Tabarmar Kashi Book 1 Page 59-60

 


Page 59



    "na samu aiki abba.....amma ba irin aikin da kuke tunani zanyi ba,aiki ne na kula da mara lafiya"


"Kula da mara lafiya kuma?" Ya tambayeta cikin mamaki,kai ta jinjina


"Banda abinki ummi,ai ba sai kinyi da kanki ba,idan kikayi bayani,sai na biya a daukowa mara lafiyan me kula dashi har zuwa sanda Allah zai bashi lafiya" kai ta girgiza alamun a'ah


"Ba jinya bace ta kullum kullum da ake kwance ba,abba yarinya ce marainiya,wadda take fama da epilepsy,tana buqatar kulawa ta wasu watanni daga gurin tsayayyar nanny da zata iya kulawa da ita da kyau"


"Ikon Allah" kawai dr mamman ya fada,ya gyara zamansa yana kallon sãahar din,abinda ya bata damar dorawa


"Zanyi aikin nan abba idan lamuncemin,bawai don neman kudi ba,sabida babu abinda na rasa daga wajenku,zanyi ne kadai saboda kwadayin lada wajen Allah,wanda na tabbatar hatta ku zakuyi tarayya a cikinsa,don Allah abba ka lamuncemin,haka kawai na tsinci kaina cikin kwadayin wannan ladan" kai ya gyada,maganarta gaskiya ne,saidai abun ya masa banbarakwai,diyarsa da aikin nanny a wani gidan?.


"Duk maganarki haka take,to amma banda abun ummin abba,ko biya kikayi akayi kina da wannan ladar ai" zamanta ta gyara


"Abba suna da wadatar da zasu iya biyan kowanne mutum,amma kudi basa iya taba siyan nagarta da cancanta" kai ya jinjina cikin dogon nazari


"Abba bazan jima ba,tana samun lafiya shikenan" ta yanke masa tunaninsa ta hanyar fadin haka. Dole murmushi ya kubce masa saboda yadda tayi maganar cikin kwantar da murya tana langabe kai,da alama da gaske har cikin zuciyarta takeson tayi aikin.


"Shikenan,kiban address,zan sa fahad ya yimin bincike akan nagartar mutanen gidan,don bazan bawa wani cikin yayyenki bama" 


"Kana iya tambayar anty farheen,ita ta fara bincikawa ma, neighbors na qawarta ne,kuma Alhmdlh basu da matsala,shi yasa aikin ya sake kwanta min a raina" fadin farheen din ya sake sanyawa hankalinsa ya dan kwanta


"Zan nemeki" ta miqe tayi masa sai da safe ta wuce sashensu.


      Washegari da safe taga sauyin fuska daga wajen maama,sai tasha jinin jikinta,abban yana fita kuwa ta kirata,sababi ta fara tare da gaya mata itakam bataga dalilin wannan aikin ba,sosai ta kwantar da kai tana kwatanta mata amma maama tayi biris. Wuni guda ana abu daya har dare,shima abban ya gaza shawo kanta,sai da tayi kiran afifa. Itama afifan qin zuwa tayi da farko,ko da tazo dinma sai ta hadasu duka ta fatattakesu,daga bisani afifan tabi bayan maama,batasan ya suka qarke ba,tadai shigo tana harararta


"Burinki ya cika new nanny" murmushi me kyau ya subucewa fuskarta,yadda tayi maganar ya tabbatar mata da ta shawo mata kan maama,saita rungumeta tana cewa


"Allah ya barmin bestie na" murmushi itama ta saka 


"Ba wani dadin baki fa,bawai ance kije ki manta da mahmud ba" baya taja tana hade rai,afifa ta bita da kallo tana jan qwafa,itadai batasan sai yaushe sãahar zata dauka daga kan wannan aqidar ba,tana addu'ar Allah ya kawo mutumin da zai sauya wannan tsattsauran ra'ayin nata.


