Tabarmar Kashi Book 1 Page 3-4
PAGE 03
?aya daga cikin yammaci ne wadda ke jerin yammacin da albarkar ubangiji ke sauka daga sama zuwa ga bayinsa dake rayuwa a doron qasa sanadiyyan haduwar hadari da samuwar saukan ruwan
sama,kama daga mutane dabbobi aljannu da sauran halittun dake qarqashin ruwa saman bishiyu da sauran bingiren da idanuwa basa iya ganinsu,raunin hankali,nakasa da kasawa irin ta abun halitta ya yiwa hankali shamaki da fahimtar wanzuwar wadan nan halittu dake kewaye damu masu tarin yawa,wanda kowanne yana qarqashin kulawa da tasarrufin ubangiji,bai gaza ba dai dai da qiftawar idanu wajen rabon arziqi ga bayinsa,da kuma isarwa da kowanne bawa gwargwadon rabon da ya kasance mallakinsa ne.A dai dai wannan lokacin,cikin qawataccen gidan abincin,muhalli me daukan hankali,sanyaya zuciya da bawa ruhi nutsuwa, sakamakon yadda aka qawata wajen da wani irin tsari mai ban sha'awa da burgewa,kwatankwacin yadda zai ja hankalin abokan kasuwanci suji basu qagara ko gajiyawa da zuwa kashe yunwa da qishirwarsu a wajen ba.
Saman kujerun dake zagaye da teburan dake jere a wajen bisa tsari na rukuni rukuni,daga hannun damanka bayan ka shigo wajen zaka iya hangenta.
Kyakkyawar matashiya,fara sol data mallaki wani irin hasken fata,irin farin da ko makaho ya shafa yasan natural ne,wanda ya cakuda da tsantsar kulawa tsafta da kuma hutu,yake kuma nuni da zurfin gogewa da wayewa da mamallakiyar fatar ke da shi.
Idan har kayi hanzari ko azarbabi zaka iya kiranta da doguwa,saidai kaso me yawa na tsahon nata babu shi sakamakon murjewar da jikinta yake dashi da ya shanye tsahon ya maidashi moderate. Wasu irin manyan idanu gareta amma kuma a russune suke,wannan ya boye girman idanun nata,kai tsaye ba zaka ce suna da girma ba har sai idan taso fidda girman nasu ne. Siraran labbanta masu kalar pink sun dace hancinta mai tsaho da tudu wanda ya hade da kwantacciyar eyebrows dinta dake bisa tsari kamar an zanata.
Sanye take da wata tattausar exclusive atamfa da bata tara tarkacen kaloli ba,hatta da zanen jikinta bai wuce dayan biyun ba,kalolin da suka dace da yanayin jikin da aka ra?awa atamfar,dinkin doguwar riga ne daya bude sosai daga qasa,daga sama kuma ya zauna mata cas kamar a don ita aka halicci atamfar dama dinkin gaba daya. Ta lullube kanta da wani madaidaicin mayafi wanda yayi mata aikin mayafin dama dankwalin da bata damu da daurashi ba,sai kwantaccen gashin daya kwanta daga gaban kanta,wanda duk bayan minti daya zuwa biyu take sanya zara zara yatsun hannunta tana jan mayafin tana sake rufe gaban kanta da kyau.
Wasu lafiyayyun plate shoes ne a qafarta,mahadin qaramar handbag dinta ta kamfanin saint laurent dake ajjiye tsakiyar table din dake gabanta wanda ta gagara zama a kai.
Duk da daya hannun nata wayarta ce a ciki,amma hakan bai hanata harde hannayen nata a qirji ba, kyakkyawar fuskar nan babu digon fara'a ko daya akai,sai dan qaramin bakinta da take dan motsawa kadan kadan,alamun dake nuni da cewa a matuqar qagauce take da tsaiwarta a wajen.
Ba ita kadai ba,koda kaine a wajen wala'alla ka shiga sahun masu tayata ginsa da tsaiwar,sakamakon yadda idanu sukayi yawa a kanta a wajen. Duk da cewar wannan din ba shine karo na farko ba a rayuwarta ba,ba koma. Sabo ko baqon abu bane cikin rayuwarta ba,amma a yanzun da komai ya canza cikin rayuwarta,al'amura masu yawa suka kutsa cikin rayuwarta suka kuma shude da abubuwa masu yawa da matuqar muhimmanci a wajenta ya sanya komai ya sauya......ya dasa mata tsanar kowanne kalar kallo da zai fito daga qwayar idanuwan da suka kasance mallakin ?A NAMIJI,idan ka dauke mutane hudu rakkin dake da matsanancin muhimmanci cikin rayuwarta.
