Tabarmar Kashi Book 1 Page 49-50
Page 49
Juyawa yayi ga likitan dake tsaye a gefe abinsa kamar ma baisan abinda yake wakana ba
"Me kake jira likita?,ci gaba da aikinka" sai ya waiwaya gareta
"Kika musanta ko kikace zakiyi taurin kai.....zakici gaba da shan baqar wahala ne a hannuna,babu kuma wanda ya isa ya qwaceki".
Zumbur ta sake miqewa ganin likitan ua dosota,har batajin ciwo da zubar jinin jikinta,da gudu ta doshi qofa,amma kafin ta isa adam din ya rigata,ya kankane qofar,daga bayanta kuma likitan yana tsaye yana jiranta,ta duba hagu dama babu ba wani gurin tsira sai qofar toilet,don haka ta kwasa ta nufa can da gudu.
Harta wuce drawer dinsa ta hangi wayarta akai,ta dawo da baya ta finciki wayar ta qara gudu zuwa toilet din,idanun adam suka kai kai,ya baro bakin qofar da wani irin mugun sauri ya biyo bayanta,kafin ya iso ta samu nasarar shigewa bandakin,ta tura qofar,ta kuma danneta da bayanta. Hannunta na rawa ta kunna wayar,ta fara laluben wanda zata kira,zuciyarta tayi mugun karyewa sanda ta tuna a yanzun kusan dukka wanda take saka ran samun daukinsa baya qasar baya tare da ita,daga qarshe ta yanke shawarar kiran ummin afifa.
Wayar tana ringing adam dake bakin qofa yana dannota iya qarfinsa tare da qoqarin bankadeta ya bude qofar,ta runtse ido tana sakin kuka,bakinta fal addu'ar kada Allah ya bashi ikon cimmata har sai ummin ta dauka,muddin bata dauka da wuri ba tasan cewa kashinta ya bushe,a yadda ta zubar da jinin nan,babu wani cikakken qarfi yanzu haka a jikinta da zata iya ci gaba da tare qofar.
Ringing din ya tsaya,muryar ummin ta bayyana radau tare da yin sallama
"Zasu kasheni,zai kasheni" abinda ta fada kenan cikin qaraji,saboda nasarar bankado qofar da adam din ya samuyi,dalilin da ya sanyata faduwa gefe qasa warwas,taku biyu ya isa gabanta,yasa hannunsa ya damqe bakinta da kyau,ta inda babu damar da zatayi magana,ya zubamata ido da wani irin kallo na zallar rashin imani yana duban fuskarta tare da ja mata zazzafan gargadi da idanun nasa,sannan ya miqa hannu ya dauki wayar da har zuwa lokacin ummi ke fama cewa hello hello jin shuru ba'a sake magana ba.
Kiran ya kashe sannan ya sakar mata baki,ya koma saman toilet ya zauna yana maida numfashi,ransa a matuqar bace
"Kin ginawa kanki da kanki rami,zakisan cewa bani da imani" yana fadin hakan ya kamata,saidai taqi miqewa tsaye sam,bai damu ba ya riqe hannunta da kyau ya fara janta a qasa kamar kayan wanki,bai ajjiyeta ko a ina ba sai a gaban likitan
"Kayi mata allurar bacci,ka hada mata data 'yan shaye shaye me qarfin" tana ji tana gani ya danneta aka hada ruguntsumin alluran aka dirka mata,a hankali jikinta ya fara saki,saidai idanuwanta basu daina zubar da ruwan hawaye ba,hakanan bakinta bai fasa fadin
"Allah ya isa,Allah ya sakamin,Allah ka yimin sakayya".
Bai ko dubeta ba ya jawo stool gabanta ya zauna,yayi kiran ummi. Bugu daya ta daga a matuqar rikice
"Me yake faruwa da sãahar din?"
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,muna cikin mummunan tashin hankali" ya fada da muryar kuka wadda a wajen ya qirqireta
"Me ya faru?"
