Saran Boye Complete Hausa Novel

 

[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*


2
       *_SARAN ƁOYE!!_*


  *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

..
*_ƊANƊANO DAGA ZAFAFA BIYAR 2021_*


No. 1

...........Tun a farkon shigowa anguwar zaka shaida lallai ana biki, musamman da gidan da ake taron ya kasance shine na biyar a farkon shigowa layin. 
      Cike titin layin yake da yara da ƴammata harma da manya maza da mata. Musamman a cikin babban haraban massalacin dake manne da katafaran gidan da tun daga kallon gate ɗinsa zaka san ya wuce raini a gine da yalwar girma. 
      Rumfunane guda uku a tsaye, waɗanda gaba ɗayansu an cikasune da fararen kujeru bisa tsari. Rumfar farko cike take da manyan malamai masu faɗa aji a ƙasar dama wasu ƙasashen ƙetare musamman na musulmai. Rumfa ta biyu kuwa matane zalla a cikinta tundaga ƙanan har zuwa manya. Rumfa ta uku mazane suma manya da yara.
      Babban abin birgewar da ƙayatarwar shine shigar kamala da mutunci dake tattare da jama'ar wajan. Duk da taron bikine kowa ya suturta jikinsa, babu wani mai shigar ALLAH wadai ta nuna tsiraicin da ake laɓewa da sunan biki.

       Duk da cikar da wajen take da shi hakan bai hana yawaitar mutane a cikin gidanba shima. Lallai da gaske gidan babban gidane, dan a kallo ɗaya zaka fahimci gidan family house ne, dan kuwa yafi ƙarfin mallakar mutun guda kai tsaye. Daga jikin gate ɗin gidan zaka iya ganin dukkanin yawan ɓangarorin gidan da aƙalla zasu iya kai sashe biyar zuwa shidda, ginin iri ɗaya ne babu wani banbanci game kallo da ga nesa, saika shiga daga cikine ka fahimci kowa da kalar tsarin da yafi buƙata a nasa sashen.
          Lokacine bana banbance minene a cikiba, ko mi aka tsara. dan haka nabi ayarin mutane masu kai kawo zuwa sashe na biyu da yafi ɗaukar jama'a. Kasancewar duk mutane na a harabar masallaci wajen da za'a gudanar da walima ya bani damar kutsa kai har cikin ɗakin da naji ana masa ishara da amarya na ciki.
         Ƴammata ne da a ƙalla zasu kai goma zuwa sha a ciki, kowacce nata ƙoƙarin ƙimtsa jikinta dai-dai buƙatarta cikin doguwar riga milk color mai adon golden ɗin furanni da aka ƙawata da stones a gabanta da ƙarshen hannun. Hirarsu suke da dariya har baka iya jin mi wani yake faɗa. 
          “Oh ALLAH, Aure mai saka kowa hankali. Su o'e tunkan Yah Ab.. Yaci ƙaniyar bakin harya mutu haka?”. Ɗaya daga cikin ƴammatan dake naɗa ƙaramin golden veil a kanta ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya. Kusan a tare duk suka juya suna kallon wadda ke kwance saman gado ita kaɗai ta juya musu baya, kwance take rubda ciki da ɗaurin ƙirji sai ƙaramin hijjab a jikinta. “Hhhhh! Wlhy kuwa Iman, kinga dai bakin tsiwa tun jiya ya mutu”. Wata tabama mai maganar amsa tana dariya itama da ƙarasawa jikin gadon, yayinda suma sauran suke dariya suna nufar gadon. Sai da suka zagayeta sannan suka haɗa baki wajen faɗin “Gobe zata fashe!!!” tare da ƙyalƙyalewa da dariya suna tafawa.
             Ƙaramin tsaki wadda ke zaune can gefen mirror tana kwalliya taja tare da taɓe baki, taɗan hararesu idanunta cike da ƙwalla, cike da fushi ta ajiye hodar da take shafawa ta fice daga ɗakin.
          Bama susan tanayiba, dan sukam hankalinsu nakan amarya suna cigaba da mata ihun “Gobe zata fashe!! Gobe zata fashe!!!”. Faɗi suke da ihu sosai suna dariyar tsokana irinta ƙawen da ƙuruciya ke ɗawainiya da su, dan gaba ɗaya yarane ƙanana da bazasu wuce 16-17 ba.
       Hawayen da tun ɗazun take haɗiyewa ne suka silalo saman kumatunta a hankali. Bata motsaba, kamar yanda bata buɗe ido ta kalli ƙawayen nata dake mata shaƙiyancin ba. Ita kaɗai tasan mi takeji a ranta tun daren jiya. Tabbas wannan ranace data daɗe tana fatan zuwanta itada masoyinta Yah Abdallah tun bata gama sanin ciwon kanta ba. Sai dai batasan miyasa tunda aka shiga satin bikin jikinta yay sanyi ba kuma. Tasan hakan bazai wuce nasaba da sabuwar rayuwar da zata wayi gari a cikinta gobe idan ALLAH ya kaimu ba. Ta sake matso hawayen masu zafi tana jan ajiyar zuciyar da har jijiyoyin wuyanta saida suka miƙe...........
           “Ya salam! Yaran nan lafiyarku kuwa!!?”. Akafa faɗa a bayansu da ƴar kakkausar murya. Tsitt ɗakin yayi, duk suka juya suna kallon mai maganar. Ta sake tafa hannayenta tana riƙe haɓa. “Oh ku ɗin nan, yanzu nan bama ku sakata ta shiryaba kuka zauna shiriritar da kukafi ƙwarewa akai?”.
         “Afuwan Addah”. Ɗaya ta faɗa tana ɗan sosa bayan wuya na alamun jin kunya. Girgiza kai Addah tayi tana ƙarasowa gaban gadon, “To naji, ku fita ku bani waje na kimtsata”. Ɗai-ɗai suka ringa fita suna ƙananun ƙunƙunai na alamar ba haka sukaso ba, amma sanin yau Addah babu fuskar wasa tattare da ita yasa babu wanda ya iya cewa komai. Ita dai bata kulasuba, dan yau babu ƴan wasan a kanta. Kamo ƙyaƙyƙyawar budurwar tayi ta zaunar tana faɗin, “Tashi kinji dear, kukan ya isa haka, kefa amaryace, amaryarma mai tsada ga ƙyaƙyƙyawan miji irin Abdallah. Ko bakison auren a fasa ne?”.
       Baki budurwar ta tura gaba tana sake matso hawayenta, sai kuma ta faɗa jikin Addah ta sake fashewa da kuka. Karan farko Addah tai dariya tana shafa bayanta. Tace, “Oh Rabbi, yau ga Nu'aymah shugabar tsiwar gidanmu tayi laushi darajar aure”. Ita dai sakema ƙarfin kukanta tai tana narkewa jikin Addah. Sunja kusan mintuna huɗu a haka kafin Addah ta ɗagota tana sake faɗaɗa fuskarta da murmushi, zaunar da ita tai sosai ta kama bakin mayafinta ta share mata hawayen fuskarta tas duk da wasu na silalowa kaɗan-kaɗan.
         “Haba Nu'aymah'n Abbah kukan ya isa haka mana, ko an miki wani abune?”. Kanta ta girgiza tana sauke ajiyar zuciya a jajajjere. “To wani waje ke miki ciwo ne?”. Nanma ta girgiza mata kai. “Ikon ALLAH, to minene ya sakaki kuka irin haka? Keda zakiyi auren soyayya Nu'aymah?. Ki duba kowa a family ɗin nan cikin tsantsar farin ciki yake da auren nan naku, dangi ta ko ina sun iso gobe idan ALLAH ya kaimu kawai ake jira. Umm. Hajjo, su Abbanki damu baki ɗaya kowa yana cike da farin cikin wannan alkairi. Ɗazun nan mukai waya da Angon shima jirgin ƙarfe uku zasu biyo daga Abuja, yanzu hakama sun taso inaga shi da abokansa. Ai nazata yau ranar farin cikice a gareki mara misaltuwama Nu'aymah. Uhhmm?”.
      Hannu tasa ta share hawayenta, cikin rawar murya tace, “Addah wlhy inajin tsoro ne?”. Da mamaki Addah tace, “Tsoro kuma Nu'aymah? To tsoro akan mi Uhhmm?. Ko wani abune ya faru dake bamu saniba?”. Nanma kanta ta girgiza mata tana haɗiyar zuciya dajan numfashi.
       Addah ta sauke nishi tana girgiza kai, hannu ta ɗaura kan haɓarta ta ɗago fuskarta. “Kalleni Nu'aymah”. A hankali ta ɗago manyan idanunta da launinsu ya koma Jaa, gashi sun kumburo saboda kukan data sha ta saukesu akan Addah”. “Kukan ya isa haka kinji daughter, kicire komai a ranki babu abinda zai faru sai alkairi, duk wani tsoro da kikeji ki ciresa a zuciyarki, kiyi farinciki dan gobe ranarki ce idan ALLAH ya kaimu, fatanmu ALLAH ya sanya albarka a al'amarin ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, ALLAH yasa wannan haɗi ya zamewa family ɗinmu alkairi duniya da lahira”.
         A zuciyarta ta amsa da amin, a zahiri kuwa sai tai ƙasa da idanunta alamar jin nauyin ta. Lura da hakan yasa Addah yin murmushi da lakace dogon hacinta. Tace, “Yauwa tagaban goshin Hajjo tashi ki shirya gashi can har an fara walima babu amarya”. 
     Ɗan murmushin yaƙe kawai tayi da miƙewa bisa umarnin Addah. Dama tayi wanka tuni, dan haka ta sake wanko fuskarta yanzu kawai ta dawo inda Addah ke jiranta. Ƴar kwalliya taimata da bazata takurataba, kafin ta sata ta shirya cikin atanfa zani da riga pitch da ratsin Maroon. Ɗinkin yay mata ɗagwas ajiki kasancewarta mai murzajjen jiki, dan sam Nu'aymah ba siririya bace, badai za'a kirata mai ƙiba ba, amma jikinta a mulmule yake babu alamar rama sam duk da kasancewarta yarinya ƙarama sosai. Baƙar riga mai zubin alƙyabba da tasha ado da pitch zare aka bisa da stones ta saka mata, da ɗan turare kaɗan, ta bata flat takalmi baƙi ta saka wanda yayma farar ƙafarta data sha ƙunshi jaa da baƙi ɗas. “Masha ALLAH amaryan ɗana Abdallah” Addah ta faɗa tana mata alamar tayi ƙyau👌🏼 da hannu. Ɗan murmushi tayi da maida kanta ƙasa na alamar jin kunya.
        Yarinyar ɗazun dake jikin Window a laɓe tana kallonsu ta share hawayen da take faman yi tun ɗazun, duka maganar Addah da Nu'aymah akan kunnenta da idonta suka faru, ta taune leɓenta da ƙarfi tamkar zata hudashi tana ƙoƙarin danne kukan dake neman kufce mata da ƙarfi...
      Babu ɓata lokaci Addah ta taimaka ma Nu'aymah suka fito harabar gidan, inda sukaci karo da wasu tsoffin mata su kusan biyar. Da ɗan faɗa farar ciki ta watsa musu harara tana faɗin, “Wai mi kuke da amaryar a cikin gida da har yanzun an gaza kaita wajen walima Fauza?”. Cike da girmamawa Addah tace, “Ayi haƙuri Hajjo, mun tsaya shirine shiyyasa”.
         “To wane shiri kuma nikam kamar wadda za'a kai ɗakin miji yau, kinga taho Zainabu”. Tai maganar da kama hannun amarya Nu'aymah. Babu musu Addah ta sakar mata ita tana murmushi da binsu da kallo har sai da suka isa gab da gate sannan ta sauke ajiyar zuciya. Yunƙurawa tai zata bi bayansu itama......... 
       Caraf aka riƙe hannunta. Juyawa tai da sauri, sai dai ganin wadda ta riƙotan yasa taƙi cewa uffan. Kallon gefe da gefe tai, ganin mutane nata ɗan kai kawo yasa ta sake tsuke fuska tana kallonta.......
             “A'ah! Adawiya lafiya kuwa? Fauza mi akai mata haka?”. Firgigit Addah tai da ture hannun Adawiya daga kan nata tana harararta, sai kuma ta kalli mai maganar fuska a narke. “Umm bar wannan ƴar taki kinji, bansan mike damun kansuba daga ita har Nu'aymah, canfa na iskesu sun haɗe kai a ɗaki sunata dirzar kuka ko shiryawa basuyi ba, ni wannan shaƙuwa tasu har tsoro take bani wlhy, gashi kuma mai rabawa yazo....” ta ƙare maganar da sharce hawaye tana kallon Adawiya dake jikin Umm tana kuka tamkar ranta zai fita.
      Murmushi ƙyaƙyƙyawar matar mai tsananin kamanni da Amarya Nu'aymah tayi, ta sake rungume Adawiya a jikinta tana ƙoƙarin haɗiye nata hawayen da suka ciko mata idanu. “Ya isa kukan haka Daughter, kiyi haƙuri, namiki alƙawarin insha ALLAH duk yanda zanyi sai nayi dan kibi ƴar uwarki sai kuje can kuyi karatunku tare kamar yanda kuka fara a tare kafin ALLAH ya baki naki mijin kema musha biki”. 
     Maimakon Adawiya tai murna sai ta sake fashewa da kuka tana ƙanƙame Umm. 
       “Oh ALLAH, ya isa haka mana daughter, ko sokike muma ki sakamu kukan ne uhhhmm?”. Ɗagowa Adawiya tai zatai magana Addah tai saurin tarar numfashinta tana harararta ta ƙasan ido, “Faɗa mata dai Umm, tundama ance mata ga mafita an samu ba sai tai haƙuriba, nifa banason shashanci kuma, a haka zaki bama Nu'aymah ƙarfin gwiwar yin farin ciki? Haba mana, k........”
        “A'a Addah ya isa haka mana, a barta taji da abinda ya dameta dan ALLAH, ɗiyata muje ki shirya kinji, tarema zamu fita wajen walimar da anyi sallar la'asar”. Ɗan satar kallon Addah Adawiya tayi, ganin harar data watso mata ƙasa-ƙasa ya sakata saurin ɗagama Umm kai alamar to. Kamata Umm tai suka bar Addah a wajen, tabisu da kallo ƙasa-ƙasa tana ɗan murmushin jin daɗi......
        “Uhhm Fauza! Dama ke naketa nema ashe kina anan”. Wata mata dake tunkarita ta faɗa. Juyawa tai da sauri ta kalli matar, sai kuma ta saki murmushi da faɗin, “Oh! Ya salam Yaya, wlhy namafa manta na barki kina jirana a kitchen, rigimar ƴaƴanki ta ɗaukemin hankali”. Ƴar dariya sukai a tare, tare da barin wajen suna cigaba da maganarsu.

         A waje kam dai har yanzu ba'a kai ga fara gudanar da komaiba, sai dai wata ɗaliba a cikin ƴammatan da zatai sa'anni da amaryace ke karatu cikin zazzaƙar muryarta, wanda hakan yasaka wajen yin tsitt ana saurarenta.
         Wasu zafafan motocine guda biyar suka shigo cikin layin, duk da mutane hakan bai hanasu kutso kaiba kansu tsaye jikin ƙofar babban gate ɗin harabar massallaci. a take mafi yawan mutanen dake a wajen walimar hankalinsu ya koma ga kallon motocin da sukai parking a jere abin birgewa. Kowa ya zuba ido yaga su wanene zasu fito a ciki?....
       Ni kaina sai da na sauke numfashi da faɗin Masha ALLAH, saboda fitowar wasu samari masu ji da lokaci da gayu daga motar, da gani babu tambaya waɗanan abokan angone dama angon kansa, bankai ga cankar angonba wani mafi ƙyawun haiba da tsarin kwalliya a cikinsu ya fito a motar tsakkiya waya manne da kunnensa yana murmushi. Sanye yake cikin ɗanyar shadda Maroon color sai maiƙo take da ɗaukar idanu. Ya saki lallausan murmushi yana gyaɗa kansa alamar amsa mai maganar daga can, sai kuma ya sauke wayar ya tura aljihu dabin abokansa dake tsaitsaye suna kallon ƴan taron walimar da suma mafi yawansu su suke kallosu da kallo. Kafin yace wani abu ɗaya daga cikinsu ya juyo yana faɗin, “Woow Ab harfa na canko amaryarka”. Ɗan hararsa yayi da ɗauke kai kamar bazaice komaiba, sai kuma ya sake kallonsa yana wani furzar da numfashi. “Malamai dalla kallon ya isa haka, ku bakwa ganin su Baba Malam duk mu suke kallo suma”. A tare duk suka juyo da kallonsu garesa suna dariya, wanda yay magana ɗazunne ya sake faɗin, “Hahh! Go gefe malam, kai dai faɗa mana kishi kakeyi dan ance anga Angel ɗinka”. “Shashasha, to idan nayi kishin laifine?”. Abdallah ya faɗa yana ratsa tsakkiyarsu yay gaba. 
     Cike da shaƙiyanci sukabi bayansa suna dariya ƙasa-ƙasa da faɗin, “Shege uban zumuɗi, anya kuwa zaka cika alƙawarin da kaima su Baba Malam na barin ƙwailarnan taka tai karatu? Karfa muji nanda wata tara ana nemanmu a labour room”. Duk da yana jinsu sarai bai tankaba, sai dai ya ƙawata fuskarsa da wani sassanyan murmushi daya ƙara fidda ƙyawun fuskarsa...

          “Huuhm Nu'aymah! Gafa Soulmate ɗinki nan tafe tamkar wani ɗawisu a tsakkiyar furanni”. Iman ta faɗa a hankali cikin kunnen Nu'aymah da kanta ke'a duƙe lulluɓe da abaya batasan wainar da ake toyawaba. 
     Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke da ɗan ɗagowa kaɗan, idanunta ne suka sauka akansa. Taja ajiyar zuciya tana lumshe idanunta wani sanyi na ratsa mata ƙirji. Sosai take tsananin son Yah Abdallah, kamar yanda tasan itama yana sonta fiyema da yanda take sonsa. Yah Ab farin cikinta ne, jinin jikinta ne, nutsuwarta ne, shiɗin na musamman ne a gareta, dan yana ɗauke da mataki uku ne na martaba a gareta. Shi ɗin jininta ne ɗan uwanta, sannan masoyinta tun batasan kantaba. Malaminta kuma na farko ta ɓangaren ilimi. Shiyyasa komai nasa abin girmamawane a gareta......
       “Hy Baby! Kallon ya isa haka karki cinyesa mana”. Nanah ta faɗa tana ɗan mangare kan Nu'aymah. Karon farko da tunda aka wayi garin yau Nu'aymah tai murmushi har fararen haƙoranta suka bayyana, ɗan harar Nanah tayi da Iman da suke mata dariyar shaƙiyanci. Ta maida kanta ƙasa tana faɗin, “Sa'idiniyya kawai”. Nanma dariyar sukayi, ita kuma ta lumshe idanunta daga cikin hular abayar tana maijin nutsuwa da farin cikin isowar angonta lafiya bayan tsahon shekaru biyu kenan basuga junaba sai dai a waya da hoto da video call.

        Isowar ango Abdallah da abokansa tayi dai-dai da shigar lokacin sallar la'asar, dan haka aka sanar da zuwa ai salla.
       Mimmiƙewa mazan suka shigayi suna nufar bayan masallacin domin yin alwala, masu alwalar zuhur kuma da bata karyeba suna shigewa ciki. Matanma ba'a barsu a bayaba, wasu cikin gida sukaita shiga, wasu kuma sama inda massallacin mata yake.

★★★★★

       Baƙi da suka janyema Umm hankali ya saka Adawiya samun damar silalewa ta nufi ɓangarensu. Nan ɗinma akwai mutane babu laifi, musamman da a yanzu aketa shigowa domin gabatar da sallar la'asar. Sashen Abbansu ta shige, inda ta tabbatar bazata samu kowaba sai su ƴan gida. Ilai kuwa babu kowa sai ƙamshi dake ta tashi mai daɗi. Ɗakin farko dake a falon sashen ta buɗe ta shiga, babbane yasha kayan more rayuwa tsaf, ta zube a saman gadon tana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya mai tafiya da kuka mai ƙarfi da hasala zuciya.......
             Turus Addah data fito daga bayin ɗakin fuskarta jiƙe da ruwa alamar tayo alwalar yin salla tayi a bakin ƙofa tana kallonta, a take idanunta suka rine da ɓacin rai, cikin faɗa tace, “Wai wane kalar shashancine wannan kikema mutane haka Adawiya?!!”.
        Adawiya da sai yanzu tasan da shigowarta ta taso da gudu ta faɗa jikinta da sake fashewa da wani sabon  kukan, “Addah Wlhy ina sonshi, idan baku auramin shiba mutuwa zanyi, wlhy saina kashe kaina Addah. Dan nafita sonshi ku taimakeni.............”
       Ta fashe da wani irin kuka tana zamewa zata faɗi ƙasa jikinta na rawa. Da wani irin kallo Addah ta bita harta zube ƙasan yaraf, taɗanja jikinta baya tana jan tsaki zata raɓata ta wuce. Saurin tashi Adawiya tai zaune ta riƙo hannunta. “Wlhy Addah inhar baku aura masa niba saina kasheta!!”.
       Baya Addah tai da sauri zata faɗi ƙasa tana mai waro idanu waje sosai akan Adawiya, bakinta na ɓari tace, “Ki kasheta Adawiya?!”.
           “Da hannun nan nawa kuwa”. Adawiya ta faɗa tana zazzaro idanu waje itama da ɗaga hannunta tana nunama Addah............✍


Hummmmm!!!! Turƙashi. Masu karatu wannanfa shine ana dara sai ga dare yayi😲. Mi kuke tunani akan wannan labari? Wacece Adawiya? Sannan wacece Nu'aymah? Wanene Kuma Abdallah?. yaya zata kasance? Minene zai faru kuma? Wace amsa Addah zata bama Adawiya?......
        Amsar waɗanan tambayoyin duk suna a Littafin SARAN ƁOYE!! da ke cikin tawagar littatafai biyar na zafafa 2021 dake shirin zuwa muku insha ALLAHU nan bada jimawa ba😉😋. 

Wlhy karku bari ayi babuku, dan ZAFAFA BIYAR 2021 fa da zafinsu suke tafe, na tabbatar muku tafiyar wannan shekarar ta dabance MASOYAN AMANA😋🤗🤗😀😀.


ZAFAFA BIYAR 2021


Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
 MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.


Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070



💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍



ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*



           *_SARAN ƁOYE!!_*


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


Free page😋


No. 2

.................Tsaki Addah taja tana ballama Adawiya harara, ta tsallaketa ta wuce tana faɗin, “Sai kije ki kashetan shashasha kawai mara tunani”.
         Kuka sosai Adawiya ta sake fashewa da shi. Ta rarrafa har inda Addah take shirin kabbara salla ta riƙe mata ƙafafu. Cikin fushi Addah ta ƙwace ƙafafunta tana nuna Adawiya, “Wlhy idan baki shiga hankalinkiba Adawiya zan bala'in saɓa miki, wai wane irin iskancine wannan? Ki shiga hankalinkifa tunkan nai miki abinda zakiyi dana sani a taron bikin nan. Dalla tashi ki ficemin anan, ba kashe Nu'aymah ba ki babbakama gidan wutama mu ƙone ƙarewar hauka. Wawuya kawai!!”.
          Yanda Adawiya taga ran Addah ya ɓaci tasan zata iya cin ubanta kamar yanda ta faɗa, tana ganin ta kabbara salla saita tashi ta fita tana kukanta. Addah mace ce mai yawan wasa da fara'a, idan har kaga fushinta to lallai an kaita maƙura, shiyyasa idan tai fushin dolene kaji shakkarta. Su kansu ƴaƴanta tana rayuwa da sune tamkar ƙawayenta, hakama sauran yaran gidan. Wannan halayar tata tajan yaran a jiki yasa kowane yaro yazama ɗan ɗakin Addah a gidan, suna sonta sosai, hakama iyayensu sunajin daɗin yanda take son ƴaƴansu da basu lokacinta.
          
         Can bayan ɗakunan sashen samarin gidan Adawiya ta nufa, dan tasan canne kawai babu mutane. Waje ta samu ta zauna tasha kukanta, yayinda zuciyarta ke shirya mata mugayen abubuwa game da Nu'aymah da matakin da zata ɗauka a kanta na dakatar da wannan auren, tayi alƙawarin kota halin ƙaƙa saita mallaki Abdallah a safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai kuma ta rabashi da Nu'aymah, idan kuma har hakan bata tabbata ba to sai dai suyi zaman kishi ita da Nu'aymah kokuma kowa ya rasa. Dan ko sama da ƙasa zata haɗe bazata barma Nu'aymah Abdallah ba wlhy........
        “Adawiya! Adawiya!!”. ta jiyo ana ƙwala mata kira. Tsaki taja mai ƙarfi kafin ta miƙe tana kakkaɓe jikinta daya ɗan ɓaci da ƙasa, duk da ma ita ko shiryawa batayiba. Fitowa tai inda zata iya ganin mai kiran nata. Da sauri taja baya saboda karo da suka kusa ci da Yah Abdallah. Ƙirjinta yay wani mugun harbawa, a take ta fara neman nutsuwarta ta rasa. Kwarjininsa da matsanancin son da take masa suna neman birkitata gaba ɗaya ta kasa riƙe kanta....
         Sassanyan Murmushinsa ya sakar mata yana ɗan ware idanunsa a kanta, “Oh Hassanar amaryace haka bata ko shiryaba?”. Duk da maganarsa batai mata daɗiba saita saki masa murmushi, ta matsa kusa da shi tana shaƙar ƙamshin turarensa mai daɗi, “Yah Abdallah dama ka iso?”. 
       “Ya za'ayi ki sani tunda ance kina nan kinata kukan rabuwa da Husainar ki”. Baki ta buɗe zatai magana sai kuma ta fasa tana kallon Amal data rako Yah Abdallahn. “Kiranmi kike ƙwalamin ke kuma?”. Baki Amal taɗan taɓe tana cigaba da latsa wayar hannunta, “Kiranmi zan miki ni kuwa, dama Yah Abdallah ne ke nemanki, shine akace anga kinyo tanan”.
      Kafin tace wani abu Yah Abdallah yace, “Nine na sakata, wani aiki zakimin, Amal jeki abinki”. Kai Amal ta jinjina masa, tai gaba abinta batare data sake kallon inda Adawiya take ba. Sai da tai nisa da su sannan Abdallah ya sake kallon Adawiya, ganin shi take kallo sai yay murmushi. 
       “Yaya dai ƙawar amarya na canja miki ne?”. “Sosaima kuwa Yah Abdallah”. Adawiya ta faɗa cike da yanga tamkar ba itace ta gama darzar kukaba yanzun.
      Murmushi yayi yana ɗauke kansa da faɗin, “To na gode. Kinsan aikin da zakimin?”. Kai ta girgiza masa batare da tace komaiba. “Sonake kije wajen Walimarcan ki satomin amaryata nan inason ganinta”. Wani takaicine ya soki zuciyar Adawiya har fuskarta sai da ta nuna hakan. Da mamaki Abdallah yace, “Yaya dai?”. “Babu komai Yah Abdallah” ta bashi amsa da rawar murya.
          “Okay, to maza ki shirya saiki ɗakko min ita, karfa ki bari kowa ya ganki musamman ma Hajjo”. Kanta ta ɗaga masa kawai, dan tasan idan tai magana kukane zai ƙwace mata. Da kallo Abdallah ya bita harta ɓacema idanunsa, haka kawai tausayin yaran ya kamashi, kowa yasan irin shaƙuwar dake tsakanin Adawiya da Nu'aymah tun ƙuruciya, sun tasone tamkar tagwaye a gidan, komai tare ake musu shi, yanzu kam ace zasu rabu rana tsaka ai dolene kaji tausayinsu.

        Adawiya kam koda ta bar wajen sashen Hajjo kakarsu ta nufa, babu kowa duk ana wajen walima, dan ana idar da salla kowa ya koma, daga cikin gidanma kana jiyo lecture ɗin da aka fara. Kwanciyarta tayi dan ta rantse bazata kira Nu'aymah ba.

★★★

        Tun Abdallah na kallon hanya na jiran ɓullowar amaryarsa Nu'aymah da Adawiya harya koma duban agogo. Kamar wasa sai ga mintuna ashirin sun shuɗe babu Adawiya balle Nu'aymah, abinda zuciyarsa kawai ta basa Hajjo ta hana Adawiya ɗakko Nu'aymah ne, maybe kuma tanacan tana wayon yanda zasu baro wajen. Ɗan murmushi yayi yana lumshe ido, sosai yake cike da ɗoki da ƙaguwar son ganin Nu'aymahr sa, yanason yaga yanda ta sake komawa yanzun........
         Kiran da ake masa a wayane ya katse tunaninsa, ya zaro wayar daga aljihun gaban rigarsa ya duba. Zaid ne, kamar bazai ɗagaba sai kuma ya amsa tare da ɗorawa a kunnensa. “Hello Jibiya wai kana inane?”. Kamar bazaice komaiba sai kuma yay guntun tsaki da kallon agogon hannunsa. “Ina cikin gida mana, miya faru?”. “Cikin gida kuma? To mi kakeyi acan bayan kowa duk yana nan har amarya. Gashi nan Baba malam na nemanka to”. Baice masa komaiba ya yanke wayar. Badan yaso ba ya baro cikin gidan ya koma wajen walimar.
         Inda Nu'aymah ke zaune kusa kakarsu Hajjo ya kalla, tana zaune a yanda ya barta tun ɗazun, babu kuma alamar Adawiya a wajenma. Ɗan tsaki yayi a ransa ya ƙarasa inda Baba Malam yake.