Har yanzu guri daya idanuwanta suke kalla ba tare data barsu sun gusa da kallon gurin ba ko sau daya,nisan taku masu dan tazara ne a tsakaninsu da budurwar data zubawa idanu,wadda ke tahowa gurin da mabanbancin yanayi tsakaninta da wadda ke a tsayen ta kasa zama, idanuwanta cikin nata tana sake karantar zallar tsanar data yiwa wanzuwarsu a gurin harta iso
"Am very sorry bestie......" Ta fadi a taqaice cikin son kaucewa ganin yanayin fuskarta,ta miqa hannu ta gyara mata zaman kujerar dake bayanta,sannan ta mayar da dubanta gareta
"Have a seat" ta fadi mata suna hada idanu. Tsareta da ido tayi na wasu sakanni,ba tare data shirya ba dariya ta qwace mata,tasa hannu tana qoqarin rufe bakin
"Afifa....." Ta buda baki ta kirayi sunanta da wata irin murya me zaqi da laushi,fararen manyan idanunta na ragaita saman fuskar wadda ta kira da afifan
"Kiyi haquri ki daina kallona da manyan idanun nan naki haka,sai ki saka na daburce,kiyi haquri ki zauna,mintuna kadan zasu kawomin na gaya musu sauri mukeyi" jimmm tayi na wasu sakanni sai kuma tasa hannu ta matso da kujerar dab da ita ta koma da baya ta zauna.
Hirarrakin mutanen dake zaune daura dasu ta fara shiga mata kunne tana haura mata ka,duk da cewa ba suna magana bane da sauti sosai,zamanta tsakiyar halittun da a wajenta suke masu ban tsoro yasa takejin kamar a kunnenta ake maganar,sai tasa hannu taja jakarta ta fara kici kicin fiddo earpiece ta maqalawa kunnenta ko zata samu sassaucin jin muryoyin da bata qaunar jin irinsu.
Tsaf afifa ke karantar ta,ta zuba mata idanu tana kallon yadda gaba daya walwala tayi qaura daga kan fuskarta,kamar wadda ke zaman waqafi cikin kurkuku.
A nutse ta sanya earpiece a dukka kunnuwanta bayan ta sadar dashi da wayarta,tana jin feeling na insecurity a tattare da ita. Duk da taqi yarda idanuwanta su kalla kowanne sashe na wajen,gudun yin tozali da mugayen halittun MAZA dake wajen,amma all her body tana jin akwai wani ido dake karakaina saman jiki da fuskarta,bayan idanuwan da suka jima suna kallonta na mafi yawan mazan dake zaune a wajen.
Cikin wani irin coolness take latsa wayarta,ranta yazo mata iya wuya,tayi watsi da hirar da afifa keta qoqarin sanyata yi akan dole dole. Rashin samun hadin kan SÃAHAR din ya sanya afifa kama kanta bisa dole,tana zuge zip din jakarta order dinsu ta iso,waitress ta ajjiye tray din a tsakiyarsu cikin nutsuwa da girmamawa,tana kuma basu haquri na delay din da aka samu
"Ki maidashi takeaway" saahar ta fada a taqaice da sassanyar muryarta tana miqewa a nutse,karo kuma na biyu kenan da tayi magana tunda sukazo wajen,ta miqa santala santalan fararen yatsun hannunta tana daukar kyakkyawar handbag dinta tare da zare earpiece din kunnenta ta riqesu a hannu daya,ta tura kujerar baya ta fice a tsakiyarsu tana laluben hanyar fita da kyawawan fararen idanunta da suke da wani irin sheqi da daukar hankali
"Ki making payment kafin ki fita" afifa ta fada a gaggauce tana miqewa hadi da tattara sauran kayansu dake kan table din,tasan tsaf saahar din zata fita ta barta da karbo kayan da kuma biyan kudin.
