SIRADIN RAYUWA Complete Hausa Novel

  •     *SIRAD'IN RAYUWA*





*_Wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wadda tasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*


*Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki*👇👇


ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*


_saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)_👇👇


 0903 234 5899


*IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU*👇👇



09033181070


_akwai yiwuwar ganin sabbin qirqirarrun sunayen garuruwa da gurare_




1995



*Tushen Labarin*





    Malam bilyaminu usman,haufaffen bafulatanin nijer a haihuwa da yare,ta wani fannin kuma d'an qasar *KAISA* kuma bahaushe magidanci mai halayya da dabi'u da al'adu irin na wasu daga bara gurbin hausawa,wadanda basu gama fahimtar abinda addini yayi magana akai ba kan iyali da haqqoqinsu dake bisa wuyan dukkan wani magidanci,walau saboda jahilci ko kuma sun take ne da gangan bisa son zuciyarsu da soye soyen rayuka.


     Haifaffen agadez iyayensa dukkaninsu suka kasance xallar fulanin niger,fatauci da neman kudi yakawoshi qasar kaisa,wanda a yanzun ita tazame masa mazauni na dindin.



      Shiga da saninki kusan shine laqabin da mutane suka yiwa gidansa bayan da halayyarsa tafito qarara na auri saki,mutum ne ma'abocin aure aure,wanda har hakan yazame masa jini da tsoka,bai kuma daukeshi a wani abun aibu ko abun Allah wadarai ba,ya auri mata aqalla da suka doshi goma,wanda mafi yawa daga cikinsu kowaccensu tana da yara a gidan,walau maza ko mata.



     Yana da tarin yara da suka kusa su ashirin da biyar,wanda dukkaninsu warin takalmi ne,mutum biyu uku uwarsu daban,harda masu mutun d'ai d'ai da uwarsu ta haifesu su daya tak cikin wannan gurguxu zuga da harqalla ta gidan,kamar yadda BILKISU take 'ya daya tilo da mahaifiyarta tahaifa cikin gidan.



      Kusan dukka wadan nan tarin yara nashi yara mata sunfi yawa,saidai mazan da aka soma haifa masa na farko farko mutum uku daga ciki sun tasa,babu wani batun samun sauyi salama ko tallafi daga tasawar da sukayi,domin suma kowannensu takanshi yakeyi,ci sha sutura ko muhalli mai kyau bai cikin tsarinsa bare akai ga jigo kuma uwa uba ilimi,hasalima za'a iya cewa baisan kwana da tashin wani cikin iyalinshi ba,kowa yana riqe ne da kanshi.



     Saidai kash,dukka wadan nan halayen nasa hakan bai hana a bashi aure ba,a duk sanda tabusa mishi,ko ranshi ya raya masa,yayi katari da budurwa ko bazawarar da ranshi ya kwanta mai da ita,tofa bazaiyi qasa a gwiwa ba wajen zage qwanjinsa da qarfin aljihunsa koda qarfin aljihun wasunsa ta hanyar cin basussuka yakashe mata kudi yakawota gidanshi.



    Dukkan matar daya aura takan fantama a lokuttan da take cikin amarci,takanyi yadda takeso,takumayi yadda taga dama,saidai kuma da zarar wannan dama ta subuce daga hannunta shikenan itama zata shiga sahun 'yan ci dakai da neman na wanki da wanka,wanda hakan kan sanya wasu kasa jurewa,wasunsu sukan kai harsu haihu,yayin da masu zuciya a kusa,masu qarancin haquri kan tafi da ciki su haife a gida,bayan wani lokaci su dawo masa da yaro ko yarinyar da aka samu.



     Cikin dukka matan daya aura mutum biyu ne tak suka iya jumurin xama dashi,mace tafarko itace kattume,wanda itace matarsa uku daya aura,tana da yara a gidan balaifi,hakanan takama sana'a ka'in da na'in,tana daukan nauyin kanta dana yaranta,hakanan cikin yaran takan yiwa wanda taga dama,hatta shi kansa malam bilyamun wani lokaci yakanci cikin arziqinta,hakan yasanya babu ganin girma girmanawa ko ganin mutunci tsakaninsa da kattume,idan ta hadosu babu wanda bazaiji kansu ba,bata shakka ko shayin zazzaginsa,ko lafta mishi baqaqen maganganu,hakanan yake zaune da ita shima saboda wataran yakan jingina da ita,sa'annan tazama tamkar wata kujera a gidan,duk wani harqallarsa da auri sakinsa a gaban idanunta yakeyi,hakanan za'ayi zaman a gama yasallami mace yasake jajibo wata.



      Mace ta biyu data juri zamanta a gidan kuwa itace maimunatu,maimunatu macen da bai taba auren matar dayaji sonta cikin jiki da zuciyarsa ba irinta,macen dayaso har zuwa randa tabar duniya,macen da haryau yake marmarinta duk da qasa tarufe idanunsa,macen da bata taba daga kai ta kalleshi ba duk da mugunyar halayyarsa.



Yakance maimunatu tayi!,saboda ta soshi,ta qaunaceshi,takuma zauna dashi,duk da banbancin ahalin,daraja,nasaba,kyau arziqi da dukiya dake tsakaninsu,tazarace mai yawa tsakaninsa da maimunatu,amma duka bata duba wannan ba,a zamanin tanunashi takuma zabeshi cikin dubban samari masu kyau dukiya da aji da take dasu a zamanin.



    Mahaifinta dan kasuwane da yayi suna,hakanan ya shahara wajen arziqi,kamilin mutum mai managartan halaye,nagartarsa tasanya bai duba matakin arqizin bilyaminu ba a wancan lokacin yadauki maimunatu yabashi,duk da cewa su biyu tak Allah ya azurtashi dasu a duniya.



      Duk da tarin wahala da fama da take a cikin gidan bata taba fasa halin da take ciki ba,tun mahaifanta suna da rai har Allah yadauki abinsa,hakanan taci gaba da zama dashi,sam babu jituwa tsakanin bilyaminu da qanwar maimunatu mai suna zuhriyya saboda yadda take ganin yana gasa 'yaruwarta,ita kuma bata daga kai bare ta nuba mishi bacin ranta,tsabar sanyin halin maimunatu yakawo hakan,tun zuhriyya na budurwa idan tazo gidan bata kwana,iyakarta awa biyu uku tayi tafiyarta,don tace ba zata iya ganin baqinciki da takaici ba,kusan har tafi maimunatu jin zafin abun,don ko gaisuwa bata hadata da bilyaminu,hakan yasa ya shina yake cike da haushinta,yakance

"Duk abinki dai baki isa ki raba qaunata da maimunatu ba"

"Dana isa din ai da tuni na raba wallahi da baka kai warhaka tare da ita ba".



      Haihuwarta tafari tasamu Bilkisu,yarinyar data fita daban cikin ahalin gidan da 'yanuwanta gaba daya,hakan kuma baya rasa nasaba da dangin mahaifiyarta data dauko wadanda suke jinin fulani,kakarta mahaifiyar maimunatu kuma shuwa ce.



     Yadda komai na halittar bilkisu yake daban tun tana qanqanuwarta,saiya zamana komai nata ma daban yake,tsafta kwalliya da ado kullum cikinsu take,maimunatu tana da tsafta gason gayu da ado,uwa uba alokacin takan samu kudi cikin gadonta da mahaifinta yabari,na gidajen da ake mata haya da sauransu.



Duk wanda yakalli bilkisu saiya kuma dubanta,komai nata tsaf gwanin birgewa,uwa uba ga kyau da Allah yayi mata,sai hakan yasake zame mata ado da qawa.



      Bilkisu nada shekara shida Allah yayiwa mahaifiyarta maimunatu rasuwa,duk dacewa a sannan tana da qarancin shekaru amma ta koka sosai,har hakan yabaiwa mutane mamaki,kukan nata saiya zama wani gwanin tausayi.



Zuhriyya kusan tafi kowa jin mutuwar ba kadan ba,tayi kuka tayi kuka har taji babu dadi,mutuwar 'yaruwarta daya tilo datake gani taji dadi ta girgizata matuqa,a lokacin saura watanni aurenta,amma babu yadda ta iya hakanan ta dangana.



A sannan taso daukar rainon bilkisu,amma bilyaminu ya qeqashe qasa yace sam bazai bata ba,dama can shiri suke na,bata taba nadamar rashin jituwarsu ba irin wannan lokacin,sai taji dana sanin bata aikata dukkan abinda ta aikata din ba sabida rasa damar daukar bilkisu datayi,ta wani bangaren kuma saita sake qullatarsa dajin takaicinsa,saboda duk sanda tatuna rayuwar da 'yar uwarta tayi duk da wadatarsu wanda shine sila saita sakejin qinsa a zuciyarta.



Ta fannin dangi ma bata samu goyon baya ba,kasancewar bata da aure itama riqonta ake, hakanan bikinta gab yake,tilas ta tattara ta haqura,duk da yadda taso daukar bilkisu kamar mutuwarta,saidai kullum tana hanya tana jelan ganin bilkisun,duk da tarin wulaqanci da take gani daga wajen bilyaminu amma tashanye,ita bilkisun kawai take kalla.



A sannan yarinyar bata gamu da wata matsala mai yawa ko.matsatsi ba,saboda zuhiryya kusan kwana a gidan ne kawai batayi,idan tayi nawar duniya ta tsallake kwana daya bata je ba,duk sanda taje zata mata wanka ta gyarata,ta siya mata duk abinda ranta yakeso,tawuni da ita,ta sanyata taci abinci sosai,a haka aurenta yatashi.



To yanayin aure bazaiyiwu tadinga sakaraftu ba kullum tana kan hanya,saiya zamana duk sati take zuwa ganin bilkisun,a sannan ta fuskanci akwai 'yan matsaloli na rashin kula daga matar uba dashi ubanma gaba daya,sai tasake ninka kulawarta akanta.



Ganin haka yasanya mijin zuhriyya sake shiga maganar karbo bilkisu,nan ma bilyamu yace Allah ya kasheshi shi bazai bada diyarsa ba,a sannan har duqawa zuhriyya tayi tana roqonsa kan hakan amma yace sam,haka tanaji tana gani ta haqura,saidai taci gaba da kulawa da bilkisun har zuwa tsahon wasu shekaru,wanda a sannan bilkisun takai shekara goma sha biyar.



A lokacinne yanayin aiki yadauke anty zuhriyya da mijinta zuwa qasar brazil,wanda zasu kashe shekara shida a can.



Ba qaramin tashi hankalinta dana bilkisun yayi na gaba dayansu,saida maigidanta ya kwantar mata da hankali,yakuma tayata shiryawa bilkisu duk abinda tasan zata iya buqata na tsahon lokaci.



To,ta hadu da uba mai son abun duniya,kusan duk abinda aka aje matan shida matarsa akaci,hakan yasanya kayan basuyi wani tsahon rai ba suka taru suka qare,abinda yarage mata kawai school fees dinta,wanda shima don anty zuhriyyan taje tabiya na shekarun da suka rage mata,hakanan islamiyya an mata total ta biya na shekarun.



A sannam bilkisu ta sake tantance tsakanin aya da tsakuwa,tasake gane dacin maraici da rashin uwa,ta gane ranar anty zuhriyya,saboda cikin qanqanin lokaci tasoma tagayyara,hatta da sitturunta zuwa wasu abubuwa nata masu daraja tasoma adabo dasu saboda ba ita kadai ke amfana ba.



Dalili kuwa shine,yarinyace da tunda tabudi idanu ta fahimci rayuwar gidan nasu Allah yazuba mata qauna da tausayin qannenta,kusan dukkaninsu suna qarqashin kulawarta ne,idan ka gansu saika rantse da Allah uwarsu daya ubansu daya,zata iya hana kanta tabasu,zata iya hana idanunta bacci su suyi,zata iya yadda ta wahala su su huta,saidai a wannan lokacin dukka wani qoqarinta yagaza,saboda bata da matallafi,sa'annan bata da wani sana'a ko aiki da takeyi.



Kafin wani lokaci tsanani yayi tsanani,wanda yasa tasoma tunanin wacce sana'a zata kama?,duk da bata da komai bata da kowa,saita soma wankau,lokacin da malam bilyaminu ya fahimci haka nan yadinga surfa ruwan bala'in ba za'a maida masa gidansa gidan tsummokara ba,duk da gidan na wani kyaune dashi na azo a gani ba,hasalima yana buqatar gyare gyare saboda tsufa daya soma yi,tanaji tana gani ta watsar.



Daga bisani tasamu aiki a maqotan unguwarsu,gidan wata mata da ake kira da umma luba.



Takan fita wajen aikinta tun safe har dare,wani lokacima takan kai goma kota kwana a can,Idan tatashi a aikin saita biya gida wajenta ta amsa,duka duka albashin nata dubu biyu ne da dari biyar,hakan yasa baya kaima tarin qannen dake gareta ko ina bare tasamu ta tsinanawa kanta wani abu.



Babban tashin hankalinta a rayuwa taga qannenta cikin wani mayuwacin hali na buqata,kuma bata da abinda zata basu ko tayi musu,wannan yasa tasake dagewa wajen daukarwa kattume tallan abinci ranakun da babu makarantar boko da safe kenan,kusan sana'arta kenan,wanda a ciki take ci tasha ta yiwa kanta da yaranta sutura,harma wani lokacin shi mai gayya mai aikin ya rabo yaci a jikinta randa yatashi bashi dako asi.



Ko daya kattume bata da mutunci ko tausayi musamman akan kudi,akan kudinta zata iya yin komai,bata da lamuni bare daga qafa ko misaqala zarratin,tana iya dafa abinci ta hana dukkan wani yaro dake gidan sai wanda taga dama ko kuma yaranta,takance

"Ubanku mara zuciyar bai kawo ba,don haka bazaku karyani ba,duk maiso yamiqo kudinsa yaci abinci" abun na matuqar baiwa bilkisu mamaki da daure mata kai,hakanan takan shiga tashin hankali duk lokacin da irin hakan tafaru babu kudin da zata baiwa kattumen ta bawa yaran abinci,idan 'yan mutuncin na kusa duk sanda ta dawo daga talla zata zuba mata maidan dama,anan ne zasu hadu duka suci,idan wannan bata samu ba,saita karbi bashi idan aka bata albashinta tabiya ta,tana kuwa rubuce da adadin abincin nawa ta karba din,hakanan tana ankare da lokacin biyan bilkisun albashi,da zarar lokaci yayi zata nemi kudinta.



_wannan itace BILKISU da salon nata rayuwar. Ko yaya nata SIRADIN RAYUWAR YAKE?,ku biyo 'yar mutan huguma,itake dauke da amsoshinku_



******  *******  **********



      *2005*




   K'arfe takwas na dare take takawa a hankali cikin layukan unguwar tasu,iskace irin ta sanyi ke kadata hagu da dama,tana kuma kada dan yalolon hijabin dake mannewa a jikinta kasancewarsa na roba,uwa uba tsufa da shan jikin da yayi wanda ya rage kaso hamsin cikin dari na kaurin asalin yadin.



Kusan hankalinta bai jikinta,tayi nisa qwarai cikin tunani wanda har hakan yasa ya bata damu da wanda ke gabanta ko bayanta ba bare gefanta,tunanin nata dukka yana kan qannenta data bari wuni guda sur yau a gida,batasab me sukaci ba yaudin,ko umna kattume ta basu abinci?,ko yauma tayi musu irin halin nata data saba,da yunwa suka kwanta ko kuwa sun qoshi?,duka ire iren abinda yake damunta kenan tunda ta fito daga gidan umma luba takamo hanyar gidan nasu,wanda duk da yake cikin unguwa daya suke amma akwai 'yar qaramar tazara a tsakaninsu.



Hannu tasa tadan share kyakkyawar fuskarta da takejin qurar hazo samanta,wanda hakan ita bai dameta,takan dauki lokaci mai tsaho kafin ta sanya mudubi gaban idanunta takalli fuskarta,duk wata halitta takyau da Allah yayi mata baiwarsa saidai tajita daga bakin mutane,bata taba tsaiwa ta kalla ba bare ta tantance,hasalima bata da wannan lokacin ko kadan a rayuwarta.



"Yammata daga ina haka?" Ta tsinci muryarshi daga bayanta,gabanta ne yayi wani mummunar faduwa,tun kafin tajuya tasan waye,ko kusa ko alama ta tsani duk wani abu da zaya hadata dashi,bata qaunar tarayyarsu ko alaqa dashi,hakanan ta tsani irin abinda yake mata,ita kwata kwata bata sanya kanta cikin jinsin mata bare har wani yace zai damu da rayuwarta da sunan soyayya,a wannan halin da take ciki?,tana ganin babban zaluncine a gareta wani dan adam ya takura mata da kalmar so ko qauna.



kalmace dako sau daya bata taba magana akanta ba walau a zuci ko a fili,a karan kanta ko ita da wani,towai dawa ma zatayi zancanta?,wa take dashi,bata da kowa bata da abokin magana shawara ko tattaunawa,bata da wanda zata gayawa shawara ko damuwarta face 'yan qannenta,wanda su kansu basu gama fuskantar rayuwar ko matsalarsu ba bare su fuskanci ta wani.



Koda tana da wani gata ko wani tsayayye,tana ganin babban zunubine a shekarunta qwalli goma sha biyar kacal ta jefa kanta a wannan layin.



Tana tsaka da wannan tufka da warwara yasha gabanta,yaja birki yana kallonta,tsantsar baiwar kyawun da Allah ya mata ta bayyana tarwai a dan ragowar hasken farin wata wanda hazo yayi nasarar dakushe kaso mafi yawa na hasken nashi,qare mata kallo yaci gaba dayi yana jin yadda yake sonta cikin zuciyarsa,bilkisu nada wani irin kyau mai sanyi da shiga zuciya,hakanan komai nata mai kyaune,kama daga kallonta,tafiyarta da maganarta,hatta da shurunta ma,komai nata abun burgewa ne,duk da tarin talauci da fatara daya musu katutu kuwa,yasha rayawa a ranshi wannan da a gidan wadata take ba shakka ba qaramin haddasa fitina kyawun nata zaiyi ba,matuqar yasamu dukkan wani abun buqata da zai bayyana kanshi yadda ya kamata,ba kamar yanzu daya tabbatar da cewa duk da yadda yake ganin kyawun nata fatarar da suke ciki ta wawashi kaso mai yawa ta boye ba.



Da wannan damar tayi amfani ta kewayeshi cikin matuqar sauri da wani irin hanzari tawuce,to ba ma'abociyar iya saurin bace ita,hakan yasa baiyi wani taku mai yawa ba ya cimmata,yayin da zuciyarta taci gaba da bugun uku uku,Allah Allah kawai take takai gida wannan qaramar alqar tasu ta yanke.



Dab da dakalin qofar gidansu yake a zaune,shi daya da alama yaudin babu 'yan tayin hirar nashi duk dare da suka saba zaman kisan dabe,masu matattar zuciya kusan irin tashi,kuma 'yan amshin shatar nashi,hakan yasanya tasu tazo daya dasu sosai

"Ke bilki,bilki!,zo nan" ta tsinci muryar mahaifin nata a sanda yana kwado mata kira a sanda take gab da shigewa soron gidan nasu.



A matuqar sanyi ta sauya akalar tata zuwa inda yake zaune,ta gefen idanu tana iya hango sabi'u wanda yasamu wani waje ya lafe bai qaraso inda suke ba sakamakon ganin mahaifin nata da yayi zaune a qofar gidan nasu.



A ladabce ta isa gabanshi kana ta durqusa da dukkanin gwiwoyinta,kanta na kallon rairayin dake shimfide gabanta

"Gani baba" sai yatashi yazauna sosai daga kashingidar da yayi,ya gyara hularshi dake niyyar zamewa tazauna sosai a kanshi

"Yauwa" yafada yana sake gyara zaman rigar wuyanshi kamar wanda ya qwaci kanshi daga hannun 'yan dambe

"Dama cewa nayi zan samu wani abune a wajenki?,yau natashi bani dako sisi wallahi,waccar kafirar kuma yau tsiyarta ta motsa ganin na tada sabon ginin dakuna,ta hanani abincin daren ma kwata kwata" wani dunqulallen abu mai tauri taji yazo mata iya wuya ya tokareta.

7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑    *SIRAD'IN RAYUWATA* 👑






*_Wannan littafin na kudine,amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*


*Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki*👇👇


ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*


_saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)_👇👇


 0903 234 5899


*IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU*👇👇



09033181070



2




Zuciyarta cike fal da mamakin halayya da dabi'un mahaifinta da koda yaushe take kwana tatashi dashi,tabbas babu shakka banda wasu abubuwa da suka bayyana qarara cewa shine mahaifinsu,da babu abinda zai hana ta musanta cewa ta tsatsonshi tarin yaran da yake dasu suka fito,ciki kuwa harda ita.



"Yi sauri ki miqo min mana maigado,yunwa fa nakeji ba 'yar kadan ba" yafada yana miqa mata hannayen nasa,sai data ja numfashi takaishi qasan hunhunta sannan ta daga oily eyes dake sheqi da walainiya kamar an diga musu mai,ga wanda bai sani ba kuma zaiyi tsammanin qwalla ta tara kuka take shirin yi,cikin sassanyar muryarta wadda ke bayyanar da yanayin nutsuwa da Allah yazuba a halittarta tace

"Bata biyani ba baba".



Wani baci ranshi yayi,kai kace ajiya yabayar yazo karba kuma akace mishi an kashe,hura hanci yayi yafidda iska zazzafa daga dukkan hanci da bakinsa yana jin takaici,don harga Allah yasa rai sosai da kudin,don ya jima da haddace ranakun da take karbar albashin nata,tamkar shike zuwa mata aikin

"Oho,kicemin aikin banza kike zuwa yi,babu uwa babu riba,duk yadda nadauke kai nayi haquri jumuri da juriyar barinki kina aikin ashe bazai iya kashemin takaicin komai ba,to gaskiya bazan lamunta ba" sosai gabanta yafadi,qafafunta sukayi sanyi harsai data kasa jurewa ta gyara durqusonta a gabanshi,tana tsoro,tana tsoron kada ya hanata zuwa aikin,wanda Allah da manzansane gatanta ita da qannenta sai aikin wanda bai kashe masu qishirwa koda cikin cokali cikin qishirwar abubuwan buqatun rayuwa da suke dashi,saidai duk da haka hausawa kance da babu gwara babu dadi,hakanan yafi babu,da sassanyar muryarta tace

"Ta yimin bayani baba,tace itama tana jira a biyata nata albashin ne saita sallameni,kamar daga can inda za'a bada albashin dukka ma'aikatan gidan ne basu nan" jim yayi yana tunanin ta inda zai wanye,idanunsa na hango masa inuwar hamza,kamar ya fahimci ya biyota ne yanason magana da ita,idan kuwa hakane yasamu inda zai samu kudin da yau zai siyawa bazawararsa tsire kamar yadda yacika mata baki yakuma alqawarta mata.



"Shi kuma wancan da kuke tare fa?" Ya fada yana nuna saitin inda hamza ke labe,gabanta yasake faduwa karo nabiyu,idan akwai abinda ta tsana shine babanta ya ganta da wani,akwai abubuwa masu tarin yawa da hakan zai iya faruwa da zubewar qima da mutunci da zai iya faruwa,kaita girgixa dasauri ba tare da juya takalli inda yake nuna matan ba,saboda tana da rauni,bata da qarfin zuciya wajen iya shirya qarya tazauna yadda yadace,farad daya zai iya ramfota,wanda ita kanta tasan hakan bazai mata dadi ba

"Babu kowa"qur ya mata da idanu,yafi kowa sanin halin bilkisu cikin yaransa fiye da kowa,yanayinta kawai ya karantar dashi komai,kamar zaice wani abu sai kuma yafasa yamaida idanunshi ga inuwar da yake hangowa

"Kai!,yaka!,fito nan!" Ya qwalla kira wanda hakan ya tabbatarwa hamzan da cewa yaganshi,saboda haka yafito sum sum kanshi a qasa.



Sam ba haka yaso ta kasance ba,yaso ace yajema mahaifinta tasigar data dace,ta sigar da addini ya shimfida,cikin girma mutunci da martaba,yanemi izinin zuwa wajen bilkisun.



A ladabce ya tsugunna gabanshi kamar yadda bilkisu ke tsugunne,kanshi a qasa yana shafa sumar kanshi cikin kunya yace

"Gani baba,barka da warhaka"

"Barka kadai" ya amsa mishi a gaggauce yana dan qare masa kallo ta hasken farin wata

"Da alama tare kuke da maigado,kaine surukin namu kenan?" Cikin kunya yasaki murmushi kanshi har yanzu a qasa ba tare da yace komai ba,sai ya gyara zamanshi donya qagu yakai inda yakeson kaiwar yatashi yawuce wajen lami,hankalinsa nacan wajen dare da dada yi

"To madalla,ai abu yayi kyau,Allah ya tabbatar da alheri"

"Amin baba,na gode,Allah yasaka da alheri"

"Amin yaro,ai babu komai,idan Allah yaso sai kaha bilkisu takace" sosai kalaman sukayi nauyi a zuciya da qwaqwalwar bilkisu,wanne irin nau'in rayuwa ce wannan?,baida masaniya ko damuwa ma da sanin waye hamza a farkom fari kafin akai ga kowacce magana amma har wani abu mai kama da yanke hukunci na qoqarin kunno kai ciki?,ama ture ta wannan da d'ai bata taba koda gwada yau gata a amatsayin ta wani ba,abu na qarshe a rayuwarta da bata taba tunashi ba,yayin da kalaman suka yiwa hamza dadi,don bai tsammaci komai zaizo da sauqi har haka ba,hakan yasanyashi ya karkata aljihun wandonshi na baya ganin baban yamiqe yanata karkade rigarsa wanda ba wani qura ta diba ba,yana yin hakanne saboda yakawo tsaiko da jinkiri koda hamza zaiyi wani abu.



"Ga wannan baba babu yawa" yafada yana miqa masa kudin daya zaro,babu wani kara alkunya ko tayi yasanya hannu ya amshe caraf yana fadin

"To Allah yayi albarka yaro kaji....ke maigado....zanje unguwa,idan kingama ki sakaya qofar" kai kawai ta iya dagawa tanajin yadda kowacce gaba ta jikinta tayi mata nauyi,daga haka ya juya yasoma bin layinsu yana qirga kudin bakinsa har kunne yana wassafa yawan bajintar da zaiwa lami dasu,wadanda yake fatan su zama silar da tarkonsa zai kama kurciyarta tashigo gidansa.



Shurune ya ratsa wajen,yayin da bilkisu ta kasa koda qwaqqwaran motsi daga inda take duqen,ta gefan hamza kuwa ci gaba yayi da kallonta,yanajin qaunarta da wani farinciki na takar sa'ar samun karbuwa wajen mahaifinta karon farko tana ratsashi,shi kansa ya yabawa kansa kan namijin qoqarin da yayi wajen tsallake matakai guda biyu masu matuqar tsauri a wajensa kafin isa kan bigiren da yake kai yanzu,mataki na farko shine fitowa ya bayyanawa bilkisu soyayyarshi a gareta,duk da wani kwarjini da kamewa ta musamman da Allah yayi mata,duk kuwa da qarancin shekarunta,mataki nabiyu yadda ayau harya tsaya gaban mahaifinta magana ta gudana a tsakaninsu.



A hankali tamiqe daga tsugunnon tasoma takawa zuwa shiyyar qofar shigewa gidansu,hakan shiya farkar da hamza daga duniyar tunanin daya tafi,cikin zafin nama yayi dan tattaki ya cimmata

"Bilkisu,ya zaki tafi ko gaisawa bamu...." A nutse ta daga idanunta ta kalleshi ba tare data furta komai ba,sai yaji kwarjininta ya cikashi harya danja baya kadan yana dubanta,ta kalleshine kamar yadda tasaba kallon kowa amma sai yaji wani iri harya kasa sake ce mata komai har zuwa sanda ta tura qauren gidansu dake dab da qarasa karyewa gaba daya su jingineshi tashige.



Ajiyar zuciya yasaki mai nauyi,yana qaunar bilkisu irin qaunar da baisan adadinta ba,duk da cewa shi a karan kanshi yana ganin kamar tafi qarfinsa a zubi da baiwar kyau da Allah yayi mata,kamar yadda abokanshi sukan sha gaya masa

"Hamza,kabar ganin yarinyar nan tafito daga gidan masu qaramin qarfi,ba tsarar aurenka bace,irinsu kyawunsu shune jarinsu,duk talaucinsu baka rasa wani hamshaqin mai kudin da zai qyallosu yayu wuf dasu,sannan uwa uba akwai qishin qishin din dangin babarta masu wadatane,ba'asan dai dalilin wanzuwarta a haka cikin wahala ba". Wadan nan kalaman dama ire irensu yasha jinsu bakin abokansa da yawa,amma yakan basu amsa da cewa

"A rashin tayi akan bar araha,a rashin kira kuma karen bebe ya b'ata,hakanan matsoraci baya zama gwani,kudai kubarni na gwada sa'ata kawai" da wannan tunanin yasaki ajiyar zuciya kana yasoma takawa yana barin layin,cikin zuciyarsa yanajin ko iya haka yasoma taka matakin nasara kan bilkisu,kuma yana fatan nan gaba nasarar tashi tafi haka.



Baqiqqirin tsakar gidan nasu yake,babu hasken fitila ko kadan banda wadda ke fitowa ta tsakankanin labulen dakin umma katti kamar yadda sukan kirata,banda tallafi da rahamar ubangiji na hasken farin wata babu abinda zai hana mutum mai qarancin gani yazuba tuntube a tsakar gidan nasu dake warwatse da kwanukan da sauran tarkace nan dacan,wanda basu wuce na sana'ar abincin daren umma katti ba,kusan haka al'adarta yake,duk sanda tagama sana'arta ta dare tashi take tawuce daka abinta tashiga sabgoginta na irgen kudi dakuma wassafa abinda zata siya gobe bayan tatake cikinta dana yaranta,dana mai rabo cikin yaran mijin nata,tacusa kudinta qasan filo tamaida kanta takwanta tahau jan minshari,aikin kusan na bilkisu ne,wanda duk safiyar duniya bayan ta idar da sallar asuba bata maida kanta ta kwanta,saita kintsa gidan,kana tayiwa qannenta wanka itama tayi tashirya cikin tsummokaran unifoarm dinta tawuce makaranta.


Ajiyar zuciya tasaki tadinga ratsa kwanukan tana wucewa zuwa dakinsu da take hango haske kadan kadan,wanda hasken take da yaqinin na acibal bal din data hada musu da kanta,amma tayi mamakin ina suka samu kudin kalanzir din suka zuba,idanunta nakan dakin cike da tausayin yaran harta isa bakin qofar dakin.



Da sallama ta daga labulen tashiga,dukkaninsu suna zaune kusan su goma gaban tabarma qwaya daya da sukayi tarayya wajen kwana akai,tun daga jikkunansu basai ankai ga fuskokinsu ba ya isa ka gane tsantsar rashin gata da kulawa dake tattare dasu,gamida buqatuwar tallafi cikin rayuwarsu.



A hankali take nazartarsu,fuskokinsu babu walwala sam,idanunta yasauka kan wacce ke kwance kan tabarmar,hauwa'u ce,da sauri ta cire takalmanta ta qara hanzari zuwa cikin dakin a dan rude tana fadin

"Subhanallahi,hauwa'u jikinne?"

"Tunda kika tafi yaaya yau bata fito ba,zazzabi take tayi" cewar daya daga cikin yaran,wadda tadan daresu duka a shekaru.

Saita waiwayo tana dubanta

"Baba yaga yadda take?" Ta tambayesu,sai kusan dukkansu suka kada kai

"Kunci abincin dare?" Tasake tambayarsu

"A'ah" suka bata amsa kusan a tare,don babu wanda cikinsu cikinsa baya kiran ciroma,ciwon 'yar uwar tasu ya sanya suka daina damuwa da yunwar sosai,don dama kwana da yunwa ba wani sabon abu bane a wajensu.



Zallar mamaki yasake cikata,wacce iriyar rayuwa suke haka wadda bata da wani maraba da rayuwar marayu,marayunma marasa galihu,wadanda basusan uwa uba ko wani dangi nasu ba,hauwa'u na daya daga cikin yaran da take matuqar tausayi cikin qannen nata,kasancewar taqamaimai a yanzu babu wani tartibin waje da za'a ce ga inda dangin mamanta suke,sakamakon fulani ne na tashi baban nasu ya aura,sadda xaman ya gagara sukazo suka mashi diyarsu suka bar masa tashi gamida karba mata takardar sakinta

"Ina hannatu?"ta tambayesu bayan ta lura da cewa bata dakin

"Tafita roqo mata magani a chemist" sakin hauwa'u tayi tamiqe da hanzari,sam bata qaunar idan dare yasoma yi taga daya daga cikinsu a waje,hannatu kusan itace babba a cikin yaran,saboda ta tasamma shekara sha hudu,shekara biyu bilkisu ta bata

"Ina zuwa" ta fada da hanzari tana ficewa,dukka yunwa gajiya,damuwa dama abinda ke damunta damuwar yaran saita murqushesu,tunaninta na farko inda zata sama musu abinda zasuci,na biyu maganin da hauwa'u zata sha kome qanqantarsa,tana tsaka da wannan tunanin sukayi karo da hannatu wadda itama ke tafe cikin damuwa,kasancewar hauwa'u ce aminiyarta cikin yaran duka gidan,duk da ta bata shekara biyu itama,amma tasu tafi zuwa kusa.



Sosai bilkisu ta hada rai tana dubanta

"Daga ina kike?" Maimakon ta amsata sai hawaye yabiyo kuncinta,cikin muryar kuka tace

"Naje samowa hauwa magani a chemist din bala amma ya hana" kukan yarinyar ya kashe mata jiki da zuciya sosai,maimakon fada dataso mata saita kasa,ta kama hannun hundatun

"Amma bana hanaku fita ba daga sanda akayi sallar magariba ba hindatu?ban isa na gaya muku kujiba?" Kai tashiga girgizawa sosai,har yanzu tana hawayen tace

"A'ah wallahi yaaya kin isa,jikinta ne har huci yakeyi,tanata rawar sanyi,shi yasa na kasa zama,amma kiyi haquri" shuru tasakeyi tana hadiye wani abu mai daci da tauri,yaran tamkar sun fahimci babban qalubalen rayuwa,gibi gamida nakasa da rayuwarsu ke ciki,sai suke qaunar junansu sosai tamkar uwa daya uba daya suke,tsahon wasu mintuna sannan ta iya bude bakinta

"Ki daina kuka,zata samu lafiya,amma kada ki sake fita,banason fitar dare kwata kwata" 

"To yaaya"

"Muje ciki" tafada,hannatun tayi gaba tana biye da ita a baya har zuwa tsakar gidan.



Dakinsu ta shige yayin da ita kuma ta durfafi dakin umma katti,bakinta dauke da addu'a Allah ya dorata a kanta,yasa tasamu abinda zata baiwa yaran suci sukwanta.



A hankali ta yaye labulen bakinta dauke da sallama,tana kwance kamar yawancin daga ita sai daurin qirji da dankwali mai santsi wanda bai dauru sosai ba,saijsn gwarti take abinta,duka rumfar tata cike da tarkace,yaranta duka sunyi bacci sai lariya dake zaune saman kan uwar tana cin abinci.



"Yaaya,kin dawo?" Tafada,kasancewar akwai fahimtar juna tsakaninsu,duk da yadda uwar kan kyaresu idan taga suna nunawa juna qauna

"Nadawo lariya,umma tayi bacci?"

"Eh amma bata dade ba" kan bilkisu tace komai lariya tasoma bubbuga saman kan umma kattin tana cewa

"Umma kitashi ga yaaya bilki tadawo" kafin takai ga hanata har umma kattin tatashi,a fusace tazauna dungurgur tana gyara zaman dankwalinta dake shirin zamewa tana duban lariyan

"Me za'a siya da saikin tasheni" sai datakai lomar shinkafar bakinta sannan tace

"Ba abinda za'a siya,yaaya bilki ce tazo nemanki" maficin da take firfita dashi wanda garin bacci yazame yafadi ta jawo takai mata bugu

"Shine don tsohonki zaki tasheni haka sai kace wata diyar gwamna,du randa kika sakemin irin haka saina sassabar miki" itadai lariya cigaba tayi dacin abincinta,sai data gyara zamanta sosai fuska a dinke ta maida kanta ga bilkisu wadda ke rakube kamar wadda ruwa yaciyo

"Bashina kikazo biyana da kika saka aka tasheni sa tsohon daren nan?" Gabanta ne ya yanke yafadi,babu alamun zata samu abinda tazo nema kenan da alama,kaita kada a sanyaye

"A'ah,amma in sha Allahu zuwa jibi za'a biyani zan kawo miki"shuru tayi ranta a bace na wasu sakanni sannan tace

"To meye?"da qyar ta iya buda baki tace

"zuwa nayi don Allah idan za'a samu sauran abinci wajenki,yarancan duka ba wanda yaci abinci,ga hauwa na kwance ba lafiya" sake dinke ranta tayi

"Ai kinsan rabon tsohonki da cefane a gidan nan ko kawo qwayar hatsi yau sati guda cur ko?,kuma duk randa yakawo din idan na dafa ba wanda nake hanawa ai" tasan magana ta yada mata amma saita shanye

"Nufina abincin siyarwa,saimu saka a lissafi...."

"Babu" ta fada da hanzari tana katsar numfashinta gamida juyawa da niyyar komawa ta kwanta

"Akwai wanda kika rufe da abun tatar taliya fa" raliya tafada,saita daga kai ta watsa mata harara sannan tace

"Tunda kece uwata aisaiki dauko ki bata ko?,zakici qaniyarki kema idan idan kika qureni,xan barki da iya abincin da tsohon naku ke kawowa kiga idan zaki rayu" daga haka ta maida kanta tayi kwanciyarta tana qananun mitoci

"Yara sai shegen ci,na rana ma dana dubi Allah nabasu ashe basu gani ba zuba idanun na dare sukeyi,sai kowa ya lashi walqiya ya kora da ruwa ai ya kwanta".



A sanyaye ta juya tafuta daga dakin tana tunanin meye dabara ta gaba,a haka har takai soron gidan batama sani ba,tana yunqurin fita wani tunani yazo mata,saita koma wajen tukwanen shinkafar umma katti dake jiqe.



Tsintsirar da ruwan dake ciki tayi a hankali har zuwa sanda ya qare,ya zamana saura qanzon shinkafa dake can qasan,cikin kwanukan dake wajen ta dauki guda daya ta wankeshi tas,sannan ta saka hannu ta dinga tsame qanzon tana zubawa a farantin,haka ta dinga yi harta tsame qanzon tas,ta sake wankeshi,ta tsaneshi dakyau,ta tsaya tana dubanshi sanda yake digar sauran ruwan da bai gama digewa ba tana wassafa yawanshi,duk da bashi da yawa,duk da bazai ishesu su qoshi ba,amma tasan a qalla zasu rage wata kafar,ba zasu kwanta da yunwa mai hana bacci ba,to amma inda gixon ke saqar inda zata sama musu mahadi,tasan cewa ba za'a rasa mai da yaji wajen umma kattin ba,amma tayi imanin koda ta roqa ma a yadda yau take kan tsininta ba zata bayar ba,tunda abun yau ba iyasu kadai ya shafa ba,harda mai dugungurun gum dinma gaba daya wato babansu.



Ta dauki tsahon mintuna kana ta taka da kwanon a hankali zuwa dakin,tana shiga kowannensu yazubawa farantin idanu,da alama a zaqe suke,hakanan cikinsu cike yake da yunwa,jira kawai suke su samu abun sawa a bakin salati,tausayinsu yasake cikata,inama ace wani abincine mai kyau da dadi a hannunta da zata ciyar dasu,wanda zasu kwanta suna murna cikinsu a qoshe taf kamar kowanne yaro mai gata da 'yanci?.



Saita isa tsakiyarsu ta aje farantin tana cewa

"Bari na samo maku mai da maggi ko gishiri kunji?" Fuskarsu fadade da fara'a da farinciki na qanzon da aka samu suka amsa da to,hannatu tace

"Umma tabarki kin debo?,dazu dazan kankare mana muci hanani tayi ta sheqa masa ruwa" tausayi yasake cikata har idanunta wannan karon ya hada qwalla,ba shakka duk yaron da aka haifeshi cikin gidan nasu ya fado cikin wata jarrabawa ne ta rayuwa,hakanan dukkaninsu ababen tausayi ne,duk da cewa gwara wasu da wasu a cikinsu,tunda akan samu wadanda iyayensu kan leqo da abun arziqi suga yaran nasu,saidai kusan da zuwan nasu da babu duka sammakal,don da zarar uban ya qyallara idanu yaga abinda aka kawo din zai rage mishi wani nauyi zai dauke,ko yace ayi amfani dashi a gida,wanda kwana daya ko biyu ya qare,maimakon abarwa yaron da aka kawowa yamora.



Kasa bata amsa tayi saboda batason suga qwalla a idanunta ko rauninta,tana tunanin idan sukaga rauni a nata idanun yaya nasu zuciyoyin zasu kasance?,saboda haka ta juya kawai tafice a dakin,saidai tana isa tsakar gida ta kasa riqesu suka soma bin kuncinta,tasanya tafin hannunta a hankali tana sharewa gamida dosar qofar fita gida qafafunta kamar ba zasu dauketa ba,duk da bata da yaqinin samun abinda zataje nema,amma tana fatan a dace kodon yaran.



Karo suka kusayi da wanda ke ke shigowa,dukkaninsu sukaja baya yana fadi cikin fada fada

"Kai,waye wannan?!"

"Nice" ta fada a tausashe tana daga kai don ganin waye,sulaiman ne,yaya a wajenta wanda suka hada uba daya,kusan rabi da rabi yake rayuwarshi a gidan,saboda kaf nauyinsa baikai mahaifinsa,d'a ne ga matar malam bilya ta farko wadda suka jima da rabuwa,tafiye tafiye yake qwadagonshi da neman kudinsa,kuma ba laifi yana samun na rufawa kanshi asiri,duk da bai tsinanawa uban komai sai abinda yaga dama,saboda haushi da takaicin yadda ya watsar da rayuwarsu dake cike a zuciyarsa.

7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑    *SIRAD'IN RAYUWATA* 👑





*_Wannan littafin na kudine,amana ne a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*


3



"Maigado?,ina zaki haka?" Ya fada bayan ya sassauta muryarsa daga fada zuwa sanyi,maimakon tabashi amsa saita sadda kai tana wasa da yatsunta,hawayen da take qoqarin riqewa tun dazun suka balle mata,daidai lokacin da nepa suka kawo wuta,hakan ya taimakawa sulaiman wajen ganin hawayen nata

"Lafiya?,cewa nayi ina zaki,idan babu amsa kuma matsamin nawuce"

"Zanje na samowa yara mai da yajin da zasuci abinci ne" shuru ya ratsa tsakani sulaiman najin takaici na sake ratsashi,mai hali dai bai fasa halinsa?,saiya sanya hannunsa a aljihun wandonshi yaciro dari biyar da yayi niyyar baiwa baban nashi a yau yamiqa mata

"Ungo wannan,ki saya muku wani abun" hannunta har rawa yake saboda murna da dadin dataji,wani abu da yaketa qulle mata numfashi tun dazun taji ya saketa,farinciki yacikata har murmushi ya subuce mata

"An gode yaya sule,Allah ya qara budi"

"Amin" ya fada yana binta da kallo sanda take ficewa cikin hanzari,sosai yarinyar take bashi tausayi,yana lura da kuma ankara da yadda take dawainiya da rayuwar yaran bakin qarfinta,tamkar ita ake haifawa su,ko kuma daga cikinta suka fito,ita kanta abar tausayice,saboda baya manta sanda mahaifiyarta take raye gatan data samu,baya kuma manta sanda anty zuhra take nan,duk da baisan meye dalilin bacewar anty zuhran da daina ganin gilmawarta cikin rayuwarta ba,da wannan tunanin yacusa kanshi cikin gidan.



Abu kala kala ta dinga ayyanawa a ranta,tayi tunanin siya musu suci su more a daren da kudin,har tayi hanyar sai kuma taja ta tsaya turus tana juya kudin a hannunta,idan har tace zata siya musu abu me dadi suci to kuma gobe fa waye zai basu?,hakan ya sanya ta sauya tunani,ta nufi kanti ta siya musu garin kwaki da suger,sannan tashiga gidan gwaggo rabi maqociyarsu ta siyi mai da yaji maidan dama,takuma siya gasarar koko da yake suna saida ita,ta ayyana a ranta gobe bazasuyi tashin yunwa wunin yunwa ba,mai da yajin yanzu zata zuba musu a qanzon suci,ta rage wani gobe ta kwada musu da garin,da safe kuma ta dama musu kunu susha,tuna hakan kawai ya jefa murmushi kan fuskarta,harya bata qwarin gwiwa da karsashin nufar gida bayan ta siyawa hauwa'u paracetamol satches daya,tana fata ko zazzabin ne kawai ya saukar mata,duk da tasani ba shine ainihin maganin daya kamata tasha ba,amma ragi ragi ne.



A hanzarce tashiga soron gidan nasu wanda jan qwai na wuta ya haske,saita hangeshi rakube daga bayan qofa riqe da takardar tsire yana kaiwa baka da sauri da sauri,da alamu baison wani ya ganshi,gabansa kuma robar fanta ce qaramar 35cl.



Motsin da yaji ya sanyashi saurin cilla ledar tsiran da gara robar saqon qofar yana boye hannunsa dake cike da maiqo da quli qulin tsire,saita sadda kai kamar bata ganshi ba zata wuce,yayin da jikinsa yabashi cewa tariga data ganshi,saboda haka yahau nade tabarmar kunya da hauka

"Ke maigado daga ina kike a daren nan?" Kafin ta bashi amsa yadora da bambami

"Banason iskanci da diban albarka fa,wato yawon dare kikeson koya ko?,ina cewa baki jima da dawowa daga wajen aiki ba shine yanzu zaki sake zargawa qafarki igiya ki fice?"

"Kayi haquri baba,maqot...."

"Rufen baki ki wuce ki bani waje,sakarya kawai" bata sake yunqurin cewa komai ka kare kanta ba tawuce ciki,don dama ta qagu ya sallameta din,tunda tasan fadan gwaggo a kofa yakeyi,idan da sabo ta saba da ganin dabi'unsa kala kala,ita abinda yafi damunta yabarta takaiwa 'yan uwanta abinci,idan yaso idan tadawo ko gutsi gutsi da namanta zaiyi yayi.



A zagaye ta samesu da farantin qanzon kai kace tururuwa ta samu hasken candle guda daya,tasauke ajiyar zuciya tana godewa Allah daya sanya tasamu mahadin da zata kawo musun,da batasan ya zataji ba a yadda ta samesu.



Cikin hanzari ta hada kwadon tsaf,tasa kowanne ya wanke hannu suka soma ci a tare,bayan sun gama ta baiwa hauwa'u paracetamol din tasha sannan sukayi shimfida da zannuwan da sukan lullube sumuntin dakin su kwanta.



Sai data tabbatar da kowanne ya sanya haqarqarinsa ya kwanta sannan ta zare yalolon hijabinta ta fita zuwa tsakar gidansu dontayi alwalar da zatayi shafa'i da wuturi,abu na qarshe da takan gabatar duk dare kafin ta kwanta,saboda bakoda yaushe take samun damar tashi sallar tsakar dare ba.



Tana bakin famfo a duqe tana daura alwalar amma tana iya jiyo cecekucen baban nasu da baba katti,cin mutuncine dai data saba masa duk sadda ta hadosu,tana iya jiyoshi yana cewa

"Abincine dai ki jiqa kayanki ki sha,da baki bani ba ai Allah yabani wanda yafi naki,bakin da Allah tsaga baya hanashi abinci,kuma wallahi nasan maganinki,na gane take takenki,saboda kwana biyu kina ganinki ke kadaice cikin gida kike tunanin kinfi qarfina kinsha kaina,to zanyi maganinki ne,mu zuba dani dake,shege ka fasa" qaramar guda umma kattin tasaki kana ta dora da cewa

"Ahayye,yoni Allah na tuba wane darene jemage bai gani ba?,aisai na ranar mutuwarsa,kare kuma da kudinsa sai yasha lahaula,kai kaga zaka iya,ga fili nan ga mai doki saura sukuwa...." Itadai daga haka tasamu ta gama alwalarta tashige daki tana mai qyamatar rayuwa irin ta gidansu,ta tuna mahaifiyarta,duk da cewa sanda tarasu bata da wayo amma tana iya tuna wasu abubuwa dangane da ita,hawaye ya sake cika mata idanu sanda taga nan da nan bacci ya kwashe yaran,ta kabbara salla tana maida dukka damuwarta baya don ganawa da ubangijinta.



Ta jima saman abun sallar tana addu'a kamar yadda tasaba sannan ta shafa,ta nufi can bangon dakin inda akwatinta take,wadda asanda take sabuwa ta zuba kyau da d'aukan hankali,anty zuhra ce ta taba siyo mata ita dab da sanda zasu tafi,budeta tayi ta ciro unifoarm dinta tana dagawa,tun daga tsarin dinkin da kalarsu zakasan cewa na private school ce mai tsada,duk da yadda suka tsufa amma tsarinsu bai bace ba,a wanke suke fes kamar yadda bata taba barinsu babu wanki duk da yadda suke neman agajin hutu saboda tsufa,saita zauna anutse tasoma musu ninkin guga,ta shinfidasu qasan wajen kwanciyarta,tana fatan su miqe kafin safiyar gobe,saboda batasamu gogesu ba yau,duk da cewa a kwance suke saboda laushi da sukayi dakuma sabo da guga,sai data gama jerasu sannan ta shinfida zaninta a sama ta kwanta kamar sauran 'yan uwanta.



Ta kafin bacci ya ziyarci idanunta saboda tarin tunane tunane na rayuwa da abubuwan da suke cikinta na qalubale iri daban daban,daga qarshe dai sarkin barayin yayi nasarar saceta,baccin da yake cike da mafarkai na burikanta na rayuwa da takeso ta cimma,ciki kuwa harda inganta rayuwar qannenta.



*****   ******   ******  *****



Sanye da daurin qirji da kuma lullubin hijabinta tashigo dakin nasu wanda yake share fes kamar ko yaushe,kai bakace ana kwana a dakin ba saboda tsananin tsafta,duk da cewa babu komai qasan dakin sai sumunti da kuma tabarmar da kusan rabi da rabinta a cinye yake da suke kwana akai amma saika zuba abinci akai kaci.



Fitowarta kenan daga wanka bayan tagama tsaftace gidan,takumayi wanke wanke kamar yadda tasaba kullum kwanan duniya,sai data tsugunna ta rarrabawa duka qannen nata kunu a cikin kofin sannan ta miqe tasoma shiryawa,idanunta akan ratattaken agogon da iya awanni kawai yake iya nuna mata,ta maqalashi saboda tashinsu sallar asuba dakuma lokacin tafiyarta makaranta,tana qiyasta mintinan da zasu kaita makaranta daga nan gida,tana saka ran ta isa kafin lokacin da za'a soma assembly yacika.


Mai kawai ta shafa,sannan ta goga alimun a hammatarta,kafin ta dangwali turarenta dan duri da take siya duk qarshen wata,unifoarm dinta dake saman akwati ta dauko tahau sanyawa,cikin mintina qalilan tagama shiryawa tsaf.



Wani irin sassanyan kyau unifoarm din sukayi mata,kai kace wasu kaya ta saka na azo a gani,ya fidda sigarta sosai fiye da kayanta na gida,abu dayane tak ya musu cikas tsufan da sukayi,saidai tsaftarsu tadan boye wani daga cikin aibunsu.



"Takwas tanayi hannatu karki bar kowa kuwuce kamarantar allo,kar nadawo acemin yau wani baije ba,hauwa'u kawai na yarda abari tasake jin qwarin jikinta tukunna"

"To yaaya" hannatu ta fada sannan suka fara mata rige rige na adawo lafiya tana amsa musu harta fice daga dakin,ta ratsa tsakar gidan nasu tana wuce custumers din baba katti dake siyen qosai harta fice daga gidan gaba daya ta dauki hanya cikin nutsuwa kamar yadda tasaba.



Ajiyar zuciya tasauke sanda tashiga harabar makarantar taga ba'a fara fita assembly ba,hakan ya alamta mata ba qaramin sauri tayi ba.



Kamar ko yaushe ajin yasoma cika,saboda makarantace dake da tsari da doka,ba kasafai dalibanta ke makara ba,duk da cewa makaranta ce ta 'ya'yan masu hannu da shuni.



Babu wanda zaiji sallamarta ma idan tayi saboda kowa sabgar gabanshi yake,hayaniya ce ke tashi,saboda haka saita wuce direct sit dinta,wanda kowa dama yasan wajen zamanshi kuma anan yake zama koda yaushe,kujerarka da table dinka kai kadai harda 'yar locker daga qasa.



Ganin kamar akwai sauran lokaci yasa tazauna tazuge jakarta tana sake gyara zaman litattafanta,gamida sake dubasu daya bayan daya taga kota dauko kowanne,lokaci lokaci masu shigowa takan daga kai ta amsa sallamarsu,wasu idan sun kirayi sunanta ta amsa tare da qoqarin dora murmushi kan fuskarta.



Kusan ita daya take rayuwa cikin ajin tsahon shekaru,bata yarda ta rabi kowa ba,kamar yadda babu wanda ta bawa fuskar ya rabeta,ta sani ko ba'a gaya mata ba dukkaninsu kaf ajin matakin rayuwarsu da nata ba iri daya bane,kallo daya zakayi ka tantance hakan,akwai mutane da dama da sukaso qulla qawance da ita amma ta toshe wannan kafar,wanda hakan yasa wasunsu suka qullaceta suke ganin tsabar girman kaine,ko don taga tana da kyau?,ko kuwa ubanta qila wani shegen ne wanda wala'alla yafi dukka nasu iyayen hawa tudun muntsira.



A hankali daga bisani kuma sai abubuwa da yawa da suke gani tattare da ita suka sauya tunaninsu suka sakasu acikin duhu,na farko dai ita ba'a mota mai kyau da tsada ake kawota kamar su ba,koda motar haya bata hawa bare akai ga ta gida,a qafa kulli yaumin take zuwa,abu na biyu,bata zuwa da abinci mai tsada irin nasu hakanan idan lokacin break yayi bata kashe ko ficika da sunan siyan wani abu da zata saka a bakinta,hasalima saidai ta dauki litattafanta a sannan ta sake sabon xaman karatu,ko kuma tafice daga ajin tatafi can baya inda babu mai ganinta bare ya dameta ta zauna,harsai an gama sannan tadawo cikin aji,na uku tunda suka soma karatu basuga wani sauyi daga sutturar unifoarm jaka ko takalmi ba daga gareta,kamar yadda yawancinsu ba unifoarm guda daya garesu ba,duk da haka kuma lokaci zuwa lokaci sukan sauya da sabo koda ace bai tsufa ba,wannan sune abubuwan da suka sauya tunanin wasu da dama a kanta amma banda mutum guda AFNAN ABDALLAH KAISA.



Yarinyar da jinin sarauta ke zagayawa a jikinta,hafaffiyar diya ga sarki Abdallah mu'az kaisa,babbar masarauta wadda keda qarfi iko da kuma izza,masarauta ce mai matuqar girma da fadi da iko cikin dukka masarautu dake nahiyar,masarautar da a tarihinta dama can gwarzuwar masarauta ce wadda tayi shuhura takuma yi suna.



Baya ga jinin sarauta dake yawo a jikin afnan 'yar gata ce wajen mahaifiyarta,sannan uwa uba Allah ya hore mata baiwar kyau hakanan tana da qwaqwalwa da basira da saurin gane karatu,saidai dukka wadan nan abubuwan sai taga tamkar bilkisu bilyamin nason zartata kyau dakuma kaifin basira,sannan yanayin da take kallon bilkisun tana mata kallon mai zallar girman kai,bayan bataga wani abu da zata nuna mata ba game da gata ko sarauta,kusan kowa na ajin neman fada yake a wajenta dason samun shiga,amma sai taga hakan sam bai damu bilkisu ba bare ya dadata da qasa,hasalima rayuwarta take ita daya abunta ba tare data damu da shiga sha'ani ko shirgin kowa ba,sai Allah ya jarrabi afnan da dora dukka idanunta da damuwarta kan bilkisu,tana fata dai dai da rana daya bilkisun ta rabi kota shigo gonarta,amma hakan bata taba gittawa ba,dalili kenan daya sanya haushin bilkisu yasake cikata,tasake amannawa ranta cewa zallar girman kaine kawai ke damun bilkisun ba komai ba.



Hakan saiya haifar da takura ga bilkisu,afnan ta sanya mata idanu duk wani motsinta,koda hanyace ta hadasu sai tayi wani abu na nuna wulaqanci takura ko muxanci a gareta,babu abinda bilkisu ta tsana a rayuwa irin wulaqanci muzanci ko toxarci,tana da haquri dauke kai da kawaici,to ammafa bata jurar wulaqanci,duk inda tasan zata wulaqanta idan tashiga takanyi namijin qoqarin janye jikinta daga wajen,ta san afnan din ko wacece,don tanajin yadda sautari 'yan ajin ke hirarta gamida yadda kowa keson ace itace babbar qawa a gareta,duk da kuwa har yau bata da wata gwana guda daya a cikinsu,ta auna takuma sani cewa ita din ba kowan kowa bace akanta,dalili kenan daya sanya tasake qauracewa hada koda hanya da ita,babu abinda take bari ya gitta tsakaninsu saidai tsautsayi wanda baya wuce ranarshi,tsakaninta da afnan ko kallo bata bari ya hadasu saboda gudun bacin rana,tana gudun ranar da zata kaita bango ta tabbatar abun bazai musu dadi ba,wanda bata fatan hakan saboda gudun fadawa bigiren da ba nata ba,tunda tasani koma meye yafaru ita zafa zamo a qasa,bata da wanda ya tsaya mata,bata da wani gata bare galihu irin nasu.



     Ã†™ararrawar data buga ita ta alamtawa kowanne É—alibi lokacin fita assembly yayi,hakan ya sanya kowanne É—alibi tattara komatsansa zuwa filin assembly,ciki harda bilkisu.



Kamar kullum haka tabi layi da kowanne dalibi kebi saboda gudanar da abun a tsare,a É—arare take kamar kowanne lokaci,gani take kamar kowa kallonta yake,kamar kowa ya lura da tsufan unifoarm dinta,kamar kowa yana iya ganin aibun dake tattare da ita.



Cikin sahun daliban daya dake baya ta tabo ta gabanta tana shuna mata bilkisu wadda rashin tazara dake tsakaninsu yasanya karaf idanuwan bilkisun ya nuna mata su,amma saita dauke kanta ta maida idanunta ga abinda ake gabatarwa a wajen,duk da haka kunnuwanta suna iya jiyo mata maganganunsu,duk da cewa dafarko bata jin me suke fada

"Gafa mutuniyarki" saita tabe baki

"Sai shegen kyau amma da alama babu abun" dariya suka saki ƙasa ƙasa sannan ta sake cewa

"Anya ko ba 'yar aikin wani gidan bane suka taimaketa suka sata a school din nan?,don ko kusa ko alama batayi kama da wadanda iyayenta zasu iya sata a nan ba" dariya dayar tasake ƙunshewa sannan tace

"Da alama dai kam..." Maganar da principal yasoma ita taja hankalinsu ya hanasu ci gaba da tattaunawa akan bilkisun,wadda tuni tashiga dogon nazari da tunani,abinda ta fuskanta shine,duk sanda talaka yayi gangancin shiga tsarar masu hannu da shuni ya banu?,ba gasu iyayen ba baga Æ´aÆ´ansu ba,ta lura kamar gado ko kuma halayyace a jininsu,mafi yawa yaran suma sukan taso da irin wannan É—abi'a da halayya irin ta iyayensu,saboda za'a iya cewa sun taso sunga sunayi.

7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑    *SIRAD'IN RAYUWA* 👑





*_Wannan littafin na kudine kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*


09032345899

Ko

09033181070


*_KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.._*




4




    Har aka kammala assembly É—in ba zata iya tuna abu Æ™waya É—aya data É—auka ba,bata dawo hayyacinta ba sai data tsinto sunanta ana kiranta amatsayin wadda zata rufe taron da karatun Æ™ur'ani,kamar yadda tasaba yawancin lokuta ita ake kira.



      Wata baiwa ta musamman Allah yayi mata na dadin murya da iya rero Æ™ur'ani,saidai zata iya cewa ta tsani wannan kiran,kiran yakan sanyata taji gaba daya ta muzanta,kana ta tsargi kanta,amma babu yadda ta iya haka ta taka zuwa gaban taron assembly din dake cike da dalibai da malamai,cikin daddaÉ—ar muryarta dake cike da tsoro har tana É—an rawa rawa tayi basmala sannan tasoma karanto ayoyi daga cikin suratul anbiya'i shafi na qarshe.



   Kamar koyaushe dukka idanu sukayi mata caa,kowanne akwai abinda ke kawo cikin ranshi dangane da ita,wanda mai tunani na Æ™arshe ke ayyana

"Kyakkyawar sura mai É—auke daddaÉ—ar murya,cikin tsaffin tufafin makaranta",abu mafi ban mamaki a idanuwansu,don kaf fadin makarantar babu wanda yake da suturar unifoarm maqasqanciya irin tata,banda Allah yayi mata baiwar tsafta da iya kula dasu da ba'asan yanayin da zasu kaya ba,ita kanta tasan da cewa zasu tashi tamkar na almajirin dake karatu a tsangayar da babu kulawa.



   Gamawarta yayi dai dai da shigowar motar dake kawo afnan makaranta,wanda hakan ke nuna yau ta makara kenan,wanda ba kasafai hakan ke faruwa ba,bata daga cikin sahun daliban dake makara,gajeran jawabi aka dauraye dashi kana aka sallami kowanne É—alibi kamar yadda aka saba.



    Dai dai Æ™ofar aji sukayi kaciÉ“us da afnan wadda ke Æ™oÆ™arin amsar jakarta daga hannun wata matashiya da suke kusan sa'annin juna,wadda kusan koda yaushe itake riÆ™o mata jaka da sauran abinda tazo dashi makarantar har zuwa Æ™ofar aji,wani lokaci kuma har mazauninta,duk da cewa itama É—aliba ce amma da alama an sanyata makarantar ne musamman saboda afnan É—in,don kusan itace take mata dukkan wata hidima data shafi makarantar,kamar É—auko mata jaka yayin zuwa da komawa,da kuma kuma kawo mata abincin break,siyo mata wani abu idan tana da buÆ™ata dadai sauransu.



    Wani kallo ta jefawa bilkisu,wanda sarai ta ganta amma ta É—auke kanta kamar bata ganta,don ita ko É—aya bata a cikin lissafinta,hakanan bataga na meye zata damu kanta da rayuwar wani ba.



    Kamar kullum kuma kamar ko yaushe,ta bada dukkanin hankalinta ga karatunta,don tanaji a zuciyarta shine abu guda É—aya tak da zai iya kaita ga tudun muntsira nan gaba,duk da bata da yaÆ™inin yadda rayuwa zata kasance anan gaba,akwai yiwuwar ci gaba ko kuwa guguwar data afko tsakiyar rayuwarta zata sanya dukkan Æ™arfinta ta sake aza mata nauyin da dole zai sanyata takai Æ™asa saman gwiwoyinta?.



    Daidai lokacin da aka saba fita don É—alibai su huta na tsakiyar lokacin karatu aka kada Æ™ararrawa,babu É“ata lokaci kowanne yasoma tashi daga mazauninsa don yasamu ya sarara yakuma huta,ga bilkisu ma haka take,saidai yau ta É—anyi nawa sakamakon note da bata gama kwafa ba saman allo,gwanar sauri ce ta fannin rubutu,amma saboda wanki data mai yawa jiya a gidan umma luba na kayan sawarta yatsunta ke mata zugu har zuwa yanzu,tayi wankinne tana fatan idan an lissafa zata hada mata da albashinta wani abu ya daÉ—u akai wanda zata riÆ™e a hannunta bayan ta gama biyan bashin umma katti saboda Æ™annenta da bata Æ™aunar ko misÆ™ala zarratin tagansu cikin yunwar da bata da abun basu.



Mintina goma kyawawa ta daɗa kafin ta kammala,zuwa sannan ajin nasu yasoma ɗumamewa da ƙamshin abinciccika da kuma snacks kala kala,ta zuge jakarta a nutse ta maida littafinta,kana ta zari wani da zata duba zuwa lokacin da za'a koma ɗaukan darasi.



   Dai dai lokacin afnan da Æ™awayenta suna saman babbar darduma mai kyau da laushi da sukan shimfida suci abinci anan,wanda duka cikin kayan afnan ne da take zuwa dasu,gab da zata qaraso inda suke ta jiyo jan tsakin afnan din,cikin murya dake cike da izza tace

"Bansan nayi kuskuren zabar school din nan ba sai daga baya,nayi tunanin zata zama best makaranta cikin list na makarantun da magajiya tabani na zaba,sai kuma naga kaman ba haka ba"

"Me yafaru?" Halima ƙawarta dake buga game a tablet dina ta fada bayan ta dakata da game din da take,kaman ba zata amsa ba sai kuma tace

"Ina ganin mutanen da ba ajin rayuwarmu daya ba a cikinta,hakan ai zubewar girma ne,qasqanta ce a wajenmu" ƙarshen maganar tata yazo daidai da sanda bilkisu tazo dab dasu,dukka sai suka ɗaga kai suna kallonta kana suka sheƙe da dariya,saboda sun fuskanci inda maganar tata ta saka gaba

"Don't mind mana......kinsan da yadda aka shigone?,may be 'yan alfarma ne kamar yadda basira take tare dake anan,ki gane mana" farha É—aya daga cikin aminan afnan ta fada.



     Wani abu ta hadiye tanajin maganar na mata suya har cikin ranta,É—aya daga cikin dalilan kenan daya sanya bata bari koda hanya ta hadata da afnan din,saita Æ™ara sauri tafice daga ajin gaba daya,tana Æ™oÆ™arin sharewa da manta abinda kunnuwanta suka jiye mata.



    Æ™arfe biyu na rana aka tashi kamar yadda Æ™a'idar makarantar take,kamar yadda ta sabawa kanta tana daga cikin sahun farko farko na É—aliban da suke riga kowa fita daga makarantar,saidai yauma tayi nauyi kamar dazun,sakamakon kwantan note da malamin daya shigo musu a period din Æ™arshe ya musu da bata kammala ba,da sauri sauri ta kammala ta hade kan litattafanta ta baro ajin,gaba daya hankalinta kuma yakoma kan Æ™annenta da gidan aikinta,tana fatan yau idan taje ta dace umma luba ta sallameta da kudin aikinta.



     Kamar kowanne lokaci dai harabar makarantar zuwa wajenta akwai ababen hawa sosai,waÉ—anda dukkaninsu sunzo É—aukan É—alibai,haka ta dinga ratsawa harta samu hanya tafice gaba daya tadauki hanya zuwa gida,cikin tafiyarta dake cike da nutsuwa da kamun kai,saidai tun batayi nisa ba taji Æ™ugin mota daga bayanta,wanda kafin a ankara tazo ta wuce da mugun gudun daya haddasa tashin Æ™ura har saman fuskarta,da hanzari ta daga kai tabi motar da kallo,É—aya daga cikin motocin masarautar kaisa ne,gakuma tabbacin fuskar afnan ta glass,wanda suna haÉ—a idanu taja glass din xama ta zuge.



     Kai kawai bilkisun ta kaÉ—a,wai na meye?,meta tsare mata?,da wannan tunanin da É“acin ran tadinga takawa zuwa gida,zafin rana qura da yunwa irin ta kowanne dalibi dake kwasota daga makaranta tana sakadarta.



Dukkaninsu babu wanda bai haddace lokacin dawowarta daga makaranta ba,saboda haka batayi mamaki ba data samesu zaune dukkaninsu suna dakon dawowar tata,ƴar rige rigen taryarta suke,tana kallonsu fuskarta cike da murmushi,zuciyarta cike da farinciki idan ta tuna a ranar yau tana da abinda zata basu suci,babu abu mafi ɗaga hankali da sanyata cikin ƙunci irin ranar da zatazo,suyi mata irin wannan tarbar amma bata da abun basu.



Sai data dora hannunta saman kan kowa ta amsa oyoyo ɗinsa,hauwa ce ta ƙarshe,ta dubeta cikin kulawa

"Fillo(da yake wani lokaci da sunan da take kiranta kenan),kice yau da celebration jiki yayi kyau kenan ko?" Kaita daga tana murmushi

"Na warke yaaya,naji sauƙi ai,harma na ɗebowa umma katti ruwa" duban yarinyar take sosai,ba zata hanasu yi mata aiki ba saboda ko babu komai a matsayin babarsu take,saidai wani lokaci tana mamakin rashin imani da tausayin umma katti,a yanzu tana da yaƙinin idan ta ƙarasa cikin gidan akwai abinci cikin abincin da take saidawa,amma babu wanda zata iya sanma cikinsu,idan kaga ta bayar ta ranar ba ƙaramar sa'a suka taka ba,ko ranar babansu ya kawo cefane,ko wani cikin custumers dinta yaji tausayinsu ya siya musu

"Ya akai hannatu?" Bilkisu ta tatambayeta sanda take kada kansu zuwa cikin gidan ganin yadda tazuba mata idanu,saita saki murmushi tace

"Babu komai" daga haka ta hada kansu dukka suka shige ciki.



Ilai kuwa tana tsakiyar kulolin abincinta tana ciniki tana haɗa kan kuɗinta,tanayi tana 'yan waƙe waƙenta duniya tayi mata daɗi,donko kula da sannu da gida da bilkisu tayi mata batayi ba,itama bata damu ba ta jasu suka shige daki,domin idan da sabo ya zame mata jiki,ba baqon lamari bane a wajenta.



Tasan yunwa suke ji,saboda haka tasoma ɗauko garin ta wanke tabarshi ya jiƙa kafin ta sauya kayanta,wanda da zarar ta dawo take fiddasu daga jikinta,bata sake tabarsu,don idan tabarsun suka sake jin jiki bata da wata madafar.



    Tana canza kayan tasake lura da hannatun dai tana kallonta kamar dazun,sai data gama sanya atamfar tata riga da fallen zani wadda tadan soma jin jiki tayi haske daga ainihin kalarta ta daura dankwali sannan ta isa gaban hannunta ta duÆ™a

"Anya kuwa lafiya kike hannatu?irin wannan kallo?,kamar yau yaaya maigadon ta zama baquwarki ne?" Sai ta saki murmushi wanda idan kalura dakyau akwai abinda ke damunta a zuciya,saita sake kallon nata sannan tace

"Ba abinda yake damuna yaaya,kawai ina sha'awar yadda kike zuwa makaranta abinki,sai nakeji a raina dama nice ke,inason naga na iya karatu da rubutu irin naki,inason na zama likita nadinga saka fararen kayan nan,ina yiwa mutane allura" daga yadda take maganar zai gaya maka har cikin zuciyarta da gaskene,hakan saiya kashe jikin bilkisu,ta ƙaƙaro murmushi tace

"Hannatu,wannan karatun saboda ku nake,saboda kuma ku samu kuyi karatun nake nawa karatun,karatuna nakune,na muku alƙawarin in sha Allahu nan gaba dukkaninku sai kunyi karatu yadda ranku yakeso,kowa zai zama abinda yakeso da izinin Allah,kudai kuyimin addu'a ko yaya nasamu aikinyi kunji" dukkaninsu babu wadda fuskarta bata faɗaɗa da fara'a ba,wanda hakan ya nuna mata yadda sukeson karatun sosai,saidan kawai babu yadda zasuyi ne,da wannan murnar tabarsu tajawo garin kwakin tasoma kwaɗa musu,kafin daga bisani ta rarrabawa kowa itama tazauna cikinsu sunaci tare tana sake jansu da hira,tare da basu labarin abubuwan da take da burin yi musu nan gaba idan Allah ya hore mata,hakan kuwa yasake faranta musu da basu qwarin gwiwa,kowa yadinga jefa mata tambayoyi tare da sake karanto mata abinda yakeso,bata gaza ba bata kuma qosa ba tadinga bin kowa tana bashi amsa daidai da yadda yakeson ji,tana kuma cike da fata a cikin zuciyarta ta cika musu mafarkansu.



    Cikin raha da annashuwa suke ci kai kace sun samu naman kaza ne,haka kowa yacinye yasha ruwa,cikin ikon Allah dayake ba wani ci ne dasu ba duka sun Æ™oshi alhmdlh,sannan tasake gyarawa ta É—auki hijabinta tamusu sallama tawuce wajen aikinta,bayan ta jadda musu banda yawo,ana kuma idar da sallar magariba dukkaninsu suwuce makarantar magariba,itama sai an taso daga makarantar dare sannan zata dawo gida.



Tunda tafito daga gidan nasu ta fuskanci layin nasu cike yake da jama'a,a rayuwarta bata ƙaunar irin wannan ranar da samarin layin nasu kan zauna su kafa dandalin hira,wanda yawanci duka bai wuce zancen wane da wance,meyake faruwa a wannan gidan,wancan gidan me ake ciki?.



     Hakance kuwa ta kasance,don tunda ta doso majalissar aka sauya topic É—in yakoma kanta,matashi nafarko da ake kira auwali shiya soma tankawa

"Tubarkalla ma sha Allah,kaf unguwar nan....kai bama unguwar nan ba,nidai a rayuwata ban taɓa katarin ganin yarinya mai ƙuruciya da kyau irin yarinyar nan ba" wani daga can sashen ya cafe zancan

"Sai rashin dace da uba da tsantsar rashin gata da talauci ba....kaini wallahi ban taɓa ganin asararren mutum irin ubanta ba,Allah yabaka kadarar yara mata amma kayi watsi da ita?ita kadai wannan yarinyar kadarace,ba qaramin jari bace a wajensa amma bai sani ba"sai wani shima ya kama

"Ai yarinyar nan wallahi inda ace ni wani shege ne da tuni na saka kai nayi wuf da ita,kai wannan idan tasamu wani hutun dajin daɗin aiba ƙaramar mace za'ayi ba" sai sauran sauka sanya dariya,wani daga ciki yayi hanzarin katsesu

"Kai gatanan fa takusa isowa,kada kusata ta tsargu da Allah,waske kawai".



    Dai dai lokacin da abubakar saddiÆ™ ke tsaye daura dasu,jikin wani shago daya siya kati ya tsaya yana lodawa,dukkanin maganganun cikin kunnuwansa sukayisu,baiko É—ago ya dubesu ba saboda hirar tasu sam batayi masa ba,hakanan yasamu kanshi da sha'awar É—aga kai yaga wacce halitta suka sanyawa idanu haka,daidai sanda yagama sanya digits na katin ya dannan request kana ya É—aga kai yana kallon sashen da yake tsammanin tanan ta taho.



    Baisan ya akayi ba,baisan me yasa yasamu kanshi da binta da kallo ba kamar sauran,duk da cewa baya cikin É—abi'arsa sam,saiya lumshe idanunsa kana yabude sanda ta tserewa ganinsa,kunnuwansa sukaci gaba da jiyo masa hirar samarin suna ci gaba da É—orawa daga inda suka tsaya,hakanan yaji bazai iya jurar ci gaba dajin abinda suke faÉ—a a kanta É—in ba,saboda haka ya taka zuwa inda ya aje motarsa Æ™irar kia Æ™arama mai Æ™ofa hudu yabude yashiga yazauna yana kiran wanda yasanya kuÉ—in saboda shi.



Sun É—an É—auki tsahon wasu mintuna suna magana dashi kafin su kammala,ya datse kiran yana sauke numfashi,hakanan saiya samu kanshi da gaza tafiya yana sake nazari kan wasu abubuwa,daga bisani uzurin dake gabanshi yasanya tilas yakunna motar yana barin layin,saidai yanaji ajikinsa tabbas lallai akwai yiwuwar dawowarshi unguwar nan gaba.



Kamar kullum aiki tasamu sosai gidan umma luba,tunda ba kasafai take iya tsaiwa ta kauda komai ba agidan,don wani lokaci sammakon fita take wajen aikin nata,musamman idan akwai wani abu da za'a gudanar ko wani aiki na musamman.



Bata damu ba don ya zame mata jinin jiki,ta zage tayi dukkan abinda ya kamata,kafin wani lokaci gidan yakoma hayyacinsa sannan ta É—ora mata girki kamar yadda tabar mata sallahun ta girka É—in amma kuma kaÉ—an,don ba kasafai ma ake mata girkin ba,saboda yawancin lokaci zuwa lokaci takan taho da lafiyayyen abinci daga can gidan aikin nata,har itama wataran idan rabo ya rantse takan samu.



Tana tsakar gida bayan ta idar da sallar magariba tana addu'ar Allah yashigo da umma luba yau da wuri don tasamu zuwa makarantar dare,saboda yau zata bada haddar akhdari da sukeyi,addu'arta taci,don kuwa ana gab da soma kiran sallar isha'i sai ga sallamarta.



   Cikin girmamawa bilkisu tamiÆ™e tana mata sannu dazuwa,ta amsa fuskarta a sake da fara'a tana cewa

"Sannu mai gado da aiki" murmushinta mai sanyi tayi ta amsa

"Yauwa sannunmu"

"Wayyo Allah makashin kakata" tafada tana sauke uban faggon kayan dake daure a kanta bayan tasamu gefan abun sallar bilkisu ta baje,da alamu a gajiye take sosai

"Bani ruwa in soma sha don Allah bilkisu,ki zubomin abinci yau a tsaye muka wuni,hidimar tafi ta kullum yawa" saita miqe a nutse takawo mata ruwan da abincin,sannan tasamu waje tazauna,tana jira ta sallameta tawuce.



     Tana cin abincin tana sakowa bilkisun hira,duka kusan na gidan aikinta ne da irin ayyukan yau da sukayi,umma luba badai surutu ba,sai kuma akayi katari ita bilkisun bamai yawan son magana bace,amma duk da haka ita bai dameta ba,duk sanda taso hira takan zauna tayita zuba mata labarine koda da murmushi zata amsata bata damu ba,a haka harta gama cin abincin ta wanke hannu sannan bilkisu tamiqe tana jawo takalmanta

"Umma zan wuce gida"

"A gurguje haka,ki tsaya yau Allah yayi albashinmu ya iso kema na sallameki,nasan kina da buƙatu da yawa...kai wannan rayuwa Allah ya iya mana"ta qarashe fada tana tabe baki,bata amsa ba sai komawa da tayi tazauna tanajin ranta yana mata fari,don ba ƙaramin jin daɗin samuwar kuɗin tayi ba.



    Jakarta ta rataye data shigo da ita ta janyo,ta zuge zif din tana fidda sabbin kudi Æ™ar daga ciki bakinta har kunne tana cewa

"Ai in gaya miki yau shar damu,albashi harda ƙari,wai amma ƙarin da muka samu mu samu mabuƙata dake cikin anguwrmu muyi musu sadaka....kinji fa,saikace mu ba mabuƙatan bane,ai babbar buƙata kawai najisu a lalitata,atoh"ɗan murmushi bilkisun kawai tayi,don ita zancan bai burgeta ba,don wannan tana ganin yashiga nau'in ha'inci,tunda tamkar an amince maka ne an baka wani aiki amma ka gaza cikashi,banda hakama ita kanta shaida ne su umma luban suna ƙaruwa sosai da gidan da suke aikin,saboda ana yawan musu kyautar abinci ɗanye akai akai,harshi kansa kudinma koda ba lokacin albashinsu bane,hakanan suturu babu laifi masu tsada tana dasu duka silar gidan aikin,amma dayake ɗan adam ɗan adam ne,batasan mesuke da buƙata ba kuma.



KuÉ—in aikinta cas ta irgo ta bata

"Ungo riƙe nan,ga kuɗin watanki saura na wanki"hannu biyu tasa ta karɓa kamar kyauta ta bata tana godiya,sannan ta sake irgo wasu ta bata

"gashi wankin ki na dubu ne da ɗari biyu" sosai taji daɗin ƙarin,don bata tsammaci zata samu har haka ba

"Na gode"

"Nice da godiya ai mai gado,saboda yadda kikemin ɗin nan sai ƙalilan masu amana,tsahon lokaci ko cokali ban taba nema na rasa ba ai kuwa kinga ba duk mutum ba....ungo cikin kuɗin sadakar dai na bada wani abu,aidai nayi tunda na fitar komai qanqantarsu" dubu daya tasake miƙa mata,data hada kuɗaɗen hannayenta sai taga ta kusa tasamma dubu biyar,abinda ba zata iya tuna yaushe ne hakan tafaru ba,riqe kudi masu yawa har haka ba.



    Harta miÆ™e ta sake dakatar da ita

"Sake zama ƴarnan ki dangwali alfanun riƙon amana"tayi magana tana janyo ƙullin uban kayan data shigo dasu tana sake cewa

"yau muma mun dangwala mun dangwala harmun godewa Allah,kayan ɗiya kuma jinin sarauta yauni luba a hannuna,muma zamu raɓawa jikinmu irin suturarsu,muji abinda suke ji,wannan karamci nasu ya isa". Tana maganar tana kokawar bude qullin kayan.



   Tana kwance kayan wani daddaÉ—an Æ™amshi na musamman ya bule wajen,kayane faggo guda kamar za'a sunce dila,namijin É—aurin da aka masa yasa baka ganin yawansu sai an bude.

7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑    *SIRAD'IN RAYUWA* 👑




*NA*


*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*



*_Wannan littafin na kudine kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,babu cigiya,babu a dauko mana_*



09032345899

Ko

09033181070



*_KI/KA/KU DUBI GIRMAN ALLAH KU SIYA DA KUDIN KU, DON GUDUN SHIGA HAKKIN WANDA SUKA SIYA, DAMA WADANDA KE SIYARWAR MUNA MARABA DA KASANCEWA DA MASOYAN MU.._*




5



"Zauna ki lissafa duka Æ™annenki ki zabar musu kowa yasaka,yau fulani inajin juyen kayan drower É—insu sukayi....ki zaÉ“a na saida na saidawa,na bada na bayarwa,don ba shakka waÉ—an nan kaya yadda suke fes kamar ba'a sanyasu ba Æ™aramin kuÉ—i zan samu dasu ba Allah mai gado" murmushi takuma saki wannan karon mai sauti,tana sake jinjina son kuÉ—i irin na umma luba,kayane masu asalin kyau daraja da tsada,wanda duk wanda ya kalla koda bakasan kuÉ—insu ba amma kasani ba masu 

ƙarami ko matsakaicin kuɗi bane,tanajin umma luba naci gaba da sambatu gami da bata labarai,ta tsugunna tana duba su hauwa'u tana zaɓarwa kowa,duk da sauran tasan sun musu yawa amma haka ta ɗauka musu,tana kintatar zata bayar a maida musu dai dai jikinsu.

"Ana abu a masarautar KAISA,wani abunma sai jibi idan Allah yakaimu" takai ƙarshe tana sakin guɗa,da alamu dai cikin nishadi take yadda ya kamata.



Sunan masarautar dataji ya fito daga bakin umma luba sai taji duka kayan sun fice mata arai,AFNAN itace abu na farko daya soma faÉ—o mata a rai,kenan kayan sjn fito ne daga gidansu?,wala'alla ba za'a rasa nata a ciki ba,sai taji kamar ta barwa umma luba kayan,amma hakan bazai yiwu ba,saboda niyyar alkhairi tayi a gareta,dole ya hade kansu ta bata leda babba ta saka ta mata godiya kana tafito.


Kamar yadda ta qudirta din bata koma gida ba sai data shiga makaranta ta bada haddar dake kanta,saboda bata son ta  rasa rana daya cikin ranakun zuwanta makaranta,musamman da a yanzu suke gab da kammala haddace qananun litattafan addini su tafi zuwa manyan,ba qaramin dadin karatun takeji qwarai da gaske,koda yaushe takan godewa Allah wanda bayan ya hanata wasu abubuwa na rayuwa amma bai hanata hasken ilimi da qaunarsa ba,ba ita ba koda qannenta a yanzu ba zaka kirasu jahilai ba ta fannin addini,tunda alhmdlh dukkaninsu suna zuwa makarantar Allo da safe,suje ta magariba bayan sallar magariba.



A hanya take tunanin abinda zata siya musu suci,saboda tasan bata bar musu abincin dare ba,hakanan babu yaqinin za'a basu suci,taso siya musu wani abun amma duka abinda ta lissafa zaija kudine,sai taliyar hausa ta fado mata a rai,idan ta siya kuma akwai bata lokaci kafin dahuwarta,mai yiwuwa su qosa ko wasu daga cikinsu ma suyi bacci,saita wuce gida kawai tana fatan asamu sauran abincin sayarwa wajen umma katti,tunda ba'a rasata da saura.



Tun daga soron gidan mamaki yacikata fal jiyo muryar mahaifinsu yana hira cikin walwala da dariya

"Allah hakimu,yau kuma wanne manzan rahamar aka saukar mana?" Tayiwa kanta tambayar zuciyarta cike fal da taraddi,ba zata iya tuna lokaci na qarshe data jishi cikin irin wannan yanayin cikin tsakar gidansu ba,idanma zata tuna din zata iya cewa tun aurenshi na qarshe da yayi suka rabu,da wannan tunanin ta qarasa kutsa kai cikin gidan.



Bata sake daskarewa ba sai data ganshi tsakiyar yaran,ko ina farantai nashe nashe da shinkafa da miya kowa na kaiwa baka,data lura dakyau ma sai take ganin kamar tsokokin kaji saman abincin,a haka ta dinga takowa idanunta akai,tana jin tamkar mafarki take

"Ke meye hanka,kalli gabanki mana,idan kuma yunwa kikeji kije ki amshi naki abincin wajen kattime" muryar mahaifinta kenan dake magana yau cikin cikakkiyar isa sabida cikakken awo da cefanen da yake ganin yayi,maganar tashi taja hankalin 'yan uwanta kan shigowarta,dukka suka bar abincin sukayi wajenta,wasu suna mata sannu da zuwa,yayin da wasu keta faman nuna mata rasha da gwabar da yau suka samu a gidan nasu,wanda sun manta rabonsu da samun koda arziqin fara damai da gishiri bare miyar kaji,wasu daga cikinsu ma namam suketa tura mata taci,saita maida hannayensu cikin sanyin jiki,don ita sam abun bai mata ba,hakanan bai burgeta ba,suma don basu gama sanin ciwon kawunansu bane,ta tabbatar da walakin,hakanan akwai wata a qasa,cikin tattausar muryarta da take tsarin halittarta tace

"Na gode,maza kuzauna kuci"

"Kujimin ja'iran yara,yo itama da nata kason ai,banson kilbibi idan zaku zauna kuci ku zauna" baban nata yakuma fada,duk sai suka zauna sukaci gaba da cin abincinsu.



Sai a sannan tadubi sashen da baban nata yake a ladabce tace

"Barka da wuni baba,an wuni lafiya"

"Lafiya lau,sai yanzu kike dawowa?" Ya fada kamar yana ganin takai dare da yawa,kai ta jijjiga kawai

"Eh....na tsaya makarantar dare ne"

"To madalla" ya amsa yana afa lomar shinkafa bakinsa,miqewa tayi zata wuce dakinsu,sai kuma ta fasa taga gwara tasoma sauke nauyin bashin kudin umma katti a kanta,saboda haka tasauya akalarta zuwa dakin nata,dai dai lokacin da baban nata ya qwalawa umman kira yana cewa

"Kattime....kinga...gwara ki fito ki sake abinki,kici kazarki kisha jar miya ki godewa Allah da budin daya kawo yau"

Wani mugun tsaki ta saki sanda bilkisu ke saka kai dakin

"Ka hutar da yawun bakinka,aiba saika fada ba abinci zancishi,tunda haƙÆ™ina ne Allah ya Æ™wata yabani yau,amma duk wani iyayinka da É—igiminka na riga dana daÉ—e da haddacesu,jiya bayau bafa,nasan dai Æ™arshen alawa qasa,to mu zuba mugani,Allah ya bada sa'a" ta qarashe zancan tana dukan cinya gamida zunkuda zamanta,da alama masifa tana cinta.



Sallamar bilkisun ma sama sama ta amsa mata,bata bata dukka hankalinta ba sai dataji da biyan bashi tazo mata,saita maida kai sukayi lissafi ta cire mata kuÉ—inta,tasa hannu kuwa ta amshe abinta ta linke kana ta tura mata kwanon abinci har guda biyu,daya shinkafa daya miya

"Ga naki kason nan,yau Allah yayi babu kwanan yunwa" umma kattin ta fada tana sake gyara boyon kudinta,da kallo tabi kwanukan,ita sam ko daya abincin bai bata wani sha'awa ko armashin ci ba,saboda ba umma katti ba,ko ita tasoma shanshano abinda ke shirin faruwa cikin gidan,wata ƙila ma nan da wasu 'yan kwanaki masu zuwa

"Allah ya amfana" kawai ta fada tana É—iban kwanukan tafice zuwa dakinsu,yaran na ganin fitowarta kuwa dukka suka bita daki sukabar baban anan,don dama ba wani sabo ko shaquwa bane tsakaninsa dasu.



Kaya tacanxa ta ninke wadancan don sune nadan fitar sannan taxauna sosai tajawo kanukan tasoma budewa,dai dai lokacin da amina wadda itace qarama a cikinsu tace

"Yaaya yau abincin yayi dadi wallahi,hadda naman zakara irin na gidansu hasana" ta qarashe maganar alamun walwala da annashuwa na bayyana muraran saman fuskarta,sai murmushi ya subewa bilkisun,yayin da hauwa hannatu da umaima suka sanya dariya

"Wai kice aikin babba ne aminatu,zakara ne bama kaxa ba"sai a sannan maganar ta bawa yarinyar dariya itama

"Ku matso maza musake ci" hannatu ta zaro ido tana sha cikinta

"Ai yaaya duk cikinmu yau ba wanda baiyi mugun qoshi ba,ni har amai nake ji wallahi,saboda nayita cine ina hutawa,don bansan yaushe zamu sake qoshi haka ba" da qaramin murmushi mai dauke da tausayi take dubansu sannan tace

"Bakin da Allah ya tsaga ai baya hanashi abinci hannatu" daga haka taja abincin tana ci,jifa jifa suna hira tana tattambayarsu abubuwan da suka faru bayan bata nan,da yake haka dabi'arta take,idan tadawo cikin hikima a cikin hira take bugar cikinsu wasu abubuwan,wanda anan ne idan taji wani kuskure da wani yayi ko ba daidai ba saita gyara mishi kota tsawatar masa.



"Ya akayi ne hauwa kuluwa?" Bilkisu tafada sanda take gama cin abincin da tsakurarsa kawai tayi ta ture,saita sauke hannun daga tagumin datayi tana murmushi

"Yaaya,duk kin fimu kyau,sai nadinga ji dama nice ke" murmushi mai sauti ya subuce mata,har fararen jerarrun haqoranta suka bayyana

"Toh?,yau kuma hauwa'u"

"Nima yaaya,na dade ina gani,ko qawayena idan sukazo sai suyita kallonki,suce kamar ba gidanmu daya ba,waike kin fimu kyau,kalar 'yan gayu dake" hannatu tayi nata sharhin daya sanya bilkisu dariya dole,sai data tsagaita sannan tace

"Kuma duka masu kyaune hauwa'u,bakigama ke 'yar fillo bace,gashinki ma yafi nawa santsi dakyau,kema hannatu baki kallon mudubi?" Maganar saita dan jefa yarinyar cikin tunani

"Yaaya" takira sunan bilkisu a sanyaye wanda hakan yayi calling attention na bilkisun sosai

"Na'am" ta amsa mata da dukka hankalinta

"Da gaske ni 'yar fulani ce?,amma ban taba ganin mamana ko 'yan uwanmu ba,tunda mamana ta tafi ban sake ganinta ba,kodai bazan sake ganinta ba yaaya,ko itama mutuwa tayi kaman mamanki?" Shuru ya ratsa dakin,yarinyar na dubanta tana jiran amsa daga bakinta bilhaqqi,maganganun yarinyar sosai suka taba ranta,suka koma soso wani sashe maigirma na zuciyarta,tausayinta yasake ninkuwa a ranta.



Kama hannun yarinyar tayi a tausashe sannan tace

"Mamanki bata mutu ba tana nan da ranta,kullum tana tunaninki kuma tanason ta ganki,amma wataran saidai kawai ki ganta tazo ganin hauwanta" murmushi ya kubcewa yarinyar,cike da nuna zumudi da kuma fata mai tarin yawa tace

"Da gaske anty?"kai ta jinjina mata alamun tabbatarwa

"Da gaske jidda" sai farinciki ya mamaye fuskarta.



Da wannan hirar ranar suka kwanta,yayin da suka tadawa bilkisun tabo sosai cikin zuciyarta,don kowanne yanuna sha'awa dason ganin mahaifiyarsa,inama ace itama zata samu dama koda sau daya taga tata uwar,ta zanta da ita ko sau dayane kuwa?,tausayin yaran take wani lokaci fiye da kanta,don gwara ita tasan dukkan wanda yamutu haihata haihata shida dawowa doron duniya,amma sufa?,ta qyamaci halin mahaifinta dakan raba yaran da iyayensu yakuma kasa riqesu yadda yakamata,yayin da wasu daga cikinsu iyayen ne a karan kansu suke fushi saboda abinda mahaifinsu ya aikata su watsar da yaran.



A daren ranar sai datayi kuka sosai kafin bacci yayi awon gaba da ita.



☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



*MASARAUTAR KAISA*



    Kamar yadda muka fada a baya babbar masarauta ce mai cike da iko mulki da wata cikakkiyar izza,tun shekarun masu tsaho da suka shude a baya har kawo yau,wanda tana gogayya da dukkan masarautun da suke maqwabtanta dama na nesa da ita,masarauta ce data cika ta tumbatsa da wani irin salo na mulki mai cike da adalci da qasaita na daban uwa uba kwarjini da daukaka da Allah yayi mata.



Babbar masarauta ce wadda take da fadin qasa,tarin al'umma,kaisa garine da yayi iyaka da kano da jigawa,garine mai albarka noma da kiwo,hakanan al'ummar ciki na rayuwa ne qarqashin adalin sarkinsu maimartaba sarki Abdallah mu'az nuhu kaisa,wanda tun tale tale na kafuwar garin mulkin garin a hannunsu yake,shi kansa gadon gado yayi daga iyaye da kakanni.



Gidan sarautar kaisa babban gidane wanda zaka iya kiranshi kai tsaye da gari guda,mai dauke da sassa sassa bisa tsari da fasali tun daga farkon gidan, gidajen ƙananun bayi da manyansu,bayi,masu qananun muqami da matsaikaita,securities na gidan wasu daga cikin dogarawa da sauran hadimai na gidan,haka tsarin yake daki daki har zuwa ainihin unguwar da matan sarki suke da iyalanshi da sauran makusanta.



Sarki Abdallah adalin sarki ne wanda al'ummar garinsa kejin dadin mulkinsa qwarai da gaske,yana da tausayi ga talakawanshi,mutum ne mai sauqin kai duk da awasu al'amurran bashi da sauqi ko kadan,hakanan kaifi daya ne shi,magana daya yake babu canji,mutum ne mai qoqarin riqo da addini duk da cewa yayi karatun boko.mai zurfi,don kafin zamowarshi sarki ya riqe muqamai iri daban daban masu tarin yawa,tun daga qananu zuwa manya,don har ambassador ya tabayi,kafin daga bisani yadawo gida bayan Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa ya amshi sarautar garinsu.



Sarki Abdallah nada matan aure hudu,ta hudun da ya aura bayan zamowarshi sariki ta rasu bayan ta haifi yarinya daya dashi,matarshi ta farko hajiya saratu ya aureta ne tun kafin zamowarshi sarki,a lokacin yana ministern mai na qasa,wanda basu jima sosai da ita ba don haihuwarta biyu Allah yayi haduwarshi da mayarsa ta biyu haj adama,wanda sun dan zauna zaman kishi lokaci maidan tsaho kafin Allah yasake yin aurenshi da Aishatulhumaira,a lokacin yana ambassador a qasar mali,diyar sarautar qasar itama kamar yadda yake.



Tun haduwarshi da ita tashiga zuciyarsa qwarai da gaske takuma tafi dashi,saboda wani irin kyau da Allah yayiwa aishan,kowa yasan yadda kalar fatarsu da yanayin kyansu yake wanda yake dan zubi da na ethopian's,uwa uba jan aji da shan qamshinta wanda ya amsheta qwarai yakuma dace da matsayinta,wata irin mace ce da Allah ya zuba mata kwarjini da farinjinin manema,don shi kansa a sannan sai daya danci wuya kafin yasameta.



Sai neman auren aishan yazama wani abu na daban wajen haj saratu da adama,tun daga sanda sukayi binciken kan wacece aishan hankalinsu yatashi qwarai da gaske,suka kasa sukuni saboda sunga cewa tako ina tafisu,sannan shi kansa mai gayya mai aikin sun fahimci kamar yana zumudin abun,duk da yadda yake qoqarin boyewa da dannewa,duk ta yadda zasu shiga a fasa abu ya faskara yaci tura,tilas daga qarshe dai suka shirya plan na tararshi gaba da gaba,suka sameshi a falo yana hutawa suka tada mishi maganar,yayi qoqarin fahimtar dasu da lallashinsu amma suka toge,daga qarshe ma suka sanya masa kuka hajiya saratu tace

"Kawai dai duka take takenka mun gane ,mun fahimci inda kasa gaba kuma mun fahimci me kake nufi,saboda Allah yabamu haihuwar 'ya'ya mata bamu haifan maka maza saboda kana sakaran ka amshi sarauta kana neman magaji tun yanzu,to ai muma bamu muka baiwa kanmu ba,kuma cikin daya haifi 'ya mace shi zai haifi da namiji" shuru yayi na mamakin kalamanta,sabodashi sam ko sau daya ma bai taba darsa wannan tunanin cikin ranshi ba,saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah,shi kanshi mai martaba a sannan yana nan da ranshi bai mutu ba bare yayi wani tunanin mulki.



Idanu kawai ya zuba musu,suka dinga tashin hankali kala kala har akayi auren,yabar aisha a qasarsu saboda shima a sannan yana can yana aikinsa,sam ita aishan bata damu dasu ba,duk da tana da kishi tana kishin mijinta saboda yadda take sonshi amma ko zancansu bata masa,taja mutuncinta sosai,tun bata fahimci yadda suke kishi da ita ba harta gane,saboda haka tasan halin kowacce cikinsu duk daba qasa daya suke ba,kuma abdallah baya mata zancan kowacce cikinsu amma ta fahimci kowa,macace mai matuqar saurin gano abu,kaifin basira da hangen nesa,yanayin yadda abubuwa ke gudana idan yakoma can wajensu kawai ya isa ya bayyana mata komai.



Basu sassauta kishinsu a kanta ba sai datayi haihuwar fari itama tasamu diya mace,kai kaga walwala da sakin jiki,harma suka yanke haj saratu zataje har can mali barka da taron suna,shi kansa yayi mamakin yadda suka sake din,amma bai kawo komai a ranshi ba donshi bai saka zancan haihuwar mata ko maza a wani babin ba,hasalima ya manta taqaddamar da sukayi dasu lokacin auren aishan,sai yayi murna sosai saboda yana tunanin sun sassauto ne saboda zuri'a da aka soma hadawa.




Haka kuwa akayi,ta shirya tsaf tayi siyayya ta alfarma suka tafi da duka yaran su hudu,nata biyu nimra da zunaira,sai na adama biyu Aafiya da afra.



Gidansu aisha gida ne na karamci suma,saboda haka tasamu saukar girma data sake sanyata ta bambance aya da tsakuwa,bugu da qari duka yadda suke hasashe ashe abun yawuce hasashen nasu,don yadda taga anata hidimar bikin sunan jaririyar cikin gidan nasu,aishan 'yar gata ce gaba da baya.



Tunda tazo suka gaisa aka kai mata yarinyar bata kuma bari sun hadu ba,saidai duk wani abu daya kamata ayiwa baqo dama wanda bai zama dole ba duka an yiwa saratun,takuma aiko aka mata godiyar kayan barka,saidai a jikinta taji cewa ba zuwan Allah tayi ba,to koma mene batajin zata bari kota yarda a cutar mata da diya,don tun sanda ta haifeta take mata mugun so.



Yadda saratu tazo data tashi komawa saiya zaman gwiwa kusan a sanyaye,don ta ganewa kanta abubuwa masu yawa,ciki kuwa harda kyau da Allah ya yiwa yarinyar na daban,ga uwa uba gatan data gani ana nuna musu,koda ta dawo ta baiwa adama labari sai sukayi zugum,inda daga qarshe adaman ta katse tattaunawar tasu da cewa

"Koma meye dai mu godewa Allah data yiwo mu,don inda namijine kuma saita Allahu,sai abinda idanuwanmu suka gani kenan".



Tafi tafi haka rayuwa ta dinga tafiya har zuwa sanda maimartaba ya kwanta ciwo,wanda ciwon nashi kusan shine silar daya sanya abdallah ajiye aikinsa na ambassador,yadawo gida gaba daya saboda shine babban danshi,wanda kuma sukagi shaquwa dashi fiye da kowa,wannan karon harda aisha itama tabiyo mijinta nigeria donta zauna dashi,a sannan dukka matan nashi ciki garesu,saidai akwai bambancin watanni,na saratu shine mai watanni bakwai,adama wata shida,yayin da aisha nata keda wata biyar,saboda tsayinta da yanayin shigarta yasama ba kowane ke lura dashi ba.



A wannan zaman da sukayi tare da sake karantar kowa tsaf ciki da bai,haka suma sun sake fahimtar tazarar data musu a zuciyar mijin,katsam saiga al'ummar gidanma kusan suna neman komawa qarqashinta,kasancewarta mai budadden hannu,ba baya bace wajen kyauta,duk da tarin izza da qasaitarta,duk da bata cika sakin fuska ko faran faran da jama'a ba,amma duka wannan bai damu mutane ba,da yake yanzun kusan kowa yafi ga abun hannun dan uwanshi.



A wannan lokacin tsakanin adama da da saratu kowa fafutukar ganin ya haifi da namiji yake a cikinsu,kudi suka dinga bararwa suna baiwa malamai na Allah daba na Allah ba ana abubuwa iri iri saboda su haifi namiji,gamida alqawura iri iri ga hadimansu na duk wanda yazama silar samun namiji a cikinsu zasu 'yantashi,masu 'yanci kuma zasu wadatashi,saboda kowacce tana ji a jikinta lokacine yayi da mijinsu zai karbi sarauta,wanda hakan ke nuna cewa abu na gab zuwa kansu.



Amma a zahiri idan sun hadu kowacce fata takewa 'yar uwarta nako itace tasamu babu komai,saidai kowanne ta qarqashin qasa akwai hadimansa dake masa aiki a sashen kowaccensu ba tare da kowannensu yasani ba.



Ta fannin aysha kuwa hankalinta a kwance yake,sabgarta kawai take da kula da mijinta,da kuna tayashi kulawa kan lalurar mahifinsa,sun tuttura mata sabbin fuska don su shiga jikinta kamarsu amma basu samu wannan damar ba,saboda halinta na dabanne ita,tana da matuqar wayo da takatsantsan,don haka ita basu da wani labari daya danganceta ko sassanta sai dan abinda ba'a rasa ba.



Wata biyu da dawowarsu a safiyar wata asabar saratu ta haihu,tashiga tashin hankali da matuqar girgiza sanda unguwar zoman dake amsar haihuwarsu ta shaida mata diya mace tasamu,babu jimawa labari ya karade gidan,ranar sashin nata tamkar zaman makoki akeyi,saboda kowa yasan yadda ta qwallafa rai akan da miji kuma bata samu ba,dukkanin hadimanta ranar kaffa kaffa suka dinga yi,babu wani mai qwaqqwaran motsi ko dariyar kirki,a haka labari yasamu adama,tayi rawa tayi shewa tayi juyi gaban mutanen da take gani amintattun tane,wadanda sune suka kawo mata labarin,saidai batasan cewa sune makasan nata ba,kana ta umarci hadimanta maza su shirya abinci mai rai da motsi a kaiwa saratu,itama tana bisa hanya.



Isar abincin da isarta sassan saratun ba wani tazara mai yawa,donta qagauta taje ta ganema idanunta

"Haka Allah yashirya,qaddararsa kenan" adaman ta fada cikin fuskar jimami sanda take zaune kusa da saratu wanda ke kashingide saman wata kujerar hutawa dake wani daki na musamman da aka kebe saboda hutawar.



Nannauyar ajiyar zuciya saratun ta saki,kana a hankali ta dora idanunta kan adaman,tuni labarin abinda tayi ya rigata isowa,saboda haka tar take kallonta,saita miqe tazauna sosai sannan tace

"Qaddararmu ce gaba dayanmu halan" saita san dakata tana ci gaba da duban adama tana shaqar numfashi sannan ta dora

"kuma na rantse da sarkin da babu wani saishi,indai ni saratu uwar gida ga Abdallah bani nasoma haifa mishi É—a namiji ba,babu matar da zata haifa É—a namiji cikin gidan nan".



Gaban adama yafadi tsoro yadan shigeta,kada fa yazamanto namiji ne a cikinta saratu ta aikata abinda zaisa yakoma mace,amma a zahiri saita dubeta duba na mamaki

"Tofa....kamar yaya,me kike nufi?" Sai data koma ta kashingida sannan ta bata amsa a taqaice

"Lokaci zai nuna" daga haka bata kuma tanka mata ba,saita aje mata yarinyar saitin qafafunta tamiqe tana cewa

"Lamarin ubangiji dai rubutacce ne,Allah ya qara lafiya,nina wuce" binta tayi da kallo,sai ta saki shu'umin murmushi

"Kinsan ubangiji ne adama?,muzuba mugani" ta fada cikin ranta,kana ta waiwaya tadubi yarinyar daketa bacci abinta batasan ma me ake ba,sai taji dama ta bude idanu ta ganta a matsayin d'a namiji ba mace ba,takirayi daya daga cikin barorinta tadauki 'yar ta maidata cikin gadonta.

7/11/21, 4:28 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRADIN RAYUWATA* 👑



*_wannan littafin na kudine,kuma AMANA ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar a dama dake,nemi wadan nan lambobin ki saya ki karanta ta hanyar data dace cikin nutsuwa sa kwanciyar hankali,babu cigiya babu a dauko mana,SIYI DA KUDINKI KISAN KEMA KIN ISA_*


0903Â 234Â 5899

KO

09033181070



6




Sanda abdallah yazo ganin É—iyarsa ya amsheta hannu bibbiyu cikin farinciki kamar sauran haihuwar,ba tare da nuna wani abu har fili da zuciyarshi,abinda yadan sake kwantar mata da hankali kenan,duk da burin dake ruruwa cikin zuciyarta wutarshi bata ragu ba bare ta mutu,taji alwashin duk tsiya duk runtsi itace zata fara samawa abdallah magaji ta kowacce hanya,ba zata taba bari wata cikinsu ta karbi wannan kambun ba.



Aisha kam sai bayan kwanaki uku da haihuwar sannan ta taka taje cikin rakiyar hadimanta wanda kusan dukkaninsu amintattun tane,saboda an hadasu ne da ita tun daga masarautarsu,qalilan ne wadanda suke haifaffun masarautar kaisa.



Tajewa da jaririya kyautar saitin gwal sarqa dan kunne abun hannu harda zobe da awarwaro,tun daga ranar bata sake komawa ba.

Suna akayi kamar yadda aka saba gagarumi,yarinya taci sunan sa'adiyya mahaifiyar saratun suna kiranta da walida,hakanan taci gaba da rainon walida tana zuba idanu kan cikin adama da aisha.



Kwanaki arba'in darda doriyar takwas akai itama adama ta haife nata cikin bayan sallar la'asar,itadinma Allah ya nuna isarsa,buwayarsa da kuma ikonsa,tun la'asar akayi haihuwar amma dif babu labarin abinda ta haifa din,tana canbtana tantama da tunanin idanuwansu ne basuga dai dai ba amma namiji ne,sam bata ta wahalar da yarinyar tasha wanda ba'a samu ta fara kuka ba saida qyar,har sai bayan sallar magariba sannan komai ya tabbata.



Sosai tashiga rudu da tashin hankali itama,don dukka malamanta kowa ya tabbatar mata da cewa namiji ne zata haifa wannan karon,abu na farko data soma fada shine

"Tabbas ba shakka wannan surkullen saratu ne,kuma wallahi bataci banza ba,sai tasan dani take zancan".



Itama tuni labari ya dade da isar mata,tasa aka shirya lafiyayyen abinci aka aika sassan adaman kamar yadda itama tamata,sannan tashirya cikin tawagarta suka je barka

"marhaba lale,ashe abokiyar tagwaitakar walida ta iso..." Ta qarashe tana dariya dariyar da zata nuna maka hakan ba qaramin dadi yayi mata ba kenan.



Adaman na zaune a lokacin tanacin farfesun naman rago,saidai jinsa take kamar tana tauna plagyl tana hadiya ne,fuskarta kai kace dare biyu akeyi,maganar saratu yasa tazuba mata idanu,kana cikin kauri da kaushin murya tace

"Burinki yacika,amma kisani...komai nisan jifa qasa zai fado,hakanan na rantse da girman Allah kamar yadda kikaci alwashi nima naci....dukkanin wanda yayimin kan kara saina masa na itace" saman cinyarta ta isa tadora mata yarinyar tana sakin murmushi sannan tace

"Ga fili gamai doki nan....saura sukuwa" saita soma takawa tafice daga dakin tabaiwa barorinta dake can falon farko umarnin su aje saqon kayan barka suzo suwuce.



Wannan ma aishan kamar wancan karon,batazo na sai bayan kwana uku,itama ta bata kwatankwacin abinda ta baiwa walida tatafi.



Tun daga wannan ranat dangantaka tayi tsananin tsami tsakanin saratu da adama,aka shiga takun saqa naban mamaki,yiwa juna zagon qasa,da zamba iri iri.



Aisha na gefe batasanma sunayi ba,dama babu abinda zai hadata dasu,yanayin halayensu yasa ta sake takatsantsan da komai da kuma kowa,hatta da diyarta bata barinta ta qetare sashenta bare tayi nisan kiwo,saboda batajin zata iya dauka idan wani mummunan abu yasameta.



Sai dukka hankulansu ya karkata yakoma ga aishan sanda tashiga watan haihuwarta,kamar tunaninsu ne yazo daya,kowacce saita soma mata aike dake nuna tsantsar kulawa,bata taba cewa kada a karba ba,amma kome suka kawo din bata yarda ya rabi inda take.



Ziyara da suka shiga kawo.mata akai akai kuwa kai tsaye ta soketa ta dakatar dasu ba tare da shakka ko shayin gayawa kowaccensu ba kai tsaye,hakan yasake basu mamaki yakuma tabbatar musu aishan da halayenta na dabanne,kuma lallai jinin sarauta na yawo a jikinta koma bayansu da za'a iya cewa taka haye.



Yadda ta fahimci sunayin saiya sanya nata qaunar samun da namiji,sai taji tanason ta haifa da namijin taga yaya zasuyi?,tanason ita tazama mace tafarko da zata samarwa abdallanta magaji.



Kwana hamsin da biyar cikin dare naquda ta kamata ganga ganga,a lokacin kusan mafi yawan al'ummar gidan da suka damu da rashin lafiyar mai martaba har zuciyarsu kusan idanunsu biyu,cikinsu harda al'ummar sashenta,a daren abdallah yana can sassan maimartaba cikin dakinsa suna fama dashi saboda yadda ciwonsa yatashi ainun fiye da kowanne lokaci,saita kira mutum biyu cikin amintattunta suka kebe iyasu suna kula da ita.



Daidai lokacin data haifi ABDUL_AZEEZ bawan mabuwayi,a sannan mabuwayin ya nuna buwaya da ikonsa yadauki ran sarki mu'az nuhu.



Kaqqarfar ajiyar zuciya tasauke

Tana furta kalmar

"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmus salihat".



Ita da kanta ta hana afitar da jinsin abinda ta haifa din tun cikin daren,sai zuwa wani lokaci data shirya susani din.



Sanarwar haihuwar abdul_azeez ta karade gidan hade da sanarwar mutuwar mai martaba,wanda hakan ya taimaka wajen janye hankalin mutane wajen son sanin me aka haifa?,wanda wannan yabata damar shiryawa sosai da tsara yadda zata fuskanci gaba,ta riga data sani haihuwar abdul'azeez zai iya zame mata wani babban qalubale a rayuwarta tsakanin abokan zamanta.



Abdallah bai samu shigowa ganinta ba sai bayan sallar magariba,tana zaune tana kallon yadda yaketa faman murmushi yana kissing yaron kamar zai maidashi ciki,duk da cewa yana cikin alhini da jajjaɓi na rashin da yayi amma fuskarshi ta nuna farinciki mara misali,hakan shike nuna shaidar cewa yanason magaji kamar yadda kowanne mutum keso,amma shi kansa baisan yana da wannan feelings din ba,saiyau feeling din ya bayyana kanshi da kanshi

"Allah kenan,mai kyauta yakuma amsa a duk lokacin da yaga dama,Allah ya amshi mai martaba sai gashi ya bani wani copy din" cikin tayashi alhini aisha ta girgiza kai

"Allah yayi mishi rahama,yasa can tafi nan"

"Amin don annabin rahama....amma wannan fa" saiya dakata yana sake jujjuya abdul'azeez a hannunshi,sai murmushi yasake kubce masa

"Dan somalia ne,aisha kinmin wayo,ku yadauko zam,dan da alama har kalar fatar ma,na tsira da minahil kenan?" Duk da yadda zuciyarta itama take babu dadi saboda rashin da sukayi saida murmushi ya kubce mata,sai daya tattofeshi da addu'a sosai kana yamiqa matashi ya mata sallama.



Har ya fita yadawo ya dubeta

"Zan aiko da saqon da za'ayi masa amfani dashi,ki tabbata an masa amfanin dashi yadda yadace"

"In sha Allahu" ta fada 



Washegari kuwa sai gashi,wani rubutune mai garin magani da za'a masa wanka dashi akan towel,sai a shanya towel din yabushe,da wani irin man shafawa da za'a dinga shafe masa duk jikinsa duk dare idan zai kwanta,kobai fada ba tasan na tsarine,kuma taji dadin hakan sosai.



Duk da wannan rasuwa da akayi hakan bai hanasu son sanin me aisha ta haifa ba,duk da basu samu zuwa ganinta ba amma sunata faman aiki gami da leqo 'yan bugar ciki ko ince leqen asiri,saidai hadiman nata 'yan gaske ne,don har sukayi suka gama basu san me aka haifa din ba,har sai ranar bakwai din mutuwar mai martaba

A ranar ne akayi radin suna ba tare da wani shagali ba saboda mutuwar

Kuma a ranar ne aka nada Abdallah kan karagar mahaifinsa,yazama shine sarkin garin kaisa.



Ba qaramin girgiza zukatan maqiya sukayi ba sanda saqon radin sunan jariri yakai musu da sunan MUHAMMAD ABDUL'AZEEZ,don haj saratu saboda tsabar rudewa cewa tayi

"Abdul'azeez ko aziza?,anya kuwa kunji dakyau?" Tafada cikin razani da rudani tana duban barorin nata.



Dukkaninsu kawunansu suka sadda kamar sun aikata mata wani laifi,sannan daya daga cikinsu tace

"Ki yafemu ranki ya dade,tuba muke....amma ba shakka abdul'azeez shine sunan yaron" sauran duka suka jijjiga kai alamun hakane

"Zaku iya tafiya" tu buqaci su bata wuri,saboda yanzu babu abinda take da buqata sai kadaicewa.



To bangaren adama ma kusan haka abun yake,amma ta dake itama takuma shirya kyautatuttuka ta aika sassan saratun hade da saqo,wanda tace tana tayata murnar samun magaji,Allah ya rayashi.



Tunda taga saqon tasan cewa da biyu adaman ta aiko dashi,hakan kuwa ya qular da ita yakuma fusatata,amma dole ta danne a idanun mutane ta amsa takuma aika mata da saqon godiya.



Bayan nan haka tasake shirya kyaututtuka kala daban daban na alfarma masu yawan gaske ta aika sassan aisha,tace kyauta ce zuwa ga yarima abdul'azeez daga uwarshi,itama aishan ta karba,takuma bada tukuici mai tsoka,irin tukuicin dake nuna zallar isa da qasaita.



Murmushi adaman tayi sanda taga tukucin,tadinga kada qafa tana ayyanawa wala'alla aisha ta yaba shi yasa ta bada irin wannan tukucin haka,take wani shiri yafado mata aranta,ta tafa hannuwanta cikin nishadi ta kashingida tana tsara yadda komai zai gudana.



Tun haihuwar abdul'azeez take nuna mishi soyayya da qauna mai yawa,wani irin so takewa yaron,yashiga zuciyarta da yawa,har takan gaza tantance shida minahil wa tafiso.



Wani kwarjini da farinjini Allah yabashi tun daga quruciya,hakan yasa ta sake takatsantsan dakuma kaffa kaffa a kanshi,ko ina zai shiga akwai sanyawar idanu akanshi saboda tsaro,wannan yayi tasiri qwarai wajen rage hanqoran mafarautan rayuwarsa,yakuma takurasu tare ta qara musu qaimi wajen ganin sun aiwatar da qudurinsu.



Ta bangaren adama kuwa ta bada himma sosai don ganin ta nunawa duniya tana qaunar abdul'azez,haka tadinga qoqarin ganin ta jashi jikinta ta yadda komai zai tafar mata a sauqi,saidai babu wannan damar daga wajen ayshan,ita da abdul'azeez din saidai ta ganshi daga nesa,idan ma kuwa zata ganshi a kusa ta gaban idanun masu tsaronshi ne.



Tsakanin fulani adama da fulani saratu tun haihuwarsu ta uku babu wadda tasake koda batan wata,hakan yasanya zargin juna a tsakaninsu,kowacce tana ganin 'yar uwartace tayi mata wani abu,hakan yasanya dukkaninsu suka sanya aka rufe mahaifar juna ba tare da sun sani ba.



Bayan haihuwar abdul'azeez da shekara hudu aisha tasake haifan diya mace wadda taci sunan mahaifiyar mai martaba suna kiranta da uswa,bayan ita sai arifa sannan sumaira da huda auta.



Kusan a iya cewa aisha itace tauraruwar maimartaba ko ace giwarsa,tun asali bawai sai zuwa yanzu ba,badon komai ba saboda dukka cikin matanshi babu tamkarta wajen damuwa da lamuransa gamida nuna mishi qauna kulawa da soyayya,hakanan halinta dabanne cikin matanshi,duk da tana da kafiya jajircewa kan dukka abinda tasa gaba.



Idan taso abu tana sonshi ne da dukka zuciyarta,hakanan idan taqi abu tana qinsa ne da dukka zuciyarta,kaifi daya ce ita,ba'a fiya sauketa daga ra'ayinta ko sauya mata al'amura ba.



Baya ga mijinta da iyaye 'ya'yanta sune abu nabiyu da take so sosai a rayuwarta,cikin 'ya'yan kuma sai abdul'azeez tashi qaunar tafi takowa,tun lokacin da aka taba samun galabar cutar dashi sau biyu ta fidda duk wani qasaita izza da isarta,ta sake qaro rashin yarda da tsaron lafiyar yaran nata.



Sosai aka samun nasarar kwantar dashi kwanciyar da ba'aso har abada yatashi ba,saidai zakaran da Allah yanufa da cara,aishan macace data yarda da malamai wadanda zata biya kudi ayi mata sauka duk wata ko sati da addu'o'i kan tsaronta dana yaranta,duk da itadin bata damu can da saitayi da kanta ba,wannan shi yakawo sassaucin lamarin Allah yayanke masa ya tasheshi da wuri.



Tun a sannan tadaura dambar dukkan wanda bayason ganin abdul 'azeez a matsayin yarima saita hanashi bacci

Ta dora buri sosai bisa rayuwarshi

Tana qaunarshi da bashi kulawa fiye da kowa cikin yaranta

Zaka iya taba kowa ta daga maka qafa amma banda abdul'azeez

Zata iya daukan komai sabodashi,hakanan zata iya haqura da komai saboda abdul'azeez

Tayima rayuwarshi babban tanadi

Taci buri da alwashin saiya zama wani shima tamkar yadda mahaifinsa yazama kafin zamantowarshi sarki

Duk wanda yakwana yatashi cikin gidan yasan zallar qaunar da take masa

Saidai duk da wannan yasan wacece mahaifiyarshi sarai,yasan tsarinta yasan halayyarta ta kaifi daya ce!



A yanzu burinta nafarko shine abdul'azeez yayi karatu mai zurfi bakin rai bakin fama,wanda take hasashen shine mataki nafarko da zai soma zama wani haske mai kaifi a gareshi dazai nunawa duniya shi,sunansa yayi fice,yakuma shiga loko da saqo na duniya fiye da sunan mahaifinsa.



Yana da wannan ra'ayin,yana da burin haka,sai akwai abu guda daya tak daya kawo sauyawar ra'ayinsa da nata,burinta guda daya daya zama tarnaqi a rayuwar abdul'azeez,buri guda daya daya kawo sabanin ra'ayi tsakaninsa da ita,abu guda daya dayake neman dagula rayuwa da nutsuwarsa,duk da takan gaya masa

"Abd'azeez,kada kace zakaja da dukkan abinda na shimfida maka,dukkan abinda nakeyi inayine saboda kai,saboda 'yan uwanka,saboda kare suna da matsayi na masarautarku data mahaifina,ka ajiye naka da ra'ayin da burin,na maka alqawarin cewa AKWAI LOKACI!".



Dukkan wani qoqari da juriyarshi ya tattarata waje daya don ganin sun tafi doro daya bisa tsari da ra'ayin mahaifiyarsa,saidai koda yaushe qoqarin nasa yana neman gazawa,akaran kanshi bashi da yadda zaiyi da kanshi,da da akwai da babu makawa zai kasance kamar yadda takeso dinne,saboda babu abinda yake qauna a duniya sama da mahaifiyarsa shima,yadda tabashi qauna haka yake qaunarta koma fiye da hakan,zallar soyayya irin ta d'a da uwa.



Wannan shine taqaitaccen tarihi kan masarautar kaisa,duka sauran abubuwan da basu bayyana ba zasu bayyana kansu a nan gaba,muje zuwa.......🤙ðŸ½Ã°Å¸¤™Ã°Å¸½

7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA*👑



*_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina buqatar siya ki tuntubi wannan number_*



0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





7





   A hankali tasauke labulen harabar tata wadda take iya ganin dukkan abinda ke kaikawo cikin gidan,duk data sauke labulen amma saitaci gaba da tsaiwa gabanshi duk kuwa da cewa bata iya hango abinda ke ci gaba da gudana saboda kauri da nuyin labulen,amma kuma kunnuwanta naci gaba da jiye mata bushe bushe da tashin algaita data mamaye ilahirin gidan gaba daya.



"Tuba nake ranki ya dade,Idan da sabo yaci ace kun saba da ire iren wadan nan abubuwan dake faruwa cikin gidan nan" saita sauke hannayenta daga goya kana ta waiwayo tana duban wadda ke tsaye a bayanta kanta na kallon qasa cikin nuna girmamawa

"Ko jikina bazai taba sabawa da wadan nan al'amuran ba bare zuciyata,mansura...ni kadai nasan yaya nakeji a zuciyata duk sadda yaran nan yadawo hutu gidan nan,idan yatafi kan cika da fata da burin yatafi kenan,ko duriyarsa banson a sake ji,amma.....kullum jiya iyau,komai ya faskara,aisha bansan da wadanne iri bokaye da matsafa take aiki ba" takai qarshen maganar tana dafe goshinta da hannu kana ta yarfar dashi

"Allah ya huci zuciyarki,tabbas wataran haqanmu zata cimma ruwa,tunda dukkan mai nema yana tare da samu" kai kawai ta kada,ba tare data amsa maganar tata ba tace

"An gama shirya dukka kyaututtukan da kayan ciye ciyen?"

"An gama ranki yadade" ta amsa mata tana rusunawa

"Shikenan.....kije,bayan wasu lokuta akai ace injini,ina masa barka da dawowa,sannan ina nan tafe in duba lafiyar dana" tafadi maganar tana jin dacinta har qasan zuciyarta,duk wannan abun tana yine saboda babu yadda zatayi,tana yine saboda tacimma wani buri nata wanda tasoma aiki akai,amma aysha ta dakatar da tafiyar lamarin ta hanyar turashi wata qasa uwa duniya waida sunan karatu,sai taja qwafa tana neman daya daga cikin kujerun alfarma dake mamaye da qaton falon tazauna.



_fulani saratu_



    Babbar haraba ce da aka qawatata da shuke shuke masu sanyaya rai da debe kewa,kashingide take saman wani tafkeken kilishi wanda aka qawata zamanshi da tuntu masu zanen gidan sarautar kaisa da wani yadi mai taushi,wanda duk da taushinsa zanen sarautar da rubutun jiki bai hanashi fitowa ba.



Ita daya ce zaune a wajen kamar yadda ta buqata takuma shaidawa barorinta bata buqatar kowa kadaici takeso tsahon mintuna talatin,saidai duk yadda taso tasamu hutu takuma katange kunnuwa da idanunta wajen jin duk wani sauti alama ko shaida na shigowar abdul'azeez cikin gidan ta gaza cimma gaci,sarewa da algaitar dake tashi saika rantse daura da itane bawai nesa da inda take ba.



Sake gyara kashingidar da har yanzu batajin dadinta tayi gamida jan wani dogon tsaki,bayan tadire tafurta a hankali

"Wannan wacce irin masifa ce!" Idanunta da zuciyarta taf da wasu al'amura da sukayi shekara da shekaru suna sukan ranta.



A hankali take takowa farfajiyar da mahaifiyartata take,duk da idan kadubi fuskarta zaka karanci damuwa qarara a cikinta,jin takunta yasanya fulani saratu daga kai tana duban inda take jiyo takun,ganin walida ce yasanyata maida kanta tana dakon isowarta

"Barka da warhaka mama" walida tafada bayan tazauna gefan kilishin da haj saratu ke zaune akai,bata amsata ba sai data koma tazauna sosai tasauke ajiyar zuciya idanunta kan walidan

"Barka kadai....ya akayi?" Kai tadan rausayar cikin nuna alhini kana ta hadiye wani abu sannan tace

"Mama....dama yau yarima zai daw....."hannu tadaga mata cikin katseta

"Dakata,bansan wani da irin wannan sunan ba,ki kirashi da sunan da mahaifinsa ya rada masa" kaitadan jinjina,tajima da sanin cewa mahaifiyarta bataso ko qaunar taji ankira abdul'azeez da wannan sunan ko misaqala zarratin

"Afuwa....abdul'azeez"shuru yaratsa nadan sakanni,tamkar ba zatace komai ba kana ta ƙuta tace

"Gashi kuwa idanunki sun ganemiki?" Wani busasheshen murmushi da babu armashi ko farinciki a cikinsa ko misƙala zarratin tasaki sannan taɗora

"Akullum aikin mahaifiyarsa kenan,rufe dawowarshi harsai ana yagobe ko randa zai dawo,koda yaushe aisha gani take itadin me wayo ce,bayan duk wayonta babu ruwan ƙaddara da wannan,hmmmm".



Sam walida bata bi takan zancanta,don ita duka waÉ—annan salon maganar tasu bata cika fahimtarsu ba,asalima basa gabanta

"Mama....kaman yadawo a lokacin da bamu shirya masa ba,yadawo a lokacin dabai dace ba" sosai tasanya ƙwayar idanunta cikin ta walidan,tana karantar rudewa ƙarara cikin idanun nata

"Me kike tsoro?"

"Makarantata,kada mai martaba yaqi yarda da maganar tafiyata karatu"

"Akan wanne dalili?" Ta jefa mata tambayar data sanyata ƙara zama

"Mama,kinsan kome maimartaba zaiyi wanda yashafemu sai yayi shawara da abdul'azeez,akowanne lokaci yakance idan babu shi nan gaba shine ubanmu,kuma kinfi kowa sanin yadda bayason wata cikinmu tafita wata ƙasa karatu,afnan kawai ta ishemu misali.....".



Kalaman walidan tamkar wani tuni ne ko fami a zuciyar haj saratu,saboda haka ta tsaida walidan

"Saboda shi abdul'azeez din shine uban kowa?,ko zamansa muke?,ko a ƙarƙashinsa muke?,wai tsoron ma me kikewa ƙaninki?,yaron da kika baiwa kwana hamsin harda doriya....to wannan karon kuwa bazan lamunta ba,abarmin yarana suyi karatu a duk inda sukeso kuma sukaga dama,saboda shima babu uban daya takurashi,asalima shida kansa ya zabi ƙasar dayafiso sannan yatafi,don haka zuwanki makaranta babu fashi indai ina raye,banason ma nasake jin wata magana kan wannan batun" sosai walidan taji dadi,cikin farinciki tadan rungume hajia saratun

"Allah ya qara miki lafiya da nisan kwana"

"Amin" ta amsa ciki ciki saboda bacin ran dake damunta,walidan tabude baki zata sake cewa wani abu wayarta dake saman cinyarta wadda ke jone da erpiece dake cikin kunnenta tadauki kida,saita saki mahaifiyar tata tahau duba kiran,kana tamiqe zumbur tana zura takalmanta

"Ki gayawa mabaruka akawomin ruwa da lemo" kaita gyada mata tayi gaba data amsa wayar.



A hankali jeron gwanon motocin suka dinga fakawa illa qwara daya data ci gaba da kutsa kai zuwa cikin gidan masarautar,wata iriyar mulmulallaiyar mota ce mai ruwan gold,'yar qarama ce wadda dududu bata da wani girman arziqi amma sai azabar kyau da tsada dakuma daukan hankalin mutane.



Bata tsaya ba harsai data isa qofar sassan fulani aisha kana ta tsaha cak,kamar qiftawar ido wani hadimi dake zaune gaban motar yayi wuf yafito,ya tsaya bakin qofar motar yayi qyam yana jira a bashi umarnin bude murfin motar.



Tsahon minti daya kafin ataba glass din motar wanda ya fidda sautin qwas sau daya,sautin na gama direwa a kunnensa yayi maza yabude yana cewa

"Gaba salamun baya salamun magaji ga mahaifinsa,taka lafiya cikin amincin Allah da kiyayewarsa,Allah ya kare mana kai,ya zamar maka jagora kuma majingina yarima kuma sarkin gobe"



Sautin kirarinsa yaqare daidai sanda yasanyo qafafunshi dake saye cikin takalmi half cover shoe irin na maza na zallar fata qirar qasar italy mai dan banzan kyau da daukar idanu,kafin wasu sakanni gangar jikinsa tabiyo bayan qafafun nashi,wasu shegun suit ne suka bayyana ash colour masu madaukakin kyau da jan hankali,sun zauna masa a jikinsa tamkar saboda shi aka qirqiresu,fuskarsa da hannayensa dake daure da wani tsadden agogon gwal sune abu na qarshe da suka fito,hasken ranar dake kwance saman sararin subhana ya haska kwantacciya kuma lafiyayyar fatarsa wankan tarwada,wani irin choculet colour skin wanda ko cikin wankan tarwadan ma bakowanw ke dace da irin nau'inta ba,nau'in fatar dake tsada wanda tsantsar hutu dajin dadi suka hadu suka qara mata ado da qawa da wani irin launi mai daukar idanu.



ƙawatacciyar fuska wadda komai nata ke bisa tsari mai qayatarwa,cikakken gashin idanu da madaidaicin gashin gira wanda qasansa wasu irin madaidaitan idanune wanda basu cika girma ba,hakanan sunfi gaban qananu,saidai wani irin shape ne dasu dake dake cike da kwarjini da maganadisu dakan narkar da zuciyar duk wanda ya zubawa su,musamman 'yammata da yaken dilmiyasu cikin kogin soyayyarsa cikin daqiqu qalilan,kyakkyawan hancinsa mai matsaho da tudu wanda ya ta qasanshi ya qawatu da gashin daya zagaye fuskarshi zuwa habarshi,wanda yasha gyara da wani irin salon aski mai qayatarwa,yakuma fidda kyawawan labbansa,wadanda suke Da surkin ja,daga cikin jerarrun haqora farare tas sun sake qawata fuskar tashi,sai dimple qwaya daga daga kumatunsa na hannun dama.



Miƙewa yayi sosai bayan yafito daga motar yana duban sassan mahaifiyar tasa,tsaiwar tasa ita ta bayyana yanayin tsari na jikinsa,yana da tsaho da murjajjen jiki,wanda murjewarsa yasake tasiri wajen boye adadin tsahonsa,faffadan qirji da kakkauran damtse duk da ya boye cikin rigarshi amma dukkan alamun qarfi da samartakarsa sun bayyana qarara a zahiri,duk kuwa da cewa bazai wuce shekara ashirin da biyar ba

(Lol,masu karatu zasuce wai wannan kyau haka,yawanci ko baka qimanta jarumin littafinka da wannan siffar ba kuda kanku haka kuke hasasoshi,beside ma novel din dukka yakan tafine bisa tafarki biyu,ilimantarwa da kuma nishadi).



A hankali yasoma takawa kai tsaye zuwa sassan fulani aisha,wanda a duba daya kacal da zaka masa ka tantance yadda jinin sarauta daga tsatso biyu na uwa da uba ke zagaya jininsa,yazauna masa kuma ya zame masa jiki,duk inda zaya gifta sai barori da hadiman dake sashen da wadanda wata sabga tashigo dasu dama 'yan ganin ƙwaƙwaf sun zube suna miƙa gaisuwa,kamar yadda yake a tsarinsa yakan ɗaga musu hannu ne kawai yawuce,a haka yadinga kutsa kai har zuwa cikin ainihin ginin dazai sadashi da falo nafarko na mahaifyar tashi.



Kyakkyawar macace hakimce saman ɗaya daga cikin kujerun alfarma royal dake kewaye da falon,ta zarta munzalin ƙuruciya hakanan batakai shekarun da za'a kirata da dattijuwa ba,duk da cewa ta tasamma shekara hamsin babu uku amma baka isa kace tana da waɗannan shekarun ba,mulki da tsananin hutu gamida jin daɗi sun wawashe kaso mai yawa na dukka hasashen da zaka iya yi mata na shekaru yaboye,saika tsammaci tana cikin shekararta ta talatin ko talatin da ɗaya zuwa da biyu ne.



Wankan tarwada ce itama amma saboda hutu yasa fatarta ke nemam juyewa zuwa fara irin farin nan mara haske sosai,duba daya zaka mata kaga izza mulki dakuma qasaita shimfide saman fuskarta.



Sanye take da wani lace na alfarma wanda aka yiwa dinki na manyan mata,wuyanta kunne hannuwa da yatsunta dukka kowanne akwai abun ado,fuskarta wadace take da fara'a,tun sanda kunnwanta suka jiyo mata sautin algaita na isowar shalelen nata fara'a taƙi barin fuskar tata,farincikinta ya gaza ɓuya.



"Salamu alaikum....Allah ya taimakeki,yabaki yawan rai,ina iya ƙarasowa?" Dayake cikin farinciki take ayau din dakanta ta amsa mata

"Bismillah lubabatu" cikin nutsuwa da girmamawa ta ƙaraso falon,wanda ba kowa ne yataba ƙetarashi ba,face ire irensu makusanta,kuma amintattun fulanin,fuskarta fadade da fara'a tazube a gabanta

"Allah ya qara miki lafiya tauraruwar mai martaba,hasken masarautar kaisa,uwa a wajen yariman kaisa....sarkin gobe da ikon Allah,Allah yayi,yarima ya qaraso lafiya,yana gab da shigowa nan,yana neman izini" murmushi yasube ma fulani aisha har saman lebanta,wanda ba kasafai suka fiya ganin hakan ba

"Albishir dinki lubabatu yayimin dadi,ko yaushe saqonki mai dadi ne,kije a bude miki store,kidauki dukkan abinda kikaga kinaso,ladan wannan albishir din naki...yarima kuma basai an masa iso ba,yana iya shigowa duk lokacin dayake da buqatar hakan,kice ina masa maraba" sosai tasake duqawa cikin madaukakin farinciki,tana ayyana iya abinda yau zata diba a store din

"Kinfi gaban haka Allah ya taimakeki,gado kikai ai ba taka haye bace,saqonki yanzun nan zai isa ga kunnen magajin mai martaba,godiya nake...godiya nake...." Hannu ta daga mata,don zuwa yanzu ta qagu kawai taga yaron nata,don haka umma luba tamiqe ta hanzari tafice.



"Assalamu alaikum warahmatullah" ya ambata cikin Muryarshi mai taushi,mai kuma cike da samartaka irin ta matashin da ilimi da mulki suke aiki a jikinsa,miqewa tayi tana murmushi idanunta bisa kanshi,tana jin qaunar yaron nata har cikin ranta

"Wa'alaikumussalam warahmatullah,maraba da yarima" murmushi yasake shima wanda yafidda ainihin kyansa,murmushi na daya daga cikin abubuwan dake masa kyau a dabi'unsa,saudai kash,shidin ba ma'abocin fara'a bane bare murmushin kansa,duk inda kaga murmushinsa to tabbas wajene mai muhimmanci,ko kuma wani muhimmin abune yafaru

"Allah ya qara miki lafiya da nisan kwana Ammi" yafada sanda yake isowa gabanta ya duqa saman gwiwoyinsa tamkar qaramin yaro,hannunta tasanya saman lallausar sumarshi tana cewa

"Alhmdlh,na godewa Allah daya sake kawomin kai gida hutu cikin qoshin lafiya,Allah yaci gaba da albarkatar rayuwarka"

"Amin ummina" ya amsa mata cike dajin dadi sannan tabashi umarnin tashi,yasamu daya daga cikin kujerun yayiwa kansa mazauni bayan tazauna.



Gaisawa suka sakeyi,tana karance dashi,yadda suka saba dai,saidai ta lura akwai dan sauyin yanayi tattare dashi,maganar da suka tabayi watannin baya tadawo mata akai,sai take fatan ba lamarin bane har yanzu cikin ranshi ya kasa barinsa ba kamar yadda ta umarceshi,saidai koma meye zata tabbatar data sake cire masa batun cikin ransa har zuwa lokacin data tanada.



"Kaje ka huta,bani kadai ba har 'yan uwanka na marmarin ganinka,muna da isashshen lokacin zama mu gana,har wata nawa?...." Ta tambayeshi tana dubanshi fuskarta na fidda murmushi,yana tsaye hannunshi guda cikin aljihunsa,saiyadan rusunar da idanunsa zuwa duban wani sashen kana ya amsa mata cikin sanyi

"Ba wata ba ba satittika ba ammi,i forever came back" yanayin fuskarta saiya soma sauyawa daga murmushi zuwa hade rai,wani kallo take masa wanda dama ya tsammaci sama da haka daga gareta

"Me kake cewa azeez?,kadawo kamar yaya?,bayan aqalla akwai shekara daya da wasu watanni a gabanka kafin kagama,kuma kafi kowa sani koda ka gama din bawai zaka dawomin bane yanzu,zaka dora da masters dinka har zuwa inda nake ganin lokaci yayi da zaka dawo kaci gaba da rayuwa cikinmu,karka soma,kada ka yarda kayi abinda zai bata tsarina koya batamin rai,kafin kowa sanina,kafi kuma kowa sanin tsarikana akanka,saboda haka karka soma yin duk wani abu da kasan zai wargatsa tsarina" dukkanin idanunshi yazuba mata da wani irin duba dayake nuna zallar buqatar a tausaya masa a fuskanceshi da nashi buqatun,saita dauke kanta daga dubanshi,saboda ita kanta tasan da idanunshi kadai yana iya karya lagonta,saboda wata baiwa ta musamman da Allah yayi masa cikin idanun,murya a narke hakanan a sanyaye yace

"Please ammi...listen tome" 

"Kawuce ka huta,koma meye daga baya ka sanar dani,amma kasani,bazan yadda da dukkan abinda zaici karo da tsarina ba" daga haka ta baiwa kubra daya daga cikin amintattunta umarnin shigowa

"Allah yabaki nasara....aikene daga sassan fulanin masanawa...."

"A hada da nata da nasu duka ayi yadda aka saba" ta katseta ba tare data bari ta qarashe bayanin nata ba.



Shuru ya ratsa falon har kubran tafice,sannan shima yasoma takawa a hankali yabi sawayenta yana furta

"Na barki lafiya",da ido tabishi harya gama ficewar,tasauke ajiyar zuciya tana lalubar kujera tazauna bayan tadauki wayarta dake daura da ita tasoma neman wani layi,tana jin tausayinsa yana ratsata,amma tilas takauda kai saboda anata ganin tsarinta shine tsari,kuma ko meye tanayi ne don ci gabansa da alfanunsa.



A hankali yatura qofar qawataccen falon nasa cikin wata iriyar kasala ta zuci da gangar jiki,falone na qarshe wanda daga shi sai dakin baccinsa,yalwatacce kuma qawataccen falo wanda komai dake cikinsa kalolin milk ne da gold,komai qanqantar abun kuwa,komai dake cikinsa yana alamta maka gidan da kake kuma sashen wanda kake ba tare daka bata baki wajen tambaya ba,sarauta zalla,komai nadauke da tambarin masarautar,hatta kuwa da kujerun dake falon,falone wanda yake gaba gaba cikin jerin manya kuma tsararrun faluka dake kafatanin gidan,wannan shine qiyasi da wadanda suka samu katarin taba shiga falon sukayi.



Iska yafesar mai zafi daga bakinsa yana kallon manya manyan hotunan dake maqale a falo,wanda bana kowa bane face nashi maimartaba da mahaifiyarsa fulani aisha,wani shi kadai,wani shida ita,wani shida mai martaba wani su ukun,hotunane da sukayi bala'in kyau suka kuma dace da yadda aka shiryasu,hatta da frames nasu suma milk ne da gold.

7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA*👑



*wannan littafin na siyarwa ne,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar siya ki tuntubi wannan numbers din*



0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



8




Gaban daya daga cikin hotunan ammin dake saqale ya qarasa ya isa gabanshi,sosai yazuba mishi yana kallonshi kai kace itace tsaye yana fatan ta karanci tsantsar gaskiyarsa takuma tausaya masa,ya rasa da wanne irin yare zai mata bayani tagane,duk daya fahimci ta gane inda yasa gaba,saidai bata da sha'awa ko niyyar yi masa abinda yake da muradi.



A qalla yashafe kusan mintuna goma ahaka,kana da kanshi ya lumshe kyawawan idanunshi sannan yabudesu,dai dai lokacin daya sauke ajiyar zuciya yasanya hannunshi yana sassauta daurin tie dinshi,kana ya zareshi ya jefar,yasoma rage duk wani kaya da yasan zai takura masa dake jikinsa,a haka ya isa bedroom dinsa yatura yashiga yazauna bakin zagayyen gadonshi yana cire sauran kayan da suka rage.



Sai daya gama cire sauran kayan da sukayi saura a jikinsa sannan yawuce toilet dinsa dake manne da dakin gadon.



Ya shafe a qalla kusan minti talatin sannan yabude qofar toilet din yafito daure da towel,gargasar jikinsa tayi luf saboda ruwa datasha sai sauran ruwan dake diga tun daga sumarshi zuwa qafarsa,a maimakon yazauna shafa mai saiya koma gefan gadon yasake zama,ya jawo locker dake manne da gadon yasoma laluben wani abu.



Mintina qalilan ya debo layukansa na qasar nan yasoma qoqarin cire nakan wayarshi ya sanyasu,bai kammala ba wani abu dake daga saman gadonshi yadanyi wuta gamida 'yar qararrawa,kai kawai ya daga ya kalli abun yamaida kansa ga abinda yakeyi,yasan wani ne ke falon farko yana jiransa,hakanan yakejin baison doguwar magana duk da dama haka halittarshi take,hakanan baison ganin kowa.



Yana gama hadawa yakunnata ya sanyata saman gadon yatafi gaban madubi yasoma shiryawa,nikam tsaiwa nayi ina kallon ikon Allah,kowacce gaba da irin nata man da turaren tamkar macen dake tashen budurci haka yadinga shafa kowanne a muhallinsa,yana cikin fesa body spray wayarshi tadauki tsuwwa,saiya dakata yana komawa da baya don ya duba waye yakirashin.



'Safwa' da manyan baqi shine sunan daya bayyana saman screen din wayar,saiya dauke kanshi yaci gaba da abinda yakeyi din ba tare daya daga ba,saboda yasani tariga da tasan tsarinshi,idan ta katse din ba zata sake kiranshi ba.



Saidai a wannan karon sabanin baya kiranne yasake shigowa,cikin mamaki yasake dubawa,ba ita bace sufyan ne,mutumin da yakeso ya kammala shiryawa yakirashi,babu bata lokaci yadaga wayar yakara a kunnenshi

"Thank god,yauna taki sa'a,ringing biyu kayi picking,'yan iskan yau basa kusa hala?" Yasan me yake nufi,kuma yaudin baijin wani jokes a kanshi irin wanda sukanyi lokaci lokaci a tsakaninsu,murya can qasa yace

"Kana ina?"

"Bansan wannan taqamar taka prince,ka dawo zaka fara kenan,nine maganinka,any way ina dab da shiga garin abuja ne yanzu"

"Oh shit!" Yafadi yana runtse idanunsa

"Hey friend,yaya dai?"

"Baida amfani tunda baka nan,see you later" daga haka ya katse kiran,ya cusa hannunsa guda saman sumar kanshi yana yamutsata,yana buqatar taimako,yana buqatar tallafi,yazama lallai yayi dukkan mai yiwuwa ammi ta fusakanci,ta gane matsalarshi,bayaso yakai ga fadawa ga halaka,yana qyamatar hakan matuqa da gaske,saiya nufi wardrobe dinsa yasoma binciken kayan da zai sanya da hanzari.



Falon dake manne da bedroom dinshi yadawo yazauna hannunshi riqe da wayarshi,yashafe aqalla awanni kan wayar da alama akwai abinda yakeyi kafin alamun dake bayyana anason ganinsa sushiga kadawa,karo na wajen biyar yana basarwa kafin daga bisani yatashi ya isa gaban cctv camera din dake nuna mishi duk wani sashe na gidan,ya fuskanci daga falo na uku ne,saiya shiga inda camera din falo na uku take,afnan ce tsaye bakin madannin qofar,fuskarta na nuna alamun qosawa,sanye take da doguwar riga wadda tabude daga qasa sosai tarufe har qafafunta,kanta yane da mayafi wanda iyakarsa wuyanta,tadan bubbuga qafa alamun gajiya da tsaiwar,saiya daga yabata izinin shigowa.



    "Yaaya....barka da warhaka" tafada cikin nuna farincikin ganinshi

"Ammi tace zaka shigo,amma shuru munata jira,an kawo maka abinci kace a dakatar,shine ta aikoni in gaya maka,ka qaraso sassanta acan xamuci abincin rana tare" kai ya kada mata kawai,wanda hakan yasa tadan bata rai

"Yaaya,har yanzu baka daina ba?,baka bani amsa bafa"

"Am coming" ya amsata a taqaice,idan dasabo sun saba da halin miskilancinsa,wanda tun usuli haka yake,duk da kuwa yadda ammi taso ta sauyashi,koda qannenshi ne yadinga sakewa dasu suna hira amma abun yaci tura,ba kowanne lokaci magana take damunsa ba,tasan ci gaba da tsaiwarta bashi da wani amfani saboda haka tajuya tafice cikin ranta tana mita

"Shi mutum Allahn daya yishi koyaushe kaman wani kurma ko bebe,bakinsa ko tsami bayayi,saikace mai ciwon kunne wanda bayajin me mutane ke fada bare ya amsa su" da wannan qananun mitocin tafice takoma zuwa nasu sassan.



    Zaune yake yana fuskantar ammin tashi cikin shigar qananun kaya da suka sake haska quruciya da kyansa,tazarar dake tsakaninsu dukka kayan abincine da abunsha nau'i daban daban

"Abdul'azeez" muryar amminsa ta ratsa dodon kunnenshi,wanda hakan yasa ya dakata daga shan tataccen ruwan inibi zalla da yaketa faman yi tun dazun,gaba daya jin cikinsa yake a cunkushe,bayajin sha'awar cin komai,saboda matsalar dake barazana da rayuwarsa yana jin tafi qarfin komai

"Ammi" ya amsa mata muryarsa a tausashe

"Matsalar dake gareka har tayi girman da zaka gaza cin abinci?" Ta qarshe maganar tana kafeshi da idanunta cikin son sake karantarsa,saiya ajjiye kofin hannunshi ya hade hannayen nasa waje daya,yana matuqar jin kunyar yin maganar da ita akoda yaushe,abu babu wani wanda zai masa maganin damuwar indai bai tsaya yabude baki yayi magana da itaba yadda yadace

"Hakan nada alaqa da cemin bazaka koma karatu ba?" Tasake jeho masa tambayar.



   Wani nauyi yaji yahau kanshi sosai yadda ta tsareshi da idanu,irin wannan maganar banda abokai ba zaka iya yinta da kowa ba,to amma ci gaba da shurunshi na nufin fadawarshi halaka,saboda duk duniya ita kadaice zata lamunce mishi yasamu mafita

"Kiyimin afuwa ammi,nayi qoqarin nabi tsarinki kamar yadda kika umarceni amma hakan yaci tura,kiyi haquri ammi ki fuskanceni,idan na aikata wani abu da yake ba dai dai ba tamkar na zubar da mutunci da qimar masarautar nan dama taku masarautar,sa'annan bamusan ta wacce fuska abokan adawa zasu bibiyemu ba,wala'alla dukka abinda zan aikata din yazama sun tonoshi,yazama wani makami da zasuyi amfani dashi,wanda zai ruguza duk wani shiri naki akaina ammi,ammi....kiyimin afuwa,kamar yadda nataba gaya miki a baya" saiya sake sadda kanshi yana jin nauyi

"Ina da buqatar aure ammi,idan kikayimin,na miki alqawari bazai dauke hankalina koda ya kadeni daga dukkan qudurin da kika tsara ba,komai zai tafi yadda kike muradi ammi na miki alqawari".



Shuru ne ya ratsa ilahirin falon kai kace babu wani sauran me rai sai na'urori,kowanne tsakaninshi da ita akwai abinda ke kaikawo cikin zuciyarsa,tasani tabbas abdul'azeez tun shekarun baya abinda yake da buqata kenan,tun baikai ga furta mata ba,amma sai tayi tunanin cusa masa ra'ayin karatu tuquru dason maidashi wani madaukaki zaisa ya manta da komai yabi tsarinta,tana ganin a yanzu abdul'azeez tayi quruciya da yawa,yayi qanqanta ace yayi aure,totally bama plan dinta kenan ba,hakan yaci karo da dukkan wani tsarinta,yayin da gefan abdul'azeez zuciyarsa ke cike da fata dakuma burin samun nasara a wannan karon,yanajin cewa indai yayi failing wannan karon to kuma babu wata sauran nasara da zai kuma saka ran samu,hakanan yana tsoron abinda zai biyo baya,bashi da tabbacin ci gaba da wanzuwa a bigiren da yake kai yanzu,komai na iya faruwa dashi,duk da ko sau daya baya yiwa kansa fatan haka

"Abdul'azeez!" Ta kirashi da wani tune dake nuna komai zata fada din daga zuciyarta take gaya masa,magana kaifi guda kamar yadda dabi'arta take!

"Kamar yadda nima na gaya maka a bayane,zancan yi maka aure a yanzu yaci karo da dukkan wani tsari nawa,hakanan zai iya zama silar rugujewar komai,zan maka aure abdul'azeez....amma ba yanzu ba,akwai lokaci,zan maka aure alokacin da duniya tasan waye yarima Abdul'azeez,zan maka aure lokacin daka zama irin mutumin da nakeso,zan maka aure asanda ka qarasa zama cikakken mutum mai raza da firgita zuciyar maqiya abokan gaba da abokan adawa,zan maka auren a lokacin aure na kece raini,irin auren da zai shiga bakunan al'umma,kamar yadda na zaba maka mata wadda tadace takumayi dai dai da yarima abdul'azeez,hakanan idan kayi haquri zan cika maka daya burin naka,amma ayanzu abdul'azeez....a karo na farko ni mahaifiyarka ina mai baka haquri daka dakatar da gudanuwar wannan tunanin a ranka,gaba daya ma abdul'azeez shekararka nawa,25 years fa?,kai kana ganin da wadan nan qananun shekarun naka zaka iya daukan duk wani responsibility na aure?,gefe daya ga goal dinmu da muke son muyi achieving duka at d same time?" Saita kada kai

"Taura biyu ba zata taba taunuwa abaki ba lokaci daya,kayi qoqarin cika dukkan wani buri nawa kagani abdul'azeez,babu abinda zaka nema ka rasa daga nan har zuwa lokacin da zaka bar duniya".



Shuru yakuma biyo baya,cikin qananun mintoci qwaqwalwarsa tayi masa bitar kalamanta,sai kawai yajanyo kwanon dake cike da alkubus yasoma zubawa,saboda yana ganin no way out kuma,abinda yafimishi yaci gaba da azumin tadawwu'i da yakeyi,duk da cewa wani lokaci yakan gamu da tasgaro da wahalhalu,daga lokacin dayayi buda baki zuwa wayewar gari,ci gaba tayi da nazartarsa saidai ta kasa fahimtar kowanne yanayi tattare dashi,hakan yake wasu lokutan idan yaso,duk yadda kaso ga karantarsa sai hakan ya maka wuya,tasauke boyayyar ajiyar zuciya cikin ranta tana fata da saka ran maganar tawuce a wajenshi ne.

"Zaka koma makaranta da zarar hutunka ya qare kamar yadda aka saba,banason mai martaba yasan komai,wannan tsarina,banason kuma yasan da zamansa" kai kawai yasake jinjina mata.



"Auta?,wa nake gani kamar auta?"kubra daya daga cikin amintattun fulani aisha ke fada dai dai sanda take shigowa farfajiyar dake hade da falon da abdul'azeez da mahaifiyarsa ke zaune,cikin waninirin hanzari ta janye kunnuwanta daga laben datayi musu,sannan cikin lokaci qanqani tayi qoqarin yanayinta na masu gaskiya

"Saqo nazo zan kawowa yarima daga sassan fulani adama,to nasamu kuma babu kowa ciknku,kuma ta jaddada min muhimmancin saqon,shi yasa nayi yunqurin neman iso da kaina"

"Saqo?,wanne irin saqo?" Kubra tafada tana jifanta da duban tuhuma,saita miqa mata wani farin yanki dake nannade da wani abu a ciki,kamar ba zata karba ba sai kuma tasa hannu ta amsa tana jifanta da wani kallo

"Kinfi kowa sanin cewa idan fulani na ganawa da yarima,a irin wannan lokacin haramunne ga kowanne cikinmu yarabi wajen sai wanda ta yarjewa,kada ki sake wannan kuskuren ko gangancin,saboda data ganki da kanta kinsan hukuncinki basai na fada ba,a sauka lafiya" tafada tana nuna mata hanya,cikin girmamawa tace

"Godiya nake" kana da hanzari ta wuce kubran,zuciyarta fal farinciki na samun nasarar da tayi kubra bata ganota ba,uwa uba yau tasan tana da gwaggwaban kyauta na iyakacin abinda kunnuwanta sukaji mata,duk da maganar data jin bata zama wata cikakkiya da za'a fahinta ba,amma matuqar akayi dogon nazari ana iya fahimtar wasu abubuwan.



Tsaye tayi tana nazarin yadda tasamu auta a tsaye bakin qofar,bata karanci wani abu ba,amma hakanan taji hankalinta bai kwanta da ita ba,saita jujjuyaa saqon kana taju tafice dashi,don tasan koda an isar dashi ga fulanin abinda zatayi shi zatace nata tayi itama.



Daidai lokacin da wayarta dake saman cinyarta tadauki tsuwwa,tamaida idanu tana kallon kiran uswa babbar diyarta da bata jima da aurarwa ba,wadda ke aure a masarautar kano dake shigowa wayarta,ta dauki wayartata daga saman cinyarta kana tasake cewa

"Maimartaba yana bahrain,dazun kafin isowarka suka tashi,yatafi taron sarakunan arewa,yace ka nemeshi da layinsa nacan" daga haka tadauki wayar uswa din.



"Zaka koma makaranta da zarar hutunka ya qare kamar yadda aka saba,banason mai martaba yasan komai,wannan tsarina,banason kuma yasan da zamansa" fulani adama tasake maimaita maganganun da auta ta gaya mata,ta jujjuyasu tana nazarinsu yafi sau shurin masaki,karo na wajen goma sannan tamiqe tasake tattaki hannayenta goye a bayanta,cikin murya mai amon sauti tafurta

"Nasani wallahi nasani,tabbas akwai wani boyayyen abu da aisha take boyewa,ba shakka nasan da wannan,babu yadda za'ayi ke daya tal kika haifi da namiji wanda babu ko shakka ayau mahaifinsa yarasu ko yayi murabus zai maye gurbinsa,amma ace kin turashi karatu wata uwa duniya,kin zareshi daga dukkan wata harka ta sarauta tamkar shidin agola ne ba jinin gidan ba,tabbas akwai abinda aisha kike shiryawa" saita waiwaya tadubi auta

"Inama ace kin samo gundarin jimlar cikakkiyarta,ba shakka da ayau kin karbi 'yanci" sosai furucin yabugi auta harya sanya jikinta tsuma,tazube gaba daya kan gwiwoyinta tana duban fulani adama

"Indai hakane....namiki alqawarin bankado miki dukkan wani shiri nasu muddin numfashina matuqar zan zama 'ya"

Kai fulani adaman ta jinjina tana fidda murmushi kana tamata nuni da tana iya tafiya.




☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



     Tamkar wadda aka bugewa gwiwoyi haka ta dinga qarasowa gaban gidan nasu idanunta qur kan gidan kamar wadda keson fahimatar yanayin gininsa don zana taswirarsa,duk wata yunwa da gajiyar tafiyar qasa data kwaso daga makarantar zuwa gidan tatafi babu ita,a yanzun fargaba kasala da mutuwar jiki su suka maye gurbin wadan nan.



     Masu aikin gini keta kwaso qasa daga ciki suna fiddota waje,wanda kana ganin yawan qasan zakasan cewar wani sashe na gidan aka buge yabada wannan qasar,mahaifinta na coge qofar gidan cikin 'yan aikin yana sake musu bayani da wassafa musu abinda yakeso suyi masa,da gaske ne kenan hasashenta na dab da zama gaskiya?.



Hankalinta yayi matuqar nisa cikin duniyar tunani,har ta manta da cewa tsaye take qofar gidan nasu,saida taji wani hannu dake cike da qasa yana tabata ana cewa

"Yaaya oyoyo" sannan hankalinta yadawo jikinta,saita waiwaya tana duban gefanta,umaimace,jikin nan yayi budu budu da qasa kai kace tayi birgima ne cikin yashi

"Ya haka umaima,meyasaki wasan qasa bayan na hanaku"

"Gini ake mana yaaya a gida,sabon gini,har cikin dakinmu ma" tayi maganar cikin zallar quruciya gamida nuna murnarta a fili,lallai quruci dangin hauka,batasan hakan me yake nufi ba shi yasata take wannan farinciki,to amma kuma mamakinta datace gini har a cikin dakinsu,kada dai ace abinda yatabayi shiya sake maimaitawa,cikin sauri taja hannun umaiman suka shige cikin gidan da saurinta.



Duk da wannan aikin ginin hakan bai hana umna katti sana'arta ba,saidai duba daya zaka yiwa fuskarta kasan yau koma me aka mata a cike take fam,a nutse tabi tsarin ginin da aka soma yiwa kwaskwarima da kallo

"Ina mahaifinta yasamu kudin yin gini?,bayan yau kwanaki biyu baisiyo koda qwayar hatsi ya kawo gidan ba?" Tayiwa kanta wannan tambayar,babu mai bata amsa,hakanan tambayar bata da wani cikakken amfani a wajenta,tunda bayau tasoma gani ba,kusan wannan shine karo na uku a iya girmanta bayan tayi wayo cikin abinda zata iya tunawa,banda abinda yafaru cikin quruciya

"Me kike ne haka akaina,idan zaki gaba gwara kiyi karki fado kaina,don wannan ba abun mamaki bane wajen ubanku mai halin 'yan bunsuraye,wanda bai ganin akuya ya qyale ba tare dayabi ba,tunda kikaga haka ai amsar dayace,yaga wata akuyar ne zaibita" maganganun umma katti masu matuqar muni da kaifi suka katse tunaninta,saita maida kanta ga umma kattin bayan ta janye baya,da alama tun dazun take neman hanyar fidda kalaman bakinta,amma abun yayi muni da yawa,idan bata duba 'ya'yanshi ba da wasunsu a sannan ke cikin gidan a qalla ya kamata ta duba masu siyen abincinta da maginan dake wajen,idan su ba baqi bane game da yadda sukan aibata junansu maginan da masu siyayyar fa?,saita janye hannun duka qannen nata zuwa dakin nasu da tunkafin ta qarasa ta fuskanci aiki yabi ta kansa.



   Ilai kuwa an kwakwashe kusan rabin dakin an bar musu dan ragowar filin da take da tabbacin ba qaramin quntata zasuyi ba yayi zamansu,tunda dukkaninsu qara girma sukeyi,wannan ne karo nabiyu daya taba datsar dakin nasu yaqara cikin gininsa duk sa'ilin daya tashi aure,cikin baqinciki take duban yadda kayansu sukayi budu budu da sumunti,tana tuna awanni shida baya kafin ta fita makaranta yadda suka hadu ita da qannen nata suka killace kayan da dakin tsaf gwanin sha'awa,amma idan ka kalleshi a yanzu ba zaka tsammaci haka ba.



    Saita nufi akwatinta da sauri tana addu'ar Allah yasa kudinta data adana musu suke jalauta rayuwarsu basu salwanta ba,tajawoshi tabude tahau dubawa.



Nannauyar ajiyar zuciya tasaki harda lumshe idanu lokacin data iskesu yadda suke

"Mai gado!,ke bilki!" Muryar mahaifinta dake kwada mata kiran mafarauta ya ratso dakin,da alama dab yake da isowa,sai tayi hanzarin cusa kudin tsakanin cinyoyinta,daidai lokacin daya qaraso din



"Au,kema baqinciki kike da raya sunnar da mahaifinki zaiyi?" Yajefa mata tambayar da batasan hawanta ba bare saukarta,bata da wata mafita illa girgiza kai alamun a'ah

"Yar nema,sai anyi magana saiki shiga kadawa mutane kai kamar namijin qadangare,to idan ba baqinciki kike ba kina ji ina qwala miki kira ki kasa bude baki ki amsa min?"

"Banji bane baba,kayi haquri" tafada cikin rauni da sanyin murya,yanayin yadda tayi maganar saiya tuna masa da mahaifiyarta maimunatu,sai jikinsa yadanyi sanyi,ya qaraso cikin dakin yana dubanta

"Kiyi haquri maigado,ina nema mana sauqine kinji?" Yafada cikin muryar lallashi,cikin mamaki ta daga kai tana dubanshi,sauqi kuma wanne iri?,bataga wani alamu na neman sauqi daga mahaifinta cikin rayuwar da suke ciki ba,ganin bata fahimta ba saiya sake cewa

"Eh,kinsan annabi yace idan kana cikin talauci kana da mace daya ka ta biyu,idan ka qaro baka rabu dashi ba ka qaro ta uku,idan ka qaro baka rabu dashi ba ka cike ta hudu" tamau kanta ya qulle,duk da tasani babanta yayi dogaro da wannan hadisin qaryar ne tunda dadewa yake aikata dukkan aure aurenshi,hadisin da bashi da tushe balle makama,hadisin da bashi da muhalli ko digo cikin addininmu,hadisin qaryar daya halakar da magidanta da dama,amma tana da yaqinin a yanzun bazai taba fahimtar bayaninta ba idan ma tace zata fahimtar dashi

"Don haka shi yasa naketa wannan abun ko Allah xaisa a dace....nadan ragi dakinku zan mata bandaki a cikin dakinta,saboda balaraba tacemin batason bandakin hadaka,kinsanta gwanar tsafta ce,Allah dai yakawota zaki ganewa idanunki" ya qarashe maganar yana washe baki kamar wanda aka yiwa albishir.



Itadai kanta na duqe a qasa takasa koda dagoshi saboda kunya da nauyi harya gama maganarshi yamiqe tsaye,saiya sanya hannunshi a aljihunsa yafiddo dari

"Ungo wannan ki riqe a hannunki keda qannenki kuci abinci,karki bari wancan baqar kadarar tagani don silaina yau bazai shiga hannunta ba 'yar baqinciki,nasan yadda kiketa dawainiya dasu,kedin diyar albarka ce,kinyo gadon halin uwarki,Allah yaqara miki himma,yabaki miji na aurar dake na huta,ko yaron nan yamiki magana zai fito maigado karki masa halin miskilancin nan naki na banza,ki bashi dama kinjiko?" Bata da wani xabi illa tace masa to,saboda ta qagu ma yafice din yabasu guri.



Ranar bazata fita aiki ba saboda umma luba ta gaya mata zatayi kwana biyu gidan sarki,don haka tazage ita da qannen nata suka gyara ragowar filin dakin daya rage musu suka goge simintin da tsumma.

7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA* 👑



*_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina ds buqatar siyan naki kema ki garzaya ki nemi wadan lambobin_*


09032345899


9




    Ya jima tsaye gaban mudubi yana qarewa kanshi kallo kai kace wata matashiyar budurwa ce data gama ado tanason tantance meye baiyi ba a jikinta tasauya,saidai shi tsaiwar da yayi sam bata da alaqa da irin wannan,yana tsaye ne yana duban kayan da amminsa ta aiko mishi dasu ayau,wanda yana da tabbacin nuni take masa da cewa ya aje qananun kayansa yakoma irin wannan shigar har zuwa lokacin da zaya koma inda yafito.



     Kayane irin nasu na sarakai,wanda suka ji aiki ko ina dake nuna zallar sarauta,wani irin yadine ruwan bula mai turuwa wanda aka yiwa aiki da goldin din zare,sai wasu lausassan takalma rufaffu masu wata iriyar lanqwasa daga gabansu,hakanan an shirya musu duwatsu masu haske da qyalqyali daga samansu,takalma ne masu matuqar kyau daraja da tsada na zallar fatar damisa da gashin jimina,sai rawani da aka nada mishi wanda yadace da shigar tasa da kuma kalar kayanshi,yasan kuma ta sanya rawanin ne saboda umarnin data bashi nayau ya tabbatar yashiga anyi xaman fada dashi.



     Sosai shigar tasauya kamanninsa,saidai ta qara masa kwarjini dakyau,tasake maidashi wani mai shekaru ta boye quruciyarsa.



      Yana mamakin yadda ammin ke nuna mishi qauna da gata mai yawa amma ta gaza faranta mishi kan abu daya,abu dayan dashi a nashi ganin da kuma wajensa bai daukeshi a wata matsala ba.



     Don kanshi ya gaji da tsaiwar,ya daga kanshi a nutse yaduba agogo,lokacin daya kamata ace yashiga yayi,saboda haka yanufi wayarsa da niyyar sanyata a silent yasakata a aljihunsa.



      Saidai yana tsaka da qoqarin maidatan kira yashigo wayar tashi,kamar kowanne lokaci sunan Safwa yabayyana kan fuskar wayar,saiya tsaya yana duban sunan kamar baqone a wajensa,baisan iya adadin sau nawa tayi kiranshi ba daga dawowarsa zuwa yanzu,saidai kosau daya bai daga ba bare yabi bayan kiran nata bayan ya tarad da miscal,hasalima wasu lokutan shine da kanshi yake rejecting,don sam baiga amfamin ci gaba da tarayyarsu ba,tamkar ciwone,wanda maimakon azuba mishi magani sai ake bashi guba,saboda haka yasanya hannunshi yayi rejecting da kansa kana yaci gaba da abinda yake.



     Kamar hadin baki kiran sufyan yasake shigowa,ya dakata daga qoqarin sakata a aljihu da yakeyi,ya daga kiran yakara akunnenshi

"Mazaaa.....ya mutumina kana gida ne?" Ya fada da alamun nishadi saman fuskarsa,cikin salon maganarshi dake cike da qasaita yace

"Ya akayi?,ina gida....but amma zan shiga wajen maimartaba za'ayi zaman fada dani" wani dan qaramin ihu sufyan yasaki najin dadi

"Kace kawai zaka soma shiga harkoki kaga ya suke?" Qaramin tsaki yaja saboda shi sam a yanzun ba wannan bane babbar damuwar dake neman durqusar da rayuwarsa ba

"Ba wannan ba.....tunda nazo bamu hadu da maimartaba ba yayi tafiya,sai cikin daren jiya yadawo....."

"Ohkey....anjima zan shigo,ina fata nasamu daddadan labari na amincewar ammi?"

"Aside this matter sufyan,saika shigo kawai" daga haka ya datse kiran yana jefa wayar a aljihu,sannan yasoma ficewa daga dakin.



     Duk inda ya gifta saiya tsaida zirga zirgar duka wani hadimi ko barori dake kaikawo cikin gidan har sai yawuce,kwarjininsa kadai ya isa yacika maka idanu,kowanne sashe yagifta gaisuwa suke miqa mishi,basu damu da yadda yake wucewa ba tare daya damu dako daga musu hannu ba,saboda sun riga sun kwana sun tashi da tsabar miskilanci irin na abdul'azeez din,wannan ba wani sabon lamari bane a wajensu.



     Tun daga nesa ya hangota tana tahowa ita da airah,diyar fulanin masanawa tafarko,wadda duka duka ba zata wuce shekara goma sha biyu ba.



Tunda suka hangoshi kowacce cikinsu tasake shiga nutsuwarta,shikam yi yayi kamar bai gansu ba,saidai yana sane da tahowarsu,saboda komawarshi ta qarshe yaba qwafe da walidan,yasha attempting na koya mata hankali ammi keda dakatar dashi

"Ba abinda bazaka gani ba tattare da yan uwanka...amma abinda bakeso dakai shine,babu ruwanka da ita,kadauke kai da idanu daga dukkan abinda zatayi".



Saidai wani abu guda,tun yana qanqani mutum ne da baison raini,yadda jinin sarauta ke yawo ajijiyarsa haka kusan dukka halaye da dabi'unsa suke,hakan yasanya lamura da dama babu ruwanshi dasu.



Suna gab da iske juna yayiwa dogarawanshi inkiya,tuni suka bace daga farfajiyar,kowanne yasamu saqo da kunnuwanshi bazasu jiyi tattaunawar abdul'azeez da 'yan uwan nashi ba yatsaya qyam yana jiran umarni

"Barka da warhaka hamma yarima"airah ta fada cikin girmamawa yayin da walida ke qoqarin wuceshi tamkar ma bata ganshi ba ko bata sanshi ba,duk da yadda zuciyarta ke tsalle saboda tsaro dakuma kwarjinin abdul'azeez daya cika wajen.



Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata data sanyata tsaiwa cak,take cikinta yajuya fuskarta tasoma hada gumi,amma sai tayi yunqurin saita kanta sanda kalaman mahaifiyarta yafado mata

"Karki sake karki kuskura kici gaba da bashi wata qofa da xaisa ya rainaki,kin bashi kwanaki kusan dari a duniya kafin isowarshi,karki yadda kwarjininsa ya firgitaki koda kinji razani a ranki.....haka halittarsa take,amma dole mukoyi fada da wannan kwarjinin nasa....wanda nake da yaqinin annamimiyar mahaifiyarsa ce ta nema masa....".



Taku uku yayi zuwa gabanta yana duban shigarta sama da qasa,shigace da sam bai dace ace tana ratso cikin gidan da ita ba,gidan dake da tarin hadimai maza da mata,ya mata jan kunne kusan kashi uku akan hakan amma bata sauya zani ba,saboda daurin gindi data samu daga wajen mahaifiyarta.



Dauke kai yayi kana ya gotata kadan kamar zai shige,idanunsa kan airah da take cikin yalwatacciyar doguwar riga da wadataccen mayafi,sam mahaifiyarta bata barinta tayi qazamar shiga tun tana qanqanuwarta

"Saunawa naja miki kunne kan dressing dinki cikin gidan nan?" Cikin tsananin jarumta ba tare data iya juyowa ba sun hada idanu tace

"Gaskiya abdul'azeez kafita daga sabgata.....idan ka manta bari na tuna maka,nidin yayarka ce,gaba nake dakai" tana kaiwa tasauke boyayyar ajiyar zuciya,wani qaramin miskilin murmushi yasaki,yamiqa hannu yariqo airah kana yadawo gabanta yatsaya yana duban qwayar idanunta

"Ko kadan baki taba wani abu dazai nuna cewa gaba kike dani ba,beside ma ayanzun koda bakiso nine gaba dake.....shigar qanwarki bata isheki misali ba?" Saiya daga yatsanshi yanunata dashi

"Wannan shine karo na qarshe dazan sake jan kunnenki game da wannan....ki kiyaye" saiya saki hannun airah yasoma tattaki zuwa gaba,kana ya basu alamar ya kammala da abinda yake,cikin sakanni suka bayyana sukaci gaba dayi masa tattaki har zuwa fadar.



ƙawatacciyar fada ce mai girma da yalwa,wadda tana jerin ɗaya daga cikin fadodi na alfarma cikin jerin fadar da sarki mu'az yake da ita,komai na cikin fadar kama daga shimfidu na alfarma zuwa kujerun zama,adon zanen (dagi) dakuma dardumai dake jikin bangon dukka golden ne da ratsin silver gami da maroon wanda kusan yafi yawa.



     Hakimai da yawa sun isa gurin a sannan,harda shi kansa mai martaban,saboda haka yaratsa cikin nutsuwa ya isa gaban mahaifin nashi ya miqa gaisuwa kamar yadda kowa yakeyi sannan ya yiwa kanshi masauki daura da mai martaban.



     Sun shafe a qalla awanni biyu cur ana zaman fada kafin daga bisani mai martaban yasoma sauraron shari'u daga talakawansa,abdul'azeez yana zaune daga gefe yana kallon yadda mahaifinsa kebin komai daki daki cikin hikima,kana yayi hukunci bisa adalci,sosai abun yaburgeshi,saiyaji duk a zaman wannan yafi qayatar dashi,zaman yatashi aka rufeshi da addu'a,maimartaba yawuce zuwa sassansa bayan yasa an shaidawa abdul'azeez umarninsa na cewa yasameshi a sassansa.



    Su biyune rak cikin falon duk girmanshi,sai tarin kayan abinci da kayan marmari da aka ajiye musu

"Matso abdul'azeez" cewar mai martaba yana duban abdul'azeez din cikin tsantsar qauna da kulawa.



      Sau tari abdul'azeez din kanyi mamakin yadda mahaifin nasa ke sakewa dashi sosai,sukanyi hira cikin yanayin da dazaka ganshi kai bakace shine MAIMARTABA SARKIN KAISA BA.



      A bayan fage mu'amala yake musu irin ta uba da 'ya'yansa,bama iya abdul'azeez din kadai ba,har duka sauran 'yan uwanshi ma.



     Cikin girmamawa yamatso,yasanya hannu kamar yadda shima maimartaban yasanya nashi hannun,duk da abdul'azeez don ba gwanin cin abinci da hannu bane,amma wannan karon abun saiya qawatar dashi.



      "Yaya makarantar?,da fatan komai yana tafiya yadda yakamata?" Ya jefa masa tambayar sanda suke tsaka dacin abincin,kaiya jinjina yana qoqarin hadiye abincin bakinsa

"Ina fatan babu wata damuwa?,don na qagu lokacin da zaka kammala karatun yayi kadawo cikin ahalinka" kai yakuma gyadawa kamar wani qadangare yana qoqarin boye abubuwan dake yawo saman fuskarshi,don yasani sarai maimartaban ba baya bane wajen iya karantar mutum shima tamkar amminsa

"Ma sha Allah,Allah ya taimaka"

"Amin Allah ya taimakeka" yabashi amsa a ladabce.



     Shuru yasake ratsawa kafin maimartaba yasake magana

"Ga 'yaruwarka nan....ta dage itama so take tafita koda egypt ne ta hada degree dinta" amamakance abdul'azeez yadaga kai yana duban maimartaba,sai akayi arashi shima shi yake kallo,hakan yasa yadan sauke idanunsa qasa yana ci gaba dakai abinci bakinsa,ko kusa ko alama baya yiwa 'yan uwanshi mata sha'awar barin qasarsu zuwa wata uwa duniya neman karatu har wata qasar,saboda su kadai sukasan me idanunsu suke ganemusu,yaran musulmi 'yan arewa hausa amma idan kagansu saika rantse da sarkin daya halicceka basusan wata kalma kota ZO IN KASHEKA da hausa ba,hakanan saika rantse basusan inane alqibla ba bare kayi musu tunanin musulunci,shi a karan kansa yatuna yawan 'yamnatan dake kara kaina da artabu a kanshi,duk da sautari kwarjininsa na taka musu burki,uwa uba bashi da fuska kamar yadda sauran samari keda ita,sakewa da sakin jiki da fuskawa duk wadda ta doshesu.



     "Abdul'azeez" kiran damai martaba yamasa yadawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi,saiya dago yana duban mai martaba,dakatar dacin abincin yayi shima kamar yadda yaga mai martaba ya dakatar

"Ka gayamin meye ra'ayinka kan hakan,don ban sake magana ba kan lamarin ba,ba jirayi dawowarka ne,saboda kaidin watan watarana kaine uba a wajensu,koda kuwa akwai wadanda suka girmeka a cikinsu".



     Cikin nutsuwa yabude baki yasoma magana

"Inda zai yiwu Allah ya qara maka lafiya....ni a nawa ra'ayin bana sha'awar daya cikinsu tafita wata qasar karatu....koda wacece kuwa a cikinsu.....,zaifi kyau dakuma kwanciyar hankali kowacce tayi karatu a qasarta....koda bazasuyi ba cikin qasar KAISA ba" daga haka yayi shuru yana jiran abinda maimartaba zaice.



     Kai yake jinjinawa,shi kansa wannan hukuncin shine hukunci mafi kwanciya cikin ranshi,sai yaji abdul'azeez din nasake samun wani matsayi na musamman a idanunshi,kamar yadda halayensa da dabi'unsa suka banbanta hakama tunaninsa,duk da qananun shekarunsa da basu haura ashirin da biyar ba

"Wannan tunanin naka yayimin abduk'azeez,Allah ya albarkaci rayuwarka kaida sauran 'yan uwanka"

"Amin ya Allah Allah ya taimakeka....godiya nake".



     Daga haka suka shiga tattaunawa kan wasu lamuran daban,wasu sun shafi masarauta ne kai tsaye,wasu kuma sun shafi al'amuran da suka dangancin sarki mu'az a karan kanshi.



      Saida lokacin sallah yayi sannan suka tashi,yafita yabar maimartaba yana shirye shiryen fitowa don halartar sallar azahar cikin jam'i a masallacin dake mallakin masarautar kamar yadda yasaba duk lokacin da yake qasar matuqar ba tafiya yayi ba,wanda hakan yasake tasiri qwarai a zukatan dukka jama'ar gidan dama sauran al'ummar dake wajen masarautar.



     Doka ce cikin gidan naduk wani bawa hadimi ko barori su saki dukkan aikin da suke da zarar lokacin sallah yayi suje suyi,wannan na daya daga cikin sirrika na daukakar masarautar,da samun wani irin kwarjini da haiba na musamman.



     Yana gab da isa masallacin saqo ya riskeshi na nemanshi da amminsa take,hakan yasanya suna kammala sallar yawuce sashen nata,duk da yaso yafita yadansha iska yaga garin sosai,don tunda yazo bai samu ya miqe qafa ba,sai yake jinsa duk a takure,sakamakon sabo da yayi da qasar daya fito,wanda take wadace da guraben hutawa dakuma shan iska.



      A falo na uku yau yayi burki,jakadiya ta isarwa da ammi saqon zuwan nashi,daidai lokacin tana zaune tana waya da babbar aminiyarta qwaya daya a duniya,wadda take iya raba sirrinta da matsalolinta da ita,kamar yadda itama take raba nata matsalolin da ammin,saboda tsabar shaquwa dakuma dadewa da sukayi tare tun zuwan ammi qasar nijeria,saita yanke kiran tana bawa surayya uzurin zata kirata.



     Kamar koda yaushe,cikin shiga ta alfarma dake nuna izza da mulkinta ta tako zuwa falon

"Barka da warhaka ammi" ya furta yana duban yanayin fuskarta,bata amsashi ba har sai data zauna kana ta amsa masa,tare da jefa masa tambaya

"Meya faru tsakaninka da safwa?"

"Takawo qarata kenan as usual?" Ya tambayi kanshi da kansa can qasan zuciyarsa ba tare daya furtawa ammin ba

"Babu komai....takawo qarata ne?" Da idanu ta kafeshi nawasu sakkani sannan ta amsa mishi

"Tabbacin baka da gaskiya kenan,ka gayamin meya faru tsakaninku?.....ta shaidawa jakadiya kadaina daga wayarta tun sanda kadawo,hakan na nufin kasoma daukar mataki na bijiremin?" Kai yakada,sam shibai kawo hakan a matsayin wani abu ba,saidai tuncan mutum ne shi da baison takura ba,bare shidin dabai dauki soyayya abakin komai ba bare tadameshi,hasalima yayiwa kanshi alqawarin bazai taba soyayyar ba,hakan yasanya yabaiwa ammin tashi hadin kai dari bisa dari lokacin data zaba masa safwa a matsayin matar da takeso ya aura aduk sanda lokacin auren yatashi.



    Ya auna safwa kan mizanai saiyaga tacika kaso saba'in cikin dari,hakan yasanya yaga bashi da wata matsala da hakan,zai iya karbarta.



        Safwa diya ce ga wani hamshaqin dan kasuwa ibrahim khalilu attah da yayi suna yayi shuhura hakanan yayi fice a garin kaisa kano jigawa dama sauran garuruwan dake arewa harma da kudancin nigeria,dan kasuwa ne na gasken gaske wanda ya mallaki kadarori masu tarin yawa ciki harda rijiyoyin man fetur,safwa ita daya Allah yabasu,hakan yasanya tasamu gata na gaban misali,hakanan tatashi cikin wadata ba tare da tasan wata kalma da talauci ko babu ba,shagwabbiya ce wajen iyayenta,suna matuqar ji da ita dakuma lelenta,hakanan suna gudun duk abinda zai bata ranta,safwa nada kyau dai dai nata,fara ce qal wanda hakan yasake qarawa halittarta ado,bata dawani kauri ko kadan,don haka bakayi kuskure ba idan ka kirata da siririya.



       Shekararta ashirin da uku,duka duka shekara biyu kacal abdul'azeez yabata,saidai yanayin kwarjini haiba da cikar saiffa yasa zakayi tsammani yabata shekara kusan goma ne.



       Tana masifar son abdul'azeez,don kusanma tafishi farinciki da hadin da akayi musu,duk da cewa tana qoqarin nuna darajarta ta mace,tana danne soyayyar da take masan,abdul'azeez yacika duk wani buri nata kan aure,hakan yasanya tariqeshi da dukkan iyawarta da dabarunta na diya mace.



       Balaifi,tayi tasiri a zuciyar abdul'azeez din,duk da miskilancinsa kan hanashi maida mata martani yadda yakamata,ita kuma hakan yana masifar takurata,soyayya takeso suyi tuquru bawai ta lalacewa ba,aah soyayya irinta turawa wanda ako ina basa iya boye abinda ke zuciyarsu.


       

       Mahaifiyarta na daya daga cikin jerin gwanon qawayen fulani aisha da tasu tazo daya,cikin burikanta na ganin ta gina rayuwar abdul'azeez din da ingantattun dirkoki tako wanne bangare yasa taga babu diyar data dace da abdul'azeez din sai safwa,tana yiwa mahaifiyarta tayi kuwa babu jinkiri ta amince da hakan.



      Akwai banbancin halaye da dabi'u masu yawa tsakaninsa da safwa,saidai dukkaninsu basu daukesu a wani abu can dazai kawowa relationship dinsu cikas ba.



"Abdul'azeez dakai nake fa?" Ammi tasake tambayarsa bayan wasu mintuna dayin shurunsa,dazai iya,dakuma zai yiwu daya gaya mata mawuyacin halin da yake shiga aduk sanda zaiyi doguwar hira da safwa,wanda wannan shine babban dalilinsa na qaurace mata

"Akwai dalili ammi,amma banyi saboda wata manufa data sabawa tsarinki ba...."

"To banaso,ban kuma son naji wani abu mai kama da matsala tsakaninka da ita"

"Ayimin afuwa,in sha Allahu za'a gyara" ajiyar zuciya tasaki,yana daya daga cikin abinda yasa take qaunar abdul'azeez,bai taba tsallakewa umarninta,idan ta nuna tanason abu yakan fita sonshi,baya yarda koya bari wani abu ya bata ranta akanshi

"Allah ya albarkaci rayuwarka,ya baka zuriya ingantacciya wadda zata bika fiye da yadda kake mana"

"Amin ammi,na gode"



     Ganin lokaci yadan ja yasanya ya haqure da fitar,yabarshi idan sufyan ya iso sa fita tare,sai yazarce sassansa don ya kwanta yahuta kafin sufyan din ya iso.

7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: *ZAFAFA BIYAR 2021*




*_DANDANO DAGA LITTAFIN_*



*SIRAÆŠIN RAYUWAR BILKISU*



*Tare Da Alƙalamin*



*_SAFIYYA HUGUMA_*





       Tamkar mutum mutimi haka take zaune cikin falon gidan,daga kunnuwanta har idanuwanta basa iya ganin komai,basa kuma gane kome face mai rayuwarta ta gaba zata haifar mata.



      Hannunta na dama dunqule yake da takardar data zamto tamkar wani mubudi ne na rayuwarta ta gaba,takarda ce da saqon dake ciki take jinsa daidai da saqon ranar mutuwarta,riqonta kawai zafi yake mata tun daga tafin hannunta har zuwa qwaqwalwa da zuciyarta,yakuma zarce zuwa ilahirin jikinta gaba daya.



     Duk da cewa tana tsammanin zuwan ranar,duk da cewa tasan cewa lallai lallai komai daren dadewa irin wannan ranar tana tafe,takuma shirya zuwanta tun daga ranar da aka soma lissafin kasantuwar kwanakin har zuwa randa zata risketa,saidai batasan me yasa ba,meye dalilin data tabata har haka ba,batasan meye dalilin da jikinta da zuciyarta suka girgiza har haka ba,sabone?,ko kuwa tunanin me gobenta zata haifar mata ne?,meye matsayinta meye sakamakon rayuwarta?,wanne sabon shafin zata bude?



      Karo na qarshe ladingo tafito tafito da akwatinta da take jin shine abu na qarshe a cikin dakin data mallaka,ta qarasa inda take aje musu kayansu shima ta ajeshi,ta qarasa gaban bilkisu ta tsaya cikin rusunawa

"An gama fitar da komai,ance jirgin qarfe biyu zamu bi,yanzu haka mai motar dazai daukemu zuwa filin jirgin yana kan hanya...."



       Qwaqwalwarta tajiyo wani sashe na maganarta,saidai bata fahinta duka ba,cikin jimla guda ta tattara maganartata,qwaqwalwarta ta aika mata da saqon

"Tafiya zakuyi,zaku koma nigeria,zaki kuma cikin gidanku".



      Tamkar wadda ake bawa umarni sai kawai tamiqe,cikin qarfin hali tasanya hannu tagyara zaman qaramin hijabinta,kana tasoma takawa a hankali kamar mai tafiya saman qayoyin da aka shimfidawa hanyarta tayi hanyar bedroom din daya zama shine matattarar dukka wani tarihi nata.



      Idan ka kalleta a sannan zaka iya rantsewa tashigo dakinne tana son fayyace da ainihin qasar wanne waje aka gina dakin saboda yadda takebin kowacce kusurwa ta dakin da kallo sama zuwa qasa da kallo har na tsahon wasu daqiqu.



       Sauke idanunta tayi awani sashe can na dakin,tasoma takawa a hankali kamar wadda maganadisu yake janta zuwa arean,tasa hannu tasoma shafa wajen,yana yawan tsaiwa a wajen duk da cewa cikin duhu take ganinsa,yana son wajen sosai duk da bata taba ganinsa muraran ba,saita sake matsawa da jikinta wajen,ta lumshe idanunta tana shaqar daddadan qamshin da wajen yake fitarwa,tabbas qamshinsa ne,abinda duk cikin rayuwar datayi mai kama da mafarki tafi riqewa,saikuma qaqqarfar ajiyar zuciya wadda tasaka dukkan gabbanta suka saki,hawayen da uta kanta batasan na meye ba suka ziraro daga idonta guda daya.



      Kamar wadda aka tsikara tajuya da sauri tanufi qofar ficewa daga dakin,dakin da zuwa yanzu yakoma zallar kangonshi babu komai ciki tamkar wasu rayuka basu taba wanzuwa a ciki ba,batasan inda kayan suka koma ba tunda dama ba mallakinta bane.



      Girgiza kanta take dasauri tana gayawa kanta,tabbas bata tsira da komai ba,babu abinda ta tsira dashi koda kuwa hoton fuskarsa ta zahiri ne face ragowar qamshinsa daya barwa hancinta da qwaqwalwarta tabonsa.



       Cak ta tsaya tana duban gabanta,kana ta duqa a hankali takai hannunta tadauki zoben daya dauki hankalinta qwarai,zobene da tasha ganinsa a yatsunsa,abun guda daya tak datake iya banbance dangane da duk wani abu daya shafeshi,cikin sauri tadauki zoben ta damqe a hannunta kana cikin sassarfa tafice daga dakin ta zarce da ficewa daga gidanma gaba daya don tanaji cewa izuwa yanzu itama ya kamata ta yanke dukka sauran abinda yayi saura.



        Tanajin ladingo na mata magana saidai bata ko tsaya ba bare ta waiwayo ta dubeta,fatanta shine ta raba kanta da komai daya wanzu a shekara guda,ta yanke dukkan wani abu dake da alaqa da shekarar........




*_tofa masu karatu!!!,daya daga cikin rukunin gungun ZAFAFA BIYAR KENAN!,WADANDA ZASU ZO MUKU DAGA ZAFAFAN MARUBUTANKU NA MUSAMMAN,SAURAN SUNE KAMAR HAKA_*



SARAN BOYE

_BILLYN ABDUL_


ABINDA KE CIKIN ZUCIYA

_HAFSAT RANO_


MIN ƘALB

_MAMUHGHEE_


KIBIYAR AJALI

_MISS XOXO_


Duka BIYAR 5 zaku samesu akan garabasar naira 700 kacal,


Guda hudu 4 Kuma 500,


Guda uku 3 Kuma 450,


Guda biyu 2 Kuma 400,


Guda daya akan 300.


Ma'ana

Each one is 300

2 is 400

3 is 450

4 is 500

5 is 700


Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇


ACCOUNT NO- *0812652655*

ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*

BANK NAME: *ACCESS BANK*


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇


 0903 234 5899


IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇



09033181070


Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne

SABUWAR SHEKARA 

SABON SALO


TEAM#ZAFAFABIYAR🔥

7/11/21, 4:29 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA* 👑



*_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina ds buqatar siyan naki kema ki garzaya ki nemi wadan lambobin_*


09032345899


9




    Ya jima tsaye gaban mudubi yana qarewa kanshi kallo kai kace wata matashiyar budurwa ce data gama ado tanason tantance meye baiyi ba a jikinta tasauya,saidai shi tsaiwar da yayi sam bata da alaqa da irin wannan,yana tsaye ne yana duban kayan da amminsa ta aiko mishi dasu ayau,wanda yana da tabbacin nuni take masa da cewa ya aje qananun kayansa yakoma irin wannan shigar har zuwa lokacin da zaya koma inda yafito.



     Kayane irin nasu na sarakai,wanda suka ji aiki ko ina dake nuna zallar sarauta,wani irin yadine ruwan bula mai turuwa wanda aka yiwa aiki da goldin din zare,sai wasu lausassan takalma rufaffu masu wata iriyar lanqwasa daga gabansu,hakanan an shirya musu duwatsu masu haske da qyalqyali daga samansu,takalma ne masu matuqar kyau daraja da tsada na zallar fatar damisa da gashin jimina,sai rawani da aka nada mishi wanda yadace da shigar tasa da kuma kalar kayanshi,yasan kuma ta sanya rawanin ne saboda umarnin data bashi nayau ya tabbatar yashiga anyi xaman fada dashi.



     Sosai shigar tasauya kamanninsa,saidai ta qara masa kwarjini dakyau,tasake maidashi wani mai shekaru ta boye quruciyarsa.



      Yana mamakin yadda ammin ke nuna mishi qauna da gata mai yawa amma ta gaza faranta mishi kan abu daya,abu dayan dashi a nashi ganin da kuma wajensa bai daukeshi a wata matsala ba.



     Don kanshi ya gaji da tsaiwar,ya daga kanshi a nutse yaduba agogo,lokacin daya kamata ace yashiga yayi,saboda haka yanufi wayarsa da niyyar sanyata a silent yasakata a aljihunsa.



      Saidai yana tsaka da qoqarin maidatan kira yashigo wayar tashi,kamar kowanne lokaci sunan Safwa yabayyana kan fuskar wayar,saiya tsaya yana duban sunan kamar baqone a wajensa,baisan iya adadin sau nawa tayi kiranshi ba daga dawowarsa zuwa yanzu,saidai kosau daya bai daga ba bare yabi bayan kiran nata bayan ya tarad da miscal,hasalima wasu lokutan shine da kanshi yake rejecting,don sam baiga amfamin ci gaba da tarayyarsu ba,tamkar ciwone,wanda maimakon azuba mishi magani sai ake bashi guba,saboda haka yasanya hannunshi yayi rejecting da kansa kana yaci gaba da abinda yake.



     Kamar hadin baki kiran sufyan yasake shigowa,ya dakata daga qoqarin sakata a aljihu da yakeyi,ya daga kiran yakara akunnenshi

"Mazaaa.....ya mutumina kana gida ne?" Ya fada da alamun nishadi saman fuskarsa,cikin salon maganarshi dake cike da qasaita yace

"Ya akayi?,ina gida....but amma zan shiga wajen maimartaba za'ayi zaman fada dani" wani dan qaramin ihu sufyan yasaki najin dadi

"Kace kawai zaka soma shiga harkoki kaga ya suke?" Qaramin tsaki yaja saboda shi sam a yanzun ba wannan bane babbar damuwar dake neman durqusar da rayuwarsa ba

"Ba wannan ba.....tunda nazo bamu hadu da maimartaba ba yayi tafiya,sai cikin daren jiya yadawo....."

"Ohkey....anjima zan shigo,ina fata nasamu daddadan labari na amincewar ammi?"

"Aside this matter sufyan,saika shigo kawai" daga haka ya datse kiran yana jefa wayar a aljihu,sannan yasoma ficewa daga dakin.



     Duk inda ya gifta saiya tsaida zirga zirgar duka wani hadimi ko barori dake kaikawo cikin gidan har sai yawuce,kwarjininsa kadai ya isa yacika maka idanu,kowanne sashe yagifta gaisuwa suke miqa mishi,basu damu da yadda yake wucewa ba tare daya damu dako daga musu hannu ba,saboda sun riga sun kwana sun tashi da tsabar miskilanci irin na abdul'azeez din,wannan ba wani sabon lamari bane a wajensu.



     Tun daga nesa ya hangota tana tahowa ita da airah,diyar fulanin masanawa tafarko,wadda duka duka ba zata wuce shekara goma sha biyu ba.



Tunda suka hangoshi kowacce cikinsu tasake shiga nutsuwarta,shikam yi yayi kamar bai gansu ba,saidai yana sane da tahowarsu,saboda komawarshi ta qarshe yaba qwafe da walidan,yasha attempting na koya mata hankali ammi keda dakatar dashi

"Ba abinda bazaka gani ba tattare da yan uwanka...amma abinda bakeso dakai shine,babu ruwanka da ita,kadauke kai da idanu daga dukkan abinda zatayi".



Saidai wani abu guda,tun yana qanqani mutum ne da baison raini,yadda jinin sarauta ke yawo ajijiyarsa haka kusan dukka halaye da dabi'unsa suke,hakan yasanya lamura da dama babu ruwanshi dasu.



Suna gab da iske juna yayiwa dogarawanshi inkiya,tuni suka bace daga farfajiyar,kowanne yasamu saqo da kunnuwanshi bazasu jiyi tattaunawar abdul'azeez da 'yan uwan nashi ba yatsaya qyam yana jiran umarni

"Barka da warhaka hamma yarima"airah ta fada cikin girmamawa yayin da walida ke qoqarin wuceshi tamkar ma bata ganshi ba ko bata sanshi ba,duk da yadda zuciyarta ke tsalle saboda tsaro dakuma kwarjinin abdul'azeez daya cika wajen.



Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata data sanyata tsaiwa cak,take cikinta yajuya fuskarta tasoma hada gumi,amma sai tayi yunqurin saita kanta sanda kalaman mahaifiyarta yafado mata

"Karki sake karki kuskura kici gaba da bashi wata qofa da xaisa ya rainaki,kin bashi kwanaki kusan dari a duniya kafin isowarshi,karki yadda kwarjininsa ya firgitaki koda kinji razani a ranki.....haka halittarsa take,amma dole mukoyi fada da wannan kwarjinin nasa....wanda nake da yaqinin annamimiyar mahaifiyarsa ce ta nema masa....".



Taku uku yayi zuwa gabanta yana duban shigarta sama da qasa,shigace da sam bai dace ace tana ratso cikin gidan da ita ba,gidan dake da tarin hadimai maza da mata,ya mata jan kunne kusan kashi uku akan hakan amma bata sauya zani ba,saboda daurin gindi data samu daga wajen mahaifiyarta.



Dauke kai yayi kana ya gotata kadan kamar zai shige,idanunsa kan airah da take cikin yalwatacciyar doguwar riga da wadataccen mayafi,sam mahaifiyarta bata barinta tayi qazamar shiga tun tana qanqanuwarta

"Saunawa naja miki kunne kan dressing dinki cikin gidan nan?" Cikin tsananin jarumta ba tare data iya juyowa ba sun hada idanu tace

"Gaskiya abdul'azeez kafita daga sabgata.....idan ka manta bari na tuna maka,nidin yayarka ce,gaba nake dakai" tana kaiwa tasauke boyayyar ajiyar zuciya,wani qaramin miskilin murmushi yasaki,yamiqa hannu yariqo airah kana yadawo gabanta yatsaya yana duban qwayar idanunta

"Ko kadan baki taba wani abu dazai nuna cewa gaba kike dani ba,beside ma ayanzun koda bakiso nine gaba dake.....shigar qanwarki bata isheki misali ba?" Saiya daga yatsanshi yanunata dashi

"Wannan shine karo na qarshe dazan sake jan kunnenki game da wannan....ki kiyaye" saiya saki hannun airah yasoma tattaki zuwa gaba,kana ya basu alamar ya kammala da abinda yake,cikin sakanni suka bayyana sukaci gaba dayi masa tattaki har zuwa fadar.