"Ibtila'i ne ya samemu,na fita lafiya na dawo na tarar da ita cikin wani yanayi,ina shigowa kawai ta cakumeni ta fara fadin mugu azzalumi,ka cuceni zaka kasheni,Allah ya isa,Allah ya sakamin,ina tsammanin mummunan gamo tayi,don cewa tayi waita ganni da wata muna aikata alfasha,bayan kuma ni dawowata kenan daga tafiya,kwanana uku bana garin,yanzun haka gata ta sume,da qyar na samo kanta,duk tayi fashe fashe a dakinta" salati ummi ta saki tana sallalami cikin matuqar tashin hankali
"Yanzun tana ina?"
"Gamu a gida,amma na yiwa wani malami waya yana kan hanyar zuwa"
"Ganinan nima" ta fada a gaggauce tana kashe kiran.
Iska ya furzar daga bakinsa,sannan cikin hanzari ya fara kiran wata number wayar daban. Bugu uku aka daga,sai ya miqe yana fita a dakin,yana amsa wayar a gaggauce.
Sake lumshewa idanunta sukayi hade da wani zazzafan hawaye,zuwa lokacin sama sama takejin komai,hakanan dishi dishi take ganin abubuwa,amma duk da haka kwanyarta bata daina aiki ba,bata kuma daina haska mata girman cin amanar da adam yake Shirin aikata mata ba,wadda tafi abinda ya aikata mata a baya girma da muni. Kafin ya dawo bacci tuni yaci qarfinta.
Sanda ta farka ta ganta ne kawai kaca kaca cikin shirgi da shara,tana yashe a qasa cikin dattin,gaba daya dakin ya kacame,hatta da mirror da wanda ke jikin sif din a farfashe yake,duk wani kayan ado da qawa dake dakin wanda hannu zai iya kaiwa gareshi a fashe yake.
Cikin mamaki ta miqe ta zauna tana jin kallon ko ina,ita daya ce qwallin qwal a ciki,saita zabura ta miqe ta sauri ta nufi bakin qofa,tana fatan ta samu qofar a bude.
Tana isa bakin qofar muryar ummi ta fara jiyowa,wannan ya sanya da azama ta dora hannunta kan handle din ta fara jijjigashi tana fadin
"Ki taimakeni..... kasheni yakeson yi,ki budemin,ki tafi dani don Allah" ta furta iyakar budewar muryarta,wadda bata da wani amo sam sam kasancewarta mai sanyin murya tun asali.
Adam dake zaune qasan kujera wurjajan ya daga jajajyen idanunsa da sukayi jajur ya kalli qofar,kamar yadda idanun ummi dake sharce hawaye itama suke duban qofar
"To hajiya kinji irin takeyi,kuma duk sharrinsu ne" cewar wanda ke zaune daura da adam din,cikin babbar rugar malum malum harda rawani,da kuma tsayayyen gemun da wala'alla ciko ne akayi masa yayi irin wannan cikar,hannunsa kuma zabgegiyar tasbaha ce yake ta janta daya nabin daya
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,wannan wacce irin jarabawa ce ta saukarmiki sãahar da qananun da ko ashirin basu haura ba?" Ta fada cikin kuka
"Hajiya kar ayi sabo,shi lamarin ubangiji haka yake,jarrabawa kuma babu ta inda bata saukarwa bawa" malamin qaryar ya fada yana shafa gemunsa cikin nuna zallar taqawar da babu ita ko kusa ko alama cikin zuciyarsa
"Yanzu ba yadda za'a yi na ganta?" Da sauri ya girgiza kai
"Ai hajiya muddin aka rabata da wannan dakin ba abinda bazai iya faruwa ba,zasu iya dauketa ma a nemeta a rasata,shi kansa likitan da kikaga ya fita yanzu saida Allah yasa bacci ya dauketa ya iyayi mata gwaje gwajen da yayi,shima kuma yaga alamun tabuwar kwanya kadan,duk da hakan na iya yiwuwa duk cikin sharrinsu ne".