             Masha ALLAH, anyi taron walima an tashi lafiya, inda malamai suka ragargaza lectures masu ratsa jiki ga ma'abocin saurare. Gaba ɗaya an gina sune akan zaman aure da kurakuran da muke tafkawa a cikinsa da hanyoyin magancesu, inda amarya da angonta sukasha addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________

        Tunda aka tashi jikin Nu'aymah sai ya sake yin sanyi, maimakon ta nufi ɗakinsu da suke zaune da ƙawayenta sai ta nufi wajen Umm. Kanta tsaye ɗakin Umm ta wuce, sai dai bata ciki sai ƴan uwanta. Gaishesu tayi suna tsokanarta da amarya-amarya, ita dai kanta a ƙasa ta sulale ta fito. Sashen baba malan ta nufa, dan tasan Umm bazata wuce tana a canba ko wajen Addah.    
         Tun shigowarta corridor ɗin daya shiga tsakanin falon Baba malam dana Umm taga takalman Umm da Addah, ɗan murmushi tayi tana sake jinjina wannan irin ƙauna ta iyayensu, ƙofar falon ta ƙarasa tare dayin sallama, daga ciki suka amsa mata da bata iznin shiga.
       “Ah ah! amarya da kanta. Miya farune?”. Addah ta faɗa tana murmushi. Kallon Umm da batace komaiba Nu'aymah tayi, sai kuma ta duƙar da kanta hawaye na cika mata ido. Addah tace, “Kinga zonan”. Takawa tai a hankali zuwa garesu, ta zauna a ƙasa jikin ƙafafun Umm data cigaba da abinda takeyi tamkar batasan da shigowar Nu'aymah ba. 
        “Ƴar albarka miya farune? Ko kewar Umm ne ya motsa?”. Maimakon Nu'aymah ta bama Addah amsar tambayarta sai hawaye suka gangaro mata a kumatu, ta kwantar da kanta bisa cinyar Umm tana jan ajiyar zuciya a jajjere. 
      Dauriya kawai Umm keyi dama, taja ɓoyayyen ajiyar zuciya da girgiza kanta tana kallon Nu'aymahn. “Ke kuma wannan shashancin fa?......”
      “A'a babu wani shashanci Umm”. Addah ta faɗa tana kamo hannun Nu'aymah cikin nata. “Baby faɗamin miya faru? Ko har yanzu tsoron dai?”. Kai Nu'aymah ta ɗaga mata, sai kuma ta ɗago ta kalli Umm da itama kallonsu takeyi. “Umm dan ALLAH ni banason auren a fasa kawai”.
         “Afasa kuma Nu'aymah?! Miyasa?”.
       “Addah wlhy ni naji banaso yanzun kawai”.
        Sosai abin ya bama Addah dariya, ita kanta Umm sai da tai murmushi tana girgiza kai, dan babu komai a maganar Nu'aymah sai zallar ƙuruciya da sakarci. Umm ta janyeta a jikinta tana miƙewa da faɗin, “Wannan shashancin ba daniba, Addah bara nayi nan kinji”.
      Sauri riƙeta Nu'aymah tayi tare da sake cukuykuye ƙafafunta tana kukanta, “ALLAH Umm nidai banaso, gara na zauna a wajenku Please”.
       “Oh ALLAH, Nu'aymah banason sakarci kinji, sakarni naje nayi abinda zai amfaneni”.
          Kallon Umm Addah tayi, cikin magana da yaren ido taima Umm alamar ta lallasheta Please. Umm zatai magana Addah ta girgiza mata kai tana miƙewa ta fice ta barsu. Ajiyar zuciya Umm ta sake saukewa a sanyaye, kafin tai guntun murmushi da komawa ta zauna a inda ta tashi. Kama Nu'aymah tai ta tadata ta maidota kan kujerar kusa da ita ta zaunar. Hakan ya bama Nu'aymah damar faɗawa jikin Umm ta rungumeta.
         Karan farko Umm tai ƴar dariyar ƙarfin hali da rungume ɗiyar tata itama. “Ke wai bakisan kin girmaba Nu'aymah? Aurefa za'a ɗaura miki gobe idan ALLAH ya kaimu amma kike halin yara har yanzun?”.
        “Umm ni wlhy na fasa, zan zauna a wajenku nayi karatun kawai”. Dariya Umm ta sakeyi da ɗago fuskar Nu'aymah ta share mata hawayenta. “To naji ya isa haka nan kukan ko”. “To Umm za'a fasa ɗin?”. “Tambayi Abbanki ga shinan”. Umm ta faɗa tana kallon Abba daya shigo kusan mintina biyu kenan harya zauna kusa da Nu'aymahn bata saniba yana kallonsu kawai. Tashi Nu'aymah tayi daga jikin Umm takoma jikin Abbanta. 
         “Maman nan nawa dai shagwaɓanta yayi yawa”. Ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi yana shafa kanta. Ɗagota yayi ya zaunar sosai, tare da saka hannu ya share mata hawayenta gaba ɗaya. “Kinga faɗamin miya faru?”.
         “Abbah a fasa kawai”. 
    Waro idanu ya ɗanyi cikin mamaki, “Mamana mi za'a fasa?”. “Abbah aur.....” sai kuma ta kasa ƙarasawa tai ƙasa da kanta.
          “Ina jinki faɗamin mana!”.
“A...Abbah auren, ni yanzu na fasa”. 
           Kallon juna sukai shi da Umm dake kallon Nu'aymah cike da damuwa, Sosai ta basu tausayi da dariya, amma duk sai suka danne kayansu. Abbah ya riƙe hannayenta da sukasha ƙunshi cikin nasa, cikin muryar lallashi yace, “Mamana kin daina son yayan nakine?”. “A'a Abbah”. Ta faɗa kanta a ƙasa. “To miyasa kikeson a fasa?”. “Abbah banason rabuwa daku nidai”.
         Murmushi Abbah yayi tare da sauke ajiyar zuciya, “To ai ba rabuwa zakiyi damuba Nu'aymah, kuma shima Abdallah ai ɗan uwankine mai gatantaki ma fiye da kowa a gidan nan, duk kuma sanda kikeso ya kawoki wajenmu zai kawoki”. Idanunta cike da kwalla ta kalli Abbah, “To Abbah ina zai samu kuɗin jirgi yayta kawoni kullum tun daga Saudia?”. “To ai dama ba kullum ba Mamana, keda zakiyi karatu tayaya za'ace za'a kawoki gida kullum koda anan zaku zauna ma. Duk dai sanda kuka sami hutu sai ya kawoki, kuma muma zamu dinga zuwa ganinku ai ko”. Shiru tai batace komaiba, sai hawaye keta sake mata zarya.
       Cikin hikima da wayo Abbah da Umm sukaita mata nasiha da ƙara ƙarfafa mata gwiwa harta daina kuka ta koma dariya kamar ba ita ba, kusan awarta ɗaya da rabi a wajensu sannan ta tafi kiran da hajjo ta aiko Farida tai mata.

              Tafiya take tana ƙunƙunin haushin Hajjo, dan tasan kiran datai mata bai wuci sakata shiga cikin ruwan lalle ba, itako ta tsani abun dan ƙyanƙyami takeyi, amma jarabar kakar tasu bazai bari ta fito ta faɗa ba.
         Gabanta ne ya faɗi jin an kamo hannunta, ta juyo a firgice zata wage baki tai ihu aka rufe bakin.
      Cikin muryarsa mai sanyi da nutsuwa yace, “Matsoraciya nine. Na gaji da wasan ɓuyar da kikeyi dani malama”.
      Ajiyar zuciya Nu'aymah ta sauke jin Yah Abdallah ne, ya saketa yana cigaba da ƙawata fuskarsa da murmushi da ƙare mata kallo daga sama har ƙasa. “Saboda kinsan kin sake haɗuwa fiye da da shiyyasa kiketa faman ɓoyemin kanki ko?”. 
       Hannu Nu'aymah tasa ta rufe fuskarta da shi tana murmushi, “Yah Ab banfa san kazo ba”.
        “Kutt!”. Ya faɗa yana zaro idanu waje, “Wato bama kisan nazoba?”. Kai ta jinjina masa da ƙyalƙyalewa da dariya. 
          “Lallai yarinya na yarda kin girma kam, idan ba tsoroba buɗe fuskar ki faɗamin ido da ido mana”. “A'a ai basai na buɗeba tunda dai kaji na farko”. “Hahyh! Zaki min bayani gobe idan ALLAH ya kaimu ai”.
        Kasa cemasa komai tai a kan hakan, saima ta risina kawai ta gaidashi. Ya amsa mata cike da kulawa idanunsa na cigaba da yawo a jikinta, duk da akwai ƙaramin hijjabi tare da ita, rayawa kawai yake a ransa ‘anya baiyi gangancin ɗaukar alwashin rinon Nu'aymah ba kuwa? Kai da sakel wai anbama mai kaza kai’.......
          “Yah Ab bara naje hajjo ke kirana”. 
     Maganarta ta dawo dashi hayyacinsa. Ajiyar zuciya ya sauke daɗan kallon gefensu, sai kuma ya kalleta sosai yana gyara tsaiwarsa. “Babie kinga manta da tsohuwar can kinji, musamu guri mu zauna muɗan zanta na yaushe gamo, ke koma ɗokin ganina baƙyayi bayan kuma shekara biyu kenan baki ko ganniba”.
          Murmushi tayi tana ɗan kallonsa ta gefen ido, a ranta godiya takema ALLAH daya mallaka mata Yah Ab matsayin masoyi, gobe idan ALLAH ya kaimu kuma iyanzu mijine. Ya haɗa abubuwa masu yawa na gwaranzan mazaje da kowacce mace zatai alfahari da samunsa, ita kanta tasan ta cika mai sa'a ta gaske, dan ba'a wajeba ko'a cikin yayyenta, ƴan uwanta tasan akwai masu tsananin sonsa, amma ya dage kai da fata sai ita, tun batasan kantaba, tun ana masa faɗan yay aure idan ta girma sai ya ƙara da ita har kowa ya zuba masa ido dan yaƙi amincewa, a cewarsa ita kaɗai ta ishesa rayuwa, dan haka zai jirata ko tsahon shekara nawane. Damuwa da rashin auren nasa ya saka iyayensu yanke hukuncin aura masa ita bayan sun kammala secondary wata uku kenan, acewarsu taje ta cigaba da karatun a ɗakinsa kawai..........
           “Ina kika tafi kika barni Noor?”. Ya faɗa yana kaɗa mata hannunsa saitin fuskarta. Ajiyar zuciya ta sauke da duƙar da kanta tana murmushi. “Muje” ya sake faɗa yana nuna mata hanya.
      Babu musu ta bisa zuwa can bayan sashen Hajjo, inda kuma ya kasance gaban sashen Abbansu Musbahu. Zama sukai a fararen kujeru dake a wajen, basufi mintuna uku da zamanba sai ga Adawiya. Sosai Nu'aymah taji daɗin zuwan ƴar uwar tata, dan dama a takure take da kasancewarsu su biyu kawai ita da Yah Abdallah. Shiko sam baiso hakanba, amma sai bai nunaba ya biye musu sukaita zuba masa shirmen surutunsu.
       Ganin hirar dai bazata yuwu shida Nu'aymah kawai ba sai ya miƙe bayan kamar mintuna 35 da zamansu, umarni ya basu suje su kwanta, shima zai koma wajen abokansa suna jiransa. Sam Adawiya bataso hakaba, dan wani irin farin ciki ta tsinta kanta a ciki na kasancewa da Yah Abdallah a ƙarƙashin inuwa ɗaya. Sai da yaga sunbar wajen sannan shima ya miƙe ransa duk babu daɗi, dan yaso su tattauna abubuwa masu muhimmanci shi da Nu'aymah amma Adawiya tazo ta tsare ko ina.

           Ɗakinsu dake a sashen su Nu'aymah suka nufa, inda ƙawayensu suke. Wasu sunyi barci, wasu ko na hira a waya da samarinsu, wasu kuma cheating, ƙalilanne ke hira a tsakaninsu.
        Yusrah data fito daga bayi tace,  “Aymah wai ina kika shiga Hajjo nata nemanki? Sai masifa takeyi tun ɗazun, dan tazo ɗakin nan yafi sau goma”. 
            “Yah ilahi, dan ALLAH da gaske Yusrah?”. “Wlhy karkiji wasa, tambayi su Nanah ma kiji, har Addah ma sai da tazo nemanki. Ina kikaje to ke?”.
            “Muna tare da Yah Ab ne fa da Adawiya”.
   “Ohhh! Kice soyayya ce ta lula dake sama. Aiko daga ke har Yah Ab ɗin kunga banu da jaraban Hajjo da safe idan ALLAH ya kaimu, ga ruwan turare can Addah tace idan kin dawo ki shiga ciki”.
         A sanyaye ta amsa da “to”, sauran kuma suka sanya mata dariyar tsokana.
      Bata kulasuba ta nufi toilet ɗin, Adawiya kuma taja tsaki ta fice daga ɗakin batare dasu sunma lura da itaba.

_______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
__________________________

         Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

Muna godiya da zaɓin zafafa biyar😍😘👌🏼🤗

________________________________

         Har Nu'aymah ta cire kaya zata shiga bahon da Addah ke haɗa mata ruwan turare saita tuna da tabar wayarta a sashen Abbah, gashi Yah Ab yace mata zasuyi magana ta Cat. Towel ɗin wankanta babba ta cira daga ƴar durowar da suke sakawa, ta ɗaura sannan ta fito ɗakin ta ɗauki babban hijjabi dogo ta zumbula. Batace ma kowa komaiba ta fice daga ɗakin zuwa sashen Abbah.
       Sai da tai sallama a ƙofar ɗakin aka bata iznin shiga sannan ta shiga, Abbah ta iske shi da Abban Abuja suna shan shayi, ta gaida Abban Abuja kanta a ƙasa dan haka kawai yau kunyarsa takeji fiye da kullum shi Da Mamah. Shikam fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonta, “Mamana ai tun ɗazun nake baza idon ta ina zan ganki amma kin ɓoyemin gaba ɗaya”.. 
        “Lah Abba ba ɓoyewa nayiba, ALLAH bammasan ka iso ba”. Ƴar dariya yayi irin ta kamilan mutane, yace, “To shikenan na amince mamana, kina lafiya ko?”. “Eh Abba lafiya lau”. “To Alhmdllh Mamanmu”.
      Juyawa tai batare da tayi zancen wayarba, dan da anan ta barta tasan Abbah zaiyi magana. Tunanin zuwa inda suka zauna da Yah Ab tayi danta duba ko acan ta yadda bata saniba.
         Gidan yayi shiru, dan mafi yawan mutane ƴan biki sunyi barci kasancewar har 12 ta gota, sai ɗai-ɗaiku marasa barcin wuri. Duddubawa ta farayi kasancewar akwai wutar Gen da aka tada, kamar wasa saita jiyo ring ɗin wayar acan gaba da inda take. Cikin mamaki da kila wakala ta nufi inda takejin, sai dai a ranta tana son ƙin gaskata wayartace, tafi tunanin wanine mai irinsa dai.
     Tana tafiya Ring ɗin wayar na sake gaba, da kuma ya yanke zataji an sake kira, saita fara tunanin ko Yah Ab ne keta jera mata kiran? Ƙila ya hau online bai gantaba. To amma miyasa kamar ana tafiya da wayarne?. Babu mai bata amasa, ƙuruciyarta baisa ta fahimtar da ita akwai matsalaba kuma ta cigaba da bin sautin ring ɗin wayar har ta iso ƙaramar ƙofar da akai daga cikin gidan ta ɓulla massallacin ƙofar gidansu, inda su Abbah kebi da asuba yin sallar asuba dasu ma kansu idan suna buƙata ko zasu shiga islamiyya.
       Anan ne ta tsaya cak tana waige-waige. Sai kawai taji an jeho mata abu akan fuska. Saurin saka hannu tayi ta janye guntun handkerchief ɗin da aka jeho mata fari tas. Kafin ta samu damar yin wani tunani akan hakan ko neman taimako taji duk jikinta ya saki idanunta na wani lumshewa kamar wadda hankalinta ke neman gushewa daga gareta.
      Daga haka bata sake sanin mike faruwaba kuma...............✍

Tashin hankali, to wanene kuma ya da wannan aiki😲🤦🏻🚶🏻?.

Amsarku na a Littafin SARAN ƁOYE dake cikin rukunin littatafai biyar na ZAFAFA 2021 da a yanzu haka sun fara zuwa muku da ɗumi-ɗuminsu, karku bari a baku labari guys, wannan tafiyar tanada banbanci sosai dana baya ina ƙara tabbatar muku😉👌🏼😀😍😍😘💃🏻😋.

           ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*



              *_SARAN ƁOYE!!_*


        *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


Free page😋.



No. 3

...............Sama-sama takejin motsin mutane na matsota, sai dai bata fahimtar maganar da sukeyi balle ta ɗauki muryar kowa. Ta dafe kanta dake tsananin juya mata tare da jingina jikinta da bangon daya raba gidan nasu da massallaci. A hakanma dai bata tsiraba, garin cigaba da mata hajijiya yakeyi. Tai ƙasa zata zame ta faɗi aka riƙota. Ƙoƙarin buɗe ido take taga wanene? amma ta kasa saboda nauyin da sukai mata, haka ta sake jiki ga koma wanene ya riƙeta sosai, kafin ya fara janta suna takawa a tare batare da tasan ina suka dosa ba.
          Tabbas taji an sakata a mota an kwantar, amma daga haka bata sake sanin komai dake faruwaba a duniyar, dan barci mai nauyin gaske yayi awan gaba da ita.......

★★

            A ɓangaren Abdallah kam yata jiran Nu'aymah ta buɗe data amma sai yaji shiru, sai kusan 12 yaga tazo online ɗin, yay mata magana sai dai ta buɗe saƙon amma bata amsashi ba. Hakan yaso sosa ransa, amma kuma daya tuna ƙuruciya na bala'in ɗawainiya da Nu'aymah sai ya watsar da abin yay kwanciyarsa, a cewarsa ai daga dai gone idan ALLAH ya kaimu duk wani zagaye-zagaye ya ƙare kuma, tunda ta zama tasa. Da wannan tunanin yay barcinsa batare da ya sake bi takan wayarba ma.

______________________________
   
           A firgice ta farka jikinta jiƙe sharkaf da gumi. Baba malam dake saman abin salla ya kalleta da mamaki, sai kuma ya ajiye Al-Qur'anin hannunsa ya miƙe zuwa gareta. Zama yay kusa da ita ya rungumeta dan ya kula sam bata cikin hayyacinta, da alama kuma wani mafarkin tayi mara daɗi. Sai da sukaja kusan mintuna huɗu a haka ya tabbatar numfashinta ya dawo dai-dai sannan ya ɗagota ya bata ruwa ta sha. Sai da tasha kamar rabi ta miƙa masa sauran tana sauke ajiyar zuciya. “Jannat! lafiya kuwa?”. Ya faɗa yana share mata gumin goshinta.
        Umm taɗan dafe kanta tana kallon mijin nata, “Abban Nu'aymah mafarki nayi wlhy, kuma akan Nu'aymah ne. Inaga bara naje na dubata a ɗakinsu” tai maganar tana ƙoƙarin sauka ƙasa. 
     Saurin riƙota yay da faɗin, “Ah ah Jannat”. Kallonsa tai tamkar zata fasa kuka, muryarta a sanyaye tace, “Inaji a jikina Nu'aymah tana cikin damuwa  Abbansu”. Murmushi yayi daɗan girgiza kansa. ya kamata ya maida ya kwantar tare da duƙawa ya sumbaci goshinta. “Nasan maganganunta na ɗazun da kika saka a ranki yasa kikejin kamar bata da lafiya, ki kwantar da hankalinki Jannat, ƙuruciyace kawai ke ɗawainiya da Nu'aymah, idan bamu ƙarfafata ba karmu yarda taga gazawarmu muma, kiyi haƙuri kimata addu'a kinji”.
      Kanta ta ɗaga masa tana haɗiye kukan da ya cika mata idanu, sai kuma tai ɗan murmushi domin ƙoƙarin danne abinda ke azalzalar ranta har yanzun. Kanta ya cigaba da shafawa a hankali da tofa mata addu'a har barci ya sake kwasheta. Ya sauke numfashi a hankali da sake sumbatar goshinta sannan ya miƙe ya koma inda yake da.

    ______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________

      WASHE GARI

   Tun kiran sallar farko wasu daga jama'ar gidan da makusantansu suka tashi aka fara ƙaƙainiyar ɗaura abinci. Hajjo data kwana da haushin Nu'aymah da batazo kirantaba ta nufi sashensu Nu'aymahn tana faɗa akan yau sai taci ƙaniyarta duk da ranar aurenta ce.
         Masu kai kawon fita can waje inda aka ɗaura girki sunata gaisheta, amma amsawa take sama-sam dan a ƙule take, tana nufar ɗakinsu Nu'aymah. Babu wanda ya tashi a cikinsu, dan mafi yawansu basuyi barici da wuriba, Hajjo ta kunna fitilar ɗakin tana kiran sunan Nu'aymah. “K Zainabu! Zainabu kina inane wai?”.
        Amal ce ta fara farkawa saboda bata da nauyin barci sam, ta tashi zaune da ƙyar tana murje idanunta da faɗin, “Kai Hajjo! Kinzo mu kin tadamu da kwakwazonki wlhy”. “Ubanki Lurwanu ne ke kwakazo, mara kunyar banza”. Tura baki Amal tai tana komawa ta kwanta dan taji haushi Hajjo ta faɗi sunan Abbansu.
       “K ni tashi dan gidanku ki faɗamin ina Zainabu take?”.
      “Ba tana sashenki ba” Amal ta faɗa tana juya ma Hajjo Baya. “K Safiya banson lalata, dan gidanku tana sashena zanzo nan nemanta ne?”. 
        “ALLAH Hajjo tana sashenki, bayan ta dawo muka faɗa mata kina nemanta shine ta tafi can”. Nanah data tashi yanzu itama ta faɗa cikin muryar barci.
      Hajjo tace, “To sai dai idan tana ɗakin uwarta ko kuma wajen Fauza. Dan nidai ban gantaba, Adawiya ce kawai ta kwana a ɗakina”. Nanah tace, “To sai dai idan tana sashen Addah, dan ɗakin Umm su Mom ne suka kwana, nasan kuma Nu'aymah bazataje cikinsu ta kwanta ba Hajjo”. 
       “To bara na dubata wajen Fauzan, kuma saiku tashi kuyi salla tunda lokaci yayi”. “To” kawai Nanah tace. Amal kuwa bata sake maganaba har Hajjo ta fita.

       Hajjo na fita Umm na shigowa, tadasu ta shiga yi dan su Nanah ma komawa sukai suka kwanta ganin Hajjo ta fita. Sai raba idanu Umm keyi a tsakaninsu nason ganin Nu'aymah, sai dai sam babu ita a cikinsu. Kafin ta samu damar tambaya Hajjo ta sake shigowa Addah biye da ita a baya.
       Cikin girmamawa Umm ta rissina tana gaida Hajjo. A taƙaice ta amsa mata da tambayarta ko Nu'aymah a ɗakinta ta kwana ne?. Gaban Umm yay masifar faɗuwa, ta girgiza kanta da haɗiye yawu da ƙyar. “A'a Hajjo ba can ta kwanaba”.
       “Yau mun shiga uku”. Cewar Addah tana ida shigowa ɗakin sosai. “Ku batare kuka kwana da Nu'aymahr ba ne wai?”.
        Yusrah tace, “A'a Addah, batare muka kwana da itaba, bayan kin haɗa mata ruwan turare kin fita suka shigo ita da Adawiya, to na faɗa mata dai ga ruwa can kin haɗa mata ta shiga ta amsa da to. Sai dai tana shiga bata jimaba ta fito ta fice daga nan, ni dai har barci ya ɗaukeni bata dawo ba, kuma kusan nice ƙarshen barci”.
         Tashin hankaline ƙarara ya bayyana a fuskar Umm dasu Addah, basu tsaya jan zancenba suka fito daga ɗakin domin neman Nu'aymah a sauran sassan gidan ko taje wani ɓangaren ta kwana.

          Ɓangaren Momy mahaifiyar Abdallah suka fara shiga tace rabonta da Nu'aymah tun a wajen Walima, amma bara a duba kotazo ta shiga ɗakin su Amal bata saniba. Sun duba ɗakinsu Amal babu kowa sai ƙannen Amal ɗin biyu dake barci. Sauran ɗakunan kuma duk akwai baƙi da wahala ace ta shiga can, amma duk da haka sai da suka shishshiga suma. Amma babu ko mai alamarta.
     Sun koma sashen Abba Musbahu nanma dai matarsa Ammi da Ummah sunce basuga Nu'aymah ba, an kuma shiga ɗakin su Yusrah da ƴammatan sashen yayun su Nu'aymahr nanma babu ita, sai su kaɗaine da sauran ƴammata sa'anninsu na gidan da baƙi. Sake dawowa sukai Sashen Addah aka duba ko ina nanma dai babu ita, suka koma sashen Hajjo nanma haka. Zuwa yanzu kam hankalin kowa ya fara tashi, dan ko sallar Asuba wasu sun kasa samun nutsuwar yinta. 
      Duk da ba'a tunaninta a sashen samarin gidan haka dai aka shiga canma ko za'a dace. amma kuma bata nan. Yanzu kam dai kowa ya tabbatar Nu'aymah bata gidan, samarin gidan dasu Baba malam duk sun dawo massallaci suma an haɗu anata taraddadi, sai sake tambayar su Yusrah da akasan suna tare akeyi da Adawiya data dage take rusar kuka tamkar ranta zai fita.
       Gari ya waye tangaran, waɗanda basuyi sallaba suka samu sukaje suka yiyyyi batare da hankalinsu na tare da suba. Umm kam tama kasa magana sai ajiyar zuciya da taje faman sauke a jajjere. Shi kansa Baba Malam binsu kawai yake da kallo. Hajjo tuni ta fara kuka itakam. Ango Abdallah kam nasa tashin hankalin ai ba'ama magana, danshi ya dage sai sake bin ɗakunan gidan yake lungu da saƙo yana dubawa.

       Kamar wasa saiga ƙarfe 11am ta buga babu Nu'aymah babu mai kama da ita, saima cin karo da akayi da takarda a jikin Windown ɗakinsu an ajiye. Sai kayanta ƙwara huɗu da alamu suka nuna jehosu akayi ta Windown maybe.
        Nanah ce taga takardan, dan haka ta nufi inda su Baba malam ke tsaye da sauran ƴan uwansa ta miƙa musu da faɗa musu inda ta gani. Abban Adawiya ne ya amsa takardan daga hannun Nanah, ya buɗe yana gyara tsayuwarsa. Duk idanu su Baba malam suka zuba masa da ƙaguwar sonjin minene a ciki.

        Assalamu alaikum iyayena.

                 Kuyi haƙuri da abinda zaku wayi gari da shi daga taskar kuskurena, wlhy yanzu bana son Yah Abdallah akwai wanda zuciyata keso. Nasan babu wanda zan faɗamawa a cikinku ya fahimceni balle akai ga yarda, amma wlhy ina masifar son Ameer fiye da yanda kuke zato da tsammani. Banason na wahalar daku wajen ɗauramin aure da Yah Abdallah nazo kuma na zama sanadin ɓata zuminci da aka gina tunkan samuwarmu daga baya, shiyyasa na zaɓi bin Ameer mu gudu, shi kuma ku aura masa wata a cikin ƴan uwana. Na muku alƙawarin idan komai ya lafa zan dawo gareku ku ɗaura mani aure da masoyina Ameer. Ina fatan bazakuyi fushi dani ba dan ALLAH 🙏🏻😭.
           Na barku lafiya.
Daga ɗiyarku Zainab Sooraj Hashim (Nu'aymah).

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________

        Tsit wajen yayi babu wanda ya iya ko ƙwaƙwaran motsi, Baba malam sai faman kaɗa kai yake kawai zuciyarsa na kaikawo.
      Hajjo ce ta ƙaraso wajen ganinsu cirko-cirko. “Lafiya? Na ganku cirko-cirko? Ko anji labarin inda take ne?”.
       Duk kasa bata amsa sukayi, hakan yasa ranta ɓaci ta daka musu tsawa. “Wai kuna cikin hankalinku kuwa? Ina magana kunmin shiru kai ɗan Malam” ta ƙare maganar idonta akan Baba Malam (Abban Nu'aymah) dan bata faɗar sunansa saboda shine na fari, sai dai tace ɗan Malam.
       “Kiyi haƙuri Innah, da kanta ta gudu”. “Ban gane da kanta ta gudu ba? Kana haukane?”. Kasa amsa mata yayi, dan shi kaɗai yasan kalar tashin hankalin da yake ciki a halin yanzun.
      Abba Musbahu ne yace, “Innah inaga muje ciki, wannan ba maganar nan baceba”.  Zata sake magana ya kama hannunta suka nufi sashenta tacan baya inda falon mahaifinsu yake. Bin bayansu su Abban Abdallah sukayi, Baba Malam dai bai iya motsawa ba har tsahon wasu mintuna kafin ya bisu.

           Bayan haɗuwar duk wanda ya kamata a falon, Abba Musbahu ya sake maimaita abinda ke a rubuce a takarda, wadda Nu'aymah ta ajiye kamar yanda kowa yaji.
        “Kai wannan zancen ban yarda da shiba, ina Zainabu taga wayon wani yin wannan iya shegen? Wanene ma Amiru yake ko uwarwa? Tunda muke a gidan nan waya taɓa ganin Zainabu da saurayi ma?”. Hajjo tai magana ranta a ɓace.
      Shiru falon yayi, dan kowa yasan maganar Hajjo gaskiyace, babu wanda zaice ya taɓa ganin Nu'aymah da saurayi bayan Abdallah, dan Nu'aymah yarinyace mai shegen tsiwa da rashin tsoro, ko cewa akai ana sonta kai tsaye take faɗin an mata miji a gidansu. Bama ta yarda saurayi yay zuwa biyu wajenta........
      “Ina magana kowa yayi shiru, wlhy ni dai ban yardaba, sai dai idan wani munafukine ya sacemin jikata”. Hajjo ta faɗa tana fashewa da kuka.
       Baba Malam ne ya kalli Hajjon zuciyarsa na masa zogi, yace, “Innah karki saurin kareta, kinsanfa yaran yanzun ka haifesune amma baka haifi halinsu ba, mudai fara bincikar ƴan uwanta ƙila wani acikinsu yasan Ameer ɗin”.
       Girgiza kai Abdallah yayi shima cike da damuwa, “Baba ALLAH koni ban yarda wannan takardar Nu'aymah ce ta rubutata ba, mu dai bincika gaskiya”.
         Baba Malam yace, “Abdallah batun ba ita ta rubutaba kam bazai yuwuba, dan wannan rubutun natane, kuma da bakinta a jiya da daddare ta samemu da batun ita a fasa wannan aure ta fasa, bayan mun lallasheta ni da mahaifiyarta ta tafi sai gashi ta sake dawowa daga baya, sannan muna tare da Rudwan, sai dai nasan ganina tare da shi yasa batace komaiba ta gaidasa ta fita. Kaga kenan a lokacin ta silale tabar gidan?”.
          Addah tai saurin faɗin, “A'a dan ALLAH Yaya karmu yanke hukunci, mudai bincika ɗin ta bakin Abdallah”.
      “Humm” kawai Baba malam ya faɗa zuciyarsa na ƙuna, dukda shima dai wani gefe na zuciyarsa nata masa wasiwasi akan al'amarin.

        Yaran gidan duk aka tattaro, sa'anninta su Amal da yayunsu mata harma da ƙannensu mazan da matan. Ɗaya bayan ɗaya aka tambayesu ko sunsan Nu'aymah nada wani saurayi?. 
       Mafi yawancinsu sunce basu saniba, sai ƙalilan da sukace sun taɓa ganinta kusan sau huɗu da wani saurayi baƙi. Sai dai takance Yah Abdallah ne yake aikosa wajenta.
     Da mamaki Abdallah yace, “Ni kuma? Kai gaskiya a'a. Wlhy tunda nake ban taɓa aiko wani wajen Nu'aymah ba sai Ahmad kawai, gashi nan kuma zaune tare damu. danni ko abokaina da yawansu basusan Nu'aymah a ido ba”.
      Sosai abin ya sake ɗaure kan kowa a wajen. Adawiya dake sharɓar kuka tace, “Tabbas akwai wani Ameer dake zuwa wajenta, amma acewarsa shiɗin abokin Yah Ab ne, kuma ko jiyama ai yazo wajen walima”.
     Duk kallonta sukai. Abdallah yay saurin faɗin, “Wlhy kamar yanda na faɗa ban taɓa aiko kowa wajen Nu'aymah ba, amma k Adawiya zaki iya ganesa ne?”.
       Kanta ta ɗaga musu tana sheshshekar kuka.