ƙawatacciyar fada ce mai girma da yalwa,wadda tana jerin ɗaya daga cikin fadodi na alfarma cikin jerin fadar da sarki mu'az yake da ita,komai na cikin fadar kama daga shimfidu na alfarma zuwa kujerun zama,adon zanen (dagi) dakuma dardumai dake jikin bangon dukka golden ne da ratsin silver gami da maroon wanda kusan yafi yawa.



     Hakimai da yawa sun isa gurin a sannan,harda shi kansa mai martaban,saboda haka yaratsa cikin nutsuwa ya isa gaban mahaifin nashi ya miqa gaisuwa kamar yadda kowa yakeyi sannan ya yiwa kanshi masauki daura da mai martaban.



     Sun shafe a qalla awanni biyu cur ana zaman fada kafin daga bisani mai martaban yasoma sauraron shari'u daga talakawansa,abdul'azeez yana zaune daga gefe yana kallon yadda mahaifinsa kebin komai daki daki cikin hikima,kana yayi hukunci bisa adalci,sosai abun yaburgeshi,saiyaji duk a zaman wannan yafi qayatar dashi,zaman yatashi aka rufeshi da addu'a,maimartaba yawuce zuwa sassansa bayan yasa an shaidawa abdul'azeez umarninsa na cewa yasameshi a sassansa.



    Su biyune rak cikin falon duk girmanshi,sai tarin kayan abinci da kayan marmari da aka ajiye musu

"Matso abdul'azeez" cewar mai martaba yana duban abdul'azeez din cikin tsantsar qauna da kulawa.



      Sau tari abdul'azeez din kanyi mamakin yadda mahaifin nasa ke sakewa dashi sosai,sukanyi hira cikin yanayin da dazaka ganshi kai bakace shine MAIMARTABA SARKIN KAISA BA.



      A bayan fage mu'amala yake musu irin ta uba da 'ya'yansa,bama iya abdul'azeez din kadai ba,har duka sauran 'yan uwanshi ma.



     Cikin girmamawa yamatso,yasanya hannu kamar yadda shima maimartaban yasanya nashi hannun,duk da abdul'azeez don ba gwanin cin abinci da hannu bane,amma wannan karon abun saiya qawatar dashi.



      "Yaya makarantar?,da fatan komai yana tafiya yadda yakamata?" Ya jefa masa tambayar sanda suke tsaka dacin abincin,kaiya jinjina yana qoqarin hadiye abincin bakinsa

"Ina fatan babu wata damuwa?,don na qagu lokacin da zaka kammala karatun yayi kadawo cikin ahalinka" kai yakuma gyadawa kamar wani qadangare yana qoqarin boye abubuwan dake yawo saman fuskarshi,don yasani sarai maimartaban ba baya bane wajen iya karantar mutum shima tamkar amminsa

"Ma sha Allah,Allah ya taimaka"

"Amin Allah ya taimakeka" yabashi amsa a ladabce.



     Shuru yasake ratsawa kafin maimartaba yasake magana

"Ga 'yaruwarka nan....ta dage itama so take tafita koda egypt ne ta hada degree dinta" amamakance abdul'azeez yadaga kai yana duban maimartaba,sai akayi arashi shima shi yake kallo,hakan yasa yadan sauke idanunsa qasa yana ci gaba dakai abinci bakinsa,ko kusa ko alama baya yiwa 'yan uwanshi mata sha'awar barin qasarsu zuwa wata uwa duniya neman karatu har wata qasar,saboda su kadai sukasan me idanunsu suke ganemusu,yaran musulmi 'yan arewa hausa amma idan kagansu saika rantse da sarkin daya halicceka basusan wata kalma kota ZO IN KASHEKA da hausa ba,hakanan saika rantse basusan inane alqibla ba bare kayi musu tunanin musulunci,shi a karan kansa yatuna yawan 'yamnatan dake kara kaina da artabu a kanshi,duk da sautari kwarjininsa na taka musu burki,uwa uba bashi da fuska kamar yadda sauran samari keda ita,sakewa da sakin jiki da fuskawa duk wadda ta doshesu.



     "Abdul'azeez" kiran damai martaba yamasa yadawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi,saiya dago yana duban mai martaba,dakatar dacin abincin yayi shima kamar yadda yaga mai martaba ya dakatar

"Ka gayamin meye ra'ayinka kan hakan,don ban sake magana ba kan lamarin ba,ba jirayi dawowarka ne,saboda kaidin watan watarana kaine uba a wajensu,koda kuwa akwai wadanda suka girmeka a cikinsu".



     Cikin nutsuwa yabude baki yasoma magana

"Inda zai yiwu Allah ya qara maka lafiya....ni a nawa ra'ayin bana sha'awar daya cikinsu tafita wata qasar karatu....koda wacece kuwa a cikinsu.....,zaifi kyau dakuma kwanciyar hankali kowacce tayi karatu a qasarta....koda bazasuyi ba cikin qasar KAISA ba" daga haka yayi shuru yana jiran abinda maimartaba zaice.



     Kai yake jinjinawa,shi kansa wannan hukuncin shine hukunci mafi kwanciya cikin ranshi,sai yaji abdul'azeez din nasake samun wani matsayi na musamman a idanunshi,kamar yadda halayensa da dabi'unsa suka banbanta hakama tunaninsa,duk da qananun shekarunsa da basu haura ashirin da biyar ba

"Wannan tunanin naka yayimin abduk'azeez,Allah ya albarkaci rayuwarka kaida sauran 'yan uwanka"

"Amin ya Allah Allah ya taimakeka....godiya nake".



     Daga haka suka shiga tattaunawa kan wasu lamuran daban,wasu sun shafi masarauta ne kai tsaye,wasu kuma sun shafi al'amuran da suka dangancin sarki mu'az a karan kanshi.



      Saida lokacin sallah yayi sannan suka tashi,yafita yabar maimartaba yana shirye shiryen fitowa don halartar sallar azahar cikin jam'i a masallacin dake mallakin masarautar kamar yadda yasaba duk lokacin da yake qasar matuqar ba tafiya yayi ba,wanda hakan yasake tasiri qwarai a zukatan dukka jama'ar gidan dama sauran al'ummar dake wajen masarautar.



     Doka ce cikin gidan naduk wani bawa hadimi ko barori su saki dukkan aikin da suke da zarar lokacin sallah yayi suje suyi,wannan na daya daga cikin sirrika na daukakar masarautar,da samun wani irin kwarjini da haiba na musamman.



     Yana gab da isa masallacin saqo ya riskeshi na nemanshi da amminsa take,hakan yasanya suna kammala sallar yawuce sashen nata,duk da yaso yafita yadansha iska yaga garin sosai,don tunda yazo bai samu ya miqe qafa ba,sai yake jinsa duk a takure,sakamakon sabo da yayi da qasar daya fito,wanda take wadace da guraben hutawa dakuma shan iska.



      A falo na uku yau yayi burki,jakadiya ta isarwa da ammi saqon zuwan nashi,daidai lokacin tana zaune tana waya da babbar aminiyarta qwaya daya a duniya,wadda take iya raba sirrinta da matsalolinta da ita,kamar yadda itama take raba nata matsalolin da ammin,saboda tsabar shaquwa dakuma dadewa da sukayi tare tun zuwan ammi qasar nijeria,saita yanke kiran tana bawa surayya uzurin zata kirata.



     Kamar koda yaushe,cikin shiga ta alfarma dake nuna izza da mulkinta ta tako zuwa falon

"Barka da warhaka ammi" ya furta yana duban yanayin fuskarta,bata amsashi ba har sai data zauna kana ta amsa masa,tare da jefa masa tambaya

"Meya faru tsakaninka da safwa?"

"Takawo qarata kenan as usual?" Ya tambayi kanshi da kansa can qasan zuciyarsa ba tare daya furtawa ammin ba

"Babu komai....takawo qarata ne?" Da idanu ta kafeshi nawasu sakkani sannan ta amsa mishi

"Tabbacin baka da gaskiya kenan,ka gayamin meya faru tsakaninku?.....ta shaidawa jakadiya kadaina daga wayarta tun sanda kadawo,hakan na nufin kasoma daukar mataki na bijiremin?" Kai yakada,sam shibai kawo hakan a matsayin wani abu ba,saidai tuncan mutum ne shi da baison takura ba,bare shidin dabai dauki soyayya abakin komai ba bare tadameshi,hasalima yayiwa kanshi alqawarin bazai taba soyayyar ba,hakan yasanya yabaiwa ammin tashi hadin kai dari bisa dari lokacin data zaba masa safwa a matsayin matar da takeso ya aura aduk sanda lokacin auren yatashi.



    Ya auna safwa kan mizanai saiyaga tacika kaso saba'in cikin dari,hakan yasanya yaga bashi da wata matsala da hakan,zai iya karbarta.



        Safwa diya ce ga wani hamshaqin dan kasuwa ibrahim khalilu attah da yayi suna yayi shuhura hakanan yayi fice a garin kaisa kano jigawa dama sauran garuruwan dake arewa harma da kudancin nigeria,dan kasuwa ne na gasken gaske wanda ya mallaki kadarori masu tarin yawa ciki harda rijiyoyin man fetur,safwa ita daya Allah yabasu,hakan yasanya tasamu gata na gaban misali,hakanan tatashi cikin wadata ba tare da tasan wata kalma da talauci ko babu ba,shagwabbiya ce wajen iyayenta,suna matuqar ji da ita dakuma lelenta,hakanan suna gudun duk abinda zai bata ranta,safwa nada kyau dai dai nata,fara ce qal wanda hakan yasake qarawa halittarta ado,bata dawani kauri ko kadan,don haka bakayi kuskure ba idan ka kirata da siririya.



       Shekararta ashirin da uku,duka duka shekara biyu kacal abdul'azeez yabata,saidai yanayin kwarjini haiba da cikar saiffa yasa zakayi tsammani yabata shekara kusan goma ne.



       Tana masifar son abdul'azeez,don kusanma tafishi farinciki da hadin da akayi musu,duk da cewa tana qoqarin nuna darajarta ta mace,tana danne soyayyar da take masan,abdul'azeez yacika duk wani buri nata kan aure,hakan yasanya tariqeshi da dukkan iyawarta da dabarunta na diya mace.



       Balaifi,tayi tasiri a zuciyar abdul'azeez din,duk da miskilancinsa kan hanashi maida mata martani yadda yakamata,ita kuma hakan yana masifar takurata,soyayya takeso suyi tuquru bawai ta lalacewa ba,aah soyayya irinta turawa wanda ako ina basa iya boye abinda ke zuciyarsu.


       

       Mahaifiyarta na daya daga cikin jerin gwanon qawayen fulani aisha da tasu tazo daya,cikin burikanta na ganin ta gina rayuwar abdul'azeez din da ingantattun dirkoki tako wanne bangare yasa taga babu diyar data dace da abdul'azeez din sai safwa,tana yiwa mahaifiyarta tayi kuwa babu jinkiri ta amince da hakan.



      Akwai banbancin halaye da dabi'u masu yawa tsakaninsa da safwa,saidai dukkaninsu basu daukesu a wani abu can dazai kawowa relationship dinsu cikas ba.



"Abdul'azeez dakai nake fa?" Ammi tasake tambayarsa bayan wasu mintuna dayin shurunsa,dazai iya,dakuma zai yiwu daya gaya mata mawuyacin halin da yake shiga aduk sanda zaiyi doguwar hira da safwa,wanda wannan shine babban dalilinsa na qaurace mata

"Akwai dalili ammi,amma banyi saboda wata manufa data sabawa tsarinki ba...."

"To banaso,ban kuma son naji wani abu mai kama da matsala tsakaninka da ita"

"Ayimin afuwa,in sha Allahu za'a gyara" ajiyar zuciya tasaki,yana daya daga cikin abinda yasa take qaunar abdul'azeez,bai taba tsallakewa umarninta,idan ta nuna tanason abu yakan fita sonshi,baya yarda koya bari wani abu ya bata ranta akanshi

"Allah ya albarkaci rayuwarka,ya baka zuriya ingantacciya wadda zata bika fiye da yadda kake mana"

"Amin ammi,na gode"



     Ganin lokaci yadan ja yasanya ya haqure da fitar,yabarshi idan sufyan ya iso sa fita tare,sai yazarce sassansa don ya kwanta yahuta kafin sufyan din ya iso.

7/11/21, 4:30 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAD'IN RAYUWATA*👑



*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar siya kema,ki tuntubi wadan nan lambobin donki siya ki karanta cikin aminci_*



0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070


10




      A nutse take karantar hauwa'u yadda tazauna tana dinke rigar dataketa saurin tasaka da zare da allura don kada ta makara makarantar Allo yaaya maigado tayi mata fada.



      Karo na wajen hudu dinkin yaqi yiwuwa tasaki rigar kamar zata sanya kuka,tausayin yarinyar yakamata,kusan dukka suturunsu akode suke hakanan a dangale suke ma'ana sun musu kadan,hatta da ita bata tsira ba,saidai dama dama itan,saboda tana da dabarar tattala kayan dakuma ware na fita dana zama a gida,bugu da qari kuma kayanta masu tsada ne wanda su take sawa a zamanin da anty zuhriyya na rayuwa kusa da ita,hakan shiya sauqaqa musu tasu kodewar.



      Sai a sannan ta tuna da kayan da umma luba tabata,koda bata sonsu dole tabasu su suyi amfani dasu tunda suna da buqatar hakan,kuma babu wata hanya data wuce tabasun,saboda haka ta sauke ajiyar zuciya,ta laluba inda tasakaya qullin wanda ba wanda ya taba taba kayan cikin yaran bare ya tambayeta meye a ciki,haka suke da wannan ladabin

"Kinga hauwa kulun majadan,ajjiye wannan kayan naduba miki wasu ki saka" ta qarashw maganar tana ware qullin,cikin zumudi hauwa ta aje kayan ta isa gaban qullin tana ware idanu akan kayan cikin murna

,bakin yarinyar ya kasa rufuwa,saidai batace komai ba tana dai kallon kayan har bilkisu tagama duba mata wadanda zasuyi mata dai dai tamiqa mata

"Saka mu gani" dasauri ta amsa tamiqe tasoma zurawa bilkisu na kallonta harta gama

"Ba shakka sutura itace mutum" bilkisu tafurta a zuciyarta,kayan sai suka haska yarinyar tasake wani kyau,ita kanta yarinyar kallon kanta da kanta take farinciki fal ranta,sai juyawa take tana dudduba jikinta

"Yaaya....gaskiya kayan nan sunyi kyau,kinga yaaaya sunmin kyau ko?"

"Sosai kuwa hauwata" sai kuma ta dakata da murnar da take ta dubi bilkisu

"Yaaya,dama ajjiyewa mukayi saida sallah ko?" Tausayinta yasake kama yarinyar,kusan su biyune ita da ita basu samun damar sanya sabbin suttura da salla,saboda daga ita har ita sun rasa dangin mahaifiya da zasu nuna musu kulawa,har gwara sauran akan kawomusu daga dangin mahaifansu koda 'yar leda ce,aqalla kala daya ko biyu,ga zatonsu qarine kawai,mahaifinsu na musu,abinda basu saniba shine,ya manta rabon daya siya fallen atamfa wa yaransa,amma yakan iya hadawa bazawara lefe akai yabiya sadaki ya aurota yakawota gidansa.



      Saita soma daure kayan tana bata amsa

"Saka abinki,kita addu'a da salla nayi miki ko guda daya ne kinji?" Fuskar yarinyar ta washe ta nuna zallar farincikinta

"Aikuwa kullum ina miki yaaya,amma zan sake dagewa"

"Yauwa kuluta" cikin farinciki da walwala tatafi makarantar allon tana cewa yau duk makarantar babu mai irin kayanta.



       Sai data gama duk abinda zatayi sannan tazauna,umma luba bata nan,ta gaya mata zatayi kwana biyu a gidan aikinta,asabar da lahadi,to itadinma yau yazama ranar hutu a wajenta,babu makarantar boko babu zuwa wajen aiki,saboda haka tayi kwanciyarta cikin daki tadauko litattafanta na makarantar dare tasoma bibiya.



       Bata fita ba saida fitsari ya matsota sannan ta aje littafin tamiqe tazura hijabinta kafin tafitasaboda tasan koda yaushe ba'a rasa mutane cikin gidan nasu.



      Tana fita hasken fentin da ake shafawa ginin da aka kammala daga gefe guda na tsakar gidan nasu ya haske tsakar gidan tarwai,baka ganin komai sai qyallinsa da qamshinsa,idan aka dauka maka hoto na sashensu da sashen da ginin yake saika rantse da ubangijinka cewa gida biyu ne bawai dukka ginin suna qarqashin gida guda bane.



      Duk yadda taso dauke kai kamar yadda tasaba amma sai data maida idanunta ga mahaifinta daketa faman fara'a yana hira da masu fentin,tunda aka soma aikin ginin ya sallamawa fita ya tare gindin ginin,ya zazzage duka kudadenshi da yake boyo da mammaqo akan ginin,ya saba wannan ba farau bane kanshi,kusan duk sanda zaiyo sabon aure hakance take kasancewa,saidai wannan karon kamar abun na daban ne,da alama ita wannan din tafi duka sauran nabaya da aka auro wayewa.



      Saita tuna awa guda baya data wuce yadda akayita tababa dashi kan yabada kudin sukari azuba akunu yara susha,har yake kumfar bakin bashi dako asi,yana ganinma yayi qoqari da ayau xai ciyar dasu abincin safe rana harma dana dare

"Nifa matsalata dake kenan katti,baki da godiyar Allah ko kadan,duk fadi tashin da mutum yake akanku da zarar yace zai raya sunnar ma'aiki saiki tattaro dukka bala'in duniya da tsangwama ki aza masa,ina laifina ma da aka samu qwayar hatsin da za'aci din?" Hannu ta tafa baqinciki na ciciyar ranta,ta rasa me yasa wannan karon auren nashi yafi ci mata rai fiye dako yaushe,kodon yadda yaketa rawar qafa ne oho

"Tsakanin ni dakai ai za'a gane wanda bashi da godiyar Allah,kai har kana da bakin magana ma?,ai wallahi idan dakunya a idanunka malam baka data cewa" saiya miqe yana karkade rigarsa yana cewa

"Saikiyitayi ai,idan kunso karkusha kunun ku zubar" yasanya kai yafice abinsa,bayan tana ganin sanda ya aika umaima tasiyo masa nashi sukarin na talatin yajuye dukka cikin kunun yashanye abinsa.



      A sanyaye taci gaba da takawa zuwa rubabben bandakin nasu dayake matuqar buqatar gyara amma yakasa sanya masa koda kwano daya na sumunti ayi masa kwaskwarina,gashi yayi gini sukutum da guda,a maimakon ayi musu kara ahada da bandakin a gyara amma sam su basu da wannan darajar,umma katti kuma tun kafin sannan ta rantse ta maya silai biyar ba zata sanya ta gyara bandakin ba,qatti suda ubansu suzo su dinga tsugunawa,kowa ya karba a haka.



      Koda tafito dakin nasu tasake komawa ta kwanta,tajawo littafin da niyyar ci gaba da karatu saidai wannan karon karatun ya gagara,tilas ta ture littafin gefe,ta gyara kwanciyarta sosai,saita fada cikin duniyar tunani,wanda duka tana tunanin makomar rayuwarsu ne ita da sauran 'yan uwanta.



     Hakanan taci gaba da kwanciya har suka dawo sukaci abincin rana suka wuce islamiyya,wanda wani malamine cikin layin nasu yadaukesu kyauta fisabilillahi,gidan yau tamkar sallah yake a wajensu,saboda yadda akaci aka qoshi abinda suka jima basu samu ba.



     Bayan sallar la'asar yaro yayi sallama 

"Wai ana sallama da bilkisu" kalmar tashiga kunnenta,duk da tana kwance sai data miqe tazauna sosai tana kasa kunnenta dakyau waiko bataji dadi dai bane

"Kai....kace tana zuwa" caraf mahaifinta ya bada amsa ba tare daya damu da tambaya ko bin diddigin wanda yake sallamar da ita ba.



      Ba'a rufe cikakken minti daya ba ta tsinci muryarshi yana qwala mata kira

"Me gado!,ke me gado!!" Ba shiri ta yayibi hijabinta dake aje gefanta ta yafa tafito.



      Saman jarka tasameshi zaune riqe da kwandon wanka,da alamu ma wankan yake da shirin shiga amma yafasa

"Maza jeki waje ana sallama dake....kya sama mana ma abun cefanen gobe,don gaskiya aljihuna ya gaza,mawuyacine asamun na tuwon gobe,gashi tattali nake kafin zuwan amarya,kada tazo ya zamana babu komai a hannuna" kamar an dasata a wajen haka tayi shuru tana juya maganarsa,shi abinda ma yadameshi kenan?,ba damuwarsu bace tashi damuwar,abinda yadameshi daban,nashi tunanin daban?,bata taba tunanin ya taba kwana da matsalarsu da har zai tashi da ita ya sanyata cikin jeri da lissafin matsalolinsa

"Tashi mana ki wuce kije a'ah,kijimin yarinya anata maganar kamar kurma" maganarshi ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka takoma bakin qofar dakin nasu tadauki takalmanta tadurfafi qofar gidan tana tunanin waye wannan haka?.



     Tunda ya hangi tahowarta ya zuba mata idanu yana dubanta,saiya tuna ranar farko da yaji matasan layin nasu suna wassafa halittarta da tsarinta,tashin farko yaji wani susa cikin ranshi,yayi hanzarin dauke idanu lokacin da take gab da isowa inda yake.



      Idanunsa yalumshe lokacin da tayi masa sallama,ba shakka muryar ta dace da mamallakiyarta yafurta a zuciyarsa kana ya amsa mata yana daidaita nutsuwarta,kallo daya tayi masa ta sadda kanta qasa bayan ta furta masa kalmar

"Ina yini" saboda yadda taga kamalarsa ta banbanta data sauran wadanda take gani,hakanan bata sanshi ba,bata taba ganinsa ba,bata kuma san me yake nema a wajenta ba,da fari ta tsammaci hamxa ne yadawo daga tafiyar da ya aiko mata da saqon zaiyi,amma ga mamakinta sai taga sabanin hakan.



       "Malama bilkisu,ina fatan ban miki dirar mikiya ba....,ina neman afuwar zuwana ta wannan siga,duk daba haka naso ba,naso na fara neman izini daga wajen baba kafin nakai zuwa gareki,sai zuciyata ta kasa haqurin hakan,karna cikaki da surutu da yawa,da farko dai ni sunana abubakar saddiq,haifaffen garin nan mazaunin unguwar daaba,wani uzurine yakawoni nan unguwar taku cikin layinku naganki,kuma lokaci daya naji kinyimin...dalili kenan dayasa na kasa nutsuwa harsai danasan wacece ke" kalmarshi ta qarshe ya sanyata daga fararen idanunta takalleshi dasu,bata fahinta ba,don kawai yana sonta saiya samu lasisin bin diddigin rayuwarta?,akanme?,bayan ita batasan da wanzuwarshi doron qasa ba?,ita batasan meke birgesu dangane da ita ba,bataga abu ko guda daya ba,amma su sun damu cukurkudaddiyar rayuwarta,amaimakon sun qyaleta da aikin warware rayuwartata tamiqe kamar takowanne mutum,saisu sake aza mata wani nauyi na daban da take kallonshi a amtsayin abinda xai sake tauyeta.



     Saman fuskarta ya karanci kaman ta amshi xancan nashi abaibai,saboda haka yasake mata qarin bayani

"Sai dana binciko gidanku dakuma lokuttan dazan sameki,ina fata zaki karbeni hannu bibbiyu kamar yadda zuciyata tashin farko ta amsheki" nannuyar ajiyar zuciya tasauke kai kace tseren gudu tagama,ita duka bata fahimci ma me yake nema ba,amma a iya qaramar fahimtarta kamar yanason yace mata soyayyarta yake nema?.



       Yakamata zuwa yanzu bakinta yasoma buduwa,tadinga bude baki tana bayani wa duk wanda yazo da quduri makamancin wannan a kanta,cikin lallausan muryarta da tayi kama da wanda yajima shuru ba tare da yayi magana ba tace

"Ni bana soyayya,kayi haquri don Allah" ga mamakinta murmushi saki lokacin da take yunqurin komawa cikin gida

"Dan tsaya mana malama bilkisu" saita tsaya cak ba tare data waiwayo ba,yasake dawowa bangaren da zata iya ganin fuskarsa sosai yace

"Ni ba sauri nake ba,kuma ba gaggawa nake ba,inason ki bani dama mu fahimci juna na wani lokaci tukunna kafin ki yanke hukunci,zuwa lokaci na yadda dukka hukuncin da zaki yanke din daga zuciyarki yafito,ba kamar wanda kika yanke yanzun  ba" tana qoqarin sake wuceshi yafidda kudi daga aljihunsa yamiqa mata

"Ga wannan ki karba don Allah" duban kudin tayi sannan ta dubeshi,duk wanda zai mata kyautar kudi a yanzu gani take kamar ya raina inda tafito ne,abinda yaduba kenan yadauki kudi yabata,saboda haka kamar yadda tasaba saita girgiza kai tayi shigewarta cikin gidan da hanzarinta.



*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar siya kema,ki tuntubi wadan nan lambobin donki siya ki karanta cikin aminci_*



0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



      "Kai amma bansan kana haifar yaro dan baqincikinka ba sai yau,yanzu ke don tsohuwarki ina da buqatar kudin nan yaron nan yabaki kudi kiwuceshi kamar yabaki kashi?,to tun ranki bai baci ba ki koma ki karbo kafin yayi zuciya yawuce da abinsa" muryar mahaifinta kenan data mata dirar mikiya lokacin data fado tsakar gidansu,mamaki yasata tsaiwa kamar an dasata,kenan yana labe yana kallo da sauraren dukka abinda ke faruwa?

"Ba zaki koma ba!" Yafada cikin kurari da hargagi kamar mai shirin bugunta,hakan ya bata tsoro daya sanya ta juya a sukwane tana tsara yadda zata kubcewa qudirinsa,sai sukayi karo da yaro hannunshi riqe da kudin

"Wai gashi a baiwa bilkisu inji saddiq,wai yatafi" kafin yaron yadire sauran kalaman bakinsa tuni malam bilya yayi caraf da kudin cikin hannunsa yana cewa

"Yaro jeka,kaima Allah yayima albarka,da ina da naira biyar dana baka" yayi maganar yana irga kudin,sum sum ta gotashi tawuce daki,bata iya tsaiwa baqinciki da takaici fal ranta,tana baqinciki da takaicin halayen mahaifinta,yana girmama kudi fiye da komai,shin yaya rayuwar qannenta zata tashi nan gaba?,wannan dalili yasa ta maida hankali qwarai wajen cusa musu kyakkyawar tarbiyyar da take da yaqinin zata kama gangar jiki da ruhinsu matuqa.



       "Kai kai,kan uban nan,kyautar naira dubu biyar cas lokaci guda?,ah....lallai mai gado hasashena na cewa zaki zama mabudin arziqina yazama gaskiya,ina kika samo wannan yaron?" Ita baki daya kunya yake bata baya ga mamaki,saita gaza amsa masa sanda yaje matsowa bakin qofar dakin yana jiran amsarta,wanda muryar umma katti data fito daga daki dauke da kwanuka ta gasa masa harara takuma ce

"Andaiji butur wallahi,anan kafi kauri,ka gama daijin kunya" kusan tunda sabon ginin dake cikin gidan ya kammalu duk wani kuzari nata da karsashinta ya ragu,bacin ranta yadadu

"Ke wa yake ta tataki,aike yanzu allurar kishi ce take damunki,kuma haka zata gama motsa mikin ki kuma haqura" saiya bar wajen ya dauki botikinsa daya cika da ruwan wanka yanufi bandaki yana sake bude sabon babin mita da manufa biyu,yasan taji nawa yasamu,kada tasamu fuskar tambayarshi wani abun

"Ruwan wanka ma a matsayinka na miji an mance rabon da akai maka bare na alwala,Allah dai ya sawwaqa,wannan ba dole ka nemo mai maka ba" maganar data tunzura zuciyar umma kattin kenan tahau sababin bala'i itama,itadai bilkisun tana jinsu,tun maganar tata bata cika mata kunne ba harta dameta,saboda haka tamiqe tahau rakito ayyukan da ada babu su cikin dakin,sam sai taji ashe fitar da take aiki ko makaranta rahama ne,da batasan yaya zaman gidan xai kaya mata ba.



      Sai yamma lis su hannatu suka dawo daga islamiyya,tana zaune suka shigo,saita lura fuskar hannatun ita da hauwa'u fal take da bacin rai,da kallo tabisu kana daga bisani tace

"Lafiya?,hauwa'u me yafaru?" Cikin fushi hannatun tamiqawa bilkisu wata 'yar guntuwar takarda,saida bilkisun ta karba ta duba,sai taga sunan wani littafi ne na koyon larabci ajiki

"Meya faru?" Muryarta na nuna zallar bacin ranta tace

"Tun rannan malamin ajinmu yake mana bulala saboda bamu dashi,bamu nuna miki ba saboda baki da kudi yaaya,sai yau muka nunawa baaba koxai siya mana,waisai yace mutafi mubashi waje bashi dakudi,ko mukai miki ke zaki siya mana,wai baaba komai mukace yasiya mana sai yace bashi da kudi yaaya?" Kafin takai ga saisaita tambayar yarinyar akanta hauwa'u ta jeho mata wadda tafita nauyi

"Wai baaba bashine ya haifemu ba?" Sai tambayar hauwa'un tafi jan hankalinta akan ta hannatu,duk da qarancin shekarunsu hakan yana nuna halin ko inkula dayin biris dasu da yakeyi yana ci musu rai kenan?,kuma suna sane da komai,bata fuska bilkisun tayi tana duban hauwa'u,alamun maganar bata mata dadi ba,tuni yarinyar ta karance ta,don haka tadora

"Kiyi haquri yaaya,baaba baya mana irin abinda abbansu nawal da abbansu amira yake musu,su komai sukace sunaso abbansu yanayi musu amma banda mu".



     Ajiyar zuciya tasauke tadubi hannatu dake tsaye

"Zauna" tace mata,saita zauna din,yanayin fuskarta yasanya yaran duka suka nutsu,tasoma magana cikin sigar lallami da kwantar da murya

"Baaba yana sonku kuma shiya haifemu gaba daya,abinda yasa kukaga baya mana komai saboda bashi dashi ne,kafin ahaifeku baba yana mana komai,yanzune bashi da kudi,kunga kuma dole muji tausayinsa ko?,duk sanda kukayi sallah kudinga masa addu'a,Allah yabashi kudi,Allah yasa yadinga muku abinda kukeso,amma daga yau banason in sake jin hira mai kama da wannan,idan nasamu kudi nan da kwana goma zan siya muku littafin,kuyi haquri kunji?" Duk suka gyada kansu,saidai da alama bayanin data musun bai gama ratsa su ba,don haka ta bagarar da zancan ta hanyar cewa

"Kowa yaje yayi alwalar sallah magariba,yau muna gama cin abincin dare zan muku tarihin sahabbai" sai kuma duka suka warware cikin murna da farinciki,don suna son tarihi sosai,tasaki murmushi sanda suke fita,saita sauke idanunta kan kwanon abincinsu da yake tazarce wanda duka umma katti ta gwamutsasu ta hado musu na dare da rana,ba tare da la'akari da zai ishesu ba ko kuwa a'ah.



______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃ðŸ»Ã°Å¸’ƒðŸ».


        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauÆ™i😻😻😄🤗.


______________________

7/11/21, 4:30 PM - My Mtn Number: *S R B*


*_wannan littafin na kudine,kuma amana ne a hannun duk wadda tasiya,gamai buqatar mallakar nata na qashin kanta ta tuntubemu ta wadan nan lambobin_*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




12




       Da sallama mustapha yashiga dakin,saidai abdul'azeez din bai samu amsawa ba,yana zaune gaban gadonshi gefan drower ya zazzage magunguna daga kwalayensu yana balla daya bayan daya.



      Idanun mustapha a kanshi harya qarasa gaban gadon yatsaya akanshi hannayenshi harde a qirji yana duban abdul'azeez din harya jefa magungunan yakora da ruwa,duk da yaga tsaiwar mustapha amma baice mishi komai ba,saiya soma ma qoqarin rage jibgegiyar rigar sanyin dake jikinsa saboda gumin dake yanko mishi,yazareta ya wurgar gefe,ya fidda takalmin qafarsa saura safa kana yakoma saman gadon yamiqe sosai rigingine.



       Sai a sannan mustapha ya magantu

"Azeez....sai naga kamar baka kyauta ba da korar kamal da kayi daga gidan nan,ko bsbu komai jininka ne fa" idanu abdul'azeez kawai ya zubawa mustapha tsayin wani lokaci yana dubanshi,kamar bazaice komai ba kana ya motsa bakinsa

"Shine hukuncin da yafi dacewa dashi,bazan zauna a banza ina yaqi da kaina da qoqarin kare mutuncina ba suna son maida min hannun agogo ba" ya qarashe maganar yana maida numfashi,shi daya yasan me yake ji cikin gangar jikinsa,maganinma sam kamar baya mishi aiki zuwa yanzu haka yakeji

"Gaskiya ka fada,amma haka zakayi haquri tunda kai kanka kasani mai martaba ne da kansa yahadaku zama tare...."

"Koshi da zaiji meke faruwa sai ran kowa yabaci ciki harda ni danaqi qaya masa"

"Duk da haka,tafiyarsa fa kaman yasake samun dama ne tayin duka yadda yaso babu mai cewa bari....."

"We will talk later pls musty" ya fada yana tashi da hanzari,yajawo locker dake kusa dashi din dai again yaciro ruwan allura da syring,daidai lokacin da mustapha ke duba kwalayen magungunan daya gama sha yanzu bai samu maidawa ba.



       Da wani irin zafin nama ya warce syring din daya cika da ruwan allurar da nufin yiwa kansa cikin hargagi yana fadin

"Baka da hankali ne azeez?,ka haukace?!" Kai yake girgizawa mustapha

"Kar kace zaka hanani pls"baibi takanshi ba ya tsiyaye ruwan alluran saman carfet din dake gaban gadon cikin bacin rai,kana yakoma kusa dashi yazauna yana tattare magungunan waje daya

"Azeez,kanason ka nakasta kanka ka yiwa kanka illa haka kawai?,kasan illar wadanda tablet din da injection din daka soma yiwa kanka?,hakan fa na nufin tablet din sun daina aiki a jikinka sabida yawan yadda kakesha saidai allura?,kanason ka wayi gari duk sanda kayi aure yazamana baka da wani desire irin ta da namiji saboda already ka kashe taka da qwayoyin kasheta?" Da idanunsa da suka sauya launi yake duban mustapha

"Bani da wani zabi daya wuce wannan....indai ba halaka kukeso na fada ba" daga haka yasauka daga saman gadon cikin rashin qarfin jiki yawuce toilet.



      Ko kayan jikinsa bai cire ba ya sakarwa kansa shower,sanyin ruwan yadinga ratsashi tun daga tsakar kanshi har tafin qafarsa,tun shekarun baya da suka shude tun baisan meye ba lamarin yake damunsa,ya rasa wacce irin halitta gareshi,yana da yaqinin aure shine kadai hanya daya ta maganin matsalarsa,saidai ya rasa dukkan wannan damar saboda ammi taqi fahimtarsa,azumin litinin da alhamis baya wuceshi amma wani lokaci kamar ma bayayi,rashin mafita ya sanyashi tilas rungumar magungunan kashe sha'awa badon yana so ba saidon babu yadda zaiyi,ko sau daya istimna'i ko romance da mace ko duk wasu hanyoyi da wasu matasa ke amfani dasu don ragewa kai zafi basu tab burgeshi ba,bare uwa uba zina,abar da yafi qyamata kaf rayuwarshi ita da shaye shaye.



     Yajima kafin yayi wanka gaba daya duk da sanyin da ake a qasar kana yafito,sanda yadawo dakin mustapha ya riga daya fita,saidai ya tattare dukka magungunan yafice dasu harda na locker dinsa,sai yasa qafarsa yatura locker takoma ciki,ya isa ka makunni yakunna room heater yaqure zafinta donta dumama mishi dakin dakyau,ya qarasa bakin qofa ya murza ke yarufe dakin kana yadawo yashurya cikin wasu kaya masu laushi da kauri.



      Rub da ciki yadawo yayi saman gadon nashi yana lumshe ido yanajin yadda dumi ke ratsashi,duka ranshi a jagule yake har yanzu babu dadi,takaicin zuwanshi club din da jamil yajashi hakanab ba gaira ba dalili har yanzu yaqi barin zuciyarshi,kawai yana wasafa rashin mutuncin da zaiwa jamil dinne shima.



             *NIGERIA*




       Daidai lokacin da safwa ibrahim attah ke zaune cikin dakin hutawarta ita da qawarta islam,zaune take saman wata qawatacciyar kujera doguwa mai azabar taushi,irinta qwaya daya tak duk cikin dakin,sanye take da dogon wando silk ruwan qwaiduwar qwai,sai wata riga sakakkiya wadda bata kamata ba sam,sphaghetti hand ce mai wani madauri daga gabanta peach colour,kanta dake da santsi da tsaho na fake tsakiyar kanta,tamiqe dukka qafafunta saman kujerar daga gefanta dan madaidaicin table ne dake dauke da lemo mai sanyi da wasu qananun kofuna na alfarma,sai dan qaramin plate da aka dora gasashshiyar kaza mai romo 'yar kadan,da alama ta kwadayi ce kawai.



        Islam na gefanta saman wani kafet mai azabar laushi,tayi rub da ciki da system a gabanta tana kallon wani series na koria.



       Tsadajjiyar wayarta ce a hannunta tana laluban number yarima abdul'azeez,tana zuwan kan sunan data sanya masa wato Sweetberry ta lumshe idanunta tana fatan yau taci sa'ar samunsa,tabude idanun nata sannan ta dannan kiran.



       Islam din na ankare da ita tun dazun data fuskanci shurunta yayi yawa,bata tanka ba sai yanzu

"Addu'ar neman nasarar daga wayar prince din ake?" Hannu ta dora mata saman lebanta alamun tayi shuru,batace komai ba tamaida kanta ga kallonta tana sauraren jiran jin abinda zai biyo baya.



       Idanunshi da suka soma nauyi yabude jin qarar wayarshi,banda yana tunanin kada ammi ce takirashi da babu abinda zai sashi kula wayar,a kasalance yajanyo wayar yana duba me kiran

"Sweetsafwa" sunanta ya bayyana saman wayarshi,sunan data sauya mishi da kanta bayan ta gama mita ranar dayaje gidansu ana ya gobe zai dawo bisa umarnin ammi.



      Maida wayar yayi wajenta bayan ya sanyata a silent don sam bazai iya dagawa ba,yasan tabbas idan yadaga zata karya duk wani budget nashine,abu na farko da zata soma masa wannan shagwabar tata da ba kasafai yake iya jureta ba.



     Baisan sau nawa takira ba,baisan me yaci gaba da faruwa ba sakamakon bacci da yayi awon gaba dashi.



       KyaÉ“e fuska tayi sosai wanda hakan ke nuna koda yaushe kuka zai iya suÉ“uce mata.



      "Please sweetberry,please ka daga mana" ta qarashe fada kuka na kubce mata,ganin harta masa irin kiran da baiso wato sama da sau biyu amma bai daga ba,sai islam kawai tasaki baki sororo tana kallon ikon Allah

"Safwa....ke kikema namiji kuka?" Ta tambayeta cike da mamaki,saboda itadin shaida ce kan irin dimbin mazan dakeson safwa din,banza safwan tayi mata sai data gana qwallarta sannan tamiqe tashige dan bandakin da aka tanada cikin dakin saboda buqatar gaggawa,fuskarta ta wanke sannan tafito tagogeta da qaramin towel,ta wurgar dashi kana tazauna kan wata kujerar daban sabanin wadda tatashi akai

"Kina mamaki islam?" Pause tasanyawa film din da take kalla kana tamiqe daga rub da cikin da tayi tazauna sosai ta gyada kai tana duban safwa din

"Karki mamaki,ana magana ne akan abdul'azeez abdallah mu'az,yariman garin kaisa,d'a daya tilo namiji ga mahaifinsa,ke kanki kin sani koda ban fada ba prince azeez ya cancanci kowacce irin soyayya tako ina hakanan takowanne fuska,inason azeez irin son da bansan iyakarsa ba,kuma shima yana sona,amma kullum yana sanyani inajin kamar alfarma yayiwa rayuwata yasoni,miskilancin azeez shine abu nafarko da yake hadani dashi,na rasa ta yadda zan canzashi" hannayen islam cikin najuna tana dubanta,hakanan tana fahimtar abinda take fada,tasani safwa tayi nisa a soyayyar yariman kome kuma zaka gaya mata babu lallai ita taga hakan kamar yadda kai kake gani a idanunka,duk abinda tafada kan abdul'azeez haka yake,amma bata da abinda zatace mata,don haka saita dage kafadunta tadan taɓe baki

"Hakanan zakici gaba da tolerating miskilancinsa tunda kina sonshi harki saba,mai yiwuwa nan gaba ya rage koya daina idan kuka zama mallakin junanku" kalmarta ta qarshe ta faranta ran safwa sosai,harta saki murmushi data kasa riqeshi

"Allah yasa qawata,harkin faranta min" murmushi itama islam din tayi tana komawa kwanciyarta,saita sake daukar wayarta ta tura mishi gajeran saqon kar takwana sannan ta lalubi number daya daga cikin cook na gidan donta kawo musu abincin rana ta kwashe na gabansu.



        ☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸




      Tun daga nesa ta hangeshi tasoma neman wajen buya,saidai ina tuni ta makara don kuwa ya hangota.



      Hamza ne fuskarsa fadade da fara'a,sabanin fuskar bilkisu da take a dinke kamar koda yaushe,wanda idan ba farin sani kayi mata ba da wuya kasan murmushinta.



      Duk yadda taso tawuce amma dole hakanan ta tsaya,don batason yabita har cikin layinsu bare yakai qofar gidansu

"Ranki ya dade,tun dazu kina raina,ashe kina kusa dani" tanajin nauyin mutumin daya girmeta ta tsallakewa gaidashi,don haka cikin sanyin muryarta tace

"Ina wuni"

"Lafiya qalau gimbiyata...da alama kamar bakiyi kewata ba ko?" Ya jefa mata tambayar,saita dan motsa kadan

"Sauri nake inason nawuce gida" sanya hannunshi yayi cikin aljihunsa yana cewa

"Babu damuwa,yaushe zan shigo mu gaisa,dazu nadawo daga tafiya,koma ki tambayeni?"

"Sannu ya hanya" tafada cike da nuna qaguwa,don dukka hankalinta ya karkata ga gida

"Alhmdlh" yafada yana miqa mata wani dan qaramin kwali dake cikin leda

"Ga tsarabarki,ki qarasa gida da ita,kina iya hadawa ki kunna kafin na shigo din" sai data dubi abinda yake miqo matan sannan ta girgixa kai

"Ka barshi,na gode" cikin hanzari tayi baya kadan sannan tawuceshi,saiya bita kawai da kallo,yana mamakin halayya da dabi'un bilkisun,komai nata daban yake,shi kansa sautari cikin jikinsa da zuciyarsa saiya dinga jin anya zaya samu bilkisu?,anya bilkisu tayi dai dai da tsararshi?,yakanyi saurin qaryata zuciyarsa da kwabar kanshi,yana ganin kamar maganganun wasu daga cikin abokansa dake maza hasashen yiwuwar rashin samun bilkisu suke son tasiri a ransa.



      Baibar wajen ba har sai daya daina hangota,saiya saki ajiyar zuciya yana juyawa don barin layin da niyyar randa zaije zai tafar mata da ita,don a ganinsa ya kamata zuwa yanzu ace tana riqe waya a hannunta,kodon yasamu damar jin muryarta koda baya nan.



      Saura kadan yaci karo da abokinsa dake tsaye bayanshi yana kallonshi,suna hada idanu yasaki murmushi mai kama da dariya

"Irin wannan kallo haka?,ko daukota kawai zakayi ku wuce?" Dariya hamza yayi yana dan dukan kafadar mudassir

"Mtsweew,bari kawai abokina,yarinyar tashigemin rai da yawa,fatana kawai shine nagama samun kanta,tana da dan wuyar sha'ani da rashin saurin sabo,har yanzu ta kasa sakin jikinta dani bare na fahimta komai" yana maganar ne lokacin da suka fara tattakawa tare shida mudassir

"Top class mace kenan,haka akeso ai,bawai kawai tashin farko ta sallama komai da komai ba,kamar wata haaja a kasuwa" hannu yabawa mudassir suka tafa

"Allah mutumina?"

"Allah kuwa,kaidai kaci gaba da jumuri" sake tafawa sukayi cikin dariya kana sukaci gaba da takawa tare suna ci gaba da tattaunawa kan bilkisun da irin halayenta daya fuskanta.



       Bayan sallama datayi a tsakar gidan nasu sai kuma tasoma binsa da kallon mamaki,kullum abun mamaki bai qarewa cikin gidan nasu,baqine dangin abbanta daga nijer,qannenshi biyu sai yayarsa da kuma qanwar mahaifiyarsa wadda take tamkar a maxaunin mahaifiyarsa tunda tajima da rasuwa.



      Ba zata iya tuna lokaci na qarshe da suka zo gidan dan uwan nasu ba da sunan ganin iyalinshi ba,koda yaushe idan ka gansu to baban nata ya tashi qara aure ne,abun yana daure mata kai,tamkar basu damuwa da rayuwarshi,kamar bashi da mafadi?,kamar basu bibiyar al'amuransa,haka siddan duk lokacin daya tashi qara aurenshi zai gayyatosu ne,su kuwa tinqis tinqis haka zasu taso su taho biki,batajin akwai wadda ta taba tuhumarshi ko tambayarsa labarin matarsa da sukazo biki wancan karon meye rabashi da ita?,amma abinda ta fuskanta shine,kamar yana riqa maqudan kudade ne yaje yamusu yayyafinsu.



        Jiki a mace ta jingina da bangon da yasha fentin farar qasa albarkacin zuwan amarya,wanda iya tsakar gidan akwai yayiwa,dakunansu kuwa ko oho,tazame tanemi gefan tabarmar da suke kai tazauna.



       Cikin nuna girmamawa tayi musu sannu da zuwa,saidai sam babu wani sabo ko sakin jiki a tsakaninsu,don hatta yaran sun sansu dai a idanu amma basu wani saba ba,don ba ganinsu din suke ba bare ace wani shaquwa ta shiga tsakaninsu,don haka itama tana gama gaidasun tamiqe,tana jin yadda suke yaba girmanta da kyanta,saita jefesu kawai da murmushin yaqe,harta shiga dakinsu bataji motsi ko taga gittawar umma katti ba,batasan cewa tana qule a daki ba,baqinciki da bacin rai kawai ke sakadarta,shi yasa tunda tabasu tabarma suka shimfida nan tsakar gidan bata sake bi ta kansu ba.



      Abun mamaki da daddare saiga kular abinci lafiyayya ana shela kowa yafito ya karba,tana zaune inda take bata ko motsa ba amma ta tura yaran su su karbo suzo suci su kwanta,har suka gama ci suka gama santinsu tana kallonsu bata motsa ba,sai data tsinto muryar mahaifinta yana qwala mata kira kana tamiqe a sanyaye tafita da faranti a hannunta.



      "Yarinyar nan bilya babu inda tabaro maimunatu,ai bilya kayi asarar mace,har yau baka maida kamar maimunatu ba"

"Hmmm,bari kawai binto,ai maimunatu diyar albarka ce,bansan dame zan saka mata ba,maiminatu 'yar aljanna ce na shaida hakan tun kafin ta rasu"itadai tana tsugunne mariya qanwarshi na zuba mata abincin batace komai ba har aka zuba matan tamiqe zuwa daki.



      A gaba tasaka kwanon abincin,tunanin mahaifiyartata ya bijiro mata,kewarta ta bijiro mata,zataso sake rabarta,zataso tasake jin duminta,ta jingina a jikinta ta gaya mata damuwarta,saidai tasan ina,mai rabawar ya riga daya raba,babu wani sauran abinda yarage sai haquri dangana da kuma binta da addu'a.



*****   ******    *****



      A nutse yake fitowa daga dakin nashi sanye da farar riga mai dogon hannu da rufaffen wuya,farace tas ta kama jikinsa duk da cewa tana da dan kauri,sai wandon jikinsa shima farine kamar rigar daya zarta gwiwa duk da cewa sanyi akeyi,fuskarsa tayi fresh babu wannan fushin ko digo daya shigo dashi dazun,saidai wannan daurewar da miskilancin na tattare dashi.



     Zuciyarsa ta rage nauyin datayi,saboda yasamu cikin baccinsa yayi mafarki wanda hakan ya qara mishi relief,kai tsaye falon yanufo hannunshi riqe da wayarshi yana neman layin safwa,don yasan halinta sarai,yanzu haka qilan tana nan a dame.



      Mutum biyune zaune a falon jabir da mustapha suna kallo,hada idanu sukayi da jabir saiya dauke idanunshi gamida mazewa,yayin da azeez ya jefeshi da wani kallo wansa shi jabir din yasan ma'anarsa sarai,kuma yasan laifinsa,dauke kansa azeez din yayi yanufi kitchen,a can yasamu abinci a cooler,yasan aikin mustapha ne,don kaf gidan shi kadai yake da juriyar dafa musu abinci suci,saidai yau an samu akasi sam baya sha'awar abinci kowanne iri ne,don haka ya hada coffe mai zafi yajuye a wani qawataccen qaramin flask wanda yafi kama da butar shayi,yadauki cups dinsa guda biyu bayan yazuba dambun nama daya taho dashi tun daga gida nijeria a wani dan qaramin plate sannan yafito zuwa falon.



      Yana shirin zama mustapha yace

"Kafito kenan" kaiya gyada mishi daidai lokacin da safwa tadaga wayar tashi,kamar kuwa yadda yazata hakance ta kasance,kukan shagwaba ta sake masa,shuru yayi idanunsa a lumshe yana saurarenta kana yana neman daukin Allah,sai daya barta ta rage qorafinta sannan yadakatar da ita cikin sanyin muryarsa fiye da yadda take ada saboda yanayin jikinsa da babu qwari kamar yadda yasaba jinsa,ko mustapha dake gefansa baijin me suke fada

"Don't stress your self sweetberry....duk tyn din da kiks kira kikaji banyi picking ba to ina da uzurine zan duba kiran kuma zan biyo ,i made it clear?"ya qarashe maganar da sigar tambaya,daga haka suka dan taba hira duk da batayi tsaho sosai ba,yace mata baijin dadine yau sosai,amma idan yasakeyin bacci yatashi zaiji fresh then zai kirata,yasauke wayar daga kunnensa yajawo kofin shayinsa yasoma shan a hankalin yana hadawa da dambun.



       Akaran kanshi shurun azeez din yasa yasake tsarguwa,cikin sigar jan hankali yakirashi

"Prince" shuru yamasa kamar baiji ba,bayan wasu mintuna yasake maimaita kira,sai azeez din ya aje kofin hannunsa ba tare daya dubi sashen da jabeer din yake ba yace

"Wannan shine lokaci na qarshe jabir,karka kuma maimaita abinda kayimin yau"

"What?....daga yin abu don na taimakeka?" Sai a sannan yadubeshi ya watsa mishi wani kallo kana yace

"To hell with your taimako,banaso kuma kar ka sakemin irin wannan" yasan qwarai ya fusata,yana qoqarin danne dariyarshi ya hada hannyenshi biyu waje daya yace

"Is ok,ba za'a qara ba,am so sorry" saiya janye idanunsa daga kanshi,kana yamiqe a nutse yasoma takawa ya isa gaban socket din kayan kallo zai cire charger din system dinshi,yanaso yayi amfani da ita cikin daki

"Amma yarima.....kamal fa,kayi haquri yadawo" sake waiwayowa yayi yadubeshi fuska a dinke

"Abokin cin mushe?" Kai ya girgixa dariyar nasake cinsa

"Nooo....tunda kamasa haka surely zai sauya"

"Ba yanzu ba" ya bashi amsa yana takawa zuwa dakinsa abinsa ba tare daya waiwayo ya dubeshi ba.



      "Prince taurin kai,prince kafiya,kai wannan mutum...." Jabeer yafada yana tsalle gamida tsallakowa zuwa inda azeez yatashi yaja cup din tea din yasoma surbewa yana hadawa da sauran dambun,kafada mustapha ya daga

"Yadai fiki gsky magana ta haqiqa,kawai kuyi qoqari kuma ku sauya a karan kanku kodon mutuncin addininku"

"Zamu sauya amma ba yanxu ba,don banga dalili ba hakanan da quruciyata,da dukiyata da kyauna nazauna ban mori rayuwata ba,shima yanaso,tsabar iya takura kaine" dubanshi kawai mustapha yayi,da alama shima yafara sallama lamarinsu,dukkan alamu sun bayyana wanda yayi nisa bayajin kira saidai gyaran Allah kawai.



______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃ðŸ»Ã°Å¸’ƒðŸ».


        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauÆ™i😻😻😄🤗.


______________________

7/11/21, 4:30 PM - My Mtn Number: 👑 *SIRAƊIN RAYUWATA*👑




*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar siya ki tuntubi wadan nan lambobin_*



0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





11




       Rashin samun damar malamin na halartar darasin sa a ranar yasanya daidai period din ajin yazama dandalin hira ga daliban,duk da cewa yawanci koda malami bazaizo ba to akwai wanda zai riqe mishi hissarsa ta ranar,to amma yau hakan bata samu ba,kasancewar yau da gobe sai Allah,hakanan tafi gaban wasa.



        Rukuni rukuni ne na dalibai kowa ya kama dabarshi,wasu na saman wajen rubutu wasu na kan kujerunsu na zama,kusan group din afnan Abdallah mu'az yafi kowanne cika da yawa,saidai kana dubansu kasan kowacce tana jine da kanta,duk da hira suke haiqan amma babu wata hargowa a ciki,duk wannan abun da ake bilkisu na saman nata kujerar karatun,ta dora kanta saman wajen rubutu takwantar tamkar mai bacci,saidai ba bacci take ba,littafi ne a hannunta tana nazarin c.a da za'ayi musu a gobe.



      Duk yadda ta maida hankalinta ga karatun hakan bai hanata jiyo hirarrakin group din afnan ba,kusan kowacce tana bada labarin yayyenta maza ne na gida da sauran abubuwan daya shafesu,afnan din tana tsakiya batace komai ba sai binsu da kallo da take tana kuma saurarensu,yayin da wani tsagi na hankalinta kuma jifa jifa yake kan bilkisu,haushinta na kamata,itakam tana mamakin yadda mutum yake iya rayuwa baya magana,yadda mutum yake iya rayuwa shi kadai,babu 'yan uwa ba abokai bare qawaye,ta tabe bakinta lokacin da hanan tace

"Princess baki bamu labarin naki yayun ba,nasan it will be sweeter than ours" wani murmushi tasaki tana tuna miskilin yayan nata,ya azeez mai aljanun miskilanci,miskili kafi mahaukaci ban haushi,sa baka dariya sai hamma tatuna wasu daga cikin kirarin da ammi kan masa musamman idan yabata haushi

"Yayana guda daya ne,prince abdul'azeez" ta qarasa maganar cikin nuna alfahari,sautin muryarta na cike da nuna qauna da kulawa ga dan uwanta,da kuma wasu alamu dake nuna tana matuqar ji dashi,sai dukka suka sake bata kunnuwansu,don dama bata taba musu wata magana makamanciyar wannan ba,kowa ya zaqu yaji me zatace

"Uhmmm....tell us about him" hanan da kusan tafi kowa zaquwa tafada tana murmushi.



"Komai zance akan yaa prince na dabanne kamar yadda yake na daban,i have never ever seen mutum kamarshi,shi na musamman ne koda cikin gidanmu ma,tun daga yanayin halittarshi zuwa attitude nashi,kyakkyawa ne yayana,har wataran nakanyi buri dama nice nake da kyanshi" zaro idanu hanan tayi tana cewa

"Wow!,duk yadda kike din nan afnan?" Kaita gyada tana dubanta

"Yes,kyansa ba irin nawa bane,ya hade da kwarjini,kinga banson miskilancinsa,i hate miskilanci"sai kuma tayi shuru tana duban bilkisu a sace,wanda ta tabbatar bilkisu taji abinda tace

"Yana iya wuni shi daya,koda yana cikin mutane kina iya irga maganan da yayi qwara nawa ce,mma duk sanda naso inyi masa mita ko qorafi....u know what?" Duka sai girgixa kai

"Daya kalleni saina kasa cewa komai,there is something special in his eyes,kwarjini....yayana badai kwarjini ba"

"Wow...wow" hanan tasoma fada tana tafa hannayenta kana tasake matsowa gaban afnan sosai

"Pls friend....ki bani yayan nan naki mana,wallahi har naji nakamu" ihu duka wanda yake team din yasaki wanda yashiga har tsakiyar kan bilkisu,ta runtse idanunta don sam batasan hayaniya,saita kifa littafinta saman kan nata,amma duk da haka bata tsira daga jiyo cecekucensu ba,kowacce tana fadin saidai ita.



     "Wait.....relax 'yammata" afnan tafada tana duban kowaccensu

"He already taken out" duka sai sukayi shuru suka zuba mata idanu,yayin da itakuma take murmushi

"By who?"

"Miss Safwa ibrahim khalilu attah"

"The attah's daughter?" Humaina daya daga cikinsu tambaya tana zare idanu,waiwaya afnan tayi ta dubeta sannan ta kada kai

"Qwarai" saita sauke ajiyar zuciya tamaida jikinta ga kujerarta tana cewa

"ƙarshen magana?"

"Kaman yaya?" Hanan ta tambaya da alama maganar batayi mata dadi ba

"Zan gwada sa'ata indai zaki hadamu" tasake cewa da afnan,dubanta tayi kana tace

"Da zan baki shawara dasai nace its better ki haqura,nasan ya azeez farin sani,daya daga cikinmu ina da yaqinin ba zata taba burgeshi ba,nasan halayenshi da tsarinsa,even safwa ammi ce ta hadasu...,bayaga haka ma....ya azeez hanan am sorry to say yana da tsada mai yawa,tun a yanzunma da yake da shekara 25 ya kike tunanin gaba,he's belong to mata masu aji da tsada,ina da tabbacin zai rainaki ne saboda yana da kamar safwa....duk fadin makarantar nan wa kike tunanin tafi kowa kyau?" Dukkaninsu kuma lokaci daya idanunsu yakai kan bilkisu,hakanan cikin jikinta taji idanuwa barkatai a kanta,hakan yasa lokaci daya taji wata irin tsarguwa da takura.



        Dariya afnan tasaki saboda ta karanci inda suka maida hankulansu

"Koda za'a maidata cikin sahun wasu a duniya,banajin zatayi attaracting dinshi...he's diffrent kamar yadda na gaya muku a baya".



       Tsam bilkisu tamiqe bayan ta aje littafinta tasoma ficewa daga ajin,don gaba daya hirar tasu tasoma gundurarta duk da bada ita akeyi ba,amma ta fuskanci wasu al'amuran an soma jefata a ciki wanda ba huruminta bane.



       Bata dawo ajin ba har sai data tabbatar malami yashiga sa'an nan takoma,ta tattara hankalinta dukka kan karatun,saidai wata sabuwa kuma,yunwar dake sakadar cikinta ta hanata fuskantar wasu abubuwan,saboda jiya abincinta su hauwa'u ta barwa,don a jiyan baban nasu baiyi cefane ba,da safe ma bata samu abinda zataci ba,amma yau tana saka rai,saboda umma luba tadawo zata leqa gidanta aiki,a haka taci gaba da daurewa har lokacin tashi yayi.



      A gajiye tulus ta isa unguwar tasu,kamar ko yaushe ta karya layinsu cike da fargabar yau kuma wanne sabon abu zata tarar a gidan nasu.



      Karaf kuwa sai idanunta suka sauka kan 'yar qurqurar anata sauke kaya da sukafi kama dana jere ana shiga dasu cikin gidan nasu,hakanan gabanta ya yanke yafadi,baban nasu bazaidai haqura ba kenan,tunda yadaura niyya sai yayi kamar yadda yasha maimaitawa kullum kwanan duniya?.



      Jiki a salube ta isa qofar gidan sanda masu qurqurar suka tasheta da niyyar qarawa gaba,tafidda wani dunqulallen farin hayaqi daya wuce kai tsaye zuwa hancin bilkisu,ta shaqeshi har huhunta,wanda a take yasake murda mata ciki yakuma tashi yunwar dake sakadarta.



       Tana shirin shiga gidan saiga umaima da bushira dauke da babban faranti,samansa kwanuka ne jere reras a kai,idanu tazuba musu tana dubansu har suka qaraso,take ta fahimci daga ina suke,ranta yabaci qwarai,ta tsuke fuska tana dubansu sannan ta jeho musu tambayar 

"Daga ina kuke?"

"Umma kattice tace mudaukar mata abinci mu zaga mata dashi yau bazata siyar a gida ba" cikin bacin rai ta daka musu tsawa tana dubansu

"Talla?,tallah umaima?,mena gaya muku game da talla?," shuru sukayi dukkaninsu,jikinsu yayi sanyi sosai,a rayuwarta babu abinda ta tsana irin tallar diya mace,ta yarda suyi dukkan wani aikin wahala a biyasu amma banda talla,tallan ma yara qanana kamar umaima da bashira da basu gaza shekara takwas goma ba?,kawai saita isa gabansu ta debe kwanukan daga kansu tamiqa musu jakar makarantarta tanufi cikin gidan suka rufa mata ba.



     Bayaga sallama bata qara kan komai ba,saboda ranta dake bace hatta masu jeran amaryar baban nasu ma bata duba ba,wanda bakajin komai cikin gidan sai karadinsu,ga kular abinci da lemon roba baja baja da alama sunci sun hantse,sai data isa qofar dakin umma kattin sannan ta aje kwanukan gabanta,suka dakata daga hirar da suke ita da baquwarta da alama tana labarta mata abinda ke faruwa ne

"Ina kudina?" Abinda tasoma tambaya kenan tana miqawa bilkisu hannunta,saita waiwaya kawai ta miqawa itama su umaiman hannu,sunsan mai take nufi,don haka suka miqa mata kudin tamiqawa umma kattin taja hannunsu,bata tsaya jin mitar da take ba nasun dawo mata da saura,hala ma hamshaqiyar yayar tasu ce ta hanasu.



       Duban umma kattin baquwar tayi

"Wai wannan ma diyarsa ce?" Tabe baki umma katti tayi cikin takaici

"Hmmm,aiba lallai harki tafi ki gama shaida yaransa ba,don wasu ma basa garin sun bazama neman kudi"

"Amma kuwa tubarkalla ma sha Allah da ita,ashe yana da zankadediyar yarinya har haka?,wannan wallahi dazai bada ita akai aikatau ba qaramin kudi zaku samu ba" baki umma kattin tariqe

"Rufani ki sayani,wannan da kike gani da qanwar uwarta na kusa ma ba lalle kiganta a gidan nan ba,donma uban ya kafe kai da fata aida tuni bata a nan" nan tadan labartawa baquwar tata wani abu game da bilkisun.



       A daki kuwa dukkaninsu sunyi shuru suna kallonta saboda ba kasafai suka fiya ganin fadanta ko bacin ranta ba,saiduk kowa jikinsa yayi laushi,don bacin rai bata bi takan danqararriyar dafa dukan da aka aje mata ba ta daura zani da hijabi tashiga wanka,sai data fito tasanya wata doguwar rigar atamfarta da itama tasoma nuna gajiyawarta sannan taja abincin ta tsakura

"Ku tashi ku shirya mu futa gaba daya" ta basu umarni sanda tature kwanon tanajin taste din bakinta babu dadi.



     Daga shigowarta zuwa yanzu cikin gidan anyi guda anyi habaici har batasan sau nawa ba,sai taga haqurin umma katti yau daya da bata tanka musu ba duk da rashin haqurinta,kuma wala'alla baquwartace ta hanata.



     Bata bar gidan ba duka sai data kada kansu takaisu har qofar islamiyya suka shiga sannan tawuce gidan umma luba.


******   ******


"Yar halak,yanzu nake zancanki balaraba kinganta ta iso" cewar umma luba dake zaune qasan rumfar dake qofar dakinta tamiqe qafafunta,gefanta wata matace wadda a qalla zasuyi shekaru guda itada umma luban,murmushi bilkisun tayi ta qaraso gefan shimfidar ta zauna tana cewa

"Ina hanya ai,makaranta,yau banyi sauri a hanya ba"

"Aiko tunda nadawo na kasa kauda koda tsinke ina zaman jiranki" murmushi kawai tayi wannan karon,ta gaida umma luban kana ta waiwaya da niyyar gaida baquwar tata,sai suka hada idanu,tun dazun da alama bilkisun take kallo,tadan kauda kanta itama bilkisun haka,ta gaidata ta amsa cikin sakin fuska,daga haka bilkisun tamiqe tasoma aikinta.

Duk giftawar da zatayi idanun matar yana kanta.



      "Nikam lubabatu ina kika samo wannan yarinyar haka?" Baquwar ta tambayi umma luba

"Wai bilkisu?,can qasanmu take wallahi"

"Amma kinyi sa'ar yarinya ta iya aiki,saidai nayi mamakin yadda take dakyau haka luba amma aiki take"

"Wallahi balaraba,halin rayuwa,amma banda haka bikisu ai tafi kyau da babban gida,nikaina wani lokaci nakan kalleta na qara,a haka ma wai don bata kwalliya,kullum haka dai zaki ganta cikin tsummokaran kayanta"

"Ma sha Allah,gaskiya Allah yayi mata baiwa,wannan kyanta tasamu wani babban gidan ko wani babban mutumin yayi wuf da ita" dariya umma luba tasaka

"Tunanina da naki ya zama daya,yanzun duk wannan kyan idan ba'ayi wasa ba saiya tafi a banza,saikiga wani qaramin yaron daga can cikin loko ya kwashi garabasa,bayan matar manya ce" qarasowar bilkisu wajen yakawo qarshen maganar tasu.



       Batafi awa biyu ba baquwar tayi musu sallama tatafi,saiya zamana daga bilkisun sai umma luba,bakin umma luban baya shuru,bata taba iya zama haka,haka tadinga jan bilkisun da hira kamar yadda tasaba,yau kusan duka hirar tata kan yariman kaisa ne,maganganun afnan na daxu zuka dinga dawo mata,kusan maganganun saunyi daidai da nata,sam hirar bata wani bata sha'awa ba,ita da zatayi shuru da bakinta tabarta ma tayi tunanin yanayin da gidansu da rayuwarsu zasuci gaba da kasancewa da yafiye mata wannan hirar.



       Gab da magariba tagama komai da komai,saita sanya hijabinta tana yiwa umma luban sallama

"A'ah,bazaki tsaya kici abincin ba?" Murmushi kawai tayi,umman tasanta da alkunya,wala'alla tanaso amma bazata iya tsaiwa ci ba,saboda haka tace mata

"Dauki kwano ki diba kyaci a gida".



☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



      Sanye yake cikin wata jibgegiyar rigar sanyi baqa wadda taqara mishi qiba sosai,saidai ta masa kyau ainun,an nata wani irin adon zane da jan zare wanda yasake qara mata qawa,abun mamakin duk sanyin daje busawa a wajen yasaki hular rigar baya,bayan kanshi babu komai sai gyararriyar sumarshi daketa qyalli.



       Wandon jikinsa sosai yadace da rigar jikinsa,sai rufaffen takalmi hightop wanda yasake qawata adon nashi.



         Shi dayane zaune saman table din,gabanshi kwalabe ne na lemuka guda uku da kofuna guda biyu,duk da cewa darene amma wajen tarwai yake da haske kamar kayar da allura kuma kasunkuya ka dauki abarka.



        Kallo daya zakayi mishi kasam cewa ranshi a bace yake,yazuba lemon yasha shi kansa baisan adadin kofi nawa bane.



        Kusan dukkan yarinyar dake wajen babu wadda bai dauki hankalinta ba,matane kala kala a wajen birjik nau'in yare daban daban,kama daga turawa larabawa 'yan africa da 'yan asia,saidai akwai wani babban abu dake hanasu qarasowa inda yake,kwarjini!,kwarjininsa yacika wajen gaba daya,hakanan ya dusasar da kyau da qasaitar duk wani namiji dake wajen.



        Ajiyar zuciya tasauke mai nauyi tana duban wayenta guda biyu

"Friends....gaskiya banjin zan iya haqura dashi a yau,nayifa qoqari,watanni nawa ina faman boye mishi kaina,haqurina ya qare,ya kamata na bayyana mishi kaina,sonshi yayimin yawa a raina,kullum cikin mafarkinsa nake,ya kamata koyaya nashiga jikinsa" cewar wata farar budurwa ma'abociyar tsayi,saidai matuqar kana wajen zakayi mamakin jin yaren hausa na fita daga bakinta,saboda kallon farko idan akace ka yanke mata addini ko qabila ba zaka taba dangantata da qabila ko yaren hausa fulani ba,caraf takusa da ita ta riqe mata hannu

"Minal....kibi a hankali,bakisan waye prince ba shi yasa kike tunanin tunkararsa kanki tsaye" zame hannun nata tayi tana miqewa 

"Na sani,nasan ba ordinary bane kamar sauran samari da muka sani,anyway zanje na tareshi yau komai ta fanjama fanjan,tunda shima mutum ne ai kamar kowa ko?" Tafada taba dage musu gira,sun fahimci me take nufi saboda haka suka sheqe da dariya gaba dayansu itama tana tayasu,kana tasoma takawa tana nufar inda yake zaune cikin wani salo da sauya tsarin tafiyarta.



      Abun haushin shine harta isa baimaga tahowar tata ba,wannan karon harya miqe tsaye yana duban agogonshi bisa dukkan alamu tafiya zaiyi

"Hey!" Ta fada a hankali lokacin da take tsaye dab da bayanshi,a nutse yawaiwayo sai suka hada idanu,take murtikewar fuskarshi ta ninka yadda take ada

"Ina fatan ban matsawa prince ba ko?" Tafada tana jifanshi da wani shu'umin murmushi gamida dan kada jikinta cikin dabara,har yanzu dai dubanta yake ba tare daya amsa mata ba,hakan kuma ita yayi mata,saboda haka still tana murmushi tamiqa masa hannunta

"Am minal abdulhamid" hannun nata yabi da kallo wanda sukaci fixing na faratan 'yan kanti zaqo zaqo dasu,sa'an nan aka bisu da jan farce aka lullubesu dasu,sai qyalli suke zubawa.



      Dauke idanunshi yayi yamaida cikin nata,wani kallo daya sanyata faduwar gaba,da kanta tasauke hannun nata ganin yana niyyar qagewa ba tare daya maida mata martanin gaisuwarta ba

"Kaman baka da interest da gaisawa da mata b....."

"Hey!" Yafada cikin kaushin murya

"Getout of my sight" yafada calmly kamar bamai bacin rai ba,murmushi tasaki itama kamar maganar tashi bata dameta ba

"Calm down yarima.....niba fada nazo muyi ba,nazo ne....."

Wani mugun tsaki yaja wanda har sai daya janyo hankalin mutanen dasuke daura dasu,dukka suka waiwayo suna dubansu,hannunshi yasanya yadauki wayarshi yasoma takawa don barin wajen.



       Gaba daya sai taji ta muzanta yadda aka zuba mata idanu,har kamar ma sauti sautin dariya take jiyowa daga wani sashe na wajen,ranta taji ya sosu,cikin kunya da sagewar gwiwa tasoma tattaki don barin wajen itama,saboda yariga daya gama kunyatata har a gaban wadanda take daga musu kai,bataga sauran abun zama tayi ba kuma

"Batasan waye prince bane" sanda tazo gifta wasu 'yammata fararen fata taji sun furta cikin harshen turanci,batako waiwaya ta dubesu ba saboda idanunta da suka cika da qwalla taci gaba da fita daga wajen.



       Tana isa farfajiyar wajen abdul'azeez na ficewa da motarsa daga wajen da gudu,sai tabi motar da kallo tana jin ciwon ran abinda yayi mata,tunda take ba'a taba yarfata irin haka ba,amma taci alwashin saiya kawo kanta gareshi sai yadda ta juyashi.



        Tsararriyar unguwa ce mai kyau da tsari kamar yadda mukasan yanayin unguwannin qasashen qetare suke,gaban wani qayataccen dan madaidaicin gida yayi parking motar tasa cikin sauri yakasheta,bai damu yada kulleta ba yashige cikin gidan.



      Spare key din dake hannunshi yasanya yabude qofar yatura yashiga kamar wanda wani abu ya biyoshi.



       Matsakaicin falone wanda bai cika girma ba can,saidai kuma ya qawatu da kayan alatu iri iri cikin tsari da burgewa,saman daya daga cikin kujerun wani kyakkyawan matashine,saman cinyarsa wata matashiyar budurwa cikin qazamtacciyar shiga suna sumbatar junansu,da alama sun soma nisa a duniyar da suka lula,amma qarar bude qofar da abdul'azeez yayi yadawo dasu hayyacinsu.



      Cak ya tsaya yana watsa musu wani irin kallo daya sanya yarinyar cikin rawar jiki sauka daga kan cinyar saurayin,sannan cikin rawar jiki tasoma tattare ya nata ya nata tun baice komai ba ta lalubi qofa ta fece,yayin dashi kuma idanun abdul din suka masa nauyi,amma saiya waske kawai yahau yarfar da hannu kana tamiqe yana maida botiran rigarsa,yabude baki zaiyi magana abdul'azeez ya rigashi cikin bacin rai da kaushin kurya

"Kamal....sau nawa zan gaya maka?,sau nawa zan gaya maka kamal?" Cikin dan daure fuska wanda ake kira da kamal din yayi taku biyu yasake matsowa gaban abdul 

"C,mon haba prince,waime yasa kake babu kamar ba wayayye ba,kana da matsala wallahi ka cika kwafsawa mutane...." Kanshi yanuna da muqullin motar dake hannunshi

"Nine ma nake kwabsawar?" Saidai kafin kamal ya bada amsa an turo qofar falon an sake shigowa da sallama,duk cikinsu babu wanda ya iya amsa sallamar sai carko carko da sukayi,abdul'azeez naci gaba da fidda hucin bacin rai.



       Matashine shima wanda a qalla zaiyi shekarunsu ya qaraso yana dubansu

"Weting d hapin guys?,kuka tsaya kamar zakaru?"maimakon amsa sai abdul'azeez din ya maida idanunshi kan kamal

"Na baka awa daya,ka tattara komai naka kaficemin daga gidana..."

"Ah....kamar yaya?,meya farune?,azeez!....tsaya mana" matashin daya shigo yanzu yasoma yunqurin tsaida abdul'azeez wanda tuni yayi hanyar corridor din da anan dakin gadonshi yake,ko waiwayowa baiyi ba don haka yamaida hankalinsa ga kamal

"Kamal,kasake maimaitawa ko?" Yajefa masa tambayar,kafadunsa duka ya daga 

"Eh sai meye?,taqamarshi yace nabar mishi gida,to hell shida gidan nashi,saime don na tafin?ko yaushe shi sai zafin rai da yiwa mutane fada,waye ya girma ne a cikinmu" Kaiya soma girgizawa yana matsawa gabanshi

"A'ah kamal,kada kace haka,azeez yafika gaskiya,kai kanka kasan abinda kuke aikatawa din ba dai dai bane,tunda koda wasa ba zaku taba bari yaje kunne ko idanun iyayenku ba,kuma kafi kowa sanin ba abinda ya kawoku qasar nan kenan ba,bugu da qari kasan situation na abdul'azeez,yana da duk wata dama da zaiyi yadda yakeso ya gusarwa da kansa wannan damuwar,amma koda yaushe qoqarin kaucewa da takatsantsan yake saboda bin umarnin Allah,donme shi yana kiyayewa amma ku kuna qoqarin jefashi a matsala kunayin abubuwa irin wannan a gaban idanunshi yana kallo,bayan kusan raunin dake cikin zuciyarsa?"

"Kaga....kaga malam mustapha dakata da Allah,sauraramin,dama mun dade da sanin kaine munafukinsa dan shishshigi kuma,daa kafin zuwanka aiba haka muke zaune ba,duk da yana magana amma ba kamar haka ba,kasan dai wata kusan tafi wata ko?" Murmushi mustapha yasaki,ya gane kamal nason mishi gori ne,saboda shi din d'ane ga qanwar maimartaba,shi kuwa mustapha haduwar jini ce kawai da Allah yasanya tsakaninsa da abdul'azeez din

"Na sani,amma duk inda gaskiya take dole a gaya maka ita kamal koda bazakaji dadi ba" wani mugun tsaki yaja sa'annan yajuya yashige dakin da yake nashine shida abokin kwanansa yasoma tattare komai nashi,sam hakan baiwa mustapha dadi ba,yasani dole ne suga kamar shi yashiga tsakaninsu,saboda haka ya juya yanufi dakin abdul'azeez kai tsaye.

7/11/21, 4:30 PM - My Mtn Number: *S R B*


*_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,gamai buqatar mallakar nashi xai iya tuntubar wadan nan lambobin kai tsaye_*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

________________________________

______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃ðŸ»Ã°Å¸’ƒðŸ».


        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauÆ™i😻😻😄🤗.


______________________




13




       Babban club ne na masu aji da naira wanda yake hada manyan yara daga qasashe daban daban matasa masu jini a jiki,daga can wani kebantaccen waje zaka hangeshi zaune saman teburin daya qunshi kujerun zama guda biyar,kowacce kujera akwai mutum akwai,saishi cikon na biyar din dake zaune tsakiyarsu,ba abinda yake bankawa cikinsa hayaqi,wanda duk sanda yazuqa ya fesar sai kaga wani dunqulallen farin hayaqi yatashi sama yacure guri guda kai kace an hura wutar itace ne da jiqaqqen itace ko wutar ta mutune tana neman agajin fifita,daga saman teburin akwai saura saura da burbushin wadanda yasha masu tarin yawa,bayaga kwalbar abunsha wanda babu ko kokwanton cewa ba zallar abunsha bane da baisa buguwa ba.



       "Kamal.....ka tsaida wannan hayaqin da kake bugawa cikinka kamar babur,tell us me yake faruwa,kasoma gaya mana kuma but u keep quite".



        Sauran ta hannunsa yayiwa kyakkyawar zuqa sai gata ta qare,yadorata saman table din yakashe kamar yadda yayiwa sauran,kana yafeso dukka hayaqin waje ya qarawa sama hazo sosai sannan ya muskuta ya gyara zamanshi

"Kamar ni....ni prince AA zai kora daga gidanshi?" 

"What!" Suka fada kusan a tare kowa yana dubanshi,baqinciki yasake cika kamal yanajin takaicin yadda ya tozartashi cikin abokanshi dasuke sake ganin girma da qimarsa sakamakon cewa azeez din dan uwanshi ne na jini

"Amma baaabaa....ba cousin dinka bane?" Kai ya gyada

"Cousing dina ne amma yayimin haka" ya qarasa fada cikin dacin rai,daya daga cikin matasan wanda shima yaciro tashi tabar yakunnata yasoma busawa sannan yace

"Ni dama guy din fa ya tsayemin a rai,kishi nake dashi wallahi yadda kasan nasa bakin bindiha na harbeshi,kwarjininsa yayi yawa,kamar komai an bashi a rayuwa,amma....yakamata kamal kadauki mataki,dont let it to be in vain" kai yake jinjinawa,abinda yakwana biyu yana kitsama ranshi kenan yadda zai jawo abdul'azeez ruwa,ya tabbatar idan hakan tafaru zasufi samun sakewa suyi duka yadda sukeso cikin walwala tunda shima yazama dan hannu

"I know his week point,na rantse da Allah saina rama,saina dauki fansa....ba lalacewa yake gudu ba?...." Saiya saki murmushin jin dadi kana yasanya hannunsa yadaki table din dake gabanshi,dukkaninsu sun fahimci me yake nufi,don haka dariya ta gauraye wajen,daya daga ciki yasake cewa

"Maan...kace kwanan nan muma kuttun farinjininmu zai fashe if he join us,zamu sake zama big boys fa"

"Qwarai kuwa"

"Amma kunyi suya kun mance da albasa,banji kunyi magana kan hanyar da zaku jawoshin ba,aikine mai wahala idan kun manta na tuna muku,kai kamal kafi kowa sanin waye prince azeez".



      Kai ya jinjina idanunsa akan matashin

"Nafi kowa cikinku sanin wannan....nakuma tsara yadda zamu gudanar da komai,kamar yadda nasan yanayinsa zamu hilaceshi da mace,amma mace wadda tacika ta isa mace,anan matsalar take,ban gano wata mace wadda zata dace da plan din ba,takuma jure shi" shuru ne ya ratsa tsakani,kowa na nazarin maganar kamal din,don a nan gizo yake saqar

"Wow!.....na tuna....minal" daya daga ciki yafada da sauri har yana zunkudawa gaba kan kujerar da yake kai,da alama abinda yatuna din yayi mishi dadi

"Wace minal?" Kamal ya jefa masa tambayar

"Itace yarinyar da take da interest akan prince harta kasa boyewa ta bayyana mishi,amma ya tozartata cikin jama'a,na tabbata ina da yaqinin idan mukaje mata da wannan maganar komai zai tafi"

"Ya take?" Kamal yasake tambayarsa,gira ya dage masa yana sheqewa da dariya

"Minal ta hadu,idan nace maka haduwa ina nufin ta hadun din"

"Good" kamal yafada yana murmushi,yabude baki zaiyi magana wayarshi tadauki kida,yaja dan tsaki kana yacirota  yana duba mai kiran,mahaifiyarsa ce,saboda haka ya daga.



        "Nayi qoqarin kiran me martaba na shaida mishi abinda ke faruwa,saidai kuma yayi tafiya baya qasar kaisa,amma gobe xai dawo,dole yaji wannan maganar,tunda shi bashi da mutunci,baya ganin kowa da gashi,kana dan uwanshi har zai iya korarka daga gidan saboda yasamu daurin gindi daga mahaifiyarsa?,na shaida mata abinda ke faruwa tacemin wani wai zata bincika?,bincike na meye?"

"Rabu dasu mom,na rantse saina dauki fansa kan abinda yayimin din,karki damu na gana tsars yadda komai xai gudana"

"Kome zakayi kayi,amma karka sake kayi abinda zai nakasta shi ko illatashi"

"Baki da damuwa,sai munyi waya" yafada yana katse kiran yakoma wajen abokan nashi sukaci gaba da tsara yadda komai zai gudana.



☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



      A washegari cikin gidan nasu akayi É—an Æ™warya Æ™waryar wuni,itadai bilkisu bata fasa zuwa makaranta ba bare wajen aikinta,don bataga wani sabon abu ba game da lamarin,hakanan batasan zaman me zatayi cikin gidan ba.



       Sanda tadawo kuwa kusan babu kowa sai 'yan kawo amarya,tadinga bin tsakar gidan da kallo yadda akayi kaca kaca da abinci,ta dinga jin ciwon hakan cikin ranta,don a qalla abincin idan aka tattara yakai abincinsu na kwana da kwanaki wanda mahaifin nasu bai iya cida su,amma saboda aure yau gashi abinci a gidansu har soro,haka ta tsallake tawuce cikin gidan.



       Taji dadin yadda tasamu hannatu ta killace qannen nata duka a daki,data shigan sai tayi qoqarin sakin fuskarta,har zuwa lokacin data gama duk abinda zatayi,tasa kowannensu yasamu guri ya kwanta,ba jimawa kuwa Allah ya taimaketa dukka sukayi bacci,don haka ba'a kunnensu akayi badaqalar shigowar malam bilya da kazar amarya babu ta umma katti ba,da qyar su batulu suka shiga fadan suka sasanta yawuce abinsa dakin amaryarsa yana rawar qafa kai kace a ranar yasoma aure.



          Sati guda amarya tayi tana cin amarci kai kace budurwa ce a maimakon kwanaki uku,cikin kwana bakwai din gidan babu yunwa babu qishirwa,girki ake kamar kowanne gida sau uku kuma aci a qoshi,duk da cewa ita amarya ta tsaya kai da fata kan girkinta zatayi daban,bazatayi girkin hadaka ba,hakan kuwa babu musu tasoma dora tukunyarta,wanda kullum ta Allah sai anyi tashin hankali tsakanin malam bilya da umma katti,saboda banbanci cefane da yakeyi qiri qiri,miyarta tafi takowa maiqo da zaqi.




       To sannu sannu dai a haka rayuwar cikin gidan taci gaba da garawa,babu wani abu daya sauya,kullum sai qarin tsanani da nauyi dayake dake hawa a kafadar bilkisu,don bayan wasu kwanaki ya watsar dayi musu cefane ya kama na amarya ita kadai,ungulu takoma gidanta na tsamiya.


☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



      Sati guda rak kamal yayi maimartaba yayi magana da abdul'azeez tilas yace dawo gidan,hakanan ya sake tattarawa yadawo saidai bai fasa aiwatar da qudurinsa ba.



       Saidai kuma duk yadda minal taso janyo abdul'azeez jikinta ta jefashi cikin sabgarsu kamar yadda kamal yabuqata abun yaci tura,haqarsu ta gaza cimma ruwa,wanda har tasoma sarewa takuma baiwa kanta amsar lallai abdul'azeez din bazai jawu ba,don ta gwada dukkan wata fikira da basira tata amma abun yaqi ci yaqi cinyewa,wanda daga qarshe tasamu kamal ta shaida masa.



      "Kayi haquri kawai,don yariman yawuce dukka tunaninmu,ina ganin ka ajeshi gefe kawai ka kama wata sabgar taka" cikin fusata yadaki bencin dake gabansu

"Ba zaki gane bane,bazaki fahimta ba,idan har abdul'azeez yazama dan hannu inajin kaf makaranta ba za'a samu wadanda suka kafa tarihi cikin rayuwar bariki ba irinmu,zamuyi komai cikin wadata da qasaita ne....amma indai wannan bata samu ba,ina da wani plan din,tunda taurin kai gareshi,zan masa mai gaba daya,sai nayi tarnishing image dinshi a idanun kowa idan ma yanajin shi wani ne,sainasa kunya ta hanashi shiga cikin al'umma,atlast zanyi amfani da wannan hanyar nayi destroying duk wani tanadi da suke da batar da sunanshi da yarima a masarautarsu,kin shirya aiwatar da wannan aikin?,idan kin shirya ki fadi ko nawa ne farashin aikin ki,zan biya".



      Shuru minal tayi tazubawa kamal idanu,a mamakance take kallonshi,jiki da zuciyarta sun bata cewa lallai akwai wata a qasa,bawai a dalilin korarshi a gidan yasa zai aikata dukkan wannan abun ba,ba shakka akwai dama wani qulli duk yadda akayi tsakaninsa da yariman tun bayau ba,dan gyara zamanta tayi still tana kallonsa

"But....amma kamar kana da wani plan ne apart from dalilin da nasan ya sanyaka zaka mishi wannan abun" hannu ya daga mata alamun dakatarwa

"Wannan duka ba huruminki bane...just idan zakiyi ki fadi price" murmushi tasaka tana qarewa kamal kallo,a ajinta tana ganin kamal yayi qanqanta ya gaya mata magana haka,don haka tace dashi

"Ban amshi contract dinka don kudi ba,don basu na rasa ba,na amsa ne saboda nawa interest din,saboda haka,bani da sha'awar yin aikinka,inaga abinda zaifi kanemi wata" takai qarshe tans miqewa tsaye gamida qoqarin saba jakarta a kafada.



        Kallonta yake ganin da gaske tafiyar zatayi,idan tatafin kuma baisan inda zasu samu wata kamarta ba,bugu da qari yana buqatar privacy,baisan mutane da yawa susan maganar ta yadda zaya zamana babu wani sirri kenan

"Wait minal pls.....zauna kiji wani abu daya kafin kiwuce" sai data juyo ta kalleshi sosai,kana kuma a hankali takoma gurbin data tashi tazauna,ta zuba masa dukkanin idanunta alamun tana saurarenshi.



       Sai da yayi gyaran murya kadan gamida gyara zamanshi,yasake matsowa kusa da ita yadda zata jishi sosai

"Koda baki da buqatar kudi amma kina buqatar yarima ko?" Kaita gyada

"Of course.."

"Good,bari to na gaya miki abinda zai iya faruwa,wanda inada yaqinin koda ba hundred parcent bane to 99.9 parcent hakane" shuru sukayi dukkaninsu kafin yadora

"Duk wadda tasoma cikin galaba kan azeez takaishi wannan dunuyar ina mai tabbatar miki itave zataci gaba da kasancewa dashi,koda azeez zaiyi bariki,zaiyi bariki ne ta musamman ba irin ta kowa ba,kinsan dalili?"kai ta girgixa tana sake bashi dukka hankalinta

"He is arrogant kinsan da wannan,and he prides him self cewa babu wata mace data isa tayi dauke hankalinsa zuwa wannan hanyar,babu soyayya a ranshi bare a samu damar kaishi hanyar da muke kai,kinga,zai zamana yana boye sabon halinsa don kar asani a masa dariya,zai dinga qoqarin samun sirri ta hanyar yin mu'amala da mace guda,duka bayan wadan nan kuma....azeez yana da qyama da qyanqyami,so dat,kiyi tunani kigani,idan xaki iya barwa wata wannan opportunity din da kika samu....fine" yana gama gaya matan yamaida bayansa makarin kujerar yajingina yana dubanta,yana fatan maganganunsa su shigeta,ya tabbata matuqa sukayi nasarar bata azeez,babu makawa sune zasu shiga takarar neman zama sarkin kaisa,kamar yadda dokar qasar ta tanadar matuqar an samu yariman dake da damar hawa mulki da wani babban alfasha.



        A hankali take jujjuya maganganunsa,wanda fiye da rabin zuciyarta tatafi kan cewa ta karba tayi koda babu ko sisi,saboda samun yarima azeez a wajenta shine babban biyan da za'ayi mata

"I can do it" ta amsa mishi,saiya saki murmushi kana yace

"Well,yayi kyau,shikenan zamuyi magana,zan gaya miki yadda komai zai kasance,rana dakuma lokaci" daga hakan sukayi sallama tadauki qaramar jakar hannunta tafice daga wajen.



       Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



       Sassanyar safiya ce wadda ke cike da lullumi da wani irin yanayi me dadi a qasar ta mexico,daidai lokacin da yarima ke fitowa daga bandakinsa dake manne a cikin dakin baccinsa,agogo yasoma dubawa lokacin daya fito don yaga lokacin daya rage mishi kafin shigarsu lacture,saiya dauke kanshi yana ci gaba da goge jikinsa dake cike da gargasa da qaramin towel din dake hannunshi bayan wanda ke daure a qungunshi.



       Dan tsayawa yayi yana duban dakin,sai yaga kamar ba yadda yabarshi ba a sanda yashiga yashiga toilet,kamar wani abu ya canza,a nutse yasoma tattakawa yana sake qarewa dakin kallo dakyau,saidai bai sake ganin komai ba don haka yanufi gaban mudubi yadauki manshi mai taushi da qamshi yasoma shafawa yana sakin tsaki bayan yatuna cewa yau su ukune ma kawai suka kwana cikin gidan,tunda safe kuma daya shiga kitchen zaisha ruwan dumi yatarar duka sun fice,da alama kowanne cikinsu yana da lactures din safe.



       Sai daya gama shafa man,ya gyara sumarshi dakyau bayan yashafe ta da mayukan gyara gashi kala kala kai kace macace,sannan ya isa gaban ma'ajiyar kayanshi yasoma duba kayan da zai sanya.



       Gaba daya shigar fari yayi hatta da agogon hannunshi,yakoma gaban mudubin yayiwa kanshi ruwan turaruka masu sanyin qamshi da kwantar da rai,bedsite dinshi yajawo yadauki abinda zai dauka da wasu takardu daya gama dubawa daren jiya dake gefan madubin nashi kana yafito bayan ya murzawa dakin nashi key,don ba kasafai yake barin dakin nashi a bude ba,musamman idan yasan zaiyi nisan kiwo,mutum ne mai tsari da doka,sam bai yadda ana shiga mishi daki barkatai,shi yasa ko yana ciki to zaka samu qofarshi ya turota badai ka sameta a bude ba.



     Kafin yafita daga corridor dinsa kira yashigo wayarshi,dan qaramin murmushi yafidda ganin me kiran,saif ne,amininsa dan wazirin mai martaba,waziri musa adamu,cikin yanayin dake nuna akwai sabo da shaquwa tsakaninsu yadaga wayar soma magana,daidai nan ya qaraso falon gidan.



      Babu kowa cikinsa kamar yadda ya zata,sai yayi tsaye yana ci gaba da amsa wayar harya gama,motsin daya jiyo daga kitchen shi yaja hankalinsa yamaida dubanshi can,sakan talatin saiga kamal na fitowa daga kitchen din,dauke da madaidaicin plate wanda akai cups ne guda biyu da plates guda biyu wanda ke dauke da soyayyen plaintain.



       Da murmushi kan fuskar kamal din ya qaraso yana cewa

"Na tsammaci kafita ai"

"Ina dai niyya,kai kadai ka rage a gidan"

"Eh,nima nagama shiryawar break kawai zanyi nafita....bismillah zo muyi break din" yafadi yana aje farantin,kallon tea da plaintain din yayi cikin mamaki,don yasan kamal din mugun lazy ne,yawanci a kitchen yake karyawa a gurguje yafice,amma yau sai gashi da kinkimo faranti,kamar zaiyi magana sai kuma yafasa,ya qarasa gaban farantin yadauki cup daya daya rage a saman farantin don kamal din yadauki dayan,yasoma kurban tea din,saiya samu hannun kujera yazauna don yasan haramcin shan abu a tsaye.



      "Ohk,on my way" yaji kamal din yafada cikin hanzari ya aje cup din hannunsa,ya debi plaitain din yawatsa a bakinsa a gurguje yadubi yarima azeez

"Prince nawuce" kai ya kada mishi kawai ba tare da yace komai ba,yana qoqarin shanye sauran tea din hannunshi shima yafice.



      A nutse ya isa inda 'yar qaramar motarsa mai azabar kyau ke aje,wadda take da budadden sam,yabudeta kana yashiga yazauna

"Oh my god,whats happening?" Ya fada sanda yake da niyyar tada motar,saboda wani irin feelings da bai taba jin makamancinsa ba dake taso masa yana ratsa sassan jikinsa,har tsigar jikinsa tana tashi,uwa uba kuma uban kasala yakeji kamar wanda ya shekara yana aiki.



       A qalla yakashe minti biyar yana jira ko mode dinsa zai daidaita,saidai sam babu wani sauyi tattare da yanayin da yake ciki,saima uzzura da lamarin yake,abun saiya soma bashi tsoro bayan mamaki,a kasalance yakashe motar yazare muqullin yafita daga ciki yasoma takawa zuwa cikin gidan,har wani jiri jiri yakeji,yana dafe da jikinsa yasanya muqulli ya bude gidan yashiga,da qyar ya iya kai kansa dakinsa yazube saman gado yana sake jin kowacce gaba ta jikinsa na sake mutuwa,yana kuma sake fita daga hayyacinsa,feelings din dake tare dashi yana sake ta'azzara kamar zai zauce.



        Daidai lokacin kamal yafito daga maboyarsa,yaisa varender gidan wadda daga ita sai ainihin falon gidan,yatura qofar falon dako samun damar rufeta abdul'azeez bai samu ba,kamal dinne ya qarasa rufeta,kai tsaye yashige kitchen.



      Tana zaune kan daya daga cikin kujeru ukun dake kitchen din,hannunta riqe da wayarta da alama charting take,cikin wata iriyar shiga wadda bata da maraba da tsirara,komai na jikinta ya bayyana,qamshinta kuma ya gauraye ilahirin kitchen din.



       Tsaiwa kamal yayi yana qare mata kallo gamida hadiyar yawu da lashe baki,ji yake inama ace shine zata jewa a wannan siffar tata,alamun motsin mutum ya sanyata hanzarin dago da kanta,suka hada idanu da kamal saita zabga mishi harara,ta tsani yadda yake da shegen kallo da yadda yake yawan bibiyarta da idanunshi,ta riga data gama karantarshi tun ba yau din ba,saidai ita sam bai mata ba,hasalima baikai ajinta ba ko kusa ko alama a yadda takejin kanta a matsayin babbar yarinyar dake harka da 'ya'yan wasu,ko wasun kansu a baya,bare a yanzun da babu wani da namiji dake burgeta ko take gani sai abdul'azeez din,yashafe tauraruwar kowanne namiji a idanunta.



      Basarwa yayi yaqaraso kitchen din kamar mai rada yace

"Komai yazama ready,ki sameshi a bedroom dinsa,a yanayin da naga yake ciki bazai iya tsallakewa trap dinmu ba,i wish u all d best" yana gama fada yajuya yafice daga kitchen din,batayi jinkiri ba itama tabiyo bayanshi,saiya dakatar da ita,yadauko laptop dinsa wadda ya saitata da camerar da zai nadi komai,wadda ke maqale jikin qarfen da aka sanyawa net aka lullube gadon azeez din dashi,yakunnata ta kama,saiga hoton abdul'azeez din zaune saman gadonshi,qanqame da jikinsa,idanunshi a runtse gam,babu abinda yake fiddawa sai gumi.



      Qaramar dariya yasaki mara sauti kana yace

"Uhmmm,lokacinki yafara" batace komai ba tajuya zuwa sashen daya nuna mata,saiya zaro wayarshi ya danna lambobin wayar mahaifiyarsa,bugu uku ta daga

"Mom,komai ya kammala,yanzu haka za'a fara aiki,saiki addu'an samun nasara"

"Allah ya bada sa'a son,wannan nasarar idan ta tabbata ba shakka dukkan abinda zai biyo baya mai sauqine,rushe aysha da abunda tafi tutiya dashi duk duniya shine babban aikin,Allah yabada nasara,sai naji feedback"

"Ok mom" ya fada yana kashe wayar,kana yamaida dukka hankalinsa kan laptop din yana jira yaga shigar minal dakin azeez,har wani lumshe idanu yake yana sake relaxing cikin kujerun,ko banza shima zai more da kallon yadda komai zai wakana,yakuna sakin murmushi yana hango yadda vedion da hotunan zasuyi destroying azeez da mahaifiyarsa cikin masarautar kaisa.......



_____________________________



*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*


*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*


*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*


*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*


*ALBISHIRINKU KANAWA*


*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*



_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_




*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*


*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*


*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*


08033990209



*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌ðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: *S R B*


14


*_wannan littafin amanace a hannun duk wanda yasiya,ga mai buqatar mallakar nashi saiya tuntubi wadan nan lambobin_*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070


______________________

KUNA BUƘATAR A TALLATA MUKU KAYAN SANA'ARKU A PAGES ƊIN BOOKS ƊIN ZAFAFA BIYAR 2021?.


To kuzo ga dama ta samu💃ðŸ»Ã°Å¸’ƒðŸ».


        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.


Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.


Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.


Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauÆ™i😻😻😄🤗.


______________________




   

      Duk taku daya da zatayi na kusantar dakinsa sai taji wani matsananciyar faduwar gaba ta sameta,karon farko a rayuwarta tunda tafara irin wannan harkar data taba samun haka,sanda ta isa qofar dakin tsaiwa tayi cak bayan ta dora hannunta a handle na qofar,tanajin yadda zuciyarta ke bugawa sosai,ta lumshe idanunta tana son baiwa kanta qwarin gwiwa gamida hasashen nasara,kana tatura qofar cikin sauri kawai tashige.



      Daga can sashen kamal yasaki ajiyar zuciya sanda minal ta bayyana cikin dakin,yana sake gyara zamanshi sosai tare da sake saita komai tare da bada hankalinsa gaba daya.



        Yaji bude qofar amma bai damu yadago ba,saboda yana zato da tsammanin daya daga cikinsu mustpha ne yadawo,baiso kuma kowa ya fahimci yanayin da yake ciki,infact ma baison takura,baisan ya akayi ya manya bai rufe dakin da muqulli ba.



      Tsaiwa tayi tana dan qarewa dakin kallo,yadda ya hadu haka komai nashi yake hadadde,yadda ya tsaru haka komai nashi yaje a tsare,yadda yake maikyau haka komai nashi yake me kyau,ta sake gasgata yarima azeez din na dabanne,saita sauya shawara,gwara tayi maaa shigar gaba daya,tana da yaqinin a yadda taga jikinsa na wani irin rawa bazaiqi karbarta ba,hakan shiya baiwa minal damar soma raba jikinta da duk wata sutura data shigo da ita,kana ahankali tasoma takawa zuwa gadon da yake zaune akai.



      Kamar a mafarki yasoma yin wasu abubuwa da suka sake birkitashi,cikin qanqanin lokaci tasoma cin galaba akanshi,wani irin bugu zuciyarsa take masa kamar zata tsaga qirjinsa tafito,yana kallonta,yana kuma son hanata amma ya gaza,abinda yake ji cikin jikinsa yanason yafi qarfinsa,tsahon wasu mintuna tana neman qarasa gusar mishi da hankali don tacimma burinta dana kamal,tamkar qiftawar idanu taji an harbota daga saman gadon zuwa tiles din dake shimfide qasan dakin

"Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim" daya soma fadi tundaga zuciyarsa harta fito saman bakinsa yaci gaba da maimaitawa muraran a fili,ya rarrafa yasauko daga saman gadon yanaci gaba da maimaita addu'ar.



     "Kut!" Kamal dake jiran komai yasoma wakana yafara recording yafada yana miqewa zumbur daga kashingidar da yayi zuwa zama dafa'an,cike da mamakin ta yaya yayi escaping?,duk wata jijiya ta jikinsa sai data tsinke,ya hade hannayensa yana murza tafin hannayen nasa waje daya.



     zuciyarsa na wani irin tafasa,bacin rai yafito mishi muraran saman fuskarshi,kauda kanshi yayi sam ba tare daya dubeta ba tunda ya fuskanci babu suttura a jikinta,saiya sanya qafa ya tura mata kayanta,cikin rawar jiki dakuma tsoron yanayin da taga fuskarshi ta koma tasoma maida sutturarta,tana gamawa tasoma laluben qofar fita,tsawa ya daka mata mai qarfi

"Wacece ke?,daga ina kike?,ta yaya kika iya shigowa har inda nake?" Cak ta tsaya numfashin tsoro na fita da gudu daga qirjinta,lallai duk a baya yunqurin banza tayi tunda baima gane wacece ita ba,wani gumi ya karyo mata sanda taji yana takowa inda take tsaye saita kasa waiwayowa.



      Hannu ya sanya kamar zai shaqeta saiya fasa,yakuma fasa mata wata tsawar data sanya gumi yanko mata,daidai lokacin da mararsa tariqe saiya duqa riqe da marar tasa,da wannan damar tayi amfani tayi wuf ta bude qofar tafice kamar zataci da baka.



       Bai kuma bi ta kanta ba saboda yanayin dayake ciki,yaja jikinsa daqyar yaisa inda yake aje magungunanshi ya lalubosu,qara yawansu yayi akan qa'idar yadda akesha,saboda a yanayin da yake ciki baya jin idan yabi qa'idarsu ba zasuyi masa aiki ba.



       Minti biyu yaji kamar baisha komai ba,saiya sake jawo satches din yakuma ballan adadin na dazu yasake sha,cikin gaggawa dason tsaida halin da yake ciki ba tare da yasan silar shan wani abu bane yasa yatsinci kansa a yanayin ba,yadinga ballar maganin cikin fitar hayyaci yana sha har suka danganashi da ficewa daga hayyacinsa gaba daya,bai iya gane waye kusa dashi ko abinda ke faruwa a inda yake ba.



      Tun lokacin da kamal ya fuskanci abu ya kwabe yayi hanzarin tattara laptop dinsa yafice daga falon kada azeez yafito ya taddashi,don haka sanda minal tafito bata taddashi ba,itama bata wannan take ba,don haka bata tsaya nemanshi ba tafice itama tatari taxi tafada sai gida.



       Sai daya bada minti ashirin qwarara yasake dawowa cikin gidan,jin shuru babu alamu ko motsin azeez yasa yanufi dakinsa,sosai ya rikice ganinsa cikin wannan yanayin,ba ranshi suke so ba,sunanshi suke so su bata,darajarshi da matsayinsa kadai sukeso su amsa,cikin rudewa yakira number asibiti mafi kusa dasu,babu bata lokaci suka iso da motar asibiti suka daukeshi.


*****************



        Madaidaicin filine na musamman daga wanu sashe na sasasanta wanda aka qawatashi da abubuwan daukan hankali da more rayuwa iri daban daban saboda hutawar fulani aisha.



      Kamar yawanci lokuta haka yauma,tana kashingide cikin filin saman wani tattausan kilishi wanda aka zagayeshi aka kuma qawatashi da wasu irin manya da qananun filalluka wadanda ke dauke da zane da tambarin gidan sarautar kaisa,daga dama da hagunta kuwa barorinta ne wadanda suke amintattu a wajenta,wanda sukan zauna lokaci lokaci ayi hira sukuma bata labarai dakan debe mata kewa.



       Yauma hakance ta kasance,shugabar zaman wadda koda yaushe baka rabata da labarai a bakinta umma luba ce,murmushi kawai fulani aisha ke fitarwa,da alamu labarin da umma lubar take bata ya qayatar da ita matuqa.



      Daya daga cikin wayoyinta dake aje gabanta suka dauki qara,daya daga cikin barorinta data fi kusa da ita ta miqa hannu ta dauko kana ta rusuna cikin girmamawa tamiqa mata,hannu tasaka ta amsa tana duba mai kiran,abdulrashid ne,dan waziri musa adamu,hakanan tasamu kanta da miqewa tazauna sosai,barorinta suka dau kirari

"Allah ya taimaki uwar yarima,magajin maimartaba qwaya daya tilo" hannu ta daga musu alamun tana buqatar shirunsu,ta kara wayar a kunnenta bayan ta daga.



       "La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" fulani aysha tafada tana miqewa tsaye kamar wadda aka tsirawa allura,take suma dukka sauran barorin suka miqe suka tsaitsaya,donsu tabbatar tunda sukaga haka sun tabbata babu lafiya

"Allah yayi miki jagora yakula da lamarinki" umma luba tafada cikin nuna tsantsar kulawa da damuwa,saita sauke wayar daga kunneta tanajin zafi yana ratsata duk da iskar dake kadawa a wajen,a hankali takoma tana zama a inda tatashi bakinta yana furta

"Ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagisu"

"Amin ya Allah.....amin" suka kusan hada baki wajen fadar haka.



       Shuru ya ratsa wajen na wasu mintuna kanta a qasa tana maimaita maganar da abdulrashid ya gaya mata,shudewar wasu mintuna kana ta daga kanta a hankali tace

"Ina laure?...." Da hanzari ta matso tana zubewa a gabanta

"Gani ranki shi dade..."

"Ki gaggauta zuwa ki shaidawa jakadiyar mai martaba,a shaidawa maimartaba,akuma yimin iso inason ganinsa da gaggawa yanxu yanzu"

"An gama ranki ya dade....Allah ya huci zuciyarki" tafada tana miqewa da matuqar hanzari tasauka daga wajen tayi dan nesa kadan tadauki takalmanta tabace daga filin.



      Shurune yaci gaba da wanzuwa a wajen,kowa yashiga cikin nutsuwa da taitayinsa,umma luba ta matso gefanta,cikin salo da dabara tasoma magana cikin kalaman kwantar da hankali da sanya nutsuwa

"Na gode" fulani ta ambata tana dagawa umma luba hannu,da alamu taji dadin furucinta,saidai a yanayin datake ciki bata buqatar dogon xance.



      *_fulani adama_*




      A daidai wannan lokacin daga can cikin quryar dakin gadon wanda babu mai shiga ciki sai ahalinta ko yaran cikinta,a lokacin da take yunqurin amsa kiran koda gittawar tsuntsu bata amincewa barorinta abarshi yawuce ba bare bil'adama.



       Kirane daga qanwar maimartaba mahaifiyar kamal fauziyya mu'az kaisa,qaramin murmushi fulani adama tasaki,tun jiya taje jira taji daga gareta,kuma jikinta yana bata aiki yayi nasara,wanda indai hakan tafaru rabi cikin burinkanta sun soma cika,a duniya babu wadda ta tsare mata gaba da baya irin aisha da dukka abinda suka fito daga tsatsonta,har yaranta mata gani take suna samun soyayya daga wajen maimartaba fiye da nasu yaran

"Ya ake ciki?,ina fatan komai ya kammala" ta tambaya muryarta na nuna tsantsar jin dadi

"Inafa!,komai yana shirin kwabewa,yanzu haka yarima yana kwance gadon asibiti unconsciouse" tsaki taja tana jin sam wannan bai dameta ba,inda zai mutu ma salin alin da tafi kowa farinciki a duniya

"Ba wannan bane ya dameni,an samu nasara?"

"Ta ina fulani?,ya tsallake duk wani tarko" take fuskarta ta sauya,bacin rai ya mamaye zuciyarta,ta yaya?,wannan wanne irin yaro ne,dogon tsaki taja takatse wayar kawai ba tare data iya sake furta komai ba,saita kasa zama,tahau safa da marwa cikin dakin tanason baiwa kanta damar yin tunanin abinda yadace tayi.



      "Allah ya taimakeki,Allah yabaki yawan rai,zaishiga sallar la'asar,idan yafito ki taddashi a sassansa" miqewa tayi ba tare data ce komai ba,tanajin ba zata iya zama a nata sassan ba har zuwa sanda zaiyi sallar yafito.



       Daga nan bata sake tsayawa ba saidata dangana da ainihin bedroom dinta,ta canza shigarta,cikin qaramin lokaci tafito a fulaninta sak,ta wani sashen kuma gimbiya diya ga sarkin mali,a gaggauce tafito tabaro sashen nata zuwa sassan maimartaba qarqashin rakiyar mutum uku rak,suma suna zuwa wani shinge da babu mai shiga sai iyalan nasa suka juya suka koma suka barta.



       Kasa zama tayi cikin tashin hankali take kaiwa tana kawowa,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta qasar mexico,hankalinta a tashe yake qwarai,tana tsoron wani mummunan abun yasamu abdul'azeez din,abdulrashid yaqi mata cikakken bayani bare ta fahimci silar ciwon nashi.



      Tana jin takun shigowar maimartaba tayi hanzarin juyowa tana dubanshi,itama shi take kallo,dukkanin rauninta ya bayyana,har kamar idanunta ma sun tara ruwan hawaye,duk da basu kai ga zubowa ba.



       Yasan meke faruwa,hakanan yasan rauninta,dukkanin rauninta abdul'azeez ne,bata iya jurewa idan wani abu ya sameshi,saita nufeshi da sassarfa kuka yanason qwace mata,ganin haka shima yaqara sauri yatareta,tafada jikinsa saita saki kuka mara sauti,bayanta yake shafawa a hankali cikin sigar lallashi ba tare da yace komai ba,tsawon wasu daqiqu sannan yace

"Duka ina jarumatar dana sanki da ita ayusher?,ummm..." Muryarta can qasa saidai duk da haka zaka fuskanci tana kuka ne tace

"Ina tsoron ko wani keson cutar min dashi ranka yadade,bisa alamu azeez baida lafiya sosai" saiya dagata daga jikinsa yana duban fuskarta gamida girgixa mata kai

"Um um,ko kadan aysha,nace kidaina kawo ire iren wadan nan tunanin a ranki kan abdul'azeez,yanzu dubi fuskarki....sam.hawaye bai dace da fuskar saraki irinki ba" dole yanayin yadda yayi maganar ya sanya murmushi yakubce mata,kai kace ba shine qasaitaccen sarkin nan bane ma'abocin kwarjini da izza,sai tasa tafin hannunta tana share hawayen daya bata mata fuskar,kana yajata saman daya daga cikin kujerun ya zaunar da ita

"Yanzu me kikeso ayi uwar abdul'azeez?"murmushin yasake kubce mata karo na biyu,yasan takanta sosai,saita duqar da kanta tana murmushi ba tare datace komai ba

"Anaso aje wajen yarima azeez aga halin da yake ciki ko?" Ya bata amsar tambayar da kanshi yana dage gira,kaita jijjiga da hanzari harsai da murmushin shima yakubce masa

"Ki shirya gobe ku wuce keda duk wanda kika zaba" hannayensa ta kama cikin murna tariqe qam

"Na gode your royal highness....Allah yaqara girma,yajiqan magabata" cikin lumshe idanu dajin dadin addu'arta yace

"Ameen"

"Sai alfarma daya da nakeso ayimin" tafada tana wasa da hannunshi da har yanzu bata saka ba

"Uhmm,inajinki" shuru tadanyi na wasu sakanni sannan tace

"Inason maganar rashin lafiyan azeez yazama asirtaccen zance Allah ya taimakeka ina neman alfarma" shuru yayi nawasu sakkani yana kallonta murmushi nafita saman fuskarshi ba tare data sani ba saboda idanunta suna qasa,yadade da sanin nata yarda da kowa ba indai akan Abdul'azeez ne

"Wai...dani da abdul'azeez wa akafi sone" da sauri ta daga kai tana ware idanu,dariya nason qwace mata,saiya ci gaba da kallonta yana cewa

"Yes,inaso inji" hannu tasa kamar zata rufe bakinta saita fasa tasoma magana

"Kaine maqyanqyshin abdul'azeez fa,kaga dole taka soyayyar ta dara tashi,albarkacin soyayyarka shi kansa yake ci" murmushi ya fidda,aysha badai iya nunawa miji qauna ba

"Um um....kadda nasaki jiki fa,ki gadi gaskiya anya abun cikin qwai baifi qwan dadi ba" kanta tadora saman kafadarsa tana dariya

"Ko kadan qwan gaba dayanshi yafi dadi" ana tsaka da wannan aka nemi izinin shigowa falon da suke,yasan koma waye wanda yashafi iyalinsa ne don haka yabada izinin shigowar.



       Fulani saratu ce,cikin shiga ta alfarma ita dinma,amma haske aysha saiya dusashe fiye da nata rabin adon,ganin aysha a wajen saita tsuke fuska ta qarasa shigowa da sallama,daga shi har ayshan kowa na mazauninsa daban saboda jin anason shigowa,ya amsa sallamar yana marabtarta kamar yadda yasaba yima matanshi,ta amsa masa amma sam fuskarta babu wani walwala ko fara'a,abu daya ne dataji dadi shine tadda aishan datayi a wajen,hakan yayi mata daidai,zatayi maganganunta son ranta,tunda dama ganawar ta nemi yinta ne saboda yaron aishan

"Magana nazo muyi dakai Allah ya taimakeka"

"Ina saurarenki saratu,Allah yasa lafiya".



       Gyara zamanta tayi tana sake hade fuskarta,kana a fakaice ta watsawa aisha harara wadda batama san tanayi ba

"A gafarceni ranka yadade,magana ta gaskiya ce nazo na gaya maka,duk da hausawa sunce daci gareta,tuba nake ranka ya dade kan maganar walida ce..." Saita danyi shuru tana maida numfashi,yayin dashi kuma yaci gaba da kallonta dakuma saurarenta ba tare daya ce komai ba

"Da yarana,dana adama dana aisha ina tsammani dukkansu Æ´aÆ´anka ne,hakanan kowanne yana da haqqi akanka,koda wanne irin jinsine,bayan haqqi da suke dashi suna buqatar a daidaita su dayi musu adalci kan komai a cikin gidan nan....zancan tafiyarta makaranta,ranka yadade da farko baka wani tsaurara ba kace zaka yi tunani da shawara,amma tunda abdul'azeez yazo yatafi kace fau fau babu wadda zatabar qasar kaisa da maqotanta tafita a nijeria zuwa baquwar qasa karatu,Allah yabaka yawan rai,caa nake shi wanda aka nema shawarar yabayar a yanzu haka zancan da mukeyi baya qasar nan,sai daya zaba qasar da yakeso sannan yatafi,a irin wannan ranka yadade yaran zasu dinga ganin kamar ba'a musu adalci saboda su yara matane,idan batun jinsine babu jinsin da bazai lalace ba idan yaso,shi kansa akasan me yakeyi a can din......" Da sauri aysha tamiqe jin tazo inda ba zata iya jurewa ba,kuma batason sanya baki cikin maganar ko digo saboda girmamawa gashi maimartaba,don haka tasoma takawa zata fice daidai sanda sarki abdallah ya dagawa saratu hannu yana dakatar da ita,bataji me yake ce mata ba itadai ta sanya kai tayi gaba abinta.



       Tana tafe a hanya tana mamakin abinda ta tsarema matan,ta tabbata banda kariyar Allah,da kaifin wayo da basira da Allah yabata da tuni sun gama batar da ita itada irinta a tarihin masarautar kaisa,tasan tana takatsantsan da bata duk wani shirinsu sun sani ko basu sani ba,amma ko sau daya bata taba yarda ta jefi yaransu da wata mummunar kalma ta batanci ba,tunda tasan duk inda za'aje azo yayyene ga nata yaran,kuma jinin abdallanta ne.



       A ranar tagama tsara komai na tafiyarta,takuma zabi mutanen da zatayi tafiyar  dasu,ta basu umarnin kowa yashirya,don a sassanta duk wanda zasuyi tafiyar zasu kwana,duk da amintattunta ne bata yarda su kwana akowanne guri ba sai a nan,cikin murna da zumudi kowanne yasoma shirinsa a sirrance ba tare da kowa yasan meke faruwa ba bare susan inda za'a din.



      **************



      "Alhamdulillah" bilkisu ta fada tana sauke ajiyar zuciya lokacin data shiga soron gidan nasu,don bata tsammaci zata ita kawo kanta gida ba daga makaranta,duba da irin doguwar tafiya da tazarar dake tsakanin gidan nasu da makarantar saboda azababbiyar yunwar dake sakadar cikinta,wanda rabonta da abinci tun daren jiya wanda shima wanda tasamo ne daga gidan umma luba suna yanyana sukaci ita da qannen nata.



       Sosai ta ware hancinta tashaqi qamshin soyayyar miyar dake tashi har soron gidan nasu,wanda kanaji ko ba'a gaya maka ba ta wadatu da nama,qamshin na shiga har cikin hanjinta taja qafafunta ta shige tsakar gidansu.



       Sauka idanunta sukayi kan varender dake qofar dakin amaryar baban nasu wadda ake kira da jummai,itace zaune kan kujera 'yar tsuguno,tasha kwalliya da wata atamfa tata koriya shar,fuskar nan tasha jar hoda da jan jambaki wanda ada ake kira da kanta kile,idanun nan badau da kwalli ga jagira data ja layi daya a kan gashin girarta,idan gidan karuwai kashigo saika rantse magajiyar karuwai ce,gabanta rishonta ne tanata juya miyar data budade hancin kowa dake cikin gidan.



      Dagakai tayi tana duban bilkisu ba tare data amsa sallamar da takeyi ba,zata iya cewa tun zuwanta gidan babu wani abu qwaqwqwara daya taba hadata da ita,tundai ita bilkisun ba mazauniyar gida bace,koda ace mazauniyar ce sam bata da kwarafniya,saika wuni a gidan bakaji muryarta ba,koda kajinma to fada takewa qannenta kan wani abu da sukayi wanda ba dai dai ba,saika taka mata ka zubar mata bata daga kai ta kalleka ba bare ta nuna damuwarta,duk da ta tsani raini da wulaqanci abu biyu da ba kasafai take iya juresu ba,hakan yasa takan qauracewa sabgar jama'a ainun sai idan ta kama.



       Sai data leqa rumfar umma katti tashaida mata ta dawo yadda tasaba,duk da cewa ba wani magana mai dadi take gaya mata ba,wani lokacima takan hantareta ne kota jefeta da baqar magana

"Ke da'alla can,naji kin dawo saime?,wata uwar kike tsinanamin da zaki damweni dakin dawo?,'yar wahala wadda kullum take qarewa a gantalin neman boko,bokon da nake da yaqinin bazai tsinana miki komai ba,idan kinso in kika tafi makarantar karki dawo,amiki daki acan,ina nan ina fama da baqincikin ubanku daci dakai da tufatar dakai amma kin dameni da wani umma nadawo,mtseeww" haka take balbaleta da masifa dakuma mita duk sanda 'yan wulaqancin ke kusa,ko kuma wani abu ya hadosu da babansu,itakam takan cika da mamaki a kullu yaumin,yau koda ace umma kattin bata zauna da mahaifiyarta sunsan juna ba bai kyautu tadinga mata haka ba,ta tsammaci yadda suka zauna da mahaifiyarta takuma yi haquri da ita itadin me riqeta ce?,bata mantawa sanda mahaifiyarta keda rai,yaran babansu da iyayensu suka fita suka barsu sun kusa biyar a sannan,mamanta itake musu komai cikin kudin da ake aiko mata daga gidansu,yadda take kula da bilkisu haka take kula dasu,bata barsu sunyi kukan rashin komai ba harsai data koma ga mahaliccinta,shi yasa har yanzu duk da basa zaune qarqashin mahaifinsu duk wanda Allah yakawo gidan zai mata alkhairi komai qanqantarsa,saboda tunawa da abinda mahaifiyarta maimunatu tayi musu.


      Babu wanda yatankawa wani tsakaninta da lami bayab sallamar datayi har bilkisun tawuce dakinsu,dakin babu kowa yadda ta tsammata sun wuce islamiyya,ta soma rarraba idanu tanason taga me sukaci,data daga kwanukansu saitaga burbushin garin kwaki,aje kwanukan tayi tasaki ajiyar zuciya,duk da tasan shita bar musu tayi tunanin basuci ba sun aje mata,tunda idan suka fuskanci bataci abinci ba saisuqi ci su aje mata su su haqura.



       Tana fidda kayan makarantar tana tunanin kudin extra lesson da za'a soma yi musu saboda shirye shiryen zana jarabawar waec da neco,komai da zata buqata an riga da an biya amma babu kudin extra lesson,wanda tasan cewa anty zuhriyya batasan zai taso ba,da babu shakka saita bayar,wasu qwalla masu dumi suka taru a idanunta,wanda bata iya dannesu kulli yaumin idan tatuna da qanwar mahaifiyartata wadda ita ta maye mata gurbin mahaifiya,kullum tatashi daga shimfidarta da safe tana tashi ne da begenta,haka nan tana kwanciya ne da tsananin kewarta da burin ganin shekarun sun cika ta dawo zuwa gareta.



       Hakanan jiki a sanyaye ta daura zani tafita ta watsa ruwa,tadawo ta shirya duk da yadda yunwa ke sassaqarta,amma dole taje gidan aikinta.




*_Shin kina ko kana sa sha'awar koyon ilimin ICT?_*


*_Ko kuna da sha'awar yadda ake hada cartoon?_*


*_Ko kana da sha'awar yadda zaka bunqasa kasuwancinka ta hanyar online?_*


*_Matsalarki ko matsalarka rashin makarantun da zasu koyar dake/kai ilimin computer ta fannnin larabci?_*


*ALBISHIRINKU KANAWA*


*_Kukanku ya qare,matsalarku tazo qarshe,shahararren kantin nan na yanar gizo wato RAHAMALLS yazo muku da makarantar koyon sarrafa computer a sauqaqe wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI)_*



_Sun tanadarmuku qwararrun malamai wanda zasu koyar daku bisa tsarin da kuma cikakkiyar qwarewa ta yadda zaki fahimta fiye da yadda kuke zato_




*ga masu buqatar aji na musamman har cikin gidajensu,makarantar ta shirya tsaf don baku darussa har cikin gida*


*sannan akwai tsarin ajujuwa na musamman bisa yanar gizo wato(online classes)*


*kaidai maza garxaya ka tuntubesu akan wanannan lambar waya*


08033990209



*_akwai ragin kaso hamsin cikin dari na kudin registration ga kowanne dalibi_*👌ðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½Ã°Å¸‘ŒðŸ½

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: *S R B*


*_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,gamai buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadan nan lambobin kai tsaye_*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



15




       Har zata fice taga alamun baban nata yana dakin amaryartashi,wanda dama yawancin lokuta anan yake wuni abinsa akwance,sai yamma zuwa dare zai fita nemo mata na cefanen gobe,don sudin tamkar masu haya a gidan suke,wadanda babu wani haqqinsu dake rataye saman wuyanshi,bai damu da cinsu shansu suturarsu ko lafiyarsu ba,yabasu muhallin zama ne kawai,wanda shima yakan yanka lokaci zuwa lokaci duk sanda yatashi wani zarafi na aurensa.



       Shawartarta zuciyarta tayi,yaudau karon farko a rayuwarta,lokaci na farko tunda tayi wayo tsakaninta da mahaifinta,ta waiwaya ta duqa gabanshi ta roqeshi ya mata wata hidima qwaya daya cikin rayuwarta mana,takai minti goma tana shawara da zuciyarta daga qarshe tayi qundun bala takoma tataka zuwa varender da tunda aka ginata bata taba koda gogar gininta bare akai ga takawa.



       Bakin qofar dakin ta tsaya tayi sallama a nutse,yana daga ciki tajishi yana amsawa

"Waye ne?,waye a nan?" Yasake fada

"Bilkisu ce" ta amsa a sanyaye,tanajin alamun tashinsa daga kwanciya da alama akwance yake

"Mai gado,shigo mana,yaukin gama baqin ran naki kenan zaki shigo kiga dakin uwartaki" yafada yana kakkabe shimfidarsa,batabi ta wannan ba tacire takalmanta dasukayi qasa sosai saboda dadewa dakuma tafiya tasanya kai falon.



      Yana zaune saman kujerar da aka qarawa laushi da bargo,yayin da lami ke zaune gefansa tana kallon bilkisun harta shigo,kai tsaye ta isa gabanshi ta duqa tana gaidashi ya amsa yana jiran jin me zatace,cikin sanyinta da nutsuwarta tace

"Baba....zuwa nayi na roqi alfarma wajenka,karatunmu yazo gangara,zamu zana jarrabobi guda biyu,to kowacce tana da muhimmanci wajen dalibi,hakan yasanya aka ware mana lokaci daban wanda za'a dinga mana wani karatun bayan wanda muke a marantar,to akwai kudi da kowanne dalibi zai bada saboda malamai zasu dauko qwararru wadanda zasu dinga mana wannan karatun,za'a dinga biyansu ne...." Saita tsagaita tana tunanin qarasa gaya mishin,zamansa yagyara yana washe baki

"To yanzu cewa akayi nazo za'a daukeni kenan nima a dinga biyana?" Da mamaki ta daga kai ta dubeshi,amma saita sadda kai tana girgiza kai

"A'ah,cikin kudaden da anty zuhriyya tabiya babu kudin wannan,shine nace don Allah ko zaka taimaka ka biyamin".



      Tsaf ya hade girarsa yana dubanta

"Kai,amma maigado bansan baki imani ba saiyau,yanzu don Allah keda kike fita aiki kullum yaumin nida kowa yasan kasuwanci yanzu ya durqushe sai lahaula wala qawwata illa billah nizaki duba kice nabaki wasu kudade?,yo aini da kikayi sallama na zaci anmiki albashi kika dubi halin da nake ciki kikazo kibani wani abu a ciki nima,gaskiya maigado kin bani mamaki,hankalinki ashe a qauri yake....to bari na gaya miki zance na gaskiya,ni yanzu bana maganin kome,kinganta nan lami baiwar Allah couse couse takeson ci amma haka na bata haquri shinkafa take dafawa yanzu....shawarar dazan baki idan kin samu ki biya,idan bakisamu ba ki tattara ki haqura da karatun,dama ni ya isheni" tabe baki lami tayi tana dora qafarta daya kan daya

"Uhmmm....ni bilya ma baikenka nagani,kana da zuqeqiyar yarinya kamar wannan amma ka sakata a gaba kanata ciyar da ita babu gaira babu dalili,tun farko aida kudin makarantar ka karba kayi mata kayan daki kasamu wani mai damshi damshin ka aurawa,qila da tuni yanzu yanzu ya biya maka hajji ana kiranka da alhaji" yatsanshi ya ciza yana kada kai

"Kumafa wallahi kin kawo shawara lami,dadina dake hankali,kinga waccar dosoruwar bata taba bani irin wannan shawarar ba wallahi,to amma yanzu ai tunda takusa gamawa kudin da sukayi sauran basu taka kara sun karya ba....".



      Miqewa kawai bilkisu tayi ba tare data tsaya ta qarasa jin cecekucen dasuke ba,ta sanya takalmanta tafice daga gidan tanajin iska na yawo da ita.



      Tana tafe a hanya amma sam hankalinta baya tattare da abunda ke gudana kan hanyar,tayi matuqar nisa a duniyar tunani,wani irin quntata zuciyarta tayi,tanajin hucin hakan har saman fuskarta,kukan zuci take mai ciwo,wanda yafi na fili radadi da yankar zuciya,tana jajantawa yara da yawa cikin fadin duniya masu mahaifi irin nata,tayi amanna marayu da yawa sun fisu gata,marayu da yawa sun fisu daraja da kima,ya ilahi mahaifinsu meya hau kanshi haka?,Allah yayi masa daraja da baiwar 'ya'ya amma shi baisan da hakan ba,meye marabarsa da matacce?,wanne abu zasu iya adarwa kan gata da wani abu mai muhimmanci da uba ya yiwa 'ya'yansa,dame zasuyi tutiya?,da ire iren wadan nan tunanukan ta qarasa gidan umma luba.



      Taje ta sameta a hargitse da tulin hirarta,bakinta har kunne yau Allah ya yarda zata daga daga qasar nijeria masarautar kaisa zuwa mazako,duk da yanayin da take ciki hakan bai hana murmushi subucewa daga fuskar bilkisun ba,na yadda tafadi sunan qasar,dakuma yadda taketa lodar kaya kamar zata ta shekara a can

"Mexico ake cewa umma....sannan wadan na kayan da kika diba ai sunyi yawa,idan zaka wata qasar ba kaya kake loda ba,idan sati biyu zakuyi kala bakwai ma ya isheki" baki tasaki tana kallon bilkisu

"Ke 'yar nan,tafiya cefa ta alfarma,ga qafata ga qafar fulani fa,a qalla muyi sati biyu ko uku" murmushi takuma yi

"Duk da haka umma"

"To yo ai gwara da kikazo,don ni niyyata iya adadin kwanakin zan diba harda qari ma,matso ki zabarmin" tafada tana bata waje.



       Anutse ta shirya mata komai,hakan kuma yayi mata dadi har tace

"Bude store dina ki daukar muku taliya goma,macaroni goma,shinkafa kwano biyu,samambita yakusa qarewa dauke ragowar kwa dafa kuci keda qannenki" sosai hakan yayiwa bilkisu dadi,tasan da yardar Allah bazasu galabaita ba sosai.



☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



*_MEXICO CITY_*




      Tsaye takan gaba gadon da aka kwantar dashi,hannayenta saman kanshi idanunta qur akan fuskarsa,kana ganinsa kasan cewa lallai da gaske bashi da lafiya sosai,har cikin zuciyarta takejin ciwon nashi tamkar ita dince babu lafiya,sakin ajiyar zuciya tayi tana sauke hannun nata daga saman kanshi kana ta juya a hankali tafice daga dakin zuwa office din likitan don suyi magana,tana son jin cikakken bayanin abinda yake damun azeez din.



         Dukka hankalinta yana kan likitan lokacin dayake rubuce rubuce jikin file din azeez,harya gama kana ya daga kai cikin harshen mutanen qasar mexico yasoma mata magana,saita sauya harshe zuwa turanci

"Am sorry" ya fada yana murmushi,don shaf ya mance da cewa ba 'yar qasar bace,saiya koma mata bayani zuwa yaren englishi

"A yanayin halittar yaronki a bincinkenmu mutum ne mai matuqar buqata,wanda baya biyan buqatarsa takowacce hanya dazai rage yawan ruwan halittar dake taruwar mishi,a maimakon hakan saiyake amfani da wasu qwayoyi da zasu gusar masa da dukkan wata sha'awa da zata taso mishi,wanda sannu a hankali suka zame mishi jiki suka bi jikinsa,har aka kai matakin da basa iya mishi aiki sosai a jikinsa,saiya koma yin allurar da ake ta jijiya,wadda tafi qwayoyin saurin isa inda akeso.....to,bayan hakan gaba daya,bamu sani ba tunda bama tare dashi,amma a shekaran jiya an kawoshi ranga ranga,mun karbeshi mun kuma bashi taimakon gaggawa,wanda daga qarshe bincikenmu ya tabbatar mana da cewa yasha maganin ne daya wuce qa'ida,wanda har hakan yanaso ya masa illar,illar da idan ba aure yayi ba to komai zai iya faruwa dashi".



       Shuru yayi yana maida numfashi,cak tunanin fulani aysha ya tsaya,don ko kusa ko alama bata taba kawowa kanta wannan ba cikin jerin abubuwan daka iya zama sila ko sanadi na ciwon azeez din ba,mganar likita tasake katse mata tunaninta

"Saboda an kai matakin da magungunan sun daina aiki a jikinsa,banda ma yana da qarfin jini da tuni sun kashe masa sha'awarsa gaba daya,a yanzu kuwa idan yaci gaba da shansu komai yana faruwa dashi" saita lumshe idanunta tana jin maganganun likita na sauka É—ai É—ai cikin kwanyarta

"Godiya muke likita" ta fada a taqaice tana miqewa a nutse tabar office din.



       Duk da sunyi waya maimartaba amma bata shaida masa asalin ciwon dake damun azeez din ba,kamar yadda take da yaqinin daga ita sai abdulrashid suke da masaniyar haqiqanin abinda yake damunsa da abinda yayi silar shigarsa cikin ciwon,ta fannin abdulrashid sam baiyi mamaki ba,duk da cewa ba qasa daya suke karatu ba amma yasan azeez din na yawan ta'ammali da magungunan duk sanda lamura suka ci tura,don yana yawaita zuwa wajensa akai akai musamman qarshen mako,kamar yadda shima azeez din yakan ziyarceshi duk lokacin daya bushi iska.



       Duk da cewa su abdulrashid din suna tsaye a kanshi amma kasa tafiya tayi masauki anan dakin da aka kwantar da azeez din ta kwana,duk motsi ko wani juyi da zatayi idanunta na kanshi tana tunanin mafitar daya kamata ta sama mishi mafi sauqi kuma cikin sirri.



      Cikin dare yafarka sau daya,suka hada idanu yasaki murmushi,yana tason ya mata magana bacci yasake rinjayarsa,bai sake farkawa bai sai washegari da asuba.



       Sati guda cif ya kwashe cikin yanayi na jiyya kafin yasoma watstsakewa,a kwana na goma kuma ya watstsake sarai,har zuwa sannan bata nuna mishi tasan komai game da ciwon nashi ba,hakanan basuyi magana dashi ba,saima ticket data siya musu na tafiya qasar mali,wanda ta diba musu zasuje suyi sati biyu a can,badon komai tayi wannan tunanin ba,tayi hakanne don zuwa ta shawarta da makusanciyarta abokiyar shawararta kan lamarin azeez din,don batason ta koma kaisa ba tare da wata qwaqwqwarar mafita ba da zata zama maslaha ga rayuwarshi.



        A sannan saida ya kwana uku kamal yaje dubashi,da sunan cewa baya garin da suke makaranta sun turashi wani bincike kan course din da yake a wani gari daban,tunda yashigo azeez din ya kafeshi da ido,hakanan yaji ya dora alamun tambaya a kanshi,duk da cewa bai dora dukkanin zarginsa da zato akan kamal din ba,amma haka kawai yanayin daya nuna yakejin bai masa ba.


*****************



       Karfe goma da rabine na safiyar ranar talata,cikin falon alfarma dake babban sashe da aka tanadarwa fulani aisha cikin masarautar qasar malin wadda take qarqashin sarauta da jagorancin mahaifinta.



       Duk da cewa tayi rashi na uwa amma hakan sai bai sauya komai game da gata dakuma qimarta cikin gidan na,matan uban suna mata kallo ne irin wanda sukewa 'ya'yansu.



       Su biyune tak cikin falon,tunda sukazo anan tasauka ita da azeez din,saidai akwai tazara sosai tsakanin dakinshi da nata,yayin da 'yan rakiyarta suma suke wani sashe na musamman maicin gashin kanshi.



        A gaban fulani saratun yake zaune saman lallausan carfet da yayiwa falon qawanya,yana sanye da wando wanda yawuce qaurinsa da kadan bai kuma kai har can qasa ba,farine tas sai rigar jikinsa wadda ta kasance ruwan toka me haske.



      Farfesun kayan ciki yake sha a hankali da cokali,kana dubanshi kasan yasamu lafiya dakuma cikakken nutsuwa,yayin da fulani aysha ke jefa yankkiyar kankana a bakinta duk da cewa safiya ce.



        Duk wani motsinsa yana kan idanunta har zuwa sanda tagama shan tata kankanar ta aje cokalin da farantin,tazauna sosai cikin wani salo dake karantar damai kallo tsantsar izza da isar mulki dake yawo a jininta.



      Tafin hannayenta ta hade waje guda kamar yadda tashigar da yatsunta cikin na juna, anutse ta furta

"Me yasa ka yanke shan qwayoyin da zasu iya kassara maka rayuwarka ta d'a namiji har abada azeez?" A bazata tambayar tazo masa,don bai taba tsammanin maganar ta isa kunnenta ba,da yaji shuru yayi zaton likitan ya saya komai ne,saboda haka saiya nemi ya qware da da romon farfesun,har sai daya aje bowl din hannunshi,ya nemi ruwa ya kwankwada sarai sannan yaji dama dama,ya aje gorar ruwan yana maida numfashi,gami da tattaro irin amsar da zai bata saman harshensa.



      Ya daga idanunsa a hankali ya motsa bakinsa da zummar yin magana

"Dakata....bana buqatar kalaman kariya daga bakinka,ka kasa jurewa azeez,ka gaza ka daure ka isa ga matakin da nakeso ka isa a duniya.....,ba yadda zanyi dakai,nawa shine inyi iya abinda zan iya,sauran naka ne,tunda rayuwarka ne,dole saida gudunmawarka komai zai gudana yakuma tafi dai dai yadda ni da nake gefe na tsara maka" bashi data cewa sam,tunda komai yariga ya bayyanar mata,sai yayi shuru yana saurarenta kawai,idanunsa saman kofunan da suka yi amfani dasu yanzu.



      "A matsayin da kake kai yanzu,dole ne a matsayina na uwa na sama maka mafita ta dukkan hanyar da zata kasance mafitar ce a wajenka....." Sai tayi shuru da alama magana mai muhimmanci zata fada,yayin da abdul'azeez yayi shuru yanajin wani sanyi yana ratsashi tun daga saman kanshi zuwa qafafunsa,wani nauyi na raguwa daga qirjinsa,fata sa kawai shine kunnuwansa su jiye masa kalaman amincewar ammi na yarjewarta kan yaje yayi aure

"Zakayi aure abdul'azeez" shuru tasake tana qara tariyo dukkan abinda suka tattauna da shawarar data bata cikin daren jiya,wanda taji ta gamsu da shawarar dari bisa dari,wata qaqqarfar ajiyar zuciya yasauke,wani munafukin qaramin murmushi nasan ratsowa ta saman miskilar fuskarsa ya bayyana kansa,saidai ya hana hakan faruwa,sai taci gaba da cewa

"Zakayi aure amma ba irin auren dana tanadar maka ba,zakayi aure amma AUREN KASHE GOBARA".



        Da sauri yabude idanunsa fes kan ammin don bai fahimci abinda take fada ba,sam bai fahimci hausarta ta qarshe ba,yaci gaba da kallonta kamar yadda itama take kallonshi,tasan cewa yashiga duhu ne kuma yake da buqatar qarin bayani,tasan kuma dama zai buqaci hakan.



      Sake gyara zamanta tayi tana sakin ajiyar zuciya,itama idanunta a kanshi tace

"Zakayi aure abdul'azeez kamar yadda buqatar hakan tataso,saidai ba safwa zaka aura ba a halin yanzu ba" kadan fuskarsa tasauya saboda ta sake jefashi cikin duhune,maimakon yafita zuwa haske saiya sake shigewa cikin duhun

"Eh,a yanzun zan aura maka yarinyar da xaka zauna da itane iya tsahon adadin zaman rayuwar karatunka harka kammala,sannan daga bisani zaka auri safwa a lokacin da muka tsara ni da mahaifiyarta,irin auren da nake buqata,irin auren da mukayi tanadi dakuma buri,ina fatan ka fahimci abinda nake nufi?".



      Gaba daya sai komai yazo mishi a baibai,dukka bayananta suka cunkushe mishi waje daya,kamar ya fahimta abinda take fada wani sashe kuma sai yakejin kamar bai fahimta ba,ya hadiye yawun bakinsa da qyar yana duban ammin,yamotsa bakinsa zaiyi magana ta daga mishi hannu tana miqewa

"Ba shawararka nake nema ba,wannan shine kawai mafita azeez,no way face mubi wannan,so kawai abinda yarage shine kajira,zan shiga ciki wajen maimartaba..." Daga haka tasoma takawa tafice daga falon.



       Wani zazzafar iska yafitar daga bakinsa ya nutsa dukka yatsunsa cikin sumar kanshi yana yamutsawa,kanshi na wani irin yamutsawa.



       Me yake shirin faruwa ne?,saiya miqe ya koma saman kujera yakwantar da bayansa sosai a makarar kujerar yana ci gaba da barin idanunshi a rufe,sarrafa maganganun ammi yake yadda zasuyi daidai da qwaqwalwarsa da kuma tunaninsa

"Auren kwangila?,ko auren yarjejeniya?,ko kuma me?" Yadinga maimaita tambayar kansa shi daya cikin makeken falon.

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: *S R B*


16


*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,gamai buqatar mallakar nashi saiya tuntubi wadan nan numbers din_*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_______________________________


*Ina mata 'yan birni 'yan qwalisa masu burin sanyaya gidansu da daddaɗan ƙamshi mai tsayawa a zuciya da ruhin maigida?,shin kina da labarin ANNUR PERFUMES?,wadanda bayan sun gyara miki waje da ƙamshi su kuma gara miki ciki da kayan matsi?sannan su rabaki da infection?,WOHOHO wani kaya sai amale,ANNUR PERFUMES sun shara wajen saida*


*HADADDIYAR HUMRA*

*KWALACTURE*

*TURAREN WUTA*

*MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)*

*DECORATIONS NA TSINTSIYA*


*_UWAR GIDA DA AMARE KUZO GA NAKU_*


*_MAZA GARZAYA GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!_*


*KO A NEMESU TA LAMBOBIN WAYA KAMAR HAKA*


07086341096 ko 07069037534


_muna maraba da masu siyan ɗai ɗai ko sari_🤗🤗


*INGANCI KYAU RAHUSA DA KUMA INGANCI SAI ANNUR PERFUMES*👃ðŸ½

________________________________


16




      Kusan ranar wuni yayi shi kadai a sashen da aka saukeshi yana son daidaita tunaninsa da maganar,yanason aunata kan ma'auni da mizanin dacewar hakan ko rashin dacewar hakan,dukkan wasu 'yan uwa dakeson ganinsa dayi masa sannu babu wanda ya baiwa damar ganinsa,ya zabi zaman shi kadai wuni guda sur.



       Sai daga bisani ys tabbatar da cewa yana buqatar abokin shawara,waye a ciki?,sufyan ko abdulrashid?,daga qarshe yaji zuciyarsa tafi amincewa da kiran abdulrashid din,shi tuni yakoma kwana biyu da zuwansu mali.



        A iyakacin abincin da aka jera masa babu abinda ya iya sha sai tattacen gamayyar ruwan kayan marmari,bayan sallar isha'i yasamu yakira abdulrashid din.



     Cikin nutsuwa da aminci ya fayyace masa duk abinda ake ciki,bayan shuru na wasu 'yan mintina kana yace

"Abdul'azeez,a rashin uwa akanyi uwar daki,babu wata hanya ko mafita data rage banda ka karbi wannan tsarin,tunda kana da yaqinin cewa matuqar akaci gaba da tafiya kan wannan tafarkin komai zai iya faruwa,ina ganin kawai ka bada dama shine"

"Amma....abdulrashid,mai martaba fa baisani ba bazai kuma sani ba a tsari na ammi" shuru yasake yi yana jinjina kai

"Matuqar yasani din kaima kasan dukka hakan ba zata taba faruwa da amincewarsa ba" shuuru kowannensu yasake yi kana daga bisani yayiwa abdulrashid din sallama saboda har yanzu yana da buqatar kadaici har zuwa yanzu.


***************


      Ko cikin gidan kebantaccen wajene da babu wanda ke shigarsa sai an lamunce maka.



         Fulani aysha ce zaune saman daya daga cikin kujerun dake wajen,hannunta riqe da wayarta,da alamu magana take mai matuqar muhimmanci,don ta bada dukkan hankalinta ga wayar.



      Bayan tagama sauraran dukkanin bayanin aminiyartata saita sauke ajiyar zuciya

"Amma inda nake ganin matsalar take saudat.....inda zan samu yarinyar da zata dace da ra'ayin azeez,kinfi kowa sanin halayyar yaronki,donko safwa ma ke zaki bawa wani labarin yadda aka qarke,inason komai yazama cikin sirri,inason yazama tamkar auren sirri tun daga qullashi har zuwa sanda zai qare,kin sani sarai muna tsakiyar magauta da abokan adawa,kowanne yazuba idanu yana son ganin bullar wani abu da zai riqa wajen bata rayuwa da duk wani ci gaba da daukakarmu".



       Shuru hajiya saudat tayi tana dan tunani kana ta amsa

"Haka zancenki yake,saidai ni a anawa ganin samun yarinyar bazai zama wani abu mai wahala ba,ta fanni daya ne za'a samu yarinyar da komai zai tafi mana dai dai,ba tare da an samu wata matsala ba,ko daga baya aje ana jeka ka dawo,za'ayi mai gaba daya ne,kuma komai bisa yarjejeniya da amincewar iyayen kansu da ita yarinyar..." Sai tayi shuru tana sauraren fulani aisha,wadda dukka ta qagu taji ya abun yake

"Ke nake saurare saudat,idan na fahimceki kamar kinason kice da farko dole yarinyar tazama diyar masu qaramin qarfi kenan marasa hali?" Kai ta gyada kamar tana kallonta

"Tabbas haka nake nufi"

"To amma ta ina zamu samu kenan?"

"Kina da amintattu aisha,wadanda suke kusa kuma suke rayuwa tare da talakawan qasar kaisa,a nawa tunanin....a cikinsu idan kika basu asirtacciyar cigiya to ba shakka za'a dace" murmushi ne ya kufcewa fulani aisha jin duk wani qulli ya kwance,har farincikin hakan ya bayyana saman fuskarta

"Qwarai qwarai aminiyata,wannan tsarin yayi,hakan kuma za'a zartar.....zan kiraki"

"Ohk....sai munyi waya"

"Ma sha Allah" ta fada tana sauke wayar daga kunnenta murmushi na shimfide saman fuskarta.



      Tabbas idan tabi wannan tsarin komai zaiyi dai dai,hakanan komai zai tafi yadda ya kamata,saita miqe tana takawa cikin wajen a hankali tana sake zurfafa tunaninta kan yadda zata tsara komai bisa basira da fikra gamida kaucewa idanun 'yan adawa,yayin da wani sashe na qwaqwalwarta yasoma lissafo mata mutanen da zata tuntuba cikin amintattun nata wanda tasan ba zata samu matsala ba haihata haihata.......

_tofa masu karatu,ba'a fara wasan ba,muje zuwa_.



****************



       Satinsu uku a mali azeez yakoma bakin karatunshi,yayin da fulani ayshan itama ta tattara tadawo nigeria.



        Sai data huta sosai sa'annan ta buqaci ganawa da barorin nata,cikin matuqar sirri da takatsantsan,mutum uku ta kira a cikinsu harda umma luba,da zummar idan bata samu yadda takeso ba saita sake kebe wasu ukun ta sanyasu cigiyar da neman.



       A nutse tayi musu cikakken bayani dazai gamsar dasu,bisa sharudda da dokokin irin yarinyar da take da buqatar a sama mata,shuru sukayi kowanne cike da fata da burin cewa asamu dacewa ta bangarensa,domin tabbas indai hakan ta tabbata ta bangaren mutum sun sani cewa kakarshi ta yanke saqa,basu bar wajen ba saida kowacce ta tabbatar wa da fulani aisha cewa zatayi iyakar qoqarinta wajen samo yarinyar data dace.



****************


      Tunda fulani aishan tayi maganar umma luba tashiga dogon tunani da nazarin wadda zata kaiwa fulanin,zataso ace cikin jininta zata samo mata yarinyar,saboda romon domokaradiyyar da take da yaqinin yarinyar ita da danginta zasu kwankwada,bugu da qari ba qaramar daraja bace wajen mace auren yarima azeez koda kuwa cikin mafarki ne,koda cikin sirri ne kamar yadda xai faru a yanzu,ba shakka madaukakiyar daraja ce cikin kundin tarihin rayuwar diya mace hada auratayya da jinin gidan sarautar KAISA koda kuwa hada jinin na minti daya ne.



        Washegari ba zata shiga gidan maimartaba ba,don fulani ta basu hutu na sati guda,kowacce taje tayi bincike takuma zo mata da labari mai dadi kafin zagayowar satin.



        Tana zaune a faffadan tsakar gidanta tana ninke kayanta da jiya bilkisu ta wanke mata su tas,kamar yadda yake yanzu bata da matsalar mai wanki,saboda bilkisun duka ta hada harda wankin nata saboda kudin aikinta ya qara auki.



      Sallamar bilkisun ita ta sanya daga kai tana duban qofar gamida amsa mata,fuskarta a washe kamar koda yaushe tana fadin

"Me gado,yana ganki haka dawuri" dan qaramin murmushinta tasaki tana isa gefan tabarmar umma uwalen tadan dosana,duk da sun debi shekara kusan uku tare amma kullum bilkisun kamar baquwa take a gidan,kasancewarta mutum bamai saurin sabo ba,umma luban tayi mitar tayi qorafi kan tadinga sakewa amma har yanzu jiya iyau.



      "Yana ganki tun lokaci bai qarasa ba?" Tasake tambayarta

"Yau banje makaranta bane"

"Aiho,to,koda naji" saita miqe cikin qarfin hali tana qoqarin kama aikinta,duk da cewa sam yaudin bata jin dadin jikinta,kusan shine ma silar data sanya bataje makarantar ba yau,amma tadaure tazo aikin saboda batason tayiwa albashinta gibi,umma luba akwai kirki idan taso,amma fa tana da qaunar dukiyarta.



        Jifa jifa tana ninkin tana duban bilkisun,yau shurun nata sai taga yasake yawa,amma tasan koda ta tambayeta ba gaya mata komai zatayi ba,mutum ce ita wadda bata iya bude baki ta fadi matsalarta ba,duk da tana tsammanin koma meye baya rasa matsala da yanayin da suke ciki a gidansu ba,tunda kusan umma luban tasan komai,duk da bilkisun bata taba bude bakinta ta gaya mata ba,kasancewar umma luban mutum ce mai dan shige shige da kuma jama'a yasa tasan komai.



        Tana zaune dai a wajen tana karantar bikisun,gabanta yafadi sanda bilkisun ke rataye hijabinta saman igiyar shanyar dake tsakar gidan da niyyar daura alwala,gashinta mai tsaho santsi da sulbi ya bayyana tun daga gaban goshinta zuwa gadon bayanta,kamar tasan tana kallonta tayi hanzarin janyo dankwalinta mai santsi dake niyyar zamewa ta sake daureshi saman kanta,hakanan umma luban tasamu kanta da qarewa halittar bilkisun kallo.



       "Tabbas wannan duk inda ake neman mace tacika mace,kuma koda fulani aisha nakaiwa ita na tabbatar zatayi mata dari bisa dari,banda rama dake jikinta ma da Allah ne yasan yadda za'a ga cikarta,wannan tayi kuma nasan zataja hankalin yarima azeez" haka umma luban tasamu kanta da nazartar yanayi halitta dakuma halayyar bilkisun harta kammala dukka ayyukanta tayimata sallama zata wuce,saita diba kusan rabin abincin data dafa tace tatafi dashi suci ita da qannenta,bataqi ba,don bata da tabbaci ko yaqinin abinda zasuci idan takoma,don hatta da amaryar gidan mai qyallin goshi yau sai da suka haura da baban nasu,da alama hantsi yasoma duban ludayi,sa'annan zani yasoma sanin mazaunai,saura kadan itama bisa dukkan alamu tabi sahu ,hannu bibbiyu ta saka ta amsa tayi mata godiya kana tawuce.



         Tana jin hamza yana kiranta amma taqi ta tsaya,bakinta cike da addu'ar kada Allah yasa ta cimma babanta bare yaji aiken da zai jero ya tilasta mata tafita ta saurareshi ba,don a yadda take jin kanta din nan a yanzun kwanciya kawai buqata ko abincin bai gabanta.



       Tana basu flask din kuwa tamaida haqarqarinta ta kwanta,duka sai yaran suka damu suka dinga tambayarta abinda ke damunta,cikin qarfin hali tayi musu dabara tace gajiya tayi,suci abinci maza suma su kwanta.



       Ranar kusan kwana umma luba tayi tana auna dukkan matakai da sharuddan amsar macen da zasu kawo da fulani aysha ta gindaya musu da yanayin halin rayuwar da bilkisu take ciki,duk ta inda ta auna sai taga bilkisun tahau ma'aunin,cif da cif,bataga gibi tako ina ba,can qarshen dare daga qarshe ta yanke shawarar fara tunkarar bilkisun da maganar,don harkar zatafi kyau ace yarinyar tasan komai,kuma tayi amannar babu yarinyar da za'ayi wannan tayin tana cikin halin rayuwa irin na bilkisun da zataqi amsar wannan gwaggwaban tayin.


☀ï¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸Ã¢˜€Ã¯¸



Duk yadda taso tayiwa bilkisun maganar amma dole ta haqura har tsawon kwana biyu,saboda ciwon dai saida yasanya bilkisun takwana biyun bata fita,duk qaunarta da aikinta dakuma makaranta amma dole haka ta haqura,sai qannenta ta turawa umma luban suka shaida mata bata da lafiya. A wakankin kuwa taji jiki sosai,rama tayi qwarai. Umma luban tayi amfani da wannan damar ta dinga aiko mata da dafaffen abinci mai yawa wanda tasan zai ishesu ita da qannenta.



       Sosai hakan yayiwa bilkisun dadi,yakuma rage mata radadin ciwon,koba komai tana samun salama cikin ranta idan ta daga idanu taga qannenta suna da abincin da zasuci.



       A kwana na uku ta sake qwarara jikinta don zuwa taci gaba da aikinta,don tana lissafe da kwanakin da bataje na,hakanan ta shirya tafito,tasamu babanta a tsakar gida ta gaidashi tawuce. Ajiyar zuciya tasaki,tsawon kwanakin bata samu arziqin paracetamol ko na naira biyar ba daga wajen mahaifinta,hasalima ciwo kanshi baisan tanayi ba,wannan kuwa bawai wani baqon abu bane a wajenta,kusan haka tasu rayuwar take.



       "A'ah,mai gado,kin warke ne da kika iya fitowa?" Umma luba ta fada cikin nuna tsantsar kulawa,duk da babu wata matsala data taba ratsa tsakaninta da umma luban saboda tsantseninta da kiyayewarta da takeyi amma tayi mamakin yadda yau kulawar ta ninka ta baya tazama ta musamman

"Eh,naji qarfin jikina ne shi yasa nafito"

"Ai da kin bari kin sake jin dama dama"

"Babu komai umma"

"Allah to ya qara sauqi ya qara lafiya"

"Amin amin"

"Amma dai kinje asibiti ne ko?" Murmushi kawai tayi mata ba tare data amsa ta ba,hakan ya baiwa umma luban amsarta,saita kama haba tana dubanta

"Kai,maigado Allah ya fidda ku cikin wannan halin rayuwar,Allah ya kawo miki agaji ya dandasheki da miji da zai zama silar fitarki daga quncin da kike ciki keda 'yan uwanki,ki huta suma su huta...kiyi aikin daidai gwargwado yadda zaki iya kinji,Allah yabaki lafiya,ke abar tausayi ce bilkisu" ta qarashe fada cikin nuna jajjabi. Ita kanta bilkisun taji maganganun har tsakiyar zuciyarta,taji zuciyarta ta karye sosai har hawaye yana shirin zubo mata,ta danne zuciyarta ta soma aikinta a hankali kuma a nutse yadda ba zata jigata ba.



       Kamar kowanne lokaci duk sanda tagama aikinta gida take tafiya koda qarfe nawa ne,ta qaraso tasamu umma luban cikin falonta tana zaune ta qurqurar tv dinta a gaba tana kallo,a zahiri kallo take amma a badani tana tsara yadda zata tunkari bilkisu da maganar ne,harta fahimta takuma amince.



      "Au....kin gama kenan?,aida kin tsaya,albashinki nakeson biyanki,kuma inaso muyi magana dake" tafada tana miqewa daga kwanciyar datake,ta janyo jakarta wadda bata rabo da ita a qugunta tazuge,tamkar an yiwa bikisun rahama haka taji,don sam bata tsammaci samun albashinta a yanzu ba,idan tasamu ma to nan sa kwanaki bakwai ko goma masu zuwa ne a lissafinta.



       Kudade ta lissafo ta miqa mata,saidai tun kafin takai ga karba tasan cewa kudin kamar sunfi adadin albashinta,karba tayi ta cire kudinta kana ta miqawa umma luba sauran

"Kudin sun haura,na dauki nawa" kai ta girgixa

"Babu komai bilkisu,ki riqe duka" juya kudin tayi fuskarta cike fal da mamaki,a qalla kudin sun doshi dubu goma harda albashinta,mamakinta ya kasa boyuwa,ta daga idanu tana duban umma luban,sai tayi mata murmushi kana ta gyara zama

"Wannan ba komai bane maigado,nan gaba kadan wala'alla ke zaki dinga kyautar kamarsu koma sama dasu,wataqil nan da wani dan lokaci kadan ire iren wadan nan kudaden canji ne a wajenki ba wai kudi ba,amma dukka hakan zata farune idan da amincewarki da kuma yardarki".



      Gaba daya kamar ta sanya zare da allura ta dinke qwaqwalwar bilkisun tsaf haka taji,bata gane komai daga cikin maganar da take gaya mata ba,saita samu kanta da zubawa umma luban idanu qur kamar zata samu amsar tambayarta ne saman fuskarta,karo na farko kenan tun sanda suke tare.



      "karki damu maigado,yanzu zan miki bayani" cewar umma luban tana sake matsowa daura da bilkisun gamida tattara hankalinta waje guda

"Maigado,wata dama ce tasamu,wanda iya hangena da hasashena babu wadda ta dace da samun wannan damar saike,saboda dama ce dazata fidda ki daga qangin da kike ciki ke daduk wani wanda ya jibanceki,zaki rayu irin rayuwa ta gata keda 'yan uwanki hadda mahaifinki,zakiyi arziqin da babu lallai talauci yasake rabarki...maigado....ana nemawa yarima d'an sarki Abdallah mu'az sarkin kaisa yarinyar da zai aura". Hakanan gabanta yayi wani mummunar faduwa,ta dubi umma luba kafin ta dauke kai,cikin zuciyarta tana mamakin to ita din meye nata a ciki?,wannan ai sam ba maganarta bace,bama abinda ya shafeta bane bare tashiga ciki,meye ma alaqarta da maganar da har zata zama sikar samun sassauci cikin rayuwarta,a hankali cikin sassanyar muryarta tace

"Allah yabashi,yakuma tabbatar da alkhairi" saita motsa da alamun tashi zatayi,da hanzari ta tsaidata

"Ai dukka maganar taki ce" saita kuma dubanta cikin rashin fahimta

"Eh bilkisu,don babu wadda ta dace ta cancanta tasamu wannan damar kamar ke,zaki auri abdul'azeez abdalllah na tsahon shekarun dazaiyi a qasar da yake karatu,aure ne wanda za'a yishi bisa amincewarki data mahaifanki,kuma za'a daura auren ne da sanayyar qididdigaggun mutane,yayi shige da auren sirri saboda ba kowa akeson yasani ba,fadin irin alkhairin da zaki samu daga lokacin da kika amince zuwa rabuwarku,irin sallamar za'a miki ma bata baki ne,ina da imani da yaqinin zaki samu abinda zai sauya rayuwarku keda duka 'yan uwanki mahaifinki dama wanda kikaso kika kuma zaba,ke hatta ni din nan na tabbatar da cewa na gama warkewa maigado ta silarki idan kinso"


*Tirqashi!,yaya zata kaya?!*ðŸ¤Ã°Å¸½Ã°Å¸¤Ã°Å¸½

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: *S R B*

17


*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,ga mai buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadan nan numbers din_*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

________________________________


*Ina mata 'yan birni 'yan qwalisa masu burin sanyaya gidansu da daddaɗan ƙamshi mai tsayawa a zuciya da ruhin maigida?,shin kina da labarin ANNUR PERFUMES?,wadanda bayan sun gyara miki waje da ƙamshi su kuma gara miki ciki da kayan matsi?sannan su rabaki da infection?,WOHOHO wani kaya sai amale,ANNUR PERFUMES sun shara wajen saida*


*HADADDIYAR HUMRA*

*KWALACTURE*

*TURAREN WUTA*

*MUSK(AL MISKI THAHARA/AYSHA/BLACK AND RED MISKI)*

*DECORATIONS NA TSINTSIYA*


*_UWAR GIDA DA AMARE KUZO GA NAKU_*


*_MAZA GARZAYA GAIDA LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK!_*


*KO A NEMESU TA LAMBOBIN WAYA KAMAR HAKA*


07086341096 ko 07069037534


_muna maraba da masu siyan ɗai ɗai ko sari_🤗🤗


*INGANCI KYAU RAHUSA DA KUMA INGANCI SAI ANNUR PERFUMES*👃ðŸ½

___________________________________


      Cak qwaqwalwarta ta tsaya da aiki na wucin gadi,komai yayi mata dif tamkar qwaqwalwar tata bata taba wani aiki ba,ta daina fahimtar komai sai maganganun umma luba dake mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,sun dade suna maimaita kansu kafin tasoma fahimtar abinda takeson gaya mata

"Taje ta bada fansar kanta da budurcinta wa yariman qasar kaisa na tsahon shekara daya" a dunqule idan ta fahimta kamar hakan umma luba take nufi ko?,ta jefi kanta da tambayar,saita daga idanunta dasuke walainiya ta xubawa umma luba su,shin tasan ma'anar abinda take fada kuwa?,anya hankalinta daya?,a cikin hayyacinta ma take?,bataga alamun wasa saman fuskarta ba face tsantsar gaskiya dason isar da saqo bare tace wasa take mata,karon farko data motsa labbanta 

"Ban gane ba umma,ban gane abinda kike nufi ba" murmushi tasakar mata dukka bisa qoqarinta na kwantar mata da hankali

"Kin gane maigado saidai kicemin kin rude,kuma tabbas koma wacece da bata zaci samun irin wannan damar ba ta sameta sama taka dole rudani ya shigeta,kije kiyi tunani kawai nan da jibi,saboda kwanaki biyar yarage mana muje mukai duk wadda muka samu" wani abu ya tsaya mata iya wuya,ta fahimta takuma fuskanta,wato bazasu akayi suyi farautar yara marasa galihu irinta,musamman idan akayi katari da masoya abun duniya masu kwadayi shikenan kaya ya tsinke a gindin kaba?,duk haqurinta duk sanyinta ba zata lamunci a qasqanta mutunci da darajarta ba,lallai ya kamata idanma umma luba tana da wani tunani na daban a kanta ta warware matashi,don a gaba bata fata hakanan bata sha'awar ta sake soko wata magana makamanciyar wannan a tsakaninsu iya zamansu,koda tanason aure koda lokacin da zatayi aure yayi ita ya kamata ta zaba bawai a zabeta ba,bare a yanzu da qaramar qwaqwalwarta take cunkushe da matsaloli,gajeriyar rayuwarta take quntace take kuma takure,a gaba daya tunaninta da abinda idanunta suke gabe mata shine,aure gaba dayanshi matsala ne,babu komai cikinsa face jefa kai cikin damuwa da matsaloli,me yasa ma zata yarda anan kusa da qananun shekarunta ta fada matsala kwatankwacin matsalolin da taga umma katti da sauran matan da babanta yake aurowa suke fadawa?,shi yasa ko daya bata sha'awarsa,koda ya zame mata dole tana duban nisan zangon da zata qara diba kafiin ta fada komarsa

"Aure a nawa qaramin tunanin ana yinsa ne a sanda namiji da mace sukaga juna suna so,suka kuma amince da juna,shi namijin zai tattako koya tura wakilansa zuwa gidansu yarinya su nema masa aurenta,baya ga haka babu wani sharadi da ake gina aure a kansa na cewa bayan lokaci kaza akwai wani abu kaza dazai faru,yakan zama tarayya tahar mutuwa a yadda nake ganin yana faruwa a mafi yawancin gidaje,kiyi haquri umma luba,ni bazanyi aure ba,koda zanyi aure toba yanzu zanyi ba,ki nemo musu wata,nasan da yawa zasu amince,zan wuce gida sai Allah yakaimu gobe" da mamaki take duban bilkisu,ashe yarinyar ta iya magana har haka,ashe tana da zurfin tunani da hankali?,koda ba'a gaya mata ba iya zamanta da bilkisu ita zata bada shaidar ta iya talaucinta,hakanan ba makwadaiciya bace,amma bata taba zaton zata bijirewa wannan tayin ba.



      Ganin da gaske bilkisun tafiyar xatayi,kuma idan har tatafin wata qatotuwar dama ce mai gwabi da zata subuce mata,wadda samu ko maida kamarta saitaci wuya,wala'alla ma cikin abokan aikinta wata takawo tata kuma a karbeta ta rasa dukkan wata dama matsayi da daukaka da zata samu a masarautar kaisa,zumbur tamiqe tana qwalawa bikisu kira wadda batakai ga fita ba,gabanta tasha tana dubanta cikin kwantar da murya da karyar dakai

"Haba maigado,haba,qauna ce fa tasa na zabeki na tsallake dubbai,ya kamata ki dinga sara kina duban bakin gatari,a yadda kikeson 'yan uwanki na zaci zaki iya sadaukar da farincikinki saboda tasu rayuwar ta inganta?,kin gwammace ku dawwama a haka bilkisu bayan ga dama da kika samu ta fidda kowa daga qangin da yake ciki?,shekara daya tak fa rayuwarki zata inganta,me za'a gutsira daga jikinki?" Idanunta masu maiqo tazubawa umma luban tana dubanta ganin yadda ta haqiqance,itadin ba tsararta bace hakanan basu saba 'yar tankiya ba,inda sun saba din da taji amsa dai dai da ita,datace bata amsa yadda ya kamata,tana tsammanin a yadda idanun al'umma suka rufe kowa ya tasa kudi gaba fiye da mutuncinsa itama bikisun haka take?

"Kiyi haquri umma luba kamar yadda nace miki dafarko bazan iya ba,don Allah ki duba cikin dubban ki zaba wata,nasan za'a dace" daga haka tarabeta tafice daga gidan,tanajin iska na dibanta,hakanan maganar na ratsata fiye da yadda ta tsammata,sai taji tun daga kan hanya kamar zazzabinta daya sauka yana niyyar dawowa,maganganun sukaci gaba da juyin waina a tanda cikin qwaqwalwarta,ta rasa ma wanne zata kama.



      Tsaka da haka taji kamar ana ambatar sunanta a sanda take qoqarin shigewa gidansu,yanayin yadda sautin ke fita saitaji kamar tasan me kiran,don haka ta tsaya cak ba tare data waiwayo ba,hakan yabashi damar qarasowa gabanta,abubakar saddiq ne,sanye cikin shadda dinkin tazarce,kansa babu hula,kana masa kallon farko zakasan yana ji da gayu da samartaka,jifanta yayi da murmushi saita janye idanunta daga kanshi,hakanan yake mata kwarjini,tasamu da qyar ta tattara lafuzan gaisuwa saman lebunanta ta aika masa,ya amsa idanunshi kan labban nata dake masifar burgeshi,ya fuskanci bayan kyau yari yar tana da wani qasaita da izza wadda wala'alla itadin batasan tana dashi ba,miskilancinta yana burgeshi,hakanan yanayin dakiya da basarwarta.



       "Kwana biyu baki ganni ba,amma koki cigiyata ko?" Yafada yana dan fidda murmushi gami da shafar sumarshi,maganar tasa ta sake tarwatsa tunanin dake fareti a kwanyarta,saitayi kaman zata kalleshi bisa mamakin furucinsa saikuma ta basar,ta nemeshi akan me?,idanma tasan inda yake din ya cancanci ta nemeshi?,yasake sakin murmushi ganin yadda tasake basarwa

"Koda yake bakisan inda nake ba ko?,kuma baki sha'awar amsar numberta ba kosau daya,koda kin saninma nasan masu suna bilkisu da sarauta,da wuya anemi din,to gashi na sake kawo kaina a karo nabiyu,kuma sai naga kamar sauri kike,ko zaki aramin minti goma cikin mintunanki muyi magana?" Da sauri ta girgiza mishi kai alamun a'ah,duk da hakanan take ganin qimarsa,amma a yanzun bata sha'awar dogon magana,dan shuru yayi alamun baiji dadi ba,amma saiya dage kafadunsa

"Ohk,ba damuwa,asake samin wani lokacin saina dawo muga juna....,ko a bani phone num saina kira ko?"



        Kafin tabashi amsa babanta yafito daga cikin gidan,tunda taganshi tasan komai zai baci ne,don haka tabude bakinta dasauri tace

"Sai jibi in sha Allahu,babu damuwa" yasaki murmushi,don ba qaramin dadin amsar jibin data bashi yaji ba

"Allah yakaimu,na gode qwarai". Kafin ta amsa ya iso garesu,don haka saita wuce zuwa cikin gida kawai tabarshi da sadiq,koma meye ita bata sha'awar yafaru a gabanta.



        Ko kadan a cikin ranta bata ji ta daina zuwa aiki gidan umman luban ba,a nata ganin komai yana da muhallinsa,yadda maganarsu keda muhalli na daban haka aikinta ma,babu abinda zai shafi wani,saidai yadda maganar ta tsaye mata yasanya washegari bata da qwarin jiki dana zuciyar tafiya gidan aikin.



       Rashin zuwan nata yasanya umma luba babu abinda bata saqa ba,abu na farko tsoron tawaye daga wajen bilkisun kamar yadda ta raya,don haka wata washegarin ta yanke gwara ta fuskanci fulani da maganar,wala'alla asamu wata mafitar.



      Kamar kowanne lokaci idan zatayi ganawar sirri da amintattun nata,waje ne kebantacce wanda yake cike da sirri da aminci,fulanin aysha ce daga tsaye cikin shigar alfarma dake nuna xallar mulki da sarauta,yayin da umma luba ke zube a gabanta,kanta a qasa bayan ta kammala dukkan bayananta.



      Tattaki fulani aysha tayi tana nazarin maganar da umma luban tazo mata da ita,tasan tunda lubabatun takasa sukuni kan lamarin babu ko tantama yarinyar ta cika mace,takuma cika dukkan sharuddan data gindaya musu kafin fararwarsu aikin,ba shakka ba umma luba kadai datasan yarinyar ba,har ita kanta tacika da mamakin yadda za'a samu wasu ko wata cikin qasarsu da zata iya bijirewa wannan tarin alkhairi dasu a nasu ganin suke ganin kamar alfarma ce sukayiwa koma wacce diya ce,eh mana alfarma,tunda banda wannan dalilin da ko cikin mafarkinta bata taba hasashe ko hango azeez din yana nema ko auren daya daga cikin yaran talakawansu ba,azeez din mai tsada ne,saboda haka dole komai dazai rabeshi yazama mai tsada mai daraja

"Kin tuntubi mahaifinta?,idan kin tuntubeshi shidin me yace?" Fulani ayshan ta jefa mata tambayar,ta girgixa kanta da sauri

"Tuba nake Allah ya taimakeki,sam sam na manta da wannan,ai Allah yabaki yawan rai ina da yaqinin cewa idan na tuntubeshi ma magana ta qare,yanzu kuwa zan tashi,bazanyi qasa a gwiwa ba zan sami mahaifinta" murmushi fulanin tayi cikin zuciyarta,don idan ka kalli saman fuskarta ba zakaga alamunsa ba,saita soma takawa zuwa saman daya daga cikin kujerun tana dauko wata jaka tana kuma magana da umma luban

"Ki jaddada masa matsayin wanda ake nemawa diyarsa koda shima zaice zaya musa,daga yanzu bana buqatar a sake magana da ita yarinyar,yardar mahaifinta tamkar yarda ce,abunda nake da buqata kawai shine,hoton yarinyar don inason in ganta dakyau,na tantance kuma na tabbatar da dacewarta da yarona" tana kaiwa nan taciro kudade rafar 'yan dubu dubu tana miqawa umma luba,jikinta na rawa cikin sauri ta amshe tana zuba mata godiya kana tataso cikin farinciki tafito daga falon tana cusa kudin cikin zaninta,tana kuma jaddadawa kanta lallai zatayi dukkanin me yiwuwa taga komai yatafi yadda akeso,takuma cimma nasara.



       A lokacin da umman luban tazo tana daga daki kwance,taji murya kamar tata,amma sanin cewa babu wani abu da zai kawota gidan saitaci gaba da kwanciyarta tana jan istigfari cikin ranta kamar yadda tasaba yi a yawancin lokuta idan bata da abunda zatayi,ita daya ce cikin dakin tana sanya ran gobe tawuce wajen aikinta,dukka qannenta sun tafu islamiyya,Allah yasanya weekend ne gobe take saka ran zuwa har makarantar boko.



       A falon amarya ladidi tasauka,lokacin yana zaune saman daya daga cikin kujerun falon,gama sa'insarsu da ita kenan akan shinkafa,tace haram tabashi abincinta yaci,tunda rabonshi da kawo cefane yau kwanaki uku kenan,yayi barazanar da muzuran duka a banza ladidi ta dauke kanta,yunwa ce kawai ke sadakarshi,gashi babu ko sisi cikin aljihunsa,yasan ko giyar wake yasha bazai tunkari katti tabashi abinci ba,don tunda ya qara auren nan taja masa layi,irin layin da bata taba ja masa ba,ta tattarashi dukka ta barwa ladidi shi,ta yaranta kawai da sana'arta take.



        Ya sake shafa cikinsa yana tsinewa talauci karo na babu adadi,sam a rayuwarsa bai taba kawowa zai tsunduma cikin talauci irin na wannan qarnin dana yafa ba,dai dai lokacin da ladidi ta dage labule suka shigo tare da umma luba

"Baquwa ce takeson magana dakai" ladidi tafada tana wucewa uwar dakanta don adana miyarta data gama soyawa,yabi kwanon da ita kanta ladidin da kallo yana hadiyar yawu kamae tsohon maye,don tuni qamshin miyar yagama cika mishi ciki yasake tada mishi yunwarsa.



     Gaisuwar da umma luba keta faman rattabo masa tadawo da hankalinsa,saiya maida hankalinsa gareta yana amsawa cikin yanayin nuna rashin sanin mutum,saita taqaita masa wahalar dakai ta gayamishi wacece ita

"Uwar dakin maigado ce,gidan da take aiki" gyara zamanshi yayi gabanshi nadan faduwa,yayin da wani sashe na zuciyarsa yacika da fatan Allah yasa kudin aikinta takawo mata ganin kwana biyu bata je ba ya amsa ya kalmashesu ya rage radadi na kwana biyu

"Au.....to....to,madallah,ina fata lafiya daiko?" Murmushi tayi tana gyara zamanta

"Lafiya lumi,sai alkhairi dake tafe dani" jin haka yasa yasake tattara nutsuwarshi yana dubanta,tadan karkace ta zaro rafa daya ta dubu dubu cikin irin wadda fulani aisha ta mata kyautarta ta aje gefan malam bilya,bin kudin yayi da kallo a mamakance cikin ranshi yana qissima abubuwa da yawa

"Kadda ace kudin aikin nata takawo mata,to amma maigado na karbar maqudan kudi haka masu yawa amma bata taba jin qaina ba?,kodai yau Allah ne ya toni asirinta?"

"Wadan nan....dama wasu masu tarin yawa zasu zama mallakinka matuqar ka aminta da maganar da nake tafe da ita" mamakin jin zai mallaki kudin suka kamashi,saiya dafe kudin yana sake gyatta zamanshi 

"Wacce magana ce wannan baiwar Allah?".



      Ba tare data boye mishi komai ba tayi masa bayani filla filla,ta shaida masa yadda sukayi da bilkisu a gidanta,sannan ta rufe bayanin nata da gaya masa irin tarin maqudan kudaden da zai samu da alkhairi iri daban daban.



      Ba malam bilya bs,hatta ladidi dake daki wadda dama fakare tayi batasan sadda tafito zuwa falon ba tana rarraba idanu tare da qissima yadda zata sake kame mijinta malam bilya matuqar hakan ta kasance

"Kan ubancan!,amma ban taba sanin baqincikin maigado ya ta'azzara har haka ba da tuni na jima da nema mata maganin samun salama,ashe yarinyar nan bata qaunata duk ban sani ba sai yau?" Yafada yana duban ladidi wadda tasamu waje daura dashi tazauna itama tana neman muhallin da zata tofa tata

"Ai malam kada kasake kada kabari wannan damar tawuceka,koda a mafarki kasameta aika more ballantana a gaske" ladidi ta tofa din kamar tadda bakinta yaketa motsi tunda tafito

"Niko ladidi idan nabar hakan ta kasance a cikin tababbu marasa rabo ai nine sahun gaba,maigado zataci ubanta,wanne amfani zatamin na tsahon shekara gudan dazai kawomin wannan alkhairin" da sauri umma luba ta dakatar dashi

"A'ah malam,bada zafi zaka mata ba,kayi mata cikin hikima da lallashi wataqila tafi fahimtarka a matsayinka na mahaifinta,kaga babu yadda ban kwatanta mata ba amma taqi,ni kuma qauna ce tasa na zabeta cikin dubbai,inasonta da wannan alkhairin" wuyar rigarsa daya zame yajawo yazauna sosai saman kafadarsa,cikin nuna isa da hura qofofin hanci yace

"Yo yarinyar dana haifa a cikina ma saina tsaya ina lallabata?,ai indai nine na haifi bilkisu to kije kawai ki shaidawa ranki ya dade.....koma ku rankaya tare mu sanar mata na bawa yarima ita,zan mata lallashi nafarko amma idan na fuskanci asara takeson jaza mana tofa bazan mata ta dadi ba....kekam babu abunda zamuce dake sai godiya,don ba qaramin masoyinka bane zaiga alkhairi haka ya rungumo ya nufoka dashi".



        Kowannensu cike da farincikin zuwa gabar samun cikar burinsa sukayi sallama,don bata tsaya taga bilkisu ba bare tasan da zuwanta ko suyi magana.



       Miqewa malam bilya yayi yana jinsa yau da wani irin nauyi sanda yake cusa rafar kudinsa a aljihunsa,ganin yasoma haramar ficewa sai ladidin ta lanqwasa murya

"Malam,bakaci abinci ba zaka fice" harara ya watsa mata

"Ki riqe kayanki mana kici ko zaki qara kumari,an gaya miki ni matsiyaci ne?,ni nan da kike gani duk inda nayi arxiqi bibiyata yake a jinina ne"

"Kayi haquri malam....karka watsamin qasa a ido mana,ta yaya zaka iya shawo kan yarinyar nan bayan kasan cewa mace sai mace 'yaruwarta,nina gama tsara yadda zamusha kanta amma naga kana da niyyar botsarewa" jin ta ambaci kalmar shawo kan bilkisu yasan kuma ladidin akwai hikima saiya sassauto,yana wani ciccin magani murya ciki ciki yace

"To yanzu ya za'ayi?" Tamiqe da hanzari tana cewa

"Kasan kwananta wajen nawa kamar bata da lafiya,kuma gidan nan kasan cewa ba wani cikakken abinci gareshi ba,yanzu haka qila tana kwance bataci komai ba,bari na zuba maka abincin saina tasota itama na zuba mata tazauna kunaci tare kana janta da hira harka sako mata zancan" dariya yasaki

"Yauwa ladita,ladi ga tsiya ga dadi" ya qarashe maganar yana komawa mazaunin daya tashi dazu,yayin da itama tasaki dariyar tana wucewa zuwa uwar dakanta,tasamu farantai biyu tayi zubin shinkafa da miya da salad harda nama tafito falon dasu,ta ajesu dukkaninsu a gabanshi kana tafice don kiran bilkisu.



     Cikin mamaki ta amsa sallamar jin muryar wadda yau tashigo dakinsu,matar da tunda tazo gidan ko ta qofar dakin nasu bata taba wucewa ba bare tayi batan kan shigowa koda me yake faruwa kuwa cikin gidan.



      Tilas tamiqe tazauna ganin murmushi saman fuskar mama amarya makar yadda yaran gidan suke gaya mata,saita qaraso tadan tsaya daga gefan bilkisun

"Sannu maigado,jikinne dai?" Wani mamakin yasake kamata,saita daure ta gyada kai harda qarin bayani

"Alhmdlh nasamu sauqi ma"

"Masha Allah,naji dadi,babankune sai haquri,baya kyautawa wallahi sam,koda baka da kudin hidima da iyalinka amma ai aqalla ka jasu a jikinka ko?,yanzu gashican duka yadamu,yanason miki sannu amma yana nauyin wai bai siya miki magani ba tunda kika kwanta"

"Baban namu!" Tayi subutar bakin fada cikin muryar dake nuna zallar mamaki idanunta kan ladidi,don iya abinda hankalinta zai iya tunawa bata taba ganin alhini saman fuskarsa don daya daga cikinsu bashi da lafiya ba,kai ta gyada tana murmushi

"Shi dinfa,shi matsalarsa idan baida kudi saiya watsar da kowa maimakon yayi bayanin bashi dashi ne,yanzuma shine ya aikoni yace kizo yana son ganin jikin naki" kusan daskarewa tayi,don bata ma gane ba saida ladidin tasake gaya mata,sannan tamiqe jiki ba qwari ta ciro mayafinta dake rataye jikin qofa cikin mutuwar jiki tabiyo bayan ladidi,don hakanan kawai jikinta ya bata dukka abinda yake faruwa ba gaske bane bogine,akwai wani abu aboye a qasa,don ruwa baya tsami banza,dabi'ar data zama jini da tsoka tsahon shekaru sama da ashirin ba qaramin abu bane zai sauyata cikin gaggawa haka ba,amma kome meye zataji zata gani,don kusan tafi kowa karantar halayyar baban nata cikin yaranshi,saboda dogon zama da sukayi tare dakuma baiwar fikira da Allah yayi mata na saurin fahimtar abu.

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: *S R B*

18



*_Zafafa biyar na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,gamai buqatar mallakar nashi saiya tuntubi wadan nan numbers din_*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




18





       Sanda suka shiga dakin tuni ya soma nisa wajen kai lomar abincinsa,bakinsa cike da shinkafa yake nuna masa inda ya aje daya plate din yana cewa

"Qaraso nan maigado,sannu,Allah yayi miki halin juriya irin na maimunatu na" duk da tazauna a inda ya nuna matan amma bata dubi abincin dake wajen ba,don sam ko kusa ko alama ko amafarki bata taba kawowa a ranta nata bane

"Gani baba" ta fada kanta a duqe kamar yadda suka saba yawancin lokutta,saboda tsananin rashin sabo da rashin jansu a jiki

"Yaya jikin naki?" Sai data masa duban mamaki kana tasake maida kanta qasa ta amsa

"Da sauqi alhmdlh,na warware"

"To madalla,madalla" soma yunqurin miqewa tayi,ya dakatar da ita da sauri

"A'ah,zauna mana ga abinci nan kici,kya tashi bayan ke aka zubowa?" Duban abincin tayi tadubi baban nata,yasan cewa tambayoyine fal a bakinta,amma kasancewarta bamai yawan surutu ba sautari kana gane tana da abun fada ne da hanyar duban abu da idanu

"Zauna kici maza,keda ba isashshiyar lafiya gareki ba" mama ladi tasaka baki,saita koma tazauna cikin matuqar sanyin jiki tajanyo abincin gabanta.

 


       Tsananin rashin sabo da mamaki suka sanyata kasa kai koda loma daya bakinta,sai faman juya abincin kawai take da cokali tana sauraren hirarrakin da baban nata yaketa soko mata,wadda ta kasa bashi cikakkiyar amsar koda abu daya,saboda jinta take gaba daya banbarakwai,har zuwa lokacin daya kammala cin nashi abincin,saita aje cokalin itama tamiqe

"Zauna mana me gado,wai saurin me kikeyi?,magana zamuyi ai" yafadi dai dai sanda mama ladi ta jiye mata ruwan randarta mai sanyi a kofin silba a gabanta tadora da cewa

"Shine ai,kamar ana cizonki".



        Shuru ne ya ratsa dakin na wasu mintuna yana kama zaren maganar farawarsa zuwa qarewarsa,sa'annan yaja wata gyaran murya mai kauri kafin yasoma magana

"Wato maigado haka Allah yake lamarinsa,saika haifi yara rututu amma a cikinsu sai Allah ya daukaka darajar wani,yayi masa nasibin da kaf cikin yaran naka babu maishi,wani al'amarine ya tunkaromu na alheri wanda dukkaninmu alherin xaibi ya shafi kowa da kowa haula da zuri'a,amincewarki kawai muke nema harni mahaifinki".



      Yana fadin hakan taji gabanta ya yanke yafadi,tasoma ambatar sunan Allah tana addu'ar rabbi yasa ba abinda zuciyarta take raya mata bane,idan kuwa shine ta tabbatar da cewa ta kade daga ita har ganyenta

"Gidan sarautar garin nan suke neman izinin hada zuri'a dani ni malam bilya na shekara daya,wanda acikin shekarar zasu azurtani na zama daya daga cikin jerin alhazawan da ake zance,nasan ke yarinya ce mai biyayya,ba zaki taba cewa komai ba akai,saboda haka tunima na bayar da aiken cewa nabasu ke!" Kamar saukar ruwan sama da tsawa haka taji maganar tashi,ba tare data shirya ba wasu hawaye masu dumi suka soma layi tun daga cikin idanunta zuwa saman kuncinta. Lahaula wala quwwata illa billah!. Ta sani dama tasan xa'a rina wai an saci zanin mahaukaciya,tasan cewa matuqar wannan batun yashiga kunnuwan mahaifinta to magana ta riga data qare.



       Dukkaninsu sunga hawayen dake zirya a fuskarta,hakan yasanya mama ladi gyara zama gami da dora nata sharhin

"Duk É—a nagari burinsa shine ya farantawa iyayensa yacika burinsu,kuma alhmdlh kedin kin samu shaida a wajen mahaifinki,don kaf Æ´aÆ´ansa babu wanda yake naci da damuwa dayimin zancanshi shida mahaifiyarsa irinki,shi yasa muke da kyakkyawan fata dakuma zaton ba zaki watsa mana qasa a idanunmu ba,don ke kanki basai an gaya miki ba cewa babbar masarauta ce take nemawa babban yaro kuma magaji a wajenta aure,kinga wannan bama lamari bane da za'a ce an tsaya ana jayayya akai ko tantama ba" duk da hawayen dake idanunta hakan bai hanata duban umma ladi ba,ba abun mamaki bane donta fadi hakan,saboda sama taka ta ganta,batasan cinta shanta ba bare sutturarta,ba'a maganar lafiya da ilimi harta kawo wannan minzalin,idan akwai wanda zata zarga shine mahaifinta,da har ya amshi wannan wasan yaran hannu bibbiyu yake da muradin wanzar dashi,ba tare daya tuna cewa diyarsa bace ita jininsa ce,dukiya ta rufe masa ido,koda baisan komai na dawainiyarta ba,baison ciwo da zafinta ba amma ai tsatsonsa ce

"Kayi haquri baba,karka bada aurena ta wannan sigar don Allah,hanyar da duk wani mutumin qwarai yaji zaiyi Allah wadai da ita,idan ka matsu ne na matsa daga gabanka,kana iya neman wanda zai aureni saboda Allah,ya riqeni saboda Allah,yaqaunaceni saboda Allah,yakuma zauna dani saboda Allah,wanda zaiga girma da mutuncinka martaba dakuma qimarka,ka duba maganata don Allah" ta qarashe fada cikin rauni,duk da cewa tafada ne koda wani abu zai iya taba ranshi ya waiwaya yadubi abinda yakamata,tasanshi sarai akwai kafiya da tsaiwa kan maganar da yakega tayi masa kuma itace dai dai,ba kasafai ake sauko dashi daga dokin naƙi ba idan yahau.



       Cikin hargagi da kaurara murya yace

"Ke bilkisu!,naji duk abinda kikace da uwardakinki,nasan kuma dama ra'ayinki kenan,to ba yardarki nake nema ba,hakanan ba shawartarki nake ba,na yanke hukunci ne a matsayina na mahaifinki wanda yake da iko dake,ki yarda kokar ki yarda wannan ya rage naki,tashi ki fita ki bani waje".



       Wani irin duhu duhu da hajijiya take gani,haka ta dinga laluben hanya,a daddafe takai kanta dakinsu,tazube tana sakin wani marayan kuka,karo na barkatai tasake fadawa cikin halin bege da fatan inama ace anty zuhra tana nan,inama ace anty zuhra zata dawo kafin mai afkuwa ta afku,tasan idan da tana nan zatayi dukkan maiyiwuwa ta hana faruwar lamarin,duk da matsananciyar Æ´ar tsamar dake tsakaninta da mahaifin nata.



       Ranar za'a iya cewa ba ita kadai ba,hatta da Æ´an Æ™annenta babu wanda ya runtsa,ta kasa boye tashin hankalinta sam,kuka tayi mai yawa wanda ya qara yawan zazzabin da tayi tunanin yatafi kenan ashe yana labe,yasamu mafaka kuwa yasake rafketa.



************



      Washegari bayan duka qannenta sun wuce makarantar Allo,tana kwance a daki ita daya,tanaji tana gani makarantar data ci burin taje yau hakanan tabi ruwa,don bata da Æ™warin jikin da zata iya niÆ™ar uwar tafiyar data saba.



       Mama ladi ce tayi sallama tashigo dakin dauke da kofin silba da faranti mai dauke da kunu da wainar gero

"Sannu maigado,tashi kisanyawa cikinki wani abun kinji,su iyaye haquri ake dasu ana musu biyayya don a wanye qalau" hakanan ta qaraci babatunta ta fice,batako daga kai ta dubeta ba bare ta tanka mata,kamar ta sanya qafa ta shure abincin haka gaji,abun sam babu Allah a ciki,yau da qyar tasamu ta hadawa qannenta abinda sukaci da safe suka wuce makaranta,babu wanda yadamu da basu koda danyar qwayar gero,amma ita din yanzu gashi ana bibiyarta da abincin har shimfidar kwananta.



      Umma katti ce ta bankada labulen dakin tashigo,fuskarnan a dinke tsaf kamar hadarin kaka,wanu kallo takewa bikisun sannan tace

"Wai me yake hadaki da waccar matar da naga daga jiya zuwa yau sai wani haba haba takeyi dake?,ko wani sabon munfurcin da tuggun xa'a hada baki dake a qullamin?,to idanma hakane ina mai gargadinki dajan kunneki ahir dinki,kuma shima munafukin uban naku wanda nasan da saninsa ake shirya komai zanje yanzu nasameshi,don ba'a siya sai dana gama dawainiya daku daci daku sannan azo za'amin wannan iyayin ba ehe" daga haka tajuya tafice tana mita.



     Batasan ya suka Æ™arke ba,amma ga mamakinta da daddare itama saigata da nata abincin tana mata magana cikin lallama,inda ta dangwarar da wancan da wanda mama ladin tasake kawo mata a nan ta dangwarar da natan itama.


*********     ***********



      Kashingide take saman lallausan carfet din dake madaidaicin falon alfarmar tana amsa wayar sumaira,wadda ke karatu a qasar kano jami'ar bayero,tana hannun yayarta uswa dake aure a masarautar kanon.



       Yanayin yadda take amsa wayar kawai ya isa ya nuna maka zallar yadda qaunar 'ya'yan nata,wanda dama hakan aqidartace,halayyarta ce son Æ´aÆ´a

"ƙarshen watan nan muke sanya ran zuwa ma ammi,mu duka harda anty uswa,su irfan zasu samu hutu" cikin jin dadi tace

"Allah ya kawominku lafiya,dama inason ganinku gaba dayanku" daga nan sukayi sallama kana ta maida kanta ga umma luba dake duƙe gefe tana jiranta

"Uhmm,ina saurare" gyara zama tayi tana fidda murmushi

"Ai Allah yabaki yawan rai,Allah ya dafa miki tuni an wuce wajen,don mahaifinta ma yace yabaku,ai babu mai iya ja daku,ya amince yabaku ita" murmushi fulani tasaki,sannan tatashi tazauna sosai

"Dakyau,aikinki yana kyau lubabatu,tun zuwanki nafarko naji dukka hankalina ya karkata kan naki zaben da kikayi,saboda na tabbatar ayadda kika kasa zama kikazo kika shaidamin komai yarinyar ta hau mixanin da nakeso,hakan yayi". Farinciki ya cika zuciyar umma luba,tana ganin kakarta gab take da yanke saqa cikin masarautar kaisa

"Allah yabaki yawan rai,godiya nake,na gode da yabon dana samu daga gareki,yanzun Allah ya taimakeki kina da buqatar ganin yarinyar ne a kawota?" Hannu ta daga mata kana tace

"Bani nake buqatar na ganta ba,inajin yarima shi yafi cancanta ya ganta,idan tayi masa shikenan sauran ayyukan sun gama kammaluwa,abinda kawai yarage sai daurin aure,dakuma biki daga can nasu bangaren,don a nan bangaren namu,bana fatan koda ƙadangaren gidan nan yasan da maganar balle jama'a" cikin girmamawa ta rusunar dakai

"Baki da wata matsala Allah ya taimakeki,yadda kika dama haka kowa zaisha,tauraruwar mai martaba,hasken masarautar kaisa....in shaidawa yarinyar su shirya tafiya can ƙasar da yarima yake kenan?" Kai ta girgiza

"Eh....su shirya cikin satin nan zan sama muku visa keda ita da mahaifinta da mahaifiyarta"

"Angama ranki yadade,Allah yasa ki gama lafiya,godiya nake,nizan koma don nasamu zarafin isar da saqonki" ta furta cikin zumudi da farinciki,don nata manta qasar ba,bata kuma manta irin dadi da kashe ƙwarƙwatar idanu da sukayi ba,duk da cewa dubiya sukaje amma sukam fes haka suka dinga jinsu,kamar wancan karon wannan karonma sai data wanke umma luba da kudi,ba tare data damu da cewa kwanaki kadan ta bata wasu masu yawa ba.



       Zuciyarta fes,ranta fari qal,babu tunanin komai a ranta,saima hasaso yadda komai zai tafi dai dai take,yanxu abinda yarage shine tasoma nema musu visa kamar yadda ta gayawa umma luba,wayarta dake aje gefanta tadauka tasoma neman wata number,saikuma ta tsaya saboda wani É—an gajeran tunani da tayi,tasauya akalar kiran nata zuwa layin azeez,tana kiran tana mita can qasan ranta ita daya,tunda sukayi maganar da ita bai sake tada zancan ba,iyakaci idan yakira suka gaisa sukayi maganar data shafesu shikenan,kamar ma bai damu ba ko nashi da interest akan zancan,itakam babu abinda zai dakatar da ita,tasan gata ne zata masa,don ta yadda yake sharewa kuwa tasani da zarar taga matar a gefanshi zai ware ya manta komai.



      Yanzun kam dole tasoma samunshi da maganar,tasan halin miskilancinsa,sai suje yaqi ganinsu harsu dawo suyi zuwan banza,wannan kadanne daga aikinsa.



       Dai dai lokacin da azeez din suke zaune a wani wajen kebantaccen wajen shaqatawa,wajene da za'ace yana da tsarki akan sauran guraren shan iska dake mexico city.



      Komai nashi farine da ratsin baqi dan kadan,kamar yadda na lura kusan dabi'arsa ce son farin abu,farin wando ne a jikinsa mai azabar kyau wanda ya zarce gwiwarsa amma baikai idon sahu ba,sai shirt me gajeran hannu,v neck wadda tafidda qirar halittarsa,kallo daya zaka yiwa dantsensa kasan yana daga qarfe,qafafunsa rufaffun takalma ne hightop suma farare qal dasu kamar ba'a taba sanyasu ba,sai kanshi dake saye da p_cap fara mai adon baqi a jiki,wadda ya jawota ne sosai tarufe fiye da rabin fuskarsa dake duqe kacokam kan farar laptop dake saman cinyarsa,yana latsata a nutse da hannunsa dake dare da baqin agogo rolex na fata wanda yazauna sosai a hannun nashi.



       Saboda shi abokan nashi suka shirya wannan fitar bisa amincewarsa bayan ya tabbatar da tsarkin wajen,amma idan kaga yadda yayi shakulaton bangaro da hirar tasu saika zaci shidin bare ne a cikinsu ba tare suke ba,duk da irin shewa da suke bugawa irin ta zaratan samari da jini ke yawo a jikinsu,hakanan duniya ke gara musu yadda ya kamata.



      Suma basu wani damu ba,tunda idan da sabo sun saba da halayyar azeez,ba kasafai zaka sameshi yana hira ba,ba qaramar sa'a ka taka ba duk sanda kuwa ka sameshi yana hirar,ba kowacce irin hira ke burgeshi ba,hakanan ba'a kowanne yanayi yake zama ya bata lokacinsa wajen yin hirar ba,koda yazauna a cikinsu zaka sameshi da waya ko tab a hannu yana wani abun daya shafeshi.



        Iska da yanayin gurin daya mishi ma shine yazaunar dashi har tsahon wannan lokacin,baya ga haka da saidai kawai su taddashi gida yawuce abinsa.



        A sannan wata budurwa ta iso,duk da cewa shigar doguwar riga tayi amma kuma hakan bai hana wasu daga sassan jikinta fitowa ba,yalolon mayafin data yafa dinma iyakarsa wuya,qafarta sanye da hill shoes,kallo daya zaka mata ka bata sunan 'YAR DUNIYA,saboda dukka yanayinta ya nuna hakan.



