'YA da UWA,wani abu ya taba zuciyarsa ya kuma tuno masa shekarun baya,a lokacin da yake da shekaru kwatankwacin na fadeelan,lokaci da maji ke riqe hannuwansa kamar haka ta kaishi makaranta sannan ta wuce gurin nata aikin. Anutse ya zare idanunsa daga kansu,ya maida qafafunsa cikin motar tare da jan murfin motar. Karo na biyu idanunsa suka sake sauka a kansu. Dai dai sanda ta zame hannunta daga na fadeela tana gyara yafen lafayar jikin nata,zara zaran yatsunta da aka sakawa lalle a jiya suka bayyana hakan sai ya tuna masa da wani lokaci can baya, ranar farko data mige cikin taron ma'aikata kamfani don ta gabatar da nata aikin. A ranar dukkan wanda ya kalla cikin mazan dake hall din idanunsa vana kanta, daya bayan daya ya dinga bin fuskokinsu da kallo ba tare da sun sani ba,haushi da takaicin da ya sanya yace ta hada file din kenan zai duba a gida ko office ba tare data garasa cinye mintuna goman da suka rage ba.


A yau ma sal ya samu kansa da sauke dubansa saman fuskokin guards din nasa dake tsaye suna dakon fitowarta. Daya bayan daya yake nazartarsu,sai ya janye idonsa yana furzar da iska daga bakinsa. Kusan mutum biyar a cikinsu idan idanunsa sun gaya masa dai dai kamar ita yaga suna kalla. Jamal daya daga cikinsu ya hanga yana gyara tsaiwarsa tare da gyara zaman glasses dinsa. Haka kawai yaji wani abu me nauyi yana sauka a hankali saman qirjinsa. Jamal na daya daga cikin mazan da Allah ya jarabta da son mata,mutum ne me yawan kule kule, abinda ya sanya tasu sam batazo daya da toufeeq ba. Kusan sau biyu yana dakatar dashi kafin ya samu ya maida hankalinsa ya kuma dai daita kamar yadda tsarin duka yaransa suke.


"Madam…madam" muryar adama daya daga cikin

masu aikin dake aiki a sassan hajiya qarama ta ziyarci kunnenta. Cak ta tsaya tadan juya kadan har adama ta


qaraso

"Abincin makarantar fadeela ne......inji hajiya qarama" ta fadi a ladabce. Sosai ta kalli qawatacciyar lunch bag din dake rige a hannun adama, mamaki yana sauka a ranta.


Yaushe har aka canza tsarin baiwa fadeela abincin makaranta?, lallai da gaske matar nan take, qaramin murmushi ya subucewa fuskarta wanda ya sake qara bayyana kyanta


"Ki gaya mata ummarta ta riga ta tanadar mata komai" ta furta tana daga mata lunch bag din hannunta. Kalla adama tayi saita juya tana komawa ciki. Saita juya tana ci gaba da tafiya tare da jan siririn tsaki, tsanar matar yana samun gurbi cikin zuciyarta.


Idonsa ya dauke daga kanta yana lumshesu,yadda ta juya tsukakken bakinta da yasha Marron lipstick yana wulgawa ta cikin idanunsa,ya rasa me yasa tsiwa take mata dadi,idan tayi tsiwar kuma sai ta sake maidata kamar wata qaramar yarinya.


Tun kafin ta garaso tayi noticing motar da yake ciki,don haka sai ta tsaya daga motar da aka kebe saboda kai fadeela makaranta da kuma sauran uzurorinta, budewa fadeela gaba tayi,ita kuma ta shiga seat din baya.


Jibril ne ya duga vana rufe motar sannan ya zagayo yana gogarin tashinta


"Madam tace zamu fara sauke fadeela a makaranta sannan mu wuce" jibril ya fada cikin girmamawa. Mamaki ya kamashi, me kenan?, bayan yarinyar nada driver?,so a lokacin bashi da lokaci dogon surutu,don haka ya gyada masa kai kawai,motocin suka fara tashi a nutse suna ficewa daga gidan.


Sanda security na gidan ya kammala rufe qofar bavan fitarsu a sannan hajiya garama ta garaso farfajiyar gidan a birkice, cikin matsanancin fushi take bin shatin tayoyin motar da kallo


"Uban waye yace ki dawomin da abincin saboda ta fadi haka? me yasa baki tsaidasu ba kin kuma shaidamin kafin fitarsu daga gidan?"