        Hajjo tace, “Nifa gaskiya har yanzu ban yardaba sai naji ta bakin Zainabu, ko naga wata shaida da zata tabbatarmin da cewar guduwa tai da kanta. Kowafa yasan yanda Zainabu keson Abdallahi a gidan nan tunma bata san kantaba, bata tashi nuna mana bata sonshiba sai daren da za'a ɗaura mata aure da shi. Waye ya kawo wannan takardar? A ina kuma ya ganta?”.
        Nanah tace, “Hajjo nice na kawo, abayan Windown ɗakinsu na gani an ajiye, kuma harda kayantama a ƙasa”.
        “Muje na gani”. Cewar Hajjo tana miƙewa. Sauranma duk tashi sukai suka bita. Kamar yanda Amal ta faɗa haka suka taras, hardama ƙarfen zif ɗin akwati da alamu ya nuna ɓallewa yay wajen rufewa ko buɗewa.
      Maigadin gidan baba malam yasa aka kira masa, aka tambayesa ko yaga fitar Nu'aymah a gidan?. Yace shikam bai ganiba, dan tun sha ɗaya da kwata ya rufe gate ma, kuma babu wanda ya sake shiga da fita.
       Omar ne ya bada shawarar a duba ta ƙaramin gate na massallaci to. Babu musu akabi shawararsa, da yake yau da asuba ta babban gate duk su baba malam suka fita massallaci sai ga sayin takalma an gani dana akwati. Ƙaramin sayi na mace, sai babba da alama ta nuna takalman mazane, sai sayin jan akwati dake biye da sayin takalman har wajen massallaci, sai dai kasancewar akwai kwalta a titin layin sai ba'aga inda sayin ya tsaya ko ya nufa ba.
       Sun dawo cikin gida ana taraddadai saiga wani yaro riƙe da wayar Nu'aymah acewarsa cikin filawoyin massallaci ya gani.
      Amsar wayar Abba Musbahu yayi aka hau dubawa bayan anba Adawiya ta cire lock ɗin dan ita kaɗai ta sani. Ana buɗewa a kan WhatsApp aka samu wayarma, cikin kuma inbox ɗin wani datai saving da suna (Sweet Ameer). Scrolling saƙwanin Abba Musbahu yayi ya koma har can farko ya fara karantawa. 
     Gaba ɗaya hirarrakine tsakanin Nu'aymah da Ameer kuma ta soyayya harma da alƙawarin auren juna kota halin ƙaƙa. Har zuwa saƙon ƙarshe-ƙarshe da duk ya zam na ƙulla yanda zasu gudu ita da shi.
     Zuwa yanzunkan kowa jikinsa yayi sanyi, Umm da baba malam sai faman haɗiyar zuciya suke na ɓacin rai, duk da zuciyar Umm sam taƙi gaskata gaskiyar wannan al'amari, dan tafi kowa sanin wacece ɗiyar tata da halayyarta harma da tarbiyyar data bata. Babu abinda Nu'aymah ke ɓoye mata a rayuwa, dai-dai da hira idan tayi ita da Abdallah saita sameta har ɗaki ta bata labari, daga ƙarshe-ƙarshen nan nema take ƙwaɓarta dan kartaje bayan sunyi aure tace zata cigaba dayin hakan. Abinda ya tsoratata a zancen shine sunan Ameer, dan lallai kusan sau huɗu Nu'aymah na kawo abu tace Yah Abdallah ya aiko mata ta hannun abokinsa Ameer, kuma gaba ɗaya saƙwanin har gida yake zuwa ya sameta ya bata. To gashi kuma shi Abdallah yace baida abokima Ameer ɗin balle ya aikosa wajenta. ‘Innalillahi wa'inna ilairraji'un. Mike shirin faruwa da ɗiyarta ne haka? Ya ALLAH ka bayyana abinda ke ɓoye akan wannan al'amari dai cikin sauƙi’. Wannan sambatun Umm keta famanyi a cikin ranta zuciyarta na mata zafi da ɗaci. Yayinda ɓacin ran da take gani shimfiɗe a fuskar mijinta ke sake tada mata hankali.

       A yanzu kowa ya yarda Nu'aymah guduwa tayi, sai dai Hajjo dai bata daina faɗin cewar tana wasiwasiba, dan da cataima sai dai idan Ameer wani abu yayma Nu'aymah harta bishi. Babu wanda yabi takan zancenta dan suna ganin akwai ruɗun tsufa tattare da ita.
          Ana cikin wannan taraddadi Abdallah yaci karo da saƙon Nu'aymah a wayarsa wanda baisan da shiba. Danshi tunda yay mata magana yaga bata bashi amsaba ya jiya wayar bai sake bi takantaba, tunda da safe kuma an tashi da tashin hankalin rashintane.
            
          Assalamu alika.

    “Yah Ab kayi haƙuri karkaga ban maka adalciba, kasan shi so tsuntsune, gobe ya tashi kan wannan ne ya koma kan wancan. Tabbas na soka a baya kamar babu wasu maza a duniya sai kai kaɗai. Kaima kasan akwai ƙuruciya a kaina a lokacin, shiyyasa sam na kasance bansan Zaɓin daya dace dani. Yanzu kam idanuna sun buɗe ras, zuciyata ta samo zaɓinta. Nasan kozan shekara faɗama iyayenmu bana sonka yanzu bazasu yardaba, bakuma zasu fahimceniba sai sun aura min kai, shiyyasa na zaɓi guduwa, idan komai ya lafa saina dawo a auramin zaɓina. Kaima dan ALLAH ka nema dai-dai kai ka aura kaji. Na barka lafiya Yayana, ina fatan bazaka zauna jirana ba, kuma bazakayi fushiba.

         Ƙanwarka Nu'aymah Sooraj Hashim.

      Cikin matsanancin fushi Abdallah yay wurgi da wayar hawaye na sulalo masa saman kumatu masu masifar zafi, jikinsa sai rawa yake na ɓacin rai. Dama shi haka yake bai iya fushi ba.
        Duk kansa samarin sukayi suna tambayar lafiya?. Kansa ya dafe yana cigaba da kukansa kamar wani yaro ƙarami. yace, “Wlhy ina sonta, amma miyasa Nu'aymah zatamin haka? Minene aibuna dan ina ƙaunarta. Wlhy bazan iya auren kowaba sai ita”.
        A tsawace Baba malam ya miƙe yana faɗin, “Dole ne kuwa ka auri watanta a yau ɗin nan Abdallah, ita bata isa kunyatamu ba, bayan mun tara mutane. Inaso daga yau, daga yanzu ka manta da Nu'aymah a cikin zuciyarka har abada kamar yanda nima na manta da ita matsayin ɗiyar cikina”.
          Cike da tashin hankali kowa yake kallonsa a falon, dan kowa yasan dama Baba malam yanada zuciya, sannan kaifi ɗaya ne shi, idan yace A dolene A ɗin za'abi, idan yace A'a shima dolene abi............✍

Wannanfa shi ake kira da gaba kura baya sayaƙi😥. Nu'aymah kizo ki bamu gaskiya batu ko masan ina matsalar take ne?.😭

         
  ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.



*_Typing📲_*


      

               *_SARAN ƁOYE!!_*



    *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


Free page😋


No. 4

WAIWAYE ADON TAFIYA.

          Malam Hashim musa shine asalin mai gidan. Babban malami mai tarin ilimi daya taka rawar gani a duniyar musulunci. Yasha gwagwarmaya ƙwarai da gaske na ganin ilimi ya yaɗu da faɗaɗa cikin al'ummarmu ta nagartattun hanyoyi.
       Kasancewar yayi gwagwarmayar rayuwarsa ta neman ilimi lokacin ƙuruciya a garin Jibiya ta jihar katsina sai ake kiransa da suna ɗan jibiya. 
        Matan Malam Hashim ɗan Jibiya biyu kacal a duniya. Zainabu (Hajjo) sai Zulaiha.
     Ƴaƴansa Huɗu duk maza, kuma dukansu Hajjo ce ta haifesu, dan har Zulaiha ta koma ga ALLAH bata taɓa ko ɓatan wataba.
        Sooraj mahaifin su Nu'aymah da ake kira da Baba Malam shine babban ɗansa. Sai Rudwan mahifin Abdallah wanda shima yanada iliminsa sosai, amma shi yana kasuwanci ne, duk da suma su Baba malam suna kasuwancin. Sai Mustapha Mahaifin su Adawiya, shima dai malamine dan tare da Baba Malam suketa ƙoƙarin cigaba da ginin da mahaifinsu ya bari na yaɗa ilimi. Sai auta Musbahu, shine mahaifin su Yusrah, shima dai malamine, yanama addini hidima yana kuma business.
         Kamar yanda kukaji a farko gidansu Nu'aymah gidan manyan malamaine sananne, sannan kuma ƴan kasuwane na gaske, dan har sunada kamfanin dake sarrafa Mangyaɗa da kuma sabulu, suna kuma sufurin kayan masarufi sosai ta hanyoyi daban-daban cikin farashi mai sauƙi duk daga kamfaninsu mai suna ƊAN JIBIYA FAMILY.
          Kamfaninsu sanannen kamfanine dake da haja a lungu da saƙo na ƙasarnan sabida sauƙin kayansu. Sannan kuma sanannun malamaine da duniyar musulinci ke alfahari dasu a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sunada manyan makarantun da ake koya ilimin addini zallah a cikin kano dama wasu jihohi maƙwafta, suna kuma da gidan marayu nasu na kansu da suka assasa domin ladan ya ringa isa zuwa ga mahaifinsu da ALLAH yayma rasuwa kusan shekaru ashirin da suka shuɗe.
     Family ne da alkairansu a bayyane yake wa duniya duk da suna ƙoƙarin ɓoye kansu dan kar asan sune keyi. To amma masu iya magana kance alkairi dankone baya faɗuwa ƙasa banza.

           Sooraj (Baba Malam) shine ya zame musu tamkar mahaifi bayan rasuwar Malam Hashim, ya kama ƴan uwansa ya dunƙule kansu waje ɗaya babu mai jin kansu sai ALLAH. Suna ƙaunar junansu matuƙa da mutunta juna. Komai nasu sai sun nema shawararsa kamar yanda shima idan zaiyi wani abu sai ya tarasu ya nema tasu duk da suna a ƙasa dashi.
       Tun mahaifinsu nada rai suka gina wannan gida daya kasance gari guda, dan malam Hashim ya mallaki filin ne tun anguwar babu wasu gine-gine kirki, da farkoma noma yakeyi a filin, sai da yaransa suka fara tasawa ya zagayesa yay massallaci da islamiyya, ya kumayi ƙaramin gida a ciki yana zaune da iyalansa. Bayan rasuwarsa arziƙin kasuwancinsu ya ƙara haɓaka sai suka gyarashi aka faɗaɗa massallacin da Islamiyyar, suka kuma ginama kowa sashensa inda zai zauna da iyalansa. A hankali harkoki na ƙara haɓaka musu suna sake gyara gidan har ALLAH ya kaisu ga wannan matsayin suka kasance cikin tsakkiyar birnin kano.

     Sooraj (Baba Malam) ya jima baiyi aure ba, dan sai da takai har Hajjo na nuna masa ɓacin ranta akan hakan, sannan yay auren zuminci da wata ƴar ƙanwarta mai suna Salamatu. Rana ɗaya aka ɗaura musu aure su Uku, shi da ƙannensa biyu. Mustapha (Abban Adawiya) da Rudwan (Abban Abdallah) Bayan aurensa da Salamatu ta haifa masa yara uku duk maza. Yayinda shima Rudwan matarsa keda yara uku a lokacin, Maza biyu mace ɗaya. Abdallah shine babba, sai Omar, sai Aysha. Amma Mustapha matarsa bata haihuba.
     Shekarar da Musbahu zaiyi aure a shekarar ne Matar Baba malam Salamatu da ƴaƴanta uku, sai matar Mustapha sukai haɗari a hanyarsu ta zuwa Jigawa suka rasu. Lokacin shi Rudwan matarsa na fama da laulayin ciki bata bisuba, sai yaran kawai. Dukansu ALLAH yay musu rasuwa a motar, Abdallah ne kawai keda sauran kwana a duniya. Shima dai ya bugu, dan yasha doguwar jinya kamar bazai rayuwaba ALLAH dai ya raya kayansa bayan yasha wahala. Gida ya koma babu yara ko ɗaya sai Abdallah kawai, sai kuma cikin jikin Momynsa.
      Ba ƙaramin tashin hankali suka shigaba a wannan lokacin, dan Hajjo yitai kamar ta zare dan kiɗima, gawarwakin jikokinta biyar da surukanta biyu da driver aka sallata a rana ɗaya kolaci ɗaya, haka aka jera kabirburansu abin tashin hankali😭. (Ya rabbi ka gafartama iyayenmu damu baki ɗaya😭🙏🏻).
      
       Bayan rasuwar matan su Baba malam basu sake maganar aureba har Momyn Abdallah ta haifi cikinta namiji, wanda aka maidama suna Omar, bayan kamar wata biyu da haihuwarta amaryar Musbahu ma ta haihu mace, ita kuma taci suna Jameela.
          Hajjo nasan su Baba malam su ƙara aure, amma kuma tausayinsu yasa ta kasa takura musu, sai dai ta cigaba da binsu da addur fatan samun mata nagari da zasu maye musu gurbin matansu. Ansha kawo musu matan aure har gida, musamman kasancewarsu malamai kuma masu kuɗi Alhmdllh. Sai dai basu taɓa amsaba, dan basu farfaɗo daga magagin rashin family ɗinsu ba.
       Bayan shekaru biyu da rasa iyalansu ƙwatsam ALLAH ya haɗa Baba malam da Firdausi (Umm) a wajen wani walimar yaye ɗaliban makarantar BUK. Tunda ya ƙyalla ido akanta bai ɗaukeba, duk inda ta shiga ta fita idanunsa a kanta, gashi babu damar mata magana saboda sune manyan baƙi a wajen, hasalima shine yay lecture wa ɗaliban mai ratsa jiki. Inda itama anan Umm ta mutu ason wanda tasan ko kallo batama ishesaba, amma kasancewarta mace miskila ta gaske, kuma mara son yawan magana sai ko a fuska bata nunaba.
     Kamar yanda Firdausi (Umm) ta mutu akan son Malam Sooraj Hashim haka babbar ƙawarta, aminiyarta Fauza (Addah) itama ta mutu akansa lokaci guda, sai dai itama ɗin dai bakinta bai furtaba, sai dai kasancewarta mace mai faranfaran da barkwanci dason jama'a sai taita yabashi har Firdausi ta gaji tai mata ƙorafin ta isheta. Dariya tayi a wancan lokacin, dan itace kaɗai ta iya zama da Umm kasancewarta mace mai bahagon hali, ga rashin son wasa, dan sam Umm bata da fara'a, bakuma tason yawan wasa kamar ƙawarta Fauza (Addah).
          Ahaka taro ya tashi lafiya Fauza da Firdausi na begen abinda basa tunanin zasu samu a zukatansu, sai dai kuma abinda basu saniba shine Malam Sooraj tunkam yabar makarantar yasa ake bibiyar masa Umm, har aka tashi kowa ya kama gabansa ana binsu a baya har gida anguwarsu. Mai bin nasu yana ganin inda suka shiga ya koma da baya yaje ya sanarma Malam Sooraj Hashim. Baba malam yaji daɗi matuƙa, bai kumayi ƙasa a gwiwa ba ya sake sakawa aka bincika masa mahaifin Firdausi (Umm).

            Firdausi (Umm) da Fauza (Addah) ƙawayene konace aminai. Anguwarsu ɗaya, hasalima katangarsu ɗaya, sannan iyayensu Aminaine tun zamanin ƙuruciya. Hakanne ya saka iyayensu matama zama ƙawaye na ƙut da ƙut da babu maijin kansu. A taiƙace ma dai sun zama ƴan uwa. Umm itace ta sakama Fauza suna Addah, saboda sunan babbar yayarsu kenan itama, suna kiranta Addah, shine itama sai take cema ƙawarta Fauza Addah, ahankali suma sauran ƴan gidan suka koma kiranta Addah.
       Mahaifin Fauza (Addah) yafi na Firdausi (Umm) arziƙi, dan yana ɗaya daga cikin ƴan kasuwar leda da akeji dasu a cikin kano a wancan lokacin, sannan kuma ɗan boko ne sosai. Mahaifin Fauza (Addah) shike ɗauke da nauyin karatun Umm tun daga firamare har zuwa jami'a. Dan yayun Umm duk iya aji shida na firamare babansu ya ciresu yay musu aure. Itako tana bala'in son karatu, musamman da taga Fauza (Addah) zata cigaba dayi, tata roƙon baban ya barta amma yaƙi, yace itama aure zai mata kamar yayunta. Hankalinta ya tashi, dan haka ta nufi mahaifin Addah ta sanar masa. Shine ya lallasheta, ya kumace ta kwantar ta hankalinta indai karatune zatayi insha ALLAH, shinema zai ɗauki nauyin komai na karatun nata har sai iya inda ta gaji ita da Addah.
    Taji daɗi sosai, dan tasan indai yayama babanta magana bazai musaba saboda ƙaunar da sukema juna. Ilai kuwa, baban Addah nama baban Umm magana ya amince, atare aka kaisu makarantar sakandire, bayan sun kammala kuma suka nufi jami'a duk da Mahaifin Umm baiso hakaba, amma kunyar amininsa ta hanashi yin magana ya zuba ido.
    To da yake komai aka sakama rana zaizo ƙarahe sai gashi cikin hukuncin ALLAH sun kammala, a randa suka kammala ɗin kuma Umm tai gamo da mijin aure.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________

        Bayan kwana biyu da haɗuwar Umm da Malam Sooraj Hashim Jibiya yazo har gida da kansa wajen babanta ya nema izinin yin magana da ita, tare da tambayar ko an mata mijine?.
     Baban Umm yaji daɗi sosai, dan babu wani mahaluki dazaiƙi jinin gidan Malam Hashim Jibiya, nagartaccen gidan dake cike da nagartattun mutane, manyan malamai da ake alfahari dasu a ciki da wajen ƙasarma gaba ɗaya.
        A take babu wani jan zance ya amsa masa da ya nema so wajenta, inhar tana sonsa shikuma yayi alƙawarin aura masa ita. Malam Sooraj (Baba Malam) yayi farin ciki da wannan karamci, haka ya koma gida cike da ɗokin wannan al'amari, da tarin godiyar UBANGIJI kuma. A ranar baiyi magana da Umm ba, sai bayan kamar kwanaki biyu ya sake dawowa gareta. Inda akai masa masauki a gidan su Addah, a falon babansu.
     Duk da Addah tayi murnar ganinsa a gidansu sai bata zaƙeba har saida taji dalilin zuwan nasa. Jikinta yayi sanyi hartasha kuka jin ba wajenta yazo ba. Dan tun ran walimar yayesu zuciyarta sam bata huta daga begensaba, tanason faɗama ƴar uwarta Firdausi (Umm) amma takasa furtawa, duk sanda ta tunkareta da zancen sai taji gabanta na faɗuwa.
       A yau da taji ƴar uwarta yake so saita godema ALLAH da bata furta mata zancenba, ta kumayi alƙawarin mantawa da Malam Sooraj Hashim jibiya a ranta har abada, dan tafi ƙauna da farin cikin ƴar uwarta ta samesa fiye da ita. Haka ta cire komai a ranta taita ƙoƙarin mantawa da shi, ta kuma cigaba dama ƴar uwarta addu'a da murnar samunsa matsayin mijin aure.
           Tun daga wannan ranar Addah bata sake zama tayi koda tunanin Malam Sooraj ba har aka ɗaura musu aure da Umm. A ranar da aka kai Umn gidan Malam Sooraj Hashim Jibiya, aranar Addah tai gamo da Malam Mustapha ƙaninsa da yazo ɗaukar amarya. A take shima soyayyar Addah ta shigesa, baiyi ƙasa a gwiwa ba kuma ya sanarma ɗan uwansa. Kamar yanda yabi nasa neman auren bisa matakin shari'a haka ya bima ƙaninsa har iyayen Addah suka amince suma.
         Kwatanta muku kalar farin cikin da Addah da Umm suka shiga a wannan lokacin ɓatama lokacine, sunyi kuka sunyi murna har basu san adadiba, ba ƙaramin godiya sukaima UBANGIJI ba daya sake dunƙulesu a gida ɗaya matsayin matan yaya da ƙani. Itama Addah ba'aja wani dogon lokaci ba aka ɗaura aurenta da Mustapha aka kawota.
       Da farko ganin kan Addah da Umm a haɗe yake ya saka Momyn Abdallah jin haushinsu, ta ware kanta bata shiga cikinsu duk da ɗanta Abdallah kullum yana wajen Umm. Dan tunda tazo gidan yazama ɗan ɗakin amarya, ahankalima ya dinga zare kayansa yana komawa dasu sashen Umm. Tun Momynsa na faɗa harta haƙura ta zuba masa ido kawai. Daga baya kuma ma saita kwantar da hankalinta suka ƙulle kansu su huɗu ganin Addah da Umm basu da damuwa. Ita dama matar Abba Musbahu babu ruwanta, dukansu tana girmamasu da mutintasu kasancewarsu matan yayun mijinta. Duk da kuwa bazasu girmetaba sai dai suyi sa'anni ma. Ita kanta Momyn Abdallah ba girmarsu zataiba, kawai dai an mata auren wurine saɓanin su da duk sunyi karatu.

         Addah ta samu ciki da zuwanta gidan, amma Umm shiru kakeji. Sunyi murna sosai da cikin Addah, har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ɗanta Namiji santalele. Wanda yaci suna Hashim, amma suna kiransa da malam ƙarami. Babu jimawa matar Musbahu ta haifo nata cikin itama Namiji, yaci suna Ahmad. Itama tsakaninsu babu nisa da Momyn Abdallah datai haihuwa ta biyar, itama ta haifo mace aka sake maida mata Aysha.
      Sosai su Baba malam sukai farin ciki family ɗinsu ya dawo kamar da. Inda sukema Umm Addu'ar itama ALLAH ta kawo mai albarka. Haka haihuwar matan gidan ta cigaba da tafiya a jajjere. Sai da sukai haihuwa hurhuɗu kafin ALLAH ya bama Umm ciki itama. Kowa ya tayata farin ciki sosai, musamman ma Addah da ayanzu takeda yara huɗu, Ɗaya namiji Uku mata. Sai Momyn Abdallah nada huɗu, maza biyu mata biyu. Matar Abba Musbahu nada huɗu itama duk maza.
      Umm ta haihu Namiji sannan su Addah duk suna fama da laulayi ƙananun ciki, sai dai kuma kwanan jaririn Uku ya koma. Sosai Umm tasha kuka, amma daga ƙarshe saita share hawayenta dan tasan ALLAHn daya bata ya karɓa ya fita sonsa. sannan ma yaran gidan babu wanda kemata shamaki da nasa, faɗi tashinsu sukeyi a sashenta kamar nata, musamman ma Abdallah da ƴaƴan Addah da inba faɗa maka akaiba bazaka taɓa sanin ba nata baneba.
     Cikin amincin ALLAH bata rufa wata uku da haihuwa ba saiga wani cikin, inda shima Baba malam yay murna matuƙa fiye ma dana farko. Su Addah sun rigata haihuwa. Matar Abbah Musbahu ce ta fara haihuwar ƴarta mace da taci suna Yusrah, sai Addah ta haihu itama mace, aka saka mata Adawiya, sai Momyn Abdallah ta haihu itama dai mace, aka saka Safiyya sunan mahaifiyarta, sai dai ana mata alkunya da Amal. Bayan haihuwarsu da watanni itama Umm ta sake haifo ƴarta mace mai kama da ita. Wadda taci suna Zainab, da yake sunan hajjo ne sai ake mata alkunya da Nu'aymah.
      Bayan haihuwar Nu'aymah da kusan shekara biyar Umm ta sake haihuwar yaro ɗaya namiji Muhammad, daga nan kuma shiru kakeji bata sake ko ɓatan wata ba. A lokacin Addah ta sake haihuwa uku, mata biyu da namiji ɗaya. Sai yazam tana da yara bakwai. Mata shidda maza biyu. Itama Momyn Abdallah ta ƙara biyu ƴammata tagwaye, tanada mata huɗu maza uku itama. matar Abbah Musbahu ko ɗaya ta ƙara shima namiji, tanada maza biyar mace ɗaya kenan. Daga haka haihuwar ta tsaya musu su duka babu wanda ya ƙarayi.

      Rayuwar gidan tacigaba da gudana cike da birgewa da ban sha'awa, inda ALLAH keta ƙara ɗaga darajar mazajensu ta ɓangaren yaɗa da'awa da ilmantar da bayin ALLAH da taimakonsu ta hanyoyi da dama. Suma kuma ba'a barsu a bayaba wajen yima addini hidima. Ƴaƴansu sun tashi kansu a haɗe cike da tarbiyya kula. Komai tare ake musu.
       Akwai shaƙuwa sosai tsakanin Abdallah da Nu'aymah, dan tunda aka haifeta ya kasa ya tsare. Komai yaci sai ya ragema Nu'aymah duk da alokacin yayi girma sosai, dan harma ya kammala firamare yana shirin shiga sakandire. Babu mai dukan Nu'aymah ya kwana lafiya a gidan. Umm ce kawai yake ma ɗan kawaici, itama zaita fushi da itane koda bazaiyi maganaba. Komai ma Abdallah na Nu'aymah ne, firarsa Nu'aymah, fushinsa sai an taɓa Nu'aymah, kukansa sai Nu'aymah na kuka. 
      Itama kamar tasan abinda yake yi, tanama kowa ƙiwa a gidan amma banda Yah Ab, duk abinda ta samu saita rage ta ajiye masa. Tun kowa na ɗaukar lamarin nasu wasa har aka fahimci yafi ƙarfin wasan aka koma binsu da addu'a.

         Nu'aymah nada shekaru tara a duniya su Baba malam suka buɗe kamfanin mangyaɗa a garin Lagos, hakan yasa dole Malam Rudwan Hashim Jibiya (Abban Abdallah) ya koma can da iyalansa dan ya dinga kula da shi. Lokacin komawar tasu kam anga tashin hankali wajen Abdallah saboda rabuwa da Nu'aymah. Da ƙyar aka yakicesa daga jikinta, danfa shi yace inhar zaije sai dai da ita, kokuma a barsa anan wajensu. Ganin yanda yay matuƙar ɗaga hankalinsa yasa Hajjo sakawa a barsa nan gida badan Momynsa tasoba. Idan anyi hutu ya ringa zuwa musu, idan kuma sunzo shikenan.
        Haka yana gani iyayensa suka lula Lagos aka barsa a kano saboda Nu'aymah. Bayan tafiyarsu Abban Abdallah da shekar biyu shima Abba Musbahu daya ƙara auren mata ta biyu ya bisa tare da Ammin Ahmad, yabar amaryarsa anan gidan yana zuwa weekend, dan aiki yayma Abban Abdallah yawa acan shi kaɗai, ga harkar Addini gata kasuwanci, ga nashi kuma yanayi shima.
      Gida sai ya koma daga hajjo sai Umm da Addah da Ummah amaryar Abba Musbahu. Iyalan Baba Malam dana Abba Mustapha kenan. Sai idan sun sami hutune matan kanzo da yaran nan suyi, sukuma su Abbah sai suke zuwa weekend idan matan nasu sunzo nan.
        Haka rayuwar ta cigaba da tafiya, shaƙuwa na sake ƙulluwa tsakanin Nu'aymah da Abdallah, hakama tsakanin Adawiya da Nu'aymah, dan sun taso sa'anni su biyu tunda su Yusrah suna Lagos. 
     Komansu tare ake musu, babu maijin kansu, Hassana da Hussaina ma ake kiransu saboda shaƙuwa. A hankali Adawiya ta kwaso kayanta ta dawo ɗakin Nu'aymah dake sashensu, suka zama a ɗaki guda, makaranarsu ɗaya, ajinsu ɗaya. Kai komaima nasu ɗayane. Gefe ga soyayyar Nu'aymah da Abdallah, inda itama Adawiya son Abdallah keta mata saƙa a zuciya batare da kowa ya saniba har ita kanta. Bata tashi farga dason da take masaba sai da yay mata babbar illa a jini da zuciya, har takai bazata iya haƙura ta barma Nu'aymah ba.

         Tunda Abdallah ya kai minzalin aure bayan kammala karatunsa na degree aketa fama da shi yayi aure amma yaƙi, acewarsa Nu'aymah yake so. An lallaɓashi akan ya auri wata idan Nu'aymah ta isa saiya ƙara da ita, amma sam yace bazata saɓuba, zai jirata ko shekara nawane. Abin ya bama kowa mamaki, dan lokacinma fa Nu'aymah da Adawiya suna firamare aji shidda ne. Haka kowa ya haƙura aka zuba masa ido, sai ma ya koma karatu da kasuwancinsa na kansa daya ƙirƙira, ya duƙufa wajen faɗaɗa karatunsa na addini kuma tamkar iyayensa. 
           A wannan shekarar Abban Abdallah ya sake komawa Abuja da zama inda canma suka buɗe reshen Company ɗinsu na mangyaɗa, sai aka bar Abba Musbahu a Lagos. Tunda suka dawo Abuja Momyn Abdallah ta fara jan yaronta jikinta sosai, a hankali ta janye ra'ayinsa ya koma Abuja da zama wajensu, inda harkokin kasuwancinsa suka fara faɗaɗa daga Nigeria zuwa ƙasar Saudia. Lokacin kuma Adawiya da Nu'aymah sun shiga sakandire.
     Suna aji uku a secondary Abdallah ya koma kara faɗaɗa iliminsa na addini a ƙasar Saudia inda yake kasuwancinsa yanzu, sai yazam baya zuwa sai dai aiko da kaya Nigeria Omar da Ahmad na kulawa dasu suma suna aika masa na Nigeria can.
       
       Nu'aymah yarinyace ƙyaƙyƙyawa fara masha ALLAH, dan tana kama da mahaifiyarta sosai, yarinyace mai shegen wayo ga rashin tsoro ga tsiwa. Tsula tsiyarsu suke ita da Adawiya fiye da zato, kullum cikin jan faɗa suke a makaranta daga boko har islamiyya. Duk da rashin jinsu yarane masu kaifin basira da hazaƙa musamman ma Nu'aymah, tana da matuƙar ƙoƙari, dan tun tana aji biyu na secondary tayi saukar Qur'ani, bayan tayi da shekara ɗaya itama Adawiya tayi. Bayan duk sunyi sauka suka juya hadda, tare da karatun sauran littatafai kuma. 
     Hazaƙar Nu'aymah a makaranta yasa suna aji biyar wani malami ya bada shawarar a barta kawai ta zana ssce a wannan shekarar, koba komai zata kammala jami'a da ƙarancin shekaru. Baba malam ya amshi wannan shawarar, musamman daya duba maganar auren Nu'aymah da Abdallah da kowa ke jira, ya yanke shawarar tana zana ssce za'ayi auren sai taje ta cigaba da karatunta a ɗakin mijinta kawai. amma saiya sa suyi ssce ɗin tare da Adawiya. Wannan shine ya sakasu gama makaranta a wannan shekarar. Adawiya dasu Amal nada shekaru sha bakwai cif, Nu'aymah kuwa bata cikaba har yanzu, tana sha shida da wasu watanni dan su Adawiya sun girmeta...............✍   


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_Typing📲_*


      

               *_SARAN ƁOYE!!_*



    *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


Free page😋

     _Daga yau free pages sun ƙare masoya. Ku garzayo domin samun waɗanan littatafai guda biyar akan farashi mai sauƙi. Dan girman ALLAH kibi ta hanyar data dace ki mallaki naki😅, karki zama cikin masoya masu mana SARAN ƁOYE akan kasuwancinmu😢🙏, muna alfahari daku aduk inda kuke. Muna godiya kuma da ƙaunar da kuke nuna mana irin trillions ɗin nan. Idan nace ku na dabanne ina nufin na daban har cikin raina😘😘🤝🏻_.


*_Masu buƙatar mu saka musu tallar kayan sana'arsu zasu iya zuwa suyi magana damu domin tayasu tallata hajojinsu a yanar gizo😘🤝🏻_*.