        Kai tsaye gaban kamal ta tsaya,cikin nuna tsantsar rashin kunya da rashin tarbiyya tadubeshi

"Ka gama guje gujen naka?" Saiya dubi sashen da azeez yake,saidai da alama baima kosan da zuwan nata ba,baya fatan yasan da zuwan nata,don har yau kusan idanun azeez na kanshi,kuma sharudan daya gindaya masa suna nan,duk da yayi niyyar bijirewa amma mommynsa tace yayi haquri ya karba haka,suci gaba da zama tare,saboda akwai wani target nasu kan azeez din,matuqar yabari misunderstanding yasake shiga tsakaninsu to target dinsu zai samu matsala

"Pls lisma,kije zan sameki a gida,ko wani wajen" zare glasses din idanunta tayi tana cuna baki

"Baka isa kasake yaudarata ba ai,kayi na farko kuma kayi na qarshe,bari na gaya maka kamal,ni gaba nake dakai na rantse da Allah akan bariki da iskanci" tafada tana dan daga murya da alama temper dinta tasoma hawa.



      Ganin haka cikin wadanda suka san tsakaninsu da lisma din suka soma bata baki,gamida lallabarta taje din kamar yadda yace,sun mata alqawari zai sameta kamar yadda yace.



        Kusan duk abinda ake a kunneshi amma saika rantse baya wajen,ko baisan da zuwan nata ba,yana sauraren komai,yana tunanin ba sabgarsa bace ko abinda yashafeshi,hasalima yana ganin zubewar qimarsa ce kamarshi ya tsaya wani maida magana ta hadashi da watsatstsun 'ya'ya irin wadan nan,saidai kalaman data sake fada suka ja hankalinsa harta daga kai yana dubanta fushinsa yanason motsawa

"Ku rabu dani naci uwa da uban dan iska,maqaryaci macuci mayaudari kuma maha'inci,jinin asara haihuwar iska" idanunsa ya lumshe na wasu sakanni kana yabudesu,yamiqe cak yana aje laptop dinshi daga inda yatashin yana kuma qoqarin controlling anger dinsa kafin ya isa gareta,saidai hakan bata samu ba saboda maganganun data ci gaba da fadi.



       "Getout of there!" Yafada cikin wata kakkausar murya data ja hankalinsu dukka harda masu bata haqurin,waiwayowa tayi tana neman wanda ya bata wannan umarnin kai tsaye kamar ubanta ta yagashi shima,saidai suna hada ido saqon ya isa qwaqwalwarta,wannan ba kalar wanda ake iya yagawa bane,kwarjininsa kadai yana karya lagon koma waye kai,maimakon magana saita maida glasses dinta ta rabashi sum sum tawuce daga wajen bayan ta kalli kamal taja masa qwafa alamun zancan bai mutu ba.



       Idanunsa qur bisa kamal wanda kallon yariman ya rudashi,baison yadda yake zubawa mara gaskiya idanu haka,ran azeez ke tafasa sosai,saboda yanajin xagin datawa kamal din kamar da familynsu gaba daya take,kusan laifin kamal yafi nata yawa a wajensa,tunda yasan cewa idan babu qira meye zaici gawayi?,idan bai kulata ba ina taga fuska da qwarin gwiwar zuwa ta tsaya haka a gabanshi tana gaya masa wadan nan muggan kalaman.



       Akwai magana da yawa a bakinsa,amma saidai baison yace komai da zai tozartashi cikin bainar jama'a masu yawa,tunda dai jininsa ne,hakanan bugu da qari ammi ta masa magana kan yadinga controlling fushinsa akan kamal,tunda dan uwanshine,uwa uba kuma akwai 'yar tsama sosai tsakaninta da momi mahaifiyarshi,so kada tadinga ganin kamar ita ke sanya azeez din yana yiwa kamal din wasu abubuwan.



       Ã†™oÆ™ari yayi yasoma hadiyr fushinsa,harya isa inda ya aje system dinsa ya dauketa yakashe sannan yasoma takawa don ficewa a wajen,tunda sukaga hakan sunsan tafiya zaiyi,don haka babu wanda ya tsaidashi.



       Yana gab da ficewar wayarshi tadauki tsuwwa,daya duba yaga ammi ce saiya qi dagawa,harsai daya isa motarshi yabude yazauna asit dinsa kana yabi kiran nata.



      "Kana lafiya ko?,jiya banga kiranka ba"

"Lafiya qalau ammi,jiya duka wayar tawa a kashe take,muna da test ne,dana gama karatu sai kawai nabarta a kashe saida muka fito,sanda muka fito kuma dare yayi anan babu damar kira"

"To ma sha Allah....kan maganar nan ta aurenka.....yanzu haka nasa an samo maka yarinyar,ina tunanin cikin satin nan zan turo maka ita ka ganta,idan tayi maka shikenan,inaso ne ayi komai a gama within two to three weaks".



      Dayaji ta bagarar da zancan tun wancan lokacin ya zaci tabar maganar ne,sam ya manta shaf da batun,don har yashiga sabgoginsa,bashi data cewa kuma bashi da damar musu,tunda yasakar mata ragamar komai kuma tayi din bai isa ya canza ba,cewarsa a'ah kamar ya taso da wani case ko wata matsalar ne tsakaninsa da ammin,gwara ya amsa koda baiso,koda babu abinda zata amfana masa,amma ko daya baya da buqatar zuwan yarinyar,koma ya take ba matsalarshi bace shi

"No ammi....basai tazo ba,kawai ku qyaleta" sai tadan bata fuska kamar yana gabanta kana tace

"Kamar yaya?,dama an taba aure ba tare da anga juna ba?" Shuru yadanyi na wasu daqiqu sannan yace

"Ba wani matsala bace,itadinma bata ganni ba tace ta amince" kai ta girgiza

"Akwao banbamci tsakaninka da ita,saidai kuma idan akwai wani abu daka shirya kake kuma boyemin....ko kuma kana da wadda kake da muradi daban da kakeso ayi hadin da ita" shima kai ya girgiza kamar tana wajen

"Ba haka bane ammi,indai ke tayi miki nima na tabbata zatayimin,sannan bawai abu bane na dindin ba bare ace ana buqatar dogon nazari ko zabe,it was just like a game...babu damuwa" sai datayi shuru sa'an nan tace

"Is ohk,amma zan amshi koda pic dinta ne na maka sending ta email dinka saika duba" bayason yafiya mata musu,saboda tana da wani girma da daraja a idanunsa,hakanan tafi qarfin komai kamar yadda tafi gaban komai,don haka yace

"Alright ammi,na gode" ƙaramin murmushi tasaki

"Anything for you" tafadi,daga haka suka kashe wayoyinsu.



      Sauke wayar yayi daga kunnenshi yana sauke ajiyar zuciya,kana ya waiwaya yana duban almustapha daya shigo motar sanda yake gab da gama wayarshi,mutum nabiyu rak a rayuwarsa da yasan abinda yake gudana,saidai shidin bai bayyana masa cewa shekara daya ne rak zaman nasu ba,tun kafin mustapha yayi magana azeez yarigashi

"She prepared anything" murmushi yayi yana dukan kafadarsa

"Dan gata" ganin yanason maida maganar wasa saiya saki qaramin tsaki yana fitowa daga sit dinsa ya zagaya zuwa inda mustaphan ke zaune yabude murfin motar yana cewa

"Kaimu gida da Allah" yana dariya mustaphan yafito saukayi exchanging seat,ya tada motar suka fice daga gurin,yayin da azeez yayi relax a kujerar motar kawai yanason yayi emptying qwaqwalwarsa daga kowanne irin tunani.

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: 19



*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*



*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*


_______________________________



*_kina buqatar kayan qwalama da kwadayi da kuma maqulashe😋😋,abubuwan motsa baki masu kyau tsafta da kuma inganci?_*


*_Garxaya ki nemi MRS SCHOOL TREATS_*


*_nasan zakuce to me kenan?_*


*_RUGUNTSUMIN GAMAYYAR WAJEN SAMAR MUKU DA KAYAN MAQULASHE IRI DABAN DABAN,DA SUKA HADA DA_*


*tuwon madara mai kwakwa da marar kwakwa*


*da kuma*


*Gullisuwa*

*_dukka na zallar madara mara algus_*🤗 


*_cikin nagartacce tsafatatacce_kuma ingantaccen package mai kyau_*


*SIYAN DAYA KO SARI*

_Kar kuyi sanya,maza ku nemeta a tudun wada,hayin buba GUSAU_

_ko kuma akan numbar waya 08069706638_


*_SUNA AIKAWA KOWANNE GARI DA IZININ ALLAH CIKIN AMINCI_*


*_biyan buÆ™atar abokan hulda shine burinmu_*ðŸ¤Ã°Å¸½Ã°Å¸¤Ã°Å¸½


19




    Wani irin farinciki ne yake ratsashi tun sanda umma luba ta gama gabatar da saqon fulani aisha,bakinsa ya kasa rufuwa,lallai arxiqin daya dade yana mafarkin samu yanxu yasameshi,maganar hausawa gaskiya ce da sukance DARE ÆŠAYA ALLAH KANYI BATURE,yaushi malam bilya akewa albishiri din cewa za'a rushe gidanshi yazabi kalar irin ginin da yakeso ayi masa,yakuma zabi sana'ar da yake da sha'awar yi,hakanan yazabi irin motar da yakeso yadinga hawa,rawa ne kawai bai taka ba gaban umma luban,amma koda tatafi bai iya daurewa ba sai daya taka din,mama ladi tana tayashi,cikin ranta tana godewa Allah daya sanya batayi gaggawar barin gidan ba,ashe da ita za'aci arziqi,sai daya gama sa'an nan yasoma tambayar mama ladin

"Ina mai gadon take ne,kiramin ita na shaida mata tashirya,sati uku ya rage mata a gidan nan"

"Anya ko tana cikin gidan nan,tun sassafe naji karakainarta da yara tana shirin fita makaranta" idanu ya fidda waje

"Ai bataji ba kenan?,bata yarda da hanata zuwa makarantar da nayi ba?,zamu gamu,nida itane,har makarantar zanje yanzu kuwa" ya fada yana shura takalmansa yafice daga gidan cikin hanzari zuwa makarantar tasu,don yanajin kamar bilkisun nason jawo masa wata asara ce dashi kuma bazai iya jurarta ba.



      Kwanakin gaba daya tunda take zuwa makarantar kusan babu abinda take tsinanawa banda kwanciya,koda yaushe zaka sameta kife da fuskarta saman tebur,tashin hankalin da take ji yana fuskanto rayuwarta jikinta ya bata ba qarami bane,ta yaya ya akayi mahaifinta ya aminta da wannan bahagon tunanin?,me yasa ya amincewa wannan wasan yaran saboda dukiya kawai?.



     Hakanan tasamu kanta da yawan duban sashen da bilkisun ke zaune,duk da bamai yawan magana bace amma koda tana zaune ne shuru to zaka sameta da littafi a gabanta tana dubawa,koda ba zatayi hira da kowa ba,duk da basa shiri,babu wata magana mai dadi dake hadasu,amma saita tsinci kanta da rashin jin dadin sauyawar bilkisu,ko ba komai a baya sukanyi compatition a aji wajen bada amsa a subjects da dama idan malami yayi tambaya,sukanyi rige rigen miqa classwork tsakanin ita da ita,duk da talura badon ita bilkisun takeyi ba,amma rashin ganin hakan kwana biyu duka sai taji babu dadi.



      Kasa shuru tayi ganin kusan awa guda bata motsa daga yadda take ba,ta tabo hanan dake gefanta

"Wai meke damun bilkisu kwana biyu" cikin mamaki hanan tadubi afnan din,don tunda suke bata taba jin takirayi sunanta ba saboda takun saqarsu,kai ta girgiza

"Oho mata,waya sanmata ne" idanunta kan bilkisun dake duqe saman benci

"Kamar tana cikin damuwa" sake daga kai hanan tayi daga kwafar note din da take ta dubeta

"Meye damuwarki a ciki ke idan hakanne" kafada ta daga

"Nima ban sani ba" daga haka tabar zancan,saidai batasan me yasa idanunta suka kasa sauka daga nahiyar da take ba,har zuwa lokacin da aka aiko kiran bilkisun daga office din principal.



     Tayi mamakin kiran,don tunda take bata taba yin wani laifi ba cikin makarantar ballantana tace ko wani abun tayi akeson ganinta,hakanan tamiqe tana gyara hijabinta cikin kasala da mutuwar jiki taja qafafunta tafice.



       Ba jimawa afra tafita fitsari,sai gata tadawo tana qunshe dariya,hanan ta dubeta

"Lafiyarki ke kuma?"

"Wallahi wani abun tausayi nagani kuma abun dariya,mutuniyar billy ana can ana sharbar kuka a office din principal,babanta yazo yacireta daga makaranta,aure zai mata,aurenma na dole,ke kinga baban nata kuwa?,kamar wani mai tallan agwaluma,ke wallahi me yanke flowers din gidanmu yafishi kyan gani,kuma kina gani kinsan babanta ne wallahi" dariya duka wadanda ke role din suka fashe dashi,ga mamakinsu afnan kallonsu kawai tayi ba tare datace komai ba,tausayin bilkisun taji ya saukar mata,ashe da gaske ne ita din ba diyar kowa bace?,ashe abinda yake damunta kenan cikin kwanakin nan?,shiko me yasa zai cireta daga makaranta,duk qoqarinta da himmarta nazuwa makaranta,kaf ajinsu itace take daukan na daya kowanne tearm,afnan din ke mara mata baya ata biyu,ko ya gaji da biyan kudin makarantar tasune?,tunda a yadda afra ta siffantashi tabbas ba qaramin namiji bane mai irin wannan qaramin qarfin dazai iya biyan kudin makarantarsu

"Wai bakiji mutuniyarki bane?" Hanan ta tabo afnan tana fada dariya tana cinta,wani kallo tayi mata sannan tace

"Naji mana,amma banga abun dariyar bane,tunda dai macace 'yaruwarmu,muma xamu iya fadawa irin qaddararta" shuru kowannensu yayi da mamaki suna duban afanan din

"Kuna mamakine?,bilkisu bata taba yi mana laifin komai ba,inda ace za'a titsiyemu da bulala ace mu fadi abinda ta taba yi mana duk cikinmu babu mai amsa,saimu da muke cusguna mata ma amma bata taba tsayawa ta biye mana ba...."



       Shigowar bilkisun ajin yakatse sauran maganar tata,kallo daya zaka mata kasan tasha kuka bana kadan ba,tawuce seat dinta tazauna gamida maida kanta yadda yake dazun.



       Har duka periods din suka qare aka tashi daga makarantar bata dago kanta ba,saida kusan kowa a ajin yafice yabarta kana ta hada jakarta da qyar tawuce itama.



      Duk da uwar ranar da ake qwalawa ko kadan zafinta bai dameta ba,qunci da baqincikin dake cikin zuciyarta yafi ranar zafi da quna a gangar jiki da zuciyarta,da mahaifinta za'a gama hannu a tarwatsa rayuwarta?,wadanne irin azzaluman masu sarautane su?,wadanda basu damu da buqatar kowa ba saita qashin kansu,dama duka qarya ce da shaci fadin mutane da suke cewa

"Masarautar kaisa badai adalci ba,dukka mai neman adalci to kansa tsaye yanufeta" gashi ita yau adalcin take nema xalla daga garesu amma sun gaza dubanta,indai da gaske ne daga masarautar kaisa akeson shirya mata wannan abun,indai da gaske ne afnan jinin masarautar kaisa ce iya dabi'u da halayenta kawai sun isa su gaya mata cewa lallai sudin mutane ne masu dagawa zalunci da takura,inama ace wanda yamutu yana dawowa yau ummanta tazo taga halin data tafi tabarta a ciki,inama ace wanda yayi nisa yanajin kira anty zuhriyya tazo taga yanayin datake shirin afkawa ta tsamota,tasamo mata adalci da nutsuwar ruhi.



     Tafiya kawai take ba tare da tasan inda take jefa qafarta ba,bata ankara ba tajita tsamo tsamo cikin wani ruwa,sai a sannan ta maida hankalinta,ta duba dakyau sai taga ashe kwatace,dai dai sanda motar dake dauke da afanan take dosowa wajen.



      Tun daga nesa taga kamar bilkisun,a hankali ta bada umarnin ya gangara gefan titin,tana tsaiwa motar tabude murfin da kanta kana tafito tana qarasowa inda bilkisun ke tsamo qafafunta tana son ci gaba da tafiya ba tare data damu da tsaiwa tayi ratse koda a fanfunan gefan hanya bane ta gyara jikinta.



      Riqotan da akayi ya sanyata tsaiwa

"Bilkisu bilyamin" taji an furta a hankali,yadda aka kira sunan yasanya tagene daya daga cikin 'yan makaranta ko ajinsune,saita waiwaya don taga waye,mamaki ya cikaya ganin afnan abdallah mu'az kaisa tsaye tana dubanta cikin alhini da mamaki

"Ya akayi kika fada kwata bilkisu,me yasa bakihau mota kin koma gida ba bayan baki da lafiya" kai ta kada

"Ba komai,yanzu zan isa gida" tasan ta fadane kawai,amma ko ba'a gaya mata ba tasan akwai tazara tsakanin unguwarsu da unguwar da makarantar tasu take

"Ki tsaya ki wanke jikinki,karki dinga tafiya ana kallonki" bata tsaya jin amsar bilkisun ba tayi magana daga cikin motar,saiga drivern yafito cikin hanzari hannunsa dauke da ruwan roba manya guda biyu.



     Baki tasake yadda taga afnan din ta balle ruwan roban takama gefan unifoarm din nata cikin rashin damuwa tana tittilewa a jiki tana wanke ruwan kwatar,saita kai hannu da sauri ta riqeta

"Zubamin zan wanke dakaina" murmushi ta sakar mata,bata musa din ba taci gaba da xuba matan tana wankewa,lokaci lokaci tana satar kallon bilkisun,harga Allah tausayi take bata,ta tsani kalmar auren dole,koda a littafine take karantawa tota aje littafin kenan,saboda bata manta dauki ba dadin da aka dinga yi cikin gidansu ba lokacin da maimartaba yaso baiwa arifa yayarta tabiyu wani ba,yadda arifan tashiga tashin hankali qwarai harsu kansu saida suka tayata shiga damuwa,daga baya dai Allah ya warware da yake wani baya auren matar wani.



     Tas tawanke,ta kama inda zai matsu ta matse kana ta yarfe

"Na gode" tafada a sanyaye tana duban afnan,tare da mamakin meya sauyata haka?,don ko amafarkinta bata taba tsammanin afnan din nada tausayi da sauqin kai ba

"Ba komai,kishiga mota saimu saukeki a hanya" motar takalla kana ta kalli afnan,tana qoqarin hadiye wani abu dake taso mata,hala afnan tana cikin masarautar kaisa ne amma batasan dukkan abinda ke faruwa ba,da zata iya data gaya mata cewa a yanzun ta tsani dukkan wani abu daya shafi masarautarsu,saidai ko Allah ma yace kada laifin wasu mutane yasa ka kasa yi musu adalci,babu ruwan afnan cikin batun,don ga alamu sun suna batasan ma meke faruwa ba,wala'alla data sani ko kallon tsiya ba zata mata ba bare na arziqi,a yadda suke da ita abaya na rashin jituwa a tsakaninsu

"Ki barshi,zan iya qarasawa ai,kada na bata muku mota da danshi,kinga a jiqe nake,na gode sosai" saita soma takawa,tausayinta takeji sosai,ba zata iya barinta tawuce ba,saitasha gabanta

"Don girman Allah kishigo mu saukeki,bakyau maida alkhairi" ta kashe mata jiki,tilas tabita tabude mata murfin motar,sai data soma shiga sannan itama afnan din tashiga.



      Wani sassanyan sanyi ne yasoma ratsa kowanne loko da saqo na jikin bilkisu yana busar da gumin da ada ta hada saboda tafiya a zafin rana data soma,sanyin da rabonta data jisa tun lokaci anty zuhriyya na rayuwa a kusa da ita,duk da yanayin da take ciki sanyin ya mata dadi,saita lumshe idanunta kawai tana jin yadda motar ke tafiya wani suuuuu kamar ba saman kwalta suke tafiya ba,kai kace a iska ko a sama suke tafiya.



      "Kiyi haquri xan miki shishshigi bilkisu,duk da ina zaune aka gayamin,ban sani ba gaske ne koba gaske bane,amma indai da gaskene auren da bakiso za'a miki,kizo na kaiki wajen abbana,na tabbatar da cewa zai hana faruwar hakan,don tun daga cikin gidansa zuwa al'ummar qasarsa ya haramta auren dole tun daga kan yayata arifa" idanunta tabude akan afnan,ashe haifaffiyar sarkin kaisa din ce ita,hakan na nufin ita din 'yaruwa ce ga yarima wanda akeson bata?,uwa daya ko uba daya ko uwa daya uba daya?,rashin sani yafi dare duhu,batasan daga can zancan yataso ba take da yunqurin kaita don samun adalci,akwai adalci da gaske irin wannan a masarautar amma ya kasa biyowa ta kanta?,waishin ins matsalar take ne?

"Karki damu,babu damuwa,na gode da kulawa" abinda tace mata kenan,don koda ace ba daga gidan tushen matsalarta take ba bazata iya kai mahaifinta qara kan zai aurar da ita ga wani ba komai lalacewar mahaifin nata.



        Basu sauketa a hanya ba kamar yadda da farko afnan ta fada ba sai da suka danganata da bakin layin

"Na gode" tasake maimaitawa tana duban afnan din,itama ita take kallo cikin murmushi tace mata

"Babu komai" koda sukayi gaba da kallo tadinga bin unguwar tasu,tana ganin tarin banbance babance qarara,wane sashe na zuciyarta yana sake cika da tausayin bilkisun,da kuma ganin kuskurenta qarara na sanya 'yar tsama ga innocent mutum kamar bilkisun,wadda bata taba taka mata ba bare ta zubar mata.



**************



     Cikin irin kebantattun lokutta da take warewa ne domin iyalinta,tana zaune a falonta na musamman,sanye take da doguwar riga mai hade da hula na wani irin yadi mai sulbi da taushi,afnan ce kanta saman cinyarta,hannunta riqe da wayarta,saidai hankalinta bai kan wayar tata gaba daya,ta ta'allaqashi ne wajen bawa amminta labarin bilkisu,da abinda ta fuskanta daga rayuwarta duk da bata taba bude baki anyi magana makamanciyar haka da ita ba,har sai da fulani aysha ta soma gajiya dajin labarukan autar tata afnan tace da ita

"Baki da sauran abunyi mata ai afnan,tunda tace babu komai tagode" cikin shagwaba irin ta wadanda suke auta a wajen iyayensu tace

"Toni ammi tausayi take bani wallahi,da bama shiri amma yanxu tausayinta nake"

"Ai shikenan,saikiyitayi,daga min cinya hakanan na huta" tana dagawar jakadiya tayi sallama bakin qofar falon tana jiran abata izini tashigo,saita dubi afnan

"Idan kin fita ki mata ixini" amsawa tayi dato tana gyara yafen mayafinta,kana ta wuce jakadiya kuma tashigo.



      "Allah yabaki yawan rai....an shaidawa ubabatu kuna son ganinta,gata kuma ta iso"

"Anyi mata izini tashigo"

"An gama Allah ya taimakeki" daga haka tajuya tafice,cikin qiftawa da bismillah umma luba ta bayyana cikin falon.



      Babu jinkiri fulani aisha tasoma zayyana mata dalilin kiran

"Da farko munason ki shaida musu a sanda zasu tashi zuwa gidan zama nawucin gadi kafin a kammala musu ginin gidansu kafin lokacin da za'a daura auren....zamu dauketa zuwa gidan da za'a kebeta...inason ayi mata horo na musamman,ayi mata gyara na amare na musamman irin gyaran da aka jima ba'a yiwa wata diya ba,duk da cewa xabinmu ce zuwa wani lokaci amma ko babu komai zatayi tarayya da jininmu ne,sabida haka inason a sauyata amantar da ita wacece ita,a dabi'anceta da dabi'a ta gidan sarauta,halayyarsu yanayin maganarsu da sauransu saboda yarima yaji dadin zama da ita ba tare da yana tuna wani abu na daban ba,ko yaji damuwa cikin ranshi,bayan wannan inason ayi mata training na yadda zata kula kanta,babu buqatar takoyi yadda zata zauna dashi,don iya aikinta kawai zataje tayi,kula da komai nashi yana da masu yi masa shi,bana buqatarma takoya din saboda wasu dalilai nawa dana barwa kaina sani,abu na iko,inason ki shaida musu,su lissafa dukkan adadin dukiyar da sukeso a matsayin dukiyar auren 'yarsu,ko nawa ne zamu biya,su fadi ko nawa suke da buqata daga nan har zuwa ranar rabuwarsu,bisa sharadin idan an rabun,zasu manta cewa 'yarsu ta taba auren mai suna abdul'azeez,yariman masarautar kaisa,munason rabuwa tahar abada,ta rayu takuma ci gaba da rayuwa babu shi ko digo cikin tunaninta,wannan shine babban bangare kuma babban sharadi na tafiyar alaqarmu,samun akasin hakan kuma dai dai yake da faruwar kowanne abu...." Saita tsagaita tana maida numfashi

"Wannan sharadin kusan shine abu na farko dana fara shaidawa mahaifinta,yakuma yarda yayi na'am da hakan dari bisa dari" kaita gyada cikin nutsuwa sannan tadora

"Ko a mafarki bama buqatar su hado diyarsu da wani abu,itadin kawai zallarta muke da buqata....abu na qarshe shine,za'a daura aurensu cikin masarautar mali cikin ahalina ba'a qasar kaisa ba,daga nan zamu dauketa zuwa muhallin da zata zauna na tsahon shekara daya,ba zata bar wajen ba harsai sanda kwanakin suka cika"

"Allah yabaki yawan rai an gama,wannan saqo zai isa kunnensu da izinin Allah" kai tasake jinjinawa

"Da kyau,ina da buqatar hotonta wanda zai turawa yarima don yaga irin zabinmu....jibi zata bar gidansu zuwa gidan da muka tanadar mata tazauna,zamu aika da mai hoton can,inason a zaman ya kasance kina daya daga cikin masu kula da ita,har zuwa lokacin da zasu wuce mali,tukuicinki kuma kizauna ki zaba dukkan abinda kikeso a duniyar nan,matuqar mun mallakeshi xamu bakishi"

"Godiya nake Allah ya taimakeki,wannan karamcin naki da bashi da kwatankwanci bakina yayi kadan yayi miki godiya,kalmomin bakina sun qare fulani". Umma luba ta fada cikin rudewa da zallar farinciki.



      Ƙarfe biyu da rabi na dare ne amma saika tsammaci tsakiyar rana ce tarwai saboda yadda idanunta suke a bushe kuma a soye raqayau,babu digon wani abu mai suna bacci tattare da ita,bata jin koda alamarsa duk kuwa da yadda ya qware wajen iya sata.



      Ji take kamar zata zauce a duk lokacin data tuna kalaman da mahaifinta ya gama rattaba mata daxu bayan sallar isha'i,YA SAIDA ITA,YAYI CINIKINTA wannan itace kalma mafi sauqi daya kamata mahafinta ya gaya mata akan hanyar dayabi ta dogon sharhi kan buqataun masarauta akanta


Jin zantukan nashi take tamkar a shirin film ko kuma a qagaggun labari na hikayoyi,wadan nan sharuddan da dokoki dukkansu sunfi kama dana matar da za'a siyeta a matsayin baiwa ba 'ya ba,ta ina zata fara?. Ta ina lamarin zai yiwu?. Saita waiwaya tana duban qannenta dake kwance suna bacci ba tare da sunsan gagarumin tashin hankalin dake fuskantarsu ba. Ta ina zata soma barin wadan nan bayin Allahn da yafi kyau a kirasu da marayu?. Ta yaya zasu iya jurewa rashinta?. Wa zata barwa su?. Umma katti?,mama ladi?,koko mahaifinsu da yafi kowa rashin damuwa da rayuwarsu,wanda asanda take masa bayaninsu ma cewa yayi basu da wata damuwa tunda zasu samu sauyin muhalli,zasu kuma samu ci sha da suttura maikyau.



      Wani abu dake mata yawo saman kwanyarta kamar ana mata tafiyar tsutsa haka tadinga ji,ta dinga kaikawo tana tafiya tsakanin qannen nata daga bango zuwa bango na dakin. Ji take kamar ta zura da gudu tabar gidan...tabar qasarma gaba daya,da sauri ta juya tafice daga dakin,saita tsinci kanta tayi hanyar soro tana muradin ficewa.



      Sanda tabude qofar gidan babu abinda yasoma mata maraba sai zallar duhun dare,wanda ya cukudu da haushin karnuka daya cuka anguwar tasu

"Wa kika barwa su?" Daga qasan zuciyarta aka jefa mata tambayar data sanyata tsaiwa cak

"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azim". Tasamu kanta da furtawa sau babu adadi,wanda wannan ya taka rawa wajen sanyayar jikinta,tamaida qofar ta kulleta kamar yadda take,kana ta janyo qafafunta zuwa cikin gidan.


 

        Maimakon tanufi dakinsu kai tsaye saita durfafi bakin famfonsu gadan gadan,ta kunnashi kana ta duqa gami da tara hannayenta,saita bige da alwala.



      Bata damu da neman abun salla ba,hakanan saman dandaryar sumuntin dakin ta tada sallar,sallar data jata har zuwa lokacin da akayi kiran assalatu,ta bada farali wanda daga wannan bata kuma sanin abinda ke faruwa ba,gwanin iya sata ya saceta duk da yadda take kokawa dashi da nuna mishi nata maraba da ziyararshi.



        A kallon farko zaka san cewa babu wani abu da yayi kama da sukuni tattare da ita,duk wata wulgawar da yaran zasuyi binsu take da kallon zallar tausayi,bata ankata ba tuni mahaifinta yagama gaya musu cewa zai aurar da yaayarsu,wanda hakan yayi masifar dugunzuma hankulansu gaba daya,tana zaune tana saqa da warwara sai ganin yara tayi sun sata a gaba gamida zagayeta,gabanta na faduwa tana fatan ba abinda take hasahe bane ta tambayesu lafiya

"Aure wai zakiyi yaaya inji baaba,kema aure zakiyi ki tafi kibarmu mudaina ganinki yaaya?" Hauwa ce tajefa mata tambayar cikin matuqar mutuwar jiki dakuma saddaqarwa.



      Da idanu ta dinga binsu da kallo dai dai da dai dai,tana jera kalaman da zata gaya musu,saidai yanayin dake saman fuskar kowannensu ya sagar mata da gwiwar kowanne yunquri nata,tausayinsu yasake ninkuwa cikin zuciyarta,qwarin gwiwarta da karsashin data tattaro suka baje,ta rasa abin cewa,sai kawai ta sanya musu kukan data jima tana boyewa,karo na farko a rayuwarta,karon farko data nuna gazawarta a gabansu,abinda komai girman nauyi da tsanani bata taba bari gazawarta ta bayyana koda saman fuskarta ba,saboda tasani itace kadai qwarin gwiwarsu,itace kadai hope dinsu,batason tayi abinda zata kashe musu fata da burinsu da dukka suka aza wuyanta.

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: 20


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

________________________________




       Kuka take haiqan irin kukan dake nuna zallar tashin hankali da shiga taskun rayuwa,fuskarta kife a tafin hannun hannatu,yayin da dukka yaran suke kewaye da ita,kowannensu kuka yake kamar yadda yayar tasu take,kai...tama zarta yaya a wajensu,uwa ce kuma ubace gata sannan jigo cikin rayuwarsu.



      A yau din da ake niyyar tsigeta daga cikinsu akaita can wata uwa duniya ji take kamar ana shirye shiryen zare ranta ayi jana'izarta ne,tana hasashen rayuwa babu qannenta,bayan babu wani tartibin hannu da zata barsu,dukka bayanan da mahaifinta yayi mata akansu basu gamsar da ita ba,me jiya tayi ballantana yau,meya tsinanawa rayuwarsu a baya bare a yanzu,ya ilahi me tasa babu wanda yaduba kokenta?,babu wanda yaduba quncinta?,babu wanda ya waiwaya yaduba uzurinta?,kowa yasanya buqatarsa gaba fiye data kowa?,kowa nashi muradin shine a gabansa?.



       Dai dai lokacin data soma jiyo hargagin mahaifinta daga tsakar gidansu wanda yasoma zama filin Allah,saboda tuni akayi nisa wajen rugujeshi,yana zubawa umma katti masifa,wadda a yanzu take tsananin yi masa biyayya da takatsantsan,kan tashiga tafito da maigadon,ubanme takeyi mutane suna jiranta a waje?,kai kace irin amaren nan da ake shirin kaisu gidajen mazajensu a yammacin daurin aurensu.



       Kafadarta umma katti ta dafa cikin tausasa harshe tace

"Haba maigado,kamar zaki barsu hannun bare?,bayan ga mahaifinsu gani da nake kamar uwa a wajensu?,ki kwantar da hankalinki,kamar yaune zakije ki dawo ki samesu lafiya kinji?,don Allah karki tashi hankalinki". Sai a sannan ta daga rinannun idanuwanta tana kallon umma katti,kallo take mata irin kallon da wanda aka cuta yakewa azzalumi,tsahon xamanta tare da ita zata iya cewa bata taba jin lafazi mai dadi daga bakin umma kattin ba sai a dan tsukinnan da aka fara wannan sabgar,bata daukan zamanta tare dasu a matsayin wami abu mai alfanu,tunda shekarun dukka da suka shude basu canza komai ba,sai yanzu?,amma yata iya,dole tayi magana da ita,cikin muryar dake nuna kuka ya suqeta tace

"Ga amanar Allah nan a hannunki,Allah shine shaida umma"

"Karki damu,qannenki ba zasu tagayyara ba,mu da zamu shiga rayuwar daula da hutu?,rashin abinci da suttura dukka fa zai zame mana tarihine a rayuwarmu" ta qarasa fada tana murmushi da alamu abun yana mata dadi,cikin qunci da takaicin umma kattin tadauke kai daga gareta,dole tayi farinciki tunda tasamu mafita ba tare da an taba martabar nata diyan ko guda daya ba,saita dubi hannatu,ta kama hannunta tariqe tsam hawaye naci gaba da kwaranya

"Hannatu,bayan babu ni kece makwafina....na baki dukka amanar qannenki....ina fata zaki zama jaruma,zaki sanya dukka qarfinki ki tallafesu a yayin da sukayi rauni" kuka tafashe dashi sosai,cikin sheshsheqa tace

"In sha Allahu yayaa,zamuyita miki addu'a Allah yadawo mana dake" saita dauke idanunya daga kan hannatun tamaida kan qannenta,kowanne da abinda ta gaya masa gwargwadon sanin halinsa da tayi,hauwa'u ce tashin hankalinta yafi nakowa,takuma sanyata kuka fiye da wanda tayi a baya,da lafuzzan bakin yarinyar tafice daga gidan ba tare data jira rakiyar da umma katti da mama ladi keta qoqarin yi mata ba,ba tare data jira ba tabude motar da kanta tashiga,kana ta cure waje daya saboda sanyin ac da bala'in da takeji yana gigita rayuwarta,tana sake fashewa da wani kuka mai azabar radadi dacin rai kamar ana yankar zuciyarta ta sake kame jikinta waje daya

"Shikenan yaaya idan kika tafi kema,kinga har yanzu ba'a ga mamata ba,bayan kince ko batazo ba ke zaki kaini gurinta,shikenan kema kin tafi ko yaaya?".



      Batasan motar tatashi ba bare taji alamun tafiyarta,tunani ne kala kala fal cikin kwanyarta,zuwan abubukar saddiq tatuna,mutum na farko bayan afnan da taga yanuna damuwa qarara saman fuskarta kan yanayin datashiga,fuskarsa ta hango lokacin da babanta ke rattaba mata ya zaba mata miji,biki saura sati biyu,karya sake ganinsa qofar gidansa,data san da zuwan wannan ranar data tsaya ta saurari abubakar,wala'alla ya zame mata garkuwa,da tasan da afkuwar wannan mummunar qaddarar dako amanar qannenta tabari a hannunshi,duk da batasan wayeshi ba,batasan halayyarsa ba,amma hakanan jiki da zuciyarta suke bata gwara shi akan mutanen gidansu,jikinta yake bata zai iya,zai iya kula mata dasu,saidai dukka bakin alqalami ya riga daya bushe babu makawa.



       "Ranki ya dade mun iso" taji ana fada daga gefanta,abinda ya sanyata dago kai kenan cikin mamaki tana duban mai maganar,umma luba ce,saidai wannan karon tana maganar cikin qanqan da kai da wani irin respect,kai kace ubangidane da yaronshi.



      "Duk abinda akace kiyi bakiyi ba,ko kika musa tsahon wannan yarjejeniyar,Allah ya isa tsakanina dake ban yafe miki ba" taji zuciyarta na tuna mata kalaman mahaifinya na qarshe,wanda dasu ya sallameta,wata iriyar dakiya taji tazo mata,wai meye yaragewa saura a rayuwarta?,tabarsu kawai,tazuba musu idanu koma me zasuyi suyi,idan sunso su rabata da ranta.



        Cikin mutuwar jiki ta zuro qafafunta tasauko daga motar,sai kuma ta tsaya cak tana duban gidan,tsoro yana son shigarta.



     Wani irin qawataccen gida mai cike da ni'imar dake bayyana kanta tun daga farfajiyar gidan ba tare da kakai ga shiga cikin gidan ba,tasan cewa sanda suka baro gidansu rana ce tarwai mai zafi a sararin subhana,amma ga mamakinta gidan babu alamun rana tattare dashi,sai wata irin iska mai dadi dake kadawa,ko ina luf luf yake,kamar ka shiga wata qasaitacciyar gona,tafiyar da sukayi daga gidansu zuwa nan din a qiyasinta bazai wuce tafiyar awa daya ba bare tace kafin su isone yammaci lis tayi

"Ga hanyar da zamu shiga cikin gidan nan,ki kwantar da hankalinki,tun daga nan zaki gane kin soma samun sauyin rayuwa" umma luban ce dai tasake fada cikin taushi tana nuna mata hanya,ala wadai da sauyin rayuwa irin wannan,sauyin rayuwar da zai doraka bisa wani SIRADI da bakasan qarshensa ba,sauyin rayuwar da zai sanya asiyeta tataho bauta kwatankwacin yadda ake cinikin bayi ada,wanda banbancinsa da wancan kadanne,sauyin rayuwar daxai binne dukka wani buri nata,ya rabata da 'yan uwanta,ya katse mata karatunta,ita kuwa me zatayi da wannan sauyin?,dukka wadan nan maganganun tana yinsu ne a lokacin da suke takawa zuwa hanyar da zata sadasu da falon gidan.



       Tun daga falon ta fahimci lallai akwai banbanci mai tarin yawa da sauyi da rayuwarta ke fuskanta,makeken falone wanda yake dauke da dukka abubuwan more rayuwa,saidai bata da nutsuwar xama ta kalli wani abu,a qalla ta tadda ma'aikata nata kawai kusan guda biyar,suna shiga suka soma zubewa cikin girmamawa suna gaidata,bata iya amsawa ba saboda abu uku,baqinciki haushi da takaici,abun sam bai burgeta ba ko kadan,umma luba bata barta anan ba sai data danganata da wani hamshaqin daki daya amsa sunansa,dakine da iya kallonshi ma wata ni'imace ta daban bare kasancewa a cikinsa,ko daya bai bata sha'awa ba duk da yadda aka tsarashi,aka kuma qawatashi,saita zabi zama qasan dakin tana ririta zuciyarta gamida wassafa yadda rayuwarta zataci gaba da gudana cikin wannan dakin.



       Azahar tanayi umma luba ta gabatar mata da abinci har cikin dakin ba tare data nemi ta fito muhallin da aka tanada ba saboda cin abinci dake falon.



       Wata iriyar lafiyayyar shinkafa ce da kaza da hadin salad,sai farfesun nama dana kifi kala daban daban,bayan nau'ikan lemuka,ko a idanu abincin yafi qarfin cikin mutum daya,amma dukka aka jere saboda ita daya,ko kadan abincin bai burgeta ba bare ya bata sha'awa,a sannan tunaninta shine,su hannatu sunci abinci?,idan sunci me sukaci?,waye yabasu?,waye yakula dasu?,sai wani kukan ya balle mata,a maimakon cin abinci saita sanya kanta tsakanin qafafuwanta taci gaba da rerashi.



        Sosai umma luba tazauna tana bata baki gamida lallashi dason shawo kanta,ko daya batason ganinta kojin kalaman bakinta,don kusan itadin itace ummul aba'isin fadawarta kowacce musiba a rayuwa,banda ta zabeta...banda tazo har gida ta shaidawa mahaifnta....takuma yi masa romon bakan abinda zai samu....da tuni iyanzu tana csn cikin qannenta,duk da rayuwarsu babu wadata sai fatara qunci talauci da yunwa,amma tanajin tafiye mata sau dubu fuye da wannan rayuwar da batama soma fuskantarta ba,rayuwar da akayi cinikin 'yancinka na wasu watanni aka miqaka ga hannun wasu.



       Ganin cewa umma lubar ba zatayi shuru ba saita miqe kawai ta durfafi inda ta nuna mata dazu bayan sun shigo a matsayin bandaki,tatura tashige kana ta maida qofar tarufe,saita samu gefan bathtube tazauna ta dora daga inda ta tsaya,sai datayi mai isarta,taji ta rage wani nauyi sosai daga qirjinta sannan ta dubi agogon data lura dashi cikin bandakin tun shigowarta,lokacin sallar azahar yayi harma yadan gota,don haka tazarce da daura alwala kana tafito.



       Sanda tafito babu kowa cikin dakin,da alana tagaji da jira tafita,saita kintaci gabas kawai ta tayar da sallarta,ko bayan ta idar dinma bata kallo sashen da abincin yake ba,haka taci gaba da zamanta tunani kuma ya qulla qawance da ita.



     Ã†˜arfe biyar da 'yan mintuna na yammaci taji an dan taba qofar,tsahon sakanni batace komai ba tana duban qofar,sai taji an turo an shigo,baquwar fuska ce da bata santa ba,hannunta riqe da wani abu,cikin girmamawa ta rusunar da kanta tana cewa

"Ranki ya dade,mai gyaran jiki ce ta iso,tace a shaida miki,daga wajen fulani take" jim tayi kamar ba zata amsa ba,saidai ko bata amsa din ba babu abinda zaya canza,don haka saita miqe kawai tana gyara hijabinta wanda tun daga gida ta taho dashi

"Ammm....afwa ranki ya dade,ga wadan nan kayan,su zaki canza kafin kifita" wani kallo ta watsa mata kana tawuceta tana shirin ficewa,saboda tsabar wulaqanci suturar da tazo da ita daga gidan uban nata ma sai an rabata da ita saboda tsabar raini,da sauri tace

"Ranki yadade kiyi haquri ki canxa,fitarki a haka zai janyomin matsala,ki taimakeni" tsaiwa tayi tana dubanta,yadda ta marairaice mata ya tabbatar mata da iya gaskiyarta ta fada mata,sai taji tausayinta ya tsarga mata,wala'alla itama bata da iko da kanta sai abinda aka bata umarni,saita dawo da baya ta amshi kayan daga hannunta,ganin haka yasanyata juyawa tafita daga waje don ta bata damar canzawar.



      Saman gado tazube kayan kana tasoma daddagasu da É—ai É—ai da É—ai É—ai tana qare musu kallo,ko ba'a gaya mata ba tasan cewa kayane masu daraja da tsadane,wani santsi da sulbi suke,doguwar riga ce mai wani irin wadataccen mayafi,haka ta ware kayan ta sanya ba tare data damu da kyansu ko tsadarsu ba,kawai zatayine saboda matar kada ta gamu da matsala kamar yadda ta nemi alfarma a wajenta.



      Wani kebantaccen dakine na musamman ta taras da matar zube ita da kayan aikinta,kana gani kasan ta kusamman ce,kuma takanas aka daukota saboda aikin,dukkan abinda ake bilkisu idanune nata,tsahon awanni biyu cas tuni an soma fidda ainihin kyan choculet colur skin dinta,an yashe duk wani datti ko gashi dabai dace da saman fata ba,hakanan gashinta tana kallo aka masa É—ai É—ai akayi masa wankan tsarki,duk da cewa shidin bawai datti ne dashi ba,saidai wani samfurin gyara da aka masa yasake masa tsaho santsi dakuma laushi.



***********



     Kwanaki uku kenan tana cikin wannan gidan,wanda dukkan wani nau'in abubuwa na morewa rayuwa babu abinda ba'a aje mata ba,saidai iyakarta dakin sai dakin da ake mata gyaran jikin da babu abinda tafi tsana a duniya sama da yammaci yayi azo wannan hidimar,bata taba yarda ta taka wami wajena gidan na daban ba baya ga wannan dakunan guda biyu,abinci kuwa iyakarta na safe sai kuwa na dare,kowanne tsakurarsa kawai take abisa dole badon son ranta ba,gadon dake dakin kuwa iyakarta dashi kallo,ko sau daya bata taba kwatanta kwana akanta ba,yan uwanta ne tsaye a ranya fiye da komai,hatta da makarantarta yadda ta qwallafa rai tariga daga sallama amma tunanin qannenta bai bar ranta ba,kwanakin ajere ana mata wannan hidimar ta gyaran jiki,cikin jikinta a karan kanta tasan cewa akwai gagarumin sauyi,amma taqi baiwa kanta cikakkiyar damar karantar haka bare har takai ga duba xuwa wannan.



        Ta dade da zubawa sarautar Alla idanu,takuma zama kamar mutum mutumi,saboda tasan cewa tawayenta babu abinda zai qareta dashi,kanayin tawaye ne a inda kasan kana da abin fada kana kuma da gata sa'annan za'a daga kai a dubi buqatarka.


***************



     Wasu irin kalolin fitilune ke kamawa da kashe kasu  a qaramar harabar da aka qawata kawai saboda daukan hotunam bilkisu da za'a turawa yarima azeez,daga gefe tana zaune saman wata qawatacciyar kujera,ba kujerar bace abar kallo,kwalliyar da aka mata mai kyau sanyi da kuma tsari shine abun kallon,ga dukkan wanda yasan bilkisun kace ya kalleta tayi sharhi guda daya tak zai gaya maka cewa

"Ban taba sanin haka bilkisu keda kyau irin nayau ba,ashe choculet fatarta ba qaramar baiwa bace dakuma qarin sirri cikin kyanta".



      Wasu irin kayane dake nuna alfarmar masu alfarma a jikinta,suke kuma nuna mulki da qasaitar dukkan masarautar da suka fito daga cikinta.






*_kina buqatar kayan qwalama da kwadayi da kuma maqulashe😋😋,abubuwan motsa baki masu kyau tsafta da kuma inganci?_*


*_Garxaya ki nemi MRS SCHOOL TREATS_*


*_nasan zakuce to me kenan?_*


*_RUGUNTSUMIN GAMAYYAR WAJEN SAMAR MUKU DA KAYAN MAQULASHE IRI DABAN DABAN,DA SUKA HADA DA_*


*tuwon madara mai kwakwa da marar kwakwa*


*da kuma*


*Gullisuwa*

*_dukka na zallar madara mara algus_*🤗 


*_cikin nagartacce tsafatatacce_kuma ingantaccen package mai kyau_*


*SIYAN DAYA KO SARI*

_Kar kuyi sanya,maza ku nemeta a tudun wada,hayin buba GUSAU_

_ko kuma akan numbar waya 08069706638_


*_SUNA AIKAWA KOWANNE GARI DA IZININ ALLAH CIKIN AMINCI_*


*_biyan buÆ™atar abokan hulda shine burinmu_*ðŸ¤Ã°Å¸½Ã°Å¸¤Ã°Å¸½

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: 21


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_________________________________






   BaÆ™iƙÆ™irin ranta yakekamar yadda fuskarta take a murtuke kai kace saqaon mutuwa aka aiko mata dashi,idanunta na kafe waje daya ranta yana suya,babu wata sauran daraja itakam data rage mata,hotunanta sune abun dauka da turawa wani da namiji?,hawaye taji masu dumi sun taho daidai lokacin dame hoton yagama saisaita komai yafara daukan hotunan.



      Ji tayi zuciyarta ba zata iya dauka ba,saboda haka tamiqe ana tsaka da dakn hotunan tawuce zuwa dakin da shine masaukinta,sai data tabbatar data kulle qofa sannan ta sanya kanta jikin qofar tasaki kuka mai ciwo.



     Ta jima a haka tana kukanta,wanda ba kowa take kokawa ba wannan karon sai kanta da rayuwarta,sai data gaji don kanta kana taja jikinta zuwa cikin dakin tana fidda kayan jikinta wadanda take jinsu tamkar qaya.


**************



      Batasan murmushi take ba a sanda take kallon hotunan har rakai qarshensu,lallai lubabatu ta cancanci a qara mata wani abu kan tagomashin da akayi mata,don ta iya zabe,zabe kuwa na haqiqa,tasan cewa azeez bazai taba kushe wannan yarinyar ba,zata dace da ra'ayinsa qwarai.



       Sauka tayi ta kunna data dinta da kanta,kana tashiga email dinta ta tura mishi dukka hotunan,sannan takashe datar tasoma laluben wayarsa.



       Daidai lokacin da yake sanye da dogon wando da rigarsa mai dogon hannu irin ta sport,qafarsa sanye da rufaffen takalmi wanda zaiyi dai dai da jogging din da yakeyi cikin hasken rana a wanda baiyi zafi da yawa ba,hakanan a layin unguwannin nasu dayafi kama da titi saboda kwalta dake shimfide akan kowanne layi.



     P_cap ce a kansa,kansa saye da headphone wanda idan bakasan me yake yi ba,zaka zaci waqa ko kade kade yake ji,kamar yadda yawancin samarin yanzu suka maida wannan dabi'arsu,a maimakon wannan yanajin tafsir ne na daya daga cikin malamanmu.



      Baisan da tahowarta hakanan baisan ta iso kusa dashi ba sai datayi wave din hannunta a gaban fuskarsa kana ya lura,a nutse ya waiwaya yana dubanta bai fasa tattakinsa ba,itama shi take duba fuskarta qunshe da murmushi har haqoranta suna bayyana,sanye da kayan motsa jiki irin na mata a jikinta,tana ta qoqarin daidaita kafada dashi don kar yawuceta

"Hey!" Tasake fada duk da bata da tabbacin xai jita saboda abinda ke kunnenshi,ya ganta sarai yakuma gane me tace,amma sai yadauke kai kamar bai gani ba ko babu wani mutum a wajen,gamida dan qara hanzari wajen sassarfar da yakeyi,take kuma ya zarce mata,yana kuma kaiwa qarshen layin saiya karya kwana ta yadda yasan zai bace mata.



     Tsaki yaja bayan yadanyi nisa,yanajin haushin yadda bata da zuciya,hakanan yanajin haushin yadda take shige masa hanci da qudundune da yawa,farar fata ce wadda duk da baisan yaren ta ba amma  yanayinta ya nuna masa tabbas baturiya ce wadda baisan daga wacce qasa tafito ba.



      Qarar wayarsa ta dakatar dashi,yatsaya yana qoqarin ciro wayar daga aljihunsa hadi da neman daya daga cikin kujerun da akan ajiyesu haka siddan qasan bishiyoyin dake jere a layin haka siddan saboda hutawar masu wucewa,yadan lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya ganin ammi ce,yazauna sosai yana daga kiran ya kara akunneshi,bayan gaisuwa da suka saba kamar kullum tashaida masa tatura masa saqo na hoton yarinyar,yaduba idan batayi masa ba ayi gaggawar canza masa. Da to kawai ya amsa mata,yana shirin aje wayar takira sunanshi

"Kome kake,koda bata maka ba ba za'a daga abun nan nan da kwana goma ba,already nayi magana da mr james,an gama shirya wannan gidan dana shaida maka,acan nakeso kazauna,ka sameshi ka amshi keys din gidan a hannunsa,kaduba kaga idan akwai abinda baiyi maka ba kobai dace da tsarinka ba,karka manta....bana buqatar kowa yasan dalilinka na barin wannan gidan,hakanan banason kowa yasan inda zaka koma din,dole rayuwarka ta zama cikin privateness,ina fatan ka fahimta?" Kai ya gyada,sai kuma yatuna ba'a gabanta yake ba,dole yabude baki yayi magana don haka yace

"Naji ammi,godiya nake"

"Ohk" ta amsa a taqaice tana datse layin.



     Aje wayar yayi a gefansa,kana ya finciki water bottle dinshi yabude yahau daddakar ruwan,sai dayasha sosai kana ya bame murfin yana sauke qaqqarfar ajiya zuciya,koda yaushe yana kwana ya tashi da mamakin tsarin amminsa,why me yasa ba zata bari yayi aurenshi da safwa ba kamar yadda aka tsara,dama aure yana hana karatu?,dama ana gindayawa namiji lokacin da zaiyi aure ne?,daidai ne hakan ka hana danka ko 'yarka aure harsai zuwa wani lokaci da suka cika maka qudurinka?,dole a haka zai bita har takai ga gacin tsarinta,amma bayajin zai iya hada jiki ko shinfida da kowacce mace bayan safwa har qarshen rayuwarsa.



      Yana gama wannan tunanin ya dauki wayarta tasa da bottle dinsa yaci gaba da tafiya don ya isa gida ba tare da yayi koda sha'awar yabuda hotunan yarinyar ba bare ya ganta,don baya sha'awar yaga ko wacece,don yasan ko wacece itan ba zata taba kama qafar safwa ba,daga inda yake yana iya hangen gida,don haka yaci gaba da takawa a hakali tunani iri iri yana bijiro masa.



       Yana taka qafarsa a qofar gidan wani kiran yasake shigo masa,daya duba yaga safwa ce,kamar tasan ita yake tunani,sai fuskarsa tadan washe,wanda yawanci idan kaga irin hakan saman fuskarsa to yana nuna maka murmushi yayi a sannan,bai jinkiri ba ya amsa kiran kana ya maqaleta a kafadarshi yana saka key don bude qofar gidan.



      "Kamar kinsan tunaninki nake?" Ya fada cikin sassanyar muryarsa,safwa dake kwance saman gado idanunta a rufe batasan sanda tabudesu tarwai ba,fuskarta cike da murmushi,bakinta yakasa rufuwa har sai datace

"What?,are u kidding me?" Murmushi yasaka mai sauti

"Ina miki qarya?"

"No my prince,it was just amazing" ta amsa masa tana zama sosai saman gadon,farinciki yana lullubeta

"Ohkey,let me repeat my self,tunaninki nake sanda kika kirani" farincikinta ya kasa boyuwa harsai data saki qaramar qara,tana bala'inson azeez ya nuna mata ko yaya ita din wani bangarene na musamman a rayuwarshi,hakan ba qaramin faranta mata rai yake ba

"Yau duka wannan kalamin naka shine babbar kyautar dana samu wadda babu wani abu da zai iya siyanta,thank you for making my day sweetheart" murmushi yasakeyi yana shiga falon sosai.



      A falo yacire takalmanshi yana ci gaba da amsa wayar sannan yawuce kitchen don yasamu abu mai zafi ya qarawa cikinsa,ya hada coffe mai yawa har a sannan yana amsa kiran safwan kana yasake dawowa falo.



      Sak ya tsaya yana dubanshi fuskarsa cike da mamaki sanda yaganshi yafito daga corridor din da babu wani daki sai nashi dakin,kamal ne,shima azeez din yake kallo

"Ina zuwa baby" azeez ya fada yana zame wayar daga kunneshi yana ci gaba da duban kamal dake tsaye.



       Ko a karon banza nauyi idanun azeez din kewa mutum bare a wannan karon da akwai qamshin rashin gaskiya tattare dashi,don haka yasoma kame kame da kanshi

"Oh...ashe sai yanzu kake shigowa,no wonder  naje inata knocking amma naji shuru"

"Really?,ina cewa munyi sallama dakai harka amshi aron mota ko?"

"Yeah,na dawo ne saina bawa su jabir suna da lacture sun kusa makara kuma shida mustapha" shuru yadan ratsa,abdul'azeez najin kamar ba gaskiyar ya fada masa ba,amma saiya share kawai,yazauna yaja coffe dinsa yasoma sha,yayin da kamal yayi gaba da sauri yana jin kamar wanda aka sunceshi daga wani tarko.



*******   ********   ******


     "Har yanzu na kasa gano meye abinda suke shiryawa,na kasa karantar da gano meye ne taketa jaddadawa yaron ya kiyaye,batason kowa yasani,taqi yarda ko bada fuskar da za'a shiga jikinta,amintattunta dukka sun kasa siyuwa,wai garin yaya aisha keson zamar mana gagara gwari?" Ta qarashe tambayar tana duban saudatu qanwa ga maimartaba abdallah sarkin kaisa,hakanan mahaifiya ga kamal.



      Nannauyar ajiyar zuciya tasauke

"Aisha wata irin macace ta daban mai wayo basira dakuma fikra,babban matakin nasararta shine rashin saurin yarda da sakin jiki wa mutane,amma koma meye wannan karon bazamuyi sanya ba,zamu durfafeta ita da dukkan shirinta tuquru,sai munga abinda ya turewa buzu nadinsa....yanzu haka na tura kamal dakinsa bincike koda zamu samu wata makama na abinda ke wakana,kiranshi kawai nake jira,shi yasa na hanashi yin nesa dashi,dakuma hanashi rabuwa dashi,zamansu tare dole zaici gaba dayi mana amfani,hakanan dukkan wani shirinmu xai dinga saurin samun nasara fiye da ace suna nesa da juna" kai fulani adama ke kadawa cike da qaguwa,yayin da saudatun ke kallonta can qasan ranta itama tana shirya nata qudurin daban wanda fulani adaman batasan da zamansa ba.



        Kiran kamal ne yashigo wayar mahaifiyarsa,dukkansu kiran yaja hankulansu,ta daga kana ta sanya handsfree,muryar kamal tafito tangaran

"Mom....babu abinda na iya samu ko ganin cikin dakinsa,ba wata shaida ko alama da zata bamu hasken komai fa" dukkaninsu gabansu ya fadi,ransu yabaci,cikin hasala hajiya saudatu tace

"Kamal...ka duba kuwa dakyau?" Hannu ya yarfar

"Haba mom,ke bakisan masifar da naso fadawa ba ne saboda yadda na tsaya bincikawa ko ina,saura kadan yakamani fa,daya kamanin kinsan me zai iya faruwa?,baida sauqi gayen nan fa ko kadan" 

"Shikenan,zan nemeka" ta fada tana yanke kiran gamida maida hankalinta ga fulani adama da hankalinta yayi masifar tashi,ji take kamar ta kurma ihu,kenan saidai su sake sabon lale?,dukka hope din da suke dashi ya rushe?,ita a jikinta tana jin tabbas akwai abinda yake faruwa,abinda idan ya bayyana zai sama musu hanya mafi sauqi da zasu tarwatsa yarima azeez da mahaifiyarsa dama 'yan uwansa,su rusa dukka wata martaba tashi datake idanun al'ummar qasar kaisa.



      "Sun binne kuma sun boye komai,amma inaga...muci gaba da namu shirin,babu abinda zai dakatar damu" saudat ta fada tanason qara musu qwarin gwiwa.


*********    *****   *******



    Cikin kwanaki qalilan dukkan wani shiri ya kammala,fulani tagama shirya komai,takuma sanar a can mali kan daurin auren azeez din,saidai ko a can dinma sanarwar ta bulla ne a iyakacin mutanen da tasan ba zata samu matsala ba,hakanan labarin bazai taba zuwa kunnen maimartaba ko wani da bataso ba.



       Fannin gidan malam bilya daya zama alhaji bilya saboda umra da yaje ta sati biyu a tsukin da ake masa ginin gidan kuwa gini ya kammala,ginin da ko a mafarki bai tana zaton zai mallaki gida kamarsa ba,kowa yasan ginin daa dana yanzu ba daya bane,don duk sanda aka tashi rushe tsahon gini za'a maida na zamani akan samu ashe babban fili ne,to shima kusan hakanne,gidane babba ba'a gane hakan ba sai da aka rushe aka mayar na zamani,babban falo da dakuna harda bene na maigida alhj bilyaminu.



      Umma katti tadauki ciki da falo haka mama ladi,sai yaran suma aka ware musu babban daki mai hade da bandaki da aka zuba dukkan furniture da suturar sawa dai dai da kowa.



       Kafin kace meye tuni alhj bilya ya shaidawa danginsa abun arziqin daya sameshi dakuma bikin diyarsa,nan da nan saiga dangi sun fara zuwa,wasu suga gida susa albarka su tafi,wasu kuma su zauna zaman jiran biki,ko a jikinsa sai dadi da hakanma yamasa,don bashi da matsalar abinci,duk kuma wanda yazo sai yace masa sirikinsa wanda zai auri bilkisune ya masa wannan hidimar,kamar yadda yake cikin sharadinsu ko sau daya bai ambaci sunan angon ba.



      *******   ******  *******



      Duk da motar baqaqen glass ne da ita hakan bai hanata ganin irin sauyin da gidan yasamu ba muraran,ci gaba tayi da duban gidan har sanda motar tasu ta cusa kai ciki,kana aka zagaya sashen da take zaune aka bude mata,ta zuro qafafunta dake sanye da half cover takalmi da yafi kama dana sarauta.



      Bata lura dasu ba saiji tayi gaba daya an taho da gudu an qanqameta,ta daga kai tana dubansu,amina ce hauwa'u sai umaima,yayin da hannatu take qarasowa cikin hanzari da sassarfa

"Yaaya...kin dawo?" Suke jero mata tambayar kusan a tare,sai taji idanunta sun soma tara qwalla kamar yadda yazame mata jiki,ta tsugunna ta rungumesu gaba daya cikin jikinta,inama ace tadawo cikinsu xasu zauna ne din din din kamar yadda suke a baya,abinda basu sani ba shine kwanaki biuu kacal xata qara tare dasu tasake musu nisan dayafi wanda tayi musu a yanzu



     Sun jima a haka ba tare data iya ce musu komai ba,sannan daga bisani tace da hannatu

"Kaini ciki" da murnarta tayi gaba suna biye da ita,kowa yana qoqarin bata labarin irin sauyin da suka soma samu,kunnuwanta kawai ta iya basu tana saurarensu,ba shakka ko makaho yasan cewa sun sami canji,tun daga muhalli dama yanayin sutturar dake jikinsu,saidai ko sau daya zuciyarta taqi maraba da wannan sauyin wanda yake kamar fansa ne na mutuncinta,ko madadine na darajarta wadda nan bada jimawa ba za'a watsata.



        Umma katti tasoma arba da ita a babban falon gidan,tayi darashe darashe saman luntsuma luntsuman kujeru tasanya tv a gaba tana kallo,gefe kuma mutum ukune cikin dangin abbanta wanda suke zaman jiran biki,bikin da takejin za'ayi bikine na saidata ko miqata a mazaunin baiwa.



      Bakin umma katti har kunne tamiqe cikin bada wani irin girma da karramawa tana mata sannu da zuwa,hakama sauran wadanda ta taras,nan aka shiga ana akasa ina aka aje da ita,abun har mamaki yadinga bata da daure mata kai,bata jima a falon ba tawuce tabi qannenta zuwa daki,don tanason taji yadda suka rayu sati biyun da basu tare.



         Shuru tayi tana jin wani sashe na zuciyarta nayin sanyi bayan ta gama sauraren dukka labaransu,babu takura,sun rayu cikin kulawa ci sha da sutura mai kyau,hakanan babu wanda yake tsangwamarsu tsakanin umma katti da mama ladi,hasalima mama ladin na jansu a jiki sosai,tana cewa sune 'ya'yanta yanzu tunda bata da É—a cikin gidan.



       "Ya Allah,ka sake sanya tausayin wadan nan bayi naka cikin zukatansu,kasa suyi musu riqo nagartacce fiye da yadda sukayi niyyar yi" tasamu kanta dayin wannan addu'ar cikin zuciyarta.



      Tunda tazo ta fuskanci ta zama ta musamman cikin gidan,kowa kaf kaf yakeyi da ita,kwananta biyu ana uku suka tashi gagarumin yinin biki cikin gidan,wanda kaf dinsa babu dangin mahaifiyarta ko qwalli daya,basu san ma wainar da ake toyawa ba,daga dangin uba maqota sai dangin kishiyoyin uwa,wanda sukayi farin fitar dango suka cika gidan don kada aci arziqi suma babu su,zuciyarta tacika fal da mamaki dakuma tunani,wasuma mutanen sam ta manta dasu cikin babin rayuwarsu saboda halin qaqa nikayin talauci da suke fama dashi,amma ayanzu kowa ya dungumo yace shidin nasu ne,kuma lallai lallai dashi za'ayi.



      Duk wannan abun da akeyi su kadai suke kidansu suyi rawarsu,don ita wadda ake kira da amaryar batasanma anayi ba,tana daki liqe da 'yan qannenta tana morewa sauran awannin da suka rage musu tare,hatta da dakin da aka ware mata cikin gidan cike fal da sutturu na alfarma wanda zatayi fitar yinin biki dasu nata kalla na bare ta bude tashiga,hatta da barorin da suka taho tare ta sanyasu sun koma gida,don bata da buqatarsu,batason ma ganin wani abu daya danganci masarautar dazai dinga tuna mata da al'amarin dake gabanta na tsahon kwanakin.



      Su dinma hakan baidamesu ba,tunda dai sun samu dukka abinda sukeso,abinci da abubuwan sha na kwali dana roba gasunan birjik sai wanda ka zaba.



      Darensu na qarshe tare tajima dasu tana musu karatun rayuwa wanda ba lallaine su fahimta ba,koda zasi fahimta dimma to hannatu itada umaima ne kawai zasu gane me take nufi,saiko hauwa ba'a batun su amina dama da basu ma gama sanin kansu ba bare su fahimci maganganu irin wannan.



      Sun jima sosai a hakan,wanda daga bisani har bacci yadaukesu itan tana zaune tana tufka da warwara.



*****    *****    *****  ******




      Cikin qasar da take mallakin mahaifi ga fulani aisha aka daura wannan sirritaccen aure,tayi matuqar mamakin ganin yayunta maza har qasar ta mali bayan mahaifinta.



       Duk da cewa yarima azeez din yana qasar a sanda aka daura auren amma koda gilmawarsa bata gani ba da sunan mijin da zata aura ba,hasalima da zaka ritsata kan waye mijin nata?,koda za'a jera mata maza cikinsu hardashi bazata iya tantanceshi ba,hatta da fulani aishan bata samu ganinta ba bare mai gaba dayan,wanda hakan yasake tabbatar mata lallai ta durfafi wani bigire na rayuwa na daban,saidai batasan ya tafiyar zata kaya mata ba....

7/11/21, 4:31 PM - My Mtn Number: 22


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





      A hankali ta daga rinannun idanuwanta da suka jima da sauya kala tun daren jiya har zuwa wannan lokaci da awanni kadanne suka wuce da daura aurenta tana duban wanda ke shigowa katafaren dakin da aka ajeta,aka kuma wadata da dukkan wani nau'in abubuwa na more rayuwa.



       Macace mai cikar haiba gamida kamala,a shekaru ba zata haura shekara arba'in da takwas ba,tana da dan jiki kadan,ba zaka kirata da mai qiba ba,tana da tsaho saidai ba wani can ba,wanda bisa dukkan alamu ma qibar murjewar jikinta ne ya sake boye tsahonta,kallo daya ta fahimci itama tana daha cikin hadiman gidan sarautar kaisa,duk da cewa bata taba ganinta ba sai yau.



     Karon farko kuma a ganin farko data yi mata,taji tadanyi mata kwarjini,hakanan bataji irin abinda ta saba ji dangane da sauran matan da suke hidima da ita ba wadanda suka fito daga gidan

"Assalamu alaikum" tayi sallama matar hannunta riqe da kaya,wanda hakan yasaukar wa da bilkisu wata iriyar nutsuwa data jima rabon data ji irinta,ta motsa labbanta,karon farko tunda tazo qasar mali ta amsa mata itama cikin nutsuwa

"Wa'alaikumussalam warahmatullah" yadda yanayinta yake nuna nutsatstsiyar macace ita haka ya qaraso wajenta a nutse,ta ajjiye kayan kusa da bilkisu,sannan tazauna daga wata kujera da take fuskantarta

"Bilkisu ko?" Ta tambayi bilkisu tana dubanta,sai data daga kai ta kalleta,ason ranta ba zata amsa mata ba,don bata tsammanin akwai wanda baisan sunanta ba cikin gurguxunsu,amma sai taji tayi qimar da ba zata iya shareta ba,don a qalla ta haifeta,don haka ta gyada mata kai,itama kai ta girgiza

"Ma sha Allah,bilkisu...kowanne bawa tun yana cikin mahaifiyarsa da watanni hudu ake rubuta masa dukkanin qaddararsa,Allah S W T yakan umarci mala'ika yaje ya busa masa rai,kana ya rubuta masa dukkan qaddararsa har makomarsa bayan ya mutu,ita rayuwarmu mallakin mahaliccinmu ne,kowanne bawa da kika gani bakya rasa wani abu daya zuwa biyu cikin rayuwarsa da bayasonshi,amma kasancewarsa cikin littafin qaddararsa hakanan yake karbansa hannu bibbiyu yakuma godewa mahaliccinsa kan hakan,harma wataran kiga yana rayuwa kamar babu wannan damuwar a tattare dashi,kamar mu dai....." Ta furta tana nuna kanta

"Allah daya haliccemu a matsayin bayinsa dukka daya muke a wajensa,amma daya tashi.....ya qaddara cikin bayinsa akwai bayin bayinsa,mu saiya sanya salsala da zuri'armu cikin tsatson bauta iyaye da kakanni,bakuma wai don baya sonmu ba,aah yana qaunarmu kamar kowanne mutum,don ya hanemu sabawa ko guduwa daga wajen iyayen gidajenmu,aikata hakan haramunne akan dukkan wani bawa abun mallaka wa uban gidansa"

"Subhanallah" bilkisu ta fada cikin ranta,kana ta daga kai tana kallon matat,macace cikakkiya kamar kallon data mata dazu,mai cikar haiba da kamala,amma tatashi a sahun bayi?,bayi da takanji ana maganarsu cikin littafin hadisi kona fiqhu,yau ga burbushinsu a wannan zamanin?.



     Kamar tasan me bilkisun ke kitsawa saitayi murmushi

"Baki godewa Allah dabai  sanyaki a sahun bayi kamarmu ba?,duk da muma babu abinda aka tauyemu dashi,saidai har abada bawa bawa ne,harsai sanda yasami 'yanci,koda yasamu 'yanci ma cikin tarihin rayuwarsa sunan ya taba BAUTAR abun halitta bazai taba gogewa ba" saita sake matsowa kusa da bilkisu sannan tace

"Sunana hafsa,amma kusan dukkan masarautar kaisa suna kirana da sodangi,nidin jakadiya ce ta yarima azeez,saidai 'yantacciya ce kamar yadda aka 'yanta iyaye da kakanni na,kamar yadda kowanne yarima da ake saka ran zamantowarshi sarki yake da jakadiya wadda kusan ita zatayi rainonsa har yagirma,bayan yazama sarki kuma zai riqeta ne a makwafin uwa,na gaji jakadanci daga wajen kakata,ita tayiwa sarki mu'az jakadanci,mahaifiyata kuma Allah ya jiqanta ita tayiwa sarki abdallah mahaifin azeez,ni kuma a yanzu ni nake masa.....an umarceni dana tafi tare daku zuwa mexico,nazauna daku har zuwa lokacin da aka dibawa zamanku ya qare,bilkisu.....nasan an shiga haqqinki an kuma shiga hurumin rayuwarki,hukuncine da fulani aysha ta yanke a lokacin da bana kusa da ita,duk da cewa ta quduri niyyar yin hakan ban isa na hanata ba,amma a qalla inada yaqinin bisa shawarata wasu abubuwan za'a samu sauyi da sauqi,duk da cewa ba hurumina bane,ina mata tsoron ranar da komai zai bayyana a fili....." Ta fada tana kada kai sannan tadora

"kiyi haquri ki amshi jarrabawarki,ki kusanta kanki da ubangiji,komai zaizo miki da sauqi....sai kuma alfarma daya da nake nema ki taimakeni kiyimin" hakanan taji maganganun jakadiya sodangi yana shigarta,ta iya kalamai masu cike da hikima taushi da kwantar da zuciya,hakanan sai ta dinga ganin girma martabarta cikin idonta sosai

"An doramin dukkanin nauyi da alhakin kula daku,an jaddadamin ns tabbata komai yana tafiya yadda ya kamata har zuwa qarshen lamarin,ki taimakeni kibi duk umarnin da aka bani nabaki don girman Allah na roqeki" ta fada tana hade hannayenta waje daya,nauyin roqon datake mata takeyi,don haka da sauri ba tare data shirya ba tace

"In sha Allahu mama"

"A'ah,taimakeni ki kirani da sunan da kowa yake kirana,saboda ke a yanzu matsayinki sama yake da nawa,kusan dai dai yake da akiraki matar magajin sarki koda ta wucin gadice kuwa" kai ta kada

"Bazan iya ba,zanyita kiranki da maman indai ba zunubi na aikata ba" murmushi kawai tayi tajawo kayan data shigo dasu ta miqa mata tana cewa

"Ina fatan zaki saki jiki dani,ki daukeni kamar wata taki" karon farko murmushin da batasan ya akayi yazo ba ya subuce mata,duk da cewa iyakacinsa saman labbanta

"Ki sanya wadan nan kayan zamu wuce mexico yanzun nan,kafin nan mahaifinki zai soma magana dake,idan kin gama ina falo saiki sameni in miki jagora,idan kuma kina da buqatar wani taimakon yayin shiryawar taki ki shaidamin nashigo na taimaka" daga haka tamiqe tafice,bilkisu tabita da kallo kafin tadawo da kallonta kan kayan,haka kawai taji cikin kaso dari tasake da matar kaso goma,wanda ita kanta batasan dalili ba.



      Durqushe take gaban mahaifin nata kamar yadda kowacce amarya kan tsaya gaban mahaifinta don amsar nasihar ban kwana,cikin wata iriyar shadda da aka yiwa dinkin babbar riga ta alfarma yake,yacika kujerar yanata baza rigarsa,jinsa yake kansa daya da shugaban qasa,gyaran murya yayi sa'an nan yasoma magana 

"Amm....dafarko maigado babu abinda zance dake saidai nace Allah ubangiji yayi miki albarka,yadda kika min biyayya kema Allah yasa ki dace haka,Allah yajiqan maimunatu,yasa ta huta,wanda ba shakka naso ace tana raye taga wannan lokaci" ya fada yana share qwalla wadda ko digon danshi babu a idanun nashi bare kuka

"Abinda nakeso dake bilkisu kiyi biyayya,ban yafe miki ba idan kika saba kan dukkan abinda aka umarceki dashi,kibi duk umarnin da kowaye cikinsu zai baki,Allah yayi miki albarka,ya qaddaea saduwarmu". Wannan kusan itace sallama ta qarshe data dimga tunawa tsakaninta da mahaifinta sanda take zaune cikin jirgi tana qoqarin maida qwallarta,a maimakon tsoro da zullumi dakan cika dukkan wanda yasoma shiga jirgi karon farko yake tsintar kansa a ciki a'ah,maganganun mahaifinta ne kadai ke bitar kansu cikin kwanyarta.



      Su uku rak ne taga sun shiga cikin jirgin wanda suke tafiyarsu daya,daga ita sai mama sodangi,sai wata matashiya wadda a qalla zasuyi sa'annin juna da ita wanda taji mama sodangi tana kira da rakiya.



      Tafiyar awanni suka sauka a qasar mexico,mexico city,tuni motar da zata daukesu ta iso,da alama ma tun kafin isowar jirgin nasu take dakonsu.



     Motace maikyau ta alfarma,aka zuba kayansu sa'annan suka fice daga babban filin sauka da tashin jiragen sama na garin.



     Duk da yadda zuciyarta take a cunkushe amma hakan bai hana idanunta wulqawa bisa titina da kyawawan gine ginen da suka qawata garin ba,shuru ne ya biyo baya cikin motar,sai mama sodangi da drivern da yake baqar fata wanda da alamu ma dan qasa nijeria ne suke taba hira jifa jifa,da alamu ba yaune karon farko da suka san juna ba.



       Shudewar wasu mintunan na daban suka isa unguwar,wadda tsarinta dakyanta ya fita daban,bata sake gasgata hakan ba saida suka sanya kai cikin gidan,tana biye da mama sodangi wadda take kamar 'yar jagora a wajensu,yadda take saka kai cikin gidan ya isa ya shaida maka ba baquwa bace cikin gidan,ta sanshi sosai.



      Sai data soma sada bilkisu da wani daki daya sanya bilkisun tsaiwa cak cikin 'yar fargaba tana dubanshi,komai na dakin fari ne da gold,an tsara dakin ne dai dai da ra'ayin tsari da colours din da azeez yakeso,kusan wannan shine favourite colour na bilkisun,ba wani tarkace bane a dakin amma komai na cikinsa mai aji da kyau ne,yana da fadi sosai,akwai cupboard dressing mirrow sai wani lafiyayyen dunqulallen gado da aka lullubeshi da wani ni'imtaccen farin net,akwai bedside lockers hagu da dama na gadon,wanda akan kowacce akwai fitila akai,sai wata corner daga can hannun hagu na dakin da aka dan mata ado aka aje litattafai na karatu na turanci,da fitila wadda take shige data gefan gadon,saidai tafi ta gefan gadon girma da dan haske,gaba kadan da wajen sofa ce qwaya daya iyama fara qal da ratsin gold,daga gaban gadon lallausan carfet ne madaidaici da wani dan qaramin table mahadin gadon,qasan dakin ba tiles bane hakanan ba carfet bane,wani shimfidadden abune mai kyau da ita kanta batasan sunanshi ba,labulaye ne masu kyau tsari dakuma kauri zagaye da dakin,farare ne da akayi musu adon wata rumfa daga saman kowanne golding colour haka madauran labulen suma duka kalarsu kenan,dakin bai cika haske sosai ba,saidai bashi da duhu kuma,amma luf luf yake,wanda akwai yiwuwar idan yamma tayi lis babu hasken qwan lantarki to babu shakka zai iya yin duhun.



      Qaqqarfar ajiyar zuciya tasauke tana ambaton sunan Allah,kana ya dosana mazaunanta a gefan gadon,tunanin gida yana bijiro mata,tana shanshano irin nisan tazara data yiwa gida,bama gida kawai ba qasarta ta haihuwa gaba daya,wanda tunda take wannan shine karo na farko data taba barin qasarta zuwa wata qasar.



       Tana nan zaune bayan awa guda aka mata knocking,rakiya ce,ta nemi izinin shigowa ta bata,cikin girmamawa ta neme izinin gyara mata kayan sawarta da sake karkade mata dakin,duk da bawani qura yayi ba bare datti,bata hanata ba ta bata dama,tana nan zaune a inda take tana kallonta lokaci lokaci,harta gama kana tashiha bandakin na wasu mintuna tafito,da alama sake wankeshi tayi.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 23

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070___________________________

*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*



*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸™Å½Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯ðŸ½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸‘¯Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*



*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ðŸ¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾






      Mintina ashirin tsakani mama uwani tashigo dakin,fuskarta dauke da murmushi tadubi bilkisu

"Lokacin wanka yayi,sai kuma abinci idan kina da sha'awar ci" kai ta girgiza don ita babu wata yunwa da takeji,wanka kuwa harya soma zame mata jiki,wasu irin mayun sabulai man shafawa da turarukan wanka suke bata take amfani dasu,bata taba ganin set irimsu ba tunda take,sun sake fidda ainihin kalarta,sun kuma qarawa fatarta kyau sheqi dakuma santsi,kamar wadda akewa wankan inji,saita miqe ta durfafi bandakin.



*******    ******    ********


      Satinta guda cas a gidan ba tare da taga wani da za'a iya kira da sunan mai gidan ba,hakanan ita kanta mama sodangi bata taba yi mata wata magana data danganci aurenta ba,a satin gaba daya zaman daki tadinga yi safe da yamma har zuwa dare kwanciyar bacci,bata aikin komai a gidan,daga wanka sai bacci sai cin abinci,sai kuma idan ta gaji ta kwanta,don ko kallo batayi,daga bisani data gaji ne takan zauna tayi tilawar izifi hamsin data samu haddacewa,sannan tayi na sauran litattafan data haddace wanda suke kanta,idan tagaji tasake komawa ta kwanta,takuma fadawa tunanin duniya.



     Tunda mama sodangi ta mata tayin ko falo tasamu tadinga fitowa tana kallo ko hira dasu,ta nuna bata sha'awa bata sake takurata ba koyi mata maganar ba,sau tari takan jiyo hirarrakinsu ita da rakiya,kodai na cikin gidan sarautar kona duniya,wani lokaci kuma taji kwarafniyarsu a kitchen idan suna hada abinci.



      Dukkan wani abu na buqata a gidan babu abinda babu,hatta da tsinken sakace a ajjiye yake yana jiran ayi amfani dashi,hakanan duk abinda ta nuna tana da sha'awa ko tanaso saita sameshi,saidai ita sam bataga manufa ko amfanin zamanta cikin gidan ba,tasha yiwa kanta tambaya,waishin an daukota ke don a hanata yawo ko a hanata ganin jama'a?,an daukota ne don a killaceta ta rayu ita kadai?.



        Yanayin rayuwar data taso ya sanya cikin kwanaki takwas kacal kwanciyar taso sanya mata zazzabi da ciwon jiki,saboda ta riga data saba kullum cikin struggling take,tattakin zuwa makaranta da dawowa da qafafunta,aikin gidan umma luba har zuwa dare,wankin qannenta da nata wani lokaci harda na mahaifinta da hidimar kula da qannen nata,sai gashi yanzu shuru bata aikin komai,hakanan babu kowa kusa da ita.



       A kwana na goma ne takai maqurar takura,don haka bayan ta idar da sallar la'asar saita nemi medium mayafi tayi rolling dashi,ta zura slippers dinta tana niyyar fita,sai kuma taji ta kasa fitar,don haka takoma gefan sofa tazauna hannayenta dafe da saman sofa din tana dan tura qafarta gaba da baya tana tunanin yadda zata fita din.



       'Yan maganganu taji daga falon,muryar mama sodangi ce,sai daga baya kuma tadaina jin motsinta,bayan kamar minti goma sai gata ta turo qofar dakin tashigo.



     Kamar koyaushe da murmushi saman fuskarta,wanda shike sanya bilkisu jin nauyinta,bai kamata koda yaushe tana kallonta da fuskar murmushi ba,ita kuma ta dinga maida mata da daurarriyar fuska,dole takan sanya itama tasake mata murmushin a yawancin lokutta.



      "Ranki ya dade yau za'a leqamu kenan?,aiya kamata,kinma yi qoqarin zaman,gwara ki fita kiga gidan,bakiga ma gidan ba bare akai ga fita kiga gari" murmushi tasake yi mata,yadda take maganar kamar tanayi da sa'arta ne,sam babu ruwan sodangi,tana da sakin jiki da haba haba da jama'a,yadda takejin hirarrkinsu da rakiya kawai ya isa ya gaya maka haka.



      Juyawa tayi zata fita don haka tamiqe tabita a baya har suka iso falon,babu kowa sai rakiya dake xaune qasar carfet ta zubawa tv idanu,da alama tana dason kallo,ganin fitowar bilkisun ya sanyata miqewa zumbur tana cewa

"Barka da fitowa ranki ya dade" cikin girmamawa,abun saiya mata banbarakwai

"Yauwa rakiya" ta amsa mata fuska a sake duk don tasaki jikinta,don ita bata ga wani bambanci ba tsakaninta da rakiyan,zata iya cewa tama fita ita a wajenta.



     Saman carfet din itama tazauna yadda tagansu zaune maimakon kan kujera

"Subhanallah,ya zaki zauna a qasa Allah ya taimakeki?" Kai ta gyada

"Nafison nan din" jin ta fadi hakan yasa ta qyaleta.



       Kamar falon zai dauki shuru sai kuma mama sodangi ta soma sako hira,ba dadewa rakiya ta biye mata sukaci gaba da hirarsu yadda suka saba,basu saka bilkisun ba,hakanan itama bata sanya musu baki ba don bata da abun cewa,bata da ilimi kan hirar tasu,saidai tana saurarensu,rabi kuma idanunta nakan tv tana kallon wani film da ake haskawa a daya daga cikin tashoshin talabijin na qasar mexico.



      Kusan awa daya da rabi wayar mama sodangi tadauki kida,da hanzari ta daga kana cikin girmamawa tasoma gaida me kiran

"Allah ya taimakeki kowa da komai lafiya qalau.....gata yauta fito muna tare da ita" shiru tayi nadan lokaci sannan tace

"Yau muna tare da yarima,yashigo gidan dazu awa daya data shude,ya bada uzurinsa Allah ya taimakeki ayi masa afuwa,yanzu haka yana dakinsa a sama yana hutawa".



       Sai a sannan bilkisu ta fahimci dawa ake magana,takuma fahimci dalilin da yasa tun sanda tashigo falon tadinga jin wani baqon lallausan qamshin turare,ashe shine yashigo gidan?,tayiwa kanta tambayar,sai taji wata matsananciyar faduwar gaba,tamkar wadda aka tsikara tamiqe zumbur ta nufi hanyar dakinta don komawa,mama sodangi dake amsa waya tabita da kallo tana mamakin abinda ya tasheta.



       Har zuwa dare bata sake ba bata kuma saki jikinta ba,gani take kamar zuwa kowanne lokaci zai iya neman yin magana da ita koya nemi ganinta,gefe guda kuma tana taraddin wayeshi?,mutumin qwarai ne ko na banza?,yarone ko tsoho?,managarcin mutum ne ko akasin haka?,kai tana tsammanin ma mawuyacine ya zama nagartaccen,saboda tana hasashen babu ta yadda za'ayi nagartaccen mutum ya yarda yayi irin wannan auren,daga qarshe ma taga baiken kanta na takurawa kanta da tayi da ire iren wadan nan tunanukan,tunda koma meye halinsa koma yaya yake bazata iya canza qaddararta ba,hakanan ba zata sauya abinda yariga daya faru ba.



       Qarfe bakwai na dare yasauko daga saman nashi,ya tsuke cikin qananun kaya da suke sake fidda zallar quruciyarsa muraran,hakanan shigar tasake yi masa kyau ainun,ba abinda jikinsa yake sai fidda sassanyan qamshin turarensa wanda yake iske mutum tun kafin shi din ya qaraso wajen.



      Da dan sassarfa yake saukowa yana duba agogon dake daure a hannunsa,da alama sauri yake zai fita,mama sodangi dake zaune bayan ta idar da sallar isha'i ta waiwaya jin takun saukowarsa

"Ranka ya dade kafito kenan?" Ayagance cikin nuna aji na masu ajin yace

"Eh....zan danje wani guri,zan dan jima amma acan,so koda ban shigo da wuri ba babu wani damuwa"

"Amma baka tsaya kaci abincinka ba,sannan....." Saikuma tadan sadda kai alamun girmamawa

"Baka nemi ganinta ba ita kanta,fulani takirani daxun,na baka dukkan kariyar data dace...." Labbansa ne suka dan motsa da alamu murmushi yake sonyi,mama sodangin kamar uwa ce a gareshi,banda haka babu mahalukin da zai tsaya yayi masa wannan maganar ko suyita dashi

"Karki damu da dukka wannan....tace na karba plan dinta na karba,nayi mai wuyar aiko?" Shuru mama sodangin tayi bata sake cewa komai ba,don bayaga mahaifiyarsa itace mutum ta biyu data san halinsa fiye da kowa,sai yayi gaba kawai,harya kusa kuma sai yace

"A hadamin salad kafin ku kwanta,idan nadawo zanci" ya qarashe maganar yana ficewa daga gidan.



     Ajiyar zuciya mama sodangi tasaki,itadai taga yadda za'ayi wannan auren,amma ta wani fannin tana ganin qoqarin azeez da tsananin biyayyarsa ga mahaifiyarsa,tunda bai nuna rashin amincewarsa ba ko kadan,ya amshi dukkan wani tsari na fulanin yadda takeso.



      Kusan raba dare tayi zaune tsuru cikin duhun dakin,ta kasa samun nutsuwar da zatayi bacci,duk wani motsi da ake cikin gidan kan kunennta,mama sodangi itace mutum ta qarshe data kwanta bayan tagama hada mishi salad din ta aje masa tare da sauran dukkan abinda zaya buqata,don tasan bazai tana yarda yaci girkin rakiya ba,hasalima bataga wannan fuskar da zata dafa mishi wani abu ba,zata iya cewa batama taba ganin yana magana da ita ba,duk da tana hidima ne a qarqashin sassan mahaifiyarsa.




      Sai data daina jin motsin kowa da komai kafin daga bisani bacci yayi awon gaba da ita.



*******   *****    ********



      Duk da yadda ta matsu takuma gaji da zaman dakin amma hakanan a kwankin taci gaba da zaman,tun randa tafito falon bata sake fitowa ba,tunda taji yashigo gidan zuciyarta ta bata tabbacin yadawo kenan,kuma koda yaushe za'a iya samunshi cikin gidan,ba tare da tasan bai fiya zama a gidan ba,yawanci idan yafice tun safe sai dare,da darenma idan yadawo yagama abinda yake sake fita yake,bacci ne kawai ke dawo dashi gidan.



       Wata guda ta kwashe a haka,saboda tsabar zaman waje daya fatarta tayi wani mugun murjewa ta qara haske kamar wadda ke shafa wani mai,saidai takura dakuma yawan tunanin gida data sanya a ranta ya sanya ko qanqani batayi wata qiba ba.



       Wata guda da kwanaki uku a wani dare tana tsaye bakin window tajiyo satar amsar lokuttan da yake dawowa gidan cikin hirar mama sodangi da rakiya,saita saki ajiyar zuciya,takoma tazauna tana qiyasta da lissafa yadda zata dinga tsara fitarta falo da dawowarta dakinta,qaramin murmushi ya kubce mata,sai takejin kamar tasamu wani qaramin 'yanci,kamar fursunar da aka kwance daga kurkuku.



      ******    *****    *******


       Washegari tsaf ta shirya abunta da wuri,sai daukin lokacin dataji yana fita takeyi yayi tafito daga dakin,kamar wadda zata wata qasa zuwa wata,tana zaune gefan gado,lokaci lokaci tana duba agogo har lokacin yacika,saita sake gyara zamanta ta qara mintina ashirin qwarara akai sannan tamiqe tana gyara rufin kanta,ta murda qofar dakin a hankali ta fito.



      Babu kowa a falon,amma tana iya jiyo motsinsu da 'yar hirarsu sama sama cikin kitchen,batayi qasa a gwiwa ba tasauya akalar tafiyar tata zuwa kitchen din,lokaci lokaci tana bin duk inda tawuce da kallo,ko ba'a gaya maka ba kasan gini da tsarin gidan dukka turawane suka yishi.



      Sallamarta tasa suka waiwayo da hanzari,nan suka marabceta dakyau,dukkansu suna mamakin ganinta yau har cikin kitchen din. Mama sodangi ce ta miqa mata kujera cikin nuna farinciki tace

"Zauna mana,ai bakya tsaya ba ranki ya dade" murmushi kawai bilkisun tayi,taja kujerar tana zama a lokaci guda kuma tana gaida mama sodangin,ta amsa cikin kulawa da jin dadi,hakanan Allah ya daura mata qaunar bilkisu da damuwa da halin da take ciki,sam batajin dadin yadda ta matsawa kanta ta tattare kanta a waje daya,don dai bata da yadda zatayi ne,hakanan batason wuce gona da iri da kuma shige hurumin aikinta,shi yasa kawai tayi shuru,tana addu'ar Allah ya daidaita lamarin,wanda ta lurama tanayi ne dominsa sam kamar bata gabanshi,hasalima naya wunin gidan ballantana tace.



       "Kiyi haquri,kinji abun breakfast shuru ko?,na tsaya na soma hadawa yarima ne kafin namu,saboda zai fita,yau naji dadi sosai daya nemi abinci,don ba kasafai yafiya neman abinci ba cikin gida" ta tafas batace ba,don sai take ga kamar bada ita ya dace mama sodangi tayi wannan maganar ba,domin itan kamar baquwa ce.



       Taji dadin xaman kitchen din sosai,bata dai cewa komai a maganarsu amma tana sauraren hirarrakinsu da kuma motsinsu sanda suke hada hadar hada abun karin safe,sanda aka gama mama sodangin ta ware mata nata,sai taji sha'awar tazauna taci a cikinsu,don ta manta rabon data ci abinci da wani,tun sanda tabaro gida cikin qannenta.



       Da farko sunqi sun soma dari dari,daga baya da sukaga ta saki sai suma suka sake,sosai taci abincin har tayi mamakin kanta,don rabonta dacin abinci mai yawa kamar wannan harta manta,lallai ba shakka mutum rahama ne,yayin dasu mama sodangi ke mamakin yadda ta tsame hannunta haka da wuri,don su a ganinsu abincin da taci bai wani kai yakawo ba,murmushi kawai tayi,su a wajensu ne haka,amma ita a wajenta abinci taci mai yawa,ta riga data saba kusan dukkansu har qannenta cikinsu ya riga ya kanannade da yunwa,shi yasa komai yunwar da sukeji kuma komai yawan abinci basa masa ci mai yawa.



      Dadin da xaman yayi mata yasa bata koma daki ba,kusan tare suka yini anan falo,tun bata biyewa hirarsu har tasoma murmushi kawai,ta lura ko tsakanin rakiya da mama sodangin akwai shaquwa sosai da sabo,wala'alla shi yasa aka hada tafiyar tasu tare.



     Bata koma daki ba sai data kintaci cewa kowanne lokaci daga yanzu zai iya dawowa,saita musu sallama tawuce ciki.



         Tun daga lokacin saiya zame mata jiki,daga zarar ta fuskanci yafita saita fito su wuni tare da mama sodangi da rakiya,tsahon zamanta bata taba jin muryarsa ko ganin gilmawarsa ba,hakan kuma baya rasa nasaba da yadda take takatsantsan da komai nata.



       Lokaci yaci gaba da garawa a haka,sannu sannu tasoma sakin jiki dasu mama sodangi,sai gashi takan dan buda baki ta amsa hirarsu daya biyu,daga baya sai ya zamto dukkan abinda za'a girka tana sanya hannu ta tayasu da wasu abubuwan,kamar blending kayan miya,yankan salad,gyara kifi ko nama da sauransu,tunda dama mama sodangi itake girkin gidan.



        Tafi tafi sai sabo yasoma shiga tsakaninsu,ta fara fahimtar halayyarsu kamar yadda suma suka soma fahimtar nata halin,tasoma jin mama sodangi kamar mahaifiya a gareta,saboda yadda kalaman bakinta ke fita kullum irin na uwa ne,hakanan kulawar da take bata itama irin ta uwa ce,tasoma jin rakiya kuma kamar ta samu sabuwar 'yar uwa,wadda zata rage mata kewa da radadin 'yan uwanta data baro,abinda bata taba sanin tana dasu ba a halayenta sai suka soma raguwa,kamar miskilanci,zaman shuru da sauransu,a gidansu da makaranta idan bada qannenta ba bata sakewa tayi hira da kowa,sai gashi a yanzun tana iya hira da mama sodangi da kuma rakiya kanta,don sun san yadda zasu ja hankalinta suyi hira da ita,duk da cewa ko sau daya bata taba gaya musu ko basu labarin abinda ya shafi kanta ko ahalinta ba,saidai tana yawan ambatar qannenta da basu labarinsu,da kuma fadin yadda tayi kewarsu,hakan da mama sodangi ta fahimta yasa taga bari tayi wani abu,me zai hana ba zata qara fadin sakewar datayi ba ta amintar da ita?,saita shaidawa fulani cewa ya kamata a siyawa bilkisun waya,saboda bata da ita,kuma tana da buqatar jin mahaifinta.



        Ita ta sanya azeez ya siya wayar ya kaiwa mama sodangi,ita kuma ta kaiwa bilkisu da kanta,saidai tace mata jiya data fita yi musu cefane ne tabiya tasiya mata saboda qannenta,bata shaida mata daga hannun data fito ba,don yadda ta karanci bilkisun idan taji wala'alla ba zata taba yarda ta amsa ba.



        Farinciki tare da qaunar mama sodangi ya cikata,sanda ta riqe wayar a hannunta anty zuhriyya ce kawai tasoma fado mata,sai taji idanunta sun tara qwalla,ta tuna sanda tayi mata alqawarin waya a randa ta kammala secondry school,tace itace gift dinta,ashe qaddara zata zo ta ra ganawarsu,ashe qaddara batayi mata tanadin gama makaranta ba,babban burin rayuwarta,ashe dukka ba zata gani ba.



      Data kalli wayar dakyau sai taga ta mata girma,kamar ta girmi girma da matsayinta,kamar tayi zari idan ta riqe waya kamar wannan,saita maidawa mama sodangi ta mata bayani a sama mata wadda bata kai wannan ba,murmushi kawai mama sodangi tayi,can qasan ranta tana fadin da tasan su waye ahalin sarautar gidan kaisa da batace wannan wayar tamata girma ba,amma saita lallabata cikin dabara harta amintar da ita riqe wayar.



        Kusan wayar saita tashi bata da amfani a wajenta,tunda bata da lambar kowa da zata kira ya sadata da mahaifinta shi kuma ya bata qannenta,taji muryarsu,hakan yasa ranta yadan sosu,saita aje wayar gefanta,taja filo ta dora kanta kana tayi rub da ciki.



       A irin haka mama sodangi ta shigo ta sameta,tazo dubata ne ganin shuru bata fito ba

"Na tsammaci kina nan kina waya da gida?" Saita miqe ta zauna sosai tana dubanta,don ta sosa mata inda yake mata qaiqayi

"Mama ban riqe lambar kowa ba cikin gidan" Dan shuru tayi maman tana nazari,sai kuma tace cikin hanzari

"Lubabatu fa?" Maimaita sunan bilkisu tayi a ranta,ko itadinma bata da lambarta,koda tana da lambarta ma bata jin xata iya kiranta,maganar mama sodangi ta katse mata tunaninta

"Inada lambarta,bari na kira ta idan tana da lambar ta bayar,idan kuma babu taje ta amso miki ko?" Kai ta gyada tana jin sanyi cikin ranta,qaunar mama sodangi na sake yawa cikin ranta

"Na gode" ta furta sanda take shirin fita a dakin,da murmushi ta juyo

"Babu godiya a tsakaninmu,don kedin uwar dakina ce,dole nayi duk mai yiwuwa don in faranta miki" daga haka tafice.



      Ba'a rufa awa guda ba mama sodangi tadawo da lambar mahaifin bilkisu,kasa zama tayi sanda taji tashiga tana ringing,sai tayi tsaye gaban mudubi tana kallon kanta da kanta,wayar kange akunnenta cikin zumudin son jin an daga.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 24

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_________________________

*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*



*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸™Å½Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯ðŸ½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸‘¯Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*



*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ðŸ¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾




     Daf da zata tsinke kamar ba za'a daga ba taji sallamar mahaifinta na ratsa dodon kunnuwanta

"Wake magana?" Ya tambaya

"Baba....bilkisu ce" ta fada bakinta yana dan rawa

"Bilkisu?!....wace bilkisun?"

"Mai gado baba"

"Ke!....mai gado?,ince dai lafiya ko?" Ya tambayeta,saita sauke ajiyar zuciya

"Lafiya qalau baba". Daga haka tasoma gaidashi ya amsa mata sannan tace

"Baba...su hannatu nakeso ka bani zamuyi magana dasu"

"Kina tantama ne kan lafiyarsu ko.maigado?" Ya jefa mata tambayar,da sauri tasoma girgiza kai kamar yana kallonta

"Ba haka bane baba,kawai najima bangansu ba banji muryarsu ba,shine kawai dalili" ta qarashe fada tana fatar kada ya hutsance mata ya hanata magana dasu

"Keda ganinsu kam ai sai bayan shekara daya....yanzu dai ina kasuwa,amma idan nakoma zan hadaki dasu,shikenan dai ko?" Kai ta gyada a sanyaye,badon taso ba,don tasone a yanxu yanzu suyi magana,amma babu yadda ta iya.



       Haka tazauna zaman jira,duk bayan minti daya saita irga mintunan da suka rage yakoma yakirata yabasu,rakiya tadinga mata dariyar ta qosa da yawa,yayin da mama sodangi take kallon ta cike da tausayi,don tasan ita kadai tasan ciwon da taji na rabuwa da qannenta da tayi.



        Murmushi tayi sanda rakiya ke ci gaba da yi mata dariya

"Rakiya kowa fa yabar gida gida ya barshi,dan uwa dadine dashi" sai taga ta kauda kai tana murmushi

"Mu duk bamusan wannan ba ko mama sodangi?" Da yake ta koyi cewa mama a wajen bilkisu,murmushin maman tayi kawai ba tare da tace komai ba.



       Sai bayan wajen awanni takwas sannan baban nata yakira,a sannan har tayi laushi,ta sanya wayar a gaba kawai da tugumi,ta yanke tsammanin zaya kira,tana dagawa muryar hannatu tasoma ji,wayyo Allah,farinciki kamar su faso wayoyin suga junansu,tana iya jiyo muryoyinsu dukkanin yaran a rude,kowa so yake ya ganta kuma yayi.magana da ita,da qyar tayi controlling kukanta don kada ta karya musu gwiwa,tasa hannatu ta sanya wayar a handsfree,sannan tace da daya da daya kowa yayi.magana da ita.



        Haka aka dinga bin layi,kowa tana biye masa tare da bashi lokacinta sosai,sam.ta manta a agaban mama sodangi take,saita dinga jinta kamar gata a gida a gaban qannan nata,duka saida suka gama gaisawa da kowa sannan tasoma tambayarsu kan abinda ya dameta

"Kuna cin abinci?,kuna zuwa makaranta?" Hannatu ta amsa mata

"Kullum yaaya sai munci har sai munce mun qoshi,dakinmu mu kadai babu mai takura mana,an kawo.mana kaya masu yawa dakyau,duka mun bada wadan can,kuma baba ya sanyamu a makaranta islamiyya harda ta bokon da kikace zaki sakamu,kinga ya hutashsheko" wata nannauyar ajiyar zuciya tasaki tana godewa Allah,wannan labarin data ji shi ya rage mata damuwarta kaso hamsin cikin dari,yakuma haifar mata da wata 'yar qaramar nutsuwa da a baya bata sameta ba,lallai addu'a bata faduwa qasa banza.



        Tun daga ranar tasamu abunyi,kullum ta Allah saita kirasu da daddare taji ya suka wuni?,me sukeyi yanzu?,tun tana dari dari da tunanin baban zaiyi fada,koya hanasu wayar harta saki jiki,ganin bai sake cewa komai ba,ga mamakinta harda mama ladi wataran saita amshi wayar sun gaisa,wannan yasake haifar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali.



       Uwa uba kuma ganin babu wani abu daya biyo bayan auren nata,rayuwarta take cikin gidan daga mama sodangi sai rakiya kadai take gani,wanda take zaman dominsa bata taba ganin gilmawar koda mai kama dashi ba bare shi,koda sautin muryarsa bata taba ji ba,saidai taji mama sodangi lokaci bayan lokaci takan jefa zancansa tsakaninta da rakiya,yarima yace in masa kaza,ko dauke abu kaza saboda yarima yakusa shigowa,hakan yasa wasu lokuttan da yawa take manta meya kawota qasar?,take manta cewa ma tana da wani abu waishi aure,saita sake sakewa,batasan cewa BABBAN QALUBALE NA BIYE DA RAYUWARTA A GABA BA.



      Zamansu da rakiya yasa ta fuskanci tana da rauni wajen karatun addini dana boko ma,hakan yasanya ta dorawa kanta nauyin karantar da ita daga ilimin da Allah ya bata bayan kowacce sallar la'asar,tashiga internet tayi browsing duka litattafan da zata fara koya matan,suka baiwa mama sodangi ta nemi inda ake printing akayi musu,saboda ita din kamar 'yar garice a qasar,tasan kan qasar sosai,kuma hakan baya rasa nasaba da yawan zuwa da fulani aisha keyi tare da abdul'azeez tun bai fara ma karatu anan ba.



        Yanayin qwarewar bilkisu yasa mama sodangi itama taji sha'awar zama ayi karatun harda ita,sai daliban nata suka zama biyu,anan falo suke zama ta karantar dasu,a sake suke tambayar dukkan abinda basu sani ba,ita kuma ta basu amsa daidai gwargwadon saninta dakuma yadda hukuncin yake a alqur'ani ko hadisi,sosai karatun yake musu dadi har ita bilkisun,don ya sake taimaka mata wajen debe mata kewa,tare da tuno mata wasu karatuttukan data manta.



       Wannan zaman yasake haifar da sabo sosai a tsakaninsu gamida fahimtar juna da qauna.



      ****    *****    ****    *****



      Ƙarfe hudu harda wani abune na yammaci,dai dai lokacin bilkisu na zaune a falon gidan,cikin doguwar riga data nada mayafinta a kanta,duk da cewa ba wani zama yayi sosai ba amma ya mata kyau sosai.



      Gefanta rakiya ce itama,wani series suke kalla,su duka sun bada hankalinsu kai,duk da cewa rakiyan ba fahimta take ba,bilkisu ce ke gaya mata duk abinda yake faruwa ta hanyar subtitile,don ba yaren turanci suke ba,harshen qasar mexico ne.



      Mama sodangi ce tafito cikin doguwar riga da wadataccen mayafi,hannunta riqe da wayarta dakuma atm card,idanunta a kansu ta qaraso falon

"Tashi rakiya muyi sauri mu dawo,yau siyayyar da yawa"

"Toh" ta fada tana miqewa da hanzari,sai bilkisu ta bisu da kallo

"Mama yau kuma ni kadai za'a bari kenan a gidan" dubanta tayi

"Ranki ya dade siyayyar tana da dan yawa ne,shi yasa na gayyaci rakiya muje tare,nasan koda na gayyaceki ba lallai ki amsa" ta qarashe tana murmushi,don tasha yiwa bilkisun tayin tazo suje din kodan ta miqe qafarta amma bata taba zuwa ba.



     Ga mamakinta sai taga tamiqe tana cewa

"Xanje" tayi hakanne don kawai tana tsoron gidan,tana tsoron xama ita kadai,uwa uba data duba time ma dawowarsa sai taga mintuna kadan suka rage,tana tsoron yadawo ya taddata ita kadai ya zatayi?.



      Fidda wayarta maman tayi tana cewa

"Ta kwana gidan sauqi ai,amma bari mu tambaya maigidan tukunna" jin ta ambaceshi sai bilkisun ta qara sauri tawuce daki,don kada ma tace mata ta tambaya da kanta.



     Mintuna qalilan tasake shiri tafito,tayi tsaf da ita,hakanan ta aje wani kyau mai daukan hankali,duk wani sirrin kyau nata da wahala da talauci suka boyeshi yanzun ya bayyana sanadin hutun data samu,qiba ce har yau babu abinda ta qara,tana nan 'yar firit dinta.



      Taji dadin fitar sosai,taga gari yadda ya kamata,tsari da yanayin garin yayi matuqar burgeta,tun daga ranar saiya zamana sukan fita tare lokaci bayan lokaci,cefane ko wankin kai ku kuma shan iska kawai.



      A haka rayuwa taci gaba da garawa,bata sanshi sanshi ba,bai santa ba,bata taba ganinsa ba bai taba ganinta ba,bata taba nemansa ba,bai taba nemanta ba,tamkar kowa zaman kanshi yake ba tare da wata alaqa ta hada dayansu da dayan ba.




*_BAYAN WATA BIYAR_*




      Duk ranar Allah da zata fito ta fadi saita lissafa adadin kwanakin da suka rage mata cikin gidan da garin gaba daya,kwanakin da suka rage mata takoma qasarta kuma cikin ahalinta.



      Ayanzun watanni biyar data shafe gani take taci nisan zango mai yawa a tarin tafiyar dake gabanta,hankalinta akwance yake sosai fiye da baya,sai taga ashe dukkan yadda ta tsammaci abun ba haka bane,ashe da tasan haka tafiyar zata kasance da babu damuwa ko kukan da zatayi,idanma zata koka din.....zata koka ne kadai saboda rabuwa da zatayi da 'yan uwanta na tsahon lokaci....


_tofa masu karatu,yanzu wasan zai fara_



      *****   *****   ******



      Kamar kowanne yammacin rana ta Allah buwayi da sukan zauna bilkisun ta dora musu karatu,yauma suna zaune a falon gidan bayan gama sallar la'asar da mintuna qalilan,ayau mama sodangi tana kitchen tanason kammala abincin darensu,kafin tazo sai bilkisu tasoma yiwa rakiya nata qarin karatun don kada a bata lokaci.



     Tana sanye da wani skert ne dogo wanda yafi zubi da buje,mahadi da hijabin jikinta wanda dukka tsahonshi bai zarta qugu ba,yadine mai taushi ruwan madara da aka yiwa dige dige dakuma adon furanni da dark pink,fuskarta tafito sosai tayi kyau kaman wata baby,hakanan kayan sun haskata qwarai,ta baiwa qofa baya,yayin da rakiya ke kallon qofar.



      Da fari sunji qarar tsaiwar mota a qofar gidan,basu kula ba,don sunyi tsammani maqotansu ne sukayi baqi,don sunsan su din babu mai zuwa wajensu a irin wannan lokacin,tunda dai lokacin dawowar azeez baiyi ba a yadda aka saba bare suce shine.



       Mintina kadan bayan nan sukaji ana taba qofar parlour dinsu,kafin suyi wani yunquri an bude qofar,da alama wanda yabude din yana da muqullin falon.



        Tare suka daga kai gaba dayansu,saidai yadda bilkisu taga rakiya ta miqe cikin girmamawa da tsananin nutsuwa yasa bilkisun kasa juyawa,wata matsananciyar faduwar gaba da bata taba jin irinta ba kaf rayuwarta ta ziyarceta lokacin da sassanyar muryarsa ke furta sallama afalon,muryar data karade dukkan kunnuwanta suka zarce zuwa ga qwaqwalwarta,tsintar muryar rakiya tayi tana fadin

"Barka da warka Allah ya baka yawan rai,barka da isowa" kanta a qasa,bisa dukkan alamu dokarsa ce baya son ana kallonsa,itadai bata sake jin muryarsa waida zummar amsa gaisuwar da rakiya ke kwarorowa ba,tamkar mutum mutumi haka bilkisu taci gaba da zamana wajen a daskare,zuciyarta tana wani irin gudu kamar zata fasa qirjinta,yayin da gumi yajiqe mata fuska zuwa wuyanta,bata motsa ba sai dataji ya kammala.takunsa gaba daya da alama ya gama hawa saman,sannan tayi wani irin yunqurawa ta kwasa da wani azababben sauri tawuce dakinta.



      Da kallo rakiya ta bita harta qulle,saita maido dubanta ga littafin da suke karantawa tana danne dariyar dake taso mata,tabbas batasan waye azeez ba,inda tasan wayeshin da bata damu kanta kan boye kanta haka ba,ko yanzun ma kallo guda tak yayiwa muhallin da suke zaune bai qara na biyu ba ya qara gaba,bai damu daya duba baquwar daya gani xaune a wajen ba sam,sai wani murmushin yasake kubce mata sanda take hango fuskokinsu a tare

"Zasu fa dace da juna" ta fadawa kanta da kanta a fili,sai kuma ta damqe bakinta tana zare idanuwa tana duban falon,Allah yasa babu kowa,litattafan nasu tahau tattarewa kawai tabi mama sodangi kitchen.



        "Wai kaddai ace harkun gama karatun,duk saurin da nake nagama na cimmaku" sai data aje litattafan saman freezer tana danne dariyarta sannan tace

"Inafa aka gama mama,yarima ne yashigo muna tsaka da karatun,tana ganin yashigo ta kwasa tawuce daki shikenan karatun ya qare" murmushin itama mama sodangi tayi tana kashe gas din,itakam wannan abun nasu batasan farko tsakiya ko qarshensa ba,fata dai Allah ya zabama rayuwarsu abinda yafi zama alkhairi tayi addu'ar cikin ranta.



       A mugun gajiye yashigo gidan,don asubancin da yayi yau yafita a gidan yajima baiyi irinsa ba,wanka kawai yayi yadawo yaxube a katafaren falonshi,kwanciyar rub da ciki yayi bayan ya tasa ruwan cikinsa da filo yana lumshe idanuwa,sanyin ac dana sauran ruwan jikinsa yana ratsashi.



       A hankali yasoma jin tsohon feeling dinshi da yaketa qoqarin adanawa yanason taso mishi,don haka saiya mirgina yakoma kwanciyar rigingine,kana ya jawo wayarshi yayi kiran abdulrashid,saboda kwana biyu basuyi waya ba.



     "Mr ango,yanzun nake cigiyarka a raina,ina tunanin idan nakoma gida na kiraka,tunda kai angonci ya boyeka" idanunsa ya lumshe kana yabude yana dan dukan tsakiyar kanshi,don sam bai gane angoncin da abdulrashid din ke magana akai ba

"Angonci ne mefa?" Dariya abdulrashid yasaka

"Karka rainawa kanka hankali....bansani ba nima" sai a sannan yatuna cewa shidin fa andaura mishi aure watanni kusan hudu ko biyar da suka shude

"Allah ya shiryeka abdulrashid..."

"Kaidai zance Allah ya shiryeka azeez,wannan attitude din naka bansan sai yaushe zaka rabu dashi ba" murmushi yasaka mai dan sauti

"Wanne attitude gareni?,wai har na kaika?,kaga kira nayi mu gaisa ba fada ba" ya fadi yana dakatar dashi.



      Hira sukayi mai dan tsaho sosai,wanda ta jawa abdul'azeez din lokaci,har lokacin magariba yakusa sannan ya aje wayar,yashiga bandaki ya sake watsawa jikinsa ruwa,don shi wani irin mutum ne mai mugun tsafta da qyanqyami,hakanan wanka baya isarshi.



      A gurguje yake shiryawa din yanason fita kamar kullum wayarshi tasake daukan ruri,safwa ce,saiya yarfar da hannu

"Safwa!" Kana ya daga wayar

"Its time for prayer fa" ya gaya mata a taqaice,saboda qa'idarshi ce bayason kiran waya lokacin sallah.



     Kamar yana gabanta ta murguda baki kana ga juya idanu

"U r in mexico and am in nigeria mr man,ko ka manta ne?" Qaramar dariya yayi

"Yes maaaa"

"Ohk,no more excuse da zaka bani,yanzun lokacinane gaba daya"

"Bance a'ah ba,but...yanzun lokacin sallah ne,and i have visitors,friends dina ne daga wata qasar....nayi alqawari i wil cal you" shagwabe mishi tayi yadda ta saba,wanda hakan ya sanya yaji tsigar jikinsa na wani xubawa yarrrr,ya lumshe idanunsa yana sauraren kukanta,a hankali yabude bakinsa

"Stop it please safwa,i said i promise" ajiyar zuciya tasauke

"Na yarda,amma vedio call?"

"Yes" ya amsa mata a taqaice,hakan ya mata daidai,saita saki murmushi tana masa sallama,yau rana ce ta musamman a wajenta,don ba kasafai yafiya yarda suyi vedio call ba,yakance mata tsarinsa kenan,don haka tana aje wayar ta dira daga kan gadonta cikin sauri,tahau hargitsa cupboard dinta,ta ciro wani riga da skert ta watsa saman gadon tawuce toilet cikin sauri kamar wadda ake jira,tanaso ayi mata gyaran gashi na garari,don tasan azeez din yana matuqar son suma,tun ranar data sani din kuwa duk randa zayazo sai taje an mata gyaran gashi an mishi ado mai kyau azubo dashi yadda zaike gani,saidai kosau daya bai taba tankawa ba,saidai ya kalla yadauke idanunshi,hakan bai dameta ba,saboda tasan halin miskilancinsa,ko iya kallon da zaiyi ita ya gamsar da ita.



      Wanka tayi sharp sharp sannan tafito ta shirya,kana ta zari muqullin motarta tafito.



        Saman daya daga cikin kujerun alfarma dake katafaren falonsu na farko tasamu mahaifiyarta zaune akai,yayin da wata mace ke durqushe gabanta riqe da qafarta,da alama pedicure take mata,itan kuma tana riqe da wayarta tana latsawa,kallo daya zaka mata kasan hamshaqiyar hajiya ce data jiqu da naira.



       Dago kai tayi da sauri tana duban safwa data rungumota ta baya

"Fita zakiyi?" Ta jefa mata tambayar tana karantar zallar farincikin dake shinfide kan fuskarta,kai ta gyada

"Zanje retouching ne amma,yau azeez ya yarda zamuga juna" saita saketa cikin sauri tanufi qofa,baki wangale ta bita da kallo,xasuga juna kamar yaya?,qasar zaizo?,bata samu damar mata tambayar ba don tuni takusa kaiwa ga qofa,saita daga murya kawai tace

"Banda tuqin ganganci,ki dawo kuma dawuri tun babanki baizo yaga ke daya kika fita ba"

"Ohkey mom!" Ta fada yadda zata jiyota,saita girgiza kai kawai ta maida kan wayarta,ita kanta tana jinjina yadda diyar tata take bala'inson abdul'azeez din,tamkar babu wani namiji da yayi saura a duniya saishi,saidai tana godewa Allah daya sanya wanda takeso din ya cancanci a soshi,ba gama garin mutane bane.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 26

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_________________________

*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*



*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸™Å½Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯ðŸ½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸‘¯Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*



*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ðŸ¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾

_____________________________

   Bata tsaya an mata wani iso ba kamar sashen fulani aisha,kawai ta cusa kanta inda tasan xata samu fulani adaman,a sannan tana zaune ne ita diyarta Aafra,'yarta ta biyu wadda ayanzu haka kudin aurenta ke hannu,duk da ba'a sanya rana ba,tanason hadata ne da autarta ta aurar dasu lokaci daya.



      Da sauri tazauna tana gyara zamanta ganin shigowar gaggawar da saudat din tayi mata tana duban yanayinta,gaidata afra keyi,maimakon ta amsa saita ce

"Bamu waje zamu gana da babarki" duban maman nata tayi kamar ba zata tashi ba,amma inkiyar da fulani adaman tayi mata ya sanyata miqewa tana tura baki,ta dauki wayarta tana gyara yafen mayafinta tafice.



       Qaqqarfar ajiyar zuciya tasaki sanda take zama,cikin damuwa fulani adama tadubeta

"Wai lafiya kuwa saudat?"

"Inafa lafiya,har yanzu haqarmu ta gaza cimma ruwa,daga sassan aisha nake,komai nasu yana tafiya dai dai,da alama ma yadda suka tsara,babu alamun wani abu dake damuwarsu,akwai matsala fa adama,tabbas akwai matsala,wankin hula zaya kaimu dare".



      Maganar itama ta sanya damuwa a ranta,saita sauke ajiyar zuciya cikin damuwar tace

"Yanzu babu wani abu kenan da xamu iya yi,ba shakka wannan babban abun kunya ne a wajenmu"

"Ina zuwa,akwai wani aiki dana sanya ayimin" saudat ta fada bayan ta zaro wayarta ta soma danne danne.



        Dab da kiran zai katse muryar kamal ta bayyana

"Hey mom" ya fada da alamun muryarshi na nuna tafiya yakeyi a qasa

"Hey....kana ina ne?" Dan tsaki yaja yana yarfa hannu

"Ganinan a qasa,mom nayi nayi ki matsawa daddy ya siyamin mota amma kinqi,kullum saidai mu qare da aron ta wancan dan girman kan,haba da Allah bafa girmanmu bane,shi yasa kowacce beb ka taya sai kaga hankalinta na kanshi indai ta sanshi"

"Kaga dakata.....kaima kasan halin babanka sarai,bazai siya ba,shi yasa naketa fafutuka wannan lamarin ya tabbata komai yadawo hannunmu,bama mota ba har private jet zaka mallaka" dan tsalli yayi gamida sakin ihu,wanda qila da anan gida nigeria yake sai an tsaya kallonshi

"Wow mom....akwai kuwa latest news"

"Dama shi nakira ji....gayamin ya ake ciki"

"Yarima ya daina kwana a gida kwata kwata,kusanma sai ku kwana mu yini wani lokacinma sai yayi almost two to three days bamu ganshi ba,infact....dana lura dakyau ma sai na fuskanci da yawa daga cikin kayanshi basa gidan"

"Me hakan ke nufi kenan?" Tayiwa kamal tambayar,amma idanunta suna kan adama

"Well,ina tunanin kamar yasauya gida ne fa"

"Ina yakoma"

"Idn't know gaskiya mom,kinsanshi da tsare gida,bayason yawan tambaya ko sanya idanu"

"Dole kazama mai tambaya,kuma dole kazama dan sa idonsa koda bayaso,ya zama lallai ka binciko mana ainihin abinda yake faruwa,dakuma inda yakoma"

"Ohkey....i will do my best" daga haka ta katse wayar tana duban adama.



      Babu wanda ya iya cewa dan uwanshi da komai,har tsahon wasu mintuna kafin adama ta magantu

"Tabbas aisha ta sauyawa abdul'azeez gida ne,kuma ina da yaqini da tabbacin akwai dalilin da yasanya tayi hakan,akwai abinda takeyi ko take shirin yi wanda take boyewa batason kowa yasani" kai saudat tajinjina cikin gamsuwa

"Hakane,nima na yarda da hasashenki....zan matsawa kamal har sai ya binciko mana komai cikin qaramin lokaci" tattaunawa sukaci gaba dayi a tsakaninsu ta yadda zasu bullowa komai harna tsahon wani lokaci.


*******    *****    *********



      Tunda yatashi a safiyar yau gaba daya yaji bashi da sha'awar fita ko ina,don hatta da qasan gidan bai sauko ba bare mutanen gidan susan yana cikin gidan.



      A samanshi yayi wankansa yadda yasaba,yashirya cikin kaya marasa nauyi dukka farare kamar yadda yawanci yafi son fararen kaya a shigarsa,yana da coffe maker ya hada coffe dinsa da wani sauran cake yasha,yagama dukka sabgoginsa a waya,kamar kiran ammi da maimartaba da sauran mutanen da yake da hulda dasu,yakira safwa ma suka dan kashe wasu lokuta kana ya katse wayar,ya debi litattafan makarantarshi,ya isa can quryar falonsa ya murda wata qaramar qofa saiga wani qawataccen balcony dan madaidaici da aka bullo dashi ta backyard na gidan,wajene da aka masa kwalliyar furanni daketa bawa wajen qamshi kala kala,tun daga qasa har jikin bangon wajen,sai kujerun hutawa guda uku da table,daga balcony din kana iya ganin backyard din fes.



     A nutse ya isa kan daya daga cikin kujerun yazube litattafansa,kana yasoma tattakawa harya isa gaban qarfen da aka tokare balcony din dashi,dafe qarfen yayi yana qarewa backyard din kallo,kafin yadauke idanunshi ya cillasu cikin gine ginen da yake iya hangowa cikin unguwar.



       Shuru unguwar take kamar kowanne lokaci,sai mutane tsilli tsilli dake wucewa,wanda yawanci a qasa suke tafiya da alama ba nisa zasuyi ba,wasu mata wasu maza,wasu mace da namiji wani lokaci da 'yan yaransu.



       Ajiyar zuciya yasauke sannan yasake dawowa yazauna kan kujerar bayan ya kwashe litattafan ya azasu saman cinyarsa,yasoma budawa a hankali yana nazarin karatuttukan ciki.



         Sosai karatun yake masa dadi,saboda yanayin wajen dakuma yadda yake sake fahimtar abinda yake karantawa sosai kamar ana bude qwaqwalwarsa ana zuba masa shi.



      A hankali yasoma jin surutu,wanda da fari yayi qoqarin tokare hayaniyar don kada tashiga karatunshi ta bata mishi yanayin da yake jin dadinsa.



      A hankali a hankali sai surutun yasoma yawa,yakuma so ya dameshi,hakan yasa yasoma mutsu mutsu yana yana gyara position na zamanshi ko xai daina jin hirar,saidai abanza, duk yadda ya gyara zaman baijin canjin muryoyin da yakeji.



       "Bilkisu!" Yaji an qwala kira,hakanan yaji kamar an fusgi hankalinsa,saiya dauke kansa daga kallon littafin zuwa bangaren da yaji muryar tana fitowa.



      Su biyune zaune saman wasu 'yan kujeru masu kyau da aka tanada a wajen saboda hutawa,sun tasa botiki kowa dai dai a gabansa suna faman wankin inner wears,sunata hira gami da dariya da alamu lokacin na musu dadi,kuma babu abinda hake damunsu,da alama sune suka isheshi da surutu kenan tun dazun.



       Su biyu ne,rakiya da wata wadda baisan ko wacece ba,sanye take da doguwar riga na wani yadi mai sulbi da qyalli wanda kana masa kallo daya zakasan ya jibanci gidan sarauta,an masa dinkin doguwar riga,wadda daga sama ta kamata datayo saman cikinta kuma zuwa qasa ta bude sosai,hannunta gajere ne sosai don ko gwiwar hannu tsahonsa baikai ba,gashin kanta da yasha gyara shekaran jiya yana fake a ribbom,duk motsin da tayi sai jelarsa ta tayata motsawa,fuskarta akwai alamun nutsuwa da walwala,amma wacece ita?,ya tambayi kansa yana zuba mata idanunshi gamida sake karantar yanayinta

"Idan kun gama bilkisu ga abinci can na kammala" cewa mama sodangi dake qarasowa wajen tana dubansu.



      Wannan karon baiji me ta fada ba,saidai fuskarta shimfide da murmushi take wa mama sodangin magana,bata qara minti daya ba maman ta juya tabar wajen,yayin da kuma sukaci gaba da aikinsu da kuma karadinsu,shi kuma yaci gaba da nazartarta.



       Baisan adadin lokacin daya kwashe ba yana bibiyar lamarinsu,daga bisani ya farga,tamkar wanda aka tashi daga barci yayi firgigit,ya janye idanunshi daga kansu yana jan wani mugun tsaki,haushin kanshi sosai ya kamashi,baiga dalilin da xai sanyashi xama yana wannan abun ba,yaduba agogon dake maqale a wani saqo dake wajen,yasake jan tsaki haushi yana sake cikashi ganin lokacin daya narkar a banza,saiya tattare takardunsa kawai kana yawuce ciki,yasanya maqulli ya rufe qofar.



        Kan gadonshi ya fada da qarfinsa cikin rub da ciki yana sauke qaqqarfar ajiyar zuciya,hakanan wata kasala tana lullubeshi,sai ya lumshe idanunsa yana furzar da iska daga bakinsa,surarta yadinga gani cikin duhuwar idanunsa tana masa yawo,sai yayi hanzarin bude idanun nasa gamida maida kwanciyarsa rigingine,ya kuma goye hannayensa a qirjinsa idanunsa suna kallon rufin dakin.



       Wasa wasa saiga abun nason shiga tunaninsa,saiya miqe yasake zama sosai yana jan tsaki,babu shiri yatashi zumbur ya isa cupboard dinsa yasoma zaro.kayan da zai iya sanyawa,sam babu plan din fita a yanzu a tsarinsa,amma dole yafita,don baison yazauna yayita fama da tunanin da zai dameshi,ya shirya a gaggauce kana ya rufe saman yasauko yafice daga gidan gaba daya,bayan yadauki motarsa dake aje gaban gidan.



       *******    *****    ********



     Cikin madaukakin farinciki take takowa zuwa inda yake tsaye a filin sauka da tashin jiragen sama dake mexico,jinta take cikin wata duniya ta musamman,yau da kanta ta kawowa azeez din ziyara,abinda ta dade tana so tana kuma sanya rai.



      Murmushine sosai kan fuskarta tana kallonshi,yayin da shima ita yake kallo,fuskarsa ta washe alamun akwai fara'a sosai shima bisa tashi fuskar,dab da zata qaraso inda yake tasoma sassarfa saboda yadda fa qagu ta ganshi,ji take kamar ta shekara bata ganshi din ba,ta taho da sauri da niyyar fadawa jikinsa,da hanzari yakauce yana mata murmushi kana ya kada dan yatsanshi manuni

"Nooo...." Saiya mata nuni da mutanen dake zirga zirga a wajen da idanunsa,kafadunta ta daga tana tabe baki gami da bata rai,cikin idn't care manner,baisan me yasa take daukan wasu abubuwan ba'a bakin komai ba,tsabar wayewa ce ko boko ne ya mata yawa oho bai sani ba,ko kuma sangarta ce da gata?,ita ba rayuwar waje tayi mai yawa ba bare yace abunne yashigeta,sam tana ganin don yayi hugging dinta ba wani komai bane,hakanan bata dauki kisses a tsakaninsu a bakin komai ba inda yana biye mata,tana ganin ai suna son juna kuma auren juna zasuyi,so ba wani abu bane don suna body contact,tunda ba maj gaba daya suke ba sun kame kansu,saidai sam shi bai yarda da wannan tsarin ba,tunda yasan kanshi,yasan matsalarsa yasan kuma yaya jikinsa yake,ko baya ga hakama shi abun baya burgeshi,yafison komai yazo a lokacin daya kamata yakuma dace,sai yafi bada armashi da ma'ana.



       Har yabude mata motar tashiga tana zumburo baki,yasan don ya hanata ta rungumeshine yasa take wannan kumbure kumburen,saiya basar kamar bai lura ba,yasoma tunanin inda zai ajeta,daga bisani ya yanke ya tambayeta

"Ina madam takeso ayi mata masauki?" Cikin muryar dake nuna fushi tace

"Inda yallabai yake zaune mana" ya gane sarai inda take nufi,gidan da suke zaune shi dasu kamal da mutspha harma da jabir,bazai soma wannan gangancin ba,yaje yakaita cikinsu ya aje,ita kanta ziyarar tata banda tare da antynta sukazo qasar ta sauka a wani gari ita kuma tace zata qaraso ta kwanan musu ko dayane da yace ya yafe,baison yafadiwa antyn haka taga kamar ya gwasale mata 'yar 'yaruwarta ne,duk dashi wannan ba damuwarsa bane koda zata ji haushin,amma ita safwan a karan kanta ta jima tana masa nacin xata zo takanas daga nijeria zuwa mexico,shike dakatar da ita,sannan uwa uba yasan baya bata attention dinsa kan soyayyarsu yadda takeso saboda dalilansa da suka ta'allaqa da yanayinsa,dakuma yadda ita a karan kanta take mu'amalantarsa yana masa tsauri da yawa,dakuma jefashi cikin yanayi.



        "Zabi wani wajen dai" saita dage kafada

"To daya gidan" kafadanshi yadaga,yana ganin can din babu matsala sai yace

"Alright". Ko kafin su isa gidan tuni ta warware daga fushin da takeyi dashi,don dama bata iya wani dogon fushi dashi.



        Tana zaune gefan gadonta tana warware kalbar dake kanta,wadda rakiya tayi mata bayan tsefaffaen kan ya dameta,sallama cikin wata lallausar murya ta ratsa falon kana ta isketa har dakinta,sai tabar duk abinda take tana saurare ko zata sake jin wani abun bayan sallamar,bata sake jin komai ba face muryar rakiya cikin tsananin girmamawa tana fadin

"Barka da zuwa Allah ya taimakeka....barka da warhaka yarima"

"Yarima?" Ta tambayi kanta gabanta na wani mummunan faduwa da batasan dalili ba,indai zata san cewa yana gidan,indai kuma za'a ambaceshi ko yaya sai taji wannan fargabar da faduwar gaban,tamkar wadda akace gashinan shigowa saita rarumi dankwalinta tana rufe tsefaffen kanta,kana ta rarraba idanu cikin dakin,gabanta naci gaba da faduwa,zuciyarta na mata saqe saqe gamida raya mata abubuwa masu yawa.



       "Tana madafa....bari nayi kiranta" tasake jiyo muryar ruqayya tana fada cikin sauri,duk da bataji me yace daga can sashen ba,amma tabbas mama sodangi ya buqaci gani,hakanan tasamu kanta da tashi cikin sanda ta isa bakin qofar dakin nata,ta sanya hannu da niyyar murza muqulli,wata zuciyar tace zai iya yiwuwa ajiyo qarar taba qofa,tunda cikin falon babu kowa

"Wow swerry,gidan nan yayimun fa" muryar safwa ta katse shurun da falon yadauka bayan wucewar rakiya

"Am so glad to hear this" ta sake jiyo lallausan muryar tana fada a taqaice,ci gaba tayi da tsaiwa hakanan ba tare da tasan dalili ba harta jiyo muryar mama sodangi na fitowa daga kitchen.



       "Barka da dawowa" ta fada itama akwai alamu na ban girma a muryarsa,manyan idanunshi ya lumshe yana gyada kai kawai,yanayin yadda yake maganarshi idan baka sanshi ba zaka tsammaci yanga ce yakeyi,saidai hakanan yanayin halittarsa take

"Yauwa sodangi....ga baquwa nan,sunanta safwa,zatayi kwana biyu" cikin girmamawa tace

"Fulani ta shaidamin.....Allah ya baki nasara barka da zuwa" dan murmushi safwa tasaki dadi yana ratsata,tanason harkar da za'a dinga bata girmanta ana kuma kambamata,tunda tasan takai ayimata hakan,saita gyada kai kawai tana cewa

"Barka kadai sodangi,mun sameku lafiya?"

"Lafiya qalau gimbiya safwa" sunan yasake faranta mata rai,hakan yasa lokaci daya taji mama sodangi tayi mata a ranta.



      Miqewa yayi don dama a hannun kujerar yake a zaune,sai safwan ta dubeshi da shagwabar nan tata

"Ina zuwa kuma?" Cikin sanyin muryar kamar yadda yasaba,kai bakace ya iya hargowa ba,shi yasa duk wanda yaganshi a sa'ilin da yake fada take daban mamaki,bazakace shi bane

"Zan qarasa schedules dina nayau" kafada ta maqe tana dubanshi

"Sam ba yarda ba,kamata yayi kayi cancel duk wani schedules naka har sai na koma,tunda kasani saboda kai nazo ai" tuni mama sodangi tajuya don komawa kitchen,don abun yadan mata nauyi,tunda bata taba ganin hakan ba,hasalima duk fadar safwa da ake yau tasoma ganinta.



       Girarshi yadage sannan yace

"Really?"kawai saita sake mishi kukan shagwaba,kusan bataji me yace mata ba,amma taji takun hawanshi sama,kasa barin wajen tayi har zuwa sanda aka gyarawa safwa dakin da zata zauna,daganan bata sake jin komai ba,saita saki qofar takoma bakin gado tana sakin ajiyar zuciya a jejjere.



        Dai dai lokacin karatunsu harda wasu mintuna akai taji anyi knocking qofar dakin,saita sake yin wuri wuri,duk da kusan awa biyu cif bata sake jin wannan muryar da take da yaqinin tashi bace,sai muryoyinsu rakiya da mama sodangi wani lokaci dana baquwarsu wadda da alama tacika tambaya dakuma surutu.



       Shahadar quda kawai tayi tabada daman shigowa,rakiya ce a shirye tsaf riqe da litattafansu a hannunta,fuskarta qunshe da murmushi take duban bilkisu,zamansun tare dakuma shaquwarsu yasanya daga ita har rakiyan kowanne yake mance matsayin dan uwanshi a tsakaninsu,sukan kalli juna ne tamkar qawaye,sau tari mama sodangi ce kan jawa ma rakiya kunne kada ta mance matsayim bikisun,itakuma bilkisu sam hakan bai mata dadi,don ita bataga wani matsayi daban dake gareta ba,uwa uba ma ita tafi jin dadin mu'amalarsu a hakan dari bisa dari,rakiya a matsayin qawa kuma 'yaruwa,mama sodangi a matsayin uwa,hakan yafi gamsar da ita,tun suna takatsantsan da kiyayewa har suma suka saki,suka kuma dauketa a yadda takeso su dauketan

"Akramakillah.....hala yau bazamu samu darasi ko guda daya ba?" Wayarta da take browsing da ita ta sauke bayan ta kashe datar,baya ga kiran 'yan uwanta tana jin dadin wayar sosai,duk da cewa bata charting ko guda daya,amma ta zame mata wani dandali na daukar karatu,tasan ingantattun link na manyan malamai da take shiga tadauki karatu sannan tafito,ta qaru fiye da zatonta,takuma sake imani da cewa,ita waya yadda ka dauketa hakan take,kamar kwalba ce,asali a tsaftace take,idan kaso kazuba ruwa ko lemo,idan kaso kazuba giya,wannan kai ka gurbatata.



       Cikin sanyin murya tace

"Rakiya bamu kadai bane bafa a gidan" murmushi ya subuce mata,tana mamakin yadda bilkisun take bala'in tsoron gamuwarta da yarima abdul'azeez,ko ita da take hidima cikin gidansu,take kuma qarqashin ikonsu tsoronta baikai wannan ba,abun nasu yana da matuqar daure kai,ance mata aure aka musu,amma dagashi har ita babu wanda yataba ganin wani?,batasan koshi ya taba ganinta ba(eh ya taba ganinta amma rakiyan bata sani ba),babu wanda ya taba hada inuwa da dan uwanshi,duk da batasan ainihin rayuwar aure gaba daya ba,amma ta tabbatar wannan ba shine aure ba.



       "Dodon yafita tun dazu,babu kowa cikin gidan saimu" harararta tayi kadan kana tayi shuru  kamar bata yarda ba,sai kuma ta sauke ajiyar zuciya

"Muje" ta furta tana saukowa daga saman gadon,tazura slippers dinta tana ware dankwalin kanta tayi rolling dashi tabi bayan rakiya suka fice tare.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 25

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

____________________________

*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*



*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸™Å½Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯ðŸ½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸‘¯Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*



*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ðŸ¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾




      Lokacin daya dawo dare yayi,saidai bawani dare can ba,a sannan sha biyu ne harda rabi,da muqullanshi daya saba amfani yabude gidan yabude yashigo,falon tsit babu kowa kamar yadda yakan tarar kullum idan yadawo,kai tsaye ya haura zuwa sama inda dakinshi yake.



       Alwala yasoma yi kamar yadda yasaba zama da alwala akai akai haka ammi takoya mishi tun ba yanzun ba,yakuma saba yatashi da dabi'ar,alqawarin daya yiwa safwa yana cikin ranshi,mutum ne shi mai.matuqar kiyaye alqawari dakuma qoqarin cikashi,don haka yaja laptop dinshi yakunna.



       Kiran safwa yasoma yi,wadda tajima gaban system din nata tana tsammanin kiranshi,harta soma kumbura jin shuru har yanzun bai kira ba,saidai idan ta tuna yana da cika alqawari sai kuma fushin nata ya sassauta,don haka yana kira ta daga.



       Tarwai ta bayyana cikin screen din nashi,ta cika screen din gaba daya,tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata lafiyayyar baqar riga ta wani yadi wadda ta haska fara tas din fatarta,gashinta na reto a kafadarta guda,fuskarta fes da madaidaiciyar kwalliya,labbanta sunata qyallin lipstick ta hasken screen system din.



       Murmushi ta sakar masa tana kashe masa idanu daya,saiya lumshe idon nashi yana jin tsigar jikinsa na tashi,uwa uba yanayin kwanciyar da tayi din batayi masa ba,saboda ana ganin wuyanta zuwa qirjinta sosai,duk da basu bayyana ba gaba dayansu amma kana iya hango tudunsu

"Tashi sosai ki zauna" ya fada qasa qasa yana lashe busassun labbansa,murmushi takuma sakar masa,taji dadi ta sanyashi a yanayi,tana son taga yasauya saboda ita,anata ganin wannan kawai shine xai nuna ma'aunin qaunar da yake mata,hakanan zai bayyana adadin yadda ya matsu su zama mallakin juna kamar yadda itama ta matsu,tunda tasan bazai taba buda baki ya gaya mata yadda take da buqatar ji ba

"Meya faru da kwanciyata kuma?"

"Ki gyara kawai ko nayi cutting up kiran" tasanshi sarai zai aikata,don haka ta miqe zumbur tazauna tana tura baki gaba,saiya saki wani qaramin murmushi wanda iyakacinsa labbansa.



       Bata iya wani dogon fushi da shi,don haka ba bata lokaci tasauko suka soma hirarsu,anan yayi realising lallai safwa batasan da zancan plan da ammi tayi na,saboda kusan rabin hirar tasu tayau tana nuna mishi yadda take bala'in kishinsa,daga qarshe ma ita yabarwa fagen yaxuba mata idanu yana kallon yadda labbanta da sukasha man lebe suke motsi.



       Cikin jikinsa yaji tabbas akwai matsala idan sukaci gaba da zama a haka,don haka ya yanke shawarar samun abun mai zafi da zai rage masa abinda yasoma ji


       Yasake kallon agogon dake aiki qasan system din,dare ya riga da yayi,bai kyautu ya tashi sodangi ba yanzu,don haka ya sanya laptop din a sleep bayan ya nemi uzuri wajen safwa ya dantse kiran,yamiqe ya zura slippers dinshi yasauko qasan.



      Dai dai lokacin da yunwa ta hanata sakat sakamakon qin fitowa da tayi taci abincin dare,har suka gama abinda suke suka tafi suka kwanta.



       Don dole ta tashi da hanzari jin yadda hanjinta ke curewa waje daya,slippers dinta itama kawai ta zura tana tattare hannun rigar baccin jikinta,wadda take riga ce iya cinya mai dogon hannu da wandonta dogo na wani lallausan yadi ruwan hoda,kanta babu dankwali,sai gashinta jelarsa ke reto a bayanta yana kuma qyalli saboda mai da gyara da yasha,ta bude qofar dakin nata a hankali kamar wata barauniya,ta tsaya ta kasa kunne,sai data tabbatar bataji motsin komai ba sannan tasoma takawa a hankali zuwa kitchen din.



      Cikin qaramin plate tazubo abincin kana ta dawo falo,tvn dake aikia falon wadda sun manta basu kashe ta ba taja hankalinta suna nuna wani shirin girke gike,saita tsaya gaban tvn da plate din a hannunta tana yafitar abincin kadan kadan tana ci,idanunta da dukka hankalinta yana kan tvn.



       Taku biyu rak yayi ya hangi mutum gaban tv,abun sai yaso daure mishi kai gamida bashi mamaki,a hankali yake qarewa bayanta kallo,a jikinsa yakejin baquwa ce,don sam batayi yanayi ko zubin rakiya ba bare yace itace,duk da ba wani kallonta yake ba amma yasan ba ita bace

"Wow" bilkisu tadan fada cikin birgewa,saboda abinda cook din ta hada yayi matuqar burgeta yakuma bata sha'awa.



        Sautin muryarta yasake tabbatar masa da zarginsa,saiya ci gaba da saukowa idanunshi a kanta.



       Jin takun saukowa daga step ya sanya gabanta mummunar faduwa,ta soma zazzare idanu,babu abinda yazo ranta illa

"SHINE!" zuciyarta ta gaya mata da qarfi

"Wala'alla ma dakinki zashi" zuciyarta ta sake gaya mata,sakin kwanon hannun nata tayi da hanzari ba tare data shirya ba,a miliyan tayi dakinta kamar zata tashi sama batare datako waiwayo ba bare taga waye,wanda hakan ya baiwa sassan jikinta damar motsawa dakyau,bataci biriki ba sai data tabbatar ta isa dakin,kana ta sanya muqulli tarufe qofartata gam.



      Mamaki ne yasanyashi tsaiwa yana kallonta gamida mamakin wacece wannan?,ganin baida amsa saiya tabe baki gamida dage kafadunsa yawuce zuwa kitchen donyin abinda yafito dashi.



      Koda yakoma dimma hirar kadan suka qara ya bata haquri,ya qarasa shanye coffe dinsa kana yayi shirin kwanciya yakwanta,kafin bacci yadaukeshi yatuna abinda yafaru mintunan da suka wuce,saiya tabe baki gamida jan qaramin tsaki,idan bamai matsalar qwaqwalwa ba wazaiyi haka?,kawai daga jin taku saika yar da kwanon hannunka kahau gudu,sake gyara kwanciyarsa yayi yana jan tsaki gamida rufe idanunsa,ya aje komai gefe yanason bacci ya daukeshi.



      ******    ******   ******   ****



      Kimanin qarfe sha daya ne na safiyar ranar,su ukune zaune a falon nata saman dining suna karyawa,fulani aisha da yaranta uswa da sumaira.



      Diyar uswa ce akan cinyarta tana bata farfesun nama a hankali yayin da suke taba hira wadda ta shafesu,daidai lokacin jakadiya ta qaraso,ta zube tana shaida mata saqon son ganinta da saudat(qanwar maimartaba mahaifiyar kamal) keson yi.



      Kai ta gyada kana ta bada izinin ganinta,ta dauke idanunta ta maida kan yaran nata,sai ta yiwa sumaira inkiya data dauki sahla dake saman cinyarta,ita kuma ta miqe tana goge hannunta da tissue.



     Cikin nutsuwa qasaita take saukowa daga wajen dining din zuwa ainihin falon,tana sane da zuwan saudat din gidan kimanin kwanaki hudu,amma bata nemeta ba kamar yadda ta nemi sauran abokan zamanta.



       Tuntuni tasoma shaqar wani abu dangane kan saudatun,hakanan takejin sam takunta bai mata ba,tun kafin yau dama ba wani alaqa mai kyau bace can can tsakaninta da saudatun tunda aka aurota,hakanan jininsu bai hadu ba,hakan kuma baya rasa nasaba da aurotan da yayi a wata qasa,wanda a lokacin saudat din sam bataso hakan ba,akwai qawarta dataso hadashi da ita kamar kamar me,taji ba dadi sosai,don a sannan ita dayace ta rage mishi qanwa kuma abokiyar shawara,dama duka duka su ukune Allah ya baiwa sarki mu'az,Allah ya yiwa babbar yayarsun rasuwa,tabar yaro daya wanda yake hannun saudat din tana riqo.



       Cikin qasaita shigo shan qamshi da kallon komai É—ai É—ai tashigo falon,don dukka cikin gidan babu sassan da yakai na fulani aisha kyau da tsaruwa da kayan ado na alfarma dake sake nusashe dakai cewa nan fa akeyin sarautar,don ita gada tayi daga fannin mahaifi dakuma miji,sarauta saidai ta nunawa wasu

"Bismillah" ammi tafada tana nuna mata daya daga cikin kujerun cikin nata salon qasaitar da isa,saida saudatun tazauna kana itama tayiwa kanta mazauni kan kujera maicin mutum biyu,kana ta dora qafarta daya saman daya idanunta kan saudat

"Matar dan uwana" ta fada kamar yadda ta saba kiranta dashi

"Maman kamal....yaushe a gari?" Ta fada a dake,saita dan yatsina fuska

"A qalla yau kwanana hudu cikin gidan nan,amma da mamaki idan kikace bakisan da zuwa na ba" hannayenta ta watsa kafin ta hadesu waje guda

"Ba abun mamaki bane,saboda kowanne mutum akwai irinsa,ba kasafai na fiya damuwa ko bibiyar al'amuran dake wakana cikin gida ba,indai lamarin bawai yajibanceni bane" wani duba ta mata tanason fahimtar meta fada din,magana ce cikin magana ko kuma magana tayi kanta tsaye ba tare da kowanne nufi ba?,saita gyada kai sa'an nan tace

"Haka ne" daidai lokacin da sumaira ke saukowa rungume da sahla,kana ta qaraso cikin girmamawa,fuskarta a sake kasancewarta maison jama'a fiye da kowa cikin 'ya'yanta,tazauna saman daya daga cikin kujerar tana gaida saudatu da suke kira da mom,gami da tambayarta 'yan uwanta yaran saudatun wato safna da safina

"Qalau" ta amsa a taqaice,daga bisani uswa ta sauko itama ta gaidata,saidai ita daga gaisuwar bata qara komai akai ba saima qoqarin miqewa da take don barin wajen,kasancewarta gwanar miskilanci ce itama kamar dan uwan nata abdul'azeez,dukka fulani aisha na ankare da yadda take amsa gaisuwar tasu,wanda tasha bamban da yadda take treating su walida qwarai

"Ke zonan,don uwarki me yasa ne baki da hali,kodon kinga mun aurar dake ne yasa kike ganin kanmu daya" ta fada cikin zafi zafi,kamar da biyu take maganar.



      Uswa dake tafiya ta waiwayo kana tace

"Wa wai?,ni?" Wanda ita harga Allah bada wani abu tayi maganar ba,kusan nature dinta kenan

"Ban sani ba" ta amsa mata a gadarance.



      Batace komai ba ta dawo din tasamu waje taxauna,saita soma fada mara dalili,ta inda take hawa bata nan take sauka ba,waita yaye kowa bata neman kowa.



       Dukkan wani takunta da abinda fulani aisha ke nema ya gama bayyana kanshi,don haka saita shareta yadaga waya tasoma amsa kira,bata tsagaita ba har sai data gama taga yaran suna tashi suna wucewa ciki kana ta ajjiye.



        "Æ´an mexico ana can dai,Æ™iri kiri an hana abdul'azeez dai rayuwa cikin ahalinsa,bayan bashi da wadanda suka fisu" saudatun ta fada kamar meyin fada,murmushi fulani aisha tasaki cikin nutsuwa tana aje wayar hannunta,kana ta daga idanun nata ta zubawa saudatu su.



       Ã°Å¸‘‘ *SIRAÆŠIN RAYUWATA*👑



*_wannan littafin na siyarwa ne,kuma amana ne a hannun duk wanda yasiya,idan kina buqatar siyan naki ki tuntubi wadannan lambobin_*


09032345899



25




      Lokacin daya dawo dare yayi,saidai bawani dare can ba,a sannan sha biyu ne harda rabi,da muqullanshi daya saba amfani yabude gidan yabude yashigo,falon tsit babu kowa kamar yadda yakan tarar kullum idan yadawo,kai tsaye ya haura zuwa sama inda dakinshi yake.



       Alwala yasoma yi kamar yadda yasaba zama da alwala akai akai haka ammi takoya mishi tun ba yanzun ba,yakuma saba yatashi da dabi'ar,alqawarin daya yiwa safwa yana cikin ranshi,mutum ne shi mai.matuqar kiyaye alqawari dakuma qoqarin cikashi,don haka yaja laptop dinshi yakunna.



       Kiran safwa yasoma yi,wadda tajima gaban system din nata tana tsammanin kiranshi,harta soma kumbura jin shuru har yanzun bai kira ba,saidai idan ta tuna yana da cika alqawari sai kuma fushin nata ya sassauta,don haka yana kira ta daga.



       Tarwai ta bayyana cikin screen din nashi,ta cika screen din gaba daya,tana kwance rub da ciki saman gadonta,sanye da wata lafiyayyar baqar riga ta wani yadi wadda ta haska fara tas din fatarta,gashinta na reto a kafadarta guda,fuskarta fes da madaidaiciyar kwalliya,labbanta sunata qyallin lipstick ta hasken screen system din.



       Murmushi ta sakar masa tana kashe masa idanu daya,saiya lumshe idon nashi yana jin tsigar jikinsa na tashi,uwa uba yanayin kwanciyar da tayi din batayi masa ba,saboda ana ganin wuyanta zuwa qirjinta sosai,duk da basu bayyana ba gaba dayansu amma kana iya hango tudunsu

"Tashi sosai ki zauna" ya fada qasa qasa yana lashe busassun labbansa,murmushi takuma sakar masa,taji dadi ta sanyashi a yanayi,tana son taga yasauya saboda ita,anata ganin wannan kawai shine xai nuna ma'aunin qaunar da yake mata,hakanan zai bayyana adadin yadda ya matsu su zama mallakin juna kamar yadda itama ta matsu,tunda tasan bazai taba buda baki ya gaya mata yadda take da buqatar ji ba

"Meya faru da kwanciyata kuma?"

"Ki gyara kawai ko nayi cutting up kiran" tasanshi sarai zai aikata,don haka ta miqe zumbur tazauna tana tura baki gaba,saiya saki wani qaramin murmushi wanda iyakacinsa labbansa.



       Bata iya wani dogon fushi da shi,don haka ba bata lokaci tasauko suka soma hirarsu,anan yayi realising lallai safwa batasan da zancan plan da ammi tayi na,saboda kusan rabin hirar tasu tayau tana nuna mishi yadda take bala'in kishinsa,daga qarshe ma ita yabarwa fagen yaxuba mata idanu yana kallon yadda labbanta da sukasha man lebe suke motsi.



       Cikin jikinsa yaji tabbas akwai matsala idan sukaci gaba da zama a haka,don haka ya yanke shawarar samun abun mai zafi da zai rage masa abinda yasoma ji


       Yasake kallon agogon dake aiki qasan system din,dare ya riga da yayi,bai kyautu ya tashi sodangi ba yanzu,don haka ya sanya laptop din a sleep bayan ya nemi uzuri wajen safwa ya dantse kiran,yamiqe ya zura slippers dinshi yasauko qasan.



      Dai dai lokacin da yunwa ta hanata sakat sakamakon qin fitowa da tayi taci abincin dare,har suka gama abinda suke suka tafi suka kwanta.



       Don dole ta tashi da hanzari jin yadda hanjinta ke curewa waje daya,slippers dinta itama kawai ta zura tana tattare hannun rigar baccin jikinta,wadda take riga ce iya cinya mai dogon hannu da wandonta dogo na wani lallausan yadi ruwan hoda,kanta babu dankwali,sai gashinta jelarsa ke reto a bayanta yana kuma qyalli saboda mai da gyara da yasha,ta bude qofar dakin nata a hankali kamar wata barauniya,ta tsaya ta kasa kunne,sai data tabbatar bataji motsin komai ba sannan tasoma takawa a hankali zuwa kitchen din.



      Cikin qaramin plate tazubo abincin kana ta dawo falo,tvn dake aikia falon wadda sun manta basu kashe ta ba taja hankalinta suna nuna wani shirin girke gike,saita tsaya gaban tvn da plate din a hannunta tana yafitar abincin kadan kadan tana ci,idanunta da dukka hankalinta yana kan tvn.



       Taku biyu rak yayi ya hangi mutum gaban tv,abun sai yaso daure mishi kai gamida bashi mamaki,a hankali yake qarewa bayanta kallo,a jikinsa yakejin baquwa ce,don sam batayi yanayi ko zubin rakiya ba bare yace itace,duk da ba wani kallonta yake ba amma yasan ba ita bace

"Wow" bilkisu tadan fada cikin birgewa,saboda abinda cook din ta hada yayi matuqar burgeta yakuma bata sha'awa.



        Sautin muryarta yasake tabbatar masa da zarginsa,saiya ci gaba da saukowa idanunshi a kanta.



       Jin takun saukowa daga step ya sanya gabanta mummunar faduwa,ta soma zazzare idanu,babu abinda yazo ranta illa

"SHINE!" zuciyarta ta gaya mata da qarfi

"Wala'alla ma dakinki zashi" zuciyarta ta sake gaya mata,sakin kwanon hannun nata tayi da hanzari ba tare data shirya ba,a miliyan tayi dakinta kamar zata tashi sama batare datako waiwayo ba bare taga waye,wanda hakan ya baiwa sassan jikinta damar motsawa dakyau,bataci biriki ba sai data tabbatar ta isa dakin,kana ta sanya muqulli tarufe qofartata gam.



      Mamaki ne yasanyashi tsaiwa yana kallonta gamida mamakin wacece wannan?,ganin baida amsa saiya tabe baki gamida dage kafadunsa yawuce zuwa kitchen donyin abinda yafito dashi.



      Koda yakoma dimma hirar kadan suka qara ya bata haquri,ya qarasa shanye coffe dinsa kana yayi shirin kwanciya yakwanta,kafin bacci yadaukeshi yatuna abinda yafaru mintunan da suka wuce,saiya tabe baki gamida jan qaramin tsaki,idan bamai matsalar qwaqwalwa ba wazaiyi haka?,kawai daga jin taku saika yar da kwanon hannunka kahau gudu,sake gyara kwanciyarsa yayi yana jan tsaki gamida rufe idanunsa,ya aje komai gefe yanason bacci ya daukeshi.



      ******    ******   ******   ****



      Kimanin qarfe sha daya ne na safiyar ranar,su ukune zaune a falon nata saman dining suna karyawa,fulani aisha da yaranta uswa da sumaira.



      Diyar uswa ce akan cinyarta tana bata farfesun nama a hankali yayin da suke taba hira wadda ta shafesu,daidai lokacin jakadiya ta qaraso,ta zube tana shaida mata saqon son ganinta da saudat(qanwar maimartaba mahaifiyar kamal) keson yi.



      Kai ta gyada kana ta bada izinin ganinta,ta dauke idanunta ta maida kan yaran nata,sai ta yiwa sumaira inkiya data dauki sahla dake saman cinyarta,ita kuma ta miqe tana goge hannunta da tissue.



     Cikin nutsuwa qasaita take saukowa daga wajen dining din zuwa ainihin falon,tana sane da zuwan saudat din gidan kimanin kwanaki hudu,amma bata nemeta ba kamar yadda ta nemi sauran abokan zamanta.



       Tuntuni tasoma shaqar wani abu dangane kan saudatun,hakanan takejin sam takunta bai mata ba,tun kafin yau dama ba wani alaqa mai kyau bace can can tsakaninta da saudatun tunda aka aurota,hakanan jininsu bai hadu ba,hakan kuma baya rasa nasaba da aurotan da yayi a wata qasa,wanda a lokacin saudat din sam bataso hakan ba,akwai qawarta dataso hadashi da ita kamar kamar me,taji ba dadi sosai,don a sannan ita dayace ta rage mishi qanwa kuma abokiyar shawara,dama duka duka su ukune Allah ya baiwa sarki mu'az,Allah ya yiwa babbar yayarsun rasuwa,tabar yaro daya wanda yake hannun saudat din tana riqo.



       Cikin qasaita shigo shan qamshi da kallon komai É—ai É—ai tashigo falon,don dukka cikin gidan babu sassan da yakai na fulani aisha kyau da tsaruwa da kayan ado na alfarma dake sake nusashe dakai cewa nan fa akeyin sarautar,don ita gada tayi daga fannin mahaifi dakuma miji,sarauta saidai ta nunawa wasu

"Bismillah" ammi tafada tana nuna mata daya daga cikin kujerun cikin nata salon qasaitar da isa,saida saudatun tazauna kana itama tayiwa kanta mazauni kan kujera maicin mutum biyu,kana ta dora qafarta daya saman daya idanunta kan saudat

"Matar dan uwana" ta fada kamar yadda ta saba kiranta dashi

"Maman kamal....yaushe a gari?" Ta fada a dake,saita dan yatsina fuska

"A qalla yau kwanana hudu cikin gidan nan,amma da mamaki idan kikace bakisan da zuwa na ba" hannayenta ta watsa kafin ta hadesu waje guda

"Ba abun mamaki bane,saboda kowanne mutum akwai irinsa,ba kasafai na fiya damuwa ko bibiyar al'amuran dake wakana cikin gida ba,indai lamarin bawai yajibanceni bane" wani duba ta mata tanason fahimtar meta fada din,magana ce cikin magana ko kuma magana tayi kanta tsaye ba tare da kowanne nufi ba?,saita gyada kai sa'an nan tace

"Haka ne" daidai lokacin da sumaira ke saukowa rungume da sahla,kana ta qaraso cikin girmamawa,fuskarta a sake kasancewarta maison jama'a fiye da kowa cikin 'ya'yanta,tazauna saman daya daga cikin kujerar tana gaida saudatu da suke kira da mom,gami da tambayarta 'yan uwanta yaran saudatun wato safna da safina

"Qalau" ta amsa a taqaice,daga bisani uswa ta sauko itama ta gaidata,saidai ita daga gaisuwar bata qara komai akai ba saima qoqarin miqewa da take don barin wajen,kasancewarta gwanar miskilanci ce itama kamar dan uwan nata abdul'azeez,dukka fulani aisha na ankare da yadda take amsa gaisuwar tasu,wanda tasha bamban da yadda take treating su walida qwarai

"Ke zonan,don uwarki me yasa ne baki da hali,kodon kinga mun aurar dake ne yasa kike ganin kanmu daya" ta fada cikin zafi zafi,kamar da biyu take maganar.



      Uswa dake tafiya ta waiwayo kana tace

"Wa wai?,ni?" Wanda ita harga Allah bada wani abu tayi maganar ba,kusan nature dinta kenan

"Ban sani ba" ta amsa mata a gadarance.



      Batace komai ba ta dawo din tasamu waje taxauna,saita soma fada mara dalili,ta inda take hawa bata nan take sauka ba,waita yaye kowa bata neman kowa.



       Dukkan wani takunta da abinda fulani aisha ke nema ya gama bayyana kanshi,don haka saita shareta yadaga waya tasoma amsa kira,bata tsagaita ba har sai data gama taga yaran suna tashi suna wucewa ciki kana ta ajjiye.



        "Æ´an mexico ana can dai,Æ™iri kiri an hana abdul'azeez dai rayuwa cikin ahalinsa,bayan bashi da wadanda suka fisu" saudatun ta fada kamar meyin fada,murmushi fulani aisha tasaki cikin nutsuwa tana aje wayar hannunta,kana ta daga idanun nata ta zubawa saudatu su.



        "Komai na rayuwa ai lokacine,sau da dama wasu abubuwan sukan xama alkhairine a rayuwar dan adam,musamman nisantar wasu gurare da muhallai,karki damu innar abdul'azeez,akwai lokaci" sarai ta fahimci magana take gaya mata cikin magana,saita miqe tana tabe baki tana duban aishan da wani irin kallo

"Ni zan wuce,dama leqowa nayi mu gaisa,tunda ku baku neman kowa" murmushi tayi kamar babu wani cikin maganarta daya bata mata rai,kana ta miqe tana dubanta

"A haba,mukan nemi mutane mana,musamman wadanda mukasan muhimmancinsu me yawa ne cikin rayuwarmu,sa'an nan tarayyarmu dasu tana da wata fa'ida da alfanu,kamar dai ke" tasan gatse tayi mata sarai,takuma fahimci babu wani abun dazai kashe bakin aishan,don haka tayi gaba,zuciyarta cike fal da quluwarta,tare da ninka alwashin qudurinta cikin ranta.



       Murmushi tasake sosai sanda saudatun tafita

"Kainuwa kenan......dashen Allah" tayiwa kanta da kanta kirari,kana takoma tazauna inda tatashi,tana ci gaba da wassafawa da qiyasta yadda abubuwa zasu ci gaba da wakana.



       Rai a bace ta isa sashen adama,wanda har takai dukka barorin daketa faman miqa mata gaisuwa cikin girmamawa babu wanda ta amsawa ko mutum daya.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 27

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_________________________

*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*



*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸™Å½Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯ðŸ½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸‘¯Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*



*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ðŸ¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾





      Kamar yadda tace din babu kowa cikin falon sai mama sodangi itama dake jiran fitowarta,ta gaida maman kamar yadda tasaba duk yammaci sannan tazauna suka fara karatun.



        Sai data soma dajin kataratunsu na jiya sannan tadora musu da wani sabo bayan ta tabbatar sun fahimta wancan kuma yazauna yadda ya kamata.



        Awa guda kacal sukaci a karatun aka bude qofar dakin da bilkisu tasan babu kowa a ciki,hakan yaja hankalinta don dama a tsorace take,ta daga kanta da hanzari tana duban qofar dakin,safwa ce ke fitowa,sanye da wasu riga da wando masu azabar kyau da suka amsheta,saidai sun bayyana duk wata sura ta jikinta,tashin qamshi take sosai,kanta yasha gyara,hakanan a fake yake da ribbom kalar kayanta,hakan yasake qawata kwalliyar tata.



       Ido suka hada da bilkisu,suka kalli juna na wasu sakanni kafin bilkisun ta janye nata idanun,itama safwan ta janye tana qarasowa falon,gami da mamakin wacece wannan maikyau haka?,choculet beauty.



       Saman kansu ta tsaya,alamun sangarta qarara suna bayyana tattare da ita,ta dubi mama sodangi

"Sodangi da Allah inason peppersoup din kifi,Allah yasa kuna da?"

"Eh akwai ranki yadade.....akwai"

"Ohkey" ta fada tana zagayawa saman kujerun  don ta zauna,da alama ta gama bada nata umarnin kenan,da niyyarta ta fada takoma cikin dakin,amma hakanan batasan meye yaja hankalinta ba taji ra'ayin xaman falon,saita zauna daga bayansu tadora qafarta daya saman dsya tana dan latsa wayarta,yayin da wani sashe na hankalinta yake kansu.



      Tunda mama sodangi tabar falon zuwa kitchen don yin aikin safwan sai bilkisu take jinta incompatible,zaman sam bai mata ba,ta dinga tsarguwa tana jin kamar safwa na kallonta ne,uwa uba batasan wacece safwan ba,don haka ba tare da wani dogon sharhi ba ayau ko tambaya suka rufe da addu'a ta tattara tawuce daki.



      Fuska safwa ta yamutse,don me ita ba zata kulata ba kamar kowa?,donme ba zata girmamata ba kamar saura?,wacece ita?,don taga tana da kyau

"Wacece waccan" safwa ta jehowa rakiya tambayar data rudata lokaci guda har tahau inda inda,wanda da safwan ta gogu da rayuwa yaci ta karanci wani abu

"Na.....'am....iyee?" Take gumi ya yanko mata,ta sanyata a tsaka mai wuya,batasan ainihin amsar da zata bata ba,sa'an nan tana ankare da gargadi dakuma jan kunnen mai qarfi da mama sodangi tayi mata koda safwan zata tambayeta wace bilkisu,kuskuren da tayi guda daya shine bata tambayi mama sodangin amsar Da zata baiwa safwa ba a duk lokacin data jefa mata tambayar ba kamar yanxu

"Yar uwata ce,tare mukazo" tasamu kanta da shirya wannan qaryar,baki safwa ta tabe tana kada kai

"Shine take acting kaman wata tsiya,baku shaida mata wacece ni ba?" Kai ta kada da sauri

"Bata sani ba Allah ya taimakeki,kiyi haquri,rashin sanine,tayi kuskure amma zan mata bayani,saidai duk da haka tana da matsala,bata magana mai tsaho,likita ya hanata" ita kanta yadda ta shirgo qaryar tabaiwa kanta da kanta mamaki,amma babu yadda ta iya,don shine kawai mafitar da zata kare kanta da bilkisun ma gaba daya.



        Sai taji zuciyarta kuma tayi sanyi

"Barta kawai tunda lalura gareta,na tsammaci izza ce"

"Ko kadan ranki yadade" tasake fada da sauri,daga haka safwan bata sake cewa komai ba,saita maida kanta ga wayarta,rakiya kuma ta miqe tanufi kitchen tana sharce gumi.



     Zaune yake kawai cikin motar bayan ya fakata daura da wani wajen wasan yara dake kusa da unguwarsu,ya jima zaune a ciki a yadda yake,bawai don yana wani abu ba ko kuma yana da abunda zaiyin ba,hakanan kawai baya son komawa gidan,ya tabbatar da cewa indai baiyi da gaske na safwa zata zo ne ta tafi bayan ta tayar masa da qaton tabon da yaketa qoqarin warkarwa amma abu ya gagara,tunda a halittarsa ne,jininsa ne haka babu yadda ya iya.



      Sam bashi da sha'awar komawa yaci gaba da tu'ammali da magungunan,dalili kenan daya sanya yake gudun duk wani abu da zai sanya ya nemesu.



      Wayarsa dake hannunsa tun dazun tadauki sauti,wanda hakan ke nuna kiranshi ake,da hanzari yaduba,sai yaga ammi ce,don haka yadan kwantar da kujerar da yake zaune akai ya jingina bayansa sannan yadaga

"Barka da warhaka ammi" gyaran murya tayi kadan sannan tace

"Yauwa....barka kadai,ya makaranta?"

"Alhmdlh ammi,ya maimartaba"

"Komai lafiya....azeez nace ba?"

"Na'an ammi"

"Meye dalilin da zaka sauke safwa a gidan da yarinyar nan take?,ina hankalinka yatafi?,ko so kake ka jawo mana matsala ehen?" Cikin kwantar da murya da girmamawa yace

"Babu komai ammi,babu abinda zai faru" shuru tadanyi na wasu sakanni sannan tace

"Ka tabbatar da abinda ka fada,idan ba haka ba..."

"Please ammi karki damu,ba abinda zai faru....in sha Allahu"

"Ina saka ran haka". Daga nan suka aje wannan maganar suka shiga wata kuma daban.



       Shiga nan fita can,bashi ya isa gida ba saida dare yashiga yasoma danyin nisa,duk da daya batayi ba,yabude motar bayan ya fakata yakashe,yakulle sannan yanufi cikin gidan.



       Bai tsammaci zai taddata a falon ba,saiya sameta zaune tana kallon tv,hannunta riqe da cup na lemo.lokaci lokaci tana kurba,duk tayi hakanne don kada bacci ya dauketa ba tare daya dawo ba bata sani ba.



      Kai ta daga suka hada idanu,sosai ta bata rai,don bataji dadi ba,wuni taso suyi tare ta morewa zuwanta,amma ta lura kaman yana avoiding dinta ne,baison zamansu inuwa daya,bayan duka don shi tazo din.



       Ya lura taji babu dadi sosai,don haka ya sakar mata murmushi wanda ya wanke dukkan wani bacin ranta tashun farko,saita saki ajiyar zuciya kawai tana lumshe idonta,lokaci guda kuma ta budesu akanshi,take tahau shagwabar tata data saba,yasamu daya daga cikin kujerun yadan dosana kamar yadda yasaba zama a falon,bai wani fiya zama harya sake koya dauki dogon lokaci ba.



     Dole wannan karon yadan zauna da ita,yabiye mata,yadan jima duk asonshi na yaja ra'ayinta karta bishi samanshi,saidai ina sam bata yarda ba,cewa tayi saita rakashi tazauna tayi gadinsa har yayi bacci sannan tasauko,a yadda yasan sangartar safwa,yasan bataqi ya matsa mata ma gefan gadonsa ta kwanta ba,zatace tunda su sunsan babu wani abu tsakaninsu to ina ruwansu da wani,yadan dafe goshinsa da hannunsa yana ayyana yadda zaiyi da ita,saidai kafin ma yagama tunanin ita harta aje cup din hannunta tadauki key din daya shigo dashi da wayarsa tasoma haurawa saman,saiya bita da kallo kawai,babu yadda zaiyi da ita,iyaka idan sunje ya lallaba tasauko,don haka yamiqe yabi bayanta.



       Dai dai lokacin da mama sodangi ke fitowa daga dakinsu,tunda taha safwa batayi bacci ba hakanan itama saita kasa,yanzun kuwa data ga tayi saman azeez din duka sai taji ranta a jagule,bata shakkar azeez amma tana sane da abinda yake damunshi,kuma babu wanda yafi qarfin shaidan sai wanda Allah ya kare,ita sam wannan ziyarar ta safwa batayi mata ma'ana ba,tayi mamakin duk tsantsenin fulani da kularta akan azeez data bari safwa tazo,kodon tana ganinta a tsakaninsu?,gaba daya saita kasa nutsuwa takoma tazauna tana kasa kunne taji saukowar safwan.



       Ko a jikinta haka ta baje saman gadonshi tana masa hira,kamar yadda suka saba ba komai yake iya bude baki ya bata amsa ba,a hakanma yana qoqartawa duk don kada taga ya wulaqantata,haka yashiga wanka da kayan jikinsa yashirya a ciki sannan yafito.



       Idanu tasa tana qare masa kallo,yadda kayan suka bala'in masa kyau,quruciyarsa qarara tasake bayyana,hakanan wannan sihirtaccen kyan nasa mai kashe gangar jiki da zuciya,shima kallonta yake hannayensa harde a qirji,yadda suka zubawa juna idanu yasa yasoma jin wasu abubuwa na yawo cikin jikinsa,yayi nisa wajen qoqarin yaqar abunda yake ji din,bai ankara ba yajita cikin jikinsa ta rungumeshi tana sakin qaqqarfar ajiyar zuciya,take qamshinta yasoma shiga hancinsa,gashinta dake fake yasoma gugar fuskarsa,tsigar jikinsa ta zuba,ya janyeta da sauri daga jikinsa,idanunsa na nuna zallar bacin rai

" meye haka safwa?"ya fada a kausashe,saita sake zuba masa idanu kafin daga bisani qwalla tacika idanunta,tajuya masa baya da sauri ganin suna niyyar gangarowa

"Saboda na rungumeka yarima shine kakemin tsawa haka?" Ta fada muryarta tana rawa,sai yayi qoqarin cooling kanshi,yasani wala'alla shine mutum na farko daya soma.mata tsawa a rayuwa,tunda yasan sarai irin gata da shagwabar da take gaban iyayenta

"Babu komai nagode,nina kawo kaina,ko kuma nace soyayyar da nake maka ta janyomin" saita soma takawa zata fita daga dakin,don harga Allah taji haushi sosai,a wajenta runguma ba komai bace,don hatta da mahaifinta takan iya rungumeshi,a wajenta da waccar da wannan duka daya ne,sannan idan kanason mutum ba komai bane hakan,tunda ba wani abu ka aikata da zai nuna a jikinka ba.



       Karon farko daya kama tsintsiyar hannunta,wanda sai dayaji sosai ajikinsa,dukkan gabbansa suka amsa,ita kuma abinda ya sanyayar da ita kenan,saboda makamancin hakan bata taba faruwa ba a tsakaninsu.



       Saman kujerar dake dakin ya ajeta,kana yazauna sosai a gabanta yana duban fuskarta

"Duba da girmanki kike wani kuka?,kin manta shekara biyu kawai.na baki zaki zauna gabana kina kuka?,oya share hawayen" murmushi ya kubce mata,saita sanya bayan hannunta tana goge qwallar data soma zubo mata,sai data gama tsaf sannan yace

"Akwai abubuwan da mu a idanunmu zamu dinga kallonsu ba komai bane,saida a addininmu haramunne kuma dole kowanne baligi da baliga su gujeshi,kamar yanzun,kebancewar da mukayi kadai ni dake musulunci ya hanata,kinsan dalili?"saita girgaza kai

"Saboda indai mace da namiji suka hadu a wani kebantaccen waje wanda daga shi sai ita,to ba shakka shaidanne na ukunsu matuqar ba ma'aurata bane su,i did'nt mean anything,nasan xakita tunanin abubuwa kala kala,to duka ba wannan bane....yanxu kinga dare yayi,bai kamata ace muna nan zaune a tare nida ke kadai ba,kije dakinki ki kwanta,i promise gobe xamu wuni tare" kalamansa sun wanke duk wani fushi da bacin ranta gaba daya,ba lafuzzan bakinsa ba,hatta da sound din azeez din mai taushine da wanke zuciya,ta jima bai zauna haka ya jera mata kalamai masu nuna kulawa da lallabawa haka ba,saboda tsabar miskilanci da jinin sarauta dake yawo a jininsa,shi yasa yau take jinta a duniyar sama tana yawo.



       Salin alin ya rakata har qofar dakinta tashige,sai da yaga ta shiga sannan ya saki ajiyar zuciya,dai dai lokacin da mama sodangi itama ta maida qofarta tarufe tana sakin ajiyar zuciyar itama,ba shakka akwai matsala kuma za'a samu damuwa ita tasani,jikinta yana bata mawuyacine idan ba lokacin karbar qaddarar bilkisu bane nabiyu ya durfafota,kafin ta kwanta ta yankewa kanta shawara,shawarar da take fatan xata canza komai,ciki harda tunanin bilkisu dakuma rayuwar azeez gaba daya.


*******    *******    *******


      Washegari hakanan babu yadda ya iya ya kashewa safwa lokacinsa gaba daya,wuni gida sur,daga nan zuwa can,wuni yayi mata dadi qwarai fiye da dukkan wasu wuninnika na rayuwarta,tayi yadda takeso takasance da azeez din son ranta,wanda tsahon tarihin soyayyarsu basu taba kashe awanni haka masu yawa tare ba.



       Saidai duk da hudubar da yayi mata daren jiya hakan bai sanya ta fasa tabashi ba,musamman idan taga wani abu daya burgeta ko yayi mata,hakan yasake takurashi da matsa mishi,ya fuskanci kusam dabi'arta ce haka,ta saba har batasan sanda takeyi ba,haka yadinga qoqarin kakkauce mata har zuwa sanda suka dawo gida.



      A ranar kam yayi kwanan wahala qwarai,yasan kuma dalilin tashin ciwon nasa bai rasa nasaba da safwa din,shi yasa washegari da take shirin komawarta hakan ya masa dadi,duk da cewa bai nuna ba.



      Tun safe take ziryar samanshi amma saita tadda qofar a rufe,tayi kiran wayoyinshi dukka a kashe,yana dakin kuma duk knocking din da takeyi yana jinta,yana sane yayi hakan,don baiso tashigo ta qarawa wuta fetur.



      Data gaji take tambayar mama sodangi

"Ina tsammanin yafita ne,qila akwai wani uzuri daya fiddashi" wannan amsar da bilkisu taji ta bata ya sanyata jan tsaki,tana ziro qafafunta qasa da niyyar fitowa daga qunshen data yiwa kanta,cikin zuciyarta tana cewa

"Ashe bainan,inataso nafita amma nake zaune".



      Riga ne a jikinta shirt mai gajeran hannu sosai,wanda hakan ya bayyana santala santalan hannayenta,iyakar rigar qugunta,sai wando high waisted wide leg daya dace sosai da rigar,baqar doguwar riga ta dora akai mai sulbi saqar wasar oman,tayi rolling da mayafin rigar,sai tayi wani kyau,kai kace baqar balarabiya ce.



      Dai dai lokacin tasan dukka suna kitchen,don kusan dama da ita ake girkin,tasan lokacin kowanne abu,don haka can ta nufa kai tsaye.



       Gab da zasu shiga sukayi kacibus da safwa tana fitowa,hannunta riqe da cup data cikoshi da fresh milk,bayan ta gama zirga zirgar neman azeez din.



      Kallon juna sukayi,bilkisu ta rabata tawuce,yayin da safwa din ta bita da kallo harta shige,kana ta qarasa ficewa daga kitchen din,zuciyarta na raya mata bilkisun sam batayi kama da hadimai ba,batasan me yasa yarinyar ke tsaye mata ba,take kuma cika mata idanu.



     "La la la,mama kika ce tare zamuyi,badon na shigo ba saidai acemin an gama?" Tafada tana duban qullin alkubus da mama sodangi ke bugawa zata turara

"Aina dauka yau hutun uwar dakin nawa ne yamotsa,tuba nake" murmushi tayi kawai tana hayewa saman wata kujera mai dogon mariqi tana duban rakiya dake qoqarin hada miyar alkubus din,mamakin inda suka samu kayayyakinmu na nigeria takeyi,saidai bata tambaya ba,don ba mutum ce ita mai bin qwaqwqwafi ba

"Ba amana" ta fada a taqaice tana jifan rakiya da hararar wasa,dariya tadan saki kana tace

"To ya zamuyi?,tunda so kike ki sake zama ta É—aka ta É—aka"

"Kul" mama sodangi tayi saurin kwabar rakiyar,sai ta sadda kai

"Afwa mama". Murmushi kawai bilkisun tayi,wani lokaci maman tana bata dariya,ita har yau wani girma take bata,bayan itadin bamai girma ko qima bace,saita sauko ta cire after dress din nata tana amsat bugun daga hannun maman

"So nake nakoya sosai,shi kadaine yafi wahalar dani a girki".



       Suna tsaka da aikin safwa tasake shigowa zata aje cup din hannunta,hakanan idanunta suka dinga yawo kan bilkisu,saboda yadda dirinta da shape dinta suka bala'in fitowa ba,ba namiji ba ko.mace ta kalleta ba shakka zatasan cewa ba qaramin ajiya Allah yayi a wajen ba,sai a sannan tasake yarda,bawai tsaho kawai sirantaka ko farar fata ce zallar kyau ba,tunda ga choculet colour skin mai matsaikacin tsaho dauke da qirar data bata mamaki,bata mantawa kwanaki saida ta dinga amfani da supplement don ta fidda qirarta sosai kawai donta burge azeez dinta,tabi sassalkan gashinta da kallo,wanda bugun fulawar da take yahadu da santsin gashin yasanya daurin dankwalinta warewa,gashin duka ya bayyana.



       Cikin sakan qasa da talatin sassanyan qamshinsa ya baibaye ilahirin kitchen din,kafin daga bisani lallausar muryarsa mai cike da kwarjini dakuma izza tabiyo baya da kyawawan lafuzza na sallama.



     Dukkansu suka juya,banda bilkisu wadda cikin sakanni da basu wuce uku gudun zuciyarta ya ninku,kowacce gaba ta jikinta tadauki rawa,zuciyarta kuma take yanke ta gaya mata waye,sai taji kamar an kafeta,ko wuyanta ba zata iya motsawa ba bare ga juya,dana sani da nadamar abinda yafito da ita daga daki suka baibayeta,tanajin yadda mama sodangi da rakiya suke gaidashi cike da tsa tsar girmamawa yana amsawa cikin ginshira da isa ta sarakai.



       Sam bai kula da mutum ba bayan wadanda sukayi magana dashi,har sai da safwa dake tsaye a bayanta tayi magana cikin shagwaba

"Hey dear....karkacemin kana cikim gidan nan?" A hankali yadauke idanunshi daga kanta,duk dabaisan wacece ba amma zuciyarsa ta gaya masa yarinyar rannan ce,abu guda daya tak dabai manta ba tsaho da sulbin gashinta da idanu sukan iya gani koda bilkisun na nesa dakai,wani abu yakeji yana tsirga masa,dalili kenan daya sanya ko cikakken kallo bai yiwa mace sai idan ta kama dolen dole

"Hey...." Ya amsa mata kwai a taqaice,yana sake qoqarin lanqwasa kansa da yiwa idanunshi shamaki wajen maida dubanshi ga halittar dake tsaye,ganin kamar yana gab da gaza hana idanunshi saiya juya zai fice,safwa ta rufa mishi baya,yayin da mama sodangi ke tambayarshi idan yana da buqatar wani abun yafadi akawo masa

"Ba abinda nake buqata" ya amsa mata ataqaice yana ficewa.



       "Yarima yarima kenan

"Wai nikam mama,dama can haka yake,bayacin abincine waishi" dan dariya mama sodangi tayi

"Kin taba ganin mutumin da baya cin abinci?kawai dai mutum ne shi mai qa'ida tun yana yaro,hakanan yana da tsantsami,abu qalilan zai gani ya fasa cin abinci ,yana da tsari dakuma kalar abincin da yakeso,baya son qazanta ko kadan,shi yasa zakiga kamar baicin abinci,yana da zabi,ba kowanne yake ci ba"dukkaninsu babu wanda yalura da yanayin da bilkisu ke ciki ba.



     Hannayenta ta zare daga cikin flour sannan ta yayibi after dinta da dankwalinta,tanason fita tana kuma tsoron kada ta samesu a falo,idanunta ta runtse kana ta saka kai,saidai cikin sa'a babu kowa a falon,hakan shi ya bata damar wucewa da sassarfa zuwa dakinta.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 28

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_________________________

*_INA KUKE MATA MASU AJI,MATAN DA SUKE DA BUQAYAT GYARAN JIKINSU DA INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BASA CUTAR DA JIKI KO LAFIYA_*



*KINA DA LABARIN ZEE HERBALS APHORODISIAC?*


*wadda ta tanadar muku ingantattun supplenmt masu maida tsohuwa yarinya*


*magungunan da suke gyaran jikin diya mace su maisheki wata ta daban cikin mata*💆ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸™Å½Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*magungunan da xasu sanyaki qyalli da sheqi,su ciko miki gami da tada duk wata komaÉ—a ta jikinki ki ganki dai dai da zamani*👯ðŸ½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸‘¯Ã°Å¸½Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


*karki xama 'yar kallo,kuma karki bari ayi babu ke*

*garzaya maza ki nemesu a shafinsu na INSTAGRAM http://www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac*


*ko kai tsaye ta WATSAPP https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz*


*_KO KI KIRASU KAI TSAYE BABU WANI JIRA TA WANNAN LAMBAR WAYAR 08169380189_*



*_ZEE HERBALS APHRODISIAC A INGANCI BASU DANA BIYU_*ðŸ¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾Ã°Å¸¤Å¾Ã°Å¸¾






         Siyayya sosai azeez din yayiwa safwa,bawai don bata dashi ko tana buqata ba,a'ah,sai don kyautatawa dakuma amminsa daya tabbatar da cewa zataji dadin hakan,don ya fuskanci a rayuwa tana matuqar qaunar tarayyarsu da safwa din.



       Shi da kanshi ya kaita airphort bayan ya siya mata ticket,sukayi sallama,sai a sannan hankalinsa yakwanta,saidai ta tafi ta barshi da tarin ciwukan da baisan lokacin warkewarsu ba.


*******    ******   ********



     Karo na uku kenan data kawo mata wani abu cikin cup tace ta shanye,kuma wai ita kadai,don bata bari ko a gaban idon rakiya tabata,akwai yarda da aminci tsakaninsu,don haka babu wani zato ko kokwanto,barema dukkan abinda take batan akwai dandanon madara sosai da garÉ—in wasu abubuwa da batasan meye ba.



       Tana tsaye saman kanta tana dubanta,har ga Allah tanayine saboda taimakon bilkisun,tana kuma yine cike da fata da kuma saka ran kome zaya faru bilkisun taci gaba da zama a matsayin da take dashi yanzu,wannan shine babban fata da burinta na komai ya canza.



      Jikinta yana bata komai yana iya faruwa sa bilkisun cikin kwanakin,hakan yasanya hatta da ruwan wanka sabulu da turare nata na dabanne,wanda hakan yasake tsumata da sauya mata fata da odour na jikinta zuwa wani yanayi na musamman,duk da batasan manufar mama sodangin ba,amma canje canjen data qara gani akan nada yabata mamaki,saidai batayi magana ba,tayi shuru tana kallo.



        Sai data shanye sannan mama sodangin tazauna a gefanta tana dubanta,cikin tausasawa tace da ita

"Ina fatan baki manta matsayinki cikin gidan nan ba,dakuma abinda yayi silar barowarki qasarki" wani mummunan faduwa gabanta yayi,kana ta daga kai tayi ta dubi mama sodangi cikin mamakin jin furucinta,ta tuna mata da wani babban abu da ita ta manta dashi ko tace ta shagala,wanda tasan yin hakan tamkar yaudarar ce tayiwa kanta,saita gyada mata kai a sanyaye

"Kome zaya faru bilkisu ki tareshi da kyakkyawan fatan zai sauya dukkan zuciyoyi da tunani zuwa bigiren alkhairi a taki rayuwar,kiyi haquri da dukkan.abinda ka iya faruwa,kome zanyi zanyine dominki bilkisu,zanyine don hakan yazama sila na wanzuwar abinda ba'a taba kawoshi cikin tsari da tunani ba" saita miqe ba tare data iya kallon idanuwan bilkisun ba,itama saita bita da kallo harta fice,bata iya gane komai cikin kalamanta ba,bata sani ba ko qwaqwalwarta ce tayi qanqanta da kalaman sun mata girman da bazata iya fasasu ba,daga bisani data gaji da qoqarin fassara komai saita watsar tashiga sabgarta.



        Cikin kwana daya tal mama sodangin tasauya mata dukka kayan baccinta da nau'in wasu kaloli masu kyau tsada da daukan hankali,duk da basuyi mata ba ita a yadda takeso amma haka ta haqura,saboda tunawa kanta da tayi wacece ita?,karta zarme da yawa,itadin tamkar aikin kwangila ne ya kawota gidan,so zabe ko nuna ra'ayi duka ba nata bane.



      Abu na biyu data lura dashi shine yadda mama sodangi ta maida musu lokuttan kwanciyarsu daga qarfe takwas na dare,sabanin da dasai tatafi daki ta kwanta ma tabarsu,musamman alokuttan datasan cewa yarima yana iya shigowa,shima duka bata damu ba,idan ta koma dakin taji batajin bacci sai ta dauki wayarta ta rage dare da ita har zuwa sanda zataji bacci,kusan kwanaki uku kenan hakan ma faruwa kafin mai afkuwa ta afku,mai afkuwar data sanya ta gane dalilin samun dukkan sauye sauyen data gani.




          *12:30 am*



       Tun sanda tabar falon takoma dakinsu take kwance tana juyi daga farkon gadon zuwa qarshensa da wayarta a hannu tana browsing abubuwan da tasan zasu amfaneta,tun tanayi cikin marmari harta gaji bayanta ya qage,don haka ta aje wayar ta sauka daga gadon,mintuna wajen biyar takashe tsaye gaban ma'ajiyar kayanta dake lafke da kaya,wanda ita kanta batasan sanda ta tarasu ba,dukka mallakinta ne,hakanan lokaci lokaci takanji mama sodangi na waya da wata mace da take kira da fulani,wadda har yanzu batasan matsayin matar ba,duk da tajima tanajin sunanta bakin umma luba kafin mama sodangin,saidai tafi zargin ita ta asassasa dukkan wani abu dake gudana a yanzu cikin rayuwarta.



       Takanji tana tambayarta me suke da buqata?,yaya zamansu yake,takanji ta aiko mata da kudi tace ayi siyayya,sukan aje mata sabulai mayuka suturu da taruruka masu dan karen tsada kyau da gyara jiki duk bayan wasu lokutta,saidai bata sani ba,ita fulanin ce ke bada umarnin ko a'ah,amma tafi tunanin ita dince,tunda sauyin bai faruwa yawancin lokaci sai bayan mama sodangi tayi waya da ita.



      Bakinta ta tabe,ita sam a rayuwarta a baya bata san wani sanya kayan bacci ba,sai gashi lokaci daya an mata sabo dasu,hakanan ta zari daya daga cikinsu da takejin tafi kwanta mata,mai wani irin taushi da sulbi,ta cire kayan jikinta sannan ta sanyata,ta daure madaurin dake jikinta kana ta daga kai tana duban agogo.



       Idanu ta zaro tana mamakin lokuttan data bata har haka akan waya,bacci takeson tayi amma qishirwa takeji sosai data sanya maqogaranta bushewa,dole tana da buqatar ruwa,don haka ta zura slipper mahadin kayan data gani a jiki,tabude qofar dakin a hankali ta durfafi kitchen,don tasan a canne kawai zata samu ruwa mai irin sanyin da takeso.




        Zaune yake a daya daga cikin corner din kitchen din,idanunsa aruntse,hannunsa daya riqe da cup na ruwa,yayin da dayan yafin hannunsa ya runtse qwayoyin yana tantama da tunanin yiwuwar shansu ko a'ah,yayima kanshi alqawarin yadaina sha tun a wancan lokacin,to amma yanayin daya samu kan nashi a yanzun bashi da wani solution idan ba shan zaiyi ba,hakanan rashin shan nasa baisan wanne irin sakamako zai haifar masa ba,wala'alla sai yafi nashan tablet din muni.



       Takun daya soma ji yasanyashi bude idanunsa da suka kada suka canza launi zuwa bakin qofar,karon farko da yaga fuskarta sosai fiye da gani guda biyun da yayi mata a baya,a hankali take takawa zuwa inda fridge din yake,alamu sun nuna kamar tana tsoron wani abu ne,wala'alla daren daya soma yine,ci gaba yayi da qare mata kallo har zuwa sanda ta dauki ruwan taci gaba da takawa cikin sanda wanda tafi kama da yanga tabar kitchen din ba tare data lura da wanzuwarsa a wajen ba.



      Sosai yasake rintse idanunsa kamar zai shigar dasu ciki,wani abu yana yawo sosai a jikinsa,ganin da yayi mata tamkar wani fami yasake zame masa,saiya kasa ci gaba da riqe kofin hannunsa,ya ajeshi gefansa hannunsa na rawa.



       Ya kusa mintuna biyar kana yamiqe yana qoqarin daidaita kanshi yafice daga kitchen din,sanda ya iske falo saiya kasa ci gaba da tafiya zuwa samanshi

"Halal dinka ce,halal dinka ce" yaji wani sashe daga qwaqwalwarsa yana gaya masa tamkar wanda akewa magana atsakiyar kanshi.



      Tabbas bashi da wata mafita,yakai irin stage din da idan ba allura zaiwa kanshi ba zaiyi wuya ya iya controlling kansa,ya riga da ya yiwa ammi alqawarin barin allurar dama magani gaba daya,kamar wanda mayen qarfe yake ja haka yadinga jinsa kamar ana fusgarsa zuwa cikin dakin,sannu a hankali har ya isa bakin qofar,yasa hannunshi saman handle din yamurza tabude ya sanya kanshi ciki.



       Dai dai sanda qofar tabude bilkisu dake kwance tsakiyar gadonta tana sauraren bacci ya sureta tabude dukkanin idanunta cikin sauri da wata irin matsananciyar faduwar gaba,saidai bata iya ganin komai ba sakamakon duhun dake mamaye a dakin,wanda tuni dama takashe duk wata fitila ta dakin don tagama shirin baccinta.



      "Waw.....waye?" Ta tambaya cikin tsananin tsoro,bai amsa mata ba yaci gaba da nufar direction din da yasan zai kaishi zuwa inda fitilar gefan gadon take,a nutse yadora hannunshi ya kunnata,wani qaramin haske da baikai yakawo ba ya bayyana,hasken da bai iya nuna maka zahirin fuskar wanda kuke magana dashi.



        "Way....waye?" Ta sake tambaya cikin kakkarwar murya karo na biyu

"Abdul'azee" ya bata amsa da wata iriyar gajiyayyar murya,abdul'azeez?,tasake furta sunan can qasan zuciyarta,sunan data jima da haddaceshi qyam a qwaqwalwarta,sautin muryarsa da qamshin turarensa suka qarasa bayyana mata wayeshi,gaba daya jikinta yasaki yamutu,ya lumshe idanunta tanaji a jikinta koma meye a yau komai ya qare yazo qarshe,damar da take tunanin ta samu ko zata samu ta qare mata,tasan qaryarta,bata da bakin wata magana ko yunquri,anzo wajen da zatayi bautar da take tunanin ita aka kawota tayi,wasu zafafan hawaye suka biyo kuncinta,ta cure waje daya tana jin kaduwa da tsoro har cikin hanjinta,tanajin kamar ana mata bushara da cewar mala'ikan mutuwa ke isowa gareta.



       Ba zata iya cewa ga yadda akayi ya kawo kanshi gareta ba,kamar yadda ba zata iya adar da yadda komai yasoma wakana ba saboda tsantsar tashin hankalin data shiga,yau cikin wata qasa cikin wani dare a cikin wani irin yanayi zata rasa 'yancinta da alfaharinta na diya mace,wanda tasan dama kamar an riga da anyi cinikinsa tun ba yau ba an biya iyayenta.



       Abu uku xuwa hudu kawai zata iya tunawa,yanayin qamshinsa,addu'ar dataji yanayi tun afarko,muryarsa da bata tantance me yake fada ba,da kuma 'yar banzar azabar data ci,wanda shine abu na qarshe da bata sake sanin meke faruwa da ita ba harsai bayan wasu awanni data farka,ta fuskanci azabar data sha da kuma zallar tsoro da baqinciki suka hadu suka sumar da ita.



       Lokacin data farka ta fuskanci akwai mutum kusa da ita,ta qanqanuwar fitilar gefan gadon take iya hango inuwarshi,saidai bata iya ganin fuskarshu,xaune daura da ita,da 'yar qaramar tazara a tsakaninsu,da alamu babu wani bacci daya iya daukanshi,idanunta ta maida ta rufe,saita fashe da kuka,kukan daya sanya abdul'azeez ya fahimci cewa ta farka bayan dukka taimakon gaggawar daya bata

"Am really sorry" ya furta a hankali yana jin zuciyarsa sam babu dadi,taji sarai abinda yafurta din da qaramar murya can qasa,tana jin sanda tamiqe ya soma takawa sannu a hankali yafice daga dakin ba tare da ya waiwayo ba.



      Bai rufa minti biyar da fitar ba taji an kuma turo qofar,kana aka kunna makunni qwan dakin,haske ya mamayeshi,ta tsammaci shine don haka bata bude idanunta ba,hakanan bata fasa kukan da take ba

"Bilkisu" aka kira sunanta,a sannan ta fuskanci mama sodangi ce,saita bude idanun nata da suka kumbura suka mata nauyi ta dubi maman,fuskarta sam babu wata walwala ko digon fara'a,tasoma takowa inda bilkisun ke kwance,ita kuma tasake maida idanun nata tarufe,takuma dora kukanta daga inda ta tsaya.



      Mama sodangin kusan ita ta gyarata tayi mata komai kana ta kakkabe mata dakin tacire zanin gadon ta sauya wani,ta barta tana sallah daga xaune itakuma tasake ficewa,daga yanayin yadda take aikin xaka tabbatar jikinta itama a mugun sanyaye yake,ga bilkisu kuwa hawaye sunqi barin idanuwanta,tana daga xaune take sallar don ba xata iya tsaiwa ba,koda ta idarma saita hada kanta da gwiwa tana kuma sakin wani tsumammen kukan,dukkan abinda yafaru da ita a daren jiyan yadinga tariyar kansa da kansa a kwanyarta.



       Shi kadai yadinga sakin ajiyar zuciya qasan shower din idanunsa a rufe lokacin da ruwan ke sauka yana ratsa kowanne sashe na jikinsa,yana tuna dukkan abinda yafarun,wanda yake jinsa tamkar a mafarki,kamar ba shine abdul'azeez ba,yana feeling guilty ta wani sashe na zuciyarsa,yayin da wani sashen kuma yakejin he is innocence,matarsa ce,abinda yayin akwai tarin bambanci tsakaninsa da wanda shedan yakeso yayi,koma meye dai aure aurene,kuma matarsa ce,duk da har yanzu gulitiness din da yakeji a zuciyarsa yana nan,amma yanajin wani yanayi na daban a gangar jikin nasa da zuciyarsa gaba daya,duk wani nauyi daya dade saman zuciyarsa da gabbansa yanajin babu shi,yanajin kansa fresh,tamkar ranar amminsa ta haifeshi,yayin da wani irin happiness ke kutso yanayin da yake ji yana ratsashi,kallo daya zakawa fuskarsa ka karanci hakan,duk da cewa baisan hakan yana bayyana ba,da ire iren wadan nan tunane tunanen ya kammala tsarkake jikinsa sa'annan yayi wanka yafito.



       Mama sodangin ce tasake shigowa dakin karo na biyu,dauke da kofi me cike da kakkauran tea sai zuba qamshin ganyan shayin ahmad tea yake,yana fidda turari,tayi sallama duk da bilkisu bata amsa ba,tasamu gefanta tazauna tana riqe da kofin,saita ajeshi gabanta sannan tace

"Ki daure ki saka wani abu cikin cikinki,likita nakan hanya,zata dubaki" ko motsawa bata iyayi ba bare ta daga kanta,lallashin duniya mama sodangi tayi mata amma bata iya motsi ba,ta sani koda ta kurba abune mawuyaci ya iya wucewa maqogoranta,a haka sukaci gaba da zama har sanda rakiya taturo qofar dakin ta shaida mata zuwan likita.