Kallo daya ta yiwa gun biyan kudin ta sauya akalarta zuwa parking lot na gurin cikin takunta me jan hankali,koda karen hauka ne ya cijeta ba zata yarda ta qarasa da qafafunta wajen ba,ba don komai ba sai don gun cike yake da maza,mai amsan pyment din,wanda zai bata receipt.....kai kowa da kowa ma,wannan ya qarawa zuciyarta qunci da damuwar data tashi da ita yau,damuwar da bata shura wasu satittika bata tsinci kanta a ciki ba,wani abune daya zame mata tamkar JARRABI,duk kuwa da irin qarfin tuwo dana qwanji da take sanyawa kowacce fitowar rana da faduwarta gurin yaqar komai da komai,tare da sake samun nutsuwa da tabbatuwar binnuwar komai,binnewa ta har abada,saidai tasan cewa......ba komai KADDARA ke shafewa ba.....ba komai tsahon zamunna ke samun nasarar lullubewa ba...ba kuma komai zuciya da ruhi ke sarayarwa shekaru ba.
Amsa kuwwar sallamar dake ratsowa daga bayanta zuwa cikin kunnuwanta tayi dai dai da sanda take zura key zata bude kyakkyawar qaramar farar motar,cak ta dakata da abinda take shirin yin yanayin fuskarta yana sauyawa kadan kadan kamar wahainiya,kwanyarta ta sarqe da tunani da kokwanton ba ita ake aikewa da saqon sallamar ba,wannan ya bata karsashin sake zura key din tana murzashi.
Kamar yasan abinda kai kawo a zuciyar tata ya rage mata wahala ta hanyar sake kusanto inda take tsayen yana maimaita sallamar da muryarsa mai sanyi,ta dan runtse idanunta kadan cikin salon da yafi kama da lumshesu sannan ta budesu kai tsaye tana zubesu saman fuskar matashin dake tsaye a gabanta,cikin jikinta tana jin kamar ya yarfa mata garwashin wuta.
Wani irin kwarjini ya dakeshi,karon farko da ya fara jin irin haka kaf tsayin rayuwarshi akan wata diya mace,cikin salo da gogewa ya dunqule hannunsa yakai bakinsa yana jan gyaran murya tamkar mutumin daya qware,idanunsa cikin nata yana son ya koyawa kansa juriya a kallonta. Ba tun yanzu ba,tun sanda suka wanzu a cikin wajen cin abinci ya fahimci akwai wani kwarjini na musamman a tattare da ita,wanda yayi imanin shine ya zame mata qaqqarfar garkuwa daga zamantowa abar tayawa ko tunkarar kowanne irin namiji,yayi imanin a irin kyan da Allah yayi mata,ba kowanne namiji bane zai iya mata kallo daya ya kauda kansa,koda ya kauda kansa yana da yaqinin ba kowa keda qarfin mallakar zuciyarsa ya hanata qyasata ba
"Am sorry,kiyi haquri na tsaidaki ba tare da nasan naki uzurin ba.....but......da farko dai sunana mahmud,ko zan iya sanin naki sunan tare da yimin alfarmar aron lokaci koda mintuna biyu ne rak cikin tsadaddun lokutanki?" Kyansa,ajinsa da qwalisarsa masu dukan zuciya da idanun kowacce diya mace da suka bayyana muraran basu nata narkakkun idanun da matacciyar zuciyar ke kallo ba,abinda take gani yasha banban da abinda kowacce mace zata hanga daga gurin mahmud din......tafi hangen wata muguwar dabba dake neman abun farauta......muguwar halittar ?a namiji dake laluben halitta mafi rauni irin ta diya mace ya cutar da ita.......dukansu haka suke!,dukansu halinsu daya!,gaba dayansu basu da tabbas!,babu imani ko tausayi a qirjinsu!. Kalmomin da suka tasowa daga qasan zuciyarta suna mata amsa kuwwa a kowanne kunne nata,suka kuma taso da wani lullubabben yanayi me tarin daci dake danqare qasan narkakkiyar zuciyar dake dauke da tarin ciwo,suka soma sauya kalar launin fatarta zuwa bacin rai qarara,saita juya tana jan siririn tsaki,ta dora hannu zata buda murfin motar ta shige don yiwa kanta katanga da kuma kariya daga shaqar inuwa guda ita dashi.
Hannu yasa ya dafe murfin motar yana karyar dakai
"Kar muyi haka dake beauty.......kaina bisa wuyana indai cikin kalamaina akwai wadanda suka bata miki rai" sakar masa murfin tayi,taja da baya a nutse ta zagaya daya side din motar,zuciyarta tafasa takeyi kamar ta ballo ta fito daga qirjinta,ta bude kujerar zaman banza ta fada,ta maida murfin ta rufe ta kuma saka lock ta kulle kowanne murfi. Relaxing bayanta tayi da makarin kujerar hadi da lumshe idanunta,don ko inuwar mahmud batason gani a wajen bare mahmud din kanshi,ta fitar da siririyar iska me zafi daga bakinta hannunta na dafe da kanta.