No. 5

.................“Indai har a yau dole sai an ɗaura auren Abdallah da wata kamar yanda Yaya Malam ya faɗa, to kuwa sai dai a ɗaura masa da ɗiyar ƴar uwata Nusaiba!!”. 
        Abban Abdallah dake shirin fita wajen ɗaurin aure ya tsaya cak daga ƙoƙarin saka maɓallin rigar farar shaddarsa ƴar ciki yana kallon Momy ta mirror. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya cigaba da abinda ya keyi. 
        Ƙarasa shigowa cikin ɗakin tayi ta tsaya a bayansa cike da damuwa. Sai da ya gama saka maɓallin guda uku sannan ya ɗauki babbar rigar itama ya warware zai saka. Saurin riƙe rigar Momy tayi hawaye na zubo mata saman fuska. Yanzu kam kallonta yayi da ƙyau yana ƙoƙarin haɗiye damuwarsa. “Na zata mun gama wannan maganar tun shekaru uku da suka shuɗe Khadija”.
      Sosai ta fashe masa da kuka yanzun kam tana kallonsa cikin ido, “Abban Abdallah dan ALLAH ka fahimcen......”. “Anƙi a fahimcekin Khadijah!!”. Ya faɗa a tsananin tsawace jikinsa har yana rawa. Ya fisge rigarsa dake a hannunta tare da nuna mata hanya alamar ta fice masa a ɗaki.
       “Abban Abdal.......” “Khadija!!!”. Ya kira sunanta da tsawa fiye dana farko. Baya taja a firgice ta manne da bango, sai kuma ta fashe da kuka bakinta na rawa alamar tanason yin magana amma tana shakka. 
    Tsaki Abba yay ya jefa babbar rigar saman gado yay ficewarsa ya barta a ɗakin. Can bayan ɗakunansu ya zagaya yanata huci. (nace, “Ashe ba Baba malam bane kawai mai zuciya a gidan😂).

        Zubewa ƙasa Momy tayi tana kuka abin tausayi, kusan mintuna huɗu da fitar Abba akai Knocking ƙofar dayin sallama. Saurin share hawayenta tayi ta miƙe tsaye jin muryar Abdallah. Sai da ta kalla kanta a mirror ta sake cirar tissue ta gyara fuskar da ƙyau sannan ta amsa masa sallamar da bashi izinin shigowa.
      Jikinsa a sanyaye ya shigo, ya ƙaraso cikin ɗakin sosai idanunsa akan mahaifiyarsa da itama kallonsa take cike da tausayawa. Matsowa tai da sauri kafin ya ƙaraso, ta kama hannunsa ta zaunar a bakin gadon tana faɗin, “Abdallah kana lafiya dai ko?”. 
           “Momy bana a lafiya wlhy”. Ya faɗa tamkar zai fashe da kuka. Murmushin ƙarfin hali Momy tayi, kusa da shi ta zauna tana ƙoƙarin haɗiye tata damuwar. Ta kamo hanunsa cikin nata ta rumtse. “Abdallah nasan dole ka tsinta kanka a cikin ruɗani game da wannan al'amarin, sai dai dan ALLAH ka kwantar da hankalinka kaji, kasa a ranka haka shine mafi alkairi shiyyasa ALLAH ya ƙaddara hakan. Nu'aymah ba ita bace autar mata, bakuma dama an halicceka domin ita kawai bane ba........”
      “Momy karkice haka, wlhy ina son Nu'aymah sosai, da sonta na rayu tun ban gama sanin ciwon kaina ba. Amma dan ALLAH Momy ki faɗamin inada wani haline mara ƙyau da zaisa Nu'aymah ta ƙini?”.
    Murmushi Momy tayi, takai hannu saman kumatunsa ta shafa. “Baka da wani aibu Abdallah na, babu wata mace da zaka tunkara da kalmar so ace ta gujeka. Itama ƙuruciya ce da rashin sanin ciwon kai ke ɗawainiya da ita. Shawara ɗaya zan baka shine ka kwantar da hankalinka, ka cigaba da addu'a kuma, inhar Nu'aymah alkairi ce a gareka, ALLAH kuma ya ƙaddara zata kasance cikin matanka ALLAH ya dawo da hankalinta gareka. Idan kuma ba alkairi bane aurenta ALLAH ya cire maka ita a zuciyarka kaji. Zan tayaka da addu'ar nan nima insha ALLAH”.
     Kansa ya ɗaga mata hawaye na sulalo masa a ido ɗaya. Momy ta saka babban yatsanta ta ɗauke masa shi tana murmushi. “Banason ganin wannan hawayen Sweetheart kaji”. Nanma kai kawai ya jinjina mata yana haɗiye tsantsar damuwarsa.
      “To amma Momy ni banason a auramin kowa, a bari kawai zan jira Nu'aymah. Na roƙi Baba Malam hakan amma yaƙi saurarena, nasa Abba ma bazai saurareniba tunda basa tsallake maganar Baba malam”.
       Shiru Momy tai kamar wadda ta tafi tunani, sai da Abdallah ya ɗan taɓata da kiran sunanta sannan ta sauke gajeren numfashi da kallonsa. “Abdallah kaima ka sani babu wanda ya isa canja abinda Yaya Malam ya faɗa a gidan nan, ko Hajjo goyama duk abinda ya sharɗanta baya takeyi. Babbar damuwata kar ace za'a aura maka cikin ƙananun yarannan Yusrah ko Adawiya, dan kaga dai Hajarah da Kubrah duk sunada samarinsu kuma kowa yasani a gidan nan, tunda har an tsaida magana, jira kawai ake su kammala karatunsu a ɗaura musu aure. Abdallah kullum shekaru kake ƙarawa ba ƙuruciya ba, ka kai minzalin da ya kamata ace ka ajiye iyali tuni, da ace baka zauna jiran gawon shanu ba da yanzu ɗanka ko ƴarka zai kai shekara biyar koma fiye da haka Abdallah. Abdallah dubeni tsufa fa nakeyi, ina buƙatar jikokina kamar yanda nasan kaima kana buƙatar mace tare da kai. Ya kamata ace ka auri yarinyar da zata iya kula da duka ɗawainiyarka ba wadda zakai tunanin zaman raino ba Abdallah. Kayi nazari akan maganata ka ɗaurata a mizanin fahimta. Aysha, Sumayya, Badariyya, Maryam duk ƙannanka ne a gidan nan, amma ka duba shekarunsu nawa da yin aure?, dukansu sunada ƴaƴansu abin sha'awa, duk da matane ba kamar kai namiji ba”.
        “Momy duka na fahimci maganarki, to amma kinga nima ai bansan wadda zasu aura mani ɗinba, amma nasan Abbah ya sani, ki tambayesa kozai sanar miki?”.
       “Bazai sanar mini ba Abdallah, sai dai kaine nakeson ka kawoma kanka mafita”. “Mafita kuma Momy? Tami?”. 
      Numfashi ta sauke tana sake kallonsa da ƙyau. “Abdallah kaje ka samu Baba malam ka sanar masa ka yarda su aura maka duk wadda sukaga ta dace, amma su haɗa maka da Nusaiban Fatima {Gwaggonka}”.
        “Momy Nusaiba kuma? Momy baki haƙura da zancen nanba dama? ALLAH ni bantaɓa jin Nusaiba a rainaba Momy, ina mata sone na ƙanwa kamar yanda nakema su Aysha”.
         “Abdallah basai kaso Nusaiba ba yanzun, idan kukai aure tana gidanka a hankali zaka fara sonta. Yarinyarnan ƙyaƙyƙyawa ce itama, sannan tanada tarbiyya da hankali kaima ka sani ai”.
     Shiru Abdallah yay kawai yana kallon Momy, a cikin ransa sai faman faɗin, ‘Nu'aymah kina inane? Dan ALLAH ki dawo gareni, ki taimakeni ki ceci zuciyar da bata taɓa fashi a ƙaunarki ba, ki taimaki numfashin da ke burin rayuwa da naki har abada. Nu'aymah miyasa kika kasancemin mai SARAN ƁOYE ne.........?’
          “Abdallah!”. Momy ta faɗa tana girgiza shi. Kallonta yay da sauri dan baiji mitace ba. Zaiyi magana Abba ya shigo ɗakin. Duk da ya gansu sai ya ɗauke kansa kamar baisan da suba, rigarsa ya nufa ya ɗauka yana ƙoƙarin sakawa. Tashi Abdallah yay ya tako zuwa gabansa, taimaka masa yay ya saka rigar sannan ya kallesa. Zaiyi magana Abbah ya ɗaga masa hannu. “Banason jin komai Abdallah, kaje ka shirya ka fita massallaci, dan da an idar da sallar Juma'a za'a ɗaura maka aure kamar yanda Yayah ya faɗa”.
      Ƙasa Abdallah yay da kansa yana haɗiye zuciya da sauri-sauri, baice komaiba ya juya ya fita idanunsa cike da ƙwalla.
      Ɗauke kai Abba yay ya maida ga mirror inda yake hidimar cigaba da shiryawa. Momy kuwa tabi ɗan nata da kallo tamkar zata fasa kuka.

__________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
______________________

          Masu posting a facebook dan ALLAH wannan roƙonane a gareku dama na WhatsApp da ko ina.. Nasan duk masoyin ƙwarai nason cigaban masoyinsa. Tabbas soyayyace ta sakaku kai littafina can, kuma inajin daɗin hakan da alfahari da wannan soyayya. To amma dan ALLAH ina roƙonku ku tausaya mana banda littatafan mu na ƙuɗi. Kamar wannan SARAN ƁOYE na kuɗi ne, yana cikin ZAFAFA BIYAR 2021. daga yau kuma free pages sun ƙare, gamai buƙata yazo ya biya naira 300 kacal sai ya cigaba da samu dan girman ALLAH Masoya amana adalci🤓😥🙏🏻.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________

            Hankalin Umm a tashe yake matuƙa gaya, taƙi yarda ta fita wajen ƴan uwanta balle ta sanar musu halin da ake ciki. Tunda Baba Malam da yaƙi saurarenta itama ya fita bayan yayi shiri taketa kai kawo a ɗakinsa. Lokaci zuwa lokaci tana share ƙwallar dake ziraro mata.
        Sam zuciyarta ta kasa yarda Nu'aymah guduwa tayi da kanta. Tasan wacece ƴarta, tasan tarbiyyar data bata. To amma a yanda al'amarin ya zone babu ta inda ita kanta zata iya bama Nu'aymah kariya koda a wajen mahaifinta ne. Balle kuma sauran jama'ar gidan. ‘Shin miya samu yarinyarta ne? Ta yaya tabar gida?’ tai maganar a fili tana fashewa da kuka maiban tausayi.
        
“ALLAH sarki Umm kiyi haƙuri ALLAH na nan😭🚶🏻”.

___________________________________

                 Gaba ɗaya yanayin shagalin bikin a cikin gida ya canja, mazane kawai a waje da basusan mike faruwaba keta walwalarsu. Hakama abokan Abdallah sai faman fantamawa suke cikin farar shadda datai bala'in musu ƙyau.
      Sai da aka fara gabatar da sallar juma'a kafin a ɗora da ɗaura auren da yazoma mutane da saɓanin abinda suka gani a jikin invitation card.
         Ba mutanen waje kawai ba, hatta ƙannen Baba Malam su Abba sai da sukasha mamaki matuƙa da yanda ɗaurin auren yazo. Dan kuwa ɗaurin auren yazo musu ne a yanda basuyi tunani ko tsammani ba.
       An ɗaura auren Abdallah Rudwan Hashim Jibiya da Yusrah Musbahu Hashim Jibiya akan sadaki naira dubu ɗari. Sai aka sake ɗaurawa da Adawiya Mustapha Hashim jibiya, da Abdallah Rudwan Hashim Jibiya shima akan sadaki naira dubu ɗari. Aka ɗora da doguwar addu'ar fatan zaman lafiya ga ma'auratan daga ƙarshe.

      Babu wanda ya iya magana a cikin su Abbah, dan kuwa su duk abinda Baba Malam ya zartar akansu bama ƴaƴansu ba basu da ja. Sun gama bashi darajar Uba tun tuni, sunsan bazai cutar da suba balle kuma ƴaƴansu. Fatansu kawai ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, ALLAH ya basu zaman lafiya kuma. Itama Nu'aymah ALLAH ya dawo musu da ita gida lafiya.

          Kan Abdallah neman kwancewa yay dajin wannan al'amari, ko kammala ɗaura auren ba'ayiba ya sulale ya koma cikin gida kansa na wani kalar mahaukacin sara masa, ɗakin Abubakar cikin ƙannensa samarin gidan ya shige ya kulle kansa batare da kowa ya saniba.

        Abokansa kansu cikin ruɗani da mamaki suke, sai dai kafin su sami damar tambayarsa suka nemesa suka rasa a wajen. Dole sai tambayar juna lafiya? suka komayi. Amma babu mai bada amsa.

★★★★★★★

           Hakama cikin gidan tunda sakamakon ɗaurin aure ya iso kunnuwansu kowa ya kasa motsi, sai kallon kallo kawai akeyi da idanu baki ya gaza furta komai.
       Momyn Abdallah jitai kamar an ɗaura mata dutsen dala bisa kai. Tayayama za'a aurama Abdallah aure da yara ƙanana irin waɗan nan har guda biyu?.
      Haka taketa ayyanawa a zuciyarta, a fili kam sai laɓɓanta ke motsi maganar ta kasa furtuwa. Sai danginta ne keta ƙananun magana musamman ma Umman Nusaiba.

         Yusrah ma tunda zancen ya isa garesu ta yanke jiki ta faɗi a sume, sai da aka yayyafa mata ruwa ta farfaɗo. Kuka take tamkar ranta zai fita. Ta yayama zata auri Yah Abdallah da tasan duk duniya babu wadda yake so sama da Nu'aymah. Sannan Nu'aymah ma na bala'in sonsa da ƙaunarsa. Tunda aka wayi gari da ɓatan Nu'aymah sam bata yarda guduwa tayiba, dan kuwa a daren jiya ana wajen walima ta dawo gida tanason shiga toilet. Motsin mutum taji a ɗakin, amma tana shigowa aka ɓuya bataga ko waneneba. Kashin daya matseta ne yasa batabi takan sanin wanene ba ta shige toilet. Bayan ta shiga ta fito taji motsin fitar koma wanene daga ɗakin. Bataga kowayeba, hakan yasata fita da sauri ta zagaya ta bayan Windows ɗin saboda ƙarar jan akwati da taji kamar anayi tacan. Dan ko ina na gidan Interlock ne. Tana ɓullowa ana barin wajen, sai dai zuciyarta ta zargi mutum ɗaya a lokacin, amma bata da tabbas ɗin da zata fito tace ga abinda ta gani kokuma ga wanda ta gani. Dan babu wata ƙwaƙwaran shaida a hannunta.
         Abu na biyu Nu'aymah abokiyar firartace sosai, dan ko suna Lagos takanyi dogon Charting da Nu'aymah fiye da Amal da Adawiya, sannan kusan kullum sai sunyi waya, mafi yawan hirar da Nu'aymah ke mata kuma akan Yah Abdallah ne, dan komai na Nu'aymah da sunan Abdallah a ciki.
     Ta sake fashewa da kuka tana ƙanƙame Aminta da itama cikin ruɗanin take. Bawai auren ƴarta da Abdallah ne matsalarta ba, matsalarta yanda al'amarin yazo. Tana ganin kamar Mazansu sunyi gaggawa akan yanke wannan hukuncin. Kamar ya dace ace sun zauna sunyi dogon nazari da bincike akan al'amarin Nu'aymah. To amma ita bata da wani ƙarfin iko akan sakawa ko hanawa a gidan, sai dai kawai ta shiga jerin shiga sahun masu addu'ar ALLAH ya warware al'amarin cikin sauƙi, duk inda Nu'aymah take kuma ALLAH ya kareta ya tsareta, ALLAH ya maido hankalinta gida.

★★★★

         Adawiya da ko wanka ta kasayi saboda fargabar wadda za'a mayema Abdallah gurbin Nu'aymah da ita ta miƙe zumbur sanda labarin ya iso kunnenta. Dama a sashensu take tun bayan gama dambarwar guduwar Nu'aymah. Ta daka wani uban tsalle zata ƙwala ihun farin ciki Hajarah yayarta wadda takebi data shigo yanzun tai azamar rufe mata baki.
          “Innalillahi, Adawiya minene haka kikeyi? Kefa nagama tamkar murna kikeyi ne ko mi?”.
      Janye hanun Aunty Hajarah Adawiya tai daga kan bakinta tana hura hanci, kamar zatai magana cikin masifa kuma saita fasa. Canja yanayinta tayi zuwa damuwa ƙwalla na taruwar mata a idanu. “Aunty Hajarah ki barni nayi ihu ko zanji sanyi a raina, ta yaya za'ace ni Adawiya nice matar Yah Abdallah yau?”. A mamakin Hajarah sai taga Adawiya kuma ta fashe da dariya.
        Baki Hajarah ta saki tana kallonta dan al'ajabi. Zatai magana sai ga Addah ta shigo ɗakin.
         “K! Wane kalar iskancine wannan?!!”. Ta faɗa da matsananciyar tsawa tana kallon Adawiya data fara taka rawa. Daɓar ta zauna a bakin gado tana ɓata fuska.
     Addah ta ƙaraso cikin ɗakin jikinta har rawa yakeyi, jikake “Tasss!!” ta ɗauke fuskar Adawiya da wani bahagon mari haggu da damanta. Kifff Adawiya ta kifo ƙasa dan azaba da gushewar numfashi na wucin gadi. 
            Cikin tsananin firgici da tashin hankali Hajarah tai tsalle gefe jikinta itama na rawa, tai masifar ware idanu akan mahaifiyar tasu da akan daɗe ba'aga fushintaba a gidan.
          Addah tasa hannu ta ɗago Adawiya ta cigaba da bata maruka, sai da tai mata shidda ƙwarara sannan ta hankaɗata kan hado. Sosai wahala ma ta hana Adawiya kuka, sai sauke numfarfashi take tamkar zata shiɗe. Kallon Hajarah Addah tayi, batare da tayi magana na ta nuna mata hanyar fita.
         Zabira Hajarah tai ta nufi ƙofar da bala'in sassarfa, sai da taje gab da fita sannan ta tsaya cak saboda tsawar da Addah ta daka mata. “Idan kin fita ki sanar da kowa kinji ko?”. Saurin haɗiye kukan dake neman kufce mata Hajarah tayi, ta kalli mahaifiyar tasu tana mai girgiza kanta. “K....k...kiyi haƙuri dan ALLAH Addah”. Hanya ta sake nuna mata alamar ta wuce. Hajarah bata sake magana ba tabi umarnin Addah ta fice.

    ______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

____________________________

     Juyawa Addah ta sakeyi ga Adawiya dake kwance tamkar wadda shaƙar iskar numfashi taima ƙaranci. “Tashi dan Ubanki!!”. Da sauri Adawiya ta tashi tanaja baya daga farkon gadon zuwa ƙarshe, jikinta sai rawa yake tana kallon Addah, amma tsabar bushewar zuciya ajiyar zuciya kawai take saukewa taƙi tai kuka.
       Addah ta kalleta babu ko ɗigon rahama a fuskarta. “Waye ya taimaka miki a gidan nan wajen ɗauke Nu'aymah?!”. 
       Sai yanzune Adawiya ta fashe da kuka tana cigaba da kallon Addah. “A...a....Addah ALLAH....”
         “Wlhy kikaimin ƙarya Adawiya sai kinyi nadamar sanina. Ina kuka kaita? Ke dawa kuma kukai aikin?”.
        Kasa magana Adawiya tayi, sai kukanta dake ƙara ƙarfi tana sake jan jikinta baya. “Bazaki faɗaminba saina tona miki asiri a gaban kowa?!!!”  Addah ta faɗa da tsananin tsawa hawaye na sauka mata a kumatu.
     Zabura baya Adawiya tayi itama tana mai fashewa da wani kukan. “Wlhy Addah, w....wlhy bani bace, wlhy bansan komai akai ba”.
       “Adawiya ni na haifeki, nasan halinki, ki faɗamin gaskiya wlhy kona yankaki a ɗakin dan ubanda ya haifeki”.
       Sake fashewa da kuka Adawiya tayi tana girgiza kanta da ɗaga yatsanta ɗaya sama. “Wlhy Addah kinji na rantse ban aikata komaiba”.
         “Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un” Addah ta shiga ambata tana dafe kanta, hawayene masu cike da zafi da ruɗani ke sakko mata a gurguje, ta zube saman gadon itama ta dafe kanta.
    Rarrafowa ta bayanta Adawiya tayi ta rungumeta itama tana kukan....

_______________________

               Hayaniyar data yawaita a sashen Baba Malam ne ya fara jan hankalin sauran mutane dake a harabar gidan da sauran sassan gidan.
      Kafin da yawa suyi yunƙurin shiga sashen sai gashi an fito da Umm wadda ta yanke jiki ta faɗi a sandare alamar babu rai tattare da ita. A take hankalin kowa ya tashi. Omar ne yay azamar nufar motar daya shigo da ita yanzun nan ya buɗe baya aka saka Umm, babu tunanin neman ba'asi ko jiran umarnin iyayensu yaja motar bayan Mahaifiyar Nanah (Gwaggo Safina) ta shiga ita da Gwaggo Hafsat yayar Umm ɗin da take bimawa ya bar gidan a ɗari.
     Da yake ƴan ɗaurin aure duk sun tafi zuwa babban Hall ɗin da aka kama domin cin abinci sai ƙofar gidan babu yawan jama'a. Shima Omar daga can baba malam ya aikosa ɗaukar Abdallah da suka fahimci baya tare dasu, ga baƙi nata tambayar ango kuma, musamman ma abokansu Baba Malam ɗin, shine baba malam yace Omar yaje ya ɗakkosa a gida dan yasan Abdallahn bazai wuci gida ya koma ba. To gashi yana shigowa kuma ya iske wannan tashin hankali.
       Hajarah ce a firgice taje ta bugama su Addah tana faɗin, “Addah ki fito Umm ta rasu”.
           Wani wawan miƙewa Addah tai ta nufi ƙofa bayan ta wancakalar da Adawiya dake kwance a bayanta ƙasa. Ta buɗe ɗakin zuciyarta na wani mahaukacin bugawa. Sai dai kuma bataga Hajarah ba, sannan baƙi dake a ɓangarenta da mafi yawansu ƴan gidansu ne da ƴan Uwan Umm duk sun fice. Batako tsaya sauraren bin ba'asiba ta fice daga gidan, ALLAH ya sota ta samu Napep dake ta jigilar ƴan biki a ƙofar gidan ta shiga, sakawa tai ya ringabin bayan Omar dake zuba uban gudu kamar zai tashi sama............✍

____________________________

        Ina ma'abota son a tallata musu hajojinsu a kafafen yanar gizo suke?.

Tofa kuzo dama ta samu, dan jerin gwanon haziƙan marubanku ƴan biyar sun fiddo muku da hanyar da kuma kasuwancinku zai zagaya lungu da saƙo ta dalilin shafukan littatafai.

Ga duk mai buƙatar a saka masa tallan kayan sana'arsa a shafin littatafan mu na zafafa biyar zai iya tuntuɓar waɗan nan Numbers 0903 234 5899 or 09033181070 ta WhatsApp, idan har agama buks ɗin kana buƙata a sakamaka talla zamu saka maka akan farashi mai sauƙi. Idan kuma wasu adadin pages kake buƙata koda ɗaya ne duk zamu saka maka akan farashi mai sauƙin gaske🤓.

Kuyi maza ku kawo, mai haja shike talla, mai saya kuwa shike neman sauƙi😻😻😄🤗.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.p


[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

*_Da sunan ALLAH mai Rahma mai jinƙai_*

_Ya Rabbi ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni ni da al'umarka, ka tsare harshena da alƙalamina rubuta abinda zai cutar da ni da su😭🙏🏻_.

*_Ya rabbi ka gafarma mahaifina masoyina da dukan ƴan uwa musulmai da suka rigamu gidan amsa kiranka😭🙏🏻_*

No. 6

................Baba malam na tsaka da sallamar abokan arziƙinsa kira ya shigo wayarsa. Kamar zai share karya duba sai kuma ya cirota daga cikin babbar rigarsa. Ganin Number da akai kiran da ita yasashi ɗagawa da sauri ya ɗora a kunne yana faɗin, “Assalamu alaikum. Innah!”. Batare da Hajjo ta amsa masa sallamarba cikin kuka take faɗin, “Duk inda kuke ku taho gidan nan babu lafiya ɗan Malam”.
       “I...in...innah miya faru halan?”. A zafafe Hajjo tace, “Sai kaji abinda ya faru zaku taho? To Firdausi ce aka fita da ita babu rai”.
      Ba ƙaramin bugun ƙirjin Baba malam wannan kalma tayi ba, kafin ya samu damar yin magana Hajjo ta yanke kiran. ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ Baba malam ya fara ambata akan laɓɓansa, atake damuwarsa da yaketa ƙoƙarin dannewa take ƙoƙarin fitowa fili, ya share zufar data taru masa a gaban goshi yana busar da iska mai zafi. lumshe idanunsa yay na wasu mintuna yana ambatar addu'a. Sai da yaɗan samu nutsuwa sannan ya juya zuwa cikin hall ɗin. Ruwa ya samu ya sha zuciyarsa ta ƙara nutsuwa kafin ya tattara su Abbah da samarin gidan suka bar wajen.
        Suna fara tafiya sai ga kiran Omar, shine ya sake sanar masa da abinda ke faruwa, tare da asibitin da suke a yanzu haka. Kai tsaye can suka nufa, inda suka tarar da Addah da yayun Umm sun haɗe kai sunata sharɓan kuka. 
         Hankalinsu Baba Malam sai ya sake tashi fiye da farko, amma da yake shiɗin kamilin mutum ne sai fuskarsa bata nuna yanda yake a rikice ba. Addu'oi ya keta ambata a ransa yana cigaba da miƙama UBANGIJI kukansa.

      Sun kai tsahon mintuna arba'in suna jiran fitowar Doctor kafin ya fito. A kusan tare suka sauke ajiyar zuciya ganin fuskar Doctor ɗin da ɗan sassauci ba kamar ɗazunba. Kallonsu yay cike da girmamawa yace, “Alhmdllh ta farfaɗo. jininta ne ya hau sosai, ALLAH ma ya taƙaita mata wahala, dan irin wannan faɗuwar ga mai hawan jini babbar matsalace, musamman yanda jininta yay ƙololuwar hawa”.
        Sake sauke ajiyar zuciya duk sukayi, Baba Malam ya kauda kansa gefe tare da ɗauke ƴan ƙwallar da suka taru masa a cikin ido.

           Baba malam ne kawai aka bari ya shiga ya ganta, tana kwance idanunta rufe an saka mata ƙarin ruwa. Tai masa wani irin masifar haske a ido. Ya jima yana kallonta tausayinta na sake faɗaɗa a zuciyarsa, ya kai hannu ya shafa kanta yana magana a hankali. ‘ALLAH ya baki haƙuri Jannat kinji, ALLAH ya bamu ikon cinye jarabawar nan, kiyi haƙuri ki daina damuwa’. Ya ƙare maganar da sumbatar goshinta.
       Ya kai tsahon mintuna goma yana cigaba da kallon ƙyaƙyƙyawar matar tasa kafin ya juya ya fita a ɗakin. 

Gaba ɗaya kan baba malam ya ƙara ɗaukar zafi, gashi dama shima yana da hawan jinin. Gudun kar gazawarsa ta bayyana ya sashi samun Doctor ya nema a sallamesu su koma gida da Umm. Family Doctor ɗinsu zai cigaba da kula da ita.
       Doctor baiyi musu ba ya basu sallama, dan yasan su ɗin manyan mutanene, bazasuso cigaba da zama a asibitinba kodan yanayin da ƙasar yake na rashin tsaro.

     Bayan kammala duk abinda ya dace aka saka Umm a Ambulance. Addah ta shiga tare da Nurse ɗin da aka basu, su kuma suka shiga motocin da sukazo a ciki.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

__________________
________________________

            Sosai hankalin mutanen gidan da ƴan biki ya ƙara tashi ganin Ambulance har cikin gida. Da yawan gwiwoyin wasu ya sare a zatonsu ko Umm ta rasu ne. Sai da sukaga an fito da ita zuwa sashensu harda ƙarin ruwan da ake mata sannan aka fara sauke ajiyar zuciyoyi da ambaton Alhmdllh.
            Bayan an shiga da Umm Bedroom ɗin Baba Malam dangi suka shiga jajantama juna da addu'ar samun lafiya a gareta tare da fatan dawowar Nu'aymah gida cikin ƙoshin lafiya. Daga haka dangi na kusa suka fara zare jiki suna barin gidan, dan kam ko masu gidan basuce dasu komaiba sunsan suna buƙatar a basu wuri suji da abinda ya damesu.
       Kafin sallar magriba gidan ya ragu sosai. dan irin dangi na katsina, kaduna, jigawa ma duk sunyi sallama sun tafi tunda ba wani nisa bane mai yawa. Balle kuma ƴan cikin kano da ƴan gayyar aci shinkafa asha zoɓo😏🤐.
         Yayun Umm su Maman Nanah dai suna nan basu tafi ba sukam duk da anan cikin kano suke aure su duka. Sai kuma wasu a cikin dangin Momyn Abdallah da suma sukaƙi barin gidan.

       Har bayan sallar isha'i Umm nata barci, yau Baba malam ko wajen karatu bai zauna ba, sai Abba Mustapha ne yayma magidantan dake ɗaukar karatu bayan sallar isha'i ƙari. Shima daga ƙarin ya sallami kowa ya shigo gida. 

★★★★

        Zuwa bayan isha'in ne hankalin kowa ya koma kan sanin ina Abdallah?, dan duk wannan rugun tsumin da akeyi babu wanda yaji ɗuriyarsa. Nemansa aka shigayi a waya amma bai ɗagaba. Hakan yasa samarin gidan suka fara didduba ɗakunansu. Har hankali ya fara tashi na rashin ganin nasa sai gashi Abubakar ya samosa a ɗakinsa yana barci.
      Fita yay ya sanar musu. A tare duk suka ɗura kai cikin ɗakin, inda suka sami Abdallah kwance cikin matsanancin zazzaɓi. Da yake Doctor yazo sake duba Umm sai aka kirasa yazo ya duba Abdallah shima. Shikam damuwace ta saukar masa da zazzaɓin, sai kuma yunwa. Magunguna Doctor ya haɗa masa harda wanda zai sakashi barci, yace a bashi abinci ya ci kafin yasha.
     Haka kuwa akayi, Hajjo ta basa abinci da kanta duk da yanata cewa shi ya ƙoshi. Da dai lallashi da ban baki aka samu yaci kaɗan yasha magani. Ahmad ne ya taimaka masa yay wanka sannan aka maidasa ɗakinsa da Hajarah ta gyara ya kwanta.
     Ganin barci ya ɗaukesa sai duk suka fito, aka barsa da Ahmad kawai da zai kwana tare da shi dan ba'asan mi dare zaizo da shiba.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

___________________________
___________________________
             WASHE GARI
        ___________________
             
       Daga Umm har Abdallah sun tashi jikinsu Alhmdllh, sai dai damuwa irin ta zuciya da fitarta farat ɗaya bazai yuwuba. Bayan kammala karin kumallo aka haɗu aka tsaftace gidan, sauran baƙi duk suka kama gabansu. Su Sumayya kawai ne duk suna nan basu koma gidajensu ba.

         Bayan sallar azhar Baba malam da su Abba suka zauna tare da Hajjo, sun daɗe suna tattaunawa kafin su buƙaci ganin matan gidan suma da Abdallah.
      Cikin nutsuwa Baba Malam yay musu bayanin da zasu fahimcesa akan wannan canjin da yayi, da kuma dalilinsa na aurama Abdallah su Yusrah. Ya kuma sake nuna fushinsa sosai akan abinda Nu'aymah ta aikata. Har saida takai ƙannen nasa da matansu na bashi haƙuri.
     Umm dai batace da kowa komaiba har aka gama aka sallami kowa. itace farkon tashi ta fice a falon. Dan haka duk suka bita da kallon tausayawa. Banda Baba malam da yay kamarma baisan mi sukeyiba, yanata ƙoƙarin cigaba da danne damuwarsa a rai.