      Dr huda,matashiyar likita,wadda qalla ta doshi shekara ashirin da bakwai,mutum mai haba haba da son jama'a,uwa uba fara'a,kusan ita ta hilaci bilkisu tasha shayin dakyau kafin tafara dubata,tanayi tana tsokanarta,saidai hakan bai rage komai cikin abinda take ji a zuciyarta ba,daga qarshe saita lumshe idanunta kawai tadaina ganin kowa saijin zantukansu.



      Tayi mata dukkan abinda yadace,ta dubata dakyau ta bata magunguna,takuma fadiwa mama sodangi yadda zata mata treating wajen tawarke da wuri,baqinciki da kunya suka cikata,yanzu kowa ma sai yasan abinda yayi mata?,daga bisani tasa mama sodangi ta bata waje tace zasuyi magana da bilkisu

"Yi haquri ki bude idon ki kalleni" kasa yin yadda tace tayin tayi,saita zauna dab da ita ta kamo hannayenta

"Don Allah badon ni ba" dole ta budesu tana duban dr huda,saita sakar mata murmushi

"Hala kinwa ango gaddama ko?...." Bata da amsar bata illa shuru,saita sake murmushi tana dubanta

"Ba'a haka qanwata.....miji irin azeez kike jawa aji?" Da kallo dai tasake dubanta tana kuma sauraren maganganunta harta gama,ta dora da bata shawarwari,wadanda su da babu duka dayane a wajenta.



      Saidai yadda ta jata a jiki da yadda tasan aikinta ya burge bilkisu,har taji tadan burgeta,taji inama ace itace dr huda,inama ace itace tasamu cikakkiyar damar kammala karatunta,tana sha'awar ta zama wata,saidai almakashin qaddara yasa kaifinsa yana daddatsa rayuwarta in to pieces,wannan abun daya faru yasanya take dukkan wata dama tata a rayuwa ta qare,duk wani buri nata ya rushe,babu wani sauran abinda yarage mata kuma.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 30

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070






       Tun daga ranar da abun yafaru tasake zama so silent,takoma dabi'arta tada koma fiye da da,yawan shuru shuru,zaman kadaici dakuma tunane tunane,ta sanyawa daren suna da baqin dare a wajenta,duk da cewa mama sodangi na iyakar qoqarinta na ganin ta daidaita lamuranta,abinda bilkisu ta lura dashi shine,maman tasanya wani distance na daban tsakaninta da rukiya,bata fiya barinsu xama tare ba,hakanan rakiyan ta sauya mu'amalarta da ita,wani girma take bata kamar yadda suke a baya,kwatankwacin kuyanga da uwar gijiyarta.



       Sai yanzu take ganin wautar data tafka da har tasaki jiki,ta manta silar zuwanta mexico,ta manta abinda ya kawota,takuma manta wacece ita,sa'an nan ta manta dukkan qalubalen da takan iya fuskanta har sai daya zo ya cimmata.



       Duk yadda mama sodangi taso.dai daita komai abun yaci tura,abun yana damunta yana kuma taba ranta sosai,bata gane ba qaramin sabo sukayi da bilkisun ba har sai data maida kanta wannan yanayin nata na baya sa'an nan tagane sun shaqu da juna,ganin tana neman illata kanta yasanya tazauna da ita,maganganun da tayiwa bikisun suka sauketa daga matakin da take kai daga kaso cikin kaso dari zuwa suka kwashe kaso saba'in suka barta da talatin,sannu a hankali lokaci dakuma juyawar zamani tsawaitarsa da abubuwan da yakanzo dasu ya sanya ta kuma saki kamar baya,saidai duk da haka bata bar É—ari É—ari tsoro dakuma fargaba ba,duk da cewa daga baya itama ta ragu,saboda rashin jin duriya motsi ko sautin muryarshi tun daga ranar da abun yafaru.



 *_BAYAN WANI LOKACI_*




        Nannauyar ajiyar zuciya yasaki bayan shigowarsa dakin nasa wanda a baya yake zaune a ciki kafin ammin tasa tayi masa sauyin gida tare dasu mama sodangi,tafin hannunshi ya sanya yana murza fuskarshi gamida fuskar da iska daga bakinsa,tsabar gajiya ce ta taru tayi masa yawa,uwa uba kuma da yanayin da yake ciki wanda yana tsammanin wanzuwar al'amarin zai kawo qarshen duk wani abu dake damunsa,saidai ga mamakinsa ko sau daya lamarin yaqi barin kwanyarsa ta huta,tamkar wani famine yayiwa ciwonsa,kullum kwanan duniya rana bata taba fitowa ta fadi na tare daya tuna da daren ba,daren dako yaqi ko yaso dole ya sanyashi cikin jerin dararen da zai dinga tunawa tsahon rayuwarsa,saidai baisan a wnne bigire zai saka shi ba?,na farinciki ko na baqinciki ne?,har yanzu ya kasa tantancewa.



      Abinda kawai zai iya tunawa shine,zuciyarsa ta kasu gida biyu,yana da tabbacin cewa a ranar yasamu sauqi daga nauyin zuciya,yasamu wani irin inner peace da baisan akwaishi ba a duniya,yaji kansa tamkar jaririn da aka.haifa yau,yayin da wani sashen na zuciyarsa yake iya tuna mishi sautin kukanta,muruyart da taketa magana wdda bai fuskantar me take cewa,amma yana da tabbacin bazai wuce roqo na,zuciyarsa na yawan tambayarsa kayi dai dai?,yakan amsawa kanshi da eh duk da bada wani cikakken qwarin gwiwa ba,amma.yana da hujjar cewa matarshi ce.



         Bai fiya son abinda zai dameshi ba,don haka tun daga ranar yayiwa gidan qaura,yakan iya kwana daya zuwa biyu a wannan gidan nasu kafin yaje wancan gidan,wanda yawanci idan yaje din kwana daya biyune shima yabarshi yasauya muhalli.




       Kamar yau din dai a gidan nasu ya kwana,wanda wani lokaci hirarrkin su mustapha suna debe masa kewa,koda bazai tofa komai ba,amma.yakan zauna cikinsu yana sabgar gabanshi yana kuma jinsu.



       Wani dogon tsaki yaja kana ya miqe,ya rasa tunanin me yake daya sanyashi ya zauna har haka,baisan mene yake dagula lissafinsa ba,karatunsa ne daya dauki zafi saboda watanni qalilan da suka rage masa ya kammala ko kuwa a'ah,iya saninsa ba kasafai karatu ke damunshi ba,saboda baiwar qwaqwalwa da fikirar da Allah ya bashi,bai sani ba wannan karon....kodon hausawa sunce idan aski yazo gaban goshi yafi zafi?.....




      Wanka yayi yashirya cikin wasu qananun kaya da suka fidda sigar kyan da Allah yayi masa,mai cakude da kwarjini izza da jinin sarauta,yadauki maqullin motarshi bayan ya gama feshe jikinsa da turaruka kana yayo hanyar waje yana qoqarin kunna wayarshi dake kashe tun dazun,saboda baison yawan kira hakanan yakeji.



         Kusan dukansu yanzu suna falon,sabanin daxu da mustapha ne kawai a zaune,yanzun kamal da jabir hadi da wani abokinsu mudassir dukka suna zaune,jabir dai kallo yake na wani wasan qwallon raga da ake haskawa live,kamal da mudassir hirarsu data shafesu suke,yayin da mustapha yamaida hankalinsa kacokam kan allon computer din dake saman cinyarsa,da alama karatu yake dubawa.



       Fitowarsa tadan ja hankalinsu gaba daya,idanuwan kamal dake cike da hassada dukka suna kan azeez,yana jin inama yana da iko da a daren yau saiya qwace dukkan abinda azeez din yake taqama ya mallakeshi,saiya qwace duk wani abu da xai dinga nuna fifiko da daukakarshi a cikinsu,ciki kuwa harda kyau da kwarjininsa.



       Mustapha ne ya daga kai ya dubeshi

"Zaka dawo ne koka tafi kenan?" Agogon hannunshi ya duba kana ya amsa mishi

"No,zan danyi wani uzuri ne nadawo" kamal daketa kallonshi wanda duk bibiyarsa ya gaxa cimma gacin inda azeez yake zuwa ko kuma yakoma,ya kasa haqurin yin shuru

"Wai yarima ya kake mana asha ruwan tsuntsaye ne kwana biyu?ina kakeyin layar zana?" Wani kallo ya jefawa kamal din wanda ya sanyashi shan jinin jikinsa,saiya janye idanunsa daga cikin na azeez din

"Ka sani shima ko yabi sahun 'yan morewa quruciya da rayuwarsu" jabir ya fada cikin tsokana yana qyalqyala dariyarshi harda buga qofa,don ya fadine shi har zuciyarshi ba tare da yasan meye a zuciyar kamal ba,harara zeez ya jefawa jabir din kana yasoma yin gaba zai fice ba tare daya amsawa kowa cikinsu ba

"Abinci fa?" Mustapha yadan daga murya yana fada

"Saina dawo" ya bashi amsa a taqaice yana qarasa ficewa daga falon.



       Sannu a hankalin yake tuqinsa a nutse,harya shiga cikin unguwar,idan bai manta ba yau kwana biyu ko uku kenan rabonshi da ita,da wannan tunanin ya faka motar a qofar gidan yakasheta yafito,kana ya sanya muqullinsa ya bude gidan,ya tura falon yashiga.



       Shuru yake babu kowa ciki,dama ya tsammaci hakan,don lokacin kwanciya barci ne ga duk mutumin da bashi da wani aikin da zaiyi,saboda dare daya soma yi,karaf idanunshi suka fada sashen da dakinta yake,saiya lumshe idanu yana dauke kanshi,kana ya durfafi samansa.



       Dakin fes yake,kamar yadda ya zame masa dabi'a,baya barin dauda ko qura a duk muhallin da yasan zai zauna,ya buda duk inda yake da buqata yadauki abinda yake buqata din sannan  yakuma rufe dakin ba tare daya zauna ba yafice a dakin.



         Karo na biyu idanunshi suka sake sauka a qofar dakin sanda yake saukowa daga saman,tamkar wanda magnet yaja ganin nashi haka yaci gaba da kallon dakin,har ya gama saukowar,saiya durfafi qofar fita da sauri yanason daqile duk wani abu dakeson masa tasiri cikin ranshi.



         Murus jikinsa ya mutu lokacin daya shigar motar da niyyar tada ta,saiya kasa tabuka komai,kasala da mutuwar jiki na baibayeshi,wani irin shauqi yana mamaye gabbansa,ya tabbatar da cewa bazai iya maida kanshi gida ba a yanayin da yake ciki ba,don haka saiya kashe motar yafito yakoma cikin gidan.



      Tamkar wanda ake sauyawa direction,kamar wanda wani abu mai qarfi yake janshi saiya samu kansa da sauya akalarshi zuwa dakin nata.



      A hankali ya tura qofar,duhune yasoma yi masa sallama bisa dukkan alamu tayi bacci,a nutse yanufi inda yasan zai samu haske bedlamp,ya sanya hannunshi ya kunna,qaramin haske mai duhu ya bayyana.



      Tarwai fuskarta ta fito dab da fitilar,kamar wadda tasan da faruwar hakan,saitin fuskartata wayarta ce a yashe,da alama tana tsaka da dannata bacci yayi awon gaba da ita,saiya samu kanshi da xubawa fuskar tata idanu,karon farko daya fara aikata hakan tunda yasoma saninta,kamar ba bacci take ba,kamar idanunta biyu,idanunsa yakai kan qaramin bakinta dake dauke da pink lips,wani shock yaji wanda ya sanyashi yasoma tafiya da baya da baya,har sai daya dangana da muhallin daya soma tsaiwa farkon shigowarsa dakin yana ci gaba da kallon baby face dinta.



       Cikin baccinta tasoma jin wani irin yanayi,yanayin da yayi mata kama da wani yanayi wanda ta taba shiga watanni biyu baya da suka shude,a firgice tabude idanunta sannan ta waresu gaba daya,duk da babu abinda take iya hange sai qaramin hasken da fitilar gefan gadon take iya bayarwa,wanda bai isa yasa taga komai ba,tattausan qamshinsa da hancinta ya sheqo ya aikawa qwaqwalwarta shi ya bata amsar tambayar dake zura gudu cikin kwanyarta,lokaci guda tayi wani mugun laushi,tashin hankali ya sauko mata wanda hakan ya sanya zuciyarta ta qara gudu kan gudunta na qa'ida,bata da sauran wani abunyi illa zubawa sarautar Allah idanu,tanajin lokacin bautarta ne yayi kamar yadda sauran bayi suke,abu na qarshe daya faru shine saukar zafafan hawaye daga kuncinta.



        Ta cikin qaramin hasken take iya hango inuwar takunsa zuwa qofar dakin da niyyar ficewa bayan shudewar wasu mintuna,saita lumshe idanunsa sauran hawayen da suka cika mata idanu suka sake kwaranyowa karo na barkatai,wani irin tsanarsa taji tana ratsata karo na farko,ta wani gefe na zuciyarta taji xallar laifi mai girma akan mahaifinta,shi dinma karon farko a rayuwarta,taji zuciyarta tana jefa mishi tuhuma da zargi mai girma,abinda bata taba jin zuciyarta tayi masa ba duk da girman laifin daya ringa musu tun daga quruciya har girma sai a wannan karon.



       Wannan karon da kanta ta tashi ta gyara kanta,ko mama sodangin bata bari ta sameta a wani hali ba,saidai wanda ya rigaka kwana dole saiya rigaka tashi,yanayin qunci da rashin walwalar data ga bilkisun a ciki ya fayyace mata komai,sannan ganin yariman a gidan ya qara mata haske,wanda kwana yayi a gidan kana ya qare wuninsa gaba daya a samanshi,bai bar gidan ba sai qarfe wajen shidda na yammaci.



      Tunda yafita kamal ke ankare da yaushe xai dawo?,a wanne yanayi kuma zai shigo kamar yadda ya saba mishi,baiga shigowarsa ba sai yammaci,hakan ya qarfafa zarginsa a kansa,yakuma ci alwashin sake matsa masa lamba kozai karanto komai.



        Tun daga ranar saiya zamana indai ya fahimci azeez din zai fita saiya qirqiri wani abun da zai sanya su fita tare,koda ba waje daya zasuje din ba kuwa,sam bai kawo komai cikin ranshi ba,illa iyaka ya dauka kamal din yasoma tattara hankalinshi kan abubuwa masu muhimmancin da suka kamata dashi.




       Shudewar wata guda da sake faruwar lamarin tsakaninta dashi,a wani dare azeez din ya shirya kamar yadda yasaba lokaci zuwa lokaci don zuwa gidan yadauki abinda yake da buqata cikin gidan.



       Falon yau kamal dinne kawai zaune,wanda dama yazauna ne kawai saboda azeez din

"Zaka dan ragemin hanya mana idan babu damuwa" sai daya waiwaya ya dubeshi sanda yake daukan muqullin motar daya arawa jabir,yadda yake yawan takurashi da rage hanya masa hanya abun yasoma ankarar dashi,harya soma shan jinin jikinsa azeez din ya janye qwayar idanunsa yana yin gaba,ya fidda ran xai amsashi sai yajishi yana cewa

"Taho mu tafi".



        Duk yadda kamal din ke sanyo hirarrki azeez din bai tankashi ba,daya fuskanci yau 'yan wulaqancinne saman kanshi dole ya kama kanshi shima ya tsuke bakinsa,babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu,saima azeez din daya tura plate din waqa,wanda cikin sakanni yasoma tafiya.



        Gefan titi yaga ya gangara kana yayi parking din motar ya waiwayo ya dubeshi sai kuma yadauke kai

"Iyakata nan,kana iya sauka" bashi da sauran abun cewa,duk da baiso sauka anna din ba,yaso ne yaga yau maqurar inda yake zuwa,amma gudun tonuwar asirinsa yasa yace

"Ohkey,ba case,thanks,saimun hadu a gida ko?" Kai kawai ya kada masa,ya tashi motar yayi gaba,yayin da kamal.yaci gaba dabin motar da kallo,yana fatan Allah yakawo taxi da zai samu damar binsa kafin ya bace masa.



       Daga nesa yasoma hango tahowar wata taxi,cikin sauri ya sanya hannu yasoma tsaidata kamar ance mishi wucewa zaiyi bazai tsaya ba,a gabanshi ya tsaya,sai daya shiga sannan cikin nuna alamun yana hanzarine ya nuna mishi motar azeez data kusa qulewa,yace ita yakeso yabi,bayaso suyi missing,yayi mantuwar wasu abubuwa nashi masu muhimmanci a ciki,motar drivern ya tayar kana yasoma bin motar azeez cikin qwarewa,da alama tsohon driver ne.



       Yana tuqinsa yana dan tunane tunanensa har ya shiga unguwar,a nutse yasamu waje ya aje motar,dai dai lokacin da kamal yayiwa drivern umarnin yasaukeshi nesa kadan da inda azeez ya tsaida tashi motar,ya zaro kudinsa bayan ya gaya mishi adadin kilomitres din ya biyashi sannan ya fito.



     Cikin sanda yake bin jikin varender da bishiyoyin dake titin har ya isa wani gida dake kallon gidan da yaga azeez ya shiga,ya lafe sosai a bishiyar dake wajen gamida bada hankalinsa kan gidan yana nazartarshi,gami da  xuba mishi ido,yana karantar yanayin gidan dakyau,tare da fatan samun wani abu da zai zama hujja a gareshi.



        Ya jima tsaye a wajen,babu abinda bai saqa ba cikin ranshi,zargin da zuciyarshi tafi bashi shine,azeez din ya aje zuqa zuqan 'yammata ne yana hutawa dasu,shine yake boyewa bayason su sani,tabbas haka zatonshi yake babu shakka.



       Fitowar azeez ta sanyashi sake lafewa,ta gabanshi yaja motarshi yafice,sai daya daina ganinsa sannan yafiti yana bin inda motar tawuce da kallo,kai.ua girgiza yana wani shu'umin murmushi,sa'annan ya maida dubanshi ga gidan.



      Har ya nufi gidan gadan gadan kanshi tsaye,sai kuma ya dakata jin wayarshi na ringing,denial ne abokinsa,ya amsa kiran na wasu mintuna sannan ya maida wayar aljihunsa,ya sauya akalar tafiyar tashi yasoma neman taxi,hannu daya kuma yana laluben lambar wayar mom dinsa da niyyar shaida mata abinda yasamu gani.



       Bugu biyu ya dauka,tamkar dama tana kusa da wayar ne

"Son,ya akayi"

"Mom,breaking news!"

"Me yafaru son?,mun cimma nasara ne?" Sai daya gyara zamanshi yana murmushi sannan yace

"Alamunta dai sun fara bayyana....kinsan me yake faruwa?" Kai ta gyada cikin qaguwa

"A'ah,yi sauri ka gayamin da Allah,banason wannan kauce kaucen".



      Dukkan abinda yafaru ya gaya mata,wanda hakan yayi masifar faranta mata,harta kasa zama

"Na jiyo qamshin nasara,wulaqanci da tozarci suna gab da tabbata kan abdul'azeez da uwarsa,amma meya hanaka qarasa cikin gidan ka ganewa idanunka badalar da yake tafkawa?"

"Da zan shiga,so wani abokina yana jirana,zamuje wani waje,saina bari kawai nasoma shaida miki daga baya na koma" fada sosai tasoma yi masa

"Wanne irin shashancine wannan?,ko meye ake jiranka kayi yakai girman wannan ne?,wannan fa rayuwarka ce gaba daya akeso a gina maka ita"

Cikin nuna qaguwa da takura da fadan da take masa yace

"No mom,ba zaki gane bane,wajen da zamuje alqawari nayi,idan na saba kuma zasu dinga kallona as qaramin mutum....dole dole zanje,dole zan shiga gidan naga me yake aiwatarwa,ai kin sanni mom,meye na daga hankalinki kuma ha'an?"

"Is ok shikenan,amma duk rintsi karka wuce gobe"

"Relax mom,dole saina dai daici lokacin da nasan bazamu hadu ba,u know azeez very well,dole sai mun kula fa"ajiyar zuciya tasauke,wannan kafirin yaron tun kafin yakai wadan nan shekarun yake basu wahala

"Shikenan....saina jika" da haka sukayi sallama da juna,kamal ya aje wayar yana taune lips dinsa na qasa,saqa kawai yadda zai.kama abdul'azeez dumu dumu yakeyi,yana kuma qissima irin tonon silili nacin mutunci da zasuyi masa.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 31



*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




     Wani irin yammacine mai cike da wani irin yanayi mai dadi,dai dai lokacin da sukan xauna karatu a gidan,yauma hakkane,tana zaune da littafi a gabanta tana budawa shafi bayan shafi tana dan nazari tana jiran rakiya data tafi duba girki tadawo su dora a karatunsu,yau mama sodangi bata nan,ta fita siyo musu fruits na gidan da suka qare,amma bawai nisa tayi ba,don basu da nisa da wajen da ake saidawa.



      Wani lallausan yadine da akayi mishi dinkin doguwar riga da hijabinta,butter colour ne,haka yake zuwa readymade,kayan sun amsheta sosai,sun fidda kamarta qwarai,banda dan duhun fata da take da ita zaka tsammaci ba 'yar nijeria bace,uwa uba kuma yadda fatarta tayi kyau saboda cima me kyau dakuma zaman waje daya.



        Dai dai sanda kamal ke tsaye qofar gidan,yana duban qofar gami da sakin murmushi yana kuma shafan gemunsa zuwa gefan fuskarsa,yana cikin farinciki mara misaltuwa idan yatuna ayau zai toni asirin azeez,mutumin da a rayuwa ya tsaya masa a wuya fiye da kowacce halitta,a hankali yadora hannunshi kan qararrrawar dake shaidawa masu gidan cewa suna da baqo ya dannata.



       Doorbell ce tayi qara har sau biyu kusan a jere,hakan yasanya bilkisu daga kai ta dubi bakin qofar,saita dubi kitchen inda rakiya ke ciki,tasan babu lallai taji,kuma wala'alla mama sodangi ce,ta tsaya kiran rakiyar kamar bata lokacine,tunda maman tana da dan ciwo qafa lokaci zuwa lokaci,kuma a kwanakin yadan tasar mata,saboda haka rufe littafin ta miqe da sauri ta doshi qofar.



      Murmushine akan fuskarta sanda tabude qofar,tashin farko idanuwansu ya hadu da kamal dake tsaye,murmushin fuskar tata saiya gushe ganin baquwar fuska,tana masa duban rashin sani,yayin dashi kuma hakan yabashi damar qare mata kallo tun daga sama har qasa.



      "Wow....wow" yasamu bakinsa da furtawa ba tare daya shiryawa fadan hakan ba,ya dora da fadi a zuciyarsa

"Shege azeez...komai nashi na dabanne?why?"ba qaramin razana yayi ba da ganin bilkisun,baiyi zaton ganin halitta irin wannan ba mai kyau quruciya dakuma kwarjini a wannan muhallin ba.



       Sakin qofar tayi ta juya zata koma ciki,ganin ta tambayeshi har sau biyu bai amsa mata ba,sai wani kallo da yake binta dashi,abinda ta tsana a rayuwarta kenan mugun kallo irin wannan,uwa uba ma sai taji sam bai kwanta mata ba

"Hey babe" ya fada da sauri,saita tsaya gamida waiwayowa tana dubanshi,fuskarta a gintse,sai yaga hakan yayi masifar qara mata kyau

"Sorry baby...baki sanni ba ko?,muje ciki zan miki bayani,i think yarima bai miki bayani na ba" wani muguwar faduwar gaba taji ta saukar mata,tashin farko bayan rashin kwanta matan da taji bai mata ba sai taji tsanar data yiwa wannan mai suna yariman tana shafarsa,bata ce masa ci kanka ba taci gaba da tafiya,ya take mata baya yana ci gaba da qare mata kallo,gamida lashe lips kamar tsohon maye,ba shakka bayan komai ya kammalu saiya tabbatar da cewa ya mallaki wannan babyn.



        Inda tatashi takoma tazauna,tasake jan littafinta tana ci gaba da dubawa,yayin da shi kuma yasamu saman kujera yazauna idanunsa a kanta

"Dole azeez dole,ashe babbar harka ya samu irin wannan ya aje yana hutawa?,a ina yasamo wannan halittar?,a hakan ma ba'a ganin komai sai fuska da hannaye?,inaga anga sauran?" Saiya sake lashe labba gamida hadiye yawu muqut.



       Ya bude baki zaiyi magana rakiya tafito daga kitchen,cikin matuqar girmamawa tazube tana gaidashi,don tasan wayeshi,ya amsa mata yana mamakin me kuma ya kawota gidan ita?,me takeyi?,yaushe tazo qasar?,duk da baisan fuskarta sosai ba amma ya tabbata daga masarautar kaisa take,zai dan iya shaidata.



      Bai gama wannan mamakin ba aka sake taba qofar,rakiya ce tamiqe da hanzari taje ta bude,mama sodangi ce dauke da ledojin siyayya,rakiyan ta amsa kana ta matsa mata don tasamu damar shigowa.



      Da mamaki suke kallon juna ita da kamal,saboda duk sunsan juna farin sani,saidai ita maman ta boye mamakinta qwarai,saita maye gurbin fuskarta da murmushi gamida miqa mishi gaisuwar barka da zuwa,ta sanya rakiya ta cika mishi gabansa da drinks da kuma fruits din data shigo dasu.



       Duka sai hankalinsa ya kasu kashi kashi,ya gaza fahimtar komai,ga sodangi da rakiya daga masarautar kaisa,ga kuma wata baquwar fuska da baisan wacece ba,sannan alamu sun nuna dukka suna zaune ne a gidan,bakuma zuwan shekaran jiya jiya ko yau bane bisa dukkan alamu,to amma me azeez keyi a gidan?.



       Kusan mintuna talatin ya kwashe a gidan yana karantar komai da idanunsa,yana kuma sauraren karatun su bilkisu,yayin da mama sodangi taketa takatsantsan,don tayi yaqinin wannan zuwan da yayi babu masaniyar fulani aisha ko kuma yarima,tunda kusan tana daga cikjn mutane na gaba gaba da suka san dukkan abinda yake wakana,hankalinta bai kwanta ba har sai daya miqe da zummar tafiya,idanunsa akan bikisu wadda bata sake daga kai ta kalleshi ba tun kallon farko har zuwa sanda yafice daga gidan.



      Ajiyar zuciya mama sodangi tasaki,tana ankare da irin kallon da yake jifan bilkisu dashi,wanda sam bata gamsu dashi ba,tana ganin babu wata mafita datayi saura face ta shaidawa fulani zuwan kamal din,don koma meye a dauki.mataki,uwa uba kuma batason wani mummunan abu dazai shafi bilkisu ya bullo.



       Zaman dirshan a ranar kamal yayi yana dakon dawowar azeez din,saidai kuma ya daki gurbi,don daga makaranta ranar saiya wuce gidansu mama sodangi,can dinma bai shiga da wuri ba,ya tsaya a makaranta duba wasu karatuttuka,abinda yasa ya gagara kenan kaf cikin makarantar,sunansa yakuma tumbutsa,hakanan farinjinsa ya kere na kowanne matashi dake ji da samartaka,tako ina azeez din ba baya bane,baya ga baiwar kyau aji izza da miskilanci da yake dashi,sai baiwar qwaqwalwa,wanda nacinsa da yawan maida hankalinsa kan karatun ya maidashi haka,sau da dama yakanyi mamaki idan akace wane daqiqi ne ko kuma baya ja,saboda a iyakacin saninsa yasan Allah bazai tana halittar dan adam daqiqi ba,saidai ace kaifin ganewarka tafi ta wane,hakanan dabi'ar karatu tanason mutum mai maci da jajircewa,shi kuma haka yake,baya wasa da dukkan wani abu da yasan mai muhimmanci ne,hakanan duk abinda ya sanya a gaba saiya kaishi.



      Yana tsaka da hutawa bayan yayi É—ai É—ai saman tattausan gadonshi yana amsa wayar safwa kiran amminsa yashigo a daya wayar tasa,daga can bangaren tana tsaye ne cikin qawataccen falonta,duk da tarin kujerun da aka qawata falon dashi amma ta kasa zama,jira take kawai ya daga kiran nata

"Barka da warhaka ammi"

"Abdul'azeez,kana cikin hankalinka kuwa?" Yanayin yadda tayi maganar ya tabbatar masa lallai babu lafiya,kawai abinda ke faruwa,don haka saiya zauna sosai saman gadon fuskarshi na nuna alhini da mamaki,ko kadan baya qaunar abinda zai tashi hankalinta,har abada ammin ta musammance a wajensa,sama take da duk wata mace dake duniya,ya janyo daya wayar da yake amsa kiran safwa dashi,wanda daa yace karta katse kiran bari ya amsa wayar ammi,yayi qasa qasa da murya yace mata

"I wil cal u back,bani wasu mintuna" ba tare da ya jira amsarta ba ya katse kiran ya tattara hankalinsa kan ammi

"Nace kana cikin hankalinka kuwa?"

"Ammi....me hake faruwa?"

"Ta yaya zaka bari har kamal!....kamal yasan muhallinku,yakuma sako qafafunsa har gidan yashigo?" Boyayyar ajiyar zuciya yasauke yadda ba zata jishi ba,ya zaci wata gagarumar matsala ce,shi a wajenshi sam wannan ba wata damuwa bace mai girma

"Ammi meye a ciki?" Cikin muryar dake nuna maganarshi ta sake tunzurata tace

"Au,meye ma a ciki?,bayan kafi kowa sanin abinda yake gudana?,kasan nasan halin uwar kamal sarai....hakanan kaima kasan halin kamal din,kanason komai ya tarwatse ya lalace a lokcin da bamu shiryawa hakan ba kenan?" Idanunsa ya lumshe yakuma budesu lokaci guda,ha fuskanci me take tsoro,kada su karanci wani abu,har suje su shaidawa mai martaba

"Relax ammi....cool down please...,a sanda yazo bana nan,kuma ko ina nan na tabbatar bazai fuskanci komai ba,tunda ba'a rubuce yake a goshi ba,kin manta?" Shuru yadan ratsa tsakani,hakan yana nuna maganarsa tadan saka mata nutsuwa,jin hakan yasa ya dora

"Amma duk da haka,i wil take a seriouse action,bazan kuma bari qafarsa tazo gidan ba,kin gamsu da hakan?" Kai ta girgiza kamar tana gabanshi

"Hankalina ya tashi azeez,i know fauziyya na daya daga cikin mutanen da basu qaunata,basu qaunar su bude ido su ganni nida abinda na haifa,bare ace har nakai wani mataki ni ko su....hankalina yadan kwanta amma kadan,inajin kawai zan canza muku wani gidan ne" duk sai yaji hukuncin bai masa ba,sai passing passing ake dashi duk don aci gaba da boyeta,cikin son yardar da ita yace

"Believe me ammi,babu wani abu dazai faru,babu abinda kamal.ya isa yayi,beside ma duka duka baifi saura watanni uku komai ya qare ba,kin manta?" Da qyar da dabara yasamu yasha kanta,bayan tayita zabga mishi warning din ya kula yakumayi taka tsantsan.



       Ta bangaren kamal kuwa bayan ya gama xaman jiran nashi,har zuwa wajen biyu na dare yaji shuru,saiya miqe yana tsaki yanufi dakinsa,gefan gadonsa yazauna yaciro wayarsa yana yunqurin kiran mom,don baiyi maganar da ita ba,ya kuma tabbatar tana can tana jiransa,daya kintata lokaci yasan a lokacin bazai wuce tara na safe ba nigeria.



      Ringing daya kacal tayi ya daya,tamkar dama tana zaman jiran kiran nashine

"Ya ake ciki?" Kansa ya shafa yana qiyasta inama ace xai bata labarin ya kama azeez dinne cikin qazantaccen yanayi

"Naje mom....saidai kusan basu samu wani abuba,hakanan banga wani abu baqo ba,sai baquwar fuskar yarinya guda daya dana gani" cikin son lallai sai sun kamashi da laifi tace

"Kaman yaya?,ita baquwar fuskan itace dadiron nashi duk da ban gani ba" goshinsa yahau murzawa yana tuna zazzaqar muryar bilkisu sanda take karantawa rakiya iziyya,wadda saura qiris su sauketa,da yadda kyakkyawar fuskarta ke hade tsaf 

"Bana tunanin haka mom,don karatun qur'ani natarar sunayi" shuru hajja fauziyya tayi,fadin hakan da yayi ya warware mata dukkan tunaninta,saita koma ta zauna tana sakin ajiyar zuciya

"Sauran dake cikin gidan su waye da waye"

"Daga masarautar kaisa suke,babbar mace da yarinya,kamar naji yarinyar ana kiranta da rakiya,babbar mace kamar..." Sai yadanyi jim yanason tuna sunan,daga bisani yace

"Sodangi".



      Shuru tayi tan gyada kai,sannan daga bisani tace

"Dakyau hakanma,zansa amin bincike cikin masarautar kan su waye,meye kuma dalilin barinsu masarautar kaisa zuwa mexico" daga haka ya katse kiran,bai damu ba ya cilla wayae gefansa yana shafa kanshi da hannu daya,bilkisu na mishi yawo cikin idanunshi,saiya saki murmushi a hankali yana mamakin yadda yakeso ya jarabtu da ita cikin qanqanin lokaci haka.



       Misalin hudu da arba'in ne na yamma agogon nigeria,tara da arba'in na safe agogon mexico sanda ya shiga gidan,kusan a gaggauce yake sauri yake ya debi wasu takaddu nashi zai wuce makaranta,don qarfe goma yana da lacture.



      Dai dai lokacin da kamal yake zaune a falon gidan yana kallon news,hannunsa daya kuma yana kurban ruwan baqin tea.



      Bin azeez yayi da kallo sanda yake sallama a gaggauce yana shigowa falon,saiya aje cup din hannunshi murmushi yana subucewa fuskarshi,yana ganin ya kamata yace wani abu,ya kamata azeez din yasan yaje gidan,ya kuma kamata yaji wani abu ko yasan wani abu komai qanqantarshi akan yarinyar,don haka yamiqe bayan ya bada tazarar mintuna uku da shigar azeez dakin nasa ya rufa mishi baya.



      Da mamaki ya waiwayo sanda yaji an turo qofar dakin ba tare da sallama ba ana kuma shigowa,saboda kusan kowa ya sani,dokarshi ce,bai yadda da shigar mishi daki haka sakaka ba kai tsaye ba tare da neman izininsa ba,hakanan shima bai shiga dakin kowa cikinsu,idan ma ya shiga din to tabbas lalura ce ta kaishi ko ta kama yashiga din.



       Ganin kamal ne ya sanyashi ci gaba da gyara takardun dake saman mirrow dinsa,dama koda bai shigo ba shi zai sameshi ya masa warning,don yadan fuskanci tamkar bibiyarsa yakeson ya dinga yi,wanda shi bazai lamunci hakan ba.



       Cikin muryarsa da saman fuskarsa dukka zaka fahimci akwai nishadi da walwala a ciki,ya qaraso cikin dakin sosai yana dan qarewa dakin kallo a fakaice

"Shegen....komai nashi saiya banbanta dana kowa,kamar yana zabawa kanshi rayuwarshi" yayi maganar can qasan ranshi,amma a fili saiya tattaro dukkan juriya da dakiyarsa yace

"Hey man" banza yayi dashi kamar baiji ba,har sai daya gama abinda yakeyi ya riqe takardun sosai sannan ya juyo yana dubanshi,idanunsa ya sanya sosai cikin na kamal din,yana masa wani kallo dake qara fidda kwarjininsa,tsahon wasu sakanni,shima kallon nashi kamal yake,duk da yadda kwarjininsa keson dakusar da duk qoqari da yunqurin masa magana da yakeson yi.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 32


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*



*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________




      "Nakai maka ziyara a gidan ajjiyr baqinka na musamman,duk da ban shaida maka ba,but....amma naso nayi suprising dinka ne,tunda na fuskanci akwai abinda ake boye mana,kuma da naje din sai naga hakane,ashe akwai abun boyewar...." Ya qarasa fada yana daga gira irin na 'yan duniya,yana fidda murmushi.



       Azeez na tsaye yana dubanshi harya gama,saiya soma takawa kamar xai fice,saidai ba fitar zaiyi ba,zai rage nisan dake tsakaninsa da kamal ne,har sai daya zo dab dashi sannan ya tsaya yana dubanshi.



       Cikin muryarshin nan mai cike da izza mulki da kuma qasaita,wadda a wannan karon ta cika da gargadi da jan kunne yace da kamal

"U break my rules....kamal,nasha gaya maka...ka daina yunqurin shigomin daki ba tare da sallama ko neman izini na ba,secondly kuma....iam warning you,ka fita daga sha'anin rayuwata,abinda kaketa yunqurin shiga bazai maka da kyau ba,wannan itace shawarata" saiya ci gaba da takawa,harya wuceshi kamal na binsa da kallo,har yanzu baiji komai game da yarinyar ba don haka yace

"Idan banda akwai abinda kake boyewa meya hanaka ci gaba da zama damu ummm?....and ita din wacece ita?" Shuru ne ya ratsa dakin,azeez ya dakata daga tafiyar da yake,yana jefa masa tambayar bilkisu ta dawo masa tarwai a kwanyarsa,yana magana ne a kanta ko kuwa?.



       Sake takowa kamal din yayi zuwa bayan azeez,sannan yasake cewa

"Ita kadai nakeson sanin wacece ita,coz she attract me,na kuma ji ina da interest a kanta,so pls ko zaka hadani da ita" karon farko yaji wani mugun bugun zuciya,wanda tsahon rayuwarshi bazai iya tuna when last da yaji haka ba,saiya juyo sosai yana jifan kamal da wani irin kallo,take yasha jinin jikinsa,yana jin yana masa kallon ne da fassara ta daban,don haka ya gyara tsaiwarshi

"Am seriouse man....sonta nake da gaske,ba irin soyayyar da kake min fassararta ba...." Dakatar dashi yayi ta hanyar nuna masa qofa da hannu,sannan ya motsa labbansa a hankali

"Get out pls...zan kulle dakina" fuskar kamal din akwai damuwa sosai,amma yasan halin azeez din,dama kadan daga aikinshi ne,don haka ya daga kafadunshi sannan yasoma takawa yafice daga dakin.



     A zafafe ya rufe dakin,kana yazo yawuce kamal din dake tsaye a falo,ya tada motarsa cikin zafi kana yafice a layin.



      Har saman fuskarshi yake jin zafin,yadinga shafa sumarshi zuwa sajensa yanason lalubo meya zafafa kanshi haka da yawa bayan yayi 'yar tafiya,iskar sassanyan bishiyun dake jere gefan titin sun bugeshi,fresh air ce mai kyau ta tatattciyar safiya,daga baya abinda yayi realising kawai shine,yana da kishi qwarai,ta yaya kamal zai nemi yayi tarayya dashi kan wani abu dashi ya taba tarayya dashi?,bawai don ya damu da wanzuwarta ko wani abu bane,a'ah,kawai.har zuwa yanzu tana qarqashin ikonshi ne,idan da bayan nan ne bashi da matsala dashi,sai daya qaraci yawonsa ya tabbatar duk wata temper tashi game da kamal ta sauka sannan ya shiga aji,a sannan malamin harya kammala yafice,sai saura ya taras.



     ****************


    "Auta" fulani adama ta kira sunanta cikin izza tana mata wani duba dake nuna koma meye zata fada mai matuqar muhimmanci ne,tun kafin ma tayi magana yanayin wajen da suka kebance kadai ya isa ya gayawa auta cewa ba qaramar magana zasuyi ba. A ladabce ta masa mata

"Ranki shi dade,Allah ya baki nasara"

"Akwai mutane guda biyu a gidan nan da tabbas basa cikinsa,kuma hadiman gidan nan ne,baya ga haka suna aiki ne a sassan aisha...." Saita tsagaita gami da yin shuru,yayin da ita ta jinjina kai

"Auta inason a bincikamin cikin sassanta su waye basu nan?,idan an samu ina suka tafi,auta...." Ta sake kiran sunanta,ta amsa mata tana sadda kai

"Banason wannan karon acemin ba'a samo wani bayani game da aikin nan ba,inason kota halin qaqa nasamu wani bayani da zai gamsar dani" kai ta jinjina

"Da ikon Allah wannan karon ranki ya dade sai inda qarfina ya qare,Allah ya baki nasara zakiyi farinciki da samun baya nan"

"A tashi a bamu waje" ta fada tana juyawa autan baya.



      Koda ta fice zurfin tunani ta fada,tana tuna yadda abubuwa suke son su jagule musu,tako ina aisha ta toshe kowacce kafa ko qofa da za'a samu wani abu daya danganceta,bata taba shiga matsi da wahala kan wani abu data sanya gaba ba irin wannan lokacin,dan ko fulani saratu bata wani bata wahala ba,a yanzunma mantawa take da ita da abinda ya shafeta,don tasan ta rufe babinta,aisha yanzu itace target dinta.



       Cikin sati guda auta ta dinga shige da fice ta kowanne fanni don gano su waye basa nan din?,sannan ina suka tafi?,me suka tafiyi din?,saidai dukka qoqarinta ya cimma tura,abu qwaya daya tal tasamu ganowa shine,sodangi da rakiya ne basa nan,dole haka ta tattara abinda tasamu ta shaidawa fulani adama.



      "Allah ya tsinewa yarinyar nan,Allah ya isa tsakanina da ita" fulani adama ke fada wanda batasan harya fito fili ba saboda takaici da baqincikin daya mamayeta,tuni ta kora autarma,wadda ita tana ganin tayi namijin qoqari,saboda dukkan hadiman fulani aishan 'yan amana ne,samun wani bayanai daya danganceta daga wajensu ba qaramin aiki bane,tana da wani tsari,ba dukkan komai zata gudanar bane take bari ya fita har a sani,hakan ya sake sanyawa ta zama mai ciakakken sirri akan dukkan al'amuranta.


******    *******  *********



    Sannu a hankali kwanaki suka dinga tuawa,lokuttan da sukayi musu saura na barin qasar mexico bai wuce sati takwas ba watanni biyu kenan masu zuwa.



       Ta fannin mama sodangi da kadan da kadan take tattara dukkan wasu kayansu da  tasan cewa zasu tafi dasu,dakuma wadanda zasu barsu a nan inda suka samesu.



      Bata taba yin zancan da bilkisu ba,hasalima wani irin tausayin yarinyar takeji sosai har cikin ranta,tana jinta tamkar diyar cikinta data haifa,takan zauna sau tari ita kadai tayi ta tunanin yadda rayuwarta zata kasance a nan gaba,bayan anci moriyar ganga a yarda qauronta,dukkan wani fata nata da burinta na ganin manufar auren ta sauya sai taga ko kadan babu alamu dake nuna samuwar hakan,taso ace inama inama wannan zaman nasu ya haifar da shaquwa da soyayya mai matuqar qarfi,wadda zata zama silar wanzuwarsu a matsayin miji da mata har gaban abada.



      Tasan azeez tsaf ciki da bai,tunda itadin tamkar uwa ce a wajensa,daukar ciki da naqudarsa ne kawai batayi ba,amma ita tayi rainonsa kaf,hakanan bilkisu,adan zaman da sukayi na watanni goman nan ta karanci wasu daga cikin halayenta,wadanda dukka masu kyaune,bataga guda mara kyau ba ko abun tur,taga dacewarsu da azeez fiye da yadda ta zata,tana da tsammanin cewa tabbas babu shakka fulani aisha batasan wacece bilkisu ba,a iya nata nazarin da hangen,da kuma karantar yanayi da halayyarta da tayi,bilkisun itace irin macen da kowacce ywa zatayi kwadayin ta zama suruka a wajenta,tana da halayya da dabi'u masu kyau nagarta da kuma jan hankali.



      Abinda bata sani ba shine,itama bilkisun ta nata fannin tama irge da duk kwana daya data ragu cikin kwanakin da suka rage mata,zumudinta na komawa zuwa gida yana qaruwa,ba don komai ba,sai don tazo taga 'yan uwanta,jininta,wanda kullum kwanan duniya dasu take kwana take kuma tashi dasu,saidai kuma karsashinta yakan ragu idan ta tuna meye makomarta anan gaba?,ta rasa karatunta,ta rasa mutuncinta,sunanta bazawa a yanzu?,eh tabbas!,wannan shine sunan da zata ci gaba da amfani dashi.



       Cikin satin da ya zamana shine satinsu na qarshe cikin qasar,sai dukka yanayinta yasake canzawa,hakanan take jin wani iri a dukka.jikinta da zuciyarta,duk wata walwala tata ta tafi,sai takejinta wani iri,tamkar ranar da zata taho daga nigeria zuwa qasar,tafison zaman kadaici fiye da komai,tafison zama shuru ita daya,duk sanda ya kadaice din tana zaman takurawa kanta ta hasasowa kanta meye makomarta,dukka mama sodangi na lura da ita,tsananin tausayin bilkisun ne ke sake kamata,don ta riga data sani,koma wace macace akayiwa rayuwarta haka daga mai manufa zuwa mara manufa zataji fiye da abinda bilkisun takeji,musamman idan tasan rayuwa fiye da bilkisu,ma'ana shekarunta sun daranma nata.



*******     ******    ********



     Gagurumin shiri take na tarbar yaron nata,wanda takejinsa daya ne tamkar da dubu,shiri tayi na kece raini na bikin murnar dawowarshi tare da kammala karatunsa,saidai a wani sashe na zuciyarta tana jin cewa,koda ya dawo din zai dora ne daga inda ya tsaya,bawai zaizo yayi zama na dindin bane a masarautar,saidai tana sa mishi ran zan dan zauna dasu adadin kwanakin daya jima rabon da yayi irinsu.



      Wannan karon kusan duk wani wanda ya kwana yatashi a masarautar kaisa yasan da dawowar yarima azeez,bama masarautar kawai ba,duk wanda ke cikin garin na kaisa harma da maqwaftansa,saboda shiri fulani aishan take dan gaske,irin shirin da akecewa tsone idon maqiya.



     Kamar yanxun da take xaune gaban mai martaba,cikin ado na kece raini,har yau bata bar ado wa mai martaba ba,hakanan dabi'arta take,macace mai masifar tsafta da son ado da kwalliya,shi yasa har kwanan gobe tauraruwarta take haskawa a zuciyar mai martaba,har kullum aishansa ta dabance,tasan kanshi hakanan tasan yadda take tafiya dashi.



      Dan gyaran murya yayi yana gyara zamanshi,idanuwansa bisa kanta

"Yanzu uwar abdul'azeez da akazo aka tsareni har haka me ake buqata?,ni naga alamun ma fa anasone gaba daya a ture gwamnatina daga zuciyar yarona,tako.ina kinbi kin dha gabana a wajensa ba tare dana ankara ba?" Wata qawatacciyar dariya tayi tana lanqwasa wuyanta,tana mishi wani kallo da duk duniya shi kadai yake samunsa

"Ni na isa Allah ya baka yawan rai,abdul'azeez ai naka ne,bama shi kadai ba,uwar sa taka ce bare shi" murmushi ya fidda wanda ke nuna kalamanta sun mishi dadi,ta iya lafazi mai kyau da kwantar da zuciya,duk cikin matansa babu mai irin harshenta,shi yasa ko zaman hira yafi jin dadin yi da ita fiye da kowacce a cikinsu,duk da yana qoqarin boye fifikon kowaccensu a cikin zuciyarsa.



      "Kamar nawa zan bayar?,amma fa kada a manta,nidin almajirin dan kasuwa ne....kece hajjaju guda,don naga saida komai yazo qarshe aka nemi na bada nawa kason" murmushi tasake yi wanda yasake fidda kyanta duk da shekaru da suka fara ja

"Ko nawa ran sarki ya dade ya bayar fulani tana maraba,amma kada ya manta,kome fulani tayi da bazarsa take rawa" harar wasa ya jefa mata sanda ya dauki wayarsa

"Dadin baki ko?,salon na miki transfer duka kudin account din nawa ba tare dana ankara ba" dariya tayi

"Da na zama daya daga cikin jerin miloniyoyi mata matuqar dukiyar cikin accnt din sarkin kaisa ta dawo hannuna" dariya ta bashi sosai,yana murmushi ya mata transfer kudade masu nauyi,har tayi mamakin yawansu ta dubeshi,saiya daga mata gira shima yana duban nata yace

"Kina mamakine?,kaman ban taba hidima me yawa haka kan lamarin abdul'azeez ba kamar yau ba ko?" Kai ta gyada,saiya gyara zamanshi yana murmushi

"Nima inason yarona sosai aisha,wala'alla ma fiye da yadda ke kike sonshi,amma dole a matsayina name iyali da yawa,wanda Allah ya wajabtamin yin adalci a tsakaninsu,dole na dinga takatsantsan da kuma qoqarin daidaita matsayinsu cikin zuciyata,koda ace wani yafi soyuwa a zuciyata fiye da wani,inason abdul'azeez bawai don matsayinsa na da namiji ba,a'ah,inasonshine saboda soyayyarsa daga Allah take a zuciyata,bugu da qari a yanayin da Allah ya azurtani dashi koda daga wanne jinsi ya fito,inajin xan soshi fiye da kowa cikin 'ya'yana,ubangiji ya daukemin mahaifina a ranar daya musanyamin dashi" sai ya tsagaita yana sauke ajiyar zuciya.



      Kai fulani ta gyada,har cikin zuciyarta tana jin dadin yadda yau yake sake jadda da mata soyayyar shalelenta,iya wannan kawai ya isheta alfahari gami da farinciki tsakanin abokan zamanta

"Allah ya yiwa mai martaba raham,ya kyauta makwanci,yasa can tafi nan"

"Amin,amin ya Allah indona" ya fada yana murmushi,itama saita murmusa tana jin yana bata kunya.



        "Amma ina ganin zuwa yanzu da abdul'azeez zai dawo gida,ya kamata ace anyi maganar aurensa,saboda shekaru suna tafiya,inason ya zama babban mutum kamili,hankalinsa yasake game jikinsa,don shine magajina anan gaba kamar yadda kowa yasani" maganarsa sai tadan sanya zuciyarta rawa da yayi zancan aure,saita tuna da nata plan din duk da yake kwanaki qalilan suka rage a gamashi,hakanan ta gama shirya komai akansa shima.



      A karan kanta itama tana lissafin zuwa yanzu ya kamata ayi magana tsakanin magabatan abdul'azeez din dana safwa,a qalla asan da xaman juna,amma furucin me martaba shi yanke zaren tunaninta ba tare data shirya ba,yakuma so daga hankalinta

"Kinsan diyar wajen professer Amk?,wadda tazo kwanaki hutu ko?" Da sauri ta gyada kai,duk da bata shaida yarinyar wani can can ba,don data zo din ta sauka ne sassan fulani saratu a matsayinya na uwar gida kamar yadda shi mai martaban ya tsara,saidai kawai ta shigo ta gaidasu,sa'annan data tashi tafiya tabiyo ta mata sallama,ita kuma ta mata halin girma kamar yadda ta saba da kyaututtuka kala daban daban,tana sone taji abinda ya dauko xancan yarinyar,kamar yasan me take saqawa kuwa saiya dora

"Da mun fara magana dashi professor din,kan yiwuwar hada aurensu da abdul'azeez..." Ai yana ajewa ta kama,don ita sam maganar ma bata tsaru a kunnenta ba,ina 'yar professor ina azeez din?,tana ganin kwata kwata ba ajinsu bane

"Ai Allah ya taimakeka.....abdul'azeez tuni yana da wadda yakeso,kuma sun jima da fahimtar juna,maganar karatunsu duka ita dashi shiya kawo tsaikon shigar manya maganar" Da dan mamaki yadubeta kana yace

"Af...kice na kusa tafka kuskure....to amma,ya akayi haka?,bamu taba maganar dashi ba"

"Ni na dakatar dashi saboda karya hada karatunsa da soyayya" murmushi yasaki

"Kamar yaya?,saikace wani mace" murmushi tayi tana son sauya akalar zancan

"Kasan halin yaran nan sarai,matuqar suka sanya soyayya cikin ransu karatunsu saidai addu'a kawai,basu iya daukar abu da sauqi ba" kauda wannan zancan yayi ta hanyar cewa

"Diyar wacece ita?"

"Æ´ar alh ibrahim khalilu attah,diyar qawata kuma" idanu sosai mai.martaba ya zuba mata,wanda hakan yayi mata kwarjini sosai,saita dan basar kana ya jeho tambayarsa

"Ni dake kusan dukka musan waye alh attah....ina fata aisha ba auren hadi zaki masa ba saboda 'yar aminiyarki ce?,don kinsan na soke auren hadi a tsarina gaba daya,kaf yarana babu wanda zan sake yiwa auren dole?" Kai ta girgixa

"Sam ba haka bane Allah ya baka yawan rai,abinda kake tunani bashi bane" shuru ya ratsa tsakani sa'an nan yace

"Shikenan....duka mu ajjiye maganar tawa da taki,idan yadawo zan tuntubeshi naji nashi ra'ayin"

"Allah ya nuna mana" ta furta tana sauke boyayyar ajiyar zuciya.



       Dukkan wani abu da azeez din zai buqata ta riga data kammalashi,hatta da dukkan wani furniture na bangarensa tasa an musanya masa da wasu,ko tsinke bata bari ba,duk da cewa ba tsufa sukayi ba,tayi hakanne da biyu,na farko tasa an caje dukkan sassan nasa lungu da saqo,an tabbatar babu wani abun cutarwa a rataye ko a bunne,kana ta sanya aka qara matakan tsaro bayan an gama shirya komai tsaf.



      Hatta da gidan da mai martaba ya bashi kyauta sukutum da guda sai data sanya aka tsarashi aka kuma gyarashi yadda zai dace da tsarinsa dakuma son ranshi.



      Kyautar gidan da yafi kowanne gida qawatuwa cikin gidajen da mai.martaba kedashi ya jawo cece kuce tsakanin matan nashi,gwara adama tayi qoqari ta boye tsananin bacin rai da kuma adawarta cikin kirsa da munafurci,amma fulani saratu dake abunta gaba gadi takanas ta iske mai martaba da zancan,murmushi yayi sanda ta gama jawabinta

"Banda abinki saratu.....shifa yaron nan da kike gani dole idan yatashi aure idan bashi da yadda zaiyi na bashi gida,idan ta kama ma harda auren inyi masa dungurun gum,qannenshi kuwa daga daya wataran shine a makwafin mahaifinsu,babu wani abu dana gaza tsakanin yarana,kowanne ina bakin qoqarin biya masa buqata da sauke nauyinsa daya rataya a wuyana,hakanan ina qoqarin ganin na daidaita komai tsakaninsu,babu son kai ko fifici" jikinta ya danyi sanyi,saboda tasan cewa hakanne,tabbas yana bakin qoqarinsa na ganin yayi adalci yakuma daidaita matsayin kowannnesu,to amma tana matuqar kishi da aisha ne,da yadda akomai ta fisu,tun daga farinjini cikin gidan da kuma yawan masoya,duk da cewa wasu da yawa suna boyewa ne saboda ganin idanunsu.

"Kayimin afuwa Allah ya baka yawan rai,amma maganar gsky wannan kyauta sam batayi ba" murmushi yasake yi ganin ta kasa bada cikakkiyar hujja

"Kinga saratu...na riga na bawa abdul'azeez gida,bawai don baya da,wannan kawai ra'ayina ne,kamar yadda nake hidimtawa gamida kashe kudi wa qannensa a duk sanda zan aurar dasu,ba kuma tare da tashi mahaifiyar tayi qorafin na musu abu banwa nata yaran ba" hakanan ta qaraci qananun mitocinta da gunguni tamiqe ta fita,tanajin kamar taci wuta saboda bacin rai kishi da masifa dake cinta.



       Tsanar abdul'azeez na sake qaruwa a zuciyarta,tana jin gaba daya ya zame musu qarfen qafa,ko qadangaren bakin tulu,kullum kwanan duniya sai taji ko taga wani abu game dashi dazai sanyata bacin rai,bazata iya tuna mutum nawa ta hukunta cikin barorin sassanta ba akan abdul'azeez da tsohuwarsa,sukan manta su kirashi da sunan da tuni ta haramtashi ta kuma yi jana'izarsa a sassanta,ko suyi subutar baki su yabesu,da wannan bacin ran ta qarasa sassanta tana qulla abunyi a zuciyarta.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 33


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




      Ƙarfe biyu da mintuna ne na rana a qasar ta mexico,tun daga unguwar zuwa gidan gaba daya ya dauki shuru,baka jin motsin komai saina abubuwan da ba'a rasa ba,saboda qarancin zirga zirgar al'umma cikin unguwar da kewayenta,wanda dama ba kasafai kake jin hayaniya sosai cikinta,har dama dama ranakun qarshen mako.



        Dai dai lokacin da bilkisu ke zaune a falon gidan ita da rakiya,wayarta ce a hannunta tana danne danne,wanda ita kanta bata ce ga abinda takeyi a ciki ba,duk da tasan tana duba wasu hadisaine data sauke su take bibiya kullum har ta kusan kammalawa su duka,saidai a yau bata gane karatun,yinsa kawai take,yayin da rakiya wadda ke zaune a gefanta take kallo a tv plasma din dake girke a falon,mama sodangi kuwa tana daki tana ci gaba da tattara kayayyakinsu waje gida.



      Qararrawar dake qofar falonsu ta dauki qara,dukkansu suka kalli bakin qofar,sam babu wani kuzari a jikinta saboda haka rakiya ta rigata miqewa ta nufi qofar don budewa.



        Hausa taji rakiyan tanayi na wasu sakanni,ta saki qofar ta dawo ciki,saita wuce kai tsaye zuwa dakin mama sodangi,bata jima ba suka fito ita da maman,rakiyan takoma inda ta tashi ta zauna,mama kuma ta zarce bakin qofa

"A'ah,lawal.....shigo mana,ya zaka tsaya a nan?" Tayi maganar tana dawowa ciki,babu jimawa sai gashi ya bayyana a falon.



        Kakkauran matashi mai duhuwar fata,yana da tsaho dakuma jiki,da alamu shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas zuwa da tara ba,kallo daya zaka masa kasan baiyi kala da zallar bahaushen nijeria ba,yayi zubi da 'yan mali sosai,da alama jinin can ne.



       Bata zauna ba sai data gabatar masa da ruwa da lemo sannan ta zauna suka gaisa sosai,ya karkata ya zura hannunsa a aljihun wandonshi yafito da passport da kuma ticket yana miqawa mama sodangi

"Wannan passport dinku ne da ticket dinku,an kammala komai"

"Hala fulani ta iso"

"Eh suna can tare da yarima,sunzo bikin kammala karatun nashi,kuma ina tsammanin duka tare zasu kom....." Da sauri bilkisu tamiqe ba tare data tsaya jin sauran maganar ba,tunda taji an ambaci sunayensu ta gundura da xaman falon,tun can batasan ma meye ya zaunar da ita ba,a hankali ta taka tashige dakinta.



       Gefen gadonta ta zauna cikin wani irin kasala da mutuwar jiki,tana ci gaba da danna wayarta,wanda zuwa yanzu ta daina fahimtar komai,sai wani nisan kiwo da qwaqwawarta tayi cikin duniyar tunani.



      Mintina wajen ashirin kyawawa tana zaune a haka,bata motsa ba sai lokacin da aka turo qofar sa'an nan ta daga kanta,mama sodangi ce take takowa cikin mutuwar jiki da kasala,bata ce komai bs itama harta iso gefan bilkisun ta zauna,sannan ta miqa mata wani dan koren littafi da wata paper,sai data kalli abinda take miqo matan sannan ta sanya hannu ta karba tana juyasu

"Passport ne da ticket,na fitarmu daga mexico,nan da kwanaki biyar masu zuwa idan Allah ya yarda".



      Ba zata iya tantance mai taji ba,saidai abu guda da zata iya ganewa wani sashe na zuciyarta ya cika da farinciki da murnar samun 'yanci,yayin da wani sashen ya cika fal da fargaba da tsoro,ga wani irin cushewa da qirjinta yayi wanda batasan na meye ba

"Allah ya kaimu" ta fada cikin sauri sauri tana lalubar lambar wayar umma katti wanda kusan yawancin lokuta da wayarta take magana da ƙannenta


**************


     A hankali doguwar motar ta alfarma wadda ke dauke da iyali da kuma ahalin masarautar kaisa,wanda ya hada da fulani aisha,da yaranta duka,Aarifa uswa sumaira da afnan,tana tare da amintattun hadimanta har mutum hudu,sai kuma fulani adama wadda ta buqaci zuwan itama,tana tafe da hadima daya sai diyarta da bata aurar ba afra.



        Ko kadan fulani aishan bataso zuwan adaman ba,amma saita dake,ko a fuska bata nuna ba,tunda mai martaba da kansa ya buqaci hakan.



       Da fari adaman itama zuwan sam bai mata dadi ba,amma daga bisani da sukayi magana da haj fauxiyya saitace da ita

"Aikamar dama ce kika sami,dama da xaki nunawa duniya dashi kansa yaron kina qaunarsa,dama ta biyu kuma zaki iya sanya idanu qwarai da bin diddiginsa har zuwa ranar da zaku dawo,wala'alla idan ska dace ki samu wani hujjan kamawar komai qanqantarta". Wannan magana ta fauziyya ta sauko da ita har ta saki murmushi,tana kuma sake tabbatarwa kanta maganar fauziyya haka take bayan tayi nazari.



      Gidane wanda zai ishesu sauka su duka,babu matsi ko takura,falo ne yalwatacce mai dauke da dakuna a wani corridor na daban,fulani aisha daki daya ita da autarta afnan,uswa sumaira da Aarifa da yaran uswan biyu daki daya,daya dakin kuma fulani adama ce da  afra wadda taqi xama dakinsu uswa ta koma dakin mamanta,sai wami spare dakin Kuma dake falon gidan daura da kitchen sauran barorin da suka taho dasu suka sauka a ciki.



      Kowa dakinsa ya shiha ya kintsa yakuma huta gajiya,dai dai lokacin fulani aisha data gama wanka tana zaune saman daya daga cikin tuntun dake dakin,uswa na zaune a gabanta tana sake gyara musu kayansu,gamida jerasu yadda zasu musu dadin sawa,afnan na amsa tana jerawa cikin wardrobe din dakin.



        Ita daya tayi nisa a zurfin tunani,duk da cewa ta gama tsara yadda zata kauda dukka tunanin adama,tasan cewa anzo gabar qarshe,kuma hausawa sukace aski idan yazo gaban goshi yafi zafi,idan batayi wasa ba komai zai iya kwabe mata ta hanyar adama,a wannan lokacin da akazo gangara,sam bata tsara plan na tafiyarta da ita ba,amma dole tayi shuru da maimartaba ya buqaci hakan,don kada ta tsammaci wani abun,tuntuni ta kula,ta kuma karanci halayen fulani adama da kyau,tana da sanya idanu dabin diddigi,shi yasa take takatsantsan da duk wata mu'amala da zata sanyasu su xama a bigire daya.



      Duk da cewa hankalinta yadan kwanta data aikawa sodangi da ticket dinsu na komawa,amma dole ta tabbata sunbar qasar ba tare da fulani adama taga daya daga cikinsu ba.



       "Afnan....maza kiramin yayanku" ta fada bayan takai qarshen tunaninta gamida suke ajiyar zuciya,dan tsaiwa da abinda takeyi afnan din tayi sannan ta bata rai

"Amma gaskiya ammi saidai a wayarki,kinsan halinsa,yanzu dana cika kiranshi zaimin halin nasa"ta qarasa fada a shagwabe,kai ammi ta gyada,kafin ma tayi magana uswa ta rigata

"Nima na kirashi,amma baiyi picking ba,yamin tex dai suna school suna qarasa wasu abubuwa"

"Ohkey,babu damuwa,rabu dashi ma,nasan zai shigo gidan nan da anjima".



      Babu jimawa kukun gidan ya shaida musu ya kammala abinci,ya kuma shiryashi saman babban dining na gidan,kusan kowa a buqace yake da abinci,hakan ya sanya lokacin fitowrsu cin abincin yazo dai dai da juna.



      Kowacce jinta take ta cika ta kuma hamshaqa,fulani aishan na tsakiyar yaranta suna tsaka da cin abincin sanda fulani adama tafito,kamar zata maze itama yadda taga fulani aishan taga tayi,sai kuma ta tuna cewa ita din me nema ce wanda aka ce baya gajiyawa,don haka bayan ta zauna tasoma zuba abincin ta dubeta

" har yanzu abdul'azeez bai samu damar shigowa ba hala?" Cikin izza da sarauta ta amsa

"Eh...bai samu ba" sam amsar bata mata ba,amma saita danne,tsanarta da haushinta na ninkuwa a ranta,fatanta na zuwansu hannu yana sake qaruwar mata.



       Fulani adama din ce tafara tashi daga zaman ta wuce dakinta,sai fulani aishan da yaranta,sai kuma afra dake zaune tana charting gami da cin abincin ba tare data kula kowa ba.



      Sallamarshi cikin muryarshi dake cike da sarauta ta ratso falon,yanayin tafiyarsa ne kawai zai gaya maka tabbas a gajiye yake,waiwaya tayi tana amsa sallamar,fuskarta ta cika da fara'ar ganin gudan jinin nata,shima kai tsaye teburin cin abincin ya nufo,kowacce tasoma qoqarin shiga taitayinta,yayin da afra ta kasa zama ganin yaja kujera yana niyyar zama,saita yiwa kanta qiyamullaili ta miqe,badon taso ba tace

"Barka da yamma"

"Yauwa" ya amsata a taqaice,ta juya tawuce tana tura baki bayan ta tabbatar bazai ganta ba,cikin ranta tana ta jero mita,dama tasan koya amsa amsawar tashi bata wuce haka.



       Afnan da sumaira suma miqewa sukayi bayan sun gaidashi,don kowa yasan hali,sai wajen ya zamana daga shi sai uswa sai fulani aisha,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa tana tambayarsa

"Lafiya lau.....ya shirye shiryen?" Ya murxa goshinsa da tafin hannunsa

"Alhmdlh....komai ya kusa zuwa qarshe"

"Ma sha Alla" ta fada tana jin dadi har cikin ranta na yadda komai yake tafiya dai dai kusan dai dai da yadda ta tsara.



        "Me zakaci?" Uswa ta tambayeshi cikin kulawa bayan ta kammala cin nata abincin,so take kuma ta rashi ta basu waje,don tunda taga ammin na nemansa tasan zasuyi magana ne,baice komai ba sai daya gama kallon duka abincin dake wajen,sannan ya mata nuni da abinda xata zuba masa,sannan yace

"Ba mai yawa ba" kai ta jinjina,sai data zuba mishi komai ta tura gabanshi sannan ta miqe tana duban ammi

"Ammi zanje na shirya zandan fita,munyi da abban aira zan je gidan anty umma mu gaisa" kai ta jinjina mata,daga haka tasauka tashige ciki itama.



       Shuru ne ya ratsa tsakani lokacin da yake tsaka da cin abincin,fulani aisha tayi gyaran murya sannan tace

"Na aikawa sodangi da yarinyar nan passport dinsu har da ticket na komawa nigeria....zasu wuce daga can,don babu yiwuwar mu hadu,na gama tsara komai,da zarar sun sauka zasu danqata ga mahaifinta,abu daya yanzu ya rage takardarta,ka rubuta yau ko.zuwa gobe da safe,ahmad xaizo ya karba yakai musu,idan muka koma gida komai zai dora,mai martaba yayi magana kan yiwuwar fidda macen aure,nasan za maka magana kan diyar abokinsa prof,basai mun maimaita zance ba,ka san bayanin da xaka yi masa,da zarar ka gaya masa kuma abinda zai faru shine xai aika ga iyayen safwa....wannan shine mataki na gaba na rayuwarka da nake saka rai,kafin kuma zancan ci gaba da karatunka ya daidaita,muga wacce qasa yakuma kamata ka canza".



      Idanu ya daga ya kalli ammin,har yanzu kenan lokacin da zai zauna a qasarsu cikin masarautarsu baiyi ba kenan,ya raya haka cikin ranshi

"To" ya amsa mata dashi,daga haka wani shirun ne yakuma biyowa baya har zuwa sanda ya kammala cin abincin shima ya shige dakin daya rage guda daya yayi wanka ya sake fita.



       Washegari kusan dukansu babu wanda yazauna,duk yawo suka fita,sun zagaya garin na mexico sosai,hakan yasa fulani aisha bata samu sake zama da azeez ba,duk da cewa hankalinta yana kan maganarsu,saboda haka washegari da daddare ta nemi ganinsa.



       Cikin dakinta ya taddata ita dasu afnan gaba daya,suna ware wasu kaya da suka siyo,ita kuma tana zaune daga gefan gado,sanye da wata doguwar riga wadda tasha ado daga wuya hannu har zuwa gaban hular dake hade da rigar,idanunta nakan yaran,saidai kallo daya zaka mata ga mai hankali ya fuskanci duniyar tunani tashiga.



      Sallamarshi ta sanyasu dukka daga kai suka amsa,suka gaidashi,ya amsa yana nufar wani dan qaramin carfet dake shimfide gaban fulanin ta dora qafafuwanta akai

"Ku bamu waje" fulani tayi.magana dasu sumaira,sai duk suka ajjiye kayan hannunsu suka miqe suka fita zuwa falon gidan.



      "Barka da warhaka ammi"

"Yauwa barka kadai" ta amsa mishi fuskarta babu walwala,tana sanya hannunta gefanta ta dauko takarda da biro,wanda da alama musamman ta tanadesu,miqa masa tayi yabisu da kallo,kana ya kalli ammin,sai kuma yasa hannu ya karba

"Rubuta mata sallamarta,don ina tunanin gobe ne zasu koma".



     Baice komai ba saiya sadda kai saman takardar yasoma rubutu,sai kuma ya tsaya cak,don baisan me zai rubuta,baisan me ake rubutawa ba,idanun ammin duka suna kanshi,har zuwa sanda ya tsaya din,kai ya daga ya dubeta

"Ammi....bansan me zan rubuta ba,me ake rubutawa?" Fuskarta ta hade sosai kana tace

"Koma meye ka rubuta" shuru yasake ratsawa,haka kawai yakejin banbarakwai a lokacin da yake rubuta kalmomin NI ABDUL'AZEEZ ABDALLAH KAISA NA SAKI MATATA SAKI.....

Jim yayi yana qiyasta saki nawa,saki nawa nema?,maida bironshi yayi ya rubuta adadin da yake gani shine daidai,kana ya ninke takardar ya miqawa ammi,bata damu ta duba ba tunda tana da yaqinin ya aiwatar din ta amsa ta aje gefanta,kana ta dauki wuyarta takira ahmad shima ta nemi ganinsa,sannan ta dawo da hankalinta kan azeez

"Da qarfe nawa za'a fara gabatar da taron naku?,ina tunanin mai martaba zaizo,yakuma buqaci sanin yaushene ainihin lokacin,ban tunanin xaizo ya kawana ne,xaizo a ranar ya juya washegari wala'alla" Miqewa yayi yana amsawa

"Qarfe shida na yamma za'a fara" kai ta jinjina kana yasoma takawa

"Zanje ammi,wala'alla nasake dawowa,wala'alla kuma sai gobe"

"Allah ya nuns mana" ta amsa mishi,yana fita ta sauke ajiyar zuciya,tana jin wani nutsuwa da kwanciyar rai na ratsata,kullum ta Alla cikin fargaba take kan auren nan,kullum babu irin saqe saqen da zuciya batayi mata kan auren,sai gashi duk yadda ta zaci abun yazo mata a dai dai,kuma da sauqi fiye da yadda ta zata.


_uhmmm,nidai nace ba girin girin na tayi mai_ðŸ˜Å .


*********    *****   ********



       Ita kadai ahmad yasamu zaune a falon,duk bilkisu da rakiya na backyard na gidan,kusan tun daxun,batasan me sukeyi ba acan,bata takura musu ba hakanan bata nemesu ba,don ta fuskanci dukkaninsu kowa alhinin rabuwa da dan uwanshi yake,ita dinma kawai dakiya take,amma abubuwa da yawa ne cunkushe a ranta,lamarin bilkisu ya tsaya mata a rai sosai fiye da yadda ta zata.



      Lokacin daya miqa mata takardar tuni ta fahimci ta meye,haka ta dinga juyata bayan tafiyarsa,tanajin cikin jininta kamar saqon akanta yake,kamar itace bilkisu,tana jin wani nauyi da jinjina yadda zata miqa wannan mummunan saqo ga bilkisu,inama ace fulani nata dora mata wannan nauyin ba,inama ace ita da kanta ko azeez da kansa ta bari ya bata saqon,da hakan ya fiye mata sauqi,kuma an sauqaqa mata wani nauyin,tanajin fuskantar bilkisu da wannan saqon kamar wani zunubi ne a rayuwa.



      Tana tsaka da juya takardar aka turo qofar kitchen wanda yayi linking da backyard din,rakiya ce a gaba bilkisu na biye da ita,kallo daya zakawa fuskokinsu ka gane sam babu walwala,sabo turken wawa,kuma tasan dole suji babu dadi,don iya zaman da sukayi na shekarar sabo da shaquwa mai girma ya shiga tsakaninsu,sai ta aje takardar gefanta tana binsu da kallo.



      Haka ta kwana da takardar har wayewar washegari da zasu bar qasar,sam ta kasa miqawa bilkisun,hakanan batayi wani isashen bacci ba a ranar,sanin cewa tafiyar safe zasuyi,hakan ya sanya tun bayan sallar asuba bata koma ba,ta sanya rakiya tasoma.shiri,sannan ta nufi dakin bilkisu da kanta da niyyar tadata,saidai ta sameta saman abun sallah,hannayenta a sama da alama kukanta take kaiwa ubangiji,don haka saita koma da baya tana ja mata qofar dakin yadda ta ganta,zuciyarta na karyewa itama,tanajin kamar ta saki kuka.



      Sosai mama sodangin ta dinga sanyawa kanta dakiya da jarumta,hakanan ta hana rakiya shiga wajen bilkisun,don kada ta haifar mata da karyar zuciya da gazawa,ta tsareta da aiki a daki,ita kuma tashiga kitchen tana hada musu breakfas na qarshe,wanda bata da tabbacin cikin su ukun akwai wanda zai iya ci.



       Tana tsaka da aikin rakiya ta kawo mata wayarta,takuma shaida mata fulani ce ke kira,cikin girmamawa ta amsa wayar,takuma gaidata,daga can bangarenta tadora da bayani

"Ina fata saqona ya iske ku ta hannun ahmad?"

"Eh Allah ya taimakeki"

"Da kyau.....qarfe sha biyu jirginku zai tashi,zan aiko driver ya daukeku yakaiku airphort,daga can idan kun sauka akwai motoci biyu....daya zata dauki yarinyar ta sadata da iyayenta,daya kuma zata maidaku gida,banason asamu wata matsala,ki tabbatar komai ya tafi yadda na gaya miki" wani nauyi da rashin dadi taji yana ratsa zuciyarta,da gaske kenan rabuwar zasuyi?,rabuwar da har ba'aso susan gida ko matsugunnin bilkisun?,bata da yadda zatayi,don ita din ba kowa bace,a qarqashin iko da mulkinta take,dolenta ta amsa da to,kuma ta tabbatar mata za'ayi dukkan yadda tace.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 35

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070


________________________________




      Sosai ta ware idanunta da sukayi nauyi tana kallon qasar datayi shekara guda cif ba tare data rayu a ciki ba,ta cikin motar take bin ko ina da kallo,motar da take ciki ita qwal daya,daga ita sai wannan matar da taji an kira da ladingo,tun sanda suka sauko daga jirgi ba zata iya cewa ga inda su mama sodangi da rakiya sukayi ba,ta lura da haka,amma batace komai ba,hakanan bata buda baki da niyyar tambaya ba,wataqila yana cikin tsarinsu,wataqila dukka cikin irin nasu adalcin kenan.



       Kamar wadda ta warke daga makanta haka ta dinga bin qofar gidan nasu da kallo,gidan da shigarta daya kwanakinta biyu tal a ciki,gidan da take da tabbacin kowanne irin daukan hankali xaiyi an samar dashi ne bisa cinikin mutuncinta da akayi

"Mun iso" muryar driver dake gaban motar ta ratsa dodon kunnenta,ba tare data waiwaya ta dubi kowa cikinsu,ko tabi takan kayanta dake cikin motar ba ta,ta sanya hannunta ta bude motar ta xura qafafunta tafito.



       Duk da cewa dare ne,duk da cewa bata gama sanin kan gidan nasu ba,amma hakan bai hanata gane qofar shiga gidan ba,ta tura ta cikin qarfin hali ta bude ta kutsa kanta ciki.



      Bata manta hanyar falon nasu ba don haka taci gaba da kutsa kai,bata dakata ba sai data isa qofar shiga falon,sai a sannan taji duk wani rauni nata ya dawo,sai a sannan fargabar yadda zata tadda 'yan uwanta ya fado mata,sai a sannan fargaba da tsoron irin rayuwar da zata gudanar ta dawo mata,ta sanya hannunta kamar wadda zata kama maciji ko qadangare ta yaye labulen nasu.



       Hannatu tasoma hangowa zaune cikin falon qasan tiles din dake malale a falon,gefanta umaima ce da amina,hajara na kwance saman cinyar hannatun,da alamu kallo suke,don basu lura da labulen da aka daga ba.



      Daga gefe saman kujera kuma wata matace zaune,itama.kallon take,a qalla zata doshi shekara talatin da takwas,qafarta daya saman daya,lokaci lokaci tana latsa wayar dake riqe a hannunta.



      Wasu hawaye taji masu dumi sun ciko mata idanu,ko yaya suka rayu tsahon lokacin?,ko yaya sukaji lokacin da babu ita?,ko yaya rayuwa ta kasance musu?.



       "Ta ina ake shiga?" Taji an fada daga bayanta,data waiwaya sai taga ladingo ce janye da akwatunanta,maida idanunta tayi cikin falon,ta qara taku ta saka qafafunta a ciki,bakinta dauke da sallama wadda take fitowa da qyar.



      Dukkaninsu kamar an jona musu schoking suka daga kansu kusan lokaci guda,hakanan miqewarsu cikin tsananin mamaki wanda lokaci qanqani ya juye zuwa zallar farinciki,kana suka fara rige rigen isowa gareta,duqawa tayi a gabansu ta hadesu gaba daya zuwa jikinta,suka saki kuka kusan lokaci daya.



      "Meye haka lafiya?" Matar dake zaune saman kujerar ta miqe tana tambaya gami da binsu da kallo,fuskarta akwai alamun rashin sanin wacece bilkisun,babu wanda ya iya tanka mata a cikinsu saboda kukan da sukeyi,ladingo ce ga dubeta ta soma gaidata,ta amsa tana son jin qarin bayani,kafin suce komai umma katti ta shigo falon

"Ke hannatu,kukan me kukeyi haka?,kuda waye kuma?" Cak ta tsaya ganin bilkisu duqe a gabansu,ta waro ido tana cewa

"Mai gado?,saukar yaushe?,yaushe kika zo?" Kai kawai ta daga ta kalli umma kattin,sai taga ta sauya sosai,ba kamar lokacin data barsu ba,maganar ladingo ce tayi kutse cikin tambayoyin da take jerowa bilkisun

"Ko xamu samu damar ganin mai gidan?" Tace da umma katti,don ta fuskanci kamar ita tafi wayewa da gidan akan wadda ta taras a falon.



      Duban ladingo tayi ta gyada kai

"Eh bari ayi masa magana" daga haka ta juya zuwa wata qofa,tana tafe tana waiwayowa tana sake duban bilkisun harta shige.



        A falonsa ta sameshi yana zaune yana zuba lomar tuwon shinkafar da ladi tayi da take girkinta ne umma kattin tashiga,har ladin ta daga kai xatayi masifa sai kuma saqon datazo dashi ya sanyata yin shuru

"Kazo ga maigado ta dawo" hakanan yaji wani faduwar gaba ta saukar masa,taste din abincin ya canza masa

"Na shiga uku,tofa" ya furta a sarari kuma a hankali,itadai umma kattin gaba tayi takoma zuwa falon don ta kashe qwarqwatar idanunta,taga meye zai faru,cikin yatsina fuska ladi tace

"Wai dama da gaske shekara dayar zatayi su dawo da ita?" Waiwayawa yayi.ya dubeta ba tare daya gane ma'anar tambayar tata ba,sannan ya miqe kawai yana goge hannunsa ya dauki hularsa dake gefe yadurfafi falon.



        Yana shiga sautin kukansu yasoma sauka a kunnensa,saiya hada rai ya tsaya a kansu yana dubansu

"Wanne irin shashashanci ne wannan?,meye haka ke me gado?,ba zaku godewa Allah ba daya hada fuskokinku saiku xauna kuna kukan banxa dana wofi?" Janye jikinsu suka fara suna qoqarin tsaida kukan nasu,saidai ita bilkisun nata hawayen sunqi daina zuba.



       Cikin girmamawa ladingo ta gaidashi sannan tasoma magana

"An umarceni dana danaganata da mahaifinta,kamar yadda akayi yarjejeniya bayan shekaru guda,to lokaci yayi,saboda haka gata nan kamar yadda fulani ta umarceni,shaidarta tana hannunta,dukkan abinda suka mallaka mata gasunan sun zama nata,tun daga lefe dukiyar aure dama komai da komai,hakanan sun bata dama,daga nan zuwa shekara guda duk abinda take da buqata a matsayin sallamarta ta qarshe ta fadi dukka adadin za'a bata....saidai fulani tace na tunasar daku yankewar alaqa ta har abada....." Wani abu ya soki zuciyar bilkisun da har ta gaza daurewa ta dubi ladingo,duban da yasa bata iya qarashe bayaninta ba,har abada kuma komai lalacewa ubanta ubanta ne,wato xallar rashin adalci,wulaqanci da kuma qarfa qarfan har yakai matakin da za'a dinga aikama mahaifinta gargadi ta hanyar 'yar aike kuma baiwa?,duk da cewa shiya siyama kansa koma meye,amma abun yasoma yiwa kunnuwanta muni.



      Tsam ta miqe tana riqe da hannun aminatu da umaima,qasa qasa tace

"Kaini dakinku" da saurinsu sukayi gaba tana biye dasu,har zuwa dakin data zauna wancan karon lokacin da ake yinin bikinta,shine babu abinda ya sauya a ciki,saidai atsaftace yake hakanan komai yana shirye bisa tsari da doka,tasan za'a rina,dama bata taba tsammatar qazanta daga wajensu ba,saboda ta yadda da irin hoton data yi musu ma zallar tsafta da nutsuwa,saita qarasa zubewa anan tana sakin wani sabon kukan suna tayata,don suma bai ishesu ba,hannatu ce kawai bata biyi bayansu ba,wanda bata lura ba,har sai zuwa lokacin da zuciyarta ta gaya mata kukan ya isa haka,don bashi da wanu magani,face sake sanya qannan nata da zaiyi suma cikin wata damuwar,dole ta yiwa kanta waigi,ta goge nata hawayen ta lallashesu,kana ta shiga bandakinsu ta daura alwala ko zataji sanyi cikin zuciyarta.



      Tana fitowa daga bandakin hannatun na shigowa janye da akwatunanta,saita dauke kanta don ko ganin akwatunan su kansu batason yi takoma kusa da amintu ta zauna tana kallon yarinyar tana dan murmushi duk cikin qarfin hali,tadan qara girma da wayo sabanin sanda ta tafi.



      Hannatu ce ta qaraso ta dora mata wani abu dake nannade saman cinyarta tare da qaramar jakarta,saita kalli abun da alamun tambaya

"Kudinki ne da suka baki daga can,matar da kuka shigo tare ta baiwa baba,yace nakine bazai karba ba,baba ladi nata qoqarin sanyashi ya karba har tana yunqurin amsa nina karbo....karkiqi amsa don Allah yaaya,haqqinki ne,nakine bana wani ba,wanda akaci a baya ya isa,Allah ya amfana,idan ma kikace ba zaki karba ba babu abinda zai sauya,su zasu amsa su kuma murqushesu suci gaba da rayuwarsu ba tare da komai ya faru ba" idanunta taf da qwallar data samu ta tsayar take duban hannatun,tun daga yanayin jiki da kalamanta sun nuna hannatun bata da bace,hankali ya soma gameta,ba shakka ta sauya qwarai,ko nauyin daya hau wuyanta bayan tata tafiyar ne yasa hankalin yayi hanzarin zuwa mata haka lokaci guda?duk da dama tazarar shekara biyu rak ta bata,roqon datayi mata da qoqarin amso saqon da tayi tun daga falon,idan tace ba zata karba ba kamar ta watsa mata qasa a ido ne,don haka cikin hikima tace da ita

"Ganinsu ne banason yi hannatu" da sauri ta daukesu daga kan cinyarta

"Bazan takura miki ba yaaya,amma zanta ajjiye miki su har sanda kike da buqatarsu" ta qarashe maganar tana miqewa zuwa cupboard dinsu ta bude can sama ma'ajiyar kayanta ta cusa su sosai.



       sai a sannan ta soma duban dakin loko da saqo,karon farko hauwa'u ta fado mata

"Ina kulu ta,ita kadai ce ban gani ba?" Ta ai qarshen tambayar tana maida idanunta ga hannatu,sai taga yanayin fuskarta ya sauya sanda take dawowa mazauninta data tashi,jin bata amsa mata ba saita sake duban sauran,suma dai kamar hannatun kowa fuskarsa ta nuna zallar damuwa,gabanta yayi mummunar faduwa,zuciyarta ta qiyasta mata wani mummunan abun ya samu hauwa'un suka boye basu gaya mata ba,cikin rawar murya tace da hannatu

"Hannatu,meya sameta baku gayamin ba?" Kai ta girgiza tana duban bilkisu

"Yan uwan mamanta sunxo sun tafi da ita"

"Ya Allahu" ta fada tana dafe kanta,wataqila rabuwarsu da hauwa'u kenan har abada taxo?,yan uwan mamanta?,yan uwan maman nata da sai afi shekara biyar ba'asan inda suke ba?

"Yaaya,hauwau na kuka tana cewa ba zata bisu ba sai yaaya maigado ta dawo,sai kin dawo kin sata a makaranta yadda kika ce,saikin dawo ta ganki amma haka suka dauketa,sunyi dauki ba dadi da baba,amma suka nuna mishi halinsu na fulani,saboda da zafinsu da shirinsu sukazo,tana kuka muna kuka haka suka jata suka tafi,kiran sunanki kawai take,munfi sati bama iya cin abinci,munfi sati muna mafarkinta,daga qarshe dole muka haqura saboda babu yadda zamuyi,amma kullum sai munyi zancanta,har yau muna kewarta,ko da kika ganmu xaune a falo ma zancanta muka gamayi kenan,sai gaki kin shigo".



       Wani sabon tashin hankalin taji ya rufto mata,ji take kamar jininta ya hau,hauwa'unta,yarinyar da duk cikin qannenta taficin buri akan tazo ta ganta,saboda tasan tafi kowa qulafucinta,kukan dai da bataso tayi shiya sake dawo mata,don bata da wata hanya ta huce takaicinta da baqinciki idan ba kukan ba.


*****   *****   ******   *****




      Tun a mexico ammi fulani aisha ta shirya masa walima ta musamman,wanda tasamu halartar familynshi na kusa sosai,musamman dangin mamamshi daga mali,har safwa ma wannan karon sai data zo,da tarin kyaututtukanta na murnar tayashi karatunsa,wanda ita saura shekara guda ta rage mata ta kammala nata karatun,walima me kyau da qayatarwa akayi,kusan kwanakin duka cikin sabga yake,sai washegarin randa aka kammala walimar sannan yasamu huta,ya kulle kanshi a daki ya kashe dukka wayoyinshi.



       Saidai tun baccin baiyi nisa ba yasoma mafarkai,hakan ya tilasta masa tashi,yayi addu'a ya gyara kwanciyarsa,saidai baccin ya gaza sake samuwa kwata kwata,haka dole yanaji yana gani yaci gaba da juyo saman gadon,daga qarshe ma wanka yayi yasake ficewa,duk da hutun da yake da buqata.


******    *****   *****   *****



     Tana zaune daga gefan gadon hauwa'u wanda a yanzu ya zama nata tun bayan dawowarta gidan,saboda taqi nata dakin kamar dai wancan karon,sanye take da rigar bacci doguwa mai dan kauri,sai wani qaramin dan kwali data rufe kanta dashi.



      Misalin bakwai da rabi ne na safe,dukka yaran na zaune a gabanta sanye da unifoarm suna karyawa,wanda ruwan tea ne da bread,zata iya cewa a yadda tasan rayuwar gidansu a da,yaran sun samu 'yanci da sauyi kaso sittin cikin dari maimakon daa,a yanzu akwai abinci a gidan dai dai gwargwado,safe rana da dare,babu zaman yunwa,hakanan baban nasu ya qoqarta sakasu a makarantar boko mai sauqin kudi,dama already ta barsu suna zuwa islamiyya,kuma basu fasa zuwa ba har kawo yau,basa yawo cikin tsumma kamar yadda sukeyi a baya,saidai kuma kusan babu mai kulawa da rayuwarsu,ba'a tsangwamesu ba tsangwama mai yawa kamar baya ba,hakanan babu mai tattalinsu kamar yadda suke dai a baya,umma katti ta kama yaranta sune a gabanta yadda dai rayuwar take a baya,mama ladi da amaryar da bilkisun tazo ta taras ya rangado wadda taji suna kira da anty sukam ta mijinsu suke ko ince ta kansu,domin a zahiri kowacce na nuna mishi tattali ne,yayin da kuma a badini kowaccen kanta da rayuwarta take qoqarin ginawa,suna hangen dan abun hannun malam bilyan,sannan kuma suna hasashe da lissafin basu haihu dashi ba,basu da kowa dashi,to ba shakka idan ta tashi barewa dasu zata bare.



        Tana zaune tana dubansu suna 'yan hayaniyarsu har suka gama,hannatu ta kada kansu don wucewa makaranta,ta laluba jakarta don basu dan abun kashewa saidai babu komai a ciki,saita buraci inama ace tana da wani abu da zata basun dazai sake yawan farincikinsu,hakanan ta musu fatan dawowa lafiya suka amsa cikin cikin walwala suka fice,don wannan rayuwar da suke ciki gani suke sun samu dukkan komai,tunda basu saba irinta ba,a baya sun rayu babi ci sha suttura ko muhalli mai kyau daga mahaifinsu,a yanzu kuwa dukka sun samu,don haka a nasu ganin basu rasa komai ba.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 34


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




     Ajjiye wayar tayi tanajin wani daci da zallar rashin adalci cikin lamarin gaba daya,a iya sanin data yiwa fulani aishan macace mai tausayi jin qai da kuma kyan hali,batasan meya sauyata haka lokaci daya ba,tayi mamakin yadda tabari BURI gami da ALWASHIN watsa aniyar maqiya yakeson sauya halayya da dabi'arta,ta dauki buri mai tsaho da girma akan azeez fiye da yadda aka santa,duk da cewa dama can mutum ce mai son 'ya'ya,amma duk da haka tana da kyakkyawar halayya da dabi'a wadda ta siya mata soyayya mai girma a zukatan al'umma,sai gashi yanzun tana wasu abubuwa da suke baiwa sodangi mamaki,halayyar da sam tasan ba tata bace,rashin adalci,rashin tausayi da kuma nuna halin ko in kula akan kowa face diyoyin cikinta,indai hakane kuwa maqiya sun cucuta,dafin magauta ya ratsata,ya mata kuma tasiri da har yafidda kyakkyawar halayya daga cikin jininta ya sauya mata wata.



      Kamar yadda ta zata din kuwa babu wanda ya kalla abincin ma a cikinsu har ita kanta,kusan kowa zuciyarsa babu dadi,duk da cewa wani abu yau ya bata mamaki,ta gaza karantar yanayin da zuciyar bilkisu ke ciki a yau,farinciki ko akasin haka?,wani irin emotion take gani kwance saman fuskarta data gaza tantance a wanne bigire zata ajjiyeshi?.



      Kamar kazar sa qwai ya fashewa a ciki take shiryawa,ita kanta batasan a wanne matsayi ruhi da zuciyarta suke ciki ba,abinda ta sani kawai shine,ta tashi da qwarin gwiwa bayan ta raba dare tana tunani tare da qoqarin samarwa kanta mafita,ta sanyawa kanta wani yaqini da jarumtar amsar duk wani nau'in rayuwa da zata tunkareta.



       Tana shiryawa idanuwanta na sauka sashe bisa sashe na dakin,tana tuna dukkan yadda rayuwarta ta wakana cikin gidan tsahon shekara guda,ta runtse idonta lokacin da tunaninta yakawo ranar daya amshi mutuncinta,take dukkan wani qwarin gwiwa data tattarowa kanta ta tarwatse,saita sulale a wajen saman gwiwoyinta tana rufe fuskarta da tafukan hannunta,tana jin wani irin abu yana tasowa daga qirjinta can cikin zuciyarta,ambaton sunan Allah tasoma yi,wanda hakan ya taimaka mata ta daidaita tunaninta,saita miqe a hankali,tazauna gefan gadon,ta nutsu nadan wani lokaci sannan taci gaba da shirinta.



       Sanda take sanya kaya take kuma agogo wanda yake nuna mata mintuna ashirin kacal suka rage su fita daga gidan zuwa filin sauka da tashin jiragen sama don konawarta tushenta,qarar qararrawa taji da alama akwai mai buqatar shigowa gidan,dukka saita tattara hankalinta,har zuwa sanda taji.mama sodangi ta bude qofar,muryar wata mata taji wadda bata santa ba,saidai tana iya jiyo kiran sunanta da mama sodangi tayi da ladingo,daga haka bata kuma jin komai ba saita qara hanzari ta kammala shirinta gaba daya.



       Sake duban agogo tayi,minti goma ya rage musu,tana dauke idanunta ana turo qofar dakin,mama sodangi ce,idanunta kan bilkisu,cikin wani irin yanayi daya dasawa bilkisu fargaba da faduwar gaba,wadda ta sanya ta gaza ci gaba da kallon maman,ta sadda kanta qasa,har zuwa sanda ta qaraso inda bilkisun ke tsaye.



       Kamar wadda batasan meya shigo da ita dakin ba ta tsaya tana duban bilkisu,a hankali ta lalubo hannunta ta sanya takardar,hakan ya sanya ta daga kai tana dubanta,kai mama sodangi tasoma girgixa mata,idan ta lura dakyau ma kamar qwalla ce cike a idanunta,dukkansu babu wanda ya iya cewa da dan uwanshi komai aka sake shigowa dakin,sallamar ladingo ta karade dakin,maimakon mama sodangin ta amsa,sai kawai tasaki hannun bilkisun ta juya da sauri tafice daga dakin,ita kuma ta rakata da ido har ta bacewa ganinta,sai a lokacin ta ankara magana ladingo ke mata,ganin alamun bata ji ba yasanyata maimaitawa

"Idan babu damuwa zan soma debe kayanki na fita dasu,driver yazo za'a saka cikin mota" bata iya cewa da ita komai ba,don ji take kamar bakinta bai taba magana ba bare tasan ta yaya zata amsa mata,qafafunta tamkar lawashi saboda rashin qwari,tana jinta kamar mai tafiya a wata duniya ta daban tasoma nufar qofa don barin dakin ba tare data waiwaya tasake duban dakin ba,ba tare data tsaya ta duba ko akwai abinda ya kamata ta dauka ba,babu komai cikin hannunta sai takardar datake da tabbacin ko ba'a gaya mata ta meye ba tasan ta meye,har takai falo sannan taji kamar qafafun nata ba zasu iya qarasawa da ita waje ba,don haka ta lalubi kujera tazauna donta ragewa kanta nauyin da taji dukka gabban jikinta sun mata.



      Kamar a inuwa taga shigowar wasu matasa,wanda da alama ma'aikata ne,kamar a inuwar taga ana fidda dukka kayan gado da aka qawata dakin dasu,eh kamar inuwa zata ce,tunda hankalinta bai jikinta bare ta tantance inuwa ne ko zahiri ne.


       Tamkar mutum mutimi haka take zaune cikin falon gidan,daga kunnuwanta har idanuwanta basa iya ganin komai,basa kuma gane kome face mai rayuwarta ta gaba zata haifar mata.



      Hannunta na dama dunqule yake da takardar data zamto tamkar wani mubudi ne na rayuwarta ta gaba,takarda ce da saqon dake ciki take jinsa daidai da saqon ranar mutuwarta,riqonta kawai zafi yake mata tun daga tafin hannunta har zuwa qwaqwalwa da zuciyarta,yakuma zarce zuwa ilahirin jikinta gaba daya.



     Duk da cewa tana tsammanin zuwan ranar,duk da cewa tasan cewa lallai lallai komai daren dadewa irin wannan ranar tana tafe,takuma shirya zuwanta tun daga ranar da aka soma lissafin kasantuwar kwanakin har zuwa randa zata risketa,saidai batasan me yasa ba,meye dalilin data tabata har haka ba,batasan meye dalilin da jikinta da zuciyarta suka girgiza har haka ba,sabone?,ko kuwa tunanin me gobenta zata haifar mata ne?,meye matsayinta meye sakamakon rayuwarta?,wanne sabon shafin zata bude?



      Karo na qarshe ladingo tafito tafito da akwatinta da take jin shine abu na qarshe a cikin dakin data mallaka,ta qarasa inda take aje musu kayansu shima ta ajeshi,ta qarasa gaban bilkisu ta tsaya cikin rusunawa

"An gama fitar da komai,ance jirgin qarfe sha biyu zamu bi,yanzu haka mai motar dazai daukemu zuwa filin jirgin yana kan hanya...."



       Qwaqwalwarta tajiyo wani sashe na maganarta,saidai bata fahinta duka ba,cikin jimla guda ta tattara maganartata,qwaqwalwarta ta sake aika mata da saqon

"Tafiya zakuyi,zaku koma nigeria,zaki kuma cikin gidanku".



      Tamkar wadda ake bawa umarni sai kawai tamiqe,cikin qarfin hali tasanya hannu tagyara zaman qaramin hijabinta,kana tasoma takawa a hankali kamar mai tafiya saman qayoyin da aka shimfidawa hanyarta tayi hanyar bedroom din daya zama shine matattarar dukka wani tarihi nata.



      Idan ka kalleta a sannan zaka iya rantsewa tashigo dakinne tana son fayyace da ainihin qasar wanne waje aka gina dakin saboda yadda takebin kowacce kusurwa ta dakin da kallo sama zuwa qasa da kallo har na tsahon wasu daqiqu.



       Sauke idanunta tayi awani sashe can na dakin,tasoma takawa a hankali kamar wadda maganadisu yake janta zuwa arean,tasa hannu tasoma shafa wajen,yana yawan tsaiwa a wajen duk da cewa cikin duhu take ganinsa,yana son wajen sosai duk da bata taba ganinsa muraran ba,saita sake matsawa da jikinta wajen,ta lumshe idanunta tana shaqar daddadan qamshin da wajen yake fitarwa,tabbas qamshinsa ne,abinda duk cikin rayuwar datayi mai kama da mafarki tafi riqewa,saikuma qaqqarfar ajiyar zuciya wadda tasaka dukkan gabbanta suka saki,hawayen da uta kanta batasan na meye ba suka ziraro daga idonta guda daya.



      Kamar wadda aka tsikara tajuya da sauri tanufi qofar ficewa daga dakin,dakin da zuwa yanzu yakoma zallar kangonshi babu komai ciki tamkar wasu rayuka basu taba wanzuwa a ciki ba,batasan inda kayan suka koma ba tunda dama ba mallakinta bane.



      Girgiza kanta take dasauri tana gayawa kanta,tabbas bata tsira da komai ba,babu abinda ta tsira dashi koda kuwa hoton fuskarsa ta zahiri ne face ragowar qamshinsa daya barwa hancinta da qwaqwalwarta tabonsa.



       Cak ta tsaya tana duban gabanta,kana ta duqa a hankali takai hannunta tadauki zoben daya dauki hankalinta qwarai,zobene da tasha ganinsa a yatsunsa,abun guda daya tak datake iya banbance dangane da duk wani abu daya shafeshi,cikin sauri tadauki zoben ta damqe a hannunta kana cikin sassarfa tafice daga dakin ta zarce da ficewa daga gidanma gaba daya don tanaji cewa izuwa yanzu itama ya kamata ta yanke dukka sauran abinda yayi saura.



        Tanajin ladingo na mata magana saidai bata ko tsaya ba bare ta waiwayo ta dubeta,fatanta shine ta raba kanta da komai daya wanzu a shekara guda,ta yanke dukkan wani abu dake da alaqa da shekarar........



      **********    *****   ********



       Tana zaune daga guri na musamman da aka tanada saboda xaman baqi,daga gefanta kuma maimartaba ne sarkin qasar kaisa,daga hannunshi da nata hannun yaransu kowanne zaune a mazauninsa,dukkaninsu sun bada hankalinsu dari bisa dari kan taron da ake gudanarwa,farinciki ya lullube zuciyar kowannensu na ganin yadda dansu kuma yayansu yaketa karbar lambobin yabo da girmamawa kala daban daban.



       Kamar yadda a tsarin shiga kyan halitta,kwarjini da kuma wata irin ginshira tasa ya fita daban da sauran daliban,hakanan ma ta fannin hazaqarsa suna gamida shahararsa cikin makarantar,farinjininsa daga wajen malamai har zuwa dalibai.



       Fuskar fulani aisha tamkar gonar auduga,zuciyarta fes kamar dutsen qanqara,har hakan ya gaza boyuwa ya bayyana saman fuskarta,jerarrun fararen haqoranta irin na azeez sun bayyana kansu saboda irin murmushin da takeyi,ko iya yanzu ta tabbatar da cewa azeez din yayi zarra,yakuma fara taka irin matakin da takeso ya taka,tauraruwarsa ta haska ta danne ta kowa,sunansa ya shahara yakuma fantsama ko ina,inama ace adama tazo wajen batayi qaryar bata jin dadi ba?,koda yake koda adama batazo ba,ta tabbatar afra zata bata labarin dukkan abinda ke faruwa,uwa uba akwai waya a hannunta tana nadar komai.



       Wasu qwallar farinciki ne suka so fitowa daga idanuwanta a lokacin da aka buqaci mahaifinsa ya taso makaranta zata girmamashi saboda irin gudunmawar daya bayar,da kuma kyakyyawan misali daya baiwa dalibai,hakanan yasa makarantar tasake samun daukaka da suna,bayan maimartaba ya isa wajen sai azeez din ya nemi alfarmar mahaifiyarsa ta taso,sosai ta dinga jin farinciki,tana jin cewa taqi kadan ya rage burinta ya gama cika.



      Awa biyu cur akayi kwashe ana gabatar da taron kafin a kammala,har yanzu farinciki yaqi barin zuciyarta,cikin sigar xolaya mai martaba ya dubi fulani aisha

"Ke ko 'yar karan nan ma babu,kinga fuskarki kuwa kamar gonar qanqara?" Cikin dan jin nauyinsa tadan sunne kai kadan tana dariya qasa qasa kana tace

"Bazan iya boye farinciki na ba,don abdul'azeez bai bamu kunya ba,yayi dukkan abinda yakawoshi qasar nan,harma fiye da abinda muka zata" kai.ya jinjina shima yana sake jin dadi,alfahari da tilon dan nashi namiji yana ratsashi.



       Daga mazaunin dalibai maza kuwa kamal ne zaune kamar ruwa ya cishi,duk wani motsi na azeez din yana kan idanunshi,jin zuciyarsa yake kamar zata babbake ganin yadda yaketa samun lambobin yabo daga bakunan malamai kala kala,ya tabbatar wannan labarin bamai dadi bane akunnen mahaifiyarsa,ya rasa kuma meye hana fulani adama zuwa wajen,bayan mom ta shaida mishi tana qasar,kuma zata zo.



       Can wani sashen kuma daga rukunin mazaunin daliban dai minal ce zaune,ita dinma idanunta hankalinta da tuaninta yana ga azeez din,wani daci take ji cikin ranta da zuciyarta na yadda tayi loosing oppurtunity dinta,na yadda ta rasa azeez din,duk da ta taki babbar sa'a da bai sake tada case din ba,bai kuma sake nemanta kobi ta kanta ba,duk da cewa a hakan tana boye kanta daga gareshi,kada wataran su hadu ya tuna allura ta tono garma,wai shin me zatayi azeez ya sota kamar yadda take buri?.



      "Guy din nan ya gama haduwa,komai yaji,Allah ya masa komai" ta tsincin furucin na fitowa daga bakin wasu 'yammata dake zaune gefanta,saita waiwaya tana dubansu,ji tayi wani abu ya tokareta,kamar ta miqe ta shaqesu ganin yadda suke binsa da kallo duk inda ya motsa kamar wasu tsaffin mayu,dole ta janye idanunta daga kansu tana jan tsaki mai qarfi a fili,wanda sai daya sanya qawarta ta waiwayo tana dubanta gamida tambayarta,saidai bata bata amsar komai ba.



      Lokacin tashi nayi kamar yadda aka tsara a rubuce aka qarqare komai,a nan dalibai suka soma musayar adress da lambobin waya gamida daukar hotuna a tsakaninsu.



      Haka ce ta faru ga azeez,mutanen dake son daukar hoto dashi....musayar lambar waya da amsar adress suna da yawa,harda 'yan shishshigi,harda wadanda shi bai taba hulda dasu ba,iya mutanen da suke selective a wajensa ya tsaya sukayi wadan nan abubuwan ya qara gaba wajen da motocinsu ke fake ya barsu a wajen.



       Me martaba ne cikin motar,sai ammi a ciki,sauran duka suna wata mota ta daban,yana shiga maimartaba ya dubeshi cikin murmushi

"Wadan can mutanen da suka jiraka fa?" Sai daya waiwaya ya dubesu ta window sannan cikin girmamawa yace

"Allah ya taimakeka.....na gama sallamarsu" murmushi kawai yayi ba tare daya sake cewa komai ba,ya riga da yasan hali xanen dutse,har yanzu halayyarsa tana nan a jininsa,tun zamanin shekaru qananu har yanuzu da aka doshi shekara ta ashirin da shida.



       Lokacin da drivern ya tada motar suka fara tafiya mai.martaba yayi gyaran murya,kana cikin sautin muryarshi dake nuna tsantsar hikima,dattijantaka da kuma kamala yace

"Babu shakka duk baiwar da dan adam yaga ubangijinsa yayi masa....yayi masa itane bawai don yafi kowa ba,a'ah,yayi masa itane saboda shi din mabuwayin sarki ne,yakanyi abinda yaso a sanda yaso a kuma lokacin da yaso,dukkan wata baiwa a rayuwa tamkar jarrabawa ce ga bawa,yakan iya cinyeta,yakan iya kuma afkawa zuwa ga halaka idan baiyi takatsantsan ba,abdul'azeez...,zuwa yanzu girma ya soma hawa kanka,tunda gashi har ka soma aje wani mataki na karatu,shekarunka kuma sun bar ashirin da biyar sun soma tsalle zuwa da shida,ina fatan zaka zama mai nutsuwa da nazari a duk yanayi matsayi ko matakin daka samu kanka,ka zama cikakken mutum mai kamala da adalci,sannan kuma adali a duk wani sha'aninsa,hakan zai baka dama ta gina inga tacciyar rayuwa,ka samu iyali na qwarai,ka auri matar da bazata zalunceka ba kamar yadda kaima ya haramta ka zalunceta,wannan shine matakin rayuwarka ta gaba" hakanan yaji wani irin yanayi ya shigeshi,cikin girmamawa ya furta

"In sha Allahu".



      Murmushi fulani aisha tayi tana qoqarin danne yanayin data shiga

"Allah ya taimakeka nasihar tun yanzu?,da ka bari ai mun qarasa gida kun huta tukunna sai kuyi xama na musamman" dubanta yayi shima yana murmushi

"Kinsan hausawa sukace da zafi zafi akan bugi qarfe,kuma kowacce magana akwai muhallin daya dace ayita" kai ta jinjina kawai tana kau da kanta gefe,sai takejin kamar wata qusa ya kafa mata.



     Tans jinsu suna magana jifa jifa da azeez din har suka qaraso gidan,wanda babu kowa ciki sai fulani adama da fafur ya qirqiri ciwon qarya,saboda baqinciki da bacin rai mai martaban da kanshi ya tako zuwa bikin,saboda tsantsar soyayya d kulawar da yakewa azeez din kenan?.

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 37

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

____________________________



      A duban farko idan kayi masa,zaka tsammaci wani ciwon ne yake damunsa,saboda yadda yaketa safa da marwa cikin dakinsa,daga wancan bangon zuwa wannan,lokaci lokaci yakan sanya hannunsa saman sumarshi ya shafi kansa,yanajin qwaqwalwarsa tana matuqar daukar dumi da caji.



      "Why?,me yasa?,me yasa?,me yasa ta kasa barin tunani da qwalqwawarsa?,me yasa tun bayan nan bai taba kwanciya peafully ba ya tashi haka?,me yasa duk wani motsi nashi second ko minti saita ratsa ta ciki ta tuna mishi da kanta?,yana tsammanin komai is over kuma komai ya wuce,amma baisan me yasa wannan ya kasa wucewa ba,me yasa wannan memory din ya kasa shafewa ba.



        A hankali ya maida akalarsa zuwa bandakinsa,ya tsaya gaban famfo ya watsawa fuskarsa ruwa mai sayi sosai,har sai dayaji zuciyarsa na kwanciya,sannan ya jawo daya daga cikin qananun towel din dake jere raras ya goge fuskarsa da kyau ya wurgashi gefe ya fito.



       Yana shirin komawa yazauna don ya ragewa kansa kai da kawon da yake kamar sojan dake fareti yaji ana knocikin qofar dakin nasa,ko waye ma yasan wani makusancinsa ne kuma mai muhimmamci,tunda har ya ratsa dukka falukan ya qaraso bedroom dinsa,don haka yana daga tsayen ya bada damar a shigo.



      Abdulrashid ne,wanda shima cikin satin ya kammala nashi karatun ya dawo qasarsa garinsa kaisa,idanunshi saman azeez yana dubanshi bakinsa dauke da sallama,saiya waiwayo shima yana dubanshin lokaci guda kuma yana amsa sallamar.



      "Ya na ganka haka ko shiryawa bakayi ba?" Kanshi ya daga yaduba lokaci sannan yaja qaramin tsaki,ya soma takowa bakin gado inda abdulrashid ya yiwa kansa mazauni

"Nayita kiranka kafin na shigo ina wajen ammi,itama ta kiraka amma no answer....."

"Bacci nayi" ya amsa mishi a taqaice yana miqa hannu ya janyo wayarsa dake gefan filon daya tashi akai,abdulrashid ya bishi da kallo sanda yake buda wayar yana duba miscal din dake ciki

"Ammi ta gayamin cikin kwanakin nan kamar kana cikin damuwa?....what's going on?" Ya tambayeshi still yana kallonshi,saidai shi hankalinsa na bisa waya,miscal dinsa dana ammi ya soma tararwa,saina wani abokin karatunsa sannan na safwa,yakuma sakin tsaki kana ya maida wayar ya aje,banda ya mata alqawarin zuwa yau din,baijin akwai abinda zai fiddashi,hakanan yakejinshi cikin mode din da baison magana da kowa

"Just thirty minutes,yanzu zan shirya" ya fadi a maimakon ya amsa mishi tambayarsa yana nufar bandakin,sake dai binsa yayi da kallon,ba shakka akwai abinda yake damun nashi,duk da dama tsabar miskilancinsa yasa idan baku dade ba ko baka karanci yanayinsa ba zaka tsammaci ko yaushe cikin damuwar yake.



       Sai daya shafe kusana wanni guda sannan yasoma shiryawa cikin wani tattausan yadi mai kyau da tsada,wanda yabi lafiyayyar fatarsa ya kwanta dakyau,yana cikin fesa turare abdul yasake masa tambayar,saidai baice mishi uffan ba,alamun dake nuna baida sha'awar su tattauna kenan,sai daya gama sa'annan suka fito gaba daya.



      Abdul dinne ke tuqa motar,tuqi yake cikin nutsuwa,saboda shikam yanayin garin ya masa dadi sosai,saidai shurun dake cikin motar yayi yawa,a hankali yace

"Zuwanka kenan fa na farko tunda ka dawo,babu wani abu da za'a kai mata" tsaki yakuma ja sannan yace

"Share kawai letter".bagarar dashi abdul din yayi yaci gaba da tuqinsa.



      Ba'a jima ba dai still yakuma sakin wani tsakin,abdul.ya taka burki da qarfi uana dubanshi cikin bala'i bala'i

"Kaga malam,bafa zaka zo ka sanyani a gaba da tsaki ba hakanan babu gaira babu dalili,ban maka uban komai ba,ban kuma san meke damunka ba". A maimakon ya amsa mishi saiya bude murfin motar da wani irin hanzari ya fice kawai yana buga mishi qofar,binsa yayi da kallo baki bude,tsahon minti biyu ya tuna suna saman titi ne ashe bawani parking din arziqi yayi ba,don haka ya balle murfin motar ya biyo bayanshi.



      Saman motar ya sameshi zaune abinsa dafa'an,kamar ya manta suma saman titi ne,ga motocin dake zuwa wucewa sunata saka musu haske dake nuna wrong parking sukayi,kuma koda yaushe zasu iya hada goslow ma

"me kake haka?,baka gani saman titi muke?" Wani kallo ya masa,kana ya dauke kansa baice masa komai ba

"Oh god" abdul ya fada a ranshi,baison wannan side din na azeez,indai yasoma haka to 'yan taurin hade da uban miskilancin suna kusa kenan,zaka sha wuya idan ya taurare.



        Waiwayawa yayi yadubi titin,da gaske sun fara hada cunkuson ababen hawa da yawancinsu suka soma zuba uban horn,ya dawo da kallonshi kansa

"Ka gani ko?,pls ka sauko mu wuce muna sake bata lokaci anan" sai da yayi kamar bazai magana ba sannan yace

"U better keepquite,kar ka sake damuna"

"Naji" ya amsa mishi a kaurare yana jifansa da harara,wani kallo shima yayi masa sannan ya sauko yakoma cikin motar.



       Kansa jingine da kujera idanunsa a lumshe,yanajin sanda ya tashi motar suka soma yin gaba,bayajin koda yaje wajen safwa zai iya tabuka abun arziqi,may be ma ya qare da nuna mata halinsa,don haka yace

"Maidani gida" kallonsa yayi sannan yadauke kai yaci gaba da tuqinsa

"Kai din banza,baka isa ba Allah,minti biyar yayi yawa mu isa,ka sanya mata kuma rai,sannan yanzu kace na maidaka gida" jin abinda yace ya sanyashi yin shuru bai sake cewa komai ba har suka isa.



          Ta juya ta kalli kanta a madubi sau babu adadi,ita da me aikinsu ne wadda taketa biye mata,kwalliyar data kira takanas akazo har gida aka mata take dubawa,yau ranar ta kusamman ce,karon farko tunda ya dawo zaizo wajenta

"Halima inane baiyi ba don Allah?"murmushi tayi

"Ai tako ina kwalliya tayi,ina da tabbacin shi kansa idan ya ganki yau saita Allah,saiya susuce fiye da yadda kike tsammani" dadi ya kamata,tayi dan tsalle gami da ihu tana mata godiya,dai dai lokacin da mahaifiyarta ta leqo dakin.



        Tsaki taja ganin irin quruciyar da safwa ke yi,ita kuma halima na tayata

"Bansan se yaushe xaki gama girma ba safww,saiki fito kije suna jiranki a falon baqi" daga haka ta saki labulen ta juya,tana jiyo kwakwazonta da muryarta,dama tasan za'a rina hakan zata faru,saita saki murmushi tana addu'ar Allah dai ya nuna mata ranar auren tilon diyar tata da muradin ranta abdul'azeez.



      Sai data sanya masu aikinsu suka kai komai sannan ta qara gyaggyarawa ta fito,a qofar falon ma ta kusa minti uku tana dudduba inda baiyi na,sa'an nan ta daga labulen dakin ta shiga.



       Akan azeez din idanuwanta soka fara sauka,wani sanyin dadinya saukar mata,ason ranta idan itace zata so ya taso.da sauri ne ya iskota,kana su rungume juna kamar yadda turawa kanyi a duk sanda sukaga abun sonsu da suka dade basu ganshi ba,saidai ita din bata samu haka ba,amma idan ta lura dakyau kallonta yake ta qasan idanu,wato miskilancinsa bazai barshi ya bude dukkanin idanunsa ya kalleta sosai ba.



      Sam shi ba wannan bane cikin kwanyarshi,idanunsa da zuciyarsa ne bijiro masa da ita kamar yadda take masa lokaci zuwa lokaci,sai yake ganin fuskarta gefan ta safwa har tazo ta zauna.



       Kusan rabin hirar da abdul suka yita,ya karanci damuwa qarara saman fuskar safwa saboda yadda ta ciwa ranar da lokacin buri,don haka saya miqe ya zagaya ta bayanshi ya sunkuya dai dai kunnensa cikin rada

"Don't be a silly pls....bai kamata ba,kayi abinda ya kamata" sai ya daki kafadarsa sannan ya qara gaba ya fice.



      Ci gaba sukayi da kallon juna kawai shuru yana sake ratsa dakin,sai data gaji sannan ta saki ajiyar zuciya,ta taso zuwa kujerar da yake kai a hankali idanunta a kanshi,tana jin kamar taje ta rungumeshi cikin jikinya,saidai bata manta da sharadin daya sanya mata ba kafin ya iso,don kada ma tayi yunqurin aikatawa.



     Hannun kujerar da yake kai ta xauna,hakan ya kawo kusaci sosai tsakaninsu,cikin sanyin murya da shagwaba tace

"My prince" shanyayyun idanunshi dake sakr narkar da ita a soyayyarshi ya daga ya kalleta dasu,ya kafeta kuma dasu yana ci gaba da kallonta,itama kallonshi take,ta daga hannunta a hankali xata shafi idanun nasa,sai kuma ta tuna warning dinsa,don haka tayi saurin janye hannun nata  da sauri

"Gaba daya ka ciremin zumudin zuwanka dana kwana inayi,idan wani laifi nayi maka pls prince ka gayamin..." Wani murmushi ya saki na gefan baki yana kada kai

"Babu wani abu....just bana jin dadi ne...." Ya qarashe maganar yana miqewa idonsa still a kanta

"Zan dawo wani lokaci" ya fadi yana tattakawa a hankali harya fice daga falon,daga inda take xaune ta bishi da kallo kawai,tana jin idanunta na tara qwalla,me yasa zai mata haka?,saita miqe cikin sassarfa tayi cikin gida tana gab da rushewa da kuka.



       A harabar gidan yasamu abdulrashid tsaye jikin motar yana amsa waya,baice masa komai ba ya bude gidan baya ya shige maimakon gaba,galala ya bishi da kallo yana sauke wayar daga kunnensa,tsahon minti biyar yaji baice masa komai ba,kamar ma bai cikin motar,don haka saiyayi sallama da wanda yake wayar ya maida aljihunsa,yabude kawai ya shiga ya tada ita shima still bai cewa azeez din komai ba.



********  ***""""***  *******



      Ƙarfe biyar da mintuna ne na yammacin ranar,zaune take saman abun sallarta wanda tunda tayi sallar azahar kusan take kai bata tashi ba,kiran sallar la'asar ne kawai ya tadata,ta ajjiye qur'anin hannunta tashiga bandaki ta daura alwala tayi sallar la'asar din,ko data idar qur'anin tasake dauka taci gaba da karatunta,don a yanzun indai tana ita kadai cikin dakin shine babban abokin hirarta,cikinta babu komai,tun shayin safe data samu ta kukkurba a tsaitsaye cikin qannenta,don batason ta fita daban cin abincin tayi karo da mama ladi ko anty wani ya samu maganar dazai gaya mata wadda zata sake dagula lissafinta.



      Jin yadda hanjinta ke murdawa saboda yunwa ya sanyata aje qur'anin gefe,sannan ta miqe a nutse ta taka ta fice zuwa kitchen.



       Kamar baquwa ko barauniya haka take takawa cikin sanda,don bata fatan ta tadda kowa a ciki,addu'arta ta karbu,babu kowa din kuwa,ta samu plate ta bude tukunya ta xuba dafadukan shinkafar da akayi a matsayin abincin rans,ta saka spoon ta fara tsakura,don gaba daya cin nata tamkar na yara haka yake,cikin nata ba wani babban space ne dashi ba.



       Gabanta yayi mummunar faduwa sanda take kai lomar abincin bakinta saboda jiyo muryar anty tana shigowa kitchen din,faduwar gaban data sanyata qwarewa,saita saki cokalin tahau tari tana dafe qirjinta.



      Dubanta anty tahau yi sanda ta qaraso tana tabe baki,sannan taja dogon tsaki

"Qaryar banza qaryar wofi,dama kin lallabo kina satar abinci babu cas ba as ba dole alhaki ya sakaki ki qware ba,jarababbiya kawai....ni wallahi bansan me yasa ubanki ma ya zuba miki ido kike ci gaba da xama tsakanin matan babanki ba,bayan babu abinda baki sani ba,mu dake yanzu duka sammakal" munanan maganganun da basu dace ba taci gaba da fada,wadanda suka haddasa tsaiwar tarin cak ba tare da tasha ruwa ba,sai kuma zafafan hawaye suka biyo gurbinsu.



       Kai ta kada ta juya da niyyar bar mata kitchen din saiga mama ladi itama ta sako kai,tun daga bakin qofar kitchen din ta tsinci meke faruwa,itama saita dora nata

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ta furta wasu sabbin hawaye da har suka sanya bata ganin gabanta sosai suka kwaranyo mata,taci gaba da tafiya kawai taba laluben hanya,amma hakan baisa sun rabu da ita sun qyaleta ba,saima leqowa da mama ladi tayi ta kitchen din ta dora

"Wato muna magana ga shashashai kina ci gaba da tafiya ko?,da yake babu uwarki ciki mu duka bamu haifeki ba,koda yake tunda kika yi mana uwar takima haka zaki.mata tsaf kuwa,tunda kin balaga kinsan namiji kinsan dadinsa kamar yadda muka sani,kinga kuwa dole kiga ai kanmu daya,daya daga cikin illolin xama da bazawara kenan,muna fada malam yana ganin ba haka ba,to yau zaizo,ni ko shi a cikin gidan nan,kwana biyu sai anyi magana ya wani ce jinin maimunatu ce ke,ina ruwanmu da wata maimuna,shi ya santa,da can baisan hakan ba sai yanzu"



       Sosai kalaman suka mata girma a qwaqwalwarta,duk da haka bata fasa daga qafarta ba,burinta daya ta isa dakinsu kunnuwanta su tserewa muna nan kalaman da mama ladi da taci gaba da tsaiwa tana jifanta dasu,me ya kawo zancan mahaifiyarta a wannan maganar?,baiwar Allahr da batasan me yake faruwa ba?,batasan da wanzuwarsu ba?,ta jima kwance cikin kushewarta cikin salama shine yanzun zasu ambatota cikin haukan kishinsu da batasan meye manufar yinsa ba?,shin wai sun manta cewa itace sila na dukka wannan daula da suke ciki?,ko iya haka bata cancanci samun dagin qafa ba daga garesu?,tana jin qirjinta na mata wata irin suya,tana jin wani irin xafi cikin qirjinta,numfashinta kamar an dora mata dutse a qirjinta yana son ya fara yi mata nauyi.....



       Kamar daga sama,kamar cikin daya daga cikin mafarkan data saba yi,kamar al'amara kamar shifcin gixo sai taji sallama daga bakin qofarsu,sallamar data dauke dukkan wani kuka da take gursheqen yinsa cak! Tashi guda!,kwatankwacin yadda ruwan sama ke daukewa lokaci daya.



       Cikin hanxari ta waiwaya,ta waiwaya dinne bawai donta yarda da sautin muryar data ji ta wadda zuciyarta ta dauki shekara da shekatu tana begen sake gani bane,ta waiwaya badon ta yarda da qaryar da kunnuwanta ke mata ba,ta waiwaya ne kawai don taga wacece mai irin muryar halitta mafi soyuwa a wajenta,muryar anty zuhriyya,anty zuhriyyarta,matar da take kallonta a matsayin mahaifiyarta.



       Fes idanunta suka sauka a kanta,komai dadewar zamani,komai shudewar lokaci,hakanan komai sauyawar zamani batajin wannan fuskar kamanninta zasu bace daga idanunta,ba mai irin muryar anty zuhriyyar bace,anty zuhriyyar ce da kanta,tsaye daga farkon farkon falon tana dan sake duban falon da alamun tantamar inda take,sanye cikin wani leshi da aka yiwa dinkin doguwar riga wadda ta fito da kyau gayu da tsarinta,hadi da girma dake nuna shekarunta sun fara sauyawa zuwa na babbar mace,bawai babbar macen data tsufa ba,aah,babbar macen da ilimi kudi da wayewa suka sake bayyana aihin wacece ita.



       Dukka lebanta na sama da qasa rawa suke,kunnuwanta sun toshe ta daina jin abinda mama ladi ke fada,idanunta kadai sune kewa anty zuhriyya kallo irin na qurill,tana tsoron kada ta bace mata kamar yadda take zuwa mata a mafarki sannan da zarar ta farka ta bace mata.



       Duk da idanu da take binta dasu amma bakinta ya kasa furta kowacce kalma,bude baki tayi da niyyar sake yin sallama cikin falon idanunta karaf suka sauka kan bilkisun dake tsaye ta kuma kafeta da idanu

"Dauhgter!"

"Anty!" Suka ambaci sunan juna kusan a tare,kana kowanne ya durfafi dan uwansa da sauri sauri,saidai kafin bilkisun ta isa ga anty zuhriyyar tuni ta sulale a wajen,tana shirin kaiwa qasa anty zuhuriyya ta tallafota jikinta,a take ganinta yasoma daukewa tafara gani dishi dishi,hakanan jinta ya soma yin low,abu daya zuwa biyu ta iya jin muryar mama ladi,sai muryar anty zuhriyya data iya banbance abinda tace saboda tana jikinya ne

"Ke kuma wacece?" Sai muryar anty zuhuriyyan still data sake fada cikin tsawa

"Ahir kada ki sake ambatan sunan maimunatu,don linxami yafi qarfin bakin kaza!" Daga haka taji antyn na sake janta jikinta,daga wannan bata sake ji ko gane ko meye yake faruwa ba jinta da ganinta suka ida daukewa gaba daya......

7/11/21, 4:32 PM - My Mtn Number: 36


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_______________________________


     Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana binsu da kallo,ta jima zaune a inda suka barta tana tariyar rayuwa da abubuwan dake cikinta,anty zuhriyya?,ina take?,ina tayi?,tayi nisa da ita nisa mai yawa,irin nisan da bata zata ko tsammata ba,har yanzu mafarkin da tayi da ita daren jiya yana nan maqale a ranta,makwafi ce ta mahaifiyarta wadda bata da tamkarta,tunda dangin nasu sun mata nisan da bazata iya zuwa muhallin da suke ba,su din kuma sun manta da cewa dan uwansu ya aurar da diyarsa aqasar harta haifi diya itama ko kuwa yaya?,mahaifiya tabbas mahaifiya wani jigo ne na rayuwa,babban bango ce kuma majingina,wanda duk mutumin daya rasata ba shakka dole yayi kuka,kuka kuma da bazai yanke ba sai ranar da taka ta sameka.



       Kamar wani hankali aka qara mata game da muhimmamcin mahaifiya,ta tabbatar da cewa koda mahaifinta yafi qarfin mahaifuyarta,koda tana raye aka mata wannan auren na qarfa qarfa,tabbas bayan ta dawo ba zata fuskanci rayuwar data soma fuskanta cikin gidan ba a yanzu.



       Na farko sabuwar amaryar babanta wadda ta gama karantar tsaf kishi take da ita,na biyu daga umma katti har mama ladi duk da cewa ta dade da sanin yadda suka dauketa,amma ta tsammaci yanzun komai zai canza,albarkacin albarkacinta da kowaccensu take ci a yanzu,saidai wani irin mu'amala ce tsakaninsu,idan sun ganta ta gaidasu su amsa,idan basu ganta ba babu mai nemanta ko cigiyarta,koda zata wuni ta kwana cikin daki ba tare data leqo ba,qannenta sune sanyin idaniyarta,abokan hirarta,akwai abubuwa da yawa da suke cunkushe a zuciyarta suke damunta suna dagula lissafinta,wanda tsahon sati biyu da dawowarta harta soma ramewa,baya ga rashin abubuwan more rayuwa yadda tasamesu a baya dakyau wanda yanzun duka sun janye,babu wanda yadamu da yanayin abincin da zataci a gyarashi saboda taste din bakinta ya canza,babu wanda yadamu daya bata kudin sabulun wanka kona wanki,idan an bayarma tona qannenta ne,su kansu basu gama wadata yadda ya kamata ace sun wadata ba,saidai wannan din bata sani ba,shin daga mahaifinsu ne ko daga matansa wakilansa wadanda abun yake biyowa ta hannayensu?,duka bata sani ba,saidai dukka wannan ba damuwarta bane,kome tasamu tana ci,kome yazo.hannunta tana amfani dashi,tunda tasan rayuwar da tayi abaya gaibu ce,wadda tayi dai dai da mafarki.



      Komai zai biyo baya ko xai sameta tana da tabbacin rashin mahaifiya nada kaso mai tsoka da kuma muhimmiyar rawa da yake takawa wajen tsintar kanta a kowanne yanayi ma da take ciki,da tana da mahaifiya ko babu komai tana da kafadar da zata jingina tayi kuka,tana da muhallin da zata fadi damurta a fuskanceta,koda ba za'a yaye mata damuwar ba,za'a tallafa mata da addu'a,tana da wajen da za'a tambayeta me ya dameta?,me take da buqata,amma yanzu fa da babu uwar?,saidai tayita cinye damuwarta ita daya,ko tayita magana da 'yan uwanta data tabbatar babu lallai su fahimta abinda take nufi.



       Sai datayi wanka,tasamu kaya ta saka tana duba yawan kayanta dake da buqatar wanki amma babu sabulun da zata wanke din,batason taba na qannen nata,saboda su dinma bawai wadatar dasu yayi ba.



     A hankali take takawa zuwa kitchen din gidan,ga duk wanda yasanta kallo guda zai mata ya karanci tana cikin damuwa qwarai,akwai tarin damuwa cunkushe a ranta,babu kowa ciki dama shan ruwan shayi ya kawota,don haka tasamu kofi ta diba,duk da tanajin yadda wasu lokutta ake kyarar qannenta idan suka taba kofin daya daga cikinsu,ta dauki salar biredi dake ajjiye harta soma shan iska,wanda ta tabbatar nata ne,don kusan koda yaushe itace ta qarshe a yin breakfast a gidan,babu kuma wanda ya damu da ita bare ya killace mata.



       A tsaye takeshan shayin,lokacin ne anty tashgo kitchen din,da alamu ita keda girki a ranar,fuka a gintse,tana ta ciccin magani da harare harare,da qyar ta amsa gaisuwa bilkisun kamar wadda aka yiwa dole,sannan tasoma hada girkin rana,wanda da wurwuri takan gama duk ran girkinta,ruwan mutum yaci ruwanshi ya barshi,tasha jin suna fada da abokiyar yin nata mama ladi akan hakan,da yake ita mutunce maison abinci mai dadi,umma katti kanja gefe ta tafa hannu tace itakam 'yar kallo ce,hakanan ko anqi ko anso itace uwar gida kuma babu yadda aka iya da ita.



      "Wato ke babu abinda kika iya tsinanawa mutane,saidai idan an tuqa a baki" taji anty tana fada sanda take dauraye kofin da ta gama shan ruwan shayin,dakatawa tayi tana duban antyn cikin mamaki,don bata gane me take fada ba sam,aiki dai tasan cewa kafin qannenta su fita su suke share falon gidan da baranda tas to bata musu horon ganda ba,itake shiga kitchen ta gyara musu shi fes kullum kwanan duniya ta wanke dukka kwanukan ciki,don tasan babu lallai yaran suyi yafita yadda ya kamata,kuma ita din shaida ce,daga zuwanta gidan zuwa yau kitchen din har wani qara haske yayi akan nada,hakanan duk sanda suka gama cin abinci xata tattara kwanukan tasake wankewa,don ba kasafai ma suke kwana da wanke wanke ba yanzu tun sanda tazo,to batasan wanne aiki takeso ba kuma sama da hakan,kafin tace komai ta yaba mata maganar data tsaya mata fiye da tsammani

"Dama illar zama da gansamemiyar bazawara kenan,tana maka kallon biri kana mata kallon ayaba,idanu sun gama budewa ta gama sanin komai,kai wala'alla ko kwanan aure kayi da ubanta saita gane,mtsewee Allah ya sawwaqa" idanunta ta lumshe gaba daya tana jin wani tashin hankali na rufto mata,sunan Allah tasoma ambata don ya kawo mata agaji,tana jin wani irin zafi yana ratsa zuciyarta,ta maida kofin muhallinsa da qyar sannan ta lalubi qofar fita.



      Da qyar takai kanta daki,ta samu qasan tiles din tayi zaman dirshan tana yin filla filla da maganganun antyn,sai taji suna mata wani irin ciwo,wanda daga qarshe sai da suka danganata da zub da hawaye,kalmar bazawa ta sanyata sakr maida kanta cikin duniyar tunani,duk sanda zata daga kai ta kalli fuskarta a madubi sai wannan sunan ya fado mata,ba shakka sunanta ne,sai taji wani irin rauni da tashin hankali sun baibayeta,ba shakka duk wanda ya santa zai kuma ce wani abu akanta saiya laqaba mata wannan sunan,duk wanda yazo da niyyar aurenta sai an alaqantata da wannan sunan,mafi muni ma a cikinsu idan an tambayeta wayeshi din wanda ta aura?,bata da cikakkiya kuma tartibiyar amsa akan haka.



      Cikin kwanakin lafazan da antin ta dinga aike mata kenan,wadanda suka zama tamkar guba a zuciyarta,suka tarwatsa duk wani zaman lafiya da salamarta,suka dinga damunta gamida sanyata cikin wata iriyar matsananciyar damuwa,wadda ta bayyana har a gangar jikinta baya ga zuciya.



      Abun mamaki sai taga mama ladi itama tabi sahu,ya zamana sun sakata a gaba batare da tasan meta tsare musu ba,duk ranar Allah daga fitowarta zuwa faduwarta cikin kuka da qunci take,hakan yasa cikin lokaci qanqani dukkan wani kyau da kumari datazo dashi yayi nashi waje.



       A gefe guda kuma wani irin matsananciyar tsanar masarautar kaisa da ahalinta suka saukar mata,tasan koma meye duk wani hali da take ciki a yanzu sune sila kuma ummul aba'isin din komai,komai lalacewar uba uba ne,amma banda haka da zata iya cewa mahaifinta shine mutum na biyu daya zama sila kuma yake da alhakin komai,cikin qaramin lokaci ta sake tsanar komai ma,ciki harda rayuwarta.


********    *****   ********


"Ya Allah!" Ya fada da sauri lokacin da yake tashi daga shimfidarsa,yaxauna sosai saman gadon dafe da goshinsa.



    Ya jima zaune a haka yana maida numfashi da sauri da sauri,sa'an nan ya zuro qafafunsa yasauko,saida yasoma kunna qwan lantarkin dakin,haske ya gauraye ko ina,sa'annan ya durfafi bandakin dake cikin dakin.



       Sosai yadinga watsawa fuskarshi ruwa,mafarkin da yayi yanzu sakanni qalilan da suka shude yana dawo masa tar cikin kwanyarsa,tamkar yanxu yakeyinsa,muryarta da fuskarta na gilmawa cikin idanunsa.



      Ya jima sosai a haka,sannan daga bisani ya daura alwala,a hankali ya ciri towel yana goge ruwan jikinsa,yana kuma dawowa zuwa cikin dakin,saman gadon ya sake komawa ya kwanta,saidai wannan karon rigingine yayi bayan ya tokare bayansa da filo,lokaci zuwa lokaci yana sauke ajiyar zuciya.



       A daren ko kadan bacci bai sake xiyartar idanuwansa ba,yanaji yana gani hakanan yayi asarar daren,bai samu runtsawa ba har sai da ya bada faralin sallar asuba,sannan wani gajeran bacci yayi awon gaba dashi.


***********



      Cikin girmamawa dukka barorin dake sassan nata suke xubewa suna miqa mishi gaisuwa,saidai ko sashen da suke baya duba bare akai ga amsawa,takawa yake zuwa cikin sassan nata cike da wani irin kwarjini da cika idanu,saidai kallo daya zakayi masa ka fahimci akwai rashin kuxari da walwala a tattare dashi,musamman ga mutumin da yasan wayeshi.



      Bai tsaya ba hakanan baiyi jira anyi masa iso ba,har sai daya dangane da falon da mahaifiyarsa ke zaune tana ganawa da baqi,shigowarsa ya tashi dukka wani baqo dake wajen yafice ya basu guri,saiya samu qasan kilishin da take zaune akai yaja daya daga cikin lausasan tumtum na alfarma da aka qawata wajen ya jingina qafarshi,a ladabce yasoma gaidata.



       Idanunta qur a kanshi ta amsa mishi,kana ta jefa masa tambayar dake kai kawo cikin ranta,sati guda kenan daya gabata

"Lafiya qalau kuwa kake yarima?" Dubanta yadanyi kana yayi qas da kanshi,ya shafa wuyanshi zuwa habarshi sannan ya amsa

"Lafiya ammi"

"Amma meya haifar da rashin kuzari da alamun damuwa saman fuskarka cikin satin nan gaba daya?" Shuru ya danyi kamar me neman dalilin daya sanyashi hakan,kusan hakan ne,donshi kansa baisan wacce iriyar amsa zai bata ba,wacce amsa ce kuma ta dace da tambayarta,saiya dan ja tsaki,yana tsammanin kawai shi da kanshi yakeson takura kanshi,ko kuma dan qaramin sabo ne daya gitta ba tare daya sani ba yakeson masa kutse cikin rayuwarshi,amma anya kuwa?,wanne irin sabo ne haka cikin a wannin rayuwarsu da idan aka curesu a haduwa biyu zuwa uku kacal basu gaza awa daya da rabi ba zuwa biyu

"Bana samun ishshen baccine kwana biyu....kuma ina tsammanin gajiya ce,dana gama warwarewa komai zai koma dai dai" tashi tayi sosai ta zauna,sabanin dazu da take a kashingide,fargaba tana shigarta na kada ace daga dawowarsa wani mugun abu na shirin samunsa daga magauta

"Wacce iriyar gajiyace da zata hanaka bacci haka har tsahon mako guda?,anya abdul'azeez?,idan akwai wani abu daban da kakeji ka gayamin tun komai baiyi nisa ba,tun ba'a ci galaba a kanka ba" kanshi ya girgixa yana son tabbatar mata da cewa babu komai

"Babu komai ammi,i wil b okay"shuru ta danyi,sannan ta gyada kai

"Allah yasa".



        "Dazu mai martaba ya aika sassanka nima na aika,maisara ya isar da saqon kana bacci,anyi rasuwa ne a gidan dan maje,yaso kuje jana'iza tare amma bai sameka ba....,inaga yana da kyau idan ka fita daga nan ka nemeshi kaji daga bakinsa,idan yana da ra'ayin zuwanka saika shirya ka bishi,ya kamata irin wadan nan abubuwan ka dinga kiyayewa saboda gobenka,kada ka manta,gobe kaine kan matsayin da yake kai a yanzu,shi yasa yakeso ka zamana a gefansa"

"In sha Allah" ya amsa mata,ba tare da yasan wanne irin feeling ne ke cikin zuciyarsa ba game da maganar.



         Dai dai lokacin sumaira ta qaraso falon,wadda tayi shirinta na komawa makaranta,kafin ta zauna azeez din ya umarceta ta hada mishi abinci,ta hada masa komai ta aje gabansa sannan ta qarasa wajen ammi suka gama maganarsu sukayi sallama ta wuce.



      Bata fi mintuna goma da tafiya ba afnan ta qaraso falon,rungume take da litattafanta ta iso gaban ammi tazube littafan gamida zama sosai a gabanta bayan ta salube jakarta kamar zata shige cinyarta,cike da shagwaba take fidda safarta,idanun azeez da bata ankara da wanzuwarsa a falon ba yana kanta,ba kasafai yake maka magana ba idan kana abinda baya so,yawanci yafi sanya maka idanu harsai sanda idanunka suka ankara dashi

"Wannan karatun akwai wuya ammi....wallahi kamar na gudu" murmushi kawai ammin ta saki kana ta dubeta

"Dadi ne yayi miki yawa auta....mutum nawa ne suke neman dama irin taki amma basu samu ba?" Shuru tayi na dan sakannin da basu wuce uku ba kana ta gyada kai

"Gaskiyane fa ammi,har kin tunamin da BILKISU" kanshi ya daga da hanzari jin afnan ta ambaci irin sunan,sunan da baisan me yasa ya fara zaune masa cikin kwanyarsa da tuninsa ba,ba tare data lura dashi bs taci gaba

"Tana da qoqari sosai ammi,gasar karatu muke da ita,duk da bamu saba ko shaqu da ita ba....amma kowa yasan mayyar karatu ce,burinta a rayuwa tayi karatu....Allah sarki bilkisu,rana daya babanta ya cireta daga makarantar,yayi mata auren dole....."

"Har yanzu baki manta ba afnan,har yau?" Ammi ta fada,wanda sai a sannan ta tuna afnan din ta taba zuwa mata da qorafin akai.maganar zuwa ga mai.martaba,duban ammi tayi,fuskarta na nuna alamun alhini

"Bazan manta ba ammi,bansan tana da kirki ba nayita gaba da fada da ita,ba ruwanta ammi,innocent kamar bilkisu amma aka hanata cika burinta"

"Gskiyar yayanku da wani lokaci baku shiri saboda dan banzan surutu,idan kin gama saiki tashi ki wuce ciki" langabe kai tayi tana duban ammin,tana shirin sake magana suka hada idanu dashi,ya balla mata harara data sanya bakinta ya rufu gam,tayi gaba da sauri zata wuce

"Saiki turo uwani ta kwashe miki su,kada kisoma zuwamin anjima kina min cigiyar littafanki ina tsaka da hutawa"

"Zoki kwashe" ya fada cikin kaushin murya,ba shiri ta dawo ta tattara litattafanta tayi gaba,ya saki siririn tsaki

"Silly girl,litattafanma sai an kwashe miki an kai miki saboda tsabar sangarta,saina rage dukka barorin dake sashen nan na maida ayyukan kanku" itadai bata da bakin magana ta qara wuta tawuce nasu bangaren,ammi itama naji batace komai ba,sai murmushi kawai datayi,tun ya qarami haka Allah ya halicceshinda wani irin girma cikin zuciya da jikinsa,amma ya manta shima komai hadimaine suke masa?,saita kada kai kawai tana sake sakin murmushi qasan ranta tana binsu da addu'a.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 38

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





         Sannu a hankali ta soma qoqarin bude idanuwanta da sukayi mata wani irin nauyi,a qalla ta dauki kusan minti daya tana wannan fafutukar sannan tasamu ta budesu tana warasu dakyau don su daina ganin dishi dishi,cikin ikon Allah ganinta ya daidaita,saita sake ware idanun nata tana kallon dakin da take ciki.



      Da fari bai mata kama da dakin asibiti ba,sai data lura da wasu abubuwa da suke kamanceceniya dana asibiti sannan ta tabbatar tana cikin dakin asibiti ne.



    Babu kowa cikin dakin,sai fanka da ac da suke aikinsu cikin madaidaitan sanyin da bazai takura ka koya hanaka sukuni ba.



       Kallonta tayi qoqarin maidawa bakin qofa sanda taji an turo qofar,anty zuhriyya ce karo na biyu,qara saurinta tayi don ta iso gareta,fuskarta washe da fara'a sosai tana duban bilkisu,bata tsaya ko ina ba sai kujerar dake gaban gadon,wanda dama ita ta tashi daga kai,ta sanya hannunta ta kamo hannun bilkisu guda daya,murmushi da hawaye na qwace mata lokaci daya

"Yanzu ina ne yake miki ciwo?,mene ne yake damunki?"

"Babu komai anty" ta fada itama sabon hawaye yana balle mata,hannu tasa ta fara share mata tana cewa

"Daga yau ba zaki sake kukan baqinciki ba daughter tunda gani....bari naje na kira likita ya sake dubaki" kai ta gyada mata tana binta da kallo.



       Tana dab da fita aka turo qofar dakin,babanta ne sanye da shadda da babbar riga,ya sake kutso kai dakin yana ta raba ido,murtuk anty zuhriyya ta hade fuskarta tsaf,maimakon ta fita saita fasa ta dawo cikin dakin.



       Ko kallon malam bilyamin batayi ba harya shigo dakin,ya qaraso gaban gadon bilkisu yana yi mata sannu

"Me ya sameki mai gado?" Ya tambaya yana dubanta,kai ta kada

"Nima ban sani ba abba,kawai naji jiri ne saina fadi"

"Ashsha...Allah ya sawwaqe" ya fada yana maida dubanshi kan zuhriyya,tun ba yau ba yasan wacece zuhuriyyan,kuma kwanwarsu bata jiquwa sam

"Saukar yaushe?,ashe kin dawo" ya fada,batako dubeshi ba illa 

"Eh" data fada albarkacin bilkisu dake wajen.



        Turo qofar dakin da aka sakeyi ne ya katse shurun da yaso wanzuwa a dakin,mijin anty zuhriyya ne da suke kira da abbaaa shida yaransu gaba daua,wanda kafin ta tafin mutum biyu bilkisu ta sani,najwa da ateeq,yanzun kuwa sun zama su uku,an samu qaruwar da namiji haisam,su kansu su biyun data sani dukka sunyi wayau qwarai qwrai,kada ma najwa da take 'yar budurwar taji labari,tana da tsaho wanda da alama tsahon babanta ta dauko.



      Babansun na dauke da haisam,najwa da ateeq suna dauke da kwanukan abinci a kwanduna,bude hannunta tayi tana musu oyoyo,yayin da abbaaa ya tsaya gaisawa da malam.bilya,wanda babu jimawa yayi musu sallama ya wuce ganin kamar sun ma manta da wanzuwarsa a dakin.



       Ranar kusan wuni sukayi tare,anty zuhriyya sai nan nan take da ita,abbaa mutum ne mai sauqin kai da jan mutane a jiki,bare bilkisun da take kamar diya a wajensa,dukkan yaran kansu sun sake da ita,musamman najwa ita tafi saurin tunota,ateeq sai a hankali a hankali ya dinga tunawa yana kuma sakewa,haisam kam dama sarkin qiwa ne yana kwance jikin mamarshi.



      Ko da likita yazo ya dubata sai yace ko zuwa gobe ma zai iya sallamarsu,tunda babu wani abu dake damunta kuma,saidai sallamar washegari bata samu din ba,saboda a daren wani irin zazzabi ne mai azabar zafi ya rufeta,sosai hankalin anty zuhriyya ya tashi,ta kasa runtsawa itama daren gaba daya,sai gab da asuba aka samu ya sauka,bacci kuma ya dauketa.



      Kwana biyu kenan tana fama da nataccen zazzabin,abinda ya hana sallamar kenan,sai a kwana na uku ne aka samu ta kwana lpy,washegari da safe kuwa ta tashi da dan qwarin jikinta,hakan ya yiwa anty zuhriyya dadi,da wuri ta sanyata tayi wanka,ta bare mata daya daga cikin sabbin kayan da tun tana kwance tahau siya mata,duk da tayi mamakin kyawawan sitturun data gani a jikinta,ta bata daya daga cikin wanda ta siyo mata ta shirya,tsaf kuwa tafito,ta hada mata tea da chips ta miqa mata tana dubanta

"Yau dai babu sauran ciwo,maza ki cinye wannan tas" murmushi bikisun tayi har fararen haqoranya na bayyana,hakan ya sanya anty zuhriyyan dan zuba mata idanu,saboda yadda kamarta da yayarta maimunatu ta fito sosai,sai taja kujera ta zauna a gabanta tana dubanta sanda take cin abincin,cikinsu babu wanda yace komai sai kallon juna da sukeyi lokaci zuwa lokaci,dakin babu kowa saisu biyun,don tunda safe da abbaa yazo da yaran ya kawo musu breakfast suka koma tare,dama ko sau daya basu yarda sun zauna tare da ita a asibitin ba,sunfi sabawa da abbaansu shi yasa suke maqale dashi,don haka ta barsu tare tunda akwai mai aikinsu a gidan dake kula dasu.



       Sai data ci fin rabi sannan ta aje tana cewa

"Na qoshi anty" murmushi ta saki

"To ma sha Allah"

"Bilkisu....jikina ya bani cewa,bayan tafiyata,abubuwa da dama basu tafi dai dai yadda na tsara ko kuma yadda suka kamata ba,duk da nazo na tadda wasu sauye sauye,amma hakan bai kwantar min da hankalina ba....saura shekara biyu mu dawo amma naji dukka hankalina ya karkata nazo na ganki naga halin da kike ciki,ko bacci cikakke bana iyayi ba tare da nayi mafarkinki ba....sanar dani meke faruwa daughter ko kuma meya faru bayan bani nan"


 

      Daga yanayin yadda fuskarta ta sauya tun kafin ta furta komai ya tabbatar mata da akwai gagarumar matsala,kawai kima abinda ya faru mai girma da rayuwarta.



      Kasa cewa komai bilkisun tayi sai wani zazzafan kuka daya subuce mata,batasan cewa a baya kuka tayi mara 'yanci ba sai yanzu,sai a wannan lokacin data samu kafadar da zata kwantar da kanta ta fidda duk wani zafi da radadi dake mintsinar zuciyarta,wasu irin hawaye masu dumi suka dinga kwaranya daga kuncinta,wanda ta tabbatar duminsu tun daga zuciyarta yake.



      Shuru kawai anty zuhriyya tayi tana bubbuga bayan bilkisun ba tare data hanata kokawa ba,kuma ba tare data ce mata komai ba,zuciyarta cike fal da tsoro da taraddadin abinda kunnuwanta zasuji daga bakin bilkisun,babu abinda zuciyarta bata qiyasta mata ba,bata tsaida ita ba har zuwa wani lokaci da kukan yaja baya,ta miqe da kantabta bata ruwa mai maidaidaicin sanyi dake cikin fridge din dakin,tasha shi kuwa mai dama,sannan ta aje tana maida ajiyar zuciya.



       Tiryan tiryan ta soma bawa anty zuhriyya labarin komai,babu abunda ta boye mata har zuwa ranar da antyn ta sanya qafarta a falon gidansu.



      Tamkar wadda ta hadiyi tabarya haka ta kasa zama,idanunta tuni suka rine saboda kukan data dinga yi tun farkon labarin,har zuwa lokacin da hankalinta yayi mummunan tashi sanda taji irin auren da malam bilyan ya yiwa bilkisu,diya qwaya daya tilo da 'yar uwarta ta jini ta tafi tabar musu,duk maganar data kwaso saita subuce mata saboda tsabar masifa da tashin hankalin dake cinta,a irin wannam yanayin abbaa ya dawo kawo mata hisham.



      Shi kansa hankalinsa ya daga da yanayin daya taddasu,kasa ce ma abbaan komai tayi,sai sanya kanta itama a kafadarsa da tayi ta rushe da kuka kamar yadda bilkisun itama ke kukan,saboda labarin ya zame mata tamkar fami ne a ranta

"Bazan qyalesu ba abbaa,bazan rabu dasu ba,dukkansu kowa saiya dandana,kowa saiya debi sakamakon abinda ya aikata,har masarautar kaisan bazan qyaleta ba,koda dukkan abinda na mallaka zai qare sai nayi shari'a dasu" abinda take fada kenan,shidai baice komai ba face lallashinta da yake,yana rarrashin bilkisu kuma da baki,daga qarshe har bilkisun da share hawayenta amma kukan anty zuhuriyyan yaqi tsaiwa,daga qarshe janyeta yayi suka fice daga dakin.



      Basu dawo ba sai bayan mintuna wajen arba'in,tsakanin miji da mata sai Allah,sanda suka dawo kukan ya tsaya,saidai fuskar nan tata a dinke take tsaf,bayansu likitane suka shigo tare dashi,yakuma dudduba bilkisu ta tabbatar masa batajin wani ciwo sannan ya rubuta mata sallama.



      Cikin motar abbaan ma kusan shirune yayi musu rakiya,kowanne a cikinsu sai sauke ajiyar zuciya yake,bilkisu bata fuskanci inda suka nufa ba saida anty zuhriyya ta masa maganar titin da zaibi,wanda babu tantama titin gidansu ne

"Yanzu zuhriyya ba zaki bari ba zuwa gobe?" Ranta tasake batawa sosai tana dubanshi

"Abbaa,na riga dana maka bayanin komai,na rantse ko awa guda dukkan abinda ta mallaka bazai qara ba cikin gidan,kayi haquri bawai naqi bin umarninka bane,amma ta gama zama qarqashinsu har abada,koda bana raye na tabbatar dangina idan suka samu labarin komai ba zasu barta a qasar nan ba" shima bai sake cewa komai ba,saiya sauya akalar motar zuwa inda take kwatanta masa din.



      Mintuna kadan suka isa qofar gidan nasu,ita da anty zuhriyyan ne suka fito,abbaa na xaune cikin motar suka shige ciki.



      Tayi sallama saidai ciki cikin yadda ba kowa bane zaiji,anty ce zaune a falon ita da mama ladi,irin zaman da saikace dole aka musu,don kowacce tata ce ta zaunar da ita,don kusan rabin xaman kishi ne ke kawoshi,bata kalli kowacce cikinsu ba fuskarta kamar hadari tace da bilkisu

"Ki shiga ki tattaro duk abinda kikasan kina da buqatarsa kuma nakine kizo mu wuce" kai bilkisun ta gyada mata cike da taraddin anya idan mahaifinta yaji wannan zai yarda?,zata iya tuna kadan daga cikin dauki ba dadin da akayi tun tana mitsitsiyarta kan za'a dauketa ya hana,baya ga haka da wayonta ma ansha gwagwarmaya da duk wadanda suka zo daukan dansu da suka haifa cikin gidan,amma duk da haka bata tanka ba ta wuce ciki,saidai wani bari na zuciyarta 'yan uwanta ne maqale a ranta.



      "Waike wacece da zaki dinga shigowa mutane gida haka kai tsaye?,sannan kuma ki tsaya kina baiwa yarinyar mutane umarnin ta hada kayanta ku tafi,kuje ina?" Cewar mama ladi data miqe cikin son nuna ita din wata abace.



        Wani mummunan kallo daya baiwa mama ladi mamaki ta jefeta dashi,qoqarin tausar zuciyarta take don kada ta kai mata mari,da qyar ta ragewa kalamanta zafi sannan tace

"Kije ki tambayi wanda ya ajeki wacece ni,sannan koshi din a yau bai isa ba yayi kadan ya hanani tafiya da bilkisu,idan kuma kuna musu bismillah" jin kalamanta ya bata mamaki,saita juya cikin rawar jiki tayi dakunan malam don ta kirashi.



      Ba'a jima ba sai gasu tare yana qoqarin sanya hularshi aka,da alama tasowar gaggawa yayi

"Lafiya zuhriyya?" Shima din sai data soma watsa masa banzan kallo,tanajin kamar taje ta shaqeshi,banda maganganun da sukayi da abbaa da kuma yadda takejin kanta a yau ba shakka daga malam.bilyan har tarkacen matansa yau babu wanda xai tsira gurinta

"Au dataje ta taso ka bata gaya maka dalilin zuwa na ba?" Isowa yayi sosai tsakiyar falon

"Ta gayamin,kuma kinsan babu wannan maganar tun shekarun baya bare yanzu,bilkisu tana gidan ubanta,kuma nan ne ya dace taci gaba da zama kamar sauran 'yan uwanta" wani tururi taji zuciyarta zuwa fuskarta sunayi,saita gyara tsaiwa sosai yadda zataji dadin fidda kalaman bakinta da suka cika qirjinta,dama neman rage wasu daga ciki takeyi

"Wanne uban?,ina uban yake?" Ta maimaita tambayarta tana kallon hagu da damarta alamun nemansa take,sai data gama waige waigenta sannan ta dawo da dubanta kanshi

"Wai kai ne?,to indai kanka kake kira da sunan uba ba shakka ka cuci iyayen qwarai,kuma kayi gaggawar cire kanka daga wannan sahun,don baka da wani abu daya da zaka iya bugar qirji dashi wanda zai sanya ka samun matsayin shiga sahun iyaye,sam halayya mu'amala da dabi'unka bana iyaye bane,kafi kama da wanda baisan ciwon haihuwa ba saboda bai taba yi ba,hakanan kafi kama da d'an kama karya kuma azzalumin uba,uban da baisan komai na diyoyin daya haifa ba,uban daya gwammace ya saida 'yanci da mutuncin yarsa sabida abun duniya fararre qararre,uban daya baiwa zalunci sunan adalci,uban dake tarwatsa rayuwar 'ya'yansa da hannunsa....tir da wannan uban daya manta cewa akwai hisabi tsakanin iyaye da 'ya'ya,ya manta da hadisin da yace dukkaninku masu kiwo ne,kuma za'a tambayesu game da abinda aka basu kiwo,ya manta da zai tsaya gaban zatin Allah ya fadi yadda ya riqe ya kuma tarbiyyanci yaran da aka bashi,bana shakka bilyamin akwai tsantsar jahilcin ilimin addini bisa kanka,wanda hakan ya sanya tun karon farko da 'yar uwata ta zabeshi xabin tumun dare tayi,ba shakka mummunar qaddara mai qarfi ya sanya 'yaruwata saliha baiwar Allah,wadda bata zalunci ta hadu dakai harka shiga qaddararta ta hada zuri'a dakai,saidai duk hakan mu a matsayinmu na musulmai munsan cewa haka Allah ya qaddara"



       "Hakanan barin bilkisu da nayi a baya babban kuskure na tafka,amma shima nasan cewa qaddarar saika aikata mata zaluncin daka yine,saidai a yanzu ina mai farincikin shaida maka,ka bude dukkanin kunnuwanka kaji,ni zuhiryya,indai an haifeni da jini kuma halastacciyar 'ya ce,bilkisu tabar gidanka da sunan zama har abada,ina kuma mai jaddada maka cewa a yau,koda sama da qasa zasu hade,koda zan rasa lafiyata ko numfashina bazan fita daga gidan nan ba sai tare da bilkisu" sosai maganganunta suka tsumashi da kyau,saidai yaji kunyar yadda ta gaggaya masa maganganu gaban matanshi da yake cikawa baki,wanda tunda suka san juna da zuhriyyan duk da babu jituwa tsakaninsu amma bata taba gaya masa maganganu irin haka ba masu zafi.



        Bilkisu dake daki tare da qannenta data samesu zaune waje daya cike da alhini suka ruqunqumeta cike da farincikin ganinta,don dama tun randa suka dawo basu sameta ba suka cika da zulumin inda taje,suka soma tunanin kodai ta sake tafiya ta barsu ne?,jin muryoyin mahaifinta dana anty zuhriyya ya sanyata fitowa,dukka yaran suka biyo bayanta.



       Fitowarta taja hankalin anty zuhriyyan,ta dubeta da idanunta da suka sake birkicewa da bacin rai

"Waima kayan da zaki dauka ba daga azzaluman masarautar can kika samesu ba?" Kai ta gyada mata,cikin daga murya tace

"Bana buqatar ki dauki koda tsinke wanda ya fito daga hannunsu,ki tattarawa ki barwa masu zalama da son zuciya su qara kan yanke talaucin da suka basu,iya gyambon ma da suka barwa zukatanmu ya isa,wuce muje" a sanyaye bilkisun ke takowa zuwa qofar fita,tausayin 'yan uwanta yana ratsata,tana son cewa wani abu amma tasan yanzun ba qadamin yin magana bane.



       "Ke mai gado,karki kuskura fa ki fita" ya fada yana takowa,sai anty zuhriyya ta tsaya,ta waiwayo tana dubansa

"Kar kayi gaggawar kai kanka mana gidan yari tun lokacin shari'armu baiyi ba,ka bari har sai zuwa sanda na makaka a kotu kaida masarautar kaisa tukunna" daga haka taja hannun bilkisu suka fice.



       Tana iya hango qannanen nata dakuma jiyo muryoyin kukansu,da alama baban nasu ke korasu ciki suna son ganin 'yar uwarsu,hakan ya sanya ta fashewa da wani sabon kukan

"Kada ki damu,za'a kula dasu,tunda suma 'ya'ya ne kamar yadda kike 'ya,na miki alqawarin bazan qyalesu rayuwarsu ta tagayyara ba,zan basu dukkan wata gudunmawa da zata iya sanyasu kasancewa cikin farinciki saboda albarkacinki" anty zuhriyyan ta fada a tausashe,kai bilkisu take kadawa,tanason buda baki tayi mata godiya amma ta hanata,tadai buqaceta kawai data tsaida kukanta,tayi qoqarin yin hakan.




      Sauke ajiyar zuciya sosai anty zuhriyya tayi tana sake rungume hisham daya soma bacci a qirjinta tana tsara yadda zata tafi da komai,abbaaa yayi murmushi

"Yaudai burin zuhra na shekara da shekaru sun cika" ya fada cikin salon tsokana,murmushinta jefeshi dashi kawai,don yau bata da bakin rama tsokanarshi,abinda aka yiwa bilkisun ke mata ciwo sosai a rai,tabbas ba zata bari ba,ba zata qyale ba kamar yadda taci alwashi......




*Alhamdulillah*


*_cikin ikon Allah da nufinsa a nan zamu dakata zuwa hutun azumin ramadan,sai kuma bayan sallah idan Allah ya bamu aron rai da lafiya,muna muku fatan Alkhairi,tare da fatan za'a yi ibada lafiya,Allah ya sadamu da alkhairinsa_*ðŸ™Ã°Å¸½Ã°Å¸™Ã°Å¸½Ã°Å¸™Ã°Å¸½

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 39

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

_____________________________





    


     A falo suka tadda najwa ateeq da mai aikin anty zuhriyya suna kallo,dukkansu suka taso suna rige rigen yi mata sannu da zuwa,ta amsa na mai aikin tana miqa mata hisham

"Jeki kwantar dashi a dakinsu,ki taho min da muqullan dakunan nan"

"To anty" ta fada cikin girmamawa tana daukar hisham daga kafadarta sannan ta wuce ciki.



        Waiwayowa anty zuhriyya tayi tana duban bilkisu

"Dauhgter....ya haka,a gidanku fa kike" ta fada ganin yadda take tsaye tunda suka shigo,murmushi bilkisu tayi kana ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana dan qarewa falon kallo,wannan ba shine gidan anty zuhriyya data sani ba kafin suyi tafiya,wannan yafi wancan kyau da tsari,da alama sun sauya gida ne kafin dawowarsu,kuma wannan din na nuna cewa sabon gida ne kuma sabon gini ne,haka nan duk kayan dake cikinsa da alama sabbi ne.



      Babu jimawa ta dawo da muqullan,anty zuhriyya ta karba tacewa bilkisu ta taso suje,miqewa tayi ta bita a baya tana sake duban hanyar da suke bi.



      Wani corridor suka shiga,wanda ke dauke da dakuna guda hudu,bibbiyu suna kallon juna,sai babban window daga can qarshen corridor din,daya daga cikin dakunan ta bude ta shiga bilkisu na biye da ita.



      Babban dakine wanda ke dauke da gado two bedside drower wardrobe sai kuma madubi,malale dakin yake da tiles kalar kayan gadon,sai wata qofa dake rufe cikin dakin wanda babu tantama bandaki ne.



      Gefan gadon anty zuhriyya ta nuna mata,ta isa a hankali ta zauna,juyawa tayi ta soma qwalawa mai aikin nata kira,nan da nan ta qaraso

"Ina sabbin curtains din nan da aka kawo?"

"Suna inda kika ce na ajiye miki"

"Oya maza debosu kizo ki tayani sakawa". To tace sannan ta juya ta fita,babu jimawa ta dawo dasu a hannunta,karba tayi tana nuna mata toilet

"Shiga ki dubashi da kyau ki wankeshi fes da Allah haula"

"To anty" ta sake cewa tana nufar bandakin.



      Bilkisu dai na zaune antyn tasoma sanya labulayen da kanta,taso tayata amma ta dakatar da ita

"Kin manta daga gadon asibiti kike?,hutu yanzu shine abinda yafi dacewa dake" tana ji tana gani ta zauna ta barta da aikin,tana aikin tana janta da hira,tun bata sakewa harta soma sakin jiki tana bata amsa,wani abun kuma kawai tayi dariya,don har yanzu qannenta na maqale a ranta,tana tunanin halin data barsu.



       Cikin qasa da awa guda dakin ya koma cikakken daki,haule ta qarasa gyarashi tas,tasa aka dauko spare plasma da sauran kayan kallo aka maqala,tunda dama already akwai gurbin sanyasu a dakin,sanyawar ne kawai ba'ayi ba,wala'alla saboda ba'a buqatar dakin babu mai zama a ciki.



       Agogo anty zuhriyyan ta kalla

"Yanzu ki kwanta ki huta sosai,idan lokacin sallah yayi zan tasheki kiyi sallah" kai ta gyada mata,cikin sassanyar muryarta tace

"Na gode anty"

"Shshshsh!!,banason ki sake cewa komai,idan ba haka ba zanci qaniyarki,don na miki abu shine zaki godemin?" Murmushi ne ya subuce mata,itama saita sakar mata murmushin kana ta juya ta fice daga dakin tana sakin ajiyar zuciya.



       Sai yanzu tadan samu nutsuwa kadan data soma yin abinda ya kamata akan bilkisun,saidai tana jin cikin wajiban da suka hau kanta batayi komai ba,so take ta taba rayuwar bilkisu sosai,ta goge duk wani bacin rai qunci da tabo data taba fuskanta,duk da tasan cewa duk.yadda kakai gason goge wani tabi a rayuwar mutum,yakan iya tafiya amma lallai zai bar maka burbushinsa,walau a zuciyarka ko rayuwarka.



      Duk da taso tayi baccin amma hakan ya gagara,saboda tunane tunanen da suka cika mata qwaqwalwa,lissafe lissafe na rayuwa,kusan haka dai ta cinye lokacin da anty zuhriyyan ta dibar mata ba tare data iya runtsawa ba.



      Sanda antyn ta shigi fes da ita,da alama tayi wanka ta canza kayan jikinta,baki ta kama

"Daughter,kada dai kicemin bakiyi baccin ba" murmushi kawai tayi

"Baccinne baizo ba"

"Ki tashi kiyi sallah to,saiki fito falo muci abincin rana"

"Toh" tace tana saukowa,ta shige bandakin ita kuma ta fita.



      Dukkansu ta samesu saman dining,da alama ita kadai ake jira,cikinsu ta shige itama amma ta kasa sakewa saboda abbaa dake wajen,hakanan ta tsakuri abincin ta miqe,antyn ta karanceta,hakan ya sanya ta saka haule ta bita da wani daki.



      Ranar gaba daya kusan wuni sukayi tare da ita,basu bata wata dama da zata kebe ba bare wani tunani ya dameta,saidai duk da haka lokaci lokaci qannenta suna fadowa a ranta.



      Da daddare bayan tayi wanka tana shirin kwanciya anty zuhiryya ta shigo dakin dauke da leda,already ta riga data saba da yin wanka kafin ta kwanta tun xamanta a mexico

"Ga kayan bacci nan,da kuma wasu kala biyu spare,sai zuwa jibi idan kin huta sosai idan Allah ya kaimu zamu fita inyi miki siyayya,ki rubuta duk abinda kike buqata ki ajjiye,idan ba so kike ranki kuma ya baci ba kada ki soma cewa zaki muna alkunya,ki sanya a ranki kamar yaaya maimuna ce tace ki rubuta duk abinda kikeso" murmushi dai still tayi mata kamar yadda ta saba,sannan tayi mata godiyar data nuna mata sam bata so.



      Kwanakinta biyar a gidan basu fita ko nan da can ba,antyn natason haifar da sabuwar shaquwa tsakaninsu,tana ta son bilkisun ta sake suma yaran duka su sake da ita sosai yadda ta kamata,cikin kwanakin sosai bilkisu taga kulawa da tattali,kullum cikin ina ka saka ina ka aje anty zuhriyya keyi da ita,bata fita ko ina duk da cewa ranar data diro qasar daga filin jirgi sai gidan malam bilya,tana da buqatar zuwa wasu gurare amma dukka ta soke tace saita gama settling din komai.



       A kwana na shida ne da yamma tasa ta shirya ita da yaran duka suka fita a motarta,ita ke driving bilkisu na zaune gefanta riqe da hisham wanda yasoma sakin jiki da ita,ateeq da najwa suna baya.



        Sai da suka hau titi sosai sannan anty zuhriyya tace da ita

"Wanne abu kike ganin ya kamata a yiwa 'yan uwanki?" Duban anty zuhriyya tayi da sauri sannan tadan kautar da idanunta,bata zaci maganar nan kusa haka da wurwuri ba,idan ason ranta ne,kuma daso samu ne kowacce ta koma gaban mahaifiyarta ta kula da ita,saidai hakan kuma zai iya zama naqasu ga burinta nasin kasancewa tare dasu da kuma cikar burikansu,don babu lallai a inda zasu koma din su samu ingantacciyar rayuwa,wala'alla iyayen nasu sun jima dayin aure,babu tabbacin kuma wanda suka aura din zai riqe musu yaran nasu,dole sai hannun kakanni,wadanda suma wasunsu suna ta kansu ne bare su dauki wahalar riqe jikoki.



      Maganar anty zuhriyya ta katse mata tunaninta

"Inaga a nawa ganin,kawai mu kula da iliminsu su samu ingantaccen ilimi a makaranta mai nagarta,da sutturar sawarsu zuwa walwalarsu cikin gidan,inaga wannan shine abinda sukafi buqata" kai take gyadawa tanajin wani sanyin dadi a ranta,ba shakka wadan nan kusan sune jigon komai,kuma tana fatan idan suka samu haka ka'in da na'in komai mai sauqi ne.



       Godiya sosai ta yiwa antyn duk da ta nuna bataso,amma bata fasa ba,sai albishir na biyu daya sake faranta ran bilkisun,har ya sanya fuskarta ta washe qwarai

"Abu na gaba da nake tunani shine,zan daukeki muje ethopia,asalin danginmu dukka suna nan,jinin abbanmu can ne tushenmu" nannauyar ajiyar zuciya ta saki,karon farko da zata taka cikin ahalinta na uwa,zataga dangin mahaifiyarta wadanda kusan zata iya cewa tun tashinta bata sansu ba sai a yanzu,farincikinta ya kasa boyuwa,wanda hakan ya sake farantawa anty zuhuriyya.



       Daya daga cikin manyan shagunan saida sutturu da dukka kayan qyale qyale na mata suka  sauka,kaya sosai anty zuhriyya ta dinga lodar mata kai kace idanunta a rufe yake,kamar kuma batasan ciwon kudin ba,sannan ta koma bangaren mayuka zuwa turaruka suma ta musu diba son ranta,hakanan mayafai gyalulluka zuwa takalma,sarqoqi da kayan makeup,sai data ji a karan kanta ta gamsu da siyayyar data yi sannan taje aka mata total ta biya,babu abinda ta siyawa yaranta don bata su take ba,burinta kawai ta maida bilkisun asalim bilkisunta.


     

       Cikin satittika qalilan ta soma komawa hayyacinta,sati hudu kacal tayi wani irin kyau,ta cika sosai fiye da yadda anty zuhriyya ta tsammata,kai kanka idan ka ganta sai kayi mamaki,dukkansu sun alaqanta hakan da nutsuwa da kwanciyar hankali data fara samu,don tuni antyn ta fara maganar yadda zata zana neco da waec,tunda lokacin zanawa ya sake zagayowa,wato shekara iwar haka akayi mata karen tsayen da yaso kassara rayuwarta,ta wani bangaren kuma tana shirin yadda zata maka masarautar kaisa da malam bilya a kotu.



      Da qyar abba yasha kanta,a wani dare bayan ta gabatar masa da abinci yaci,ta kwashe kwanukan ta gyara wajen tsaf,saita dawo inda yake

"Abban najwa.....nace idan babu wani ni zanje nayi wani aiki?" Saiya daga kanshi yana dubanta cikin mamaki

"Wanne aiki ummin najwa zatayi da zaisa ta barni ni kadai?" Saita gyara tsaiwarta tana fata ya fahimceta

"Kasan na fara tsara yadda zan shigar da qarar bilkisu da masarauta da kuma mahaifinta,to so nake cikin satin nan na kammala komai a soma shari'ar,banason abun ya dauki dogon lokaci" ajjiye takaddun dake hannunsa da yake dubawa yayi,sannan ya gyara zamanshi sosai,saiya nuna mata gefanshi

"Zoki zauna muyi wata magana" a hankali cikin sanyin jiki ta tako ta zauna a inda ya nuna mata,kiran sunanta yayi cikin sautin dake nuna zancan da zaiyi mai muhimmanci ne

"Inda zakiji shawarata zuhra da kin ajjiye maganar shari'a a gefe,saboda wasu dalilai da nake ganin koda an soma shari'ar babu lallai a cimma nasara,dalili na farko shine,dukkan abinda ya faru ga bilkisu masarauta bawai gaban kansu ko qarfa qarfa sukayi suka dauke bilkisu suka aurarwa dansu ba,a'ah,sun nemi aurenta ta hannun mahaifinta wanda dama shine yafi cancanta daya aurar da ita,ya amince ya aura musu ita bisa sadaki da kuma amincewar dukkan waliyyan yaran,kinga ko a nan hujja ta qare,ba saceta akayi ba,ba'a daura auren ba saida amincewar waliyyi wakili kuma mahaifinta,abu na biyu wannan shari'ar zata zama tamkar tonon silili ne ga bilkisu,wanda baisan batun bama ya sani,ta zama abar nunawa aduk inda zata shiga,shi nasu dan namiji ne,wanda wala'alla ba kowa bane ma yake da matsayin ganinsa ba bare a nunashi,koda ana ganinsa wala'alla sau daya ne a shekara wajen hawan sallah,wannan zai zame mata qalubale wajen wanda zata aura a gaba,koshi ko ahalinsa,hakanan zai zama takura a rayuwarta,tunda shari'a ce da manyan mutane,dole zata shiga jaridu da mujallun qasar nan,hadi da gidajen tv dana redio,kuma hade da hotunanta da nashi,abu na uku,malam bilyaminu mahaifin bilkisu ne,mahaifi kuwa har abada yana nan a matsayinsa na mahaifi duk lalacewarsa,duk tarin zunubansa,ba'a sauyawa tuwo suna,hakanan zai.iya yiwuwa a sanda kotu ta yanke mishi hukunci hakan ya sosa ran bilkisu,ya kuma hanata sukuni da walwalar da kikeson sama mata.....zuhra....inason ki duba dukka wadan nan hujjojin nawa,bawai don bamu da kudin da zamu iya tsayawa bilkisu ba,saidai wasu abubuwan mukan dauke kai daga garesu,mu kuma yi kamar basu faru ba,kamata yayi yadda kika dauko hanya nason inganta rayuwarta ki dora daga nan,ki mance komai don kada ya hanaki yin abinda ya kamata" shuru tayi tana jujjuyawa gami da tattauna kalaman mijin nata,tabbas maganganunsa suna bisa hanya,saidai tanajin kamar shari'a dasu ce kawai hanyar da zata sanya ta huce,amma dole ta tsaya ta duba abinda ya kamata kamar yadda yace,da wadan nan kalaman ta haqura,ta kuma watsar da abunda daa ta qudurta aiwatarwa.


*****   *****"""""*****  ******


      A hankali yake fidda kayan jikinsa bayan dawowarsa daga zaman fada na musamman da aka gudanar a yau,cike da gajiya da qosawa yake rage yawan kayan dake jikinsa,fuskarshi kamar kullum babu walwala babu annuri,komai ma baya masa armashi ko dadi,ji yake kamar wanda aka sanya qaton kwado aka qulle rayuwarsa.



       Sai daya gama cire kayan duka sannan ya doshi bandaki,ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi wanda ya dinga ratsa sassan jikinsa,idanunsa a rufe amma qwaqwalwarsa ta tafi tunanin data saba,tunanin daya zame mata tamkar al'ada matuqar ya tashi daga gadon baccinsa har zuwa sanda zai koma ya kwanta zuwa wani daren,tunanin dake azabtar dashi qwarai,ya kuma dauke dukkan wata walwala tashi cak fiye da yadda aka sanshi a baya.



       Yana dakinsa yana tsane lemar jikinsa,tare da ci gaba da tattaki zuwa bakin mudubi,kansa yake kalla yana kuma sake goge jikinsa,baisan me yasa ta zauna masa daram cikin kwanyarsa ba,baisan me yasa tunaninta ya zame masa jini da tsoka ba,yabi dukka wata jijiya ta jikinsa,yakeson hanashi zama lafiya ba,wannan wanne irin tunani ne mai naci?,wanne irin memory ne dayake kasa barin zuciya da tunani su huta?,a iya tunaninshi komai ya qare tsakaninsu,tunda igiyar alaqar data hadesu ta jima da warwarewa,yana ganin bai kamata komai yayi zurfi haka ba,tunda dama an shirya shine na taqaitaccen lokaci,amma me yasa?,me yasa komai yake zaune daram a kwanyarsa kamar a yanzun komai ke gudana?.



      Tsaki yaja yana ja da baya daga gaban mudubin bayan ya dauki manshi da yake shafawa ya koma gefan gadon yazauna yasoma shafawa,yana kokawar kauda komai daga kansa kamar yadda kullum yake wannan yaqin,saidai kusan duka a banza ne.



     Wayarsa dake gefe ta dauki tsuwwa,saiya waiwaya ya duba,ammi ce ke kira,ya sanya hannu ya amshi kiran ba tare daya dauki wayar a hannunsa ba,saidai ya sanyata a handsfree

"Kana sassanka ne?"

"Eh ammi"

"Ohkey,ka sameni a sassana,falo na uku,zamuci abincin dare tare anjima"

"To in sha Allah" ya amsa mata yana latse kiran.



        Misalin takwas na dare ya shirya cikin qananun kaya,wadanda sukayi bala'in amsarsa,kyansa da kwajininsa dukka sun fito,ya dauki wayoyinsa sa'annan ya baro sashen nasa.



     Hadiman dake sassansa sunso masa tattaki amma ya dakatar dasu,ya nuna musu bashi da buqata,don haka shi kadai ya dinga ratsa cikin gidan nasu da ya wadata da hasken fitilu tako ina saika rantse rana ce,yanayin iskar kadai ya dinga sanya zuciyarsa cikin yanayi na daban,yaci gaba da takawa a nutse zuwa sassan amminsa.



      Daga nesa ya hangosu sun taho,sun jero da juna shi da ita,suna nufo sashen da yake shima,kanshi ya dauke kamar bai gansu ba,saidai kwarjininsa daya cika shi dashi tun daga nesa ya gaza wucewa shima,ya tako zuwa inda yake ya masa sallama yana miqa masa hannu.



     Amsa mishi yayi ya bashi hannun shima ya soma gaidashi ya amsa yana duban walida,wadda baqinciki da takaici kamar ta mutu,ya jefa mata wani kallon gargadi sannan yajuya yaci gaba da takawa ya barsu a wajen.



      Kitceh kitchen tayi da ranta,saiya saki murmushi

"No way idan ka ganshi dole ba zaka iya wucewa ba,ke kanki duk sanda kuka hadu laushi kike qara yi bare ni da nake a matsayin suruki,yana da kwarjini da cika ido" tasan da hakan sarai,amma saita tura baki

"Duk kwarjininsa amma dai qanina ne ko?,shi ya kamata idan ya ganka ya soma gaisheka" dariya yayi yana kada kai,ita kanta yasan ta fada ne kawai,amma ba abinda zai yiwu bane,haka ya lallabata sukaci gaba da takawa.



      Har aka gama serving dinsu babu wanda yace uffan,sai data gama zubawa ta tafi sannan fulani taja nata abincin gabanta tasoma ci,maimakon taga yaja nashi abincin sai taga ya janyo babban jug din tangaran wanda yake cike da ruwan tattacen inibi yahau zubawa yana dirkawa cikinsa,bata ce masa komai ba har taci kusan rabin abincin

"Hala a qoshe kake kenan?" Kai ya jinjina

"Banajin yunwa ne..." Bata kuma cewa komai ba,amma tana karance dashi har ta kammala sannan ta dubeshi

"Batun ci gaba da karatunka....har yanxu baka kammala zabar universty din da zaka ba?" Kwata kwata a yanzun bashi da wata sha'awa ta tafiya wata qasar again,uwa uba ma dukka wani buri da shima ya ciwa karatunsa a yanzun babu shi,tamkar wanda aka zarewa dukkan wata sha'awa da burinsa,amma a yanzun yana da yaqinin furta hakan ga ammi ba qaramin qalubale bane,tunda ba abunda take son ji ba kenan.



      Boyayyiyar ajiyar zuciya yasaki yana hade hannayensa waje guda

"Zan duba in sha Allahu"

"Baka kai ga soma dubawa ba kenan?"

"Sai nan gaba" ya fada don mutum ne shi da abune mawuyaci,ta riga data sanshi,don haka saita gyada kai kawai tana dubanshi tare da karantar sauyin yanayi muraran tattare dashi.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 40


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




       Zaune take tsakiya ateeq da najwa da suka baza litattafansu tana koya musu assigment,yayin da hisham yake zaune saman cinyarta yana wasa da wani abun wasan yara da ake daura musu a hannu,haule kuma na kitchen tana hada kayan girkin da anty zuhriyya ta sata ta hada din kafin ta sauko daga sama,saboda abune mawuyaci kaga ta sakarma haule dukka girkin gidan idan ba wani babban uzurine ya taso mata ba wanda bata kusa ko bazata dawo gida da wuri ba.



      A hankali ta daga hannunta ya dafe bayan wuyanta dashi,saboda yadda takejin jikinta na wani irin ciwo,qashinta kamar ana sassara mata shi,yayin da takejin zazzabi nason kamata,saisai babu alamunsa saman fatarta,da alama zazzabin cikin qashine,daurewa ta dinga yi ganin sun kusa gama assigment din,a haka a anty zuhiryya da a yanzun take kiranta da mami kamar yadda yaranta ke kiranta ta sauko daga saman nata tana dubansu.



       "Kinga ta kanki daughter,wai har yau ba's gama aikin bane" idanunta ta daga cikin wata iriyar kasala da dandatsar da takeji a qashinta tace

"Eh....mun kusa amma" fuska anty zuhriyya tadan yamutsa tana kallon bilkisu

"Daughter....anya lafiya kuwa,kinga yadda idanunki suka sauya kala" itama yamutsa fuskar tayi

"Banajin dadi ne,kamar zazzabine yakeson kamani" da hanzari ta taho inda take tana dauke hisham daga saman cinyarta

"Ashsha...tun yaushe kuma amma kika tsaya kina wani aikin daban,maimakon ki samu waje ki kwanta,maza tashi ki dauko paracetamol guda biyu kisha ki kwanta,zuwa anjima kadan mu gani,idan baki samu relief ba ki shirya nasiru driver ya kaiki kiga likita" bata musa ba ta miqe,sai a sannan taji da gaske ashe jikin nata babu dadi,ta dinga takawa a hankali harta shige dakin da suke ajiyar magunguna,ta balli paracetamol din guda biyu tasha sannan ta wuce dakinta.



       Kai tsaye gado ta fada taja duvet ta lulluba sosai tana sakin ajiyar zuciya saboda yadda taji qashinta na mutstsuka,tadan jima a haka sannan bacci yayi awon gaba da ita.



       Sanda ta farka taji dama dama,don harma ta sake wanka don ta kuma jin dadin jikinta,takuma shirya ta sauko qasa akaci abincin dare da ita,lokacin kwanciya yayi ta dauke najwa tace tare zasu kwana suka wuce dakinta.



        Saidai tsakiyar dare ciwon ya dawo mata sosai,harta kasa jurewa,ta dinga sakin nishi tana murqususu,ga wani dan banzan zazzabi mai kama da an kara mata wuta,hatta da numfashinta huci yake bayarwa,najwa nata bacci batasan me yake faruwa ba,sai gab da asuba da fitsari ya tasheta sannan ta gani,abinka da yarinta dakuma rashin sabo duk sai ya rude,ta juya da sauri ya fice daga dakin don sanarwa mamin nasu,duk da bilkisu tayi yunqurin tsaidata kada ta tashesu suna bacci.



      Minti biyar yayi yawa suka dawo tare ita da anty zuhiryyan,sanye da hijabi da alamun bacci take ta tasota,a hanzarce ta isa inda bilkisun take tana riqeta,yadda taji zafin da jikin nata ya dauka ya daga mata hankali,saita saketa tana cewa

"Bari na yiwa abbaa magana,inaga gwara kawai mu wuce asibiti" bata da sauran qarfin da zatace komai saboda yadda taketa rawar dari,kai kace an sakata ne cikin kogin qanqara.



       Cikin daren ya fidda mota suka wuce asibiti,sukabar yaran a gida su da haule,wanda suna zuwa cikin sauri aka karbeta,sannan aka bata dukkan taimakon daya kamata,cikin awa guda saiga bacci ya sureta,sai a sannan hankalin anty zuhriyya yadan kwanta.



        Da safe likita ya bada test na malaria da typoid yace ayi mata bayan ya tambaya tana da aure antyn tace aah,baccin da take yasa aka jinkirta yin test din har zuwa sanda zata tashi.



     Bacci tayi sosai saboda allurai da ruwan da aka saka mata,bata farka ba sai kusan azahar,anty ta taimaka mata saboda jirin da tace tana ji,ta shiga bandaki ta wanke bakinta,tayi alwala tazo ta rama sallar asuba data kubce mata,sannan ta dora da azahar,sai a sannan antyn ta zuba mata farfesun kifin da haule tayi da dankali jifa jifa a ciki,ya dahu sosai yadda zaiyi dadin ci,ta matso da kwanon kusa da ita

"Bismillah,ungo" ta fada tana miqa mata cup mai dauke da ruwan tea mai zafi bayan ta tura mata kwanon kifin gabanta,kanta ta dauke tana kada kai

"Bakina babu dadi ummee,kuma bana jin yunwa ma kwata kwata,cikina a cushe yake"

"Idan kika ci ko babu yawa zakiji dadin bakinki,sannan bazai yiwu ayita baki magani ba amma babu komai a cikinki,likitan dama yace idan kin tashi kici wani abu,kema.kya dan sake jin qwari,don lab zamuje yanzun za'a miki test".



      Batason mata musu,don haka ta saka hannu ta karbi ruwan tea din,kurba uku tayi mishi taji cikinta na juyawa,hakanan ba zata iya ci gaba da sha ba,saita dire tana cewa

"Ummi wallahi kaman xanyi amai,don Allah ki qyaleshi" yadda ta fara yunquri ya nuna mata da gaske take,don haka ta qyaleta,bata yi mata maganar test bama sai data kwanta tasake hutawa sannan sukaje lab din.



      Washegari result ya fito,malaria din ne da typhoid,saidai malaria yafi yawa,nan anty zuhriyya ta dinga sababi

"Dama a wannan gidan kowacce irin cuta ma ba samunta za'ayi ba tunda babu mai kula dakai,mun godewa Allah daya sanya iya tsahon shekarun ciwon da kika samu kenan".



       Kulawa sosai ta samu a asibitin,satinta guda sa'annan ta samu sauqi suka bata sallama suka dawo gida.



*_BAYAN KWANA BIYU_*



      Babu bata lokaci anyy zuhriyya tayi ma bilkisu registration na waec da neco,hakan ya sanya gaba daya bilkisu ta maida hankalinta kan karatu,duk wani buri nata ya sake dawowa sabo,kwadayin karatunta da karsashinta suka sake dawo mata,ta bude can wani saqo na zuciyarta data tattara dukkan burin karatunta ta cusashi a ciki ya zaqulo abinta ta sabunta shi,tunda a yanzun tana ganin ta samu dukkan wata dama data dace,hakanan babu wata sauran matsala da zata dakatar da ita.



       Lafiya qalau ta zana waec dinta,cikin sauqi,don duk yadda ta zaci abun zaizo mata da wahala ta dinga jin tsoro duk da karatun da tayi sai taga duka ba haka bane,tazarar kwanaki suka soma neco.



       Ranar farko lafiya lau taje itama ta dawo gida,saidai a komawa ta biyu ta soma jin jikinta babu dadi,kamar rashin lafiyar datayi a kwanakin baya tana son dawo mata,don haka ta fidda magungunanta da dama basu qare ba tun wancan lokacin ta sha,ta danji dama dama,sun kuma taimaka mata ta qarasa zana jarabawarta,har zuwa ranar da suke da paper qarshe.



       Tun a makarantar da take zana jarrabawar ta soma jin kanta na juya mata,hakanan qafafunta basu da wani isasheshen qwari,a daddafe ta dinga amsa tambayoyin,tana yi tana dakatawa ta huta,a haka harta kammala,inda Allah ya taimaketa tuni drivern anty zuhriyya yana waje yana jiranta,don haka bata wani tsaya ba ta tattara ya nata ya nata ta fito,tunda dama babu wanda ta sani,kuma iya zuwanta bata bari tayi sabo da kowa ba,abinda ya kaita shi kadai takeyi,data gama take tafiyarta.



      Tunda ta shiga motar take dafe da kanta,don tana daga zaunen amma jiri takeji,hakanan numfashinta na mata nauyi,Allah Allah take su isa gida ta samu waje ta kwanta sosai ko zata samu relief.



        Suna isa ta bude motar ta fit,tana tafiya tana hada hanya,kallo daya zaka mata kasan ba lafiya qalau take ba,a haka ta isa falon gidan,anty zuhriyya ce kadai zaune tana kallo,duka yaran na makaranta lokacin tashinsu baiyi ba,sai hisham dake zaune a gefanta yana shan madara.



      Yanayin sallamarta ya sanya anty zuhriyya dubanta tana amsa sallamar

"Yadai daughter?" Ta tambayeta tana qare mata kallo,ba zata iya wani dogon tsaiwa ba don kada ta fadi,saita doshi dakinta tana cewa

"Bab....ba komai ummi" saidai kafin takai ga isa tuni jiri ya debeta tayi luu zata fadi,cikin mugun hanzari anty zuhriyyan ta nufeta ta tallafota tana kiran sunanta,idanunta nakan fuskar antyn sanda numfashinta ke qoqarin daukewa,sannan a hankali dukka idanun nata suka lumshe.



      Abinda yayi masifar daga hankalin antyn kenan,tasoma qwalawa drivern daya kawota kira ba tare da tayi la'akari da cewa babu lallai ya jita ba,ganin babu alamun yana jinta ya sanyata riqe bilkisun ta kwantar da ita saman kujera,sannan ta fita harabar gidan cikin hanzari tana sake qwala mishi kira,tunda babu kowa gidan ta aiki haule kasuwa.



       Allah yasa yadan tsaya magana da me gadi a qofar gate din kafin ya fice yaje dauko su najwa,yanayin kiran ya alamta mishi ba lafiya,saiya taho da hanzarinsa

"Maza bude mota,daughter ya fadi" ta qarasa fada tana komawa cikin gidan cikin gudu gudu sauri sauri,sai data sake duba bilkisu cikin tsoro da firgici sannan ta haura dakinta ta yayibo hijabin sallarta tazo ta sake kamata zuwa cikin mota,sai data kwantar da ita sannan ta dawo ta dauki hisham daketa qwala kuka,ya zaci tafiya zatayi ta barshi,hankalinta a matuqar tashe,don ko abbaa batasamu damar gayawa ba saida suka isa asibitin aka karbeta sannan ta daga waya ta gaya mishi.



        Jiki a sanyaye ta isa office din likitan tana fargabar wanne ciwo kuma keda bilkisun har haka,rabbi kada yasa wata mummunar cutar ce kuma ta daban ta kamata.



       Cikin qwarara gwiwa abbaa da suka shigo tare ya dan taba kafadarta yana nuna mata wajen zama,don daya tashi daga office nan ya biyo,yaran kuwa tunda aka daukosu daga makaranta tasa aka wuce dasu gida wajen haule,ta isa inda ya nuna matan ta zauna abbaan yana binta da kallo,yasani cewa indai akan bilkisu ne raguwa ce,bata da wani jarumta ko qwarin gwiwa ko kadan,qaunar da takewa 'yaruwarta ce gaba daya ta tattarata ta koma kan bilkisun,batason duk wani abu da zai sameta,ya dade da shaida hakan tun bilkisun batakai haka ba,shidin bai zauna ba,saiya tsaya kawai saman kan zuhriyyan suna sauraren bayanin likita.



        Dukka test test din da akayi mata ya tattara ya zuba cikin file dinta sannan ya dubesu

"Mara lafiyarku tana da aure ne?" Cikin mamaki anty ta dubeshi

"Me yasa ka tambaya likita?" Kafadarshi ya daga sannan yace

"Eh,na ganta da unifoarm ne,sannan sakamakon gwaje gwajenta kamar bai dace da yanayinta ba" cikin daure kai ta sake amsa mishi

"Bata da aure" saiya dafe goshinsa sannan yace

"Ya salam" kusan abbaa yaso gano meke faruwa,don haka yayi gyaran murya

"Amm,likita ta taba aure,sannan bata jima da rabuwa da mijin ba" yanayin fuskarsa ya sassauta,saiya saki goshin nasa ya dago yana dubansu

"Good....to tana dauke da juna biyu na sati goma sha biyu"

"What!" Anty zuhriyya ta fada cikin wani irin tashin hankali,har tana miqewa idanunta dukka a waje tana duban likitan,duk da shima abbaa sakamakon ya bugeshi,amma sai yayi hanzari kama hannun zuhriyyan

"Relax zuhra....likita" ya kirashin yana dubanshi

"Bilkisu bilyamin muke magana fa?" Kai ya gyada

"Yes,ba wadda kuka kawo da azahar ba student?,shi yasa na soma tambayarki before na gaya muku sakamakon,ba typhoid yanzu a jikinta,sai malaria 'yar kadan da kuma juna biyun da take dashi" ya sake karanto musu sakamakon bayan ya sake bude file dinta yana sake karanto bayanan da aka rattaba jikin takardar,sai daya qare sannan ya daga kai yana dubansu

"Bada ubanshi ba?" Yakuma tambayarsu cikin mamakin tashin hankalin daya gani saman fuskar anty zuhriyya,murmushi abbaa yayi

"Da ubansa,kasan shiriritar mata,saboda nasa tare da mijin kuma ga ciki shine abinda ya daga mata hankali" murmushi ya saki

"Hajiya qaddarar ubangiji ai tafi gaban haka,babban abun godiyar shine daya kasance ba shege bane"

"Hakane kam....mun gode likita" ya fada yana bashi hannu sukayi musabaha,sannan yaja hannun anty zuhriyya da tuni da daina ganewa ko jin abinda suka tattaunawa a kai.



      Kuka ta fashe mishi dashi suna fita daga office din,ta dora kanta saman kafadarsa tana jin wani abu yana sukar zuciyarta,wannan zalunci ne,zalunci ne mai yawa,me yasa basuyi amfani da matakan kariya ba tunda sunsan ba zama zasuyi da ita ba donsu sauqaqe mata wahala,ta gama wancan zaman da yafi kama dana fursuna,sa'annan yanzu ga wata sabuwa ta bullo?

"Kiyi haquri zuhra hakanan don Allah,kaman yadda likita ya fada ne,mu godewa Allah daya kasance ba shege bane da ubansa"

"To meye marabar dambe da fada abbaa!" Ta fada a zafafe tana daga kanshi daga kafadarsa kai kace shine ya aikata dukkan komai,saiya saki murmushi,yasan kan kayarshi sarai,ya janyeta zuwa cikin motarsa yazaunar da ita seat din baya shima ya zauna gefanta,hannunshi ya saka cikin nata yana dubanta

"Nidai zuhrar dana sani jaruma ce gsky ba raguwa irin wannan ba,kin taba ganin bawa yayi kokawa da qaddararsa?,baki godewa Allah daya saka dan halas ne?,duk tsiya saida aka biya sadaki aka shafa fatiha sannan aka samar da cikin?,sannan wannan kukan da kike shi xaki ci gaba dayi har yarinyar ta farka ta gani,ki karya mata gwiwa kisake sata a zulumi,maimakon taga qarfafa gwiwa a fuskarki da rashin damuwa,wanda hakan shi xai qaranta tata damuwar da rungumae qaddararta,har a samu yadda akeso" cikin hikima da sanin makamar matarsa ya dinga gaya mata kalaman da suka saukar mata da nutsuwa,suka kuma sanya mata kwanciyar hankali,sun jima cikin motar sai daya tabbatar yayi cooling temper dinta sannan ya qyaleta,saidai daga qarshe ta dubeshi

"Amma abbaa dole susan da zaman cikin nan" kai ya gyada

"Eh,wannan ya zama dole,kuma haqqinsu ne dama su sani saboda gaba" wannan din itama yayi mata,don haka ta gyada kai tana sauke ajiyar zuciya,saidai can qasan ranta tana jin zafi tare da baqincikin yadda suka sanya rayuwar 'yarta cikin walagigi bisa tsarinsu da kuma son zuciyarsu.



       Bata koma dakin ba sai data tabbatar zuciyarta cikin kaso dari kaso hamsin ya sanyaya,don ko abbaa bai amince ba batajin wannan karon za'a musu shuru,gwara susan da abinsu,kuma koda ta haihu su dauki abinsu ita kuma taji da rayuwar 'yarta.



       Tana tura qofar dakin idanunta akan bilkisu,ta waiwayo suka hada idanu,yadda ta kalletan sai taga kamar tasan yanayin data kuma fadawa,hakan ya karyar mata da zuciya,qwarin gwiwarta ya ragu,tausayinta ya kamata,ta fito daga wata jarrabawar yanzu gashi katsam ba zato ba tsammani ta fada wata,me yasa tun sanda ta dawo bata kawota an dubata an tabbatar babu ciki ba,da ta sani tun kafin abun yayi nisa da wala'alla an samu mafita akansa,qaddara ta tabbatar ita ta hana kawo bilkisun a bincikar mata lafiyarta da kyau.



     Ta farka idinta biyu,saidai tana kwance a yadda take bata motsa ba,murmushi tayi mata sanda take tambayarta ya jikin nata

"Da sauqi ummi" yanda tayi.maganar sai ta sake ganin ta koma mata maimunatun ta,da sauri ta miqe daga kan kujerar da take kai jin qwalla na shirin zarto mata,ta isa ga drower din da abbaa yayi musu siyayyar kayan tea tana fito dasu,saida ta saisaita kanta sannan ta dawo.inda take tana duban ruwan da aka saka mata sannan ta maida kanta gareta

"Ya kusa qarewa,bari na musu magan suzo su cire miki ki samu wani abun kici" kai ta gyada mata ta juya ta fice ba jimawa suka dawo da wata nurse ta cire mata,ta taimakawa bilkisun ta tashi,duk da jirin da takeji ya ragu sosai.