*****Cikin takun nan nasa me cike da tsantsar qasaita da kuma wani irin aji suke nufar sassan hajiya qarama. Sanye yake da yadin baby cashmere me tsada dan qasar indai,wanda aka tsarawa wani irin dinki shi ba dinkin suit ba hakanan ba style na Pakistan ba,sosai dinkin ya qara masa kyau da kwarjini,ya kuma fidda qirar jikinsa qwarai dake dauke da siffar qarfi,duk inda ya gifta sai ya bada ajiyar sassanyan qamshin turarensa me masifar tsada daya sanya qamshin baya bajewa da wuri. Hnunsa riqe da siririn hannun fadeelan suke takawa zuwa sassan momy qarama,daga kan fuskarta har idanunta shabe shabe suke da hawaye,wanda rabi na shagwaba ne,rabi kuma tana ji har cikin zuciyarta yadda zatayi kewar mahaifin nata. Qasa qasa yake magana da ita tamkar wata babba


"Calm down my angel,ipad dinki na wajen momy qarama,nayi alqawarin kiranki kullum through video calls,i will do my very best na dawo da wuri,new nanny dinki na nan zuwa" kafada ta maqale tana zirara da hawaye


"Nikam banason wata nanny kuma,kai zanbi" murmushi ya saki saman miskilar fuskarnan tasa,sai ya sanya hannuwansa ya dagata ya azata zuwa kafadarsa yana ci gaba da takawa hadi da lallashinta cikin hikima. Duk duniya ita daya yake iya tsaiwa ya lallasa haka,banda a kanta,baisan koda hanyar yadda ake rarrashi ba.


      Suna shiga falon momy qarama na fitowa daga kitchen,hannunta riqe da mug dake cike da tea


"Badai har ka fito ba?" Agogonsa ya duba yana amsata


"Am ready to go,banason na wuce haka kada nayi missing flight"


"Gaskiya ne" ta fada tana neman wajen zama,sai shima ya zauna saman daya daga cikin qawatattun kujerun dake falon


"Na sanya jibril yayi magana da mutanen can,za'a kawo food stuff,idan akwai abinda babu ki gaya musu kawai,zan saka elyas yayi transfer ta account dinki,naki ne keda fadeela,shikenan koda wani abu?" Qasaitaccen murmushi ta saki,a duniya idan akwai wadda ta shigo rayuwa a sa'a to tana cikin sahun farko na jerin wadan nan matan,tana jin dadi,kanta kuma yana sake fasuwa a duk sanda toufeeq ke treating nata haka


"Eh to,batun nanny din fadeela ne,yau in sha Allah zatazo,wannan karon ina saka ran an samu wadda zata iya kula mana da fadeelan in sha Allah,duk da naso ka ganta kafin ka wuce" miqewa tsaye yayi


"Ba damuwa,indai tayi miki fine,just ta kula da aikinta shine abun buqata,and then ta fadi nawa takeson salary dinta,every month ko qasa da haka,duk ba damuwa indai zata kula da qa'idoji da sharuda" 


"Karka damu in sha Allah" tare suka sake fita da fadeelan,still tana maqale dashi. Kuka ta saka masa sosai security dinsa ya buda masa motar ya shiga,sai da yasa akayi kiean baaba ramatu,da wayau da dabara ta rabata da gurin tana kuka.


      Har suka fita a gidan yana jin sautin kukanta cikin kwanyarsa,ya lumshe manyan idanunsa da suka sauya launi saboda wani bacin rai daya sokeshi,sannan ya budesu sosai yana jin wani ciwo cikin ransa,sam wannan ba itace kalar rayuwar daya tsarama kansa da kuma 'ya'yan da zaya haifa ba,wannan din wata bahaguwar rayuwa ce da qaddara ta tsago da ita cikin nasa shirin da tsarin ta kuma wargaza komai


"AMEESHA" sunan da bazai taba gogewa cikin tarihin rayuwarsa ba,koda ace ya fita daga zuciyarsa da dukkan wani abu daya danganceshi. Cikin hanzari ya watsar da tunanin,ta hanyar ciro wayarsa ya laluba wata number da yayi alqawarin kira ya kira din,ya fara amsa wayar cikin wani irin sanyi bayan ya maida bayansa yayi relaxing a jikin kujerar.