Ba zata ce ga yadda mahmud yayi yabar gurin ko kuma adadin mintunan daya dauka a wajen ba,itadai taji afifa na knocking glass din,tunda ta buda ido sau daya taga itace,saita maida idanun ta rufe,tasa hannu ta laluba key din ta cire mata lock din hadi da dora key din daga gaban motar.
Sau daya afifa ta kalleta ta dauki key din ta saka ta tayar da motar ba tare da tace mata komai ba,bata da buqatar ji ko tambayar komai daga bakin saahar,tunda ta tarad da mahmud a gurin,to amma shin rayuwar saahar zataci gaba da tafiya a haka?,da kanta ta bawa kanta amsa ta hanyar girgiza kanta,dole dole......koda zasu dinga fada sau dari a rana suna shiryawa......ya zama dole ta dinga gayawa saahar din gaskiya,koda yau bata gani ba.....koda a gobe bata gane ba zuwa jibi lallai hankalinta zaikai kai,lokaci kuma zaiyi mata aikinsa,da wannan tunanin bayan sun danyi nisa saman hanya,motar shuru kamar kurame ne matafiyan,afifa tayi gyaran murya qasa qasa,cikin nutsar da muryarta tadan kalleta ta gefan ido kafin tace......
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at??
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim
Sai katura shedar biyanka anan??
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan??
09033181070
VIP????
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*Al'ummar NIJER ku kira wannan number don yin naku pyment din*
+22799643131
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*??
Zafafa????
[04/08, 4:21 pm] +234 907 013 9442: *H U G U M A*
*_TABARMAR ?ASHI_*??
_Arewabooks:Huguma_
https://arewabooks.com/u/huguma
PAGE 04
"mahmud abba gana.....kinsan wayeshi kuwa saahar?" Afifa ta jefa mata tambayar cikin kwantar da murya da salon rarrashi,kamar saahar din ba zata tanka ba,sai kuma ta motsa labbanta a hankali
"Ban damu insan waye shi ba,bana kuma buqatar na sani"
"Amma me yasa zaki wulaqantashi saahar?"
"Me yasa ba zasu gane ba.....me yasa ba zasu rabu dani nayi rayuwata ni kadai ba?" Ta jefawa afifa tambayar tana ware dukka idanuwanta akanta
"Ba zasu gane ba ba kuma zasu rabu dake ba,saboda qaddararki daban tasu daban,abinda kike hangowa daban abinda suke hangowa daban,kina yaudarar kanki ne kawai.....amma a irin surarki kinyi qarya ki hana maza su biki ko su soki" maida idanunta tayi ya lumshe zuciyarta na bugawa,bata taba jin kyanta na neman zame mata barazana ba irin a wannan dan tsukin da take gujewa mazan irin gudun da rai zai yiwa mutuwa,ta tsanesu fiye da yadda dukka wani abun halitta yake gudun kishiya,tanaji inama ace bata da wannan kyan da ya zame mata jarabta,inama ace ita mummuna ce,qila wannan munin zai siya mutu da nutsuwa,zai kuma barrantata daga dukkan wata barazana,ya hutar da zuciyarta da kwanyarta
"Duk yadda mace takai ga muni.....duk yadda takai ga zamantowa cikin matakin qasa qasa na rayuwa...... ba'a rabata da samun soyayyar maza wadda take dai dai da matsayin tata rayuwar......" Afifa ta fadi idanunta nakan hanya,kamar tasan abinda ke kai komo a zuciyar saahar din,saidai batakai ga qarasawa ba saahar ta dakatar da ita
"Na roqeki kibar kiramin sunansu a wajen nan" duk da yadda tausayin saahar ya tabata amma sai data murmusa don dole
"Bayan tsanarsu da kikayi,i think harda tsoronsu ma yanzun kikeji ko?,keda mukayi dake zaki qarasa kiyi biya kudi saiki gudu ki barni dasu suna jifana da tambayoyin ina kudinsu?, anyway alhmdlh, mahmud ya fansheki ya biya" ta qarasa fada tana waiwayowa cikin son ganin reaction na fuskar saahar din,akayi sa'a itama ta waiwaya din,saita watsawa afifa wani irin kallo kafin ta janye idanunta tana gyara kwanciyarta sosai cikin motar hadi da fadin
"Allah ya baki sa'a" kalma data sanya afifa dariya sosai,tasan sarai me saahar ke nufin aikatawa muddin tace mata haka. A haka suka qarasa gida,saidai duk yadda tayi da saahar ta tsaya ta dauka musu takeaway din cewa tayi
"Ban fara yunwa ba da zanci abinda wani ne ya siya da kudinsa,i have enough da zan iya siya cikin account dina nima,dama asali ni rakiya nayi,so na yafe" ta wuce cikin gidan cikin nutsatstsen takunta,afifa ta bita da kallo tanason sakin dariya.