____________________
BAYAN SATI ƊAYA
____________________

              Bayan sati ɗaya da faruwar komai gidan ya koma normal a zahiri. A baɗini kuwa kowa shi kaɗai yasan damuwarsa da matsalarsa. 
     Kasancewar ita Adawiya sun kammala secondary baba malam ya yanke hukuncin Abdallah zai tafi da ita can ta cigaba da karatunta, ita kuma Yusrah saita ƙarasa watannin da suka rage mata sai yazo ya tafi da ita. Kowa yayi na'am da wannan magana, dan harma an kammalama Adawiya duka shirye-shiryen tafiya.
     Kwatanta muku irin farin cikin da Adawiya take cikima ɓata lokacine, sai dai tanata ƙoƙarin dannewa saboda tsoron Addah data sanyama duk wani motsinta idanu yanzun, sannan ta daina sakar mata fuska gaba ɗaya..     
        Ganin yanda Addah taketa share Adawiya daƙin yin komai game da ɗan gyarata yasa Umm ta maidota sashenta. Gyaran da bazai cutar da itaba ta shiga mata. Musamman fatarta da kuma maganin sanyi. da koya mata dabarun zaman aure. Ɓangaren girki da aikin gidan tasan bata da matsala, tunda su duka tsaye suke akan yaransu ta wannan fanin duk da kowane sashe akwai ƴan aiki. Dan danan cikin sati guda ta canja tai fes abunta. Idan tana ɗaki ita kaɗai tata kallon kanta a mirror kenan tana tiƙar rawa da gwada yanda zata kasance da Yah Abdallah. Duk da kuwa a yanzu ko kallo basu ishesaba daga ita har Yusrahn. Ko yarda ya haɗu da suma bayayi sam, idanko yaga ɗaya daga cikinsu a waje yata fama haɗe fuska kenan tamkar an aiko masa da saƙon mutuwarsa. Hakan bai dametaba, dan tasan lokaci zaizo da sauyi wataran, kamar yanda a yanzu yazo da shi a garesu suka kasance matansa batare da mafarkinsu ya taɓa hasaso musu hakanba. 
      Tana tsananin takaici a ranta na haɗata da Yusrah da akayi matsayin matansa, amma ta wani ɓangaren hakan bai damunta, musamman da akace itace zata fara binsa, ta barma kanta yanda sauran aikinta zai kasance tsakaninta da kishiyar tata (😖Adawiya!!!!!💣).

          Yusrah kam dai tana cikin damuwa sosai. kullum cikin kuka take da roƙon Abbanta a warware auren ita bataso. Sai dai kowa yaƙi saurarenta, Amminta ce dai take tayata kuka dan tasan da gaske Yusrah bataso ɗin. Amma yaya zasuyi da ƙaddara?.

        A washe garin da aka cika kwanaki goma da faruwar al'amarine tafiyar Adawiya da Abdallah ta kama.
      Umm da kanta ta samu Addah har ɗaki tai mata ƙorafi akan yanda take share Adawiya. Sai da ta nuna mata ɓacin ranta akan hakan sosai sannan ta ɗora da mata nasiha akan ta yarda da ƙaddara mana.
        “Addah Minene laifin Adawiya tunda ba itace ta saka a ɗaura mata aure da Abdallah ba. Ba kuma itace tabama Nu'aymah shawarar ta gudu ba. A ganina addu'a ya kamata mubi yarannan da shi tare da fatan alkairi bawai tsangwama da hantara ba dan su basu da laifi”.
        “Umm bazaki ganeba wlhy, ke dai kibar......”
      “Naji bazan ganeba Addah”. Umm ta dakatar da Addah da sauri. Ta cigaba da kallonta tana faɗin, “Baki da wani abinda zaki faɗamin da zaki kare kanki, ni dai kawai ki dawo rayuwa da yaran nan kamar yanda kikeyi da. Ki kuma yima Adawiya fatan alkairi kodan sabuwar rayuwar da zata fuskanta a yau dan girman ALLAH”.
      Shiru Addah tai tana sake jinjina ƙyawun zuciya irin na Umm, haka take ita komai tana ɗaukarsa da sauƙi a rayuwarta bata zafafama kanta. Tunda abinnan ya faru babu wanda ya taɓajin furucinta kosau ɗaya akai. Ko a fuska ƙoƙarin ɓoye damuwarta takeyi. Tausayin aminiyar tata kuma ƴar uwarta sai ya sake kamata fiye da da can.

     Umm da kanta ta fita taje ta shigo da Adawiya, zaunar da ita tai kusa da Addah itama ta zauna. Su biyu suka shiga yima Adawiya nasiha kamar yanda sukeyi a duka sauran ƴaƴan Addah uku da aka aurar. Sumayya, Maryam, Badariyya. Sai da sukai mata nasiha sosai kafin Umm ta tashi ta fita ta bar Adawiya da Addahn.  

★★★★

        Kamar yanda tsari da al'adan mutanen gidan yake bayan sallar la'asar iyayen suka sake haɗuwa aka rufu kan Adawiya da Abdallah akai musu faɗa da nasiha sosai. Tare da gindaya musu sharuɗa masu tsauri akan duk wanda wani al'amari mara ƙyau ya ɓullo daga wajensa a cikinsu to lallai zai fuskanci ɓacin rai da fushinsu sosai. Daga ƙarshe aka sake musu doguwar addu'a aka sallami Adawiya da ko sau ɗaya batai hawayeba da iyayensu mata.
     Umm ta tafi da Adawiya sashenta danta kimtsata, suka bar Abdallah tare dasu Baba Malam da Hajjo da suka sake ɗora masa da Nasiha kasancewarsa shine babba.

        Ƙarfe 7:30pm gayyar yaran gidan harna ma'auri su Aysha sukaima Abdallah da Adawiya rakkiya airport dan jirgin 8:30 zasu bi zuwa ƙasar Dubai. Sai sunyi kwanaki goma acan kamar yanda Abdallah ya tsarayi da Nu'aymah sannan su wuce Saudia.
       A yanzuma dai idanun Adawiya ƙifi-ƙifi babu ko ɗigon hawaye a cikinsu. Hakan ba ƙaramin ƙona ran Addah yayiba. Hakama Momyn Abdallah al'amarin ya bata tsoro, taita kallon Adawiyar cike da alamomin tambaya a ranta, sai dai bata furtaba.

            Ko kaɗan Yusrah bataji komai a rantaba, dan ko kusa bata kawo Adawiya ma a cikin matsalolinta saɓanin Adawiyar dake jin zafin Yusrah babu gaira babu sabar. Ita Yusrah dama za'a warware nata auren da tayi matuƙar farin ciki. Amma ta ɗauka alwashin cigaba da addu'oi tana gayama ALLAH kukanta akan hakan kafin lokacin da akace zata tare.
      Basufi zaman mintuna talati da huɗu ba aka sanar da tafiyarsu. Sai yanzune Adawiya taɗanji babu daɗi a cikin ranta na kewar ƴan uwanta. Amma saita fuske ta shiga binsu ɗai-ɗai tana rungumarsu. Da tazo kan Yusrah saita wuce batace mata komaiba. Ba ƙaramin mamaki hakan ya bama kowaba, duk suka bita da kallo har Yah Abdallahn. Tsarguwa da tai ne ganin yanda ƴan uwan nata ke binta da kallon tuhuma ya sakata buɗe jakkarta ta ɗakko wani abu ta nufi Yusrah, hannunta ta kama ta saka mata abin sannan ta rungumeta kamar yanda taima kowa. 
      A kusan tare duk suka sauke ajiyar zuciya, dan da da yawansu abun yay musu cak a ƙirji hatta da ƴan uwanta da suka fito ciki ɗaya. Musamman Hajarah da taga abinda ya faru a ranar ɗaurin auren tsakanin Addah da Adawiyan.
     Sallama suka sakeyi da juna. Kafin tabi bayan Yah Abdallah da yay gaba abinsa batare da ya saurareta sun jera tareba kamar yanda taso.

“Hummm!! Wasa farin girki Adawiya👁👎🏻”.

___________________
NU'AYMAH
______________

              Tun randa aka barota daga gida bata sake sanin halin da take a ciki ba sai washe gari da yamma. Farkawa tai a tsananin firgice. Sai dai nauyin masifa da kanta yay mata na azabar ciwo ya sakata sakin ƴar siririyar ƙara da dafe kan nata da hannu bibbiyu tana sakin numfashi a wahale.
        Sake ƙoƙarin buɗe idanunta tai da ƙyar saboda nauyin da sukai mata suma. Tabi ɗakin da take ciki da kallo mai ƙaracin haske, sai dai ba dunɗum yakeba. Katifa ce kawai a ɗaki da wasu lalatattun akwatuna guda uku kalar ruwan ƙasa. Sai takalma na maza da aka jera a gefe kusan ƙafa shidda. Sai hanger a jikin bango anyi hanging farar jallabiya ta maza guda ɗaya da wanduna uku duk baƙaƙe. Sake lumshe idanunta tai ta buɗe a hankali dabin jikinta da kallo. 
     Hijjabin tane dai a jikinta har ƙasa da ta saka lokacin da zata fita neman wayarta. Ta kai hannu da ƙyar ta laluba jikinta. Towel taji wanda shima shine tasan ta ɗaura a jiyan, sai dai yanzu ya kwance duk ya zazzame daga ƙirjinta ya dawo saman cikinta.
      Juya mata da garin ya farayine ya sakata yin baya ta sake kwanciya a katifar hawaye masu a zabar zafi na silalo mata a saman kumatu. A haka ta cigaba da kwanciya tana zirarar da hawayen jikinta duk babu wani ƙarfi. Tafi mintuna talatin da kwantawa sannan aka buɗe ƙofar.
    Kasa buɗe idanu tai balle taga wanene ya shigo ɗin, tsahon mintuna biyar kafin ta buɗe idon kaɗan ta saukesu akan wanda ke tsaye jikin ƙofa sanye da baƙaƙen kaya, hatta da hannunsa akwai safar hannu baƙake. Hakama fuskarsa da facemask, idanunsa kawai take iya gani. Suma ganin kallon da take masa ya sashi ciro glasess ya toshesu. 
    Basket ɗin dake riƙe a hannunsa ya tako gaban katifar ya ajiye batare da yace da ita uffanba ya juya ya fita. Maida idanunta tai da ƙarfi ta rumtse zuciyarta na zafi. Kukanma yanzu sai ya kasa fita mata. Haka ta cigaba da zama a wajen har bayan mintuna kusan goma da fitarsa. Sai kuma ga mace ta shigo sanye cikin dogon hijjab har ƙasa. Itama fuskarta sanye take da niƙaf. 
     Batare da tama Nu'aymah magana ba ta kamata ta tayar. Bata da wani ƙarfi ko iya yin magana, dan haka ta cigaba da bin matar kawai a yanda taso. Ƙofa ƙwara ɗaya ƙarama dake a cikin ɗakin suka nufa, sai da suka shiga Nu'aymah ta fahimci toilet ne. Fas yake babu ƙazanta a cikinsa, saima ƙamshin omo da hypo daketa tashi.
      “Kiyi wanka”. Matar ta faɗa a taƙaice batare da ta jira amsar Nu'aymah ba ta fice abinta. Da kallo kawai Nu'aymah ta bita, sai dai bakinta ya mata nauyi ta gaza cewa uffan a yanzunma. Kamar bazatai wankanba sai kuma wani tunanin yazo mata. Rabonta da salla tun ta isha'in jiya. Ga shi a yanzu da alama har anyi sallar la'asar ma. Tana buƙatar ƙarfin jiki sosai, hakan kuma bazai yuwuba sai tayi wankan.
     Cikin ƙarfin hali ta zare dogon hijjabinta da towel ɗin, duk da tsaftar banɗakin a ɗarare tai wankan. Taji ƙarfin jikinta sosai, sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi a jajjere. Alwala tayi ta fito tana daddafa bango, dan akwai yunwa tattare da ita.
     Da mamaki ta kalli kayanta da aka ɗaura a saman katifar, ta bi ɗakin da kallo kamar ɗazun, babu kowa sai kayan a ajiye da kuma kwanikan abincin dake cikin basket ɗin suma an fiddosu ƙasa an ajiye.
        Bata da wani zaɓin daya wuce canja kayan tai sallolin dake kanta. Harta kammala rama sallolin babu wanda ya sake shigowa, ta kwanta saman abin sallar tana hawaye da tunanin ko wane hali yanzu Umm da Abbanta da Muh'd dama duka sauran ƴan gidansu suke ciki a yanzu na rashin ganinta?. Yah Abdallahn ta, tasan zaifi kowa shiga tashin hankali bayan Umm da Abbanta. ‘Minayi suka kawoni nan? Su wanene su? A ina nake?’. Ta faɗa a fili tana sake fashewa da kuka. Taja tsahon lokaci tana ribzar kukanta, har kanta yana masifar sara mata fiyema da ɗazun. Barcine ya fara figarta na wahala. Jin motsin shigowar mutum ya sakata tashi zaune zumbur. Matar ɗazunce, yanzuma batai mata magana ba ta ɗakko kwanikan abincin ta kawo gabanta da mata alamar taci.
      Yunwa Nu'aymah takeji sosai, dan haka batai musu ba taja abincin tahau cinsa. Taci sosai har matar tai mamakin hakan. Matar ta miƙe zata fara tattare kwanikan Nu'aymah ta kalleta cike da rashin tsoro tace, 
       “Su wanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku kuma?”. 
     Kallonta matar tayi sosai, amma sai batace da ita komaiba ta tattara kwanikan tai ficewarta. 
        Tashi Nu'aymah tayi ta nufi ƙofar da sauri, sai dai tana taɓawa tajita a kulle, fashewa tai da kuka ta koma saman katifar ta sake kwanciya tana sambatun kiran Umm da Abbanta da Yah Abdallah.

        Tun daga wannan ranar kullum hakan ta cigaba da faruwa, zasu kawo mata abinci sau uku a rana, matarnan zatazo ta gyara ɗakin ta wanke mata bayi da kayan data cire. Sannan ta haɗa mata ruwan wanka ta sakata cin abinci. Tambayar duniya tai mata bama bata amsa, haka shima namijin idan zai shigo sau goma tai masa magana baya ko mata tari. Iya kacinsa ya leƙo ya ganta ya koma.

     Haka Nu'aymah ta cinye kwanaki goman nan cikin matsanancin damuwa da tashin hankali. Babbar damuwarta halin da ahalinta zasu shiga na rashinta. Musamman ma Umm ɗinta da Abbanta da Yah Abdallah da Hajjo. Tayi kuka harta gaji ta bari ta koma gayama UBANGIJI kukanta. Dan tasan shine mai rahama mai jinƙai. Ya fita sanin dalilin da yasa ya jarabceta da wannan al'amari a daren ɗaurin aurenta da yayanta masoyinta.

       Ranar data cika sati biyu a ɗakin bayan sallar la'asar sai ga matar nan, kamar kullum yauma batai mata magana ba, saima kwashe kayanta data cire tai ta fita dasu. Bayan kamar mintuna goma sai gata ta dawo ɗauke da hijjabi wankakke gogagge. Miƙama Nu'aymah tai da mata alamar ta sanya. Babu musu Nu'aymah ta fisgi hijjabin daga hannunta tana watsa mata harara ta sanya. Ita sam bata wani jin tsoronsu, damuwarta kawai family nata.
      Matar bata kulataba, bayan ta saka hijjab ɗin ta zagaya ta bayanta ta riƙe mata hannaye. Fisgewa Nu'aymah ta fara ƙoƙarin yi amma ta kasa saboda ɗaure hannayen da matar tayi. Kafin ta samu damar magana namijin ya shigo shima. Gaban Nu'aymah yaje ya tsaya tare da fiddo baƙin ƙyalle a aljihunsa ya ɗaure mata idanu.
     Duk tsiwar da take masa bai kulataba balle ya tanka. A haka suka fita da ita a ɗakin batare da tasan ina za'a kaitaba.............✍

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*


_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

No. 8

...................Doctor na isowa aka maida Nu'aymah bedroom ɗin Hajjo. duk fita sukai suka bashi waje yay aikinsa yanda ya kamata. Sai Abubakar da aka bari kawai dan ya taimaka masa da wani abun idan ya buƙata.
        Sunyi jigum-jigum a falon Hajjo, kowa da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa wadda ALLAH kaɗai yasan minene a cikinta.

       Juyawa baba malam yay a hankali ya fice daga sashen. Sashensu ya nufa dan sai yanzune hankalinsa ya kai ga rashin ganin Umm tare da su. Babu kowa a falon, ya nufi bedroom ɗinta canma babu kowa. Fitowa yay ya nufi nasa ɗakin ko tana can. Sai dai kuma nanma babu kowa. A ɗan ruɗe ya dawo ɗakin Muh'd. Muhammad ɗin kawai ya samu yana canja Uniform ɗin islamiyya dan yanzun suka taso. Baima gansaba, sai da yace, “Muhammad ina Umm ɗinku?”
     Jiyowa Muhammad yay da sauri, fuskarsa da ɗan damuwa yace, “Abba nima ban gantaba, na shiga ko ina bata nan kuma yunwa nakeji”.
       Shigowa sosai Baba malam yay cikin ɗakin idonsa akan Muhammad ɗin. “Yunwa kuma Muhammad? Bakaci abinciba ka fita ne?”.
       “Abba lokacin nasha fura wajen Hajjo na ƙoshi, yanzu kuma zanci”. 
     Kama Hannunsa Baba malam yay suka fita kitchen da tsammanin zaiga Umm a can. Sai dai kuma mai aikinta kawai suka samu tana gyaran kayan miya. Cike da girmamawa ta gaida Baba Malam ɗin. Amsawa yay yana cirar tuffah dake cikin fruit tray ɗin da suke sakawa. Ƙarasawa yay wajen fanfo zai wanke Saude tai saurin faɗin, “Baba malam kawo a wanke”. Baiyi musu ba ya miƙa mata tuffa ɗin guda biyu daya ɗauka. Sake bin kitchen ɗin yay da kallo kafin yace, “Ina Jannat ɗin take na ganki ke kaɗai kina aiki?”.
       Saude data wanko apple ta ɗaura a ƙaramin filet tace, “Nima na shigo ban gantaba, dama naje can ƙasan layine na sayo mata daddawa data bada. To nadawo kuma na duba kamar ta fita, shine nace bara na gyara ko kayan miya kafin ta dawo”. Shiru Baba malam yayi gabansa na faɗuwa. Amma sai ya danne ya kalli Muhammad dake saurarensu. Filet ɗin tuffa ɗin ya miƙa masa yana faɗin, “Karɓa wannan kaje kaci muje salla mu dawo saika zauna cin abincin”.
         Kai Muhammad ya ɗaga masa da amsar filet ɗin. Yaron nagaba yana biye da shi har suka fice. Sake komawa yay ɗakin Umm ɗin dai zuciyarsa na bala'in harbawa. Tsaye ya isketa gaban Wadrobe tana fiddo kaya da alama wanka tayo. Ya sauke ajiyar zuciya da faɗin ‘Alhmdllh’ a fili. Hakanne yasata juyowa da sauri dan bataji shigowarsa ba. Kamar zatai magana sai kuma tai shiru tana kallonsa kawai.
       “Naje massallaci”. ya faɗa a taƙaice yana juyawa ya fita daga ɗakin. Binsa da kallo Umm tayi harya ɓace mata sannan ta ɗauke kanta hawaye na ziraro mata.

★★★★

        A ɓangaren Hajjo Doctor ya bama Nu'aymah dukkan taimakon daya dace kamar yanda ya saba a duk lokacin da ciwon nata ya motsa. Sai dai yau ta jima bata farfaɗo ba. Dan sai da sukaje sukai sallar magriba suka dawo sannan ya ƙarasa ƴan dabarunsa cikin amincin ALLAH ta farfaɗo.
         Godiya yayma UBANGIJI tare da fita ya sanar musu ta farfaɗo. Dan yau ana idar da salla gaba ɗayansu suka baro massallaci, baba malam ne kawai yay zamansa. Matanma suna idar da sallar duk nan suka sake dawowa harda yaransu da dawowarsu islamiyya sukaji komai.

      Bayan Doctor ya kammala komai ya buƙaci tattaunawa da su Abbah. Da ƙyar suka samu Baba malam ya baro massallaci yazo.
        Doctor ya gyara zamansa cikin girmamawa a garesu yace, “Gaskiya wannan karon jikin Nu'aymah yayi tsamari. Kunsan matsalarta ba'aso abu yana firgitata da tsanani. tsawa da duhu suna gaba-gaba wajen girmama ciwonta da ƙarfafa shi”.
        Hajjo ce tai saurin faɗin,  “Hakane likita, duk munsan wannan, kuma ana ƙoƙarin kiyayewa. Yau ɗinma kuskure aka samu kasan ajizanci na ɗan adam. Yanzu minene mafita?”.
           “To Hajjo ALLAH ya kiyaye gaba, amma kam yau abin yaso yin tsamari sosai a gareta, dan yanzu haka zancen da nake muku sam bata cikin hayyacinta, fatanmu dai ta dawo hayyacinta lafiya batare data manta komaiba ma bayan ta farka”.
       Da matsanancin tsoro suke kallonsa, sai dai kowa ya kasa magana. Da sauri yace, “Bamu da tabbacin hakan, komai na ALLAH ne, mucigaba da mata addu'a insha ALLAHU zata farko cikin ƙoshin lafiya. Dama inada shawara ne, dan tun kwanaki naso zuwa da zancen sai nai tafiya kuma, yau kwanana shidda kenan da dawowa ma, zan kuma iya komawa a koda yaushe dan na samu gurbin ƙaro karatu a ƙasar Australia ne”.
        A tare sukace, Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka ya bada ikon karanto abu mai amfani”.
      “Amin ya rabbi, nagode sosai”.
      Abbah Musbahu yace, “Muna surarenka. Wane shawarace da kai?”.
        “Dama akwai wani likita babba kuma ƙwararre, dan kam ALLAH ya hore masa baiwa ta fannoni da dama inhar a ɓangaren likitancine. To wani abokina ya tabbatar min har masu irin ciwon Nu'aymah yana basu taimako. Matsalar ɗaya ce, shine ganinsa. Ganinsa nada matuƙar wahala dan yana aikine a Nigeria da wajen Nigeria. Ko a yau zai iya shigowa kano ya duba marasa lafiya ya fice, zuwa dare kuma kaji bama ya ƙasar gaba ɗaya”.
            “To ai mu Doctor ko biyansa ya kama muyi sai muyi dan yazo ya duba ta”. Cewar Abban Abdallah.
        “Ai anan gizo ke saƙar Malam. Dan ko nawa za'a biyashi bazaizo gida duba mara lafiya ba. Dolene sai dai mutum yaje yay tanadin ganinsa kamar kowa, zai baka date ɗin da zaka gansa idan har ciwonka yakai shi zai dubaka, idan kuma yaga akwai mafita zai haɗaka da wani likitan da zakaje ka gani. Date ɗin da za'a rubuta maka kuma dole a sannan ne zaka gansa babu alfarma. Kwanaki yaron president ya samu wata babbar matsalar da sai shine ake fatan ya dubasa ko za'a dace. Har jirgi aka aika ya ɗakkosa daga wata ƙasar dan kawai yazo ya dubashi amma yace suje su sai kati subi layi kamar yanda kowa keyi shi bazaije ba. Kuma dole hakan akayi”.
      Babu wanda bai jinjina wannan al'amari ba a cikinsu, sukai shiru kowa na tunanin mafita kuma. Ganin haka Ahmad yace, “To Doctor idan babu damuwa ai muma sai kai mana hanya mubi hanyar data dace ɗin na ganin nasa kawai, ko'a ina yake mu zamu bisa insha ALLAH. Fatanmu dai a dace”.
        “Hakan shine dai-dai. Ga Number ɗaya daga ma'aikatansa zan baku sai ku nemesa, insha ALLAH zai muku ƙarin bayanima fiye da nawa ma, ga kuma ta abokina ma duk zan haɗa muku shima likitane zaku iya neman taimakonsa koda ni na wuce ne”.
      Rubutawa yay ya miƙama Hajjo dake a kusa da shi, ita kuma saita miƙama Baba malan da tun shigowarsa baiyi ko tari ba. Bai musaba ya amsa ya ajiye gefensa da nufin idan ya tashi sai ya ɗauka yaje ya adana. Doctor ya tattare file ɗin bayanan ciwon Nu'aymah waje guda ya sake mi[6/13, 10:48 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

     *NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 16*

                 Ta zauna Gefen  Umma tana kad'a kafa.

Naseer wani irin Mugun kallo ya Mata Yana "ga dakuna can guda biyu ki duba Wanda ya Miki ki saka kayanki a ciki idan Kuma Bai Miki ba sai kisan nayi babu yanda za'ayi sama taka ki zo ki wani ce a tasar Miki daga d'aki.

Daga Haka Naseer ya mik'e fuskarsa a balain had'e ya ko kallon B'arin da Hajara take Bai kalla ba ya shige dakin Naeema ya banko k'ofar 

Ni kuwa Yana shigewa na mik'e da Sauri cikin fad'uwar gaba da rawar jiki na fara k'ok'arin juyawa na koma kitchen Umma kuwa ta daka min tsawa tana na koma na zauna.

Da Sauri na zauna a gabansu Kamar Mai neman gafara kafin kace me har hawaye ya fara wanke min fuska

Umma na k'ok'arin Magana naji muryar Hindatun tana "Hajara zamu daidaita da Wanan Dan naki kuwa Kinga yanda yake min fa ita Kuma nasan badan komai yasa yake Haka ba sai Dan wanan kod'add'iyar Koda uban me ta fini oho"


Da Sauri Hajara  ta karbe tana "ki kwantar da hankalinki Ni zanyi maganinta idan Bata bar gidanan ba zata bar gidanan idan wuya ya kusa kasheta ko Kuma a fita da gawarta bantaba ganin nataciya irin yarinya Nan ba ni farkon ganina da ita naji batamin ba Dan Ni idan mace ta fiye kyau Tsanar ta nake Ni nasan Bata bar Dana Haka ba wlh akwai abinda tayi Masa ta juyar Masa da Kai Amma da sannu Zan dawo da hankalin Dana kanki Hindatu ke dago ki kalli cikin idona.

Da Sauri na Dago har a lokacin hawaye kawai ke zuba a fuskata  "Ga Auntynki Nan Hindatu matar Naseer Kuma zabina duk abinda take so shi za'ayi a gidanan duk aikin data sakaki ki tabbata kinyi Mata idan ba Haka ba wlh ranki ne zai b'aci kindai San halina sai dai ki bawa wani labari Dan Haka Maza tashi kije ki zab'a a cikin Dakunan can Wanda yafi girma ki gyara ki zo ki kwashe Kayanta ki Kai Mata ki saka Mata kuma.ruwan wanka idan kin fito ki daka Mana Sakwara muci  kinji ko bakiji ba"?

Da sauri na gyad'a mata Kai na mike na nufi d'akin karshe Dan yafi na tsakiyar girma da Umma ta zauna ita da Saffiya.


Ina gyara d'akin Ina kuka wai ni Haka rayuwata zata Kare daga wanan sai wanan Mai Nayiwa Umma Haka ta  tsaneni.

Ina Gama gyara d'akin na wanke band'akin dayake da ruwa a band'akin na tari ruwa a bokiti Yana cika na fito.

Na koma palon na fara kwaso kayan Hindatun Ina kaiwa daki Umma sai zagina take Tana zagin iyayena ita kuwa kawarta kur tamin Ido kamar zata cinyeni Ni kuwa na hau addua a Zuciyata Dan kallon da takemin yayi yawa ita kuwa Hindatu sai wani girgije girgije take Tana yatsina fuska.

Ina fitowa daga d'akin na shiga kitchen na fito da doya manya guda biyu na fara feraye wa Ina cikin ferayan naji Sallamar su Zahira.

Babu Wanda ya amsa musu bansan ya akayi ba  sai ji nayi Zahira ta kwalla wani uban ihu sai dum dum nakeji kamar irin an samu babba Ana duka.

Jikina ne ya hau rawa na runtse Ido hawaye na zubomin ko ban lek'a ba nasan Umma ce ke dukan Zahira na Dade da sanin Umma ta balain tsanar zahira Ni nasan tsanar data min ne ya shafi Zahira shiyasa ma a cikin Yarana Zahira ko muryar Umma taji sai ta nutsu kaga alamar tsoro ya bayyana  fuskar ta sosai dukan da takewa zahira na ringa jinsa a jikina ta Sha dukan Zahira ba tare da ta Mata komai ba  na Kuma rasa Mai Yar yarinya da Bata fi shekara bakwai ba ta Mata.


Zagin Zahira kawai take Tana durma Mata duka tana "shegiyar yarinya tun kina karamarki an koya Miki bakin Hali baki iya Gaisuwa ba wane irin tarbiya Naeema ta muku wato ita ta kitsa muku idan Kun gani karku gaisheni ayi yara basuda tarbiyya balle wanan Yar iskar yarinya Ni nasan yarinya Nan idan ta girma Yar iska zata Zama shegiya Mai halin uwarta"


Naseer dake Sallah a a guje ya fito daya Sallame Sallar sabida yanda Zahira ke ihu Dan ba karamin Jibga take mata ba.

Nadeeya kuwa Tana gefe tana kuka 

Fusge Zahira yayi cikin wani irin B'acin Rai ya kalli Hajara Yana "Haba umma  Mai karamar yarinya Nan ta miki kike dukanta Haka kamar kin samu babba haba Umma "

"Zaka iya Rama Mata tunda na daki Yar gwal Naseeru Kai baka ganin irin tarbiyya da shegiyar matarka ta musu kwanaki Dana zo suna kallona Suka k'i gaisheni yanzu Kuma sun shigo wanan Yar iskar yarinya ta zo zata wuce ta gabana har da taka min kafa duk idonka Bai bud'e kaga irin tarbiyyar da Naeema ta musu ba sanan Dan na daketa kazo ka tsaya kana min tambayoyi Na daketa Naseer zaka iya Rama Mata nidai sukayi ba daidai ba Dole na hukunta su daga Kai har Naeema San Yaya ya rufe muku Ido Kun kasa musu tarbiyya ko baki akayi ai Dole aji kunya ai tunda yarinya Nan ta kwaso uwarta nasan inta girma ba lailai tayi albarka ba"


"Allah ya Miki albarka Zahira zakiyi Albarka insha Allahu nace Ina kankame wuk'ar hannuna da har ya yankeni jini na zuba bansani ba sosai kalmomin da Umma ke jifan Zahira dashi ya ringa min ciwo har tsanar ba iya Ni ya tsaya ba har Kan zahira da bani kadai na haifeta ba Jinin Naseer daya kasance danta na yawo a jikinta har Umma tace Zahira Yar iska zata zama baza tayi albarka ba wanan wane irin kiyayya ne kuka nake kasa kasa Ina jiyo muryar Naseer na "Umma wane irin kalamai kike Yi Haka karki manta fa yarinya Nan jikar ki ce akan me Zaki na cewa baza tayi albarka ba insha Allahu yayana zasuyi albarka Umma Dan Allah Umma kiringa kiyaye kalmomin da zasu fito bakinki Zahira fa yarinya ce ballantana kice ta mallaki hankalinta Umma Kinga yanda Kika kumbura Mata jiki fisabillilahi idan Haushin Mahaifiyarta kike ji ai Bai Kamata laifinta ya shafeta ba nawa Zahira take tsakani da Allah Naeema na iya kokari Akan yaran nan ba Kuma Ina fada Dan na kareta ba"


"Ai duka nake jira kamin Naseer ya ka tsaya iya surutai"

Naseer da idonsa ya kad'a yayi ja Bai ce komai ba ya daga Zahira da numfashin kirki ma Bata iyayi ya Kai ta d'aki dawo ya rik'e hannun Nadeeya ya d'auki Humaira da ihun zahira ya tasheta take ta kuka itama"


Nima kukan Humaira ne yasa naso fitowa daga kitchen din na d'auketa na goya ta sai Naga Naseer ya d'auketa  


Hakane yasa na koma kitchen na daure hannuna da jini ke ta zuba na cigaba da aikina Ina kuka Ina tunanin abin Yi Taya ya ma Zan iya barin yayana tayaya Zan iya tafiya na bar yarana a hannun Umma da Raina Agaban idona tana azabtar min  da Yaya inaga bana Nan.