     Koda ya gama wayar shuru yayi yana juya wayar a hannunsa,kamar wanda take sabuwa ga idanunsa ranar ya fara saninta,yau din gaba daya duk wanda ya kalleshi yasan yanayin komai ne cikin sanyi,yanayin da sam bashi a halittarshi.


     Tsaiwar motocin ya janye hankalinsa,ya daga kan nasa yana duban driver dinsa


"What's happening?"


"I don't know sir,but.... lemme check" ya fada,sai driver din ya bude ya fita ya barshi shi da guard dinsa guda daya dake zaune a gaban motar.


      Ko minti uku baiyi ba ya dawo da gaggawa


"An samu matsala sir,harith ne ya bige wani tsoho......" 


"Ya salam" ya furta da sauri,ba tare da ya bari ya kammala bayaninsa ya bude qofar motar da kanshi ya sanya qafafunsa ya fito wajen,cikin sakanni guard dinnasa dukka suka fito suka take bayansa.


     Har a sannan tsohon yana zaune a qasa yanata bala'i,harith din da wadanda suke mota daya suna tsaye a kansa. Tsawa daya ya daka musu cikin bacin rai dukkansu sukaja baya suna sunkuyar da kai,ya ratsa ya tsakaninsu ya isa gaban tsohon,ya duqa zai dagoshi suka matso da nufin karbarsa,ya daga musu hannu alamun dakatarwa,ya tsugunna gaban tsohon bayan ya tadashi sosai.


"Kayi haquri baaba,am very sorry,bada niyya bane na tabbatar,amma kayi mana afuwa gaba daya" dukka wani fushi da fada daga dattijon sai ya sauka,saidai idanunsa suna zube cikin na toufeeq din yana kallonsa,ya saki ajiyar zuciya


"Shikenan,ba komai"


"Ina fata baiji maka ciwo ba ko?" Ya sake fada yana kamashi ya miqar dashi ya tayar dashi tsaye yana kade masa jiki,cikin matuqar martaba da mutuntawa,duk da alamu da suka nuna babu wani sukunin rayuwa me yawa tattare da tsohon


"Ba komai yaro,banji ciwo na,buguwa ce kadan a hannu na"


"Dole a dubaka kada ya zame maka matsala baaba" cancel din mota daya yayi cikin jerin gwanon motocin,yace su miqashi asibiti a dubashi,sannan su kaishi ga iyalinsa, yayi kiran elyas da hannu,y qaraso cikin girmamawa,ya gaya masa abinda yake da buqatar a bawa tsohon


"Okay sir" ya fada a ladabce.


"Yaro!" Yaji muryar tsohon ta kirashi dai dai sanda yake shirin saka qafafunsa a motar,ya tsaya cak ya waiwaya yana dubansa


"Ban taba tsammanin mutum me arziqi har haka zai iya tsaiwa ya saurari talakan da bai mallaki komai kamata ba,na gode qwarai da karamcinka,a duk lokacin da kaji tasowar fushi daga zuciyarka,ka yawaita ambaton A'UZUBILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM, HASBUNALLAHU LA ILAHA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBUL ARSHIL AZEEM" Shuru toufeeq yayi yana kallonsa har ya shige motar harith ya rufe,ya zagaya ya tayar da motar


"Sir..... it's getting late,we should leave" jikinsa a wani irin mace ya shiga motar yana maimaita kalmomin da dattijon ya gaya masa,daidai sanda jibril ya rufe qofar kira ya shigo wayarsa


"Maji" sunan daya bayyana kenan wanda furtasa ya hade masa da faduwar gaban da baisan dalilin saukarta ba.


      Tattaro dukka nutsuwarsa yayi sanda motar ke dagawa ta dauki hanya sosai,cikin muryar da ita daya duk duniya yakewa magana da ita,duk da baisan hakan yana faruwa ba yayi mata sallama,sannan ya gaidata,ta amsa masa da wani irin kulawa


"Ina fadeela tah?" Ta tambayeshi a sanyaye. Wani nauyi yaji ya saukar masa,ya shirya yana hanyar barin qasar,tun da bai shaida mata ba sai a yanzu?,a yanzun ma da itace tayi kiranshi?,yaya zataji idan ya gaya mata hakan?