Yalwataccen falo ne da ya sha shimfidu da ado cikin kalolin silver and royal blue,rukunin kujeru guda biyu kenan,daya nau'in kalar silver,daya kuma kalar royal din,stairs guda biyu ne qawatattu kewaye da falon da ya cika dukkan sharuddan zama qawataccen falo na alfarma dake nuni da zallar dukiya da kuma wadatar da ahalin suke ciki.
Kana sanya qafarka abu biyu zaiyi maka maraba,sassanyan qamshin turaren da humidifier ke bayarwa da kuma qamshin girkin dake fita a kitchen din gidan dake manne da falon qarqashin daya daga cikin stairs din.
Mutum biyu ne cikin falon,kyakkyawar baqa ko muce black beauty din macace da a qiyasin da idanuwanka zasu iyayi ba zata haura shekaru talatin da biyar ba. Kallon farko kawai da zaka yi mata zaka san cewa GIDAN GAYU ce,gayu da iya ado da kashewa jiki kudade masu nauyi saboda gyaransa ya samu mazauni a tattare da ita,cikin furucinta idan ka nutsu da kyau kana iya tsintar yadda harshen KANURI ya ratsata da kyau yadan gurbata hausar tata kadan,cikin matuqar girmamawa take magana da kamilar matar data kusa ninka shekarunta kadanne babu,MAAMA me shekara hamsin da biyar,farace sol da take da kamannin da SÃAHAR ainun,zallar jin dadi da samun sukunin rayuwa ya boye shekarunta sosai,saidai shi girma duk yadda kakai ga son tureshi da bawa jiki kulawa baya hanashi bayyana,illa dai ana samun sauqi yazo cikin cikakkiyar qoshin lafiya da kuma siffa nagartacciya.
Sallamar sãhaar din taja hankulansu,fuskar matar ta fadada da fara'a idanunta bisa fuskar sãahar din
"Yanzun nake shirin kiranki,ya akayi kuka dade haka?" Ta tambayeta sanda take gaggawar isowa ga matar,dukka idanunta suna kan kyakkyawar yarinyar dake kwance a gefanta saman kujerun falon tana wutsil wutsil da qafafuwanta cikin wata overall me taushi,yalwataccen gashin yarinyar yayi luf saboda gyara da yasha cikin zallar tsafta da kulawa,wannan ya sake fidda kyan yarinyar sosai.
"Sannu da gida maama" sãahar din ta fada dai dai sanda take duqawa ta dauki baby girl din,fuskarta na sake wadata da fara'a,ta daga yarinyar tana kallonta,tana jin wani tsohon emotion yana taso mata,saita sanya yarinyar cikin qirjinta ta rungumeta tana sumbatar ta.
Dukkansu a fakaice suke kallonta,kowannensu tausayinta yana ratsa zuciyarsa,duk da cewa suna qoqarin dannewa sa hana bayyanuwarsa saman fuskarsu
"Afifa ce,haka kawai ta lallabani ta jani rakiya zata kaini inda......" Sai kuma ta kalmashe ragowar maganarta cikin cikinta,tana dan shafa kan yarinyar a hankali,yarinyar tayi luf a qirjinta kamar wadda barci ke shirin dauka.
