Tabarmar Kashi Book 1 Page 47-48

 


Page 47



          Toilet din ta wuce abinta,sai da tayi fitsarin ta sake daura alwala sannan ta fito,zuwa sannan ya sauke dafe kan nasa da yayi,ya goge hannuwansa a qirjinsa,suka hada ido,ta janye nata idanun tana bin dakin da kallo kafin ta sauke a kansa


"Wannan ai wani aikin kawai ka bani,ka sake hautsinamin daki" iska ya furzar daga bakinsa yana ritsata da idanu,yana jin kamar ya yaye duk wani hijabi dake tsakanin kowanne dan adam da abokin maganarsa,ya gano inda ta ajiiye masa jakar,yana jin wani irin tashin hankali yana saukar masa,fargaba da wani irin firgici,wani sashen zuciyar tasa kuma tana cike ne da tantama,don yasan tabbas sai daya kulle dakinsa kafin ya fita,kuma tuntuni ya kwashe dukka spare keys din,suna gurinsa,kowanne kuma a cike yake babu guda daya daya bata,to amma ai jakar bata da qafafu,zata tafi da kanta ne?,ko kuwa fiffike tayi?.


"kasala ce ta saukarmin" abinda ya fada kenan ya miqe yana jan qafafunsa ya fice,ta rakashi da kallo,taja tsaki hawaye nabin idanunta,mutum har mutum,amma yaudara ha'inci gami da cin amana sun ratsashi,itakam me zatayi da adam?,batajin har abada zata sake yarda dashi.


         Cikin kwanakin gaba daya ya gama zama wani iri,babu cikakken kuzari kwata kwata a tattare dashi,tuni dafa abinci ya zama tarihi a gidan,don dama shine yakeyi,ita bata iyawa sai jifa jifa,to daga ita har shi din a yanzu babu wanda yake da nutsuwar da zai tsaya yaci abincin ma gaba daya. Saidia yayita sintiri a kanta,ita kam koda wasa taqi nuna masa tasan komai kota gane abinda yake wakana,ta kawo idanu ta zuba masa,ta rungumi addu'a kawai,tana jiran ganin abinda hali zaiyi,murje idanunsa ne zai kawo kansa ko kuwa?.


            Shi da ita gaba daya sukayi rama cikin kwanakin,basa wata doguwar magana a tsakaninsu,duk da tana ta qoqarin yin komai kamar yadda ta saba,saidai yadda zuciyarta ke mata ciwo,wani lokacin tana buqatar kebewa,sai tayi masa qaryar batajin dadin jikinta,baya cewa komai shima,saidai hakan na sake dulmiyashi cikin kogin kokwanton ita ta dauke jakar koba ita bace.


*_K A C I ? U S (M U G U N G A M O)_*


            Wai bahaushe yace kaci?us mugun gamo,sau da dama akwai zazzafar  jarrabawar da zata fado rayuwarka,har wasu lokutan idan bakayi da gaske ba ta kusan zama silar rabuwarka da imaninka(wa'iyazubillah)amma kuma sai ta zamewa rayuwarka MABUDIN ALKHAIRI,sanin gaibu sai Allah,tabbas haka yake,batuna kuma da bashi canzawa.


           A cikin wannan yanayin da rayuwarsu ke tafiya a kai,cikin huwacewa ta ubangiji Allah ya qaddara tafiya aikin hajji ga dukka familyn Dr mamman girema,matarsa,yaransa harma da jikokinsa,da 'yan uwa na kusa da sukan biyawa,ciki harda afifa. Tun asali an tsara za'a yi tafiyar harda sãahar,amma samuwar cikin jikinta ya kawo zare sunanta daga cikin masu tafiyar.


           Taji ba dadi sosai,saboda tafiya ce da sau daya suka taba yinta wannan shine karo na biyu,ko wancan karon da akayi tafiyar gab da bikinta ne,taji dadin aikin hajji qwarai cikin familynta,kuma abune dama da yakan yiwa kowa dadi idan ka gudanar dashi cikin tawagar iyalinka.