A yadda suka tsara komai abune mawuyaci ka fahimci cewa shiri ne irin na adam da muqarrabansa,cikin kwana daya tal ya maidata mahaukaciyar qarfi da yaji,kusan kullum a nan ummi ke yini,gudun tonuwar asirinsa yasa aka dinga yawaita yi mata allurar bacci da aka cakudata da allurar sanya maye,abinda ya qara nakasta garkuwar jikinta,ya zamana ko cikakken zama bata iyayi,data zauna din sai bacci,kota dinga bin kowa da kallo kamar sokuwa,sukayi amfani da wannan damar sukace maganin da malamin yakeyi mata ne ya fara aiki a jikinta.
Fadin irin tashin hankalin da iyalan Dr mamman jarma suka shiga a qasar saudiyya sakamakon mummunan labarin tabuwar qwaqwalwar sãahar da suka samu bata baki ne,kada ma afifa taji labari,wadda a jikinta ta dinga jin cewa ba haka bane,hauka yana da sila da kuma sanadi idan ma har haukanne,koda ta sanadiyyar jinnu ne suna nuna wasu alamomi kafin sukai ga taba lafiya kwanyar mutum,tunda suke da sãahar basu taba ganin wani abu na daban tattare da ita ba da yake da alaqa da irin wannan lalurar.
Mutane ne masu tsananun dattako da yarda da Allah wahidun ahadun,sun yi imani suna qofar waraka,qofar karbar dukkan addu'ar me neman,wajen biyan buqatar duk wani mabaraci,dukkaninsu sai suka duqufa da addu'a ta nema mata sassauci da waraka,tana da gata me yawa da soyayyar iyaye da yayye,hakanan qananun yaran da suka kasance 'ya'yan 'yan uwanta suna tsananin sonta,saboda ita din mutum ce me son yara qwarai,akwai soyayya da sabo sosai a tsakaninsu.
Kwanakin da suke gabansu na ranar dawowa Nigeria sai suka zame musu kwanaki mafiya tsaho,duk da haka basu bari sunyi asarar kwanakin ba,sunci gaba da addu'a da ibada,tare da samin information na halin da ake ciki a wajen ummi.
**************Ta fuskanci duk wani abu da zatayi babu abinda zai hana adam aiwatar da abinda ya shirya mata,hakanan a yadda ya tsara din ta tabbata cikakkiyar mahaukaci ga idon kowa,tana jin muryoyin 'yan uwa makusanta daga parlor din gidan masu zuwa dubiya gurin ummi,saidai ta zame ta kwanta lamo tana jinsu,don zuwa lokacin tayi kukan da batasan iya adadinsa ba,bai kuma qara mata komai ba hakanan bai rage ba,don ba abinda adam ya fasa,saidai yana gaya mata a kullum,zabin fitarta daga wannan yanayin ko tabbatuwarta a ciki yana hannunta,ta sallameshi shima a ranar zai sallameta kowa ya kama gabansa.
Kwata kwata daina tanka masa tayi,saidai ya qaraci maganarsa ya tashi ya miqe ya fice,abinda yake sake dugunzuma ransa kenan tare da qara masa bacin rai a kanta
"Banda ina tsoron na qarasa gawar daba tawa ba,tabbas da sai nayi miki dukan da zaki raina kanki,amma ko a hakan ma muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura" ya miqe yayi fatali da gantalelallen abincin da ya kawo mata,ya samu kyakkyawan mazauni akan qafafunta,zafin abincin ya ratsata,amma bata iya janye qafafun nata ba saboda wani azabtaccen ciwon kai da take fama dashi,ko gani bata iyayi sosai. Da zugin ya isheta saita zame kawai ta kwanta a wajen tana maida numfashi,babu abinda zuciyarta ke ayyano mata sai irin rayuwar da sukayi ita da adam a baya,yadda ya kula da ita ya tattalata,amma zuwa wannan lokacin ya juye ya koma mata wani irin baqirin shaidanin kumurcin maciji me cike da guba da kuma dafi.