Ina cikin had'a Miya naji Sallamar Mmn Mannir nasan Minal ta kawomin tunda Magriba ta kawo Kai 

Gaida su Umma take naji Umma na tambayarta daga Ina take

Mmn Mannir kuwa Tana Mata wanan tambayar tasan wacece ita kuwa ta had'e Rai tana Ina matar gidan take"?

Take Hindatu ta watsa Mata harara tana "Gani Nan nice matar gidan ya akayi"?

Wani kallon Tara saura kwata Mmn Mannir ta mata ta ja Tsaki tayo hanyar kitchen da take Jin motsina ciki.

Ni kuwa Ina kitchen Ina Jin maganr da suke jikina ya hau rawa.

Har kitchen mmn Mannir ta shigo ta ajiye abincin hannunta ta kunto Minal da Saura wata biyu tayi shekara biyu da bacci ya d'auketa tana "Gata Nan tayi bacci Naga alamar yau gidan naki a cike yake toh nidai shawarar da Zan baki shine wlh ki kwatarwa kanki 'yanci ki rage tsoron Nan idan babba Bai ji kunyar hawa jaki ba toh jaki bazai ji kunyar  kayar dashi ba.

Ihu kawai mukaji Umma nayi ta hau kururuwa 

Sosai hankalina ya tashi na rude da ganinta a bakin kitchen abinda ya ban tsoro yanda take zunduma ihu

"Yanzu Ni kike cewa jaka Yar nan Mai na Miki"?

Naseer a guje ya fad'o kitchen din mmn Mannir kuwa ta saki baki cikin mamakin sharrin da Umma ke neman Yi Mata

Kuka umma ta saka ta kalli Naseer dake ta tambayar Mai ya faru

Ta hau cewa "wanan yarinya Nan ce tayi Sallama muka amsa tana ganinmu taja Tsaki ta wuce mu ta shiga kitchen dinan shine Ni Kuma nayi mamakin tsakin da ta Mana shine na biyota naji dalilin dayasa ta Mana Tsaki Ina zuwa naji tana cewa Naeema wacce jakar ce wancan Yanzu Naseer har maganata Naeema keyi da wasu har a shigo Inda nake ace min jaka toh wlh daga yau Kar na Kara ganin kafar matar Nan a gidanan wlh daga yau Kar na Kara ganinta da Naeema idan ba Haka ba daga Kai har Naeema sai na dau mummunan mataki akanku da ganin matar Nan ba matuniyar arzki bace"


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun yanzu mama da girmanki kike karya da girmanki Zaki min sharri Ni nace Miki jaka kiji tsoron Allah"

Naseer kana kallo tana cemin Ina karya bazaka dau mataki ba"

Mmn Mannir Bata Bari ma Naseer yayi magana ba ta mik'a min Minal tana "ba sai kin biyo ta Haka Zaki rabani da Naeema ba ki kwantar da hankalinki bazan Kara zuwa ba kamar yanda kikeso sabida na lura bakyaso kowa ya rab'i Naeema Sabida ki yi ta azabtar da ita Kar tayi hulda da kowa ballantana a kawo mata d'auki toh Bari kiji na fada miki kiji tsoron Allah domin shi sharri Dan aikene watarana zai dawo Miki tun a gidan Duniya Allah ke hisabi kuma Zaki ga karshenki  Naeema Zan tafi xan Kuma baki shawara idan Kinga akwai cutarwa a zamanku ki hakura da Naseer tunda Zama da danta ba Dole bane daga Haka ta bangaje Hajara tayi wucewarta.

Umma kuwa hannu ta hau tafawa ta kalli Naseer tana "Ashe gulmana Naeema keyi Ashe Haka Naeema take bin mutane tana musu gulma ta abin har ya Kai har da ta  tamin sharri 
Dama Haka kike Naeema toh wlh daga yau  makarantar ma kin daina zuwa tunda acan kike haduwa da mutane kiyi gulmana har ki zageni Naeema Ina uwar mijinki toh wlh duk zagin datamin ba Ni ta zaga ba uwarki ta zaga Kai Naseeru wlh Tallahi na soke zuwa makarantar ta  ko k'ofar gida bana so Naga kafarta a da sati daya zanyi Amma na ma fasa tafiya sai na kwana biyu shegiya Mayya"

Daga Haka ta juya ta barni a durk'ushe Ina ta kuka ko kad'an ban kawo sirrin Dana gayawa mmn Mannir zata zo ta tona a gaban Umma ba Dama gudun Haka yasa tun farko naki Gaya Mata ko Naseer ma ai bazai ji dadi na fadawa wani maganar ba duk ba wanan yafi bak'anta min Rai ba sai makaranta data ce bazan koma ba Allah yasan idan akwai abinda ke faranta min a rayuwa  yanzu Bai wuce makarantar da nake zuwa nake samun ilimi ba sosai nake Kara sanin rayuwa sai gashi lokaci guda Umma ta katsemin   Mai yasa mmn Mannir zata min haka"

Dafani da akayi yasa na Dago Naga Naseer ne da idonsa ya kad'a yyi ja idan ba karya idona yamin ba har hawaye ne ya Dan kwanta a idonsa 


"Kiyi hakuri Naeema ki cigaba da hakuri watarana sai Labari nafiki Jin ciwon abinda ke Miki Amma ba komai Zan sadaukar da farincikina na faranta Miki idan Naga Umma ta cigaba da matsa Miki Zan sawwaake miki sabida ki samu yancin  Mahaifiyata ce bansan ya zanyi da ita ba Dan Allah kiyi hakuri mu cigaba da gayawa Allah Yana sane damu ko auren Nan data k'ak'a bamin ba so nake ba tilasta min tayi idan kin Gama kizo akwai sakon da Mallam Musbahu ya bani na baki"

Daga Haka Naga ya mik'e da Sauri ya nufi dakina da Minal a hannunsa.

Ahaka na daka Sakwaran Ina kuka Sosai naji komai ya ficemin a Rai na ringa Jin inama inada damar da Zan gudu da yayana ko bara ne ma na ringa Yi a titi Ina ciyar dasu Amma aka cigaba da Haka zaa Kai ga na gudun Dan na gaji Kuma Ina gudun ba'a garin Nan Zan tsaya ba Tasha zanje na hau motar da zata kaini garinmu.

Har daki na Kai musu abincin Dan sun bar palon Hindatu da Kawar Umma ne kawai a zaune Umma da alamar ta shiga bandaki.

Nazo fitowa Hindatu ta tsayar Dani tana na kawo Mata wani lemon Bata San wanan tace tana hararata 

Haka na fita na dauko Mata wani na fito daga d'akin na shiga d'akina Dan nayi Sallah Magriba Dan Ina shiga d'akina Naga Zahira a kwance tayi rub da ciki bayanta yayi jawur dayake farina ta d'auko sai sauke ajiyar zuciya take.

Naseer Kuma na d'aga gefenta Yana Dan mulka Mata jikinta da Robb bandaki na shiga da Sauri sabida kukan dake neman k'wacemin.


Ahaka naci kukana na Godewa Allah  nazo na tadda sallah Ina iddarwa na maida kaina nayi Sujjada na fara kuka Ina rokon Allah ya kawomin d'auki.

Naseer shima Yana daga daya barin nawa bansan.mai ya hanashi zuwa Massallaci ba ahaka mukayi sallar Isha muna iddarwa.naje kitchen na dauko Mana abinci dayake indai Naseer na Nan a faranti daya muke ci da yaran Minal ce kawai nake Dan Bata a baki Sabida Naseer da su Zahira na zubo abincin Dan bazan iya cin abincin ba sabida b'acin Rai.

Zahira har lokacin sauke ajiyar zuciya take Ni Kuma bana San ma na jawota jikina Dan yanda nakejin Raina kuka zanyi sosai bazan iya rarrashinta ba.


Naseer shima gani nayi ya kasa cin abincin ya hau bawa Nadeeya abinci a baki ganin Zahira Taki cin abincin yasa yace Mata taci Mana bud'ar bakinta sai cewa tayi "wlh Tallahi Abba ban yiwa Umma komai ba Nadeeya ce ta fara gaisheta shine na tsugunna Dan na gaisheta Dan Haka Umma ta koya.mana mu ringa tsugunna wa idan zamu gaida babba shine Ina tsugunnawa ta hau dukuna wlh ban Mata komai ba ta karashe tana fashewa da kuka.

Kau da kaina nayi Sabida hawayen dake tsere a fuskata Naseer kuwa sai daya hadiyi yawu Mai daci kafin ya jawo Zahira jikinsa ya hau Bata hakuri Yana Bata abincin a baki wanda dak'yar ta fara karbar abincin tana ta sauke ajiyar zuciya.

Yana cikin Bata muka ji a banko k'ofar Umma ta fado d'akin tana "badai kana nufin a d'akin ta zaka kwana ba ka dai San sai kayiwa Hindatu kwana bakwai ko"?

Dan Haka maza kazo ka wuce matarka na jiranka kafin Nan da wani wata Taran wanan Mai gindin haihuwar ta Kara haifo Mana Yarinya Mara tarbiyya"


Daga haka ta zabgamin harara ta  Kara banko Mana k'ofar.

Daga Ni har Naseer babu Wanda yayi   magana a cikinmu Ni zuwa yanzu ma na kasa kukan filin sai na zuci 

Naseer shima sai daya Dade Bai motsa ba Bai Kuma min magana ba kafin Naga ya mik'e ya janyo jakar kayansa yan Ciro wani bak'in Leda ya bud'e.

Yana "Ga sakon da Mallam Musbahu ya bani  na kawo Miki"

Da Sauri na saka hannuna na karba na duba Yar wasikar da yamin Inda yake cemin na rataya wani rubutu daya nanade da takarda a bakin k'ofata.

Sai wani shima da akayi rubutun a ciki aka nannade shi da laya yace na makala a kaina Amma na ringa kiyayewa idan Zan shiga bandaki na ringa cirewa ya Kuma ce Kar manta na ringa kwanciya da alwala a jikina.

Sosai naji dadin Aiken da Mallam Musbahu yamin Naseer ne ya ratayamin a saman bangon kofata na samu pin na makala abin akaina.


Zage zagen da muka jiyo Umma nayi na Naseer ya rainata yasa ya mik'e da Quraninsa a hannu da Sallaya da carbi  ya kalleni yacemin sai da safe.

Bance masa komai ba ya fita a Daren ranar xan iya cewa sai bacci barawone ya sace Ni akan sallaya.

Naseer kuwa Yana shiga d'akin yaga Hindatu taci kwalliya ta Dane gado tana ta Masa fari Umma kuwa Dama a Palo ya barota da jar  doguwar Riga ita da kawarta.

Bai kalli Inda Hindatun take ba  ya hau Kan darduma ya bud'e Quraninsa yayi gyaran murya Hindatu kuwa ta duro da.sauri ta tsaya gabansa tana "Wai an Gaya maka Ni hoto ce ko wancan kanjalalliyar matar taka Haka kake Mata idan ka shiga d'akinta.

Karatun da Naseer ya fara Yi da k'arfi cikin zazzakar murya yasa ta fice da sauri.

Yanaji Umma tana kiransa daga nesa Dan Bata iya isowa bakin kofar ba ya shareta ya cigaba da karatunsa Dan ko umman ma da Karatun zai koreta daga gidan


Sosai ran Hindatu ya b'aci ta hau  surfawa Umma masifa Umma na Bata hakuri.


Washegari sai Dana shirya su Zahira Dan su tafi makaranta wani irin bakin ciki ya Kara turnike Ni da yanzu nima na shirya na tafi.

Tamkar baiwa haka na zama.a gidan Dan sosai nake bautawa Umma da Hindatu dake balain.jin haushina Dan gani take duk sabida Ni Naseer yak'i kwanciyar Aure da ita Dan karatun Qurani dayaga basa so kawai yake yi daddare da safe Kuma sai ya fito ya shiga d'akina ya Sha baccinsa zuwa Sha biyu ya fice daga gidan.

Yana fita kuwa Haka zasuyi ta zagina har Hindatu ta ringa gwada kawo  hannu jikina 

Abinda na lura dashi basa iya biyoni dakina su mun Dan Umma ta Sha gwada shigowa d'akina sai Naga ta koma da gudu ta ringa cemin Mayya.

Banma San a rahama nake a baya ba sai da Hindatu tazo gidan ko hanyar waje Umma Bata barina nayi.

Naseer kuwa ya Sha fadan ya Sha zagi a wajenta Akan yak'i kula Hindatu shi kuwa sai dai ya Bata hakuri yace akwai adduar da yake yi yana gamawa zai kulata.

Ranar da su Umma suka cika sati da zuwa da sassafe na farka kamar yanda na Saba na Dora abincin Safe na fito na tashi su Zahira Dan na shirya su su tafi makaranta.

Zahira na fara yiwa wanka ta zauna a d'akin Dan indai Umma na Palo Bata fita Haka take zama adaki a yarana Zahira tana da balain San kallo duk Santa da kallo idan Umma na palon hakura take Haka ma take tsoron Hindatu sabida rankwashin da take Kai Mata a Kai.

Nadeeya ita Kuma rawar Kai ne da ita da Wasa hakane yasa Ina Mata wanka ta fito waje na hau yiwa Minal duk na dauka suna d'akin sai dana Gama yiwa Humaira na fito daga band'akin na ajiye Humaira Akan gado na fita zuwa kitchen Dan na juye ruwan tea d'in.

Ina gama juyewa na fito

Naga Umma ta Sha bakakken Kaya har kasa gefenta Kuma Hindatu ce tayi irin shigarta Haka kawai naji gabana ya Fadi da muka hada Ido ta min wanan murmushi nata Mai tsinka min zuciya da Sauri na shige d'akina Ina jan Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha.

Ina shiga d'akin naji duk ba a nutse nake ba ahaka na dauko Vaseline na hau shafawa su Zahira Sam ban lura Nadeeya Bata d'akin ba sai Dana Gama shafawa Humaira na lura Nadeeya Bata dakin.
Da Sauri na kalli Zahira cikin fad'uwar gaba Ina tambayarta ina Nadeeya take"?

Sai tacemin ai Ina mata wanka ta fita waje aguje ko wandon ma Dana d'auko musu Bata saka ba.

Hankalina a balain tashe nayi waje na tsaya a Palo Ina dube dube banganta ba na shiga kitchen  da Sauri Ina kwalla Mata Kira Nan ma shiru.

Kara dawowa nayi na shiga band'akin palon shima Bata Nan bana shiga d'akin Umma Dana Hindatu Amma sabida tashin hankali Haka na shiga Ina kwallawa Nadeeya Kira amma banganta a d'akin ba.
Haka kawai naji jikina ya fara balain rawa cikin tashin hankali Nazo tsakiyarsu Umma Ina  "Dan Allah Umma kungane min Nadeeya"?

Umma ko.kallona batayi ba sai Hindatu ce tacemin ajiyarta Kika bamu"

Da Sauri nayi waje na sauka ringa hada stair uku biyu Kamar Zan hantsulo sabida tashin hankali.

Lukman babban yaron Naseer da fitowarsa kenan Yana bud'e shagunan Naseer na nufa da Sauri.ina tambayarsa ko ya ganemin Nadeeya ko amsa gaisuwar da yakemin banyi ba.

Girgiza min Kai yayi Yana Bai ganta ba.

Ban tsaya ma Jin Mai yake cewa ba na Kara Hawa Sama Dan sai yanzu na tuna Nadeeya Bata iya saukowa sai dai a sauko da ita Dan balain tsoro ne da ita Dan Zahira ce ma take iya Hawa bene amma Nadeeya ko lekowa tayi ta kasa aguje take ja da baya Dan gani take zata iya fadowa Dan mmn Mannir har tsokaneta take ta ringa daukarta kamar zata jefota idan tazo.

Ina hawa sama na ware murya Ina cigaba da Kiran Nadeeya ya Ina duba kowane lungu da Sako nice har da duba karkashin kujera da gado.

Umma da Hindatu suna zaune a Inda na barsu ko gezau basuyi ba kamar ma basu San da hallita ta a wajen ba.

Zubewa na yi a gabansu Ina "Dan Allah Umma Baku ga Nadeeya ba wlh Ina Mata wanka Nan ta fito Palo Kuma Bata iya sauka kasa sai dai a d'auketa Dan Allah Baku ga Inda tayi ba"?

Ba Wanda ya kulani a cikinsu kamar ma bad'asu nake   magana ba hannu na Dora a kaina na fara zabga Sallati na Kara d'aukar hanyar waje a guje ko Humaira danake juyo kukanta daga d'aki ban bi ta kanta ba


A bakin kofa na ci Karo da Naseer da tunda ya fita massallaci Bai dawo gidan ba Dan yaje kasan layinmu adduar mutuwar wani bawan Allah daya rasu.

Ina ganinsa nasan shima lukman ya Gaya masa Banga Nadeeya ba 


Kara tambayata yayi "Wai baa ga Nadeeya ba"?

Ban iya bashi amsa ba na cigaba da kuka Ina na shiga uku da Sauri Naga ya hau saman Benen batare da yabi ta kaina ba  nabi bayansa da Sauri..........
[6/13, 10:48 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

     *NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 17*

              D'akina ya shiga kansa tsaye Yana kwallawa Nadeeya Kira  ya fito ya duba koina yana "Wai kamarya Ba'a ga Nadeeya ba sai kace almara Taya ya daga yiwa yarinya wanka ta fito kice baki ganta ba"?


Wajensu Umma da har lokacin basu nuna sun San Mai ke faruwa ba ya nufa Yana "Umma Dan Allah bakiga Nadeeya ta fito daga d'akin Naeema ba? 

"Toh ko Ni na saceta da zaka zo kana min tambaya"?


B'acin Rai ne yasa Naseer yace a Dan tsawace "Umma daga tambaya sai kice ko saceta kikayi wanan wane irin magana ne"


Tsaki da Bai shiryawa fitowarsa ba yayi ya wuce waje fuu Hajara kuwa ta girgiza Kai tana har dasu Tsaki yayi kyau"

Zuwa lokacin Ni nasan jinina ya hau sabida tashin hankali.
Daga farkon layinmu zuwa karshen layin mu Haka muka zaga muna kwallawa Nadeeya Kira Amma shiru.

Mmn Mannir da itama ta fito ita da yaranta tuni ta fasa fita suka hau tayamu Neman Nadeeya makotana suna da balain kirki Dan ba iya matansu ba har da mazajensu Haka suka hau tayamu neman Nadeeya Inda sukayi ta mamaki idan nace musu daga wanka ta fito na nemeta na rasa Kuma duk Wanda yasan Nadeeya yasan Bata iya saukowa daga Sama.


Kukan ma kasa wa nayi sai sallati nake har komawa nake gidan na shiga d'akina Naga ko zan ganta har zazzaga kayan wardrobe Dina nayi ko shigewa tayi Amma ba Nadeeya babu labarinta Humaira kuwa har ta gaji da kuka tayi shiru a bayan Zahira da itama ta hau kuka.

Sosai nake mamakin Umma da ta kasance kakar Nadeeya da Bata nuna ta damu da neman da muke wa Nadeeya ba hasali ma tea Dana dafa Suka zubo ita da Hindatu da kwai suka dauko gwangwnin Madara Dana Milo suna Shirin hada shayi su sha

Waje nake so na sake yi Amma na tsinci kaina da nufar wajensu Sabida daga murmushi danaga.umma na min yasa nasan tana da masaniyar Inda yata  take.


Agaban Umma naje na zub'e Ina "Umma Dan Allah na hadaki da Wanda ya halliceki ki gayamin Inda Nadeeya take Umma daga d'akina ta fito Kuma Kuna zaune anan ta fito daga d'akina Dan Allah Umma kimin komai idan ta Kama yau na hada kayana na bar gidanan wlh Zan hada Dan Allah ki dawomin da Nadeeya na tuba Umma Nadeeya bata Miki komai ba Ni na Miki Aunty Dan Allah Kuyimin Rai karku yiwa Yata komai"


Nace Ina k'ok'arin kamo hannun Hindatu 

Adaidai lokacin da Naseer ya shigo da Sauri kana ganinsa kasan hankalinsa a tashe yake

Turus yayi Agaban mu Yana yiwa Umma da Hindatu wani irin kallo da yaga kayan shayi a gabansu

Cikin wani irin murya ya fara magana Yana "Umma Anya ke Kika haifeni kuwa Umma Anya  Gaskiya Abba da Baba Suka gayamin da sukace ke Kika haifeni Umma 'yata ce fa ta b'ata ake nemanta Umma jinina fa yata da ta kasance jika a gareki ita ake nema Umma Kika zauna ke da Wanan tsinaniyar zaku hada shayi ku Sha alamar ba Abunda ya shafeku Umma wlh ba Naeema Kika tsana ba Ni Kika tsana Umma Dan da kina kaunata bazaki ringa min abinda kike min ba Zaki so farinciki na Umma mak'ota da masu wucewa ma suna tsyawa sabida su Tayani neman Yata amma ke kin zauna Zaki sha shayi wane irin kallo kike so a Miki Umma ga wayanda suka san ke Mahaifiyata ce Umma Koda baki hada jini Dani ba Bai Kamata ace mutum Mai Rai sukutum guda ya b'ata batare da kin nuna damuwarki ba Umma,Umma lamarinki ya daina bani mamaki ya koma bani tsoro Umma insha Allahu Zan ga yata Kuma zan kawo karshen komai Dan Nagaji Umma"


Daga haka yayi ball da flask din gabansu ya shige daki ya canzo kayan jikinsa ya fito da Sauri hannunsa d'auke da mukullin motarsa da k'aramin passport din hoton Nadeeya da aka Mata lokacin da zaa Saka su a makaranta ya fice da sauri.

Ni kuwa na durk'ushe a wajen na cigaba da kuka na kasa yarda Wai Nadeeya ta b'ata yarinya da nayiwa wanka da hannuna ko wando babu.

Maganar da Umma keyi cikin huci yasa na tsayar da kukana Ina kallonta

"Yau ni Naseer ya ke d'agawa murya yake min ihu sabida yarsa ta Bata lailai Naseer yayi Nisa ba karamin asiriceshi wanan tsinananiyar tayi ba ba dai Dan Nadeeya kike wanan kukan ba ba Dan Nadeeya Naseer yamin ihu Ina mahaifiyarsa ba toh sai ku ganta nagani"


"Duk wannan Abun fa laifinki ne Hajara ke Kika bar yarinya nan ta zauna dashi har yanzu har ta juyar Masa da kwakwalwa ace yau sati biyu da auren mu ya kasa kallon Inda nake tsabar wanan kanjalalliyar ta asirice shi ki barwa Umma komai ta Miki maganin shegiya"


Ta ce tana jefomin harara
Umma kuwa tayi wani irin murmushi ta mik'e tana k'ok'arin shiga daki.

Da Sauri na rik'e kafarta na saki ihu Ina ta taimaka ta fitomin da yata wlh idan Naseer ne Zan rabu dashi a yau

Tureni tayi ta shige daki.

Zahira dake lab'e a bayan kofar dakina ta fito ganin Ina ta rusa kuka Ina Kiran sunan Allah Dana Nadeeya ba irin tunanin da ba darsu a Raina ba Kar dai su Umma kashemin Nadeeya sukayi.

Zahira Humaira ta mik'o min dake ta tsalla kuka daga ita har Minal ba Mai Kaya a jikinsu sai Zahira karbar Humaira nayi na sa Mata no-no a baki take ta karba na umarci Zahira ta d'auko wa Minal Kaya ita da Humaira.

Tana tashi Mmn Mannir ta shigo ita da wasu makotana wasu ma ban San su ba duk sun zo min jaje sai Kara tambayata suke Taya Nadeeya ta b'ata ban ma iya musu magana ba sai bani baki suke suna kwantar min da hankali akan za'a ganta an Kai cigiya gidajen radio har da tv dayake Naseer nada Abun hannu duk an raba musu passport din Nadeeya.

Ni dai har lokacin sai Naga kamar zanga Nadeeya ta fito daga d'aki.


Mmn Mannir kuwa Humaira ta karba daga hannuna ta goyata Ni kuwa na mike na Shiga bandaki na daura alwala na fito na hau Kan Sallaya na tadda Sallah karatun Sallah ma da k'arfi na ringayi Ina kuka a Sujadda kuwa Haka na ringa rokon Allah ya Kare min yata a duk Inda take ta dawo gareni cikin koshin lafiya Ni nasan su Umma ne suka daukemin 'ya har tsawon wane lokacin Zan ringa irin wanan rayuwa a yau na gaji wlh na gaji ya zama Dole na dau mataki.

Ina iddarwa na  fito nayi k'ofar gida Inda duk makotana suke tsaye duk Yan layin ban gansu ba sun tafi neman Nadeeya daidai da masu shaguna duk basu bud'e ba sabida mutuncinsu Amma ace uwar mijina ita Tana daka ko a jikinta.


Waje daya na samu na zauna Ina ta tunanin ganin ta Inda zanga Nadeeya ta b'ullo addua kuwa na fili Dana zuci Haka na ringa Yi.

Lukman da danladi Mai Kai su makaranta sun dawo gidan yafi a kirga Akan suji ko an ga Nadeeya Amma shiru ba a ganta ba ahaka har Yamma tayi babu Naseer babu dalilinsa.

Kuka nake sosai Ina rokon Allah ya karemin Nadeeya har yanzu na kasa yarda Wai daga fitowa Nadeeya wanka an nemeta an rasa.



Naseer kuwa kudi ya saki sosai ya bada cigiyar Nadeeya gidajen radio da unguwa unguwa har Inda baa yi tunanin zuwa ba Haka aka ringa neman Nadeeya da passport din hotonta Sallah ma Naseer ba a nutse  yake Yi ba har kunyar ya cewa mutane daga wanka Nadeeya ta fito aka nemeta aka rasa sai kace wata Kaya.

Ahaka suka danganta neman Nadeeya kusufa kusufa lungu da sako kwaryar Kano baa ganta ba wajen Magriba Naseer da wasu Yan unguwarsu suka tsayar da motarsu Dan suyi sallah a wani unguwa kawo dayake unguwar Bata fiye cika ba a wanan lokacin Kamar daji ne sai a lokacin ake yankar fili ake ginawa.

Daya daga cikinsu ne ya nausa wajen daji dajin da yayi fitsari ya fito yayi alwala daga nesa dashi ya hango wani katon Rafi  ruwa nata Dan gudu gashi wawakeke wata Yar karamar yarinya ta bada baya tana Dan jefa abu a ciki ba Kaya a jikinta.

Murza idonsa yayi ya sake murzawa  idonsa duk da Bai ga fuskar yarinya ba sai yake ganin kamar Nadeeya Amma Dan ya gasgata zargin da yake ahaka ya ringa matsawa kusa da yarinya kafin a hankali yace "Nadeeya"

A hankali Nadeeya ta juyo idonta yayi jawur hancinta duk Majina kana gani kasan taci kuka ta gode Allah wajen a ruwan yake ma da alama baa fiye wucewa ta wajen ba 

Ihu ya saka ganin Nadeeya na ganinsa ta fara k'ok'arin mik'ewa tana mik'a Masa hannu Dan Dama Mai kawo Mata d'auki take nema shi kuwa cikin zafin nama ya Isa wajenta ya tarota da Sauri Dan kiris ya rage ta fada ciki.

Wani irin ajiyar zuciya Nadeeya ta ringa saukewa tayi lamo a jikinsa jikinta yayi zafi zau.

Shima Salisun kamkameta yayi yayi wajen da suka Parker motarsu da har Naseer ya iddar da sallah ya gaji da jiransa.

Kamar a mafarki ya hango ya fito da Nadeeya rungume a kirjinsa Bai San lokacin da ya nufesu da Sauri Yana "Mai ya sameta? A Ina ka ganta"?

Yace Yana karbe Nadeeya daga hannunsa ya hau tattab'a jikinta Inda Nadeeya tana ganin Abbanta ta fashe da kuka tana Kara kamkame shi.

Naseer kamar ya maida ta cikinsa ya rungumeta Yana shafa jikinta


Salisu kuwa ya hau bashi labarin yanda ya ganta ya Kuma ringa Al ajabin yanda Nadeeya ta iya zuwa tunda Goron dutse  zuwa Kawo idan ba mutum ne ya kawo ta Nan ba Taya zaayi tazo Nan

Naseer Bai iya Jan motar ba sai salisu ne yaja motar shi kuwa ya zauna daga bayan motar da dayan makocinsa suna ta mamakin Inda suka tsinto Nadeeya Naseer kuwa rufe idonsa kawai yayi Yana Jin kukan Nadeeya a kirjinsa Yana Jin wani irin suya a kirjinsa shi ba yaro bane yasan d'auke Nadeeya akayi Kuma ba wasu ne.suka d'auke.ta ba sai Mahaifiyarsa tunda yasan wacece ita.


Baiyi magana ba har suka iso gidan da mutane ke cike Suna jajanta b'atan Nadeeya.

Naeema kuwa taci kuka ta gode Allah tayi zaman dirshan a kasa Ana ta Bata baki


Tsayuwar motarsu yasa ta mik'e da sauri Inda Naseer shi.kuma ya bud'e motar ya fito rungume da Nadeeya

Mutane na ganin ta suka hau hamdala suna "Alhamdulillah Anga Nadeeya a Ina aka ganta"?

Sosai mutane Suka nuna farincikinsu da ganinta suka hau tambaya inda aka ganta.

Naeema kuwa da Sauri ta ture mutane ta karbi Nadeeya daga hannun Naseer tana sauke wani irin ajiyar zuciya.

Ta rungume Nadeeya Gam tana hamdala


Hajara da Hindatu ihun Murnar anga  Nadeeya ne yasa Suka fito daga d'akin da Sauri suka lek'o ta saman bene cikin tsananin mamaki Dan bakin ruwa Suka kaita Kuma suna da tabbacin fad'awa zatayi ta mutu Amma ga mamakinsu Wai an ganta Kuma su sun San Inda suka kaita sai anyi dagaske xaa San wajen.


Wani irin ihu Hajara ta saka ta sauko daga Kan benen ta zub'e a kasa ta hau buburwa ta cire zaninta ta Yar ya rage daga ita sai Dan skirt sai kuka take Tana zubawa kanta kasa.


Mamaki ne ya rufe mutane suna kallonta tare da mamakin Mai ya kawo ihun nata ita da zatayi farinciki anga Nadeeya (wlh page dinan babu fiction ko daya a gaske Haka matar Nan tayi Dan bakin ciki an ga Nadeeya)


Ni kuwa ko kallonta banyi ba na rungume yata na haye sama

Naseer kuwa kamar kasa ta bud'e ya shige Dan kunyar yanda take ihu tana watsawa kanta kasa Wai Nan da Sunan Mahaifiyarsa ce wato gawan Nadeeya taso gani

Mutane kuwa da basu San Mai ke faruwa ba hakuri Suka hau bata suna ba kuka zatayi ba ta Godewa Allah da aka ga Nadeeya ba Kuma abinda ya sameta.

Naseer shima da Sauri ya hau saman bene Yana Jin kamar kirjinsa ya fad'o

Sai Hindatu ce ta sauko ta dauko mata zaninta ta mikar da ita suka koma ciki.

Da yawa ta basu mamakin abinda tayi sabida tunda aka fara neman Nadeeya Bata lek'o ba Amma abin mamaki ana ganinta ta fito tana ihun kuka Mai hakan ke nufi.
Wasu Kuma basu kawo komai ba sun dauka kukan farinciki take da ganin Nadeeya.