          Tun ranar da sukayi waya da maama ta sanar mata tafiyarsu zata iya kamawa next week taji gana daya jikinta ya sanyaya,sai takejin kamar idan sun tafi ba zasu dawo ba,ko kuma ba zasu dawo su tarar da ita ba,cikin jikinta ta dinga jin kamar akwai wani babban abu mara dadi dake tunkarar rayuwarta,don haka cikin satin ta dinga ziryan zuwa gida. Wuni take a jikin maamanta,afifa na gefe suna hira,dukkansu sunga yanayinta ya canza,ga ramewar sa tayi,maama ta fara tambayarta


"Ko akwai matsala ne tattare da cikin?" Kai ta girgiza


"Nima bansan me yake sakani ramar nan ba maama" saita jinjina kai


"Allah ya raba lafiya,karki dinga zama haka,ki kula da kanki da kyau don Allah"


"In sha Allah" ta amsa tana maida kanta ta kwantar,tana jin kamar kada ta koma gidanta,kamar tayi zamanta tare dasu. Afifa dai tana gefe batace komai,har maama ta gama abinda takeyi ta fita ta barsu a dakin,afifa ta ajiiye nail cutter din hannunta ta kira sunan sãahar,tana daga kwancen ta kalleta


"Ban yarda da cewar babu abinda yake damunki ba,kamar yadda maama ma na tabbatar bata gamsu da xancanki ba,kawai don ita din me kawaici ce,wadda kuma bata cika takurawa sai taji sirrin da mutum ya yanke ya barwa cikinsa ba" shuru sãahar tayi idanunta a runtse tana jin heart beat dinta har cikin kunnuwanta,hawaye masu dumi suka ciko idanunta da suke runtse amma taqi basu damar zubowa,tsahon wasu mintuna,batace komai ba itama afifa bata sake magana ba,ta buda bakinta a hankali


"Tabbas akwai abinda yake damuna,babbar matsala ce da take gab da rabani da gidan aurena,idan har shuru yaci gaba da wanzuwa a bakinsa ba tare da kowanne irin sauyi na bayani ko bayyana kai daga gareshi ba,to komai zai bayyana,zan bayyana komai da kaina da kuma bakina" ta qarashe zancan tana bude idanunta akan afifa.


              Sosai afifa ke kallonta kamar meson karanto matsalar data kira din


"Amma kinsan barin kashi a ciki baya maganin yunwa?" Ta fadi bayan ta rasa wacce kalma zata fada din,don gabanta wani irin faduwa kawai yakeyi da yadda taga fararen idanun saahar din sun canza launi. Wani malalacin murmushi ta saki,ta saukar da kanta qasa


"Na sani,amma komai yana da lokaci" shuru ya sake ratsa dakin,afifa ta jima tana karantar fuskar sãahar din,sanann taja numfashi ta sauke


"Allah yasa muji alkhairi" bata amsa mata ba,tadai maida kanta ne kawai ta kwantar, Allah ne kadai yasan me gobe zata haifar,Allah ne kuma kadai yasan ya rayuwa zatayi da ita a gobenta.


           Randa ake sanya ran tashinsu tayi niyyar kwana a gida ne,don haka da shirin kwana ta taho,cikin ikon Allah wajen sha daya na dare saiga kira mahajjatan qaramar hukumarsu su fito,cikin qanqanin lokaci gidan nasu yadan cika da masu sallama da kuma wasu daga cikin wadanda za'a yi tafiyar dasu,wasu kuma daga gidajensu sun wuce airport din,ba jinkiri suka fito,motarsu daya da maama da kuma afifa,jikinta a sanyaye tana kwance jikin maaman


"Ni ina ganin idan ba dama ku koma asibiti ayi miki checkup,hankalina ba'a kwance yake ba sãahar tun ranar nan,bana ganin alamun lafiya a tattare dake,idan mukaje muka dawo still babu sauyi,zan yiwa yayanku magana ya siya mana ticket muje Egypt ko india a dubaki da kyau,jiya jiya abbanku ma yakemin qorafi" kamar maama din ta xungureta,saita sake lafewa a jikinta tana sakin siririn kuka, zuciyarta sam ba dadi,rayuwarma jinta take kawai gata nan gata nan,kukan da ya tashi hankalin maama din sosai