       Sai data kaita bandaki tayi alwala sannannta dawo ta shinfida mata abun sallah,yanayin anty zuhriyyan data canza ya bawa bilkisu mamaki,duk da batace komai ba amma ta lura komai da takeji jikinta a sanyaye yake,itadai bata tambayeta ba tahau abun sallar ta tada salla.



      Sai data gama dukka sallolinta sannan ta zuba mata abinci tace ta matso taci,kaita soma kautarwa sabida wani tashin zuciya da amai data soma ji sanadin shaqar warin abincin,ta girgiza kai

"Bazan iya ci ba ummi" fuska ta bata

"Dole kici daughter,ta yaya zaki zauna ba abinci,kina so muyi fada kenan?" Kainta girgiza qwalla na cika mata idanu,tunda take bata taba jin irin wannan feeling din ba na batason ganin abinci kojin qamshinsa ba sai yanzu,kamar an nuna mata bindiga haka taji

"Kiyi haquri ummi,wallahi bazan iyac....." Bata qarasa ba amai ya taso mata,tahau yunqurin aman da babu abinda ya fito saboda babu komai cikinta,sosai ta galabaita,don har sai da nurse din ta dawo,ta mata wata allura sannan aka sake maida mata ruwa,ta lumshen idonta tana sauke ajiyar zuciya sanda take akwancen,don babu abinda tafi buqata irin kwanciyar,gefe guda kuma tana mamakin wanne irin ciwo ne haka takeyi?,azaba da wahalar da takeji bata taba jin irinta ba,a haka bacci ya sake daukanta,anty zuhriyya na zaune gefanta tana ta qoqarin boye hawayenta.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 42

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





      Tsayin lokaci yana firfitar gamida mai maitaba innalillahi,ita kuma tana zaune tana kallonshi tare da mamakin rudewar tasa,shi duka baiyi wannan lissafin ba,ko tsabar rainin hankali ne kawai.



          A hankali ya aje hularshi gefe sannan yace

"Yanzu meye abunyi?" Baki ta tabe

"Bansan muku ba,tunda badani aka qulla ba,abinda na sani kawai shine,ta inda aka hau tanan ake sauka,kasan dukka hanyar da zakabi ka sanarwa da uban cikin ajiyarsu dake jikin 'yata,bama buqatar wani abu face su kwana da sanin akwai jininsu a jikinta" daga haka ta yunqura ta miqe,sai yayi saurin dakatar da ita

"Ya zaki tafi kuma?" Kallon banza tayi masa

"To ce maka akayi dama zama nazo yi?,saqo nazo isar maka,kuma tunda ya isa shikenan" daga haka ta juya tayi ficewarta daga falon,ta tsaya ta kirayi bilkisu suka wuce.



      Tashin hankalin da bai tana zaton zaijishi ba shi yakeji,gumi ne kawai ke yanko masa ta kowanne sashe da loko na jikinsa,bai taba hasashe ko tsammanin faruwar hakan ba,bai taba kawo hakan zai iya faruwa ba,ko kallon mama ladi dake faman tambayarsa abinda yake faruwa cikin salon bugun ciki baiyi ba.



      Zumbur ya miqe yana maida hularsa dake ajiye dafa'an a gefe saboda hasashen da qwaqwalwarsa ta bashi

"Ina zaka haka kuma malam?,wai wanne irin jarababben albishir wannan masifaffiyar matar tayi maka daya daga maka hankali haka,bayan nasan babu kalar abinda baka gani ba"

"Rayuwar 'yata....." Kawai ya fada yana yin gaba.



       Yana tafe shi daya yana zancan zuci da qananun sumbatu,tabbas ta inda aka hau tanan ake sauka kamar yadda zuhriyya tace mishi,dole susan da zaman cikin,saidai bashi da wani yaqini ko tabbacin xasu amshi maganar,tunda sun riga tunda fari sunzo da dukkan sharudda nasu,shi kuma ya karba hannu bibbiyu ya amince musu,a lokacin da idanunsa suke a rufe,matsera yake nema kawai da hanyar da zai kubuta daka dukan da talaucin yake masa tako ina,bai tsaya wani dogon nazari ko tunani ba,sai gashi yau wannan al'amarin ya sameshi bagata tan.



      Baiyi burki ko ina ba sai qofar gidan umma luba,wanda idan ka ganshi a yanzu ba zakace shi bane,saboda rushe mata shi akayi gaba daya aka sake mata sabon gini me bene,aka qawatashi da qaramin gate da fenti mai kyau harda shukoki,bayan umarar da sukaje tare da malam bilya din,da kuma kudade da aka danqa mata wanda suka isheta jari,bayan matsayi da fulani ta sake qara mata a masarautar kaisan.



        Bakinsa cike fal da addu'ar Allah yasa tana nan ya sake gyara tsaiwarshi ga qofar gidan,ya kirayi wani yaro dake shirin giftawa,ba musu yaron ya qaraso da hanzari

"Shiga gidan nan maza  kace ana sallama da luba" ya amsa mishi sannan ya tura gate din gidan ya shige,babu jimawa ya fito ya gaya masa tana zuwa.



      Shudewar mintuna biyu aka taba qofar sannan aka budeta,umma luba ta bayyana,ganin malam bilya saita saki murmushi,har haqorin makkan data maqala yana bayyana

"A'ah,dama kaine.....aida ka shigo daga ciki ko?"

"Shigowar nan kuwa zata yiwu?,don gsky a gaggauce nake" cikin mamaki take dubanshi

"Koma meye ai shirin zaune yafi na tsaye ko?" Bai sake tankawa ba yabita a baya,basu tsaya ba har zuwa madaidaicin falon gidan,da aka qawata da kayan zamani.



       Suna zama ta kira mai aikinta ta kawo masa lemo,don yanzun me aiki gareta,wadda take kula mata da gidan idan ya tafi gidan maimartaba

"Bar lemon nan luba.....babban tashin hankali ne ta tunkaroni ko ince ya tunkaromu" qirji ta dafe cikin razana ta fidda idanu

"Mun shiga uku!,wani abune ya faru?" Sai daya sanya gefan babban rigarsa ya sharce gumin fuskarsa,duk da sanyin acn dake falon wanda umma luba ta qure tana morewa jin dadin duniyarta,takan ce sai tayi qara'i yadda ya kamata,tunda hutun baizo mata a quruciya ba,yanzunma da yazo mata duk daya wai mamaci ya karye.



       "Bilkisu 'yar wajena,mai gado,juna biyu gareta....juna biyun yarima"

"Tashin hankali!" Umma luba ta furta tana zama sosai saman kujera gamida fidda idanunta waje sosai,kamar wadda bata gani,zallar tashin hankalin data furta a bakinta yana bayyana qarara saman fuskarta

"Wannan wanne irin bahagon lamari ne,ya akayi haka ta faru?,me yasa dukkanmu bamuyi tunanin yuwuwar afkuwar hakan ba?" Ta qarashe maganar tana kallon malam bilya,karon farko a bigiren farko da yaji kishin jininsa,don haka saiya hade rai tsam,shima yaso yadan motsa qwanjinsa wannan karon ko yaya ne,kamar yadda yaga zuhiryyar tayi

"Oho,wannan kuma bani zaki tambaya ba,abu daya ne,kawai ki shaida musu abinda ke faruwa,so ake su sani kawai,bawai wani abu ake bida daga wajensu ba" shuru tayi tana juya maganarsa cikin ranta,kowanne daya cikin biyun zai iya yiwuwa,imma dai idan tayi shuru nan gaba har aka haife abinda aka samu ta shiga sahun masu laifi wajen fulani,wanda hakan zai jawo mata matsala,inma kuma taje ta shaida mata hakan ya zama tashin hankali ko kuma ya ballo da wani ruwan,to kowanne tayi ciki tana zato da kokwanton babu mafita,amma kuma da ace shurun tayi wani abun ya bullo bayan watanni suyi kuka da ita,gwara ta shaida musu tun yanzun sunsan da maganar.



       Shaidai malam bilya miqewa yayi ya kade babbar rigarsa ya qara gaba,saidai koda ya isa gida kasa shiga yayi,yayi zaune anan qofar gida lamarin na masa kai kawo,yana jujjuyashi cikin ransa tare da hasashen meke iya faruwa nan gaba,wala'alla hakan ya qara masa daukaka da girma na hada jini da masarauta,wala'alla kuma ya sake fadawa wata daban.



       Dukkaninsu shi da umma luban a wannan daren basuyi wani isashen barci mai dadi ba,kowa da zancan ya kwana a ranshi yana juyashi tare da taraddadin meye zai biyo baya?.



       Washegari sam bata da agender na shiga masarauta,a yadda ta tsara sai jibi,amma zuwan ya zame mata tilas don isar da wannan saqo zuwa kunnuwan fulani,don haka tun goma na safe ta gama shirinta ta doshi masarautar kaisa.



       Sanda taje akwai baqin da fulanin ke ganawa dasu,tadai shaidawa jakadiya zuwanta,ita kuma ta shaidawa fulani,sai kuma tayi zaman jiran ayi mata iso.



      Lokacin da aka bata izinin shiga ita kadai tasan yadda ta dinga ji,gumi ya dinga karyo mata,qafafunta babu qwari ta dinga kutsa kai falon,cike da taraddadin sakamakon da maganar zata bayar.



      Sanda ta shiga tana zaune saman daya daga cikun kujerun alfarma dake wajen,fuskarta a sake take duban luba harta qaraso,ta zube cikin girmamawa a gabanta

"Allah ya taimakeki....ya baki yawan rai...Allah ya iya miki yakuma dafa miki,ya danqwafar da maqiyanki,ya qasqantasu a gabanki.....barka da warhaka ranki ya dade" murmushi tayi har cikin ranta tana jin dadin addu'ar da luba tayi mata

"Yauwa sannu luba,barkanmu....ya iyali"

"Kowa lafiya Allah ya baki yawan rai"

"To madalla,haka mukeso" shuru umma luba tayi tana jujjuya maganar,harsai da fulani ta fuskanci akwai magana bakinta,ta dago tana gyara zamanta sosai sannan tace

"Lafiya dai ko?" Kanta zuwa gefan fuskarta ta shafa,tana jin wani irin rashin sukuni

"Lafiya amma ba lau ba"

"Uhmm,gaggauta sanar dani,meye yake faruwa?" Zama tayi sosai dirshan,don a jikinta tana jin cewa maganar ba qarama bace

"Wato Allah ya baki yawan rai,jiya da daddare bayan sallar isha'i,mahaifin yarinyar nan da aka yiwa auren shekara daya da yarima Allah ya qara masa lafiya.....yazo ya taddani har cikin gida..." Saikuma tayi shuru,cikin sakanni da basu wuce biyu ba yanayin fuskar fulani ya sauya,ta zuba luba idanu tana kallonta

"Uhmmm,ina jinki,ina fatan jin badai wani abunne zai biyo baya ba,tunda mun riga da mun gama tsarawa da kuma qulla dukkan wata yarjejeniya dasu ko?"

"Allah ya taimakeki,tuba nake,amma kusan kamar baya ce ta haihu"

"Ki hanzarin fayyacemin komai,baya ce ta haihu kamar yaya?" Ta sake tambayar luba kamar mai shirin miqewa tsaye

"Yarinya dai juna biyu gareta" ta fada a hankali kamar batason fadar.




        Wani irin rugugin aradu ne ya gifta saman kan fulani aisha,zuciyarta ta wani damqe waje guda na sakanni

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un?,garin yaya haka ta faru?,ya akayi haka?,ya akayi wannan kafar ce kawai.suka bari basu tosheta ba?,saboda tayi tunanin yariman zai kauce mata da.kanshi,tayi tunanin ko bata toshe ta ba shi xai toshe da kansa,tunda yasan irin auren da nau'insa,amma ya akayi basira ta bace mata bata jaddadawa sodangi ba?,me yasa basira ta bace mata bata gayawa ita kanta luba din ba?,ya akayi basira da wannan tunanin aka daukeshi cak daga kwanyarta?,me yake shirin faruwa?,tonuwar asirinsu?.



      Batasan ta miqe tsaye har tana safa da marwa ba saida kalaman umma luba suka dawo da ita hayyacinta

"Allah ya huci zuciyarki,ki dade ki qarko,babu abinda zai faru fiye da abinda kike son ya farun"

"Kije zan nemeki" shine amsar kawai data iya baiwa umma luba,saboda ba al'amari bane da zata yanke hukunci da hanzari ba,akwai buqatar tayi zuzzurfan tunani akai,tunanin da ita daya take buqatar yinsa,ta kuma yanke shawarar abinda zai fishsheta,don wannan karon bata da buqatar kowa yaji ko yasan me ya kuma afkuwa.



       Da hanzari umma luba ta miqe tana godiya,sallamar data mata a lokacin tayi mata dadi,don dama Allah Allah take ta matsa daga wajen,saboda kwarjinin fulanin dake sake sanyata cikin firgici da dimuwa.



      Wunin ranar kaf cikin wani mawuyacin hali tayishi,maganar taketa maimaitawa tana dorata bisa mizani iri daban daban,duk hukuncin data bata sai taga batayi mata ba,tabbatuwar cikin da wanzuwarsa tamkar barazana ce ga duk wani sirri nata da kuma rayuwar azeez,zubewar mutuntakarta taba qima sa darajarta data ahalinta gaba daya.



       Ranar kaf bata sake bari kowa ya ganta ba,har zuwa dare sanda take zaune gefan gadonta sanye da kayan bacci,hannunta dauke da cup tana kurbar tea wanda ta tilastawa kanta sha don kada ta kwanta da yunwa,maganar ce dai a ranta take sake juyata gami da yi mata fashin baqi.



      Dire cup din tayi da sauri,saboda wata magana da tayi amsa kuwwa cikin kanta

"Karki zama shashasha mana.....daga sun fadi magana ki dauketa gaske..." Maganar ta shigeta sosai,sai tayi tsam da hankalinta tana dora maganar kan ma'auni

"Tabbas talakawa ne wadanda basu da komai,mahaifinta ma'abocin son abun duniya ne,babu wanda yake irin yanayin da suke ciki,wanda xai shiga daula irin haka kuma lokaci daya ayi handing over dashi ya yarda ya karba,ya kuma fita salin alin ba tare daya qirqira wasu abubuwa da zasu biyo baya ba,kudi qalilan sukan ruda irinsu,su kuma sauya musu hali da alqibla,ba shakka zasu iya komai saboda komai yaci gaba da tabbata tsakaninsu,waya sani ma ko sun qirqiro maganar ne don suyi blackmail dinsu.



      Murmushi ya kubce mata,sanda ta tattara dukkan bayanan da kwanyarta ta bata na cewa qarya suke,babu wani ciki,sunaso ne kawai suyi amfani da wannan hanyar su dinga tatsar dukiya daga garesu

"Da sun sani bata haka suka biyo ba,tabbas basu san wace aisha ba,da sun fadi abinda sukeso kawai cikin girma da an basu,albarkacin igiyar auren data taba gittawa tsakanin d'ana da d'iyarsu" ta furta a sarari,tana miqewa,sai a sannan taji duk wani nauyi da kanta yayi,da cushewa da cikinta yayi ya warware,har taji wata yunwa,sannan taji tana buqatar abinci,don haka tamiqe ta fito don bada umarnin a gabatar mata da abinci.


   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶


      Hakanan cikin daren bacci suka qauracewa idanuwansa,ya takurawa kanshi da tuhuma da tambayar me yake damunshi ne haka a kanta,sau nawa ya ganta da zata zauna haka cikin zuciya ruhi da kuma gangar jikinsa,har yake jin kamar yabar wani abu nashi tattare da ita?,kodon itace mace ta farko daya soma sharing ainihin abinda ake kira da rayuwa da ita?.



      A hankali ya dauko wayarshi dake dake aje a gefe,hakanan saiya samu kanshi da bude tsohon saqo,tsohon saqon da bai sake bi ta kansa ba tunda aka turo mishi,tsohon saqon da bai taba tunanin xai waiwayeshi ba,sai gashi yau ya samu kanshi da budewa,saqon da ammi ta tura masa na hotonta tun lokacin da ake zancan hada aurensu,yana tunanin idan ya gan hoton zai samu relief.



       Saidai tunaninsa ya saba,wani irin abu yaji yana ratsa zuciyarsa,wani irin feeling mai kama da kayi kewa da abinda kayi matuqar sabawa dashi,hankalinsa ya sake tashi fiye da dazun,don haka ya aje wayar ba tare daya fita daga gun hoton ba ya miqe.



     Bandaki ya fada kai tsaye,ya sakarwa kansa ruwa,wanka yayi cikin mintina ashirin,sannan ya fito ya soma shiryawa.



      Cikin lokaci qanqani ya gama shirinsa cikin wani kyakkyawan yadi da yaji aikin sarauta,yayi masifar dacewa dashi hakanan ya fidda ainihin shi din waye,sai da yagama feshe jikinsa da turarukansa sa'annan ya duba agogo,ya tabbatar yanzun ammi batayi bacci ba,idan ma ba abincin dare take ci ba,to bata jima da gama ci din ba,mai yiwuwa suna falonta ita dasu afnan,kamar yadda takan zauna dasu a yawancin lokuta.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 41

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*

*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*

*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

___________________________






        Cikin sati guda rak wani irin laulayi mai azabatarwa ya rafeketa ba tare da ita kanta tasan laulayin take ba,don sam anty zuhriyya ta kasa gaya mata,gani take abun saiyayi mata yawa,babu abinda take iya ci ya zauna cikinta qalau,koda ruwa ne sai anci babbar sa'a bare akai ha abinci,hakan ya sanya koda yaushe cikin qarin ruwa take,ta zabge ta sake yin wani fari bau,gefe daya ga wata rama ta musamman datayi,dukka kayanta basa zaunar mata a jiki sun mata yawa,don wani lokaci rigunan najwa zuhriyya ke kawo mata ta saka,saboda tana da dan jiki,hakanan batanson hayaniya ko hasken rana mai yawa,wani irin azababben laulayi daya sanya anty zuhriyyan ta dinga mata kuka a boye,idan ka ganta saika zaci ba zatayi raiba saboda yadda take azabtuwa,itakam.har fatan cikin ya zube anty zuhriyya takeyi cikin ranta

"Wannan baqar qaddara taki Allah ya yanke miki ita bilkisu" haka take yawaita fada,saboda ganin irin yadda takeshan wahala da cikin da batasan ma yana maqale a jikinta ba.



       Wata guda cur da satittika wajen uku sukayi a asibitin,sannan aka dan fara samun sauqi,har zuwa sannan batasan da wani ciki ba,saboda bata cikin nutsuwarta bare hankalinta da har zata lura da wani sauyi ko wata alama.



       Da wani yammaci ta farka a bacci da wani irin fitsari daya matsota,a lokacin anty zuhriyya tana sallah,idan tana wajen duk sanda zata bandaki saita rakata,qaunar ummin na sake qaruwa cikin zuciyarta dakuma tausayinta,yadda take mata ko najwa ce iyaka abinda zatayi mata kenan a matsayinta na uwa,ta aje dukkan wasu harkokinta ta tattara a wajenta,hatta da gida saidai taje lokaci bayan lokaci ta dawo asibitin,duk hankalinta da kulawarta tana kanta.



        Ganin yau jikin nata da qwari qwari ya sanya ta zuro qafafunta qasa a hankali,ta saka takalmanta ta miqe zuwa bandakin,don yau itama ta tabuka ta ragewa ummin aiki.



        Tana zuwa fitsari sai taga jini,batayi wani mamaki ba,ta kawo a ranta period dinta ce tazo

"Dama naga kamar tayi jinkiri wannan karon bata zo akan kari ba,ko saboda ciwon nan ne" ta fada tana yin tsarki sannan ta miqe,amma sai taji mararta ta riqe,tadan cije bakinta,ikon Allah,tasan bata ciwon mara idan tana al'ada,amma yaya akayi yau mararta ke mata ciwo?,ta tambayi kanta tana fitowa daga bandakin a daddafe.



        Sanda ta fito ummi zuhriyya ta gama sallar carbi take ja,ta zuba mata ido ganin yadda ta fito a duqe,da sauri ta tambayeta

"Lafiya daughter" saidata zauna gefan gadon sannan tace

"Marata ce take ciwo ummi,kamar period ne inaga"

"Periode?" Ta tambaya cikin fargana da faduwar gaba,saita gyada kanta

"Eh"

"Jini kika gani!" Ta fada tana miqewa a hanzarce har bilkisu na mamakin dalilin rudewarta haka,saita sake gyada mata kai

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ta furta sannan ta durfafi qofa da hanzari,binta kawai tayi da kallo cike da mamaki,toko bai kamata ace tana period bane?,tayiwa kanta guntulalliyar tambayar da bata da amsa.



      Sanda likita ya iso ya dubata saiya tabbatarwa da anty zuhriyya wahalar data sha ne bakin mahaifar ke niyyar budewa,saboda haka dole su bata bedrest again kona wata daya ne su gani.



      Lokacin da suke bayanin kawai kallonsu take,kanta a daure tamau,ta kasa fahimtar komai,mahaifar waye zata bude?,waye keda ciki?,kuma wa za'a bawa bedrest?,duk da tambayoyin dake cin kanta bata iya furta ko guda daya ba,taci gaba da binsu da kallo ne harya gama abinda zaiyi ya fice,dakin ya rage daga ita sai anty zuhriyyan.



       Ta lura da dimuwar da bilkisun ta shiga,da yadda take dan kallonta,da alamu tambaya ce fal kanta,tasan dama dole hakan zata kasance,tunda taji wasu magangun da bata gane kansu ba daga bakin likitan,don haka saita janho kujera zuwa bakin gadon da take kwance,ta zauna idanunta kan bilkisun,tana wassafa tare da tsara yadda zata mata bayanin da zai kwantar da hankalinta,duba da yanayin da take ciki,saboda rufewar ba zata amfana komai ba,face sanyata cikin tunani da kuma wani rudanin na daban.



      "Daughter....nasan a rayuwa,daga sanda nake tare dake zuwa sanda bama tare,kin fuskanci abubuwa da dama arayuwarki,kin kuma rasa abubuwa da dama,kuma dukka kin juresu,rayuwa mataki mataki ce,kowanne mataki na jarrabawa idan yazo.maka kayi haquri kana iya cinyeshi yakuma wuce kamar ba'ayi ba,komai yayi farko tabbas yana da qarshe,kiyi haquri bilkisu....kina da juna biyu,wanda shine kusan silar ciwonki" wani irin abu taji yazo ya cake mata a maqoshi,ba don babu wasa tsakaninta da anty zuhiriyya ba da sai tace wasa antyn take mata,amma tasan babu wannan tsakaninsu,wani irin abu takeji yana mata yawo saman ka,kalaman antyn suna bangazar juna kamar xasu wargaza maya qwaqwalwa,saita rintse idanunta tana furta

"La haula wala quwwata illa billa" daga haka bata sake furta komai ba,bata sake cewa komai ba,saidai wani abu daya tsaya mata a wuya bata samu ya sauka ba har sai ranar da aka sallameta daga asibiti,sanda ta isa dakinta ta kwanta saman gadonta ita kadai,tana lissafin abinda yake cikinta,cikakken dan halas ne ko kuwa akasin haka?,ina ubansa?,tananda tutiya ko zarrar da xata nuna ubanshi harta furta shine yayi mata cikin da take dauke dashi a yanzu?.



     Kuka ne mai wani irin nauyi a qirji da zuciya ya kubce mata,ashe haka matan dake yin cikin shege suke ji?,ashe haka suke tsintar kansu?,wanne irin bayani zata yiwa 'ya ko dan cikinta a duk sanda ya girma ya nemi mahaifinsa,shin ta yiwa rayuwasa ko rayuwarta adalci?,ta hanyar data cancanci a samar dashi kenan?.



       Wadanne irin mutanene wadan nan da babu halin girma ko dattako cikin jininsu?,wadanne irin azzalumai ne su da suka zabi rayuwarta cikin miliyoyi suka tarwatsa ta,meta musu ne haka suka hanata cimma dukkan wani buri na rayuwarta,matsalarsu dai a kullum ita ke dakatar da ita daga samun duk wani ci gaba,a duk lokacin data yunqura don ci gaban rayuwarta saisun daqileta,wancan karom sune silar karatunta,wannan karonma dukkan alamu sun nuna sune zasu zame mata tarnaqi.



        Tayi kuka mai yawan gaske,irin kukan data kwana biyu bata yishi ba,har zuwa wayewar gari,yadda idanunta suka tasa ya sanya anty zuhriyya ta fahimci irin kukan data yi,fada sosai ta dinga yi tana bala'i,saboda har yanzun ranta a bace yake itama,wani da bilkisu take kan me yasa zata zauna tana kuka,yayin da mafi yawa kuma dukka kan masarautar kaisa ne,wanda basusan halin da ake ciki ba.



      Sai data gama son ranta sannan ta sauko,taci gaba da lallashin bilkisun tare da kwatanta mata illar bacin rai da damuwarta ga lafiyarta.



       Ba qaramin jajircewa anty zuhriyya tayi ba wajen ganin ta daidaita lamari da yanayin bilkisun,wanda sai bayan kwanaki data tabbatar ta sake warwarewa ta nemi abbaa ya bata izini zataje tayi magana da malam bilya,daga nan su sanar da masarauta,don ta inda aka hau ta nan ake sauka,bai musa ba mata ba ya amince mata,don haka ta sanya lokaci yammaci liqis sanda tasan za'a iya samunsa a gida ta sanya bilkisu ta shirya suka nufi gidan.



          Cikin doguwar riga take purple,saqar qasar dubai,ta yafa mayafin doguwar rigar kawai saman kanta ba tare data nannadashi ba,mai kawai da turare ta sanyawa jikinta,amma idan ka kalleta sai kaga ta qara wani kyau na musamman,kai kace an mata amfani ne da wasu kayayyakin gyaran fata na musamman,saidai tana nan babu qiba ko kadan tattare da ita,plate din takalmi kawai ta zira,ko wayarta da anty zuhriyya ta sauya mata zuwanta gidan bata dauka ba ta fito suka wuce,daga ita sai antyn sai hisham wanda bilkisu ke riqe dashi saman cinyarta,antyn tana tuqi.



        Sanda suka isa gidan ana kiraye kirayen sallar magariba,wasu da yawa sunata daura alwala suna tafiya zuwa masallaci don samun jam'i.



      Suna shiga gidan bayan sun faka motarsu qofar gidan malam bilya yana fitowa daga cikin gidan,cikin hanzari jikinsa jiqe da ruwan alwala,yana ganin zuhriyyan gabanshinya fadi

"Jarababbiya masifaffiya,ko dame kuma tazo" ya fadi,amma gefan ranshi yana jin dadin yadda bikisun ta warware sarai fiye da sanda ya ganta a asibiti.



       Itace ta soma magana

"Munzo ganinka,gashi kuma kana shirin fita" tayi maganar fuskarta a daure tamau,wannan furucin ya sake sanyawa gabanshi ya fadi

"Da wata aqasa kenan" ya fada a ranshi

"Ku shiga ku jirani,zanje nayi sallah na dawo" bata amsa mishi ba ta juya tayi ciki,tabar bilkisu na gaidashi kafin itama ta biyo bayanta.



        Umaima da aminatu ne a falon da alama salla suma zasuyi,,suna ganinta kowacce tasoma rige rigen isa wajenta,suka rungumeta cikim jin dadi,itama rungumesun tayi tana jin dadi,don tayi kewarsu sosai,tunda tabar gidan anty zuhriyya bata sake barinta tazo gidan ba,saidai tayi musu dukkan abinda tace zata yi musun,kuma taga alamun sauyi da canji tattare dasu,bata taba kawowa cewa qaddara zata sake rabasu ba,ba zata sake barinsu su zauna tare ba.



       Murnarsu ta fiddo da hannatu dake cikin bandakinsu tana musu wankin unifoarm,itama murna ce ta cikata,suka baibaye bilkisun kowa yana son bata labarai gami da tambayoyi,anty zuhriyya na zaune saman kujera tausayinta na ratsasu,ta wani fannin kuma suna bata matuqar sha'awa na yadda suke qaunar junansu da kuma yadda suka saba,bata ankara ba taga tuni sun janyeta zuwa dakinsu,saita saki murmushi kawai tana kada kai.



      Murmushin nata ya katse sanda anty ta shigo falon,sai anty zuhriyyan ta hade ranta tsam,don ta gama karanatar kowaccensu,itama antyn bataga wajen wargi ba,don haka ta gama abinda ya shigo da ita kawai ta fita.



         Babu jimawa umma katti ta shigo,saita soma washe baki ganin zuhriyya,ita kuwa babu abinda ya sauya dangane da yanayin fuskarta

"A'ah,zuhriyya ce a gidan namu?"

"Nice" ta bata amsa a taqaice

"Maraba lale,kyazo ki zauna shuru ke kadai,aiko bamu zauna da maimunatu ba kya nemeni" wani kallo tayi mata tana tabe baki,rainin hankalinta ma yaso zarta na kowa,saidai duka zataji dasu,sa'arsu daya ma yanzu bata tasu take ba,da kowacce saita kwashi kashinta a hannu,don tanajin ciwon riqon da sukewa diyoyin mijin nasu,riqo na zallar jahilci qauyanci da kuma son kai.



      Banza ta baiwa ajiyarta harta gama sunadin surutunta,wanda yafi kama da tabarmar kunya tabata waje sanda malam.bilya yake shigowa ya umarci a bashi ruwa yasoma sha tukunna,mama ladi dake da girki ta nufi kitchen don kawo masa.



        Tana daga zaune anan ta qwalawa bilkisu kira,ta kuma jiyota,sai gata ta fito,ta qaraso a hankali ta samu gefan anty zuhriyya ta zauna,kanta a qasa,batasan yaya baban nata zai amshi lamarin ba,kuma ta yaya za'a samu warwarar qullin.



       Duban gefanta tayi ganin mama ladi xaune dafa'an,bisa dukkan alamu tana nufin gabanta za'ayi zancan kenan,don haka ta dubi malam bilya

"Kaman baka shirya zaman ba,don naga wadanda ba ahalin maganar ba zaune a wajen" ya gane sarai dawa take,don haka ya dubi ladi

"Ladi...bamu waje" haushi ne ya cikata,haushin zuhriyya take ji,don ta fuskanci bata daukar raini,hakanan bata daukesu a bakin komai ba

"Kome meye muna zaune zamuji" ta fada tana shirin fita

"Daga baya kenan,wai anyi sadaka da karuwa" anty zuhriyya ta bata amsa.



       Sai data fice sannan ta dawo da dubanta kanshi,takaici yana cin ranta tace

"Malam bilya,shukar da kayine nazo shaida maka lokacin girbinta yayi,wala'alla babu wannan cikin tsari hasashe ko shirinka ko?" Dubanta yake cikin rashin fahimta,sai kuma ya hade rai wai karta kawo masa wargi ko raini

"Kamar yaya,me kike nufi?,kefa baki rabo da jarfa,idan zakimin bayani kiyimin" gyara zamanta tayi yana amsa mishi

"Shi zan maka yanzu" sai taga baima kamata aci gaba dayin maganar a gaban bilkisun ba,saboda haka tace tatashi ta koma,cikin matuqar mutuwa da sanyin jiki ta miqe ta fice daga falon.



       "Diyarka kuma diyar maimunatu da ka bada hayarta...don haya shine sunan da yafi dacewa da aurenta,taje ta kuma dawo maka da tsarabar jika,in sauqaqe maka dogon nazari,yanzu haka juna biyu gareta" wani irin gumi ne me dumi ya karyo masa,idanunsa dukka a waje yace

"Kamar yaya zuriyya,me kike fada ne?"

"Abinda kunnuwanka suka jiye maka" ta maida masa cikin gatse da matuqar jin haushinsa. Baisan sanda ya zame hular kanaa ba yahau firfita gami da ambaton

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un".



_afwan,kuyi manage yau yayi guntuðŸ™Ã°Å¸½Ã°Å¸™Ã°Å¸½_


_ale bilya na gaisuwa,yace ku tayashi da addu'a🤲ðŸ½Ã°Å¸˜_

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 43

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




       Kamar yadda ya zata din kuwa,sanda ya isa sashen ammin tana saman katafaren dining din da aka cika da nau'in girke girke tana cin abincin dare,afnan kuwa na saman kujera zaune riqe da handout tana dubawa,daya daga cikin bayin dake aiki a sassan tana duqe gabanta tana gyara mata qafarta,sai sumaira dake kwance saman kujera tana charting,sanyin ac ne gaba daya ke ratsa falon,sai tv dake aikinta ita kadai ba tare da kowa ya damu da ita ba a cikinsu,don kowa da akwai abinda ya sanya a gabanshi.



       Sallamarshi kadai ta saka kowa cikin taitayinsa,baiwar ta zube ba tare data iya kallonshi ba ta soma gaidashi,hannu ya daga mata,kana ta miqe cikin sauri da hanzari ta soma tattare kayan amfaninta,don dama ta gama yiwa afnan din

"Barka da warhaka yaya" duka suka hada baki wajen fada tsakanin afanan da sumaira,cikin qasaita muryarsa can qasa ya amsa musu,afnan ta kare fuskarta da littafi kana murguda baki tana hararar sashen da ya nufa wato wajen ammi fulani,cikin ranta tana mita

"Wannan duk randa ya zama sarkin ma ai mun kade,kullum fuska kamar kashin shanu,amma duk da haka ya sake dado wani daurewar fuskar saboda mugunta". Sumaira kam tuni ta sauko ya kwashe headphone dinta da charger dinta ta wuce daga falon da nufin sauya falon,sai afnan din kawai ta bari,wanda dama yawancin lokaci ita kadai ce ke iya zama waje idan yazo wajen ammin tasu.



      "Barka da warhaka ammi" ya fada bayan ya zauna kan kujerar dake fuskantarta

"Ka yini lpy" ta jefa masa tambayar tana sake mamakin yadda gaba daya cikin lokutan take ganin sabbi da baqin al'adu tattare dashi,duk da ta sani cewa shi din miskili ne,wanda bayason yawan magana,mai qarancin fara'a,amma dukka wadan nan halayen nasa sun sake qaruwa tare da daukan sabon salo

"Lafiya alhmdlh" ya amsa mata,saita aje cokalin hannunta,tana hade hannayenta waje daya

"Kullum nakan qaryata lafiyarka da kwanciyar hankalinka,don yanayinka da fuskarka basu nuna hakan" sai daya dan kalleta,kana ya kauda kai

"Babu komai fa" shuru tayi kamar mai tantama akan maganar,sannan tayi ajiyar zuciya,ta dauki cokali ta soma ci gaba da cin abincinta ta sake cewa

"Amma....meya hanaka har yanzu ka zabi makarantar da zaka ci gaba da karatunka?"

"Ina nazari ne har yanzu" tsaida taunar da takeyi ta dubeshi

"Nazari kamar yaya?....kaga....na baka nan da jibi,lallai lallai kazomin da sunan makarantar daka zaba,kuma ba'a qasar nan ko maqociyarta ba"

"To" kawai yace mata,don ya kauda yanayin saiya miqa hannun ya dauki tataccen ruwan inibi dake cup,wanda ammin ta zuba da niyyar sha ya soma kurba.



       Rabin kofin yasha sannan yadan kira sunan afnan,ta amsa tana aje handout dinta ta taso,da hannu ya mata nuni ta zuba masa abinci,ta tsani wannan miskilancin nasa,dom haka saita nuna kamar bata fahimta ba,maimakon ya bata amsa saiya dauki wayarshi ma ya soma latse latse ya barta nan a tsaye,saida ammi tace

"Ki zuba mishi mana kin tsaya saman kan mutane" qafa tadan buga sannan ta zumbura baki ta soma zuba mishin,ta gama ta saka mishi cokali ta sauka ta dauki handout dinta itama ta fice kamar yadda taga sumaira tayi dazun.



      Jan plate din yayi gabansa yasoma ci,akwai tambayar da yakeson mata amma baisan yadda zata amshi kota kalli tambayar ba,haka ya dinga cin abincin yana gwada ta yadda zai tambayetan,kafin daga bisani ya tattara dukkan gwanintarsa yace

"Sun aiko sun fadi adadin abinda suke buqata kuwa?" Ya jefa mata tambayar,saboda ya tabbatar kudi ne suka rudesu har suka yarda suka aikata abinda suka aikata din,don haka zasu biyo ba'asi daga baya na kudin da akace su fadi nawa sukeso,qila ta wannan hanyar zaiji wani abu,ko yaya daga garesu.



        Mutum ne shi da bayason mutum mai kwadayi ko son abun duniya,amma baisan me yasa ita bai ganinta da wannan abun ba,baisan me yasa ya kasa mantawa da ita ba.



       Cikin rashin fahimta ammi ta dago tana dubanshi

"Wa kenan kake nufi?" Rasa yadda zai mata bayani yayi,sai daya hade lomar bakinsa sannan yace

"Yarinyar da aka turan mexico" wani irin hade rai da bai taba gani saman fuskarta ba ammin tayi,ta wani gefen gabanta yadan fadi,ta kafeshi da ido,yaji a jikinsa kallonsa take,amma saiya basar yaci gaba da cin abincinsa kamar bai gani ba.



       Dama ta kusa qoshi da abincin,maganarsa tasa sauran wajen da zata zuba abincin ya cike,saita ja kujerarta baya tana ci gaba da tsareshi da ido,a hankali cikin muryar dake bayyanar da bacin rai tace

"Meye hadinka dasu?,meye damuwarka da sun aiko ko basu aiko ba?,abdul'azeez,ina fata baka manta da maganarmu ta qarshe ba kafin in turo maka ita,ka sakata a idanunka banda zuciyarka,karka yadda ko gefen zuciyarka taje,idan taje din akwai matsala,saboda ita din ba kininka bace,sannan ita din ta wucin gadi ce a wajenka,abdul'azeez...koda wasa banason na sake jin wata magaba makamanciyar wannan daga bakinka....har abada"

"Afuwan" ya fada cikin girmamawa,daga haka shuru ya biyo baya,saita miqe tana sauka daga wajen,da alamu ranta ya baci ne.



      Shima bai wani ci gaba da cin abincin ba,cokali biyu ya qara ya miqe ya sauko daga wajen,ya mata sallama ya fito.



       Kan hanya ya dinga jin kansa yana wani daukan zafi,ranshi yana baci,baisan ainihin dalilin ba,amma yakan tuna bai samu jin komai daga wajen ammin ba,yana jin wani feeling mai qarfi nason karya zuciyarsa,irin feelings din da baisan menene ba.



      Maimakon ya zauna a sashensa kamar yadda ya tsara,sai yaji ya kasa zaman,ya dauki wayoyinshi kawai ya fito,ya soma takawa cikin gidan sarautar yana nufar sassan da xasu fiddashi daga gidan,ya dinga wuce qofa qofa gate gate,akwai tazara mai dan yawa tsakanin ainihin sassansu zuwa babbar qofar da zata fitar dakai daga gidan sarautar gaba daya,amma haka yaci gana da takawa,yanajin tafiyar kamar zata debe masa kewa ne,yana tsaka da wannan tattakin wayarshi ta dauki tsuwwa,sunan safwa ya bayyana,sai yayi rejecting kiran sannan ya kashe wayar gaba daya ya jefata a aljihun wandonsa.



******    ***"""*****   *******



     Kasa zama tayi lokacin da fulani aisha ta yi kiranta,tana son taji wacce amsa ce zata fito daga bakinta?,idan har ta amshi cikin ne tasan cewa lallai ita din tazo duniya a sa'a,ta soma aiki a masarautar kaisa da qafar dama,hakanan kakarta ta kuma sake yanqe saqa kenan,zata samu arziqi da alherin daya ninka na baya,idan kuma akasin hakan ta faru to dole kowannensu ya amshi hukuncin,don basu da qarfi ko qwanjin da zasuce zasu ja da hukuncin.



        Yau din cikin matuqar daurewar fuska ta fito,wanda hakan ya sabbaba faduwar gaba wajen umma luba,tun fulanin ma batace komai ba.



       Sai data gama dukka tattakinta sannan ta tsaya gabanta,ta dubeta da kyau cikin kaushin murya

"Ki gaya musu cewa wannan maganar cikin labarin qanzon kurege ce,qirqirarren labari ne da aka samar dashi saboda ayi wasa da hankalin masarauta,ki gaya musu,basusan wacece fulani ba,ki shaida musu sunyi kuskure,da sun sani kansu tsaye sun fadi adadin kudaden da suke da buqata...komai yawansu fulani tafi qarfinsu,amma bawai su biyo ta wannan hanyar ba,ki sake shaida musu cewa....ban tura ta mexico na hadata da yarona don tayi ciki ba,ban tura bilkisu mexico don ta dace dashi ba,na turata ne tamkar ma'aikaciya ta wucin gadi,saboda sanin kansu ne ce cewa wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa,saboda haka ki jadda musu,hawainiyarsu ta kiyayi ramata,kudi kuwa ko nawa suka yanke suna da buqata su shaida miki,gari bazai waye ba zai tabbata a gabansu,kudin da zai zamo abu na qarshe da zai shiga tsakaninmu kamar yadda muka tsara bisa yarjejeniya....kije ki shaida musu...ruwansu su haqura da batun ciki....ruwansu suci gaba dayi....".



       Kamar daga sama ya dinga jin tashin maganganun ummin sanda yake hanyar shigowa wajen ummin,da alama cikin bacin rai take maganar,sunan data kira kawai yaji tamkar an jefeshi da wani abu,kalaman da suka biyo baya kuma suka so birkita masa kwanya da kuma tunaninsa gaba daya,har ya kasa tantance ainihin furucin dake shigowa kunnuwansa yake ji ko kuwa,don haka ya kutsa kanshi kai tsaye cikin falon,burinsa kawai ya isa yaji abinda kunnuwansa suke jiyo masa hakanne?.



        Dubanshi tayi sanda ya shigo,saita dauke kai ta maida ga luba

"Kije ki shaida musu dukkan abinda na gaya miki,hakanan ki dawomin da dukkanin amsar da suka bada"

"Da izinin Allah kuwa ranki ya dade....Allah ya huci zuciyarki....a tashi lafiya" daga haka ta miqe ta fice daga falon.



       "Ummi....ciki?,waye yake da ciki?" Ya samu bakinsa da furta mata kalaman ba tare daya shirya ba,dukkan kallonta ta maida kanshi,cikin matuqar hade rai tace

"Sun shirya qara tare da tsara cewa tana da ciki,saboda idanuwansu sun rufe,suna tunanin shashashai ne mu,suna so yi amfani da wannan damar don suyita tara dukiya damu,bayan sun amince da dukkan yarjejeniyar da mukayi dasu" Hakanan yaji batun cikin ya samu kyakkyawan matsugunni cikin zuciyarsa,ya kuma zauna daram bisa kansa,hakanan yaji baida sha'awar ci gaba da zama,don haka ya qaraso tsakiyar falon,ya samu kujera daya ya zauna

"Amma ammi....bincakawa ya kamata ki soma yi,ki tabbatar da ainihin sahihancin maganar ko kuma akasinta" karon farko ya samu kanshi da musawa hukuncinta,karon farko daya soma fadin ra'ayi da views dinsa kan wani hukunci data zartas.



       Sosai take dubanshi itama,kafin daga bisani ta motsa bakinta

"Wacce jami'a ka zaba?" Ta jefa masa tambayar ba tare data bi takan qorafinsa ba.



      "B U K kano" ya fada yana motsa labbansa,kamar wanda aka yiwa dole wajen furta lafazin,wani kallo ta watsa masa

"Kana da hankali kuwa?,ka manta wacce jami'a ka gama?,ko kuwa ka manta gargadin da nayi maka na cewa banda duk wata jami'a dake cikin qasar nan?" Baki ya bude zai mata magana,cikin fusata ta daga mishi hannu gami da cewa

"Ya isheni....tashi ka bani waje tun bai gama fusata ba" tsam ya miqe ba tare daya furta abinda yayi niyya din ba,yana jin ranshi a jagule,bacin rai na mamaye zuciyarsa.



      Har ya kusa fita ta kirayi sunanshi

"Abdul'azeez" ya tsaya kana ya waiwayo,ta baiwa qofa baya don haka bai ganin fuskarta

"Idan wani abun ke damunka,ka gayamin tunda wuri mu maganceshi,idan kuma wani abu kake saqawa cikin ranka,ina mai baka shawarar kayi gaggawar cireshi....saboda bazai taba haifar maka da d'a mai ido ba".......


********    ******    ********


     Tunda umma luba ta shaidawa malam bilya saqon fulani aisha yaji ranshi yana baci,a karon farko kenan,bai taba kawowa ko tsammanin zasu ture ko su qaryata maganar cikin ba,shi kadai zancan ya dinga damu yana masa kai kawo cikin zuciyarsa,yana son shaida zuhriyya saidai baisan gidanta ba,bai kuma san inda zai sameta ba,yasan cewa koda zatayi fada masifa da tashin hankali a qalla ya samu sassauci ya gayawa kowa,haka maganar ta dinga damunsa taba sanyashi bacin rai da baqinciki.


*****************



       Misalin bakwai da rabi ne na safiyar ranar,anty zuhriyyan ta shirya don takai najwa da ateeq tahfiz da suka sanyasu dan iyakacin lokacin zamansu a kaisa kafin su tattara su koma inda suka fito,saboda gudun kada karatunsu ya samu tasgaro kafin su koma.



      Yawancin lokutta abba ne yake kaisu,amma yau anty ce zata kaisu sakamakon fita da yayi tun sassafe.



       Da kanta ta iske bilkisu a daki,ta sanyata ta shirya zata rakata takai yaran makaranta,sabanin daa da ita da haule suke bari a gidan,amma yau tace tare zasu,saboda har yanzun walwalar bilkisun bata dawo ba,duk da cewa tadan samu sauqi,amma laulayi kam har yanzu bai barta ba,don wani lokaci idan ya waiwayeta haka take wuni akwance,ba tare data kai komai bakinta ba,wala ruwa ko abinci,wani lokaci kuma ka ganta da 'yar lafiyarta.



       Yawan tunane tunane da anty zuhriyyan ta fuskanci tana yawan zama tayi shike damunta,don haka ta sake zage damtse wajen janta a jiki,hanata zaman kadaici,da qirqiro mata abubuwa da tasan zasu janye mata hankalinta.



       Da fari tayi shawara da abbaa kan zata sama mata skyline universty,yace aah,yanaga yanzu abu mafi kyau shine suyi tattalin lafiyarta tukunna,tunda har yanzu ba wani cikakkiyar lafiya ne da ita ba,sannan shi yafison idan sun koma brasil tayi karatunta a can,inda babu wani wanda ya santa bare ta samu takura ko wani abu makamancin haka,ta yarda da shawararsa don haka ta jingine wannan batun,saita sauya mata waya da laptop,hakanan lokaci lokaci takansa ana dauko mata qannenta su wuni wajenta,hakan saiya sake rage mata damuwar da take ciki sosai,duk da cewa zuciyarta har yanzu a quntace take,ta cika da tsana da zargin ahalin kaisa,hakanan ta boye wani quduri cikin zuciyarta.



      Da yake duk sanda ta tashi sallar asuba sai tayi wanka saboda ta samj temprature din jikinta ya mata dadi,yanzun ma da wankanta,kaya kawai ta sauya zuwa doguwar riga,saboda yanxun tafi ta'ammali dasu,sakamakon cikinta daya daga ya soma fitowa,don ya shiga wata na biyar,ta samesu tuni suna cikin mota.



     A hanya surutu ateeq da qawarta najwa suketa mata tana biye musu,motar bata zauna shuru ba har sai da ummin ta saukesu suka juyo iya su biyu kawai,suka daukon hanyar komawa,saidai wannan karon a hankali ummi take tuqin.



      Basuyi wani nisa ba ummi zuhriyya tace

"Inaga ya kamata mu leqa gidanku ko?,muji meye feedback na mutanen can kan batun cikinki" boyayyar ajiyar zuciya kawai bilkisun ta sauke ba tare data ce komai ba,don ita gaba daya bata qaunar tunasu ma bare maganarsu,ta ajesu can wani sashe daban na rayuwarta mai nisa,wanda take fatan watan watarana ta mance da babinsu,saidai ko hakan zai yiwu?,tunda ga wata igiya mai qarfi ta ratsa tsakaninsu?.



      Har suka je gidan bilkisun bata tanka ba,sukaci sa'a baban yagama shirin fita kasuwa kenan yana tsaye a falo yana baiwa umma katti kudin cefane,wanda cikin satin ya sake gyara lamarinsa,tare da gyara abubuwa masu yawa cikin gidan,harda wadanda ma baya yi.



       Daga yanayin yadda ya karbesu bilkisu taga wani irin sanyi da laushi mai yawa tattare dashi,ba ita ba,hatta da anty zuhriyya abokiyar burminsa ta lura da hakan,saidai yace musu su xauna minti goma yanzun zai dawo,tabe baki kawai antyn tayi batace masa komai ba har ya fice.



      Qofar gida ya tsaya yana neman yaron da zai aika gidan umma luba,saboda nashi yaran duka basa nan sun wuce makaranta,bayajin zai iya gaya musu wannan saqon da bakinsa,yana jin zuwa yanzu ya kamata ya sauya daga asalin bilya zuwa bilyaminu,ya kamata ya dainda dabawa diyarsa wuqa haka a zuciyarta,ya tabbatar dole amsar da zata biyo baya ta taba zuciyar kowacce mace,ki dauki ciki kina wahala dashi,sa'annan wadanda keda alhakin hakan suce basu yarda da batunsa ba?,ba qaramin mummunan xance bane ga kunnuwan kowacce diya mace.



      Da qyar ya samu yaro ya aika,saiya tsaya nan qofar gidan yana jiran dawowarsa,Allah ya taimakeshi sai gata da yaron,cikin mamaki take tambayarsa lafiya?

"Maigado ce da mariqiyarta,wadda take da alhakin jin komai sukesu suji amsar da masarauta ta basu" ita kanta wannan karon abun saiya mata nauyi,amma ba yadda ta iya dole ta isar da saqon,don tana da buqatar amsar da zata kaiwa fulanin,don haka ta cije suka shige tare.



       Sau daya bilkisu ta daga kai ta kallesu ta dauke kanta,mutum biyun da kullum idan ta gansu sai taga kamar taga wadanda suka sanya gatari suka rinqa sassaqar rayuwarta har zuwa qarar da ita.



       A sanyaye umma luba ta gaida anty zuhriyya datayi mata kwarjini,ta amsa mata ba yabo ba fallasa,don batasan wacece ba

"Sannu maigado" ta sake yiwa bilkisu sannu,bata iya dubanta bama bare ta amsa,saita gyara zama cikin dan da wurwura,ta gaya musu dukkan abinda fulanin ta fadi.



       Ã†˜ololuwar fushi anty zuhriyya ta shigeshi,yayin da bilkisu ta shiga wani irin yanayi wanda batasan wanne iri bane,abu daya kawai taji jiki da zuciyarta na gaya mata,basason zamansu a wajen,basason ci gaba da sauraren bayanan umma luba,duk da alamu sun nuna ta gama fadin abinda zata fada din,saita miqe tsam.idanuwansu dukka suka rakata,kowa yana jin wani yanayi game da ita a zuciyarsa.



       Haka ta dinga sanya qafarta kawai duk inda ta fuskanta,bata tsaya ba sai data isa jikin motarsu,ta sanya hannu ta bude ta shiga ta zauna,gamida curewa waje daya,taso cusa fuskarta tsakanin qafafunta ko zataji salama,amma babu damar haka,saboda cikin dake jikinta,don haka sai taja mayafin rigarta ta lullube fuskar tata,sannan ta dora ta saman tafin hannunta,tana sakin ajiyar zuciya a jejjere kamar zuciyar tata zata fito.



        Tamkar zatayi aman wuta daga qirjinta haka takeji,batason ta yanke hukunci babu yawun abbaa,amma tanajin dole ta aikawa da fulanin saqo,saqon da zai isa jikinta da zuciyarta yadda ya kamata

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 44


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




       "Inason nima ki shaida mata,ni zuhriyya qanwa ga mahaifiyar bilkisu,kuma uwa a yanzu a gareta....auren danta da bilkisu qaddara ce....wata qaddara wadda ta sanyani nayi nesa da 'yata,wata qaddara wadda a yanzun bata isa ta zama sanadin maimaituwarta ba,ki gaya mata....bilkisu ta yiwa danta nisa,tayi masa tazara kwatankwacin yadda sama ta yiwa qasa nisa,ki shaida mata ashe shi arziqi bawai kudi bane kawai....arxiqi yana a zuciya ne ba'a hannu ba,ki shaida mata,munfi qarfin dukkan wata dukiya tata da take tunanin ta mallaka,komai yawanta,ciki kuwa dan duma ne,yado yakeyi,da kansa zai fasa kansa,wala'alla kuma sanda zai fasa kan nashi,yafi dukkan qarfinta da tunaninta,ya mata nisa ya mata zarra,ki sake shaida mata dai,ta rubuta ta ajjiye,akwai ranar nadama,akwai kuma ranar qin dillanci....ki jadda da mata,ta sanyawa ranta bata taba alaqa da wata mai suna bilkisu ba,bare tayi zaton ta taba hada dangantaka da wani d'a nata,wannan shine saqona" daga wannan bata qara cewa komai ba,hakanan bata sake waiwaya ta dubi daya daga cikinsu ba ta fice,don hankalinta gaba daya yana kan bilkisu tunda ta fice.



        "Kukan me kikeyi?,bai kamata kiyi kuka ba daughter kina da uwa kamata,share hawayenki" ta fada tana daga bilkisu,saidai yanayin da ta ganta ya kadata gamida daga hankalinta,duk yadda taso shawo kan abun ya gagara,dole sai data danganata da asibiti,wanda sai data kwana biyu sannan tasamu shawo kanta,wannan dalili ya sanya ita da abbaa suka yanke shawarar fara shirye shiryensu su koma inda suka fito,amma da farko zasu fara yada zango a ethopia don kaita taga tarin dangi da 'yanuwa wadanda bata sansu ba,suma basu santa ba.



       Cikin qanqanin lokaci komai ya kammala na bilkisu,su dama ticket kawai zasu siya,don suna da visas dinsu kuma basu qare ba.



*********   """"""""" *********




         "Shaida min abinda suka sake aikoki dashi" fulani dake tsaye ta fada tana duban wani guri daban,kamar yadda ta umarceta haka ta gaya mata komai dalla dalla,bata boye komai ba.



      Ga mamakinta murmushi fulani tayi tana jijjiga kai,sannan tayi tattaki mai dan dama kafin ta dakata,tana mamakin yadda saqon ya samu muhalli me kyau a cikin zuciyarta,amma duk da haka ta bari son rai yayi mata jagoranci,ta bude baki tace

"Wannan kadai ya isa ya zamemin shaida kan cewa qarya suke,idan har da gaske suke...zasu tsaya iyakacin tsayawarsu suga sun tabbatar da gaskiyarsu,mu rubuta duka mu ajiye,maga wanda zaiyi dana sanin....tashi kije luba" ta fada tana takawa tabi wata siririyar hanya.



       **********      ***********



      Tsit falon yake wanda sai kayi tsammanin babu wata halitta a cikinsa,qarar ac ne kawai ke tashi sai na sauran na'urori dake da alaqa da dakin.



      Mutum biyu ne zaune saman lausasan kujerun da aka yiwa falon qawanya dasu,azeez ne da abdulrashid,wanda shurun ya afku ne sanadiyyar maganar da suka gama yi yanzu tsakaninsu.



      Gauruwar ajiyar zuciya abdulrashid yasaki sa'an nan yace

"Babu wanda ya zaci al'amarin zaizo a haka,yanzun maganar ta canza,ana maganar jininka ne wani sashe na jikinka,abdul'azeez's photocopy,tamkar wani copy naka ne ajiye a wani waje,wanda bai cancanci koda kowa ya wofantar dashi ba kaika aikata hakan" wata iriyar ajiyar zuciya dake nuna gazawarsa da gajiyawarsa ya saki yana duban abdulrashid,da wani irin amo a muryarsa ya sake bude baki karo na biyu

"Wannan shine the same tunani na abdul.....indai har da gaske ne,yanzu ana magana ne ta jini,ana magana ta zuri'a....ban damu da amincewarta ta yadda da shirin da duk akaje mata dashi saboda kawai dukiya ba,ina duba da jinina ne,jini na ne a jikinta...but...fulani ta kasa fahimtar hakan,taqi yarda nayi mata bayani,taqi tsayawa ta saurareni,infact tama qaryata maganar,if maganar gaskiya ne me zai faru a gaba?".



       Duban azeez din sosai abdulrashid yake,yana karantar wasu emotions dake saman fuskarsa,yana maganar ne deep inside him,akwai kuma wani babban lamari mai girma tattare dashi,bai taba ganin azeez din tunda suka taso daga quruciya zuwa yanzu ba ya damu da lamarin wata mace ba,bai taba ganinsa yana maimaita batu kan wata diya mace ba sai yanzu,koda ya take dashi kuwa idan ka dauke mahaifiyarsa,sai yanzu gashi wasu emotions na tashi daga saman fuska da kuma muryarshi,lallai wani abu na shirin faruwa.



      Ajiyar zuciya abdul ya saki sannan yace

"Ni ina ganin kawai ka shaidawa mai martaba...." Idanu azeez ya zuba masa,sannan a hankali yace

"If idan qarya ne fa,maganar ba gaskiya bace?" Shuru yasake yi na wasu sakanni sannan yace

"Akwai fahimtar juna da qauna mai yawa tsakanin fulani da mai.martaba,idan har na shaida masa ni nasan girman abinda zai biyo baya,bazai yiwa kowa dadi ba,kuma ya zamana maganar ba haka take ba...yaya kenan?,na watsawa fulani qasa a idanu,na tozartata gaban maqiyanta,na bata tsakaninta da mijinta,akwai abubuwa masu tarin yawa da zasu iya biyo baya" kai abdul ya kada,tabbas shima ya hango cakwakiya mai tarin yawa cikin aikata hakan,shuru yayi yana lalubar wata mafitar,wanda kafin yakai qarshen nazarin nasa maganar azeez din ta katse masa hanzari

"Akwai hanya guda daya da nake tunanin zata bullemin"

"Waccece?"

"Zan binciki sahihancin maganar ta hanyar matar data kawowa ammi saqon"

"Good...amma a ina zaka samu matar?"

"Ma'aikaciyar masarautarmu ce,zanyi magana da sunusi,yasan kusan fiye da rabin barori da ma'aikatan gidan,zan dorashi ya bincika min komai..." Ya qarashe maganar yana miqewa tsaye,yana jin tamkar an warwareshi daga wani sasari da aka sanya masa,kai tsaye dakin abdulrashid din ya shige,yanason ya samu bacci don ya sake samun nutsuwa na aiwatar da komai.



       Sanda abdul ya shiga dakin ya tadda shi tuni yayi nisa a kwanciyarsa,daga shi sai dogon wandon rigarsa,da fara qal din singlet,ya ware ac da fanka gaba daya,murmushi mai hade da dariya ya saki

"Problem solved"

"In sha Allah" ya amsa mishi yana lumshe kyawawan idanunsa da sai yanzu yaji bacci nason rinjayarsu.



        *******   *****   *****   *****



     Hannayenta goye a baya take kai kawo,tabbas babu wanda zai sanya sunusi binciken inda luba take sai azeez,tunda shine shugaba kuma babba a masu kula da sassansa,akan yana nufin kenan ya take maganarta,gaba daya lamarin me yake nufi?,binciken luba yana da alaqa da yarinyar nan,ko kuwa wani issue ne na daban.



      Sosai hankalinta ke a dage,karon farko data soma cin karo da wani abu da yayi kama da saba umarni daga azeez din,ba shakka zata nuna masa qarfin qwanji,da qarfin kasancewarta uwa,bata so kuma bata fata abinda zuciyarta ke qissima mata ya tabbata,ko a mafarki bata buri ko tunanin haka.



       Cikin gaggawa tasa a nemo mata azeez din tana nemansa duk inda yake,saidai kuma aiken nata bai sameshi da wuri ba,sakamakon yana wurin mai martaba suna tattaunawa,yana son xaiyi tafiya marocco,kuma a qalla zai dauki kusan sati guda a can,duk da cewa yakanyi tafiye tafiye,amma bai fiya zama ko ya dade ba saboda mutanensa.



       Lokacin daya fito daga wajensa,saqonta shine abu na farko da aka gaya masa,duk da yadda yakeso ya watsa ruwa a jikinsa amma haka ya yanke dukkan wani uzurinsa ya nufi sassanta.



       Yanayin daya taddata yasa hankalinsa ya daga,ta jefa masa wani kallo da zai iya cewa bai taba ganinsa irinsa cikin idanunta ba,sannan cikin kakkausar murya ba tare data amsa gaisuwar da yake miqo mata ba,murya mai cike da gargadi tace dashi tun bai ida zama ba

"Wannan shine karo na qarshe da zan maka magana kan wani batu daya shafesu indai nina haifeka....ka dakatar da duk wani lalube da bincike da ka sanya ake maka kan luba,don ko ka samu luba ba zaka sake samun komai ba daga gareta,abdul'azeez!....karka sake ka tsallake gonata,karka sake mu sanya qafar wando daya dakai,a karo na biyu ina sake gaya maka....ka ajjiye duk wani abu daya dangancesu daga kwanyarka,tun baka shigo gonata ba,ka fuskanci abinda yake gabanka!,wannan shine umarni na" bata bashi damar cewa komai ba tayi gaba tabarshi a nan,shi dinma baijin koda ta bashi dama zai iya cewa wani abun,saboda yadda kwanyarsa gaba daya ta dinke,ya juya cikin wani irin yanayi yana takawa shima ya fice daga farfajiyar.



       Wani irin juyawa yaji kansa yana yi,yanajin gangar jikinsa kamar ba tashi ba,karon farko da yaji har cikin zuciya da gangar jikinsa umarnin ammi bai samu masauki ba a qwaqwalwarsa,yakejin kamar bazai iya biyayya wa umarninta ba,ya miqe a hankali kamar me ciwon laka ya soma takawa,gaba daya zuciya da qwaqwalwarsa tayi nisan zango a tunani.



      Kwananshi biyu ko ammin bata ga idanunsa ba,yana cikin wani irin yanayi da iya tsahon rayuwarsa bai taba shiga ba,ya qure tunaninsa gaba daya kan hanyar da zaibi ya kawowa kanshi mafita,yafi kowa sanin ammin nashi kaifi daya ce,gaba daya 'yan hamayya da abokan adawa sun gurbata tunaninta,tabbas duk wanda ya santana shekarun baya ba haka ammin take ba,to amma kusan shi a kansa komai yakeso ya qare,shin wannan soyayya ce?,kuma gata ne?,zai iya cewa eh,amma bisa hasashe da tunanin mahaifiyarsa,saidai akwai tarin kusakurai masu yawan gaske cikin dukkan hukuncinta da take yankewa,wanda takan dora komai ne bisa mizanin ramuwa da ganin ta cimma gaci,ta cusa baqinciki da bacin rai cikin zuciyar maqiyanta,amma hakan gashi yanason shafar rayuwa da walwalarshi.


*********   *****    *********



      Kamar kowanne lokaci yau cikon kwana na uku,yana kwance shi daya a falonshi sanye da singlet da dogon wando,idanunshi saman tafkekiyar tv dake girke tana aikinta,rabin hankalinsa na kanta,yayin da wani rabin hankalin nashin ya tafi wani tunani na daban.



       Shuru sashen nashi yake babu motsin kowa,don tun kwanaki ukun da suka gabata ya sanya sunusi ya sallami dukkan hadimai da barorinshi,saboda baya buqatar kowa bare a dameshi,dukka ammin tasan da wannan amma tayi biris dashi,labarin abinda ya aikata din yazo mata,abu daya take tsoro gami da fargaba,sannan kuma bata da amsar hakan,me azeez yake nufi?,meye nufinsa na damuwa da yarinyar?,me yasa take ganin wasu alamu da take take nason soma kaucewa umarninta?,tambayoyin da takan kwashe lokutta tana yiwa kanta,saidai bata da amsar ko guda daya,tabbas matuqar ya zamanto cewa ra'ayin azeez ya soma sauyawa babu shakka akwai gagarumar matsala da take hasashen zata iya afkuwa,bata fata da ko burin abinda aka shiryashi na wani taqaitaccen zamani ya zama tarnaqi ga rayuwarta,ko ya lalata dukkan wani shiri data dauki tsahon lokaci tana yiwa rayuwarsu.



      Gyara kwanciyarsa yayi,ya soma gajiya da kwanciyar,ya lumshe idanunsa yana sake matsawa qwaqwalwarsa zuwa ga tunanin mafita.



       Kamar wanda aka tsikara ya bude dukkan idanunsa da sauri,sannan ya miqe a sukwane ya zauna sosai saman kujerar,a sarari cikin daga murya yace

"Yes!" Saiya soma lalubar wayarshi wadda tun kwana uku take a kashe ya kunnata,babu jimawa ta daidaita,saqonnin safwa ne suka fara shigo masa iri daban daban,saina abdulrashid jabir da sauran makusantanshi.



       Duka baibi ta kansu ba,ya soma lalubar lambar sunusi,bugu daya tak ya daga,cikin girmamawa ya soma miqa masa gaisuwa,bai amsa ba ya gaya mishi saqon da ya sanya yayi kiranshi

"Kana ta ina?"

"Ranka ya dade,ina can bakin sassa kamar yadda ka umarta"

"Ka qaraso ciki,inason ganinka" daga haka ya katse kiran,sa'annan ya miqe ya soma barin wajen.



       Bedroom dinshi ya tura ya shiga,ya qawataccen toilet dinsa,ruwan wanka ya hada mai dumi sosai yayi wanka,kana ya fito ya shirya kansa cikin wasu qawatattun kaya dake nuna ainihin wayeshi,sun matuqar karbarshi da kuma dacewa dashi,ya gyara sumarshi da kyau ya sanya hula data sake qawata adon nashi,sannan ya feshe jikinsa da turare baya ga na jiki daya sanya kamar yadda ya saba,ya zura takalmansa da suke mahadi da kayan,sannan ya duba agogo,zuwa yanzun yasan sunusi ya jima yana jiransa,don haka ya fito.kai tsaye zuwa falon da sukan zauna su jirayeshi a duk lokacin daya buqaci ganinsu.



      Kamar yadda ya zata din kuwa ya sameshi xaune saman kilishi yana jiransa,yana daga tsaye yayi magana dashi

"Ka nemo min sodangin,ka shaida mata ina buqatar yin magana da ita cikin sirri,sannan kuma a gaggauce"

"An gama ranka ya dade" ya fada yana ficewa da hanzari,kamar yadda ya fuskanci buqatar ganawar tasu ta musamman ce,hakanan ya samu kanshi da kasa zama,burinsa kawai sodangi ta iso,ya tabbata komai zaizo cikin sauqi,yana da yaqinin a yau zata kaishi gidansu,zaije ya ganta,sannan ya tabbatar da gaskiyar wanzuwar jininsa tattare da ita ko akasin hakan.



          Tana daga tsaye a katafaren kitchen na alfarma da ake amfani dashi wajen samar da abincin sassan fulani aisha,dukkan wani abinci da fulanin xata ci kusan yana qarqashin kulawar sodangi ne,daya daga cikin manyan amintattun ta ,wadanda takanyi amfani da shawarwarinsu,musamman idan suka dace kuma sukayi dai dai da ra'ayinta.



      Dudduba yadda ake gudanar da girkin take cikin nutsuwar nan tata da kamalarta,daidai lokacin data gama duba tattasan da aka gama markadawa,kubra ta qaraso bayanta,cikin girmamawa murya qasa qasa

"Shugaba yarima yayi aike,ya aiko sunusi,yana da buqatar ganawa dake yanzu" shuru ta danyi tana tunani,don kusan tun dawowarsu daga mexico fulani ta karbi fiye da rabin aikinta a sashensa ta dora wasu,batasan me yasa ba,amma tana tunanin hakan bai rasa nasaba da tarayyarsu da bilkisu,tanason sai tafiya ta sake nisa komai ya daidaita kafin lamuranta gaba daya su koma can,don kada ya zamana suna yawan ambarta ta kasa bacewa daga bakunansu,tana hasashe dukka dalilinta baya wuce wannan.



      Ba tare da dogon nazari ba tace

"Muje" saboda jikinta ya gama bata cewa tabbas akwai abinda ke faruwa,cikin kwanakin taga yariman ya kusa sau uku,kallon farko tasan akwai abunda yake damunshi,a matsayinta na wadda ta sanshi tun daga yarinta zuwa girma.



       Kamar yadda ta xata kuwa daga fallon farko ta fuskanci matsala da damuwa kwance saman fuskarshi,falon ya dauki shuru bayan fitar kowa,ya zamana daga ita saishi,cikin nuna kulawa da tausasawa tace

"Allah ya taimaki yarima,ko meye yake faruwa zanso najishi daga bakinka,dom ns tabbatar akwai alamun matsala da damuwa tattare dakai".



        Dukkan abinda bata sani ba ya gaya mata,bai boye mata komai ba,da buqatarsa nayin tattaki da kansa zuwa gidansu bilkisun don tabbatar da gaskiyar lamarin.



        Idanunta na kallon qasan carfet din,saidai sun cika fal da hawaye,tausayin bilkisu matsananci yana ratsata,inama ace tasan gidansu bilkisu,inama ace tasan inda zata ganta,lallai ba shakka koda zuwanta ko kai yarima zai zama sanadin qarshen zamanta a masarautar kaisa da sai taje,tana hasashe da tunanin yadda rayuwa zata kayawa yarinyar,rayuwar da zatayi dauke da cikin da bata da iko isa ko qwarin gwiwar nuna ubanshi,zata raini ciki cikin al'ummar da basusan da zama ko labarin ta taba aure ba,me zasu kalli cikin,shege kenan fa?,tanaji a jikinta zancan cikin gaskiya ne,tunda ita din kusa shaida ce na dukka abinda ya faru,meya sanya fulani ya ta sauya haka?meya qeqasar da zuciyarta ta zama wata iri bayan ba haka dukka suka santa ba?.



       Yatsunsa tasa ta dauke hawayen da suka gaza boyuwa sannan tace

"Iyakar zamana na jima banga yarinya kamar bilkisu ba,yarinyar dake da dattako da kyawawan halaye da sukafi shekarunta yawa,shekara sha shida amma zaka tsammaci ta mallaki shekaru É—ai É—ai har gda arba'in ne,quruciyarta me kyau ce da burgewa duk da rashin gata da wanda zai damu da ratuwarta,inaji a jikina zancan cikinta gaskiya ne,ba shakka tana da ciki,saidai.....ina neman afuwarka....ina kuma mejin dadin shaida maka cewa....bansan koda hanyar gidansu ba,mun rabu tun a airphort da ita,bansan ya akayi ta isa gida ba,ladingo da luba su sukasan ainihin gidansu,saidai suma na jima da daina ganin gilmawarsu cikin masarautar nan".



       Idanunsa kawai ya rufe tsahon wasu mintuna ya gaza budesu,haka nan itama shuru tayi tana taya bilkisu jin ciwo,saboda tasan cewa Allah ne kadai yasan ciwon da a yanzun yarinyar takeji a ranta.



      Izini aka nema na shigowa,bai iya bada amsa ba sai sodangi ce ta bada,saboda ta fuskanci dan aiken daga sassan me martaba yake

"Mai martaba yana son ganinka,yayo aike daga sassansa" sodangi ta shaidawa azeez,sai a sannan ya bude idanunsa da suka sauya kala,haka kawai yaji aiken ya sanya gabanshi faduwa,abinda ba kasafai hakan ke faruwa gareshi ba,ya motsa labbansa da qyar yana amsawa,sannan ya miqe yana sallamar sodangi yasake shige ciki.



       Ya jima zaune yana qoqarin controlling kansa don ya samu zuwa kiran me martaba,baya son yaje masa a wani yanayi na daban wanda zaibar ayar tambaya a zuciyar maimartabar.



        Tsahon wani lokaci sannan ya samu rage kaso hamsin na mode din da yake ciki sannan ya fito,ya samu wasu daga cikin barorinsa acan qofar waje,sunso masa rakiya kamar yadda aka saba amma ga dakatar dasu,shi kadai ya durfafi sassan mai martaban.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 45

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070

__________________________

*_kina da burin koyon sana'a wadda zaki yita daga gida a sauqaqe_*


*_kin jima kina sha'awar yadda yake hada BIRTHDAY CAKE DA DECORATION amma kin rasa wajen da zaki koya?,ko FARASHIN YA MIKI TSADA?_*


*TOFA MATA!*


*_Ga dama ta samu_*


*_UMMU AYMAAN KITCHEN ta shirya tsaf don koya muku yadda ake hada gangariyar BIRTHDAY CAKE wanda ya gama hada dukkan gamayyar kayan dadi masu sanya harshe su motsa,gefe guda kuma ta koya miki yadda zaki qawata waje da walwali da kuma walainiyar KAYAN ADO DA QAWA na wajen gudanar da SHAGALIN BIKI SUNA TARON BIRTHDAY WEDDING ANNIVERSARY da sauransu_*


*_ba'a nan UMMU AYMAAN KITCHEN YA TSAYA BA,tana da ajujuwa na musamman don koyar da mata nau'in girke girke MAIDA TSOHUWA YARINYA,hakanan tana karbar kwangilar abincin taro kowanne iri_*


*_ta fannin kayan maqulashe na fulawa ta samar da abubuwa kamar haka_*

Cake perfait

Cup cake

Samosa

Springrolls

Meatpie

Doughtnout


*SIYAN DAYA KO SARI*


*_za'a koyar dake BAKING AND DECORATION QIRI DA MUZU ta sigar zancan nan da hausawa kance GANI YA KORI JI,gani ga malama_*

*_sa'an nan kuma akwai tanadi na musamman ga masu sha'awar koya ta hanyar yanar gizo wato ONLINE,duka kan farashi mai rangwame_*


*_ZA'A IYA SAMUNTA A UNGUWA UKU,LAYIN MAI FATA ZARIA ROAD*


KO A TUNTUBETA A WANNAN LAMBAR WAYAR

08032964266


*_ZA'A GUDANAR DA KOYARWA NE ON 5&6,GARZAYA MAZA KI REGISTER*ðŸƒðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸






        Sashe ne da kusan yafi kowanne sashe dake cikin gidan tsaro kyau tsaruwa da kuma yawan ma'aikata,hakan ya sanya tun kafin ya tunkari qofa barori dake kai kawo kowanne ke qoqarin aika gaisuwarshi cikin kirari da nuna qauna da kuma girmamawa,saidai a duk sanda sukayi kirarin sai ya dinga jinsa cikin kwanyarsa,tamkar suna gaya masa cewa sarauta zata zama kota zama sanadiyyar rushewa duk wani tsari na karan kanshi da rushewar rayuwarshi,don haka ya soma daga musu hannu yana dakatar dasu,da haka har ya isa ga me martaba.



       Kayan jikinsa kawai zasu nuna maka bai jima da barin xaman fada ba,kaya ne nashan iska,saidai fuskarshi da wani sassan na jikinsa akwai sauran damshin ruwa dake nuna wanka yayi bayan shigowarsa,fulani suratu na zaune daga gabanshi tana bare mishi ayaba,bayan kofi data miqa masa wanda ta cika mishi shi da sassanyar lemo.



       A fakaice ta yiwa azeez din wani kallo kana ta dauke.kanta tana ci gaba da yin abinda take,ta tsani ya dinga kiran yaron haka a lokacin kebewa irin wannan,lokacin da take gani su kadai ya cancanta su kasance tare dashi.



       A qasan shima ya zauna,kansa a qasa cikin girmamawa ya gaida mai.martaba,ya amsa mishi cikin kulawa,fuskarsa dauke da fara'a,ya waiwaya ya dubi fulani saratu

"Barka da warhaka mama" ya gaidata itama,murya can ciki,cikin dakiya da kuma shariya ta amsa

"Barka kadai" duka mai martaba yana ankare,saiya murmusa kawai cikin ranshi,shi yana mamakin kishin qarfin hali irin na mata,a iya saninsa da abdul'azeez bai taba wani abu da zai nuna raini garesu ba,kowacce yana bata girmanta bakin gwargwado,shidai kawai barshi da miskilancinsa,qarancin fara'a da rashin son yawan magana.



       "Ranki ya dade....ki aramin wasu lokuta daga lokutanki mana" mai.martaba ya fada cikin fara'a,ta watsa mishi idanunta,duk da taso yin qorafi amma yanayin yadda yayi maganar dole ta sallama,saita aje abinda takeyi din kawai ta miqe ta basu waje.



    Bayan ta fita ya tashi ya zauna sosai daga kashingidar da yayi,yasa hannunsa ya shafi fuskarsa yana aje numfashi sannan ya kira sunan abdul'azeez,kiran daya sanya gabanshi faduwa ya amsa mishi yana sake nuna tsantsar ladabi

"Wato bansan mutane me suka dauki zalunci ba a wannan zamanin....kusan kowa ya zama azzalumi ba tare da ya sani ba,kowa burinsa ya samu wata dama komai qanqantarta ya zalunci dan uwansa,bansan wanne gardi ko dadi yakewa al'umma cikin ruhinsu ba,nayi tsammanin kowanne muminin qwarai zaiyi qoqarin gudun fanfalaqi wa zalunci iyakacin numfashinsa,komai qanqatar wannan zaluncin kuwa,koda na mummunar magana ce bare na aiki a aikace,a rayuwa zalunci na daya daga cikin manya manyan laifuka,saboda girman laifin Allah daya halicci komai da kowa yace ya haramtawa kansa da kansa shi,ya tauna tsakuwa don aya taji tsoro,ya nunawa bayi shi da yake da ciakken iko da izza ya haramtawa kansa,hakan yana nuni da cewa matuqar wani cikin bayi ya aikata wa wani dan uwanshi wannan zaluncin...bazai barshi ba saiya fidda masa haqqinsa....abdul'azeez,wallahi wallahi wallahi dukkan bawan daya zalunci dan uwansa koda da bawon rake ne bazai shiga aljanna ba sai Allah ya fiddawa wannan wanda ka zalunta haqqinsa,koda kuwa arne ne ba musulmi ba baka ci bagas ba"



      "A yau na yanke wani hukunci da naso ace kana wajen na zartar dashi,wanda har cikin zuciyata inajin cewa shine dai dai....bazan daga qafa ga duk wanda na kama da laifin xalunci ba!,ko waye shi!". Sosai kalaman maimartaba suka dakeshi qwarai,bawai kalamanshi na qarshe ba,tunda ya soma magana suke shigarsa,saiya soma hada maganarshi data sodangi,indai har da gaske ne rashin gata ne!,indai har da gaske abinda zuciyarsa ke ayyana amasa haka ne,hakan na nufin an zalunceta?,hakan yana nufin ammin tayi zalunci?,shima zai iya fadawa ciki?,to amma zaluncin cikin sani ne ko cikin rashin sani,idan har ya tabbata zalunci ne ta yaya zai kubutar da ita a matsayinta na mahaifiyarsa da yake burun ganin tsiranta,ci gaba da yi mata biyayya irin wannan tamkar bata qofa ne naci gaba dayin abubuwan da basu dace ba?.

 


      "Zanyi tafiya ethopia gobe,akwai taro da zamuyi a kamfanin dana sanya hannun jarina,naso ace muje tare dakai ko,kafin nan da shekara hudu da nake saka ran ka cika shekara talatin ka soma wakilatata,nima na soma ragewa kaina wasu al'amuran,to amma hakan bazai yiwu ba don lokaci ya qure,naso magana dakai kwanaki uku baya amma ka bace sam ba'a ganinka,don haka gobe zaka rakani airphort...zan bar riqon masarauta hannun waziri,saidai daga wannan karon inason ka soma sanin wasu abubuwa kaima,zaku riqe qasar tare,zaka zama tamkar mataimakinsa,har zuwa sanda Allah yayi na dawo".



      Baya jin xai iya cewa wani abu illa

"In sha Allah ranka ya dade,Allah ya saka da alkhairi" baya son yawan qorafi,don yasan cewa saratu na qididdige da lokacin da aka shigar mata,don haka basu dora kowacce hira ba ya sallameshi,ya kuma gaya masa lokacin da zasu fita din zuwa airphort.



      *******    *****   *********



       Akwatuna ne a gabanta a bubbude wasu da kaya da ajere a ciki wasu kuma yanxun ta soma jerawa,bisa dukkan alamu aiki takeyi ta katse ta zauna kallon takardun hannunta guda biyu.



     Wani murmushi take fitarwa dake nuna farincikin da zuciyarta take ciki,duk da tayi katatu tuquru amma bata taba tsammanin kyawun sakamakon nata zaikai har haka ba,ko kusa ko alama,dukkan jarabawarta guda biyun sakamakon sun fito mata a ba zata.



       "Kai bilkisu,basan wanne irin qauna haka kikewa karatu ba" sai data sauke ajiyar zuciya sannan ta daga kai tana duban ummi anty zuhriyya,ta sake sakin murmushi

"Inason karatu sosai ummi,inason naga ina karatu a rayuwata" murmushi ummi tayi

"Karki damu daghter,zakiyi karatu in sha Allah,har sai kinji a karan kanki kin qoshi dashi" murmushin itama tayi mata tana kada kai

"Na gode ummi sosai,na gode" yatsanta ta dora saman lips dinta

"Shshsh,Allah xaki godewa,amma nikam na sha gaya miki karki sake godemin ko?" Saita rufe fuskarta da hannunta,ummi ta bita da kallo daga fuskarta zuwa cikinta daya fito cikin tausayi,wani irin mahaukacin girma yake,wata shidda amma saika tsammaci yayi watanni tara ko goma,abun har mamaki yake basu,hakan ya sanya likitan dake ganinta yace idan ta cika wata bakwai zai sake mata ultrasound scan a sake ganin lafiyar baby,duk da cewa tace bata jin komai,hakan shima yana alamta komai lafiya yake,don badon hakan ba da zata ga wata alama ko sauyi a jikinta.



       Kusan ummi zuhriyya ce ta tayata qarasa hada kayan nata,tunda su nasu dama ba wani abu zasu dauka ba,tunda komai nasu yana can,banda ma zasu soma sauka ethopia din da babu abinda zasu dauka

"Duk abinda fa kikasan kina da buqata ki dauka abinki,don idan muka tafi din babu lallai mu dawo nan kusa,har sai sanda abbaa ya kammala abinda ya kaishi"

"Toh ummi" ta miqe tana sake laluba kayanta dakyau,dai dai sanda hisham ya callara qara,da alamu ya tashi a baccin da yake ne,ya samu babu kowa kusa dashi,da sauri ummi ta miqe

"Ga dam gidanki can ya tashi,bari na duba shi" murmushi tayi

"A shafamin kanshi,yanzu zan fito na wanke shi tas ko yaji dadin wasa da kyau" harara ummi ta jefa mata

"A haka da wannan turtsi billin naki" tayi daroya tana ficewa,ita kuwa murmushi ta saki,a hankali kuma murmushin nata saiya yanke sanda ta dora hannun nata saman cikinta,ta soma shafashi daga sama zuwa qasa,har yanzu bata ji qauna ko shaquwar da akan fada ba wai tun yaro yana ciki,bata sani ba ko tata qaddarar kenan?,ko kuma sai yazo duniya?,ko abinda mahaifi da ahalinsa suka mata ne ya danne wannan feeling din?,duka bata da wannan amsar.



      ƘoÆ™ari tayi ta watsa wannan tunanin gefe,kamar yadda ta yiwa kanta alqawarin mantawa da komai,ta kuma fuskanci rayuwarta ta gaba,don haka ta miqe,taci gaba da lalubar sauran abinda yake da muhimmanci a wajenta tana hadasu waje guda gami da ci gaba da shiryasu a kwatin nata.



       Washegari ana ya gobe zasu tafi wunin gida tayi tare da qannenta,sabanin daa a yanzu damuwarta kadan ce,ba kamar lokuttan baya da takanyi tafiya ba,saboda ta gamsu a yanzu da yanayin da suke rayuwa,yanayi mai kyau,wanda anty zuhriyya ta tsaya musu da gasken gaske,hakanan ko cikin gida ga mahaifinta taga wasu sauye sauye da bata zata ko tsammata ba,duk da tayi mamaki amma ta barwa Allah lamarinsa.



       Bayan la'asar ne,ta idar tana saman abun sallar hannatu ta qaraso gabanta da baqar leda ta ajiye maya,bin ledar tayi da kallo tana duban hannatun,don bata gane ba,sai daya zauna sannan tace

"Kudadenki ne da aka baki ranar da kika dawo din nan?" Sai a sannan ta tuna da batun,ta miqa hannu a hankali ta daukesu gamida yaye ledar tana kallonsu,kudaden da suka zama tamkar fansa ga mutuncinta fansa kuma ga duk halin da zata tsinci kanta a gaba,badan Allah yaji qanta ba ya aiko mata ds uwa a gareta.



      Maidasu tayi tamkar yadda suke sannan ta miqawa hannatu,tsayawa tayi tana dubanta,da alamu tana neman qarin bayani

"Kuyi amfani dasu keda sauran qannanki,ki kula da kanku" yawan kudin yasa hannatun ta dinga ji kamar ba zata iya dasu ba,sai suka zauna ita da bilkisun tana kwatanta mata yadda zasuyi amfani da kudin,da doguwar takards me cike da list,wanda hakan ya daukesu lokaci mai tsaho kafin su gama.



       Suna gamawa din hannatu ta dubi bilkisu da idanunta wadanda suka cika taf da Æ™walla

"Ba shakka yaya me gado kin zama uwa kuma uba a garemu,jigon rayuwarmu,ba don ke ba bansan ya rayuwarmu zata kasance ba" saita qarasa fashewa da kuka,sanyata bilkisu tayi a jikinta tana rarrashinta,itama tana qoqarin boye tata qwallar

"Kowanne bawa yana qarqashun kulawar ubangijinsa ne,babu wanda yake rayuwa saboda wani na raye,ko babu ni zaku rayu,hannatu,a yanzun kin soma bin sahun 'yammata,tunda kinkai shekara ta sha biyar,ina horonki daki kame mutuncin kanki,ki kula da kanki da kyau,kada ki yarda rashin mahaifiyarki gaban idanunki yasa ki aikata abinda yake kinsan ba dai dai bane,gwargwadon iko nasan cewa na doraku bisa turba mai kyau,wanda kunsan dai dai kunsan kuma kasin haka,koda bani kusa daku in sha Allahu ba zaku rayu cikin tsanani ba yadda kuka rayuwancan karon,ki kula dakanki da qannenki,idan hauwa'u bata dawo ba har zuwa sanda zan dawo qasar nan,nayi alqawarin in sha Allahu zan nemo mana ita a duk inda take" sallama sukayi mai karya zukata,bata bar gidan ba sai bayan sallar isha'i driver yazo ya dauketa,tabar gidan cike da kewarsu.




********    ******    **********



      Jeri gwanon motocin masarautar kaisa masu kyau tsari da daukan hankali ne suka ci gaba ratsawa manyan titunan garin kaisan,wanda zai sadasu da filin sauka da tashin jiragen sama dake garin.



       Duk wani titi da motocin suka gilma sai an samu jama'a da zasu daga musu hannu gami da kyakkyawan fatan alkhairi ga adalin sarkin nasu,daya tamkar da dubu,basu damu da cewar yana ganinsu ko baya ganinsu ba,burinsu addu'o'insu da fatan alkhairinsu ya riskeshi a duk inda zashi.



       A dai dai lokacin da yake xaune cikin motar data É—arawa duka sauran motocin kyau da tsada,gefanshi kuma azeez ne zaune cikin shigar sarauta shima,yayi kyau har ya gaji da haduwa,duk da cewa baya cikin wannan mode din,amma duka yayi hakanne don ya faranta ran mahaifinsa,ya kuma kautar da idanunsa daga gano damuwa tattare dashi.



       "Abdul'azeez" mai martaba ya  ambaci sunanshi cikin kulawa,cikin girmamawa ya amsa mishi

"Inason idan Allah ya bamu aron rai,na dawo daga tafiyar nan,zamu zauna da iyayen yarinyar nan 'yar wajen alh ibarahim,a tsaida magana me kyau kan aurenku,ya kamata zuwa yanzu a san inda aka nufa kan aurenka,bai kamata magajin sarki ya zaman bashi da future me kyau kan tara iyali ba..." Ya qarashe maganar cikin raha,wanda sam bai lura da yanayin da fuskar azeez ta fada ba,ya dora da cewa

"Sannan idan karatun ya isheka hakanan,inaga ya kamata kayi magana,kawai sai nayi reforming kan dukiyoyina da kadarorina kaci gaba da gudanar dasu,na samu na huta hakanan nima na tattara hankalina kan abu guda,duk da ita kanta sarautar ta soma gundurata,amma munyi magana da mahaifiyarka kan haka...saidai nata ra'ayin ya nuna,kana da tarin kadara wadda ta mallaka maka ita da mahaifinta,da kuma nawa wanda nake saka ran miqa maka su,tafi sha'awar ka gudanar da taka,ta yadda zaka ci gaba da tashi cikin hazaqa kishin kai neman na kai da sanin ciwon nema,duk da hasashenta na a bigire me kyau,amma dole ya kamata a duba wasu abubuwan,wanda duka ba damuwa bane,idan na zauna duk xamu tattauna kan hakan a samu matsaya" duka baice komai ba har sai da maimartaba ya kammala sannan yace

"Alla ya taimakeka,na gode bisa wannan zabi da aka yimin da kuma karramawa,ina da maganganu biyu masu alaqa da juna,zancan zuwa gidansu safwa....ina roqon alfarmar a dakata a yanxun sai zuwa nan gaba,maganar kula da harkokinka kuma Allah ya taimakeka idan Allah ya dawo dakai lafiya,saikayi tunani a nutse,ka zartars da dukkan abinda kaga ya dace"

"Allah ya bamu aron ran,amma meye dalilinka na tsaida maganar aurenka?,baka da labarin dukka 'yan uwanka nasa sun fidda miji?,inason wai da na hada aurenku dasu lokaci guda....amma...bansan naka tunanin ba,na baka lokaci,saidai kada ka bari ya tsawaita baka zomin da gamsashshen bayani ba"

"In sha Allah" ya fada yana lumshe idanu,a wannan qadamin da yake ciki baison ya sake qarawa kanshi matsala,baiyi solving ko daya daga cikin matsalolinsa ba tukunna.



        Dai dai lokacin da anty zuhriyya da nata ahalin suka isa cikin filin sauka da tashin jiragen saman,duba daya zaka musu kasan cewa happy family ne,hatta da bilkisun yau fuskarta a sake take cike da walwala,idan ta tuna inda zasu,tana fata walwalarta ta dore,tana fatan tabar dukkan wata damuwa da matsala tata a kaisa,kowa janye da akwatinsa suka shige ciki,bayan driver ya ajjiyesu ya juya da motar zuwa gida.



       Basu sake wata doguwar tafiya ba motocin nasu suka isa airphort din,suka samu wuri na musamman suka ajjiye motocin nasu,sanda maimartaba yake shirin fitowa sukayi kacibus da waalin kaisa,shi yadan kawo tsaiko saboda tsayawa gaisawa da sukayi,har aka soma screening na matafiya,ganin lokaci na shirin qwacewa yasa abdul'azeez matsawa bayan maimartaba cikin girmamawa ya sanar dashi,don haka basu sake jimawa ba sukayi sallama,maimartaba ya wuce ciki,abdul'azeez na take masa baya,bayan sun baro dukka dogaran a waje,don shi kadai zaiyi tafiyar,sai mutum daya da zai masa rakiya cikin amintattunsa.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 46



*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





         Saida komai ya kammala azeez yana tare da mai martaba,abinda ya rage kawai ya wuce zuwa ciki inda akewa manyan mutane irinsa nasu screening din,idanuwan azeez na biye dashi sanda yake wucewar,duk da ranshi a cushe yake amma hakan bai hanashi jin qaunar mahaifin nasa ba,tare da ayyana abubuwa da dama tattare dashi.



       Wani irin mutum adali,wanda bai dauki duniya da zafi ba,inda shine ke riqe da ragamar rayuwarshi,yake kuma bibiye da al'amuransa sabanin ammi abinda ya faru dashi zaya farun?,ya jefawa kanshi tambayar da baya da amsarta,saiya kada kai,abinda ya sani kawai shine,qaunarshi ta rufewa ammi idanu,har take ganin duk abinda takeyi saboda shine,kuma bisa dai dai take,amma sai yaushe ne al'amura zasu gyaru?.



       Ajiyar zuciya ya sauke yana shirin dauke idanunsa daga inda maimartaba ya wuce wanda tuni ya bacewa ganinsa.



      Karaf idanuwansa suka sauka a kanta,cikin kaduwa mamaki da bazata ya qanqantar da idanun nasa yana son tabbatar da gaskiyar abinda suka gano mishi,naci ya sanya sosai tare da sake matsawa kadan daga inda yake tsaye don kuma tabbatar da zarginsa.



       Itace a tsaye ana duba passport dinta,sanye cikin doguwar riga saqar qasat dubai mai matuqar kyau da daukar idanu,duk da yalwar rigar amma hakan bazai hanaka hango cikinta daya bullo ta cikin rigar ba,yakuma zauna sosai bisa jikinta,idanunta itama nakan passport din kamar yadda idanun me dubawar yake,bai ankara ba yaga ya miqa mata passport din da dukka sauran kayanta wanda hakan ke nufin xata wuce kenan,zata wuce ciki inda babu lallai ya ganta,idan ta wuce ina take shirin tafiya?,wacce qasa zata?,bai sani ba,amsar daya baiwa kansa kenan,amsar data sanyashi zabura cikin matuqar zafin nama da karsashi ya durfafi wajen,duk bashi da tabbacin cimmata kafin yakai wajen saboda 'yar tazara da dan cunkuson jama'a dake wajen.



       Kamar wanda ya fice a hayyacinsa haka ya dinga kutsa jama'a yana neman hanya,wanda hakan ya ja hankalin mutane da dama suka dinga binshi da kallo,wasu da yawa daga cikinsu sunsan wayeshi,sunsan matsayinsa,hakan ya sa ya suka dinga mamakin abinda yakeyi din,saidai shi sam ba wannan bace damuwarshi,damuwarshi ya samota kafin ta bace,damuwarsa ya cimmata,damuwarsa ya ganta a gabanshi,damuwarsa suyi magana,damuwarsa cikinsa dake jikinta,ya tabbata cewa yayi dashe kenan a tattare da ita.



        Saidai ko kodan burinsa bai cika ba,domin yana ganota sanda aka bata boarding pass ta bace masa kamar yadda mai martaba ya wucewa ganinsa,duk da hakan bai fasa niyyarsa ba,har yaso tsallake shingen da aka sanya,wanda hakan yaja hankalin jami'an tsaro cikin mamakin ko babu lafiya suka taso suka dakatar dashi suna tambaya,wanda tambayar ya dinga jinta kamar wani qarin bacin lokacin da datsewar burinsa ne,ya dinga fidda numfashi mai zafi yana son su matsa mishi yakai gareta.



   

       Hannunsa da daya daga cikin manyan hadiman mai martaba ya riqe shiya sanyashi maida hankalinsa jikinsa,ya waiwaya ya dubeshi cikin girmamawa da rusunawa yace,murya qasa qasa ta yadda shi daya zaiji

"Allah ya taimakeka dukka idanuwa suna akanka,ko meye kayi qoqarin daidaita yanayinka,saboda girma da qimar masarautar kaisa,da kuma gudun bacin rai fulani" wannan maganar ta sanyashi sauke nannauyar ajiyar zuciya wadda yakejin kamar anyi ajiyar dutse ne a qirjinsa,yanajin tamkar ya bangaje duk wanda ke tsaye a gabanshi ya ganshi ya cimmata,babban burinsa kenan,bai damu da dukkan wanda zai kalleshi ba,amma maganar data fito daga wane sashe na zuciyarsa ta sanya bai aikata hakan ba

"Ganinta anan din tamkar wata nasara ce a gareka,kuma haske ne da zai kaika ga inda zaka cimmata", da wannan kalaman jami'an suka samu suka tafi dashi xuwa wani kebantaccen daki,suka soma bashi kukawa ta musamman kafin su nemi jin damuwarsa.



        Sam bai damu da ababen sanyin da aka ajjiye masa ba cikin katafaren office din,gaba daya hankalinsa ya karkata ne kan wanda ke binciken list na sunayen passingers din da suka tashi yanzun bada dadewa ba,wanda dama duka duka a yau din jirgi biyu ne kacal ya tashi,biyu ya sauka,ji yake kamar ya finciki na'urar zuwa gabanshi,gani yake kamar baya sauri,haka ya dinga dunqule hannunshi waje daya yana tausar kanshi da gayawa kanshi ya nutsu,yabi komai a hankali.



      Tsahon wasu mintuna da suka biyo baya kafin mutumin ya dago daga allon na'urar,ya zauna sosai yana duban yarima azeez da kuma shugabansa dake zaune gefe shima,a ladabce yace

"Cikin jirgi na biyu daya tashi yanzun tabbas akwai mai suna bilkisu,kuma kusan ita kadai ce ma mai sunan....."

"Wacce qasa ya nufa?" Azeez yayi hanzarin tambayarshi ba tare daya barshi ya kammala jawabin nasa a karan kanshi ba,don ji yake dukka wani bayani da mutumin yake kamar bata lokaci ne,kamar bashi da amfani.



      Ganin yadda yanayinsa yake a qagauce yasa shima ya bashi amsar tambayarsa kai tsaye

"Ethopia"

"Ethopia?" Ya samu kanshi da tambayar kansa da kansa,idan yace zai tsananta tunanin abinda zataje yi can din tabbas ya yaudari kansa ne,bai gama sanin wacece ita din ba totally balle yace yasan wani abu daya shafeta,wanda zai bashi hasken tana da alaqa da canne ko 'yar can ce,abu guda daya ne da yakejin zai zame masa mafita shine,ya yanki ticket yabi dukkan wani jirgi da aka samu zashi qasar daga yanzu zuwa kowanne lokaci

"Qasar ethopia nada girma da fadi,bawai qaramin gari bane qwaya daya da zakace kana sauka zakaga wanda ya santa koya hadu da ita ya nuna maka inda take,idan kaje ina zaka dosa?" Zuciyarsa ta antayo masa da duka wadan nan bayanan da rudu yasa yaso mancewa dasu,yanaji cikin zuciya da gangar jikinsa cewa zai iya qarar da dukka numfashinsa wajen nemanta koda baisan inda take ba,to amma hanya mafi sauqi da kwanyarsa ta yi masa hasashe shine,gidansu nan ne muhalli qwaya daya tak da xai samu sahihin inda zai sameta acan inda ta tafin ba tare da jinkiri ko bata lokaci ba,jinkirin da yakejin duk bayan shudewar wasu mintuna kamar yana shudewa ne da farincikinsa,walwalarsa da kuzarinsa,yanajin kamar bashi da dukkan wata jarumta da yasan kanshi da ita.



       Da wannan shawarar ya miqe,ya miqa godiyarsa garesu cikin qasaita ya soma barin office din,yana jin wannan karon koma meye zaya faru saidai ya faru,amma babu shakka zai nemo ladingo a duk inda take,zai kuma sanyata ta nuna mishi gidan mahaifan bilkisun,bayajin zai iya jurewa wannan asarar cikin rayuwarshi,idanuwansa sun gane mishi gaskiya da sahihancin abinda ammin ke kokwanto akai,me kuma yayi saura?,har cikin zuciyarsa yana jin wani feeling idan ya tuno fuskarta da cikinsa dake zaune a jikinta,yana jin wani irin yanayi mai nauyi da wuyar fassara idan ya tuna fuskar macen data taba masa sunan matarsa da kuma cikin dake amsa sunan dansa jininsa ne kwance a wajen.



       Tunda ya koma gida bai yadda ya hadu da kowa ba,tsarinshi duka shine inda za'a nemo ladingo duk inda ta shiga a masarautar kaisa,sam yama mance da batun bar mishi kula da qasar shida waziri mahaifin abdulrashid da me martaba yayi,don hankalinshi ba'a jikinsa yake ba.



       Kwana guda da wuni guda kafin a lalubo mishi itan cikin sirri da boyewa,baya son batun yakai kunnen ammi bare ta samu damar dakatar dashi,yana son kome zai faru ya faru bayan ya cimma gaci.



       Tunda masu tahowa da ita zuwa sashen nashi suka risketa gaba daya jikinta yayi sanyi qalau,gabanta ke dukan uku uku,tasan cewa kashinta ya bushe,kuma tata ta qare kenan,saboda bata manta da gargadi da kuma jan kunne da babbar murya da fulani tayi mata ba,bayan ta sauya mata sashe ta dauketa daga cikin gidan sarautar gaba daya,to amma matuqar yarima ke buqatar jin wani bayani daga bakinta tasani cewa akaran kanta bata da zatin da zata iya jaa da kwarjininsa,bare har ta musawa buqatunsa,da wannan tunanin suka iso cikin sassan azeez cikin duhun bayan isha'i,suka ajeta a inda ya buqaci ganawa da ita kafin ya fito,taci gaba da zaman jiranshi cikin fargaba da rudani,ko ina na jikinta rawa yake kamar kazar da aka tsoma cikin ruwan qanqara aka ciro.



        Takunshi kawai ya isa ya sanya dukkan wani dake wajen ji a jikinsa,a jininsa yake kuma halittarsa ce,tarin kwarjini da haiba wanda mutane da yawa kan camfa,wasu suce siya masa akayi,wasu suce akwai kalar dabbar da yake ci wanda hakan ke qara masa kwarjini kulli yaumin.



        Tun baiyi magana ba ta sake rusunawa sosai tana miqa gaisuwa cike da tsantsar ladabi,kanta a qasa bakinta yana rawa,bai amsa mata ba,saidai ya baiwa dukkan wani mahaluki dake wajen umarni da ido nasu basu waje,cikin qiftawa da bismillah wajen ya zamana daga shi sai ita,ya gyara tsaiwarshi sosai yana dubanta na wasu sakanni,sannan kai tsaye ya jefa mata tambayar data zama silar zuwanta wajen

"Idan kin amsa min babu qarya ko boye boye to ba shakka kin kubuta,ki cire dukkan tsoron wani daga zuciyarki ki bani amsar tambayoyina dai dai,wannan shine kawai mafita a rayuwarki"

"Allah ya taimakeka.....ya qara maka nisan kwana sarkin gobe.....ya qarawa mai martaba daraja da daukaka.....ya qarawa fulani lafiya.....ba shakka kome zaka buqata daga wajena....nidin me biyayya ce ga umarninka" kai ya jinjina yana sauke numfashi,cike da sarauta yace

"Kece mutum daya tak da kikasan gidansu....ina ne gidan mahaifanta?" Ko bai fito baro baro ba tasan wa yake nufi,zuwa yanzu tana jin kamar gudawa zata qwace mata,ko bai gargadeta bama ba zata iya musu dashi ko yi masa qarya ba,tasan cewa wutsiyar raqumi tayi matuqar yin nesa da qasa

"Tana nan unguwar hayin malam amadu Allah ya taimakeka" shuru yayi yana hasashen unguwar da sunanta,bazai iya tuna wacce unguwa bace,mutumin da baiyi cikakkiyar rayuwa cikin masarautarsa bama ina zai san wasu anguwanni cikin qasar tasu,saiya katsewa kansa wahal da tunaninsa da yakeyi yayi magana ta qarshe da ita yana mai takawa yana barin wajen

"Ki zama cikin shiri" iya abinda ya gaya mata kenan ya wuce zuwa ciki.



        Cikin dare saiya dinga ganin dare yayi masa mugun tsaho,tamkar gari ba zaya waye ba,kamar safiya ba zatayi ba,wani irin dare ne daya cika fal da mafarkinta da kuma tunaninta,uwa uba kuma tunanin cikin dake jikinta wanda yayi imanin babu tantama ko kokwanton cewa nashi ne.



       Baiyi barci ba sai daya kira abdulrashid ya shaida masa komai da kuma aniyarsa na zuwa gidan gobe da kanshi,gami da neman rakiyarsa

"Ko baka fadi ba yarima zuwa ya zama dole"

"Amma inaso mu tafi da mota daya zuwa biyu,itama idan da hali daga cikin motocin gidan mai girma waziri,banason ko kadan motar masarauta ta shiga wajen,don banson labari ya zowa ammi har sai na gama aiwatar da abinda na qudurta"

"Baka da damuwa man" ya amsa mishi cikin qarfafa gwiwa.



    *******   ****    ********



       Duk yadda ya dokanta da zuwan washegarin sai gashi tazo mishi a baibai,ta kuma zo mishi da sakamakon da yake gani shine mafi muni cikin kowanne sakamako da aka taba bashi a rayuwa.



         Ko cikin motar kallonshi kawai abdulrashid yakeyi,baisan da wanne harshe zai lallasheshi ba,dukkan wanda yasan azeez dakiya irin tashi,jarumta da taurin zuciya,zaiyi mamaki qwarai idan yaga yadda ya sauya lokaci daya,daga sadda jerin gwanon amsoshin suka shiga kunnuwansu

"Tabar qasar jiya ko shekaran jiya,babu kuma wanda ya sani ko yake da masaniyar inda taje ko zataje a can din". Amsoshin dashi kansa abudulrashid suka bashi mamaki,bare azeez daketa jujjuya maganganun cikin kwanyarsa.



        Ta yaya É—a ba bawa ba za'ace ba'asan inda ya tafi ba?,shin bata da mahaifiya data damu da ita ne?,wanne irin mahaifi gareta da zai bar diyarshi tafiya zuwa wata qasa bashi da tabbacin muhallin da zata tsinci kanta?.



         Hannunsa dake dunqule tun daxun ya saka ya daki kujerar gabashi,yana jin wani zafi zugi da radadi na ratsa ilahirin jiki da zuciyarsa,amsoshin da aka bayar kamanceceniya suke da ana masa bushara da ya rabu da shukar daya dasa,shukar dake mallakinsa wani bangare na jikinsa,da ko yarsa zasu zama basusan wayeshi ba.



         Wasa wasa kafin sukai gida saiga wani irin zazzabi yana neman lullubeshi,tun abdulrashid na daukan abun wasa sai yaga da gaske ne,amma sam azeez din ya hana a shaidawa fulani,duk data aiko jin lafiyarsa saboda rashin ganin gilmawarsa wunin jiya dayau gaba daya,yace a shaida mata lafiya qalau yake,bata kawo komai a ranta ba,saita aza hakan da nauyin da maimartaba yabar musu ne na kula da qasa ya kawo hakan,ta saki murmishi tana jin dadi har cikin zuciyarta,tanajin cewa ko a yanzun babu ko tantama taci riba wajen maqiyanta.



             *_BILKISU_*



        Tun tana kuka saboda farincikin tarin dangi da gata da suke dashi ita da mahaifiyarta har hawayen suka daina zuba,sai.mamaki daya cika zuciyarta taf,ta sake yarda da cewa mahaifiyarta ta daban ce,hakanan zuciyarta mai tsarki ce,samun irinta cikin matan wannan zamanin abu ne mai matuqar wahala,ta yarda tabar dukkan wani daula jin dadi da arziqi na mahaifanta da danginta ta zauna da mahaifinta,mutumin da ko cikin ma'aikatan gidan akwai da yawa da suka fishi arziqi,amma sam bata duba wannan ba,ta martaba soyayya ta gaskiya,ta bata qima da daraja ta zauna dashi,to amma shin shidin ya biya ta?,ya saka mata da dukkan tarin alkhairinta da kara da yakanar data yi masa a rayuwa?.



         Tamkar xasu cinye bilkisu haka kowa ke haba haba da ita,ta sake yadda tabbas maimunatu ta musamman ce cikin danginta sanda taji anty zuhriyya tana qorafi

"Wato kunga makwafin maimunatu shine za'a koma 'yar gidan jiya,aci gaba da nunamin wariyar launin fata ko?,wannan karon kota ni ba'ayi,dadin abundai nidin dai nice na kawo muku ita" ta fada cikin tsokana da zolaya,wanda bilkisu ta lura tafi bada qarfin tsokanar tata ga jakakarsu,wadda ta haifi mahaifinsu,wanda ita daya tal ta rage musu,da alama kuma tare ta rayu dasu tun quruciya tasan quruciyar kowa a cikinsu

"To dama an gaya miki akwai abinda zai ture gwamnatin maimunatu ne a wajena duk da bata a duniya?,ai babushi" yanayin yadda tayi maganar xai gaya maka cewa,duk da tarin tsufanta amma hakan bai hana mutuwar maimunatu sukar zuciyarta ba,uwa uba mutuwar mahaifin maimunatun kanshi bisa dukkan alamu itama bata barta ba,duk sai jikin kowa yayi sanyi a wajen,don har abada ba zasu manta da mutuwar uba da diyarsa ba da suke ababen soyuwa a zukatanta.



       Duk yadda zata fadi kasancewarta cikin danginta a ethopia tasan baki yayi kadan ya bayyanashi,girma da tsadar lokuttan qauna kulawa da tattali ya sata ta manta duk wani qalubale data taba fuskanta,takan manta meya faru da ita a yawancin lokutta idan ba cikinta ta shafa ba,wanda yake yin wani irin girma naban mamaki,saidai hakan bai fiya damunta ba,saboda lafiya qalau take jinta,tamkar bata sha fama da azabar laulayi ba kamar bazata kai labari ba.



        Sanda suka gama satittikan da suka tsara yi sannan su wuce brasil sai sukaso riqe bilkisun,saidai anty zuhriyya tace samm qafarta qafar bilkisu,akayita ja amma taqiya,daga qarshe abbu yace su barta,don yadda ta kafe din baijin akwai abinda zai sauya ta.



        Suma din basuga laifinta can ba,tunda ita tadauko musu ita ta kawo musu,bai kyautu su gwada qarfin dantsensu suce saisun riqeta ba,tsohuwar ta dungure kanta tana cewa

"Ja'ira,har yanzu taurin kai kafiya da tsiwar tana nan,ta yaya bazanfi son maimunatu ba?"

"Eh din,nadaiji" itadai bilkisu na gefe tana murmushi,yanayin yadda suke qaunar junansu tana burgeta,waiyau ita bilkisu ce ake rububin daukarta,ana gasar nuna mata soyayya da gata.



        Lallai duniya labari ce,hakanan dukkan tsanani yana tare da sauqi,tunda ko hakane,indai ta manta dukkan wata damuwa da barazana da rayuwarta ta fuskanta a baya,babu abinda xai hana ta shimfida sabuwar rayuwa da zata baro dukkan wani miki data taba samu cikin zuciyarta,duk da tasan cewa an bar mata babban tabon da bazai taba warkewa kota manta dashi ba,saita dora hannunta ta shafi cikinta da a satittikan nan yake yawaita motsi,motsin da aduk sanda suka yishi take sake ganin girma isa da buwayar mahaliccinta daya sanya dan adam cikin dan adam,ya kuma rayashi ya maidashi mutum cikakke.



       Kwanaki uku suka qara suka tattara suka wuce brasil,yanayin rayuwar can din yayi mata dadi qwarai,ya kuma sake mantar da ita abubuwa da yawa,ta samu isashshen lokaci ta tsarawa kanta dukkan abinda takeson gabatarwa,da kuma abinda takeson zama anan gaba bayan ta rabu da cikin jikinta,kusan komai sai data tsarashi,wani cikin kwanyarta,wani kuma a rubuce,sannan ta tattara ta miqawa Allah lamuranta,ta kuma duqufa da addu'ar ya cika mata dukkan burikanta data qudurta,tare da bara da roqon kada ya sake qaddara wani abu da xai gilma ya sake ruguxa mata mafarkinta.



*_YARIMA ABDUL'AZEEZ_*




        Dukkan wata juriya da jarumta tashi ta qare,kamar yadda tunaninsa kan yadda zai nemota ya qure,zazzafar damuwa ta kwantar dashi,ciwo sosai wanda yake jinsa cikin kowanne lungu da saqo na jiki da zuciyarsa,yana jin zuciyarsa ta masa wani irin qunci,yakanji zuciyarsa tana radadi da ciwo,wanda yake saka ran nan gaba kadan komai zai iya faruwa da zuciyarsa.



         Ciwon nashi ya sake daga hankalin ammin sosai,hakan ya sanya ta saka ido sosai kan duk wani lamarinsa,sanya idanun da yayi sanadin binciko abinda ya boye,ya bayyana a gareta yaga bilkisu,ya kuma shiga fafutukar nemanta.



        Sosai hankalinta ya tashi,ta rasa inda zata sanya rayuwarta,wai meke faruwa ne?,me yake faruwa?,me yasa azeez ya kasa cire yarinyar daga rayuwarshi?,me yasa ya kasa ajeta gefe yaci gaba da rayuwarsa kamar yadda tayi hasashe ta kuma tsara?.



       Hankalinta ya sake tashi sanda ta tuna da zancan safwa,qorafin data kawo mata cikin wancan satin,duk zuwan da take duba azeez yaqi bari ta ganshi,hakanan duk wani kiran waya ko saqo da take aika masa babu feedback ko guda daya,saita alaqanta hakan da rashin lafiyarsa,ta kuma bashi uzuri tare da alqawarin dai daita komai.



       Saidai abinda basu sani ba shine,tuni ya yankema ranshi cewa,matuqar ya zauna ya rayu da wata macen cikin nutsuwa da kwanciyar hankali,tamkar ya tafka wani mummunan zalunci ne ga rayuwar wata halitta da bata taba zaluntar tashi rayuwar ba,tamkar ya fasa gobensa ne.



         Wadan nan bayanan data samu ya sanyata ta gaza zama,qarfe goma na dare ta shirya daga ita sai kubra ta nufi sashen yarima azeez,ranta a matuqar bace,zuciyarta a dugunzume,tana jin cewa wannan karon zata masa mai gaba daya ne,zata masa mai dungurun gum,zatayi masa ta yanke ta gille mai gaba daya haihuwa da hanji.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 47

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




       Dai dai lokacin da yake zaune shi daya cikin katafaren falonshi labarin isowar fulani ya riskeshi,ya daga kai ya dubi agogo sai yaga goma harda mintuna na dare,hakan ya bashi mamaki qwarai tare da tabbatar masa lallai muhimmin abu me girma ne yake tafe da ita,sai ya miqe zuwa cikin bedroom dinsa,ya sanyo wata jallabiya ruwan gold mai dogon hannu santsi da sulbi da kuma daukar idanu,sannan ya dawo zuwa cikin falon.



       Koda ya dawo tuni ya isketa tsaye tsakiyar falon,goye da hannayenta,idanunta na duban qofar dakin gadon nashi,kallo daya zaka yiwa tsakiyar idanunta kasan cewa ranta yakai qarshe wajen baci,hakanan fushi ne kwance rubuce saman fuskarta.



        A nutse yayo tattaki zuwa gabanta,ya rusuna a ladabce yace

"Barka da dare...." Bai qarasa ba ta daga mishi hannu,cikin kakkausar murya ta soma magana

"Ni na dauki cikinka cikin qunci da wahala wata É—ai É—ai É—ai har watanni tara cif,ba tare dana sauke na huta ba harsai da kakai wadan na kwanakin,na tsugunna na haifeka cikin rashin tabbacin zan rayu ko bazan rayu na,nice cinka shanka,fitsarinka,lafiyarka da lalurarka,idan kayi dariya nayi,idan kayi kuka nayi,idan kana da buqatar abu sai inda qarfina ya qare,nakan haqura da komai idan baka sonshi,hakanan nakan dauka kona rungumi duk abinda kakeso,ban daina dawainiya dakai ba da kula da dukkan lamuranka,da kuma duk wani abu da zai cutar dakai ba har kawo yau da kake da shekaru ashirin da shida a duniya......amma yau.....ni aishatu nizan maka umarni kan wasu abubuwa ka nemi bijiremin?,wai shin?,me kake nema wajen yarinyar da babu shi ga sauran mata da har xaka gagara fitar da ita daga rayuwarka kamar yadda na tsara na kuma buqata abdul'azeez!" Ta qarashe maganar cikin daga sauti dake cike da bacin rai,abinda kusan bazai iya tuna yaushe ya taba faruwa tsakaninsa da ammi ba,hakan ya sanya ya sake sadda kanshi qasa,yana jin wani rauni yana mamayarsa,zuciyarsa tana kakkaryewa gami da tsinkewa kamar zare,yayim da sautin muryarta yaci gaba da ratsa falon cikin bacin rai

"Kome zanyi nayishi ne saboda kai wanda kai din na zaka taba fahimtar hakan ba sai nan gaba!,ni na kawo yarinyar cikin rayuwarka nace kuma ta fita,na kawota a sanda baka santa ba bakuma kayi zata ba,a yanzu kuma nace bana buqatar hakan!,shin ka shirya fito na fito dani ne abdul'azeez?!" Ta saje jefa masa tambayar cikin fada sosai,wanda ya sanyashi zamewa saman gwiwoyinsa ya tsugunna anan gabanta,yana jin fadan nata har cikin jininsa,yana iya jiyo sautin bacin ranta daga zuciyarta,cikin taushin murya yace

"Ammi....maganar da sukazo miki da ita kikaqi gasgatata gaskiya ce,zancan yarinyar tana dauke da......"

"Ya isa!....ba wannan naxo ji ba,na jima da bunne batunta,na jima da bunne duk wani daya shafeta,saura ya rage naka,idan aure ne matsalarka.......ka shirya aurenka da safwa nan kurkusa,amma ka sani,dole kaje kayi karatu tuquru ka zama wani,dole matsayin da nakeson ganinka akai ka takashi,dole ka manta da an taba yin wata halitta cikin sa'o'in rayuwarka mai suna bilkisu...inhar ka shirya ci gaba da kasa cewa a sunan dan aisha diya ga sarkin mali!,idan kuma ka shirya cire jinina daga naka!,ka shirya sauya uwa to kaci gaba da dorawa daga inda ka tsaya,ni dakai aga wanda zai fasa abdul'azeez,kaci gaba nace!,amma ka shirya sauya wata uwar bani ba!" Daga haka ta juya tayi tafiyarta ba tare data tsaya taji koda kalma daya daga bakinsa ba,ba tare data waiwaya tayi masa duba na biyu ba,ta dinga takawa tana jin bacin rai sosai da tsanar bilkisu,yarinyar tana son zame mata qarfen qafa,tana son ta zame mata wata katanga daga cikar burikanta kan danta datasha wahalarsa,me yasa tun farko nata sauyawa bilkisun qasa ba ta yadda ba zasu sake haduwa da azeez din ba,banda kyau na fuska bata san kuma bataga wani abu da zaija azeez zuwa gareta ba,me yarinyar keda shi haka?,ta yiwa kanta tambayar da bata da amsarta.



        Tunda ta fita bai motsa daga inda yake tsugunne ba inda ga barshi,ji yakeyi kamar wanda ake watsawa ruwan qanqara,tun daga saman kanshi zuwa yatsun qafarshi,a rayuwa bashi da kamar ammi,hakanan babu kamar uwa cikin rayuwar kowacce halitta,kama daga mutum aljani dabba tsintsaye qwari harma da tsirrai,dukkanin wanda zai soka to bazai maka koda kwatankwacin soyayyar datayi maka bane,itace ta soka tun baka zama mutum ba,tun bata sanka da idanu ba,bata taba ganinka ba,kana boye cikin fatar cikinta amma take qaunarka,har kazo duniya baka da hankalin bambance mai kyau da mara kyau,harka zama cikakken mutum da kowa ke qaunar ka rabeshi,akwai soyayyar datafi wannan?.



       To amma abu mafi daure kai shine,ina wannan tausayin na daa da uwa?,ina wannan soyayyar?,duka ammi ta sanya qafa tayi fatali da ita?,meye abunyi a gareshi?,ya mata biyayya ya banzatar ya kuma sarayar da haqqunan rayukan da zuwa yanzu baisan guda nawa bane?,ko kuwa ya bijire mata ya shirya tunkarar dukkan wani abu da xai sameshi a rayuwa?.



         Wannan tunanin shi ya kusa daskarar da qwaqwalwarsa,har baisan adadin lokutta daya shafe durqushe a wajen ba,sai daya ji jikinsa na fidda wani irin hucin zafi dake alamta masa tempurature din jikinsa ya hau sosai,sannan ya iya dafa abinda ke gefansa ya miqe tsaye da qyar,kamar wanda ya shekara a duqe,yakai kanshi dakinsa da qyar.



        Bai damu da yanayin jikinsa ba bare yasha wani magani,tsahin daren kawai ya qarar dashi wajen yanke hukunci na qarshe a rayuwarsa,wanda wayewar garin ranar da sassafe ya isa gaban ammin,ya kuma shaida mata hukuncin daya karba cikin zabi biyun data bashi.



*_kaso na biyu cikin labarin kenan masu karatu,zamu shiga cikin kaso na uku,ku biyoni_*





    *BAYAN SHEKARA BAKWAI*



       Cikin nutsuwar 'yar madaidaiciyar motar mai azabar kyau fasali da tsari gami da daukan hankali take sako kai cikij katafaren asibitin dake zaman kanshi wanda keda mazauni cikin brasillia dake qasar brasil,bansan me ya sanya ba ban kuma san dalilin daya saka duk inda motar ta gifta saita dauki hankulan jama'a da dama dake kai kawo cikin asibitin,wasu kuma na zaune guraren da aka kebance saboda buqatuwar masu zuwa asibitin wanda a nan gida nigeria yafi kama da wajen shaqatawa ko shan iska,saboda yadda ya wadata da ababen zama masu kyau,korayen tsirrai da kuma iska mai dadi qwarai da kwantar da rai.



       Bata gushe ba motar tana ci gaba da ratsawa cikin asibitin,har sai data isa muhallin da aka tanada a dokance saboda ajiyar ababen hawa,akayi mata parking me kyau kafin a kasheta,wanda zai gaya maka drivan dake sarrafa motar ba shakka yasan abinda yakeyi.



         A qalla saida aka dauki kyawawan mintuna uku kafin qofar motar ta bude a hankali kuma cikin nutsuwa,wanda budewat motar yake dai dai da fitowar wani rantsatsen qamshi mai kwantar da zuciya da sanya nutsuwa,hadi da sanyin acn da aka kasheta a yanzu.



       Idan kakai dubanka cikin motar sai kace tirqashi!,wata halitta ce mai cikar zati haiba da kwarjini,wadda kamala da nutsuwa suka sake qawata kyanta,kwarjininta kuma yake bayyana kansa.



        Zaune take a sit din drivern da alama itace me tuqin kuma mamallakiyar motar,sanye cikin wani lallausan yadi mai azabar kyau da daukar idanu,wanda sam ba'a cika masa ado ko qawa ba,an masa dinkin riga wadda tsahonta ya kawo har gwiwa,sai kuma street skert mai matsakaiciyar tsaga wadda ba zata fidda halittar qafarta ba,tayi rolling da mayafi madaidaici wanda bata buqaci dankwali ba tunda ya rufe mata dukkan inda ake buqata,fuskarta sam babu kwalliya ko kadan idan ka dauke powder da man lebe masu taushi wanda yasa lebunan nata suka qara kyau da qyalli,sai jikinta dakw fidda wani irin sihirtaccen qamshe mai nuna tsada da ajin turaren da take amfani da shi.



    hannunta dake sanye da wani kyakkyawan zobe qwaya daya,sai agogo a tsintsiyar hannunta daketa aikinsa ta sanya ta zare muqullin motar,sannan ta waiwaya sit din gefanta ta saka hannunta tana tattara kayayyakinta dake zube a wajen,wanda takardu ne cikin wasu folders,qaramar hand bag nata wayoyinta sai labcoat dinta dake rataye a fuskar kujerar.



       Sai data gama tattare kayan tana shirin dorasu saman cinyarta don ta samu damar fita sai idanunta suka sauka kan wani qaramin lunch box da aka dan turashi qasan kujera da alama ana boyewa wani ne kada ya ganshi.



       Idanu ta zubawa lunch box din kafin ta miqa hannu a hankali ta daukoshi,sannan ta dorashi saman cinyarta ta bude.



        Komai da komai da ta zuba yana ciki,babu abinda aka taba ciki sai drinks din data zuba aka kwashe,choculets da biscuit.



        Wani murmushi ne ya subuce mata bata shirya ba,ta dora yatsanta guda biyu saman labbanta tana girgiza kai

"Amatullah....amatullah,Allah ya shirya min ke" harta maida lunch box din sai kuma ta fasa ta hada da dukka kayayyakin nata ta zuro santala santalan qafafunta dake cikin hillshoes mai igoyiyi ta fito zuwa waje.



         Nan take Dr Bilkees Bilyamin ta bayyana,kamanninta da suka dan sauya kadan sakamakon gishirin rayuwa wato ilimi daya ratsata,wayewa hutu jin dadi uwa uba nutsuwa da kwanciyar hankali data samu cikin wadan nan shekaru bakwai din.



        Tana gama kulle motar ta soma takawa zuwa wata hanya da zata sadata kai tsaye da office dinta,tana mai sauya yanayin fuskarta,ta ragewa fuskarta fara'ar dake samanta a daxun,tadan daureta tana sake maida hankalinta ga inda take sanya qafafunta.



        Daga yanayin yadda ma'aikatan asibitin ke gaidata cikin girmamawa kawai ya isa ya gaya maka ita din wata ce,ta dinga amsa musu bakin gwargwado cikin kulawa,har takai jerin inda office dinsu yake.



        Office na kusa da qarshe ta saka card dinta wanda bayan ya gama duba bayanan jiki qofar ta bude mata,ta sanya kai cikin sauri ta shige.



        Tana qoqarin maida qofar idanunta ya sauka kan wani office da yake opposition da nata office din,allon dake dauke da suna da matsayin me office din na mamallakin asibitin ya bayyana,tayi hanzari maida qofar ganin tana yunqurin budewa,bakinta cike fal da addu'ar Allah yasa ba zuwanta yaji ba ya fito,taja qaramin tsaki tana rage kayayyakin dake hannuntanta hanyar ajiyesu,donta hana kowa ya amsar mata kayan,matsayin da suke bata da girman da suke bata ita bata sonshi sam,batasan me yasa Dr adam yayi mata haka ba,ya fiya naci kafiya da kuma rashin zuciya,ta tabbata idan da wani ne da tuni ya tattara lamuranta ya watsar,amma shi ko a jikinsa wai an mintsini kakkausa,duk abinda takeyi din nunawa yake kamar ma bai fahimceta ba,sai sake shige mata ma da yakeyi.



         Sai data gama duk abinda zatayin sannan ta soma amfani da kayan wutar dake gabanta,kama daga cellphone zuwa kwamfuta,ta soma da neman wanda ke kula da office dinta,taji ayyukanta na yau.



        Akwai yaran data yiwa aiki jiya wanda dole yau zata shiga ta duba yadda suka kwana,sa'annan akwai wasu yaran da zata gani a yau din,duk da cewa sai yanzu ake gaya mata,don a qa'ida ba lallai ita zata gansun ba,amma iyayensu sun dage kan cewa ita din sukeso ta dubasu.



        Tana cikin hada kayan da zata buqata idan ya fita round din,tana kuma jiran isowar nurses din da suke qarqashin kulawarta wadanda tare zasuyi round din qofar office din nata ya bude,wanda tun bata daga kanta ta kalla bakin qofar ba tasan ko waye.



         Dr adam ne,shi kadai qofar ke budewa ba tare data bada izini ba,don haka bata daga kai ta kalli bakin qofar ba taci gaba da sabgarta.



        Dogon matashi ne,ma'abocin tsaho da kuma fari,irin farin nan qal wanda kana kallonshi xaka san cewa ruwa biyu ne,a shekaru duka duka bai wuce shekara talatin da biyu ba,amma tsahonshi ya sanya akan bashi shekaru sama da haka,daga kallon farko xaka fahimci cewa shi din ruwa biyu ne kamar yadda na fada a baya,haka yake,mahaifiyarsa haifaffiyar qasar brasil din ce,yayin da mahaifinsa ya kasance dan asalin nigeria,bafulatanin jigawa,saidai dukka rayuwarsa yayita ne yana kuma yinta a qasar ta brasil,zai iya cewa tunda yake zuwanshi nigeria dangin mahaifinsa sau daya ne.



        Cikakken likita wanda haihuwar mahaifiyarsa a qasar da haihuwarshi shima da akayi a qasar yasa ya samu damammaki masu tarin yawa,ya kuma zama shima halastaccen dan qasar,wanda hakan ya bashi damar mallakar fili da gina asibiti nashi na qashin kansa,babban asibiti na kudi wanda yayi shuhura cikin garin,yake kuma da kyakkyawan tarihi na qwarewa da iya kula da marasa lafiya,musamman mata da qananan yara,wanda a halin yanzu bilkisu take aiki a qarqashinsa,cikin asibiti bangaren cututtukan da suka shafi yara.



        Ya fada soyayyar bilkisu tun bata gama karatunta ba,bayan ta gama kuma yasan yadda yayi ba tare da masaniyarta ba ya bata aiki a asibitinsa,wada farawarta aikin babu jimawa ya bayyana mata qudurinsa,saidai ko kadan ita bata dauki kalmar soyayya a bakin komai ba,face kalma mara ma'ana mara amfani a rayuwar mutum,kalmar da bata bata sha'awa kota burgeta,hasalima tana mata kallon azzalumar kalma mai cutar da duk wanda ya raÉ“a kanshi da ita.



       Duk wani halin ko in kula da hannunka mai sanda bilkisu ta nunawa dr adam saboda ya shafa mata lafiya,ya barta ta rayu qalau cikin salama amma yayi funfurus,da fari ya dauka sonshi ne batayi,amma data gaya mishi ita bata taba soyayya bama saiya dauki tutsun da take masa ba'a bakin komai ba,yaci gaba da qoqarin kafa gwamnatinsa a wajenta,duk da yaji shakkun cewa da tayi bata taba soyayya ba,amma tunda daga bakinta yaji hakan,bashi da ikon musantawa,ya kauda kanshi daga duk wani zille zille nata,ya kafa dukka kayan aikinsa ,yaci alwashin saiya mallaketa a matsayin matar aurensa.



        Tunda yake duniya bai taba ganin macen datayi masifar tafiya dashi ba,ta kuma kwanta mishi a rai irin bilkisun ba,ta hada dukkan wani abu da yake zata ga diya mace,harma ga wanda hankalinsa bai taba bashi mace kamar bilkisun zata mallaka ba,wata irin soyayya yake mata har cikin jininsa,hatta da mahaifiyarsa tasan da zaman soyayyar da yakewa bilkisu,yaci alwashin bazai sassauta ba har sai yaga abunda ya turewa buzu nadinsa.



       Nannauyar ajiyar zuciya ya saki gami da murmushi kana ya sake hannayensa dake harde a qirjinsa tun daxun yana qare mata kallo,yayin da take zaune saman kujerarta tana ci gaba da duba wasu takaddu tana hadasu waje guda ba tare data dubeshi ba tunda ya shigo,ita ala dole bata ga shigowarsa ba,yasan kuma sarai ta gani,saidai shima yadda ta basar din yayi masa,tunda ko banza ya kalleta son ranshi,sai ya soma takowa zuwa bakin table din nata,yaja kujera ya zauna yana cewa cikin yaren nasara

"Kome kikayi kyau yake miki,kome kuma kikayi kin isa kiyishi"

"Assalamu alaikum warahmatullah" ta fada ba tare data dubeshi ba,saiya dan dafe bakinsa yana cewa

"Afwa,na sha'afa ne,kyakkyawar fuskarki ta shagaltar dani.....assalamu alaikum warahmtullah" a fakaice ta tabe baki kana ta amsa mishi ciki ciki,banu kaifi adam.din yana da dabi'u na gari,saidai hausawa sunce society da mutum ya rayu a ciki yana da matuqar tasiri cikin dabi'unsa da halayensa,dabi'unsa mafi yawa na turawa ne,wanda wasu abubuwan wajen cikakken bahaushe musulmi dan arewa abun kubya da qyamata ne,amma zaka samu su a wajensu ba komai bane,sabida tasirantuwa da sukayi da dabi'unsu,bare shi da aka haifeshi cikinsu,ya rayu dasu har yau kuma yake rayuwa a cikinsu,abubuwa da yawa na halyayyarsa tana cin gyaranshi akai,yana kuma gyarawar tare da qoqarin kiyayewa,don da wuya ya maimaita kuskure idan ta gyara mishi saboda zallar soyayyar da yakeyi mata,bata bashi dama ya sake cewa wani abu ba ta miqe tana riqe da wani file guda daya ta dubeshi

"Idan ka gama idan babu damuwa.....ka rufe min office din,zan fita round" fuskarshi babu alamun damuwa yace

"Me zanyi da office din da babu ke a ciki,wajenki nazo,ya kamata ko minti biyar a bani" saita gyara riqon takardun hannunta ta sake cewa

"Mubar aikin mu xauna hira kenan ko kuwa?"

"Da zakiyi hakan da nafi kowa murna" idanu ta dan fiddo,wanda hakan ya qara mata kyau a idanunsa

"Kafi kowa sanin cewa ba wannan nazo ba....sannan duk wani ganganci ko kuskure dazai faru a asibitinka,qasarka ba zata qyaleka ba zata hukuntaka ne,sannan waima.....shin ku turawa ba 'ance kunfi kowa kiyaye doka da qa'ida ba?" Dariya sosai yayi harta tsaya kallonshi,kana ya tsagaita ya bata amsa

"Baki fada dai dai ba,kin manta ni bahaushe ne dan nigeria?,kusan kullum saina gyara miki fa?" Kusan tunda ya soma sonta ya maida kanshi dan nigeria sosai,saboda yadda ya lura tana kishin qasarta,tana kuma yawan maganarta dason komawa can nan kusa,sabanin daa dabai damu ba,ka kirashi dan nigeria ko dan brasil duk daya ne a wajensa

"Banga alamu ba,tunda nidai a dan brasil na sanka...." Tana kaiwa nan qofar ta shaida mata akwai mutane dake tsaye a wajen,hakan ya nuna mata nurses din sun qaraso,don haka sai kawai tayi gaba abunta,batason ya sake tsaidata.

7/11/21, 4:33 PM - My Mtn Number: 48


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070






         Tsayin wani lokaci tana round din tana duba dukan yaran da suke qarqashin kulawarta,cikin nishadi take komai gami da cikakkiyar qwarewa tare da kulawa ta musamman,lokaci daya Allah ya sanya mata son aikin nata duk da cewa a fari ba shine zabinta ba,amma a yanzun sai ya zama aiki mafi girma data fi so da qauna albarkacin yaran da take ceto rayuwarsu,hakanan Allah ya bata tarin farinjini wajen yaran,duk yaron data zama likitarsa saiya qaunaceta,babu banbancin yare kalar fata qasa ko addini,hakanan Allah yake sanya sabo da qauna tsakaninsu,don da yawa ma ko bayan sun bar asibitin sukanci gaba da hulda da ita da kuma zumunci.



        Bayan ta gama dubasun ta soma ganin patient din nata suma cikin qwarewa da karsashi,ta samu sakewa don ba kasafai dr adam gake shigowa ba idan tana ganin marasa lafiya.



        Ta dan dauki lokaci mai tsaho kafin ta gama dubasun,duk da cewa can din ba kamar qasarmu bane,babu cinkoson marasa lafiya da ake tilawa likitoci tarin aikin da yafi qarfinsu,saidai ita din qwarewarta ya sanya koda yaushe bata rabo da ganin marasa lafiya.



        Ajiyar zuciya ta sauke tana duba agogon hannunta,lokacin dauko yara daga makaranta ya kusa,mintuna kadan suka rage,duk da cewa motar makaranta tana daukosu tun daga cikin makarantar har zuwa qofar gidajensu,amma yau ta musu alqawarin cewa zata zo da kanta ta daukesu,don lokacin tashinta yayi dai dai da lokacin tashinsu suma.



       A nutse ta miqe ta soma warware rolling din kanta,idanunta nakan calender dake maqale a jikin bangon office din,tana lissafin kwanakin wata da kuma kwanakin da suka rage musu tafiya seminer din da aka turasu zuwa qasar dubai,ba kasafai ta fiya son irin wadan nan tafiye tafiyen ba saboda kare mutuncinta da kuma rage zargi a zukatan mutane,saidai duk sanda wani abu na samun qwarewa ya taso daga asibitin dr adam baya yin qasa a gwiwa wajen sanya sunanta a sahun farko farko,hakan na daya daga cikin mabudin nasararta,da kuma silar zamantowarta qwararriya kuma gogaggiya akan aikinta.



       Gefe guda kuma tana samun dukkan wani qwarin gwiwa daga wajen anty zuhriyya da kuma abbaa,wanda batasan da wadanne kalmomi a kullum zata gode musu ba,hakanan batasan dame zata saka musu ba,sun bata dukkan wani taimako qwarin gwiwa da kuma goyon baya,har ta kawo matsayin da take kai a yanzun.



        A nutse ta gama warware rolling din nata,kyakkyawan gashinta daya wadatu da gyara ya bayyana,yanata sheqi da fidda qamshi,ta nadeshi da band fari qal,ta zare agogon hannunta sannan ta shige bandaki ta daura alwala,wanda kusan sabonta ne,bayan ta fito ta ciro wani tattausan handkherchief wanda ke fidda wani qamshi mai sanyi ta goge ruwan jikinta,kana ta maida dukka nadinta da agogonta tsaf.



       Lunch box din amatullah kawai ta dauka sai handbag dinta ta fita a office din,da saur i sauri ta wuce office din dr adam don kada ma ya fuskanci fitarta bare ya biyota,don tsaf zai iya shige maya mota yace sai sunje tare,abu na qarshe da tafi tsana kenan,don bata son yaranta su dinga ganinta da wani mutum na daban baquwar fuska,wanda hakan zai iya illawa tarbiyyarsu,hakanan batasan amsar da zata basu ba kan waye ne nasu,inda ma abun yazo mata da sauqi,duk da tarin wayo kaifin basira da fikira da Alla ya basu,Alla bai taba budar bakinsu sun tambayeta waye mahaifinsu ba,inda take godewa Allah kenan.



         Sai data tada motar ta soma barin harabar asibitin sannan ta hangi dr adam ta madubin gaban motar,tsaye yake harde da hannayensa yana bin motar da kallo,hakan yayi mata dadi sosai,da alama yaso cimmata,saidai hakan bata samu ba,duk yadda akayi kuma aiki ya tsareshi ya manta actual lokacin tashinta ne sai daga baya ya farga,data tabbatar saiya mata katsalandan din daya saba mata.



         Tun batayi nisa ba taji alamun shigowar saqo wayarta,bata raba dayan biyun shine,don haka ta share ba tare data duba ba taci gaba da tuqinta hankali kwance.



       Minti ashirin da biyar kyawawa ta isa makarantar tasu,daga inda ake aje motoci tayi parking tana kallon yara nata ficewa zuwa motocin dake daukarsu zuwa gidanjensu,kusan dukkanin yaran yaran turawane masu jajayen fata,wasunsu 'yar qasar wasu kuma baqin haure kamar dai su.



       Idanunta kan hanya har zuwa sanda ta hangi yaran suna nufota,kyawawan 'yan biyu masu masifar daukar hankali,duk da cewa ba jinsinsu daya ba wato mace ne da namiji amma kuma kamanninsu daya,kai daga gani basai an gaya maka ba kasan cewa 'yan biyu ne irin identical din nan,wadanda da ace jinsu guda n zaiyi wuya adinga banbance hassan da usaini ko hassana da usaina,sai Allah ya taqaita ya yosu jinsin daban daban.



         Kallonsu take sosai kamar bata sansu ba,kallonsu take tana jin wata qaunar yaran nata tana ratsata,tanajin wata soyayya ta musamman dake tsakanin uwa da 'ya'yanta.



       Murmushi ya subuce mata ita daya sanda taga sun tsaya sun danyi magana tsakaninsu,abdulrahman dake a mazaunin hassan ya hade rai yayo gaba abinsa,sau tari takan zauna ta jima ta kuma bata lokaci tana lalube tare da binciken dawa suke kama?,kaf danginta uwa da uba basu dauki kamar kowa ba,hakanan halaye da dabi'un abdur rahman sau tari suna bata mamaki,wata dabi'a ta daban kai kace babban mutum ne,dukkan tunani da hasashenta kan yanke ya kuma qare da bacin rai idan zuciyarta ta gaya mata

"Wala'alla dangin mahaifinsa ya dauko a kama,haka halayya da dabi'un ma" takan miqe cikin bacin rai kamar da wani take maganar,a sarari kuma ba'a boye ba ta furta

"Allah ya tsare,ya kiyashi 'ya'ya na"



      Abdur rahman ne ya soma isowa,ta dubeshi fuskarta har yanzu dauke da murmushi

"Sarkin miskilanci sarkin fushi,me kuma akayi?" Ta fadi sanda yake shigowa sit din kusa da ita

"Abokina ne yace wai bamu da daddy...tunda bai taba ganin daddynmu ba,shi kuwa nashi daddyn ne yake kawoshi makaranta kullum,shine yace zai bamu daddynsu,amatu tace eh muna so" wani abu mai nauyi ne ya sauka a qirjinta,wanda har yayi tasiri wajen hanata cewa komai,a haka har amatu ta qaraso ta bude gidan baya ta shiga ta rufe,saita gaza cewa da yaron komai har zuwa sanda ta tashi motar,tana jin lokacin da amatu tayi hugging dinta tana murnar xuwa daukarsu da tayi,amma ta gaza waiwayawa ta dubeta ko tace wani abu,haka taci gaba da yin shuru,tana jin yaran na sabgarsu sama sama.



       Wato komai nisan jifa qasa zai fado,sannu sannu ranar da take murnar bata zo ba takeson riskarta,wacce amsa ce zata dace da tarin tambayoyinsu da zasu ci gaba da zuwa mata dasu anan gaba kadan?,tunda koda yaushe wayo suke dada yi.



      A hankali ta waiwaya tana duban sashen da abdurrahman yake xaune da litattafansa saman cinyarsa,saita lura da wata babbar takarda daya wareta yana kallo,ta sake duba karo na biyu,hoton wannan business tycoon din ne,wanda yayi wani irin shuhura da shahara a fadin duniya,qasashe iri daban daban,zata iya cewa a shekara gudan nan taga hotunanshi taji labarinsa babu adadi,saidai a duk sanda idanunta zasuga hotonshi saita hadu da wata mummunar faduwar gaba da fargaba da batasan dalili ba,wala'alla hakan baya rasa nasana da sunan da yake amfani dashi daya danganci sarauta,wadda batasan ta wacce qasa yanki ko nahiya bace *A M YARIMA*.



      Tun abinda ya faru a wancan qarnin ta tsani duk wani abu da xai danganci sarauta,ko zai fito shafi sarauta,kama daga suna sutura da sauransu,hakan ya sanya take zaton dalilin faduwar gabanta kenan,harma ta soma tsanar ganin hotunan,wanda koda bata gansu a poster ba,takan ci karo dasu lokaci zuwa lokaci matuqar zata kalli labaran duniya a kowacce tasha,kuma zasu sako labaran kasuwanci,to abune mawuyaci suyi su qare basu sako shi ba

"Ina ka samu wannan hoton?" Ta tambayi abdul tana maida kanta ga tuqin da takeyi

"Uncle ne ya bani....mami...inason xama irin wannan mutumin idan na girma,uncle ya gayamin jajirtacce ne,inason na zama jajirtacce kamarsa" murmushi kawai tayi ganin yadda yake bayanin bilhaqqi daga zuciyarsa kamar wani babban mutum,ba tare data dubeshi ba ta sanya hannunta saman kanshi,ta shafi sumarsa sannan tace

"Allan yayi maka albarka,ina fatan ka fishi komai da komai,bakasan wayeshi ba,kullum kace kanason ka fishi ne ta hanyoyin alkhairinsa kaji?" Kai y gyada mata yana ci gaba da duban hoton daya bude din,da alama yana ji da takardar.



          Sanda suka isa gida yaran sun rigata fita,kasancewar ta tsaya tattara duk abinda suka bari nasu a motar,ta gama ta fito tana shirin kulle motar ta hangi amatu datayi gaba kanta sanye da crown a kanta irin na yara.



       Hakanan gabanta yayi mummunar faduwa,da hanzari ta gama rufe motar ta rufa mata baya,cikin taku qalilan ta cimmata sanda take dab da shiga falon gidan,ta jawota tana cire abun daga kanta,cikin fada ta soma magana

"Wannan abun fa daga ina?,ina kika samoshi?" A narke take duban ummin nata ganin yadda take fada tace

"Qawata ce ta bani" hakanan taji ranta yana baci ganinta da abun,ta zazzaro idanu tana dubanta

"Ashe baki da hankali amatu?,roqo kika koyo?,meye hadinki da wannan abun da zata baki shi?" Saita maqale kafada idanunta na cikowa da qwalla

"Ina sonshi mommy,yana bani sha'awa,shine tace tana dasu da yawa na birthday dinta,saita bani daya" wurgi bilkisu tayi da abun yana tuna mata wani abu,tana jin kamar masarautar kaisa ce a jikin abun,kamar ta bishi ta tattakeshi,ta maida dubanta ga amatu data fara qwalla,tana bin abun da idanu tana jin kamar taje ta dauko abunta

"Gargadi na qarshe zan miki,karki sake na sake ganinki dashi,bama shi ba,karna kuma ganin kin karbi wani abu daga hannun wani,idan ba haka ba saina yanka hannuwanki,kina jina?" Ta fada a tsawace tana dan murda kunneta,da sauri ta daga kai tana dafe kunnun nata da hannunta,hawaye yana sauko mata,sai kuma taji tausayinta ya ratsata,ta sakar mata kunnen tana cewa

"Oya...ku wuce ciki" dukka suka shige din da hanzari,ta maida dubanta inda tayi wurgi da abin na wasu sakanni sannna ta dauke kanta da zummar bin bayansu zuwa ciki itama,sai a sannan ta lura anty zuhriyya tana tsaye ashe tana kallon duk abinda ke faruwa,da suka hada ido saita dauke kai kawai ta matsa mata ta shige zuwa ciki.




          A dakinta ta taddasu zaune babu wanda ya cire unifoarm dinsa bare yayi wanka koya sauya wasu kayan,tana shiga dukkansu suka taso suka rungumeta,amatu na kuka sai abdulrahman ne yace

"Kiyi haquri ummi,ba zata sake ba" wani irin tausayi da qaunarsu ta sake ratsata,wani irin so yaran suke mata,basason ganin bacin ranta ko yaya yake,yanzun zasu kasa sukuni gaba daya su addabi kansu,saita duqa saitinsu ya hadesu gaba daya cikin jikinta tana shafar kan amatu tana cewa

"Shikenan ya isa,kiyi shuru" cikin lokaci qanqani suka ware,ta sake musu wanka ta sauya musu kaya,sannan sukaci abinci suka fita falo,don yau gidan babu kowa,ateeq da najwa already suna makaranta,sai weekend suke zuwa hutu,abeed sun fita tare da babanshi,sai khadija dake barci abinta saboda ta rigasu dawowa daga makaranta,ba makaranta daya suke ba,nurain kuma yana bayan anty zuhriyya din.



         Sai da suka fita sannan tayi nata wankan,ta zauna gaban madubi tana shafe lallausar fatarta da mayukanta da take amfani dasu,masu azabar taushi qamshi da tsada,tana duba saqon dr adam

"Na gode qwarai da kika gudu kika barni,amma dai duk da haka na godewa Allah daya bani ikon ganinki a yau,ina dokin zuwan gobe don na sanyaki a idanu na,ina kuma addu'ar ranar da zaki aminta na kawo miki ziyara koda sau daya ne a tarihin rayuwata" baki ta tabe,cikin ranta tana mita,tana kuma ganin iska na wahal dame kayan kara ne kawai.



        Tana gama sanya rigarta tana shirin fita anty zuhriyya ta iskota

"Sannu da aiki bilkisu" tace da ita,koda batace komai ba tasan tana mata magana ne kan amatu,yaran na gaban goshinta ne fiye da kowa,ba'a tabasu a kwan lafiya,wani irin so take musu,kamar yadda hakanan suke da tarin farinjini wajen kowa dake baiwa bilkisu mamaki.



      Bata amsata ba harta zauna gefan gadonta sannan tace

"Yanzu har amatu ta isa wannan fadan a wajenki?,yarinyar da batasan komai ba,batasan wacece ita ba?,nasha gaya miki dole kiyi haquri da wasu abubuwan da zaki dinga gani,ko munqi ko munso jinin sarauta ne su,akwai wannan jinin dake yawo a jikinsu kullu yaumin,zamu iya ganin halayya da dabi'u na izza da sarauta tattare dasu,wanda mu bamu isa mu cire musu ba tunda ahalin abunne,haka Allah S W T yaga dama ya haliccesu......so pls ki daina zafafawa da yawa haka,basusan komai ba su din,kada gudun gara ki fada zago,kici gaba dayin abubuwan da zasu sanya su saka ayar tambaya akan kansu"



       Hakane kalaman anty zuhriyya,to amma itama bayin kanta bane,wani abun batasan tana wuce gona da.iri ba akansa har sai ta gaya mata,ita din kamar uwa take mahaifiya a wajenta,cikin sanyin jiki tace

"Zan gayara mami in sha Allah"

"Allah ya yarda,bari na qarasa naga kema kaman fitowa zakiyi"

"Eh mami yanzun nan,zan baki labarin wani yaro dana duba yau,ciwonshi akwai ban mamaki da daure kai" murmushi anty zuhriyyan ta saki

"Banga abinda a yanzu kikeso sama da aikinki din nan ba,kullum akwai sabon labari,kamar ba'a nan muka dinga dambarwa muna qoqarin tanqwaraki nida abbaa ban kan ki zabi bangaren" dariya sosai bilkisu tayi har herarrun fararen haqoranta suka bayyana kana tace

"Mami banda tuna baya fa"

"Oho dai" ta fada tana dariya gami da ficewa,itama saita juya gaban mudubin nata tana murmushi,ta jawo wani turare me kama da cream.ta lakata ta soma shafe hannayenta fatar cikinta zuwa wuyanta dashi,wani qamshi mai taushi ya soma tashi cikin mintuna qalilan,ta maidashi inda ta dauko kana ta dauki wayarta ta fito.

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 50


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





        Kusan koda yaushe ta zauna takanyi tunanin me yasa ya kasa mantawa?,me yasa lamarin ya gaza gushewa daga tunaninsa duk da shekarun da suka soma gangarawa?.



        Ko sau daya bata taba tuhumarsa ko sake tunkararsa da maganar ba,domin yabar maganar tun daga ranar data bashi zabi,ya kuma zabi yi mata biyayya,ya zabi ya faranta mata,ya zabi yabi abinda ta shimfida ta kuma tsara.



       Bata manta irin wahalar da yasha a sannan shekaru bakwai baya,har hakan yaso karya zuciyarta,yaso yasa ta karya tsarin nata da hannunta,ya kusan sanyata ta maida hannun agogo baya ta kuma sauka daga kujerar naqin data hau,saidai daga baya ta qarfafawa kanta gwiwa,taci gaba da zama kan matsayin da take kai,duba da abubuwan da zasu biyo baya idan har ta biyewa son ran abdul'azeez din,cikin abubuwan da zata iya fuskanta din kuwa harda kunyata gaban abokan xamanta,wanda ta dade da sanin cewa bata da abokan gaba sama dasu,suna daga cikin mutane dake sahun farko farko dakeson ganin kunyatarta da tozartarta cikin masarautar.



       Abu mafi girma kuma dayafi wannan tsanani shine.....hukuncin da zata fuskanta daga hannun mai martaba,wanda wala'alla dukkan wani buri daya dorawa azeez din ya karye bazai kuma sake dawowa ba.



        Ci gaba tayi da kallon fuskar tashi sanda yake kusantowa inda take,tana ci gaba da tuna wasu daga cikin abubuwan da suka faru ya yarda ya kawo kanshi zai mata biyayya a sannan,saidai taci wahala ita kanta kafin zuciyarsa ta samu dangana,inda ta masa tukuici da abinda take ganin zai sake sanyashi yayi laushi ya kuma haqura,wato auren SAFWA,anyi auren irin wanda take buri,auren da labarinsa ya fantsama lungu da saqo na qasar,ya kuma bawa maqiya haushi da takaici,hakanan ya tayar da tarxoma tsakaninta da kishiyoyinta,suka dinga duban cewa kome akayi a bikin mai martaba ne ya tsaya musu,ya kuma yi musu barin dukiya fiye da yadda yakeyi aduk sa'ilin daya tashi aurar da diyoyinsa.



       Murmushi kawai yayi,ba tare daya biyewa lamari na kishinsu ba,don ya fuskanci duk yadda zai musu bayani ba zasu fuskanta ba,dukkan wata gudunmawa daya dace ya bada ya bayar bakin gwargwado,sauran kuwa ya sani dukka tsarin aisha ne.



       Abu guda É—aya daya fuskanci basu fuskanta ba daga wajen aisha ba wanda yake da yaqinin da sun karanceta da abubuwa da dama.basu gallabi kansu ba dashi,wani irin salon kishi ta iya wanda takan iya dugunzumasu tunani a lokuta da dama,ta manna musu hauka ta kuma nuna kamar batasan ana yi ba.



       Ako yaushe takan yi qoqarin yin abunda xai alamta musu cewa ita ce 'yar gaban goshinsa,koda a muhallin da ba hakan bane,aisha ce matarsa guda daya da bata taba yarda wani yagansu a rana shida ita,komai girman laifin da zai mata komai girman sabanin da zasu samu,zata fitowa ta nunawa duniya lau suke,basu da wata matsala,basu taba ma fuskantarta ba,yayin dasu kuma anasu bangaren basa iya haka,hatta da yaransu sukan samu masaniyar sabanin dake tsakaninsu,saboda qorafi rashin haquri da rashin iya yin shuru aduk sanda wani abu ya gitta tsakaninsu na rashin fahimtar juna,wanda ga aishan sam ba haka bane,bata iya yin haka,wannan yasa ta samu matsayi a wajensa da tazara mai girma tsakaninta da matansa,duk da cewa sun dan girme mata,sun kuma rigayeta kasancewa tare dashi.



        Da fari ba safwa ba,ita kanta taci wuya da azeez din kafin a samu daidaito,su zauna zaman aure na haqiqa irin na kowanne ma'aurata,saboda canzawar hali da wasu daga cikin dabi'unsa,kafin daga bisani ta samu abubuwan su daidaita,saidai har a yanzun safwan bata samu kanshi dari bisa dari yadda taso ba,yadda kuma tasha qiyastawa zata samu,kamar bata gabanshi,kamar dole yake zaune da ita,kamar akwai dalilin da yasa yake zaune da ita,tayi dukkan abinda take ganin ya dace kuma zata iya amma har yau bata samu yadda takeso din ba,tayi haquri ta tattara ta zubawa sarautar Allah idanu,tana zaune dashi sabida darajar soyayyar da take masa wanda har yau bataga namiji kamarsa ba,hakanan babu wani haqqinta da bai saukewa,saidai akwai abubuwa da yawa da take da buqata daga gareshi fiye da wannan.




       Kamar lokacinsa,kulawarsa tarairaya da soyayya ire iren wadda take gani ga turawa finafinai da litattafan turawa na soyayya,fara'arsa da walwalarsa ta zama wani abu mai tsada da wahalar samu a wajenta,amma dukka ta jure saboda soyayya.



        Ajiyar zuciya fulani ta saki sanda yake isowa gabanta,ya qarasa a hankali yadan rungumeta ta gefab kafadarshi daya,tasa hannunta a bayanshi tadan bubbuga kamar qaramin yaro,tana jin babu dadi na yadda fuskarsa take a kullum babu walwala,ya saketa yana miqa mata gaisuwa cike da girmamawa,amsa mishi tayi cikin kulawa da fara'a,kafin daga bisani su wuce zuwa ciki daga ita saishi.



      Katafaren teburin cin abinci ne da aka cikashi da kalolin abinci nau'i daban daban na alfarma,da kanta fulani take serving nashi duk kalar abincin dake wajen,harta kammala yana biye da ita da idanu baice komai ba,ta tura komai gabanshi taja kujera itama ta zauna bayan ta tsiyaya tataccen matsatstsen ruwan 'ya'yan itatuwa tana kurba a hankali,idanunta akanshi.



       Sam bata qaunar wannan shurun nasa daya sake zame masa dabi'arsa kuma jinin jikinsa,ta aje cup din tana sakin boyayyar ajiyar zuciya

"Sai yaushe ne su safwan zasu wuce?" Cikin mamaki ya daga kai yana dubanta,kana daga bisani ya cire farin eye glasess din dake idanunsa,yana jin ranshi na baci kadan kadan,kada dai ace wucewarta tayi ba tare da sanin ammin ba

"Tun inacan mukayi waya da ita cewa jiya zasu tafi,ban samu dawowa a jiyan ba shi yasa na gama musu komai daga can.....bata shaida miki ba kenan?" Murmushi kadan ammi tayi,tana jin ranta yana son ya soma baci kan wasu baqin halaye da bata so daga safwan,amma batason ran nata yakai ga baci har azeez din ya karanci hakan,tunda ko babu komai tafi kowa sanin cewa zabinta ce ita din

"Eh to....wala'alla don kada suyi missing flight ya sanya bata tsaya munyi sallama ba" sosai ranshi ya sake baci,koda bata zo ba ai a qalla ta kirata ta gaya mata ko?,baice komai ba ya ciro wayarshi daga aljihun gaba rigar suit din dake jikinsa ya soma neman layinta na brasil,dai dai sanda ammi tace

"Ba wani matsala bace,dama kawai naso na hadasu da sodangi ne,saboda yanayin kula da suhaima din,fata dai Allah yasa aje a sa'a kawai" bai tanka ba yaci gaba da neman layin,duk da yasan cewa ammin tanason dakatar dashi ne.



       Qin shiga layin yayi,yayita qoqarin nema bai samu ba,ya tabbatar idan da sun isa ko bai shiga ba zai nuna masa alamun suna qasar,to babu wannan alamar,don haka saiya sauya akalar kiran nashi zuwa ga lambarta ta qasar nan.




        Ga mamakinsa sai gashi kiran ya shiga,cikin mamakin ya kasa kunne yana jira yaji me zai faru,babu dadewa aka daga,muryar safwa ce tas tana fadin

"My prince....ka iso kenan?"

"Kina ina?" Ya jefa mata tambayar akwai alamu na bacin rai cikin sautin muryarsa,cike da rashin damuwa da nuna halin ko in kula tace

"Ina gida"

"Wanne gida?"

"Gidanmu wajen mom" idanunsa ya lumshe kana ya budesu,yana son yayi controlling fushinsa

"Ina suhaima?"

"Urppp.....sun wuce ita da mama rahama....zuwa jibi zanbi bayansu,idan ban samu jirgi ba kuma next week,kafin sannan sun gama settling na komai ko?" Kamar zuciyarshi zata fito haka ya dinga ji,magana da itama tamkar bata lokaci ne,don haka ya kashe wayar kawai ba tare daya ce mata komai ba,amma ya sani cewa saiya hukunta tata.



      Ya rasa wacce irin uwace ita da har yau batasan cewa ita din uwa bace,har yau kallon kanta take a safwanta,shagwababbiya 'yar lelen daddynta da mom dinta,bata iya raino nuna kulawa ko tattalin diyar da Allah ya bata ba,baya manta gwagwarmayar da aka sha kafin ta haife suhaima,kullum cikin kuka raki da tsoron ba zata iya haihuwa ba itakam,an gaya mata akwai wahala da ciwo,amma bai zaci wannan banzar halayyar shagwabar mara amfani zata ci gaba da bibiyarta ba,son jiki da rashin son yin komai,sai shegen son soyayya kamar wadda laila da majnun sukayi cikinta.



       Duk idanunsa a lumshe yayi wannan tunanin,muryarshi can qasa yace

"Zan soke duk wani abu da nazo yi,zan bisu gobe in sha Allah"muryar ammi da tuni ta gama jin komai ta katseshi

"Ka qarasa dukkan aikinka....babu wata matsala,ka yankarwa kubra ticket zata bisu,bayan ta isa zan tura sodangi taci gaba da zama da ita,har sanda za'a sallamesu", kai kawai ya kada baice komai ba,wannan bacin ran ya hanashi cin abinci,duk da dama cin abincin nasa ya zama sai a hankali tun lokuttan baya,amma saboda ammin ya daure yadan tsakuri wani abun.



       Kiran wayarshi da abdulrashid yayi shiya tadashi,ya yiwa ammi nuni da yana zuwa,ya fice yana amsa wayar.



      Bai gama ba har ya isa sashensa,wanda yake a gyare tsaf bayan gyara na musamman da aka masa,aka kuma sauya fasalin tsarinsa da gininsa,ya sake dacewa da zamani,wanda ba qaramin kudi aka narkar ba

"Ka jirani kawai,fitowa dama zanyi yanzun" azeez din ya fada yana katse kiran,lokaci guda kuma yana cire kayan jikinsa sannan ya shige bandaki.



       Gaba daya ya baiwa business dinsa muhimmanci da lokaci fiye da komai cikin rayuwarsa,yana jin shine abu guda daya da zai dinga debe masa kewa da rage masa damuwa.



       Minti talatin cikakku ya fito cikin rigar wanka,ya samu wata kujera dake daura da gadonshi ya zauna yana goge ruwan jikinsa,a hankali idanunsa suka sauka kan wani dan mitsitsin frame mai matuqar qanqanta dake maqale jikin drower gefan gadonshi,idanu sosai ya zubawa frame din,tsahon wasu sakanni sa'annan ya lumshe idanunsa yana jin yadda bugun zuciyarsa ke dada gudu,ya miqa hannunshi a hankali ya dauki frame din yana dubanta.



      Tsahon wadan nan shekarun babu wani abu da ya ragu tattare da ita a zuciyarsa da rayuwarsa,saima qaruwa da yayi,ya sake habaka zuwa wani mataki na daban,kullum yanaji wani sashe na zuciyarsa na faduwa yana rugurgujewa idan ya tuna da ganin da yayi mata na qarshe,duk da yadda kullum kwanan duniya yake qoqarin danne zuciyarsa to amma yana ji a jikinsa,yana kuma tsoron ranar da zuciyar tasa zata bijire,ranar da zata bi karbar umarnin ammin,ranar da zata bijirema dukkan wani umarni.



        Cikin jikinta fa?,tambayar da idan ya yiwa kansa yakejin kamar zuciya da qwaqwalwarsa zata fashe,yana jin kamar zuciyarsa zatayi bindiga,dukkan wani bin diddigi da binciken inda take har yanzu bai samu komai ba,bai samu wani qarin bayani ba da zai masa jagora ko ya bashi hasken ina take?.



       Jin ya soma shiga wani yanayi wanda idan ya shiga din yakan kwana biyu a birkice ya sanyashi maida hoton ma'ajiyarsa kana ya miqe yahau shiryawa,saidai duk da hakan qwayar idanunsa tuni ta jirkice ta sauya kala,wannan dalilin ya sanya koda ya gama shiryawa ma baqin glass ya sanyawa idanunsa a maimakon fari yadda ya saba,yana ganin kiran safwa ya share,ya sani idan har ya sake ya daga to sakamakon da zai biyo baya bazaiyi musu dadi ba dukkaninsu daga shi har ita,ganin kiran nata ma sake qona masa rai da dugunxumashi yakeyi,don haka ya antayata a black list,wanda ba wannan ne karon farko da irin hakan ke faruwa ba dama,da zarar yaga alamun zata shiga rayuwarshi,abubuwa da dama tana cin daraja da mutuncin ammi ne,da tuni ya sanya kakkaifan gatari ya datse duk wata igiyar alaqa da tayi saura a tsakaninsu,wanda hakan da zai faru sai yafi kowa samun sukuni tare da ci gaba da fuskantar rayuwarsa.



       Nannauyar ajiyar zuciya ta saki bayan ficewar azeez daga falon,tana mamakin halayen safwan wanda ada bata santa dasu ba sai a yanzun,tana jin ba dadi da yadda ta zama wata rabin mutum,wadda tsabar gata da sangarta yasa bata iya tsinanawa diyarta ko mijinta komai,komai zatayi saida taimakon ma'aikata da barori,gaba daya yarinyar kamar ba jininta ba,kamar ba ita ta haifeta ba,bata fiya damuwa da matsaloli da sabgoginta ba sai idan abubuwa sunci tura,gaba daya safwan tazo mata ba'a yadda ta zaceta ba,duk wani data xata daga gareta babu shi,badan badan ba.



       Bata jima da jin zancan cewa ta gama haihuwa da safwan tace tayi ba,don tana tsoron mutuwa,mutum biyu ne suka mutu ranar da taje naqudar suhaima a gaban idanunta,to ba zata sake ba bare a wuce da ita,tun tana daukan abun barazana da tsoro da wasu matan kan shiga a lokacin da suka haihu,harta fuskanci da gasken gaske take,tunda har zuwa yau da yarinyar keda shekara hudu bata sauka daga kan qudurinta ba,babban burinta na gaba a yanzu shine ayita haifawa a zeez din yara maza,ta yadda ko nan gaba kambun sarauta da gadon maimartaba bazai bar jikinta ba,ta lura mahaifiyar safwan itama sam bata iya tsaiwa tayi mata wani fada,data soma taga ran ya baci koya sakar mata kuka shikenan an wuce wajen,ba don tana duba wasu abubuwa ba da babu shakka ta sakewa azeez din aure,saidai akwai abubuwan da take dubayya dasu,shi kamsa azeez din tana da buqatar ganin dawowarsa cikin mode dinsa na baya.



        Daya daga cikin katafaren kamfaninsa dake da mazauni cikin garin kaisa ya nufa,ziyara ta bazata don babu wanda yasan da zuwanshi,hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,saboda sun san cewa qaramin kuskure zakayi a yau din yayi maka sanadiyyar rasa aikinka.



       Ba wanda baisan halinsa ba tun daga sanda ka soma aiki dashi kama yau,mutum mai zafi fushi fusata da tsautsarar ra'ayi,sau da yawa abdulrashid kanyi mamakin yadda ya koma ayau,saidai idan ya tuna girman abinda ke damunshi a rayuwa saiya bashi uzuri,sauda yawa shike qoqarin fahimtar da ma'aikatan kan cewa ba haka halayyar yariman take ba,akwai abinda ya sauyashi,sukan jishi ne kawai,don a haka suka sanshi,kuma a haka suke ci gaba da ganinsa har kwanan gobe basu ga wani abu daya sauyashi ba.



       Ya jima sosai cikin kamfanin yana duba abubuwan da suka dace ace ya duba din,a ranar wadanda tsautsayi ya rutsa dasu da yawa sun rasa aikinsu,saidai abdulrashid daya dinga fansarsu kamar yadda ya saba,ya sallamesu da jarin da xai ishesu su kama sana'a.



        Sai dare suka koma gida tare da abdulrashid din,don basu gama tattaunawa ba kan abinda ya hadasun,har yanzu ranshi a jagule yake,baya ga mode dinsa na yau da kullum kuma sai case din safwa,abun yana damunshi sau tari,amma a gaban ammin wasu lokuta yakan nuna bai damu,tunda yasan kome ma zatayi zabin ammin ne,abinda ta zaba mishi kenan,duk da cewa duk lokacin da tayi katari yana kan tsininsa baya daga mata qafa ko yi mata da sauqi.

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 51


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




        A gaggauce take fitowa zuwa ainihin falon gidan don ta samu abinda zata sanyawa cikinta kafin takai ga fita zuwa asibiti,wanda ayau din tana da tarin ayyuka,ciki harda aiki da zata yiwa yara uku,ba sabonta bane makara sam shi yasa gaba daya hankalinta yayi gaba.



       Duk inda ta motsa qamshi ne mai taushi da sanyi yake fita a jikinta,musamman idan kana daura da ita,duk shigar da tayi kyau take mata,musamman shigar da takanyi wadda ke killace komai na jikinta,ba zaka iya ganin komai na jikinta ba,daga fuskarta sai hannayenta,koda qafafunta ma tafi ta'ammali da irin takalman nan da ake kira da half cover,dr bilkess kenan,mace mai aji,wadda ba iya maza kawai take tafiya da imaninsu ba,hatta 'yan uwanta mata takan burgesu qwarai,da yawa su buraci dama sune ita,ba tare da sunsan tsinin data taka ba kafin takai ga wannan bigiren da take kai.



        Babu kowa a falon,dama ta zaci haka,saboda yayi safiya da yawa,don haka ta shiga kitchen ta samu ruwan zafi a kitchen,ta zuba mishi kayan qamshi,sannan ta bude fridge ta dauki samosa fresh one guda uku ta soya,tana daga tsaye ta soma gutsira tana ci,don idan ta fita din ba kasafai take cin abinci a waje ba,har sai ta dawo gida.



       "Mamiiiii" taji an fada daga bayanta,ko bata juyawa ba tasan muryar amatu ce,ta waiwaya bayan ta gama wanke hannunta tana gogeshi da tissue tana dubanta,sanye da wani riga da wando pink,wanda yau tashin wurin data yi ya sanya tana gama wanka itama tayi mata ta shiryata,tace ne ta kwanta ta koma bacci abinta sai gashi ta sake biyota,tun daxun dama take nacin zata bita asibitin

"Ya kuma akayi?" Ta tambayeta tana tsareta da ido,saita langabe kai tana shirin sakin kuka

"Please mami,kinmin alqawari fa rannan....don Allah mami na rakaki don Allah" shuru ta danyi,sam batason fiya son zuwa dasu asibitin ba,wani irin farinjini yaran keda shi,wanda yawanci.idan taje dasu asibitin ma basa zama waje daya,daga wajen wannan sai wancan,shi yasa da wuya taje dasu din,saidai yanayin yadda amatun keta mata naci ya karyata,dole ta koma ta sauya mata kaya sannan suka fito tare suka fice.



         Suna isa kuwa ta soma jawo mata idanun jama'a fiye da da,wadansun sun santa dama kuma suna son magana da bilkisun babu dama,wasu kuma ganin farko ne,da haka ta samu ta janyeta zuwa office dinta don karta bata mata lokaci.



        Minti arba'in da wani abu ta gama shirin shiga surgery din,duk yadda dr adam yaso tabar amatu wajensa amma saita zame,ta hadata da wata nurse dinta mace,don ba zata iya barin mishi diyarta mace ba,duk da cewa bawai tana zarginsa bane,amma tarbiyya ba abar wasa bace,kuma sam bata taba wasa da tarbiyyar yaranta ko qanqani.



       Cikin nasara kamar kowanne lokaci ta aiwatar da duka surgery din,bayan ta fito ta daura alwala cikin office dinta tayi sallar nafila raka'a biyu don nuna godiyarta ga Allah kamar yadda ta saba a duk sanda ta gama aiki haka successfully.



       Bata jima da idarwa ba,amatu na gefanta tana wasa aka nemi izinin shigowa ta bayar,john ne,tunda ta ganshi tasan magana ce kan wani mara lafiyan,ta saki murmushi tana cewa

"Badai xaku barni na huta ba ko?" Shima martani ya mayar mata kana yace

"Naga kamar kin manta da patient din da kika ce idan sun iso a basu gado,kuma patient ce mai muhimmanci a wajenmu kamar yadda kika sani" baki tadan tabe kadan

"Wannan patient kuna ji da ita,ban manta ba,dole saina kammala komai kafin na ganta,yanzun haka ina dab da zuwa dakin,ba room 1 bane"

"Eh madam" ya amsa mata a ladabce,kai ta gyada yayin da shi kuma ya juya ya fice.



        Sai data gama komai sannan ta maida kayanta,ta nada mayafinta da kyau ya zauna mata ta koma neat kamar yadda ta shigo asibitin sannan ta kama hannun amatu suka fito.



       Dab da zata isa dakin wayarta ta dauki ruri,ta dakata tana duba mai kiran,nabila ce,qawa guda daya tilo aminiya datayi tsayin shekarun anan qasar brasil,wadda itama zuwau ce kamar ita,saidai Allah ya hada jininsu,ya saka qawance mai qarfi tsakaninsu

"Qawa kada dai ace ba zata kikamin kin dawo?" Inji bilkisu,daga can daya barin akayi dariya

"Kedai bari qawa,mamaki naso baki" daga haka suka soma hira wadda tadanja lokaci kafin suyi sallama,bilkisu ta aje wayar tana murmushi,a sannan ta lura da amatu bata wajen,tadan dudduba bata ganta ba,tasan wajen babu hanyar fita,tafi kyautata zaton ta shiga dakin da sukazo,don haka tayi gaba zuwa dakin,ta murda qofar ta bude kana ta tura kai ciki.



       Tun kafin ta gama shiga ta jiyo muryar amatun rai rai,a hankali idanunta suka sauka kansu,su biyu ne zaune gefan gadon mara lafiyas,amatu da yarinyat da duka duka alamu ke nuna ba zata wuce shekara  uku ba,sai nurse dinsu dake zaune gaban gadon saman kujera,riqe da cup da plate na abinci tana lallabar yarinyar ta karba,daga can wata kujerar kuma wata macace zaune tana fuskantarsu.



        Duk da bata da tabbacin musuluncin matasa lafiyanta amma hakan baya hanata yin sallama a duk inda ta shiga,yanzun ma sallamarta ita taja hankalinsu,anyi katari dukkaninsu musulmai ne,don haka suka amsa mata,ta qaraso dakin hannayenta zube cikin aljihun labcoat dinta,idanunta saman fuskar yarinyar tana qare mata kallo,a haka ta iso gaban gadon tana ci gaba da nazarin kyakkyawar fuskar yarinyar.



       "Kinga momy na....zatayi miki allura idan baki qarasa cinyewa ba....kuma ma na fasa qawancen dake idan bakici ba" cewar amatu tana karyar da wuya,da alamu ta damu sosai yarinyar taci abincin,kallon amatu bilkisu tayi,kafin ta maida dubanta ga nurse din dake tsaye bayanta kadan da farantan tana tambayarta meke faruwa

"Tunda suka zo taqi cin komai" hannu ta miqa mata

"Bani" ta amshi kwanukan,duk da cewa ba aikinta bane sai taja kujera ta zauna gaban gadon,cikin lokaci kadan abun mamaki yarinyar ta saki jiki da ita harta cinye abincin,abun daya bawa mutanen dakin mamaki,har amatu da bakinta ya kasa shuru,murna ta cikata na ganin yadda ta cinye abincin duka,itama matar dake zaune a can gefe wanda alamu ke nuna tare suka zo,ita ke jinyarta tace

"Lallai likita kinzo da farinjini,Allah ya qara basira" ta fada da harshen hausa,ba tare da tana da tabbacin bilkisun naji ba,don tunda ta shigo da yaran turanci dukkaninsu suke magana,sai data amsa mata da amin sannan tasan tana jin hausar,hakan kuwa yadan bata mamaki,don ta zaci wani jinsin yaren ce daban ba bahaushiya ba,duba da yanayin kalar fatarta na daban,da kuma qira takyau da Allah ya bata.



       "Wanne likita ne yasoma dubata?" Bilkisu ta tambaya tana daukan file guda biyu na yarinyar dake gaban gadon,wanda ke dauke da qunshin dukkanin bayanan ciwon nata,daga dukkan asibitocin da suka taba dubata,nurse din ta bata sunan likitan,saita soma buda file din tana karanta kowanne rubutu dake jikin kowacce takarda tana daga tsaye.



       Yanayin yadda taga bayanan ciwon yayi tasiri jikin yarinyar ya bata mamaki qwarai,jikinta yayi sanyi,don da alama ya tabata da yawa,saita soma laluben kujera,tana zama kai lokaci daya tana daga kanta ta dubi amatu data damesu da karadi,ta sanya patient din itama bakinta ya bude ta biye mata sunata zuba surutu,cikin harshen turanci ta mata umarni ta rage sautinta ta barta ta duba file din hannunta,da alama itama yarinyar tana ji,don sai taga itama ta qara nutsuwa ta rage hayaniya,bilkisu ta bita da kallo,tana mamakin yadda ta saki jiki sosai da amatu,kamar sun jima da sabawa,sai taji dadi,don haka zai taimaka wajen warkewa da sake gano wasu abubuwan dake damunta da suka gaza ganowa.



      A qalla ta dauki mintuna ashirin kyawawa tana bitar files din kafin ta rufe tana sakin nannauyar ajiyar zuciya,a zahirin gaskiya tabata don yi mata aiki yanzu akwai babban hadari,tana da buqatar treatment sosai kafin akai ga batun aiki,don haka ta dubi matar

"Ina iyayenta?" Ta tambayeta tana kafeta da idanu

"Basu qaraso ba tukunna" cikin mamaki ta maimaita

"Basu qaraso ba kaman yaya?,kina nufin basu qasarma gaba daya?,ba tare kuka zo dasu ba?" Kai ta jinjina mata

"Mamarta dai na hanya,cikin satin xata iso"

"Tana hanya?" Ta maimaita tambayar cike da mamaki,wannan wanne irin careless ne?,wadanne irin iyaye ne haka?,yarsu ta cikinsu amma a rasa mai tattaki ya dafa mata baya neman magani?,saita maida dubanta ga yarinyar,take taji tausayinta mai girma ya kamata,verry innocent,bata san damuwa da matsalolin rayuwa ba banda wannan ciwon daya shigeta,hira take sosai da amatu kamar wadda suka jima ko suka saba,tana ta qyaqyata dariya,har hakan yaso baiwa ita kanta matar mamaki.



       Dauke kanta bilkisu tayi tana jin wani abu bayan tausayi game da yarinyar me kama da qauna,ta kira dukka nurses din da tasan suna da alhaki wajen kula da yarinyar ta gana dasu,ta nuna musu duk abinda ya kamata ace sun sani,bata bar dakin ba sai da ta soma bata kulawa,tanayi tana jan yarinyar itama da wasa kamar yadda taga amatun tanayi,ta sake mata sosai kuwa itama kamar yadda ta sake da amatu.



       Saida sukazo tafiya ta tubure saidai su tafi tare,matar tayi lallashin duniya amma ta kafe,hakanan bilkisu ta dinga qoqarin mata dabara nan ma taqi,itama amatun ranta a bace da alama batason su tafi,daga qarshe dole bilkisun taja kujera ta zauna,sukaci gaba da wasa har sanda bacci ya dauketa sannan suka samu damar tafiya,matar nata yiwa bilkisu godiya kan yadda ta nuna tsantsar kulawa da qauna.



      Ko a hanya hirarta amatun ta dinga mata kamar tasanta,bilkisun na jinta,yayin data lula duniyar tunani,tausayin yarinyar da qaunarta take sosai,da alama bata rasa dukkan gata ba,saidai kamar ta rasa kulawa musamman ta uwa,duba da yadda taketa qanqame bilkisun tana kiranta da sunan momy,har suka je gida zancan amatu kenan,haka ta zauna tayita bawa su abdulrahman labarin.



       A daren kasa bacci bilkisu tayi,tanata tunani tare da laluben hanyoyin da zasu bullowa ciwon bayan ta gama amsar treatment na sati guda kamar yadda ta tsara ko sati biyu,bata samu ta runtsa ba sai can tsakiyar dare.



       Hakan ya saka washegari koda ta shirya fita aiki idanunta akwai bacci a ciki bai wani isheta ba,saiga amatu itama ta farka tangaran sanda take fitowa daga wanka,tana mutstsuka idanunta tana kallon mamin nata

"Mami....." Saita langabe kai,bilkisu tadan bata rai

"Meye?"

"Mami yauma don Allah" sake bata fuska tayi

"Ba inda zakije,ki zauna a gida hakanan" daga haka taci gaba da shiryawarta,bata ankara ba taji ta sakar mata kuka,ita suhaima takeson zuwa ta gani,saita saki baki galala tana kallonta,sannan ta soma fada

"Wanne irin sakarcin banza ne da wofi wannan amatu?,da can dake nake zuwa?,kodon kinga kun samu hutu shine zaki tsiri bina?" Daidai lokacin da ummi zuhriyya tayi knocking qofar dakin ta shigo

"Yaya....yaya,waye ya tabamin mutuniyata?" Dauke kai bilkisu tayi daga wajen amatun tagayawa anty zuhriyya abinda ke faruwar

"Yaushe rabon da su biki banda abinki,shirya qawata kuje kinji" tsalle ta daka ta shige bandaki,ta samu abinda takeso,dama already ta iya wanka abinta sosai,murmushi anty zuhriyya tayi tana duban bikisu

"Da tayi zuwa uku zata gaji da kanta,yanzun ma rashin sabo ne"

"Ummi kawai dai kina daure mata qarqashine saboda 'yar gaban goshinki ce bata laifi,idan hakane shima abdulrahman yace zashi mana" baki ta kyabe

"Ke rabani da wannan sarkin miskilancin tsiyar,duk randa yaji zashin ya magantu da bakinsa,amma nidai tunda yarinyata nason zuwa banga abinda xaisa a hanata zuwan ba" murmushi bilkisu tayi,bata da sauran ta cewa,daga haka suka shiga maganar data shigo da ita.



        Bata lura amatu ta debo tarin choculets ba da sauran tarkacen su biscuit saida sukayi nisa,ta dubeta

"Wannan fa?"

"Suhaima zan kaiwa....Allah sarki tana ta cewa daddynta takeson gani,tafi sonshi,shi yake siya mata ya bude mata tasha" shuru bilkisun tayi,har yanzu tana mamakin abinda zai hana iyaye kasancewa da diyarsu,anya ma kuwa iyayenta basu rasu ba?,ba riqonta ake ba?,gaskiya tafi tunanin hakan,tausayin suhaiman ya sake shiga ranta sosai da raya hakan da tayi.



         Cikin kwana biyu rak suka wani irin sabawa da amatun,kullum da safe kafin bilkisun ta tashi ma ita ta rigata tashi ta shirya ta zauna tana jiranta,tun tana dojewa ba zata je da ita ba harta haqura ta qyaleta,saiga abdulrahman shima yabi sahun 'yan zuwa asibiti.



       Ranar farko da yaje zama yayi abinshi daga nesa yanata kallonsu,kasancewarsa miskili bamai son surutu ba,duk hirar da suke nashi ido,gadon ya zama kamar wajen jinyar suhaima ne da amatu bawai na suhaima kadai ba,kwana biyar amma kamar sun shekara tare,har ya zamana bilkisun kan qara lokacin tashinta akan lokacin tashinta daga aiki na ainihi,john har tsokanarta yakanyi,yakance patient din da ake jama rai yanzu ta zama best a cikin patients dinki madam,dariya kawai takanyi,itama batasan ya akayi yarinyar ta shiga ranta ba,wala'alla sabon daya shiga tsakaninsu ne da yaranta ya jawo hakan.



     ******    *****    ******



     Tsaye yake gaban ammin yana fuskantarta,sanye cikin wasu hadaddun suit masu bala'in kyau da tsada,wanda suka sake fidda kyakkyawar sura da cikar zatin da Allah ya huwace masa

"Zan wuce ammi,hankalina ya gaza kwanciya,gwara na wuce kawai,sodangin ta biyo ni zuwa jibi" sosai take sake danne bacin ranta kan lamarin safwa,ta fuskanci kwata kwata batasan abinda ya kamata ba,don  gaba gadi taketa harkokinta kamar ba wani abu tayi ba,ko jiya da fulanin ta kira mom su gaisa ko hakan zai zame musu tuni game da suhaima safwan harda amsar wayar su gaisa tana sakalcin nan nata,ko cewa akayi kasancewarka d'a guda wajen iyayenka hauka ne?,ita kuma mom din harda cewa

"Wallahi kin ganni inata fama da ita ta tafi,wai sai zuwaira ta dawo su tafi tare,ita batasan ya ake treating mara lpy ba,sai aukin kiran yarinyar a waya ta mata hira,na rasa wanne irin sakarci ne ke damun safwa haka" takaici ya hana fulani cewa komai,sai kawai tace

"Allah ya kyauta".



      "Jibin zamu taho tare ne in sha Allah,kayi mata sannu da kyau kafin mu iso" daga haka sukayi sallama ya fito.



       Sassan mai martaba aka masa iso,ya sameshi zaune tare da wasu hakimai,wanda da alama sun gama tattaunawar data hadasu a wajen,don wasu har sun miqe ma,cikin girmamawa ya isa gabansu ya duqa ya gaidasu,kowanne ya amsa cikin jin dadi da kulawa,saida suka fice sa'annan mai martaba ya maida hankalinsa kan azeez,yadan zuba mishi idanu yana kallonshi,shi kansa yadda yakanga sauyi tattare da dan nashi yana sashi a tunani,amma sai yake zaton girma ne da kuma tsabar kasuwanci babu hutu daya sanya a gabanshi

"Dan kasuwa" maimartaba ya dan tsokaneshi,Kasancewarsa mutum mai barkwanci ga jama'a,murmushi ua danyi yana dan saukar da kanshi qasa,yana qaunar maimartana qwarai kamar yadda yake qaunar amminsa,saidai akwai banbamcin halaye,wani sassauqan mutum mai sauqin hali da ra'ayi,mai saurin fahimta da bada uzuri,wanda bai dauki rayuwa da girma ko fadi ba

"Allah ya qara maka lafiya da nisan kwana" ya amsa mishi cikin ladabi

"Lafiyar dai amin,amma nisan kwana iya abinda muka hadiyo shi zamuyi mu kauce muba wasu waje" ya amsa mishi kamar yadda yakan amsa mishin lokaci lokaci,kai azeez ya gyada kawai sannan yace

"Zan wuce wajen amaryarka brasil" fuskar mai martaba ta sauya 

"Idanu dama kawai na zuba maka kaida uwarta ku gama dukka sakarcinku,da ita kanta aishan data zuba muku idanu,bansan rashin hankalin da kuka tafka ba sai a jiya" nan yahau mishi fadan barin suhaima da masu kula da ita kawai zuwa neman lafiya,fada ya dinga yi sosai,kamar yadda ya yuwa fulanin a jiya iya son ranshi,mutum ne shi mai son jikokinsa da basu kulawa,don haka azeez baiyi mamaki ba,yasan zaiyi fiye da hakan ma,ko baya ga haka ma ya tsani yaga an sarayar da haqqin wani ko wanene shi,kanshi a qasa ya bashi haquri sosai,sa'annan yayi masa sallama,bai barshi ya fita ba sai daya shiga ciki da kanshi,ya bada saqon kilishi mai yawa yace akaiwa amaryarsa,yasan yarinyar tana sonshi.



       Sosai ya shiga zurfin tunani a mota,wannan karon yanajin indai safwa ba zata iya zama jarumar uwa kamar kowacce uwa ba,to ba shakka zaya dauke suhaima ne ya dinga tafiya da ita duk inda zashi,ko kuma ya karbi sodangi taci gaba da zama da ita a madadin uwarta tunda ita batasan meye ma'anar sunan uwa ba.



       Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi yana ambaton sunan Allah sanda jirginsu ya daga daga qasa zuwa sararin subhana,hakanan yakejin wasu baqin abubuwa cikin gangar jikinsa da zuciyarsa,wala'alla doki dason ganin diyar tasa ne ya sanya haka,ya sake sakin ajiyar zuciya yana lumshe idanu,qaguwarsa dason ganin ya sauka a qasar brasil na sake daduwa,ya shiga irgen awanni ko mintunan da zasu sadashi da qasar.




*to me karatu?,shin ya zata kaya ne?,ku biyoni muje zuwa*ðŸƒðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸Ã¢Å“ˆï¸

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 52


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



        Duk wani nau'in abinda yasan suhaiman tana so sai daya siya mata kafin ya qarasa asibitin,a sannan babu kowa cikin dakin,daga ita sai mama rahama,wadda keta faman lallashinta kan ta karbi abinci taci,fir taqi yarda taci din,sai fushi da take,ta hade fuskarta tsam,sakamakon rashin zuwansu amatu yau asibitin gaba daya,wanda hakan ya faru ne saboda ba ranar aikin bilkisu bane,ranar hutu ne.



       Ã†˜ofar sukaji an turo,sannan lallausar muryarsa da yawancin lokutta take cike da sanyi da taushi tayi sallama cikin dakin,ya shigo idanunshi na akan suhaiman.



       Kallo daya zakayi mata ya gaya maka zallar farincikin da tayi da ganin mahaifin nata,badon qarin ruwa dake hannunta ba,badon kuma riqeta da mama rahama tayi ba da tuni ta diro daga saman gadon zuwa wajenshi,hakan daya fuskanta shima saiya qara azama ya qaraso gareta,ya rungumeta tsam a jikinsa yana jin tausayinta,saidai kuma yaji dadi a yanayin daya ganta,wanda ya nuna mishi tana sakun kulawa dai dai gwargwado,don gashinan ta soma murmurewa,akwai alamun raguwar ciwon tattare da ita.



       Sai da suka gama daukin ganin juna,ya baje mata dukkan wani abu da za'a iya ci saman gadon tahau hidimarta sannan mama rahama data koma can sashe daya na dakin ta zauna ta gaisheshi cikin ladabi,ya amsa mata sa'annan ya soma mata tambayoyi game da yadda ake kula da suhaiman.



       Amsar data bashi ta masa dadi sosai,sai yaji ya qara nutsuwa da asitin da kuma likitar kanta dake dubata,mama rahama tayi murmushi

"Yanzun ma fushi take saboda likitar batazo ba yau tana hutu,bataga amatu diyar matar ba qawarta,taqi taci abinci yallabai" waiwayawa yayi ya dubi suhaima,duk sai ta langwabe,ya miqa hannu ya amshi abincin wajen mama rahaman,ya dubi suhaima ya tsatssareta da idanu sa'an nan yace

"Oya.....gyara ki karbi abinci" babu musu ta aje duk abin hannunta ta tattara hankalinta ga abincin,ya diba ya soma bata a baki.



         Daga bangaren bilkisu kuwa ranar ta tashi kamar sauran ranakun hutu a wajenta,takan sake a gida saboda tasan bata da aiki,hakanan ba kasafai ya fiya fita ba,to yau dinma hakane,sunata sabgoginsu da yaran.



        Saidai babu jimawa nabila tayi kiranta,wanda kiran nata yasa dole ta fita kenan,mamarta bata jin dadi,tasan kuwa idan bata yakice taje cikin ranakun hutunta ba,ba zata samu fitar ba,don babu inda take sake fita yawanci idan ta dawo daga aiki to tana gida,a yadda suke da nabila kuma bai kamata ba,shaquwarsu tafi gaban hakan,don hakan,bayan ta gama duk wasu ayyukan gida da takewa ummi duk lokuttan da take free,saita shiga bandaki tayi wanka,kana ta tsaya gaban mudubinta tayi shiri mai kyau cikin kayan da duka amsheta matuqa,suka fidda ainihin gayunta da ya riga yabi jikinta ya zame mata jiki.



       Tun tana shiryawa ta lura amatu ta kasa sukuni,sarai tasan meke damunta,so take tace zata bita,hakan yasanya ta hade ranta itama tsam babu wasa,harta gama shiryawa ta yiwa ummi sallama ta fice.



        Ta samu jikin mamar nata da sauqi,ta zauna cikinsu suka taba hira,bata kashe awa daya ba ta yiwa nabilan sallama tace zata wuce,amma koda zuwa jibi idan ta tashi daga aiki zata sake biyowa taga jikin nata.



        A hanya harta dauki hanyar gida sai kuma suhaima ta fado mata a rai,hakanan taji tana da sha'awar shiga asibitin kodan ta dubata koda ita kadai ce cikin marasa lafiyanta,don haka saita sauya alakar motarta zuwa asibitin,cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa dr adam baya nan.



       Tana tsaka da parking wayarta ta dauki ruri,number din assadiq ce,bata daga ba sai daga gama daidaita parking din nata sannan ta sanya hannu ta dauka tana dab da tsinkewa tana yin sallama.



        Idanunsa ya lumshe,yana jin sautin muryarta har tsakiyar zuciyarsa kana ya budesu yana amsa mata sallamar

"Nayi miki zuwan ba zata,kuma saina daki gurbi bakyanan" cikin mamakin yadda akayi ya sami adress dinta tace

"Kana nufin gidanmu?" Kai ya gyada

"Yes,kina mamaki ne?"

kanta ta mirgina,murmushi na qwace mata,wani irin qwaqwqwafi ne da assadiq haka?,anya shi din ba lauya bane ko dan jarida ba?,kafin tace komai ya sake magana

"Ayimin afuwa,so nayi na mamayeki,sai kuma gashi hakan bai samu ba....akwai wani batu mai muhimmanci da nakeso mu tattauna ne akai,idan babu damuwa a sake bani lokaci sai nazo mu gana,amma alfarma nake nema,kar a lulani da yawa zuwa wasu kwanaki,kinga nidin matafiyine kuma baqo,akan hanya nake,kwanaki kadan suka ragemin na tattara nabar muku qasarku" murmushi ya sake kubce mata saboda yadda yayi maganar kamar me neman agaji,idan ba gobe ko jibi ba bata da wani isashen lokaci

"Qasarsu dai,mu tamu qasar nigeria take....babu damuwa,kana iya samuna jibi a gidan in sha Allahu"

"Godiya nake qwarai da gaske" daga haka sukayi sallama,ta kashe wayar tana fitowa daga motar,ta kulleta kana ta nufi ainihin cikin ginin asibitin,cikin takunta dake nuna zallar aji kamun kai da isa cikakkiyar mace.



        Bata nufi office dinta ba don bata tunanin ma zata shiga tunda ba aiki ne ya kawota ba,kai tsaye ta doshi sashen da dakin da suhaiman take.



       Hakanan taji wani mummunan faduwar gaba sanda ta dora hannunta saman qofar da niyyar budewa,sai tsaya cak tana mamakin yadda bugun zuciyarta ya qara gudu.



       ,taja numfashi sosai cikin hunhunta ta sauke nannuyar ajiyar zuciya,ta bude idanunta dake lumshe kana ta tura qofar dakin a hankali,tamkar barawon dake shirin shiga wani gida yin sata,inda bashi da buqatar a kamashi.



        Kadan qofar ta budu,amma tana iya hango wani sashe daga dakin,a hankali ta soma zagayawa da idanunta cikin dakin,mama rahama dake zaune gefe daya idanunta ga bango,da alama plasma din dake kafe take aiki ta tattarawa hankalinta,sai suhaima dake zaune gefan gado ta zuro qafafunta qasa,tana tauna a hankali da alama batason cin duk abinda take ci din.



        A hankali idanun nata suka sauka a kanshi,kyakkyawar fuskarshin nan babu yabi ba fallasa,ya tsare diyar tashi da kyawawan idanunshi masu cike da wani irin sirri da kwarjini na musamman,fuskarshi babu yabo ba fallasa,saidai ga duk wanda ya sanshi zai iya cewa a hakan a sake fuskarshi take.



       Dubanshi tayi na sakanni biyar tak taji bugun zuciyarta ya sake dawowa,idan idanunta suna gane mata dai dai,wannan business tycon dinne wanda hotunansa da labarinsa ya zagaye ko wanne lungu da saqo na duniya,saidai a yau tana ganin abu mafi mamaki wanda bata taba kula dashi ba tsahon ganin da takewa hotunanshi.



      Kamanni na zahiri muraran,kamannin yaranta 'yan biyunta saman fuskarshi,tamkar kaki yayi ya tofar,wani mugun bugun zuciya data ji fiye da wanda takeji ya sanyata sakin qofar ta koma da baya,ba tare data shirya ba ta tsinci kanta ta doshi qofar office dinta,ta bude kana ta shige zuwa ciki tana jinta cikin wani yanayi da bata tantance wanne iri bane.



       "Wanne irin abu kike haka bilkisu?,me yake damunki haka?,daga ganin mutum saiki birkicen?,wala'alla ma babu wata kama da suke,idanuwanki ke nuna miki haka,meye hadinsu da zasuyi kama?" Kanta ta yiwa fada sosai,ita kanta sai taji haushin kanta da kanta,ta miqe ta tsaya gaban dan madaidaicin madubin dake office din ta gyara rollig dinta ya zauna sosai,kana ta dauki jakarta ta fice daga office din bayan ta rufeshi,ta sake durfafar dakin karo na biyu.



       A hankali ta sake turawa kamar dazun,saidai a yanzu mama rahama ce kawai da suhaiman zaune,tayi sallama a nutse cikin sassanyar muryarta,cikin zumudi suhaima ke kallonta,bakinta har kunne

"Oyoyo momi...ina amatu na?" Murmushi tayi cikin tsantsar qarfin hali,saboda qamshin turaren da takeji cikin dakin,qamshine daya kama qwaqwalwa da zuciya gaba daya,qamshine daya zauna radama tunaninta tsahon shekaru bakwai,irin qamshin data sani jikin mutum daya,kuma tsahon shekarun bata sake jin qamshin jikin wani mutum na daban ba bayan shi,sai a yau daidai wannan lokacin,sa'an nan cikin dakin asibitin,wanda bata ha kowa a dakin ba face suhaima da mama rahama,don haka ta maida hankalinta kan suhaiman tana cire dukkan wani tunani daya bijiro mata.



       Cikin kulawa take duddubata bayan ta tabbatar da cewa komai yana tafiya dai dai,daidai lokacin data gama dubatan ta saqala jakarta wayarta dake riqe a daya hannun nata ta dauki tsuwwa,data duba sai taga sunan anty zuhriyya,babu jinkiri ta daga,magana sukayi ta mintuna biyu sannan ta kashe ta dubi mama rahama

"Zan wuce mama,sai jibi idan Allah ya kaimu,an kirani daga gida ne nayi baqi"

"Babu komai likita,kedai sannunki da qoqari" qarasawa tayi gaban gadon suhaima,wadda tunda taga babu amatu,sannan bilkisun na maganar tafiya tayi kicin kicin,murmushi tayi tana shafa kanta

"Naso na dade kinji baby suhaima,amma jibi da wurwuri zanzo kinji"

"Amatu zatazo?" Sai ta danyi jim,batason mata alqawari kuma bata cika ba,to amma yarinyar ta damu dasu amatun da yawa,zatayi qoqari a kawosu,idan hakan bai samu ba jibi zata qoqarta taho mata da ita

"Idan na samu dama zaki gansu,idan ban samu ba kiyi haquri kinji diyata,jibi in sha Allahu xanzo miki da ita" saita gyada kai a sanyaye,har hakan yasa bilkisun taji babu dadi,yarinyar ta kafeta da ido tana ci gaba da kallonta,kana a hankali ta bude baki tace

"Kice to ina gaisheta" kaita jinjina tana fidda murmushin zallar wayo irin na suhaiman,kamarma wayonta yafi shekarunta yawa

"Zataji" ta sunkuya tayi kissing din goshinta.



       Dai dai lokacin daya tura qofar toilet din ya fito,hannunsa riqe da handekherchief guda shida na suhaima daya tsaya wankewa tun dazun,wanda mama rahama tayi tayi ya bari ta wanke amma yace ta barshi zaiyi da kansa.