"Ko baka gida nayi kira da layin da zan sameta?" Ta jefa masa tambayar. Sosai nauyi ya sake kamashi,ya sani tana da wancan layin na baaba ramatu,to amma takan tsallake kowa tayi kiransa koda lokuttan da take da yaqinin baya tare da fadeelan,tun da jimawa ya fahimci tana hakanne don taji tasa muryar da lafiyarsa,tunda har yanzu hannayenta sun gaza iya koyar daukar wayar suyi kira a nata lambobin da layin domin suji lafiyarta,koda wasa.....koda sau daya......koda da gwaji. Wani al'amarine da yake damun qwaryar zuciyarsa qwarai cike da wata irin damuwa,amma ya gaza ta kowacce fuska.....ya gaza kawo gyara koda qanqani ne.......sau tari yanajin naqasu,gazawa da kuma kasawa,hadi da wata cikakkiyar tayawa me wawakeken girma daga rayuwarsa,amma baisan ta yadda zai gyara ba.....ta ina?,kuma a yaushe?,rashin matallafine ko kuwa?,duka shima bai sani ba.


"Allah ya kiyaye,ya tsare, ubangiji ya bayar da dukka sa'a da kariyarsa,fatan alkhairi" ta fada a taqaice ta kuma gimtse wayar.


     Wani abune ya sauko ya daki zuciyarsa,take tayi wani irin rauni,yanajin wata irin kunyarta na mamayarsa, kunyar da dukka d'a na qwarai yakeji a lokacin da yayi wani abu na sabawa ga iyayensa,duk da a karan kansa yasha gayawa kansa shi din ba na gari bane......yanajin wani irin karyewa a tata muryar,kamar wadda kuka ke shirin subucewa,amma duk yadda yaso ya juya zuciyarsa ta bita don taji meye damuwarta ya kasa,sai ya soke hannayensa guri guda yana matsesu da wani irin qarfi,kamar yana shirin ballasu.


?????? Kebantacce falo ne wanda ke dauke da wasu qasaitattun kujeru da suka zama cikamakin cikar adon falon,bashi da wani girma,amma yana da tsari me matuqar kyau tare da jan hankalin me kallo.


      Saman daya daga cikin kujerun falon sãahar ce zaune,cikin kamilalliyar shigarta ta jilbab,wanda yake hade da doguwar rigarsa me dogon hannu,gefe da gefe na dan qaramin hijabin madin rigar a tsage yake,an masa wani irin ado daga bakin tsagar,farar kyakkyawar fuskarta ta fita sosai ta tsakiyar fuskar hijabin da wani irin kwantaccen kyau me daukan hankali.


     Tun farko shigowarta gidan take nazarinsa daya bayan daya,ta kowacce fuska gidan ya amsa sunansa,ya kuma sake bayyana mata tarin dukiya tare da arziqin da masu gidan suka mallaka. Ta taso cikin gata soyayya kulawa tsakiyar nasu arziqin da dukiyar,tun daga kan mahaifinta zuwa yayyenta,hakanan dangi na mahaifi da mahaifiya,amma a yau daya,cikin mintunan da basu gaza goma ba kanta yana shirin kwancewa ta zama 'yar qauye cikin gidan.


     Ba iya wannan ba,ta lura akwai tarin doka da bin tsari daga dukkan ma'aikatan gidan,kula gami da takatsantsan da tsoron kaucewa qa'ida,tun daga mai gadi,zuwa wadda ta rakota qofar sassan hajiyar gidan,kawo wadda ta kawota wannan falon da take zaune a yanzun tana jiran isowar matar,don ta ganta ta kuma karbeta gami da sake mata bayanin aikinta cikin gidan.


     Wayarta na hannunta a lokacin tana shaidawa afifa ta iso,afifan da tace sam ita ba zata iya rakota ta ganta a bigiren 'yar aiki ba,saidai duk da haka batayi fushi ba,tana maqale a online tana bibiyar dukka motsin bestie din tata.