"Anya ba damuwa?,anya zan tafi na barki a haka?,me yake damunki?" Yadda taga hankalin maama ya tashi ya sanya ta sassauta kukan,tana kuma qoqarin daidaita kanta,batason tayi asarar aikin hajji guda saboda ita,wataqila dukka ayyukan hajjinta a wannan ne zata samu cikakken karbabbe me cike da da cewa da rahamar Allah,ba zatayi mata wannan asarar ba


"Lafiyata qalau maama,zanyi kewarku ne,duk kun hada baki kun tafi kun barni" ta fada tana kebe fuska


"Ba zamuso wani abu ya sake samun abinda yake cikinki ba,idan Allah ya saukeki lafiya zakuje umra keda adam din,hajj kuwa zagayowar shekara kamar yaune,zuwa sannan ma zaki iya yayemin jikana saiki ajjiyemin abina ku tafi" kiran sunan adam da tayi kamar wani fami ne akan ciwon dake danqare cikin zuciyarta,saita sake lafewa jikin maaman ba tare da ta sake cewa komai ba.


           Tana tsaye ita da sauran ma'aikatan gidansu da ba dasu za'a je ba wannan karon har jirginsu ya tashi,zuwa lokacin qarfe sha biyu dai dai na dare,kubra daya daga cikin masu aikin biye da ita suka koma inda motocin gidansu ke fake,ta shige daya daga ciki,drivern yaja suka bar airport din.


          Tun a motar ta hada kai da gwiwa cike da damuwa,tana jin kamar ita daya tayi saura cikin duniyar,suna isa gidan ta wuce dakin maama,gadonta ta haye ta lulluba da duvet dinta tana jin wata matsananciyar kewarta da bata taba jin irinta ba tunda suke tafiye tafiye,saboda akwai adam a gefanta,a lokuttan qauna da soyayya da kuka tsantsar kulawar da take kashe mata kewar duk wani makusancinta,a lokacin da yake nagartaccen miji tsayayye da baya gajiya da nuna mata zallar soyayya da kulawa,amma ayanzun daya zame mata tamkar wani shirgegen maciji dake dauke da uban dafi a bakinsa,dafin da takejin taqin dake tsakaninta dashi bashi da yawa,wanda da ace ya kai ga tsarta mata shi da wani zancen ake ba wannan ba.


             Cikin daren tayi wani irin kuka da yafi dukka sauran kukan da tayi a baya ciwo da yawa,ta tabbatar a rayuwa babu abinda yafi maraici d'aci da kuma ciwo,irin ciwon dake da tsananin wahala,kamar tasan qarin MUMMUNAR QADDARAR da take sake jiranta a washegari.


          Wannan kukan ya sanya tun asuba taji jikinta ba dadi,ta laluba magungunanta na anti natal ta barsu a gida,ba yanzun ta shirya komawa gida ba,to amma ya zama dole,don tana buqatar magungunan,don haka da safe bayan ta karya da abincin da take samu tana sanyawa cikinta da qyar saboda dan tayin bawan Allahn dake cikinta,tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar da a yanzun kusan suta maida kayan sawarta,kamar wata me takaba,kyakkyawar fuskar nan ta kode saboda kukan data kwana tanayi,saidai har a lokacin wannan sassanyan kyan bai gushe ba,ta karba key na daya daga cikin motocin,a yau fushin dake cinta a zuciya da tashin hankalin da rayuwarta ke ciki ya gaza boyuwa,ba fara'a ko alamun sukuni sam a fuskarta,wannan yanayin yasa cikin kulawa kubra tace tazo ta rakata?,kai kawai ta girgiza mata ta fice a gidan.


*_Turqashi!!!!,shin me zata tarar?_*????????

[01/09, 12:45 pm] Mimah Yusuf: *H U G U M A*


*_TABARMAR ?ASHI_*??

https://arewabooks.com/u/huguma


Page 48



          A qofar gidan ta tsaida motar,da nufin ta fita ta bude gidan,tunda ta sani,ya gaya mata shima zaiyi tafiya ta kwanaki uku.