       Yaga sanda aka gama kissing suhaima aka juya,yaga gefen fuskar matar saidai bai samu ganin fuskar gaba daya ba,wani mummunan faduwar gaba yaji ta ziyarceshi wanda baisan dalili ba,kamar wanda aka manne idanunshi a kanta haka ya zuba ma bayanta idanu saboda bashi da ikon ganin fuskarta,harta fice daga dakin cikin nutsatstsen takunta.



      Hakanan cikin jikinsa yakejin kamar yasan halittar,kamar ya taba rayuwa da ita waje daya,kamar ya taba sanin wani abu nata.



        Sam baisan ya bita da kallo ba,hakanan baisan yaci gaba da kallon hanyar data bi ta wuce ba duk data bacewa ganinsa ba,saida mama rahama tayi gyaran murya,wadda dukka nauyi ya cikata ganin yadda yakebin hanyar da kallo,hakanan suhaima nata masa magana amma sai baijin abinda take fada.



        Sashen da mama rahama take ya kalla,kanta na duban qasa tace

"Itace likitar suhaima,itace wadda take magana akanta daxun ita da yaranta take fushi saboda rashin xuwansu" kai kawai ya gyada,sannan ya taka a hankali zuwa gefan gadon suhaima yazauna,yana jin wani mutuwar jiki da kasala,hakanan giftawarta ta kasa barin idanunsa,saiya sanya hannun suhaima cikin nashi yana dubanta,tare da tambayarta me take cewa?.



        Washegarin bata samu kaisu ba,hakan ya sanya tayi aniyar tafiya da amatun gobe idan Allah ya kaimu.


*****    ******   ******  *****


        

            Tunda ta idar da sallar asuba take saman abun sallarta,hakanan baccin da takan samu ta koma ya qauracewa idanunta,sabanin daa da takan koma ta rintsa koda na minti talatinne zuwa awa daya kafin ta shirya,ya danganta da yanayin sammakon da zatayi,sabanin daa yau din ko kadan bata jin barcin,sai azabar mutuwar jiki gami da kasala da suka lullubeta,lokaci lokaci takanji fargaba da faduwar gaba,hakan ya sanyata ta qara yawa da tsahon azkar din da takanyi duk safiya.



      Karfe bakwai ta tashi amatu ta mata wanka sannan itama ta shiga tayi nata wankan,bayan ta fito ta shiryasu duka ita da amatun,dukkaninsu cikin african abaya wadda aka musu dinkin iri daya sak komai da komai,tun wani zuwa da anty zuhriyya tayi nigeria tayi musu tsarabarta dukka matan har ita kanta.



      A falo suka samu anty zuhriyya abeed ya tadata yunwa yakeji,ta dubesu tana murmushi

"Yau wace rana ba'a mana gori ba bamu roqa ba za'a asibiti damu" murmushi bilkisu tayi don har yanzu bata jinta dai dai 

"Qawa tayi patient a asibitin,su suka uzzuramin zanje da ita na huta da tambayata amatu da takeyi"

"Ai ya kamata.....amma fa ba qaramin kyau kukayi ba,ni sai naga abayar nan tafi kyau da jikinku,kamar yaya da qanwarta" murmushi bilkisu ta sakeyi har haqoranta na bayyana

"Kai ummi...,ai dama tana da kyau baki taba kula bane,bare wannan atamfar da suka ratsa mata ta dace da jikin abayar sosai"

"Gaskiya kam ai sun iya dinkata,ba kamar wadanda na saba gani,inajin idan muka koma saina sake siyan wasu"

"Nima suna burgeni,zan qara wasu kodon fita aiki ma" suna wannan hirar suna karyawa ita da amatun,duk daba wani abun kari na azo a gani bane,saboda dama ba kasafai take jiran abincin break ba na duka gida duk randa zata aiki,musamman idan babu 'yan makaranta ita kadai zatayi fitar sassafe.



        Wayarta ce ta dauki tsuwwa,ta janyo 'yar mitsitsiyar jakar hannunta me kyau ta fiddo wayar tana duba me kiran,sai taga daga asibiti ne,cikin yana dake nuna gaggawa ta gaske akace da ita

"Dr bilkees....kiyi hanzarin isowa asibiti,akwai matsala mai girma" maganar ta tada mata hankali sosai,tasan tunda aka gaya mata hakan akwai matsalar,don haka ta dire nata cup din ba tare data ida shanyewa ba,ta azalzali amatu ta wuce su tafi.



        Gudu tayi sosai ba irin wanda ta saba ba,duk sanda take sake kusantar asibitin gabanta na qara faduwa,har gumi takejin yana tsatstsafowa a goshinta,idan matsala ce ya saba ganinta kala kala,amma batasan me yasa yau din take a birkice ba hankalinta a tashe fiye da yadda ta saba.



      Tana aje motar a muhallin ajiyar motoci ta fito ba tare da bata lok

Uaci ba,ta kulle motar kana ta soma takawa zuwa cikin asibitin gabanta na dukan uku uku,sam batau lura da surutun da amatu keta faman zuba mata,data gajima saita dubeta cikin daurewar fuska

"Kimin shuru amatu,tun bansa an maidaki gida ba yanzun nan" gum tayi da bakin nata kuwa,saboda tasan kadan daga aikin ammin tata.



      Tun daga nesa take iya hango dakin da suhaima ke kwance,kamar akwai mutanr dai daiku tsaye qofar dakin,sabanin da da bazaka samu kowa ba,data sake wasu taku zuwa wajen saitake jin sauti kamar na sheshsheqar kuka duk da batasan muryar wace ba hakanan batasan wace me kukan ba,amma hakan yayi matuqar fadar mata da gaba,sa'annan ya sake sanyata qara saurinta ta durfafi dakin kai tsaye saboda wani abu da zuciyarta ta soma raya mata,harta saki hannun amatu dake cikin nata ba tare data sani ba,burinta shine kawai ta isa dakin taga abinda yake faruwa.

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 53

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070


      Babu inda idanunta ke kalla a dakin sai gadon da suhaima ke kwance,a miqe take sosai ba kamar yadda ta saba zuwa ta taddata yawancin lokuta tana zaune suna hira da wani ba,likitoci da nurses shida ta taras a kanta,saidai dukkaninsu suna tsaye ne,akwai alamun alhini saman fuskarsu.



      Saita kutsa tsakiyarsu ba tare da tace da kowa komai ba,ta isa ga suhaima da idanunta na ke a rufe,jikinta ne gaba daya taji ya hau rawa,guri daya ta taba a jikinta gaba daya taji wani rauni yazo mata,ba wani ba wata yarinyar ta rasu,ta koma ga mahaliccinta,saitaji tana son daina gane komai,ba zata iya ci gaba da tsaiwa ba saboda yadda taji qafafunta na rawa,saita samu jikin bango ya jingina kawai tana son daidaita numfashinta,sai a sannan ta lura da wani mutum fuskarsa kife jikin gadon saitin kan suhaimar,kamar wanda bai dakin baisan me akeyi ba.



       Idanunta ta runtse tana jiyo sautin koke koke daga wajen dakin,wanda ta tabbatar da cewa wasu ne da suka jibanci yarinyar,batasan ya zata iya buda baki ba tace musu ta mutu,ita kadai tasan me takeji a zuciyarta,sosai qirjinta yake suya,tana jin tunda ta kama aikinta bata taba mara lafiyar data shiga zuciyarta ba kamar suhaima,bata taba jin qaunar patient dinta ba kamar yadda taji tana son yarinyar sosai har cikin zuciyarta,amma sarkin dake da iko da kowa ya amshi abarsa,saita soma jan qafa ta durfafi qofar fita daga dakin.



        Suna nan tsaitsaye kamar yadda ta barsu,saidai bata iya gane fuskar kowa a ciki saboda idanunta cike suke taf da qwalla,riqeta taji anyi

"Likita ke ake jira....bata mutu ba ko?" Dubanta ta maida kan matar dake riqe da ita tana kuka,kuma ita ta jefa mata tambayar

"Saidai muyi haquri,Allahnmu yafimu sonta" abinda ta iya gaya mata kenan matar ta zame a wajen tana sake fashewa da kuka,tabbas da zata iya data tsaya ta bata baki,saidai itama tata zuciyar cike take fak da rauni da kuma alhini,don haka ta wuce zuwa office dinta.



        Dai dai lokacin da mama sodangi dake tsaye gefe guda tana matse hawaye tayi toxali da ita sanda take wucewa zuwa office din nata,daurewa kanta yayi,ta shi kokwanton bilkisu ce koba ita bace?,idan itace ya akayi tazo nan?,yaushe ta zama likita?,to amma bilkisu batakai cikar wannan ba,batakai wayewar wannan ba,bata kai gatan wannan ba......saidai kuma batajin akwai lokacin da xaixo ta kasa gane bilkisun,yarinyar da kullum take kwana da ita ta kuma tashi da ita,yarinyar da har yau ta kasa barin kwanyarta,ta kasa mancewa da ita,tausayinta yaqi raguwa daga ranta bare ta manta da ita,amma ga akayi tazo nan?.



        Tunaninta yazo dai dai dana afnan,wadda tunda ta fito ta zuba mata idanu,duk da cewa tana cikin alhinin rasuwar yarinyar,amma sai zuciyarta ke gaya mata classmate dinta ce,qawarta ce kuma abokiyar fadanta,wato bilkisu bilyamin,amma ya akayi bilkisun ta zama likita?,bayan tafi kowa sanin auren dole akayi mata,auren dolen da yayi silar tsigeta daga karatun da tafiso fiye da komai,ya akayi ta tsinci kanta a brasil bayan tasan cewa basu da qarfin da zata iya zuwa wannan qasar?,anya ko bilkisu ce?,amma ta yaya zata mantata,bayan kullum saita tunata,kullum da tausayinta take kwana take tashi,da kuma burin son sanin ina take?,ya rayuwa ta kaya mata?,indai ko bilkisu ce to zataso tabbatar da hakan.



         Tana isa office dinta ta zare rolling din kanta ta zauna saman kujerar hutawa dake office din,dafe da hannayenta guda biyu ta saki wani irin kuka,hakanan mutuwar ke ci mata rai,tana tuno yarinyar a sanda take raye,tana tuna hirarrakinsu da amatu,zancanta daya biyu abbinta,ba kasafai take maganar mahaifiyarta ba kamar mahaifinta,bata tsammanin kuma duk yadda yarinyar ta damu da iyayen nata sunzo sun ganta har ta koma ga Allah,ranta na mata suya idan ta tuna yadda tazo jiyya qasar babu dumin uwa ko uba a tare da ita,duk da cewa a sannan take da buqatarsu cikin rayuwarta fiye da kowanne lokaci,tunda duka duka shekarunta shekarune qanana qwarai,sosai tayi kuka wanda ta jima batayi irinsa ba,sai mutuwar ta tada mata tabon rasuwar mahaifiyarta.



        Tunda ya kifa kanshi ko sau daya bai dago ba,shi ba qaramin yaro bane abinda tayi a gabanshi kadai ya tabbatar masa tun daxun suhaiman ta tafi,jarumi ne na gaske a zuci da fili,ganin kukansa ba kowanne mutum bane ya taba katari dashi ba,uwa uba kuma ya tabbatar hawayensa zai zama silar rasa jarumtar mutane da yawa,hakan ya sanya ya zabi kasancewa a haka har zuwa lokacin da yaji an taba kafadarsa.



      Abdulrashid ne tsaye a kansa,ya daga kai ya dubeshi da idanunsa da suka kada sukayi jaa sosai,abdulrashid din yadan matsa kafadarsa alamun lallashi,saiya dauke idanunsa ya maida ga gawar suhaima dake lullube.



     Addu'a yayi mata sosai wadda tadan saukar da nutsuwa a zuciyar yarima,kana ya juya ya fice ya sake barin azeez dake zaune a wajen,yana iya jiyo muryoyin 'yan uwanshi daga waje,ciki harda sautin kukan safwa wadda aketa baiwa baki.



        Tsahon wasu mintuna abdulrashid ya sake dawowa,still hannunshi saman kafadar azeez,muryarshi a tausashe yace

"Sunce mahaifi ko mahaifiya ake baiwa certificate of death....likitar kuma ita ke bayarwa,so saidai dana bincika likitar ta fita,saidai xuwa gobe idan Allah ya kaimu,sun rubuta duk wata takarda,ya kamata mu wuce da ita gida,idan anan za'a binneta to,idan ma saimun koma gidane ya kamata asan abunyi" kai kawai azeez ya iya gyadawa,ya miqe cikin qwararawa kanshi gwiwa ya isa inda gawar suhaima take.



      Duk da nauyi irin na gawa haka ya dagata ya aza a kafadarshi,ba yadda abdulrashid baiyi ya ajeta a samo abun dauka su dauketa ba amma yaqi ya wuce gaba.



       Fitowarsa ta sake rura koke koken da sukeyi,hakanan suka dunguma gaba daya suka wuce zuwa harabar asibitin don su wuce gida a motocin hayar qasar.



      Fulani ce qarshe wadda take riqe da safwa tunda ta soma kuka,bata saketa ba kuma sai a yanzun data qara sauri tabi bayan azeez din,ita kanta cike take da alhini sosai,zuciyarta sam babu dadi,hakanan idanunta sun dan tasa saboda kukan datayi na rasuwar yarinyar.



     Tayi nisa a tunani taji an bugi qafafunta,ta dawo da hankalinta da sauri gabanta taba furta

"Subha....." Saidai batakai ga qarasa maganar tata ba ta tsaya saman harshenta,sakamakon ganin da idanunta suka mata na yarinyar da tunu ta miqe ta kwasa da gudu abinta cike da quruciya tayi cikin asibitin abinta,da alama babu abinda ya shalleta da bugewar da tayi dama wanda ta buge din.



      Tamkar idanunta zasu fado haka ta bita da kallo,zuciyarta na wani irin bugawa,tunda take bata taba ganin kama ta zahiri ba irin yau,bata taba ganin,to amma shin idanunta ne da suka soma samun damuwa ko kuwa gaskene?,zahiri ne?.



      Tana tsaye tana wannan saqa da warwarar har yarinyar ta gama bacewa idanunta gaba daya ba tare data sani ba

"Ammi....ke ake jira,zamu tafi" ta tsinci muryar afnan,wadda ke tsaye bayanta,cikin mamaki kuma tana bin inda taga fulani aishan nabi da kallo tana tunanin me take kallo haka?,me kuma ya tsaidata?,saidai bata ga komai ba.



      Ajiyar zuciya fulanin ta saki kana ta soma takawa afnan na biye da ita,hakanan takejin fuskar yarinyar na mata yawo cikin idanu har suka isa bakin motar aka bude mata ta shige.


     

     Hukumar asibitin tuni ta bada ambulance an dauki gawar suhaiman,wanda acikin ambulance din azeez ya tafi.



        Mai martaba da yayo waya kawai ya bada umarnin a mata suttura abunneta a nan din,Allah yayi anan qasarta take,kuma akwai musulmai a qasar,hakan kuwa akayi,isu isu suka zauna zaman jimamin rashin yarinyar,saboda ta shiga ran da yawa daga cikinsu,musamman kasantuwarta ta fito daga tsatson mutum mafi soyuwa a zukatan al'umma cikin masarautar,sai waya da suke amsa daga 'yan uwa da abokan arziqi dake nigeria ta tayasu ta'aziyya.



        Ta bangaren bilkisu kuwa kukan data sha yasaukar mata da ciwon kai sosai,hakan ya sanya ta tattara ya nata ya nata ta wuce gida kawai,ba tare data tsaya cike takaddun da tasan dole zatayi ba saboda patient dinta ce ta rasu,amma tunda taga office din dr adam na nuna alamun yana nan,saita wuce din kawai,yasan zaiji da komai,a harabar asibitin ta samu amatu ita da wata nurse da tasu tazo daya,ta amsheta suka wuce zuwa gida.



         A hanya amatun keta mata surutun ya zasu koma bata ga suhaima ba?,batace da ita komai ba,donta fuskanci batasan ta rasu ba,batasan kuma ta yadda zata gaya mata ta fahimta ba,haka yarinyar ta haqura tayi shuru,don tasan halin maman natasa sarai,aduk sanda suke mata surutu irin wannan indai sukaga shuru taqi amsasu to batason magana ne.


      ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Misalin qarfe tara ne na dare agogon qasar brasil din,dai dai lokacin da yarima ke fitowa daga wanka,jikinsa sanye da rigar wanka wadda iyakacinta qauri.



        A hankali yake takowa tsakiyar dakin,jikinsa na fidda sassanyan qamshin turarukan wankanshi,akwai qaramin towel a hannunshi yana goge ruwan jikinsa.



      A yau yana jin sauqi cikin zuciyarsa fiye da kullum,yana jin haquri da danganar rashin tilon diyarsa yana shigarsa,saidai abune da yasan cewa bazai taba mantawa dashi ba.



       Har ya isa gaban mudubi ya soma shafawa lallausar fatarshi mai saiya jiyo sheshsheqar kukanta,sam yama mance da ita cikin dakin,saboda yadda a kwanakin gaba daya ya sake dauke mata wuta fiye da yadda ta sanshi,saiya waiwaya sashen daya jiyo kukan yana kallonta.



        Tana zaune takure waje daya,ta rungume gwiwoyinya a qirjinta,jikin gwiwar tata ta kifa hoton da yake da tabbacin na suhaima ne,saiya waiwayo gaba daya ya jingina da madubin gami da rungume hannayensa a qirjinsa gami da xuba mata idanu yana kallonta.



       Cikin kwana uku ta fige ta rame,idan ka ganta saika zaci takaba take,zuciyarsa takanyi zafi a duk sa'ilin daya tuna yadda tayi watsi da rayuwar suhaima,tamkar bata damu da ita ba,koma na itace ta haifeta ba,hakanan yakanji zafi sosai idan ya tuna tahowar yarinyar wata qasa ba tare da mahaifiyarta ba,yaci alwashin hukuntata fiye da tunaninta kan abubuwan da take aikatawa harsai ta gane kuskurenta,to amma yanayin da yaga ta shiga yanzun yasa dukka wasu makamanshi suka zube,tausayinta ya soma kamashi,yasan cewa duk yadda uwa takai ga nuna halin ko in kula ga danta,ba qaramin dukanta zaiyi ba aduk randa akace yau babu shi a duniya,sai tafi kowa girgixa da jin xafi,kamar yadda a yanzun ya bayyana qarara kan safwa din,wannan dalilin ne kawai ya sanya yaji ya kamata yadan kawo sassauci cikin yadda yake matan,koda ba duka ba.



       A hankali yake takawa har zuwa inda take zaunen,saiya zauna daga gefanta,ya saka hannunshi ya zare hoton ya aje gefe,sannan ya janyota zuwa cikin jikinsa.



        Gaba daya ta shige ingarman qirjinsa tana sake sakin wani sabon kukan,wanda ke nuna dama tallafinsa take da buqata,ta cukuikuye gaban rigarshi sosai tana sakin kukan.



       Baice mata komai ba sai hannunshi É—aya daya saka yana shafan saman kanta,idanunshi na kallon wani waje daban,yayin da launin qwayar idanunsa ke soma canzawa,yana tuna abubuwa da yawa,wanda bai tsammaci zasu zo mishi ba a wannan lokacin.



        Ya tuna sanda wata ke masa kuka mai bayyana pain da zuciya ke ciki shigen wannan,amma a lokacin bai tsaya ya mata wani dogon lallashi ba,hakanan yakan tuna wataqila har yanzu a doron duniya akwai wata halitta dake dauke da ciwo mai daci shigen wannan a zuciyarta tana rayuwa a haka,me yasa?,anya kuwa lokaci baizo ba da zaibi diddigin tsohuwar alaqa ba?,anya kuwa lokaci baiyi da zai bazama ya tono wannan alaqar da take da buqatar abincikata ba?,yana ji a jikinsa zuwa yanzun koda ya bijirema ammi baida laifi,Allah ba zaya kamashi ba,saboda ya cika mata dukkan wani burinta data qudirta akansa,ya cika mata dukkan wani qudirinta?,to me yayi saura?,ya nemota ya sauke haqqin dake wuyanshi,ya nemota duk inda take.



       Tsahon wani lokaci kowannensu yana fama da tabo da ciwon dake cikin zuciyarsa kafin ya sauke ajiyar zuciya mai qarfi har qirjinsa yana dagawa,safwa dake kwance saman qirjin tayi luf bayan ta gama kukanta tana shaqar daddadan qamshin da jikinsa ke fiddawa duk da bai shafa kowanne turare ba,amma qamshi yabi jikinsa,ya kuma zauna masa sosai saboda tsabar yawan tu'ammali dashi da yakeyi kowanne lokaci

"Shikenan ta tafi my prince?,ta tafi ta barmu?" Saiya dagata daga qirjinsa,hannayenshi saman kafadunta yana kallonta

"Haka Allah ya tsara,kuma yadda yakeso haka za'ayi,koda mu ya kira dolenmu muje,bamu da wani sauran uzuri....idan bawa yayi haquri mai kyau sai hakan ya zame masa alkhairi nan gaba" kalamai ya gaya mata masu kwantar da hankali da sanya nutsuwa,sannan daga qarshe ya sanyata ta shiga tayi wanka ko zataji sanyi cikin ranta.



        Shiryawa yayi shima ya sanya kaya sannan ya bude qofar dakin ya fita.



        Falon gidan ya bulla,wanda yake dauke da dakunan da fulani mama sodangi,afnan da sauran barorinta suka sauka,don mom din safwa kwana biyu sukayi suka koma,don haka gidan saisu yasu.



       Kitchen ya shiga da kanshi,yunwa yakeji amma kwana biyun nan baya iya cin wani abincin kirki,har ita safwan ya lura da haka,don kafin tafiyar mom dinta yasha jin tana artabu da ita.



        Fresh milk mai sanyi ya ciro kwali biyu manya,saboda sosai yakejin cikinsa a fafake,mutumin daya saba baya wasa da cikinsa sam,ya dauki cups guda biyu sannan ya juya ya fice daga kitchen din.



        Yana fitowa fulani itama na fitowa daga nata dakin sukayi kacibus,cikin kulawa take dubanshi da kwalin madarar hannunsa

"Da kayi magana idan kana da buqatar wani abun,basai ka shiga kitchen da kanka ba" duban kwalin madarar yayi shima sannan yace

"Ba wani abu,ita zan dauko kawai dama"

"Kana nufin madara kawai zakusha a abincin dare?" Tayi maganar tana juyawa gami da samawa kanta wajen zama,ganin haka shima saiya isa daura da ita ya zauna yana amsa mata

"Ta ishemu,ba wata babbar yunwa bace" kai ta girgiza

"Ban aminta ba,kwana nawa rabonka dakaci abinci,ina sane fa...." Kafin yace komai ta qwalawa afnan dake daki kira,a sannan tana waya ta sauko daga gadonta ta qaraso cikin falon da wayar a hannunta,don bata tsammaci harshi yana wajen ba.



       Ganinsa awajen ya sanyata saurin katse wayar,ta soma qwaqule earpiece din dake kunnenta kana ta qaraso tana hardewa,saboda yadda ya kafeta da idanunsa masu dan banzan kwarjinin nan

"Gani ammi"

"Shiga kitchen ki samawa yayanku wani abuncin mara nauyi haka wanda bazai dauki lokaci ba" amsawa tayi da to sannan ta wuce ciki da sauri,ta sanya afnan ne saboda tasan duk wanda ta saka ya masa ba lallai yaci ba.



       "A ina maganar yarinyar nan ta tsaya ammi?" Yarima yayi magana yana duban ammin tasu,fuskarta ta nuna alamun alhini kafin ta amsa mishi

"To....ana nan dai ana addu'a,ina kyautata zaton mijin auren ne har yanzu baizo ba,tunda koda yaushe addu'a ake,hakanan duk wanda yaxo ba korarsa take ba,ana bashi dama,Allah ne kawai baiyi ba" shuru yayi kawai yana dan tunani a ranshi,dukka yaran gidan banda 'yar wajen fulanin masanawa afnan ce kawai ta rage gaban ammin,wani lokaci yakan qalubalanci mace ta zurfafa karatunta yayi zurfi da yawa ba tare da wani tsayayye ko gamsashshiyar magana a kanta ba,wasu mazan sai su dinga mata kallon tayi girman datafi qarfinsu koda ba yawan shekar gareta ba,misali ga afnan din da karatunta yake zurfi a yanzu,uwa uba kuma ta fito daga babban gidan sarauta dayake da dumbin arziqi tarihi da nasaba,ba kowane zai iya fuskantarta yace yana so ba,duk da bata rasa komai ba daya danganci kyau kyakkyawan hali nasaba da tarbiyya ba

"Allah ya zaba abunda yafi alkhairi"

"Ameen" ammin ta amsa tanajin babu dadi a ranta.



        Dukkan abinda ta burata a duniya babu wanda Allah bai mata ba,amma saiya zamana afnan din ta zama ta takashin baya ta fannin aurarwa cikin gidan,wannan shine abu qwaya daya tilo dake damunta a yanzu,bata kuma ta hanyar da zata maganceshi kota kawo qarshensa,wanda har abokan zamanta manyan abokan adawarta ke samun abun goranta mata da yada mata magana a yawancin lokuta,sauqinta ma duka yayyenta aka aurar babu sa'anninta da aka aurar bare abun ya ta'azzara,itace auta.



        Tunaninta ya sake nisa,fuskar yarinyar da yadda ta bugeta kana taci gaba da tafiya abinta cike da quruciya,abun yakan yi mata yawo aka,yana kuma dawo mata akai akai,saidai tunani guda daya dake sanya mata relief kan wani hasashe da zuciyarta ta soma mata,hasashen data kira da banzan hasashe mara tushe bare makama shine,bata ga hanya ba ko,hakanan bataga hadinsu da wannan qasar ba,bare tace hasashen da zuciyarta ke mata ne ya tabbata,babubta wata hanya da hasashenta zai iya zama gaskiya,saita saki ajiyar zuciya tana jin nutsuwa kadan kan tabbacin da daya sashen na zuciyarta ya bata.


*_da sannu sannu dai kunkuru zaije inda jirgin sama yaje wata rana,kada ku damu,ku zama masu bibiya cikin nutsuwa ba tare da gaggawa baðŸ˜Å Ã°Å¸˜Å _*

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 54


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




       Mintina qalilan afnan ta dawo ta kammala,ta miqa masa plate din dake a rufe,da idanu ya mata alama takai mishi daki,saita juya zuwa dakin,cikin ranta tana mita da qunqunin rashin ganin amfanin matarsa,da ba zata iya tsaya masa kan cikinsa ba,da sun hada muhalli saidai su suyita hidima dashi,komai tafison a mata tana daga zaune yadda take tun daga gidansu.



        "Munyi waya da mai martaba,yace ya kamata mu dawo gida hakanan,saboda jama'ar dakeson yi muku gaisuwa" kai ya jinjina sannan yace

"Kamar yaushe ya kamata kenan mu tafi,tunda ticket kawai zamu siya" dan shuru tayi kadan sa'an nan ta dora

"Idan ba damuwa nan da jibi ya kamata mu wuce" ya sake jinjina kanshi

"Shikenan,babu damuwa,gobe zanje na karbo certificate din mutuwar suhaima,jibin saimu wuce in sha Alla" ajiyar zuciya fulani ta sauke mai nauyi sannan tace

"Allah yayi mata rahama"

"Ameen ameen ya Allah" ya fada yana sadda kanshi qasa,shuru ya ratsa falon na wasu mintuna,sa'annan ya miqe yana yiwa fulanin sallama ya wuce xuwa cikin dakin.



       Ya tars safwan tayi wankan tana zaune gefan kujera shuru ba tare da tana yin komai na,idanunta a kode suke sosai,ya qaraso ciki yana dauke idanunshi daga kanta,dab da ita ya zauna ya aje kwalin madarar saman wani dan qaramin tebur,sannan ya bude ya cika cup ya miqa mata,shuru tayi kamar ba zata amsa ba,amma ganin yadda ya tsareta da idanu ya sanyata tilas ta miqa hannu ta karba,ta soma kurba a hankali shi kuma yana ci gaba da kallonta,har sai data sha fiye da rabi sannan ta ajjiye masa tace ta qoshi.



       Baice komai ba shima ya bude kwali guda ya soma kurba shima a hankali,sai daya sha kusan rabi sa'annan ya lumshe idanu yana aje numfashi bayan ya jingina jikinsa da kujerar.


¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶




    Fashin da tayi na kwana biyu saboda ciwon kan data dawo dashi tun ranar mutuwar suhaima ya sanya a ranar larabar ta shirya da wuri don tafiya asibitin,a kwanaki biyun tayita fama da wayar dr adam kamar zaya zo ya dauketa,yayi mita yayi qorafi kan rashin bashi adress na gidansu yafi sau shurin masaki,amma yaci mata alwashin kome zatayi bazaya janye ba,ta kuma rubuta ta jjiye,saiya lalubo gidansu duk inda yake,hakan daya fada ya bata dariya,don haka saita saki murmushi kawai ba tare data ce masa komai ba.



        Yau kam free take tasan amatu ba xata takurata kan zata bita asibiti ba,don anty zuhriyya ce zata biyo ta dauketa ita dasu amatun,zasuje bikin sunan wata matar abokin abbaa data haihu,to kasancewar suna garine da kowa baida wani nashi sai suka zama tamkar 'yan uwan junansu.



         Tana gaban madubinta tana shafa tsadajjen manta saqo ya shigo wayarta dake aje gefanta tana chargy,saqo ne daga assadiq,ta sanya hannu ya shafa wayar kana ta bude saqon



_saqon fatan alkhairi gami da tashi lafiya zuwa ga sarauniyar kyawawan duniya,kuma mai mulkin zuciyata,da fatan kin wayi gari cikin qoshin lafiya,Allah yasa ana nan ana tunanin yiwa wannan zuciyar data kafu a donki adalcin da zai sanya ta dore ta kuma ci gaba da rayuwa,ki huta lafiya saraniya_



       Murmushi ta saki,ire iren saqonnin dr adam kenan dake cike fal cikin wayarta,saita maida idonta ga madubin tana duban kanta gami da tuna maganar da assadiq din yazo mata da ita ranar data bashi izinin zuwa gidansu,bayan ta fito da hijabi dogo har qasa mai hannu ta tarbeshi,suna zaune saman wasu kujeru dake jere a yalwataccen balcony na gidan.



       "Allah yasa sauyin rayuwa da tsahon xamani baisa kin manta cewa assadiq yana daya daga cikin tarin masoyanki ba,idan ma ke kin manta shi bai manta ba,kuma zai saki tuna miki da jaddada miki" saiya gyara zamanshi yana dubanta

"Kamar wancan karon ni assadiq naga bilkisu,kuma ina sonta,ina qaunarta har jinin jikina,hakanan inason na aureta ta zama matata ta sunna,ina buqatar hadin kanki qwarai da kuma soyayyarki,banason na sake rasaki kamar wancan karon,kimin alfarma don girman Allah" kalmarshi ta qarshe ta mata nauyi qwarai,saita sadda kanta qasa tana wasa da yatsunta,maza da dama sun sha neman soyayyarta,mutane iri daban daban,to amma tunda can tana jin wani nauyi na assadiq da qimarsa,don haka ta buda baki a hankali tace

"Na gode sosai da kaci gaba da daakon soyayyata tsahon wancan shekarun baka sauya ba har kawo yau,naji dadi sosai da soyayyarka gareni,idan so samu ne muci gaba da addu'a gaba daya nida kai,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi,yasa gobenmu ta haifar da kyakkyawar natija me kyau" duk da cewa bata fito kanta tsaye ta amsheshi kota koreshi ba,amma amsarta tafi masa kama da cewa yaci gaba da neman soyayyarta,duk da cewa ba'a bashi dama ta kai tsaye ba,amma hakanma yayi masa,yana fatan nan gaba ya samu amsa takai tsaye gamsashshiya.



        Dai dai nan ta sauke ajiyar zuciya,ta miqe tana isa ma'ajiyar kayanta dake shaqe da dumbin suturu kala kala,masu mabanbantan kudade,ta zabi ta shirya cikin daya,cikin qananun mintuna ta shirya kanta tsaf,ta kalli kanta a mudubi,sai taga kamar yau tafi kyau fiye da kullum,ayau saita hangi kyau tsari kwarjini da ajin da maza ke yawan gaya mata tana dashi,harda wasu daga cikin 'yan uwanta mata.



        Sakin wannan tunanin tayi don bataga amfaninsa ba,ta dauki duk tarkacen da tasan zata tafi dashi,sannan ta zira takalminta da jakar hannu wadanda dukkaninsu duka dace da sutturar jikinta ta fito.



        Sanda ta gama parking motarta tana shirin kashewa ta hangi motar dr adam a gefenta,ta dauke kai da sauri tana addu'ar Allah yasa bai ganta ba,sai taci gaba da zama cikin motar tana so ya wuce ciki sannan itama ta shiga,don ta tabbatar idan ya ganta,zai tilastata saisun jera ne har ciki,ita kuma abinda bata so kenan.



        Saidai kuma addu'ar tata bataci ba,don tana tsaka da zaman taji ana knocking glass din motar,tun kafin ta bude taga shine,bata da sauran zabi illa ta fito kawai,don idan bata fito din ba shi shigowa ciki xaiyi abinsa,don haka ta dauki kayayyakinta ta bude ta fito.



       Fuskarsa cike da murmushi yake kallonta,ya bude baki cikin farinciki yace cikin harshen turanci

"Kyakkyawar laraba ce yau,naji dadi sosai da ganinki,yau inda bakizo ba,zansa mommy ne da kanta ta kiraki,ta kuma roqarmin alfarmar ki bawa danta adress din inda zaije ya ganki,tun kafin zuciyarsa ta buga" ya miqa hannu yana amsat kayayyakin hannunta,duk da bataso sakar masa ba,amma batason jan doguwar magana,dole murmushi ya subucewa fuskarta na furucin da yayi

"Bakajin kunyarta yanzu dr?" Idanu yadan fidda

"Au,ku a hausa fa abun kunya ne ko?" Sai ta soma takawa tana yin gaba ba tare data bashi amsa ba,tana bin kan tambayar tasa da gaisuwar ina kwana,ya biyota yana amsawa tare da qoqarin daidaita kafada da ita.



         Abinda take gudu dai shi yayi,dolen sai daya jera da itan,suna tafe suna haduwa da ma'aikata,suna gaidasu cikin girmamawa da mutuntawa,tun daga lokacin da kowa ya fahinci soyayyar da yake mata suke bata wani irin girma,tamkar itace dr adam din,wannan ya janyo mata hamayya daga wasu daga cikin likitoci mata dake nacin neman soyayyar dr adam din basu samu ba,saidai ita din ko a jikinta,dukansu basu dameta ba,don a rayuwarta ta yanzun ba komai take bari ya dameta ba,tace ta gama samun damuwa tun asubar fari ta rayuwarta,yanzu kuwa da komai ya warware mata bai kamata ta bari qananun abubuwa irin wadan nan nason dagula lissafinta ba.



        Bai barta ba kuwa sai da suka dangana da office dinta,don shi ya bude mata ma,yana aje mata kayan saman kyakkyawan table dinta ne yace

"Har yanzu mutanen nan basu karbi certificate na rasuwar yarinyarsu ba" ta daga kai ta dubeshi

"Na zaci tun ranar dana tafi ka sallamesu" kai ya girgiza

"Nima hankalina ba akwance yake ba,saboda yadda kika fita din na tabbatar ba lafiya ce ta kawo hakan ba" kafada ta gyada

"Ba damuwa,nan da awa daya komai xai kammala,koda sunzo zasu karba babu matsala" da qyar tasamu ya tafi nashi office din ya bata waje,bayan ya ritsata,ya kira mommynsa ya bata wayar suka gaisa.



        Batura sosai,babu ruwanta da wata kunya ko kwana kwana,hira take da ita kai tsaye,tana kuma sake roqarwa danta soyayyarta,sun dan jima kan wayar kafin suyi sallama ta bashi wayarsa ya tafi tana masa mita shi kuma yana dariya.



         Sai data gama rubuta certificate din,tayi waya daga dakin buga takardu na asibitin sukazo suka amsa sannan ta fita ita da nurses din dake team dinta,ta soma duba marasa lafiyanta,wadanda dr martin ne ya riqe mata su har zuwa yau data dawo.



         Ta shafe tsahon lokaci sosai tana duba komai,sai data tabbatar komai da kowa lafiya lau,kuma komai ya tafi daidai sannan ta nufi komawa office din ta duba sauran ayyukan dake gabanta.



        Tana shirin bude office dinnata taji ana dan kiranta da yanayi na girmamawa,ta waiwaya,daya daga cikin ma'aikatan dake buga takardunne riqe da certificate din,komai ya kammala kenan ya miqa mata,hannu tasa ta amsa tana masa godiya kamar yadda yake a al'adarta,ta tura qofar tana karanta rubutun jiki tare da lissafa adadin kwanakin da yarinyar tayi yau a qarqashin qasa

"Ranki ya dade akwai baqo" taji an fada da harshen qasar daga bayanta,ta waiwaya tana duban daya daga cikin ma'aikatansu ne

"Baqo daga ina?"

"Wai certificate xai karba" kai ta jinjina,mahaifin suhaima ne kenan,dama akwai maganar da takeson mishi,kan barin yarinyar da akayi babu uwa ko uba har wata uwa duniya,abun ya sosa mata rai,yana kuma ci gaba da sosa mata rai

"Ka bashi izini ya shigo" ta fada tana shigewa ciki shi kuma ya juya.



       Saman kujerarta ta koma ta zauna tana dan juyata kadan kadan hagu da dama tana dakon shigowarsa,ganin wasu mintuna sun shude bai shigo ba saita ciro eye glasses dinta ta sanya,ta janyo takardar wani patient dinta ta soma dubawa saboda rage lokaci.



      A hankali ya turo qofar office din bayan an bada izinin shigowa,sanye cikin trouser da shirt mai gajeran hannu,kalolin da suka masa kyau suka kuma bada ma'ana a jikinsa,qafarsa na saye da rufaffen takalmi,kanshi babu hula sai sumarshi da take zuba qyalli saboda kyau da tayi na gyaran da tasha,duk da ba mai yawa bace sosai,yanayin askin dake fuskarsa ya sake qawata zallar kyau da kwarjinin da Allah ya bashi,hannunshi daure da agogo rolex mai azabar tsada da kyau,sai gilashin idanu dake saman fuskarsa wanda ya kuma qarawa adonshi kyau da kwarjini,.



      Tunda ya shigo yake daukan hankulan mata kala daban daban cikin asibitin,musamman wadanda suka san nauyi da tsadar motar daya fito daga cikinta,takunshi kawai abun daukar hankula ne,duka wannan bai dameshi ba,baisan ma me ake ba,fuskarshin nan babu ko digon fara'a a cikinta,ba zakace ya taba dariya a duniyarshi ba.



        Maida qofar yayi yadda take saboda bin doka da qa'ida irin nashi,kana ya maido kansa cikin office din da niyyar yin salla.



       Cak kalaman bakinsa suka tsaya saman harshensa,maqogwaronsa ya kada fidda wani sauti bare harshensa ya motsa,tamkar an kafe dukkan ganinsa saman fuskar dake kallon takardar dake riqe a hannunta,kamanninta suka dinga bayyana cikin idanunsa a wancan shekarun da kuma yanzu.



       Sune dai,wadan nan kamannin daya jima da sani,wadan nan kamannin da suka hana rayuwarshi sukuni tsahon shekara bakwai da watanni,duk da cewa akwai bambamci mai tarin yawa,da suka bayyana qarara,tun daga yanayin fata,dressing da kuma yanayin ilimi gogewa da kuma wayewa.



       Amma bayajin koda shekaru dubu ne suka shude matuqar ruhinsa yana cikin gangar jikinsa wannan fuskar mai tarin daraja qima da martaba idanunsa ba zata taba bace masa ba,yanajin koda an mata sauyin fuska jikinsa zai gaya masa cewa tana tare dashi,ruhinsa xaici gaba da gaya masa cewa itace a tare dashi.



        Baisan ta yadda ya isa gaban table din nata ba,baisan yadda akayi yakai kanshi gabanta ba,yadai tsinceta tana daga fararen manyan qwayoyin idanunta dake ta walainiya kamar an diga musu mai ta dubeshi bayan qamshin turaren daya sanya mata matsananciyar faduwar gaba ya ziyarci hancinta,taso ta daure amma saita tsinci zuciyarta na gudu fiye da kima,bayan batasan daga inda qamshin ke kutso kai ba,hakan ya sabbaba mata dole ta daga kanta tana dubanshi,babban shahararren matashin attajirin dan kasuwar duniyar nan ta gani tsaye a gabanta,me ya kawoshi office dinta?,bata sani ba,saita tsuke fuskarta sosai tana ci gaba da kallonshi tanason jin me ha shigo dashi?.



       Kamanni na zahiri data sake gani saman fuskarshi irin da twince din ta yasa wani faduwar gaban ta daban ta sameta irin wadda bata taba jinta ba,dole badon taso ba taji idanunta na lumshewa,cikin zuciyarta ta ambata da sauri

"Subhanallah....ya ubangiji....ka sanya baida alaqa da mahaifinsu ko wani nashi,Allah ka sake nisanta tsakaninmu dasu" saita kuma bude idanun nata da sauri.



      Ta zaci zata sameshi a zaune ko kuma ya fita,saita sake ganinshi still dai a tsayen,hannayensa goye a qirjinsa,ya kafeta da idanunsa da takejinsu da wani irin nauyi a qirji da gangar jikinta,wani irin kallo da takejinsa ya bambamta da sauran kallo na kowa da kowa,qwayoyin idanuwa da bata taba ganin masu nauyi da kwarjini irinsu ba.



       Can daga wane sashe na zuciyarta ya zaburar da ita,tayi hanzarin maida hankalinta tana janye idanunta daga kanshi tana daukar takarda ta gaba dake gabanta,tana kuma sake tamqe fuska,tare dajin haushin yadda yazo ya tsaya mata akai,kamar wani bodey guard,ba kuma tare da taji sallamarsa ba har ya zuwa yanzu,da harshen turanci tace dashi

"Lafiya malam?,ka shigo wajen mutane babu sallama,kuma ka tsaya haka a kansu ba tare dayin bayani ko fadin dalilin shigowar taka ba" ta qarashe maganar tana duba takardar,saidai zallar mamakin kamanni da razana dake tattare da ita suna nan,kunnuwanta kuma na gareshi tana son taji me zayace,saidai tsayin wasu mintuna shuru,hakan yasa ta fusata,ta sake daga kanta cikin masifa tace

"Kaga....idan baka da abun fada kana iya fita ka tafi,akwai tarin ayyuka gaba na".



       Ga dimbin mamakinta sai taji ya damqi hannunta dake riqe da takardar,wanda yayi hakanne don son tabbatarwa da kanshi ire iren mafarkan daya saba yine ko kuma zahiri ne wannan?.



       Cikin tashin hankali ta fincike hannunta tana dubanshi,kana ta miqe tsaye cikin fushi da fada

"Meye haka malam?,hankalinka daya kuwa?" Sakin hannun nata yayi,karo na farko daya buda bakinsa cikin tashin hankali bayan ya fahimci bilkisun nan dai daya shafe shekara da shekaru idanunsa na neman gani,zuciyarsa nason jinta kusa dashi,kunnuwansa na muradin jin duk wani abu daya shafeta itace dai,itace dai a gabanshi

"Am so sorry....kiyi haquri,wannan ce kalma ta farko da nake tunanin ya kamata na gaya miki".



        Shuru tayi tana dubansa cikin mamakin kalaman da yake furtawa,me yayi mata,wayeshi?.



        Kallon rashin fahimta da take masa ya tunasar dashi cewa,bata taba ganin wayeshi ba,batasan shi din yanzu akan me yake magana ba,cikin wata iriyar murya mai sanyi yace

"Abdul'azeez abdallah mu'az kaisa,yariman qasar kais......."



       Bai qarasa ba saboda yadda yaga da mugun hanzari ta nemi kujerar data tashi dazun akai ta zauna,wutace ta dauke tsaffff! Na tsahon wani lokaci,wani irin tashin hankali taji yana rufto mata,indai kunnuwanta sunji daidai,yana son gaya mata cewa shine mutumin da yayi silar zuwan amaturrahman da abdurrahman duniya?,mutumin da yayiwa rayuwarta karan tsaye?,mutumin daya sauya qaddararta shida ahalinsa?,tome yake nema yanzu a gareta?,me yazo yi?,ko yazo ne ya qarasa tarwatsa rayuwarta?,don bata taba tunanin yazo bane domin 'ya'yansa,tunda tun suna tsiron da ba'asan ko meye ba a cikin cikinta suka nuna basu da buqatarsu,indai ko hakane yazo don ya tarwatsa sabuwar rayuwarta to qaryasa tasha qarya,ba zata taba bari suyi galaba ba koda waye gatanshi nan duniya.



       Cikin lokaci kadan ta maida hankalinta jikinta,ta tattara dukkan nutsuwarta,ta miqe a hankali saidai cike da karsashinta,jifansa tayi da wani irin kallo sa'annan tace

"And so what?.....don kaine yarima abdul'azeez kuma sai me?,ehemmm?" Ta qarasa fada tana harde hannunta itama a qirji,tana kuma jifansa da wani irin mugun kallo.



       Furucin nata ya dakeshi,bai taba zama ya tsara me zai iya biyo baya ba duk randa suka hadu,idanunshi a rufe suke,burinsa kawai ya ganta,yana tsammanin ganin nata shine abu mai wahala,idan ya gantan kome zai biyo baya sai yake ganin abune mai sauqi tattare dashi.



        Takawa ya soma yi yana nufarta,cikin wata iriyar murya da zaka gaza fasara yanayin da yake ciki yace

"Karki ce zaki fusata don Allah....ki bani dama ta yadda zamu zauna mu...."

"Dawa?.....kaga malam nifa banma ganeka ba,inajin kana da ciwon tabin hankaline ko dake tashi lokaci bayan lokaci,ya kamata kabar nan,idan kuma ba haka ba zan kira securities su fita dakai" duk da cewa yana cikin hali na dimuwa amma saida yaji maganar tata kamar wasan yara,saboda ya sani cewa koda duka securities din qasar zata kira babu wanda zai iya kama hannunshi ya fiddashi,saboda sun riga da sunsan wayeshi shi,ko baya ga haka ma bayajin akwai wanda ya isa ya fiddashi daga office din daidai wannan lokacin,zamanin daya dade yana hana idanunshi bacci kan fata da burin zuwanshi,yana addu'ar Allah ya nuna mishi shi.



       "Banajin ko duka duniya zasu taru sun isa su fiddani daga dakin nan bilÆ™ess" cike da mamaki hakanan har tsakiyar kanta taji furta kalmar sunanta da yayi,saidai duka ba wannan ne a gabanta ba,yanayin yadda ya furta maganar ta tabbatar mata da cewa ainihin abinda yake cikin zuciyarsa kenan,magana ce data fito daga zuciyarsa,a bisa kuma saurin fahimta da gane halayyar mutane da Allah ya hore mata ta fuskanci  yana da wani confidence tattare dashi.



      Bata da buqatar ci gaba da tsaiwa dashi don haka bashi da wani amfani,hakanan tana jin zuciyarta na wani irin zafi duk sanda ta tuna waye tsaye a gabanta saman rufin daki guda daya,saboda haka ta soma tattara tarkacenta dake saman tebur din cikin hanzari da gaggawa.



        Saiya sake matsowa dab da ita hakan yasa ta dago da sauri cikin kaushin murya tace

"Ka dakata malam,kada ka sake aikata irin kuskuren daka aikata daxun,domin ban sanka ba,bansan daga wacce duniya kake ba,kanme zaka nemi shiga rayuwata"

"Bilqess!"

"Karka sake ambatar suna na,don babu wani abu daya hadani dakai"

"Igiyar aurena....don har yanzu ke matatace!" Furucin da yaso tarwatsa qwaqwalwarta fiye dana daxu,yakuma so sumar da ita a duqen da take,har sai da tayi taga taga zata fadi,tallafin da yaso kawo mata ne yasa tayi hanzari tallafar kanta,ta dafe kujerar daje gefanta

"Qarya kike,kin manta su din mayaudara ne,azzalumai,da basu damu da damuwar kowa ba sai tasu?,me yasa zaki gasgata kalamansa don kawai ya fada?" Xuciyarta ke ankarar da ita,wannan tunanin ya sanyata namijin qoqarin aro juriya da jarumta ta azawa kanta,sannan ta dubeshi sheqeqe

"Wannan kuma kaita shafa,kaika sani,bansanka ba bare wata kalmar aure ma ta gilma tsakaninmu" daga haka ta rataya jakarta a kafadarta,duk da bata gama diban abinda xata diba din ba,burinta kawai tayi nesa dashi,burinta kawai ta tserema ganinsa,cikin wani mugun sauri da batasan tana dashi ba ta soma dosar qofa,baiyi qasa a gwiwa ba ya rufa mata baya

"Na hadaki da girman Allah ki tsaya ki saurareni koda na minti biyar ne,koda ba zaki yarda da dukka kalaman bakina ba,ki daina pretending kamar baki sanni ba,bayan babu wannan maganar" a fusace tana bude qofar tace

"Bazan daina cewa ban sanka ba,saboda ban sanka ba din!,donme zaka dinga bibiyata ha'ab?!"da sauri ganin tana niyyar ficewa yace

"Idan ke baki sanni ba nina sanki,na sanki sanin da babu mahalukin daya taba miki shi duka fadin duniya....idan har baki sanni ba,ina cikina?,ina yaro ko yarinyata dana bari jikinki?".



         Ji tayi jiri na neman kayar da ita,dr adam ne tsaye qofar office din yana duban fuskarta,hakanan kalaman azeez na qarshe na shiga kunnuwansa,batasan sa'adda da ta danqa masa katin rufe qofar tata a hannunsa ba,har hannuwansu na gogar na juna,tabbacin ba cikin hayyacinta take ba

" ka rufemin qofar,bani da lafiya"daga haka ta qara wuta cikin sauri gudu gudu duk don ta tsere masa.



      Bai tsaya bin takan dr adam.daya tsaidashi da tarin tambayoyinsa wadanda bai fahimtar ma me yake cewa ba,illa dai yaga bakinsa yana motsawa ba,ya rufawa bilkisu baya,yabar dr adam da binsu da kallo,baki sake,qwaqwalwarsa cike fal da tarin tambayoyi.



         Saidai qaura wambai ya rasa bilkisun cikin harabar asibitin,bayan ya tabbatarwa da kansa cewa bata bar cikin asibitin ba,yayin da take tsakankanin wasu shukoki tana hango gilmawarsa,tanajin wani tsoro da fargaba da nashigarta,me zayayi cikin rayuwarsu daya dawo yanzu?,dame suka zo musu a wannan karon kuma?"ta yiwa kanta tambayar yafi cikim carbi.



       Tayi dana sani mara iyaka kan rashin zuwanta yau da motarta,gashi anty zuhriyyan da zata dauketan har yanzu shuru basu qaraso ba,kafin wasu mintuna ta hada hawaye da gumi sharkaf saman fuskarta.



         Cikin jikinsa ya dinga jin tana cikin asibitin,hakan yasa ya kasa fita,ya dinga zirya yana duba loko da saqo na asibitin,yanaji cikin zuciyarsa zaya ganta,ya dinga yawo tsakanin cikij asibitin zuwa harabarsa.



        A karo na sau babu adadi yasake dawowa harabar asibitin,yanajin kamar zai zauce da bace masan da tayi,bayan ganinta da yayi karon farko na wasu 'yan mintuna.



       Kamar ance masa ya juya ya hangeta cikin bala'e'en sauri tana nufar wata mota dake tsaye,wadda da alama ita suke jiran ta qaraso.



      Abubuwa guda biyu duka dakeshi lokaci daya,shirin bace masan da takeyi,da kuma yarinya da yake hangowa 'yar kimanin shekara shida zuwa bakwai tana leqo da kanta ta window din motar,tana dubanta fuskarta cike da murmushi,tana zuro mata hannu gamida motsa bakinta da alama magana take mata.



       Idan ba qarya idanunshi ke masa ba,fuskarshi yake gani kan fuskar yarinyar,banbancin shekaru kawai da kuma kasancewarta diya mace,banda haka zai iya cewa tashi fuskarce,a gigice cikin rashin sanin abunyi ya dora tafin hannunshi saman tashi fuskar yana shafawa a hankali,kamar wanda ya rasa hankalinsa,kai kace yanason tabbatar da gaskiyar abinda idanunsa suka gane masa ne..........



        Bai ankara ya dawo hayyacinsa ba sai daya ga ta shige,an tashi motar ana shirin ficewa daga asibitin sa'annan ya zabura,cikin tsananin zafin nama da hanzari ya durfafi motar,sai ina tuni tayi masa nisa,har sun fice daga asibitin sun kuma harba kan titi.



       Da saurinsa ya dawo inda tashi motar take,ya budeta yashige ya tayar da ita sannan ya tasheta da wani irin gudu ya rufa musu baya.



        Da farko anty zuhriyya bata lura da yanayin da bilkisun ta shigo dashi ba,sai dataji yaran na mata surutu amma babu wanda ta kula a cikinsu,saita waiwaya tana dubanta

"Subhanallah!,daughter lafiya?,me haka?" Ta fada tana qoqarin sauka gefan titi,cikin muryar kuka tace

"Karki tsaya ummi muje don Allah" ganin yadda tayi maganar a gaggauce saita fasa tsaiwar,taci gaba da tuqin amma fiye da rabin hankalinta na kan bilkisun,tana karanto zallar tashin hankalin dake saman fuskarta.



        Motar saita dauki shuru,dukka yaran kowa ya kama bakinsa,abdurrahman da amaturrahman damuwa ta bayyana qarara saman fuskarsu,ganin yadda dukka yaran sukayi tsuru suna kallonta saita kifa fuskarta saman cinyarta,don ta tabbatar ba zata iya hana kanta kukan ba bare ta tsaidashi.



        Gudu yake zabgawa har ma ya wuce doka da qa'ida,saidai ko iri irin motar bai samu gani ba,haka ya dinga zagaye titunan dake daura da asibitin harma da maqwaftansa,shiga nan fita can,bayajin ko gajiya bata lokaci da kuma tsahon lokacin daya bata wannan aikin,tamkar wani zautacce,hatta da wayarshi dake aje gefan gear din motar daketa burari tana neman agaji bai jita ba bare ya saurareta,burinsa kawai yakai gareta,burinsa kawai ya cimmata,haka ya shafe lokaci mai tsaho yana zagaye saman titunan ba tare daya samu abinda yake nema ba,hakanan shima bai gaji da nema ba,yana fatan ko Allah zaisa ya ganta.....



        Yayi yawo mai tsahon dashi kansa baisan adadinsa ba,sai daya zagaye dukka area da asibitin yake da sauran maqwaftan unguwanni,saidai babu alamun zai ganta.



        Jikinsa ga soma mutuwa saboda yunwa da gajiya amma bai kulaa da wannan ba,zuciyarsa da qirjinsa ke masa wani irin zafi,roqon Allah yake tun qarfinsa ya tallafeshi,kada ya sanya ta subuce masa,kada ya qaddara masa wata doguwar wahalar kafin yasake ganinta,tilas daga qarshe ya gangara motarshi gefan titi,ya jingina bayansa da makarin kujerar yana lumshe idanunsa da suka sauya launi,yana fidda numfashi mai zafi,tun daga hunhunsa zuwa bakinsa da hancinsa,qwaqwalwarsa ta soma nisa cikin duniyar tunani tare da wassafa yadda al'amura zasu kaya anan gaba.



       Ã†˜arar wayarshi a karo na barkatai shi ya sanyashi bude idanunsa yana bin wayar da kallo kamar wata baquwarsa,yanajin ringing dinta kamar tsaga qwaqwalwarsa yake,saiya sanya hannu da nufin dauka ya kashe,saidai kafin yakai ga haka ma ta katse don kanta,yana shirin kashewar dai kiran ammi fulani ya shigo,bazai iya kashe mata waya ba,don haka ya daga,saidai bai iya karata a kunne ba ya sakata a handsfree

"Ba zakaci abinci tare damu bane yau?"

"Akwai wani uzuri daya riqeni,kada na tsaidaku" sauyi taji sosai cikin muryarsa,to amma ta sani ya sauya ya zama wani mutum na daban cikin shekarun,koda yaushe mode nashi na iya canzawa,don haka cewa kawai dashi tayi

"Allah ya tsare hanya"

"Amin" ya amsa suna aje wayar dukkaninsu.



       Tunanin daya fado mishi a rai ya sanyashi sake tada motar cikin hanzari,yana da hope da fatan xai samu cikakken adress dinta a a sibitin,adress din da zai zama silar kawo qarshen komai,ya kuma zama silar cimma burinsa na shekara da shekaru,don haka ya qarawa motar wuta yana burin isa asibitin cikin qananun mintoci.



*na yau da gobe ne sisters*ðŸ™Ã°Å¸½Ã°Å¸™Ã°Å¸½Ã°Å¸™Ã°Å¸½

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 55


*_IDAN kaji ƙi gudu sai in sa gudu bai shigo wajen ba. Ƴan uwa abokan tafiya, gafa magani A GONAR YARO. domin tabbas idan kaji gangami akwai labari_*.


*_Ina masu wahala kullum cikin neman maganin sanyi (imfection) amma babu biyan buÆ™ata. Kinyi na asibiti har kin gaji babu canji, na gargajiyarma taÉ“awa kike babu wani Æ™yaÆ™yÆ™yawan sakamakon. Tofa kakarku ta yanke saÆ™a. Domin kuwa ga dama a tafin hannunku. Munada maganin NI'IMA, maganin GYARAN HIPS (mai gida bye bye😉). Muna da maganin BOOBS (mai gida welcomeðŸ™Ë†). Maganin BASIR mai hana sakewar zama. Duk ku garzayo domin samunsu akan farashi mai sauÆ™i da rahusa, ga kuma inganci domin an samosu ne daga tsaftatacciyar hanya mai nagarta._*👇ðŸ»


*AISHA S BAYERO TRADITIONAL MEDICINE AND HERBAL RESEARCH CENTER...*


_KUNJI SUNAN KO? CENTER CE TA MAGUNGUNAN GARGAJIA, WANDA DUK WANI DAMUWA DAKE DAMUNKA IDAN HAR KAZO WAJEN S BAYERO TA KARE DA YARDAR ALLAH.. KADAN DAGA MAGUNGUNANTA SUN KUNSHI:_


_MAGANIN SANYI_

_MAGANIN NI'IMA SET_

_MAGANIN NANKARWA_

_MAGANIN KIBA BABBA DA KARAMI_

_MAGANIN HIPS_

_MAGANIN GYARAN NONO_

_MAGANIN RAGE KIBA_

_MAGANIN SAKA FEELING_

_MAGANIN CIDA KWAI_

_ZUMA YAR ASALI_

_MAGANIN BASIR KOWANNE IRI_

_HODAR NI̢۪IMA_

_MAGANIN MALLAKA_

_GUMBAR NONON RAK̢۪UMI_

_GUMBAR MADARA_

_TURAREN FARIN JINI_

_KAZA MARA KWAI_

_TURAREN MALLAKA 3 STEP_

_HAD̢۪IN MATAR MINISTER 1_

_KAZA ME KWAI_


_STEP 2:_


_TURAREN MALLAKA ME KWALBA_

_ME KUNAMA DAN MATSI_

_TURAREN GOSHI_

_TURAREN QIRJI_

_TAUWADAR MATA_

_MEMORY_

_KAHON MALLAKA_

_YAJIN MAZA_

_TEA  DIN MAZA_

_DAMBUN MATSI_

_MAN AYU_

_MAN DAMO PURE_

_KWALLIN IDONKA IDONA_

_GARIN SHA DAKA ME KYAU_

_KUBEWAR MATA_


_DUKA WADANNAN INGATTUN MAGUNGUNA NA GARGAJIYA HAJ AISHA NA DASU GANGARIYA.. HERBAL MAGUNGUNA NE MASU KYAU DA INGANCI.. TAFIYAYYU NA KASAR CHAD. CHADIAN HERBAL MEDICINE AND RESEARCH CENTER.. KYAU, INGANCI.. RAHUSA... SAI MAGUNGUNAN *AISHA S BAYERO TRADITIONAL MED AND HERBAL RESEARCH CENTER....*_


_NUMBER WAYAR WHATSAPP: 08121491609 KO KIRA TA NUMBER 08145873617._


_ADIRESHI: KUNTAU KARSHEN KWALTA KAN A KARASA YAN TIFA, DAIyDAI GADON KAYA CEMENT.._

Sai kunzo😘😘ðŸ¤Ã°Å¸»

_________________________

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




         Hakanan fulani taji jikinta yayi sanyi bayan ta katse kiran data yiwa azeez kan zai qaraso suci abinci?,tayi shuru tana wani nazari,tare da karantar sake samun sauyi cikin muryarsa,jikinta ya bata tabbas akwai wani abu daya faru dashi,saidai batasan ko meye ba.



         Afnan wadda fitowarta kenan ta dubi fulanin tana bata fuska

"Nikam ammi gaskiya sai nakega kamar kinfi qaunar ya yarima akaina,shi kullum kamar wani qaramin yaro,bayan ya girma har iyali gareshi?" Qaramin murmushi ta saka,ta waiwayo tana duban afnan

"Ba wanda nafi qauna cikinku akan wani,saidai kawai kina kishi dashi ne,sannan bugu da qari yayanku akwai damuwa tattare dashi,dole sai ana ci gaba da bashi kulawa da kuma saita mishi hanya"

"Damuwar mefa ummi,ni kaina na karanci sake sauyawarsa sosai a shekara bakwai din nan" tayi maganar tana kallon fulanin sosai tare da son jin abinda ke damun nashi.



        Kai ta jinjina kawai tana gyara zamanta

"Kedai kiyi masa addu'a,Allah ya yaye masa"

"To ameen" tafada tana duban qasan tiles din falon,shuru ya ratsa wajen na wasu mintuna,kowa da abinda yake saqawa cikin ranshi,kafin daga bisani afnan tace

"Ina yaje ne yayan?,inata sauri na taddashi"

"Ya koma asibiti,karbo certificate of death na suhaima" ta bata amsa tana daddanna wayarta

"Allah sarki dota..." Afnan din ta fada cikin jimami,don sosai jininsu yazo daya da yarinyar,sai kuma ta sake cewa

"Kuma fa asibitin naso zuwa nima" bata amsata fulanin,da alama wani abune ya janye mata hankali cikin wayar,ganin haka yasa afnan din ta miqe,tana shawarin ko ta sami cave kawai taje ta duba asibitin,don tun randa taga wata kamar bilkisun hankalinta bai kwanta ba,jikinta yana bata itace,amma idan har ita din ce sai tafi kowa murna.



         Dakin da mama sodangi take ta tura ta shiga,da yake yawanci idan tana da buqatar hira da ita kadai take xama tayi hirarta hankali kwance,tasu tafi zuwa daya sosai,akwai sabo mai girma tsakaninsu da shaquwa mai qarfi.



        Samunta tayi xaune saman abun sallah tana jan carbi,saidai da alama tana azkar dinne kuma tunani yana fusgar hankalinta.



       Gefanta ta zauna tana dubanta

"Mama baki idar bane?" Murmushi tadan saki tana aje carbin,a duk sanda wani cikinsu ya kirata da mama saiya tuna mata da bilkisun,zamansu tare ya sanya koda suka dawo rakiya bata daina kiranta da maman ba kamar yadda suke kiranta dashi ita da bilkisun a zamansu na mexico

"Na gama ranki ya dade gimbiya,kina buqatar wani abunne?" Kai ta girgixa tana murmushi kana tadan kashingida saman gadon nata tana cewa

"Dawai asibitin nan zanje,ina buqatar dan rakiya" gaban mama sodangi yadan fadi,itama ta tuna mata da wadda ta gani din kamar bilkisu

"Me zakije yi acan gimbiya?" Ajiyar zuciya ta saki

"Wallahi mama wata na gani kamar tsohuwar qawata bilkisu,na jima inason Allah ya nuna mini ita,to amma ina shakka da kokwanton daqayar idan ita dince,saboda ita waccan iyayenta ba masu qarfi bane,sannan tun kafin mu gama secondry aka aurar da ita,auren dole ga wanda bata so,kinga ko idan hakane banga ta yadda za'ayi na ganta anan ba" shuru mama sodangi tayi gabanta yana faduwa,wani abu yana darsuwa a ranta,a yadda afnan ke wassafa bilkisu sai takega tana magana ne kan tata bilkisun sak,babu wani maraba ko kuwa banbamci,to amma indai hakane me zai faru?,tana da buqatar tabbatarwa,tana da buqatar sanin bilkisu ce ko ba ita bace?,wadda take tunani akai ita afnan ke magana akai itama?

"Shikenan,aisai ki shirya na rakaki ko?" Cikin jin dadi afnan din ta miqe tana cewa

"Yauwa mama,aiko na gode" ta fita da hanzari don shiryawa.



          Cikin qaramin lokaci dukansu suka gama shirinsu,suka cewa fulani zasu anguwa ne,ta musu Allah ya kiyaye suka fice suka tari taxi.



         Sanda suke shiga a lokacin motar azeez ke fita daga asibitin,saidai babu wanda ya kula da wani cikinsu,wani irin tuqi yake yana jin kamar bazai iya kai kanshi gida ba,dukkan wani kuzarinsa ya tsiyaye tas.....ya buga ya raya qaura wambai su bashi adress din dr bilqees amma sunce sam ba tsarin asibitin bane,yayi haquri,idan wani issue ne yakeso su tattauna ya sameta gobe a ofishibta dake cikin asibitin,idan da buqatar ta bashi adress din zata bashi da kanta ko tayi musu umarni a bashi,saboda suna da kiyaye duk wani abu daya shafi mara lafiyansu ma bare likitansu dake aiki a qarqashinsu.



       Ganin yadda ya kafe,hakanan suna ganin girmanshi da qimarshi a matsayinsa na wani babban mutum kuma sananne,sai suka danganashi da office din mamallakin asibitin gaba daya wato dr adam.



        Yaje ya sameshi cikin tunanin meye hadin bilkisun tashi,da kuma sananne kuma fitaccen dan kasuwar duniya Aa yarima?.



        Sanda ya iskeshi a office din ya tsammaci zai samu dukkan abinda yakeso,dr adam ya tsaya ya saurareshi,ya saki nannuyar ajiyar zuciya sanda yaji adress ma yake nema,baisan inda take ba kenan?,wannan shike nuna cewa ba wani abu bane mai girma tsakaninsu yadda yake tunani,koda yana cikin sahun 'yan takarar neman bilkisun to hakan na nufin tabbas bata bashi wani matsayi mai girma ba bare hakan ya daga masa hankali kenan?,sai yaji sanyi cikin zuciyarsa,nauyin dake qirjinsa ya ragu,shima kuma ya gayawa azeez din kwatankwacin abinda sauran ma'aikatan suka gaya mishi.



        Yayi qoqarin nuna mishi muhimmancin adress din a gunshi,amma da gangan dr adam ya nuna bai fahimci komai ba,ganin xai bata mishi lokaci,kuma shi sam baida lokacin xama yayita roqonshi yasa ya tashi yabar mishi office din a fusace,ko a jikinsa don bazai taba yarda ya bayar din ba,babu abinda yafi tsana a duniya irin yaga wani na rabar bilkisu,burinsa a duniya a yanzu bai wuce ya aureta ta zama tashi shi kadai ba.



         Sanda su afnan suka isa asibitin basu samu wani information a kanta ba,hakan yasanya itama ta buqaci adress dinta,suma basu samu ba,saboda dr adam kafin ya fita daga asibitin ya jaddada cewa kada wanda yazo daga baya walau mace ko namiji a bashi adress din dr din,da qyar suka samu suka tsira da lambar waya,wanda iya hakanma ya yiwa afnan dadi,tayi serving number a wayarta da xummar idan ta koma gida zata kirata.



       Tana zaune daga gefan gadon,yayin da anty zuhriyya ke tsaye saman kanta tana sauraren abinda take gaya mata,tsayin mintuna da gama bata labarin anty zuhriyyan tana nazari,bilkisun ta buda baki a hankali muryarta tana rawa,alamun ko yaushe daga yanzu tana iya sakin kuka tace

"Ta yaya ma zai wani ce ni matarsa ce?,ta ina na zama matar tasa bayan ina da shaida ta takaddar saki da suka bani?" Ta qarashe fada,da alama abinda yafi damunta kenan cikin dukka batun.



     Nannauyar ajiyar zuciya anty zuhriyyan ta saki tana sauke hannayenta dake rungume a qirjinta,sannan ta koma dab da bilkisun ta zauna,ta kama hannayenta ta saka cikin nata,cikin tattausar murya tace

"Daughter....wannan dukka ba abun damuwa bane,dukkan abinda kike tsoro daya daga cikinsu bazan taba bari ya faru dake ba,wannan karon ko dame sukazo dai dai nake dasu,a wannan lokacin a shirye nake duniya tasan dukkan abinda ya faru,matuqar suka mana kan kara wannan karon sai mun musu na rodi,babu wanda ya isa ya rabaki da yaranki koda kuwa sarkin kaisa ne da kanshi bare danshi ko matarsa,banason kisa wata damuwa a ranki da zata hanaki walwala,kici gaba da rayuwarki kamar yadda kika saba,baki da wata matsala kisa hakan a ranki kinji?" Ta qarashe fada tana mata murmushin qara qarfin gwiwa,wanda sosai kalaman anty zuhriyyan suka bata qarfin gwiwa itama,suka kuma rage tsoron dake zuciyarta.



          A wani mugun hargitse ya koma gida,wanda kana kallon fuskarsa kasan akwai babban al'amari tattare dashi,mamaki kan meya sameshi daga futarshi zuwa dawowarshi safwa keyi,don daga dawowarsa yahau fidda kayansa gaba daya ya wuce direct zuwa toilet ya sakarwa kanshi sassanyan ruwa tsahon wasu mintuna kana ya fito.



       Duk da ruwan sanyin daya sakarwa jikinsa amma hakan bai sanya launin qwayar idanunsa komawa dai dai ba,daren gaba daya bai saurari abinci ba,bai kuma bari kowa ya dameshi da surutu ba,hasalima kebe kanshi yayi shi daya a farfajiyar gidan,yayi zurfin tunani wajen neman hanyar dazai dai daita komai.



      Wani irin dare ya gani mai tsaho baqi duhu da kuma fadi,wanda sam bai samu bacci ko daya a cikinsa ba.



     Washegari ticket nasu ya basu kawai su wuce su duka,yace musu wani aiki ya tsaidashi qasar,sam ba haka safwa taso ba,taso su tafi tare ko yaci gaba da debe mata kewa,amma hakanan tana ji tana gani tabi su fulani suka wuce.



          Suna zaune cikin airphort din afnan ta sake gwada lambar bilkisun karo na babu adadi,don tun jiya take faman kira amma sam bata shiga,harma ta soma fidda rai,ta kuma fara zargin lambar bogi suka bata saboda sunga ta matsa da son samun lambar.



        Ba zato ba tsammani taji ta shiga,fuskarta wadace da fara'a ta dubi mama sodangi

"Lah mama....kinga ta shiga" ta gaya mata ne saboda yadda taga itama ta damu ta son layin ya shiga,maganar tata ta janyo hankalin mama sodangi gaba daya kan wayar

"Ma sha Allah" ta fada amma idanunta akan wayar,itama tana dakon jin an daga kamar yadda afnan ke dako.



        Can qasa muryarta tayi sallama,saidai duk da hakan,haka bai hana mama sodangi gane muryarta ba,tabbas bilkisu ce,bilkisun ta,amma ga afnan data amsa sallamar donta tabbatar sai tace

"Don Allah ina magana ne da bikisu bilyamin?" Kai ta gyada daga bangarenta,tana aje mug dake cike da ruwan tea a gefanta

"Eh itace" murmushin jin dadi afnan ta saki tana gyara zamanta

"Ma sha Allah,kai amma gaskiya naji dadi sosai....nasan baki gane me magana ba ko?"

"Eh gaskiya....muryar ta dan kwanta min"

"No wonder.....sunana afnan abdallah mu'az kaisa,kin tunani?" Ta fada cike da confidence tana jiran amsar bilkisun.



       Mummunar faduwar gaba taji ta ziyarceta,ba shakka afnan ce,afnan ce qanwar yarima,ina suka samu phone number dinta?,ta nan zaya bullo mata kenan ko kuwa me yake nufi?,koma meye yanzun ita din a shirye take,ta shirya musu,tana jin wata dakiya na ratsa zuciyarta,don haka ta sake dake zuciyarta itama tadan saki muryarta kadan

"Ya aiko ki kenan ko?,meye saqon nashi?" Cikin mamaki da rashin fahimtar zancan tace

"Waye ya aikoni?,baki ganeni bane?,afnan ce fa,afnan classmate dinki"

"Ina magana ne kan abdul'azeez" murmushi ta saki,tana raya wani abu a ranta,toko ya yarima ya santa dama?,akwai wani abune tsakaninsu take jiran aike daga gareshi?,to amma idan har ta sanshi ya akayi bata taba tambayarsa  ita ba?,ya akayi bata taba nemanta ba?,duk da cewa shidin tasan halinsa sarai ba lallai ya gaya mata ko ya bata labarin yasan wata class mate dinta ba

"Awwnnn.....kinsan yaa prince kenan?".



       Gaba daya bilkisu ji tayi kamar tana shirin raina mata wayau ne kawai,don haka saita datse kiran tana jan dogon tsaki,ta kashe wayarma gaba dayanta ta aje gefanta.



       Duk da cewa afnan bata kai ga jiyo tsakin ba,amma mamaki ya cikata na yadda akayi bilkisun ta katse mata kira,hakanan bata nuna wani alamun jin dadin haduwarsu ba,bugu da qari kuma ta ambaci sunan yayanta kamar akwai wata sanayya sosai tsakaninsu.



       Da wannan daurewar tunanin ta waiwaya tana duban mama sodangi

"kinga mama,kodai bata gane ni bane?,na zaci zanji tayi murna"

"Ba zata taba murna ba tunda har tasan wacece ke,wace ke a wajenta" mama sodangi ta fada cikin ranta

"Bari na sake kira na qara mata bayani,nasan bilkisu ba haka take ba,hala ma ba itace ta daga wayar b....." Dafe hannunta mama sodangi tayi wanda take qoqarin taga ta sake kiran bilkisun,zuwa yanzu maman tanajin ba zata iya ci gaba da boyewa afnan alaqar dake tsakaninsu da bilkisu ba,ya kamata ace ta sani

"Karki kirata gimbiya,saboda koda kin kirata ba zata daga ba" da mamaki saman fuskarta ta kalli maman

"Saboda me mama?"

"Kinsan DANGANTAKAR dake tsakaninku?" Saita girgiza kai da sauri.



        Bata boyewa afnan komai ba ta bata labari,tayi ne da yaqini da kuma zuciya daya,tayine bisa gaskiyarta koda fulani zata hukuntata,saboda ta tabbatar cewa kosu yaranta basu san tirka tirkar da aka tafka ba.



       Girgiza kai kawai afnan keyi cikin mamaki da girgiza matuqa,yaushe duka hakan ya faru?,yaushe amminsu ta aikata wannan danyan aikin babu shawara ko masaniyar daya daga cikinsu?,me yasa ammin tasu tayi sha'awar hada wannan danyan aikin?,ko tasan itace qawata da nake yawan yi mata maganarta shi yasa tun a wancan lokacin da nace za'a mata auren dole,masarauta ta taimaka ta shiga tace a'ah nabar maganar?,saita miqe tana duban mama sodangi

"Bilkisu rayuwarta abar tausayi ce a lokacin,nasan da haka a qurarren lokacin da babu abinda zan iya yi mata,wannan abu da akayi mata tamkar xalunci ne aka yiwa rayuwarta,bai kamata nabar ammi ba,ya kamata na tunkareta da maganar...".



        Saurin riqo hannunta mama sodangi tayi tana girgiza mata kai

"A'ah,kinfi kowa sanin wacece fulani,bata haka ake bullo mata ba,ki sassauta zuciyarki ki kwantar da hankalinki,mu samu isashshen lokaci da zamuyi tunani akai" ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi bayan ta samu ta taushi kanta da qyar kana ta koma ta zauna,tayi shuru cikin zuzzurfan tunani tana sake tariyar labarin da mama sodangi ta bata,tsahon wani lokaci a hankali tace

"Ya akayi ya prince ya yarda da wannan aikin shi kansa?" Ta fada cikin salo na tuhuma,kai mama sodangi ta kada

"Bashi da laifi,saboda a lokacin yana kan qadamin neman mafita,hakanan uwa ce,umarni ya karba daga gareta"kanta itama ta girgiza

" a wajena shima mai laifi ne mama sodangi,kamar anyi amfani dashi ne an bata rayuwar wata baiwar Allah" ajiyar zuciya mama sodangi ta saki ba tare data sake iya cewa komai ba,daga haka shuru yaci gaba da wanzuwa tsakanin har zuwa sanda suka shige cikin jirgin,kana ya lula dasu duniyar sama don ya sadasu da qasata nigeria.



        Ta bangaren bilkisu kuwa tea dinta ta dauka taci gaba da sha hankalinta kwance,donta riga ta yiwa kanta da anty zuhriyya alqawarin lokacin tashin hankali ya dade da wucewa gurbin rayuwarta,tana shan tea din tana tuna wasu abubuwa,tun daga shigowarsa office dinta har zuwa kiranta yanzu da afnan tayi,sai data kammala sannan ta samu ruwa mai sanyi tasha,tabi lafiyar gadonta tana son rama bashin baccin da bata samu jiya tayi ba.



       Ta dade sosai tana baccinta kafin ta farka,ta shiga tayi wanka ta sauya kaya sannan ta dauki wayarta ta sauko qasa.



       Ta samu dukka yaran suna falo suna kallo,tabi kowannensu suka gaisa tadan tsokani na tsokana a cikinsu sannan ta samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana tambayar anty zuhriyya,najwa dake yunqurin shiga kitchen don duba abincin data dora musu tace

"Yanzun nan ta shiga daki,itama ta kwanta"

"Ok to" bilkisu ta amsa tana qoqarin kunna wayarta,donta tabbatar ba zata rasa saqonni ba ta watsapp da kuma sms.



       Tun kafin wayar ta gama saituwa kiran dr adam ya shigo,ta lumshe idanunta kana ta bude tanajin kamar karda ta daga,don batason qarin wata damuwar,amma ganin yadda yake kiran kawai ya shaida mata bazai daina kira ba harsai ta daga,don haka ta daga din.



       Ã†˜atuwar ajiyar zuciya ga sake sannan ta jishi yana cewa

"Mommy ta daga" idanu ta fiddo dukka waje,wato kusa da mommyn yake yake gaya mata ta daga,shi ko kunya baiji

"Ina ruwan bature da kunya" wata zuciyar ta gaya mata

"Kin bani wahala yau bilkis,kinsan ba zaki samu zuwa aiki ba sa'annan kuma ki kashemin waya?" Murmushi ne ya kubce mata na mamakinsa,jin yadda ya marairaice mata kamar zai saki kuka

"Au....kai na kashewa wayar ma?"

"Yes,eh mana,nasan nine babban dalilin kashe wayar,wato kada dan anacenki ya dameki ko?"

"A'ah,kawai dai banjin dadine yau din gaba daya,kuma idan nabar wayar a bude kira xaita shigowa,kuma ba lallai na samu damar dagawa ba"

"Mommy...kinji ashe bata da lafiya" ta jiyoshi adan rude yana gayawa mommyn,ta gwalalo idanu tana sake mamakin dr adam,wai me yasa ya fiya tabara ne haka?,kafin tayi wani tunani har taji muryar momyn,da alama zuwa tayi ta amshi wayar daga hannunta.



         A ladabce ta gaidata ita kuma tayi mata sannu da jiki,tana jiyo muryar dr adam sama sama saidai batajin me yake cewa,katsam ta tsincin mommyn na neman adress din gidan wai zata zo dubata,ba zata iya hanata ba,don uwa ta wuce wasa komai kashinta,saidai ta tabbatar da cewa plan ne na dr adam din,shi ya shirya hakan,kuma da tasan hakan zata faru da ba zata ce bata da lafiya ba,hakanan badon taso ba ta karanta mata adress din

"ai bamu da nisa ma sosai,nasan street din" ta gayawa bilkisun.



        Koda wayar ta koma hannunsa cikin shan kunu tayi masa magana,duk da baya ganinta amma zaka gane hakan kan muryarta

"Na gode daka hadani da mommy"

"Nifa babu ruwana,bama lallai nazo ba,ita keson zuwa ta miki sannu da jiki kuma ta ganki" tasan ya fada ne kawai,amma babu ta yadda za'ayi ace za'azo din bai biyota ba,shi me neman kuka an jefeshi da kashin awaki dama?.



        "Gashi kince baki da lafiya,kuma tafiyarku dubai larabar nan,ya za'ayi?" Mutum ce ita mai qwazo da neman sani koda yaushe kan abunda ya shafi aikinta,batason rasa tafiyar don tasan ba qaramin qaruwa zasuyi ba,don haka tace dashi

"Babu damuwa,ina saka ran kafin sannan na sake warwarewa,don yanzunma da sauqi sosai"

"To Allah ya qara sauqi ya nuna mana,sai munxo" ya fada cikin salon shauqi,da alama yana cike da farincikin samun adress dinta yau da yayi,da haka sukayi sallama.



         Tana shirin ajjiyewa wani kira data lura tun suna waya da dr adam ke shigo mata ya sake shigowa,lambar nigeria ce,kuma tana da yaqinin assadiq ne,hakanan badon taso ba shima ta daga ta saurareshi,saidai ta shaida mishi batajin dadi,hakan ya sanya hirar batayi tsaho ba yayi mata sallama,saita sake kashe wayar gaba daya donta samu ta huta sosai.

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 56


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



        Washegari da yammaci suna zaune dukkansu a falon gidan,tana sanye da doguwar riga mai hade da hula tana yiwa yaran bitar karatun addini,kamar yadda ta maidashi wajibi kan wuyanta,dukka yaran gidan suna daukar karatun addini ne a wajenta,wanda bata sanya ta tsaya sosai kan hakan,tana soke duk wani uzuri da zai taso yaci karo da karatun yaran ya kawo musu cikas,shi yasa ko tafiye tafiye bata fiya son yi ba sabida hakan,don najwa ma tuni ta sauke a hannunta,yanzu haka hadda takeyi a wajen nata dai,yayin da yaran kowanne yayi nisa a biye,ateeq ma dan yake daya sauke,baifi sura biyu zuwa uku suka rage masa ba.



       Hatta su amatu dake da shekaru shida sun doshi izifi na goma sha shida a biye,wannan abun ba qaramin dadi yakewa anty zuhriyya da abbaa ba.



        Ƙaraurawar qofar gidance tayi qara,bilkisu ta dubi ateeq

"Ko baqin abbaa ne?" Kai ya girgiza

"Anya ko?,yace su sun fasa sai dare,ko naje na tambayoshi" kai ta girgiza

"Aah qyaleshi,jeka ka bude kaga waye" ya amsa mata da hanzarinsa yana miqewa,ita kuma taci gaba da sauraron haddar da najwa ke bata.



      Baquwar fuska ce ta shigo falon da sallama,wadda bata fita tar a bakinta,kana mata kallon farko zaka gane baturiya ce,hakanan ga kama nan sosai ta fuskar dr adam akan fuskarta,da alama kenan ita ya dauko,kalar fatar ne ya dauko mahaifinsa,shi yasa haskensa baiyi bauuuu ba kamar nasu,yadan russuna haka kadan.



      Idanunta kan bilkisu da alama ta ganeta kenan,tunda tana ganin hotunanta wayar dr adam wanda yakan dauketa ba tare ma da tasan yanayin hakan ba.



        Cikin girmamawa da fara'a ta tarbeta,ta shiga kitchen da kanta ta hado mata snacks da drink,ita kuma tana ta bin bilkisun da kallo bakinta yaqi rufuwa,da alama bilkisun ta kwanta mata sosai.



      Zama tayi a qasa tana gaidata,saidai sam matar tace saidai ta dawo kusa da ita su gaisa sosai,duk da yadda takejin kunya amma haka ta daure,ta dawo gefanta kadan ta gaidata tana sunkuyar dakai,dai dai lokacin da anty zuhriyya suka fito ita da abbaa,da alama tayo masa rakiya ne zai fita.



        Tsaiwa yayi suka gaisa cikin harshen mutan qasan brasil,sannan yafice,anty zuhriyya kuma ta dawo wajen baquwar tasu,itama suka soma gaisawa da harshen qasar.



       A wajenma tsayawa yayi suka gaisa da dr adam,duk da baisan waye ba amma yaga yabata bashi girma na musamman,hakan ya sanya ya saka ayar tambaya akansu,haka dai suka gama gaisawa ya shige motarshi ya wuce.



        Tana zaune tana sauraren hirar mommy da anty zuhriyyan ta soma ganin kiran dr adam a wayarta,saidai sarai tana sane taqi dagawa,tasan ba zaua wuce yace mata yana waje ba,ta fito ya ganta,qarshe daya gane ba dagawar zatayi ba saiga gajeran saqo

"Bazanyi zuciya ba,bazan kuma tafi ba har sai naga kyakkyawar fuskar nan taki" kamar kuwa anty anty zuhriyyan tasan meke faruwa tace ta dauki ruwa da lemo takai masa,bayan ta tambayi mommyn tace mata tare suke.



        Hakanan ta sanya dan madaidaicin hijabinta saman doguwar  rigarta,ta shiga kitchen ta diba ta fice.



      Already har ya zauna saman qananun kujerun dake ajjiye a qofar gidan saman grass carfet,bai lura da tahowarta ba har sai data iso saboda ciyayin dake wajen,ta ajjiye try din yayi da shi kuma yaci gaba da kallonta,ta masa kyau sosai a idanu,tamkar ya saceta haka yakeji.



         Kujera taja ta xauna,idan da sabo ta riga ta saba da irin wannan kallon,bama wajen dr adam kawai ba,har wajen sauran maza irinsa,tasha tsayawa gaban mirrow taga waishin me suke kallo?,ta tasa menene,sai daga baya anty zuhriyya ke gaya mata cewa

"Baiwar kyau bilkisu,ke ba zaki gani ba saidai a gane miki,kedin kamar yaya maimunatu sak kika dauko,sau nawa kike cewa ina da kyau?,to kowa ya shaida din itadin me kyauce fiye dani".



       Ruwa da lemo duka ta tsiyaya masa tana miqa masa don ta katse kallon da yake matan,yasa hannu ya karba yana cewa

"Na gode sarauniyata,ashe cikin kowacce irin shiga kyau kike haka?" Murmushi kawai tayi tana kau da zancan ta hanyar gaidashi,saidai duk da haka bai haqura ba sai daya kodata son ranshi sannan suka shiga hira,wanda fiye da rabi yana sake yiwa kanshi campaign ne.



      Shuru ne ya ratsa na dan wani lokaci,har ta tsammaci ko bashi da abun cewa,sai kuma yace

"Yarima AA yarima,ya dawo neman adress dinki ko phone number......,meye tsakaninku haka?" Bata rai tayi dajin abinda yace din,wato har ya soma bin qwaqwqwafinta kenan

"Ba abinda ke tsakanina dashi,hasalima ban sanshi ba" jim ya danyi,don zam zuciyarsa bata aminta da haka ba

"Amma daga yanda yake neman sanin wani abu daya danganceki cikin rudu da rudewa,sai nakega kamar akwai wani abu a qasa" sake hada rai tayi sosai

"Am telling you ban sanshi ha dr adam,pls mubar wannan maganar"

"Chapter closed" yace da ita yana aje cup din hannunshi.



       Sun dan jima harma ta qagu su tafi,kafin daga bisani mommy ta fito,ta taka musu har bakin motarsu kana suka wuce,duk kunya ta cikata na yadda baturiyar babar adam din ke dada campaign na danta da kanta.



        Sadda ta koma haka ta tadda kaya fal sun kawo mata wai duka da sunan dubiya,ta dauka iya wanda takeso ta rabe musu saura,anty zuhuriyya nata yaba sauqin kai da son jama'a irin na mamar adam.



 *****    ****   ******   ****


       Cikin kwanakin ya dinga jinsa tamkar ba'a duniya ba,baisan akwai kwanaki.mafiya tsauri sama da shekaru bakwai da yayi a rayuwarsa ba sai yanzu,babban tashin hankalinsa da dimuwarsa na bacewarta bat kamar walqiya,har yanzu ya gaza gano indo take.



       Inda a nigeria ce ko wasu qasashen da kakan iya biya ko bin wasu hanyoyi domin sanin inda mutum yake to daya tabbatar cewa a tafin hannunsa take,saidai su qasa ce mai doka da order da kuma tsari.



       Ganin qwaqwalwarsa na neman gazawa,ga wani dan banzan ciwon qirji da ya taba fuskanta a baya nason dawo masa yasa ya nemo abdulrashid.



       Yana bahrain amma haka ya saki abinda yakeyi ya taho din,saboda tunda yaga kiran nashi ya tabbatar akwai abu na gaggawa daya taso,yasan kuma halin aminin nasa sarai,ba kowa yake iya gayawa damuwarsa ba,hakanan bashi da wani abokin shawara ko sirri saishi.



      Kamar yadda ya zata din kuwa,ya tadda yariman a birkice gaba dayansa yana neman zaucewa wajen neman bilkisun

"Na ganta abdulrashid,na ganta harda yarinya da jikina yake bani tabbacin diyata ce,amma randa na ganta ranar ta bacemin,har yau kuma ban sake ganinta ba,duk kuwa da irin qoqarin da nake"

"Ka nutsu yarima,ka kwantar da hankalinka,i trust you,kana da fikira,hakanan kana da basirar da zaka iya nemota duk inda ta shiga,amma wannan rudanin rashin bacci da rashin nutsuwar shi zai sanya dukka basirar dake gareka ta subuce maka" haka ya dinga qoqarin kwantar masa da hankalin,wanda hakan yayi tasiri matuqa wajensa,don bayan ya sashi bacci a dakinsa yace idan ya tashi zasuyi maganar shima zaije ya huta kafin sannan,sai gashi ya tashi da cikakkiyar basirar hanyar farko da yake ganin zai cimmata.



         A lokacin abdulrashid na falon zaune yana cin takeaway din daya musu yana kuma dakon fitowar azeez din,ga tsammaninsa bai tashi ba,abinda bai sani ba tuni ya tashi harya shiga yayi wanka ya kuma shirya ya fito gaba daya yana qamshin turare,duk da babu koda rabin kwalliya irin tasa saboda yanayin da yake cikin.



        A tsaitsaye yake gayama abdulrashid din shawarar daya yanke din,ganin kamar a gaggauce yake yasa ya aje takeaway din yace suje ya masa bayani a hanya,ya mara mishi baya suka fice.



       Abdulrashid dinne ke tuqi,yayin da abdulazeez keta kiram wayoyi,da alama wadanda zasu hadu dasu ne yanzu,sai daya gama yana kashe wayar ya soma magana da abdulrashid

"Zanyi amfani da damata da mutanen dana sani cikin qasar,ina da abokan harka da kasuwanci wadanda suke manyan security a qasar,zan samesu na zauna na musu bayani,inason su bani mutane daga cikin mutanensu da zan basu picture dinta,zasu lalubomin duk inda take in sha Allah,zasu xamemin tamkar informers,duk wani motsinta zan dinga sani,bazan qyaleta ba abdulrashid,tunda har tana raye bazan iya rayuwa tana wani bigiren ina wani ba,ina buqatar 'yata,inason inji duminta,inason dawowa da ita cikin rayuwata ko meye zaya faru a wannan karon a shirye nake da faruwar hakan" duk da maganarsa gasky ce amma saida abdulrashid yayi mamaki,don bai taba jin azeez din yayi kalamai kwatankwacin hakan kan wata diya mace ba tunda suke

"Hakan yayi....amma kasan cewa zaka kashe kudi" wani busashen murmushin gefan baki ya saki yana dan bubbuga wayar hannunshi cikin tafin hannunsa

"Kafi kowa sanin kudi ba matsalata bace,zan iya amincewa na rasa komai matuqar zan daidaita komai din" kai abdulrashid ya jinjina,kana yace

"Xaka iya yarima,fatan nasara"

"Na gode" ya amsa mishi yana dan zamewa ya jingina jikinsa da kujerar motar yana maida numfashi.



       Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



       Maqale take da wayarta suna waya da hannatu bayan sun gama waya da mahaifinta malam bilyaminu,ta shaida mishi tafiyar da zatayi daga nan din zuwa dubai,don duk sanda zatayi tafiyar takan shaida mishi ya mata addu'a.



        Tana ankare da amatu dake zaune gefan gadonta sanye da kayan bacci,fuskarta a hade ta hade qafafunta tana cillasu kadan kadan,dukka tana fushi ne kan bilkisun tace ba zata je dasu ba,yayin da abdulrahman ke zaune qasan dakin shi kuma yana game da game dinshi,duk da cewa shima fuskanshi a hade yake,ta rasa me yasa suke da qulafucin uwa haka?,har gwara ma abdulrahman da sauqi akan amatu maqale mata.



      Sai data gama shirya kayan tsaf sannan ta isa gaban madubi ta shirya,don already tayi wankanta.



      Cikin wata tsadaddar turn down collar long coat me belt ta shirya,wadda tayi masifar mata kyau,gami da fidda sigar kyanta,tana tsaka da rolling babban dankwalinta da zai rufe mata abinda yayi saura daya fito na wuya zuwa qirjinta wayarta ta dauki qara,sunan dr adam ta gani

"Ohhh" ta fada tana jinjina naci da matsi irin nashi,saita daga ta sanyata a handsfree

"Gani na fito,ko na tsaya mu wuce tare?" Kaman yana ganinta ta girgiza kai

"A'ah na gode....ka wuce kawai,nima gani nan" langabe mata yayi

"Dama nasan hakan zakice,shikenan na gode" bata sake cewa komai ba ta katse kiran,saita dauki wayar ta turawa assadiq saqo,saboda tun jiya ya kirata miscal kusan uku bata samu dagawa ba,kuma yau ta tashi da shiri bata bi kiran ba.



        Saqon yana tafiya ta kashe wayar ta jefata cikin jakar hannunta,daidai lokacin da amatu ta kirayi sunanta,ta daga kai tana dubanta,sai kuma tayi shuru,tasan dai bazai wuce magiya da roqo ba.



        A hankali ta dauke idanunta daga fuskar yarinyar tana lumshe idanu,sai taga kamar fuskarshi aka dora kan fuskarta,komai nashi kamanninsa tsaf gasu nan,inama ace basu dauki kamarshi ko daya ba?,inama ace da ita sukayi kama,da ba shakka sai tafi kowa murna,amma ba'a isa a hana Allah yinsa ba,ta sauke qatuwar ajiyar zuciya tana kiran abdulrahman,sai sannan yabar game din da yake ya taso ya iso gabanta,saita duqa gabanshi ta rungumeshi tana cewa

"Me zan taho maka dashi?" Dan shuru yayi kadan sannan yace

"Ball" dariya tadan saki

"Kai baka gajiya da qwallo abdul?,bayan ita fa?"

"Ko meye ma mami inaso" kanshi ta shafa shima tana duban fuskarshi kamar babansu ne a gabanta,kamar tayi yawa,harma tana mamakin yadda akayi bata taba kula ba duk da hotunanshi da take gani a baya,ko don abun baya ranta ne?,bata taba kawowa ba?,ko don bata taba tsaiwa ta masa kallon tsaf ba

"Barakallahu fika,kayiwa mami addu'a ta dawo lafiya kaji?" Kai ya jinjina sannan yayi kissing nata a goshi kamar yadda ta sabar musu.



       Waiwayawa tayi ta kira amatu itama,ta taso ta taho tana tura baki,rungumeta itama tayi kamar yadda ta yiwa abdul din tana tambayarta me takeso

"Ko meye ma mami" kumatunta ta kama taja

"Nasan zabinki,amma sai kinyi dariya" murmushi ta saki wanda hakan yama bilkisu dadi sai tace

"Lets pray together....kowa ya hada hannunshi waje daya" take kuwa suka buda tafukan hannayensu tana karanto addu'a suna amin,harta gama suka shafa gaba daya,sannan ta karanta wasu addu'o'i ta shafa musu a kansu tana cewa

"Fi amanillah" ta miqe tana duba agogo kana ta janyo akwatinta suka sauko duka harda su amatun.



        Cikin cave din data tara zuwa airphort ta fidda glass din daya kusa mamaye rabin fuskarta,wanda ya mata masifar kyau ta saka,sannan ta ciro qaramar wayarta ta kira fadwa abokiyar tafiyarta,ta shaida mata tana can airphort din,itama tace gata nan tana hanya su hade a can.



         Daidai lokacin da yake cikin dakin motsa jikin wanda a yau ya tashi da sha'awar zuwa,saboda yadda gaba daya cikin kwanakin damuwar da yake ciki tasa ya manta da batunshi,a jiya da yakejin yayi abunda ya dace zuciyarshi tana ta gaya masa zaya ganta lokaci kusa,hakan yasa ya yanke shawarar zuwa ya motsa jikinsa ko kasalar da yake ciki zata ragu.



      Wayarshi dake aje gefe ta dauki tsuwwa,sunan daya gani saman screen din ya sanyashi gaggawar barin abinda yake ya nufeta.



        "Yanzu haka tana cikin passingers da zasu sauka qasar dubai" kalmar data rudashi,ta kuma sanyashi kashe wayar ba tare daya gama jin bayanan da yake mishi ba,hakan yana tabbatar masa da cewa sun ganta kenan,dubai....me kuma zataje yi a dubai again" cikin sassarfa da hanzari ya dauki qaramin towel da daya wayar tashi kamar zaya tashi sama ya fice daga dakin.



*_tofa ƙaƙa ƙara ƙaƙa_*

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 57

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070






       Tun kafin ya qarasa gida ya kira dukka wayoyin da yakega ya dace ya kira din,ya riga ya gama yanke hukuncin cewa zaya bita,zai kasance da ita duk inda zata je a duniya,bazai sake yarda tayi masa nisa ba,ya samu information kan garin da zataje a dubai din,da kuma taron da zasuyi venue da time din,saidai kuma baisan masaukinta ba.



       Hakan yayi masa dadi,ya kuma isheshi,tare da zame masa haske na alamun nasara tattare dashi.



       Tuni ya yanki ticket cikin jirgi na biyu kuma na qarshe a ranar da xaije qasar,bai damu da tazarar yawan awannin da za'a shafe kafin tashin jirgin ba,yana shiga gida ya fada wanka ya soma shiri.


     ******    ****    ******



       Wannan shine xuwanta qasar na biyu,amma duk da haka sai takejin kamar zuwan farko,saboda yadda qasar ke qayatar da ita.



       Su uku cab ya dauko daga airphort din xuwa masaukinsu,dukkaninsu abokan aikine,kuma akwai sabo dai dai gwargwado a tsakaninsu,don haka suna tafe suna taba hira har suka qaraso masaukin.



       Kasancewar washegari itace ranar da zasu soma fita semina din,saiya kasance ranar kowacce kawai tayi wanka ta kintsa ne sun kuma zauna sun huta bayan sunci abinci,daga nan kowa ya kama sabgarsa.



       Ga bilkisu kuwa mutanen gida ta kira,anty zuhriyya ta hadata da dukka yaran suka gaisa,kafin ta kashe sa'annan tahau watsapp.



       Kamar wanda ke jiranta ashe assadiq na online,kusan shi ya riqeta lokaci mai tsaho suna hira,daqyar ya barta ta sauka,tana kashe data tana murmushi,assadiq mutum ne mai matuqar sauqin kai,hakanan ya iya hira wadda zaku kwashe awanni ba tare daka sani ba.



       Saita sauke ajiyar zuciya tana saukowa daga saman kujerar da take nade,ta taka a hankali zuwa bakin window din dakin da suke ciki,ta daga labulayen wanda hakan ya bata damar ganin cikin hotel din sosai,dama sauran gine gine da titunan dake daura da wajen,kasancewar suna bene ne hawa na uku.



        Shuru tayi na wani dan lokaci,tunaninta na daukarta zuwa rayuwarta ta baya yana tuna mata da wasu abubuwan da suka gabata na tsahon wni lokaci.



       Ajiyar zuciya ta kuma saki tana shafa dogon gashinta mai tsaho da sulbi,rayuwa ta mata kyau yadda take buqata,saidai har yanzu batasan ina ne makomar rayuwarta.



        Sakin window din data dafe tayi tana tunowa da hauwa'u,har yanzu bata samu nasarar samun yarinyar ba,yana daya daga cikin abubuwan da idan suka motsa mata takejin lallai tana da buqatar komawa nigeria a lokacin da anty zuhriyya tace,don taje ta matsa ta kuma nutsa da bincike ko Allah xaisa haqarsu zata cimma ruwa.



       "Tunanin me kike haka dr bilqess?" Ta jiyo muryar fadwa na ratsa dodon kunnenta,waiwayawa tayi inda dr fadwa ke tsaye,ta saki murmushi,kafin tace wani abu dr fadwan ta sake magana

"Kodai kina tunanin babban dr ne?,ai suna qasanmu ina tunanin,ba matsala sai a masa magana" dariya ma maganar tata ta bata,tadan dara kadan

"Manta da wannan batun dr....meke faruwa?" List da guraren da sukeson xuwa bayan gama semina din ta gaya mata ko tana da interest,ita dinma maison yawon bude idanu ce,don haka tace zataje,amma da fatan ba zasu wuce kwanaki uku ba

"In sha Allah" tace da ita.



         Tun bayan saukarshi qasar ya kasa zaune ya kasa tsaye a masaukinsa,yanata wassafa yadda haduwarsu zata kasance karo na biyu,ya sani cewa tilas ne ya fuskanci tirjiya da kafiya daga gareta,amma bai zaci zaikai har haka ba,bai zaci zata nuna bata taba saninshi kaf rayuwarta ba,bayajin yana da qarfin gwiwa dana qwanjin da zai iya jurewa wannan tarzoma tata,zuciyarsa bata da wannan jarumtar,indai har takai wani lokaci tana masa hakan tabbas komai zai iya faruwa.


      ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



       Cikin nutsuwa suke fitowa daga dakin taron bayan sun qare zamansu na yau,kallo daya zaka yiwa fuskarta kasan cike take da fara'a da alama taron ya mata dadi,rungume take da wasu takardu yayin da daya hannun nata take riqe da qaramar jakar hannunta.



       Idanuwansa qir saman fuskarta,yana jin wani irin abu mai qarfingana fusgarshi zuwa gareta,yanajin wasu yanayi yana dawo masa tar cikin kwanyarsa,zamanin da suka taba kasancewa tare da juna,lokacin da babu kowa cikin duniyarsu daga shi sai ita.



       Sam batasan da wanzuwarsa ba,saboda hankalinta kacokam nakan fadwa,da alama wani abun suke tattaunawa,bata ankara ba,bata kuma zata ko tsammata ba taga mutum ya sha gabanta kana ya tsaya cak a gaban nata yana dubanta da idanunsan nan masu cike da wani irin sirri da kuma kwarjini.



       Kallon second uku tayi masa idanunta suka dauki saqo suka aikawa qwaqwalwarta,take cikin sakannin dukka wata fara'a dake saman fuskarta ta dauke tsaf,kai kace bata taba dariya ba a duniyarta,saita kama hannun fadwa data fi kusa da ita wadda ta zuba ma azeez idanu tana dubansa cikin mamaki ta ja hannunta ta gewayeshi da zummat tafiya.



       Saidai bai bata wannan damar ba,gabanta ya sake sha,kana cikin harshen hausa wanda ya fuskanci duka abokan tafiyar nata guda biyu ba yarensu kenan ba yace

"Ki taimakeni ki bani dama komai qanqantarta da zamuyi magana mu fuskanci juna nida ke,na roqeki da girman Allah" ya qarasa fada cikin wata iriyar murya kana cikin sanyi yana hada hannayensa guda biyu.



         Cikin kalaman dake nuna zallar zafin da zuciyarta ke mata a sannan tace

"Ka sauraramin malam,ta yaya zanyi magana da mutumin da bansan wayeshi ba,na gaya maka bansanka ba,ban taba ganinka ko sanin waye kai ba,donme zaka damu rayuwata ka shugemin hanci da qudundune ne iyee?,mtsweew" ta qarasa maganar cikin jan tsaki kana cikin zafin nama ta kewayeshi ta wuce wannan karon ba tare data kama koda hannun fadwa din ba.



       Bai damu ba ya rufa mata baya,bai damu da yadda su fadwa ke binsa da kallo ba,bai damu da yadda masu fitowa jifa jifa daga dakin taron ke binsu da kallo ba yaci gaba da binta

"Wannan maganganun da kike fada kina fadarsu ne kawai saboda bacin rai,ke kanki kin tabbatar ba haka bane,kinfi kowa sanin waye azeez a duniya" tafiyar tasu batayi tsaho ba,bai kuma ankara ba yaga ta shige cab,kafin yayi wani yunqurin tsaidasu har sunja sun wuce.



        "Ya salam!" Ya fada cikin zafin rai da takaicin yadda idanunshi suka rufe bai kula da shammatar da tayi masa ba,saiya rintse idanunsa kana ya bude yana bin wajen da kallo tamkar zai sake ganinta,sai a sannan ya lura da yadda wasu ke kallon nasa,take qwaqwalwarsa ta tuna masa wayeshi?,wala'alla sun saba ganin hotonsa a mujallun qasarsu kenan

"Tur da rayuwar da zaka shahara kayi suna" ya fada cikin haushi takaici gami da jin zafi yana fadawa motarshi ya rufe bayan ya dage gilasan sama.



        Daga ranar da sunanka ya shiga cikin jama'a,labarinka ya fantsama a bakunansu,wata harka ta sanya sunanka yake shige da fice cikin bakunansu,to daga ranar idan bakayi babban nazari,dogon tsinkaye da sanya lura da takatsantsan a lamuranka ba,saiya zamana baka da wani sirri na rayuwarka,saikayi da gaske zaka zama me kulawa kamewa da kuma rufe sirrinka,kome kayi abun tattaunawa ne da bada labari a bakunan al'umma.



        Ya bude idanunsa bayan ya gama wannan gajeran tunanin,ya tashi motarsa kana ya fusgeta yana barin wajen.



         Tun cikin motar ta kifa fuskarta saman cinyarta ta soma kuka,kukane dake tuna mata rayuwar da tayi a baya,yadda ta rabu da danginta 'yan uwanta,yadda aka tsareta a wani gida tamkar siyanta akayi,yadda ta rasa abu mafi qima tattare da ita wanda har yau bai dawo ba bazai kuma dawo ba,yadda ta samu rabon yaranta ta kuma rainesu cikin wahala har zuwa haihuwarsu.



         Kafin su isa tayi kuka sosai mai yawan gaske,don haka tana shiga dakinsu ta shiga bandaki ta watsa ruwa gaba daya,batason su fadwa su shigo su sameta cikin wannan yanayin bare su tambayeta,don sirrin rayuwarta ne,private life dinta ne da bai kamata wani yaji  koya sani ba.



        Rigar material ta saka mara nauyi sannan ta hada gashinta waje daya ta tufke,wanda harda shi ta jiqa tana fatan ruwan ya ratsa har saman qwalqwalwarta ko zata ji sanyi.



       Don ta hana kanta kowanne tunani saita janyo takardun data shigo dasu tahau dubawa,saidai ba gane komai dake ciki take ba,haka yaci gaba da kokawa da tunani da kuma yunqurin duba abubuwan dake jikin takardun.



       Bata jima da yawa ba su fadwa suka shigo,ta amsa sallamarsu tana qoqarin dora murmushi saman fuskarta,saidai ga duk wanda ya kalleta yasan akwai wani abu mai girma dake cin zuciyarta.



          Daga nasu bangaren duk da sun cika da mamakin hadin bilkisu da wannan babban dan kasuwar har kuma ta masa abinda ta masan wanda ya basu mamaki qwarai,su da sukasan cewa magana ma kadai dashi wani babban dama ne kuma abun alfahari ga mutum,saidai babu wanda ya tambayeta komai,suma sai kowacce ta kame bakinta,suka shiga sabgarsu data hada da wanka da cin abinci,abincin da bilkisu bata ma tuna dashi ba bare tabi ta kansa,hakanan tana zaune har suka kammala shirinsu sannan salwa daya abokiyar tafiyar tasu ta kalli bilkisun

"Mufa mun gama shiryawa" daga idanunta dakeson mata nauyi tayi ta dubesu,sam ta mance da agender zasu dan fita yau idan sun dawo daga taron,sai tasa hannunta ta dafe goshinta

"Banjin yau zan iya fita,kumin afuwa don Allah"

"Bb komai....saimun dawo to" salwan ta fada kana suka fice gaba daya abinsu.



        Fitar tasu sai taji kamar sun bata wani space ne,don haka ta watsar da takardun gefe,wadanda dama kamar dole aka mata karantasu,ta zame ta kwanta sosai zuciyarta da qwaqwalwarta na lulawa duniyar tunanin da taketa faman hana kanta,ta lura da alama tunanin kawai sukafi buqatar yi a wannan lokacin,ta yaya ya biyota dubai?"ya akayi yasan nan zata zo?,shine abunda yafi daure mata kai.



        Baiga laifi ko baiken kansa na sake barinta ta subuce masa ba sai daya koma masaukinsa,bacci ya qauracewa idanunsa,hankalinsa ya sake tashi da zuciyarsa ke raya masa idan chance dinsa na qarshe kenan fa daya bari ta subuce masa?,idan bazai sake ganinta ba kenan?,da qarfin tuwo ya samu da qyar ya cilla wannan tunanin gefe,yana fatan damarsa ba zata subuce masa ba.



       Ya kira abdulrashid ya shaida masa komai,ya danyi shuru yana nazari sai kuma yace

"Ina ganin ta dauki zafin da ba zata taba tsayawa ta saurareka ta hanyar lallashi da lallami ba...." Haka zuciyata ke gayamin abdul,inajin kamar saina dan saka tsauri da qarfi sannan zata yarda da cewar ta sanni ma totally,wannan shine mataki na farko"

"Haka nima nake tunani.....but kada ka saka tsaurin nan naka yayi yawa,saboda kada ya haifar mata da tsanarka fiye data baya" idanunsa ya lumshe yaba gyada kai,kalmar tsanar na neman masa barazana

"Na fahimta" ya fada in a low tune.



       Cikin daren ya gama tsarawa kanshi komai,ya gama tsarawa kansa komai ta fanjama fanjam,amma gobe dole ta tsaya ta saurareshi,dole ta yadda ta sanshi,dole yaji wani abu game da diyarshi jininshi.



       Tunda suka fita duk tsahon awannin tana nan kwance inda suka barta,kiran wayar da suka mata kan ta sauko qasa ta riqe musu leda daya dan Allah basason su shiga daki su sake fitowa ya sanyata tashi ta zauna dole,sai da tadan nutsu sannan tayi rolling mayafinta ta zura plate shoes dinta ta fito zuwa farfajiyar hotel din ta soma dube dube.



           Dai dai lokacin da KAMAL ke jingine jikin motar da suka shigo hotel din da ita,wayarshi riqe a hannunsa yana danne danne,yana tsaiwar jiran budurwarshi daya kawo hotel din,wadda ya daukota ne daga mazaunin dalibai dake cikin makarantarsu yarinyar ba tare da sanin iyayenta ba,suka kwashe sati suna sheqe ayarsu,yau kuma kwanakinsu ya cika zaya maidata.



       Kamar wanda akace daga kanka ya daga kanshi yana dan duban area din,yana son ganin ko samira ta fito?,saidai....maimakon yaga samira saiya hangi wata halitta daya jima yana neman inda take,wata halitta daya dade yana jin ita kadai ta dace da rayuwarsa,ita kadai ta dace ya aura,wanda a qalla shekara bakwai kenan da ganinta bai kuma sake sake ganin nata ba,shekaru bakwai baya a mexico.



       Ba tare da dogon nazari ko tsinkaye ba ya cusa wayarshi a aljihu ya kuma tunkareta,zuciyarsa fari tas yana jin wata annashuwa

"Hey baby" maganar data firgitata jin sautin namiji dab da ita,ta waiwaya a razane,sai kuma taja baya da hanzari tana binsa da wani irin kallo,yayin da yake qare mata kallo zuciyarsa na sake tabbatar masa da cewa eh tabbas itace,saidai wannan ta hadu sosai,ta hadu fiye da shekarun baya,ta sake zama babba kuma cikakkiyar mace fiye ma da yadda yakeso

"Ya kike baby?....sunana....." Da sauri ta daga mishi hannu tana qarewa yanayinsa kallo dake nuna gogagge ne kuma mai budadden idanu

"Inajin kayi makuwa ne,bani kake nema ba" daga haka ta juya da hanzari,gabanta na faduwa tsoro na cikata ta wuce ciki.



      Baiyi qasa a gwiwa ba ya bita,saidai kafin yakai har ta shige elevator,nan ya tsaya ya saki baki cikin takaici.



       Ya sani koda yasan dakinta bashi da ikon zuwa har sai da ixininta,to amma babu wanda zai hanashi zaman jiran sake fitowarta,tunda dai yasan ba zata dawwama cikin dakin ba,daga nan zuwa safiya zuwa yammacin gobe dole ta sake fitowa,don haka saiya fita,ya samu samira na jiransa

"Munyi da wani abokina zaizo nan zamu tattauna kan business dinmu,don haka ga mota nan zata maidaki.makaranta zamuyi waya" tabe baki tayi tana dubanshi

"Amma dai ba haka mukayi dakai ba,sanda ka daukoni kana rawar qafa shine yanzu zakace na koma ni kadai?"tsawa ya daka mata wadda ta bata tsoro,dole ta rufe bakinta tayi shuru sannan tayi yadda yace din.



         Gabanta na wani irin faduwa ta isa dakin,ta samu waje ta zauna tana rufe idanunta tare da sauraren bugun zuciyarta,wannan wacce iriyar tafiyace mara sa'a?,da wadanne irin mutane take gamuwa ne tunda tazo garin?,me yasa?,su waye saisu dinga binta haka?,tana wannan tunanin kiransu salwa ya shigo wayarta wanda shi ya katseta,ta bude idon nata tana amsa kiran

"Mun iso amma bamu ganki ba"

"Na sauko naga baku qaraso ba,na riga dana koma daki,banajin dadi ne sosai"

"Ayya yi xamanki,zamu samu wani cikin ma'aikata ya taimaka mana"

"Ok" kawai tace tana aje wayar sannan ta koma ta kwanta rub da ciki tana kiran sunayen Allah don gaba daya tunaninta a birkice yake.

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 58

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




   Kusan awa guda kenan yana tsaye qofar shiga da fita na hotel din yana jiran ganinta,wayarshi na hannunsa,lokaci lokaci yakan maida kanshi ya danna na wasu sakanni sannan ya sake daga kanshi idan yaji qarar fita ko shigar wani abun hawan.



      A irin hakanne motar da suke ciki ta durfafi gate din,yayi jinkirin daga kanshi wannan karon sai da suka kusa giftashi,a sannan idanunsa suka sauka kanta daga,tana zaune daga gefan hannun hagus saitin da yake,kafin yayi wani yunquri tuni sun harba titi,hakan ya sanya baiyi qasa a gwiwa ba shima ya tsaida taxi ya rufa musu baya don yana son cimmata a duk inda zata je.



     A qalla azeez ya kusa shafe rabin sa'a a bakin dakin taron,duk bayan wasu mintuna saiya duba agogon hannunsa yana jiran lokacin zuwan nasu ya cika,dubawa ta qarshe agogon ya nuna masa nan da mintina biyar zasu iya isowa,hakan ya sakashi fitowa daga cikin hadaddiyar motar tasa,ya haye samanta ya zauna,ta saitin daya tabbaatr idan ta fito babu lallai ta ganshi,saidai shi yana iya ganinta.



       Dukkan wata mota da zata shiga kota fita tana kan idanunsa,sanye yake da wasu baqaqen qananun kaya wadanda aka yiwa rigar manyan rubutun manyan haruffa da launin jaa,hakanan rufaffen takalmin qafarsa adon jiki gami da zaren jiki duka jaa ne,hatta da fuskarshi ya toshe qwayar idanunsa da baqin sun glasses,hannayenshi harde a qirjinsa,fuskar nan babu walwala ko misqala zarratin,sak ya fito a babban boss.



    A hankali motar tayi parking daura sa tashi ba tare data kula da waye a wajen ba,itace qarshen fitowa saboda tsaiwa da tayi ta sallami me abun hawan,ta fito tana saqala jakarta kamar jiya hannunta riqe da takardu.



     Cikin taku na nutsuwa ya sauko daga baya motar ya dosheta

"Assalamu alaikum,da fatan kin wayi gari lafiya" kalmar daya fada kenan saitin kunneta,wanda hakan ya sanyata zabura har takardun hannunta suna watsewa a wajen,kana ta juyo suka hada idanu,duk da cewa ita din bata iya ganin qwayar idanunsa,amma shinyana iya ganin tata,qwayar idon data masa wani mugun kyau,ta kuma yi tasiri cikin gangar jiki da zuciyarsa.



   Baki ta bude da niyyar jefa masa magana amma sai ya rigata

"Kada kice komai,don tuni na soma haddace kalaman da kike jerantawa kullum kina bitar gayamin,idan kikace baki sanni ba inajin kamar kina kashene ni bilqees".



      Lokacin da yakai qarshen kalamansa lokacin kamal ya iso,yasauka ya sallami mai motar kana ya juyo da niyyar tunkarar wajen,saidai me?,ga mamakinsa ita ya hango tsaye da yarima abdul'azeez din,abunda yaso yadan daure mishi kai,saidai kuma daya tuna saboda shi dama ya soma ganinta sai mamakin nasa ya ragu,amma abun tambayar dama har yanzu suna tare?,wacce irin alaqa ce haka mai girma tsakaninsu da tayi lasting har tsahon shekaru bakwai?,tambayar da yayiwa kansa kenan,yana dan sake matsawa kusa dasu gami da zuba musu idanu.



      Harara bilkisu ta balla masa,saiya sake matsawa dab da ita yana son kashe duk wanu karsashi nata da kaifin idanuwansa,bayan ya zare glass din fuskarshi,har tana jin qamshin mayen turarensa sosai fiye da da.



       Wannan matsawar ta darsa wani abu a zuciyar kamal,shawara ce kai tsaye daga wani sashe na zuciyarsa,wanda shawarar tayi masa dari bisa dari,tabbas idan ya aiwatar da abinda ranshi ke raya masa burinsu na shekara da shekaru zai cika cikin qanqanin lokaci,babu jinkiri ko kuma daga qafa cikin hanzari ya zaro wayarsa ya kuma shiga camera.


  

      Ga bilkisu kuwa ganin yadda ya matse tazarar dake tsakaninsu sai kawai ta juya da sauri da niyyar barinsa a wajen,don bata jin zata iya ci gaba da tsaiwa dashi yana mata famin wasu sabbin al'amura da suka riga suka shude mata,duk da akwai burbushi cikin ranta,wanda dama shi ciwo ko rauni koda ya warke yakan bar gurbinsa jikin dan adam.



     Caraf yayi yunqurin kama mayafinta,saidai maimakon haka sai yayi nasarar kama hannunta,tattausan singalalin hannunta ya ratsa tafin hannunsa,kamar yadda lallausan tafin hannunsa ta jiyo duminsa har cikin jijiyarta.



     A fusace ta waiwayo tana watsa masa wani irin kallo

"Ka sakeni malam"

"Kiyi haquri,cikin girmamawa da lallashi kije muyi magana ta fahimtar juna ni dake"

"Idan naqi kuma fa?" Bai barta kalmar ta gama fita daga bakinta ba ya sunkuceta gaba daya ya nufi motarsa,abinda zuciyarsa ta jima tana gaya mishi daya aikata,abinda ya jima yana tunanun shibe mafita guda daya da zai kebe da ita,ya kuma bi hanyar data kamata don ta saurareshi.



      Wannan daukar nata da yayi shinya qarawa kamal qaimin daukar hotunansu a hakan lokacin da take yunqurin kufcewa,saidai ingarman sadaukin yariman ya nuna mata qashun sam.ba daya bane,hakanan akwai banbanci mai girma tsakaninsu,yayin da su fadwa daje tsaye dan nesa kadan dasu suna kallonsu cike da sha'awa,saboda yadda sukaga sunyi matuqar yi musu kyau suka kidime gaba dayansu,ganin ya sanyata a mota gamida rufewa,ya kuma zagaya yana niyyar shiga sit dinsa,da sauri salwa tabar fadwa anan ta shuga ciki kiran dr adam,wanda ya rigasu yin gaba,hakanan babu yadda baiyi dasu su taho tare ba amma bilkisu taqi,ta gaya mishi ya riga yasan tsarinta ai tun bayau ba,tun a brasil.



     Saidai fa dr adam yazo a makare,don ko qyallin motar yarima basu samu ba sai sawun tayar motar,fadwa ke shaida musu tuni ya wuce.



    Tsaye sukayi cirko cirko cikin tashin hankali kowannensu,duk da cewa he's familia amma kuma basusan ina zaya kaita ba,kuma kusan a gaban idanunsu ya dauketa cikin qarfin tuwo ya sanyata a motar,hakan ke nuna ba tafiyar dadi bace kenan bare suce dason ranta akayita.



    Hankalin dr adam ya sake tashi sanda fadwa ke gaya mishi daukanta yayi da hannunshi,tashin hankalinsa ya hadu ya cakudu da kishi mai tsanani,har baisan ya rufe su fadwan da fada ba kamar ma sune yariman,saiya fidda wayarshi ya soma jera mata kira babu qaqqautawa.



   Sosai take mishi hayaniya da masifa cikin motar,ranta a matuqar bace ganin yadda ya maidata kamar wata 'yar tsana,hakanan ya zubda mata mutuncinta da qimarta a idanun mutanen da suke ganin girmanta.



     Idan set din da suke kai ya tanka to yarima ya tankata,yasan kome zata fada yana fita ne tare da zafi da qunar dake cikin ranta,maganganun da take fada tamkar tana samun wani dan qaramin sauqi ne cikin zuciyarta,shi yasa ya zabi yayi shuru,ta fadi dukkan abinda takeson fadar,matuqar hakan zai sama mata salama cikin ruhinta.



      Tafiyar minti arba'in har suka iso masaukinsa batayi shuru ba,iya gajiya bakinta ya gaji,wanda isowarsu wajen ya sanyata dole yin shuru.



    "Ranki ya dade sauka muje" ya fada a tausashe cikin nuna girmamawa,da idanu takebin wajen da kallo,akwai jama'a nata kai kawo kowa yana sabgar gabanshi,saita dauke kanta gami da jan wani dogon tsaki

"Ba zani ko ina ba....ka mayar dani inda ka daukoni"kai ya girgiza cikin matuqar rauni

"Kiyi haquri,amma bazan iya maidake ba,inason kasancewa dake,inason inasan ina diyata take,yaya ta rayu ke da ita tsahon wadan nan shekarun?"

"Zamu shekara anan kenan" ta sake fada a harzuqe,kai ya girgiza

"Ba zamu shekara ba,saidai xan daukeki da hannuwana kamar daxun zuwa ciki,inda zamufi tattaunawa cikin nutsuwa" ya fada yana cire sit belt din dake daure dashi,da alama yana shirin daukar nata kamar yadda yace kenan.

"Idan ka daukeni zan maka ihu,in kuma gayawa duniya satoni kayi" murmushin gefan baki da yayi masifar qara masa kyau da kwarjini yayi

"Ko zaki shekara kina fada babu mai yadda dake...."

"Saboda kana taqama kaidin me arziqi ne?,kana da madafan iko da sarauta,kana da dukiya,Ka siye kowa?....ni kuwa talaka ce ba diyar kowa ba?" Ta jefeshi da tambayar cikin katsar numfashinsa ba tare data bari yakai qarshen maganarsa ba.



      Qaramin murmushin ya kuma saki ba tare daya shirya ba,duk da kalamanta qona masa zuciyasa sukayi,yasan ta fadi daya daga cikin abinda ke damunta ne a zuciya,kai ya kada

"Ba wannan ba,ke zakiso duniya ta kira uban 'yarki da barawon mutane?" Sai kalmar tayi mata gingirin aka,ta kuma sake maimaita cikin zuciyarta,take fuskar amatu ta dawo cikin idanunta,sai taga kamar amatun ce a gabanta sanda ta fuskarshi,bai sake cewa komai ba ya sanya kai ya fice.



     Har ya bude qofar tayi hanzarin ce masa

"Dakata!,kada ka soma tabani" saiya tsaya din kamar yadda tace ya goye hannuwansa a qirji yana kallonta,murmushi da baisan dashi ba yana subucewa daga fuskarshi.



   Banzar harara ta jefa masa,bayan tayi kamar ba zata fito din ba,sannna taja qafafunta ta fito tana jan dogon tsaki kamar zata tsinke harshenta.



      Tunda ta shiga kanta yana a qasa,duk yadda yakai gason tayi magana amma bata daga kai ta dubeshi ba bare tace mishi uffan,tsahon wani lokaci haka ya tashi ya miqe ya barta,babu jimawa ya soma jere mata kayan motsa bakinkala daban daban.



    Wani irin bacin raine ya cikata,me yake nufi?,an gaya mishi yunwa ce ta kawota ko mene ne?,ji tayi ba zata iya shuru ba tare data tanka mishi ba

"Ka maidani inda ka daukoni,don bance maka yunwa nakeji ba bare ka jere min wadan nan kayan a gabana" ta fada cikin matuqar hade rai,murmushi ya sakar mata yana jifanta da wani irin kallo

"Baqonka abun girmamawa ne a wajenka,duk da cewa kinqi cewa komai dani kinqi bani hadin kai....ko meye nayi miki a rayuwa babu abinda zai sanya ki fahimceni,idan na miki dai dai ko akasin haka,da gangan na miki ko ba cikin sanina bane sai zama mu tattauna,karki manta zuri'a ta shiga tsakaninmu,dole mu nemi makomarta,wanda bazai taba yiwuwa ace mace tayi ciki ita kadai ta haifa ba ba tare da uba ba,kiyi tunani,akwai wata rana da zata zo zata buqaceni,zata buqaceni koda baki so,zata buqaci sanin waye ni,zan baki mintina kiyi tunani akai"saiya miqe yana juyawa

"Bana buqatar yin wani tunani akan komai,na jima ina tunani akai,hakanan qwaqwalwata ta dade tanayin tunanika wadanda suka jima da gajiyar da ita,ta nemi hutu hutu irin na har abada,don haka bata buqatar yin tunani kan ire irenku da matsalar daya shafeku" murmushi kawai ya juyo ya jefeta dashi kana yayi gaba zuwa uwar dakin dake manne da falon,yayin da ita kuma ya bishi da harara,tana ganin baiken kanta da bata gwada ma yi masa ihun ba tun a can,komai ta fanjama fanjam.



    Yana shiga dakin ya tura qofar yana dafe goshinsa gami da sauke numfashi,ba shakka ba qaramar badaqala bace a gabanshi,amma duk yana ganin komai zaizo masa da sauqi matuqar zata dinga tsaiwa tana saurarensa,koda ba zaga amsashi ba kamar yadda tayi masa yanzun.



       Numfashi ya furzar mai dumi daga bakinsa,ya soma takawa zuwa cikin dakin,dai dai nan wayarshi tayi tsuwwa,ya zarota a kasalance yana duba mai kiran,fulani ce,don haka cikin girmamawa ya daga wayar yana karawa a kunnanshi.



      A ladabce ya gaidata,sannan ta isar da saqon da takeson isarwa din

"Wai sai yaushe zaka dawo ne?,cikin satin sama upper week za'a gabatar da hawan daba na al'ada fa,kowa da kowa zaizo,dukkan wani wanda yake jinin masarautar kaisa ne wannan karon zai halatta,harda wadanda basa a qasar,kasan kuma kusan shekara biyu rabonka da zuwa,ya kamata a wannan karon ka halarta,saboda inason koda yaushe ka dinga zama a hannun daman mai martaba,saboda shekaru suna sake turawa,ya kamata ace ana ganinka a dukka al'amuransa,tunda bashi da kamar yakai"

"Inason nima na dawo,saidai uzurin da nakeyi din ne yanzu ma na fara bare ayi maganar kammalashi"

"Wanne irin uzurine haka?" Kanshi yadan shafa yana duban qofar falon daya barta

"Kidai tayani da addu'a ammi" ga zatonta sha'ani ne daya shafi harkar business dinsa,wanda indai ta fannin ci gaban da daukakar da yake samune kulli yaumin hakan na mata dadi,saidai kuma ta wani fannin tana da damuwa sosai akanshi yariman,akwai abubuwa da yawa na rayuwarshi da take ganin bai dace da ra'ayinta ba,kamar yadda yake wofintar da matarsa da lamuranta,bai fiya damuwa da sha'aninta sosai ba,yadda yake jimawa bai waiwayi masarauta ba,bare abokan adawa su dinga yawan ganinsa,suna kuma tunawa da matsayinsa tare da tunasar da kanau cewa wataran akwai mai amsar sarauta,wataran zata amsa sunan 'yar sarki jikar sarki matar sarki kuma uwar sarki,amma tana ganin tunda har ya cika mata dukkan buri da wani sharadi data kafa masa,ya kamata ta qyaleshi hakanan kuma yayi rayuwarshi yadda yakeso shima,akwai lokacin da komai zai daidaita,akwai lokacin da zai canza wasu abubuwan a qashin kanshi

"Shikenan,Allah yayi jagora"

"Amin summa amin,godiya nake" daga haka ta sauke wayar tana sakin ajiyar zuciya.



      Tana daga kai suka hada idanu da afnan,saita dan tsareta da idanu kamar yadda ta fahimci itama tun dazun ita take kallo,ta rasa dalilin sauyawar afnan din tun dawowarsu daga brasil

"Lafiya kike?" Ammin ta tambayeta tana kallonta,saita dauke kanta ta maida kan wani qaramin littafi dake hannunta,a son ranta mama sodangi ta barta tayima ammin magana,kullum idan ta tuna da abun sai taji zuciyarta na azalzalarta ta tari ammi da maganar,amma mama sodangi ta gaya mata akwai lokaci,yin maganar a yanzun ta hangi babu abinda zai haifar sai tabarbarewar al'amuran da suke saka ran gyaruwarsu.



      "Babu komai....kawai,ina tunanin,anya ba wani abu wanda ba dai dai muka aikata ba Allah ya jinkirta min aure na?" Ta qarashe maganar tana zube idanunta kan ammi fulani.



       Hakanan taji maganar banbarakwai,ta kuma rasa muhallin da zata aje maganar,cikin rashin fahimta tace

"Kamar yaya afnan?,me kike nufi?" Wani murmushi mara ma'ana tayi tana kada kai

"Babu komai,kawai inajin hakanne cikin raina,ban sani ba koba dai dai bane" shuru ne ya ratsa tsakaninsu cikin falon,ta saka ammin cikin tunani,wanda kafin ta fita ita kuma ta miqe da litattafanta ta wuce ciki,hakanan sai ammin ta bita da kallo harta bacewa ganinta.



      Ita daya tasaki nannauyar ajiyar zuciya,sai mafarkin da tayi jiya ya fado mata,mafarkin yarinyar sosai,yadda ta bugeta a asibitin kuma taci gaba da tafiyarta,abinda ta sake gani kenan,saidai wannan karon ta tsaya ta kalleta sosai a cikin mafarkin kafin tayi gaban abinta,idanunta ta rufe tana girgiza kai,tafi zargin saka abun da tayi cikin ranta ne shi ya sanyata mafarkinta a jiyan,ko kuma kewar suhaima ce.



      *_KAMAL_*



       Saboda tsabar zumudi bai iya bari ya isa gida ba ya koma cikin motarshi ya zauna sosai,sannan ya bude data dinsa bayan yahau watsapp ya tura dukka hotunan wa hajiya fauziyya mahaifiyarsa,kana ya sauka ya lalubi lambarta ya kirata.



     Sai data kusa tsinkewa sannan ta daga,zuwa lokacin har ya qagu

"Wai ina kika shiga ne mom?"

"Baqi gareni ban lura da kiran naka ba,saida husna ta miqo min.....ya akayi?"

"Babbar jarida zan siyar miki...sa'annan babbar nasara dake alamta mana cikar burinmu nan da wasu 'yan kwanaki" baki ta tabe

"Nina yanke qauna dakai kamal,tunda har yau burinmu na shekara bakwai ka kasa cika mana shi,bayan mun sanya dukka burinmu da fatanmu saman wuyanka" wata banzar dariya ya saki sa'anan yace

"Idan nace miki nan da sati daya burinki na farko zai soma cika kafin zuwan na biyu zaki yarda?" Kai ta girgiza cikin nuna rashin tabbas

"Wai kana nufin bacin sunan yarima a duniya da kuma masarauta gaba daya?,kai anya kuwa,abun da kamar wuya,mutumin daya wuce saninmu a yanzu,ka kasa komai a sanda yake da qananun shekaru kuma shidin ba kowa bane a idanun duniya bare yanzu?"

"Wait mom....jeki watsapp dinki,amma da zarar kin kammala duban saqon...ina da buqatar jin alert na kudade masu nauyi a accnt dina kafin mu dora daga inda muka tsaya" tsaki taja

"Da gaske kamal lalacewa kakeson yi,banda haka duka duka yaushe mahaifinka ya tura maka kudade masu yawa?"

"Mom...wai kamata ta yaya bazan buqaci kudi ba,komai nawa fa saida kudi nake iya tafiyar dashi"

"Kamar wani ya hanaka tsaida hankalinka ka kammala karatunka,koka kama kasuwancin babanka da kyau,ba irin yadda kake riqon sakainar kashi dashi ba a yanzu"

"Yanzu mom na faranta miki amma zaki sakamin da haka?" Tuna batun da sukeyi ne ya sanyata cewa

"Sorry son,bari na duba" daga haka ta katse wayar,sai shima ya kashe tashi yana qunquni gami da kumbura,ya aje wayar gefe yana zaman jiran ji daga gareta.



     A hankali sai kuma yaji kamar bai kyautawa bilkisu ba idan ya bari fuskarta ta bayyana a idanun jama'ar masarautar a matsayin wata lalatacciya mai mummunan aiki,amma saidai kuma.....babu wata hanya data rage masa wadda zai iya samunta ta ruwan sanyi a amatsayin matarsa saita hakan,saboda kallo daya ya yiwa idanun yarima ya karanci wata iriyar soyayya mai kaifi da yakewa yarinyar,wanda da alama shidin baisan tana fita daga idanun nashi ba....da wannan tunanin ya kwantar da kujerarsa yana jiran kira ko saqon kudi daga mom din tasa haj fauziyya.....

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 59

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



       Tun kafin ta gama ganin hotunan ta miqe tsaye cike da zallar farinciki,haqiqa ba shakka lokaci yayi,lakaci yayi na tarwatsa fulani da iyalanta,lokacin da zasu soma cimma burinsu kan sarautar qasar kaisa yazo,irin hotunan da sukeso,irin hotunan da suke da buqata,wadanda komai bincike idan za'ayi zai tabbatar da cewa na gaske ne,ba hadin computer ba.



       Batayi wani jinkiri ba bayan ta gama bin hotunan daya bayan daya da gaggawa ta kira kamal,shima baiyi jinkirin dagawa ba,tunda abinda yake jira dama kenan

"Haqiqa lokaci yayi,kayi qoqari sosai kamal,kayi qoqari ba kadan ba,duk da naso ace sunfi haka muni amma hakanma babu laifi,yanzu meye abu na gaba?,ta yaya za'ayi hotunan su shigo masarauta?"

"Kudina tukunna mom"

"Dalla can mayen kudi kawai,dan banzan yaro mai idanun cin naira,zan tura maka 100k"

"Kacal?"

"Au kacal ne ma?,kana zaune babu cas babu as ka samu 100k amma ka raina"

"Amma mom wannan ba aiki nayi ba?"

"Aikin da zaka fi kowa farinciki dashi ba,duk badon kai nake komai ba?,idan komai yayi daidai waye zai haye karagar?"

"Oh yeah,naji shikenan"

"Yauwa"

"Yanzu mom,hotunan ya kamata ne ace an wankosu da yawa,an kuma zuzzubar ko ina lungu da saqo na masarautar,yadda kowa zai samu gani"

"Hakane....amma so muke su isa gaban idanun ubanshi,kasan yadda jamar masarautar ke qaunar abdallah,za'a iya qin kai masa saboda kada ranshi ya baci....amma na tuna wata dabara....adama,ita ya kamata ta miqa hotunan zuwa gareshi,don banason aga fuskarsa a wajen,bare sunanka ya baci nan gaba,kafin lokacin da itama adaman aiki zai biyo ta kanta"

"Good,saiku qarasa tsara yadda za'ayi,nidai naji alert"

"Naji ubana.....inajin aikin nan lokaci mafi dacewa da farashi shine,lokacin babban hawan daba na qasar kaisa,lokacin da baqi zasu cika gidan,yadda maganar zatafi fantsama lungu da saqo na qasar kaisan.....inason ka halarci hawan kaima"

"Zanzo" ya bata amsa don akwai sabuwar yarinyarshi da yayi a katsina,dama yanason zuwa su hadu,da wannan mummunan shiri da qullin sukayi sallama kowa ya aje wayarsa cike da farinciki,saidai haj fauziyya ta kasa zaune ta kasa tsaye,sai data lalubi adama don ta mata albishir.



     Duk da ba cikin yanayin take ba amma hakan bai hana idanunta bin falon da take a zaune da kallo ba,tunda take bata taba ganin dakin hotel mai kyau da tsaruwa irin wannan ba,idan kana ciki ba zaka tsammaci cewa a hotel kake ba,saidai daga ganin yanayin yadda yake sake sosai a wajen dakin ya zamar masa kamar nasa ne,irin abin nan da masu hannu da shuni kanyi,su riqe daki ya zama na saukarsu ne duk sanda suka sauka a qasar,koda basu nan ba za'a sanya musu kowa ciki ba,saidai fa suma zasu dinga biyan kudi kamar suna kwana.



      Abinda yasa ta gane hakan,qananun frames frames dake maqale a bango,wadanda sukafi kama da abun award,shaidar girmamawa da akan baiwa mutum sun kusa guda goma.



       Janye idanunta tayi a hankali tana jan tsaki,wanda yayi dai dai da fitowar yariman daga daki,sarai yaji tsakin amma sai yayi kamar baiji din ba.



      Wannan karon sanye yake jallabiyya mai azabar kyau da taushi,wadda duba daya zaka mata kasan kudinta ba kadan bane,yadda take da kyau haka tayi masa wani azababben kyau,ta fidda kyanshi mai sanyin nan da tafi da zukatan mata da yawa.



      Ganin ya nufi qofa yana shirin fita ya sanyata miqewa da hanzari tana fadin

"Malam dakata...bafa kaya ka ajjiye ba"

"Tunda muka hadu dake bilqees kike kirana da malam,kin manta sunan mijinki kuma uban 'ya'yanki?,abdul'azeez abdallah,idan kin manta kuma ba laifi kina iya kirana da abban baby" ya bata amsa yana riqe da handle din qofar,yayin da take nufo qofar da sauri tana son cimmasa ta samu nasarar fita,saidai kafin ta qaraso yaja qofar ya rufe.



       Koda ta isa taja sosai taqi koda motsi bare batun buduwa,hakan na nufin kulleta yayi kenan?,bacin rai goma da ashirin,saita dafe goshinta da tafin hannunta tana jin kamar kuka zai qwace mata,babban takaicinta batasan yadda akayi ta manta wayarta a motarshi ba,da kira daya zata yiwa adam ta tabbatar babu bata lokaci zai bayyana a wajen,dolenta ta koma da baya ta zauna,tana wassafa irin babban abunda zata masa wanda zai tursashi barinta ta tafi,bayan yayi zuciya gaba daya ya bar bibiyar rayuwarta ita da yaranta.



       Minti a qalla takwas ya bude qofar ya shigo,yana dauke da jakar tata,saidai daya hannun nashi wayarta ce,yake riqe da ita,wadda yana shirin maida qofar ya rufe ta dauki tsuwwa.



     Ita dake zaune da shi da wayar ke hannunsa dukka hankulansu ya karka ga wayar,sunan Dr adams daya gani na yawo saman screen din nata shi shi ya sanya qwayar idanunsa soma sauya launi nan take,saboda sanda yake qoqarin dauko wayar ya lura da tarin miscal da irin wannan sunan,wane kishi na masifa yaji ya motsa masa,saiya bar abinda yakeyi din ya daga wayar ya kara a kunnenshi

"Sweet angel.....ina kika shiga haka?,ina ya kaiki,kin barmu hankali tashe munata nemanki" kalaman da suka soma dukan kunnenshi kenan,cikin wata iriyar kakkausar murya fuska kamar hadarin gabas,ya dawo da wannan kamar tashi,kamar bashine ke magana cikin taushi ba a dazun yace

"Kada ka sake kiranta,domin tana tare da mijinta,idan kuma ka qiya,ba shakka tsautsatsauran hukunci zai hau wuyanka,qaton banza kawai" ya cikashe da tsaki yana sauke wayar daga kunnenshi kana ya datse kiran.



       Niyyarsa ya shiga cikin wayar ya sanyata a flight mode,saida me?,hoton amaturrahman da abdurrahman dake saman wayar a matsayin homescreen walpaper dinta yaso tafiya da numfashinsa,iskar dake fita ta kafofin hancinsa ta masa qaura na wucin gadi,har ya dinga kokawar nemota saboda barazanar tafiya da take gaba daya.



     Bai ankara ba yaji am wafce wayar,kana muryarta ta maye gurbi

"Wai waye kai da zaka dinga gayawa mutane cewa kaidin mijina ne?,wanne irin mutum ne wai kai ehenn?" Ta fada tana tsaye a gabanshi.



       Sam bai fahimtar me take fada,tunaninsa ba'a kan wanann yake ba,tuni qwaqwalwarsa tayi nisa wajen gaya masa

"Yaranka biyu ne,tabbas 'yan biyu ta haifa maka" baisan lokacin daya rarumota gaba daya ita da wayar ba ya sanyata cikin jikinsa ya matseta gam,bai damu ba,hakanan bai kulaa da yadda take kai mishi duka tako ina ba gamida yi masa gargadin ya saketa.



      "Alhmdlh,alhmdlh" shine abinda yaji bakinsa yana maimaitawa,kafin daga bisani yace

"Na godewa Allah da bai qyaleni na tafi a yadda tsarin yazo ba,na godewa Allah daya sanya wani lamari mai girma a zuciyata game dake,na godewa daya hukunta min haka cikin rayuwata,cikin sati guda kacal da nisantarki da rayuwarmu....ashe ke din wata alkhairi ce da kika shigo rayuwata,wanda dukkaninmu bamusan da haka ba?,ashe har yara biyu na bari a jikinki ba yare dana sani ba?" Ya fada yana dora hannunshi saman cikinta yana shafawa,wanda cikin hanzari ta buge hannun nasa qwalla na sauka saman kuncinta,saboda yadda ya riqeta tsam,kuma babu alamun zai saketa,ga kalamanshi dakeson dawo da komai sabo cikin rayuwarta.


     Birkitota yayi suna fuskantar juna,yana duban tsakiyar idanunta da nashi idanun da suka dade da sauya launi,wannan karon dukka kafadunta ya kama ya riqe sosai yana ci gaba da maganarsa

"Ashe har yara biyu Allah yayimin kyautarsu ba tare dana sani ba,suna rayuwa a wata duniyar ina rayuwa a tawa duniyar daban?" Bata ankara ba ya zube gaba daya a gabanta saman gwiwoyinsa yana riqe da dukka qafafunta

"Kimin alfarma ki bayyana min 'ya'yana,koda zakimin wani hukuncin na yarda zan karba...." Da qarfin tsiya cikin kuma sauri ta janye qafafunta daga gareshi,duk yadda taso nuna juriya da jarumtarta amma ta gaza,don tuni kuka mai nauyi da qarfinya qwace mata

"Wadanne 'ya'yan?,ai kai da dui wani makusanci naka ku saka a ranku cewa baku da wasu yara a duniya sama da wadanda ke gabanku,yaran da tun a ciki kuka baiwa banza a jiyarsu?,kuka yiwa duniya kyautarsu?,dasu rayu da kada su rayu ba damuwarku bace,kuka qaryata wanzuwa da samuwarsu,to kamar yadda kuka qaryata samuwarsu,inason har duniya ta nade kuci gaba da raya wannan cikin ranku,don har abada ba zasu taba zamowa naku ba".



     Ta soma yunqurin zame kafadunta daga hannunshi,tayi nasara saidai kuma ya kama hannayenta da sauri ya saka cikin nashi

"Ba laifina bane bilqess,anfi qarfina ta hanyar da sabawata zai iya zama babbar illa ga rayuwata...."

"Da bai zama illa ga rayuwarka ba yanzun ka gani ya zama illa ga jininka ko?...." Kai ya gyada

"Tabbas hakane....amma ki yarda dani....bani da laifi,koda ina dashi laifin nawa kadanne,nasan zakimin uzuri matuqar kika zauna kika saurareni...." Hannayenta ta zame ta qarfin tuow,ta cimma nasara kuwa saboda jikinsa dake a mace laqwas,yana jin zuciyarsa na masa wani irin zafi zugi da kuma quna

"Kada ka sake tabani,ka matsa daga kusa dani,sannan ka budemin qofa na koma inda na fito,idan kai bakasan illa da zunubin haka ba ni na sani"

"Babu wata illa,hakanan babu zunubi a kanmu,DOMIN KUWA KE MATATA CE" Idanu dukka ta zaro,don ga zatonta yabar wannan maganar ne,ya kuma fadeta ne a baya saboda kawai ya samu damar tsaidata.



     Idanunsa cikin tsakiyar nata qwayar idanun,kai ya gyada mata yana mai sake son tabbatar mata

"Yes...har yanzu ke matatace" nata idanun ta janye saboda yadda yake kallontan ya mata nauyi da yawa,ta saki wani malalacin murmushi da batasan yadda akayi ta qwaqwaloshi bama,ba tare da tace komai ba ta soma takawa zuwa bakin qofa kana ta soma bashi amsa

"Kabar wannan tatsuniyar kazo ka budemin qofa,domin koda jikina dukka kunne ne bazan taba yarda da wanna tazo mu jita din ba,koda zan yadda da kowacce ta tsuniya takan wannan kam bata da gurbi ko kuma muhalli" takowa yayi zuwa dab da bayanta ya tsaya

"Ba tatsuniya bace...hakanan yadda na fadi haka maganar take,inda shaidu har guda uku,wadanda na tabbatar koda a gaban alqali sun isa su zama shaida" saiya kewayeta ya bude qofar,ba tare daya dawo ba yayi gaba.



     Jinta take kamar mutum mutumi,jinta take kamar ba'a duniya ba,qafafunta kamar ansa wani abu mai qarfi an bubbuge mata su,babu qwari sam tattare da ita haka itama ta taka ta fice.



        Tun daga wannana rana ba ta sake fita wajen taron ba,wuni take kwance a gida,tana jin tamkar bata da lafiya,inda Allah ya taimaketa dr adam yana tsaye akan komai,rashin zuwan nata na sauran kwanakin bai zame mata wata illa ko asara ba,kusan duk abinda aka gudanar zata ji daga wajensu tare da gamsashen qarin bayani da 'yan qananun jotting dake sake bata haske.



       Zamanta a dakinsun sai yafi mata kwanciyar hankali,saboda tasan babu ta yadda za'ayi ya iya ganinta ba tare data fita ba,tana kuma da yaqinin yana can yana fama da zirga zirgar neman ganinta,don ta fuskanci halayyarsa cikin wani qanqanin lokaci.



        Saidai wani abu dake bata mamaki saqonnin gaisuwa dake tafe a jejjere a wayarta da wata baquwar number da batasan ta waye ba,saqonni ne dake nuna zallar kulawa da kuma bege,bata taba damuwa tasan lambar waye ba,iyaka idan ta karanta ta goge taci gaba da sabgarta.



       Ta fannin yarima bai boyewa azeez komai ba ya shaida masa,ya sake qarfafa masa gwiwa tare da fatan nasara.



       Tabbas rashin ganinta ya sanyashi a damuwa qwarai,har yanzu baikai ga ji ko samun dukka abunda yake da buqata ba,saidai abu biyu na debe masa kewa da kwantar masa da hankali.



     Abu na farko ya riga da yayi connecting wayarta da nashi,duk sanda ta tashi barin wani gari ko wata qasa zuwa wata zai sani,hakanan da zarar ta koma brasil a sauqaqe zai ga adress din inda take zaune,ta wannan fasahar kuma ya samu damar shiga gallery dinta,ya debi dukka hotunanta wadanda sukayi masa,nata dana amaturrahman da abdurrahman.



       Ranar kwana yayi yana kallonsu,ya kalli hotunan kamar zasu gudu su barshi,ya kallesu kamar ba gobe,ya kallesu kamar mai shirin yin sallama da duniya,hakanan duk tsananin jarumtarsa dakiya gami da juriya amma ya gaza daurewa wannan karon sai daya zubda qwalla sanda yake kallon hotunan yaran,yake kallon tsantsar kama ta ban mamaki dake tsakaninsu,babu wanda yake hangowa a wannan lokacin sai fulani,ko yaya zata karbi lamarin?,ya zata kaeshi?,da wanne irin ido ko zuciya zata amshi yaran,tabbas ba shakka a wannan karon ya shirya tara dama qalubalantar ko meye zai faru,ko meye zai biyo baya.


¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



     Safiya ce mai cike da wani irin ni'ima da lullumi,shi daya qwal cikin dakin yana maqale da waya a kunnenshi yana amsa kiran da safwa tayi mishi,yayin da yake ta cike wasu takardun kwangiloli,ayyukane suka taru sukayi yawa kan harkar kasuwancinsa,amma ya tare komai ya kasa komai,bilkisu ta tsaida komai cak cikin rayuwarshi,yana lissafe da yau kwanaki bakwai rabon daya sanyata a idanunshi,yanajin matuqar wasu kwanakin suka sake biyo baya,tabbas zaiyi dukkan mai yiwuwa ya isa har dakin dake masaukinsu cikin hotel din,saboda zuciyarsa ta soma gazawa.



       Maganar da safwa tayi ne yasa yadan dakata da rubutun da yakeyi

"Ina saka ran ganinka a hawan daba na wannan shekarar.....kowa da kowa zaizo,nima wannan karon zanzo,inason ganinka don nayi kewarka".



      Yasan cewa tana sonshi,hakanan tana da muradin kasancewa tare dashi,saidai wasu abubuwa da suka sanya sam zaman nasu bai fiya armashi ba,hakanan akwai tsarukansu da sam basuyi dai dai ba,bakuma su dace da ra'ayinsa ba,amma ko meye yasani cewa tarsa ce dai,hakanan tana da haqqi a wuyanshi,don haka cikin yanayi na kwantar da hankali yace

"Kada ki damu,wani babban aiki ne ya tsareni anan din,wanda bani da tabbacin zuwa din,saidai da zarar komai ya kammala zan taho ayi komai dani in sha Allahu" murya ta kwabe sosai tana jin babu dadi

"Kace kawai ba xakazo ba" kai ya girgiza

"Ba haka bane,babu tabbacin rashin zuwa kamar yadda babu tabbacin zuwan" xatayi magana ya dakatar da ita,sakamakin wani haske da sauti d wayarshi daya ware ta musamman tayi,yace zai kirata yana zuwa.



       Alama ce dake nuna mishi cewa bilkisu ta isa filin tashi da saukar jirage,hakan na nufin zata sake barin qasar,baida matsala yana da jama'a dake aiki a filin jirgin,don haka yasa aka laluba mishi inda jirgin da zai tashi yanzu ya nufa,aka tabbatar masa brasil ne.



      Already yana da visa dinsa,saboda haka yasa aka duba mishi jirgin da zai sake tashi zuwa qasar,aka tabbatar masa saidai gobe da yammaci,duk da ba haka yaso ba amma dole haka ya haqura,ya shiga shiri cikin zafin nama gamida shirya dukkan abinda yake saka ran zai wanzar idan ya isa brasil din.



      Cikin shiga dake nuna tsantsar alfarma isa mulki da kuma qasaita take nufar sassan mai martaba,wanda ta samu kira ne na musamman daga gareshi.



        Daga ita sai manyan hadimanta guda biyu,kubra da yaha,wadanda suta zaba suyi mata rakiya.



       Sau uku tana wuce gungun mutane wadanda dasun hangota suke zubewa su miqa mata gaisuwa,ta amsa musu cikin nuna zallar sarauta kana ta wuce.



      Gungu na uku da suka tadda bayan sun dan gota su ne ta tsinci muryar kubra

"Ranki ya dade,Allah ya taimakeki"

"Uhmmm,ya akayi kubra?" Dan jim tayi har sai da fulanin tace da ita

"Ina saurarenki mana,fadi buqatarki"

"Allah ya baki yawan rai....shin kin lura da yadda gungun dukka jama'ar da muka wuce ke boye wani abu da zarar sun ganki?" Cak ta tsaya da tafiyar da takeyi,tsahon sakan uku kana ta waiwayo tana duban kubra,wadda tuni suka sadda kai qasa ita da yaha cike da girmamawa

"Kamar yaya kenan?" A ladabce ta amsa

"Kamar akwai abinda suke gani,wanda ganin giftawarki ba zato wala'alla yasa suke boye abun....kin kula da haka yaha?" Kai ta gyada

"Qwarai kuwa,nima na gani har karo biyu kafin isowarmu nan".



      Dogon tunani maganar tasu ta sanya fulanin,tayi shuru na wasu mintuna ba tare da tace komai ba,kalaman kubra suka dawo da ita daga duniyar tunanin data fada

"Amma uwar gijiyata,kina iya sanya idanu a gaba koda zamu sake ganin wasu mutanen" kai ta jinjina cikin gamsuwa,kana ta juya taci gaba da tafiya tana sake nutsuwa da sanya idanu ga hanya koda zata ga abinda su kubran ke fada.



      Ilai kuwa idanunta suka gane mata,cikin barorin gidanne kimanin su hudu,maza biyu mata biyu,idan ta lura ma da kyau kama sun razana ne da ganin nata,daya daga cikinsu dake can baya kuma hannayensa na boye a bayansa suka zube suna miqa mata gaisuwa.



      Bata amsa ba,saita soma takawa zuwa inda suke zuben,babu wanda ya motsa a cikinsu jin bata amsa ba hakanan bata tafi ba,saita isa gabansu tana qare musu kallo,idanunta ya sauka akan na bayan dake goye da hannayensa a baya.....

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 60

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah SWT yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________


*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*

0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



     Har ta bude baki da zummar yin magana,sai kuma ta tuna ba girmanta bane,don haka ta juya taci gaba da tafiya ba tare data ce da kowa komai ba,sai su kubra suka rufa mata baya suma ba tare da sun tanka ba,jin batace komai din ba.



      Zuzzurfan tunani ta shiga,ba shakka akwai abinda ke faruwa,akwai abinda ke faruwa wanda ita din bata sani ba,kuma koma meye yana da alaqa da ita,lallai abun ya shafeta,amma zata bincika cikin hikimarta kamar tadda ta saba.



       Saida sukazo iyaka,wanda su kubra basu da izini ko ikon darawa daga nan din sannan tayi magana a sanda suke juyawa

"Na lura da abinda ke faruwa,kuma ba shakka abun bisa dukkan alamu ya jibanceni ne.....ku isa sassana ku jirani,kada ku tafi,ku kuma kira sodangi da lubabatu suma suyi dakona,zamu tattauna bayan na fito"

"An gama uwar gijiyarmu" suka amsa mata a kusan tare,ba tare data waiwayo ba ta saka kai zuwa ainihin sassan mai martaba.



      Cikin qasaita da nutsuwa tayi sallama a katafaren falon daya kasance yana ganawa da iya iyalinshi kawai,ba'a amsa mata ba,hakan ya bata mamaki,saita ware idanu tana kallon wadanda ke zaune cikin falon.



       Uwar gida sarautar mata ce fulani saratu,saman cinyarta daya daga cikin jikokinta ne maza,hakama gefanta jikan nata ne wanda dukkansu ba zasu haura shekara hudu da biyar ba.



       A daya kujerar kuma maibi mata ce wato fulani adama,itama tana zaune da nata jikan guda daya a gafanta tana tsinke mishi inibi cikin kayan marmarin dake jibge a falon tana bashi yana ci,shima bazai wuce shekara shida ba.



       Batayi mamaki ba don saratu bata amsa mata ba,adama ce cikin salo na kissa tadan tada kai ta amsa mata babu yabo ba fallasa.



      Ganin kamar yau din kowa akwai abinda ke cikin ranshi sai itama ta nemi tata kujerar cikin hakimcewa ta zauna,ta kuma kama kanta da kyau ba tare da tabi takan kowaccensu ba.



      Tsahon mintuna falon ya dauki shuru,bakajin komai sai darar su fulani saratu kowacce da jikanta.



      Abunda fulani aisha ta lura dashi da kyau shine,kamar abinda sukeyi din sunayi ne da biyu,don haka saita sake baiwa banza ajiyarsu.



      Jikan adama keta wasanshi cikin falon yana zagayewa,ya hau wanann kujerar ya fada kan waccan,yayin da fulani adaman ta shiga masa tafi tana masa waqa,kana ta dora da cewa

"Tattaka da kyau....yauwa,cikin ikon Allah wataran sai kaga kaine mamallakin wannan wajen....eh mana,tunda su magadan sun kasa kawo nasu magajin...duk inda aka kai magaryar tiqewa ai dole a miqo mana mu masu jikoki maza,ahaaann....ai wani hanin ga Allah baiwa ne".



      Sosai maganar ta taba fulani dake danne dannen wayarta,ta taba ranta sosai,saboda tasan bada kowa suke ba sai ita,hakanan suna magana ne kai tsaye akan abdul'azeez dinta,harta daga kai zata magantu sai kuma taga ba girmanta bane,hakanan tafi kowa sanin ta yadda take maida musu amsar magangununsu irin wannan ta qona musu rai cikin ruwan sanyi fiye da yadda sudin sukayi mata,don haka saita share taci gaba da abinda take,duk da zancan ya tsaya mata sosai cikin ranta.



     Batasan me yasa fulani adaman ta sauya cikin shekarun nan ba,kishin nata da ada take dannewa ta cinye yanzun ga kasa,takan mata gugar zana a lokutta masu yawa,saidai abinda ta lura dashi sam bata kwatantawa gaban maimartaba,akasin fulani saratu da bata iya boyewa gaban kowa ma.



      Wannan bai bar kunnuwa da qirjinta ba fulani saratu ta daga qaramin jikanta dake kan cinyarta tahau masa rawa 

"Idan Allah ya baka babu me hanaka.....wani hanin ga Allah baiwa ne" sunan Allah ta ambata can qasan ranta,sa'annan taci gaba da danne dannen wayarta kamar basu dameta ba,daya daga cikin dabi'unta dake qona musu rai,na yadda bata taba buda baki ta nuna musu bacin ranta kan wani aiki nasu,saidai su gani a aikace.



       Allah ya taimaketa ba'a qara second goma ba maimartaba yayi sallama cikin falon ya bayyana,cikin shigar da yakanyi idan yana cikin iyalinsa yana kuma buqatar ya sake sosai.



       Fulani aishan ce ta soma amsawa,wanda hakan yaja hankalinsa matuqa a kanta,adonta ya qayatar dashi,don dama babu qarya,gwanace ta wannan fanni,tun yarinta zuwa girma yanzu daya cimmata.



      Ita ta soma miqewa ta aje wayar hannunta,ta isa inda yake tsaye,ta saka hannayenta ta soma karkade mishi kujerar da yake da niyyar zama a kai,duk da ba wani datti ko qura ko qanqani akai

"Barka da fitowa ranka ya dade" ta fada tana kallonshi cikin wani salon murmushi mai qayatarwa,dolenshi ya maida mata martani ba tare daya shirya ba,duk da yadda yaso ya daure kodon su saratu dake wajen

"Barka kadai aishatu.....da fatan kin wuni lafiya" murmushi ta sake masa tana duqawa gamida soma zuba mishi abun sanyi dake cikin jug jug na alfarma na tangaran dake jere a wajen

"Lafiyata tana tattare da yadda ka wuni lafiya yallabai" ta qarashe fada tana miqa masa kofin,fuskarsa dauke da murmushinya karba sannan yace

"Ma sha Allah,na gode qwarai aishatu"

"Babu godiya tsakaninmu,amfanina kenan" da haka ta juya tana sakin murmushi zuwa mazauninta,ko iya haka tasan ta rama wani sashe daga abinda sukayi mata.



       Sai data zauna sannan ya dubi saratu

"Sarautar mata...,kuna lafiya?" Ya tambayeta yana miqawa daya jikan nata dake zaune gefe hannu,saiya sauko da gudu ya nufi inda yake,da alamu akwai sabo da shaquwa tsakaninsu,bata iya danne bacin ranta ba,don gashinan saman fuska da muryarta haka ta amsa mishi,saiya waiwaya ga adama

"Ranki ya dade?,to kefa?" Tayi qoqari ita din tadan sakaya da murmushin yaqe,ta amsa mishi a taqaice

"Lafiya".



      Sai daya gama shanye lemon da fulanin ta zuba mishi shi da jikokin nasa,yana yi yana jansu da wasa,wanda wannan shi yadan sauko dasu daga dokin da suka hau,sannan ya fara maganar data tarasu.



      Gida biyu hankalinta ya kasu,daya yana ga maganar da suke da mai gidan nasu,yayin da dayan ya lula zuwa ga tunanun abinda ya afku dazun,shin meke faruwa?.



       Awa daya da wasu motsi suka shafe sa'annan ya sallamesu,nan ma sai datayi abinda ta tabbatar zasuji ba dadi sannan ta fito abinta,tama rigasu barin wajen,don yanzun hankalinta ya tafi ga lalubo abinda ke shirin faruwa.



       Sanda take fitar da wani irin kallo adama ta bita,ta kuma saki shu'umin murmushi,duk da abinda tayin ya qona mata rai,saidai bacin ran nata ragagge ne,takan kuma cika da farinciki,idan tuna nan da wasu awanni da idan sunyi nauyi awa 78 rayuwarta ita da ahalinta zasu shiga cakwakiya,don tana da yaqinin saqon data bada ya soma bazama lunguna da saqunan masarautar,a iya yau kadai Allah ne kasai yasan adadin jama'ar  da suka gani.



     Kamar yadda ta buqata haka taje ta samesu suna jiranta,cikin girmamawa kowanne ya miqe tsaye harta samu waje ta xauna,kana suka gaisa da mama sodangi saboda yau din duka basu hadu ba.



     Shuru na dan mintuna sannan tace

"Nasan zakuyi mamakin taraku da nayi anan,duk da cewa yaha da kubra sunsan dalili,amma kudin nasan baku sani ba"

"Gaskiyane" suka amsa mata,saita gyara zamanta sosai sannan ta zayyane musu abinda ke faruwa.



       Shiru ne ya ratsa falon babu wanda yace wani abu,saita shiga nazartar fuskarsu tare da shiga nazarin amsa da mafita da kowanne zai bata.



      K'an kame hannunta umma luba tayi,wanda ke dauke da daya daga cikin hotunan data samu tsinta itama cikin masarautar tun gefin magariba,hotunan data fuskanci sun fara yawo cikin masarautar,don wannan shine na biyu data tsinta,tun dazun take ta tunanin hanyar da zatabi ta nunawa fulanin,ta kuma ankarar da ita abunda ta fuskanci ya soma wanzuwa,dalilin jimawarta kenan cikin gidan har kawo wannan lokacin ba tare data tafi gida ba.



       Sosai fulanin ta ankare da mutsu mutsun da umma luban keyi,hakan ya sanya ta zuba mata idanu,ta kuma gano yadda hannuwanta ke dunqule kamar yadda ta dinga ganin hannuwan dai daikun mutanen data wuce dazun.


   

     "Lafiya lubabatu?,ya akayi?" Ta tambayeta tana sake tsareta da kallo,ta dago da niyyar ce mata babu komai,to amma kwarjininta ya sanya ta kasa fadar hakan,saita soma inda inda irin ta marasa gaskiya,sa'anna daga bisani akan kanta dole ta fiddo hotunan guda uku ta miqa mata.



      Ji ta dinga yi kamar a mafarki sanda take kallon hotunan,yarimanta yaronta rungume da mace cikin jikinsa,har daya daga cikin hotunan ma yafi kama da kiss yake mata,don ya rufa fuskarshi ne saman tata sosai,babu wani batun almara ko zane,yariman qasar kaisa yarima abdul'azeez ne sosai.



      Wani mummunar faduwar gaba gamida fargaba ta rusketa sanda ta tuna fuskar yarinyar,qwaqwakwarta kuma tayi mata tariyar wacece ita,kaddai ace tsahon shekarun suna tare,kaddai ace data rabasun tsayin shekarun basu rabu ba suba tare da juna suna zaman haramc......



       Saita hana zuciyarta qarasa wannan mummunan tunanin,ta miqe tsaye qirjinta na suya,zuciyarta na bugawa da sauri da sauri,a matuqar rude ta miqawa mama sodangi hotunan tana jifan umma luba da kallo bayan ta yiwa kubra da yaha nuni da hannu kansu fita hade da tambayar umma luban

"Wannan ba yarinyar nan bace da kika samo sukayi aure da yarima na shekara daya ba?" Kan umma luba a qasa ta gyadashi

"Tabbas itace uwar gijiyata"

"Ban fahimta ba,a ina suka hadu,ko dama suna tare basu rabu ba?" Tayi tambayar wannan karon tana maida dubanta ga mama sodangi tana jin duk wani dabara da hikimarta suna toshewa.



       Mama sodangi da tunda ta dora idanunta akan hotunan taji wani sanyi yana kwarara cikin ranta ta daga kai tana duban fulanin,kai tsaye tace da ita

"Tabbas basa tare,canzawar yanayin yarima kawai na tsahon shekarun ya isa ya shaida maka hakan"

"Ta yaya zan tabbatar da gaskiyar hakan,bawai pretending yake min ba?".



       A wannan karon babu wanda ya bata amsa a cikinsu

"Tabbas indai abinda nake tunani ne abdul'azeez ya tafka babban kuskure,kuskure mafi girma a rayuwarsa" ta fada cikin gsananin bacin rai.



      A wannan karon kasa shuru mama sodangi tayi,cikin nuna girmamawa tace

"Ina ganin kibi komai sannu a hankali....abdulazeez yarone mai biyayya matuqa da gaske da duka duniya ta shaida,karki zafafa wannan karon,kada ki shiga raywarsa da yawa"

"Dakata sodangi!" Ta daga mata hannu cikin fushi

"Kina nufin na zura idanu?,kinaso ki cemin na qyaleshi yaci gaba da mu'amala da wannan 'yar talakawar wdda ba sa'ar aurensa ba?,na qyale ya maido rayuwasa baya bayan andade da wuce wajen?" Ta fuskanci ta dauki zafi sosai,hakanan tayi nisan da bata ko jin kira bare ta amsa,don haka saitayi shuru ba tare data sake tankawa ba.


      Shuru ya sake ratsa falon,tsanar bilkisu da ada bata jita ba tana neman samun muhalli da gurbi cikin zuciyarta,qarin wasu mintuna suka sake shudewa kafin ta sake magana 

"A kowanne lokaci yarinyar nan itake shiga tskaiyar lamurana da tsarina ta nemi wargazashi,koda yauahe saita zama dalili na bacin raina,tun daga sanda na shigo da ita k

Lamurana kawo yau,yau gashi zata zama sila na tarwastewar qima daraja da martabata data yarona a idanun duniya,abdul'azeez bai taba bujirewa ko saba umarni na ba tunda na haifeshi,koda kuwa bayaso,koda bai dace da ra'ayi ko zabinsa ba sai data shiga rayuwarsa,ta yaya zan dubeta da idanun tausayi ko qauna?,sam sam....matuqar kuma ta zama sila na bacin martabarmu ba shakka sai tayi nadamar sanin fulani aisha da zuria'arta....ku kiramin yarima a waya,ina da buqatar magana dashi" ta bada umarni kai tsaye,ba tare data damu da wanda zai kirashin tsakanin umma luba da mama sodangi ba,burinta kawai ta sameshi a waya taji muryarsa.



    *YARIMA ABDUL'AZEEZ*



      Tun randa ya koma din ya tabbatarwa da ranshi bazai iya zama ba ba tare daya risketa gidansu ba,bisa adreshin da yake gani nata a wayarshi.



      Misalin bakwai na dare ya gama shirinsa cikin shigar sarauta dake nuna ainihin asali da tsatsonsa,dukkan wani cikar kwarjini haiba da kamala sun bayyana tattare dashi,ya dauki mota shi daya ya fita,bisa jagorancin wayarshi dake masa nuni da hanyoyi da kuma titunan da zaibi har ya sadashi da qofar gidan.



      Kyawawan tafiya ta minti talatin da biyu ya tuqe a qofar gidan,cikin nutsuwa ya samu wajen daya dace yayi parking,ya kashe motar ya fito yana kallon wayarshi dake nuno mishi arrow na saitin gidan.



     A hankali ya dauke fuskarshi da kan wayar,ya aza idanunsa ga qofar gidan da yake fuskanta.



      Sosai ya zubama qofar idanu,yana jin wani abu na yawo cikin zuciyarshi da ruhinsa

"Yanzu nan ne 'ya'yanshi da matarsa suke?,yanzu haka suna ciki?" Saiya dinga jin kamar ya sanya kai kawai cikin gidan,ya shiga ya daukosu kana ya sakasu a mota suyi tafiyarsu,su tafi can da nisa inda zai koya musu sabo dashi,inda zai koya musu yadda zasu qaunaceshi,su rayu abunsu su kadai ba tare da kowa ya shiga ciki ko ya kawo musu cikas ba.



      Yanke tunanin yayi da hanzari yana maida wayar aljihunsa,kana ya soma takawa yana durfafar gidan.

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 61

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



 

     Dukkansu suna zaune a falo  suna kallo,yayin da najwa kecin abinci daga gefe guda ita da abdurrahman a kwano daya,anty zuhriyya da bilkisu kuma na zaune saman kujera,kusan anty zuhriyya ke kallon sosai fiye da bilkisu,wadda ta kasa hankalinta gida biyu,rabi yana ga tv,rabi kuma yana ga chart da suke da hannatu tana sake tambayarta lamuran gidan nasu,da sauran sabbin abubuwa da batasan dasu ba.



      Ajiyar zuciya ta saki,wadda ta saka anty zuhriyyan juyowa tana kallonta,suka hda idanu,sai bilkisun tace

"Hakanan zuciyata tayi nigeria ummi"

"Mun kusa in sha Allah,don ba lallai abba ya bari mu qara wata biyu bama.....amma tun jiya nakeson tambayarki.....wannan tafiyar nidai a idanuna sai naga sam bata amsheki ba,da kika dawo a birkice na ganki,kamar wadda taje jinya?" Shuru ta danyi zuciyarta tana raurawa,babu wanda ke saurin karantarta irin anty zuhriyyan,bata da wata uwa a yanzu sama da ita,don haka bata boye mata ba,ta karanta komai,duk wani abu daya faru daga zuwanta dubai zuwa dawowarta.



      Shuru itama antyn tayi cikin nazari da tsantsar mamaki,koda zata lamunci komai ita dinma ba zata yarda da tatsuniyarshi na cewa da yayi bilkisun har yanzun matarsa bace,wannan zallar rainin wayone da kuma rainin hankali.



      "Kamar yadda nace miki ne,banason ki sanya damuwa cikin ranki,babu wanda ya isa ya sake shiga rayuwarki kamar daa,babu kuma wanda a yanzu ya isa ya tilastaki ko yi miki dole a dukkan wani sha'ani daya shafi rayuwarki,ki rabu dashi yayita bibiyar,wala'alla lokacin sakayyarki ne ubangiji ya kawo miki,lokacin da zasu girba abinda suka shuka....".



      Dire kalamanta na qarshe yayi dai dai da soma bugawa da qaraurawar ta somayi,da alama akwai mai neman shigowa ciki kenan.



       Najwa anty zuhriyya ta yiwa umarni taje ta duba,suna ci gaba da tattaunawa da bilkisu,babu jimawa ta dawo fuskarta dauke da murmushi,saboda kalaman da baqon ya gaya mata,kada tace me kama da amatu ne,idan ba haka ba tun daga yau ganin farko zasu fara fada dashi,don tana budewar abinda ta soma gani kenan,bata kuma yi qasa a gwiwa ba ta fada mishi kanta tsaye,yana da tabbacin indai ta fadi hakan ga bilkisi,babu abinda zai sanyata fitowa,daga nan kuma an samu matsala,shi yasa ya buqaci tayi shuru,saidai duk da haka bakinta motsi yakeyi,neman wanda zata gayawa taga mai kama dasu abdul takeyi.



     Cikin mamakin waye baqon nata ta ari hijabin anty zuhriyya da yafi kusa da ita ta saka bayan antyn tace mata

"Wataqila adam ne" sai ta gamsu da hakan,don tasan akwai maganganu masu yawa a bakinsa game da ita da kuma abinda ya faru a duba,saidai kuma ai bai gaya mata zaizo ba,duk da wannan bata fasa fita ba,saboda zarginta yafi qarfafa akan cewa shi dinne.



       Yana tsayr harde da hannayensa a qirjinsa,ya juyawa qofa baya,don haka bata yadda zataga fuskarshi har sai ta iso inda yake tsaye.



      Dab dashi ta soma jiyo qamshin nan da yake tambarinsa a wajenta,yayin da shi kuma jikinsa ya bashi tana dab dashi,ya waiwayo da hanzari lokacin da ita kuma zuciyarta ke gaya mata shine take shirin juyawa cikin gida cikin tsoro fargaba gami da mamakin ta yaya akayi yasan gidansu.



       Cike da kuzari gami da karsashi yayi hanzari shan gabanta kamar zai shigr jikinta yana jifanta da wani irin kalo mai nauyi,sai tayi hanzarin ja baya cikin fushin nan nata dakan taso mata duk sanda sukayi face to face dashi

"Janyemin a hanya zan wuce" sassanyar murmushi ya saki kamar babu wani abun dake damunsa sannan yace

"A fuska kamar baki zubin masu fada ba,amma ga mamakina sai.naji kin iya,a qalla kyadan dagamin qafa kwana da kwanaki bamu hadu ba,banga alamun kinyi kewar koda takurata a gareki ba,bayan ni kuma mahaliccina ne kadai yasan ya na kasance a kwanakin,kin hanamin ganin fuskarki,hakanan ko sau daya baki bari uban daya shekara bakwai baiga fuskokin kyautar da Allah yayi masa ba,hakanan baki barsu su kansu sunji dumin mahaifinsu ba".



      Zallar rainin wayo qarara ta hango cikin kalamansa,kamar ma ba wani abu bane mai girma tsakaninsu ba,kamar ma ba wani abu ya aikata ma rayuwarta ba,yanason maida komai wasa,yana son maida komai ba komai ba,yanason kuma ya nuna kamar ya manta dukkan abinda ya farun,tunda har gashi yana so yana kuma shauqin ganin yaran da sun suna ciki suna a matsayin gudan jini basu zama mutane ba,to amma sai taga shurunta kamar ma ta bashi dama ne,don haka ta motsa bakinta bayan itama ta harde hannayenta a qirji,ta kuma yi jarumtar saka nata idanun cikin nashi,duk da yadda kaifin nashi idanun ke barazanar dakusar da nata

"Au...don Allah?,amma nayi mamaki da har kake da qarfin gwiwar kiran korarrun yaran da yaranka,ka manta wai kun dade da baiwa uwarsu su?,ya kamata kayi gaggawar ciresu daga sahun yayanka".



      Yadda take maganar cike da qwarin gwiwa fushi fushi da kuma dakiya ya burgeshi,hakanan ya sake bashi damar qarewa kyakkyawar fuskarta dake samun kulawa ta musamman kallo,jajayen labbanta masu kyawun zubi,baisan yakai hannu ba zai shafi gefan fuskartata ba sai daya kusa sannan ya ankara,yayi hanzarin janye hannun nashi,cikin laushin murya yace

"Calm down baby....fushin bai miki wani kyau,haramunne kuma mace ta dinga dagawa mijinta murya haka,mala'iku suna jinki...." Sai ya matso dab da ita har suna musayar numfashi,muryarsa na sake yin laushi da taushin daka iya kashewa duk wata lafiyayyar mace jiki yace

"Ban fada ba,hakanan har abada bazan taba cewa na barwa duniya ko uwar d'ana 'ya'yana ba....ni abdul azeez....ko cikin shege na yiwa mace bata isa na bar mata yarona ba,koda zuciyata bata taba sonta ba,mun hadune a rariya,bare ke da kike da wani babban matsayin da duk duniya babu meshi,bare yarana da suke na sunnnah,da kinsan waye azeez da bazaki fadi hakan bama,jinina yana da qima da martaba a idanuna,koda b'arin dana akayi zan girmama inda aka binneshi,pls,na roqeki da dukkan wani abu mai girma....ki barni naga yarana,ki barsu su rabeni,koda ke akaran kanki ba zaki saurareni ba,duk da koda baki saurarenin ba ina mai tabbatar miki da cewa azeez bazai taba qyaleki ko rabuwa dake ba,idan kinayin wadan nan abubuwan don na barki,ina mai farincikin shaida miki cewa....ban gaji ba,bazan kuma gaji ba....idan akwai wasu qarin hanyoyin ma ki dado dukka kiyimin,indai zaki huce,indai zaki sake bani chance na shiga rayuqarki karo na biyu".



      Mamakin wanne irin mutum ne shi ta tsunduma,dukka kalamansa yanayinsa da yadda take furtasu kawai sun isa gaya maka da gasken gaske yake.



   Baya ta janye ta daga kai zata kalleshi ta gaya masa maganar da zata hanashi barci a yau,sai taga hankalinsa ya raja'a ga bakin qofar gidan.



     A hankali ta wawaya don ganin abunda yake kalla din,amatullah da abdurrahman ne ke kokawa akan bindigar ruwa ta wasa,kowa nason karba,saidai tuni abdur rahman din ya amshe da yake shi din namiji ne,amatu ta soma tattakowa cikin kuka ta nufota,da alamu qara zata kawo mata.



      Bata taba tunanin akwai wani abu da zai sake sanyata gudu ba bayan wanda tayi na quruciya ba sai yau,tuni ta riga azeez din isa ga yaran ta cafki hannayensu,kana cikin mugu sauri ta jasu zuwa cikin gidan ta banko qofa.



     Daidai lokacin da najwa ta kasa haquri take baiwa anty zuhriyya labarin mai kama sak dasu abdul ta gani,shiya aikota kiran anty bilkisu.



      Shuru anty zuhriyya tayi tana dan gajeran nazari,ranta na raya mata waye,duk da cewa tasan shi baisan gidan ba.



     Yanayin yadda bilkisu ta shigo da yaran yasanya ta fahimci inda amsarta take,ko ina na jikinta na rawa,hakanan kuka keson qwace mata

"Maza najwa ku wuce ciki gaba dayanku,oya" anty zuhriyya ta bata umarni,ba jinkiri ta kada kan dukka yaran suka wuce ciki,falon ya rage daga ita sai bilkisun,ta qarasa ta kama hannuwanta

"Meye?,meya faru?"

"Shine ummi,bansan ya akayi yasan gidan nan ba har yazo,yaga su abdul sanda suka fita,har ya taho wajensu,ummi banason ya shiga rayuwarsu,bana son ya qwacemin su,yanzu yasan inda nake zaune" tabe baki anty zuhriyya tayi

"Don yasan gidan nan shine me?,don yaga su abdul sai meye?,kefa bai isa yin komai cikin rayuwarki ba ina gaya miki sai idan kece kika bada qofa kika yarda kin fahimta,babu abinda zai faru kamar yadda na saba shaida miki".


     

     Tana dire maganar taji ana bude qofar falon gidan,tasan kuma mutum dayane zai.haka wato abbaa,saidai kuma a yadda sukayi dashi zai dawo lokacin dawowarsa bai qarasa ba,don haka ta maida kallonta ga bakin qofar cikin mamaki harya gama budewa ya shigo.



       Da sallama a bakinsa yashigo din,saidai kuma ya karanci kamar akwai abinda ke faruwa saman fuskokinsu

"Lafiya abbaa naga ka dawo tun yanzun?" Anty zuhriyya ta tambayeshi sanda yake zama saman daya daga cikin kujerun fuskarsa na nuna alamun damuwa da kuma rashin walwala

"Wallahi jikin hajiya ne ga motsa sosai,ina can malam ke sanar min,sai naga kawai gwara na dawo mu fara shirin tafiyar nan,a haqura da qarshen watan,cikin satin nan kawai mu wuce mu sauka ringim din gaba daya" cikin yanayi na nuna alhini da kulawa tace

"Subhanallah,amma koda na kirata batace min komai ba,da sauqi kawai ta bini dashi"

"Eh ai batason a fada,haka take cewa kowa"

"Allah ya tashi kafadunta" ta amsa tana barin wajen da suke tsaye da bilkisu,itama bilkisun cikin sanyin jiki gami da sanyin murya tace

"Allah sarki hajiya,Allah ya tashi kafadunta,ya bata lafiya"

"Amin amin" ya amsa kana yace

"Meke faruwa?na shigo na sameku a tsayr carko carko,banji kuma motsin kowa a gidan ba ina duka yaran?" Yanayin damuwar lalurar mahaifiyarsa yasa taga bai kyautu ta sake qara masa damuwa ba,don haka tace

"Babu komai,kawai muna tattaunawa ne,sai kuma ka riskemu a haka" ta qarasa fada tana buda fridge don dauko masa abun sanyi,tana kuma qwalawa yaran kira tana shaida musu dawowar abban nasu,bilkisu kuma ta juya ta shige ciki tana qoqarin daidaita yanayinta.



    Mutuwar tsaye yayi na wucin gadi a wajen da suka shige gida suka barshi,yana jin wani abu yana zagaya qwaqwalwarsa yakuma tsaida tunaninsa na wasu mintuna.



    Ya jima a haka kafin yaji qafafunsa sun soma gardama da tawayen qin karbarsa,hakan yasa ya yiwa kanaa qiyamullaili ya isa ga motarshi ya shiga kana ya rufe.



      Kanshi kawai ya kifa saman sitiyari,fuskokin yaran na yawo cikin idanunsa,wata qauna mai tsanani tasu wadda ta nunka wadda yakeji a baya tana shiga zuciyarsa tana barazanar kekketata,tabbas banda uwa uwa ce,banda fulani mahaifiyarsa ce babu mahaluqin daya iaa yayi masa haka a duniya,saidai uwa ta zarta duk wani tunani dan adam,hakanan takanyi komai ne da sunan soyayya koda zai dawo daga baya ya cutar da rayuwar danta ba tare data ankara da hakan zai iya faruwa ba.



      Har uncle abbaa yazo ya wuce ciki bai sani ba,shima bai lura ba saboda yana cikin mota ne,ya tsammaci maqotansu ne suke da baqi.


¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶


     Kwanki uku ya kwashe yana jera zuwa gidan ya zauna bakin qofa,yayita jera mata kira ko saqo kan ta taimaka ta turo yaran ya gansu koda ba zasu iso inda yake ba,idan ba zata barsu ba to ita ta leqo ya ganta,baya damuwa da yawa ko adadin awannin da yake shafewa zaune a wajen ba,burinsa kawai taji tausayinsa ta kuma yi masa alfarma.



     Zuwan nasa tamkar takura yake a wajenta,duk da bata ganin koda qyallinsa,amma duk da haka bata qaunar taji saqonshi na cewa yana zaune a waje,saidai ta sharema zuciyarta,tunda babu abinda zai sanya ta fita bare ya ganta koya tareta,hatta da aiki ta dauki excuse,kuma dr adam baiqi ba ya bata.



    Tana ta kasa kunne ko dr adam din zaice wani abu?,baice ba,amma akwai sanyin jiki daga yadda ya saba waya da ita,saida aka kwana uku sannan yace ta gaya masa yaushe zaizo gida ya sameta,akwai muhimmar maganar da yakeso suyi.



      Ta riga data sani,tasan qarshen labarin,don haka tace dashi

"Zamuje nigeria mu dawo,kayi haquri idan na dawo saimu tattauna kome zamu tattauna din" bai musanta mata ba ya amsa da to.



     Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



     Kamar kullum,yauma yayi parking motarshi daga gaban gidan kadan,duk da yasan cewa babu lallai ya samu ganinta ita ko yaran,amma a yau yana jin cewa bazai iya jura ba,don haka yana kashe motar ya fito sannan ya kulleta.



      Tsayin mintuna yana duban gidan kana ya durfafeshi kai tsaye cike da qwarin gwiwa da kuma tarin jarumta,ya gaji hakanan,koda zunubin na bisa wuyansa naqin amsar cikin aiya kamata a sassauta masa hakanan,a barshi yaga gudan jininsa.



       A lokacin bilkisu na kitchen ta dora sanwar abincin dare,sanye cikin doguwar riga mai yankakken hannu A shape na wani material mara nauyi,dankwalinsa baida fadi,hakan ya baiwa kwantaccen baqin gashinta dayasha gyara daman bayyana.



      Abdurrahman ne kawai a falon shi da ateeq,amaturrahman da najwa da abid suna backyard na gidan suna wankin undies dinsu,wanda tuni sun riga da sun saba,saidai najwan na tsayawa tare dasune tana gyara musu idan sunyi kuskure.



      Sosai.hankalinsu ya tafi kan cartoon da suke kalla,hakan ya sanya daya daga cikinsu ya kasa tashi yaga waye a bakin qofa,duk da qararrawar dake kadawa,dai dai lokacin anty zuhriyya ke fitowa daga dakinta sanye da hijabin data idar da sallar la'asar tana waya da hajiya.



      Ta gama wayar don haka ta sauketa daga kunnenta,tana qoqarin katsewa tace

"Saboda sakarci kuna jin ana magana a waje amma ku kasa tashi ku bude,koma waye kenan yayita tsaiwa ko?" Ta qarashe maganar tana dosar qofar don ta bude din

"Sorry mommy" a teeq ya fada yana sake gyara zamanshi,don shi kallon yayi masa suger.


     

     A hankali ta buda qofar,idanunta suka sauka kan azeez dake tsaye sosai,irin tsaiwar dake nuna kuzari da cikakken qoshin lafiya gami da cikar halitta.



      Bata buqatar neman qarin bayanin wayeshi,kallo daya zaka masa ka tabbatar da kamanni na zahiri tsakaninsa dasu amaturrahaman,iya kamar kawai ta isa ta gaya mata wayeshi.



       "Barka da yamma anty" ya fada yana dan rusunar da kanshi alamun girmamawa,sosai ta hade ranta,fada takeso da masifa tayi masa sosai,amma baya ga hade ran saita kasa komai,tana jin kwarjininsa yana cika wajen yana kuma cika idanunta

"Yauwa....lafiya?" Bai zaci zata tambaya ba,amma kuma yana tunanin qila bata sanshi ba,don haka cikin dakiya yace

"Nazo ganin twince ne,idan babu damuwa ayimin alfarma na gansu" ya fada yana kallon fuskarta,cikin ranshi yana addu'ar samun nasara.



      Shuru tayi tamkar mai wani tunanin,tana son tace masa aah ne,tana son gaya masa maganar dake yawo kan bakinta amma kwarjininsa nason rufeta,daga qarshe sai kawai ta samu kanta da juyawa zuwa ciki,muryarta ciki ciki tace

"Bismillah" kana ji kasan wani abu ya tilastata fadan haka din.



     Nannauyar ajiyar zuciya ya saki,a hankali yana shafa qirjinsa da hannu daya gami da lumshe kyawawan idanunsa yace

"Alhamdulillahi rabbil Aalamin" a nutse yabi bayan nata zuwa ciki.



       Tuni ita ta isa cikin falon,ta kuma aika ateeq ya kira amaturrahman,ya shiga kitchen ya samu lemo da ruwa ya kawo falon,daga haka tayi shigewarta ciki.



      Da abdurrahman ya soma tozali,kasa zama yayi yaji zuciyarsa na wani irin bugawa kamar yaga abun tsoro,ya zubawa yaron idanu,wanda sam shi baisan me ake bama,kamar kuma ance kalli bayanka,saiya waiwayo,take suka hada ido dashi,tsaiwa yaron yayi shima kamar mai tunani ya zubawa azeez idanu na wasu sakanni,hakanan kuma saiya saki murmushi yana cewa

"Ina wuni uncle" murmushin shima ya sake sama,kana ya miqa masa hannunsa alamun ya taho,kamar me tunanin wani abu ya tsaya yana dubanshi,sai kuma ya taso a hankali yana takowa inda yake.



      Yana zuwa azeez din ya janyoshi jikinsa,ya rungumeshi gam yana jin wani maganadisu cikin zuciyarsa,tarin qaunar yaron tana motsawa daga ainihin zuciyarsa,koda ba'a fada ba yasan photocopy dinsa ne sak!,kamar yayi kaki ya ajjiye.

 


      "Kaiiiii" yaji ance,sai a sannan hankalinsa yakai kai,amaturrahman ce tsaye daura dasu tana kallonsu,cikin mamakin ganin me kama da ya abdul dinta.



      Tattausan murmushi ya saka yanajin qwalla na shirin taho masa,ya miqa mata hannu itama,amma saita noqe,saboda tana sa wuyar sabo da rashin yarda,abdul dake zaune saman cinyarsa yace

"Kizo kiji amatu,yace waishine daddynmu"

"Daddy?" Ta maimaita cike da mamaki da zumudi,kalmar data dade tana son ji sakamakon yadda kullum 'yan ajinsu kowa baida zance saina mom dinsa da dad dinsa,wannan ya sanyata tahowa itama harda saurinta,ya hadasu gaba daya ya sake rungumewa yana yiwa Allah kirari gami da shafar kawunansu,yana jin wani irin madaukakin farinciki yana ratsashi,wani abu daya qulle masa daga qirjinsa zuwa zuciya shekaru bakwai baya yaji yana raguwa gamida narkewa.



      Daga kitchen kuwa sanda ateeq ya shiga tana gyaran salad,ya isa ma'ajiyar farantai da kofuna ya soma hadosu hadin gambiza,saita kalleshi

"Me kuma zakayi dasu?"

"Baqi akayi ummi tace nakai musu ruwa" amshewa tayi tana maidasu inda suke tana sake zabo wasu

"Shine zaka dauki kofuna wari da wari haka?" Ita ta shirya masa komai saman farantin ta bashi,saidai kafin yakai ga fita santsin tiles ya kwasheshi ya watsar da wasu kayan,Allah yasa kofunan basu zubeba,ta qaraso da sauri ta amsa

"Allah ya shiryeka,banda abun ummi ta manta dama ba'a abun arziqi dakai?,bani nan suna can suna zaman jira" karbe tray din tayi tayi gaba zuwa falon da zummar takaiwa baqin ta dawo taci gaba da girkinta.



      Sam bata taba kawowa a ranta baqi maza bane,tunda tasan antyn babu wani namiji da take mu'amala dashi dahar zata kawoshi gida,abbaa kuma baya nan bare tayi tunanin mazanne,hakanan tunaninta ko mafarkinta bai taba kawo mata cewa wai abdul'azees bane cikin falon nasu.

7/11/21, 4:34 PM - My Mtn Number: 62


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



      

     K'arar sakin data yiwa tray din hannunta ne ya janyo hankalinsa ya kuma ankarar dashi

"Subhanallah" ya fada yana sauke su amatullah daga jikinsa wadanda yaketa musu tambayoyi iri daban daban ta yadda zasu sake jiki sosai dashi.



     Taga tahowarshin amma saita kasa daga qafarta,saboda tana tsammanin ba'a zahiri bane,har ya iso inda take tsayen ya durqusa ya tattare dukkan abinda ta zubar din ya dora saman farantin,saiya miqe yana dubanta.



     Sunyi mugun dab da juna,wanda da zai qara taku guda tak zai iya yin masauki a jikinta

"Ki dinga bi a hankali,kada ki jima kanki ciwo kija mana asara maman twince" ya furta cikin wani irin salo da sautin murya,hucin bakinsa da numfashinsa duka na dukan wuyanta,wanda ya sabbabawa tsigar jikinta zubawa,ya kuma qara gudun zuciyarta

"Muga hannun,Allah yasa bakiji dai ciwo ba" taji yana fada,bata ankara ba har ya kama hannun nata ya sanya nashi tafin hannun cikin nata,ya soma murxawa a hankali

"Alhmdlh,babu abinda yayi" kamar wadda ta farka daga wani mafarki ta fusge hannunta da mugun sauri,ta juya da niyyar barin falon,amma ina ya fita zafin nama,caraf ya kamo faffadan qugunta daya qawata da mazaunai,wadanda suka bayyana sakamakon yadda rigar tabi jikinta.


   

     Taku ya qara tana sake rage tazarar dake tsakaninsu,kamar mai rada yace

"Na gode da halaccin da kikamin,na gode da kikabar yarana suka rayu a mahaifarki sa'annan kika haifesu,kika shayar dasu kika tarbiyyansu duk da abinda suka faru,na gode na gode....." Iya qarfinta ta saka ta hankadashi,sa'annan cikin gudu kamar wata qaramar yarinya ta cilla zuwa dakin anty zuhriyya qirjinta na mugun bugu.



       Da kallo yabi bayanta har ta bace masa sannan ya lumshe idanunsa lokaci guda kuma ya budesu

"Oh my god,ya rabbi" ya furta can qasa,ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimta abinda yace ba,murmushi ya qwace masa saman fuskarshi.



      Sam ya manta da yaran saida yaji muryar amatu na cewa

"Uncle...." Ya bude idanunsa a kansu,ashefa duk suna tsaye suna kallonsu,saiya sake musu murmushi suma,ya duqa gabansu yana kama kumatun amatun

"Not uncle,its daddy right?" Saita daga kanta tana murmushi.



      Kusan morewarsa yayi shida yaransa cikin falon,don babu wanda ya sake fitowa,shi da kansa yake mamakin yadda yaran suka saki jiki haka dashi,kamar dama can sun sanshi,sai kuma ya tuna cewa jini fa ba wasa bane,daga qarshe ya jasu qofar gidan cikin motarsa,ya dinga musu hotuna kamar dama ya siya wayar ne kawai saboda su.



      Bilkisu kuwa a razane ta shiga dakin anty zuhriyya wadda ke tsaye tana linke hijabin jikinta,saita saki hijabin tana kallon bilkisun

"Kin gani ko anty,wallahi ya shigo yana falon,yana tare dasu amatu anty ya akayi ya shigo,kada ya debemin yara na" kafadarta ta kama

"Babu inda zashi dasu,ki kwantar da hankalinki" baki kawai antyn ta saka ta zubawa bilkisun idanu ganin yadda ta gaza nutsuwa,tana mamakin yadda take razana fiye da kima a duk sanda zata ganshi kamar haka,tabbas akwai dalili bayaga tsoron tafiya da yaran da take.



       Sai daga baya ta fuskanci antyn ta zuba mata idone kawai tana kallonta,hakan yasa dole ta arowa kanta nutsuwa ta kuma zauna tana maida numfashi,ganin haka yasa ta juya taci gaba da ninkinta ba tare data ce da ita komai ba,ta barta tana qoqarin daidaita nutsuwarta.



      Shikam daga can saiya kwashesu kawai zuwa shago mafi kusa dasu,ya dinga sanyasu suna zabar duk abinda sukeso,duk da basu rasa komai ba,haka ya dunga lodar musu siyayya harda ta banza da wofi,ya kashe musu kudi masu nauyi ba tare da yaji ko darr ba,saida suka cika motarshi da siyayya sai wajen zamansu kawai ya rage.



      So yake yayi wani abu da zai iya zama madadi koya cike gibin da ya afku a rayuwarsu shekaru bakwai baya,yanajinsa wani babban mai zunubi kuma mai sabo idan ya tuna an raini cikinsu ba'a gabanshi ba,an haifesu ba'a gabanshi ba,an ciyar dasu abincij wani gidan ba nashi ba,basu taba sanya suttura tashi ba ko amfanuwa da wanu abu na mahaifinsu ba,duk tarin dukiyar da Allah yayi masa,yanajin ciwo da quncin hakan sosai cikin ranshi,amma yana fata nan da lokaci qanqani komai zai zama tarihi.



      Sanda su ateeq suka gama shigo da siyayyar mamaki ya kama anty zuhriyya,tayi tsaye kawai riqe da baki da hannunta,sam yaran ma su basusan me ake ba,sai nunawa su ateeq kayan suke daya bayan daya,kowa na daukar nashi yana fadin wanda zai baiwa.



  

      Bilkisu dake daki batasan me akeyi ba,sai data fito duka a sintirinta na ganin yaran sun dawo sannan tazo ta tadda kayan.



      Sosai ranta ya baci,taji kamar ta tattara kayan ta cinna musu wuta,musamman data lura anty zuhriyya kamar bata nuna damuwa ba,kuma me yasa ma ta bari aka shigo da kayan cikin gidan

"Kun sanshi ne da kuka bishi kuka karbo kaya?,roqo kuka soma abdul?" Cikin tsoro suke kada kai,saboda basu taba ganin bacin ran mahaifiyar tasu irin haka ba,fada ta kama sosai duk idanunta sun rufe,har sai da anty zuhriyya tayi kiran sunanta kana ta tsagaita

"Ku tattara kayan kukai dakinku,najwa ki jera musu cikin kayansu,wanda zai lalace kuma ki sakasu cikin fridge"

"Amma ummi...."bilkisu tayi hanzarin fada

"Ya isa" ta dakatar da ita,ba wanda ya sake cewa komai cikinsu har sai da duka yaran suka bar falon.



      "Zauna" antyn ta bata umarni cikin nutsuwa,ba musu tabi abunda tace ta zauna,antyn tayi shuru tana dubanta na wani lokaci kafin tace

"Lokacin da suka kore cikin jikinki,saninki ne cewa bashi ubansu bane da kanshi ya aikata hakan,mahaifiyarsa ce tayi gaban kanta ta aikata hakan,bilkisu,duk duniya bayan ke kanki babu wanda ya kaini jin zafin abinda ya faru dake,hakanan har yanzu inajin zafin hakan cikin raina...amma kinsan wani abu?,akwai wasu abubuwa da nayi nazarinsu cikin taqaitaccen lokaci,abu na farko..." Ta fada tana daga yatsanta

"Daga ni ke da duk wani mai qaunarki babu wanda zaiso ace yaran nan sun tashi ba tare da sunsan waye mahaifinsu ba,ba tare da sunsan asalinsu kuma tushensu ba,idan wasu sun musu kallon 'ya'yan halali saboda sunsan sanda aka daura aurenki,da yawa zasu musu kallon shegu ne,kalmar da sai ta kusa tarwatsa zuciyarki fiye da yadda zuciyar taki taso tarwatsewa a baya,duk yadda zanso daukan fansa nuna fushi ko jin zafi kan lamarin bilkisu,bazanso su abdul su rayu ba tare da sanin waye ubansu ba" shuru tayi tana kallon bilkisun kafin ta dora

"Abu na biyu kuma...dukka hasashena da abinda ya bayyana garemu....mahaifiyar yarima ita keda alhakin komai,ta shirya komai kuma ta tsara faruwarsa yadda taso saboda tana jin cewa qarfin izzarta isa iko da kuma mulkinta sun isa susa komai dai daita,ban sani ba koda goyon bayansa,ban sani ba ko babu,hakanan ban san ko tare suka shirya ba,amma abinda nafi gasgatawa shine ita ta shirya,zan iya cewa a yanzun kamar dama kika samu,dama kika samu da zaki nuna mata kurenta,dama kika samu da tana kallo zaki kasance da yaronta ba tare data tsara faruwar hakan ba" kamar wadda aka mintsina sai bilkisun ta miqe tana kada kai.