      Qarar takalmin da ya fara ratso falon yaja hankalinta,saita kashe data dinta,ta kuma ajjiye wayar tsakanin qafafunta,ta daga kai tana aje dubanta daga guraben da sautin tafiyar yake fitowa.


      Guri guda idanunsu suka hadu nata dana hajiya qaramar. Daidaita kallonta ya sakeyi kan fuskar sãahar duk da bata kai ga qarasowa gurin ba,wani abu yana sauka a zuciyarta,tanason ta karanceta irin karatun kallon farko,tanata qoqarin daidaita zuciyarta da taji kamar ta tsaya guri daya,ta gaza wanzar mata da kowanne feeling akan sãahar din,ba kamar yadda takanji ba akan sauran dukka nannys din fadeela na baya da sukabar gidan.

[02/09, 3:47 pm] +234 810 324 4136: Page 60


*H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??


Page 60


     Cikin takunta na qasaita da nuna isa ta qaraso,ta dauke filon dake saman kujerar dake fuskantar sãahar din ta zauna,tana maida filon saman cinyarta,bayan ta dora qafarta daya saman daya


"Sãahar ko?" Hajiya qaraman ta jefeta da tambayar sunanta kai tsaye,kai ta gyada mata cikin tabbatarwa gami da furta


"Eh nice,barka da yamma"


"Barka kadai" ta amsa mata tana qare mata kallo a fakaice,zuciyarta cike fal da mamaki irin sassanyan kyan da yarinyar ke dashi,babu alama ko digo dake nuna wahala ko buqata daga jikinta,asalima ko ita din sãahar din fatarta tafi tata nuna jin dadi da hutu,to amma ta wani bangaren tasan zata samu nutsuwa,zata samu sauqi itama,ilimi zallah ya nuna kansa tattare da sãahar din.


     Gyara zamanta tayi tana sauke qafafun nata,har yanzu idanunta akan fuskar sãahar din,kyanta yana sake bata mamaki


"Nasan mrs sadeeqa ta gaya miki komai,so amma koda zata gaya mikin ba komai zata iyayi miki bayani ba kamar yadda ni zanyi miki.....da farko kina iya kirana da hajiya ko hajiya qarama ko mommy qarama,kusan nice shugabar gidan nan,kowa da kika gani ya kwana ya tashi cikin gidan nan qarqashin ikona yake,hatta dashi me gidan kansa da abinda ya mallaka ya kuma haifa......aikinki guda daya ne tal cikin gidan nan,kula da jikata tamkar ke kika haifeta,munason ta samu kulawa fiye da yadda zaki bawa kanki kulawa,saboda yanayin ciwonta,bamason kiyi nesa da ita,saidai idan tayi bacci ne, kuma koda kin koma naki dakin zakici gaba da dubata ne gudun faruwar wani abun,wankanta da tsaftarta yana wuyanki,abinda zataci kuma wannan ba dolenki bane" sai Tayi shuru tana maida numfashi. A nutse sãahar ta daga kai tana dubanta tare da nazarin kalamanta,wanda suke cakude da sautin izza a cikinsu


"Fadeela.....ita daya muke da ita,itace sanyin idaniyarmu,farincikinta shine namu, sabawa daya daga cikin ayyukankin nan suna iya zama silar rasa aikinki" ci gaba kawai sãahar tayi da nazarin mommy qarama tana kuma kallonta


"Kin fahimta?" A nutse kuma a hankali ta gyada mata kai


"Da kyau,gidan nan yana da tsari,bawai zama bane kamar na sauran gidaje da kika sani,abu na gaba kowa aikinsa ya sanya a gaba,ba ruwan wani da shiga sabgar wani,ban yarda da zama tsakanin ma'aikata ana hira ba,kowa yayi abinda ya kawoshi ya wuce mazauninsa" shuru ta sakeyi tana kallon yadda sãahar ta kame,ta kuma bata hankali tare da manyan fararen idanunta tana kallonta