             A hankali take takawa zuwa qofar gate din,saboda yadda mararta ta sake qullewa,ta saka key ta buda qofar,ta tura qaramar qofar dake maqale jikin gate din ta shige.


           Bata ankara da motarsa dake ajjiye a farfajiyar gidan ba har sai data kawo tsakiyar gidan,mamaki yadan bayyana saman fuskarta,batayi tsammanin ganin motarsa ba,to amma sai zuciyarta ta bata wataqila tafiya ce ta team,a abun hawar ma'aikata suka tafi,ko kuma yabi jirgi ne ohon masa,duk da cewa tana tsammani zaiyi wuya indai ba biya masa akayi ba ya iya samun kudin biyan kudin ticket da sauransu. Tun daga sanda ya tattara komai ya kammale,idanuwanta suka kai ta kwashe,alamu da yawa suna nuna mata sauyin al'amura da yawa a tattare dashi,akwai abubuwa da yawansu da a yanzu baya iya aiwatarwa,hakan kuma yana nuni da cewa,dama can cikin kudadensu yake dukka birgima da facakarsa. Yage wannan tunanin tayi taci gaba da shiga cikin gidan.


           Mamakinta ya sake qaruwa lokacin data bude qofar falon,kaya ne a warwatse a qasan falon,ba watsewar kayan bace abun mamakin,gamayyar kalolin sutturar mace da namiji,daya dai tabbas kayan adam ne,yadin data siya masa a dinke a matsayin gift ranar zagayowar shekarar haihuwarsa,sauran kuma ba zata iya tantance suturar waye ba,tasan dai ba tata bace.


           Wani abune ya daki zuciyarta,amma saita matse zuciyar tata daga zarge zarge da tunane tunanen data fara debo mata,koma meye a yanzun bata rayuwar adam take ba,ta kanta da tata rayuwar da rayuwar abinda yake cikinta takeyi,koda tana buqatar sanin wani abu akai,tasha maganinta a yanzu shine abinda yafi zame mata me muhimmanci,tanajin mummunar fargabar da kuma mugun bugun zuciya,amma haka ta dauke idanunta daga kan kayan,ta kuma dauke idanunta daga kan sashen dakin adam dinma gaba daya ta nufi dakinta,saidai tana zura key da nufin budewa qofar ta tura kanta da kanta.


          Wani irin gurnani da sautin nishi ne abu na farko daya fara kaiwa ga idanunta,kafin daga bisani idanun nata su iya dauko mata hoton abinda ke wakana a tsakiyar gadonta na Sunnah,tare da mijinta na sunnah,cikin gidan aurenta na sunnah.


            Ba qaramin dan gajeran yaqi akayi tsakanin ido da kwanyarta kafin qwaqwalwar ta yarda ta kuma tantance mata gaskiyar abinda idanun suka hango mata. ADAM mijinta,tare da wata mace da ba zata iya gane ko wacece ba,suna aikata fasiqanci akan tsakiyar gadonta,dukkansu haihuwar iyayensu,dagashi har ita,ko duvet basu kaarantawa kansu sun rabawa jikinsu ba bare akai ga batun sutura.


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fada da qarfi sanadiyyar fusgota tayi daga cikin bakinta qarfi da yaji lokacin da numfashinta ke niyyar katsewa daga gangar jikinta.


         Dif taji sautuka marasa dadin dake tashi sun katse,ta daga kanta da yayi mata wani mugun nauyi tana sake qoqarin bude idanunta a karo na biyu. Tayi zaton ganin kowannensu a wani muhallin na daban yana neman sutura ko maboya,a'ah.......sabanin haka sai ta sake ganinsu a tare da juna,suna ci gaba da aikata alfasharsu hankali kwance,kamar ma basusan ta shigo ba.


"ADAM!!!" Ta kira sunansa da wani irin sauti kamar na mutuwa,waiwayowa yayi yana duban tsakiyar qwayar idanunta da rinannun idanunsa,ba kuma tare da ya fasa aiwatar da abinda yakeyi din ba. Wani irin mummunan fushi da tashin hankali ya rifto mata,ta daga qafarta da zummar kaiwa cikin dakin don ta dakatar dasu,saidai taku biyu kacal tayi!,wani abu me dumi taji ya tsarga daga mararta yana bin qafafunta,abinda ya sanya mata waigi,ta dakata a firgice tana binsa da kallo.