Ni kuwa Ina shiga ciki d'akina na wuce da Nadeeya na kullo k'ofar na kwantar da ita na fara duba jikinta Naga babu abinda ya sameta sai kafafunta dai da suka balain suntume sukayi budu bud' da kasa 

Sai jikinta da yayi zafi sosai.

Bana rabo da ruwan zafi hakane yasa na hada ruwa Mai balain zafi na wanke Nadeeya tas na Kara zuba wani na hau dadanna Mata kafa sai danaga ya fara Sab'ewa sanan na dauko robbb na shafe Mata jikinta dadin wankar yasa take bacci ya d'auke ta tana ta sauke ajiyar zuciya Ni kuwa na zuba Mata Ido hawaye na sauko min ko a Ina su Naseer suka ganta.

Naseer kuwa a Palo ya zauna ya rik'e kansa sabida azabar ciwo da tunanin halin mahaifiyarsa ahaka su Hajara suka hawo sama tana ta kuka 

Suna dab da wuce Naseer


Naseer ya dago Yana "Umma ba Haka Kika so ba ko?kin so ace gawar Nadeeya na shigo dashi gidanan Umma Mai na Miki Haka Dan Allah Dan annabi Umma Mai na Miki Dan Allah Dan annabi ki gayamin na nemi yafiyarki Umma"


Naseer yace Yana durk'usawa Akan gwiwar sa kukan dayake  d'annewa  ya kwace Masa.


Hajaran Bata ce komai ba ta Shige d'akinta tana Jin kanta na ciwo sabida a rayuwarta Bata da burin daya wuce taga Naeema ckin bakin ciki  a Rayuwa tunda ta kasa rabata da Naseer gwara ta Taba abinda tasan sune ranta Dan taso Zahira ta d'auke Dan ta lura itace Mafi soyuwa a wajen Naeema sai Zahira bata futo ba Nadeeya ta fito sai gashi cikin sauki wai har anga Nadeeya bama ta mutu ba da ranta lailai Naeema tabbas akwai abinda ta taka da Bata iya cin Galaba Akan ta.

Har wani zazzabin bakin ciki tayi


Naseer shima halin mahaifiyarsa da matsanacin tunani sai daya saka Masa zazzabi

Ni kuwa Ina daga d'akina Ina Jin duk abinda Naseer ke cewa Umma kukan da Naseer keyi ya tab'ani sosai hakane yasa na Sha alwashin kawo karshen wanan matsalar da muke ciki.

A Daren ranar duk mu ukun babu wand yayi baccin kirki Dan Naseer zazzabi halin mahaifiyarsa ya hau Yi ko shigowa d'akin baiyi ba a palon yayi kwanciyarsa ko sallah daya Saba yi daddare  ma a ranar baiyi ba Ni Kuma hanyar da zata bille Dani ya hanani bacci ita Kuma Umma bakin ciki. Duk Abubuwan da takemin Ina tsallakewa gashi shugabarsu tayi fushi tace zata kwace komai daga hannunta tunda Naeema tana neman fin karfinta.

Washegari Nadeeya ta tashi fes ba wanan kumburin ahaka na had'asu na musu wanka na rufo kofata na nufi kitchen Dan na Dora Mana abinci banyi tunanin shiryasu su tafi makaranta ba Naseer ma ban ganshi a palon ba Dan tunda ya fice da asuba bana Jin ya sake dawowa sosai naji Ina tausayinsa.

Daga Umma har Hindatu banji motsinsu ba har na Gama Abunda nake na ajiye musu nasu a Palo na Kai Mana namu daki Dana Naseer.

Dan nayi alkawarin har na cimma burina bazan Kara Shiga dakinsu ba.

A faranti daya muka ci Abinci da yayana Sansu na ratsani Ina kwarara musu addua a Zuciyata.

A hankali Kuma Ina tambayar Nadeeya yanda ta ba ce bamu ganta  ba Bata iya min magana ba Dan tana da Dan nauyin baki.

Har Minal ta Dan fita baki.

Wajen karfe goma na safe na fito daga d'akina bayan na kulle k'ofar dakina har lokacin Naseer Bai dawo ba Kuma banji motsinsu Umma ba Naseer nafi damuwa nasan halin da yake ciki ba Umma ba hakane yasa nayi waje.

Ina su lukman suka hau gaisheni suna tambayar Nadeeya Ni kuwa nace Tana Nan lafiya Lau daga Haka na wuce gidan mmn Mannir Dan zuwa yanzu banida dai Sama da ita bayan Naseer dan naji Dadin yanda ta nunamin damuwarta jiya tamkar yar uwa ta Haka nake ganinta.


Banyi tunanin Zan sameta a gida ba Dan na d'auka taje makaranta  amma Ina zuwa na sameta taji dadin ganina anan muka gaisa taso ta tada maganar abinda ya faru tsakaninta da Umma  har ta Dan sakomin zancen tana zargin ita ta d'au Nadeeya Ni kuwa na Kau da zancen na hau Gaya Mata abinda ke tafe dani da taimakon danake so tamin Dan Nagaji da irin wanan rayuwar da muke nida yayana Kuma idan na biyewa Naseer Haka zamuyi ta zama muna cutuwa.

Sai data Yi Dan Jim kafin tace zata taimaka min ta hau tsaramin yanda zamuyi take naji dadin shawararta Inda ta tsaramin duk yanda zamuyi Amma fa tana tausayin Naseer.

Murmushi kawai na nata Dan Mai daki shi yasan Inda yake Masa yoyo.

Sallama na Mata akan Zan dawo anjima

Ina koma wa gida Naga Naseer ya dawo idonsa ya fada sosai yayi wani sanyi kalau kamar mara lafiya Bai cemin daga Ina nake ba na Shiga d'aki na dauko masa abincinsa Ina k'ok'arin ajiyew yace min azumi yake bance komai ba na dauke abincin na mayar kitchen na fara k'ok'arin Dora Mana abinci Rana Ina cikin girkin Hindatu ta shigo ta ajiye kwanuka tare da dalla min harara sai anan nasan Ashe ma suna Nan


Ina gamawa na Kara shigewa daki a Inda Naga Naseer har yayi wanka zai fita.

Yacemin bazai dawo da wuri ba fatan dawowa lafiya kawai na masa Yana fita na dauko katon akwatina na hada Mana kayanmu nida Yara sai danaga ba kowa a palon Naja akwatin na Kai gidan mmn Mannir Kuma cikin ikon Allah babu Wanda ya ganmu.

Kamar Naseer yasan Mai nake shiryawa tunda ga ranar Bai Kara fita ba.

Nima sai neman hanya nake kwana biyar da faruwar.haka Umma ta fito palon Wanda tunda aka ga Nadeeya ta shige daki ban Kara ganinta ba sai ranar Dan Hindatu kawai nake ganin tana Shigar musu da abinci.

Wani irin kallo take min Ni kuwa na dauke kaina Zan iya cewa wnan shine Karo na farko a rayuwata da naki gaisheta.

Girgiza Kai tayi ta had'e Rai ta zauna a Palo Naseer kuwa Yana ganin ta fito ya mik'e ya fita.

A ranar wani kallo Umma take jefamin na tsana Kamar zata kamoni ta yankani Ni kuwa Ina Gama ayyukana na shige daki.

Washegari jikina duk ba kwari na shirya su Zahira suka tafi makaranta 

Wajen Sha daya Naseer na fita na goya Humaira na karewa d'akina kallo hawaye na zubomin

Na ajiye wa Naseer wasika a karkashin gado na fito da ga d'akin

Banga kowa a palon ba Ina fita na amshi kudi wajen lukman a cikin kudin Naseer wajen Dubu goma wanan lokacin.

Na dau hanyar makarantarsu Zahira Ina zuwa nacewa mallamarsu inasan zamuyi tafiya ne an Mana rasuwa take ta Kira su Zahira suna zuwa na rik'e hannunsu muka hau tafiya sai da muka je karshen layin na had'u da mmn Mannir dake ta jirana da akwatin kayanmu.....
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

     *NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 18*

          Bansan hawaye nake ba sai da mmn Mannir da itama Naga jikinta duk yabi yayi sanyi tace "Anya Naeema kina ganin wanan matakin shi ya dace ki d'auka?Anya kina ganin kinyiw Naseer adalci kuwa?

Ban iya ce Mata komai ba Dan matsawar nayi magana kukan danake dannewa zai iya k'wacemin Agaban yayana Zahira tana da wayo tunda muka fito daga makaranta take min tambayoyi Ina zamuje yanzu ma sai kallona take.

Mmn Mannir itama sosai Naga idonta ya kad'a yayi ja Ina biye Mata Haka zamuyi ta tsayuwar  hakane yasa na Ciri hannu na fara k'ok'arin tsayar Mana da taxi Dan lokacin ba adaidaita sahu.

Dak'yar muka samu Wanda ba kowa a ciki na sunkuyar da kaina nace ya kaimu tasha.


Sai daya fito ya saka Mana kayanmu na bud'e bayan na saka su Minal Ina k'ok'arin kamo hannun Zahira ta Kara cemin "Umma Ina zamuje Dan Allah idan tafiya zamuyi mu tafi da Abba Kar shima Mama ta ringa dukansa dayake mama suke ce Mata"?

Hada Ido mukayi da mmn Mannir da har hawaye ya fara zubo Mata tana daukewa sabida Kar a gani.

Ni kuwa na saka Zahira a cikin motar da k'arfi Dan banasan magana kukan danake dannewa ya fito.

Ina zaunar da ita na shige na rufo k'ofar Ina k'ok'arin yiwa Mmn Mannir godiya Naga ta bud'e gaban motar ta hau.

Ba Wanda yayi magana a cikin mu har muka Isa Tasha muka sauka na biya Mai taxi bayan ya sauke Mana kayanmu


Mmn Mannir ce ta shigemin gaba wajen Nemo motar garinmu aka cajemu na biya sai da su Zahira suka hau sanan na juyo na rik'e hannun mmn Mannir Ina "Nagode da alkhairinki a gareni bazan manta dake ba"

Hawaye ne ya hau zubo Mata ta damke hannuna tana "Naeema Dan kin dage ne Zaki tafi da kin hakura kin zauna wuya Bata kissa watarana sai Labari da Zaki bani hadin Kai wlh zamuyi maganinta ya Naseer zaiji idan ya dawo yaga bakya Nan kin Kuma tafi da duka yaran wlh Naeema bazaiji dadi ba"


"Bazaki gane ba Mmn Mannir bazaki gane Hatsarin Zama na da Naseer ba Mmn Mannir da iya Ni kadai ummaa zata tab'a kila na iya jurewa da iya Ni kadai zata ganawa azaba kila na iya daurewa ko Dan sabida yarana Amma me Umma yanzu ta bar kaina ta koma Kan yayana Wanda duk abinan sabida su naki tafiya tuntuni Akan me Zan cigaba da zama yau idan Allah ya karemin Nadeeya gobe nasan salon da zata zomin dashi wlh Nagaji mmn Mannir ko baccin kirki bana iya yi na rasa Mai na Mata laifine Dan na auri danta yau kina ganin da iyayena suna rayye zata min abinda takemin banida kowa sai Allah sai Naseer toh shima Naseer din tace sai mun rabu toh na rabu dashi rabuwar mu bazai saka na kasa cigaba da rayuwa ba na barwa Naseer wasika Akan ya sakeni bazan iya ba Zan koma garinmu ko wanke wanke na ringa Yi Ina ciyar da yarana Dan bazan tab'a barin yarana da Naseer mahaifiyarsa ta kasheminsu ba Wlh mmn Mannir banji Ina nadamar matakin Dana dauka ba wlh nesa ma danayi daga gidan bakiji iskar danake shak'a Mai kyau ba nidai kawai ki Tayani da Addu'a watarana insha Allahu zamu sake had'uwa"

Mmn Mannir kasa magana tayi sabida kukan da take dak'yar na kwace hannuna na Shiga motar Ina shiga muka samu Karin passenger daya Yana shiga motar mu ta d'au hanya

Haka kawai naji wani Abu ya tsayamin a mak'oshi tambayar da Zahira ta Kara jefomin Akan tafiya zamuyi mu bar abbansu yasa na kifa kaina akan hannuna na fara kukan danake ta dannewa tun lokacin Dana shirya rabuwa da Naseer.

Allah yasan ba Haka naso ba Dan mijina Yana Sona Yana Kuma iya kokarinsa Dan yaga ya kyautata Min nida yayana Amma mahaifiyarsa ta daka tsalle tace sai mun rabu bansan Umma tsanar da takemin har ya tashi daga kaina zata iya tab'a min Yaya ba
 gaba gaba kila wuka zata d'auko ta caka musu ni har mamakin halinta nake Dan wlh ko dabba bazan iya cutar dashi ba ko ragon layya a da idan zaa yanka tausayi yake bani sai da akacemin babu kyau na daure na daina Dan bana ma tsayawa Inda ake yanka d'abba Amma Wai Umma ita ce take zuba wanann zalincin har Yara kanana Bata Bari ba idan dai har zata iya yiwa Nadeeya Haka na tabbata ma Naseer Bai tsira a wajenta ba.


Addua kawai nake Allah yasa  na Gane hanyar garinmu Dan shekaru dayawa rabona da can toh waye ma nawa acan ne inama Ina zuwa Naga Yaya Aliyu yazo shima Yana nemana inama na samu wasu suzo suce sune dangina inama na tambaya Mahafina ko Mahaifiyata.wani nasu da yanzu na samu wajen zuwa Amma ba komai Haka zanje ko makotammu na da idan na samu na tambayesu game da gidan da mahaifina ya Bari dan nasan kila yana hannun Mai unguwa idan Allah yasa basu siyar Mana ba sun ajiye Mana kayanmu sai na zauna nida yarana na nemi sana'a.


Biscuit da ruwa na siyawa su  Nadeeya da sai Dana tashe su daga bacci.

Zahira ce kawai batayi bacci ba ta Yi jigum da biscuit dinta a hannu ta kasa ci Dan sai data karamin tambaya na daka Mata tsawa akan ta kyalleni naji da iya damuwar da nake ciki.


Sai da mukayi nisa da Kano Naji wani irin tausayin Naseer ya rufeni ko ya zaiji waya sani ma ko har yaje gidan yaga wasikar abinda nakejin Kuma nadamarsa Bai wuce ce Masa danayi na tafi garin kaduna ba Dan nasan kila ya tafi can neman mu alhalin ba can mukayi ba.


Ahaka nayi lamo Ina kallon Motocin dake ta tsere a titi Ni nasan Umma sai ta kusa taka rawa sabida murnar tafiya ta.


Naseer kuwa tunda ya bar gida yake Jinsa kamar Mai zazzabi ahaka ya daure yayi ta zama a katon shagonsa daya bud'e dake sabon gari dake d'auke da kayan electronic Dan Naseer Kam fanin arzki sai daya ce alhamdulillah dan shagunansa zasuyi uku a sabon gari shidda kenan har Dana kofar gidansa.


Yanzu Haka ma Yana Gina wani katon gida a kasan layinsu ko Naeema Bai gayawa da ace mahaifiyarsa Bata Sako shi a gaba ba da ace mahaifiyarsa ta rungumi Naeema a matsayin matar danta da ya ce shi kam ya samu rabon duniya sai dai Kuma na lahira.

Sam yaji zaman shagon ya gundureshi ba Kuma yajin dadin jkinsa hakane  yasa duk da yawan mutane dake zuwa siyayya ya Sallame su akan bayajin dadin ya rufe shago ya nufi gida.

Ganin lokacn tashinsu Zahira ya kusa yasa ya tsaya a makarantar su Dan saura Yan mintina su tashi 

Kansa tsaye ya shiga cikin makarantar ya nufi office din headmistress din tana ganinsa ta hau gaishe shi tana Masa gaisuwar rasuwan da aka musu

Cikin mamaki Naseer yace Bai Gane ba


Itama headmistress din cikin mamaki ta Kora Masa zuwan Naeema makaranta da Sunan an musu Rasuwa ta tafi da su Zahira.

"Kin tabbata Mahaifiyarsu ce tazo ta d'auke su"?


"Itace Mana Alhaji Naseer yanzu ma wajen awa biyu kenan"


Naseer Bai tsaya jiran sauran bayananta ba ya fita da Sauri gabansa na fad'uwa Mai ke faruwa Naeema tazo ta dauki su Zahira lokacin tashi baiyi ba ko Ummansa ce ta Kara musu wani Abu


Da ikon Allah ya Kara sa gida ko parking Mai kyau baiyi ba ya hau sama g da balain sauri.

Naeema ya hau kwallawa Kira Yana kiran sunansu Zahira Haka kawai gabansa ya tsinke ya Fadi daya shiga d'akin naeema.ya duba koina Bai ganta ba fitowa yayi da Sauri.ya fada Kitchen nan ma Bata nan.

Da sauri ya fito ya Kara sauka kasa.

Yana sauka ya hau tambayarsu lukman ko sunga Naeema da Zahira.

Dukansu girgiza Masa Kai sukayi sai Mai Zama a dayan shagon ne yace yaga ta sauko ita da Minal da Humaira a goye a baya tayi hanyar titi.

Naseer Bai tsaya ya Gama Jinsa ba ya da dan gudu ya nufi gidan mmn Mannir daya San Nan kawai take zuwa Sosai yaji Yana tsoron darsa tunani a Ransa akan ko wani abun ne ya faru addua kawai yake.Allah yasa tana gidan mmn Mannir.

Tsabar tashin hankali Bai tsaya Sallama daga waje ba ya fada cikin gidan da Sallama a bakinsa


Mmn Mannir dake zaune ta buga tagumi tunda ta dawo ta mik'e da Sauri tana sallati ganin Naseer a rude yasa jikinta ya hau rawa cikin jarumta tace.masa.lafiya

Naseer da Sauri ya hau tambayarta inda take ita da Yara.
Ita kuwa tace masa Bata ganta ba sosai taji wani irinn tausayinsa daya zaro Ido Yana sallati.

Ya juya da Sauri ya bar gidan 

Sosai hankalinsa ya tashi   ya koma gidan a hargitse  

Yana Kara kwallawa Naeema Kira Dan gani yake.kamar Tana gidan..

Sai a lokacin tunanin shiga d'akinsu Umma ya Fado Masa.

Da Sauri ya fada d'akin suka dago  suna kallonsa 

"Umma Mai Kika yiwa Naeema Dan Allah Banga Naeema ba Banga yarana ba Umma Mai Kika musu Dan Allah ki gayamin kimin komai Umma Banda rabani dasu"


Wani irin kallo umma.ta hau yi.masa Hindatu kuwa ta fara zuba Mai harara cikin kishi a ranta tana ayyana Allah yasa ma Naeema ta mutu 

Umma kuwa taja Tsaki ta Kau da kanta.

Fitowa ya Kara Yi daga d'akin Yana sallati 
Ya Kara Shiga d'akin Naeema tsabar rudewar da yayi ya hau daddaga Kaya ahaka ya d'ago pillow har zai mayar ya Ajiye yaga farar takarda

Baisan lokacin daya dauka ba Yana bud'ewa numfashinsa ya fara barazanar d'aukewa

"Kafin kaga wasikar Nan munyi nisa Naseer Kayi hakuri da matakin da na dauka Naseer nagaji da ace Umma iya Ni takewa Zan iya jurewa Amma yanzu ta fara tab'a min. Yaya daga ni har Kai munsan ita ta d'auke Nadeeya duk sabida kiyayyar da takemin na rasa Mai na Mata idan bamu rabu ba Naseer watarana zaka rasani ko ka rasa yayanka Wanda nasan hakan sai yafi maka ciwo akan dai rabuwar mu banida kowa sai Allah sai Kai Amma Umma ta dage sai mun rabu na dauka auren data saka kayi zai saka na samu sassauci daga wajenta Amma bansamu sassauci ba sai Karin azaba hakane yasa na yanke guduwa da yayana muje garin kaduna ko Allah zai kawo Mai taimaka Mana rabuwar mu sai yafiyemin alheri Naseer kayiwa Umma biyaya ngd da alherinka a gareni dafatn bazaka.....

Wani irin sallati Naseer ya doka cikin fitar hayyaci Bai ma iya karasa.karantawa ba ya fita aguje ya nufi d'akin Hajara takarda rik'e a hannunsa Yana "Umma shikenan kin kasheni Umma Naeema ta gudu ta barni ta tafi da yarana sabida azabar da kikee gana Mata Umma kalli takardar Nan kiga mai tace Umma Naeema ta shiga duniya da yayana innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"


Hajara duk da batayi karatu ba karbar takarda tayi ta mik'e zaune Dan Dama a kwance take "Mai kace Kara maimaita min naji kace Naeema ta gudu da Yara"?

Umma Naeema ta gudu da Zahira da Nadeeya da Minal da Humaira Umma tace ta gaji da azabar da kike gana Mata Umma Mai na Miki kika tarwatsa.min rayuwa? Mai na Miki kika rabani da farincikina"?Umma Naeema fa Bata da kowa sai Ni Umma Mai yasa kikemin Haka idan wani Abu mahaifina ya Miki kike San ki dau fansar hakan akaina ki gayamin na nemi yafiyarki Umma uwa da tausayi aka santa umma uwa Bata cutar da dan data Haifa Umma ban miki komai ba kina ta cutar Dani Ina Miki biyayya daidai gwargwado Naeema tana Miki bansan Mai yasa Kika dage sai kin rabamu ba gashi dai ta tafi min da yara har su hud'u"

"Rufemin baki shasha lusari Kai yanzu akan mace kake kuka ka dagawa kanka hankali Haka?Kai yanzu Sabida Naeema ta rabu da Kai kake wanan surutan?anya Naseeru Haka yarinya Nan ta barka?Naeema kadai ce mace a  Duniya ko sai akace ma Dan ta rabu da Kai rayuwarka tsayawa zatayi? Karka manta fa kana da kudi kana da damar da zaka auri duk kalar macen da kakeso ta kuma Haifa maka maza"


"Ni kuma Mai matsayina a wajensa kenan da kike cewa zai auri wacce Ransa keso"?

Hindatu tace tana jifan Hajara da harara

"Ga Hindatu Nan dame Naeema ta fita Naseeru"?

"Ya kake Abu kamar ba Ni na Haifeka ba"?

Naseer kallon Hajara kawai yake hawaye na zubo Masa shi kadai yasan halin da yake ciki shi kadai yasan Mai yakeji a zuciyarsa.

Juyawa yayi a hankali ya fice daga d'akin Yana dafa bango Dan sosai yake Jin jiri na neman kayar dashi


Yana fita Hajara ta hau rawar murna rabonta dataji ta a farinciki Haka har ta manta gaskiya tafiyar Naeema da yaran ya balain faranta mata take ta fara addua Allah yasa Naeema ta lula duniya Tama hadu da ajalinta ita da yaran Dan batasan Nasser ma ya kalli wani Abu da zai tuna Masa Naeema.

Palon ta fito tana washe baki ganin Bata ga Naseer a palon ba  yasa ta zauna a kujera palon tana zai Gama koke kokensa ya gama ne.

Zamanta da Yan mintina Naseer ya fito daga d'akin Idonsa ya kad'a yayi jawur.hannunsa rik'e da mukullin mota yayi hanyar waje.

"Ina zakaje"?

Ko kallonta baiyi ba ya fice waje.

Gidan mmn Mannir ya Kara komawa da takardar a hannunsa Dan gani yake kila tana da masaniyar Inda Naeeema taje

Yana k'ok'arin Sallama mmn Mannir ta fito cikin tashin hankali ya Mik'a Mata takarda Yana 
"Dan Allah Mmn Mannir idan kinsan wajen Wanda Naeema taje a kaduna ki gaya min nasan bazata ki Gaya miki ba sai dai kawia ki boyemin Dan darajar Allah ki gayamin idan kinsan Inda zata a kaduna ki taimakamin sabida kananan yaran data tafi dasu Naeema kanta Bata gama mallakar hankalinta ba ba kuma ta da kowa babu Kuma Wanda ta sani karki boyemin Dan Allah idan kin sani ki gayamin"?

Sosai ya kashewa mmn Mannir jiki bare data ga Yana ta hawaye

Tayi wa Naeema alkawarin bazata gayawa kowa ba Amma a yanzu Anya zata iya cika alkawarin data daukar Mata bayan taga halin da Naseer yake ciki

"Dan Allah kigayamin mmn Mannir Kar ta  fada hannun mugayen mutane"?


"Naseer a gaskiya Mahaifiyarka ta takurawa Naeema Mahaifiyarka tana cin zalinta sabida tana ganin Bata da kowa mai Naeema ta Mata Haka data tsaneta nidai bansan Inda Naeema taje ba ta dai cemin zata gudu Amma bansan dgaske ta gudun ba sai yanzu da kazo kana tambayata Amma a gaskiya bansan Inda taje ba da nasani Zan Gaya maka"

Mmn Mannir tace tare da kau da kanta data tuna girman Alkawarin data daukarwa Naeema

Naseer cije lebb'ensa yayi batare da sake cewa komai ba ya tafi.

Motarsa ya bud'e ya Shiga ya zauna ya rufe Ido yana tunanin ta Inda zai fara neman Naeema wa ta sani a kaduna da zata tafi wajen wa zataje ?Mai yasa Naeema zata Masa haka ta gudar Masa da Yaya shi akaran kansa akwai abinda yake tsara musu Gaya Mata ne kawai baiyi ba Dan ya Kara shirya su gudu zuwa wani garin na Dan lokaci kafin suga ko  Umma zata hakura ta kyallesu.

Amma sai gashi Naeema.ta gudu da yayansa tashin hankalinsa Bai wuce Ina zata je ba wajen wa Kuma zata sauka Bai San har Naeema tayi wayo yin wanan tunanin ba Naeema daya sani tana da tsoro Mai yasa zata Masa Haka yanzu idan sun Isa kaduna Ina xasu kwana ita da yaran tunani iri iri Haka ya ringa yi  kirjinsa na Masa nauyi.

Take zazzabi Mai zafi ya rufeshi 

Sai su lukman ne Suka Gane bashida lafiya Suka Kira likita a kasan layinsu yazo ya duba Naseer ya mishi  allura ya Sha magani.



Dak'yar ya koma cikin gida Inda Yana Hawa sama.yaga Umma taci kwalliya ita da Hindatu fuskarsu kamar gonar auduga  sai cin kaza suke Bai kallesu ba ya Shiga d'aki a ranar ko runtsawa baiyi ba washegari da sassafe ya dau hanyar kaduna.

A takaice sai daya kwana uku a kaduna Yana bulayi duk da Bai San takaimaimai Inda zai ga su Naeema ba a cikin kwana uku ya zama kamar mahaukaci Dan ko wanka baya yi balle ya  samu cikakken bacci.

A ranar daya kwana biyar a kaduna Yana yawon nemansu Naeema Tasha tasha.unguwa unguwa ya yanke zuwa garin su Naeema Dan Haka kawai yaji kuma zuciyarsa ta karkata can.


Naeema


Duk da sauye sauyen da aka samu a garin na cigaba hakan Bai Hana ni Gane unguwarmu ba rabona da garin tun rasuwar mahaifina da Mahaifiyata  kaina tsaye gidan Mai unguwa na nufa da su Zahira da har kuka suka ringa min da Sunan sun gaji.

Sosai na ringa adduoi a Raina Akan Allah yasa Kar Mai unguwa ya canjamin sabida Yana ganin iyayena sun rasu.

Ga mamakina muna Isa ya.gane Ni Suka Kuma Mana tarb'a Mai kyau Inda naji wani irin kwanciyar hankali da nutsuwa Wanda rabona ma danaji Haka Zan iya cewa tun kafin na auri Naseer.


Sai da muka huta daddare ya aika a kirani Inda ya hau tambayata  mahaifinsu Zahira dafatan lafiya yagani da Yara.

Kuka na fashe dashi na tsinci kaina da karyar Naseer s'akina yayi

Sosai ya nunamin baiji dadin abinda ya faru ba ya min nasiha akan na rungumi kaddara zasu rik'eni tunda banida kowa sun Kuma Yi zaman mutunci da mahaifina Amma fa sai.na mayar dasu Zahira Dan bazai  iya rikesu ba baima Kamata na taho da yaran gabadaya ba.

Anan hankalina ya tashi danaji abinda yace kuka na fara yi.masa inaso na Gaya masa gaskiya abinda ke faruwa bakina yamin nauyi Kamar an dinke inaji Ina gani yace na tashi na tafi idan an kwana biyu zai saka a cikin yaransa wani ya rakani na mayarwa Naseer yayansa.


Sosai hankalina ya tashi na hau nazarin abin yi Inda a karshe na yanke kafin ya karamin magana gwara na Gaya masa gaskiya ko da zai iya taimakamin tunda Naga gidanmu na Nan a kulle Dan har maganar gidan yamin akan mallakina ne gwara na gyara na zauna a ciki nida yarana Dan canjin hannuna na ringa juyawa.


Ranar da muka cika kwana biyar a garin washegari.na karbi mukulin gidan nace Zan je na Dan gyara.

Na tafi da yarana gabadaya shigata gidan ya hau fad'omin da irin Rayuwar danayi da.iyayena cikin so da Kauna da kwanciyar hankali.

Haka kawai na samu waje na zauna na hau bawa yayana labarin iyayena  da yayana da ya tafi soja har yau banji labarinsa ba da irin San da sukemin.ina basu labari Ina kuka Inda mahaifina yake yawan Zama nake nuna musu Ina murmushi kamar ance na juya na kalli bakin kofa Naga Naseer a tsaye ya zubomin Ido Yana kallona badan nasan Naseer ba danace mahaukaci ne a tsaye a bakin kofa.......


Iabarin na da Dan tsayi shiyasa nake typing kullum na matsu Nazo. Ta tsakiyar labarin Dan haka inaga Zan Dan daddatse sabida mu fara Dan bana shiri da novel Mai tsayi Nan da Nan nake gajiya😃😃😃
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

     *NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*


*Page 19*



Cikin fad'uwar gaba na d'auke kaina banji dadin yanda mmn Mannir ta karya alkawarin data daukar min ba ba yanzu naso Naseer ya ganmu ba naso sai mun Dade na samu hutu kafin ya ganmu kasan Raina Kuma tausayinsa ne ya cike min zuciya  amma kuwa saman fuskata hade Rai nayi Dan bazan tab'a binsa ba nafi jina cikin kwanciyar hankali tunda na baro Garin Kano

Jiki ba kwari ya daga Minal Ya Dan matsar da Zahira da Nadeeya da suka kankameshi suna ihun murnar ganinsa.

Ina Jinsa suka karaso gefena ya sauke Minal ya saka hannu ya dauki Humaira Dana kwantar da ita a gefena
Ya sauke wani irin ajiyar zuciya.

Har lokacin ban yarda na kalleshi ba duk da Yana ta lallubar kwayar idona Dan mu had'a Ido daga ni har shi ba Wanda yayi magana 

Ni kuwa sosai na Kai zuciyata nesa wajen ganin na danne hawayen tausayinsa dake neman fitowa ta k'arfi da yaji ko ince tausayinmu gabad'aya.


Shi kuwa ganin naki kallonsa yace "Taimakamin da ruwa in Sha Naeema"

"Mik'ewa nayi nayi hanyar waje Dan babu komai a gidan.

Cikin gidan Mai unguwa na Shiga na d'ebo Masa ruwa a kwanun Sha na rufe na kawo masa na ajiye a gabansa.

D'auka yayi ya kafa baki sai daya shanye tas ya Ajiye anan na saci kallonsa Naga yanda yayi wurjan wurjan lebb'ensa duk ya bushe.

"Naeema Mai yasa Kika min Haka a ganina bai Kamata ki dau matakin guduwa da yaran ba da kin fadamin da na San Abunda ya Kamata nayi Sabida ki wahalar Dani Kika cemin Kaduna Kika tafi sai danayi kwana hudu a can kafin tunanin zuwa Nan yazomn haba Naeema Mai na Miki Dana cancanci ki zabi rabuwa dani"?