Lokacin data fuskanci jinin cikin da cisge mata ta qarfi da yaji ya dauke,sai tayi wanka ta daura babban towel tayi sallah,baya rufe bandakin,don bazai iya jigilar gyara gurin ba idan ta bata. Darajar sallar data fara yi sai ta fara samun nutsuwa cikin ruhinta,daga mugun likitan har annamimin malamin,duk sanda sukazo saidai tabisu da ido,kowa ya gama mugun alkaba'insa ya fice,me allura yayi,me kawo tofin qarya ya kawo ya ajjiye saboda adam din yanason ya tara evidence na cewa yana kula da ita,kuma tabbas lalurarta akwai aljanu a ciki.
Ko sau daya bata taba bata ba a lissafin kwanakin daya ragewa ahalinta su dawo,ranar da take sanya ran kwanaki biyu ko daya suka rage musu su dawo,bayan likitan ya gama dirka mata allurar ba tare da sunbi takan matsanancin ciwon kan dake gallabarta ba,wanda ya sake sanyawa ta zuqe ta rame ta koma 'yar firit,sai sassanyan kyantannan da har yanzu yana nan shinfide a fuskarta.
[02/09, 3:47 pm] +234 810 324 4136: Page 51
*H U G U M A*
*_TABARMAR ?ASHI_*??
Page 50
Idanunta a lullumshe,tana ganinsa dishi dishi,amma ranta cike fal da baqinciki da kuma zallar bacin rai na hana mata samun salla,don tana gama alwala kafin takai ga tayar da sallar suka shigo mata
"Kaji tsoron Allah" ta samu ta fusgi kalmomin daga bakinta,cikin sautin galabaita,a fusace ya dawo gabanta ya tsaya,ya sa hannu ya matse fuskarta cikin hannunsa da kyau,wani zafi ya ratsa fatarta,ta runtse idanunta a galabaice
"Ke zan cewa kiji tsoron Allah,muguwa wadda bataso a qaru da ita,kina ta sakani ina sake asarar ragowar kudin hannuna gurin siya miki alluran da zasu ladabtarmin da ke,na rantse miki da Allah bazan taba barinki ki kubuta ba har sai kin fiddomin da jakata" yana kaiwa wannan ya jefar da ita ya fice yana huci.
Duk da hankalinta ya kusa gushewa amma bata gaza tantance dacin kalamansa a kanta ba,a sannan tarwai take iya tuno sanda afifa dama maama ke jaddada mata tayi iskhara kafin ta bawa adam damar turo magabatansa, murmushi kawai tauiy,tana ganin tunda har Allah yasa abba ya karbeshi ya amince ya turo,duk da su ya Saifullahi basu gama gamsuwa ba,to ba shakka shi din Allahn ya zaba mata,bata kokwanto,bata kuma buqatar qarawa da istikhara din,kada taje hankalinta ya kasu biyu. Kuka takeson yi amma ruwan allurar yabi jikinta,haka tayi shame shame a gurin,ita bame rai ba,hakanan ita ba gawa ba.
Abu daya da bata sani ba shine,yadda take lissafin ranar dawowar su maama haka shima adam yakeyi,ya kuma gama shirya komai,da dukka wasu allurai masu qarfi da za'a sauya mata dasu,wanda zasu sake sakata cikin bacci da maye mai qarfi,su kuma zabura qwaqwalwarta,ta yadda komai qwaqwafi da hasashenka baka isa ka fahimci lafiya qalau take ba.