         Murmushi anty zuhriyya ta saki tana nuna mata kujera da hannu

"Kwantar da hankalinki ki zauna,hasashena ne,kina iya yin dukka yadda kikaso a yanzun damarki ce" saita koma ta zauna din,anty zuhriyya ta dora

"Abu guda nakeso ki fahimta kuma ki gane,wannan dalilan nason yaran susan ainihin tsatso da mahaifinsu yasa na bashi damar shigowa gidan da kuma ganinsu bawai wani abu ba daban,abu daya kuma zuwa biyu nakeso na fahimtar dake,ki daina zafafa qiyayyar mahaifinsu gaban idanunsu,saboda shaquwa da qauna mai qarfi na iya shiga tsakaninsu,ta tadda zasu fara iya gano aibun abinda kikeyin,zasu kuma iya bin bayanshi nan gaba,sannan duk koma meye ya farun ba hurumin su sani bane,don haka ki dinga qoqarin dannewa,amma baya ga haka,babu abinda ya sauya game dasu a zuciyata,hakanan ba wani sassauci ko sauran dama a kanki,sai abinda kedin kika zaba"......



      *_ABDUL_AZEEZ_*




       Ranar yau din jinsa yake daban,jinsa yake kamar an sauyashi,wani irin farinciki ke ratsashi wanda ga duk wanda yasan shi,yasan ainihin zahirin fuskarshi zaiyi mamaki qwarai idan yaga wannan yanayin saman fuskar tashi.



     Cikin nutsuwa da kuzari yake tuqin nasa,cikin zuciyarsa kuma yana wassafawa gami da ayyana yadda zai shawo kanta,yana ganin matuqar yaran suka shaqu dashi,shaquwar tasu zata taimaka qwarai wajen janyo nata hankalin.



        Sassanyan murmushi ya subuce masa sanda ya gama hasaso kansa tare da bilkisun cikin wata duniya ta musamman wadda dagashi sai ita.



      Komai ya katse masa sanda wayarsa ta soma ringing,yaja qaramin tsaki yana jin haushin yadda kiran ya katse masa daddadan tunaninsa,yanajin me yasa ma bai kashe wayar ba.




       Dai dai lokacin da fulani kenan ke tsaye tsakiyar falonnata cikin tashin hankali,tana kuma sauraron mama sodangi dake mata kiran yariman.




       Ganin ya kusa isa gida ya sanya baibi takan wayar ba,har sai daya isa wajen parking,yana tsaidata idanunsa yakai ga wayar wani kiran na shigowa,sunan mama sodangi daya gani ya sanyashi kashe motar kawai yayi,ya daga kiran ba tare daya fita a motar ba.



       Ga mamakinsa muryar ammi ce ta soma shiga kunnensa a maimakon mama sodangi

"Barka da war....." Ya soma yunqurin gaidata

"Dakata yarima!" Ta dakatar dashi a matuqar tsawace,tsawar data ratsa kunnuwansa da kwanyarsa dakyau

"A yau na yarda da cewa nidin ba koman komai bace a wajenka,ni ba wata tsiya bace....sanna yaudarar daka jima kana min tsaho shekaru game da bilkisu a yau Allah ya bayyana min komai,na gani da idona,gani kuma na zahiri,saidai abinda nakeso ka sani,ka tafka kuskuren da zai jawo rushewar komai,qimarka da tawa,darajata da taka,martabarmu gaba daya,hotunanku ya fara yawo cikin masarauta kai da yarinyar cikin yanayi na abun tur da Allah wadai da bai kamata aga dan qwarai a haka ba.....bana so ka wuce satin sama ba tare da kazo ka sameni cikin kaisa ba,sa'anan daga yau a yanzun nan nake cewa.....idan ka sake rabar yarinyar ban yafe maka..."

"Ammiiiii" ya kira sunan nata cikin wani irin sauti na gigicewa da razana

"Kada kiyi haka,kada kuma kice haka,ina buqatar yin magana dake,akwai abubuwa da yawa da baki sani ba wanda ya kamata ace kin sani"

"Abdul'azeez!,ba kana magana bane da sa'arka ba,mahaifiyarka ce idan ka manta na gaya maka,bana buqatar sani ko jin komai,ruwanka kabi umarnina koka saba,furucina zai bika" daga haka ta katse kiran ta baiwa mama sodangi wayar,cikin tashin hankali da bacin rai ta soma magana

"Inason cikin barorina a zabo min amintattu mutun talatin da zasu shiga kowanne lungu da saqo na masarautar nan,su kuma zaqulo gami da fiddo hotunan a duk inda suke,hakanan suyi aiki ba dare ba rana,subi dare subi rana su tsince hotunan a duk inda sukaga an yar a qonasu,ba shakka wannan wani shirine da aka jima anayi ana bibiyar sawunmu don a tarwatsa mu,saidai kamar kowanne lokaci, a wannan lokacinma ina da babban zaton shirinsu ba zaiyi tasiri ba,amma fa.....sai munyi babban aiki,ta yadda hotunan ba zasu shiga hannun maqiyana abokan zamana ba,bare kuma....." Sai tayi jim tana tuna girman lamarin

"Mai gaba daya mai girma mai martaba,ayi gagggawar aiwatar da abinda nace cikin sirri,kada a samu kuskure"

"An gama" umma luba ta fada suka miqe tare da mama sodangi suka fice,yayin da mama sodangi tayi nisa cikin tunani gami da nazarin al'amarin,yadda zata kaya,da yadda zata kasance,meye qarshen abun?.


_kuyi manage,banson yin muku fashin posting,babu yawa,da babu gwara babu dadi ko?inji hausawa_ðŸ˜

7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 63


*_NAFISAKABDULLAHI_*


*_Mai karatu nasan zaka ce meye wannan?_*


*_shin kai/ke ma'abociyar hawa duniyar yanar gizo ce?,kina daga cikin masu shawagi a manhajar youtube?_*


*_to maza matso,GA SABUWAR CHANNEL 'YAR YAYI DAKE DA ZAMA A MANHAJAR YOUTUBE MALLAKIN MAWAQIYA NAFISA K ABDULLAHI_*


*_CHANNEL DIN DATA HADA dukkan wani sinqi sinqin abubuwan sanya ruhi nishadi,kama da_*


*waqoqi*

*fina finai*

 *da bidiyoyi masu qayatarwa*



*_GARZAYA maza ka shiga wannan link din https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg dannan maballin SUBSCRIBE don samun sabbin shirye shirye idan an dora,sannan ka danna LIKE kayi kuma SHARING_*


*_NAFISAKABDULLAHI YOUTUBE CHANNEL 'YAR YAYI_* 🥰🥰🥰


_ZAKU IYA MAGANA DASU KAI TSAYE A SHAFINSU NA FACEBOOK_

https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi



_KO KU TUNTUBESU TA WANNAN NUMBER WAYAR_

08071172003


*karku manta SUBSCRIBE,LIKE SHARE AND COMMENT*

*SAI KUNZO*🚶ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸


__________________________

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




      Da qyar ya samu ya iya kai kanshi falonshi ya zube yana jin wani jiri jiri,astagfirullah kawai yake ambata a fili da boye,don wannan karon bayajin zai iya bin umarnin fulani kwata kwata,zaije ya tunkareta kamar yadda takeso,amma kuma bada lamarin da takeso din ba,a yanzun yana jin a shirye yake ya bayyanawa duniya bilkisu matarsa ce,a bayyane yake ya amshi matarsa da dukka yaransa,a yanzu ya sake shiryawa tunkarar duk wani qalubale daka iya fuskantoshi.



      Yanaji wayar tana sake ringing,daya duba sai yaga safwa ce,baida kuzari ko sha'awar yin magana da kowa,a yanzun kadaici yake buqata fiye da kullum don ya shiryawa tunkarar abinda zai dososhi,don haka ya maida wayar silent gaba daya,harta qaraci burari da kiranta ta gaji ta ajjiye.



 Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



         Idan tace tayi kyakkyawan bacci ko taci abinci ya tsirga mata kota zauna ta samu hutu da nutsuwa ba tare da fargaba ko tashin hankali baa kwanakin ta yiwa kanta qarya,koda yaushe cikin zulumi da aikin tsinto hotunan suke,abun yana neman ya gagari kundila saboda yadda kullum wayewar gari ake tsinto mata hotunan rututu,magana harta so ta zagaye kusan rabin masarautar,ya soma zama wani topic mai zaman kanshi da duk inda kaga mutane sama da biyu zaune suna hira kusan zancam da sukeyi kenan,don ma alkhairinsu cikin masarautar ya taimaka qwarai wajen rage yawan zargi da cecekuce.



       Saidai kuma akace dan adam baka iya masa ba,dan halak shike rama halacci,wani duk yadda kakai ga kyautata masa akwai lokacin da zai rufe idanu ya shiga sahun masu cutarka ayi dashi,koda ka shekara dari kana masa alkhairi ne kuwa,shi yasa hausawa sukace dan halak shike rama halacci,to kusan hakanne,da yawa daga cikinsu da basu duba kyautayi kyauta gamida halaccin fulanin ba,sun gauraya da 'yan kora masu aiki qarqashin fulani adama suna sake hura wutar zancan lungu da saqo,wannan yakai har kunnan fulani yadda maganar ke yawo.



         Tashi hankali sosai ta shiga,tana duba girman abinda ka iya zuwa ya dawo matuqar maganar taci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin da baqi zasuci gaba da sauka masarautar domin halattar wannan gagarumin hawan daya tara al'umma da yawa,daren data masa barci,ta jima tana ta zirya gami da tunani da son hasaso wanda ya qulla dukkan wanna tuggun,duk da zarginta yafi ga mutum biyu,adama ko saratu,a binciken data saka aka mata kusan mutanen fulani adama su fi yawa cinin masu tofa albarkacin bakinsu game da lamarin,don haka zarginta yafi karkata a kanta.



        Ta fannin fulani adama kuwa labarin dukkan yadda lamuran ke tafiya yadda takeso na zuwa mata kunnunta,abun ya mata dadi qwarai da gaske,tayi shewa tayi dara tana kuna jira da dakon ranar da zata isa gaban mai martaba fa miqa hotunan,ranar da zata samu dimbin shaidun al'umma na suma sunga hotunan na yawo a masarautar,ranar da zata tarwatsa farincikin fulani aishanta cusa mata kadan daga cikin baqincikin data jima itama tana cusa musu

"Allah ya baki yawan rai,ta qara yawan ma'aikatanta masu kwashe hitunan a duk inda muka sakesu"

"Ina umartarku daku qara yawan hotunan ninkin baninkin abinda aka saba bugawa da zubdawa,ku qara yawan sasannin da kuke ajjiyesu,so nake ya zamana hatta da maqasqanci mafi qarancun matsayin bawa a masarautar kaisa,babba da yaro ya tsinci hoton bawai labari kawai ba,ta yadda qimar abdul'azeez da mahaifiyarsa zata tafi daga masarautar nan,tafiya ta har abada" wannan shine umarnin da fulani adaman ta bayar.



        Sannu sannu saiga hoton har a hannun fulani saratu,ta jima tana qarewa hotunan kallo cike da mamaki da jinjina lamarin,tana kuma sauraren bayanin da daa daga cikin bayinta keyi.



        Murmushi ta saka daga qarshe tana ajjiye hoton a gefanta,ta zauna cikin nutsuwa tana fadin

"An hana yaranmu fita zuwa wata qasar karatu da zummar kada su lalace,lallai ya kamata nayi tattaki har zuwa sassan fulani na soma miqa jajena a qareta,tare da jiran ranar da labari da idanuwan mai.martaba zaikai kai wannan danyan aiki da yarima kaisa keyi a qasashen turawa" tana fadin maganar tana jin zuciyarta wasai,yanzun lokaci yayi da ko qaqa zata samu ta rama wani yanki daga haushi da takaicin aishan gami da kishi dake cin ranta.



   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶


     Kamar kowanne lokaci yauma tana zaune cikin daya daga cikin falukanta da ayau ta zabi ta zauna,duk da zamane kusan na alhini da fargabar abinda kowannw second na awannin ranar zai iya haifarwa,zamane kamar na makoki take,zaman tattara dukkan wasu hotuna da aka zubar a ranar,wanda kafin ta koma ciki sukan tara hotuna masu yawa,wadanda a yanzu haka hotunan har sun ninka nada,hakan ke sake tabbatar mata lallai lallai akwai zagon qasa da kuma saran boye cikin lamarin.



        Sanda aka nemi izi inta kan shigowar fulani saratu tayi mamaki qwarai,taso ta hana,sai kuma tayi tunanin idan har ta hanata din kamar tana basu isharar cewa tasan meke gudana,ko kuma haka abun yake,don haka tasa aka kwashe hotunan da ake tarawar zuwa inda kullum suke qonawa,kana ta bada umarnin ta shigo.



      Cikin wani irin taku da take jin ranta fes ta shigi zuwa falon,ta daga kanta a fakaice tana kallon yadda aka narkawa falon dukiya da tsari gamida zubi irin na masarautar mali,falo ne da aka shirya nata shi takanas daga can masarautar iyayenta,kama daga ma'aikatan da sukayi aikin zuwa dukka kayan da aka zuba din,tana kishi sosai na yadda kullum gado na sarauta ke bayyana daga wajen aishan,tanajin da tana da iko ko qwanjin qwacewa da tuni ta qwace wannan nasabar.



     Fulanin a yau tana lura da yadda take qarewa falon kallon,sabida kanta tsaye a yau takeyin hakan

"Bismillah mana" fulanin ta fada cikin qoqarinta dakiya gamida jarumta.



        Sauke ganinta fulani saratu tayi saman fuskar fulani aisha sannan ta saki wani irin murmushi wanda ya haddasawa gaban fulani aishan faduwar gaban da tunda take bata taba jinta ba akan kishiya,sai saratun ta bude baki a nutse tace

"Haifaffiyar diya ga masarautar mali,mata ga sarkin yau,uwa ga sarkin gobe ko?" Ta qarashe maganar ta sigar tambaya,bata tabajin ta kasa magana ba tsahon rayuwarta don sun yada mata magana ba sai a yau,ta hadiye wani abu mai tauri idanunta tsakiyar na saratun kamar yadda itama take kallonta,tana kuma jin dadin sauyin tanayinta

"Shi jaje ai ba lallai sai a zaune akeyinsa ba,basai na zauna ba,don a duk yadda ta kama yinsa ake,fata dai a taya wanda akewa jajen alhini" saita soma takawa tana nufar qofa,sai kuma ta tsaya

"To uwar yarima....au a yanzun fa bai kamata ke daya a rinqa kiranki da wannan sunan ba,muma ya kamata mu shiga ciki,don da alamu damar zama hakan ta zama ta mutane da yawa,duk da bamu da cikin haifar diya maza,sai ya huwacewa yaran namu mata,kinga ko cikin jikoki a laluba,wala'alla a dace da kinin abdul'azeez,kinga shikenan.....baki alaikum" ta qarasa tana sake sakin murmushi

"Kinga dai na manta zan fita ban miqa saqon jajena ba,ina miki fatan nasarar tsallake wannan guguwar data kunno muku,duk da bawai har can qasan zucia ba,na tabbatar kina sane da dukka dokokin masarautar kaisa ko?,to Allah ya sanya iya kanta kawai yariman namu ya tsaya,kada aje allura ta tono garma kuma.....na barki lafiya" daga haka ta saka kanta ta fice tana jin wani nishadi da farinciki yana yawo da ita,don tunda take bata taba ganin damuwa firgici saman fuskar aisha ba sai yau,abinda suka jima suna son gani amma basu gani din ba sai yanzu,ba shakka ita duk wanda ya aiwatar da wannan shirin ya mata dai dai,tana kuma fatan abun ya tsawaita,ta yadda zaiyi wancakali da dukkan dama da dajarta harda martabar aishan da iyalanta..



       Fulani saratun na fita itama ta miqe tana jin kamar saman allura take,jikinta ko ina zufa yake fitarwa,ba shakka maimartaba na gab da sanin wannan lamarin tunda har takai ga kunnuwan abokan zamanta,wani tsanar bilkisu ta darsu a ranta,yarinyar tana son zame mata tauraruwa mai wutsiya,anya kuwa ba komayya tayi suka hada hannu da abokan gabanta aka shirya dukkan wadan nan abubuwan ba sabida a rusata?,tunda yarinyar ta shiga cikin rayuwarsu komai yake tafiyar mata a hagunce,amma babu babban mai laifi irin azeez,lallai wannan karon zata ture dukkan wata soyayya ta hukuntashi yadda zaisha mamaki shi karan kansa.



      Zaune yake saman daya daga cikin kujerun falon yana kurbar coffe mai zafin gaske kamar zai qona harshe,dagashi sai boxer wanda hakan yayi silar tonuwar asirin qaqqarfan jikinsa dake a murde,da kuma lallausar gargasar data yiwa jikin mashi qawanya,kama daga qirjinsa singalalin qafafunsa zuwa na hannayensa.



       Fuskarsa a yamutse take qwarai,kamar yadda zuciyarsa take a yamutse,tun jiya yake lissafin yadda zai tafi nigeria ba ya barsu a brasil,ji yake kaman zaiyi wani nisa dasu mai yawa wanda kamar ba zasu sake haduwa ba kenan,kaman zasu bace masa bat.



      Wayarsa dake gefe ta dauki ringing,saiya shareta kawai,tayita kida tana katsewa har sai daya gaji ya duba mai kiran nashi.



      Daya daga cikin informers nashi ne daya dauka haya,tunda yaga sunan yasan cewa akwai labari,don haka babu jinkiri ya daga wayar ya kara a kunnensa

"Nigeria?....ok thanks" ta fada yana katse kiran.



      Cilla wayar yayi saman kujera yana fidda nannauyan numfashi daga bakinsa tare da hancinsa,tabbas ta sauqaqe masa kewarsu da yakeji,tafiyar tata kuma zuwa nigeria tayi masa dai dai,hakan shi zai bashi cikakkiyar damar da zai daidaita dukkan al'amuran,yanajin zuwa yanzun shima babu wani abu daya rage masa ko ya masa saura a brasil,don haka ya aje cup din kai tsaye ya nufi daki bayan ya dauki wayarsa,ya kuma yi booking flight,wanda ya kama zai isa nigeria ne ranar da ake gabatar da hawan daba din.




  *_ABUN BOYE........_*



    Rana ce ta musamman ga dukkan jama'ar qasar kaisa bama masarautar kadai ba,saboda rana ce da akanyi hawa na musamman,sarkin kaisa yakan kewaya jama'arsa waje waje,sukan tattaru su miqa masa gaisuwa ga wanda baida zarafin ganinshi cikin fada,wanda kume keda zarafin ganin nasa kan riskeshi acan ya miqa tashi gaisuwar,yakan zauna har zuwa lokacin sallar la'asar,wanda daga sallar la'asar dinne kuma zai wuce cikin gida ya gana da 'ya'yansa gamida jikoki da kuma 'yan uwa da suka samu halartar bikin.



       Kowanne sashe na gidan kan zamana cikin baqi,hakanan kowa kan kasance cikin ado kamar bikin sallah,yaudinma haka ta kasance,saidai ga fulani aisha,sam bata taba ganin birkitaccen bikin hawan daba da yazo mata a hagunce,a kuma yanayi mara dadi ba irin wannan,don gaba daya bata nutsuwa ko kwanciyar hankali,ta sake baza da linka masu duba mata hotunan fiye dana baya,wanda akaci gaba da tsintosun kuwa kamar ana ruwansu.



       Abinda ya sake tada mata hankali kenan,duk da tarin kwalliya da adon daga caba da sutturu masu azabar tsada da daukar idanu,duk wani abu data saba yiwa mai martaba a irin wannan rana batayishi ba,donko zuwa da suke masa rakiya sanda xai hau doki bata samu zuwa ba,wannan ya faranta ran adama da saratu,musamman adama da tuni ta gama shiryar tashin bomb a yau wanda zai qarasa gille sauran dukkan wata nutsuwa data yiwa aishan saura.



        Tsaye take a daya daga cikin bedroom dinta,tana duban tulin hotunan dake cikin wata babbar leda,yayin da guda daya ke riqe ahannunta ta tsura masa idanu,saika rantse da Allah kallonsu take,saidai tayi nisa ne a duniyar tunani da kuma neman mafita.



       A nutse afnan data yi ado sosai cikin suttura ta alfarma wadda ke alamta inda ta fito,ta turo qofar dakin mahaifiyar tata gami dayin sallama,adan firgice fulanin ta dago tana amsawa gamida qoqarin kifa hotunan saman madubi.



       Tuni afnan ta riga data fuskanci me take boyewar,wanda tuni ita ta ganshi tama mallaki wasu daga ciki,kamar yadda wasu daga cikin jama'ar masarautar suka mallaka.



       Idanunta akan mahaifiyar tata ta qaraso dakin

"Lafiya afnan?....ya akayi?"

"Su yaaya sumaira ne ke jiran fitowarki tun daxun shuru" tayi maganar tana miqa mata hotunan data shigo da su.



      Batabi takan maganar jiranta da yaran nata keyi ba,illa miqa hannu da tayi da hanzari tana karbar abinda afnan din ke miqo mata,cikin zuciyarta tana fatan Allah ya sanya ba wani mummunan saqon bane.



     Hotunan nan ne dai da kullum idaniyarta ke kwana su wuni suna kalla,ta kuma kwanta ta tashi tana mafarkinsu,hotunan dake barazana da kwanciyar hankalinta nutsuwarta darajarta da martabarta,saidai abun yakai har afnan ta samu itama?,lallai nan da wanu dan lokaci zasu isa hannun mai martaba.



      Muryar afnan itace ta katse mata dukkan tunanin da takeyi

"Ya azeez....da tsohuwar matarsa,qawata bilkisu bilyamin....yarinyar da aka tsigeta daga karatunta,aka rabata dashi,sannan akayi mata auren dole ba tare data shirya ba,aka katse duk wani buri da mafarkinta saboda laifin da bata aikata ba,saboda biyan buqatar wasu,yarinyar da nake kwana na tashi kullum.ina tunanin ko tana ina?,ko a wanne hali take yanzu?,ashe da zuriata kuma jinina wajen cutatar da rayuwarta" takai qarshen maganar da alamun abun yana mata daci a rai,hakanan idanunta nakan fulani,wadda itama ra kafeta da idanu tanason karanta da kuma fahimtar me afnan din ke cewa.



       Tsaf qwaqwalwarta ta soma shirya mata kalaman,saita hade rai sosai tana duban afnan

"Ke....banason sakarci,ki barmu da yarfe da bata sunan da akeson mana,shine ke kuma zaki shigomin da wasu kalaman banza" murmushi ta saki

"Kimin afuwa,ki kuma yafemin,ba yarfe ko bata suna bane ya kamata ace ya dameki ba ammi,saboda dama duk nisan jifa qasa zai fado,hakanan komai daren dadewa dole wannan sirrin ya fito....abinda yafi dacewa ki damu dashi shine,yadda kika sarrafa rayuwar baiwar Allah ta hanyar da kikaso,sannan kuma yaya rayuwar tata ta kasance bayan nan?,naga bakya qauna ko kusa atuna miki ta taba zama surukarki ko ammi?....to yanzu dai hanyoyi guda biyu suka rage mu daga ragowar martaba da qimarmu...na farko....inma ki fita ki shaidawa duniya cewa wannan din tsohuwar matarsa ce da suka taba aure,an dauki hoton sanda suke a matsayin ma'aurata duk da nasan ba haka bane,to amma ta yaya zaki musu bayanin yadda auren ya gudana?,shin zasu gamsu?,tunda basu da masaniyar sanda aka qullashi?,.....wa imma kuma ki bar mutane kowa yaci gaba da tofin alatsine garesu gami da aibatasu,ana mata kallon karuwa da kwartonta,wanda aikata hakan kamar qarin wani zunubinne akan wani,kuma shizai qarasa rugurguza martaba da qimar da kiketa mana tattalinta....." Tsawa tayi saurin dakawa afanan,tanajin kanta ya soma yamutsewa,dukkan idea na kubuce mata daya bayan daya,saita nuna mata qofa da yatsa

"Fita ki bani waje tun bsn bata miki ba" murmushi afnan ta saki ta soma takawa zata fita din kamar yadda ta buqata

"Ke mahaifiyata ce da bani da kamarki,hakanan bazanso naga kin shiga kowanne irin hali ko yanayi mara kyau ba shi yasa na tunkareki da wadan nan maganganun,kiyi haquri ki dubasu dakyau tun lokaci bai qure mana ba" daga haka ta fita din kamar yadda ta buqaceta.



       "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ta soma ambata a fili,kana ta zame ta zauna gefan gadonta tana zame dankwalin kanta da takejin ya mata nauyi,yaya akayi tayi sake haka lamura suka kwabe mata ne?,wannan itace babbar tambayar da take jifan kanta da ita.

7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 64

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




      Kusan cikin dakin ta wuni,har sanda akayi sallar la'asar,ta soma jiyo muryar mai martaba cikin masallacin dake cikin gidan,yana daura auren wasu daga cikin barorin gidan maza da mata da suka samu mazajen aure,wanda yake kamar aikinsa ne,ya dorwa kansa alhakin aiwatar da haka duk shekara indai aka samu masoyan da suka daidaita kansu,yakan sanya a hada bikin daba din da bikin auren nasu,hakanan shike musu komai na aure,yakan ce Allah ya sanyasu ne qarqashinsu domin muma muyi musu hidima,ya sanya wasu daga cikinsu sun zama bayi a garemu,bayan ga mahaliccinsu kawai wannan bauta take,kyautatawarmu a garesu shike nuna zallar godiyarmu ga mahaliccinmu kan ni'imomi da baiwa daya mana masu tarin yawa.



       Kusan duk abinda zaiwa barori matan da shawara da kuma sanya hannun fulani aisha yake aiwatarwa,wanda kusan ita ta qarfafi wannan shawarar tashi tun shekarun baya,takan kuma sanya itama nata kason a cikin hidimar masu kayan aure,badon mainartaba ya gaza ba,a'ah,tana yine da sunan sadaka da kuma neman lada,saidai a wannan shekarar kusan komai saidai taji labari,don bata da wannan nutsuwar,illa kudin dai data saba bayarwa bata fasa ba.



       Sai da aka gama daura auren kaf a kunnunta sannan ta miqe da qyar ta shiga bandakinta dake cikin dakin ta daura alwala ta tada salla,koda ta idar tana saman abun sallar tana tunane tunane,ta duba lokaci,taga akwai sauran kusan awa guda daga sanda zasu isa wajen maimartaba,don haka taci gaba da xama saman abun sallar tata.



       Saidai me?,bata jima ba saqo ya risketa ta hanzarta zuwa sassan mai martaba da gaggawa yana da buqatar ganinta,ta zuba jakadiyar idanu gabanta na wani matsanancin faduwa,yanayin yadda aka kawo mata saqon yana nuna kamar ba lafiya ba.



       Alkyabbarta kawai ta zura wadda ke aje tun daxun a gefe,sabanin daa da saita tsaya ta sake wanka,ta kuma fesa ado na qasaita,irin adon da tasan mai martaba na mutuwar so,irin adon da tasan zai tafi da hankalinsa,saidai a yanxun duka bata jin wannan nutsuwar.



       Tun a hanya ta lura da yadda masu satar kallonta suka yawaita,tun a nan dukka wani karsashi da qwarin gwiwa da take baiwa kanta ya soma bajewa yanayin nasa guri,tana tattaroshi amma yana sake sulalewa,da haka ta isa ga sassan mai martaba,kana ta qarasa kai tsaye ga turakarsa.



        "Wannan babban abun tashin hankali ne a garemu baki daya.....abun kunya tur da ala wadaine,tun sanda nasamu saqon na kasa samun nutsuwa bare barci,abdul'azeez fa Allah ya taimakeka?" Abinda ta soma tsinta kenan daga muryar adama,wadda ke zaune gaban mai martaba tana sharce qwalla.



        "Ya Allahu,ya naseru"ta furta cikin ranta,tana neman daukin ubangiji sanda suke hada idanu da maimartaba,wanda bisa alamu shigowarsa sasaan nasa kenan,ya soma rage kayan jikinsa adaman ta cimmasa,don bai gama fidda kayan da yayi hawan gaba daya ba.



     Karon farko a rayuwarta dataji ya mata wani mugun kwarjini,irin kwarjinin da takanji jama'ar da yake mulka wadanda suke qarqashinsu suna labari lokaci zuwa lokaci,gwiwa a matuqar sanyaye ta dauke kanta daga adama daketa hada hawaye bilhaqqi,ta isa gabanshi ta zube cikin sanyin jiki qwarai da sanyin murya tace

"Barka da warhaka"

"Barka kadai aishatu" ya amsa mata cikin kulawa yana jin tausayinta a ranshi,saboda ya lura da yadda jikinta yayi sanyi qila itama ta samu labarin komai katsam kamar yadda ya samu,yake raya haka a ranshi,saidai kuma,akwai alamun bacin rai a muryarshi da yake dannewa sanda yayi maganar.



       Kai tsaye ya miqa mata hotunan data tabbatar cewa sune,ta kuma soma gajiya da kallonsu,don ba azeez da yake danta ba,hatta da bilkisun ta haddace dukkan surori da kuma kamanninta tsabar kallon hutunan.



        Kamar ba zata karba ba,sai kuma ta tuna aikata hakan kamar bada wata qofa ko dama ce ga adama dake zaune a gefanta ta zuba mata idanu kamar tsohuwar mayya,wanda ta tabbatar tanason ganin reaction dinta ne kawai,don haka tasa hannu biyu a hankali ta karbi hotunan,ta dawo dasu gaban idanunta,tayi kamar ta kalla kana ta kifasu saman cinyarta tana fadin

"La haula wala quwwata illa billah" tana rufe idanunta saboda yadda taji zuciyarta na wani irin bugawa



     

       "Hmmm...ana zaton wuta a maqera,sai haquri,yaran yanzune ka haifesu amma baka haifa halinsu ba" adama ta soma zuba,mai martaba ne ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yana kallon aisha

"Kina da masaniya kan wani abu daya danganci hoton?" Ta yaya zata amsa masa gaban wannan makira kuma azzalumar matar,wanda daga shigowarta zuwa yanzu ta fahimci ita ta shirya komai,sannan tayi tattaki ta kawo masa hotunan har dakinsa,don haka kawai saita girgixa kai alamun a'ah.



      Dauke dubansa yayi daga gareta,kana kai tsaye ya janyo wayarsa ya soma laluben lambar abdul'azeez kai tsaye.



       Daidai lokacin da yake xaune falonshi,kace kace tsakiyar takardu laptop da wayoyinsa,bayan ya gama tsara da jiran awannin tafiyarsa su cika.



      Wayoyi yake amsawa tare da kira,yana kuma tsarawa kansa hutu da na tsahon wata guda daga dukkan kamfanoninsa da harkokin kasuwancinsa,yana tura takardun inda sukka dace su sani,yana kuma nada wakilansa,sabida a hasashensa yana saka ran zuwa wata guda mai zuwa ya gama settling komai,yana fatan hankalinsa ya soma dawowa jikinsa.



     Da sauri sauri yake komai,saboda yana riqe da awannin da suka rage masa na tafiya airphort don sauka a qasarsa nigeria.



       Wayar dake hannunsa ce ta dauki ringing,ganin sunan mai martaba ya sanyashi sake nutsuwa,ya ajjiye biron dake hannunsa ya kwantar da bayansa a makarin kujerar sannan ya daga wayar cikin girmamawa da nutsuwa.



       Baice masa komai ba har suka kammala gaisawa,kana yace

"Inason a yau ka nemi jirgi duk inda yake,ka tabbatar ka kwana a masarautar kaisa" umarnin daya soma bashi kenan,duk da yayi mamakin hakan amma saiya danne yace

"In sha Allahu nan da awa hudu zan iso qasata"

"Allah ya nuna mana" ya fada yana katse wayar,idanunsa kan adama,tariyar maganganun da abubuwan data gaya masa masu yawa ke masa kai komo kan yaron nasa,bayason yace komai bisa zargi,bayason ya yanke komai bisa labari kawai,hakanan bayason wai wai da ance ance,amma magangun data gaya masa kan yariman ba qananu bane,duk da haka shidin babba ne mai hankali,kuma jagora shugaba,yana da buqatar nutsuwa da kwantar da hankali kan duk wani hukunci da xai yanke

"Dukkanku kuje,zan sake nemanku" ya sallamesu gaba dayansu,don yana buqatar yin nazari sosai.



       Wayar azeez yabi da kallo bayan maimartaba ya katse,saiya saki ajiyar zuciya yana sake kwanciya sosai,gefe guda kuma yaji ya sake qaguwa daya isa nigeria,tuni ya gano inda bilkisu ta yada zango,yanajin kuma shine abu na biyu da xai gabatar bayan ya saurari mai martaba,sabida yana da yaqinin akwai dalilin da yasa ya kirashin ya kuma nemi tahowarsa again bayan wanda mahaifiyarsa ta buqata.


     Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



    Ba abinda take sai kaiwa da kawowa tsakanin falukan nata ta dangane da daki cikin tsantsar tashin hankali,tashin hankalin da bata taba shiga makamancinsa kamar yau,ji take inama ace zata iya tsaida komai cak ta kuma sauyashi zuwa dai dai,zuwan abdul'azeez ba qaramar barazana bace a wajenta,gashi mai martaba bai gaya masa dalilin kiran nashi ba bare ya dauki haske,ko kuma tun acan ya gama tsara abinda zaya gaya mishi idan ya iso,uwa uba tanata kiran wayoyinsa gaba daya sunqi shiga,alamu ne dake tabbatar da cewar yana hanya kenan,koya gama shirinsa na baro qasar daga yanzu zuwa kowanne lokaci,idan da so samune zataso ace ita ta soma tozali da azeez din,don suyi magana,su kuma san ya zasu bullowa lamarin,ta yadda komai bazai kwabe ba.



      A wannan yanayin taci gaba da kasancewa,har zuwa lokacin da akayi sallar magariba,sam yaranta sun kasa gane kanta,don basusan meke faruwa ba,bayaga afnan ita kadai,wanda itama babu wanda ta shaidawa banda mama sodangi.



       K'arfe uku na dare agogon brasil,takwas na dare agogon nigeria ya taso zuwa nigerian,sam sai yakega kamar jirgin baya sauri,tafiyar awanni taran ya dinga jinta kamar tafiyar shekaru tara,duk bayan wani daqiqa yana jin kamar ana sake kusantashi da bilkisune da ahalinsa,yana ji a jikinsa wannan tafiyar kamar wani mabudi ne da warwara na dukka matsalolinsa.



       Ga fulani kuwa kusan kwanan zaune tayi,dukkan wani tunani da idea nata sun watse,abu na qarshe data zabawa kanta yi shine,ta kira daya daga cikin malaman da suke mata sauka,ta shaida masa tana da damuwa ayi mata sauka daga nan zuwa safiya a yi sadaka,ta aika mishi da kudin saukar kamar yadda ta saba lokaci bayan lokaci.



       Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶




     Ana kiraye kiraye na sallar asubahin nigeria cikin masarautar kaisa motarsa ta soma shigowa babban ginin masarautar,wanda ke nuna zallar sarauta da alfarma gamida qarfin mulki da gidan sarautar keda shi tun tale tale,hakanan har yanzu yana nan bai gushe ba.



      Kai tsaye sassansa ya nufa kamar yadda ya yankema ranshi,yana ganin yanzu yayi safiya da yawa ya nemi ganin wani cikin mahaifansa ko makusantansa,wanda yana da tabbacin zaije ya samu komai a sassan yadda ya kamata,duk da cewa safwa ta shaida masa ta koma tun shekaran jiya,amma akwai wadatar ma'aikata,barori da bayi.



      Kamar kuwa yadda ya zata din,komai na killace cike da tsafta da tsari,sai ka zaci akwai dan adam a sassan,yayi masauki a katafaren dakin gadonshi wanda yake dai dai da aljannar duniya.



      Abu na farko daya fara hada ruwan wanka mai dumi sosai wanda zai dace da yanayin da yakeso,yayi wanka sosai,yanayi yana duba lokaci,duk da yasan da wuya ya samu jam'in sallar asubar,don yaji sanda suka tayar.



      Jallabiyya kawai ya sanya ya tada tashi sallar,bayan ya idar baiyi gaggawar tashi ba kamar yadda ya saba,saidai yau zaman nashi ya banbanta dana kullum,hakanan yaji ya dade saman abun sallar yana addu'o'i,qari akan wadanda ya saba,baibar saman abun sallar ba,sai daya duba lokaci,yaga yayi dai dai da lokacin da maimartaba kan zauna da duka ahalin nasa a irin wannan safiyar ta washegarin hawan daba,duk da baccin da yakejin yana fusgarsa sama sama amma haka ya yakiceshi,yahau shiryawa sosai cikin shigar dake bayyana gadon sarauta gaba da baya,jinin mulki da qasaita,shigar data qara masa kyau qima da kuma kwarjini qwarai da gaske.



      Duk wannan abun dake faruwa tun daga shigowarsa masarautar har isarsa sassansa fulani adama nada labari daga mutanenta data baza,saboda ta tabbatar yariman zaya iso kamar yadda yace,daga sanda maimartaban yayi kiransa zuwa kowanne lokaci za'a iya ganinsa.




      Murmushin jin dadi ta saki lokacin da ake shaida mata ya riga daya iso din,a hankali ta furta

"YAU ZATA FASHE!" Abun yana mata dadi sosai cikin rai,tana hango tozartar aisha ayau din,don haka ta janyo wayarta ta shaidawa haj fauziyya dake nata sassan wanda takan sauka duk sanda tazo,daga can ita kuma ta kira kamal,suka gama dukka tsare tsarensu ta hanyar wayar.



     Cikin dauriya da dakiya,da kuma rashin son baiwa abokan gaba qofa da zasu fahimci galaba akan dukkan tsarinsu a safiyar fulani aisha ta shirya,cikin shigarta dai tayau da kullum ta qasaita dake tsone idanun abokan xamanta,saidai a yau din maimakon alkyabba,tsadajjen mayafi na musamman ta nade jikinta da lallausar atamfar da tayi adonta,ta kuma iso katafaren dakin cin abincin da aka tanada saboda ranaku ire iren wadan nan cikin yaranta da 'yan jikokin da aka haifa mata.



      Kusan kowa cikin walwala yake a wajen idan ka debe ita,duk da tayi qoqarin qaryata hakan akan fuskarta,da kuma qoqarin da tayi ta aro walwala ta saka fuskar tata,saidai kallo daya mai martaba yayi mata ya fahimci ainihin halin da take ciki,saiya alaqanta hakan da abinda ya faru jiya,wanda koshi din zuciyarsa ta cika da damuwa,damuwar kada ace gudan jininsa da yake saka ran xai gajeshi,gudan jininsa da duniya duka take kallo take kuma sake tambara sunanshi da matsayinsa ya jawo musu wani abun fada da zai rusa darajarsu da martabarsu,hakan har a ransa yaji tausayin aishan,saboda yasani cewa tana da tsaiwa kan 'ya'yanta,don haka saiya yawaita sakota a hirar tasu.



     Duk da wajen akwai surutai na tashi,kowa na hirarsa da wanda tasu tafi zuwa daya,amma saratu da adama na ankare,kowacce kuma abinda take saqawa cikin zuciyarta daban.



      Sallamarsa cikin dakin yasa surutan suka dauke cak kamar anyi ruwa an dauke,hakanan numfashin fulani aisha yaso daukewa cak itama,cak ta tsaya tana addu'o'i cikin ranta,addu'o'in Allah ya sanya bashi bane,Allah yasa kunnuwanta ke mata gizo,duk wannan addu'ar da take ta kasa waiwaya ta tabbatarwa idanunta abinda kunnuwanta suke ji din.



      Daidaiku ne suka amsa sallamar tashi,ciki harda me martaba daya zuba mishi idanu cikin zuciyarsa shima yana addu'ar Allah ya sanya abinda ya gani din ya zama ba gaske bane,jikinsa yaji yayi sanyi sanda suka hada idanu da me martaba,kusan yana daha cikin mutanen da suka san halayyarsa tsaf,suke iya gane magana daga idanunsa kafin ya fadeta.



       Kamal shike zaune kan kujerar da a qa'ida nan ne wajen zaman azeez din a duk lokaci irin wannan,yauma bai fasa nufarta,idanunsa cikin na kamal din,kamar yadda kamal din shima ke kallonsa.



       Mai guri yazo dole me tabarma ya nade,hakanan yanaji yana gani ya miqe ya bashi wajen,ya koma kujerar dake kusa da ita,yana qwafa cikin ransa gamida fadin yau dai za'a yita ta qare ko?.



       Cikin girmamawa ya gaida dukkan wanda ya girmeshi a wajen,saura dake qasansa kuma suka gaidashi harda yayyensa mata da tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,duk da ransu baison hakan amma dole suka gaidashin,musamman walida da takejin kamar ta ciji harshenta,batasan me yasa suke raina kwanaki arba'in da wani abu data bashi ba,duk tsiya aidai ta girmeshi.



     Baima san me suke ba,don cikin kulawa ya maida hankalinsa ga iyayensa yana tambayarsu lafiyarsu,hakanan kowanne ya danne abinda ke ranshi ya amsa mishi,daga haka cin abincin yaci gaba da gudana,amma saidai hirarrakin dake tashi dazun sun ragu qwarai,hakanan shima dai yana zaune ne kawai ba tare daya dauki komai yaci ba,don dama haka al'adarsa take,ya riga daya saba,hakan zauna din,amma bai fiya cin komai ba har a tashi.



       Dan gyaran murya kamal yayi kamar wanda ya qware bayan sun hada idanu da fulani adama,yasa tissue yadan goge gefan bakinsa badon ya baci ba sannan yace

"Ko yaushe sake zama manyan qasa kuke,sati biyu daya wuce na ganku a dubai a hotel kai da wasu baqi mata,hala abokan kasuwancinka ne kazo kama musu masauki?" Dago kanshi yayi daga amminsa da yake ta nazari tun daxun,ya lura akwai raguwa kuzari da walwala tattare da ita,yana fatan hotunan datace masa ta gani ba daukakar lamarin tayi ta sakashi haka cikin ranta ba,yana addu'ar wannan karon lamarin yazo da sauqi,ta tsaya ta fuskanceshi,komai yazo qarshe.



     Idanunsa masu cike da kwarjini ya xubawa kamal din yana mamakin meya kawo wannan zancan a irin wannan wajen,gaban qannenshi da yayyensa da yaransu,sannan uwa uba gaban mahaifi da mahaifiyarsa,baya ga haka baima fuskanci wadanne mata ya gansu tare ba,hasalima shi ba kasafai ya fiya qulla harkar cinikayya da mace ba komai kudinta ko qasaitarta,saidai ko ta hadashi da É—a miji ko É—an uwanta,don shi yace sam bazai iya jure musu ba,baya tolerating nonsenses.



      "Kamal....kaima da tone tone kake,banda abinda mutum kamarshi,da dukiyarsa irin haka kyau da asali ka rabu da ganinsa da wasu....."

"Gaskiya fa....to ai wayewar kenan,zamanin ne yazo mana da haka" adama ta fada tana tsiyaya kunun acca a cup,tana bada amsa kamar wadda ke magana bilhaqqi.



     Gyaran murya mai martaba yayi,wanda hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,kana ya shigo da wani xancan da kusan ya shafi kowa dake zaune a wajen.



      Tsahon awa guda da rabi sannan ya sallami duk wani wanda yake qasan yariman ne,ma'ana azeez din ya girme mishi,sai sa'anni da wadanda suke shekaru guda ne kadai sukayi saura,kana ya buqaci kowa ya fito zuwa babban falon hutawar dake maqale da dakin cin abincin. A sanyaye fulani ke takawa,daqyar kuma ta samawa kanta mazauni waje daya tana qoqarin sake daidaita kanta da numfashinta.

7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 65

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




       Doguwar addu'a mai martaba ya fara jaa,sannan kowa dake wajen ya bashi hankalinsa bayan an shafa,da wanda yasan meya zaunar dasu a wajen,dama wanda bai sani ba,gyaran murya yayi,idanunsa kan azeez sannan ya fara magana.



     Wanda fulani ta dinga jin kamar yana fita da numfashinta ne

"Abdul'azeez....iyakar abinda na sani kuma Allah shine shaida,munyi dukkan wani qoqari daya kamata ace munyi wajen baka tarbiyya,mun baka kulawa da tarbiyyar data dace dakai,mun sadaukar da komai namu saboda rayuwarka ta inganta,na tsaya tsayin daka na nuns maka me kyau da mara kyau,na nuna maka halas da haram,duk da nauyin dimbin al'ummata dake kaina hakan baisa na sarayar da haqqin tarbiyyarku daga wayuna ba,daga kai har 'yan uwanka.....amma abun mamaki....abun takaici abdul'azeez,sai gashi komai yana shirin tashi a banza.....giyar kudi ta soma dibanka,kanason watsa mana qasa a idanu,abdul'azeez me kakeson zama ko kuma meka zama?" Ya qarashe maganar cikin nuna takaicinsa qarara

"Allah ya baka yawan rai....akwai wasu abubuwan da kana gani ana aikata ba dai dai ba amma kake yin shuru,kusan wannan ba shine farau ba,banson yin magana ne kawai saboda kada ayi maka fassara ta daban.....amma kamal gashinan....tare suka zauna ai a gida daya a mexico,babu abinda bai gaya min ba kan irin lamuran da yaga yana gudana,nace babu ruwanshi ya cire idanunsa yayi tasa sabgar saboda gudun fassarar mutane" hannu sarki abdallah ya daga mata ba tare daya dubu sashen da yake ba,bayason ta qara masa wani ciwon kan wanda ke damunsa,kota dora zuciyarsa bisa bigire na zargi ko zato,sai ya saka hannunsa gefan tuntun daya dora hannun nasa akai,ya ciro hotunan da adaman ta bashi tun ranar ya miqa masa

"Wacece wannan abdul'azeez?"

"Saidai kace tun yaushe suke tare ai" adama wadda tunda aka fara batayi magana ba sai a sannan,saboda sam ba haka taso ba,babban tonon silili taso gaban su waziri da sauran 'ya'yan fada masu tarin yawa,amma ko a yanzunma indai ya É“aci idanun mai martabar ai kwalliya ta biya kudin sabulu

"Saboda lamarin ya girgixani sosai....ina ganin hoton saiga kamal ya shigo,shiya shaida min sun jima tare,tun a mexico" ta fada tana sake kaurara maganar donta samu mazauni me kyau a zuciyar maimartaban.



      "Bilkisu ce,kuma matata ce" abdul'azeez ya fada karon farko tunda aka fara maganar,cikin wata kakkurar murya dake cike da dakiya da kuma jarumta,idanunsa da suka juye suka sauya launi saman fuskar adama,wadda bai taba jin ya tsaneta ba irin yau,saboda muraran ya hango zallar qiyayyarsu cikin idanunta,qiyayyar daya jima yana jin amminsa tana fadin ita adaman tana musu.



      Kusan dukkansu babu wanda wuta bata daukewa ba,saboda kalaman da suka fita a bakinsa babu wanda ya tsammaci jinsu,ta sashen abokan hamayya basu so samun amsa irin wannan da wurwuri daga bakinsa ba,inda unda sukaso a fara dashi,daga bisani a zarce da maganar DADIRONSA CE,duk da a yanzun ma basu yarda da kalmar mata daya fada ba,sunfi zaton ya fada ne kawai don ya kare kansa,ya rage girman laifinsa idanun sarki abdallah,shuru ya ratsa falon na wasu sakanni,kafin sautin salatin hajiya fauziyya wanda ya taho da kukan munafurci ya gauraye falon

"La'ilaha illallahu....muhammadurrasulullahi,sallallahu alaihi wa sallam......ke kuwa aisha kina me har dan cikinki xai wannan aika aikar baki sani ba?" Ta fada tana kama haba tana duban fulani aisha,wanda ba komai take fuskanta ba a wajen

"Tabdi,lallai inda ranka kasha kallo...abun har yakai ga auren dadi......".



      Da sauri maimartaba ya daga mata hannu

"Ya isa!" Ya fada da kaushin murya,wanda ya sanyasu shiga taitayinsu,sai mai martaban ya dubi sauran wadanda ke gurin dukkansu ya basu umarnin tashi su fita,ha rage daga matan nashi sai haj fauziyya.



      A hankali ya kuma sauke idanunsa da suka sauya kala kan azeez

"Kasan abinda bakinka yake fada azeez?" Cikin wata dakiyar ya gyada kanshi yana sadda kan nashi qasa,karon farko da wani irin kunya da nauyin mahaifinsa ya kamashi

"Afuwa nake nema,amma na sani,matatace,kuma har yanzu matatace" kalmarshi ta qarshe ita ta farfado da fulani ta daga nata idanun ta sauke akanshi.



      Wani nannauyan numfashi mai martaba yake saukewa,kana ya maida dubanshi kansu su da sukayi saura

"Ku tashi ku bani waje,abdul'azeez kawai nake da buqatar gani a nan" dukkaninsu ba haka rayukansu suka soba,kada ma hajja fauxiyya da adama suji labari,amma babu wadda keda ikon musa masa,dole suka miqe suna kakkabe jikinsu,wanda fulani saratu ita tayi saura a qarshe,domin dukkan abinnan dake faruwa ganinshi take kamar a majigi,ita kadai tasan iya adadin kudaden data kashe akan azeez din,an riga da an mata albishir din cewa....tabbas babu makawa mace daya azeez din zai aura har qarshen rayuwarsa,macen kuma zata haifa masa diya mace qwaya daya itama,zai rayu bashi da baya,bashi da wani magaji,hakanan rayuwarshi ba zata yauqaqa ba bare tayi tsaho,sai gashi a yanxun ana maganar yana da wata matar daban wadda dukkaninsu basu san da zamanta ba,tabdijan,turqashi!,qaqa qara qaqa,Allah ne kadai yasan yawan kudin data sadaukar ta kuma sarayar,haka ta dinga takawa qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba.



       Fulani aisha ce kawai tayi saura a wajen,saiya dubeta

"Har ke,kema ki bamu waje" kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta miqe itama,amma saita kasa tafiya bayan ta fita,ta zauna a falo na farko kafin wannan falon,ita kadai shuru,tana jin kamar ana yamutsa duniyarta,ta riga data sani a yau kam babu wani sauran rufa rufa ko boye boye,lallai yau komai zai bayyana,kamar yadda Allah ya yiwa azeez din kwarjini to ya gada ne daga mahaifinsa,ta tabbatar tunda ya sallamesu yana son jin gaskiyar komai ne daga bakinsa,wanda ta riga ta sani da wahala ya maka irin wannan titsiyen ka iya boye masa gaskiya,saidai ta wani sashen tana ji a zuciyarta tamkar gata ya mata,kamar wani rufin asirine ya mata daya sallamesu gaba daya,wannan tonuwar qatoton asirin ba'a yishi ba gaban adama da saratu.



      "Koda baka tambayeni ba,koda komai bai bayyana gareka ba ayau nayi niyyar shaida maka komai,amma ina mai neman afuwa daga gareka nida ammi akan dukkan abinda zakaji"

"Sanar dani komai,ban buqatar ka boyemin komai" ya fada kansa taaye,cikin ranshi cike da addu'ar Allah ya sanya ba babbar kwaba da zata rusa lahirarsu gaba dayanta suka aikata ba.



      Babu abinda abdul'azeez din ya boye masa,ya bayyana masa dukkan wani abu daya faru a can baya din

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,lahula wala quwwata illa billah" shine abinda kawai mai martaba yake iya furtawa,kansa da idanunsa na kallon qasa,shuru ya ratsa falon,kowa da abinda ke kai kawo a ransa.



       Sosai abdul'azeez yakejin wani abu mai nauyi yana ratsashi,kunya da nauyin mahaifin nasa na sake dabaibayeshi,amma wani sashe na zuciyarsa yana jinsa sakayau,wani nauyi da zuciyarsa ta dade tanaji a yau din sai yakejinta fayau,sai yakejinta empty kamar babu wani sauran nauyi daya rage a cikinta,amma kuma wani sashe na zuciyar tashi cike yake da fargaba tashin hankali gami da taraddadin irin hukuncin da zai yanke masa.



       Yasan halinsa sarai,bashi da sauqi ko kadan,hakanan baya qyalewa idan har ka aikata wani abu na ba dai dai ba,komai kuwa kusancin da yake tsakaninka dashi.



       A qalla sun kusa kwashe mintuna a shirin a zaune a haka ba tare da wani canjin yanayi ba,daga bisani ya tsinci muryar mai martaba yana cewa

"Tashi kaje abdul'azeez,tashi ka bani waje" bashi da wani zabi daya wuce ya tashin,don idan ya zauna ma bashi da sauran wani abu da zai fada,ko kuma wani abunda zai iya kare kansa ko ya kawo masa sassauci daga wajwn mai martaba,haka ya miqe yana takawa gami da laluben hanya da idanunsa da sukayi jajur,adam's apple dinsa ba abinda yake sai motsawa sama da qasa,alamun akwai wani abu daya taba zuciyarsa shima.



      Tana zaune ya giftata amma saita kasa ce masa komai harya wuce,da alamu ma bai lura da zamanta a wajen ba,sai daya bacewa ganinta sannan ta miqe cikin wata iriyar tafiya tana harhada hanya ta koma ciki.



      Tun kafin ta qarasa sallamarta ya daga mata hannu gami da yi mata nuni kan ta fice,bata musa ba ta juya wani abu yana tokare mata wuya.


*_tofa!_*



           *_Bilkeesu_*



       Kai tsaye garinsu abbaa kawai suka wuce a mota bayan jirgi ya saukesu a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano don su fara duba jikin mama.



       Kusan wannan ne zuwansu amatu na farko tun bayan da sukayi wayo,hakan ya sanya sukaita baza ido suna kalle kalle tun a hanya har bacci ya daukesu.



        Babban gidane gidansu abbaa,gidane na masu sukuni wanda ya qunshi mahaifi da mahaifiyarsa,sai kakanninsa wadanda suka haifi babansa,saidai tuni Allah ya yiwa kakanshin rasuwa,sai matarsa da har yanzun take raye suna kuma zaune tare da it,hajiya fatsima,tsohuwa mai ran qarfe,macace mai son jama'a da dattako,hakanan tasu tayi mugun zuwa daya da bilkisu tun ma tana qaramarta,da Allah ya sake hadasun yanzun kuma sai sabon nasu ya dora,don lokaci zuwa lokaci takan kira ta ko sanda tana brasil.



      .


      Sanda suka isa sashen maman abbaa din suka sauka gaba dayansu,macace itama mai kirki faran faran da son jama'a,alamu sun nuna cewa taji jiki sosai,amma ba laifi sauqi yana samuwa.



      A yunwace suka qaraso,hakan ya sanya babu dadewa ma'aikatan gidan suka gabatar musu da abincin,saida sukaci suka qoshi sannan bilkisu ta wauce sashen hajiya fatsima da suke kira da hajiya.



      Da murnarta ta tarbeta tana tsokanarta tamkar dai yadda ta sabawa jikokinta,bilkisun na maida mata cikin dariya ta zauna suka gaisa,sun sha fira sosai kafin ta sanya mai aikinta ta gyara mata daki daya cikin dakunan dake sassanta,wanda su biyune kadai a sassan daga ita sai wata jikarta data dauko take tayata zama.



       Sanda ta miqe ta miqe da niyyar isa dakin hajiya ta fadi maganar data tsaidata

"Har yanzu dai 'yata babu maganar wani?,ina nan inata kasa kunne naji kin kawomin ango,ko yanzun ma dana ganku,na zaci abunne ya taso" murmushi kawai ta yiwa hajiyan,saboda ko wancan watan abbaa da kanshi ya soma tada maganar,ita kuma a yanzun babu abinda ke daga mata hankali irin zancan aure,da wanne fuska zata kalli dukkan wanda ta aura ta gamsar dashi irin auren da tayi a baya

"A tayamu dai da addu'a" ta bata amsar data fi yawan bayarwa,don ita kanta tasan babu yadda za'ayi dama su zuba mata idanu ko tace zata dawwama a haka,amma kuma yaya tafiyar zata kasance?,me goben zata haifar mata?,wadan nan sune tarin tambayoyin da batasan amsarsu ba.



      Da zancan a ranta ta shiga dakin,wanka ta soma yi saboda huce gajiya,ta aika sassan mama akira su amatu suyi wanka aka shaida mata tuni sunyi,don haka saita qyalesu,ta bayar aka siyo mata sabon layi,don nata tsohon na ainihi yana gidan anty zuhriyya na nan,saisun isa kaisa sannan zata daukoshi ta dora,yanzun kuwa tanason yin waya ne.



      Hannatu ta fara kira ta shaida mata sun iso,nan da kwanaki kadan zasu qaraso kaisa,murna kamar tayi me

"Yanzu kuwa zanje na gayawa baba,nasan zaiyi murna" murmushi kawai bilkisu tayi,tana mamakin sauyawar mahaifin nata haka,abun kamar a mafarki,bata zata zai canza ba sai gashi lokaci guda ya canza din.



      Bayan ta gama da ita saita kira farida qawarta,ta shaida mata itama sun iso lafiya,suka sha hira sanna sukai sallama,tana niyyar ajewa saita tuna da assadiq,tasan yana nan yana tsimayen samun numberta tanan,ta jima bataga mutun mai haqurinshi ba,koda dr adam bai kama qafar assadiq wajen haquri ba,don haka ta laluba ma'ajiyar number dinta tayi kiranshi.



      Sosai yaji dadin kiran nata,har ya kasa jurewa sai daya fadi

"Harna cire tsammani,ashe jan ajinne har haka,nidai a tausayamin don Allah,a jani a hankali" dariya ma ya bata,saita sake sosai ta bashi lakacinta suka sha hira,inda daga bisani ya barta ta huta.




      Kwanansu biyu a ringim qanwar abbaa ta haihu,washegari anty zuhriyya tasa suka shirya gaba daya tace zasu rakata barka.



      Acan suka kusan wuni saboda an dade ba'a hadu ba,yammaci lis suka taho,kan hanyarsu sunata hira yaran na hayaniyarsu,basuyi nisa sosai ba gungun shanun dake tsallake titi suka sanyasu tsaiwa dole,haka suka dinga wucewa kamar ba zasu qare ba

"Kai bafulatin mutum.baidai wayo ba,yanzu wadan nan shanun idan kinji biliyoyin kudinsu zaki mamaki,amma ya gwammace yayita bautata musu ya qare rayuwarshi a jeje,guda bazai iya yankawa yaci ba,ke idan yaga ma tana ciwon ajali zama yake yayita mata kuka harta mace don bazai iya yankata ba" dariya sosai anty zuhriyya ta bawa bilkisu,saidai batayi mamaki ba,don tasan wasu daga halayyarsu na qaunar dukiyarsu,sai kuma dariyar tata ta soma raguwa,saboda tuna hauwa'unta da tayi.



       Duk tsayin shekarun nan yarinyar na maqale a ranta,da burin samota take kwana take kuma tashi,ya zuwa yanzun ta tabbatar ta sake girma ta zama budurwa,fatanta kullum Allah ya hada fuskokinsu da alkhairi,saita buda murfin motar tana cewa

"Na dade bansha madarar shanu ba irin tamu anty,don Allah minti biyar naje naji ko zasu tatsar min,wlh sha'awarta nake"

"Saikin dawo,saiki tfi da kudi,don kinsansu dason kwabo da sisi,bare suga daga mota kika fita yanzu zasu tsawwala miki kudi,Allah yasa su saida miki ma" ni huguma nace lol,fillo bayinmu,badai son kudi baðŸ˜Ã°Å¸˜Å“ðŸ˜Å“,murmushi bilkisu tayi tana ficewa daga motar tana tsokanar antyn

"Anya anty ba kishiya fillo xa'a miki ba kuwa?"

"Haba shi yama fara" ta amsa mata tana gyara zaman qaramin yaronta dake saman cinyarta.



      A hankali take dan bin bayan shanun da suka rage,ba jimawa ta soma hango wata 'yar qaramar rugga,da alamu anan suka yada zango,daga nesa tana hango yadda suke hada hada da shanun ana daure na daurewa,'ya'yan kuma da ba'a dauresu kowa yana daura da uwarshi.



         Daga nesa ta hango budurwar bafulatanar tsaye riqe da qugunta,duk da ta juya mata baya bata iya hango fuskarta amma shanun take kallo da alama,saita qarasa bayanta a hankali ta tsaya sannan tayi sallama.



      Waiwayowa tayi tana amsa sallamar da harshenta daya karye da fulatanci,bilkisu ta sakar mata murmushi tana ganin kamar ta taba ganin fuskar a wani wajen

"Sannu"

"Yauwa sannu" ta amsa mata da alamun kallo rashin sani

"Madara nakeso don Allah ko zan samu?,muna hanya ne zamu wuce" kanta tadan sosa kadan sannan tace

"Kash,gashi kuwa yanzu muka dawo daga kiwo....ba lallai a samu ta arziqi jikinsu,saidai akwai wadda adda ta tatsa dazu,idan kinaso saina kawo miki,ita ta sake tatsar wata"

"Eh inaso hakan"

"Shikenan....zo muje" ta fada tana nufar wata bukka bilkisu ta bita a baya.



       Daga bakin bukkar bilkisu ta tsaya jiranta ita kuma ta dan yaye labulen zanin ta shiga,saidai daga inda bilkisun ke tsahe tana jiyo banbamin fada daga cikin bukkar,wani da fulatanci,fiye da rabinsa kuma da hausa,data saurara saita fahimci ana maganar yin aure ne da wata bataso.



      Muryar da taji ta soma magana cikin kuka kuka hakanan taja hankalinta,ba al'adarta bace,amma saita matsa gaba kadan ko zata iya hango cikin bukkar saboda labulen daya dage ya maqale a jikin karan da aka gina bukkar dashi.

7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 66


*_NAFISAKABDULLAHI_*


*_Mai karatu nasan zaka ce meye wannan?_*


*_shin kai/ke ma'abociyar hawa duniyar yanar gizo ce?,kina daga cikin masu shawagi a manhajar youtube?_*


*_to maza matso,GA SABUWAR CHANNEL 'YAR YAYI DAKE DA ZAMA A MANHAJAR YOUTUBE MALLAKIN MAWAQIYA NAFISA K ABDULLAHI_*


*_CHANNEL DIN DATA HADA dukkan wani sinqi sinqin abubuwan sanya ruhi nishadi,kama da_*


*waqoqi*

*fina finai*

 *da bidiyoyi masu qayatarwa*



*_GARZAYA maza ka shiga wannan link din https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg dannan maballin SUBSCRIBE don samun sabbin shirye shirye idan an dora,sannan ka danna LIKE kayi kuma SHARING_*


*_NAFISAKABDULLAHI YOUTUBE CHANNEL 'YAR YAYI_* 🥰🥰🥰


_ZAKU IYA MAGANA DASU KAI TSAYE A SHAFINSU NA FACEBOOK_

https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi



_KO KU TUNTUBESU TA WANNAN NUMBER WAYAR_

08071172003


*karku manta SUBSCRIBE,LIKE SHARE AND COMMENT*

*SAI KUNZO*🚶ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸



*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




       Kyakkyawar budurwa ce zaune gefan gadon kara sanye da kayan saqi,kyakkyawar fuskar hauwa'unta data sha yabawa tana qissima girmanta,ba shakka hauwa'u ce,saboda babu wani sauyi da zai saka ta kasa gane fuskar daya daga cikin 'yan uwanta,musamman hauwa'un da kullum take kwana ta kuma tashi da begen son ganinta.



       Batasan ta kirayi sunanta ba sai da taga mutanen dake cikin bukkar dukka sun waiwayo suna kallonta,har ita hauwa'un da kanta ke kallon qasa a dazun,miqewa taga tayi daga bakin gadon karan tana fiddo idanu

"Yaaya maigado!" Ta fada da sauri kana cikin wani mugun gudu tayo inda take,ba bata lokaci ta fada jikin bilkisun suka rungume juna,lokaci daya kuma suka fashe da kuka,wanda ya janyo hankalin na kusa dana nesa,suka tattaru a wajen suka tsaya carko carko suna kallon sarautar ubangiji.



       Daidai lokacin da anty zuhriyya da kanta ke ratso wajen saboda dadewar da taga bilkisun ta danyi,gashi suna son wucewa,sai tsoro kuma ya kamata na yadda ta barta ta shigo wajen ita kadai,gashi bilkisun tabar wayarta a mota,don haka ta shigo da kanta dubata.



      Itama tsaiwa tayi tabi sahun 'yan kallo don batasan meya faru ba,ganin sunata yaren fulatanci a tsakaninsu an rasa me musu magana sai ta matso

"Ke daughter meye hakan?,daga cewa zaki sayi madara saikizo ki samu waje ki tsaya?" Kanta ta dago fuskarta ta jiqe da hawaye,tana riqe da hannun hauwa'u daketa kallon bilkisun kamar zata bace mata tace

"Anty hauwa'una ce,kuluwa ta" hakan data fadi yasa ta fahimci komai,sai a sannan hauwa'un ta waiwaya dubi dattijuwar da suka fito daga bukkar tare tayi mata magana mara tsaho da yaran fullanci,taji dai ta fadi sunanta dana babansu malam bilya,sai tsohuwar ta dubesu tana murmushi

"Ma sha Allahu,ai sai kuyi bayani,don sam bamu ganeku ba,ke É“ingel,bamu abun zama" ta gayawa budurwar da suka fara haduwa da bilkisu,saita juya da sauri ta shige bukkar.



  *_BAYAN WASU MINTUNA_*




      Hauwa'un na zauna gefan bilkisu kamar zata haye cinyarta,labari take bata na yadda tayi kewarsu,da yadda tasha wahala kafin ta sake a nan din,duk da ta samu kulawa sosai anan fiye da nasu gidan,hakanan a hannun kakar tasu wadda ta gansu tare take,wadda ita ke riqesu ita da qanwarta da mamar tasu ta haifa a gidan data sake aure,ta auri bafulatani jinsinta,yanzu haka suna tare dashi da yaransu biyar harda wannan da ake kira da bingel.


.



      "Nayi kewarku yaaya kamar me musamman ke ke dana saka rai da dawowarki,kullum ina cikin lissafin kwanakin da suka rage kidawo,ki cikamin alqawarin karatu da kikayi mana,katsam sukazo suka tafi dani bayan sunyi baram baram da baba,yanzu haka yaya maganar aurena ake da shehu,ni kuma bana sonshi yaya karatu nakeso har yanzu" ta qarasa maganar kuka na qwace mata.



      Zancan auren ya taba bilkisu da anty zuhriyyan kanta,kai bilkisun ta kada

"A'ah bazai yiwu ba,ki daina kuka kulu na,babu me miki aure yanzu sai idan kece kika ce kinaso,aurenma na dole....ki kwantar da hankalinki,kinga mun taho da yara,amma gobe zan dawo,zanga dukkan wanda ya kamata na gani,zaki koma can gida cikin 'yan uwanki,kuma in sha Allahu zaki karatu yadda kikeso" murmushi ya kubcewa hauwan duk da hawayen dake saman fuskarta

"Zaki iya daukar nauyina yaaya?,duk da naga kin zama 'yar gayu sosai,kin canza daga yaya maigadonki kin zama kamar wata baturiya?" Murmushi tayi tana tuna yawan albashin da a yanzu take dauka

"Karki damu,harda bingel ma idan kinaso zan hada da ita" idanu ta fiddo 

"Allah yaaya?"

"Da gaske nake miki kulu" shuru ta danyi sannan tace

"Amma ina tunanin koni dinma su yelwa barasu yarda ki sake daukata ki maidani gida ba sabida abinda ya faru tsakaninsu da baba,da irin riqon da suka samu labari yayimin,bare su hada miki harda bingel,kuma na sani burinmu nida bingel daya itama karatu takeso kamarni" 

"Karki damu,daren yau kita addu'a,zasu fahimta in sha Allah" tayi maganar tana miqewa tare da amsarwa anty zuhriyya yaron hannunta,ta leqa su yelwa sukayi sallama ta shaida musu zata dawo gobe tanason magana dasu.



      Har can bakin titin hauwa da bingel sukayi musu rakiya,tana riqe da hannun amatu da abdul kamar ta hadiyesu,tana jin qaunar yaran har ranta kamar yadda mamarsu ke sonta itama,tanata santin kyansu kamar kada su rabu.



      Ko cikin mota hirar hauwa'u suka dinga yi ita da anty zuhriyya,ranar gaba daya da abinda ta kwana cikin ranta,washegari ta dauki najwa da amatu suka rakata rugarsu hauwa'u,daidai sanda tasan suna dawowa daga kiwo.



      Ba qaramar gwagwarmaya tasha ba kafin su amince zata dauki hauwa'u,su kuma fasa aurar da ita ga wanda sukayi niyya da farko,don harta fidda rai ta haqura kafin su amince,amma bisa sharuddan zasu dinga zuwa ganinta duk sanda sukaga dama,hakanan itama zata dinga ziyartarsu duk sanda buqatar hakan ta taso,amma sam sunqi su bata bingel,babu musu ta amince,don tasan a yanzu dai babu wata sauran matsala,don baban nasu ba nada bane,ya sauya qwarai,kuma a yanzu bashi da abokiyar shawarar data wuce ita,ta saka a ranta zatasan yadda zata ja ra'ayinsu anan gaba su bata bingel dinma,tunda suka bata hauwa'un a yanzu.



     Anan suka tsara zasu wuce kano nan da kwanaki ukun da suka rage musu a ringim,randa zasu tafin zasu biyo su dauketa saisu wuce,akan haka suka rabu.



 Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



    Bata taba zato ko tunanin duniya zata mata qunci da baqi ba irin na wannan lokacin,bata taba tunani ko tsammanin akwai ranar da zatazo fara'ar mai martaba tayi mata wuyar gani ba,bata taba wassafawa a ranta irin wannan lokaci zaizo ba,dukkan wani abu bai mata taste a baki,kamar yadda babu wani abu dake burgeta sam a yanzun,idan ka qare mata kallo zakaga rama ta fara bayyana akan fuskarta.



     Tun daga randa suka kebe da azeez dukkan wani walwala da sakin fuska qauna da kulawa dake tsakaninsu yayi qaura,abu mafi daga hankalima yadda yayi mata shuru,har yau baice mata uffan ba,bai kuma tada maganar ba kamar ma ba'ayi komai ba,kamar ba abinda ya faru,koda taje turakarsa da sunan kwana takan zauna kamar wata baquwar amarya a gareshi,tsakaninau babu wata hulda koda ta cikakkiyar magana dake hadasu,sai maganar data zama dole.



      Ayanzun takai maqura,shirunsa kullum sake kasheta yake alhalin tana raye,tafison yayi fada,tafison ya dauki mataki akanta,tafison hukunci akan shirunsa amma yaqi tankawa ko yace komai.



       *_AZEEZ_*



     Daga nashi bangaren shima kusan hakan take,yanata kasa kunne da zuba idanu mai martaba yace wani abu,yanata saka kunne yaji kira daga gareshi,saidai har yau shuru maqatau malam yaci shirwa,babu alamun ma zaiyi wani zama dashi ko ya nemeshi.



      Hakan yayi masifar daga masa hankali gami da qara masa damuwa mai yawa,saboda dukkan wani burinsa ya azashi ga mai martaba,ya danganta samun mafitarsa daga wajensa,saidai da alama tunaninsa ya saba,failure tana shirin samunsa,shi kuma sam baishiryawa hakan ba.



     Kewar yaransa tana masifar damunsa,yana da buqatar sanyata cikin idanunsa koda zaginsa zatayi,ya tabbatar zai samu wani relief ko yaya yake,to amma bayason yaje mata alhalin baisan wanne hukunci mai martaba ya yanke ba,bayason ya aikata abinda yaci karo da shiri ko tsarinsa,duk da dukkan wani fatansa na samun matsera daga gareshi yanzu ya fara kwaranyewa,daga baya yaji dukkan haquri da juriyarsa ta qare,ya shirya kawai yayi nufin zuwa jigawa ya gansu.



      Sanda ya shirya ya nemi ganin fulani bai samu ganinta ba,rabonsa da ganin nata tun randa ya bayyanawa mai martaba komai,haka ya wuce jigawa bayan ya barwa afnan sallahu,wadda binsu kawai take da idanu,tana jiran taga yadda lamarin zai qarke,amma koma meye batajin wannan zata zuba idanu rayuwar qawarta ta tasake tashi a tutar babu,tana jin har cikin ranta zata shiga wannan lamarin a wannan karon koda ammin zatayi fushi da ita itama.



       .



      Yammacine lis ya isa garin na jigawa tarin Allah,garin yayi luf luf saboda haramar shigowa da damina keyi,wanda ake saka ran wannan karon za'ayi azumin ramadan ne a cikinta.



       Dai dai lokacin bilkisu na xaune a falon hajiya suna hirarsu abinsu,ana ya gobe zasu wuce kaisa,hajiyan na bata labarin yadda mata sukayi xaman aure azamanin daa da yadda suka bi mazansu,da kuma yadda suma mazan suka riqe iyalinsu da kyau kuma suka kyautata musu,bilkisu nata mamakin abun,daga qofar part din hajiyan su amatu ke wasansu abinsu saman kekuna.



      Sallamar daya daga cikin ma'aikatan gidan qofar sassan hajiyan yaja hankalinsu

"Isa shigo mana" hajiya tace tana sake miqe qafofinta dake mata ciwo,ba musu ya shigo,ya duqa cikin girmamawa

"Hajiya maman 'yan biyu ce tayi baqo" ya fada fuskarsa cike da fara'a,sai itama hajiyan ta washe baki

"Malam isa,ya naga kanata washe bakine,ko ta samu ne?" Da yake hajiyan akwai barkwanci,babu ruwanta sam bata da matsala,saiya sanya dariya

"Ai hajiya baqonne baqon alkhairi ne" murmushi tayi tana cewa

"Alhamdulillahi....aimu haka mukeso,to yayi kyau,ka bude mishi dakin baqi maza,zan aiko yarinye ta kawo masa ruwa"

"To hajiya" ya fada yana juyawa da hanzari

"Hajiya bansan waye ba,bansan akwai wanda na sani daya san gidan nan ba"  cikin nuna halin ko in kula da batunta tace

"Baqo ai duk inda yake rahamane,tunda ba maciyin naman mutane bane ai ba abun gudu bane,don baki sanshi ba yanzu tun kafin ki fita sai kice masa ba zakije ba ko ya koma ko kuwa yaya mai gado?,haba bilki aiba halin dattako bane" sai tayi shuru ta sadda kanta qasa,Allah ya sani hakanan takeji fargaba gamida mamakin wanne baqo zatayi a garin da take a matsayin baquwa,ba fita take ba,ba wani gu take zuwa ba,idanma wanine ya ganta ya biyota a ina?,kuma yaushe?,yana daya daga cikin abubuwan da yasa batason zuwa nigeria,ta tabbatar da cewa zata takura ne da zaryar manema,hakan kuma zai zama kamar tunzurine ga magabatanta,zasu sake damuwa ne da sanyata a gaba kan maganar aure,wanda ita kuma sam bata shiryawa hakan ba.



       Tanaji hajiyan ta saka yarinye mai aikinta ta hada ruwa da lemuka harda dambun kaza ta fita kaiwa,daidai sannan hajiyan ta sake cewa

"Tashi ki daure ki leqa" bata musa ba ta miqe jiki a salube,ta shiga daki ta dauki wani mayafinta me kauri ta yafa sannan ta fito.



      Tana fitowa yarinye na qoqarin komawa sassan hajiyan,data kalleta itama fuskarta a washe fiye da dazu,batace da ita komai ba ta wuce itama yarinyen saita wuce da saurinta kuwa.



        Zata giftasu amatu taji kukan amatun,saita tsaya ta qarasa wajen tana tambayarta meya faru,ashe bigewa tayi da keken ta kurje hannunta,ta kama hannun ta duba,sai taga kujewar ba wani mai yawa bane rakine irin na amatu,wanke mata wajen tayi da ruwa tace taje wajen hajiya akwai robb ta shafa mata tabarsu a nan ta wuce.



        Shaqar farko data yiwa iskar dake kai kawo bakin qofar falon taji gabanta ya yanke ya fadi,qamshi wani turare daya zama sananne a wajenta ke tashi,saidai kuma tako ta ina zuciyarta na gaya mata babu ta yadda wanda ta sani asalin mamallakin turaren ya iya riskarta a nan,don haka saita dake zuciyarta ta shiga cikin.



      Idanunta basa iya ganin kowa a dakin,saidai kuma hancinta na jiye mata qamshin sosai fiye da daxu,kamar ma mai turaren na gab da ita.



      Data gama dube dubenta bata ga kowa ba saita juya da niyyar ficewa ta koma inda ta fito,karab sukayi gware,taja baya da sauri numfashinta na niyyar qwace mata,sai data daidaitashi sannan takai dubanta gareshi.



       Yana tsaye bayanta dab da ita harde da hannayensa ya zuba mata idanu yana qare mata kallo,ranta ya baci ganin yadda yake binta da kallo kamar ya samu majigi,taja dogon tsakin daya sanyashi dawowa hayyacinsa,saita durfafi qofa da hanzari zata fice.



         Ina!,ta riga data makaro,don kuwa tuni yakai mata tattausar cafka,yayi kuwa nasarar danqota,ba tare da bata lokaci ba ya janyota zuwa cikin jikinsa ya lullubeta da kyakkyawan yalwataccen qirjinsa ta hanyar runguma.



       Ajiyar zuciya yaketa saukewa ajejjere kamar wanda ya farfado daga dogon suma,sam bai damu da hayaniya dukan qirji da qoqarin tureshin da taketa famanyi ba,duk sanda ya saki ajiyar zuciyar yanakanji qirjinsa ya rage nauyi,duk sanda ya tuna itace rungume a qirjinsa sai yaji kamar bashi da wani sauran matsala a rayuwarshi,saida yayi mai isarsa,har cikin ruhinshi yaji cewa ya gamsu sannan ya sassauta riqon da yayi matan yana duban tsakiyar qwayar idanunta.



     "Sai yaushe princess,har sai yaushe sannan xaki bani dama?,dama guda daya da nake buqata daga gurinki,wadda zata iya bani lokaci da zan warware miki komai" ya fada da wata iriyar lallausar murya dake cike da bege wanda ya taba sassan jiki zuwa ruhi,cikin fusata dai da qoqarin qwace kanta har yanzu tace dashi

"Baka da wannan damar,ba kuma zaka samu ba,ka sakeni nace ka sakeni!" Ta fada a tsawace,sake riqonta yayi sosai fiye da dazun,kai kace ce masa tayi riqeni,sosai ta fahimci cewa da gaske yake bazai saketa din ba,saboda haka tace

"Ba yaranka kakeson gani ba?,su kazo gani?,to sakeni na turo maka su" ta fada a fadace sosai,saiya saki wani irin lallausan murmushi dakan wuce da zuciyar 'yammata lokaci guda,ya kuma girgixa kai

"Ba yarana kadai ba,harke ina da buqata,ina da buqatar ganinki,ina da buqatar zama dake,ina da buqatar rayuwa dake,kafin sannan kuma ina buqatar tattaunawa dake,wanda tattaunawar ita zata kawo makomar rayuwar yaranmu"

"Makoma!,makoma kace?,makomar banza da wofi?,ku baku tuna ba?,bakuyi tunanin cewa ina makomarsu ba?,yaya makomarsu zata kasance,su waye zasu zama,duka sai yanzu kake wannan maganar?,ni bakuyi tunanin tawa makomar ba,saboda ba uwace ta haifeni ba,nidin ba mutum bace?,me zan koma me zaya sameni dukka baku damu ba!,ka sakeni malam" ta qarashe maganar launin fuskarta yana sauyawa,hakanan fushinta na qara fitowa qarara har cikin idanunta.



     Wani riqo yayi mata sosai yana dan girgizata

"Na yarda bilqess,na yarda da komai kika ce an miko an mikin,kuma ya cancan ci kiyi komai din matuqar zaki huce,amma ki fuskaceni da farko mana".



      So take ya fuskanceta kamar yadda yakeso ta fuskanci shi,amma ta lura babu niyya ko alamun hakan tattare dashi,kuka kuma take da buqatar yi saboda yadda takeji zuciyarta na cunkushe mata tare da tuna mata wasu abubuwa masu nauyi da suka taba wanzuwa tsakaninsu,don haka saita sulale ta tsakanin hannayensa tayi qasa kawai,kana ta fice daga tsakiyarshi ta miqe kuma tayi gaba da sauri.



        Tana fita daga dakin sukayi kacibus da yarinye

"Maman 'yan biyu,hajiya tace ya shigo su gaisa mana" bata tanka ta ba face gaba da tayi abinta,tana da tabbacin taje ta bawa hajiyan labarin cewa ga babansu amatu ne,don duk wanda ya ganshin basai ya tambayeta ba yake gane wayeshi.



      Da kallo yarinye ta bita harta bace tana tunanin kodai bata jita ba,sai kawai ita din tayi gaba zuwa falon don ta sanar masa.



      Yana tsaye idanunshi a rufe ya daga kanshi yana kallon sama,ya zuba hannayensa dukka cikin aljihunsa,da alama wani tunani yake me cin rai yaji sallamarta,saiya buda idanunsa a hankali ya zubesu akanta,ta duqa cikin girmamawa,kwarjininsa na dukanta 

"Hajiya tace ka qaraso ciki ku gaisa" a nutse ya gyada kanshi,hakanan yaji abun ya masa dadi,don haka babu musu,tanayin gaba yabi bayanta.



*_ASHA HUTUN LAHADI LAFIYA_*🚶ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Å¡¶Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸˜Å½Ã°Å¸˜Å½Ã°Å¸˜Å½

7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 67

https://youtu.be/NNr-vDOJzq8


*makaranta ce,mai wahalar samu,mai azabar tsada kuma,amma sai gata a KYAUTA!!!*


*CI KA ZAUNA LAFIYA youtube channel,ba tashar youtube kawai bace,face MAKARANTA GUDA garemu al'umma*


*makaranta ce da*


*ZATA GYARA MANA CIMARMU*

*MUSAN ME ZAMU DINGA CI*

*MUSAN ME ZAMU DINGA SHA*


*_DOMIN TSIRA DAGA CUTUTTUKA,DAMA SAMUN WARAKA DAGA GARESU IDAN AN RUGA AN SAMESU,KAMAR SU_*


_ciwon suger_

_ciwon hanta_

_ciwon qoda_

_cututtukan mafitsara_

_paralyse_

_H I V_

_Rashin gani_

_Rashin samun isashshen barci_

_ciwon cancer_

_matsalar fata kamarsu pimples quraje da sauransu_

_ciwon ciki_

_typhoid_

_malaria_

_rashin jini_

_siclier_

_asthma_

_limoniya_


*_dama dukka sauran cututtukan da suka addabi al'umma duk ta cikin ABINCINMU_*


Tare da


*DR KABIRU ABDULKARIM*

*_Likita kuma masani,wanda yayi karatu a qasar ISRA'ILA*


*_KASANCE DA TASHAR(CI KA ZAUNA LAFIYA)dake a YOUTUBE,kayi subscribing,ka kuma fara bin shirye shiryenta domin samun ƘARUWA da kuma WARAKA,BABBA DA YARO MATASA DA KUMA DATTAWA,MAZA DA MATA duk kuna da buqatarta_*


*ka dannan wannan shudin rubutun domin zuwa gareta kai tsaye*

https://youtu.be/NNr-vDOJzq8



*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



       A hankali yake takawa yana tattauna zancan cikin ranshi,baiga wasu alamu dake nuna sakkowarta ba ko kadan,yana jin zaiyi qundumbala ne kawai ya sake tunkarar mai martaba,yayi masa dukkan hukuncin da zaiyi masa matuqar zai gyaro lamarin ta dawo cikin rayuwarsa ita da yaransa.



     A bakin sassan ya samesun kuwa suna wasansu,saidai amatu na langabe zaune waje daya tun ciwon dazu,dukkaninsu sun ganeshi,kusan tare suka nufoshi kamar yadda shima ya nufesu cikin farinciki,yana jin wani dadi yana ratsashi,gaba dayansu ya rungumesu cikin jikinsa yana kissing dinsu,yayin da kowannensu ya soma cikashi da surutu yana son mishi hira.



   Ko daya baiji nauyin da suke dashi ba ya daukesu cak,daya a hannun dama daya a hannun hagu haka ya nufi sashen hajiya dasu amatu na nuna mishi ciwonta a shagwabe,ya kuwa biye mata yana sakw zuzuta ciwon,badon nuna gwaninta ko wani abuba,a'ah,har cikin ranshi yakejin ciwon shima kamar a jikinsa yake a haka suka qarasa sashen,yace bari su fito zaya kaita asibiti.


     Cikin jin dadi hajiya ta tarbeshi,shima ya gaidata cikin girmamawa,kai bakace shine wannan azeez din ba d'a ga sarkin kaisa kuma shahararren dan kasuwa na duniya ba.



      Babu yadda hajiyan batayi da bilkisu ba ta fito amma taqiya,data aika yarinye saita cema hajiyan kanta ke ciwo,shi yasan kwanan zancen,don haka bai tsawwala da yawa ba yace zai wuce yakai amatu clinic a wanke mata ciwo,kama baki hajiya tayi sannan tace

"Saboda taya bera bari wannan dan ciwon za'a kai ta ganin likita,rakine kawai irin nata,shi yasa kishinsu ya kasa daidaituwa da kishiyarta" wato mama mahaifiyar abbaa.



      Murmushi kawai yayi,ya fuskanci tsohuwar tana da yawan barkwanci da raha,hakan sai yaji yayi masa

"Zamuje mu dawo hajiya,wataqil yana mata zugi ne" hajiyan na musu tsiya haka suka fice.



     Suna fitowa harabar gidan abba da mahaifinsa dr maisara suna shigowa gidan,da qafa suka shigo da alama sun faka motarsu ne a wajen gidan,duk yadda akai kuma ba zasu jima ba zasu sake fita ne.



      Dukkansu idanunsu akan azeez,ga abbaa tuni ya fahimci komai ganinsa dauke da yaran,ga kuma kama ta zahiri nan dake bayyana kanta,yayin da dr maisara ke kallonshi cikin mamakin kamannin da yake gani zahiri game dashi da kuma yaran.



     Sun cimmashi don haka ya qarasa garesu suka gaisa kana ya koma inda yaran suke.



      Dukkansu yaran ya zuba cikin lafiyayyar motarsa,ya tada ya fice daga gidan.



       Yawo sukayi sosai dasu bayan anwakewa amatu ciwon,manyan wuraren shaqatawa dake garin,saida kowannensu ya gaji tubus sannan suka dawo gida.



       Ciki dukkansu suka shiga harda su abdul din,don tuni amatu ta soma gyangyadi saboda gajiya,saiya haye saman motarshi kawai ya zauna shuru yana kallon sararin samaniya wadda ta cika da taurari da kuma farin wata daya kai rabi saboda tuni kwanakinsa sunyi nisa,sam sai yaji baison barin qofar gidan,kamar ya dawwama anan,har zuwa sanda zatace ta yafe masa.



      Shuru anguwar,cikin layinma gaba daya shi daya ne zaune,har zuwa sanda wata mota ta shigo layin da full light dinta,amma data matso dab dashi sai aka rage hasken motar.



      Saida suka giftashi sannan ya gane su waye a ciki,bai damu ba yaci gaba da zamanshi har suka shige cikin gidan.



      "Wannan yaron waye?,kamar nasan fuskarshi" dr maisara ya tambayi abbaa sanda yake qoqarin faka motar

"Zaka iya saninsa,sanannen dan kasuwa ne,sannan kuma babansu amatu ne,tsohon mijin bilkisun zuhriyya"

"Eh qwarai,amma ina fata lafiya ko?"

"Nafi zaton bikon matarsa yake,saboda zuhriyya ta soma yimin maganar,to bamu gama ba wannan tafiyar ta taso"

"Haka ake bikon?" Dr maisara ya fada yana duban abbaa,shima abban saiya kalleshi don bai fahimci me yake nufi ba,duk da yasan mahaifin nasa baisan komai kan auren bilkisun na baya ba

"Eh...to ai banga wani support da kuke bashi ba,kada kacemin daga kai har zuhriyyan goyon bayan diyarku kuke?" Ya san mahaifin nasa sarai,yasan dattakonshi sak irin na mahaifiyarsa fatsima,babu abinda sukaqi jini irin lalacewar aure,dole ya yiwa mahaifin nasa bayani,idan ba haka ba yanzun dukkan laifin zai koma kansu.



     A nutse yaw warwarewa mahaifin nasa bakin gwargwadon abinda yasani yakuma san zai fahimta,shuru dr maisara yayi yana jinjina lamarin,kana ya sauke nannauyar ajiyar zuciya

"Tabbas ko shakka bana yi,sarki abdallah baida masaniya kan faruwar hakan,bada kuma yawunsa aka aikata komai ba,na sanshi tun kafin ya zama sarki,nasan halayensa sarai,amma wannan magana ce dake da buqatar nazari....zamuyi magana in sha Allahu,bai kamata a qyale lamarin haka ba"

"To baba,Allah ya tashemu lafiya"

"Amin" ya amsa yana yunqurin fita.



    Har ya sanya qafarsa waje sai kuma ya waiwayo

"Kar a kuma hanashi ganin yaranshi,domin su babu ruwansu dama duk abinda ya faru,kuma suna da haqqi saman wuyanshi na mahaifinsu"

"Tuni dama zuhriyya take turasu idan yazo,in sha Allah kuma za'a ci gaba da hakan" daga wannan dr maisara ya fice yana jujjuya batun cikin ranshi.



    Koda abbaa yafito sashen hajiya ya nufa,don yau duka bai samu ya shiga ya gaidata ba.



     Daidai lokacin da bilkisu anty zuhriyya da hajiya ke zaune dukka a falon hajiyar,amatu na kwance saman cinyar bilkisun.



      .



      Magana hajiyan take cikin siyasa akan abdul'azeez din,yadda take ka kirkinsa da cikar kamalarsa,saidai sam bilkisu jin maganar take kamar ta dora hannu aka tayita zunduma ihu,kamar tacewa hajiya tayi shuru,amma hakanan ta haqura ta rufe bakinta tayi mata kawaici.



      Bayan sun gama gaisawa da abbaa ne yace

"Yaron nan yarima muka samu nida baba zaune qofar gida saman mota,baba ke fadan an hanashi ganin yara ne,daga yau yace kada a kuma hanashi ganinsu duk sadda yazo"

"Shine dai dai ai,ina ruwan yara da rigimarsu" hajiya ta cafe zancan

"Ai dama ba'a hanashi ba abbaa" anty zuhriyya ta amsa tana kallonshi

"Ni wallahi da zaku nuna halin dattako,da yazo koma meye an zauna an sulhunta,darajar mace fa dakin mijinta,darajar 'ya'ya gidan ubansu,sam agolanci baida dadi,duk yadda za'a kula da yaro kuwa".



       Tsam bilkisu ta miqe tana saba amatu a kafadarta,sabida zancan bai zauna mata ba,sam sam ba irin aurenta akewa wannan gatan na zaman sulhu ba,hasalima batajin hajiya tasan ainihin yadda auren da rabuwar ta kasance,shi yasa ta fadi hakan,tadai san sanda aka sakota da cikinsu amatu,saita wuce kawai dakinta,hajiyan ta bita da kallo harta bace sannan ta dubi anty zuhriyya

"Kada su sake ku biyewa shirmenta,shi aure rai gareshi,koda kashe juna kukayi aka dawo idan da rabo sai an koma,mutuwar aure na jawo tozartar yara da tabarbarewar al'umma matuqar ba'a kwai wani qaqqwaqwaran dalili da zai janyo hakan ba"

"Hakane" abbaa ya fada daga nan ya mata sallama ya wuce,anty zuhriyya ta miqe ta biyo bayanshi.



   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Tun randa abun ya wakana tsakanin fulani adama fulani saratu da hajja fauziyya suka kasa zaune suka kasa tsaye,kowanne yanason sanin ainihin abinda ya wakana,yana son yasan ainihin labarin,shin da gaske matarshi ce?,idan matarshi ce yaushe akayi auren?,maimartaba ne ya daura masa auren yakuma boye ku kuwa?,dukka har yanzu babu wanda yasan taqamaimen asalin maganar,gashi mai martaba gaba daya ya musu dif,kai kace babu wani zance irin hakan daya taba faruwa cikin masarautar,gaba daya ya shiga sha'aninsa da sabgoginsa,ko a fuska basuga wata alama ta komai ba tattare dashi,har gwara fulani aisha sun samu labarin ta fada yanayin damuwa,amma banda wannan itama basu samu komai ba basu kuma samu wani bayani ba sabanin hakan.



      Ta gefan kamal shima hankalinsa na a tashe ne,kalmar matata ce din da azeez ya fada na neman tarwatsa shirinsa,indai ya tabbata kenan tilas ya haqura da ita?,ya sake rasata kenan duk burin da yaci a kanta ya tarwatse?,wannan tunanin shima ya saka masa damuwa,ya kuma hanashi sakat.


 

    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Kamar yadda a cikin wadan nan lokuttan suka koma shi da ita kamar wasu baqin juna,misalin qarfe goma na safiya,tana tsaye daga gefansa yana shiryawa cikin irin suturar da yake sakawa idan zaiyi zaman fada.



      A lokuttan baya itake tayashi shiryawa,ta qware tsaf ta wannan fannin fiye da kowacce mace cikin matanshi,wani lokaci har bai ganin kyan shigarshi idan ba ita ta tayashi shiryawar ba,saidai a yanzun dare daya ya soke wannan,duk lokacin data yunqura zata tallafa mishi yakan dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu,tun tana qoqarin gwadawa harta haqura,daya daga cikin horon da yake mata kenan wanda ke matuqar ci mata rai,shekaru kusan arba'in komai laifin da zata masa bai taba yi mata abu makamancin haka ba.



       Yanzun ma tana tsaye ya gama shiryawa,da sauri ta dauki cup dinsa na tatacciyar madarar shanu data tafasa masa da citta da kununfari ta miqa masa,saidai kamar kullum yauma hannu ya daga mata kawai,kana ya soma takawa zai fice.



        Kasa jurewa tayi,yau haqurinta da dakiyarta sun qare,saita saki kofin madarar ya tarwatse a nan wanda hakan ya sanyashi juyowa,har a jikinsa yaji fashewar abun da yadda take tsallakesu,amma saiya dake ya basar,itama bata damu da wannan ba ta tsallake cikin hanzari ta isa inda yake.



      Hannayensa ta kama gam cikin nata,sai kawai ta fashe da kuka,baice mata uffan ba,kamar yadda bai dakatar da ita ba har sai datayi mai isarta

"Duk hukuncin da zakayimin ka yimin don Allah,amma banason wannan shurun,wannan halin ko inkula din don Allah" a shashance yace

"Wanne laifi kikayi kuma?,kinyi wani abune dama?" Kuka ta kuma saki tana girgiza kai

"Kada kace haka don Allah,kada kace haka".



       Duk yadda yaso ture tausayinta daga ranshi amma hakan yaci tura,bazai iya tuna sanda ya ganta tana kuka haka ba,duk da hakan ya riga ya qudirta dole ya hukuntata yadda zataji a jikinta,bai taba tunanin zata tafka ta'asa mai girma haka ba,don bashi ba ba yarima ba,yarinyar data aikatawa abun,yanason ta gamsu a karan kanta ta cutar da ita,yanason ta gamsu cewa ya kamata ta nemeta,ya kamata ta nemi afuwarta,shi kansa yariman yana da laifi cikin abun,kuma koshi din bazai qyaleshi ba,saiya hukuntashi daidai da laifinsa

"a'ah,meye na damuwa kuma?,bayan kin aikata abinda ya dace ne?,kin isa kiyi shawara da kanki fa kuma ki yanke hukunci tunda shekarunki sunkai,kuma komai ya tafi daidai,meye na damuwa kuma?".



     Shuru tayi tana sheshsheqar kuka,sai ya zame hannunsa kawai yayi gaba yana juyo sautin kukanta,duk da yadda zuciyarsa ke masa nauyi dajin kukan nata.



       Yana saka qafarshi falonshi ya tadda fulani adama zaune gefen kujera,ta caba ado sosai har abun yaso bashi mamaki.



       Tana ganin fitowarsa ta miqe cikin girmamawa tana sakin murmushi

"Allah ya baka yawan rai,Allah ya tsare mana kai,ya qara lafiya da nisan kwana,barka da fitowa takawa" ta fada cikin daga murya,don tana da masaniyar aisha na cikin dakin,murmushi ya saka cikin sarauta,yana daga tsaye don baison ya zauna ta bata mishi lokaci

"Ya akayi adama?"

"Barka da warhaka"

"Barka kadai,kun tashi lafiya?"

"Lafiya qalau ranka ya dade,zuwa nayi dama in gaisheka,jiya da yau duka bamu samu ganinka ba,gashi ka barmu cikin alhini kwana biyu"

"Lafiya alhmdlh....alhinin me fa?" Sosai ta sauya fuskarta ta maida kalar jimami,kanta a qasa ta girgizashi

"Abinda ya faru da yarimanmu,kullum cikin zullumi muke kwana,muna fata Allah yasa ba wani abu mara kyau ya aikata ba,gashi babu wanda ka yiwa cikakken bayani a cikinmu Allah ya baka nasara" kanshi ya dauke don ya jima da soma karantar adaman,musamman lokacin daya matsa bincike kan daga wannw saqo hotunan suke fitowa,sai suka lura sunfi fitowa daga nahiyar da fulani adaman take,saiya soma takawa yana yin gaba kafin ya bata amsa

"Awwnnn....ashe....na mance ma wani abu ya faru,kuyu baccinku dakyau ku daina tunani,ba wani big issue bane ba,kusa a ranku kaman ba'ayi ba"

"Amma muna buqatar qarin bayanin da zai kwantar mana da hankali,ko 'yar uwarka bakaga yadda ta damu ba" saiya juyo yana dubanta

"Kije ki musu bayanin dana miki,inaga ga ishi kowa a cikinsu"

"In sha Allahu ranka ya dade" ta fada tana sunkui da idanunta ganin yadda ya tsareta da ido,daga haka ya juya ya fita cikin jama'arsa.



       Da baya da baya fulani aisha ta koma ta zauna bayan ta gama jin duk abinda ya wakana tsakanin fulani adama da me martaba,hannunta tasa tana toshe bakinta da kuka keson qwace mata karo na biyu a ranar yau,duk da taurin rai da dakiyarta,a haka kamar yayi fushi da ita,amma kuma a fakaice ta wani bangaren yana qoqarin lulluba asirinta,tabbas ta sani tsakaninta dashi wata irin soyayya ce min indillahi tun quruciya,bata taba kuma zaton qiyayyar su adaman a kanta takai har hakan ba,tasan suna sone suji komai,su samu abunda zasu qarasa tarwatsa ta,saita dafe kanta da hannu biyu tana ambaton sunan Allah.

7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 68

https://youtu.be/-kbsWo6IjOo


*_yadda zaku sarrafa albasa ke da mai gida/kai da uwargida,domin samun ingantacciyar lafiya da gyara xamantakewar aurenku,ta kuma rabaku da shaye shayen magunguna  barkatai marasa fa'ida da amfani,da kuma illata lafiyar dan adam_*


*Tare da*


*DR KABIRU ABDULKARIM*


*_dannan shudin rubutun nan,bayan ka shiga ka saurara kuma kayi subscribe,share da kuma like_*

________________________________


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




    



      Ranar ya jima sosai a fada,wanda kafin ya tashi yasa aka shaidawa mama sodangi yana buqatar ganinta bayan zaman fada.



       Zama sukayi daga shi sai ita,ba tare da sanin kowa ba,ya samu dukkan bayanan da yake da buqata kafin ya sallameta,yayi shuru abun na sake qona mishi rai,aisha ta mishi ba zata,ta kuma bashi mamaki,badon Allah ya tsare ba shi kadai yasan yawa da girman abinda zai faru,a hakanma yana ji a jikinsa tsarewarsa ce ta kawo lamarin ya tsaya iya haka,ya miqe ya shige ciki yana sake wassafa hukunci da qarshe da zai yanke kan lamarin.



    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Bayan ya tabbatar da tahowarta qasar kaisa a ranar,saiya sauya akalar motarshi zuwa masaukinsa,ya dauki dukkan abinda zai dauka shima ya nufi qasar kaisa,ya nufeta da qarfin gwiwa da tarin karsashin zuwa ya samu mai martaba kanshi tsaye,ya gaji da wannan walagigin haka,ya gaji da yadda take wajigashi tana wasa da hankalinsa duk yadda taso,yana da buqatar ayita ta qare kawai.



          Sanda ya isa bai nemi kowa ba,hakanan bai shiga masarauta ba kai tsaye,hakanan ya samu kanshi da ra'ayin sauka a village(wani gida ne nashi da aka yiwa gini na musamman,gini irin na qauye na gargajiya saidai kuma a zamanance,dukkan abinda ke cikin gidan na gargajiya ne,hatta da dakuna na bukka ne,saidai kuma ciyawar da turakunan da akayi amfani dasu a zamanance ne,hakanan katangun duka na qasa ne bulon qasa ne,saidai lailayayye sosai wanda kana gani kasan an zamanantar dashi,hakan kitchen din dake cikin gidan,kwanukan girki na qasa,kwanukan abunci na akushi ne,gadon qarfe mai rumfa amma na zamani,kawai qoramu da aka gyara wajen,kai kace ire iren na qauye ne,akwai randuna na qasa na ruwa mafitai tabarmin kaba da sauransu,duk da awani wajen tiles akayi aka saka carfet,sannan dole ta sanya aka saka ac saboda sake qawata wajen da bada nishadin xama.



      Gidane daya dauki hankali matuqa saboda yadda aka tsarashi,afnan na bala'in son gidan tun lokacin da aka kammalashi,saidai tasan babu fuska bare tace zataje,gidane na musamman a wajen maishi shi karan kanshi,yanayin wajen na qawatar dashi,saboda yadda ya cika da tsirrai da shuke shuke da ko yaushe sukan sanya gidan ya kasance luf luf cikin sanyi da qamshin qasa mai dadi,yawan tsirran ya gayyato tsuntsaye kala kala,wadanda suka kama bishiyoyin gidan kowacce na rera salon nata kukan ko waqar,idan ka shiga gidan kaida kanka kasan na musamman ne.



        Ya jima zaune a daya daga cikin falukan gidan bayan ya rage kayan jikinsa,saiya jawo wayarsa ya soma neman layin safwa,saboda kwana biyu gaba daya baida nutsuwar kiranta,hakanan itama baiga nata kiran ba,bai sani ba tana kaisa din ko ta qara gaba yadda ta saba,a halin yanzun yana da buqarta kusa dashi koda ba zata tsinana masa komai ba,amma a qalla zai dinga jin motsin mutum.



     Sam sam sai wayar tata taqi shiga,ya gwada kusan sau uku amma ana gaya mishi layin a kashe yake,yayi mamaki qwarai,saiya gwada ta mamanta itama taqi tafiya,don haka ya sauya shawara yayi kiran afnan.



       "Barka da warhaka yaya...." Ta fada cikin nuna girmamawa

"Yauwa....ko safwa tayi magana daku zata wani wajene?" Mamaki saiya cikata,itakam tana mamakin aure irin nasu,safwa ko yaushe jinta take kamar qaramar yarinya,ta kasa gane ainihin ma'anar aure,ta kasa gane cewa ta girma,saita yita yin abu kamar yau aka haifeta,shima ta nashi fannin ya rungumi kasuwancinsa gaban komai,ibadarsa ce kawai yake sakawa gaban kasuwanci,sam kamar zaman auren nasu bai dameshi ba

"Am asking you kinma mutane shuru?" Ya fada a dan fadace,da alama ranshin a bace yake

"Bandai sani ba,amma dai ganina na qarshe da ita....tazo wajen ammi bata sami ganinta ba,tace na gaya mata zata yiwa daddynta rakiya zashi yearly cheakup dinsa" daga haka bai sake jiran jin komai daga bakinta ba ya katse kiran.



        Sai yaji ranshi ya baci sosai wannan karon,ya kamata ya dauki mataki hakanan,aure ba abun wasa bane,hakanan shiba lusarin namiji bane,bazai zauna mace ta soma haihuwa dashi ba amma har yau sakarya bace,batasan ciwon kanta batasan ma'anar zaman aure ba,atleast koda zata bai kamata ta wuce haka ziqau kaman ita ke zaman kanta ba,tunda matsalolin nan suka sanyashi gaba bai sakata a idonshi ba,amma yasan ya tsare dukkan wani haqqinta.



      Idanunsa na alumshe yana wassafa matsalolinsa guda biyu wata sassanyar busar sarewar sarauta ta ratsa falon,alamun anason magana dashi,idanunsa na a rufen ya bada umarni a shigo din,daya daga cikin amintattun bahi na musamman da ya saka aka turo mishi suke kula da gida ya bayyana,cikin shiga ta musamman,kaman yadda yake kamar sutura ga duk wanda ke aiki cikin village

"Allah ya taimakeka,ya baka yawan rai.....yallabai abdulrashid ne yake neman iso" da hannu still dai ba tare daya buda idanunsa ba ya mishi nuni daya barshi ya shigo.



      Sallamar abdulrashid ita ta sanyashi bude idanunsa,ya zuba mishi idanu kamar yadda shima ya zuba masa nasa idanun yana kallonshi harya samu waje ya zauna.



       Tashi abdul'azeez yayi sosai ya zauna har yanzun idanunsa kan abdulrashid daya lura yana masa kallon qurilla,ya buda baki zaiyi magana dariyar da abdulrashid ya sanya ita ta katseshi daga fadin abinda yayi niyya,cikin mamaki yake duban abdulrashid,daga baya daya lura akwai shaqiyanci cikin dariyar tasa,sai kawai ya sake maida idanunsa ya kulle,ya kuma koma ya kwanta kamar yadda yake a dazun,har yayi dariyarsa ya qoshi don kansa sannan ya soma magana

"Mai firgitarwa yau shi ake firgitarwa?,lallai dara taci gida,inama zanga dukka matan da kake zame musu xaki idan sun ganka,jikinsu ke tsuma saboda kwarjininka,soyayyarka ke hanasu bacci da sukuni,suke kasa kallon fuskarka,yau suzo....ga wata yarinya guda daya ta birkita maka tunani...ta hana rayuwarka sukuni,ta hanaka sakat....ban taba zaton kai rago bane yarima sai yanzu,ban tsammaci cewa kai rago bane sai akan bilkisu,kaga yadda ka birkice ka hautsine?,idan na gani da kyau ma kamar ramewa naga kayi hakane?",ya qarashe ta sigar tambaya.



       Sai daya kai aya sannan azeez ya bude dukka idanunsa akan abdulrashid,cikin tattausan muryarsan nan da lafuzzansa masu kama da ana jera masa su yace

"Ragon maza nake akanta,hakanan banda wayo ko wata fikira indai akanta ne,jarumi nake kuma zaki tsakanin maza 'yan uwana,mai furgita duk yarinyar data nemi shiga gonata ko hurumina ba tare da yarda ko amincewata ba" saiya tashi ya zauna sosai bayan yakai qarshen xancan,idanunsa da suka jajjanye duka akan abdulrashid,hannunshi daya ya dora saman qirjinsa bayan ya dunquleshi,daidai saitin zuciyarsa

"Kasan me nakeji anan abdulrashid?,kasan kullum da yadda nake bacci?,kasan yadda zuciyata ke zugi?,amma sam taqi fahimtar haka,taqi ta bani dama,taqi ta gane cewa bayaga mahaifiyata itace mace ta biyu da nake tsananin so da qauna,macen da bazan iya sake jure rashinta ba,me yasa ba zata fahimta ba?" Ya fada a hankali launin qwayar idanunsa na sauyawa.



      Nannauyar ajiyar zuciya abdulrashid ya saki,tausayin azeez din yaji yana shigarsa,lallai dukkan abinda zai saka azeez din ya zauna yaba tona asirin zuciyarsa haka ba qarami bane,tunda suke tsahon tasowarsu tare,bai taba ganin yana yiwa wani abu irin wannan son ba,jarumine na gasken gaske,lallai ya cancanci a tausaya mishi.



     Bai ankara ba yaga ya miqe

"Zanje na samu me martaba,koda zaiyi gunduwa gunduwa da namana na roqeshi ya saita lamarin,shirunsa din nan abdul nasan yana nufin abubuwa ne da dama....ina zuwa" ya fada yana shigewa ciki inda zai sadashi da 'yar qoramar da aka tanada saboda wanka wadda tayi shige da swimming pool amma a gargajiyance.



    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Yayi mamaki lokacin daya ganshi cikin hakimai a fada,ya saje cikinsu cikin ire iren shigarsu shima,saidai ya dake ya kuma nuna kamar bai ganshi din ba.



      Duk tsahon awannin da aka dauka din yana nan tare dasu bai motsa ba,har zuwa sanda aka gaman zaman,sarki ya miqe yayi ciki yana biye dashi,sauran 'yan majalisar sarki suma kowa ya wuce uzurin gabanshi.



        Daga shi sai me martaba ya rage,har zuwa lokacin yana biye dashi ba tare da yace komai ba.



       Waiwayowa yayi sanda yake niyyar shigewa turakarsa,suka hada idanu da azeez,a ranar sai yaji mahaifin nasa ya masa kwarjini matuqa kamar sauran mutane,saiya sadda kanshi qasa

"Lafiya dai ko?,inason na shiga ciki na huta" me martaba ya fada yana duban azeez din,duk da yasan da walakin goro a miya.



       Zubewa yayi nan gabanshi saman gwiwoyinsa,cikin sanyi da matuqar nadama ya soma neman alfarma a wajensa gameda lamarin bilkisun,tare da alqawarin amsar dukka hukuncin da yace ya yanke a kanshi.



       Shuru ya masa har ya kammala sannan yayi gyaran murya

"Saboda ni ka daukeni qaramin mutum ko?,bayan mutuncina da kuka gama zubdawa da saidawa a idanun al'ummata yanxun kakeso na sake zuwa na É“arar da sauran da hannuna?,ai abdul'azeez ta inda aka hau ta nan ake sauka...kaje ka samu uwarka yadda kuka qulla ku warware,kasan kana sonta amma ka bari akayi wannan barnar da kai?"

"Afuwarka da yafiyarka nake nema,ba don ni ba,kodon albarkacin 'yan biyun dake tsakaninmu"

"Yan biyu!" Mai martaba ya furta ba tare daya shirya ba,ya kuma sake fadin

"Kana nufin akwai zuriyya tsakaninku?" Kai ya gyada yana sake tabbatar masa,shuru me martaba yayi bayan ya lalubi kujera ya zauna,kyawawan mintuna biyar bai iya cewa komai ba,daga bisani ya miqe bai cewa azeez komai ba ya wuce ciki ya barshi a nan.



        Daren ranar gaba daya sarki abdallah ya qarar dashi ne wajen nazari da kuma neman mafita wadd zata zama adalci sulhu kuma alkhairi a gareshi da ahalinsa.



       Jikinsa ya bashi tabbas wannan lamarin jarrabawarshi daga ubangijinsa,ya jarrabeshi kan macen da tafiso cikin matansa,da yaron da yafiso cikin yaransa,duk da tarin qoqarin adalci da biyewar da yake,hakan ya sanya daga shi sai ubangijinsa ne kawai sukasan da wannan sirrin.



       Kwanaki biyu ya dauka qwarara dukkan bincikensa ya kammala a asirce,duk abibda azeez din ya fadi babu qarya a cikinsa,hakan ya kawo masa sassauci kan hukunci da matakin da yayi niyyar dauka a kansa.




       A kwana na ukun bai samu sassauci ba sai daya ganshi kan hanyar gidan malam bilyaminu da kanshi ba aike ba,cikin mota qwaya daya mai baqaqen gilashi,dagashi sai amintattunsa mutum uku,cikin salo na bad da kama,don baka isa kace sarkin kaisa bane a motar.



*GIDAN MALAM BILYAMIN*



      Tub dawowarsu kaisa din ya zamana kusan kullum yaran na wajen malam bilya,da hauwa'u wadda har kukan dadi mlm bilyamin din yayi da dawowarta cikin 'yan uwanta,domin yayi cigiyar yayi neman har ya gaji ya haqura,albarka babu irin wadda bai shiwa bilkisu ba,don a yanxun kusan yaranshi har mazan kusan suna gabanshi,su mazan biyu daga cikinsu suke kula mishi da shagunansa,tunda a yanzun shi babu damar fita kamar daa,jikin yaqi dadi,ciwo yaqi barinsa,yau da lafiya gobe babu.



       Sau tari yakan zauna ya zubda hawayensa idan yaga yadda Allah yayi dashi,wato duk abinda kaga Allah ya hanaka mai yiwuwa akwai hikimarsa cikin hakan,me yiwuwa ya baka wani abun madadinsa wanda kai bakasan da hakan ba.



         A da yana kukan talauci da babu,yana ganin Allah ya hanashi dukiya,ashe ya masa musayarta ne da cikakkiyar lafiya,daga baya ya amshe lafiyar ya barshi da kudin,wanda kudin gashinan sun gaza siya masa lafiyar,ga kudin da zaici duk abinda yakeso,zai saka duk suturar da yakeso amma rashin cikakkiyar kafiya duka ya hana wannan,saidai ya kalla iyalansa da kuma wasu a waje suci,ashe babu arziqin da yakai na lafiya.



       Cikin wannan jimamin da alhinin ya kama mama ladida sabuwar amaryarsa sun hada kai suna kitsa yadda zasu masa gagarumar sata,saboda a cewarsu idan ya mutu ba zasu tsira da komai ba bayaga tuminin takaba,umma katti da 'ya'yansa su zasu wawashe komai.



      Wannan ma ya tashi hankalinsa qwarai,ya dinga kuka bayan ya sallami kowaccensu da saki bibbiyu,saiya dinga tuno rayuwarsa da maimunatu mahaifiyar bikisu,ta fishi kyau,ta fishi nasaba ta fishi dukiya,amma ta yarda,ta zabi ta rayu dashi badon yana da komai koya mallaki komai ba,ta ajjiye dukkan wasu qualities nata,ta haqura da rayuwar gidanshi,harta mutu bai ajewa ba bai bawa wani ajiya ba barema ta saka rai,sai gashi yanzu wadanda ya tsincesu sama taka suna neman kassarashi ta sandin dukiyar da aka samu ta hanyar diyar maimunatu,dukiyar da ita maimunatun bata dandana ba.



       Ashe duk tsiya duk masifa matar babu ba qashin yardawa bace,sabida tunda suke da umma katti bata taba yunqurin gwada hakan a gareshi ba,itadai barta da masifarta da bala'inta,son yaranta ta hana na wani,da nuna mishi yatsa,amma babu wannan mugun qullin a ranta,ranar yayi kusa sosai ya kuma yi nadama,tare da godewa Allah da yaketa haska masa gaskiya tunda sauran lokacinsa.



       To a yau din ma kamar sauran ranakun,da kanshi yayi kiran bilkisun yace ta kawo mishi 'yan biyu,ta shirya da kanta,yaran kuwa suma sunata murna,don ba qaramin son zuwa gidan suke ba,saboda yadda kowa ke nan nan dasu,ta shiryasu sosai,tayi musu adon shadda ash,wadda abba ne ya dinka musu su biyu kawai.



      Itakam babu abinda zata cewa Allah sai godiya,kowa son yaran yake,nuna musu qauna da kulawa yake.



       Da kanta ta kawosu,ta zauna suka sha hira da malam bilya din,sannan ta shiga ciki wajen 'yan uwanta suka sha hirarsu suma bayan ta gaida umma katti.



      Hirarsu suke gwanin sha'awa,duk sanda ta daga kai ta kalli yan uwannata taga yadda rayuwa ta musu kyau hakan na sake faranta mata,a yanzun haka zancan auren auren hannatu ma akeyi.



      Awa biyu kawai tayi tatafi tabarosu acan,tasan akwai masu kawosu gida,idanma sun kwana duka ba damuwa,don tasan mawuyacine su qyalesu su dawo a yau din.



       Bata rufa awa guda da tafiya ba motar maimartaba ta iso layin,a daidai qofar gidan suka faka,yasamu tabbaci yana nan,saboda a yadda aka bincika masa ba kasafai yakan fita din ba kamar yadda muka sani.

7/11/21, 4:35 PM - My Mtn Number: 69

https://youtu.be/NNr-vDOJzq8


https://youtu.be/NNr-vDOJzq8



*CI KA ZAUNA LAFIYA*

*_youtube channel_*


*TARE DA*


*DR KABIRU ABDULKARIM*


_Tashar youtube irinta ta farko,wadda ke dauke da tarin ilimi irin wanda al'ummarmu take da buqata_


_Tashar da zata koyar daku dimbin darussa,ta yadda zaku samarwa jikinku garkuwa ta cikin abincin da Allah ya yassare mana_


_zata koyar daku yadda zaku kare kanku daga kamuwa daga cututtukan da suka addabemu,ta hanyar ganyayyakin tsirrai da tsaba_


_hakanan akwai tarin sirrikan gyaran fata,gyaran gashi da gyaran jiki gaba daya,ta hanyar amfani da sarrafa abincinmu_


_tashar CI KA ZAUNA LAFIYA ke/kai/su/ita/mu kowa nada buqatarta,walau lafiya kake ko akasin haka_


*_garzaya maza kayi SUBSCRIBE sananna ka danna LIKE kayi SHARE ga iyaye,yan uwa da abokan arziqi don kada ayi babu su_*

_________________________

___

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




        Su biyu ne rak cikin falon,daga shi sai maimartaba,wanda ko a mafarki malam bilya bai tsammaci zuwanshi har cikin gidanshi ba.



     A hankali maimartaba ya sauke ajiyar zuciya kana ya miqawa malam bilya hannu,hannun ya kalla kana ya kalli maimartaba,ya sakar masa murmushi gamida bashi qwarin gwiwa,hakan ya sanya malam bilyan miqa masa hannu sukayi musabaha yana tambayarsa iyali.



      Shuru na sakanni ya biyo baya,sannan mai martaba ya soma magana cikin nutsuwa

"Da farko malam bilyaminu....banason ka kalleni da idanun sarki,inason ka kalleni da idanun uba ga mijin 'yarka,sa'annan kuma suruki a wajenka,inaso muyi magana takai tsaye,kowa ya fadi abinda ke zuciyarsa,banason kaji nauyina ko kayimin alfarma" saiya dan tsagaita yana duban malam bilyan sannan ya dora.



        "Dani dakai dukkan munsan abinda ya wakana tsakanin yaranmu shekara bakwai baya basai anyi bita ba,saidai nidin shekaru bakwai da suka shude,sun shude ne ba tare da nasan wannan lamarin ba,wanda kuma bansan da wanzuwar tashi ba sai cikin shekarar nan,a shekararnan dinma cikin satin nan,da fari ina mai baka haquri a madadina matata da dana akan wasa da akayi da rayuwar diyarka,tabbas anyi maku abu mafi muni,zalunci cikakke wanda dukkan dan adam din da aka yiwa an cutatawa rayuwarsa,nayi matuqar girgiza dajin labarin da yadda aka wofantar da jinina da yake tattare da diyarka,wanda a yanzun Allah ya rayasu....inajin nauyin magana ta gaba da zan furta,amma kuma dana zauna nayi dogon nazari akai sai naga shine mafita a rayuwar Æ´aÆ´anmugaba daya nida kai da kuma jikokinmu"saiya tsagaita yana sauke numfashi sannan ya dora

"Cikin labarin daya bani ya tabbatar min yarinyar na a matsayin matarsa ne har yau,da farko ban yarda ba na kuma qaryata,saboda ba lamari bane da hankali zaiyi saurin dauka ko ayi amfani dashi ba,amma daga bisani daya gayamin shaidun daya maida matar tasa a gabansu,saina tabbatar da ingancinsu da kuma adalcinsu,amma duk da hakanan ban tsaya a nan ba,sai dana kira kowannensu na tabbatar da cewa haka maganar yake,wanda daya daga cikinsu tana kamar a matsayin uwa a wajensa ne....alfarmar da nake nema a nan ayimin itace,bilkisu ta koma dakinta a matsayin matar abdul'azeez,bayan na tabbatar da nagartar halayenta daga bakin wadda ta zauna da ita,hakan ya alamta min tana daga cikin sahun mata na gari daya kamata a riqe da kyau,rabuwa da ita tamkar tafka wata hasara ce mai girma,hakanan ko babu wannan an cutatar da rayuwarta,babban adalcin da zanyi a yanzu a damar da Allah ya bani shine ta sake komawa a matsayin matarshi,wanda duniya duka zata shaida,shaidawar da a baya bata shaida din ba".



       Ba qaramin burgeshi sarki abdallah yayi ba,bai taba zato ko tsammatar haka ba,labarin adalcinsa da sauqin kansa ashe ragewa ake?,inama ace dukka shugabanninmu zasu kasance kamar haka?,inama a ce na sama zai kasance mai tausayi da adalciwa na qasa kamar haka?,tabbas da duniya ta zauna lafiya,da mun rabu da tarin matsaloli da suke addabarmu a yau,ba shakka ya koyi tarin darasi a yau daga sarki abdallahn,wanda yake zaune tare dashi babu wani shamaki,da ace wani zaya shigo baha ga suttutar jikinsa kuma baisan fuskarshi ba.....babu abinda zai hana yace ba sarki bane wannan.



      Ajiyar zuciya shima malam bilya ya saki,yana jin kunyar kanshi da kanshi,kowanne uba na gari yakan kauda son zuciyarsa ashe ya zabawa zuri'ar da Allah ya nashi nagartaccen abu da yasan shi dasu zasu kubuta har a gaban Allah,tabbas wannan babban darasine daya sake samu a yau

"Dukkan abinda ka fada na jisu na kuma fahimta,saidai komai bai gudana ba saida gudunmawata da goyon baya na,bawai sunsa qarfi bane sun dauki 'yar,saidai kwadayina da son tara abun duniyata da dukka shi ya janyo hakan,ba shakka nayi nadama,nayi nadama mara iyaka kuma ina kan yinta,ta yadda na dauki yarinya mafi biyayya cikin iyalina na sadaukar da rayuwarta da mutuncinta,yarinyar data fito daga mace mafi soyuwa,nagartacciyar mace daya tamkar da dubu,matar da har yau ban maida kamarta ba,amma kwadayin samun dukiya duka ya rufemin idanu yasa na manta wannan"

"Idan akwai abinda ya kamata ace raina ya baci guda daya ne,ina namen afuwa,naji baqinciki naci kuma alwashin cewa.....daga ranar da aka kore cikin dake jikin maigado,bakai ba....koma waye zayaxo da sunan sunaso daga baya,koma waye yazo da sunan zuri'arsa ne bai isa ya amshesu ba,ciki kuwa harda hukuma.....kai din mutum ne mai girma kuma adali,wanda na tabbatar dama can baka da masaniyar wannan kitimurmurar,zuwanka wannan waje a irin wannan yanayin ya sake tabbatar da kai din waye,na yafe iya haqqina,amma akwai abu daya..." Saiya dakata shima yana gyara zamanshi.



        "Daga wancan lokacin dana gane kurena,na gane gangancin da karan tsayen da na yiwa rayuwarta,saina dauki alqawari akaran kaina,sa'annan na dauki alqawari tsakanina da ubangiji na cewa....bazan sake yanke hukunci irin wannan cikin rayuwarta ba har na koma ga Allah ba tare da amincewa ko lamuncewarta ba,bazan sake yanke hukunci irin wannan kan rayuwar duka yarana ba,koda yara maza bare matan....saboda haka,a yanzu bani data cewa,sai abinda ta zaba a karan kanta" murmushi mai martaba yayi yana jinjina kai

"Ai koda ka amince surukina bazan taba yarda a zartas da komai ba saita amince da kanta,saboda dukkaninmu nida kai ba haqqinmu bane ba nata ne,sannan koda ta yardan bazan taba nemawa abdul'azees ko mahaifiyarsa sassauci ko dukka hukuncin da taso yanke musu ba,matuqar dai ta amshi alfarmata shikenan,sauran hukunci duka nata ne,yanzu wannan magana ta rage tsakanina da 'yata ne,naka ido kawai"murmushi malam bilya shima ya saki,yana jin dadin yadda ya maida bilkisu 'yarsa sosai kamar azeez din,yana niyyar cewa wani abu amatur rahman da abdulrahman suka shigo da gudu abdul din yana biye da ita,da alama wani abu ne ya hadasu.



      Tunda suka shigo gaba daya suka tafi da hankalin me martaban,numfashinsa ya tsaya cak na wucin gadi,ya zuba musu idanu babu ko qiftawa yana kallon hukuncin ubangiji,sak abdul'azeez dinsa.



       Kabbara yake a zuciyarsa yana sake kadaita Allah,iya yaran kawai sun isa su zama ishara garesu,sun isa su bayyanawa kowa cewa wani babban lamarine can dama da Allah ya boye a tarayyar bilkisu da abdul'azeez din.



      Yana zaune ya kasa magana har malam bilya ya raba gaddamar,sannan ya kalli me martaba fuskarsa qunshe da murmushi

"Wadan nan yaran kadai sun zama wani farinciki da garkuwa na zuciyata,su kadai idan na kalla nakan tabbatarwa kaina lallai alqawari Allah na haihuwarsu ne ya tabbata....amatu kuje ga kakanku can ku gaidashi" ya fada yana dagasu daga jikinsa.



      Idanu suka tsura masa,sannan suka juya suka kalli junansu suka kuma kalli malam bilya,sannan suka maida dubansu again ga maimartaba da yaketa jifansu da murmushi,ya qagu yaji dumin jikokinsa,kamar ya janyosu zuwa jikinsa saboda tsabar zaquwa.



      "Ku qaraso mana taurarin masarautar kaisa" ya samu kanshida furtawa tsabar tsananin farincikin da yakeji cikin zuciyarsa,sashe daya na zuciyarsa kuma yana jin takaici da kuma kaico na ba cikin masarautar aka haife musu suba,saidai duk da haka yana miqa godiya ga ubangiji me dumbin yawa daya sanya suka fito daga tsaftataccen tsatso,hanya ta gari,sunnar ma'aiki S A W ba haihuwar titi ba

"Ammi zata mana fada,rannan ta kusa zane abdul,sabida yayi irin abun kanka a kansa" duka shuru sukayi,suba yara bane,sun fahinci me yarinyar keson fada,sai maimartaba ya saki murmushi yana shafa nadin dake kanshin

"Idan na cire zakuzo?,kuma ba zatayi fadan ba?" Dukkansu suka gyada kansu,saiya sanya hannunshi biyu yana nufin cirewar.



      Da sauri malam bilya ya dakatar dashi

"Karka biye musu ranka ya dade.....ke amatu,abdul....ku qarasa maza ku gaidashi,ni nace muku ai,don haka ba zatayi fada ba"



      Dukkansu luf sukayi q irjinsa tamkar sun jima da saninsa,ba shakka jini ba wasa bae,sai yaji idanunsa suna son cikowa da qwalla,yau ga yaran abdul'azeez dinsa a jikinsa,jinin azeez dinsa,lallai Allah da girma yake.



    Ya dan jima da yaran har sai da yaga sun saki jikinsu dashi,sannan ya musu kyauta mai yawa,ya kuma wuce gida da alqawarin zuwa yaga bilkisu da kanshi.



     Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



    Dukkan abinda me martaba keyi babu wanda ya sani,hakanan ya nemi anty zuhriyya da abbaa da kanshi ya gana dasu.



      Nauyinsa girma da kuma shekarunsa suka hana anty zuhriyya tuburewa,mutum ne shi mai fahimta da saurin gano mutum,ya fuskanci a bacin rai take,hakanan taci alwashi sosai kan abinda akayi musun,saboda haka ya saki murmushi

"Bazan hanaki daukan dukkan matakin da kike gani ya dace ba,matakin da kike ganin shine zaisa ki huce....duk da mantawa zaiyi wahala,saboda anyi muku dukkan abunda ya cancanci dan adam yayi fushi akai,wanda koda nine akaiwa bazan qyale ba....amma ni alfarma daya nake nema shine,a maidamin surukata tare da yaranta,ta koma cikin ahalina,duk duniya kowa yasan cewa itadin ta zama familyn marigayi sarki mu'az kaisa,jikokina susan asalinsu,hakanan aurensu yaci gaba...bayaga haka bana buqatar komai daga haka".



      Ita dinma kamar shigen abinda malam bilya ya fada haka ta amsawa maimartaba cikin girmamawa

"Allah ya taimakeka....indai wannan alfarma ce mudai mun maka,adalcinka yafi gaban ka nemi abu aqiyi maka,saidai.....bilkisu marainiya ce,hakanan mun mata alqawarin cewa zata yanke dukkan hukuncin da yayi mata babu mai tursasata,saboda duk qalubalen rayuwarta ta fuskanceshi ita kadai ba tare da munsan me ta gani ba,don haka muma kuke roqon alfarmar cewa,zamu barta ta yanke dukkan hukuncin da taso" kai yake jinjinawa cike da gamsuwa

"Maganarku da hukuncinku yayi daidai,matuqar muka shigo da tursasawa cikin lamarin bamuyi adalci ba sam,hakanan ba lallai mu samu abinda muke nema ba....,a yanzun haka na baro ayyuka da yawa a fada,amma zan dawo da kaina rana ta daban na ganta muyi magana".



      Ko bayan tafiyarsa zancan suka rinqa tattaunawa a tsakaninsu,sam bawan Allahn bai dauki mulkin da yake dashi a bakin komai ba,ya dauki rayuwa da sauqi qwarai da gaske,ko a mafarki basu taba kawo cewa zaiyi tattaki har cikin gidansu ba saboda diyarsu,basu taba zatan zai nema wata alfarma ba daga gurinsu,duba da irun girma matsayi da martaba da yake da ita.



      Saidai duk da wannan babu abinda ya rage haushin fulani a zuciyar anty zuhriyyan,da kuma alwashin da taci a kanta na nuna mata kurenta koda sau daya ne tak cikin rayuwarta,tabbas saita aiwatar da wannan,saboda ta san itace kanwa uwar gami,kuma ummul'aba'isin na faruwar komai



     Cikinsu babu wanda yayi zancan da bilkisu,itama kuma batasan meke wakana ba,tasan dai a ranar anyi baqi a gidan,kuma da alama manyan mutane ne,daga haka bata fahimta komai ba,kuma bata tamnaya ba,sabida dama tambayar abinda bai shafeta din ba ba dabi'arta bace.



*ABDUL_AZEEZ*



      Duk da abinda mai martaba yayi masa na nuna halin ko inkula,da kuma korar da yayi masa hakan bai sanya ya haqura ba,ya sake iskeshi a dakin hutawarsa,bayan ya gama wani xama na musamman da dukka hakiman dake qasarsa.



      Da kallo me martaba ya bishi,yana karantar sauyi qarara tattare dashi,ga duk wanda ya sanshi duba daya zai masa ya tabbatar da cewa lallai abdul'azeez din ya sauya,hakanan akwai abinda ke yunqurin kawo masa tarnaqi a rayuwarsa.



     Bai dakata ba har sai daya isa gabanshi a lokacin da yake kashingide,ya zube bisa dukka gwiwoyinsa a gabansa kanshi a qasa

"Na sake kawo kaina Allah ya taimakeka,na sani cewa nidin me tarin laifi ne a wajenka,hakanan na cancanci dukkan wani hukunci daga wajenka,amma ina roqon yafiya da gafararka da kume neman alfarmarka kan ka shiga lamarina" ajiyar zuciya ya sauke a boye,yana mamakin yadda duk sanda zaiyi magana saiya tattarawa kanshi dukka laifin ya aza saman wuyanshi,sam baya ambata ma sunan mahaifiyarsa a ciki,kamar shi kadai ya aiwatar da abun,yanajin tausayinsa amma yana ganin bai kai stage din dazai janye horonshi haka tunda wuri ba shida uwarsa,cikin tsare gida irin wanda yakanyi lokaci zuwa lokaci,musamman idan yana shari'ar data bata masa a rai a fada yace

"Banga amfanin zuwa ka nemi yafiyata ba,bayan bani kuka zalunta ba,mai ciwo daban mai neman magani daban?,kuma ma da kake fadin na shiga case dinka azeez ashe ina da qima da mutunci har haka?,ai na zaci nidin ba kowa bane,hakanan bani da wata rawar da zan taka cikin rayuwarka,banason na sake jin komai daga bakinka,ka tashi ka nemi yafiwa wanda kuka batawa,don ni babu abinda xan iya yi maka".



       Yafi kowa sanin cewa shidin kaifi daya ne,idan yayi gaba mawuyacine ya dawo baya,daya daga cikin halayen daya gada kenan daga gareshi,don haka gwiwa a sake ya miqe ya soma takawa a hanakali hannayensa goye a bayansa,fulani aisha tayi saurin komawa da baya kafin ya risketa,zuciyarta na wata irin quna,saita fasa shigowa,ta koma izuwa sashenta,tabbas dole tasan abunyi,basu taba samun sabani koda shigen wannan ba tsakaninta da maimartaba,bare abdul'azeez da yake lelensa,ya kamata ta farka,ta kuma lalubi abunyi.



      Babu wanda ta kula koda barorinta da suka zube suna ta faman yi mata barka da dawowa,hakanan afanan data samu zaune a falo tana karatu,itama afnan bata ce komai ba,sai binta da kallo da tayi harta shige dakinta,ta dauke kai afnan ta maida ga littafinta,saidai kuma itama zuciyarta ta fada kogin tunani.



      Kai tsaye ta tsaya a gaban mudubin dakinta,kanta take qarewa kallo sosai,ba zata iya tuna wani abu daya taba damun rayuwarta ya sanyata rama haka ba irin wannan lamarin,ra hasaso azeez a idanunta,ta kuma hasaso sanda yake zube gaban maimartaba yaba masa magiya,amma yayi burus dadhi,kwatankwacin yadda yake mata itama,ta sima gajiya,ta sima kaiwa maqura,wai shin ma me zai hanata ta tunkari yarinyar ayi me gaba daya?,me zaisa ba zata sake bin wata hanyar ba,ta jarraba koda kome zai daidaita?,da wannan tunanin ta samu relief,ta kuma zauna tana tsara yadda zata gabatar da komai.



¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶


     Kalaman da memartaba ya gaya masa,sai yaji kamar yana bashi izinin ya sake yin dukkan me yiwuwa ne ya nemi yardar bilkisu,hakan ya sanya a washegari ya kuma shiryawa kamar kullum shi daya tak,bayan ya dakatar dakkan 'yan rakiyarsa ya nufi gidan anty zuhriyya.



      Sanda take fitowa daga gidan da niyyar zuwa gidansu zata dauko su amatu da suka kwana a can,daga nan kuma ta biya ta gidan biki ta su taho tare da anty zuhriyya,wadda dukkansu yau suna gidan wunin biki daga ita sai mai gadi a gidan,a lokacin ne shima ya faka motarsa,ya kuma fito yana kulleta sukayi kacibus.



      Cak ta tsaya ba tare data iya koda qara taku guda ba,yayin da shima ya tsaya daga rufe motar da yakeyi,idanunshi fes bisa kanta,zuciyarsa na wani irin bugu garwaye da wani matsanancin sonta da yaji yana taso masa.



      Tayi masifar kyau cikin shigar da tayi,babu wanda zai kalleta bai sake kallonta ba,saboda yadda tayi fresh,kana kuma kallonta zata tabbatarwa kanka ruwa biyu ce,chaculet colour din fatarta ta sake fita sosai ta qara haske,wanda sauran kadan ka kirata da fara idan ta shiga jinsin wasu masu choculet colour skin din.



     Takowa yasoma yi yana burin ya cimmata a inda take tsayen,saidai tun kafin ya qaraso din ta kuma ciki da sauri kamar wadda taga dodonta.



     Koda ta buda falonma bata tsaya a nan ba,sai data dangana da bedroom dinta,sannan ta samu kujerar madubi ta zauna tana maida numfashi,takaici ya kamata,tana ta murnar kwana biyu bai zuwa,ko yayi zuciya ne ya dauke qafa,sai kuma yau gashi katsaham,sai taja tsaki tana dora jakarta saman madubin bayan ta ciro wayarta.



     Koda ya tafin bq zata fita yanzu ba,saita tabbatar da yayi nisa da unguwarsu,don haka ta kira number hauwa'u,ta sabuwar wayar data siya mata,tace kada suji shuru,sai zuwa anjima zata shigo,sannan ta kashe ta kira anty zuhriyya itama tace sai rana ta qara yin sanyi sannan zata zo,ta kashe wayar tana jan tsaki gami da dora wayar saman madubi,sai kawai ta miqe ta zare takalman qafarta,ta kuma ware rolling din kanta,take gashinta da yasha gyara yake qyallin ya bayyana,doguwar rigar jikinta data fidda shape dinta sosai daga sama ta sake qara mata kyau,saita haye saman gadonta tayi ruf da ciki bayan ta runtse idanunta,tana addu'ar Allah yasa yabar qofar gidan da wuri.



      A qalla wajen minti goma tana a haka,ta soma gajiya da kwanciyar,ta sake gyara kwanciyar tata zuwa rigingine tana jan tsaki,gami da soma qunquni saboda takaicin bata mata lokaci da yayi,kamar a mafarki ta hangi kamar inuwar mutum wanda hakan ya razanata,ya kuma sanyata bude idanunta da sauri.



      Ji tayi zuciyarta na neman faso qirjinta ta fito sanda idanunta suka hango matashi,tsaye bakin qofar shigowa dakin,ya jingina da qofar bayan ya budeta,ya harde hannayensa duka a qirji,bayan yaui crossinh qafafunsa,tamkar mai shirin daukan hoto.



     Zumbur ta miqe cikin razana,tare da mamakin yadda ya iya ratso harabar gidan,ya qaraso har falon gidan,ya kuma riski dakinta,duk da cewa ba abun mamaki bane tunda babu kowa cikin gidan,amma babban abun mamakin shine,girman qarfin halinsa da har ya iya hakan.



      Kasa magana tayi,sai wani zama da tayi tsakiyar gadon bayan itama ta zuba mishi idanu,kamar dabbar dajin da aka kawowa farmaki tana jira taga motsin wanda yakeso ya farmaketan.



      Minti guda kafin ya saki hannayen nasa,sannan ya soma takowa cikin dakin,wanda hakan ya sanya itama ta soma motsawa sannan ta fara magana cikin hayaniya,duk da a cike take da tsoro

"Karka soma shigomin daki,ka fitarma mutane daga gida malam,nan gidan matan aure ne,don me zaka shigo musu gida babu izininsu?".



    Bai kulata ba,illa gadon daya durfafa idanunshi a kanta,yana qarewa shigar jikinta kallo,wani shauqi daya jima baiji irinsa ba na neman tasiri cikin ranshi.



    Karar wayarta dake saman madubi ya dakatar dashi,dukkansu suka dubi wayar lokaci daya,saiya sauya akalarsa zuwa inda wayar take

"Karka tabamin waya mana,meye hakan?" Ta fada da sauri cikin jin haushi,bai juyo ba bare ya tanka,yasa hannu ya dauki wayar yana duba me kiran.



     Dr adam ne,tuni ya gane waye,saboda number waje dake nuna daga qasar da aka kira,wani abu yaji ya soki ranshi,sai yayi rejecting kiran.



     Yana qoqarin maida wayar yaga sms saman screen din wayar,da sunan ASSADIQU,ya latsa kai tsaye ya sadar da kanshi ga akwatunan saqonninta


_gimbiyar duka kyawawan duniya,banason na cika damun wannan kyakkyawan ruhin mai cike da aminci,amma ina buqatar a tabbarmin da zuwan nawa,yayi ba matsala?_



     Idanunsa ya runtse na wasu sakanni,yanaji taba sake bashi umarnin ya ajemata waya,sai kawai ya kashe wayar gaba daya ya sanyata cikin aljihunsa,sannan ya juyo yaci gaba da nufar gadon da take

"Wai kurma ne kai,bakajin me nake cewa?gidan matan aure ka shigo musu baka nemi izni ba" Ta sake fada cikin tsiwa.



      Bai amsata ba har sai daya qaraso bakin gadon,ya kuma zauna a gafensa a nutse,sannan cikin narkakkiyar muryarsa yace

"Na sani,kuma nima tawa matar auren nazo gani"

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 70


https://youtu.be/-kbsWo6IjOo


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070



     Wani kallo tayi masa na tsiwa,wanda shi kuma ya jishi har jinin jikinsa

"Wace matar auren naka?,idan zaka farka daga wannan mummunan mafarkin naka ka farka,ada dai qaddara tasa na zama matarka,bada amincewata ba,ba kuma don ina sonka ko qaunarka ba,sai don......".



       Gaba daya ya fincikota zuwa cikin jikinsa da hannunshi qwaya daya tal,ya kuma haura gadon dasu gaba daya ya turmusheta,bayan ya azq mata dukka nauyinsa,abinda bata zata ko tsammata ba,hakan yaso wucewa da numfashinta na wucin gadi.



      Cikin sakanni qalilan dumin jikinsu ya gauraya,suka soma musayar numfashi duk da yadda nata numfashin yake mata wahalar jaa da kuma fitarwa saboda yadda yake a samanta ya aza mata nauyinsa,fuskarshi saitin nata,idanunshi da suka sauya launi cikin nata,duk da sun rage girma hakanan launinsu ya sauya,amma sai taji sun mata nauyi,wani yanayi can daya taba shudewa da dadewa memory dinsa yazo cikin qwaqwalwarta a take,saita birkice masa,ta soma tureshi da dukkan qarfinta,tana magana da qyar

"Ka dagani ko in maka ihu"

"Bismillah" yace da ita,alamun ya bata damar yin ihun,sai kawai ya sanya bakinsa saman dogon wuyanta,bayan ya saka hannunshi ya sauke jelar gashinta,ya soma aika mata da wasu saqonni da suka sanyata mutuwar wucin gadi cikin salo na babu zato bare tsammani.



     Hankalinta ta maida jikinta cikin sauri,ganin yadda tsigar jikinta ta soma zubawa,saboda yadda ya canza waje daga wuyan nata zuwa kunnenta,tun tana tureshi harta soma gajiya,tun tana cewa zata masa ihu harta soma cewa zata masa Allah ya isa,amma baima nuna yasan tanayi ba.



      Babban abun tsoron yadda taji jikinta na sauyawa,mood dinta yana canzawa zuwa wani yanayi mai wahalar fassarawa,duk da yadda zuciyarta take a zafafe amma hakan bai hana gangar jikinta amsar saqonshi ba.



       Hankalinta ya sake tashi ganin yana nemam shiga wata gona ta daban,taji kamar sama zata rikito mata data tuna gidan babu uban kowa bare ta nemi maceci,sauran qarfin daya rage mata ta sanya dukka ta turashi,ya motsa,saidai bai sauka daga samanta ba,saidai kamar allura ta masa ko wata tunatarwa,donshikansanya soma manta a inda yake.



      Ya tsaya cak da abinda yakeyi din,ya kifa kanshi saman qirjinta yana maida numfashi da sauri da sauri,yana kuma jin yadda itama take maida numfashin har qirjinta yana dagawa,sautin bugun zuciyarta ya fito muraran.



     A hankali ya soma saita nutsuwarshi,baiso ya daga fuskarshi a haka ta ganshi a ayanayin da yake ciki,ita dinma bata sake wani yunquri ba,don da qyar take fusgar numfashinta,tana kuma son daidaita nutsuwarta,ta yadda zata iya masa qwaqwqwaran kashedi.



     A hankali ya mirgina gefe sannan ya tashi ya zauna sosai na wasu sakanni,hakan ne ya bata damar gajin yadda ya yiwa rigarta,saita juya itama da sauri tayi rub da ciki,haushi da takaici gami da matsananciyar kunya tana kamata.



      Tana jin takunsa amma ta kasa juyowa bare ta masa tsiwa ko jan kunnen da tayi niyya,taji tsaiwarsa bakin madubinta na minti kusan daya sannan taji ya nufi qofa,sai kuma ya dakata.



      Ba tare daya juyo ba cikin wata shaqaqqiyar murya yace

"Ban zama lusari ba,ba kuma zan taba zama ba,sassaucina da sanyina ya ta'allaqa ne kan laifin da nasan mun aikata miki,har a yanzun ke matatace har a wajen Allah,ina da kishi matsananci,bazan lamunci shigar kowa gonata ba ko wucewarsa ta gefenta ba,duk wanda ya aikata hakan zai gane bani da dadi,nafi namijin goro daci,ki masa kashedi,ki kuma ja masa kunne da babbar murya cewar kada ya sake ya sake nuna ya taba saninki ko a hanya,indainyana son tsira da mutuncinsa da lafiyarsa,idan kuwa ke kika kulashi....to ban yafe ba koda ban gani ba" daga haka ya taka a nutse yayi gaba.



     A zabure ta miqe da niyyar gaya masa cewar bai isa ba,kuma shi yasan da wani igiyar aurensa a kanta,ita batasan da wannan ba,saidai kallo na qarshe daya jefeta dashi,ya kuma ja qofar ya rufe shiya kashe bakinta murus,tsahon minti guda tana zaune saita koma ta kwanta rigingine tana jan tsaki.



      Maimakon taji haushinsa sai ta soma jin haushin kanta lokacin da qamshin mayen turarensa ya soma buwayar hancinta,data bincika da kyau sai taji jikinta ke qamshin kamae ya fesa mata turaren ne,hatta da fatarta data shanshana qamshin take,hakanan bedsheet dinta,haushin kanta ya cikata,saita miqe ta zauna tana tuhumar kanta,ya akayi tayi sake haka har ya cimmata,me yasa sanda ya shigo bata shiga bandaki ta kulle ba?,wani dogon tsakin taja ta sauka daga gadon,ta isa bakin qofa ta murza muqulli sannan ta nufi bandaki,don ta tabbatar idan ba wanka tayi ba ba zata daina jin qamshin ba.



      Ita kadai a toilet tana wanka amma taja tsaki yafi cikin kwando,takanji haushin kanta ya sake kamata idan ta tuna yadda ta ruski jikin sanda tazo yin tsarki

"Allah ya isa na" ta ambata qasa qasa,bata taba tsintar kanta a yanayi irin wannan ba sai yau,kuma duk silarshi.



       Kayanta ta maida data fito,duk da sun yamutse,ta isa gaban mudubi ta kalli kanta,duk sai taji haushin rigar ya kamata,don haka ta zage zip din ta cireta ta cillata cikin kayan wanki,ta dauko wasu ta sanya.



      Tana shirin barin gaban madubi taga qaramar takarda da bironta data yi rubutu dazun aje a gefe,saman takardar memory card ne akai,ta dauke memoryn ta warware takardar.



      Lafiyayyen rubutu ne cikin tsari kamar haka

_banda a gidan wasu nake,wasunma dana shigo gidansu ba tare da izininsu ba,wanda hakan ya taka dokar addini,da yau saina kaiki duniyar da zaki gane shayi ruwa ne,ki kuma sake sako wasu twince din part two,amma ko a yanzun nasan na bar miki tambarin da zaki dinga shafawa,kina kuma tuna cewa kedin mallakin wani ce,mallakin abdul'azeez shi daya,kuma har duniya ta nade....,ga memorynki idan kina da buqata,wayarki kuma da layukanki kunyi sallama dasu,nama yi gwari da tuntuni ban rabaki da ita ba,don bansan gardin daya saya miki ba,nima na tafi da memory mai dadi a ruhina,duk da kin cakawa zuciyata mashi,kishinki zai iya halakani kafin safiya,karki kuma sake fita bada iznina ba._


           _yarimanki ne,uban 'ya'yanki kuma_



      Yayyaga takardar ta hauyi tana masifa ita kadai

"Aikin banza aikin wofi,gwara ka nema matarka tun dare baiyi maka ba,don ban yarda da wannan tatsuniyar ba,kuma abinda kayin yanzun alhaki a kanka wallahi,baka isa kamin shamaki da yin mu'amala da duk wanda naga dama ba,wayata kuma dole a adawomin da abata,tunda ba wani ne ya siya min ba ehe" haka ta dinga masifa ita kadai cikin gidan,ta koma gadon ta kwanta bayan ta canza zanin gado,sadai bata dade da kwanciyar ba taji sam kwanciyar babu dadi,hakanan ta dinga tariyo mata abinda ya faru dazu,don haka ta kuma jan tsaki,sannan ta sauko daga gadon taja dankwalinta ta daura,tama fice daga dakin gaba daya zuwa falo,da niyyar daukar landline ta kira anty zuhriyya,don yadda takejinta sam a yanzun bata son fitar

"Kodai gargadinsa ne ya miki tasiri" wata zuciyar ta tambayeta,kamar ita da wani tace

"Haba,shi din banza,bai isa ba"Ta baiwa kanta da kanta amsa,tana isa wajen wayar ta zauna sannan ta janyota ta fara kiran.



      Anty zuhriyya cewa tayi tayi zamanta ma kawai,sa biya su dauko yaran duka saisu dawo tare,hakan itama ya mata dai dai,saboda wata muguwar kasala da takeji,kuma hakanan taji fitar ta fice mata aka.



       Har zata tashi sai kuma ta koma ta zauna ta kira assadiq,tambayar abinda ya samu wayarta ya fara yi,saita rufe masa kan cewa babu chargy ne,ta sanyata a chargy,sannan ta gaya mishi amincewarta na zuwanshi a goben.



      Hira yake janta dashi,amma sai taji sam hiran bata mata dadi,don haka ta dauki uzuri ta aje wayar,sai kawai ta zame a nan ta kwanta,don gaba daya batason komawa cikin dakin,saboda qamshinsa da har yanzu bai bar dakin ba.



      Anan dinma bawai ta tsira bane,haka abun ya dinga fado mata arai,ta dinga juyi tana canza kwanciya gami da jan tsaki ita kadai.



      Tun a hanya yana tuqi yake jinsa cikin wani irin nishadi mara misaltuwa,kallo daya zaka yiwa fuskarsa ka karanci hakan,a lokacin ya dinga tuhumar kansa,mai yasa ma ha tsaya yana kallonta a baya bai mori lokaci irin wannan ba?.



       Yanayin ya dawo masa da memory masu yawa da suka shude a wancan lokacin,ya tuna first night dinsu,wani irin baudadden first night,wanda ko a labaru shidai bai taba jin irin nasu ba,saiya saki murmushi,ya saka hannunsa guda daya da baya tuqi da shi ya shafi qirjinsa

"Zan qawata darenmu na farko da zamu sake rayawa fiye da tunaninki,na miki tanadin soyayyar da sai ta kusa zautaki ta kuma zauta tunaninki" ya furta haka shi daya cikin zuciyarsa,da wannan yanayin ya isa gida,kana kai tsaye ya wuce sassansa.



       Toilet ya fada yayi wanka,sannan ya dawo ya fada saman gadonshi bayan ya fito,bai jima a duniyar tunani ba bacci yayi awon gaba dashi,baccin dake cike da wata irin nutsuwa daya jima bai sameta ba,baccin daya cika da.mafarkai,shida bilkisu cikin wata rayuwa mai dadi irinta ma'aurata,wajen da baikai ba a mafarkinsa sai daya kai,hakan ya sanya bayan ya farka dole ya sake wanka,zuciyarsa ta sake cika fal da shauqinta bege da wata iriyar zazzafar qauna,hakanan ya fito shi daya yana shawagi cikin wani lambunsa dake sassansa,yana jin zuciyarsa fayau,sai nishadi da soyayya da suka cikata maqil.



      Bayan ya koma daki abun mamaki saiya tadda miscal din safwa jingim,tsaki yasha yana gyada kai ya aje wayar baibi ta kanta ba,ya rantse wannan karon zaka ga ainihin kalarsa da bata taba gani ba,zai saita musu tunani tunda su ya fuskanci basu dashi.



¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



       Tsaye take gaban mudubinta riqe da soson hoda da take shirin shafawa fuskarta amma ta kasa,saita buge da kallon kanta,ta rasa me yasa hakanan batajin wani karsashi a jikinta,farinciki ko dokin zuwan assadiq sam,bayan ita ta bashi iznin zuwan,komawa tayi saman kujera ta zauna riqe dai da soson

"Ko gargadinsa ke razanar dake?,ko don maganar da yayine kikeson ki fasa fita?" Zuciyarta ta tambayeta,saita kada kai da sauri

"Allah ya sawwaqe,shi din wa?" Tayi maganar tana fara shafa hodar a fuskarta.



       Turare tadan dake fesawa kadan,sannan ta zura hijabinta mai hannu dark pink,wanda ya haskata sosai,ta zura slippers sannan ta fito.



       Suna falo dukansu suna kallo,anty zuhriyya ta fita kitso tun daxun,daga ita saisu cikin gidan ta dubesu

"Najwa,akwai girki a kitchen,ki duba kafin na dawo"

"Tohm mami" ta amsa mata tana sake gyara zamanta saboda yadda kallon yayi mata dadi.



      Amatu ce ta nace saita bita,hakanan badon taso ba ta barta suka fita tare.



       Yana daga qofar gidan saman motarshi,cikin mamaki ta dubeshi

"Ya baka qaraso ciki ba?" Murmushi ya saki

"Nishadi nakeji yaukam,sai naji nafison zaman nan din,kona bude miki motata mu zaua ciki?" Wani kallo ta jefa masa mai kama da harara,saiya qyalqyale da dariya,don yasan kwanan zancan,ba abinda tafi tsana irin zance cikin mota,shi yasa shima ya tsokaneta da hakan.



      Shirmen amatu ya tsaya biyewa har sukaci lokaci kafin ta shiga gida ya kuma saurareta

"To ya akayi?" Ya fada cikin murmushi yana dubanta,saita daga kai daga wasa da take da yatsunta tun daxu data fada duniyar tunani duk zaman hirarshi da amatu,murmushi kawai ta saki

"Kai za'a tambaya" gyara zamanshi yayi

"Kinsan meye?"

"Saika fada"

"Hajiya na bala'in son na kai mata ke ta ganki,tunda na soma mata zancanki itama kullum maganar kenan,ta matsu taga nayi aure,saboda na soma mata zancan rabi'a,har ta saka rai kuma taji shuru" murmushi tayi ta kada kai

"Lokacine,zamuje idan yayi".



      Daidai lokacin anty zuhriyya ke dawowa daga gidan kitson ita da abeed,suka gaisa da assadiq,saidai yanayin fuskarta a yau ba kamar yadda suka saba gaisawa ba,hakanan tayi gaba tana dan binsu da kallo wanda hakan ya sanyawa bilkisu tsarguwa.



       Tun safe yake fama da kanshi kan yadda yakejin matsanancin son ganinta,duk yadda yaso hana kanshi ya kasa,saboda haka daga masallaci da yayi sallar la'asar kawai yasaka cikin hadiman gidan mutum biyu suka daukoshia mota suka kawoshi.



       Suna dosar unguwar farincikinsa na daduwa,yauma kota halin yaya yana jin saiya ganta koda bataso,saidai kuma me?,suna kusantar gidan fara'arsa tana raguwa,tun idanunsa na ganin masa kamar ba dai dai ba har ya tabbatar ita dince dai tsaye,tsaye tare da wani.



      Wani bala'e'en wutar kishi ce ke ruruwa cikin ransa da zuciyarsa,lokaci daya kamanninsa suka canza,ya dinga furzar da huci,tun kafin su qarasa ya sanya suka faka motar,yayi shuru zaune a ciki yana kallonsu daga inda yake.



      Da qyar ya iya daidaita numfashinsa sannan ya dakatar da hadimin dake yunqurin bude masa qofa,ya bude da kansa,qafafunsa ya soma zirowa kafin gangar jikinsa ya biyo baya,hannayensa zube cikin aljihunsa yake takawa zuwa inda suke tsaye,idanunsa a kansu harya cimmasu.



       Sam basu ganshi ba,tana bashi amsar wata tambaya da yayi mata,wadda tambayar tayi matuqar bata dariya,sai suka hada idanu da ita.



      Cak dariyar ta tsaya mata,gabanta yayi wani mummunan faduwa da batasan dalilin hakan ba,hakanan taji dukka gwiwoyinta sunyi sanyi,koda batasan fuskarshi sosai ba amma tasan cewa zallar bacin raine a saman fuskarsa.



      Sauyawar yanayinsa ya sanya assadiq juyawa shima,suka hada idanu da yariman,saiya dan zuba mishi idanu,shahararren dan kasuwan da ya jima yana ganin tarin kama mai yawa tsakaninsa da yaran bilkisun,abu biyu ya  hanashi mata maganar koya tambayeta,abu na farko yana tsoron amsar da zaiji daga gareta,tace masa eh shine mahaifinsu amatu,wanda indai.hakan ya kasance,bayajin matar data taba mallakar mutum kamar azeez din zata soshi so na qauna har zuciyarta,ta kuma aureshi da zuciya daya,a ma'aunin cancanta da kaiwa mizani ko kusa ko alama bai isa ya hada kafada da yariman ba,tako wanne fanni ya mishi shal,babu bigiren da zaya iya tsaiwa ya hada qualitynsa da nashi,tun daga kyau,ilimi,zati cikar halitta da haiba,uwa uba dukiya da nasaba.



      Abu na biyu kuma idan ya tuna tun asali,auren dole akayima bilkisu,wanda bayajin akwai macen da za'a aura mata mutum kamar abdul'azeez kaisa din ta kira auren da sunan auren dole,mutumin da tarin cincirindon 'yammata ke buri da fatar ya waiwaya ya dubesu koda sau daya ne,koda bada batun aure ba,koda iya friendship ne kawai amma basu samu wannan damar ba,sannan bayajin mutum kamarshi zai auri macen da baiso ko bata sonshi,saboda dama da Allah ya bashi na iya auren duk irin nau'in macen da yakeso,daga kowanne irin nau'in jinsi yare ko qabila,wadan nan tunane tunanen da yake yawanyi su suke gaya masa ba abinda ya hada bilkisunshi da shi,face kama kawai daga Allah,wadda ke nuna zallar qarfin ikonshi,isarshi qudirarsa da iradarsa,kamar yadda yaji ana cewa,kowanne dan adam akwai masu kama dashi a doron duniya mutum saba'in.



        Kallo daya tak ya yiwa assadiq yasha jinin jikinsa,hakanan ya sake tsaida hankalinsa tsam,a hankali ya bude bakinsa cikin izza da qasaita yace

"Banason in cutar dakai,amma kada ka yarda ka qara minti biyar qofar gidan nan" yana kaiwa haka ya damqi hannun bilkisu yayi gaba.



     Turje turje ta fara yi tana fadin ya sakar mata hannu,amma baiko waiwayeta ba har ya isa bakin motarsu,ya baiwa hadiman umarnin su fita subar mishi key din a jiki.



      Haka kuwa akayi,ya sanyata a mazaunin kusa da driver ya rufeta,sannan ya zagaya daya set din ya zauna ya rufe sannan ya tashi motar da wani irin mugun gudu daya tsorata bilkisu ya fice daga layin.



      Tafiya sukayi ta wajen mintina talatin kafin yaja wani wawan burki daya sake tsoratata,ba tare daya kashe motar ba ya waiwayo yana dubanta,ya zuba mata rinannu kuma narkakkun idanunshi,cikin jikinsa can qashinsa yakeji kamar zazzabi nason kamashi,yayin da yaketa controlling fushinsa,saboda baiso yayi abinda bai kamata ba,ko ya wuce gona da iri.



      Dauke nata idanun tayi daga irin kallon da yake mata,cikin hade girar sama data qasa tace

"Ina kake shirin kaini,ka maidani inda ka daukoni,koka budemin na fita kaji ko?".



      Shuru yayi mata kamar baxaiyi magana ba,sai daya tabbatar ya rage kaso mafi yawa ma fushin dake cinsa sannan ya bude baki,cikin murya mai sanyi kaman an sanyashi a ruwan qanqara,saidai kuma cikin fushi dake bayyane qarara cikin muryarshi yake cewa

"Bakisan ainihin waye azeez ba....nayi imani da hakan,kozan lamunci komai bazan lamunci wasa da izgilanci da igiyar aure na ba,kiyi komai saboda an taba ranki,amma banda wasa da martabar aurena....idan da naso,zan iya daukarki,na kaiki wani waje wanda ba wanda yasani,tunda kedin mallakina ce,amma bazanyi hakan ba,saboda aikata hakan kamar nayi amfani da qarfina ne maimakon neman yarda da aminci afuwa da kuma shafe laifuka da mantawa dasu,amma ki kiyaye,ki kiyayi aikata ire iren wadan nan abubuwan,na rantse daga yau duk wanda na sake kamawa yazo wajenki da sunan tadi sai na masa daurin da babu wanda ya isa ya fito dashi,sai nasa ya bata,bacewa ta har abada...." Sosai kalamansa sun shigeta,kuma daga yanayinsa ba shakka zai aikata sama da hakanma a kanta,to amma batason ta nuna mishi weekpoint dinta bare yaci gaba da amfani da hakan,saboda haka cikin tsiwa tace

"Saboda kuna da mulki?,kuna da kudi?,kuna da fada aji?,saboda kai wanine?" Bai amsa mata ba,hakanan bai fasa tada motar ba,illa dai kawai yayi wani qaramin murmushine na gefan baki,idanunsa na akan titi,yayi ribas din motar ya koma titin daya baro,sai a sannan yayi magana guda daya

"Lokaci ne....kibi a sannu 'yammata" yayi furucin yana qoqarin cooling mind dinsa,don ba qaramin zafi yakeji qirjinsa yana masa ba,kamar ana kara masa garwashi.



      A qofar gidan ya sauketa,fit ta fice ba tare data waiwayoshi ba,ya bi takunta da kallo harta shige,sannan ya lumshe idanu yana jin yadda qirjinsa keci gaba da zafi,ya sake juya akalar motar a hankali ya fita a layin ya harba titi.



      A bakin falo ta tadda anty zuhriyya tsaye,kamar dama tana dakon shigowarta ne tace

"Ina kikaje?,na aika qofar gida kizo akacemin baki nan,babu motar assadiq din kuma a wajen" duk sai ta dibibice,ta rasa yadda zatayi mata bayani kuma me zatace mata?.



      "Ta dawo?" Ta jiyo muryar abbaa dake saukowa daga sama,saita waiwaya ta dubeshi

"Eh gata nan"

"Yauwa maigado,ki qarasa dakin baki kina da baqi" ya fada sanda yake qarasowa cikin falon riqe da wasu takardu.



      "Baqi kuma?" Ta fada cikin ranta cikin mamaki,tabbas taga baqin wasu kyawawan motoci a harabar gidan,amma bata taba kawowa cewa baqinta bane,to baqi daga ina?,kuma su waye?,ganin babu wanda zata yiwa tambayar sai kawai ta juya ta fice zuwa dakin baqin ranta cike fal da wasi wasi.



*_PLEASE SUBECRIBE MH CHANNEL SAUTIN HIKIMA_*👇ðŸ½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½


Watch

And 

Share ðŸ™Ã°Å¸½Ã°Å¸™Ã°Å¸½


https://youtu.be/p_fqPX2Ni9Y

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 71

https://youtu.be/0PAxvmzE1Uw



*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





       A hankali ta shiga falon bakinta dauke da sallama,hakanan takejin wani irin nauyi ta kuma kasa daga idanunta ta kalli falon bare taga su waye a ciki har sai data iso ainihin falon.



       Faduwar gaba taji saboda ganin fuskar dattijon wanda ke amsa sallamarta cikin sakin fuska dake cikin nadin farin rawani me ratsin gold,kwarjini da haibarsa sun cika falon gaba daya

"Maraba da 'yata bilkisu....maza qaraso nan" ya fada yana nuna mata daura dashi,ganin tana niyyar sulalewa ta zauna daga bakin qofar falon.



     A hankali ta qaraso,sannan ta zame ta zauna a qasa kamar dazun kanta na kallon qasa,ta motsa labbanta da qyar wanda batasan me yasa tunda taga mutumin takejin wani irin nauyi ba tace

"Barka da warhaka"

"Barka kadai diyata,marhaban da surukata bilqisu" kasa amsa mishi tayi,sai gingirin da taji kanta yayi mata.



      Shuru na wani sakanni sannan taji yayi gyaran murya sannan ya fara magana cike da dattako da kuma nutsuwa

"Sunana abdallah mu'az kaisa,mahaifi ga abdul'azeez...." Saiya dan dakata,yayin data sake daga kai a sace ta kalleshi,eh babu shakka,ga kama ta jini nan tsakaninsu,saita sake sadda kanta,yaci gaba da magana cikin hikima da nutsuwa

"Ya akaji da hidimar rayuwa,ina 'yan jikokina?" Gabanta yadan fadi,yasan dasu ne dama?,garin yaya?,waye ya gaya mishi gidan anty zuhriyya?

"Suna lafiya alhmdlh"

"Ma sha Allah"

"Amm....na samu labarin dukkan abinda ya faru tsakaninki da iyalina cikin satin daya gabata,a gaskiya ko a mafarki ban taba kawowa aisha ko abdul'azeez zasu aikata wani abu makamancin haka ba sam,sai gashi abun mamaki hakan ta faru,abun yayi matuqar girgizani da kuma daga min hankali,hakanan ya sakani cikin shakku da nazari..." Saiya dakata yana maida numfashi,da alamu abun yana tabashi sosai har yanzu cikin zuciyarsa

"Nazo da kaina wajenki diyata don na baki haquri,na kuma nemi gafararki.....karki dauka nazone a madadin abdul'azeez ko mahaifiyarsa,a'ah,nazo ne on behalf my self,nida kaina naga ya cancanci nima na baki haquri,saboda an cutatar da rayuwarki,an ruguxata ba bisa amincewa ko yardarki ba,an miki ta qarfi,kiyi haquri kiyi haquri ki kuma yafe ma masarautar kaisa gaba daya" wani irin kwarjini da nauyinsa takeji,da yake bata haqurin kamar zata nutse a wajen,indai har ta cika cikakkiyar yar adam,wadda ba butulu ba,ai bata da bakin magana sai godiya ga Allah,domin a yanzun ya mata komai,rashin cewa bata yafe din ba bataga me zai qareta dashi ba,don haka tace

"Ranka ya dade na yafe,Allah ya yafemu gaba daya" murmushi yadanyi sannan ya sake cewa

"Na gode qwarai da gaske....sannan akwai alfarma ta biyu da nakeso kiyimin,kada kice zaki duba wani abu ki tursasawa kanki wajen yin wannan alfarmar,a'ah....wannan zabinki ne,sai yadda kikace,ina mai neman alfarma a wajenki daki koma dakinki,kamar yadda abdul'azeez ya shaida min cewa ke matarsa ce,bayan ya maidaki gaban shaidu guda uku,mata biyu namiji daya,na kuma tabbatar da gaskiyar hakan....ina neman wannan alfarmar daga gareki ne domin kubutar da mutunciki da nasa da kuma na mahaifiyarsa da zaki taimaketa akan hakan" kanta ta daga da sauri ta kalleshi suka hada idanu,saitaji nauyi tayi maza ta sake duqad da kanta,alfarmar ta mata nauyi da yawa,har yaso ya fuskanci haka,saiya dora da cewa

"Kiyi haquri,ki kuma taimakemu,neman komawarki bawai yana nufin ki yafewa abdul'azeez ko aisha ba,kina iya ci gaba da hukuntasu ta yadda kikaso....sannan koda kin amince...zaki koma dakin nakine a duk sanda kikeso,igiyar aurenku ce banason a tsinkata kodon albarkacin albarkar yara har biyun da Allah ya baku,sa'annan shi kansa bazan shaida masa hakan ba,har sai kin gama hukuntashi son ranki,kin kuma gamsu a jiki da zuciyarki cewa hukuncin yayi miki.....don Allah diyata" ya furta yana dan zamowa kamar zai sauko qasa.



       Sosai taji wani irin nauyi da kunya,da kuma tsoron kada fa ya sauko ya durqusa mata,mutumin da aqalla yama girmi mahaifinta bare ita,data tabbatar sa'ar autarsa afnan ce,don haka cikin firgici da sauri ta furta kalmar

"Na amince" ba tare data shiryawa fadar hakan ba.




      Tana iya jiyo ajiyar zuciyarsa,ya saki murmushi wanda ya bayyana sannan yace

"Alhmdlh,alhmdlh,ba shakka kin cika 'ya ta gari,kuma nagartacciyar uwa ga jikokina,na gode miki sosai bilkisu,na gode qwarai da gaske,ubangiji ya albarkaci rayuwarku,yadda aka miki katsalandan a rayuwarki ina roqar sarki Allah ya sake miki juyi da sauyin rayuwa mafi alkhairi" addu'a sosai ya dinga jerowa tana amsawa da amin,har zuciyarta tayi wani irin taushi,hawaye ya soma sauka saman fuskarta.



       Sanda ta fita sai data turo.masa su amatu,sun jima a wajensa kafin su dawo cike da kyautuka.



      Batasan iya dadewar da sukayi ba,saboda tunda ta dawo tana dakinta a kulle,kwance saman gado tana rusgar kuka,tana kuma tuhumar kanta,anya batayi kuskuren amincewa zata koma rayuwa cikin wadan nan ahalin ba?,ta kuma amince babu neman shawara ko yarda antyn tata wadda take kamar mahaifiya a wajenta,wadda ta tsaya tsayin daka,kai da fata wajen inganta rayuwarta,harta kawo bigiren da take kai a yanzu,uwa uba kuma mahaifinta,duk da shi ya kasance sila kuma dalilim afkuwar komai,amma a yanxun ai ya canza,iri sauyin da bata taba zata ba,kuma kusan yama fita jin ciwo duk sanda ya tuna yadda al'amuran suka gudana.



       Ta fannin anty zuhriyya tana ankare da ita,ta kuma san kwanan zancen,don haka ta hana kowa rabar dakin da take,ta bata lokaci,tasan nan da wasu lokutta zata sauko komai zai daidaita,saboda ko a yanzun itama tafi mata sha'awar takoma gidan uban 'ya'yanta,amma har yanzu akwai jiqaqqiya tsakaninta da fulani,batajin zata barta haka.



       Ganin har sallar isha'i bata fito ba ya sanya anty zuhriyyan ta nufi dakin nata,inda tabar duka yaran suna cin abincin dare,tayi knocking qofar,a sannan bilkisun na saman abun sallah,wanda tun sallar magariba bata tashi daga kai ba,tayi istihara yakai sau goma duka a waje daya,tana neman zabin Allah,sai taji ta samu nutsuwa 'yar kadan cikin zuciyarta.



      Tashi tayi ta bude mata,ta shigo idanuta a kanta,kana ta samu gefan gadon bilkisun ta zauna kana tace

"Tunda baqonki ya tafi baki fito ba,hala lafiya lau?" Kanta a qasa tana murza tafin hannunta,tana jin wani nauyin anty zuhriyyan kan hukuncin data yanke ba tare da shawartarta ba,ta rasa ta inda zata soma gaya mata,sai taji qwalla ta cika idanunta

"Na aikata wani ganganci na saurin amincewa da alfarmar daya nema a wajena ba tare dana shawarci uwa a wajena ba,saboda girma da shekarunsa...." Murmushi mai sauti anty zuhriyya ta saki wanda ya baiwa bilkisu mamaki

"Kada ki damu daughter....qarshe dai kice kin amince zaki komawa aurenki ne....alhmdlh....hakanma kamar wani tarnaqine ga maqiya da zaki musu,kada ki damu,duk hukuncin da kika yanke ina bayanki dari bisa dari,matuqar babu cutarwa ko keta dokar Allah" wani wawan ajiyar zuciya ta sauke mai sauti a sarari,anty zuhriyya ta kalleta,can qasan ranta cikin sigar tsokana

"Daughter.....irin wannan ajiyar zuciya haka?,haka dama kikeson yarima?" Da sauri ta dubeta tana gwalalo idanu cikin mamaki

"So ummi....don Allah kibar fada,wallahi naji dadine da ranki bai baci ba" kaitake gyadawa tana gumtse dariya

"A'aha,ga abu a sarari na gani,soyayyace zallah..."

"Wallahi ban taba jin sonshi a raina ba ummi" ta fada kamar zata saki kuka,anty zuhriyyan ta tarbi numfashinta

"Meye na saurin shiga masallaci haka?yo in banda soyayya meya hana 7yrs idonki ya qyasa wani harki aureshi?,saida kika jira yarimanki"

"Ki yarda dani ummi...kin manta ban taba sanin fuskarsa ba....Allah ba qaunarsa"

"Shshshs!!!!" Anty zuhriyya tace dariyar da take boyewa tana qwace mata

"Bansan sakarya bace ke sai yau,uban yaran naki kike cewa baki qaunarsa baki taba qaunarsa ba?,tome zobensa yakeyi a wajensa?" Idanu ta sake fiddawa,sam ta mance dashi,ya akayi antyn ta gani

"Su amatu na ajewa" dariya sosai ta saka sannan ta dubi bilkisun da kyau

"Kina sonsa,baki sonsa yanzu ba wannan zancan akeyi ba,abinda na sani kawai shine,zamu qona ran abokan adawa....zan kuma soma gyaran diyata tun yanzun,zan soma shiryata komawa gidan uban 'ya'yanta" sosai bilkisu ta narke,gabanta na faduwa ta kalaman anty zuhriyyan

"Nifa anty bazan koma yanzu ba,saiya gane kurenshi,kuma ma idan na koma ai kamar yaci galaba a kaina" idanun ta zaro itama

"Gane kure kuma na nawa daughter?,har abada kuma koda kin koma koda baki koma ba kece kikaci galaba a kansu,kin gama dasu,tunda kika haifa musu yara,gasunan,duk wanda ya kallesu yaga masarautarsa KAISA zammm....so ki aje kome gefe ki fara karbar gyara daga wajena" daga haka ta miqe tana niyyar fita,sai bilkisun tace

"Zanje gobe naga baba"

"Allah ya kaimu" ta amsa mata tana qarasa ficewa daga dakin.



      ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶


      Motoci biyu ta tanada domin yin mata rakiya,don tana da buqatar sirri,ba kowane takeson yasan inda zata da kuma abinda zai kaita ba,sai wasu motoci ukun da aka cika da kaya na alfarma iri iri,kayan qyale qyale na mata,saika rantse da Allah wani lefen 'yar gatan xa'a kai,kama daga tufafi,kayan kwalliya mayafai jakankuna takalma da sarqoqi harda gwalagwalai.



       Cikin shiga ta alfarma ta nemi izinin fita wajen maimartaba,ya kuma bata izinin ba tare da yasan inda xata je ba,bare azeez wanda tun jiya daya dawo gidan yake kwance a sashensa cikin wani irin ciwo mara misaltuwa,ba tare da sanin kowa ba.



        Tun safe data tashi ta kammala dukkan ayyukan da tasan tana yi cikin gidan,kana fa koma dakinta ta shirya tsaf cikin wata doguwar riga da aka mata dinki da shufom da duwatsun shuwarisky masu qyalqyali da daukar idanu,saita bada wani samfur na daban,ta kuma haskata sosai,hakanan tayi kyau kai bakace ita ta haife amatu da abdul ba,tsaf zaka mata kallon budurwa.



        Tana fitowa falon tana lalubar atm dinta cikin jaka,don tana son ta yiwa babanta siyayya idan ta fitan kafin taje gidan,amatu ta kalleta

"Mami....nazo muje?"

"Babu da wanda xan fita,nima ba jimawa zanyi sosai ba,abinda ko wanka ma bakuyi ba,ku zauna bazan dade ba....,gidan daba baqonku bane,kusa ko yaushe kuna tafe.....ummi zan wuce"

"Saikin dawo,ki gaishesu,yauwa...,idan kin dawo ki tsaya don Allah ki tsaya a bawa road ki karbomin dinkunan nan wajen latif"

"In sha Allah" ta fada a gaggauce tana ficewa a falon.



      Najwa anty zuhriyya ta kalla

"Yau kam da alama qazanta kukeji ko?" Najwan ta dubi anty zuhriyya

"Wlh yau bansan zubawa jikina ruwa"

"Kyaji dashi,tunda ke baki da niyya hada kan abeed amatu da abdul ki musu,duk sanda kikaso ke kyayi" waiwayawa tayi ta dubi abdul,kamar yadda ta zata din kuwa ya hade ranshi qyam,cikin dariya dariya tace

"Ummi kema kinsan ba'ayiwa abdul wanka tuntuni ya yaye kanshi" duban yaron tayi,yaro qarami sai manyance,shi Ala dole ba za'a jikinsa ba,shi yasa ya daina yarda ayi masa wanka

"Ku shiga tare idan kin gama musu ki hada masa nasa ruwan na daban yayi,ai babban mutum ne dama bai kamata anty najwa din ta dinga ganin jikinsa ba" dariya sukayi gaba daya,shima sai a sannan ya sassauta fuskarshi.



        Ba'ayi minti biyar da shigar yaran ba mai gadi yayi knocking qofar falon,ta bashi izini ya tura qofar ya shigo,yana tsaye daga bakin qofar falon ya gaya mata saqon

"Hajiya....baqi kukayi cikin motoci,suna son a bude musu ne su shigo" tayi mamaki sosai,saboda iya saninta tasan basu da wani baqi,amma sai tace a bude musu su shigo din,ya amsa da to kana ya juya ya fice,saita miqe,ta isa window din dake can qarshe yana fuskantar harabar gidan,ta yaye labulen tana leqen masu shigowa.



      Motocin da taga suna shigowa sai suka bata mamaki,saita saki labulen ta koma falo tana jiranjin su waye zasu shigo.



      A hankali ta soma jin kamar banbadanci da kirari har zuwa qofar falonta,tana daga tsaye tana duban qofar falon,fulani ne akan gaba,sauran barorinta biye da ita.



      Sosai anty zuhriyya ta zuba mata idanu,tana hango kamannin dake tsakaninta dasu amatu da kuma yarima azeez,cikin sakanni 'yan kadan kwanyarta ta gaya mata ko wacece matar.



     Dukkan wani hade rai da bacin rai ta tattaro ta azawa fuskarta,ta kuma ci gaba da kallonsu har zuwa sanda suka gama shigowa 

"Su waye ku?" Ta fada kanta tsaye idanunta cikin na fulani

"Mu baqi ne daga masarautar kaisa....muna tafe ne tare da uwar gijiyarmu,amarya ga sarkin kaisa,mahaifiyar yarima abdul'azeez magajin sarki,wanda ya taba auren diyarku" wani kallon banza ta watsawa mai bayanin,sannan ta kuma sake maida idanunta ga wata dake kusa da ita

"Ba wannan dogon bayanin na buqaci ji daga gareku ba,wa kuke nema?,saboda babu wata alaqa data taba hadamu da wata masarauta ma balle ta qasar nan a iya namu sanin"

"Uwargijiyarmu ce tazo ta gana da tsohuwar surukarta domin samun sasanci" kubra mafi kusanci da fulani cikin hadiman ta fada,sake watsawa mai bayani na gaba kallon banza tayi sannan tace

"Kece zakiga bilkisun?,ko kece uwar gijiyar da kiketa rattabo bayani haka?,mu duka ahalinmu babu wata data taba rabar masarautar kaisa bare tayi auratayya da waninku,so ina tsammanin kun samu buguwar qwaqwalwa" zata sake bada amsa fulani ta daga musu hannu,gami da nuni da cewa dukkansu su fice,ba'a rufa wasu sakanni ba duka suka fice din kuwa,falon ya zamana daga ita sai anty zuhriyya.



        "Na tattako da kaina nazo ne domin samun maslaha,da kuma gyara barakar dake tsakanin maimartaba dani kaina da kuma yarona...inason a wannan karon idan so samu ne.....ta shiga masarauta ta bayyana yafiyarta ga abdul'azeez dani kaina,na mata alqawarin bata dukkan abinda takeso,na mata tanadin rayuwa mai inganci,hakanan ko a yanzun ma da tarin alkhairi nake tafe,idanma tana buqatar ta sake koma masa ne a matsayin matarsa,a shirye nake akan hakan,matuqar komai zasu daidaita".



     A kaikaice anty zuhriyya ke mata wani kallo,zuciyarta taxo iya wuya,wannan damar take nema babu shakka kuma gata tazo mata,idan har bata amayar da dukka abinda ke zuciyarta ba,idan har bata hana idanun fulani bacci ayau da zafafan maganganu masu quna ba tabbas ita din bata haifu cikin uwarta da ubanta ba,hakanan bata da rana a wajen bilkisu.

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 72


*Shiga tasharmu ta SAUTIN HIKIMA kayi subscribe,don samun da dadan litattafai*

👇ðŸ½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½Ã°Å¸‘‡Ã°Å¸½

https://youtu.be/0PAxvmzE1Uw


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





    "Matsalar guda daya kenan....bakya ganewa....kuma ban saka ran zaki gane ba,tunda har yanzu baki gane din ba,amma bari na baki wasu alamomi ko zaki gane din" sai anty zuhriyya ta gyara tsaiwarta tana harde hannayenta a qirji,tana kuma yiwa fulani wani irin kallo

"Hala sanda kuka shigo gidan nan idanunki a kulle suke,koda a bude suke toba shakka girman da munin abinda ke zuciyarki ya rufe miki idanu.....ki kalla gidan nan da kyau,tun daga waje zuwa ciki....mun miki kama da mabuqata?....koda munyi zubin mabuqata,ba shakka Allah ne ya yisu,kuma ya yisu a hakanne bawai don baya sonsu ba,ya yisu ne saboda jarrabawa da sanya rayuwar kowanne bawa bisa mizanin jarrabawa,kuma ya yisu a hakane badon masu kudi mulki ko sarauta sun kasance mafiya soyuwa a wajen Allah fiye dasu ba"



      "Naji kina wasu maganganu,duk da bani da tabbacin cikin hayyacinki kike,to idan ba'a hayyacinki kike ba gwara ki koma daidai,dukka tatsuniyar da kika lissafa dai dai take da dawowar matacce duniya,a yanzu bilkisu ya muku nisa,hakanan ta tsere muku,kwatankwacin yadda sama ta yiwa qasa nisan taraza mai tarin yawa"

"Koda ace xaki hada dukkan abinda kika mallaka keda ahalinki kaffffff......baku da abin maida bilkisu cikinku saboda girma ko martabar wannan abun,mu MUTUNCI muka zaba,MARTABARMU tafi gaban komai,hakanan KIMARMU babu wani abu da za'a mata farashi ko a daidaita ta dashi,KUDI ba shine arziqi ba,DUKIYA ba itace wadatar zuci ba,hakanan ƘYALE ƘYALEN RAYUWA ba shine samun nutsuwa da kwanciyar hankali na,saboda haka shawara guda daya xan baki.....sawunki a likkafa ki fita salin alin ki koma inda kika fito,ke da dukka wani tarkace naki da kike masa kallon arziqi ko kuma dukiya,koda sawun tayar motocinku bana buqatar tozali dasu bayan gushewarku bare wani abu daban".



      Mamaki mai dimbin yawa,al'ajabi data dinga jinsa kamar a mafarki su suka dinga mamayarta,a iya tarihin rayuwarta,babu wani wanda ya yaba tsayawa haka ya gasa mata maga ganu makamantan wannan,ta tashi tsahon rayuwarta ana mata biyayya,ta tashi tsayin rayuwarta ana girmamata,ta tashi tsahon rayuwarta ana kiyaye dokokinta da bacin ranta,amma yau sai ga wata halitta tana gaya mata magangun da bata taba jinsu da kunnenta a kanta ba tsayin rayuwar tata,cike da zallar mamaki tace

"Kinsan me kike fada kuwa?,shin kin riqe kuqa dawa kike magana?" Murmushin takaici anty zuhriyya ta saki,kana ta tako dab da fulanin ta tsaya a gabanta

"Kinci sa'a ban riqe sunarki ba,amma dai nasan cewa ina magana ne da wata uwa kuma mata ga sarkin qasata,mace mai yawan dagawa alfahari da kuma zallar zalunci danne haqqin marayu da rashin sanin darajar dan adam.....ki fitamin a gida tun labarin zuwanki baikai kunnen sarki abdallah mu'az ba,tun ban wargaza shirinki da yayi saura ba" gaba daya ta gama daureta da jijiyoyin jikinta,siffofin data siffantata dasu sai suka tsaya mata a rai,koda yaushe jama'arta kallon mai kyauta tausayi haqqin na qasa da ita suke mata,amma yau sai gashi an siffantata da siffofi mafiya qyamata a awajenta.



      "Ummi....ni wannan nakeso anty najwa yau ta sakamin" 

"Nima wannan ummi don Allah...amma taqi wai saidai idan mami ta dawo" muryoyin amatu da abdurrahman da suka fito a guje a jere riqe da kayan a hannunsu ta karade falon kowa na saurin nunawa anty zuhriyya.



         Cak idanunta suka sauka kan fuskokin da suka kusa sanyata shidewa,fuskoki guda biyu masu kama ta sak da sak da fuskar abdul'azeez dinta,ta wani sashen kuma tata fuskar take hange jikin tasun,sai take ganin kamar mafarki kamar almara,don haka ta soma matsawa gaba kadan don tagani abinda idanunta ke gane mata da gaske ne

"Kul!ahir dinki!" Ta tsinci muryar anty zuhriyya kamar mai bata umarni tana fadi

"Karki soma kusantar inda suke.....kamar yadda kika koresu tun suna gudan jini....,sun koru koruwa ta har abada,sun barranta daga kasancewa jininki,ina fata zaki hanzarta fita,don bamu buqatar gama nunfashinmu da naki" daga haka ta qarasa ta kama hannayensu zuwa ciki,suna waiwayen fulani tare da tunanin wacece ita?.



       Wani irin gumi ne ya yanko mata,qafafunta taji sun matuqar sanyi kamar ba zasu iya daukar gangar jikinta ba,su waye wadan nan yaran masu tsananin kama da abdul'azeez

"Jikoki,yayan bilkisu da abdul'azeez" wani sashe na zuciyarta ya bata amsar tambayarta,mummunar faduwar gaba ga ziyarceta,tare da wani gumin da yafi na dazu dumi da jiqa sassan jiki,kada dai ace sune cikin data kore samuwarshi?,kada dai ace da gaskene,da gaskene abinda suka fadi,a sanda ta hana azeez ya mata bayani,a sanda ta kasa tsaiwa ta saurareshi?.



       Wani irin mugun sarawa kanta yake,a matuqar salube jikinta taja qafafunta da qyar ta fice,tana jin sanda suka take mata baya suna binta da kirari harta isa bakin motar,ganin batace a sauke kayan ba ya sanya ba wanda yayi maganarsu,aka tada dukka motocin suka fice daga gidan.



      Cikin motar riqe take da kanta,babu abinda ke mata kaikawo sai magangun anty zuhriyya,daga qarshe kuma fuskokin yaran su mata kutse cikin tunanin nata,gaba daya kwanyarta ta burkice,tana da buqatar qarin bayani,don haka ta shaidawa kubra,ta gayawa driver sassan yarima azeez zasu wuce kai tsaye,a kuma bincika a tabbatar mata yana nan kafin su isa din.



        Har wani huci anty zuhriyya takeyi ita kadai,ranta a bace yake,wato yadda malam bilya ya zubda musu qima akan kudi har yanzu da wannan take kallonsu?,koda yake ko yanzun alhmdlh,ta fadi da yawa daga cikin abinda ke mata kaikawo a qirjinta,ko a yanzun ta rage wani nauyi da radadin.



      Sam batayi niyyar shaidawa bilkisu ba,abbaa kawai tayi niyyar gayawa,don kada yaga jinkirin komawar bilkisu dakinta,don ta tabbatat ta gayawa bilkisu abinda ya faru za'a samu hutsancewarta ne kan komawar,ita kuma tafiso ta koma din,ko don yadda yarima yake binta,ta koma taga qarshen iko da iyawar aisha fulani!.



         A hankali tayi sallama falon da yake mallakin mahaifin nata,ya daga kai yana amsa mata lokacin da yake shafawa qafafunsa man zafi,wadanda a yanzu kuma kusan suner rabin matsalarsa,don ko barcin kirki sai sunso suke barinsa yayi.



      Murmushi dauke a fuskarsa yake maraba da bilkisun,kai bakace shine wannan malam bilya din ba,wanda a baya bai damu da kuka ko dariyarta ba.



       Itama fuskarta dauke da murmushi ta qaraso cikin dakin,ta aje jakarta cikin sauri tana karbar kwalban man tana cewa

"Baba bari na samu ladan nima,naga hannunka bai kaiwa wani wajen" ta fada tana xama gabanshi ta soma shafa masa

"To ya zanyi,ita yanxu kaltume kafin ma ta samu damar zuwa ta shafamin na gaji da jira,hidima sun mata yawa,barin yanxun da take ita kadai" cikin salo tsokana bilkisun tace

"To kodai bazawarar da na gano a bayan layinmu xanwa magana?" Daquwa ya watsa mata

"Uwariyo....yauni na xama kakanki maigado?,ai ni yanzu mace dayace a duniya inda tana nan xan iya zama da ita,kuma nake marmarin zama da ita,nakejin inama zan ganta,saidai ta yimin nisan da babu damar sake haduwa har sai na cimmata,maimunatu,mace ta gari da banga irinta ba kaf rayuwata,salihar mace da nake yaqinin biyayyar miji zata sadata da aljanna in sha Allahu,ina miki fata maigado,duk da kin debi da yawa daga cikin halayenta,amma ina miki fatan biyayyar miji da haquri koda kwatankwacin na maimunatu ne" ya tuna da mahifiyarta,kuma sosai abun ya taba ranta,saita sadda kai qasa,maganar da yayi kamar yasan lamarin dake tafe da ita.



       "Kamar akwai magana a bakinki mai gado" ya fada yana dubanta,shuru tayi na wasu sakanni sannan tace

"Kayi haquri baba,nayi wani hukunci ne ba tare da na baka dama ko naji ta bakinka ba" bata boye masa dukkan yadda sukayi da maimartaba ba ta shaida masa,murmushi ya saki,ya tabbatar batasan saida ya soma ganinsa ba kafin ita

"Baki kuskure ba maigado,abinda kikayin shine dai dai,kuma yanzun dukkanmu bamu da wani sauran hukunci a kanki,dukan hukunci naki ne.....duk yadda zan soki bilkisu kona kare miki haqqi ko martabarki bazaikai naso ganinki a dakinki ba,cikin martaba da rufin asirin aure,saidai idan harke din hakan bai miki ba" shuru tayi tana nazari.



      Muryar mahaifin nata ta katseta,magana yake mata cikin sanyin murya da lalama,gami da nasiha da kuma sake neman afuwarta kan abinda ya aikata mata.



       Ta jima a wajen shi,har zuwa sanda lokacin da ya tabbatar da cewa ta nutsu a xuciyarta sannan ya rabu da ita ta shiga cikin gidan wajen 'yan uwanta



    A ladabce sunusi sarkin sassan yarime ke amsawa fulani ke amsa mata cewa yariman yana ciki,yanason mata bayanin cewa kwanakin duka da suka biyo baya suma basuga wulgi ko duriyarsa ba,amma basu samu damar hakan ba harta wuce zuwa ciki.



      A mamakance take bin ko ina na falukanshi da kallo,babu wata alama dake nuna mata cewa yana nan din,dukkan alamu sun nuna cewa kamar an dauki wasu kwanaki ba'ayi amfani da bangaren nasa ma gaba daya ba,ko wanne qwan lantarki na a kashe,ba abinda keyi sai ac da keta fidda uban sanyi,tanayi tana kashe wasu,wasu kuma tana rabuwa dasu,cike zuciyarta fal da mamaki,ta tsammaci ma bai qasar,donko sanda sunusi yace mata yana nan tayi mamakin jin hakan.



      Bedroom na qarshe tayi nasarar samu a bude,an kara qofarshi,ta tura da sallama a bakinta ta shiga,idanunta na saman gadon dake nuna akwai mutum kwance.



      Can qasa taji anyi magana,bisa dukkan alamu amsa sallamar akayi

"Abdul'azeez" ta kirayi sunanshi tana tsaye daga gefe,yadan motsa kadan,sannan bayan shudewar minti guda ya yaye bargon daya rufa a hankali ya miqe ya zauna,bayan ya jingina bayanshi da makarin gadon.



     Cikin tashin hankali take kallonshi,kamar ba azeez dinta ba,gaba daya ya feÉ—e,hakanan ya rame ya zabge,fuskarshi har ta soma tara gashi wanda batasanshi dashi ba,cikin hanzari ta qarasa gefan gadon a rude tana furta

"Ya salamu ya Allah,me ya sameka?" Tana kallon yadda qirjinsa ke dagawa da kuma fitar numfashinsa.



      Idanunsa a kulle,shi kadai yasan ya yakejin jikinsa yace

"Banajin dadi ne"

"Bakajin dadi ko baka da lafiya kwata kwata abdul'azeez!" Ta fada a dan zafafe sannan ta sake cewa

"Tun yaushe ne baka da lafiyar amma babu wanda ka shaidawa?,kazo ka kwata ka kulle kanka kai kadai?,so kake ka mutu?" Ta sake fada cikin fada

"Qaramin yarone kai abdul'azeez?" Ta kuma tambayarsa.



     Kasa amsa mata yayi saboda wani radadi da yakeji,ta fuskanci hakan,don haka hannunta na rawa ta ciro wayarta ta soma laluben wata lamba ta kira,umarni take badawa kan maza maza a fidda mota cikin sirri xa'a fita da yarima zuwa a sibiti,ta gama wayar ta kashe,saita rasa me zatayi banda sannu da take masa,ranta gaba daya a jagule kuma a tashe,meya sameshi haka amma bata da masaniya,Allah ne yasan kwanaki nawa yayi a haka,wannan matsalar gaba daya ta shiga rayuwarta,ta canzata,ta hanata aiwatar da komai yadda ta saba,ta zuba mishi idanu tana kallon yadda yake kokawa da numfashinsa.



       Safwa ta fado mata a rai,haushi takaicinta ita da mahaifiyarta ya qarar mata a rai,ta zabawa azeez safwa ne saboda ya samu gata da kulawa irin wadda safwan taga ana bata a gidansu,ta zabeta ne domin ta zame masa macen aljanna,macen da zata zamar masa nutsuwa da hutu,sai kuma gashi tunda akayi auren ba abinda aka tsinta a zaman nasu,hakanan babu abinda xa'a dorar.



      Cikin mitina qalilan aka fita da azeez din zuwa babban asibitin kudi kuma mallakin likitan gidan,tunda ta gaya masa bata yarda a dubashi ko a kwantar dashi cikin asibitin gidan ba,don ta tabbatar dukkan wadanda suke musu bita da qulli,da kuma binsu da sharri idanuwansu na kansu,don haka ta gwammace ya xauna a sibitin likitan,cikin dakuna da aka tanada na musamman mafiya tsada a asibitin.



       Taso shaidawa maimartaba kafin tafiyarsu,to amma tasan cewa yanzun yana zaman fada ne,ba lallai ta samu ganinsa ba,don haka ta yanke tafiya ta shaida masa daga baya,don gaba daya hankalinta ba'a kwance yake ba.



       Yanayin yadda yaga jikin yariman ya sanya aka fara bashi taimakon gaggawa,daga qarshe suka qara masa da oxcygyn saboda yadda numfashin ya soma masa wahala.



       Cikin mamaki likitan ke tambayar fulani meke damun yariman?,a iyaka binciken da sukayi basuga wani ciwo ba,illa damuwa data masa yawa,da kuma yawan tunani daya sanyawa ranshi,wanda hakan ke neman yin barazana ga lafiyar zuciyarsa.



       Cike da mamaki take kada kai

"Ban sani ba likita,bansan me yasaka har haka cikin zuciyarsa ba"

"Nina sani" afnan wadda ta biyosu asibitin daga baya ta fada,waiwayowa fulani tayi tana kallonta cikin mamaki,kanta tsaye ta soma magana

"Bilkisu,bilkisu ce a ranshi,ita ya saka cikin zuciyarsa,itace kuma silar ciwonsa da samuwar sauqinsa" daga haka ta miqe abinta ta soma takawa zata fice,da fulanin da likitan da baisan tushen maganar ba gaba daya suka bita da kallo harta fice daga office din

"Anyway....koma meye damuwarsa ya kamata a kawo qarshenta indai anason ya samu lafiyar zuciyarsa" maganar likitan data dawo da ita hayyacinta kenan.



       Ita kadai a dakin da aka kwantar dashi take kai kawo tana tuna maganar afnan cikin qwaqwalwarta

"Bilkisu,bilkisu?" Ta maimaita sunan a hankali,sannan ta daga kanta ta dubi yadda yake kwance yana bacci da taimakon iskar oxcygyn.



        Tunda take dashi bazata iya tuna sanda ya kwanya ciwo ba har haka,ace har gaon asibiti,mutum ne shi mai jumurin ciwo kowanne iri ne,yakan yi harkokinsa alhalin baida cikakkiyar lafiya,a haka zaiyi harkokinsa harya gama ciwo na cinsa a tsaitsaye ya kuma warke abunsa.



       Amma da gaske bilkisun ce?,indai kuwa ita dince kamar yadda afnan ta fada bai haqura ba kenan?,idan kuwa bai haqura ba shin akwai shekaru ko wasu abubuwa da zasu zo su sanyashi haqurar?,idan ciwon nan ya zama ajalinsa fa?,qatotuwar tambayar data rufto kwanyarta kenan,ta sanya jikinta ya soma rawa,ba shiri ta samu sit ta zauna tana kiran sunan Allah,sai taji a jikinta kamar zata rasa yariman ne,sai taji kamar lokacin rabuwarsu ne yazo,cikin sauri da rawar jiki ta jawo jakarta,ta fidda wayarta ta lalubi lambar mai martaba.



       A dake ya amsa sallamarta kamar yadda yake mata a wadannan kwanakin,cikin sanyin jiki da sanyin murya tace

"Saqona bai iske ba halan Allah ya taimakeka"

"Ya iskeni mana,amma me zan muku?,Allah ya bashi lafiya,inajin ke kika zabarma rayuwarsa hakan aiko?,kinga kenan ai babu matsala,saidai nayi fata da addu'ar Allah ya taimaka" daga haka qita ya kashe wayar.