         Jini ne jajir yake saukar mata, shigen jinin data gani a wancan lokacin na baya,wanda ganinsa ya tabbatar mata da zuwan qarshen zaminin cikinta,a yanzun kuma me yake shirin alamta mata?. Da wacce jarrabawar zubarsa zaizo mata?, qwaqwalwarta batayi nisan kiwon da zata lalubo mata amsar tambayarta ta fara kokawa da numfashinta,a hankali ta soma gani dishi dishi,dukkan wani jarumta ta gabban jikinta ta fara zagwanyewa,saita fara sulalewa tana yin qasa,inda daga bisani ta kife kif a akan fuskarta kuma saman cikinta.


*******Ba zata iya cewa ga iya adadin awannin data dauka kafin dawowarta duniya ba,iya abinda zata iya tunawa kokawa data fara yi da zuciya da ruhinta,kokawar da batasan a gaske take yinta ba,har sai lokacin da taji ana bada umarnin riqeta,ba jimawa taji an daddanneta,bawai iya hannuwanta kadai ba,harda qafafunta,ta kasa motsa koda yatsarta,a sannan ta yanke shawarar buda idanuwanta taga ko cikin kabari take wannan al'amarin yake faruwa da ita?.


          Ba cikin kabari bane,cikin dakinta take,saman gadonta data tabbatar  an gama yamutsashi da qazantaccen al'amarin da idanunta suka gani a dazu,hannunta guda daya qarin ruwa akeyi mata,wani dogon baqin mutum dake sanye da lab coat yana tsaye kusa ruwan yana qoqarin zuba wasu allaurai,daga daya bangaren kuma adam ne,wanda ya haye fiye da rabon gadon,kuma shike daddanne da ita.


            Wani azababben bacin rai tsana da kuma mummunar qiyayyarsa ce ta zarto tun daga asalin qasan zuciyarta har zuwa saman fuskarta,wani irin qarfi yazo mata,tayi yunquri me qarfi sai gashi tayi nasarar ture adam din gaba daya gefe,saboda ya saki jikinsa,bai dauka zata iya aiwatar da hakan ba.


         K'arin ruwan da ake mata tasa hannu ta fincike,take ruwan ya soma zuba a qasa,jini kuma ya ballewa hannun nata,kafin takai ga miqewa adam din ya miqe tsaye yana dosowa inda take


"Karka sake ka matso inda nake,karka kuskure ka qaraso kusa dani,mugu azzalumi,macuci fasiqi,na gama zama dakai har abada wallahi,nayi nadamar saninka a rayuwata,nayi nadamar hada jikina da nayi da naka qazantaccen jikin" tana gama fada ta diro qafafunta qasa cikin fushi qasa,saidai tana miqewa ta jita fayau,kamar iska zata kayar da ita,jini me dumi ya sake zarto mata,amma duk da haka bata dakata daga fita da take niyyar yi ba. Ta tsani ganin koda inuwar adam bare ta hada daki daya dashi,ballantana kuma har suyi musayar numfashi,burinta kawai ta ganta ba a cikin gidan ba kota wanne hali,saidai tana kaiwa bakin qofa taji an fincikota an watsar,kafin ta gama gane ainihin abinda yake faruwa,an saukewa kyakkyawar fuskarta lafiyayyun mari guda biyu,wanda saida kunnenta ya dauke ya daina ji na wucin gadi,idanunta kuwa wasu irin taurari ta gani sun gifta,bata dawo hayyacinta ba adam ya bayyana a gabanta.