A washegari aka shiryo raihanatu aka kawota gidan da sunan zata dinga kula da sãahar,saidai duka hakan wani shiri ne da akayi don amintar da zukatan iyalan dr mamman girema. Da qaqqarfar gargadi momee ta tsare raihanatu akan babu ruwanta da dukkan abinda zata ji ko zata gani a gidan adamu,iyakar abinda akace tayi shi zatayi,wanda ba'a sanyata ba kome zai faru kada ta tsoma hannu ko bakinta,sabawa wannan umarnin nata,dai dai yake data rasa rayuwarta gaba daya,maganar datayi mugun daga hankalin raihanatu kenan,fitsari ya balle mata,ta roqi momee kan tayi haquri,kada ma ta kaita,saboda ta fahimci akwai abubuwa masu muni dake faruwa da anty sãahar din mutuniyar kirki me qaunarta,duk da bata gama fahimtar komai dari bisa dari ba,to amma jikinta da zuciyarta sun bata,kumnuwanta kuma sun tsinci kadan daga cikin wasu qulle qullen da momee din keyi tare da adam din.
"Bakin alqalami ya riga ya bushe,tunda har wannan gargadin nawa ya shiga kunnenki dole zargi xai darsu a ranki,tunda zargi ya darsu kuma dole kici gaba da rayuwa damu harmu cimma gaci" tana ji tana gani aka tattarata aka kaita gidan.
Cikin kwana daya tak ta dinga jinta kamar cikin maqabarta take rayuwa,gunji da buge buge hadi da fashe fashen da takanji duk bayan wasu lokuta daga dakin anty sãahar din yana mugun dugunzuma mata hankali tare da daga mata hankali,kamar afifa,itama a jikinta ta dinga jin cewa tabbas sãahar ba zata haukace ba,Allah bazai taba barin mace me kyakkyawar zuciya irinta ta samu tawaya da naqasa irin wannan ba,idan tace ga sau nawa tayi kuka a kwana biyun nan saboda tsananin tausayin sãahar to tayi qarya,cikin dare bata iya bacci,har cikin ruhinta takejin tashin hankali da kuma damuwa da yanayin da sãahar din take ciki,don haka ta dinga shimfida abun sallah tana miqawa ubangiji kokenta akan ya kubutar da sãahar din daga dukkan kaidi da sharrinsu. (Ita kyakkyawar mu'amala da kuma kyakkyawar dabi'a yado takeyi,a yayin daka shiga tsanani,sai dukkan wanda yake tare da kai ko kuma ya sanka sai ya shiga damuwa me tsanani,wanda bai sanka bama sani na haqiqa labarinka yakeji,sai shina zuciyarsa ta shiga tayaka damuwa da kuma alhini,wannan duka sirrin kyakkyawar zuciya da kyakkyawar mu'amala ce,wannan soyayyar daga ubangiji take,a yayin da ya soka saboda nagartarka,sai ya sanya wannan soyayyar taka a zuciyar dukka bayinsa,suyita qaunarka ba tare da kun hada komai dasu ba,wasu ma baka taba yi musu wani abu na kyautatawa da zasu iya nunawa duniya ba,amma dai kawai suna jin labarinka,sai suji soyayyarka ta shiga ruhinsu,ya Allah,kayi mana baiwa da tsarkin zuciya da kuma kyakkyawar mu'amala ???? da daukacin bayinka)
*_RANA BATA ?ARYA_*
Inji bahaushe,tunda ya samu labarin a gobe ne ake sakaran isowar jirgin KABO AIR da mahajjatan da suka hada da iyalan Dr mamman girema adam ya kasa zaune ya kasa tsaye,a ranar sãahar taga izaya nau'i daban daban,wata allura data sake birkitata akayi mata,tun safe bata farka ba sai yamma liqis,babu azahar ba la'asar,abinda yafi komai qona mata rai. Tana yunqurin tashi yana sanya muqulli ya bude qofar dakin,idanuwansa da suka canza launi suka kuma zuzzurma saboda bala'in da yakeji rayuwarsa tana ciki ya zuba mata,ya tako ya tsaya a kanta,sai kuma ya kalli agogon hannunsa,ya girgiza kai da sauri
"Nafison allurar da tafi wannan qarfi" ya fadi kansa tsaye,saboda ba tun yau ba,baya shakkar fadin dukka wani shiri nasa a kanta,ta dade da gama haddace koshi waye,ainihin tarihin rayuwarsa da komai nasa da yadda ya shirya faruwar komai kawo yau.