       Cikin mamaki tayi saroro,sai wayar ta sulale daga hannunta,ta saka hannayenya biyu tana rufe bakinta dasu gamida furzar da zazzafar iska,wani abu ya dunqule mata a maqoshi,bata taba zaton rana makamanciyar wannan na zuwa ba tsakaninta dashi,saita miqe da sauri ta isa gaban gadon tana duban fuskarsa data fada,zancan mai martaba na dawo mata

"Haka kika zabarwa rayuwarsa aiko?" Kai ta girgiza ta dora hannu saman kansa tana shafawa a hankali,kamar me neman amsar abinda ya dace tayi.



        Ajiyar zuciya me qarfi mai martaba ya saka,bayan ya kashe wayar gaba daya sai yaji ya kasa nutsuwa,yanajin kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a asibitin,amma dole ya dake ya kanne,harsai fulanin takai kanta da kanta inda yakeson taje din,harsai ta saitawa kanta hanya tukunna

"Allah ya bada lafiya,ya taqaita maka" yayiwa abdul'azeez din addua a fili can qasa yana jingina bayansa da dan gadon hutawar da yake kai,yana jin damuwa sosai cikin ranshi.



        "Lafiya kuwa Allah ya taimakeka?" Ya tsinci sautin adama saman kanshi tana jeho masa tambayar,sam ya manta ya sanyata ta dauko mishi lemon tuffa a falo,sai ya miqa mata hannu yana amsar lemon ba tare daya amsa mata ba.



      Bata haqura ba dai ta zauna daura dashi

"Kowa yaga fuskarka yasan kana cikin damuwa,idan don abinda yarima ga aikata ne saidai muce kayi haquri,kowanne bawa da jarrabarsa,dama ko cikin yaranka sai kaga Allah ya fitar maka da zakka a cikinsu,wani halinsa daban,shi yasa ba jinsi ake roqo ba da nagari,wasu matan sai suzo sufi mazan nagarta.....amfanin Allah ya baka yaran da yawa kenan,idan wani ya bata maka sai wani ya faranta maka aiko?".



       Da mamaki saman fuskarshi ya sauke cup din yana dubanta

"Wani abun na gaya miki yarima yayi?" Sai tadan dirirce kadan

"Au...to ai na zaci abinda ya farune satittikan da suka gabata" bai sake cewa da ita komai.ba ya maida kofin bakinsa,wasu wasi fal ranshi yanata auna maganganu da ayyukan adaman cikin lokuttan nan,yayin da ita kuma tayi tsam da ranta,gefe guda na zuciyarta ya cika fal da haushi da takaici,duk yadda sukaso jin wani abu abun ya faskara,wani sashen kuma yana kwabarta na ta taka a hankali kada kwabarsu tayi ruwa,tunda tafi kowa sanin waye sarki abdallah din.

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 73


*_ina miqa saqon godiya a gareku,haqiqa na yaba da karamcinku,na kuma gode da addu'o'inku,wadanda suka yimin ta private da kuma wadanda sukamin cikin grp,na god sosai,Allah ya qaremu da lafiya,ya kuma rabamu da dukkan abun qi amin summa amin_*

____________________________

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





       Ranar ranta a bace haka anty zuhriyya ta wuni,bilkisu nacan gida batasan meke faruwa ba,don a can ta wuni,koda ta dawo batace da ita komai ba,sai da abbaa ya dawo take shaida masa abinda ya farun.



      Murmushi yayi kawai sannan yace

"Na lura da abubuwa masu yawa,me martaba ya boyewa matarsa komai ne,batasan meke faruwa ba,akwai kuma abinda yakeson aiwatarwa,kada ki saka wannan abun cikin lissafin damuwarki,mu jira lokaci,nasan abinda ya shirya din xai bayyana"

"Kamar me abban najwa?" Ta tambayeshi

"Karki gaggawa,ki jira ki gani" ya fada yana bude foodflask din abincin data aje masa yana duba meta dafa,yayin da ita kuma ta shiga zurfin tunani sosai.


   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Yadda yake jin jiki a lokutan hakan yake samun kulawa daga wajen likitoci,sosai hankalin fulani yake a tashe kamar yadda hankalin me martaba yake,saidai shi ya danne ya kuma boye,bai bari kuma ta gane hakan ba.



       Kamar wata safiya yana zaune dakinsa yana lazumi,saidai gaba daya hankalinsa da tunaninsa yana kan azeez din dake kwance a asibiti.



        Daga bakin qofar mihrabin da yakan zauna yayi sallah da lazumi yaji sallamar afnan,yayi mamaki qwarai jinta a irin wannan lokacin,don bata taba zuwar masa haka ba,sai daya amsa sannan ya bata izinin qarasowa.



      Cikin nutsuwa kuma a ladabce ta samu waje ta zauna,ta gaidashi ya amsa mata cikin kulawa,shiru tayi na wani dan lokaci har sai daya tambayeta sannan ta soma magana cikin sanyi

"Abby....zuwa nayi na roqeka alfarma,don girman Allah kayi haquri,ka yafewa ammi da ya azeez kuskuren da suka aikata ko ince ganganci,ka daure ka shiga lamarin ya azeez,wallahi sosai yakejin jiki a asibiti,ina kuma da yaqinin cewa,inda ace bilkisu na tare dashi bazai shiga wannan yanayin ba" shuru yayi yana dan murmushi na wasu sakanni,sannan ya bude baki a nutse yace

"Haqiqa abinda aisha ta aikata yayi mugun bani mamaki da kuma girgizani,din ban taba kawo mata aikata hakan ba,laifin kuma bana kowa bane face na mahaifiyarkin,na riga dana yafe musu,amma yafiyar ba yana nufin karna dauki mataki akai ba,lamarin azeez na riga dana shigeshi tuntuni,saidai nabar sauran damar hannun yarinyar da aka zalunta,amma su ban basu damar su sani ba,saboda inason su gama horuwa,na baiwa mamarki haske na yadda zata gyara kurenta amma har yanzun bata dau hasken ba bare ta gyara,bani da yadda zanyi,iyakata nayita zama na zuba ido naga randa zata dauki haske,ta kuma dauki matakin gyaran,wanda gyaranta shi kadaine zai qarasa kawo qarshen wadan nan matsalolin" fuskar afnan ta fadada fara'a da kuma haske,cikin zumudi tace

"Kana nufin abby ka dawo ma da ya azeez matarsa?" Kai ya gyada

"Hakane,ban kuma lamunci ki gayawa kowa ba kamar yadda nima ban shaidawa kowa,nayi hakanne kuma bisa wani dalili nawa" kai take gyadawa tana sarawa salo da hikima irin na mahaifinta,tabbas ya cika cikakken adalin shugaba kuma jagora,sai yanzu take sake gane abinda yasa jama'arsa ke masa son so

"Allah ya saka da alkhairi,ya kuma qara girma abbi,amma don Allah kaje kaga ya azeez" murmushi ya kuma saki sosai yana dubanta

"Kin taba ganin an shiga tsakanin hanta da jini,dole zanje,amma sai bayan wani lokaci dana diba"

"Hakanma muna godiya" ta fada tana murmushi.



      Hira suka taba wadda suka dan jima basuyi irinta ba,kana daga bisani sukayi sallama,harta kusa fita daga wajen yakira sunanta

"Karki manta,bance ki gayawa kowa yadda mukayi ba"

"In sha Allahu abbi....amma abbi inason naje naganta anty bilkisun" kai ya gyada

"Babu laifi....ki miqa gaisuwata zuwa gareta" ran afnan fes ta fita daga wajen maimartaba,hakanan hankalinta akwance yake yanzun,tasan na zasu rasa nagartacciyar suruka irin bilkisun ba.



  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



     Cikin zumudi da farinciki take shiryawa,bayan ta samu dan rakiya a sirrance zuwa gidansu bilksun,ta kuma nema rakiyar mama sodangi itama a sirrance,bayan ta shaida mata dukan abinda ke faruwa,wanda hakan ya yima mama sodangi dadi matuqa,kamar ta taka rawa haka ta dinga ji.



       Babu wani jinkiri suka gama shirinsu tsaf,suka kama hanya.



       Dai dai lokacin da bilkisun ke zaune saman wasu kujeru dake farfajiyar gidan,hannunta riqe da wani dan qaram littafi tana dubawa bayan tashin anty zuhriyya yanzun nan zuwa cikin gida.



       Tsiya tayi mata ta kuma yi mata tas kan taqi gado taqi mawanka,duk kayan gyaran data kawo mata sai taqi amfani dasu,tace gyara dole kuwa babu fashi,kodon ta rikita musu yarima,ta kuma sake qular da aisha babarshi,itakam komaima jinsa take kamar a mafarki,hatta da komawar duk data amsa amma jinta take kamar wasan yara.



       Batasan yadda zuciyarta da gangar jikinta suka dauki abun ba,itadai gata nan ne dai kawai ta zubawa sarautar Allah idanu,taga yaya qaddararta zata kaya.



       Karar dage gate yadanja hankalinta,ta daga kai ta kalli motar dake shigowa,sai kuma ta maida taci gaba da karatunta,hakan ya sanya har suka fito bataga su waye ba,sai dataji takun tafiya sannan ta kuma daga kanta.



       Sosai gabanta ya fadi sanda tayi arba da mama sodangi da kuna afnan a tafe,ta miqe tsaye cikin wasu wasi tana kallonsu,mama sodangi bata ganta ba,afnan ce ta hangota,saitayi wajenta da sauri hannaye bude cikin nuna zallar farinciki da kuma hargowa irinta farinciki sanda ta sake tabbatarwa lallai bilkisu classmate dinta ce

"Billy bilya!" Ta ambaceta da sunan da akan kirata dashi wani lokaci.



       Haka kawai saita samu kanta da subucewar murmushi kan fuskarta,itama ta bude hannayen nata dukka tana dariya,har afnan ta qaraso suka rungume junansu,kowanne zuciyarsa na farincikin ganin dan uwansa.



       "Wayyo Allah na,ashe da gaske dai kece,har taraddadi nake kar naxo.na samu ba kedin da nake tunani bane,bilkisu ina kika boye haka?,meye labari?" Da mamakin yadda bakin afnan din ya bude take kallonta,cikin dariya tace

"Mu qarasa ciki mana" saita juya sashen mama sodangi

"Mama....sannu da zuwa" ta furta a hankali,tana tuna wasu abubuwa da suka shude zamanin baya a rayuwarta,kai mama sodangin ta kada

"Bani amsawa,bayan an manta da nine a tsaye" dariya sukayi dukansu kana suka rankaya zuwa cikin gidan.



       Ko daya a cikinsu anty zuhriyya bata gane ba tunda bata sansu ba,iyaka sun gaisa cikin mutunci,tasa najwa ta aje musu abunci da kayan motsa baki ta wuce ta barsu.



        Hira sosai suka daka,tun daga labarin rayuwar makaranta,suns tuna yadda suka rayu,da yadda afnan din ta dinga qwarzabar billy,a nan wajen tace

"Kinsan wani abu?,alokacin fa burgeni kike,kawai so nake ki kulani muyi qawance,ke kuma kin qi,ni kuma inajin haushin na xubda daraja na fara zuwa wajenki,ina tsoron kada ki yarfani girmana ya zube,shi yasa nake miki haka" dariya sosai ta baiwa billy,ta karya wuya tana cewa

"Ni a sannan guguwar data taso rayuwata a gaba tasa bana ganin kowa sai ita,da kuma yadda zanyi na kawar da ita".



     Sun dau lokaci sosai suna hirar,har sai da mama sodangi tace

"Kinga idan abinda ya kawoki dama kenan....ni matsa nayi abinda ya dameni" murmushi afnan tayi sannan ta tattara dukka hankalinta akan bilkisu

"Biko kashi na biyu muka sake zuwa yifa?" Bilkisu na dubanta ta tambayeta

"Bikon mefa?"

"Matar yayana" ta bata amsa kai tsaye tana dubanta,sai tadan matse fuska kadan sannan tace

"Awwnnn" daga haka kuma tayi shuru,tana tunsnin meya hana mahaifiyarsa sanya baki ne cikin maganar?,bayan itace qashin bayan komai?,sai wadanda bada su akayi ba keta zuwa,lallai ba shakka akwai matsala kuma akwai damuwa kenan.



        "Bilkisu.....a matsayina na uwa ga yarima ba mahaifiya ba,bayan maimartaba nima gani nazo da kaina nema mishi afuwa a wajenki,don a yanxun bashi da ikon iya magana dake,yana gadon asibiti yana jiyya" waiwayowa tayi tana dubansu jin abinda sukace,sai afnan ta dage gira

"Yes...kin kwantar dashi,kuma komai.na iya faruwa da zuciyarsa....kima Allah kiyi haquri anty billy" ta qarashe fada tana hade hannayenta biyu waje daya.



      Murmushin qarfin hali ta saki tana kama hannayen afnan kana ta sauke

"Bari....girman me martaba da darajarsa yafi gaban haka,ya riga ya roqa alfarma kuma na masa,so wannan ya riga da ya wuce"

"Indai da gaske ne to gaskiya ki tattara kayanaki ki tafi jinyar yayana" afnan ta fada tana langabewa cikin nuna alamun tausayi,dariya ce ta qwacewa bilkisun kana ta kada kai

"Bazai yuwu ba afnan,kiyi haquri" kamar zata saki kuka haka tayi,amma dole ta haqura,daga haka akalar hirar ta koma ga mama sodangi,ta soma tambayarta rakiya

"Rakiya ai tana gidan mijinta,yaranta biyu yanzu haka" murmushi ta saka tana mata fatan alkhairi,tare da tuna zaman shekara dayan da sukayi,zama me dadi a tsakaninsu,wanda sam ba zata mance dashi ba.



        Suna tsaka da hirar dirvern gidan ya dawo dasu amatu daga tahfeez,ba afnan ba,hatta da mama sodangi sai data kusa narkewa a wajen saboda tsabar mamaki da wasuwasi,ai kafin kace meye tuni afnan ta isa wajen yaran tun kafin su qaraso ciki ta cafesu,basusan wacece ba,basusan dawan garin ba sai suka hau baza idanu,muryarta na rawa kamar zata saki kuka ta dubi bilkisu tace

"Don girman Allah kice wadan nan twince din ya yarima ne,kice nashine karkice aah" dariya da tausayin xallar soyayyar yaran data gani cikin idanunta ya kamata,murya can qasa ra furta

"Nakune" qatuwar ajiyar zuciya mama sodangi ta saki,ashe itama abinda takeson ji kenan,sai kuma dukka suka tattara duk wani attention nasu kan yaran.



      Tun yaran suna baza idanu suna dari dari sai gasu sun sake,tana sake nanata musu ita din wace,kafin wani lokaci kuwa suka riqe radam a kansu,qarshe sai gasu suna qyaqyata dariya tare tana basu labarai ita da mama sodangi.



      Ganin yaran ya hanasu tafiya da wuri har kusan sallar isha'i,koda suka tashi tafiya dinma kafewa afnan tayi da magiyar don Allah bilkisun ta bata su aro koda na iya yaune,gobe ta dawo mata dasu

"Kiyi haquri,bazai yuwu ba" tace da ita,hakanan jikinta a sanyaye ta saukesu suka wuce,bayan ta cika wayatta da hotunansu kamar ba gobe.



      Cikin kwanaki biyu rak ta wanko hotunan,ta kuma cika sassan fulani dasu waje waje,wanda da ace wajene da kowa ke iya shiga ba shakka da.labari ya cika masarautar,randa fulanin ta soma gani ta jima tsaye tana qarewa yaran kallo,tun randa ta dora idanunta a kansu suka tsaye mata cikin xuciya da ruhi,taji wani abu mai kama da soyayya da qauna na ratsa zuciyarta,kwatankwacin yadda takeson mahaifin yaran,abu daya ya hanata kasa magana a kansu,duk da yadda kullum take kwana ta tashi dasu a ranta.



      Batasan afnan na bayanya ba sai data yi gyaran murya,sai kawai tayi gaba ba tare data waiwayo ba,kamar ba kallon hotunan nasu ta tsaya yi ba,dariya ta kama afnan

"Uhmmm,ammi kenan,idanma zaki bi hanya tun wuri gwara kibi,saina taya abbi wannan yaqin wallahi".



¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Ko ina na jikinta rawa yake cikin tashin hankalin da bata taba riskar kanta a ciki ba,ba ita ba....dukkan wanda ke wajen hankalinsa a tashe yake,wasu daga ciki ma sun soma kuka,saboda yanayin da aka fita da yarima azeez.



       Lambar mai martaba ta kira,tayi sa'a yana available,bugu uku ya daga

"Idan ma ba zaka zo ka ganshi ba,to na roqeka ka yafe masa,saboda yanayin daya shiga din,bamu da tabbacin samuwar ruhinsa......duk da cewa nice silar komai,dukka laifin yana wuyana a qa'ida....amma ina roqar masa afuwarka" kalamanta sunyi masifar daga mishi hankali,don haka bai iya maida mata amsa ba ya katse kiran,sannan ya bada umarni cikin gaggawa aka tada motoci ya nufi asibitin.



       Fulani adama da fitar ta kasance kan idanunta saita jinjina kai,tana baiwa kamal umarnin bin ayarin motocin me martaba,yaga inda suka nufa,don sama bata yarda da yanayinsa a 'yan lokuttan nan ba,ta sakawa sauyawar mood dinshi ayar tambaya.



       Yanayin daya samesu a ciki ya tabashi shima,tsahon awa guda kafin su maidoshi dakin,bisa qwararan dokikin banda hayaniya sam,hakan ya sanya maimartaba ya baiwa kowa umarnin komawa gida,abar mai jiyyar shi kadai,tunda akwai masu kula dashi,sai a sannan yake tambayar ina safwa?,ita ya kamata ta zauna dashi,tsananin bacin rai ya hana fulani bashi amsa,inda ace tana da iko ba shakka yau da ita da kanta zata sallami yarinyar,saboda ko kusa bata ga rana ko amfanin auren nasu ba.



       Duk yadda yaso zuwa asibitin washegari bai samu dama ba,saboda baqin da masarautar tasu sukayi daga qasar jigawa,saidai ya samu bayanin cewa jikin nasa da sauqi sosai,don harma ya dan farka,hakan ya dan sake saka masa kwanciyar hankali.



      Washegari ana idar da sallar asuba,gari yana yin shaa ya shirya zuwa sake dubashi ba tare da wasu mutane 'yan rakiya masu yawa ba.



        Lokacin da ya tura qofar dakin saiya sameshi saman abun sallah,ya jingina bayanshi da bango,ya fada sosai ya qara haske,da alamar gyangyadi ne ya debeshi saboda tasirin allurai da ruwan da aketa saka mishi,wanda ciki akwai na bacci.



       Saida ya tsaya ya gama qare masa kallo sannan ya saki murmushi,babu shakka ba'a cika baki a soyayya,hakanan babu wanda ya isa ya bugu qirji yace yafi qarfin soyayya,ko yace shidin jarumi ne a wannan fagen,ko wayeshi kuwa,bai taba ganin wani abu daya karya abdul'azeez din,ya cire masa dukkan wata jarumata tashi da qwarin gwiwa ba irin wannan lamarin,saiya ci gaba da takawa a hankali har yakai bakin daddumar ya xare takalmansa,sannan ya zauna a gabansa,kasancewar daddumar tana da yalwa,ya langwashe qafafunsa yana ci gaba da kallonshi,sannan a hankali ya saka hannunshi ya bugi cinyarsa........

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 74

*_kunsan me ake kira da ƘURE ADAKA?_*


_To ba kowa bane illa MAAB LUXURY HOME_


*_Wadanda suke a shirye kuma kullum a tafe wajen kawo muku ingantattun kayan qawata gida masu inganci da kuma kyan gaske_*


*idan matsalarki inda zaki samu kaya 'yan yayi masu inganci to kakarki ta yanke saqa,koda kuwa saqar qarfe ce,saboda zuwan MAAB LUXURY HOME*

_SUN TANADAR MUKU KAYA KAMAR HAKA_

_dinner set_

_serving trays_

_cutlery set_

_jugs_

_foodflask_

_thermoflask_

 

*kai dama dukkan wani nau'in kaya na qawata gida da maidashi aljannar duniya*

*_hausawa sukace gani ya kori ji,maza garzaya wadan nan shafukan namu don ganewa idanunku irin kayayyakinmu_*


*instagram* https://instagram.com/maabluxuryhome?utm_medium=copy_link


*facebook*:maab luxury home

*website* 

http://maabluxury.com


_Ko ka tuntubesu ta lambar waya kamar haka_

+491521 4642007


*suna nan a garin kano,maza taho ayi daku*ðŸƒðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸Æ’ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸

_____________________________

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070




        "Tashi rago kawai" kalmar daya fada kenan,firgigit azeez ya bude idanunsa yana ambaton sunan Allah,saiya maida nutsuwarsa jikinsa cikin mamaki ganin me martaba zaune a gabanshi,kanshi ya sadda cikin jin nauyi,sannan a hankali cikin muryar marasa lafiya yace

"Barka da asuba" maimakon ya amsa mishi sai yace

"Ban taba tsammanin cewa kai din rago bane sai yanzu,shine ka zauna akan mace zaka mutu saboda tsabar ragwantaka?" Shuru azeez din yayi qirjinsa na bugawa,shi kadai yasan me yakeji,yana da tabbacin ba zasu gane ba,yayin da me martaba yaci gaba da kallonshi yana murmushi sannan ya kuma cewa

"Dago kanka ka kalleni"yayi maganar yana nade hannun rigar dake jikinsa me zubin alkyabba,dagowar yayi kamar yadda me martaba yace yana dubanshi

"ka ganni nan?" Ya fada yana nuna yatsarsa

"Ba'a tabani kasani akan mace ba,idan na qudirta a raina saina sameki saina samu.....ka tambayi mamarka....itace babbar shaida,mutum nawa na kasa a mali,na rabota dacan na kawota nan,amma kai mace daya ka kasa controlling tunaninta da soyayyarta zuwa kanka....koda yake,Allah baya goyon bayan zalunci" ya fada yana maida hannun rigarsa,wanda ya nadeta ne dama don ya nuna mishi qwanjinsa sanda yake masa misali da qarfin da yake dashi na qwatar soyayya.



       "Tunda kai ka gaza yin komai mu munyi maka.....na maka bikon matarka amm...." Baiko jira yaji qarshen maganar ba gaba daya ya kama hannunshi ya riqe gam,bakinsa yana motsi ba tare da ya iya furta komai ba,dubanshi me martaba yake shima yana dariya

"Sakarmin hannu mana,yada saurin murna haka bakaji qarshen zancan ba" kunya ta kamashi,ya zame hannunsa daga cikin na me martaba

"Zata koma aduk sanda ta gamsu a karan kanta,wanda ni na bata wannan damar,saboda kada shiga haqqin nata yayi yawa" saiya sauya yanayin fuskarsa sannan ya koma sarki abdallahnsa sosai

"Abdul'azeez,abinda kuka shirya kuka aiwatar kaida mahaifiyarka yayi.masifar batamin rai da bani mamaki,ya nuna cewa bakusan daraja da qimata ba,hakanan baku daukeni a bakin komai ba,duk da cewa laifin mahaifiyarka shine kaso casa'in cikin dari,kai kuma kana da goma...."



        "Abdul'azeez,nine uba kuma mahaifi a gareka,nine wanda nafi cancanta tun asali ka soma shaidawa cewa kana da buqatar aure,bawai mahaifiyarka kadai ba,dukkan wata dama ta sakin fuska da yadda zamu shaqu da juna na baku ita,sabida ire iren wadan nan abubuwan na rayuwa,bare kace babu fuskar da zaka shaidamin hakan,inda na godewa Allah ka shaida matan itama,baka shiga baragurbin rayuwa da matan bariki ba,irin yadda wasu daga cikin matasa da suka samu dama irin taku suke shiga ba,na godewa Allah daya zama kun hadune ta halastacciyar hanya,hakanan jikokina sun fito ya halastacciyar hanya"



"Abu na biyu shine,babu biyayya ga abun halitta wajen sabawa mahalicci,a duk sanda ka fuskanci mahaifiyarka takauce hanya,kayi qoqarin dawo da ita hanya ta mu'amala me kyau,da kuma tausasa lafazi,idan hakan bata samu ba kuma,itama tana dana gaba da ita,kayi qoqarin shaida musu saboda kauda ita daga fadawa halaka,wanda kai baka aikata hakan ba,sai kaci gaba da yi mata biyayya ba tare da kayi yunqurin shaida min ba"


"Na uku baka duba dukkan nauyin haqqin dan adam dake wuyanka ba,ka iya sakar musu yarinya don kawai mahaifiyarka ta baka umarni,wannan shine kuskure na qarshe mafi girma wanda ayanzu kaga ishara,saidai ka roqi Allah wannan jiyyar dakayi ya zame maka kaffarar zunubin dake tsakaninka da mahaliccinka,ita kuma yarinyar kayi qoqarin neman yafiya da afuwarta itama,ka kuma riqeta da kyau riqon tsauri,ka gyara duk wata baraka data taba giftawa tsakaninku,Allah ya gani,ni nayi iya nawa yin,sauran gyaran kuma ya rage naka".



      Kanshi a qas,cike da gamsuwa da kuma nadama yakewa mai martaba godiya,qauna da qimar mahaifin nashi na sake qaruwa cikin ranshi,bai wani jima sosai ba yayi mishi sallama ya tafi.



      Sosai ya shiga zurfin tunani bayan fitar me martaba,can qasan ranshi yanajin wani dadi da farinciki na musamman yana ratsashi,ji yake kaman ya fice daga asibitin a yanxu ya tafi ganinta,saidai kuma babu wannan damar,saboda wani plan da ya tsara ma ranshi,wanda itace ha ya mafi sauqi da zata kawo masa bilkisun har dakin asibitin ba tare da anja wasu dogayen kwanaki ba.



      Daga dakin da aka kwantar da azeez din likitan dake ganin azeez din me martaba ya nemi gani,yaci sa's kuma aikij kwana yayi,kuma baikai ga tafiya ba.



     Maganganu sukayi dashi har na wajen mintun ashirin,kana daga bisani yabar asibitin.



      Cikin 'yan rakiyarta hadimai ta shigo cikin asibitin,wanda tun kafin takai ga shiga dakin da azeez din ke kwance likitan ya nemi ganinta idan ta iso,bata jira ya isketa ba,ita ta iskeshi a office dinsa,don dama cike take da fargaba da taraddi kan bayanan da zataji kan sakamakon da gwaje gwajen azeez din.



       "Ranki ya dade kamar dai yadda na taba gaya miki ne a baya,babu abinda ke shirin illatar masa da zuciya ta hanyar gagarumin hawan jini irin damuwa,damuwace a zuciyarsa wadda da alama ba tun yau ba yake fama da ita,wanda idan har ba'a dauki matakin yaye masa ko kawo masa qarshenta ba yaci gaba da kasancewa a halin da yake ciki nan da kowanne lokaci za'a iya rasashi,naso boye muku amma naga babu amfanin hakan,na riga dana shaidawa me martaba ma wannan bayanin,saboda haka inaga abinda yafi kawai shine,ayi qoqarin ganin an kauda masa da wannan damuwar,idan ba haka ba komai na iya faruwa"



       Duk da acn dake karade office din,amma hakan bai hana gumi yankowa fulanin ba,ta kasa furta komai illa

"Na gode dr" daga haka ta miqe ta fice daga office din.



       Duk wanda suka taho tare yasan cewa ta sake ficewa daga hayyacinta,dakin da azeez ke kwance ta tura ta shiga,idanunta a kanshi,saitaganshi kwance miqe kamar yadda ta barshi a jiya,babu wani alamun sauyi,kada dai ace tun jiyan ba wani ci gaba da aka samu?"tayiwa kanta wannan tambayar,sai taji hankalinta ya tashi,ta qarasa bakin gadon ta tsura mishi idanu,ramar da yayi ta bayyana muraran,saita dora hannunta saman sumarshi a hankali.



       Karon farko taji wani abu mai kama da tausayi da nadama suna shigarta,abinda ta aikata din ya dinga dawo mata tiryan tiryan,ya akayi?,garin yaya ta fice haka a hayyancinta,idan hadin auren da rabasun da tayi tana sane kuma akwai.manufa daga baya hujjojin da suka dinga bayyana kansu meya hanata karbesu?,azeez ne fa,yaron daya fita daban cikin 'ya'yanta,mutumin da tun daga quruciya zuwa girma bata bashi umarni ya tsallake ba,baisan cewa a'ah ba kan dukkan wani umarni nata ba,komai tace masa yakan ce to,komai tsananinsa ko rashin dacewarsa da nasa ra'ayin,me yasa zata katase masa farinciki cikin rayuwarsa?,me yasa ba zataso abinda yakeso ba?.




      Saita tuna da twince dinsa,idan itace aka rabata dashi da afnan yaya zataji a ranta?,ta tuna dukkan wata gwagwarmaya da tayi cikin masarautar kaisa,wanda dukkanta ta yita ne saboda kare yaranta,saboda ta rayu dasu,amma shi me yasa ta zama silar rabuwarsu tsahon shekaru,amma duk da haka bai fasa mata biyayya ba,bai taba fasa kallonta a matsayin uwa ba,bai fasa mata biyayya ba,tabbas ya cika da na halas wanda ya cancanci samun aljanna,indai hakane....indai yayi dukka komai saboda ita itama ya kamata tayi komai saboda shi,idan tace komai din ciki harda dawo masa da bilkisun dama yaranshi cikin rayuwarsa gaba daya ba tare da jinkiri ba.



       Tana kaiwa qarshen tunanin ta sauke hannunta daga kanshi,sannan ta juya da hanzari ta doshi qofar fita,abdul'azeez da tun tsayin tsaiwarta saman kanshi yana jinta,saiya bude idonsa guda daya a hankali ya bita da kallo,yana jin qamshin nasara cikin ranshi.



       Ta bude handle din qofar ta jata baya ta zura jikinta zata fita suka kusa gware,safwa ce a gaba cikin yanayi na rudewa,mahaifiyarta na biye da ita,sai mai aikinsu wadda babba ce biye dasu da kwanduna na alfarma riqe a hannunta.



       Kallo daya zaka yima fulanin kasan qasaitar ta motsa,san fuskarta babu wannan annurin da yanayin da takan tarbesu dashi,a tsaitsaye daga nan bakin qofar sukayi magana da bata wuce biyu ba da mmn safwa tayi gaba,tana kiran sunayen hadimanta da zata fita dasu din.



      Yau din tun safe da suka tashi bilkisu ta hada kan matan zuwa kitso da gyaran gashi,anty zuhriyya kuma ta dauki samarin don su rakata siyayya kasuwa,saboda shiryen shiryen daukan azumin watan ramadan da akeyi a sati me zuwa,hakan ya sanya gidan babu kowa sai mai gadi da kuma me aikin anty zuhriyyar.



       Tafiyar mintuna talatin fulani aisha ta yima gidan anty zuhriyyar tsinke,tun daga bakin gate me gadi ya gaya mata cikin girmamawa basunan saboda ya shaida wacece ita,amma saita zabi zama ta jira dawowarsu koda awanni nawa zasuyi.



      A farfajiyar gidan ta umarci dukka hadiman nata su zauna su jirata,yayin data shiga gidan ita kadai.



      Mamaki sosai ya kama mai aikin anty zuhriyya ganin wacece baquwar tasu,don wancan karan da tazo ita taje ganin gida batasan da zuwan nata ba,fuskar fulani aishan ba boyayya bace musamman ga ma'abota kallon tv ko yawaita karatun jarida,kasancewar tana da qungiyoyin tallafawa gajiyayyu da marasa qarfi,hakanan tana yawan bada tallafi a duk wani sha'ani da xai taso cikin qasar kaisa,hakan yasanya mai aikin yi mata tarba me kyau bayan ta shaida mata basu nan,amma sun jima da fitama,sunce kuma ba zasu dade ba,tace babu damuwa,zata jirayi dawowarsu.



       Wayar dake cikin kitchen ta dauka ta kira anty zuhriyya don shaida mata tayi baquwa

"Wacece?" Ta tambayeta,cikin zumudi ta shaida mata

"Matar me martaba ce wallahi ummi"

"Matar me martaba?" Ta ambata cikin mamaki,tare da tunanin meye kuma ya sake dawowa da ita

"Eh wallahi,harma ta zauna tana jiran dawowarku". Itama anty zuhriyyan sai abun ya bata mamaki ya kuma daure mata kai,to meke tafe da ita?,koma meye batason haduwarsu da bilkisu,don hakan kamar zai sake tarwatsa duk wata 'yar yarda da nutsuwa dake zuciyar bilkisun,don haka tace

"Ohk,shikenan muna hanya" daga haka ta katse kiran,saita lalubi sabuwar lambar bilkisun kan wayar data sauya.



      Bugu biyu ta daga,tambaya ta soma jefo mata

"Kina ina?" Bata kawo komai a ranta ta amsa.mata

"An gama mana ummi,yanxu muka fito daga wajen,mun hau titi ma" ajiyar zuciya ta sauke,babu yadda zatayi ta maidata,hala yau din ya zama dole ne su hadu shi yasa Allah ya shirya hakan,jin tayi shuru yasa bilkisun cewa

"Lafiya ummi?"

"Babu komai,saikun iso,nima ina hanya" ta kashe wayar ta mayar jaka,saita haqura da sauran abubuwan da bata siya din ba,aka zuba mata sauran siyayyar a mota itama ta dauki hanyar gida.



      A qofar gida me adaidaita ya saukesu bilkisun suka shigo gidan da qafa,amatu na shiga da gudu tana biye da ita tana qwala mata kira tare da matan fadan gudun banza.



      Daidai lokacin da fulanin ke zaune a falon,jin sabbin muryoyi ya sanyata zubawa qofar shigowar ido bayan ta miqe ta sake matsowa tana jiran ganin masu shigowar cikin qaguwa.



       Amatu ce first,don haka tayi caraf ta dauketa,wanda yarinyar bata zaci haka ba,hakan yadan bata tsoro,data kalli fuskarta kuma saita tuna lokacin data taba zuwa gidan,tayi wajensu,anty zuhriyya ta hanata tabasu,hakan ya sake bata tsoro,saita saki wani dan guntun ihu tana zillewa daga hannunta.



       Tunda ta shigo farfajiyar tayi arba dasu jikinta taji sam bai bata ba,tunaninta daya daga ina suke?su waye su?,dan ihun amatun ya sanyata zabura itada najwa zuwa cikin falon gidan cikin gudu gudu sauri sauri.



       Dai dai lokacin da me aikin anty zuhriyya ke dariya tana cewa

"Meye haka biyu?,baki santa ba ko?,ai dafa gareta dama,uwarta tafi ganewa fiye da kowa".



         Cak bilkisun ta tsaya ana kallon kallo tsakaninta da fulani,fulani na qare mata kallo zuciyarta na gaya mata tabbas itace bilkisun,don ta jima da haddace fuskarta a tarin tulin hotunan da aka dinga ruwansu cikin masarauta,yayin da bilkisu zuciyarta ke bugawa da wani irin sauri,idan har dai dai idanunta ke gane mata fulani aisha ce a gabanta,matar me martaba,mahaifiyar yarima azeez,matar da takan ci karo da hotunanta ko ganin fuskarta a akwatunan tv na qasar nan,mai tarin bada tallafi da taimako ga mabuqata,matar da take ga halinta ya saba da ayyukanta,matar da kullum taga ana yabonta mamaki kan cikata,taga zallar rashin sanin wacece ita yasa jama'a ke yabonta,matar data zama silar wanzuwar komai cikin rayuwarta.



       Sallamar anty zuhriyya ta karade falon wanda itama ta fado ne da hanzarinta,a hankali ta waiwaya suka hada idanu da anty xuhriyyan,saita dauke kai a hankali ta soma takawa zuwa hanyar dakinta ba tare data furta wata kalma ba.



      Babu wanda ya tsaidata cikinsu,hakanan ba wanda yace mata komai harta bacewa ganinsu,sai data bace din kana anty zuhriyya ta qaraso zuwa cikin falon,fuskarta a tamke,murya a kausashe ta soma magana

"Me kuma ya sake dawo dake cikin gidan n......"

"Sulhu,sulhu nake nema domin girman Allah da darajar manzonsa" tayi maganar cikin matuqar sanyi tana hade hannayenta biyu waje daya,domin a yanzun ta shirya yin komai don ta daidaita lamura,don ta wanke kanta,don kuma ta maida komai kan muhalli da mixaninsa

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 75

*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





      Duka qarfinta ta tattare ta turashi kana ta tashi daga rungumar da yayi mata tana kyabe fuska da hade rai,dariya ya saka sosai har ya bata mamaki,ta saki baki kawai tana kallonshi

"Ai na zaci baki gama kallon nawa bane shi yasa na riqeki da kyau saboda ki kalleni yadda ranki keso" kunya tadan kamata,saita soma sauka daga gadon,sannan ta durfafi qofa.



       Saidai ina,tun kafin ta qarasa ya rigata,ya tura qofar ya murza key din dake jiki,sannan ya harde hannayensa a qirji ya zuba mata idanu da tsumammun idanunsa,wadanda ciwon da sukayi ya sake sanyawa suka zama wasu irin masu saurin narkar da zukata

"Tunani kike madam zaki fita dakin nan ta sauqi?,inaa na daina wannan saken,tunda kika shigoshi saikin samu ladan aure,kin kuma warkar da zuciyar dake cike da shauqi da qauna...." Yana kaiwa aya ba zato ba tsammani taji an sunkuceta,ta soma qoqarin qwacewa tana cewa ya sauketa amma ina,sai daya direta bakin gado

"Karka sake tabani,kuma da nasan ma ka warke da ban zuwa wlh" da baya da baya ya koma gefan daya gadon dake kallon wanda take kai ya zauna idanunshi a kanta,sai daya zauna ya dage mata gira daya

"Kiyi duk boren da zaki na yarda,kome xakiyi kiyi am ready,amma.ina mai.tabbatar miki baki fita dakin nan sai zuciyata ta warke" idanu ta fiddo

"Me hakane?,kasan dai bani kadai nazo ba"

"Yes,kamar yanda nasan babu me tuhumata game da xamanki nan din,tunda dai matata ce ko?" Shuru kawai tayi,ta fuskanci kome xata fada bazaya yadda ba,amma duk abinsa idan sun tashi tafiya ai za'a nemeta,kuma dole ya barta ta fita.



      Shima shurun saiya masa,ya zuba mata idanu yana qare mata kallo,gami da tuna abubuwa masu yawa a kanta,tun tana mitsitsiyarta shekara sha bakwai,duk da ba wani gani ya mata.mai yawa ba,amma har yanzu hotunan moments din nanan a qwaqwalwarsa.



      Batasan idanunsa tamkar dafi suke a gareta ba sai da kallon da yake jifarta dashi ya soma hanata sukuni,duk inda ta motsa saita dinga jinta a takure,cikin kwarjininsa tana jin ya cika dakin gaba daya,don haka cikin jarumta ba tare data iya duban qwayar idanunsa ba tace

"Ban fiye son kallo bafa gaskiya"

"Sorry ma" ya fada yana sakin wani sihirtaccen murmushi,sai kawai ya zame ya kwanta a gadon daya koma din,yaci gaba da kallonta ta qasan idanuwa,wanda wannan takejinsa har cikin qashinta,kamar yafi na daxun dafi,don haka ta gyara zamanta,ta juyawa sashen da yake baya,amma duk da haka bata fasa jin tasirin kallon ba cikin jikinta.



     Mintina kusan ashirin,kamar babu kowa cikin dakin,qarar wayarta ya karade dakin,ta budeta da sauri tana duba mai kiran,anty zuhriyya ce,saidai kafin takai ga dagawa taji ya amshe wayar,baki ta saki tana binsa da kallo har zuwa sanda ya ansa wayar

"Ku tafi kawai anty,tace zata zauna,tana jin kunyar gaya miki ne" abinda taji yana fada kenan,wanda ya sanyata zaburowa zata karbe wayar tana fadin

"Ba haka nace ba Allah ummi" wanda ta makara,don tuni ya kashe wayar.



       Sai yayi tsam, yana jiran isowarta,wanda bata ankara ba sai sake tsintar kanta tayi a jikinsa,yasa hannayensa gaba daya ya rungumeta cikin jikin nasa yana shaqar daddadan qamshinta da tun daxu ya tafi dashi.



      Cikin kunnenta yake rada mata

"Relax mana.....relax" hakanan taji dukka jikinta ya saki sanda sautin maganar ya shiga kunnenta,saita daina kici kici din da takeyi,a hankali cikin sanyi yaci gaba da magana

"Ba mutum ne ni maison tashin hankali ko fada ba,pls ki taimakeni mu fahimci juna,ki sassauta fushinki da hukuncinki har sai na warke,na miki alqawarin zan dauki duk wani hukunci kome girmansa,na miki alqawari bazan sake tabaki ba tunda bakiso,amma kimin alfarma kiyi.jiyyata,wala'alla daga nan bazan sake rayuwa ba" haka kawai taji jikinta yayi sanyi,bata sake cewa komai ba,hakanan shima bai qara riqetan ba ya saketa,ta koma mazauninta na daxun,saiya sake kunna wayarta dake hannunshi ya soma latsawa yana cewa

"Bari na sake yiwa anty bayani....tunda dazun kince bake kika ce ba" idanunta a kanshi take dubanshi tana mamakin baijin kunya zai iya magana da ita haka kai tsaye?,bata gama mamakin ba muryar anty zuhriyya ya fito ta cikin wayar,saiya miqe ya nufi bakin wondow yana amsa wayar,ta bi bayanshi da kallo,verry giant and gentle prince taji zuciyarta na fada,dukka kamanninsa da abdul sun fito sosai,sai yanzu ta lura hatta yatsun qafa ma iri daya ne.



      Idanunta ta lumshe sanda ya waiwayo manne da wayar a kunnensa,saidai tuni ya ganta tana kallonshi,baice komai ba ya miqa mata wayar,wanda sai daya hada da hannunta kadan sannan ya sakar mata,cikin sauri da yadda tsigar jikinta ta tashi ta kara wayar a kunneta

"Karki damu,kiyi xamanki,lada xaki samu,pls daughter ki saki jikinki,abinda ya faru ya ruga ya faru,kuma a yanxun muna da yaqini da kuma kyautata zaton ya wuce" kasa amsa mata tayi saboda nauyi da kunya,har sai data kashe wayar da kanta.



      Sau uku fulani na aikowa a dubasu amma qememe yana jin knocking yaqi budewa,itama batayi magana ba saidai ta daga kai ta kalleshi alamun tanason a bude din,amma saiya wani lumshe ido kamar baisan me ake ba,yana kwance abinshi saman daya gadon yana qare mata kallo son ranshi shauqinta da begenta gami da wata qqaqqarfar soyayyar da bai taba zaton akwai irinta ba tana ratsa kowacce gaba ta jikinsa.




      Wajen shidda na yammaci fulanin ta tako da kanta tare da likitan da yake dubashin,wanda shima zuwanshi na biyu kenan amma qofar na garqame,hakan ya sanya fulanin zuwa da kanta.



      Mamaki sosai ya kamata sanda ta ganshi ya bude qofar sannan ya koma,sai kawai itama ta maze kaman bata gani ba,yayin da kunya ya hana bilkis sukuni.



       "Toh fa...inaga ya kamata ayi sallama hakanan ai ko?" Likitan ya fada qasa qasa,ta yadda azeez ne kawai zaijishi,gira ya yamutse shima cikin qas da murya yace

"Haba likita...yaushe aka fara bikon bare a gama,da mun koma gida mutane ne zasu damemu" dariya taso kama likitan hakanan ya danne don kada fulani taji.



      A ranar abbaa shima yazo dubashi,tana ji tana gani ya taho mata da madaidaiciyar akwatinta dauke da kaya,ta bata fuska tana kyabe baki,wato ta lura da gaske mutanen nan dai suke,yarima dake daga kwance yana kallon duk abinda ke faruwa,sai hakan yayi masa dadi,yakanji duniyarsa tamkar ta daidaita ne,sabanin daa da yake jinta a hargitse.



      Kwana biyu rak tayi amma gaba daya ya gama narka mata jiki da wata iriyar soyayyarshi ba tare data sani ba,duk wani alqawari da yayi na ya daina tabata ya dade da karyashi,idan ta buda baki zatayi qorafi saiya langabe mata yace aishi patient ne,koda tayi niyyar nesantarsa saiya janyo abinda zai kawo kasuwancinsu,kamar sanyata ta zauna ta bashi abinci a baki,wanke mishi hannu tayashi shaving uban suman daya tara da sauransu,kuma koda a gaban fulani ne baiji kunya,idan bilkisun ta soma masifeshi kuma saiya wani koma mata kalan tausayi,wani sa'ilin fulanu saidai ta dauke kai idan yana tabararshi da baiko jin kunya,kai bakace shine wannan sarkin miskilancin hada gira da uban kwarjini ba,idan kuma taga ba zata iya ba tabar musu dakin,dataga ma ciwon nashi kamar na shaqiyancine saita rage zuwa ta dade,yawanci tafi zuwa daga yammaci zuwa bayan magrib ta koma gida abinta,ita kanta bilkisun ta soma rasa gane ma'anar xamansu a asibitin,don dai itakam bataga wata cuta ba,banda tablet da yakesha,wanda ta tabbata ko a gida ya zauna zaya iya shan abunshi basai cikin cikin asibiti ba,amma haka taja baki tayi shuru,ta zubawa sarautar Allah idanu.



      Tun randa ya amshi wayarta ya hanata ita,yace tayi haquri amma bai bata sai randa ya siya mata wadda yaga dama da hannunshi,haka ta haqura tasa aka laluba mata wasu litattafai a kasuwa da zasu qareta kan fannin data karanta na likitanci,ga anty zuhriyya daga ita har yaran tun ranar da sukazo tare babu wanda ya kuma dawowa.


    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Yau kam tunda ta tashi take cin magani,duk da dama bawai wani fara'arta yake samu ba,saidai yau taci alwashin babu abinda xata yarda yasa ta hada jikinta da nashi,don ta karanci wayo kawai yake mata.



     Ita kadai tasan yanayin da take tsintsar kanta duk yayin da hakan ta faru,duk da cijewa da qaryata kanta da takeyi,sau tari saidai ta shiga bandaki tayita maida numfashi harsai bugun qirjinta ya daidaita,sannan wani lokaci ta daura alwala ta fito,abinda bata sani ba shine,ya jima da karantar yadda moode dinta kan canza a wasu lokutan,yakanci dariyarshi shi kadaine kawai ba tare daya nuna mata ba,amma yanajin dadi sosai har cikin ranshi na yadda salonshi ke aiki.



     Duk wani abu da tasan zaya buqata ta aje mishi kusa dashi,ta gama shirinta tsaf wanda dama nan cikin toilet din dakin take sanyawa muqulli ta shirya,ta yane jikinta da mayafinta mahadin kayan,ta haye kan daya daga cikin cusion din dakin ta nade a kai taja littafinta guda daya tahau karatunta.



     Ta qasan idanu yake qare mata kallo,yau tayi masa kyau sosai fiye da kullum,jajayen lips dinta sunata qyallin lipgloss,saiya lumshe idanunsa kana ya sake budesu a kanta,duk da batasan yana kallonta ba,ya gama karantarta tsaf,saidai a yau din zaiso ace cikin jikinsa ta wuni kacokam gaba daya,yana sheqar wannan daddadan qamshin nata da baya gajiya dashi

"Bilqess" yayi kiranta da wani irin sauti daya ratsa jikinta sosai,saita daga manyan idanunta a hankali ta zubesu cikin nashi tana lumshe ido gami da budesu lokaci guda,alamun ina jinka.



     Lallausan murmushi daya sake bayyana kyanshi ya sake mata yana sake nutsa idanunsa cikin nata

"Uhmm....yau kuma rowar maganar ma akemin?" Ya fada da wani irin salo daya sanyata tilas ta janye idanunta ta maida kan takardar dake gabanta,saboda wani irin kwarjini da nauyi da taji sun mata,ba zata iya ci gaba da kallonshi ba

"Breakfast dina fa?" Ya tambayeta cikin wani taushi

"Na shirya maka komai ai,gasunan kusa dakai" ta fada cikin siririyar muryarta,ya jima yana kallonta,sai yaja break din ba tare daya sake ce mata komai ba ya soma ci,don ya fuskanci a tuburenta take,amma zaya sauko da kayarsa.



     Wunin ranar haka ya dinga takale takalen sakata abubuwan da yasan dole zasu kawo kusancinsu,saidai gaba daya taqi wayon yauta daki karatun,duk sai yakejinsa sukuku babu dadi,baison kanshi tsaye ya isa gareta ne,da tuni aikin gama ya gama,yasani dole yabi komai mataki bayan mataki.



       "Ki taimaka ki wankemin qafata,tayi datti" ya fada yana dan jujjuya qafar kamar gaske,a lokacin tana saman abun sallah,saita daga kai kawai ta dubi qafar da yake maganar tayi dattin,dariyace ma taso kamata,qafar dako qura babu alamunta tattare da ita amma ita ake kirawa datti,tasan cewa kawai neman abun magana ne,kuma ba zata biyeshi ba,don yau lafiyar Allah ta wuni,to haka zataso ta kwana,jin taqi kulashi sai yace

"Shikenan,idan ammi tazo ta wankemin"

"Yaron ammi kawai" ta fada qasa qasa,sarai yaji me tace amma sai yace

"Na'ammm,in taso ki wankemin ne?"

"Ni bance ba" ta fada da sauri,dariyarsa ya qumshe kawai yana jinjina kansa,batasan wayeshi ba da taki kiransa da wannan sunan,soyayyarta ta maidashi duk yadda take ganin nasa a yanzu.



      Ranar kuwa ana idar da la'asar saiga ammi fulani ta iso,kamar kowanne lokaci ta rungume bilkisu a jikinta,harga Allah yanxun wata qaunarta ta daban takeji cikin ranta,abinda safwa da sukayi shekara da shekaru ta kasa yi ita gata zaune kawai saboda azeez din,tabar komai saboda shi da sunan jinyarsa,duk da manyan manyan zunubansu a wajenta,safwan da har yau nata kuma zuwa dubiyarsa ba,sai mamarta ke aikin aiko da abinci da saqon gaisuwa,da sunan safwa din bata da lafiya,mura waike damunta,hakanan tun daga wancan lokacin daidai da second daya bata taba ganin wani kallo na rashin girmamawa ba daga bilkisun.



      Saida suka gama gaisawa sannan ta isa ga yariman,bilkisu ta dinga jefa masa harara a fakaice,sai a bayan idanun fulanin ya koma kamar wani yayayye,amma data iso saiya koma.namiji sosai,musamman idan ta shigo ne da afnan ko wasu daga cikin barorinta,yanzun zai aro dukka izzar mulkinsa.



    Suna fita din kuwa ya kalli fulanin

"Ammi qafafuna babu dadi,a taimaka min a wankemin su,na rasa wanda zai wankemin" 

"Ba matsals,sai na gyara makan,duk da banga wani datti ba sosai ba" ta fada tana miqewa,tilas bilkisu ta tarbeta,ta amshi aikin,qasa qasa tana jifarsa da harara,shi kuma yana qumshe dariyarsa,gamida jifanta da wani irin kallo me kashe jiki.



      Qafa daya aka wanke fulani ta duba agogon gold dake daure a tsintsiyar hannunta

"Gida nakeson komawa,akwai wasu mutane da nayi musu alqawarin zamu gana" ta fada tana duban yariman kai ya gyada,yasan bazasu wuce daya daga cikin qungiyoyin tallafinta ba da take dasu,cikin tausasawa ta dubi bilkisu

"Diyata,na gode sosai kinji" cikin jin kunyar fulanin ta saki murmushi kawai,ta musu sallama ta fice.



      Sai data biya wajen likita ta masa magana ya rubuta musu sallama nan da gobe,saboda tana ganin lokaci yayi zuwa yanzu da zata qarasa aikin data fara,babu musu ya amsa mata,don shima ya idanunsa sun soma gajiya da ganin tabarar da yariman keyi.



     Sai data gama dukkan abinda takeyi kana ta isa turakar me martaba,bata taddashi ba sai itama bata damu can ba,saboda kusan ta saba yanzun da halin ko inkula da yake nuna mata,sabanin daa da yake nuna zumudi da kulawa duk lokacin daya kasance zata kwana wajensa,tsufa ko shekaru duka basu canza wannan ba,saboda tasan kanta sosai.



       Bandaki ta shiga tayi wanka,sannan ta dawo cikin dakin tana shirya jikinta cikin qamshi,sanye da rigar towel yalwatacciya.



      Dai dai lokacin da me martaba ya turo qofar dakin ya shigo,bakinsa dauke da sallama,ta waiwaya ta amsa mishi,saita dauke kanta tana ci gaba da shafa man da takeyi,zuwa yanzun tana jin nauyin dake qirjinta yana yin nashi waje,tsoron dake danqare a zuciyarta yana kwaranyewa,tana jin nutsuwa sosai irin wadda ta jima bataji irinta ba,domin kuwa tana jin a yanzun ta aikata abinda ya dace,wanda yake shine dai dai,ta hada ahalin da ada ta zama silar tarwatsewarsu,sukayi nesa da juna,irin nisan da daya bai iya ganin daya.



     Yadda tayi mishin saida murmushi ya kubce masa,duk tsufa ko girman mace baka rasata da wasu halaye irin na quruciya,a hankali ya qarasa bayanta,kana ya sanya hannunsa ya riqo nata hannun ta baya.



      Waiwayowa tayi ta dubeshi,saita sake dauke kai ba tare da tace komai ba ta maida hankalinta ga madubi,tana jin wani rauni yana ratsa zuciyarta

"Aisha" ya kira sunanta a tausashe,wanda ta jina rabon data ji hakan,kiran daya mata ya qarasa tsinka zuciyarta,sai kawai ya waiwayo gaba daya ta fada jikinsa gami da sakin kuka.



     Tsam ya riqeta yana jin sautin kukan nata har zuwa wani lokaci ba tare daya hanata ba,sai data sassauta sannan ya janyeta zuwa bakin gadon ya zaunar da ita.



     Kansa a qasa ya saki ajiyar zuciya,sannan cikin nutsuwa ya soma magana

"Ta kowacce fuska matuqar kana son ka zama cikakken adali,wanda zaka tsira gaban ubangiji ranar gobe qiyama,to ya zama qarqashin jagorancinka babu bambanci,hukunci yana iya hawa kan kowa a duk sanda ya saba tsari da qa'ida... Koda kuwa a karan kanka ne ka sanyawa ranka cewa hukuncin na iya biyoka ta kanka idan har hakan ta kama,babu babban soyayyar da zan nuna miki aisha daya wuce a duk lokacin da kika aikata ba dai dai ba na doraki kan hanya,na kuma nuna miki kurenki ta duk hanyar data dace,ta kuma yanayin da nasan ba zaki manta ba,kuma nan gaba ba zaki sake yunqurin aikata wani abu me muni makamancin haka ba,kin riga da kin gane kuskurenki tuni,tunda har gashi kin gyara,kin dawowa da azeez din iyalinsa har inda yake kwance kamar yadda kika nesanta su a baya"



"Aisha...kudi mulki ko dukiya duka zancan banza ne,duk da kike ganinsu masu qarewa ne wataran su barka daga kai sai mahaliccinka da kuma abinda ka aikata,duk d'an da yake masarautar kaisa ina masa kallon uswa aafiya aafra sumaira afnan nimra ko zunaira ne,wato kamar yaran cikina ne,dukkan abinda ka yiwa dan wani kamar naka ka yiwa,saboda Allah bazai qyale ba,sakamakonshi bashi da iyaka,xai iya juyewa kan yaranka a lokacin da wala'alla ma baka raye cikin duniyar"



"Abdul'azeez.....Allah ya baki yaro daya tamkar da dubu,yaron da bai taba sabamin ba kamar yadda kema bai taba saba miki ba,duk da yana da tsatstsauran ra'ayi,aqida tarin miskikanci da nashi tsarukan,amma akanmu yakan zub da wannan gaba daya yabi namu zabin da ra'ayin,koda bai dace da nasa ba,a matsayinki na uwa,a maimakon ki fahimci zurfin haquri da kawaicinsa,ki barshi yayi aure a sanda yaso,sai kikace a'ah...." Shuru yayi yana sauke ajiyar zuciya sannan ya dora

"Na godewa Allah,kuma ina godewa Allah da yayimin babban rufin asiri da kuma gata,ya tsaremin yarona daga sharri da dattin mummunan aiki,mummunan zunubi dake tarwatsa dukkan wata al'umma,komai kwanciyar hankalinta da wadatarta wato ZINA,zunubin dake tarwatsa ahali,ya gadar da baqinciki da baqinjin cikin wannan ahalin dama al'umma gaba daya,ni nasan ba wayo ko dabarata bace ta tsaremin shi,mahaliccina ya dubeni ne,ya dubi zuciyata,ban taba rabar diyar kowa ba da nufin aikata mummunan aiki ba,kamar yadda mahaifiyarsa take,shi yasa ya dubeni ya tsaremin nawa ahalin,na gode masa qwarai da wannan"



"A wannan lokacin da kika hanashi auren,idan da Alla ya qaddara mana jarrabawa,a yadda yake da tashen quruciya,da farinjini irin wanda nida ke duk bamuyi irinsa ba,Allah ne kadai yasa me xai faru,da wala'alla har yanzu yana cikin qazantacciyar rayuwar da ni dake duka bamu isa mu fiddashi ba,qila da wadan nan kyawawan 'yan biyun ba'a samesu ta hanyar halas ba,tunda Allah ya riga daya tsara lokacin haihuwarsu yayi,dalili kenan daya sanya wani lokaci nake baki uzuri dan qarami kan abinda kika aikata,lokacin zuwan yaran duniya ne yayi,kuma dole sai sun shigota"



"Yaro baya qanqanta da aure kamar yadda yarinya batayi,wani tunani da shirme ne maras tushe bare makama da muka azawa kanmu,wanda babu shi cikin adininmu face zallar yahudanci,wanda hakan ya jagoranci rayuwar al'ummarmu data yaranmu wajen rugurgujewa,kuma har yau mun kusa waiwaye muyi dubayya wa kusakurenmu mu gyara ba"


"Shin me yasa ba'a haramta zinar wuri sai auren wuri?,ba inda musulunci ya qayyadewa wani mutum shekarun da zaikai kafin yayi aure,akwai sahabin da yayi aure yana da shekaru goma sha bakwai kacal a duniya,randa aka kai mishi matar ya kwana da asuba aka fita yaqi dashi yayi shahada acan ba tare daya samu damar yin wankan janabar daya samu daga matarsa ba"



"Ta yaya mutanen da suka fimu tsarkin jiki zuciya dana zamani gaba daya zasu dinga aurarwa kamar yadda ya kamata,amma mu zamu rintse idanunmu,a dai dai lokacin da zamani ya lalace,mu aro aqidun mutanen da basa tsarkin kashi,basa wankan janaba,zina abar ado ce a wajensu,mutanen da suke qasqantattu,mutanen da Allah yayi alqawarin gadar musu da qasqanci ya zama tambari a garesu,mu dauki aqidar sai yaranmu sunkai wani matakin kafin muyi musu aure koda suna da buqatar hakan,a daidai sanda zamani yake sake lalacewa da tabarbarewa,bama tunani ko hango illar abinda zai faru,muna ganin kamar ci gaba ne,eh ci gaba ne,amma irin namai haqar rijiya,yana ganin haqarsa na zurfi saidai qara limewa qasa shidin yakeyi,koda yaushe karki bari magauta su tunxuraki ki aikata abinda ba dai dai yake ba,nafiki sanin yawan magautan da kike cikinsu,hagu da dama,gabas da yamma kudu da arewa,Allah ya doraki a kansu saboda jajircewarki,karki bari ki aikata abinda zai xame miki abun dariya da gwalo tir da Ala wadai"



"Naji dadi da kika gano kuskurenki aisha,kika kuma gyara,ina fatan hakan zai zamo darasi a wajenki" cikin gamsuwa da bayanansa,da kuma matuqar sanyin jiki take gyada kai,saita zame daga gefan gadon ta gurfana gabanshi

"Tun daga randa na hada wannan abun ban kuma samun cikakken nutsuwar ruhi na ba,kullum tunani da fargabar abinda xai je ya dawo nake,ko iya wannan nutsuwar da Allah ya ciremin tabbas ya horani,banda sauran abubuwan da suka biyo baya,ba shakka nayi nadama....nayi nadama ta gaske,ina fatan kaima zaka yafemin mijina,kayimin afuwa"

"Na yafemiki,Allah ya yafe mana gaba daya"

"Amin" ta amsa,saiya saka hannunshi ya dagata daga durquson da tayi yana cewa

"Miqe maza maza,kada barori da bayi suga uwar sarki zube a qasa" murmushi tayi tana rausayar da qwayar idanunta

"Nidin ba kowan kowa bace matuqar ina gabanka,wannan dukka suna tasiri ne a ayayin da bana gabanka ina tare da wasu mutane daban" murmushi ya saki sosai har fararen haqoransa irin na azeez suka bayyana,har abada yana alfahari da aisharshi,ta iya kalamai masu kwantar da zuciya,da sanya miji cikin nutsuwa.



             *_ASIBITI_*




      Shuru ne yaci gaba da wanzuwa bayan ficewar fulani daga dakin,saidai gaba daya jikinsa ya gama macewa,saboda yadda take mishi wankin qafar sai.yakeji kamar wani susa ko tafiyar tsutsa take masa,ya saki jikinsa gaba daga jikin filon daya kare bayanshi dashi yana ci gaba da qare mata kallo.



     Babu abinda jikinsa ke buqata a lokacin illa yaji duminsa,ya kuma san cewa ba zata taba yarda tazo ta sauqi ba,don haka saiya saki qaramar qara yana rintse idanunsa gam.



     Da sauri ta dago tana dubanshi,ganin tsahon minti guda shuru yasa ta motsa labbanta a hankali

"Mene ne?" Shuru ya mata bai amsa mata ba sai sake rintse idanunsa da yakeyi,shurun nasa yadan daga hankalinta,saita saki abinda takeyi ta tako gefansa a hankali

"Amm....nace lafiya?,menene?" Bata qara sakan guda ba ta tsinci kanta a qirjinsa,ya matseta gam yana sakin lallausar ajiyar zuciya dake nuni da cewa sai yanzu zuciyar ta samu nutsuwa,hannunsa ya dora saitin zuciyarsa

"Nan ne yakemin ciwo sarauniyata....." Saiya kama hannunta ya dora saitin wajen,sannan ya dora tafin hannunshi saman hannunta,dumin hannunsa ya ratsa har qwaqwalwarta,ya sanyata rintse idanunta ko zata samu sassaucin abinda takeji

"Bansan ya zan fasalta miki yadda nakeji ba kullum kwanan duniya bilqees....abinda na sani shine,tunda ammi ta kawoni duniya ban taba son wani abu makamancin son da nake miki ba,banyiwa saninki wani dogon zango ba,amma abubuwan da suka faru cikin gajeran zangon da mukayi tare dake shekaru dubu sunyi kadan su ginasu a zukatan wasu masoyan....don Allah" ya fada yana kamo habarta da hannunsa,wanda hakan ya bashi damar kallon tsakiyar qwayar idanunta,kamar yadda itama take kallon nashi idanun da suka wani narke,suke nuna zallar shauqi da shagala cikin duniyar soyayya,idanun da takeson ta daina kallonsu don kada suci gaba da yi mata illa amma ta kasa,kamar mayen qarfe,ya riqe ganinta cikin nashi ganin,yana kuma aika mata da wasu irin saqonni da duk juriya dakiya ko girman kan mace bata isa ta kubce masa ba,daya daga cikin irin tarin baiwar da Allah yayi masa,iya jefa soyayya cikin mintina qalilan a zuciyar duka wadda yaso.




       Saiya sake qas da muryarsa,ya sanya bakinsa saitin kunnenta

"Don Allah....ki bani dama koda baki sona ne nemi soyayyarka da qarfin qwanjina,idan na kasa nida kaina zan baki dukkan damar da kikeso" kamar ta kurma ihu haka takeji soboda yanayin daya saukar mata,kanta takeson qwacewa amma ya zare duk wata laka dake jikinta,yana shirin sake furta wani abun bayan ya kuma kusantar da bakinsa cikin kunnenta aka tura qofar dakin.



      Qarat faduwar wani abu dukka yaja hankalinsu,saiya daga kanshi yana duban qofar dakin,kamar yadda bilkisu data zame jikinta take duban qofar.



      Matashiya ce wadda aqalla zatayi shekaru talatin zuwa da biyar,doguwa fara sol,idunta a warwaje kamar wadda aka watsawa barkono tana kallonsu,dukka jikinta ko ina rawa yakeyi,da alama magana takesonyi amma ta maqale mata a baki.



      Ta fannin azeez safwa ya gani,saiya janye idanunsa daga kanta a hankali yana duban bilkisu da tuni ta tashi a jikinsa tana gyara rigarta daya cukuikuyeta,fuska a hade murya a dake kamar bashi ba yace

"Zoki qarasa wankemin,lokacin magrib ya kusa" daga kai tayi ya dubeshi da niyyar gaya mishi saidai ya qarasa,amma duba daya ta ma fuskarsa taga ba irin ta daxu bace,wannan a daure take tamau zallar kwarjini ya cikata,saita kasa masa musun,ta qarasa gabansa ta duwa ta riqe qafar,daidai lokacin da sautin

"Prince!!!!" Da qarfi ya fito daga bakin wadda ke tsaye bakin qofar.



      A nutse ya waiwaya ya dubeta sau daya tak,saiya yaga hawaye ne ke saukowa saman kuncinta,a lokaci guda kuma tana girgiza kai,saikuma ta juya da gudu gudu sauri sauri tabar wajen.



     idanunsa ya janye daga wajen yana lumshesu gami da jan tsaki,da mamakin sauyawarshi haka ya sanya bilkis daga kai ga dubeshi,tambayar fal ranta,wacece wannan din?,meye alaqarsu?,me yasata furgici haka da ganinsu tare,amma ganin bai sake wani motsi ba ita dinma saita share kawai taci gaba da aikinta,wanda wannan karon harta gama baice komai da ita ba,hakanan bai sake wani motsi mai qarfi ba,saidai fuskarsa kawai ta nuna kamar akwai alamun bacin rai haka.

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 76


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





      Dukkansu tsaye suke a harabar asibitin ana gyara tsaiwar motocin da zasu wuce gida a cikinsu bayan likita ya rubuta musu sallama.



     Gaba daya ya kafa ya tsare,hakanan yana gadin duk wani motsinta da idanuwansa cikin wani zazzafan kallo,saita basar taqi dubar sashen da yake,duk da tanajin tasirin kallon har cikin bargonta.



       Sau tari takanyi mamakin kanta,takanji cikin jiki da ruhinta kamar ta jima da saninsa ko sabawa dashi,takanji komai nashi daban a zuciyarta,ta gaza cankar meye wannan din.



     Dai dai lokacin da wasu barori suka qaraso inda suke,cikin girmamawa suka rusuna

"Ranki ya dade,fulani tace ki qarasa mota ki shiga ku tafi" azeez dake tsaye ada yayi gyaran murya,duk sai suka shiga nutsuwarsu,cikin wasu sakanni suka bar wajen.



       A hankali yataka zuwa inda fulanin ke tsaye,yadan shafo sumar kanshi kadan sannan yace

"Da wai na dauka zamu wuce ne"

"Ina?" Ta fada tana balla mishi harara,saiya kasa amsa mata

"Ka turomin ita mu wuce,lokaci na qurewa" ta fada tana shigewa mota,kamar ya saki kuka haka ya dinga ji,amma babu yadda ya iya,haka ya juya murya a cushe yace mata

"Ki qarasa ammi na jiranki" batace komai ba ta soma takawa inda fulanin take,saidai tana ta qumshe dariyarta ne,sannan bugu da qari ita kanta hakan ya mata.



      Shuru ne ya ratsa cikin motar sanda suke keta titin zuwa masarautar kaisa,wanda ta fuskanci ba xasu maidata gida ba kenan?,don ko anty zuhriyya da sukayi waya daxun a wayar fulani kamar abinda ta nuna mata kenan

"Abdul'azeez ya shaida miki yana da wata iyalin bayanke?" Muryar fulani ta katse mata tunaninta.



      Kaman daga sama taji xancan,amma zuciyarta data gaya mata mutum kamar abdul'azeez din,matsayi daraja da daukaka irin tashi ace ace daman tsayin wadan nan shekarun bashi da iyali,don haka ta aro nutsuwa ta sanyawa kanta,sannan ta girgixa kai a nutse

"Bai gaya min ba" sai fulanin ta saki ajiyar zuciya,a hankali ta soma warware ma bilkisun irin yanayin da azeez din ya shiga bayan rabuwarsu,ciwon da yayi bayan ya amince zai rabun da ita kamar bazaiyi rai ba,da kuma aurensa da safwa.



       Can qasan zuciyarta ta saki wata sassanyar ajiyar zuciya,tana jin yadda zuciyarta ke sake nutsuwa dashi,amannar data gaza bashi sai taji a yanzun ta bashi,wani girma qima da darajarsa ta dagu cikin idanunta.



       Laifinsa dan kadanne,amma saboda girma da qimar mahaifiyarsa ya gaza gaya mata ainihin waye me laifin har kawo yanxu,sai data ji daga bakinta tukunna,lallai ya cika da na halas,domin kuwa kowanne mutum yunquri yake ya kare martabar mahaifansa a idanin duniya,komai tarin zunubi laifi ko lalacewarsu

"Ina fatan wannan ya wanke dan abinda yayi saura a zuciyarki,naga har yanzu jama yaron nawa rai da aji akeyi" ta fada cikin tsokana da barkwanci,duka sai taji kunya ta kamata,ta sunne kai kawai tana murmushi.



    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



     Cikin hikimar nan tata ta gama tsara yadda zata bayyanawa duniya yarima azeez da iyalinsa boyayyu wadanda ba'a sansu ba.



        Tunda ta tafi da bilkisun ta hana kowa ganinta,daga ita sai afnan sai mutum biyu na musamman data dauko masu gyara bilkisun suke ganinta,sai kuma amintattaun hadimanta dakewa bilkisun karatu kan yadda gidan sarauta yake,yayin da ita kuma a gefe daya da kanta take xama ta koyama bilkisun hanyoyin kama zuciyar miji da kuma mallakeshi babu boka ba malam.



      Abun na saka bilkisu cikin kunya mai yawa,tun tana kunya harta sake saboda ta soma sabawa da jin kalaman bakin fulanin,a hankali saita fahimci ita din macace me hikima da fasaha,Allah ya hore mafa dabaran zaman duniya,wanda lallai dole tayi xarra tsakanin abokan zamanta.


   

      Ita kanta a jikinta tasan cewa akwai sauyi mai yawa,gyara ne data sameshi ciki da waje wanda ya sake bayyana zallar baiwar kyau da Allah yayi mata,ya kuma maisheta wata jinsi daban.



   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



    Zazzafar iska ya fitar daga bakinsa yana sauke wayar daga kunnensa bayan ya gama sauraren kalaman safwa,kai yake gyadawa kawai,kana daga bisani ya nitsa yatsun hannunshi cikin sumarshi.



     Wai me yasa mata aduk sanda suka sanyaka a tarakunansu idan bakayi wasa ba dukka lissafinka saiya tarwatse,ba dauki matsalar safwa wani abu ba,amma ayau tabbas banda tana cin albarkacin ammi ne da bata isa ta gaya mishi wadan nan kalaman data gaya masa a yanzun ba.



      Gefe daya ga bilkisu,yarinyar da yakejin ta jima da zams mahadi na numfashinsa bama rayuwarsa ba,wadda yakeji a yanxun itace duniyarsa,idan babu ita tabbas duniyarsa zata tarwatse ne gaba daya,saidai itama a yanxun ta masa tsada,ko sau daya ammi taqi bari ya ganta tun randa ta daukota daga asibiti,ta kaita wani waje daban ga boyeta,duk wayo da dabararsa amma ya gaza ganinta,da qyar yake samun barci sau tari,ga uban ayyuka da suka shafi kasuwancinsa,wadanda a yanzun suna tafiya ne slow sabida rashinsa a gurare da dama,yaci burin ya ragesu gami da gyara wasu abubuwan ko daga gidane kafin komai ya daidaita ya koma kan harkokinsa amma hakan ya gagara,bilkisu ta hana ruwa gudu gaba daya.



       A wajen twince dinshi kawai yake rage zafi,wadanda ammin taja mishi kunne kan ko sau daya kada ya shigo dasu masarautar,tana jiran lokacin shigo dasu yayine,sanda ta shaidawa maimartaba ta kuma yi shawara dashi kan abinda ta shirya murmushi kawai yayi

"Aisha....aisha sarkin dabara,Allah ya bamu aron rai da lafiya" ya fada kawai yana dubanta.



       Sosai yaran ke debe masa kewa,yakan kwashesu ya kaisu gidansa na musamman wato village,su kwana biyu tare,shike musu wanka ya hada musu abinci,idan kuma suna da abinda sukeson ci xaisa a musu order a kawo masa har gidan.



      Wannan ya haifar da shaquwa da kuma sabo mai yawa tsakaninsu,jini ya soma aikinsa,soyayyar uba da 'ya'yansa ta soma zagayawa tsakaninsu,har wani lokacin sukan kwana su wuni basu tambayi mamarsu ba,sosai yake basu kulawa da dukka qarfinsa.



      Miqewa yayi yana sanya hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sauke ajiyar zuciya,yanajin ayauma zai gwada sa'arsa ko xai samu damar ganinta,ya zura wasu lausasan rufaffun takalma na sarauta a kyakkyawar qafarsa,sannan ya isa gaban madubi yana sake kallon kyakkyawar fuskarshi,wadda kwanakin baya ba haka take ba,a yanxun ta sake kyau saboda aski da gyara data samu,gami da nutsuwar samun abinda ruhinsa keso kusa dashi,fuskar tashi ya shafa yana sakin murmushi shi kadai,duk sanda yako tunata takan sanya murmushi saman fuskarsa,shi kansa yana jinjinawa irin son da yake mata,duk wani bacin ran safwa sai yaji cikin kaso dari babu kaso tamanin,juyawa yayi ya taka a hankali ya fice daga katafaren dakin gadon nashi.



      Duk wanda yayi yunqurin masa rakiya dakatar dashi yakeyi,shi sam baison irin wannan bibiyar ta gidan sarauta,shi yasa yake tsara yadda zai kwashe iyalinsa gaba daya suyi gaba,suje su bude rayuwarsu iyasu isu,babu takurawa bare sanya idanu ko matsi.



        Tunda ya shiha sashen fulanin suke zubewa suna miqo gaisuwa har ya dangana da falonta na qarshe.



     Babu kowa cikin falon sai afnan dake zaune tana kallo,ta daga kai a hankali tana amsa sallamar da yayi wadda take ciki ciki kamar wanda aka yiwa dole,dama tasan idan bashi ba babu me aikata hakan,yana daga tsayen ya tambayeta

"Ammi fa?"

"Bata nan,tadan fita"

"Ina princess?" Ya sake tambayarta yana kallonta kanshi tsaye,sarai tasan da wadda yake,amma saita dake ta kuma gimtse kamar bata gane ba,bayaga haka ammi ta ja mata kunne karta bar kowa ya ganta ma,yanzun nan ta shiga ciki daura alwala da wala'alla yadda basusan da shigowar nan tashi ba ya cimmasu tare

"Wa....?"

"Keep quit,ni abokin wasanki ne?" Ya fada a hankali yana fidda mata idanun nasa masu tsananin kwarjini,take ta shiga taitayinta,ya kuma tuna mata yariman na asali,qasa qasa cikin qunquni take fadi bayan ta nuna masa dakin da yatsanta

"Ni ina ruwana,ni nakar zomon?,ko ratayar ma ni ba'a bani ba" baijita ba,don tuni yasa kansa cikin dakin cikin sauri kamar wanda za'a kama.



       Tana tsaye baki mirrow tana goge ruwan alwalar dake fuskarta,wanda saboda tsabar kyau da gyara da fatarta ta samu ruwanma bai zama sosai saman fatar tata,ta gama ta dauki comb ta gyara gashinta daya wargaje wajen shafar kai,tana qoqarin maidashi ta hadeshi waje guda ta hangeshi dab da bayanta ta cikin mudubin,saita zaro idanu tana niyyar juyowa,saidai tuni yayi caraf ya kama qugunta ya kuma mannata da jikinsa,cikin taushi da sanyi ya dora kanshi saman kafadarta,bakinsa da hancinsa duka suna sansanar wuyanta,wanda hakan ya sanya tsigar jikinta tashi lokaci daya,hakanan ya kashe dukka wata laka ta jikinta,saitayi collapes cikin jikinsa,tana tsintar kanta itama da kallonshi ta cikin mudubi kamar yadda yake duban qwayar idanunta shima.



      Kamar masu kallon quda haka suka dinga kallon juna ta cikin madubi tsahon lokaci,kowannesu saida jikinsa ya gaya masa sannan ya juyo da ita suna fuskantar juna,still idanunsa cikin nata,ya sanya hannu ya gyara mata gashinta daya sauko gefan fuskarta,cikin sanyi ya sunkuya ya sumbaci tausasan labbanta kana yace

"Ko kadan baki kewata madam?,dake za'a hada kai a sake bani wahala ko?,kina so ne na sake komawa gadon asibiti karo na biyu?" Maganar tasa sai taso bata dariya,ta saki murmushi

"Gadon asibiti kuma?" Gira ya dage mata

"Eh yes,gadon asibiti" dan qwace jikinta tayi tana murmushi gami da bashi baya

"Nifa gaskiya ban shirya zama da ragon namiji ba" sake kamota yayi,don tsaiwarsu ta mishi dadi,baison ta raba jikinta da nashi,cikin zuciyarsa yasaki murmushi yana taune lips dinsa kadan na qasa,shi kadai yasan meya tuna sai yace

"Aiko ki shirya zama da raggo,don a kanki kam bani da wata juriya ko kadan....but saidai kinsan a inda ragwantaka take aiko....i mean ba ainihin ragon da kike magana bane,tunda kin dan shaida idan xaki iya tunawa...." Saiya duqa saitin kunnenta ya gaya mata wani abu daya sanyata qwace jikinta da sauri bayan ta saka hannuwanta ta rufe fuskarta,ta yaya zata manta wannan lokacin,lokacin da asannan takejin tafi kowacce halitta baqinciki a duniya,tafi kowacce halitta rashin sa'ar rayuwa,ta kuma fi kowacce halitta asara,saidai a yanzun tunaninta nata sauya mata dararen guda biyu zuwa darare masu tarihi arayuwarta,daren farkon daya bambanta da kowanne daren farko.na kowanne ma'aurata,tana danne kunyarta da boye dariyarta tace

"Lalala nifa ba haka nace ba,kuma ni ba haka nake nufi ba" wani murmushi yake jifanta dashi hade da wani kallo da zai gaya ma mutum cewa ya dade da narkewa cikin duniyar qaunarta

"Zoki gayamin to yaya ne?" Ya fada yana qoqarin kai mata cafka,saidai knocking din da akayi a bakin qofar ya tsaidashi,ya kalli qofar saiya basar kamar baiji ba,ya sake maida hankalinsa a kanta yana sake takawa zuwa inda da durqushe,bai qarasa ba aka sake qwanqwasawa,tsaiwa yayi cak,kana cikin qasaitacciyar muryar shin nan yace

"Afnan!....zaki bar wajen ko sai nazo na bata miki?"

"Ba afnan bace,uwar afnan dince" ya tsinkayi muryar fulani,saiya dafe goshinsa da tafin hannunsa,ya salam,asirinsa ya tonu?,bilkisu kuwa tuni ta miqe ta bude bandaki ta shige ta maida qofar ta rufe,da wanne ido zata iys kallon ammin idan fa shigo ta gansu tare.



      Qofar ya nuna ya bude,tana tsaye tana kallonshi,ta tsareshi da ido.sosai,kunya ta kamashi amma saiya maze ya rabeta zai wuce

"Ina bilkisun?"

"Tana toilet" ya amsa mata yana wucewa

"Ka jirani anan" ta amsashi tana shiga ciki.



       Dakin tadanbi da kallo har saman gadon,a gyare yake ba alamun wani ya hau,saita saki ajiyar zuciya,batason yakai ga tabata yazun,harsai ta gama shiryata tsaf ta yadda zai sake raina kanshi

"Idan kin gama.boyon ki sameni falo" ta fada tana dake dariyarta,don taga alamun jinta ne ya sanyata kulle kanta a bandakin,ta juya ta fice tana jin sanyi cikin ranta da Allah ya azurtata da suruka irin bilkisun,tana tuna abinda ya faru awa daya data shude tsakaninta da safwa da iyayenta.



       Ta shirya ne da kanta zataje ta zayyane musu komai ta kuma kawo gyara kamar yadda tayi na bilkisu,tunda ita ta shirya komai,lokacin data iske mahaifiyar safwa suna tare da safwan,kanta na saman cinyarta uwar na shafa kan nata kamar wata jinjirar goye,da alamu ma kuka ta gama yi,shigowar fulanin ya sanyata yin zumbur ta miqe,bata ko tsaya gaidata ba ko mata magana ta haye sama abinta,inda katafaren sashinta yake kamar dama can a gidan take zaune,bawai aure take a wani waje ba.



        Sama sama suka gaisa da mommyn safwan,itama tana ta wani cin magani,bata boye mata komai.ba ta fayyace mata tare da neman suyi haquri safwan ta koma dakinta ta zauna kamar kowacce mace,cikin daure fuska take amsa mata

"Amma dai wannan abun hajiya aisha ke kanki kinsan zallar cin amana ce da rashin gaskiya,ya za'ayi yana tare da yarinyarmu amma har a zagaye a aura masa wata?,kuma harda yara tsakaninsu,ace kuma waike bakisanma suna tare ba,hakanan bakisan da yara tsakani ba sai bayan wasu shekaru,ai hankali ma bazai kama ba,gaskiya bazan boye miki ba,naji zafin wannan abun sosai,kuma bawai ni kadai ba,hatta da daddynta yaji ciwo sosai,kuma ni bani data cewa sai abinda yarinya tace,saboda haka zan turota kuyi magana tsakaninku" daga haka ta miqe ta haura dakin safwa,wanda sai data kusa minti arba'in zaune tana jiransu,da alama bayan ta gama bata labarin komai sai data sha kanta da qyar kafin ta yarda ta fito,sai gata ta sauko tana wani kumbure kumbure.



      Da harshe irin na uwa fulani aisha tayi magana da ita cikin lallashi da fahimtarwa,saidai tana bude bakinta cikin tsanar sakalci da sangarta tace

"Nifa yanzu na tsaneshi ma,saboda maci amana ne mayaudari,na bashi amana dari bisa dari amma yamin wannan yaudarar tsayin shekarun da muke tare dashi?,ni bazan koma gidansa ba saidai.idan har zai saketa ya rabu da ita,ni kadai na rayu a gidanmu kamar yadda momy na take ita kadai wajen daddy,so ni banga wani dalili da zai sani in zauna da wata ba" tadan murguda bakinta ta miqe ta koma inda ta fito,yayin da fulani ta bita da kallo cikin mamaki da takaici,saidai batason bacin rai ya kaita ga yanke hukunci da sauri,ko meye itace sila dole ta daure koma me zata gani ta kawo gyara iya iyawarta,haka ta miqe ta iske barorinta suka bar gidan.



        Sai data iske mai martaba ta sanar mishi da komai,yayi shuru yana mamakin irin nasu dattakon su kuma a matsayinsu na iyaye,sai yayi ajiyar zuciya kana yace

"Zan samu lokaci nida kaina na iske ibrahim din,komai zai daidaita in sha Allah" da wannan ta baro wajensa,saidai ranta cike fal yake da mamakin abinda sukayi matan.



         A falon ta iske azeez tsaye hannayensa zube a aljihu,idanunsa saman tv,saidai ba ita yake kallo ba,duka tunaninsa na ga bilkisu ne,zama tayi sannsn tace dashi

"Xauna" hannayen nasa ya cire kana ya zauna saman kujerar datafi kusa dashi,a nutse ta soma masa magana

"Inason kome safwa zata ce da kai,kayi haquri har sai al'amura sun daidaita" shuru yayi yana juya maganar aransa,hakanan jikinsa ya bashi akwai abinda ke faruwa,amma dai saiya amsa mata dato,kana ya miqe ya nufi fita daga sassan.



      Baiyi wani nisa ba yaji kamar muryar afnan na kiranshi,ya dakata ya waiwayo yana dubanta harta iso,sai data qaraso kuma sai tayi laushi kanta a qasa tace

"Yaa azeez....ammi ta boye maka ne,bata gaya maka komai ba" nan ta gaya masa dukkan abinda ya faru kamar yadda fulanin ta bata labari bayan ta dawo.



      Wani irin bacin rai yaji yana hudashi,har wani tururi yakeji saman fuskarshi,idanunsa kafe jikin wata bishiya daura dasu,saidai a badini ba ita yake kallo ba.




      Bazai taba lamunta wata halitta ta wulaqanta masa mahaifiya ba,bare mace macen ma matarsa,wadda a musulunce take a qarqashinsa,bayan ita din harda mahaifiyarta itama?,uban me suka musu?,duk iskanci da sakalcin da yarinyar takeyi bai taba daga kai ya duba koya dauki mataki mai tsauri ba duk sabida darajar ammin da takeci su basu gani ba?,bazai taba lamunta ba,koda da ruwan gold daka qerata kuwa bata isa ta taba mishi.mahaifiya ba,inda yasan ma inda ammin ta tafi da bai barta ba,don ko sabon aurene ya qara baida laifi a irin rayuwar d sukeyi da safwa din,wadda sam batasan muhimmancinsa ba bare auren dake kanta,tsabae sakacinta ya bada gudunmawa wajen mutuwar gudan jininsa suhaima,ko sun dauka ya manta ne?,ko zuba musu idanun da yayi suna zaton shi sauna ne ko baison ciwon kanshi ba?,kai kawai ya jinjina bai iya cewa afnan komai ba ya soma takawa yana barin wajen.



      "Gwara a gaya masa gaskiya,kada ta dawo tazo taci gaba da wannan iskancin banzan kamar wadda aka yaye daga nono" afnan ta fada tana juyawa tana barin wajen.



       Kiran da taji ana mata ya tsaidata,daya daga cikin barorin gidanne,ta qaraso da hanzari hannunta dauke da wani kyakkyawan kwando da aka saqa da hannu da wata iriyar ciyawa

"Ranki ya dade,mangwaro na tsinko a lambun gidan nan,irin wanda kikeso,naga yafi dacewa dake" murmushi ta saki,ta saka hannu tana yaye dan qyallen da aka rufe kwandon dashi,ta dauki daya tana cewa

"Amma kuwa kin kyauta asiya,a wanke yake?" Tayi tambayar tana kaiwa bakinta

"Fes ma uwar dakina" ta bata amsa tana murmushi itama.



      Kai ta jinjina bayan ta gutsira

"Yayi,irin nawa ne kuwa har dandanon,muje ki ajemin,kin cancanci a baki tukuici" cikin farincikin yadda ta amshi kyautar tata tadan rusuna kanta

"Kinfi gaban haka mai hannun alkhairi irin na uwarta,godiya nake" daga haka suka rankaya tare suna taba hira abinsu,kai bakace asiyan qasa da ita take ba.



¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



       Cikin satin kyakkawan saqon katin da aka qawata adonshi da ruwan gold ya zagaya lungu da saqo na masarauta kaisa dama qasar kaisa gaba dayanta,tare da wasu qasashe maqwabta dana nesa da suke wannan duniya dama garuruwa baki daya,katin daya daga hankalin maqiya da abokan adawa da yawa,katin daya faranta ran wasu,katin daya sanya ayoyin tambaya cikin ruhi da zukatan wasu,ya sanya wasu rayukan kuma cikun zumudi da son ganin zuwan wannan rana.



        Katine dake dauke da gayyata ta musamman zuwa babban bikin taya yarima Abdul'azeez abdallah mu'az kaisa da mai dakinsa Bilkisu bilyamin murnar cika shekara takwas cif da auren wedding anniversary,sunan dake manne saman katin shi ya sanya al'umma da dama tambayar wacece?,tunda da yawansu sunsan safwa ne,babu wanda yasan da wanzuwar bilkisun.



       Duk da cewa fulanin da fari ta dauka komai zai daidaita tsakaninsa da safwa ta hadasu dukka ta musu,rashin samuwar hakan da gudun bata lokaci yasata kawai aiwatarwa.



      Sanda kyayykyawan katin daketa sheqi ya isa hannun safwan kamar tayi qaramin hauka haka taji,ta dinga koke koke kaman qaramar yarinya tana sake tabbatar da cewa azeez yaci amanarta,kuma babu ta yadda zata koma masa,babu bata lokaci ta dauki waya ta tura masa tex,ya gani ya karanta,ya kuma yi murmushi kawai sabida ya riga ya wuce wannan babin,yaci kuma da irgen kwanakin daya bata kawai,duk da bai fahimci wasu daga cikin kalamanta ba,don baisan me fulani ke shiryawa ba a lokacin.



      Cak ta tashi fulani adama hajja fauxiyya da shalelenta kamal a tsaye,hankalinsu a matuqar tashe suka hadu domin tattaunawa kan lamarin,kowa ya kawo tashi shawarar,wanda suke hasashen cikin biyu abu daya ne zai faru,imma dai taron ya zamewa aishar abun kunya da tonuwar asiri gareta da iyalanta,ko kuma ya zama wankuwar laifi da fidda kai daga zargi a idanun al'umma,wanda daga qarshe sukaga babu wata mafita,illa dai kawai su zuba idanu suga yadda taron xai kaya,daba bisani sai susan matakin dauka na qarshe,don na zasu bata zuba idanu ko lamuntar wahalar da suke da fadi tashi na shekara da shekaru ya tashi a banza ba.




       Ta fannin fulani saratu itadinma cikin dimuwa da tashin hankalin take,ya tabbata dai yana da wata matar kenan bayan safwa?,duk kudin data zuba kan amata aiki akansu ya tashi abanza kenan?,hakan bai sanya ta saduda ba,kudi ta sake zubawa masu ciwo duka akan azeez din,saidai kowa ya amshe kudinsa ya kuma kalmashe,sannan ya bita da qaryar ta zuba idanu daga nan zuwa bayan taron,zataga abinda zai faru,bayan kowa ya bincika yaga aikin yafi qarfinsa,amma babu wanda ya gaya mata,saboda yana tsoron rasa kwasar ganimar kudaden data je musu dashi.



     Tayi imani dasu,ta kumayi imanin duk abinda suka fada haka yake,don haka tadan samu 'yar nutsuwa kadan ta sama ranta zata jira din daganan zuwa ranar taron taga me zaya farun kamar yadda suka alqawarta mata,harta samu damar qarfafawa su walida gwiwar su halacci taron da suka shaida mata gayyatar da fulanin tayi musu,don tana ji a jikinta suke da nasara a ranar.



     Abinda bata sani ba,tun farkon lamarin fulani aishan ta bada kudin sadaka masu tarin yawa kan ayi mata sauka babu adadi kamar yadda ta saba,wannan karon kan Allah ya daidaita komai cikin hikimarsa da ikonsa,ya kuma karesu ita da dukka ahalinta daga sharrin mai sharri mutum ko aljan.



      Yadda al'amura ke gudana da shirye haiqan,kai kace auren afnan zatayi shi yake sake daga musu hankali,shiri take na qasaita isa ixxa da nuna zallar mulki da sarauta daga inda aka gajeta ba taka haye ba,hatta wasu sassan na gidan ta saka an sake gyaresu domin saukar baqi.



       Duk abin nan azeez bai sani ba sai daga baya,shi daya ya dinga murmushi yana shafa kanshi,qaunar mahaifiyar tasa da tausayinta na sake ratsashi,farincikin da yaji a lokacin ba dan kadan bane,don haka shima saiya soma shirya nashi gagarumin walimar sanyawa auren albarka,ya kuma soma tura katin gayyata ga dukka wani abokin arziqi ko na huldar kasuwanci nashi dake fadin duniya,tare da shirya musu tafiya umara suyi azumin ramadan acan shi da ita dasu amatu,ba tare da sanin kowa ba banda anty zuhriyya.



       Duk wani jini ko ahalin me martaba sai data tabbatar da goron gayyata ya isa gareshi,ciki harda yaran su fulani adaman da kanta ta aika musu ba tare data bi takan iyayen ba,hakanan nata yaran sumaira uswa da aafiya dukkansu kowacce ta dokantu tazo gidan,don basu taba haduwa da bilkisun ba.



     Ga me martaba kuwa sanda ta miqa mishi katin ya gama karantawa saiya saki murmushi,yasani cewa tayine domin ta sake wanke kanta a idanunsa,tayi ne donta wanke yaronta daga zargin masu zargi,sannan tayine donta daga hankali ta dugunxuma hankalin abokan adawa yadda ta saba,hakanan tayine donta wanke kanta ta kuma bayyanawa duniya abinda ada ta boyeshi da hannunta,ta kuma qarasa aikinta,wanda takeji har jiki da zuciyarta shine abunda yayi saura da zatayi ta qarasa gyara dukkan alaqar data bata a baya,bawai kawai zallar manufar  WEDDING ANNIVERSARY bace kawai,kamar zata jefi tsuntsaye da yawa ne da dutse daya

"Aishatunnabiyyi.....Allah ya nuna mana,ya bamu aron rai da lafiya" murmushi tayi tana amsa mishi.



     Shi a karan kansa yakejin abun yayi dai dai,ya kuma burgeshi,shima saiya samu kansa da dokin zuwan wannan rana.



      Bilkisun batasan dukan yadda aka shirya abun ba,duk da tasan da taron,harma ta gayyaci farida ita kadai,saidai yadda afnan ta kasa zaune ta kasa tsaye abun ke bata mamaki,a hankali kuma ta gano ba qaramin shiri sukema abun ba,ita abunma daure mata kai yake,yadda fulanin ke nuna mata qauna tare da qoqarin karbe fadar anty zuhriyya qarfi da yaji

"Alhamdulillahil lazi bi ni'imatihi tatimmussalihat" takan furta lokaci lokaci kawai,saboda tasan banda Allah babu wanda ya isa ya mata hakan.


*_na gode da uzurinku gareni,kuci gaba da haquri har zuwa sanda zamu rufe littafin,fatan alkhairi🙋ðŸ¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸Ã°Å¸™‹Ã°Å¸¾Ã¢€Ã¢™€Ã¯¸_*

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 77




      Cikin dimuwa sukayi gware da juna lokacin da hajja fauxiyya ke kai kawo tana jiran shigowar fulani adama,dukkansu goshinsu ya bugu sosai,kowanne ya hau sosawa amma sam ba wannan bane damuwarsu ba,tsantsar tashin hankalin da suka gani yanzu a wajen gudanar da taron weddinga anniversary din ya shafe komai,ya shafe duk wani zafi da radadi da zasuji.



      Cikin zallar tashin hankali adama ta kama hannun fauziyya

"Da gaskene wai fauxiyya abinda idanuna suka ganemin kuma naji ana fada?,abdulazeez keda wadan nan 'yan biyun masu kama da juna?,don Allah kicemin mafarki nake" ta fada tana jijjiga hannun fauxiyya wadda itama gaba daya tashin hankalin da take ciki take jinta kamar ba cikin duniya ba

"Adama....adama na fiki shiga tashin hankali" ta fada tana buga cinyoyinta da hannu,duk yadda fulani adama taso daure kukanta wannan karon ta kasa,sai kawai ta dafe kanta da hannu biyu ta saki kuka tana fadin

"Wallahi aisha ta cucemu,ta shammacemu,tako ina tasha damu,ta zarcewa tunaninmu,aure tayi masa a boye da hadin bakin maimartaba,ta yadda ba zamu iya cutar dashi ko abinda suka samu ba,tanuna mana wannan kodaddiyar yarinyar a zuwan ita kadaice matarsa,Allah ya isa aisha,kin kadar da tunaninmu na tsahon shekaru,inda muka nufa daban kema inda kika nufa daban" saita sake kukanta sosai,saboda yadda abun yake mata ciwo a zuciya,duk wata hanya da take ganin ta dace tabi don tarwatsa matar da ahalinta amma ya gagara,tsayin shekaru aishan bata taba barin tunaninta ya huta ba da laluben hanyar daukar fansa mafi ciwo ba,sai gashi yanzu dukka dararen data bata a rayuwarta sun tashi a banza,hannun agogo ya sake komawa baya fiye da yadda yake ma a da.



       Hajja fauxiyya sam ta kasa zama,sai kaiwa da kawowa takeyi kamar wanda ta hadiyi tabarya,gumi kawai ke yanko mata,tana jin abun kamar mafarki take wanda za'a iya tashinta kowanne lokaci.



       Daga can dakin taron kuwa 'yan qananun gulmarmaki ke tashi,mafi yawa daga bakin munafukai ne,kowa yana tattaunawa da abokin zamansa,yayin da mafi yawa mamaki yafi cika zukatansu,musamman wadan da zukatansu ke cike da alkhairi da kuma qaunar fulani aisha na yadda ta fita zakka cikin dukka matan me martaba wajen tausayawa da sauraren matsalolinsu,tunaninsu yafi karkata kan akwai babban dalili da yasa auren ya zama a rufe har zuwa yaran da suka samu,sun ta'allaqa hakanne saboda samun tsaro a rayuwarsa data yaran daya samun,wanda qilan sai yanzun ne suke ganin lokaci yayi da ya kamata a bayyanawa duniya su.



     Tun tana zaune tana ganin zata jura,tana danne gudun da zuciyarta ke qarawa tare da ganin al'amarin kamar almara ce har juriyarta ta gaza,a hankali fulani saratun ta sulale daga inda take zaune ta zube a qas ba tare data shiryawa hakan ba,tsabar razana da ganin yaran da tayi baya ga matarshi bilkisu,hankalin yaranta yakai gareta,suka isa wajen da gaggawa suna girgizata,idanunta na kansu saidai babu baki ko damar motsa hannu,haka aka dauketa zuwa cikin gida cikin tashin hankali,yayin da yarima azeez da bilkisu harma da fulani aisha ke can suna gaisawa da jama'a cike da zallar farinciki,wanda hatta da bikisun a yau tana jin kanta ya daban kuma ta musamman.



      Duk inda suka gitta sai idanun kamal ya musu rakiya,yana daga zaune a inda yake tunda yazo,zallar kishi wanda hassada tafi yawa a ciki ke cinsa,kanshi yakewa tambaya,waishin me yasa duk abinda ya burat a rayuwarsa saiya zama mallakin azeez dinne,yaso suna daukaka dukiya da uwa uba kudi,dukka ciki babu wanda ya samu,amma sai gashi azeez din ya mallaka,yaso bilkisu tun ranar daya soma ganinta,sai gashi ta zama matarsa harda kyawawan yara biyu.



      Idanu ya lumshe yana gayawa kansa tabbas wannan karon bazaiyi faduwar baqar tasa ba,sai ya dasa baqinciki a rayuwarsu,wannan murmushin saiya juyashi ya koma kuka da alhini,saiya miqe da hanzari,cikin qarfi da zallar bacin rai yake takawa yana barin gurin,tare da ayyana da kuma tsara yadda zai gudanar da komai a daren yau basai gobe ba.



      Sosai taro ya bada ma'ana,hakanan ya qawatar,ya kuma faranta ran zuciyar masoya masu qaunar fulani da ahalinta.




       Gagarumin zaman cin abinci ta sake shiryawa tsakaninta da memartaba da duka iyalin nata a wani waje na musamman cikin gidan,saidai lalurar data samu fulani saratu bagatatan wadda ba'asan dalilin samuwarta ba ya sanya zaman ya kasance daga ita sai 'ya'ya da jikokinta.



       Karfe bakwai na dare aka sanya zaman zai kasance,kusan tunda aka tashi daga wajen taron tana tare da fulani,anty sumaira uswa da aafiya,wadanda sukejin kamar su hadiyeta ita da twince,abun mamaki yadda bata zata ba yaran sun sake sosai cikin gidan,kamar dama can sun saba dasu,sai wajen bayan la'asar sannan fulani ta hadata da zababbun barori masu mata hidima zuwa qawataccen sassan yarima azeez dake gidan bisa rakiyar afnan.



       Tunda aka tashi shima bai samu zama ba,hakan ya sanya basu kuma haduwa da ita ba,yana can wajen baqinsa,wadanda wasunsu ke masa sallama suna komawa inda suka fito,tunda tafiya ce ta jirgi,wasunsu kuma zasu kwana ne a qasar kaisan,su jira walimar daya shiryawa a washegari.



      Tamkar baquwa haka ta zauna a sassan,gashi afnan ta koma ta barta,daga ita sai yaran,wadanda suma baqunta bata gama sakinsu ba.



      Ana magariba afnan da kanta tazo daukan amatu da abdul,tare da kayan da za'a sanya musu,iri dayane sak kayan,sai bambancin danki na mata dana maza,kaya ne dake nuna zallar sarauta da kuma tsadar da suke dashi,ita kanta da aka gama shiryasu kallonsu kawai take,saita lumshe idanu,ta tsinci kanta da godiyawa Allah daya bata su a matsayin yaranta na cikinta,wani lokaci sai taga kamar ba ita ta haifesu ba,kamar ba daga jikinta suka fita ba,ana gama shiryasun afnan ta kalleta

"Anty saidai fa ki taho donmu munyi gaba,kowa twince yake jira" murmushi tayi 

"Wariyar launin fata zakimun?,kafin ki sansu wa kika fara sani?" Dariya ta saki

"Ke,amma yanzun gsky sun qwace fadar,saidai kiyi haquri daga ke har ya azeez din" dariya ma ta bata,saita tura qofar toilet kawai ta shiga don tara ruwan zafi su kuma suka fice.



       Tana tsaka da shiryawa ya turo qofar,a raxane ta juya,don bata taba tunanin shigowarsa dakin ba a lokacin,saboda taga dakuna da yawa,bata kawo zai shigo nan din ba.



      Idanunshi a kanta yake takowa inda take,yayin da ita kuma zuciyarta ke bugawa da sauri,tama rasa inda zata nufa don ta boye har ya cimmata,a bayanta ya tsaya a hankali ya kuma jawota jikinsa ya rumgumeta tsam yana sakin ajiyar zuciya

"Barka da warhaka gimbiya" ya fada a hankali kamar meyin rada,idanunta ta lumshe,tsigar jikinta na tashi,ta kasa amsa mishi harya sake cewa

"Maimakon ki jirani inxo muyi wankan tare?,tunda baki jirani ba dole ki sake wani kam" kafin ta ankara ya sunkuceta yayi bandakin da ita,saita kasa musa masa ko qwatar kanta.



     Cikin bathtube din cike yake da ruwan data tara,don haka zare dan towel din jikinta kawai yayi ya tsullumata a ciki shima yabi bayanta,kamar xata narke saboda kunya haka taji,ta dinga qoqarin ya fita ya bata koda towel dinne ta daura amma sam yaqi,yayi mursisi abinsa,kamar ma baisan tana yi ba,daga qarshe ma saiya sanyata a jikinta ya soma aika mata saqonnin da suka mantar da ita akan me take magana.



      Sai daya gama aika mata da saqonni son ranshi sannan ya barta ya soma wanke jikinsa,ta runtse idanunta don bata son ganinsa a haka,yana ganinta saiya tari ruwa mai sanyi ya watsawa fuskarta data yi wani kyau da haske saboda gyaran data sha

"Zakima sabane,sannu sannu wataran ma ke zaki min wanka,gwara ma ki shirya" tana jinsa harya gama bata bude idanunta ba,sai daya daura nashi towel din sannan ya miqa mata hannu

"Taso na sa miki muje mu shirya,mun wuce lokaci,nasan mu suke jira" kafada ta maqale,don ba zata iya tasowar yadda yakeso ba,murmushi kawai ya sakeyi saiya ciro towel din ya aje mata gefan bathtube din ya juya baya,da sauri ta dauka ta miqe ta daura,tazo ta rabeshi zata wuce,saiya kamo.hannunta yasake janta zuwa jikinsa,daurewa kawai yakeyi,yanaso ne ya nuna mata ainihin qauna da soyayya wadda yake ganin kamar tana doubting samunta ko tabbatuwarta daga wajenshi,hakan yasa ya yima ranshi alqawarin sai ya gamsar da ita cewa yana mata so guda daya tak ne.



      Duk yadda take dojewa bai barta ba,don kusan tare suka shirya,cikin kayan da itama batasan da zamansu ba sai daya bata,wohoho,zo kaga zallar kyau iya kyau,kamar kwatankwacin wanda sukayi a taron daxun,wanda ita da kanta sai data tofa addu'a ta shafa a daxun saboda maganin baki,yana riqe da hannunta suka baro sashen zuwa sassan fulanin.



       Yana labe a inda ya tanada sukazo suka giftashi,ya bisu da kallo ranshi na sake quntata,zuciyarsa da shaidan na sake ingizashi tare da bashin qwarin gwiwa na aikata abinda ya qudirta,saiya ciro wayarsa ya turawa fulani adama dan gajeran tex

      _sun fita zuwa wajen,ina da tabbacin ba zasu wuce awa guda ba,dasun dawo zan shaida miki,kiyi qoqarin kiranshi zuwa sassanki_


      Daga haka ya maida wayar aljihunsa yana jan qwafa qasa qasa,gamida sake cin buri kan abinda zai aikata din.



      Lokacin da suka isa tuni suka samu kowa ya hallara su kadai ake jira,cikin qauna da kulawa kowa ya taresu,sannan suka fara gabatar da abinda ya tarasu a wajen.



       Kallo daya zaka musu kasan cewa ahalin na cikin zallar farinciki qauna da kuma fahimtar juna,zuciyar fulani aisha a wanke fes haka yau takejin kanta,idan ta dubi iyalin nata sai taga kaman tafi kowa sa'ar rayuwa,hakanan qima da qaunar bilkisu kowanne lokaci sake yawa take a ranta,kunyarta kawaici da girmama na gaba da ita,bambanci take gani muraran tsakaninta da safwa,wanda ada bata bambance ba sai a yanxu.



      Yadda suke ta janta a jiki da nuna mata kulawa yasanya dole tadan sake a cikinsu,don ma yarima ya hanata sakat da mayun idanuwan shin nan,duk.inda ta motsa yana biye da ita,batasan me yakeso ba hakanan,amma ita kanta zuwa yanzu tasan cewa mahaukaciyar qaunarshi ta mata mugun kamu,kamun da take zaton ba yau jiya ko shekaran jiya ya kamata ba,ta rasa yaushe ne?,a ina?,kuma a wanne lokaci?.



     Sun dade sosai a wajen,don basu tashi ba sai sha daya saura,qiri qiri suka riqe twince suka ce wajensu zasu kwana,hakanan tana ji tana gani tana kuma jin nauyi tabi azeez din suka wuce sashensa,zuciyarta cike da fargabar wanne dare zata fuskanta a yau din?.



      Tun daga farkon sassan ya baiwa duk barori dake hidimawa sashen hutu sannan suka wuce zuwa ciki,suna isa falon ya harde hannayensa yana dubanta da narkakkun idanunsa

"Zabi bedroom din da kikeso,wanda zaki kwanta ki huta sosai" maganar da yayi tadan kwantar mata da hankali,tadan dauke kai kamar ba zata nuna ba,murmushi ya saka,ya nufi wani wanda ke daura da nashi dakin

"Na zaba miki nan" 

"Na gode" ta furta qasa qasa,ita gaba daya yadda yake kallonta yana sanyata cikin wani yanayi ne mai nauyi,gami da kunya,gabanshi gadi yake komai,dazun har gulmarsa uswa da afnan sukayi,saidaya jefesu da harara sannan suka guntse bakunansu.



       Tana jiyo qarar wayarshi sanda take shiga dakin,duk da batasa dawa yake magana ba,amma taji takun fitarsa daga falon gaba daya,hakan ya bata sukunin sauya kayanta zuwa na bacci masu kauri yalwatattu,bata da sauran abunyi,saboda haka ta nade tsakiyar gado,ta jawo wuyarta daya mata kyautarta dazu me azabar kyau da tsada ta soma dudduba cikinta.



     Cike da mamakin ha durfafi sashen fulani adama,yayi mamaki qwarai da yau ta daga waya ta kirashi da kanta wai tana son ganinsa,baya ga haka wai a daren,a daren ma qarfe shadaya da wani abu na dare?,abunda bazai iya tunawa sau nawa ya faru ba a rayuwarsa,hakanan ya danne mamakin har ya isa ainihin sassan nasa,ya kuma samu baiwa daya tana jiransa,tayi masa jagora har ainihin falon da fulani adama ke zaune tana jiransa.



       Da mamakinsa da murmushi ta tarbeshi,harda miqewa tsaye tana fadin

"Maraba da yariman kaisa....sannu da zuwa" saiyadan dubeta kadan cikin mamaki sanda take nuna masa wajen zama

"Zauna mana,bari a kawo maka abunci da abunsha,na tabbata da qyar idan ka samu saka wani abu a cikinka saboda hidimar jama'a" kai ya girgiza yana soke hannayensa a aljihun wandonsa

"Bana buqatar komai,naci abincin dare tare da ammi na" cikin yaqe da boye takaici tace

"Ai amminka badai qoqari ba,duk damu an waremu ba'a gayyacemu ba" cikin zaquwa dason jin dalilin kiran yace

"Uhmmm" kawai,don dukka wadan nan maganganun nata baiga ma'anarsu ko muhallinsu ba face salo na batawa kai lokaci

"Ka zauna mana yarona,idan kaqi cin abinci ai bazaka qi shan komai ba" kafin yace komai ta kira daya daga cikin hadimanta,ta bata umarni ta kawo tatattaccen ruwan inibi kamar yadda tasan cewa azeez din yafi sonshi.



      "Allah yasa lafiya dai ko?" Ya fada yana kafeta da idanu,saboda kame kame da yaga tanata yi

"Eh lafiya....amma saurin me kake ne,ka bari a kawo maka lemon mana"

"A qoshe nake,kiranki ne kawai ya fiddo ni"

"To...to ai shikenan.....dama akan abubuwan da suka faru ne wunin yau,yanzu ace shekaru har takwas abdul'azeez kana da mata harda yara biyu amma babu wanda ya sani a cikinmu?,aiko babu komai dai mudin kamar iyayenka muke,idam yau babu ranta mu xaka ci gaba da kallo a matsayin iyaye ko?,sam banji dadi ba,saiya zamana kenan bamu da maraba da sauran jama'ar waje dama talakawan gari ko?" Dan qaramin murmushi ya sake na gefan baki yana yada kanshi gefe kadan,sam baiga muhallin maganar ba,a yadda ma take magana kamar bata shirya yin maganar ba kawai yin kanta maganar take,ya jima da gama karantar halayyar matar tsaf,tun yana ganin kamar amminsa na daukan tsattsauran matakin nesantasu harya fahimci gaskiyar mahaifiyarsa,ya sani,makira ce ta gaske,maida dubansa gareta yayi

"Kinsan komai sai Allah ya nufa,to sai yanzu ya nufa ku sani"

"Eh hakane,amma duk da haka maganar gaskiya bamuji dadi ba,don innarka fauziyya ma don tabar nan wajen ne,amma fada ta dinga yi kamar zata ari baki,da qyar na tausheta" haka ta dinga soko maganganu marasa kan gado da sam bashi da alaqa dasu.



         Bilkisu kuwa na tsaka da saita wayarta taji an turo qofar,da mamakinta tasa kai don taga waye,tasan cewa kamar ya mata sallama a fakaice ne sanda take shigowa dakin,to meye ya dawo dashi.



       Saidai wanda ta gani din abun ya mugun kadata da razanata,wata fuska da batasan ga wacece ba tsaye gabanta tana qare mata kallo.



     A hankali ta aje wayar gefe itama idanuwanta qur a kanshi tana son inda ta sanshi

"Malam lafiya?,waye kai,ta yaya zaka shigo dakin matar aure haka kai tsaye ba tare da neman izini ba?" Ba amsa illa ci gaba da qarewa surarta kallo da yake,wanda kallon ya bata tsoro sosai,saita soma sauka ta daya barin don ta dauko.mayafi ko hijabi ta qara suturta jikinta,Allah ya taimaketa ma kayan ba masu fidda tsiraici bane.



       Tafiyarsa taji a bayanta sanda take sanya hijabin,tayi hanzarin juyawa tana daidaita shi a jikinta

"Ka fitar min a daki,baka da hankali ne?,ko kai mahaukaci ne?" Ta fada cikin qaraji da tsawa.



      Wani shu'umin murmushi ya saki

"Dukka ina jinki,kuma ni ba tashin hankali ya kawoni ba,wala'alla ke bazaki gane ni ba,amma ni bazan taba iya mantaki ba,tun shekaru takwas dana taba ganinki zuwa watannin baya zuwa yau,na dade ina kishi da baqinciki da yarima,duk abinda nake buri a rayuwata sai naga shi ya samu ni kuma ban samu ba ciki kuwa harda ke,nayi burin aurenki,nayi burin samunki amma sai gashi lokaci daya yarima ya sameki,duk neman da nake shekara da shekaru ya tashi a banza,saboda haka nazo cikin salama ki bani na dandana yadda shima ya dandana,ko hakan zai ragemin zugin asarar rasaki da nayi,ki bani hadin kai,don har mu gama bazai dawo ba,idan kuma kinqi zan amsa ta qarfin tuwo,don naci alwashin bazan barshi wannan karon ya tsira dake ke daya ba".



      Batasan lokacin data daga hannu ta zabga mishi mari ba,tunda take a duniya bata taba jin tashin hankali irin wannan ba,tuni bacin rai zallah ya bayyana saman fuskarta

"Wanne irin jakin mutum ne kai?,wawa wanda baisan darajar aure ba,ko karuwa idan kana da kunya bai kamata ka gaya mata wannan maganar kai tsaye ba,bare matar aure mai mutunci,kayi gaggawar barin sassasan nan gaba daya,tun kafin na tara maka jama'a!" Murmushi ya saki yana shafa wajen yana sake matsowa inda take tsaye

"Naga alamar dai ba zaki bani hadin kai ba,saidai na yimiki fyade na karba ta qarfi" yana gama fadar haka ya danqi.hijabinta cikin zafin nama yana neman rabata dashi,kafin kace meye wannan kokawa ta kaure tsakaninsu,bilhaqqi ya sakar mata dukka qarfinsa da mazantakarsa kan sai ya keta haddinta,yayin da take dukka qoqarinta wajen ganin ta kare kanta ta tsira da mutuncinta.

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 78


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070





     Miqewa yayi daga dosana dawawunshi da yayi saman hannun kujerar daya zauna akai tun dazun yana duba agogonshi,yaga alamar surutun nata bamai qarewa bane,kimanin minti arba'in da zuwanshi kenan amma babu wani abu me muhimmanci data gaya masa,sai soki burutsu da kwashe kwashen zance

"Allah ya bamu alkhairi" ya fada yana durfafar qofa,tanason ta sake tsaidashi ta bata mishi lokaci amma kuma ya mata kwarjini da yawa yadda ya hade fuska,hakanan tana kallonshi har ya fice

"Ja'iri,wannan baqin ran naka yau za'ayi maganinsa,gwara a soma tarwatsaka,muga qaryar fadin rai da izza,dan banza shi da uwarsa".



      Haka kawai ya dinga ji gabanshi na wani irin faduwa,irin faduwar gaban da bai taba jin irinta ba,ya lumshe idanunsa kana ya bude a hankali kuma a fili ya furta

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil,wala udwana illa alazzalimin" saiya danji faduwar gaban ya ragu,yaci gaba da tafiya a hankali yana dosar sassan nashi,yana kallon yadda sawu ya soma daukewa a gidan,kamar ba shine yayi cikar kwari dazu ba,da alama kowa ya nufi makwancinsa.



       Sosai ya galabaitar da ita ya kuma qarar mata da sauran kuxarinta,hijabin jikinta ya tsarge,cikin tashin hankali tasa hannunta ta cukuikuye hijabin sosai ta hanashi sauka daga jikinta,cikin qarfin hali tasa qafafunta ta harbi cikinsa,yayi baya yana dafe da cikin saboda yadda ya qulle masa,hakan ya bata damar yunqurawa ta durfafi falo,shima ya miqe ya rufa mata baya.



       Qafa ya sanya mata ya tadeta a tsakiyar falon,ta tafi luuu tayi qasa,wanda kafin takai qasa ta sanya hannunta,hakan yasa ta fadi akan hannun,wani irin zafi ya ratsa qwaqwalwarta,wanda batasan sanda ta saki wani gigitaccen ihu ba.



       Kamar a mafarki yaji sautin murya kamar ta bilkisun tana fitowa daga sassansa,cak ya tsaya yana son tantance abinda yaji,sai kuma ya qara sauri zuwa ciki saboda wani bugu da zuciyarsa ta fara yi harya wuce na dazu.



      A gaggauce yake ratsa falukan har zuwa sanda ya isa falon da bilkisun suke,daidai sanda yake tura qofar daidai lokacin daya sanya hannu ya fincike hijabin jikinta da taketa faman riqe dashi yana fadin

"Baki isa ki tseremin ba,har sai na cika burina a kanki,bazan zuba idanu yayita yin nasara a kaina ba tsahon......." Maganar da bai samu damar qarasata ba kenan yaji saukar wani irin naushi a bakinsa,tsananin zafi yasa ya kasa tantance daga inda dukan yake,sai wasu taurari da suka soma kewaye kwanyarsa zuwa cikin idanunsa,kafin ya koma hayyacinsa yaji wata kyakkyawar shaqa data kusa wucewa da duka sauran numfashinsa da yayi saura,sai a sannan idanunsa suka sauka kan azeez,wanda launin fuskarsa zuwa idanunsa gaba daya suka sauya tamkar an watsa musu ruwan barkono

"Me...mmee......" Yaketa qoqarin yin magana,saidai azeez din ya riqe dukkan wata kafar numfashinsa,har sai da numfashin ya kusa katsewa sannan yayi jifa dashi waje guda

"Me kakeyi cikin dakin iyalina?,me kake shirin aikatawa kamal?" Ya fada a zafafe yana durfafarsa,cikin qarfin hali kamal din ya miqe yana son nuna nashi qarfin halin

"Me kake haka?,karka kuskura ku sake dukana malam na gaya maka" ya fada yana nunashi da yatsanshi,zallar haushinsa da yakeji shekara da shekaru a yanzu suna taso masa,tsana da qiyayyar yariman.



      Bai kuma ankara ba ya wankeshi da wasu zafafan marin kuncin hagu da dama,sannan ya sake kaiwa fuskarsa naushi,wanda hakan ya baiwa haqoransa na gaba guda biyu da tun naushin farko suka soma girgidi damar xubowa qasa.



       Duka tako ina yake kaiwa kamal din,wanda tun yana yunqurin yaga ya rama harya fuskanci zarrarsu ba daya bace ya soma qoqarin qwatar kansa ta hanyar bude qofofi yana neman hanyar da zai kubuta,yayin da azeez ke biye dashi bai fasa ka masa duka ba duk inda ya samu a jikinsa cikin tsananin fushi kishi da fitar hayyaci.



       A haka har suka fito zuwa babbar farfajiya,daidaikun masu giftawa wadanda basu kai ga zuwa makwancinsu ba suka soma labewa cikin mamaki,suna kallon yadda azeex din ke jibgar kamal cikin hasken fitilun gidan.



       Hannu daya yasa ya damqi wuyan rigar kamal din ya tayar dashi tsaye,kana ya soma janshi zuwa sassan da mahaifiyarsa hajja fauziyya ke sauka.



       "Kiramin masu horon gidan qasa su sameni a wancan sashen yanzu yanzu" ya fadawa wani bawa da sukayi arangama dashi a hanya ba tare daya dubi sassan da bawan yake ba,wanda cikin hanxari da zallar biyayya ya wuce don isar da saqon yariman nasu.



        Daidai lokacin da hajja fauziyyan ke zaune a katafaren falon dake sashen,sam hankalinta ba'a kwance yake ba tunda fulani adama ta gaya mata abinda kamal din ya tafi aiwatarwa,sam shirin da tsarin baiyi mata ba,har sukaso sudan haura da fulani adaman,saboda tana ganin don ba danta bane shi yasa ta aikashi aikata wannan alfashar,abinda kawai yadan kwantar mata da hankali idan ta tuna cewa idan suka cimma muradinsu to wannan zai bude musu wata qofa da zasu iya cimma muradinsu,amma matuqar komai ya daidaita xata cire adama me daga tafiyar,daga ita sai yaronta xasu amfana.



       Bugun qofar da wani irin qarfi,da kuma faduwar wani abu kamar kayan wanki a gabanta shiya dawo da ita daga tunanin data lula,azeez ta gani tsaye a gabanta yana fidda huci da wata irin kama da bata taba ganinsa da ita ba,ta duba gabanta da kyau,sai taga kamal yashe cikin jini dake fita daga hanci da bakinsa.



     A razane ta dora hannu aka ta kurma ihu,koda ba'a gaya mata ba tasan cewa lamari ya lalace kenan,idanunta a warwaje a matuqar tsorace tace

"Na shiga uku ni fauziyya,me zan gani haka?,abdul'azeez dan uwan naka zaka kashe?,jama'a kuzo ku tayani gani,yariman kaisa zaiyi kisa" ta soma kwaroroto wanda ya janyo hankulan jama'a,na nesa dama wadanda ke tsaitsaye saman hanya suna jimantawa gami da tattauna abinda suka gani din yanzu.


  

        Tuni qofar sassan ya soma cika da 'yan ganin qwaf

"Na kawo miki shine ya gaya miki meyaje aikatawa kafin a wuce dashi" azeez ya fada cikin fushi yana fidda idanunsa

"Meya maka haka abdul'azeez?,ashe shaye shayen naka da ake fada dai da gaskene?,to wallahi bazan yarda ba,abinda kayi masa saika karbi sakamakonka" ta fada tana matsar qwallar qarya.



       Dai dai lokacin da masu gadin gidan qasa suka qaraso(masu kula da sashen manyan laifuka na prison din masarauta)

"Ku kamashi kuje ku kullemin shi" ya basu umarni yana mai juyawa don barin falon,yana jin yadda hajja fauziyya ke maganganu tana kurin ba wanda ya isa ya fita dashi,saidai sahun giwa ya take na raqumi,haka suka qwamusheshi suka ingizashi inda yariman ya buqata.



      Zabura tayi daga inda take takure tana kuka sanda ya tura qofar ya shigo,tana ganin shine saita maida kanta taci gaba da kukanta,ya isa inda take ya dagata gaba daya ya sanyata a qirjinsa ya rungumeta tsam yana sakin wata nannauyar ajiyar zuciya,yana jin wani irin ciwo da qunci idan ya tuna yadda yaxo ya tadda kamal na shirin cin zarafin bilkisun,banda doka da shari'a tabbas sanda ya riqe wuyan kamal bazai sakeshi ba har sai numfashinsa ya wuce,yana jin wani irin zafi tun daga zuciyarsa zuwa gangar jikinsa,kamar ana masa feshin wuta,huci kawai yake fiddawa yana sauraren sautin kukanta da yakejin kamar ana yanka mishi zuciya ne.



      Tsahon lokaci suna a haka,sannan ya janyeta zuwa ciki,bandaki ya wuce da ita,ya zaunar da ita a toilet sit ya hada ruwan mai dumi sosai sannan ya iso inda take,idanunshi cikin nata yana nata qwarin gwiwa ya soma cire mata rigar baccin jikinta,sai daya rabata da komai sannan ya sanyata cikin ruwan zafin,ya tabbatar jikinta ya gasu yadda ya kamata sannan ya sake mata wanka banda wanda tayi daxu sannan ya maidota cikin dakin.



       Wasu kayan ya sauya mata marasa nauyi masu taushi sannan ya suka koma saman gadon ya sake sanyta cikin jikinsa,kanta na saman qirjinsa,har yanzun kuka take,hakanan shima ya gaza furta mata komai bare ya hanata,don wata gobara ce take tashi daga zuciyarsa,yana wassafa hukuncin daya dace da kamal ne kawai,tsattsauran hukuncin da baiga abinda zaisa ya sassauta mishi ba,tunda yayi gigin shiga gonar data masa nisa,ta masa zarra,kwatankwacin nisan da tazarar dake tsakanin sama da qasa.



        Sai can tsakiyar dare ya jita shuru bayan kukan ya dauke gaba daya,ya daga fuskarta daya tasa saboda kuka,yayi kissing kyakkyawan lebanta zuwa goshi,sannan ya gyara mata kwanciya a jikinsa yana jin wani qaunarta da kishinta na sake ratsashi,ya sake matseta gam cikin jikinsa kamar wani zai qwace masa ita.



      Kwanan zaune yayi,saida aka kira sallar asuba sannan yayi yunqurin zuwa bada farali,zuwa lokacin ita dinma ta farka,sai data fara shiga tayi alwalar sannan shima yayi,shiya jagorancesu sukayi jam'in sallar tare suka idar,tsahon wasu mintuna bayan idarwar tasu sannan ya waiwayo yana fuskantarta,hannuwansa ya miqa mata,batayi jinkiri ba ta isa jikinsa,habarshi saman kanta ya soma lallashinta cikin taushi har zuwa sanda ta sauke ajiyar zuciya tana jin nutsuwa na shigarta,don jiya har barawon baccinya saceta bakinta na dauke da addu'a zuwa wayewar garin yau.



      Wayarshi dake daura dasu ta dauki ruri,daga inda yake zaune ya miqa hannunsa ya jawota,sam yama mance da ita tun jiya,daya duba sai yaga me martaba ke kiransa.



       Cikin girmamawa ya daga ya soma gaidashi,ba tare daya amsa ba yace

"Duk abinda kake ka barshi kaida iyalinka kazo ka sameni yanzun nan a babban falo" bai jira amsarsa ba ya katse kiran,saiya aje wayar kawai,ya miqe zuwa ma'ajiyar kaya dake dakin ya budeta,ya fiddo yalwatacciyar jallabiyya da wadataccen hijabi ya miqawa bilkisu

"Ki saka,zamuje wajen me martaba" alamun tsoro ya gani qarara saman fuskarta,saiya durqusa gabanta,ya kama hannayenta ya saka cikin nashi ya matse,idanunsa cikin nata

"Baki da buqatar ki tsorata ko ki raxana,zaki gaban managarcin mutum ne mai adalci,indai kuma ina tare dake babu wata halitta data isa taci zarafinki kota tozartaki matuqar ina numfashi a doron qasa" wannan ya bata qwarin gwiwa,saita miqe ta soma shiryawa,shima ya sauya kayan jikinsa sannan suka fito.



       Yayi mamakin ganin mutanen dake hallare a wajen kamar ba safiya ba,kamal da mahaifiyarsa wanda yake zaune jikinta,da alamu sai daya ziyarci asibiti,cikin daren ne ko kuwa bayan sallar asuba ne bai san mishi ba,fulani adama,amminsa da babbar diyar me martaba yarinyar fulani saratu.



      Cikin girmamawa ta gaida kowa sannan ta samu waje ta zauna,bayan shudewar wasu mintuna me martaba ya fara magana

"Me dan uwanka kamal ya aikata maka har haka cikin dare kahau dukansa kamar wanda Allah ya aiko,ka masa jina jina irin haka?".



       Wani abu me tauri da daci ya hadiye,baison ma ya maida maganar,amma dole ya fadeta,bai boye komai ba ya zayyanewa mai martaba,yana kaiwa aya fulani adama dake zaune gefe,wanda tun jiya da lamari ya baci take cikin taraddadi da tunanin yadda zata fidda kanta,tayi gudawa tafi sau a qirga,saboda ta tabbatar indai wannan abu ya fito da sunanta to Allah ne kadai masanin hukuncin da zai biyo baya,salati ta saka mai qarfi da salallami

"Kai kuwa kamal meya kaika aikata wannan tabargazar,matar dan uwanka?" Da mamaki hajja fauziyya ta dubeta,tabbas banda yau din tana tsoron tonuwar asirin fulani adama nata tonuwar asirinne da ba shakka saita bankadata.



       "Kai kamal...anyi haka?" Me martaba ya tambayeshi,cikin hali na ciwo ya gyada kai

"Eh anyi haka,amma ita ta kirani,ita ta nemeni" kalmar data kusa ruguza zuciyar azeez da bilkisu,wadda batasan sa'adda data daga kanta ba,cikin zare idanuwa take kallon kamal din,tana jin jinin jikinta kamar ya daskare

"Qarya yake!" Fulani aisha ta samu kanta da furtawa cikin fushi,duk yadda taso ta hana kanta magana amma wannan karon ta kasa.



       Basu ankara ba har azeez ya isa inda kamal ke jingine jikin babarsa,yasa qafarshi ya take qafar kamal din,ta bada wata qara da yake bada tabbacin babu makawa ya karye,idan bai karye ba to ya samu mummunar gocewar qashi

"Gaya musu gaskiya!" Ya fada cikin qaraji

"Abdul'azeez!!!, agabana?" Me martaba ya fada cikin tsawatarwa,dole ya koma ya zauna ya fidda hucin bacin rai yana jin kamar yasa bindiga ya fasa kan kamal.



       Shuru ne ya biyo baya na tsahon lokaci kana ya gyada kai

"Zanyi bincike....zanyi bincike kuma duk wanda na samu shike da laifi bazan daga masa qafa ba dai dai minti daya ba" maimartaba ya fada cikin kaushin murya,saiya waiga ya dubi Aafiya

"Ya ake ciki da likitan saratu" kanta a qas cike da alhini tace

"Sakamakon ganin abinda ya razanata da tayi,yace ta samu mummunan stroke wanda yake da wuyar magani,bugu da qarima wai jini yahaura qwaqwalwarta,akwai yiwuwar lokaci zuwa lokaci a dinga samun wasu dabi'u mabanbanta tare da ita"

"Ya salam" me martaba ya fada yana lumshe idanunsa,ya budesu a hankali yana musu umarnin tashi su tafi.



       A yanayin da taga yariman ya shiga wunin ranar sai ta soma tausayinsa fiye kanta,zallar bacin rai qarara,bata tana tunanin haka yake da zafi da kuma fushi ba sai yau,kusan wunin ranar haka suka wuni suka kwana.



      Ta fannin su hajja fauziyya kuwa sun cika da farinciki,saboda suna ganin sun samu hanya sassauqa da zata kawo musu qarshen komai,hakanan babu wani abu ko wata hujja da zata kubutar da bilkisu kota wanketa.



       A kwana na biyun ana ya gobe kwanakin da me martaba ya diba na zai sake nemansu su cika,wajen goma na dare taga ya tashi zumbur daga inda ya maida wajen kwanansa wato dogiwar kujerar falon dake daura da dakin gadon,ya zura slippers dinsa ya fice,saita bishi da kallo cikin mamaki,don tun daxun take lallamarshi ya tashi yasha koda fresh milk ne,saboda babu abinda yaci wunin ranar,duk da fulani itama tayi iya yinta yaci wani abu.



      Ba'a jima ba sai gashi ya shigo da wata laptop riqe a hannunsa,ya zauna bayan yaja qaramin table gabanshi ya dora akai,ya daga hannu ya mata nuni akan tazo,jiki a sanyaye ta iso,sai yaja hannunta ya zaunar da ita gefanshi,gami da dora kanta saman kafadarshi,dukkansu fuskokinsu na kallon laptop din.



       Bata gane ne yakeyi ba,illa taga kaman ya rubuta wani kwanan wata ya shigar,sai vedio ya fara motsawa,tsayin mintuna kadan ta fahimci cctv camera record ne,sai kuma ta gane date din ranar da akayi wedding anniversary dinsu,tun daga rana yana wucewa har zuwa sanda duhu ya fara shigowa.



       Sannu a hankali saiga gilmawar mutum cikin sanda,yayi zooming hoton saiga kamal quru quru cike da alamu na rashin gaskiya,saiya tafi next camera da zata kaishi daga falo na qarshe zuwa qofar bedroom din,take ta soma nuna masa gilmawar komai ciki harda kai kawon kamal,labewarsa,shigowarsu shiryawarsu da fitarsu dawowarsu da sanda azeez din ya sake fita,fitar data bashi damar afkawa zuwa cikin dakin.



      Tsayin mintunan da suka kwashe suna gwagwarmaya a ciki saiga fitowarsu falon again yana yunqurin rabata da hijabin jikinta da qafa daya sanya mata ta zube a qas,fincike hijabin da shigowar azeez din,anan ya tsaida record din,ya sanya tafukan hannayenda duka saman fuskarsa yana shafa fuskar,a hankali ya furta

"Alhmdlh,na godewa Allah daya tunasar dani akwai camera a sassan nan,na godewa Allah zahiri da badini" ita kanta ajiyar zuciya ta sauke me nauyi,wata nutsuwa na ratsa zuciyarta,ita kanta wannan shine abu na biyu daya taba gigita rayuwarta lokaci guda,tana tunanin ta inda gaskiya zata bayyana,kana ta kubuta,amma da yake Allah mabuwayin sarki ne,sai gashi ya kawo musu warwarar komai.



       Ranar dukkansu baccinsu ragagge ne,kowanne na tsumayin ketowar alfijir saboda bayyanar da gaskiya.



          A yau din zaman ya sauya salo,saboda samun qaruwar amintattun memartaba cikin xaman,gudun kada yaje ya zartar da hukunci kan kuskure,hakan ya sanya dole ya sakosu cikin lamarin.



       Dukkansu tsakanin su ukun shi bilkisu ko amminsa ba wanda yace musu ta tafas sanda suka zage suna maida yadda akayi cike da son rai,da kuma son yiwa qarya kwaskwarima su fidda kansu,dukka saida duka gama zancansu damar magana ta dawo bangarensu sannan ya miqe da laptop din,yayiwa me martaba bayani a taqaice sannan ya kunna ta soma aikinta.



       Gaba daya falon ya dauki shuru,kowa ya bada hankalinsa ga computer din cike da mamakin abinda suke gani din,dai dai gurin da kamal din ya fincike mata hijabi me martaba ya rintse idanunsa gami da bada umarnin a dakatar da recording din.



       "Oh ni adama naga ikon Allah,yanxu kamalu matar aure matar dan uwanka zaka yiwa fyade,wannan wanne irin lalacewa ne?" Ta fada tana zabgo salati gamida nuna tsantsar alhininta,duk a shirinta na fidda kanta daga wannan tarkon

"Meye banbancina dake?,ni xuwa nayi kawai na aikata,amma kome da saninku da shawararki akayi ko?" Ya fada cikin fushi dajin haushin yadda ta soma luguiguita maganar tun me martaba ko yan fadarshi basuce komai ba,inda yake kallon hakan a matsayin tunzuri kawai dason sanya me martaba ya yanke hukunci me tsauri akansa.



      Maganar kamal din ta sanya kallo ya koma sama,sai kowa ya zubawa fulani adama ido,wadda ta zare idanu ta dafe qirjinta da hannu biyu kana tace

"Sharri?,sharri zaka yimin kamal?,fauxiyya kina jin danki?,yanzu irin sakayyar da zakumin kenan?" Yatsina baki tayi tana jin komai ta fanjama fanjam,ba zata bari sunan danta shi kadai ya lalace ba

"Eh to ai gaskiya ya fada,ba sharri yayi miki ba da kiketa wani haqiqancewa" sarai ta fuskanci kai sukeson hade mata su turota rana,don haka taga gwara kawai ayi mutuwar kasko

"Kice dai da saninmu duka,ku daina magana kuna ingizamin laifi na kada mana fauxiyya" shewa hajja fauziyya tayi,ta soma ratttabo.irin shawarwarin da fulani adaman tasha bayarwa akan yariman da uwarshi,ganin tana kwance mata zani a kasuwa yasanya itama ta soma lissafo nasu shirye shiryen,sai kowa yayi tsit kawai aka zuba musu idanu suna tonawa juna asiri kamar zasu doki juna.



       Tsawa me martaba ya daka musu ganin abun yana neman wuce gona da iri

"La'ilaha ilalallah,muhammadurrasulullah" me martaba ya maimaitawa,hatta fulani aisha da wasu shirye shiryen tasan dasu amma ba qaramin mamaki tayi dajin wasu abubuwan ba,da hannu me martaba ya sallami fulani aisha da iyalinta,suka baro su adama zaune a gabanshi.



        Shuru ne ya ratsa tsakani a lokacin da suke komawa zuwa sassansu,kowa da abinda ke mamayar zuciyarsa,imani ya sake ratsa zuciyar fulanin,tabbas ta sani cewa addu'a ce ta tare mata dukkan wannan masifa da bala'in da sukaso sanyata ita da iyalinta a rayuwa,ba shakka addu'a babu abinda ta bari,amma meta musu a rayuwa haka?,kawai donta hada miji dasu?,kawai don ta fisu siyasar iya zama dashi?,shin ita meye laifinta?,me yasa basuyi tunanin makomarsu a wata rana mai zuwa irin wannan ba?,lallai sau tari bawa shike xabawa kansa qarshensa sakamakon irin ayyukan daya gabatar da hannuwansa.



      Ajiyar zuciya azeez ya sauke sanda sukaxo hanyar da zata kai kowannw sashensa,ya bude baki zaiyi magana fulani ta daga masa hannu

"Duk wata magana ta qare abdul'azeez,Allah ya fitar daku,ya fitar dani ya kuma fidda kowa,kuje kawai ku huta,ku samu hutun da baku sameshi ba" murmushi yadan fidda,koda yaushe yana sake jinjinawa mahaifiyarsa,koda yaushe tana hidimawa farincikinsu,tsayayyar uwace daya tamkar da dubu

"Inaso ki bani izini zuwa yammacin yau mu wuce saudiyya....already na siya mana ticket,kuma yau dama a qa'ida tafiyar zata kasance,so banyi tunanin komai zai warware a qanqanin lokaci haka ba,sai nayi tsammanin zamuyi missing tafiyar yau shi yasa nabar maganar"

"Na muku izini abdul'azeez,Allah yaci gaba da tsaremin ku a duk inda kuke,bari nasa afnan ta shirya ma su amatullahi kayansu" daga haka ta janyo bilkisu jikinta

"Kiyi haquri daughter,an bata muku ranakunku masu dadi ko?,amma ina da tabbacin yarona zai maida miki mafiyansu" wata iriyar kunya ta kama bilkisun,saita sunne kanta a kafadar fulanin,yayin da azeez shima ke fidda wani qawataccen murmushi yana jifan bilkisun da wani narkakken kallo,anan fulani tayi gaba ta barsu,saiya matsa kusa da ita ya sanya hannunshi cikin nata a tausashe suka fara takawa,kamar bazaiyi magana ba sai kuma yace

"Kinji abinda ammi tace,kinaso na maida miki madadin kwanakinki wadanda suka fisu taushi da dadi?" Shuru tayi ta kasa amsa masa har suka kusa isa sashensu,saiya saki ajiyar zuciya sannan yace

"Nayi alqawarin nuna miki zallar so da zai saki ki nutsu da soyayyar da abdul'azeez ke miki ta gaskiya ce,tarayyarmu zata fara ne daga sanda kika bani amanna da kanki" bata gama fahimtar zancanshi ba amma saita share,gudun kada ya sanyata a kunyar da zata kasa sukuni.



      Basu wani zauna ba da kanshi ya shiga hada musu duk abinda suke da buqata don tafiya,abinda ya bata mamaki yadda taga sassan nashi akwai komai da zata iya buqata a ciki,kamar dama can ta taba zama a ciki.



       Kamar yasan abinda ke ranta ya biya da ita gida ta yiwa malam bilya sallama,dukkansu suka shiga 


       Adaren yayiwa me martaba sallama suka wuce filin jirgi bisa rakiyar uswa sumaira aafiya da afnan,wadanda suma a gobe suke saka ran wucewa gidajensu tunda komai yayi settling.



      Kamar yasan abinda ke ranta ya biya da ita gida ta yiwa malam bilya sallama,dukkansu suka shiga suka gaidashi cikin girmamawa da karramawa,wanda hakan yayima bilkisun mahaifinta harma da 'yan uwanta dadi,saboda girman da sukaga sun bashin sam.basu zaci haka ba.



       Ta tadda 'yan uwanta maza biyu cikin su ukun da Allah ya baiwa malam bilya sun waiwayo gida,babu wani cikakken lokaci na doguwar magana,amma tace su jirayi dawowarta,dama tana da qudurin nemansu koda su basu waiwayo gidan ba,ranta duka babu dadi,don dukansu babu wani gagarumin ci gaba ga rayuwarsu,kawai dai anata nemawa kai na rufin asiri ne,amma dai jiya iyau haka suke.


      

       Suna hanya bilkisu na kusa da afnan,afnan din cikin murya qasa qasa tace

"Layinki fa da akayo swapping,wannan baturen likitan ya addabeni fa da kira,zan sunna masa rashin mutunci wallahi,baisan yanzun kinfi gaban wasa ba?" Ta fada cikin hade gira,murmushi bilkisun ta saki

"Karki masa rashin mutunci don Allah,ni da nakeso kiji dashi" ido afnan ta zuba mata cikin rashin fahimta

"Kamar yaya naji dashi?,gashi nace zan masa rashin m kince a'ah" dariya tadan kamata,saita dan daki cinyarta

"Haba qawata,ki fahimta mana,kiji dashi kawai nace fa" dan janye cinyarta tayi

"Rufan asiri ki daina kirana da qawarki,karki jamin balbalin bala'in mijinki yace na raina mishi mata,barni dai a qanwarki" 

"To naji" ta fada tana dariya,sai maganar bilkisun tadan jefata a tunani,kimanin minti ashirin kuma saita saki murmushi tana gyara zamanta.



       Saida jirginsu ya tashi sannan su afnan suka baro airphort din,suna saman hanya kowa na yaban bilkisun da yadda ta shiga ransu farat daya,tare da fadar bambance banbance masu yawa tsakaninta da safwa

"Dama tun da can bilkisu bilyamin ta dabance wallahi" cewar afnan,ta fara bata labarin rayuwarsu ta makaranta,da yadda a baya ta tsangwama mata,suka dinga dariya suna mamakin abun

"Yanzu gata sama dake,ta zama yayarki" inji sumaira,murmushi afnan ta saki

"Wallahi kuwa,dama bakasan matsayi da baiwar da Allah ya yiwa mutum ba,shi yasa akace kabar wulaqanta ko yima mutum kallon banza,saboda rayuwa wataran bakasan ya zata kaya ba,saika tsinci kanka a qarqashinsa watan watarana,duk da dani ni dama tun da can qasan raina ina sonta,miskilancinta ke bani haushi a wautata" haka sukaci gaba da tattaunawa har suka kawo gida.



¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶   Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶  ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶



     Babban abinda ya kaisu qasa mai tsarki dama ibada ce,ibadar kuwa sukayi tayi tuquru baji babu gani,babu wanda keda lokacin wani a tsakaninsu,hatta da yaran sun sanyasu sun himmatu wajen addu'o'i,dukkan wanda bilkisu ta sani ba wanda bata saka a ciki ba baya ga kanta 'yan uwanta yaranta dama surukanta da iyayenta,kwanakin qarshe qarshe suna gab da komowa gida saita tsinci zuciyarta ta karkata ga yiwa aurenta addu'a kan Allah yasa ya zama silar farincikinta dana mahaifanta duniyarta da lahirarta,sai ta sanya afnan,cikin zuciyarta tana jin fata da qaunar haduwa da qulluwar soyayya tsakaninta da dr adam,tabbas da tafi kowa farinciki.



       Duk da ibada sukaje amma a wata gudan sun sake fresh da kyau saboda kwanciyar hankali,bilkisun ta yita daukar hankalin azeez din amma yana dakewa yana son cika alwashin daya ci.



      Daga saudiyya kai tsaye ya dauketa suka wuce dangin mahaifiyarta,abinda bata san ya shirya masa ba sai ranar da zasu tafi,hakan ba qaramin faranta ranta yayi ba sosai,don dama anty zuhriyya nata saka ran zasu,to amma saboda yawa da suka dada dole akwai buqatar qara samun kudi da zasuyi tafiyar dashi.



      Sunyi farinciki qwarai na ganinta da mijinta dama yaranta,dama already suna da labarin maida aurenta,sunso zuwa a sannan,amma ciwon da mahaifiyar mahaifin nata tayi a sannan yasa basu samu zuwa ba,saboda ta galabaita kamar bazatayi rai ba.



      Sun shiga dangi sosai kamar wancan karon,su zaga gidan 'yan uwa qwarai,sai daidaiku da sukayi nisa sosai,kuma duk inda ta sanya qafa tofa tare da azeez ne,hakan ya sanya kafin su taho dangin maman nata da yawa suka sanshi,sati daya suka musu suka musu sallama suka barsu cike da kewarsu,suma sukayi alqawarin zuwa musu nigeria duk sanda wani abu ya sake tasowa.



       Ga wani mamakin nata daga can sai gasu a mali dangin fulani aisha,acan taga tarbar girma kamar yadda ta samu daga dangin mahaifiyarta,taga yadda mulki ke aiki,ta tabbatar da cewa sarauta da mulki ba qarya bane,lallai duk wata dagawa ko nuna isa da fulani ko ahalinta zasuyi basuyi qarya,bakuma suyi a banza ba,gada sukayi,ba takawa da hayewa ba,anan ta sake ganin zallar gata da azeez keda shi,kowa nan nan yake dashi da iyalinsa,wani lokaci idan ana lelensu kallo kawai take binsa dashi,saita ringa ji cikin zuciyarta anya batayi xari ba?,anya baifi qarfinta ba?,anya bai girmi ajinta ba?,daga baya da kansa ya karanceta,ranar tana masa wannan kallon ya kama hancinta mai tsaho da tudu yadan ja

"Karki shanyemin kyauna mana gaba kuma kice na miki tsufa kona miki muni,wannan kallon ki adanashi haka,yana son karya min qwarin gwiwata da hanani cika alqawarin dana dauka,ki cire duk wani shakku ko tantama dake ranki,abinda azeez ya sani kawai shine,yana miki zazzafar qauna har muddin numfashinsa,ba gama garin qauna da kika sani ba wadda kika saba jinya ba a bakin kowa" saiya girgixa kai yana sakar mata wani murmushi na musamman sannan ya dora

"zai kuma ci gaba da qaunarki har ranar da za'a tasheshi a qiyama,shi naki ne har abada,kamar yadda kike tashi har abada" ya sunkuya yayi kissing goshinta kana ya soma takawa zai fice,don dama ya gama shirinsa ne zaije su gana da kakanshi ya tsaya amsar breakfast daga hannunta,kamar yadda yanzu ya zame masa al'ada,baicin komai daga hannun kowa.indai har bilkisun bada kanta ta bashi ba,yakance yafi shiga cikinsa ya xauna yaddda ya kamata.



        Kwanaki goma sukayi cikin dangi me dadi,a kwana goman nan itama taga dangi dangi sun ganta,sun kuma nuna mata qauna da kulawa kamar su riqesu suyita zama dasu karsu tafi,musamman su amatu da suketa daukan hankalinsu,don wani zubin saisu wuni bata gansu ba.



      A kwana na sha daya ya tashi da wayar abdurashid

"To baban soyayya,abun nema ya samu,sai kayi haquri hakanan tunda an cimma buri,kaje ka duba babban kamfaninka,kawai matsala,nayi qoqarin gyara komai amma ya gagareni,dole saika shiga da kanka"

"Naji,kar a sake kirana a irin wannan lokacin" ya fada cikin dakiya yana katse wayar,saiyabar abdulrashid da waya galala,daga bisani kuma ha saki dariya,yarima ne,yasan xai aikata fiye da hakan.



        Kusan kamfanin shine zuciyar duka kamfanoninsa,samun matsalarsa zai iya jawo durqushewar harkokin kasuwancinsa dama shuhurar sunansa,don haka ya maida hankali wajen samawa su bilkisu visa din shiga qasar.



       Randa ya gaya mata sai tace

"Daka barmu mun koma gida,kai sai ka wuce,ka tarad damu a can" wata harara mai kashe jiki ya aikata mata dariya nason qwace masa,yaso ya dago dalilinta na fadar hakan,tanason kasancewa tare da mijinta amma har yanzu nunawa take baya gabanta,batasan idanuwanta da yanayinta na bayyana mishi komai ba,shi kuma ya zuba mata idanu ne kawai yanason yaga gudun ruwanta,to tana ganin kamar ba amfani kenan kasancewarsu tare shi yasa tace ya barsu su tafi shima ya wuce

"Naqi wayon,ai bari kiji.....wannan wata tatsuniya ce asanda nake abdul'azeez dina da bashi ga tsuntsu bashi ga tarko,yanzu kuwa cikakken magidanci nake me iyali,kisa a ranki duk inda na jefa qafata to akwai taki a wajen" idanu ta fidda

"Aikina fa....ka manta da aikina a brazil?" Yana tattare kayayyakin da  sukaci abinci ya bata amsa,don idan dai yana nan kusan shike hidimar yaransa,harma ya hada da nata,abun yana matuqar daure mata kai,yakan zama wani na daban idan yana cikin iyalansa,kai bakace basaraken yariman nan bane,kuma fitaccen dan kasuwa na duniya

"A sanda kike qarqashin umminmu kenan ko?" Sai daya gama hade kayan yakai yara da sukayi bacci daki ya dawo sannan ya kuma dubanta

"Kina tunanin kamata matata zatayi aiki?,aikinma qarqashin wani kodadden bature daya taba sonta?,lallai ko da daga ranar sunana mahaukaci" rasa amsar bashi tayi,kawai saita bishi da kallo,ya dawo da baya ya hure mata idanun da iskar bakinsa.



¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



      Isarsu qasar yasa ya sake zama busy sosai,baida cikakken lokacin kansa ma,yana can yana gyara abubuwa da maidasu kan saitin tsahon lokacin daya kwashe baya cikin kamfanin baya kuma ziyartarsa.



       Hatta da yara sunyi bala'in missing dinsa,sun riga da sun saba dashi,kusan kome shike musu,amma yanzu saidai maminsu tayi musu,wuni suke suna tambayarta shi,saidai ta kira musu shi a waya ta hadasu.



      Lamarin bilkisun nata bashi dariya da kuma qayatar dashi,ita kanta batasan tana nuna mishi fushi da daukewa lamuranshi kai ba,emotio n ne naso da qauna tun daga zuciyarta amma batasan yana tasowa yana tambara kanshi ba,gamida bayyana muraran cikin ayyukanta ba,ita duk a nata zaton tana jan ajinta ne da nuna ko a jikinta.



       Ranar da al'amura suka soma daidaita yayi qoqarin dawowa da wuri saboda yaran,ya cimmata a kitchen tana qarasa hada abincin dare,da yake tunda suka sauka tace tafi ganewa ta dinga musu girki,don haka ya musu siyayyar komai na iya adadin kwanakin da yake saka ran zasuyi cikin qasar.



       Tunda ta amsa sallamarsa saita ci gaba da hidimarta,ya saki murmushi yana aje briefcase din daya shigo da ita,ya taka a hankali zuwa bayanta,ya kama qugunta da hannayensa suka biyun ya mannata da jikinsa.


  

      Kusan tare suka saki ajiyar zuciya,saidai ita bata shiryawa hakan ba,hakan yasa ta sake hade rai

"Yarafa,kada su shigo" saiya dan rabata da jikinsa,ya sanya kanshi a bayanta ya kwantar sosai

"Bugun zuciyarki ya saba da yadda asali,hakan shike qaryata duk wani lafuzzan bakinki da kike furtawa,kina qaryata kanki da kanki ne kawai,koda baki fada ba na sani kema kinji dadin dawowata,right?" Zame jikinta tayi

"Kayine dama saboda yaranka,nasan kuma zasu fini jin dadin hakan,sannu da zuwa" ta fada a gajarce,saiya saketa yana sakin dariyar daya kasa danneta,shi kansa zuwa yanzun yakai bango,ya gaji yana buqatar akai qarshe,hakan ya sanya ya tsara nan da kwanaki hudu zaiyi qoqarin kammala komai su wuce qasarsu su samu isashen hutun da zai bude mata sabbin shafukan darussan madarar soyayya masu wahalar mantawa a duniyar ma'aurata

"Shikenan,bari na tafi inda ake maraba dani" ya fadi yana daukan jakarsa,kamar tace masa ya dawo yaci gaba da tsaiwa da ita amma saita kasa,tana daga kitcen din tana jiyo dararsu da yarab,saita saki murmushi data tuna wata interview da akayi dashi dazu data kalla a tv,kamar bashi ba yanzun,acan zallar kwarjini tsare gida da aji kawai take kallo daga hamshaqin matashin dan kasuwar,amma a yanzu ya koma magidanci mai samawa iyalinsa farinciki da walwala,kamar ba shine na cikin tv din ba,totally dabi'unsa suna burgeta dari bisa dari,wanda ita kanta batasan sa'adda daya shiga rayuwarta har haka ba.

7/11/21, 4:36 PM - My Mtn Number: 79


*_wannan littafin na kudine,kuma bisa amana,fiddashi ko yadashi tamkar zalunci ne_*


*_Allah S W T yana cewa NI NA HARAMTA ZALUNCI ABISA KAINA,KUMA NA SANYASHI A TSAKANINKU ABUN HARAMTAWA,KADA KUYI ZALUNCI!_*


*_Addu'ar wanda aka zalunta bata da hijabi tsakaninta da ubangiji_*

_____________________________

*Ga wanda ke buqatar mallakar nashi,saiya tuntubi wadannan numbers din*


0903Â 234Â 5899

Ko

09033181070






       Tunda suka sauka a nigeria ita kanta tasan ranar ta musamman ce,wani sabon salon kulawa take samu daga gareshi,tsokana yake mata da gayya,kome zai mata zai mata shine in a romantic way,ta yadda zan taba har can cikin zuciyarta.



       Kai tsaye masarautar kaisa suka fara sauka,suka kuma yada zango a sassan fulani aisha,wanda ta shirya musu walima,duk da gidan a dan cike yake sakamakon hidimar bukukuwan sallah da akeyi,akwai baqi a gidan da masu zuwa xiyara su fita.



      Har bayan magariba tana tare da fulani,wadda a yanzun take daukar bilkisu kamar afnan babu wani banbanci,harma tafi gatanta bilkisun akanta,hakan ya qara sanyawa bilkisu ta saki jiki sosai,kuma take mata kallon uwa.



       A wunin ranar ta shiga sassan fulani saratu don ta duba jikinta,har yanzu dai tana nan jiya iyau,ba wani abu daya sauya,komai sai an mata,hatta bayan gida da fitsari a wajen take sai an gyara.



       Abun ya baiwa bilkisu tausayi sosai,me rai ba'a bakin komai yake ba,yanzu kake mutum yanzu kake ba mutum ba,gadai dukiya sarauta da asali duka tana da,amma basu isa su bata lafiya ba,kuma basu hana qaddararta fada mata ba,sai taji tsoron Allah ya sake kamata.



       Baki afnan ta tabe sanda bilkisu ke mata zancan

"Dukkansu abinda suka shuka shi suke girba,itama ashe akwai nata boyayyen abun data aikata sai daga baya nauyin haqqi yasa take fallasa kanta itama,kamar yadda su mama adama sukayi,kinsan idan zunubi da haqqi ya yiwa mutum yawa Allah kuma yaso kamashi da kansa yake tonawa kansa a siri,yanzun haka ita mama adama bamusan ina tayi ba,tuni me martaba ya qara mata wuta da takaddar saki,wanda mu a masarautar nan indai kina matsayin matar sarki kuma akaga ya sakeki lallai kin aikata wani babban zunubi,koda ba'a san meye ba to zai zame miki abun kunya ne sakin daya miki,ba kuma lallai kowa ya aureki ba,baresu da dukka baqin dake cikin gidan nan a gabansu suka fita suna maida magana ita da anti fauxiyya suna ci gaba da tonawa kansu asiri,ita anty fauxiyya an nesantata da masarauta na shekara goma,kamal nacan yana jinya tun daga randa abun ya faru daga qarshe aka gano yana da cutar HIV ne,yanzu meye amfanin irin wannan rayuwar?,shi yasa koda yaushe akeson ka shuka alheri,don ba zaka taba shuka ƙaya ba sannan kace inibi kakeson cira,sam" sosai labarin ya sake kada bilkisu,ya kuma sake zame mata darasi,kusan duk wanda tasan ya aikata zalunci ko wani sharri sai taga qarshensa sakamakonsa baiyin kyau

"Allah kasa mufi qarfin zuciyarmu,kada ka bamu ikon zaluntar kowa dai dai da qwayar zarra" ta samu kanta da furtawa a sarari,afnan ta amsa da amin

"Amin"



       Ba'a wani jima da idar da sallar magriba ba yashigo sassan fulanin,tunda suka dawo yau din yana tare da me martaba a fada,da yammaci kuma suka rabu abdulrashid ya janyeshi,sai yanzu ya samu ya yakice,don ya shiryawa ranar yau din sosai.



       Daf da ita ya zauna har cinyoyinsu na gogar juna,ko kunyar afnan baiji ba

"Ina ammi" tana dan kauda kai tace

"Tana wajen me martaba" saiya maida dubanshi ga bilkisu cikin wani kallo me kashe jiki

"Tashi kawai mu wuce.....na gaji princess,ina buqatar na huta hakanan" kafada ta maqale kamar qaramar yarinya

"Bamuyi sallama fa da ita ba,sannan su amatu suna tare da ita,kaga dole saimun jira sun shigo"

"Nooo....ba wannan lokacin" ya fada yana miqewa yana zura mata wayarta a handbag dinta dake aje gefanta,da sauran kayan da yasan nata ne.



      Dole badon taso ba ta miqe ta gyara yafen mayafinta tana duban afnan

"Muje ki bani ajiyata" batace komai ba ta miqe,saita waiwaya ta dubi azeez dake tsaye yana qare mata kallo

"Zan karbo saqo"

"Minti daya.....karki wuce haka" ya fada yana nuna mata da yatsa.



        "Ungo,gwara ma ku tafi,anaso ana kaiwa kasuwa" afnan ta fada tana miqa mata leda mai kauri wadda fulani ta bata daxu,bata buda ba saboda haka batasan meye a ciki ba,fusga tayi tana jifan afnan din da hararar wasa

"Dama waye yace miki ba'aso din bare akai kasuwa,yafi qarfin a kaishi kasuwa,ko a gidama sai mai rabo" baki afnan ta rufe dariya na kamata cikin jin dadi

"Allah y bada haquri,ashe haka yayan nawa yake da bala'in tsada?" Tana murmushi dayafi kama da 'yar dariya dariya ta soma takawa zata fice sannan ta bata amsa

"Qwarai kuwa,idan baki sani ba gwara ma yau ki sani" dadi ya cika afnan din sosai na yadda ko yaushe soyayyar yayan nata da qawarta ke sake bayyana muraran a idanun kowa.



       Su biyu ne rak cikin motar,bai yarda kowa ya bisu ba,domin yana buqatar kadaicewa sosai,tare da nuna mata ainihin abinda ke ranshi,duk da zuwa yanzu shi kanshi yayi amanna cewa bata tantamar komai a kanshi.



      Hannunshi cikin nata sanda yake tuqin,yana dan murzawa a hankali,wanda hakan ya kuma kashe mata jiki,sai tayi laqwas cikin sit din motar,sanyin ac yana ratsata,ga wani feeling na daban kan mijin nata.



       Juyawa yayi kadan ya dubeta akayi sa'a suka hada idanu,saiya saki murmushi yana maida kanshi ga titi,cikin tattausan muryarsa can qasa kamar wanda ya fara bacci yace

"Ina fata zaki marabceni zuwa sabuwar duniya,zaki jarabtu da soyayyata kamar yadda na dauki tsahon shekaru ina cikin jarabawar taki soyayyar" murmushi tayi tana sunne kanta,saiya dan tsuke fuska

"Princess....wannan kunyar...Allah ya gani zata cuceni,bana sonta wallahi indai a yanayin da muke daga ni sai kene,a rayuwar aurena gaba daya da matata ban rubutata cikin lissafi ba,pls ki barni naci duniyata da tsinke" dariya maganar tashi ta bata,saita rufe bakinta da dayan tafin hannun nata,tana ci gaba da sauraren maganganunsa,wanda babu komai ciki face zallar mayen giyar qaunarta,inda ita kuma suke qara ruguxa duk wani qwarin gwiwa nata,suna sake cusa mata soyayyarsa mai tsananin qarfi.



       Da ido ta dinga bin gidan sanda duka isa,village ya kaita,tun daga harabar gidan yanayinsa ya dinga saukar mata da wata nutsuwa ta musamman,komai anyi qoqarin yinsa ne bisa tsarin qauye da gargajiya,har wani qamshin qasa ke tashi na musamman,duk da dama damina ta soma sauka yadda ya kamata,hakan ya baiwa duk wani tsiro dake gidan damar fidda ainihin kalarsa,duk da dama ko da can kafin daminar haka zaka samu tsirran gidan,sakamakon samun ciakkiyar kulawa da sukeyi daga masu kula da gidan.



       Rungumota yayi zuwa jikinsa,a hankali ya rada mata

"Inason irin wannan nature din,shi yasa nakeson gidan nan,idan ina cikin nishadi indai ina qasar kaisa,nakan zabeshi a matsayin wajen dazan huta" kaita gyada a hankali,itama zabinsu yaxo daya,don lokaci guda gidan ya mata sosai.



       Tunda suka shigi ciki shike jan ragamarta,shike mata komai nata idanu,wanka suka fara yi suka hada da alwala sannan ya jasu jam'i suka gabatar da sallah,doguwar addu'a yayi musu,wadda ta sake ninka mamakinta akanshi,yanayin yadda yake addu'ar kawai ya isa ya shaida maka ya samu ilimin addini dai dai gwagwardo,suka kammala suka shafa,sannan ya waiwayo inda take zaune saman abun sallarta,fuskarsa dauke da fara'a ya matsa gabanta kadan

"Duk da wancan lokacin bamu samu damar yin salla da addu'a ba,har yanxu muna da dama aiko princess?" Murmushi kawai tayi tana tuna darenta a wancan rana,wani irin bahagon dare da bata taba jin koda labarin dare irin nata ba,saiya sanya hannunsa ga goshinta,ya karanto addu'ar da annabi yayi umarni akan kowanne ango ya yiwa amaryarsa.



      Yunwa takeji sosai don bataci wani abun kirki ba,don haka ta langabe waje daya,kamar ya sani ya dubeta

"Muje mu samu wani abu muci ko?,dare na dada yi" ba musu ta miqe tabishi a baya.



       Madaidaicin daining ne me kyau da akayi da wani irin katako na zamani amma an mishi suffar gargajiya,yadda taga an jera akushi saman teburin sai abun ya sake burgeta harta saki murmushi,shi yaja mata kujera daya ta zauna kana yana daga tsaye ya soma sarving dinta da nau'in abinci mara nauyi

"Yunwa fa" ta fada a shagwabe tana shafa plate tummy dinta,ya gane abu me nauyi takeso,saiya girgiza mata kai

"No my dear.....saiya hanamu rawar gaban hantsi....right?" Ya qarasa maganar yana kanne mata idanu,saita dauke kai cikin kunya,don tuni ta baro jirginsa.



       Basu dauki dogon lokaci ba suka kammala,da kanshi ya kaita wani bedroom wanda ta cika fa mamakin tsarinsa shima

"Welcome to my world dear" ya fada yana janta cikin jikinsa,hannayensa saman cikinta

"Anan nake fatan bude sabuwar rayuwa wadda zata jagorancemu zuwa gina wata sabuwar rayuwa cikin sabuwar duniya...."saiya dan zameta daga jikinsa da sauri yana cewa

"Ina zuwa...get ready kafin na dawo" ya fada yana murmushi gami da nunata,bata iya amsa masa ba saboda yadda qafafunta ke rawa harya fita,saita samu gefan gado ta zauna tana qoqarin saisaita kanta.



      "Kin manta ke din ba bilkisu bace shekara takwas baya?,yanxun ke dr bilkess ce,maman 'yan biyu,kuma mata ta aure" zuciyarta ta tunasar da ita,hakan ya zaburar da ita ta miqe ta soma shirya kanta cikin yanayin datake da tabbacin zai faranta ran azeez din.



         Cikin tattausan rigar bacci wadda ta tsaya mata iya gwiwa ta shirya kanta,ta gyara kanta da kyau cikin mayuka da turarukan qamshi data gani saman madubin,kowanne lungu da saqo.na jikinta ta bashi haqqinsa,sai data kusa kammalawa ta tuna da ledar da ammi ta bata,sai kawai ta janyo ta budeta.



      Wadansu irin turarukane designers masu aji tun daga kwalbar ma bare akai ga kudinsu,tun tana kalla a tsaye sai data janyo kujera ta zauna cike da mamaki,ita kadai amma tana jin kunyar kanta da kanta tare da mamakin nau'in turarukan,turare ne na hammata,qasan gwiwar qafa,na gwiwar hannu daban,na bayan kunne daban,na qasan cibiya daban,na matse matsi da cinyoyi,ga wani na gashi shima,harda na mutstsukawa a tafin hannu zuwa yatsu da kuma na jiki gaba daya,sai wata yar qaramar takarda da rubutu da bai wuce layi daya ba.


_kiyi amfani dasu daughter yadda suke,Allah ya albarkaceku_


        A nutse ta bude kowanne ta kuma yi amfani dashi a muhallinsa,kana ta baibaye jikinta dana jikin.



       Ita kanta sai data lumshe idanu tana shaqar yadda jikinta ya game da wani irin qamshi mai ratsa zuciya da qwaqwalwa jiki da bargo gaba daya,ta sauke ajiyar zuciya tana maida turarukan cikin kwalinsu.



       Daidai sanda ta gama ya turo qofar da sallama a bakinsa,sai tayi tsil a inda take tsaye,saboda bataso ya ganta a hakan ba,don ko gashinya bata samu hadewa ba,bayan ta gama feshi shi haka ta sakeshi ta barshi ya bazu saman kafadunta

"Wow....wow" ya fada idanunsa kamar xai fado qasa yana dubanta,saiya kasa qarasowa a hankali ya soma sassarfa,wanda yana zuwa sama yayi da ita gaba daya,sai kuma ya soma shanshanata lungu da saqo a zafafe kamar wani tababbe,cikin wani irin low tune yace

"Ina kika samu turaren da nafiso a rayuwata princess?....na sake yarda na kuma sake tabbatarwa keta musamman ce....kece mahadin rayuwata" tun daga nan ta fuskanci ya soma sakin layi,ba'a rufa minti biyar ba jikinsu ya yiwa qafafunsu nauyi,tsaiwar ta gagaresu,yana riqe da ita ya isa makunnun fitila ya kashe,ya qarasa gefan gadon still ya kunna wata iriyar fitila mai suffar duma wadda take da sauqaqqen haske,kana iya ganin mutum sosai amma ba tarwai ba,ya qarasa saman gadon da ita a hankali ya direta kana ya biyo bayanta.



       Wasu irin xafafan saqonni masu narka tsokar zuciya yake aikata mata,wanda duk inda kakai ga dauriya baka isa ka tsallake musu ba,abinda ya bata tsoro shine yadda tun daga nan bakinsa ya kasa shuru,duk inda hannunsa ko bakinsa yakai saiya yaba mishi kafin ya wuce gaba,ga tsoro ga kunyar yadda yake gaya mata wasu irin lafuzza masu nauyi kanshi tsaye,baiko jin nauyi ko tuna komai,ga wata iriyar soyayya dake son narka mata zuciya,daga qarshe jikinta na rawa ta dora yatsanta saman lips dinsa dake rawa kamar wanda kejin sanyi a hankali tace

"Shshshshsh" saiya dago fuskarta gaba daya ta yadda zai kalleta da kyau,ya nutsa duka yatsunshi cikin lallausan gashinta yana dubanta da birkitattun idanunsa data kasa jurewa kallonsu koda na seconda daya kuwa,kansa ya girgiza,cikin rawar murya yace

"I can't,bazan iya yin shuru ba princess....idan nayi shuru abun zaimin yawa,saina haukace,qwaqwalwata ita kadai ba zata iya dauka ba,keta musamman ce,wallahi keta dabance tun daga nan,na gaya miki tun daxun,na soke wata aba mai haruffa biyar a sanda muke tare wato kunya,saboda nan din duniyarmu ce mu biyu,daga ni saike....ki taimakeni don Allah ki kaini duniya ta gaba..." Shuru tayi tana saurarensa jikinta na tsuma,wasu irin hawaye masu dumi na farinciki suna silmiyo mata,bata taba kawowa ko a mafarki rayuwar zata juye musu haka ba ita dashi,bata taba kawowa lokaci zai sauya komai ba a tsakaninsu,harsu sake zama qarqashin inuwa daya ba,a sanyaye idanunta a lumshe ta gyada masa kai,saiya soma jera mata godiya yana sanya harshensa saman fuskarta yana dauke hawayen dake kai,daga bisani kuma taji ya sake kunna daya daga cikin qayayen dakin,hasken ya qaru duk da baikai na farko ba,saita bude idanunta da sauri,ta sake maidasu da sauri ta rufesu saboda kunyar ganinsa da taji ta kamata tana girgiza masa kai alamun ya kashe qwan,saiya girgiza kanshi

"Am sorry my princess,wancan karon a wancan ranakun baki ganni ba,ki bari a yau a yanzu ki ganni,ki ganni a yadda nake,ki ganni a abdul'azeez dina,ta yadda zamu sake sanin juna dakyau,ta yadda zaki sake yarda nidin a wajenki ba kowa bane,ta yarda zai sake yarda cewa idan ina hannun bilkisuna ni ba yarima bane,ba dan kasuwa bane,ba kowa bane face bawa wanda sai yadda taso zata juyashi" kai ta girgiza,har yanzu jikinta rawa yake a tsorace take 

"Kayi haquri ka kashe,duka na yarda duk abinda kakeso na yarda dashi din" dole ya rage din kamar yadda ta buqata,kana ta sakar masa ragamarta ya kaita duniyar data manta da kalarta,ta kuma.manta da yadda ake shigarta,sai gashi a wannan daren ya tuna mata da komai,ya tuna mata da wani abu da tayi tsammanin ya faru bazai kuma maimaituwa cikin rayuwarta ba kenan har abada,sai gashi ayau komai.ya dawo sabo fil tsakaninsu.



       Shi kansa yasan ba qaramar juriya da jarumta ta nuna ba,saboda shi kansa baisan yawan bashin daya tarawa kansa ba saida akazo wajen,saboda tashin hankalin tunanin rasata daya shiga ya bunne dukkan wani feeling nashi,nutsuwa da kwanciyar hankalin daya samu yanzu suka dawo da komai sabo,hakanan itama ta nata fannin ta tsorata da lamarin,sai taga ashe a wancan karon imani da tausayi kawai ya nuna mata sabanin yanzu data ji a ajikinta bakin gwargwado.



      Washegari duk wani bashin tarairaya da kulawa da a wancan lokacin ya bar mama sodangi dashi sai daya bashi kaf,tamkar darensu na farko haka ya lalace wajen kula da ita,ita kuma ta baje kolin shagwabarta son ranta harda mara dalili ma,kwana daya rak ya ida daga mata qafa,next day ya kasa haquri yace shifa saiya koma,babu yadda ta iya haka ta bashi dama,a washegari tayi tunanin zasu je su koma gida amma sai taga shi zama ma kamar lokacin ya fara,data masa qorafi sai kawai ya kalleta,ya miqa mata hannu a hankali ya mata masaki zuwa jikinsa saman cinyarsa sannan ya bata amsa

"Nifa bazan rayu cikin jama'a ba dake,saboda zan iya barin abun magana,sonki yamin yawan da bazai barni na iya katabus ba,koda xamuje musun ma keda fita daga gidan nan saikin goge,kin zama 'yar hannu qwarriya irina,so nake mafa idan mun tashi fita mu fita da tsarabar wasu twince din wa ammi,naga alamun tana buqatar jikoki birjik,tunda du wadan can sun tsaya gayun banza da wofi,basa haihuwa sai bayan wasu shekaru" kunya ta sanyata kwantar da kanta saman kafadarsa tana murmushi

"Amma su amatu fa?" Kanta ya dungure da dan yatsanshi

"Kajimin yarinya,an gaya miki su suna ta tamu ne?,affy ta gayamin ko tambayarmu basa yi sun xama 'yan gida,kina tunanin ma ammi zata bamu su?,gwara ma ki dage ki samo mana namu eheeennn...." Saiya tura hannunshi cikin rigarta,tasa hannu da sauri ta dafeshi tana turo baki

"Haba mana princess,dan kadan fa,yaufa sau daya na É—ana" saiya shiririce mata,yadda ta bada kai da kanta ba tare data shirya ba.



       A ranar ya turama safwa sakinta,tare da rufe dukkan wani babi nata,dama nutsuwa yake son ya sake samu,yana sane da rashin albarka da suka sake yiwa amminsa bayan tafiyarsu cikin azumi data aika ma safwan da kayan buda baki da sunan azeez din,abinda yasa yaji har zuciyarsa koda itace autar mata ya barta kenan.



       Cikin kwanakin gaba daya basu da aiki banda suci susha su kwanta,sai hirarrki da bitar rayuwar kowa,kowa yana baiwa dan uwansa labarinsa tun daga quruciya xuwa girma.



        Labarin rayuwar bilkisun ya karya masa zuciya,ya qasa sanyashi jin cewa zafi ko sanyi,wuya ko dadi babu abinda xai rabashi da ita,ya sake jin cewa ita din tashi ce,haduwarsu wata rubutacciyar qaddara ce daga Allah.



       A zaman nasu kowa ya dinga qoqarin fahimtar dan uwansa,bawai bare baki sukayi akayita xuba soyayya tsurarta ba,tunda suna sane da cewa zomu zauna zo mu saba,kuma rayuwar yau zaqi ce gobe madaci,hakanan indai xa'a zauna tare dole wataran za'a samu sabani fada ko rashin jituwa,hakan ya sanya kowanne ta wani fanni yake qoqarin fahimtar ra'ayi zabi da halayyar dan uwansa domin wanzar da zaman lafiya a rayuwar aurensu.



       Duk hankalinta yana gida,tanaso ta samu 'yan uwanta maza kamar yadda tayi alqawari bayan ta dawo,hakanan tanason zuwa taga anty zuhriyya,duk kullum Allah sai sunyi waya,amma tana son taje ta ganta,don ba qaramin kewarta tayi ba.



        Da qyar randa suka cika kwana goma cikin gidan ta lallabashi ya amince xata,amma qafarta qafarshi,tace ta aminta.



        Cikin daya daga cikin sabbin motocinsa dabai taba hawa ba samfurin wannan shekarar suka fita,daga ita saishi sai driver ba tare da rakiyar kowa ba.



       A mota yayi xamanshi,yace idan baba yana nan ta mishi magana ya leqo su gaisa,idan kuma bai nan shikenan ta gaida mutanan gida,ta samu malam.bilyan ya dan samu ya fita miqe qafa,umma katti ta aika kan ya shigo ko ruwa yasha amma yace aa,dole suka barshi.



      A zaman da tayi dasu ta yanke bude manyan shaguna kowanne dai dai qari akan na mahaifinsu,saidai wannan dinma zai xama kamar qarqashin na malam bilyamin dinne ta wata fuskar kuma kamar nasu,zasu dinga raba ribar da aka samu gida uku,su baiwa malam bilya daya daya su su riqe bibbiyu,uwar kudin kuma a sake juyata.



        Hakan ya faranta musu matuqa da gaske,basu taba zaton a rayuwa bilkisun zata musu rana irin haka ba,kudaden data fadi zata zuba cikin kowanne shago kawai ya gaya musu ba qarami shaguna xata bude ba,sun nemi alfarmar ta tayasu da addu'a,Allah yayi riqo da hannayensu.



        Daga nan gidan anty zuhriyya ya kaita,ta dinga dariya hannunta riqe da bakinta

"Anya bilkisu wannan komawar itama ba wani rabon ne yayi kira ba?,kinga yadda kikayi mulmul kuwa?,wannan soyayya da yarima ke baki karta sangartaki da yawa" maganar ta sata kunya sosai,tadanfi jimawa wajen anty zuhriyya suna tattaunawa da kuma sauran shawarwari data qara bata,sannan sukayi sallama tare da uwar tsarabar da yarima yasa aka shigo da ita kamar yadda aka kai gidansu,wanda duka batasan dasu ba.



       Basu fita a gidan sunje masarauta ba sai da suka kwashe wata guda a gidan,duk da shi yaje ya amsa kiran me martaba,wanda ya dinga fada kamar zai cinyeshi danye kan sakin da yayiwa safwan

"Allah ya huci zuciyarka,banda wani sauran zabi tunda ta nuna ra'ayin bata da sauran sha'awar zama dani,ban isa na mata dole ba,sannan babu wani goyon baya daga wajen magabantanta,suma bamu da ikon tilastasu su bamu diyarsu" wannan furuci nasa yasa fafan baiyi wani dogon zango ba

"Aure rai gareshi,saikaci gaba da addu'a idan da rabo.nan gaba za'a koma dole"

"Rabbi kasa bai cikinnqaddarata har abada" ya fada can wasan zuciyarza ba tare daya bari.me.martaba yaji ba,ita kuwa fulani banu a inda tace banda

"Allah ya kyauta,yasa hakanne mafi alkhairi" dariya yaso qwace masa,bai taba tunanin akwai lokaci da zaizo hakan ta faru ammin ta dauki abun da sauqi har haka ba.



      Randa xasu gidan murna kamar bilkisu tayi me,shi kuma ya dinga hade rai,harsai data tambayeshi cikin salon tsokana tsokana

"Da kaje za'a isheka da gaishe gaishe tun daga bakin qofa,ko ina ma'aikata birjik,kuma kome kayima iyalinka saiya wani zama abun kallo,kamar kaidin ba mutum bane kamar kowa" dariya ma ita ya bata

"To ai laifinka,kune idan kuka shiga mutane saiku ishesu da hada gira,ku cikasu da kwarjini,kaga kuwa duk abinda xakuyin zai xama sabo a wajensu" damqa yakai.mata

"Zaki to kuwa jawo a fasa zuwa,tunda kinama goyon bayansu ne" a shagwabe ta kama kunnuwanta da hannayenta biyu

"Tuba nake yallabai,ayimin afuwa,inason naje naga mamata ammi".



        Sanda suka isa sassan fulani saita kasa sakewa kamar baya,nauyinta da ada takeji yanxun ya sake daduwa,datace mata

"Baqin haura katanga,babu sallama saidai a lalubeku sama ko qasa a rasa" kamar xata tsaga qasa ta shige haka taji,afnan ta soma taya ammin bilkisu ta jefeta da harara,qasa qasa tace

"Kici gaba,dab nake da tona asirin soyayyarku da baturen likita adamu wajen yayanki" saita kama hannunta da sauri ta riqe tana fadin

"Tuba nake antyna,kimin rai,karki ballomin ruwa,ki bari komai ya gama dai daita don Allah".



       Yadda afnan ta fada kusan hakanne,su amatu yaran ko a jikinsu,sunata shagallensu a gidan,suna zuba shagwabarsu son ransu,'yan gata tako wanne fanni,baga ammin ba baga me martaba ba baga sauran jama'ar gidan ba,wanda rashin fulani adama a gidan da lalurar fulani saratu yasa da yawa da basu gane alkhairinta ba wadanda abaya basa jam'iyyarta yanzu ta zama tasu,sun gane ashe a baya bautar banza kawai suke a inda ba'asan qima da darajarsu ba.



       Ranar sunsha hira sosai da mama sodangi irin wadda suka jima basuyi irinta ba,batasan tayi kewarta ba sai a sannan,zataso a bata mama sodangi su zauna tare,saboda matar tayi tako ina,amma.batasan ya yanayin tsarin nasu yake ba,batason ta cika azarbabi da yawa.



¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶    ¶Â¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶Ã‚¶



     Tare dasu akayi bukin babbar sallah na bana,fulani ita ta sake zama cikakkiyar me masaukin baqi,ta karbi kowa babu banbamci,kama daga yaran adama dana saratun gaba daya,abinda ya sanyayar da gwiwar yaran,suka soma sauya tunani a kanta,tare da sare kaso mafi yawa na qullaci da qiyayyarta da aka dasa musu cikin zukatansu,musamman yaran fulani saratu wanda sun jima da fara saduda,ganin yadda bata bari mahaifiyarsu ta wulaqanta ba daga wajen jama'ar gidan ko mijinta ba,tana bakin qoqarinta wajen ganin ta samu kulawa yadda ya kamata.



       Hawan sallar na bana ya bada qaye sosai,tawagar yarima da abdul sunfi kowacce tawaga daukar hankali jan magana da jawo cecekuce,a ranar ko cikin gidan duk inda ka gifta hirarsu ake,saboda kome iri daya suka sanya,sai suka tashi kamar hassan da usaini,banbancin kawai shekaru ne.



       Hutun sati guda kawai da bukin sallar ya tashi komawa bakin kasuwancinsa,sanda yake shaidama ammin hade ranta tayi tsaf

"Wai kana nufin na debi yaran nan na baka kuyita yawo dasu,baku nan baku can?,tab....a'ah wallahi bada ni ba,kudai kuje saikun dawo,duk sanda kuka waiwayomu ku kuka jiyo,amma bada jikokina ba".



      Koda ya shaidama maimartaba shima bayan ammi ya goya,don shi kansa yaran sun shige jikinsa da zuciyarsa sosai,duk da yana qoqarin boyewa saboda sauran jikoki da kuma idanun al'umma,amma dole wani abun bazai boyu ba,don abudul har kujera guda aka masa kusa data me martaba cikin fada a madadin mahaifinsa,sau tari dashi ake zaman fadar,don dole ya haqura suka soma shirin tafiyar shida bilkisunsa.



      Kafin tafiyarta sai data tabbatar an gama kome na kasuwancin yayyenta,malam bilya wannan karan kasa jurewa yayi sai daya saka kuka,yadda ya riqesu a baya da abinda yayi ya dinga masa ciwo,da qyar ta kwantar masa da hankali.



       Tun cikin jirgi ta soma jin wani zazzabi na cikin qashi,yarima nata zolayarta dako qwallonshi ya shiga raga ne?,sai tsoro ya kamata saboda tuna azabar da tasha laulayinsu amatu,amma kuma kwana biyu da isarsu data huta taji ta warware sai hankalinta ya kwanta,ta dinga ma yarima daya qwallafa rai gwalo tana cewa

"Dama ni nasan babu wani abu" kaman yayi kuka don har ranshi yaso ace ta kamu ne

"Bari murna yarinya,don ni jikina ya bani,kuma na riga da nasan nayi winning" tana sheqa masa dariya tace

"Shikenan zamu gani ai" qaramin ya tsansa ya miqo mata

"Mu daura....duk wanda yayi winning a tsakaninmu zai sadaukar da wani abu ma dan uwansa"

"Na yadda" ta fada tana miqa masa yatsarta tana dariyar mugunta.



        Saidai kuma tun ba'ayi nisa ba ta fuskanci yariman nata ya riga da yaci gari,sai taja bakinta ta tsuke tana tsoron tsiyar da zai mata.



          Saida laulayi ya soma tabata ya debe ta suka nufi asibiti sannan komai ya bayyana,murna kamar ya maidata cikinsa haka ya dinga zumudinsa tana kallonshi,ji yake kamar ya lasheta,godiya ya dinga zuba mata kamar ita ta baiwa kanta,kula sosai ta samu daga wajen likitoci da nurses din,wanda hakan ya sauqaqa mata wahalar laulayin ba kamar nasu amatu ba.



       Baice mata komai ba saida suka dawo gida,bayan sun samu nutsuwa ya miqa mata hannu

"Alqawarina....me za'a sadaukarmin?" Saita langabe kai a shagwabe

"Pls mana (Ameer),ban da lafiya fa?" Dariya ta qwace masa,yadan mintsini cinyarta,saita sake masa kukan shagwaba gaba daya tana fadawa jikinsa,ya sanya hannayensa kuwa ya tattareta gaba daya cikin jikinsa yana sake shagwabata

"Abu daya fa,abu daya fa baby zaki bani" ta sake tura baki gaba

"To meye?" Sai daya dagata sosai ya zaunar da ita saman cinyarsa,idanunsa cikin nata,ya sanya tafin hannunsa tsakiyar nata

"Rayuwarki nakeso ki sadaukarmin,ki mallakamin rayuwarki,kome runtsi kome wuya ki zama a tare dani" qayataccen murmushi ta saki wanda ya bayyana jerarrun fararen haqoranta

"Wannan ai tsohon alqawari ne tsakanina dakai ameer" kai ya gyada

"Yes na sani,amma wannan na musamman ne" saita kama hannunta ta dora saman qirjinta

"Allah ya zama shaida haka zuciyata cewa na mallaka maka komai nawa,idan nace komai ina nufin komai din" qanqameta yayi sosai cikin jikinsa,yana jin kamar yafi kowanne namiji sa'ar mace a duniya,kamar yafi kowa sa'ar samun soyayya.



        Wannan cikin kusan tare sukayi rainonsa,ya kasa shuru sai daya shaidawa amminsa,wanda tsananin murna ya hanata sukuni,ba yadda bata so ya dawo da ita gida ta zauna da ita ba amma ya toge,hakan yasa dole ta shirya mama sodangi ta bisu.



       Hakan ya farantawa bilkisu rai sosai,saita kuma sakewa abinta,tana jin kamar wata uwace a tare da ita,zamansu da mama sodangin kamar wancan karon,cikin girmama juna nishadi da walwala.



      *_BAYAN SHEKARU BIYU_*




     A hankali riqe da hannu juna suke takowa zuwa sassan mahaifiyarsu mahaifiya ga kowa dake cikin masarautar,jarumar mace mai cike da sanin ya kamata,jajirtacciya mai qoqarin kamanta adalci kan kowa kamar yadda ta kurba wannan halayya daga wajen maigidanta wato fulani aisha.



      Mutum biyu da suka kasance taurari,abun kwaikwayo,kuma tamkar zuciyar masarautar kaisa wato *_bilkisu bilyamin_*  da *_yarima abdul'azeez abdallah mu'az kaisa_* su suka samu tsaiwar mutane da dama makusantansu da suke maraba da zuwansu,bayan shudewar shekara guda basu tako qasar ba,sakamakon wani gagarumin aikin fadada kasuwancinsa daya riqe a zeez din a gurare da dama,ya hanashi shigowa masarautar kaisan,shida mai dakinsa da akoda yaushe take kamar aljihunsa,don idan kaga zara tabbas zakaga wata.



        Sarauniya kuma uwargida bilkisu sanye cikin wani material na alfarma kuma na musamman da aka masa dinkin riga da zani da yalwataccen mayafi,sai wasu takalma masu tsinin dunduniya masu madauri,hannayenta saye da wasu banguls masu kyau da nuna alfarma masu hade da zobuna qwaya biyu,sai yar hand bag dake maqale a hannunta wadda ta shiga da kayan jikinta.



      Kallo daya zakayi mata ka tabbatar ta gama zama cikakkiyar mace mai cikakken aji ilimi da sanin ciwon kai,fuskarta fadade da fara'a take gaisawa da kowa,yayin da gogan nata yarima ke gefanta sanye da wasu suit da suka dace da matsayinsa da tsarinsa,shi dinma ya sake zama wani cikakken mutum da kwanciyar hankali shekaru da nutsuwa suka ratsashi,yanata shafan sumarshi yana satar kallon ammi wanda yasan ta cika fam dashi.



       Daga bayansu kuma mama sodangi ce dauke da wasu kyawawan yara guda biyu,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan identical twince ne zubin masarautar kaisa kamar yadda su amatu suma suka dauko gida,yarane masu ban sha'awa da birgewa 'yan kimanin shakaru bibbiyu sanye da suit suma na yara,daya na kafadar mama sodangi da alama bacci ne ya daukeshi,dayan kuma na riqe a hannunta yana takawa da qafarshi,ita kanta mama sodangin kallo daya zaka mata ka karanci qarin samun canji da kuma ci gaba a rayuwarta.



      Sosai ta kalli sashen da wata mata ke tsaye wadda keta faman sunne kanta da mayafi,data lura sosai sai taga ashe umma luba ce,murmushi ta saki tana qarasawa inda take ta soma gaisheta,cikin diriricewa ta hau amsawa,sai bilkisun tayi qas da murya

"Komai ya wuce ya kuma zama tarihi,ya kamata ki manta kema" daga haka tayi gaba,wanda maganar ta sanyaya jikin umma luban,ta kuma samu nutsuwa fiye da da a zuciyarta.



      Sannu sannu suka wuce dukka jama'ar har suka dangana da falon da babu kowa,daga su sai fulanin saisu da yaransu,ta miqa hannu ta amshi ahmad dake bacci daka gun mama sodangi,ta kama hannun muhammad ta jashi shima zuwa jikinta

"Sannu da qoqari sodangi,Allah ya saka da alkhairi,kunsha hanya,ki qarasa masauki ki huta" murmushi ta sake

"Babu komai Allah ya taimakeki,inajin kamar ina yiwa yarana na cikina ne,ammm mun miki laifi,shi yasa nadan tsaya mu bada haquri" murmushi fulani ta saki tana jefawa yarima harara

"Baki da laifi ko daya adama,rabu dashi ki tafiyarki" cikin girmamawa tace

"Toh,amma dai duk da haka muna neman sassauci,na barku lafiya" ta juya tana murmushi ta fice daga falon.



       Waiwayowa fulani tayi tana jifansa da harara bayan ta samu kujera daya ta xauna tana kwantar da mahmud ta dora muhammad saman qafafunta

"Mara gaskiya dama ko a ruwa gumi yake,sannunka da qoqari abdul'azeez,da kana nufin zaka hanata zuwa bikin qannenta har biyu da taka qanwar kenan?,saiyau ranar dinner sannan kaga damar tahowarku,baya ga haka shekara guda baka leqo kaisa ba,to indai zaka ci gaba da hakan ba shakka zaku koma ne babu su mahmud,gwara suma su zauna wajena" kanshi a qasa cikin rusunawa yace

"Afwa ammi,in sha Allah na miki alqawarin hakan bazai sake faruwa ba"

"Yafi maka dai" ta fada tana miqawa bilkisu hannu,sai itama ta miqa mata sukayi musabaha kamar yadda suka saba,tun tana kunyarta harya zame mata jiki,cikin murmushi da nuna kulawa take mata maraba sannan suka fara gaisawa,kullum kwanan duniya qimar bilkisun da iyayenta sake daduwa suke a idanunta,bama kamar yanzu data zama silar haduwar auren dr adam da afnan dinta

"Ammi ina amaren suka shiga ne?"

"Tana can sassan baya ita da qawayenta" saita miqe cikin zumudi

"Bari na gansu" da haka ta fice ta basu sarari ita da azeez din.



     Tsalle afnan ta daka ta daneta

"Karki jimin ciwo amaryar dan bature" ta saketa tana cewa

"Harna soma fushi da ya yarima wallahi"

"Au hakama kikace?,saina koma,da ameer din nawa zaki fushi"

"To matar amir,ayimin afuwa" sai suka saki dariya a tare tana tambayarta shirye shirye tana laluban wajen zama.



      "Wai bilkisu ce wannan?" Cewar wata mace dake xaune da yaro a cinyarta,duka suka waiwaya tana murmshi bilkisun tace eh,afnan ta qaraso

"Baki ganeta bane?" Kai bilkisu ta kada mata

"Farha ce fa,ga halima kuma" ta fada tana nuna mata su,cikin farincikin haduwa dasu suka fara gaisawa,kowacce cikinsu kallon bilkisu take tana qarawa,tare da mamakin yadda Allah ya sauya komai,har farha ta kasa daurewa sanda bilkisun ta musu sallama kan zata leqa gida taga ya shirye shirye suke saida ta tambaya afnan

"Ikon Allah ne,Allah ne ya hadasu bani ba" itace amsar data bata.



       Yanayin da bilkisun ta samu gidan nasu ya mata dadi sosai,kallo daya zakawa gidan kasan suna cikin wadata,yayunta sun tsaya sosai kan gidan,Allah kuma ya akbarkaci kasuwancinsu qwarai,don yanzu malam bilya yana gida ne kawai yana hutawa,bayaga gini na alfarma da aka buge gidan aka qara masa girma akayi.



        Sai data gama duba komai ta tabbatar babu matsala sannan ta kebe da amare hannatu da hauwa'u suma ta tabbatar basu da wata matsala sannan ta sake dawowa cikin gida aka shiga hidima sosai da ita,tuni aka soma shirye shiryen tafiya dinner wadda fulani ce ta dauki nauyi aka hade duka data afnan,bilkisun nata tsokanar hauwa'u da amaryar assadiq,itadai batasan ya akayi na,sai da za'a amshi kudin aurensu sannan ta samu labarin shi ya samu nasarar dauke kuluwar tata.


       Tun kafin a tashi daga wajen dinner din tasa aka dawo da ita gida saboda tasan halin yarima sarai,duk da ta gama sakankancewa zata kwana a gida ne,hakan yasa su ahmad ma wajen umma katti ta barsu,taji dadin zuwan saboda sun tattauna sosai da anty zuhriyya,yanzu haka duk dawainiyar yaran ta karatu ta daukewa abbaa shi,duk da yana da qarfin dauka amma tana tuna zallar halaccinsa shi da umman tata,wanda bata da abun biyansu,anan taji zancan kawowa najwa kudi da akesonyi cikin satin,taji dadin hakan sosai,don tasan tana nan kenan za'a kawo din.



       Saida driver dinta yana sauketa taga motoci a fake kamar na yarima,tayi mamakin me zai kawoshi goma da rabi na dare nan,tunda tasan dole zai barta ta kwana,sai gobe zata koma masarauta,saidai tana fita a motar aka bude daya daga cikin qofofin motar,a nan ta fahimci yariman ne,don haka ta doshi motar sannu a hankali.



        Sit din gaba ta bude kamar yadda ta fahimci shike jan motar da kansa,tana shiga kafin tace komai ya rufe qofar ya kuma tashi motar da gudu yana barin layin,baki sake take kallonshi

"Abban amatu....ya haka?" Fuska a hade yadan dubeta sannan ya kauda kai

"Kamar yaya fa?"

"Ni da zan kwana gida kuma ina zaka kaini?"

"Ni kika tambaya nace na barki?,ina cewa ammi kika tambaya ko?" Zata sake magana ya dora hannunsa saman labbansa 

"Shashshsh" sai tayi shuru bata yi maganar ba kamar yadda ya buqata,amma kuma fuskar nan a hade tana zumbura baki.



     Motar ta dauki shuru na wasu mintuna,sai kuma ya saki nannauyar ajiyar zuciya,kana ya miqa hannunsa daya ya danja hancinta

"Cikin kowanne yanayi kyau kikemin,princess kema kinsan ba yadda za'ayi muna qasa daya gari daya na iya kwana babu ke a gefena,bazan iya barinki kwana ko inaba,idan nayi hakanma na tabbatar bazanyi bacci ba a ranar,ki gafarceni,kinfi kowa sanin haka nake".



      Ba shakka gaskiya ya fada,tafi kowa sanin halayyar yarima akanta,baya iya jurema rashinta ko qaqa,tun bata saba ba tana qorafi harta saba,anty zuhriyya tasha gaya mata hakan wata daraja ce a wajen mace,wata da wanzuwarta da babu duka dayane wajen miji,sai a yanzun take sake gasgatawa,kafin tace wani abu kuma taji sautin muryarsa kamar me qunquni yana cewa

"Idan kuma abun hakane kawai saina sake lalubawa ko zan samu wadda tayi koda kwatarki ce na samu na dinga ragewa da ita tunda nan an fara gajiya dani".



        Harara ta jefa masa mai tafe da kallon so,sai ta fasa mishi kukan shagawaba,ba shiri yayi parking ya hau lallashi,sai data ja ajinta abinta son ranta sannan tayi shuru,ya sauke ajiyar zuciya duk da yasan na wasane amma baya fatan wata rana tazo dazai bata mata da gangan tayi kuka kansa irin haka

"Kin dagamin hankali fa" murmushi ta sake masa

"Afuwa nake nema,bana fatan na zama silar hakan a rayuwarka" yana shirin sake tada motar yace

"Na sani,amma duk da haka yau saikin biya bashin wannan kukan da kika saka na bata lokutta ina lallashinsa,a daren nan ina buqatar qarin twince,dukka yammata pls" murmushi ta kuma sakewa tana sake jin sabuwar qaunarsa,bata taba ganin mutane masu son yara irin jinin fulani aisha ba,duk da yadda ta gaji amma batajin zata iya hanashi yayi yadda yaga dama da rayuwarta

"Baka da case in sha Allah,afnan ta gayamin har yanzu jikokin basu ishi ammi ba" saiya waiwayo cikin fara'a yana dubanta

"Na dade da sanin bilqeesa ta jaruma ce,ina fata Allah yasa yarana su dauki halayyarta,yasa kuma ta zama min uwargidana har a aljanna" hannyenta ta daga sama alamun addu'a

"Nima fatana kenan,Allah ya barmin yarimana har a aljanna...." Tun kafin ta qarashe ya cafe ya amshe da amin,hakan harya baya dariya shima ya biye mata yana tayata cike da zallar qaunar juna da farincikin rayuwa.




*TAMMAT WALHAMDULILLAH*🥰🥰🥰🥰


_Anan na kawo qarshen wannan littafi nawa na siradin rayuwar bilkisu,ina fata Allah ya yafemin dukka kura kuran dake ciki,ya hadamu a ladan_



_duk inda akace zo mu zauna zo mu saba,ina neman afuwa ga duk wanda na sabawa kona masa ba dai dai ba,ta hanyar lafazi ko aiki,zan iya cewa ajizanci ne irin na dan adam,da fatan zaku gafarceni,Allah ubangiji ya sadamu da rahamarsa,yasa idan muka tsaya gabanshi zamu tsaya ne don amsar lada da kyawawan ayyukanmu,ba domin tuhumar juna ba_🤲ðŸ½Ã°Å¸¤²Ã°Å¸½Ã°Å¸¤²Ã°Å¸½



_ina mai barar addu'arku da bakunanku masu albarka kan wata buqata tawa,ina fata ubangiji ya cikamin ita alfarmar ma'aiki S A W nida sauran dukka al'ummar musulmi_



_Saqon jinjina da godiya ga mabiya ZAFAFA BIYAR 'YAN AMANARMU wanda kullum basa gajiya da patronizing dinmu,ubangiji yaci gaba da buda muku da yauqaqa arziqinku,yabarmu cikin amana da aminci_



_muna muku fatan alkhairi,sai haduwa ta gaba idan ubangiji mai kowa mai komai ya yarje mana lafiya da tsahon rai,haqiqa muma zamuyi kewarku🥰🥰🥰_



_SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASHHADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'A TUBU ILAIKA_🤲ðŸ½Ã°Å¸¤²Ã°Å¸½Ã°Å¸¤²Ã°Å¸½Ã°Å¸¤²Ã°Å¸½Ã°Å¸¤²Ã°Å¸½Ã°Å¸¤²Ã°Å¸½



©ï¸Ã‚®Ã¯¸ *ZAFAFA BIYAR 2021*


No comments