"Magana ta qarshe" ta furta tana zama serious sosai


"Nasan kinsan kalar ciwon da yake damun shelelenmu,right?" Kai ta jinjina tana ci gaba da sauraronta


"Yauwa,akwai magunguna da takesha,so gaskiya banason yawan qwayoyin da yake yawan bata,saboda haka duk lokacin da ya dace tasha magani zan shaida miki,kota waya,ko na tako har zuwa sashen da kaina,ban yarda ba ko sau daya ki dauki magani ki bata ba tare da sanina ba" wanann maganar ita ta zowa sãahar din a hagunce,sai ta gyara zamanta itama,ta kuma dora qafarta daya saman daya ba tare da tasan tayi hakan bama


"Amma why not ki yiwa likitan magana,idan zai yiwu da kansa zai fada,zai kuma rage mata,idan wasu kuma za'a yi exchanging dasu duka zai fadi"


"Look!" Hajiya qarama ta fada tana fidda idanunta waje


"Ina cewa ko minti biyar banyi ba da gaya miki rule's na gidan nan,who are you da zaki shiga lamarin da bai shafeki ba daga zuwanki?,na gaya miki hakanne don na taimakeki,bijirewa hakan zai iya shiga list na dalilan rasa aikinki" mamaki ne ya kama sãahar,tadan yamutsa fuska kadan tana juya maganar a ranta,kaf cikin maganar bataga inda tayi wani lafazi da bai dace ba


"Ke ba kowa bace face nanny da zatayi aiki a biyata" zuciyarta da kwanyarta suka tuna mata matsayinta cikin gidan,sai ta zame qafafunta data dora saman na juna a hankali lokacin da taga hajiya qaraman na kallon yadda ta hade qafafun


"Am sorry,zan kiyaye in sha Allah"


"Kin samawa kanki lafiya" ta furta tana sake tsuke fuskarta,saida can qasan ranta tana cike da mamakin yarinyar,kwata kwata batayi kama da masu aiki ba,koda kuwa makaho ne ya shafa zaiji hakan,duk da sun nema well educated amma kuma wannan kamar ajinta ya d'ara wajen.


      Waya ta dauka tayi kira na qasa da second goma sha biyar,cikin minti daya tak matar ta iso,daya daga cikin masu aikin gidan,wanda basai ka tambayi hakan ba,saboda uniform da take sanye dashi,ta rusuna cikin girmamawa


"Sabuwar nanny din uktie,a kaita sassansu,ki damqata a hannun baaba ramatu"


"An gama ranki ya dade" ta fada cikin rusunawa,luggage din sãahar din ta dauka tayi gaba,don dukka nanny din data kasance ta fadeela ce a gidan,tana samun wani respect da kyautatawa darajar fadeelan,wannan haka tsarin gidan yake.


      Har takai qofa momy qarama na rakata da kallo,batasan me yasa yarinyar ke jan hankalinta har haka ba,yadda take takunta a nutse daya na bin daya kadai yana nuna mata kamar akwai wata extra qasaita a jinin yarinyar


"Sãahar" ta kirayi sunanta da dan kaushi kadan,dakatawa tayi sannan ta waiwayo tana dubanta


"Mrs sadeeqa nada matuqar kirki,tana kuma da darajar da zata baki dukkan wata kima da martabawa a gidan nan,ba tare da ko na miki screening ba na dauki aikin kula da 'YAR SO na baki,ki kula da kyau,kada kuma ki gota iyaka" har yanzu kalaman matar basu daina bata mamaki ba,sai ta saki wan siririn murmushi ta jinjina kai kawai,sannan ta juya a nutsenta tana barin falon,tabi bayan ma'aikaciyar.


       Kamar ko yaushe katafaren ni'imtaccen falon nasu a tsaftace yake sannan killace,iskar na'urar sanyaya daki tana busawa ta kowacce kusurwa na falon tana cakuda da qamshin fresheners.