Stool ya jawo zuwa gabanta ya zauna,sai ta miqe taja baya da sauri,duk sanda ya zauna gab da ita tana jin kamar ta cinnawa kanta wuta ne saboda tsabar tsanar data yi masa,duk ranar kuma da yayi kwanciyar aure da ita,ikon Allah ne kawai yake sanyata taci gaba da rayuwa. Takanji zuciyarta ta wani irin kumbura kamar zata buga,saidai bakinta baya rabo da kiran sunayen Allah,ta haka kadai take samun sassauci.
Wani mugun murmushi ya saka ganin yadda taja baya
"Kwantar da hankalinki,yau da gobe bana neman komai daga guriki,so nake sai sha'awata ta taru nayi miki wankin babban bargo,ta yadda tafiyama zata gagareki,da haka sai na sake lanqayawa aljanunki nace sun fara ma kwanciya dake,hanya mafi sauqi da zan rattabamiki sakinki uku qwarara bayan na karbe jakata daga gurinki" maganganun nasa sune abinda suka sake fusata qwarai da gaske,karon farko data saki murmushi ta zauna sosai tana kallonsa.
"indai har yanzu wannan jakar tana cikin mafarkinka,ba shakka ba zaka gushe ba cikin buri da fata har qarshen rayuwarka,kayimin duk iya sharrin da zaka yimin,ka laqabamin dukka ciwon dakaga dama,kayimin dukka iya muguntar da kake jin ka iya,amma karka manta,Alla baya bacci,kuma baya barin zalunci,kuma alqawarin ne yayi rantsuwa sai ya taimaki wanda aka zalunta,bani da baqinciki koda ta sanadinka na mutu,amma ina me sake jaddada maka,daukan fansa daga ubangiji tana nan tafe zuwa kanka,a kusa ko a nesa" dariya sosai ya saki,ya dawo gabanta ya tsugunna
"Waya gaya miki inason ki mutu?,kuma ma a hannuna?,har yanzu ina sonki,ina qaunarki,kodon wannan kyakkyawar surar taki da bata gushewa,bin qwaqwafinki da bincikenki ya sanya kika tono wuqar yanka kanki,idan da ace baki zurfafa bincike ba,cikin biyu za'a yi daya,ko muci gaba da rayuwarmu a gefe ina tawa irin rayuwar dana zabawa kaina na kuma saba da ita,ko ki tashi dare daya ki nemeni ki rasa,amma zaki ci karo da takardar sakinki,salin alin koma gaban iyayenki ba tare da kin cutu da komai ba illa dukiyar kawai da zan kwashe,dukiya kuwa ana iya maida madadinta" kamar yau ta fara ganinsa haka ta zuba masa ido,ta karanci cewa yayi wani mugun nisan nisan da ko kira baya ji,tana zaune a nan idanunta suka fara lumshewa,ya miqe ya tsallaketa ya fice abinsa.
*_W A S H E G A R I_*
Tun daga airport su da motocin da suka daukosu basu saukesu ako ina ba sai gidan sãahar din,tun kan hanya afifa ta fara kuka tana jin tsinkewar gaba da tashin hankalin yadda zata riski 'yar uwarta,hakanan maama daurewa kawai takeyi. Iya su yasu ne,yayyenta maza dukkansu sun wuce Egypt suna laluben asibitin da za'a kawota ayi mata magani,don sunce ba zasu iya dawowa su ganta a haka ba.
Mutum biyar ne a falon nasa,malamin bogin da yake kira da sheik usama,sai almajiran daya hayo guda hudu,bude da qur'ani suka karantawa,shi kuma da baisan ko bihim ba yana zaune a qasa,ya tanqwashe qafa yana faman can tasbaharsa me dubu.
Shine ya fara miqewa da sauri sanda su maama ke shigowa falon ya daga musu hannu alamun suyi shuru.
[02/09, 3:47 pm] +234 810 324 4136: Page 52
No comments