"Ina afifan takaimin ke?" Matar da suke kira da suna anty farheen matar aure ga dan uwanta shaqiqi ta furta cikin nuna kulawa,dukka idanunta suna kan sãahar din tana son jin amsar tambayarta
"Anty,ki tayani tambayar qanwarki dai,bayan tsanar data yiwa maza,hala ta fara tsoronsu kuma" afifa dake shigowa Parlor din hannunta riqe da ledar takeaway dinsu ta fada fuskarta yalwace da murmushin da baka rabata dashi,akasin hali da dabi'ar dake tsakaninta da sãahar kenan. Kafin anty farheen tace komai sãahar taja wani dogon tsaki tana sakarwa afifa harara
"Don dai tuwon gobe ake wanke tukunya" ta fada mata tana takawa a hankali zuwa gaba,dariya ta subucewa afifa,yayin da maama da anty farheen suka murmusa
"Inyeeee,to barkanki da kike sake jin hausa haka da kyau" afifa ta fada cikin salon tsokana tana neman gurin zama. Ta fuskanci idan ta biyewa afifa surutu zata yita sanyata,bayan ciwon kan data so saka mata yanzu,don haka ta waiwaya ga anty farheen
"Brother fa?"
"Yana gurin abba,inajin dama ke yake jira tun dazun" kai ta jinjina,ya kirata a dazun sanda take zaman jiran afifa,don haka ta fara takawa a hankali zuwa hanyar da zata sadar da ita da sashen mahaifinta,baby aleena na kwance saman kafadarta
"Nazo nayi rakiya?" Afifa ta fada tana bude ledarta,ci kanki batace mata ba kamar yadda tayi zato,ta wuce abinta,sai afifan ta saki dariya tana fidda kayan cikin ledar
"Me yasa kikeso ki dinga tunzuramin qanwa ne afifa?,za'a ji kanmu fa" anty farheen ta fada dukka idanunta akan afifa bayan maama ta miqe zuwa dakinta dauke da ledar kayan da farheen din ta kawo mata kyautarsu,fuskar farheen din a sake ta yiwa afifa tambayar. Ta buda takeaway dinta ta saka fork a ciki tana dariya
"Abun sãahar ne anty kamar sake gaba yake,duk waje idan akwai maza suka wuce uku saita sakawa gurin karan tsana?,me yayi zafi haka?" Kai farheen ke gyadawa a hankali idanuwanta akan afifa,ta bude baki a nutse tace
"Babu halittar dake saurin ruguza dukkan buri mafarkai yadda da aminci na diya mace irin halittar da namiji,idan ta dace da abokin rayuwa na gari......sai kiga tana yiwa maza dukka kallon abu daya,hakanan idan aka samu akasi shima haka abun yake,a dukkanin kafatanin rayuwa kuma babu abinda yakai ciwo irin cin amana ha'inci ko yaudara daga wajen wanda ka miqawa dukkan yarda aminci da kuma qauna,a maimakon ka samu ninkin abinda ka bayar.....ko ka samu koda ace kwatankwacinsa ne, a'ah......sai ka samu akasin dukkan abinda kai din ka miqa,ba kowanne yanayi muke fahimta ba.....har sai lokacin da muka samu kanmu a kwatankwacin irin wanna hali ko yanayin" kai afifa ke gyadawa,maganganun farheen sun shigeta,musamman daya kasance kamar wani tuni ne ta sakewa afifa bawai kuma don afifan ta manta ba,a'ah.....don dai kawai zuciyarta ta kwadaitu dason ganin wasu abubuwa masu kyau na wanzuwa cikin rayuwar sãahar din tata,gyara zamanta sosai afifa tayi tana fuskantar farheen tana kuma ajiiye meatpie din hannunta data gutsura saman dan qaramin farantin tangaran din data kirayi baaba sa'a ta kawo mata,ta kawo seriousness ta dora saman fuskarta,da gasken gaske abinda bakinta zai furta a yanzu yana daya daga cikin abubuwan da ya shiga list na burikanta a yanzu
"Amma anty......shikenan sanadiyyar kuskure ko son zuciyar wani sai kabi ka kashe taka rayuwar?,saboda wani laifi na wani can mutum guda sai ayiwa kowa kudin goro a tsundumashi cikin matsalar da babu ruwansa?,matsalar da baisan da wanzuwarta ba?" Kai farheen ta girgiza,bata kai ga cewa komai ba afifa ta dora
"Mahmud abba gana fa anty....... bakiga cin kashin da taso yi masa ba yau,don kawai yayi mata magana" tun kafin afifa ta qarasa farheen ta fidda dukka idanunta waje tana dubanta cikin yanayi mamaki matuqa da gaske
"How comes afifa?" Dukka kafadunta ta dage tana yarfa hannu,alamun abun itama sam bai mata dadi ba
No comments