      Sau biyu me aikin tana sallama kafin qofar glass ta falo na biyu ta bude,baaba ramatu ta fito cikin kamalarta da carbi a hannu,da alama tana azkar din yammaci ne


"Qaraso mana,ke da baquwa ce?" Tayi tambayar idanunta akan sãahar dake tsaye a baya


"Nanny din fadeela ce hajiya tace a rakota" juyawa baaba ramatu tayi tana duban sãahar,sai kuma ta sakar mata murmushi


"Maraba,sannu da zuwa,Allah yasa tana jin hausarmu" tayi maganar cikin tantamar sãahar din tasan zo na kasheka da hausa. Murmushi ne ya subucewa sãahar din,karon farko tun shigowarta cikin gidan,yadda dattijuwar tayi magana cike da barkwanci yana burgeta


"Ina yini?" Ta fada a nutse don kore shakku daga zuciyar baaba ramatu,a mamakance riqe da baki t juyo ga sãahar


"Ma sha Allah,lafiya alhamdulillah,sannu da zuwa"


"Yauwa sannu" ta maidawa baaba ramatu


"Shigar mata da kayan nata ciki,dazu dazu aka kammala kintsa dakin muje ko 'yata?" tayi maganar da sakakkiyar murya tana yi mata jagora ga tsararren hallway din da zai sadaka da dakunan baccinsu.


     Daya daga cikin qofofin dake kulle baaba ramatu ta tura ta shiga tana cewa sãahar


"Bismillah" sai tabi bayanta,bakinta dauke da addu'ar shiga sabon guri ko zama a baqon guri. Daki ne me yalwa wanda yake dauke da qawatattun kayan gado 'yan asalin qasar turkey,komai na dakin kwantacciyar kalar yellow green ne me kyau da daukan hankali,kalolin dake qarawa idanu qarfin gani,dakin nada wani irin tsari me burgewa,bai cika girma ba,hakanan bai cika qanqanta ba.


"To ga dakinki nan,idan kina da buqatar wani abun kina iya magana a kawo miki,aikinki kawai ki kula da fadeela" baaba ramatu ta fada cikin murmushi. Murmushin itama tayi


"Bana buqatar komai,amma ina ita babyn?,inaga ita ya kamata na fara gani ko?" Qaramin murmushi ya sake sauka a fuskar baaba ramatu,haka kawai kallon farko taji sãahar tayi mata,fadeelan bata tana nanny irinta ba,yawancinsu tun daga hanyar shigowarsu gidan zuwa hanyar isowarsu dakin suke rudewa da kalle kalle da kuma santin tarin dukiyar dake jibge a gidan,hakanan duka cikinsu babu wadda ta taba tambayar a kaita gurin wadda tazo gidan aiki dominta,har sai baaba ramatun ta buqaci hakan


"Tana dakinta,tun dazun taqi fitowa rigima takeji,tunda babanta yayi tafiya dazun ya barta take fushi da kowa harda ni dana daukota daga waje,ko abinci taqi ta karba" baaba ramatu ta fadi tana dan dariya.


      Kai sãahar ta girgiza tana dan murmushi


"Ayyah,tana kewarsa ne tun yanzu,muje na gani ko zata yarda ta fito" gaba baaba ramatu tayi tana dan yi mata hirar fadeelan,yadda halayyarta da dabi'unta suke. Qofar dakin dake facing ta sãahar din baba ramatun ta tura ta bude, tsararren dakinta cikin kalolin white cream ya bayyana,wani irin daki da yafi kama da dakin hamshaqiyar mace me aure,dakin dake aka sanya masa dukkan wani abu na buqata jin dadi da kayan qawa,wanda hakan bai sanya ya cika tarkace da yawa ba,sai wani irin kyau da tsari na musamman daya bayar,ga tasirin tsafta sosai a tare dashi,ko ina qal qal yana fidda qamshi me dadin gaske.


"Fadeela" baaba ramatu ta ambaci sunanta sanda suke shiga dakin. Tana nade cikin duvet,ko motsi batayi ba


"Ki tashi ga sabuwar me kula dake tazo ganinki" kafadarta ta maqale,ta kuma bubbuga qafafunta


"Bana sonta" idanu baaba ramatu ta zaro waje tana kallon sãahar cikin rashin jin dadin kalaman fadeela,sãahar din da siririyar muryar fadeelan ta sanyata dariya tare da qarin dariyar zallar quruciyar data fuskanta tattare da ita


"Kul na qarajin kince bakiso wani,bakya sonta?"