           Wata irin tsaiwa yayi a kanta,ya raba qafafunsa biyu a tsakiyarta yana duban qwayar idanunta da kyau


"Ina zakije da?,ai yanzu aka fara wasan,wasa ne me kyau dake nuni da kyakkyawan shirin bugashi da kikayi,wanda inda kinsan true color din abokin buga wasan naki da baki tarki yin irin wannan wasan dashi ba" mamaki ya sanya ta daga fararen idanunta da suka taruwar jini a gefe tana kallonsa


"Eh,idan kuma har baki shirya ci gaba da buga wasan ba........hanya guda daya ce gareki,ki fiddomin jakata da kika dauke" kai tsaye babu wani bata lokaci ko dogon ta fahimci abinda yakeson fada


"Jakarka?" Ta fada bawai don tanason musawa ko kokwanto ba


"Yes jakata,wannan ne zai sanya na baki damar tafiya salin alin,ina tsananin sonki sãahar,don ban taba samun mace me zallar madarar kyau da cikakkiyar ni'imar da take iya gamsar dani,da wani irin dandano da dadi na musamman kamarki ba,amma wallahi wallahi nafison kudi fiye dake,kuma nayi imanin su zasu sake samarmin wata macen wadda ta fiki ma wala'alla a wata nahiyar duniyar,matata ba zata taba hanani yin duk harkokin da nakeso ba,saboda itama bai hanata tayi tata rayuwar ba,amma ke muddin zanci gaba da zama dake,duk wata shaqatawata da jin dadina saidai na ajjiyeshi a gefe saboda wai kiyaye mutuncin addini da kuma samun dorewar soyayyarki da zaman lafiya a tsakaninmu,kamar yadda nayi tsahon uku babu kadan a zaman da mukayi......wanda nikam bazan iya ba,inason rayuwa" ya qarashe maganganun nasa yana sakin wani mugun murmushi.


           Saita zama speechless,ta narke a wajen tana kallon adam din cikin tsantsar mamakin daya gama daskarar da ita a gurin


"Me kike kallo?,zaki ban jakata na sallameki ko saimun ci gaba da buga game din?"


"Da kudadena halalina zakayi wannan shaqatawar?" Ta jefa masa tambayar da tafi qona mata rai,tafi kuma yi mata ciwo a ranta


"Really,kin fini tarawa da yawa ai,sannan acan gida ma an tara miki wasu ana kan tara mikin ma kinga ya kamata naci gadonki tun kina raye,tunda na taqaita miki wahala ban bari kin haihu dani ba,wancan cikin na saka miki tablet yabi rariya salin alin,wannan ma yana fara girgidi na sanya aka zaquleshi aka watsar,don haka ina binki ladan aiki ma" sosai ta sake razana da bayanansa,ta miqa hannu ya shafo jinin dake bin qafafunta har yanzu ta kawoshi dai dai fuskarta tana kalla,wasu zafafan hawaye suka fara bin kuncinta,shikenan,shima ta rasashi. Wata irin dakiya taurin rai da zafin zuciya ne suka saukar mata a lokaci guda,ta daga fararen idanunta da a yanzun suka rine zuwa jajaye ta kalleshi da muryarta data qara kauri ta kuma cakude da sautin kuka


"Yadda idan mutum yabar duniya sunyi bankwana da ita kenan har gaban abada.......haka nan wannan jakar tabar hannunka har abada,koda hakan yana nufin rasa numfashina ne" miqewa yayi zumbur yana dubanta saboda girgiza da yayi da jin furucinta,yasan halinta tsaf fiye da kima,KHADIJA tana da matuqar taurin kai a wasu lokutan,hakanan ita din kaifi daya ce,idan tace YES tofa YES dinne,hakanan idan tace NO zaiyi wahala ta dawo tace YES. Da qyar ya tattara qwarin gwiwarsa,ya saki dariya ya qara taku biyu zuwa gabanta kamar zai take yatsun qafarta


"Nasan halinki fa,shi yasa na shiryawa dukkan wani taurin kan da zakizo min dashi,wuya da kuma azaba babu abinda bata sanyawa a barshi ko a aikatashi,idan ke qwararriyar 'yar wasa ce to kin hadu da qwararren me buga wasan"


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at??


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim

Sai katura shedar biyanka anan??


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan??

09033181070


*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*


+22799643131


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*??


Zafafa????


[02/09, 3:47 pm] +234 810 324 4136: Page 49


*H U G U M A*


No comments