"'Kiyi haquri hajiya,ban zaci...." Kyakkyawan mari ta sauke a fuskar adama tana wani irin huci,wanda hakan da tayi dai dai yake da haushin kaza huce kan dami. Har ta buda baki zatace wani abu sai kuma ta fasa,saboda koma meye yanzu zata fada din bashi da amfani, saboda komai ya riga ya ruguje, amma tabbas ba zata taba bari komai ya tafi a banza ta ruwan sanyi haka ba. Tana takawa cikin qida take gava mata


"Ki cewa bala va shirya nan da awa daya zai kaini

makarantar su ukhtie " bata tsaya jiran amsa ba tayi

gaba cikin tsananin fushi.


A kan idanunsa yana ganin sanda ra budewa

fadeela gofa ta rataya mata jaka da lunch bag dinta,ta

tsugunna tayi kissing dinta ta kuma rada mata wata

magana dashi kansa baisan me tace mata ba,fadeelan ta

doso motarsu,ganin haka ya sanyashi bude murfin motar

tun kafin ta garaso. Murmushi fal saman fuskar

yarinyar, saboda hirar da sukayi da säahar din cikin

motar, tana jaddada mata daga yau itace zata dinga

kawota tana kuma maidata gida. Kidding goshinta yayi

sai tace


"Yau abby ka rakoni makaranta, inajin dadi sosai "

hannunta da a yanzu suka zama masu kauri ba kamar a

baya ba ya kama yana murmushi ya jinjina kai, sai ya

sanya hannunsa saman kanta ya shafi kan


"'Barakallahu fiik, ayi karatu da yawa" hannu ta daga

masa tana masa bye bye, idonsa ya sauka akan motar

fadeelan, säahar ta koma ta zauna cikin motar,har

fadeela ta juya ya kirata


"Angel" sai ta dawo da sassarfa,ya danyi shuru yana juya

maganar a ransa,bayason ya fadi ta dauki maganar da  wata manufa daban,haka kawai cikin zuciyarsa yakejin bai dace su zauna mota guda daga ita sai driver ba,yayi gogarin hana kansa gain baiken hakan amma ya kasa,idanunsa nata sake dawo masa da irin kallon da ya gani daga idanunsu jamal a dazu


"'Kije ki gayawa autynki ta dawo wannan motar".

Shuru tayi tana duban fuskar fadeela sanda take gaya mata saqon toufeeq din, kafin takai ga yin komai fadeelan ta dauki handbag dinta tayi gaba da sauri tana cewa


"Nima bari na tayaki aunty" bata da sauran zabi illa bude murfin motar da tayi ta fita a hankali tabi bayanta.


A nutse ta zauna elyas ya maida murfin ya rufe, qamshinta ya mamaye motar,ta gyara zamanta sosai tana maida dubanta ga bakin qofa sannan tace


"Good morning" a taqaice, saidai ko uffan bataji yace ba.


Ranta ya baci sosai, ba abinda a yanzun yake takura mata irin wannan gaisuwar data zame mata qadangaren bakin tulu,idan tayi ya amsa mata da qyar,idan kuma bata yin ba tana tsoron abinda ya furta zai aikata mata.


"'Good morning" ta sake fada adan qufule, idanma bata maimaita ba tasan tsaf zaice bata gaidashi ba. Dukka gaisuwan nata yaji sarai, amma yadda ta juya baya tana fuskantar gofar sannan ta gaidashi kamar dole ya bashi haushi, yadan dauke idanunsa daga kan system din ya aza mata su


"Wani ne yace dole saikin gaidani?, ki riqe kayarki bana so daga yau,don ba qanfar gaisuwa nakeyi ba,na saka miki dokarta ne saboda na saitaki kan abinda ya dace" daga haka ya maida dubansa ga allon system din. A yau din karon farko taji jikinta ya sanyaya da yadda yayi mata magana,babu wannan fadan Sam cikin muryarsa sai wani irin softness har cikin ranta taji abun bai kamata ba,don haka ta gyara zamanta da kyau tana dan fuskantarsa


"Barka da asuba" fa furta itama da sanyin muryarta.

Tsigar jikinsa ne yaji ta zuba,ya daga idonsa a nutse sai suka hada ido,kowannensu ya janye dubansa da sauri


"Barkanki"



"An tashi lpy"


"Alhamdulillah" ya fada ba tare da ya sake dubanta ba, daga haka ta rasa abinda zata sake fade, saita ja bakinta tayi shuru tana maida dubanta ga hanyoyin da suke ratsawa da gudu.

[21/09, 9:16 am] Mimah Yusuf: "HUGUMA*


No comments