"Eh ta koma,saboda nima daddy ya tafi...." Ta fadi tana yaye duvet din da sauri,sai kuma ta tsaya cak tana rarraba kallonta akan fuskar sãahar dake jifanta da murmushi. A hankali ta zame duvet din duka daga fuskar tata tana ci gaba da kallon sãahar.


     Waiwaya sãahar din tayi ta kallo baaba ramatu


"Baaba a kawo abincin nata" 


"To shikenan" ta fadi tana juyawa ta fice daga dakin,cikin ranta tana jin cewa sãahar din zata bada fiye da abinda ake zata.


     Bata taka ba taci gaba da kallon fadeela tana murmushi,har sai da yarinyar ta miqe ta zauna sosai da kanta,sannan ta sauke hannuwanta ta taka zuwa bakin gadon ta zauna daga gefanta


"Kiyi haquri" sãahar ta fada tana kallonta,tana iya ganin sanda ta waiwayo da sauri tana kallonta,saita sake mata murmushi


"Ummmm"


"Ba abinda kika yimin fa amma kike cewa nayi haquri"


"A'ah,kince bakya sona,na dauka nayi miki wani abun" kai ta girgiza da sauri,saita shagwabe mata


"Abby ne ya tafi ya barni,bayan yace bazai sake tafiya ba dani ba" siraran hannuwan yarinyar ta kamo tana kallonsu,babu wata qiba sam,kamar bata cin wani abu da zai gina mata jiki,duk da daular da take ciki,saidai kyau da gogewar fata kawai


"Abbynki ba zaiyi qarya ba,lallai uzurin da sai yayi tafiyar ne kuma ba tare da ke ba ya kamashi,but na tabbatar bazai dade sosai ba" murmushi ya qwacewa fadeela


"Shima haka yacemin"


"So....you must trust him" kai fadeela ta jinjina tana murmushi


"Wait.....yanzun kinci abinci?" Kai ta girgiza fuskarta na sake narkewa,ido sãahar ta zaro


"Eehhhh,bakyason abby ya dawo yaga kin zama qatuwa?,baby fadeela ta zama 'yar lukuta?" Dariya fadeelan ta saki,yadda sãahar din ke bubba hannayenta tana mata sign na qiba


"Inaso auntie,inaso"


"Good,chubby fadeela"


"Yes anty,not slimy,a chubby,a daina tsokanata a school"


"Aha,oya gate up" tayi furucin tana miqa mata hannunta,sai tayi hanzarin dora nata hannun,cikin kulawa sãahar ta riqeta sosai ta sauko da ita tana karantar yadda walwala da farinciki ya maye gurbin bacin rai data dawo ta sameta a ciki,wani irin nau'in tausayinta ya sake saukar mata,saita ajjiyeta saman lallausan carfet din dake gaban gadonta,itama ta zauna akai,ta fara diban abincin tana bata a baki.


"Kin iya feeding mutum like my abby" murmushi sãahar tayi


"Really?" Kai ta gyada mata


"Okay,nayi alqawarin zaifi na Abby din naki gaba kadan. Wani dariya me cike da nishadi fadeelan ta saki, sãahar ta tsaya kawai tana kallonta,an gaya mata tana da wuyar sabo sosai,nannys dinta suna jimawa kafin ta fara sakin jikin dasu,duk da ba wani dogon zango sukeyi ba a gidan,amma sai gashi ita lokaci guda ta sake sosai da ita.


uhmmm,ga sabuwar nanny a sheqar da batasan ta waye ba, za'a dore kuwa?,to lokaci shi zai nuna mana,asha hutun weekend lafiya,fatan alkhairi a gareku gaba daya,masu comments ina gani na gode sosai,gurin amsa comment dinne baya dannuwa,but am really appreciating

[05/09, 6:07 am] +234 902 488 9500: *HUGUMA*



*_TABARMAR KASHI_*


No comments