Cikin hade Rai Dan yasan dagaske nake bana San komawa gidansa marairaicewar da.yake bashi zai Saka na bishi da yarana ba 

"Idan na Gaya maka Naseer hakuri zaka bani kace mu cigaba da Addu'a kullum kalmar kenan alhalin sababin abubuwa Umma ke kara bijiromin dashi kana kallon irin dukan da take wa Zahira duk sabida tsabar tsanar da tamin ta ringa jifanta da mugayen kalamai Wai baza tayi albarka ba Yar iska zata Zama kuka na fashe dashi Dan kalmomin Nan data jefi Zahira dashi ya balain yimin ciwo na cigaba da Magana Ina iya wanan Bai isheta ba ta d'auke min Nadeeya tsabar bakin cikin an ganta Naseer ta fito tana kururuwa Tana watsawa kanta kasa Naseer da kiyayyar ta zata tsaya iya kaina wlh Zan jure amma yanzu ta fara tab'a min Yara bazan jure ba Naseer ba tare aka halliceni dakai ba zaka iya rabuwa Dani ka cigaba da rayuwarka kana da Daman da zaka auri Mata hud'u ka Shimfid'a irin rayuwar da kake so dasu a ganina idan kana kaunata zaka so samun kwanciyar hankalina na Kuma Rayu cikin farinciki Ina kaunarka har a Raina Amma idan akwai cutarwa gwara mu hakura ka sauwake min ikon Allah yasa kagani a zaune a yanzu har nake maka magana a cikin Minal ba irin azabar da Umma Bata gana min ba ta window na duro danake nakudarta sabida Kar ta kasheni banajin addua Zai iya sauko da Umma ta kaunaceni Allah na tuba Umma sosai nake ganin tsanata a idonta Dan Haka Naseer na hadaka da girman Allah ka sauwakemin albarkacin  yaran Nan ka gyara min gidanan da iyayena Suka barmin na  Rayu da yayana cikin kwanciyar hankali idan ma bazaka iya bani jari ba Ni zan nemi aikin da Zan ciyar dasu Naseer Dan Allah ka sauwakemin na gaji wlh Nagaji"


Na karashe Ina fashewa da kukan da nakejin yinshi ne kawai zai saka naji zuciyata ta rage nauyi da zafi idan har Zan tuna wani zalunci da umma tamin sai kirjina yyi nauyi Haka Zan ta kuka har sai naji sanyi a Zuciyata


Naseer kuwa Bai iyamin magana ba in Banda idonsa daya kad'a.yayi ja jijjiyoyin kansa sukayi rud'u rud'u ni nasan sabida gaban yayansa yake shiyasa yake ta mayar da hawayen daya cike Masa ido.

Zahira kuwa da Nadeeya duk da karancin shekarunsu Haka suka hau kuka suma.
Naseer kuwa kamar maganuna bulala Suka Masa a jiki a Haka ya zauna jiki duk ba kwari nasan Dan muna gaban yarane da ya janyoni ya rungumeni ya rarrasheni.

Sai Dana ci kukana na koshi na mik'e tare da d'aukar Humaira.

Ban kalleshi ba nacewa su Zahira suzo mu koma gidan Mai unguwa Dan ko tabarma babu a gidan namu bansan wayanda suka kwashe ba

Naseer Bai mana magana ba har muka fice


Muna zuwa na bawa Zahira tabarma da ruwa a buta Akan ta Kai Masa yayi sallar Magriba.

A hanyar Kai masa ruwa da tabarmar 

Mai unguwa ya ganta ya hau tambayarta inda zata je ita kuwa tace Masa Abbanta zata kaiwa.
Take Mai unguwa ya hau washe baki cikin farinciki zuwan Naseer 

Yana iddar da sallah ya shigo har d'akin da aka bamu muka zauna da yayana ya daga labulen Yana "Ashe babansu yaran Nan yabi yo sahu Kai Masha Allah naji dadin zuwan da yayi Allah ya daidaita ku Dama kullum sai nayi addua akan Allah ya sa ya mayar dake dakinki Dan shine rufin asirnki an Riga an haifi Yara har hudu ai sai Kuma ayita zaman hakuri Allah ya Kara kau da fitina Zan Masa magana shima Bari na saka a kiramin shi


Nauyin Mai unguwa da yanda ya nuna farincikin zuwan Naseer yasa na kasa Koda magana har ya fice daga gidan.

Sosai naji da gasken bazan koma gidan Naseer ba shiyasa na bi dashi ta ruwan Sanyi Dan ya bani takarda ta Amma idan yak'i kuwa ya zama Dole na fito na gayawa Mai unguwa halin da nake ciki da mahaifiyarsa nasan shima idan yaji bazai so na koma ba tunda neman rayuwata Dana yayana mahaifiyarsa take.

Ana iddar da sallah ishai Mai unguwa ya aiko a kirani
Ina zuwa yace na Kira Masa Naseer ba yanda zanyi Haka na juya na nufi gidanmu  Dan na Gaya masa rufin asirinsa shine ya sauwake min cikin ruwan Sanyi sabida bana San na ringa fallasa Sirrin mahaifiyarsa.

Ga mamakina Ina Isa Naseer na zaune a Inda muka barshi ga tabarma da ruwan da Zahira ta Kai Mai a gefe ya tsurawa waje daya Ido  kirjinsa sai sama da kasa yake 

Bansan lokacin Dana taka da Sauri na Isa wajensa tare da durk'usawa a gabansa ba 

Yana dagowa ya wawuroni ya kankameni cikin wani irin murya daya karyar min da ba iya zuciyata ba komai na jikina 

"Naeema taya Zan soma rayuwa batare da ke ba Taya Zan soma rayuwa da wata matar idan ba ke ba Naeema nafiki Jin ciwon halin da kike ciki sanadin halin Mahaifiyata na kamu da mumunan hawan jini ban taba fada Miki bane Naeema Tayaya Zaki ce na sawake Miki ya kikeso nayi da Raina ke da yarana nake gani nayi farinciki da Ana canja uwa da na Dade da canja Umma badan Mahaifina da Abba sun tabbatarmin da ita ta haifeni ba Naeema da sai nace Umma ba Mahaifiyata bace Dan Uwa da tausayi aka santa uwa bata cutar da dan data Haifa na rasa yanda zanyi da Umma nayi nasihar nayiwa waazin duk tak'i ji bakece Bata kauna ba Naeema Ni data Haifa nine Bata so Dan tasan farinciki da kwanciyar hankalina kune Naeema wlh da Umma zata ce na mallaka Mata duk abinda nake dashi zata barni mu Rayu cikin kwanciya hankali ko daki dayane na Kama Mana na ringa dako muna ci muna Sha da.naji dadi na.rasa yanda Zan mata  Dan Allah Naeema rabuwa Dani bashine mafita  ba na yarda Zan Kara nema miki wani gidan batare da saninta ba Ni Kuma zance Mata har yanzu banganki ba"

"Naseer bazan koma Garin kano ba sai dai ka gyarmin Wanan gidan ka ringa zuwa kana ganinmu "


"Ya zamuyi da Karatun yaran namu kasuwanci na fa danake yi a garin Kano wlh Zan iya takuna bazan Bari Umma ta.san naganki ba Zan ringa zuwa ko sau ukune sati Dama akwai wani karamin gida Dana siya a sharada inaso na zuba Yan haya tallansa akamin Mai gidan na bukatar kudi shine na siya kawai Zan gyara miki ki koma can wlh Umma bazata Sani ba"


A takaice duk ta Inda na b'ullowa Naseer sai ya zame ya kalamanceni abinka da tsakanin mata da miji sai Allah tuni Naseer ya shawo kaina duk alwashin Dana Sha yabi iska muna zuwa gaban Mai gari yayi wa Naseer fada da naseeha washegari muka fara shirye shiryen komawa Naseer sai lallab'ani yake Yana riritani (Nafeesa Naseer na balain Sona rabuwa daya k'iyi  Dani ya jawo Mana masifu da ko makiyina bana fatan yyi kwatan rayuwar da mukayi)

Matar Mai unguwa ita ta yarfamin kitso da Jan lalle na garjajiya yayana ma.aka musu kitso


Naseer kuwa ya cika Mai unguwa da abun arzki da matansa da yayansa tun kafin mu taho aka fara gyara gidanmu Inda Naseer ya bawa Mai unguwa kwangilar Ana Gama gyarawa a nemi Yan haya a saka a ciki kudin Kuma ya ajiyemin.


Hotel ya Kama Mana da muka iso sosai Naseer jikinsa ke rawa kamar Wanda yayi sabon aure duk wani Abu daya gani sai ya siyo Mana Dan sati daya ya kama Mana abinda ke fita dashi kawai gyaran gidan sharada ne da Abubuwan bukata da zamu yi amfani dashi.


Inama Umma ta saka Mana albarka a aurenmu ta daina daga Mana hankali da sai nafi kowace mace dacewa da gidan miji Dan ranar da muka kwana biyar Naseer ya siyomin set din sarka da dankunne har da zobe na daham Dubu talatin a lokacin ba karamin kudi bane sababin Kaya kuwa Haka ya cike Mana shi a akwati biyu atamfofi na ma kuwa Mai karamin kudi a ciki shine dari bakwai Wanda a kudin yanzu Zan iya yin Dubu biyar.


A Dan tsakanin kuwa sosai na dage da Addu'a Naseer kuwa shima Bai zauna ba.

A ranar da muka cika sati daya muka tare a karamin gidan Naseer dake sharada.

Cikin kwana biyu ya samowa su Zahira makaranta har da Minal suka fara zuwa 

Har wani Dan sheki yake Yi na kwanciyar hankali.

Ni kuwa Inda ya kasance d'akina sai Dana rataya abinda Mallam Musbahu ya bani Dan dazan tafi sai Dana cire na kaina kuwa bana Wasa dashi sai idan Zan shiga bandaki nake cirewa Ina fitowa kuwa na maida kayana. 


Dak'yar na  samu na Shawo Kan Naseer akan ya koma gidan  Sabida Kar Umma ta zargi wani Abu Yama nuna Mata ya hakura Dani zai zauna da Hindatu anan ya harareni nayi dariya nace yayi maganinta cikin sauki da kafarta zata gudu sai a lokacin yace na kawo shawara Mai kyau shi Kuma zai na karyar tafiya Yana zuwar mana.

A ranar da zai koma goron dutse da yamma Inna zuwaira da zata iya haifata tazo gidan Ashe Naseer Mai Tayani Zama ya Nemo min wacce Kuma zata ringa Tayani aikace aikace idan ya dawo Kuma sai ta tafi idan zai tafi sai ta dawo.

Sosai naji dadin zuwanta Dan Zan samu Mai debb'e min kewa kila ma har Abu Idan ya shigemin duhu Zan iya neman shawarar ta.

Naseer sai daya ajiye Mana komai har da kudin da bansan Mai zai yi.dasu ba Wanda har dagewa.nayi bazan karba ba Dan cemin yayi kullum sai yazo har abinci ma anan Zai  ringa ci kwanciyar bacci ne zai ringa Mai dashi gidan.

Wajen karfe Tara ya Isa gidan fuskarsa kalar tausayi kamar gaske irin neman Naeema yake.

Tun Kan ya karasa Hawa sama yake jiyo Shewa.

Da Sallama ya tura k'ofar 

Ba Wanda ya amsa sai juyowa da sukayi gabad'aya suna kallonsa Hajara har da mik'ewa tayi dage tana kallon bayansa Wai ko ya dawo da Naeema sai data ga shi ka dai ne ta washe baki tana "ko Kai fa ka hakura kazo ka zauna da Yar albarka tace.tana nuna Masa Hindatu.


Naseer Bai ce komai ba ya hau kallon mutanen palon Hindatu ce da Saffiya da Lami har dasu Tijjani sun zauna a tsakiyar Palon sai barjen Naman kaza suke ga kwalaban lemo a bubude.

Wato ma budurinsu kawai suke da Naeema ta tafi shi Kuma daga tafiyarsa shine su Saffiya suka dawo gidan.

Ba wacce yayiwa magana a cikinsu har Tijjani dake gaishe shi


Ya d'auke kansa tare da nufar d'akinsa Kai tsaye yana Jin muryar Umma tana duk hade Ransa Naeema bazata dawo ba idan ma.zai ware ya ware.


Sai daya Dan gyara d'akin ya watsa ruwa ya kwanta ya hau tunani su Naeema Dan lokacin ba wayar hannu da ya Kira yaji lafiyarsu Naeema

 Dan kwanakin da yayi dasu ba karamin nutsuwa da kwanciya hankali ya samu  ba babu abinda ya Kai Zama da iyali dadi.

Bai San da shigowar Hindatu ba sai ji yayi ta fado kansa shi kuwa ya mik'e da Sauri ya wancakalar da ita ya fara binta da wani mugun kallo Yana "duk ranar da Kika Kara shigomin daki wlh sai na balla Miki kafa juya ki fita"


Hindatu da Sauri ta fita ko minti biyu baayi ba Suka dawo d'akin da Hajara cikin masifa ta fara magana tana "Wai Mai kake nufi dani.ne. Naseer akan me zaka auri Yarinya Kuma ka ringa wulakanta ta toh wlh ka kaini bango Kar sake ka Kara korarta daga d'akin Nan Dan nan da wata tara inaso a haifomin jika Ni naga masifa duk da shegiyar matarka ta Shiga duniya ka ki nutsuwa ka dawo hankalinka toh wlh ka nutsu Dan nasan Tama Dade da mutuwa an rage mugun iri"


Wani irin kallo Naseer yabi Hajaran dashi ya d'auke kansa Bai ce Mata komai ba sai data gaji Dan kanta ta fita waje tare da Kara rufo musu kofa har da su mukullin.

Hindatu kuwa har da wani murmushnta ta Kara haye.gado tana murmushi.

Naseer shima mik'ewa yayi ya kullo k'ofar da mukulli ya zare ya saka key din a aljihunsa ya Shiga bandaki ya dauro alwala yazo ya hau Kan Sallaya.

Tuni ya ware murya ya fara karatun Qurani Hindatu kuwa ta mik'e hankali a balain tashe ta nufi wajen kofa ta fara jijigawa sabida Karatun sosai yake kona fatar jikinta.


Naseer kuwa Yana ganin Haka ya mik'e ya Ajiye Quraninsa ya nufi wajen Hindatun ya rik'e hannayenta biyu da k'arfi ya cigaba da karatunsa da k'arfi Yana tofa Mata yawun bakinsa.

Hindatu kuwa da iya karfinta take ihu tana Kiran sunan Hajara Dana Mahaifiyata take Hajara ta Gane Mai ke faruwa hankalinsu ya tashi.

Hajara kuwa ta bud'e k'ofar d'akin sai dai Naseer ya kulle k'ofar ta ciki itama da Sauri ta dawo Baya 

Abinda basu fiye Yi ba b'acewa Dan sai Abu yaci tura sosai suke amfani da Wanan karfin.

Akan Dole Hindatu ta b'ace daga hannun Naseer 

Duk da Naseer ya tsorata sai Haka ya cigaba da karatunsa da k'arfi tsoro na Kara shigarsa
[6/13, 10:50 AM] Queen Meenali👑: *NAGA TA KAINA*

     *NA SADNAF*🌸🌸


®️ *_PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
         _{We Don't just entertain nd educate we also touch the heat of readers P.M.L}💪🏻_



*Free Novel*

*Page 20*

               Duk da yasan Hindatu da mahaifiyarsa suna cikin kungiya Bai San haka Abun yake ba yanzu macen da take tsafi wacce take Mayya mahaifiyarsa ta aura Masa Maganar Allah ne basa so suji kenan ma Mahaifiyarsa ba musulma bace toh a wane sahu zai sakata kenan kafura ko me innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Amma Abun mamaki mahaifinsa ya bashi labarin Mahaifin Hajaran Dalibansa ne Kuma musulmi toh Ina Hajara ta Samo wanan halin nata ko a cikin danginta akwai kafuran arna da basa sallah ne shiyasa ta Kauce hanya Haka bacewar da Hindatu tayi a hannunsa ya Kara gasgata Masa zargin su suka d'auke Nadeeya Yana ta imagining yanda hakan zai yiwu Wai mutum.ya b'ace sai da yaga zahiri.

Sosai.ya Kara k'arfin muryarsa Yana Shan alwashin ma Kiran mutane zaiyi suzo su Masa Saukar Qurani a gida.


Yana Jin Hajara na kwalla Masa Kira daga nesa da d'akin ya shareta


Shugubarsu kuwa ranta ba karamin b'aci yayi ba dan karatun ba iya Hindatu ya tab'a ba har da ita hakane yasa cikin bacin rai ta bayyana gabansu Hajara da lami Hajara kuwa suka zub'e a kasa suna k'ok'arin Magana ta daga musu hannu ta Shiga d'akinsu ta d'auke tukunyar Tsafin su da mudubinsu da duk shine karfinsu.

Tace wa Hajara sai ta hukunta su zata dawo musu dashi Kuma Hindatu bazata sake dawo wa Naseer ba

Kafin ma suyi magana har ta b'ace.

Hajara zaman dirshan tayi a kasa ta hau kuka Dan ko kad'an Bata San abinda zai  rabata da Karfin tsafinta gashi Naseer yaja Mata daga ita har yayan nata an kwace musu k'arfin.

Naseer kuwa tsoro yasa ko bacci baiyi ba  sai da aka  Kira sallah asuba ya fito da alwala baiga kowa a palon ba sai Tijjani dake ta sharar bacci.

Shau da Masa carbin hannunsa yayi ya mik'e a firgice

Naseer kuwa yace Masa ya tashi su tafi.massallaci ya Fadi hakane sabida yaga ko shima baya sallar ga mamakinsa sai yaga ya mik'e yayi band'akin palon ya d'aura alwala ya fito.

Tare.suka.tafi Massallaci Naseer kuwa Bai dawo  gidan ba sai da gari ya waye sosai wajen Shidda da rabi ya shigo gidan.


A Palo ya tarar da Hajara da idonta ya kumbure sabida kuka ta zauna tana ta jijiga kafa.

Wani irin kallo take Masa kamar zai wuceta kuma ya fasa ya tsugunna ya hau gaisheta.

"Burinka ya cika ka batamin komai Naseer na Haifeka Amma bakada burin da ya wuce ka bak'antamin toh burinka ya cika Hindatu ta bar rayuwarka Amma fa kasani wlh Tallahi sai na Kara Nemo wata na aura maka ita Idan Dan Naeema.kake ta haukar Nan toh wlh gwara ka Shiga hankalinka"


"Umma Maganar Allah ne bakwaso ko me karatun Qurani ne bakwaso nayi a gidana umma kinsan kuwa Allah ya hallicemu ne Dan mu San shi.mu Kuma bauta Masa Umma jiya karatun Qurani nake Hindatu ta b'ace a hannuna Umma kinsan kuwa hanyar da kike Kai b'ataciya ce ba mai billewa bace Umma Dan Allah Dan annabi ki tuba ki komawa Allah Umma wanan tsaface tsafacen ba Inda zai bille dake Umma tun sanin Dana Miki ban taba ganin kinyi Sallah ba Umma balle azo Kan sauran ibadan Umma lokaci Bai kure Miki ba ki tubarwa Allah ki dawo kan hanya Umma na saka ki a islamiyya ko Ni na koya Miki sabida kisan Allah "


"Naseer Ni ka saka a gaba kana zagi yanzu so kake kace bansan Allah ba kafura ce Ni ko me a takaice dai kana so kace Ni jahila ce ko Naseer Dan Hindatu ta b'ace a hannunka sai aka ce maka nima Ina bacewar Naseer Banga laifinka ba Naseer Kai da ka daga hannu ma zaka Mareni yanzu ai kanka ba daidai bane tunda wancan mayyar yar ta Shiga duniya ka haukace tunani ma ba daidai kake ba maganar da nake ma daban Wanda kake min daban idan ma.duk.kana wanan surutan ne Dan Kar Kayi aure wlh sai kayi

Kaji ma na Gaya maka.sanan wadanan munafikan daka saka a shago ban yarda dasu ba ka koresu Tijjani ya rike maka shagon.

"Umma Tijjani bazai iya rikemin shaguna uku ba ba yanda Zan Kori mutanen da suke samu a karkashina Zan dai bawa Tijjani jari ya rik'e kansa namiji ne shima ai ya kawo girman da zai Yi aure.

Safiya da Lami Kuma ya dace ace sun fito da mazajen aure Haka Dan wanan ba rayuwa Mai kyau suka zabawa kansu ba"


"Naseer  a takaice dai kora da Hali kakeso kayi Mana toh bari kaji na fada maka babu Inda zamuje Kuma jari ba iya Tijjani zaka bawa ba har dasu lamin  ka Gama duk abinda ka Dama Aurene sai kayi Dan ban Haifowa Naeema Kai ba yarinya duk tabi ta  saka ka fice daga hayyacinka"


Naseer tashi yayi ya Shiga d'aki ita kuwa ta cigaba da bambamin fad'a kamar zata Ari baki.

Ahaka ya shirya ya zo ya fice daga gidan


Bai tsaya a koina ba sai a sharada lokacin Naeema tana daki tana bacci Inna  zuwaira Kuma tana Dan Kara gyagyara gidan su Zahira kuwa Suna makaranta

Sai a gidan ya Rama baccin dake kansa yaci abinci ya huta sukayi ta Hira kamar basu da wani matsala  yaso kwana sai da Naeema ta dage Masa Akan Kar ya kwana Dan Hajara na iya ganewa

Yana dawowa kuwa gidan ya d'auko Quraninsa a Palo ya hau karatun Qurani Dan sosai yake so su Umma su ma su bashi space ya sarara Amma ga mamakinsa ba Wanda ya tashi a cikinsu ya gudu kamar yanda suka Saba.

Sosai kansa ya daure da mamaki Hajara kuwa sai jefa Masa harara take sai daya Kai Aya ya mik'e zai Shiga d'aki tace "wato k'arfi da yaji kake so mu bar gidanan babu Inda zamuje Naseeru muna Nan tare da.kai zanyi maganin taurin kanka


A Haka rayuwa ta kasancewa Naseer da Naeema.

Acan  yake yin komai kwana ne kawai baya yi a gidan shima da an kwana biyu zai cewa Hajara tafiya ta taso Masa ahaka zaije yayi sati ko sati biyu a gidan Naeema sosai suke taka tsantsan Dan Kar Hajara ta  gano  suna tare.

Duk da lokacin sosai ta matsa Masa da zancen aure har mamaki take yanda Naseer din yake rayuwarsa batare da ya damu ba gashi ba komai na tsafi da zasu iya gano komai a game dashi Koda akwai yanzu idan Suka so ganin Naeema ta mudubi basa iya ganinta har mamaki suke Nan kuwa basu San layyar data saka a kanta bane.ya hanasu ganinta shugabarsu ma sai cewa.tayi kila ma Naeema mutuwa tayi shiyasa basa ganinta

Naeema sosai Jin dadi da kwanciyar hankali ya zauna Mata har ta ringa tunanin duk wanan lokacin Mai yasa dabaran hakan Bai fad'o musu ba.


Naseer shima sosai ya samu kwanciyar hankali sai zai je gidansa da mahaifiyarsa take ciki yake d'auko wata fuskar ya aza idan yaso ma tsokano Hajara idan tana Masa zancen aure shi kuwa sai yace Mata Shi bazai yi aure ba sai Naeeema ta dawo anan fa Hajara xata hayayyako kamar zata masa.baki tayi ta cewa Naeema ai ta mutu ko ba mutuwa tayi ba Bata isa ta dawo gidansa ba.

Ahaka har sai da suka kwashi watani shidda cas watarana ya dawo daga gidan Naeema.

A Palo ya tarar da Hajara ta balain had'e Rai Safiyya Kuma tana zaune a gefenta.

Gaishe ta yayi ya mik'e zai wuce d'akinsa Hajara ta dawo dashi ya zauna.

Ta fara magana cikin b'acin rai "Naseer kana so kaga b'acin Rai na ko kana so sai na balain Bata maka kafin  mu shirya dakai ko ka Nemo matar aure ko na nemo maka da kaina na gaji da ganin ka Haka ko na nemo maka matar auren

Sai ka wulakanta ta kamar yanda ka wulakanta Hindatu na baka Nan da sati biyu ka nemo matar aure idan ba Haka ba wlh da kaina Zan Nemo maka Kuma baka Isa ka wulakanta ta ba"


"Tom Umma Zan nema Ina ta ganinsu babu wacce tamin ne Amma insha Allahu zanyi kokari na nema din"

Daga Haka ya mik'e ya shige dakinsa

Fada Hajara ta ringa yi bayan ya Shiga d'akin Saffiya kuwa ta tab'a ta tana "Umma Anya Yaya baya tare da Naeema kuwa "?

Wani irin hantsulowa Hajara tayi daga Kan kujeran ta dafe kirjin ta tana "Mai kikace Suna tare fa  kikace Mai kika gani kikace Haka"?


"Umma kema kinsan yanda ya Naseer yake San Naeema yake Kuma San yaransa banajin da basa tare zai samu kwanciyar hankali Haka ke bakiga yanda.yaya ya danyi kib'a Yana sheki ba wlh kila Raina Mana hankali yake"?


"Zan Miki baki wlh Safiyya karki soma min wanan fatan idan suna tare a Ina ya ajiyeta Naga dai gida yake zuwa ya kwana sai idan tafiya ta Kama shi yake kin kwana a gida kin manta bama.ganinta a mudubi shugaba.kuma data duba da kanta tace kila hatsari sukayi suka mutu"


"Hmmm toh shikenan tunda Kikace Haka Amma nidai gani nake da Yaya baya tare da Naeema bzaki kansa fes Haka ba"


Mik'ewa Hajara tayi da Sauri tana "idan kuwa hakane Safiya na gano rainamin hankali sukayi wlh sai nayi wa Naseer baki wlh sai na kashe Naeema da hannuna Kinga Banga ma ta zama ba ya zama Dole mu koma Calabar muje mu bawa Shugaba hakuri ko Dan na ringa sanin abubuwa da ke wakana wlh tunda ta kwace komai namu banajin dadi Banga ta zama ba ya zama Dole mu d'auki hanya gobe"

Sosai hankalin Hajara ya tashi da maganar da Safiyya ta Mata washegari kuwa da sassafe Bata ma jira Naseer ya dawo daga Massallaci ba Suka dau hanya su uku Dan Tijjani tunda Naseer ya bashi jari ya Kama wani shago a gwammaja ya zuba kayan provision yake siyarwa Bai ma fiye dawowa gida ba.


Naseer sosai yaji dadin tafiya da Hajara tayi dasu Safiyya cikin kwanciyar hankali ya koma sharada da zama dama sabida gidan ya masu kad'an ya Kara siyan  fili a jikin gidan aka hade da yake da kudi a hannunsa tuni gidan yayi kyau da tsari.

Arziki Kam har yaci uban na da Dan Naseer yanzu Yana da gidaje sun Kai shidda filaye kuwa zasuyi hudu Kuma duk manya shagunansa kuwa shidda.banda wasu kasuwanci da yake danyi kudi na shigo Masa.

A cikin wanan shekarar yake burin idan Allah ya amince zasu je aikin Umara shi da Naeema.

A kuma cikin wanan yanayin Naeema ta Kara samun ciki Wanda Naseer ya balain kwallafa Rai akansa yake Kuma sawa a addua Allah ya azurtashi da samun da namiji.

Naeema kuwa tunda Naseer ya dawo gidan yace Masa Hajara sunyi tafiya hankalinta ya kasa kwanciya Haka kawai takejin kamar babu alheri a tafiyar tasu hakane yasa ta dage da Addu'a duk da Bata tab'a Zama ba adduar ba Naseer ma har ya zama Masa jiki adduar.

Hajara kuwa dak'yar shugabarsu ta hakura ta maida musu karfinsu Inda ta gargadesu da nisantar duk Inda ake Karatun Qurani anan Hajara tasa a duba Mata Naeema ta mudubinsu ko tana rayye anan suka duba Amma duk Inda suka kai ga tsafinsu basu iya ganin Naeema ba Naseer kawai suka gani a zaune a kasuwa Yana ta zabga lissafi.

Satinsu uku a Calabar suka dawo.

Naseer bai.ma San sun dawo ba sai daya zagayo wajensu Lukman Dan ya karbi takardar lissafi da sukeyi yasan sun dawo.

Sosai yaji Bai ji dadin dawowarsu ba.

Ahaka ya b'oye abinda ke Ransa ya musu Sannu da zuwa.

Sai a lokacin Hajara ta ga kibar da Naseer yayi na kwanciyar hankali.

Yana tashi ta kalli Safiyya tana "Akwai wani Abu a kasa wlh ban yarda da Naseer ba gobe idan ya fita inaso kiyi ta bimin bayansa har kiga Mai yake ciki"

Naseer kuwa ba a San Ransa ya kwana a gidan ba 
Washegari da sassafe Naseer ya fice daga gidan ya nufi gidansa dake sharada.

A Haka Safiyya tayi ta binsa a baya batare da yasani ba har ya Shiga gidan.

Sabida tsabar balai Haka Safiyya ta labe a kangon jamaa sai da Naseer yaci ya koshi yayi wanka ya shirya tafiya kasuwa.

Haka kawai Naeema ta ringa Jin fad'uwar gaba jikinta ba dadi addua kawai take a ranta har  Naseer ya tafi.


Safiyya kuwa cikin mamaki ta ga Naseer ya fito daga gidan daga wajen gate Naeema ta rakoshi da Hijabinta tayi wani irin fari Kamar ba ita ba


Bata tsaya ma ganin tafiyar Naseer ba ta fita titi da balain gudu ta hau taxi Suka nufi goron dutse sai vibrating take Kamar itace Hajaran.

Ko parking din kirki Mai taxi Bai Gama yi ba ta fito daga motar ko kudin Bata bashi ba ta hau sama da balain sauri Tana kwallawa Hajara Kira 

Zumbur ta mik'e tsaye 

Tace "Wlh Naga Naeema Yaya Yana tare da naeema"


Yaraf Hajara ta zub'e a kasa kamar an doka Mata guduma ta Kara mik'ewa cikjn tashin hankali tana Kika ce me"?


Safiyya hannun Hajara kawai ta jawo Suka sauka da gudu Suka fada taxi din tana ce Masa ya maidata Inda ya d'auko ta zata hada Masa kudinsa.


Hajara wani irin jijjiga kawai take Tana vibration har suka Isa sharada.

Jikinta sai rawa yake yanda zata.shake Naeema.

Suna sauka Safiyya ta hau buga gidan da hannu biyu.

Ina zaune naji Ana buga gate da balain k'arfi mik'ewa nayi cikin fad'uwar gaba na dafe kirjina haka kawai Umma ta fado min a Raina.

Inna zuwaira ce ta bud'e gidan tana bud'e gidan Safiyya ta bangajeta suka shige suka hau kwallawa Naeema Kira ahaka har Suka shiga palon dana daskare a tsaye tunda naji muryar Safiyya.

Kallon kallo muka fara da Umma tana tsaye daga bakin kofa Ni kuwa in Banda sallati babu abinda nakeyi.......ƙama Hajjo yana faɗin, “Da wannan zaku gansa dole, dan ƙa'idarsa sai yaga bayanan ciwon mutum na baya inhar ya taɓa ganin likita akan hakan”.
     Nanma godiya suka sake masa. Hajjo ta sake miƙama baba malam. Amsa yay ya saka Numbers ɗin da aka bashi a cikin file ɗin ya ajiye.
     Kasancewar lokacin sallar isha'i yayi duk sai suka fice har Doctor. Bayan an idar da salla Doctor ya sake dawowa tare dasu Ahmad ya shiga ya ƙara duba Nu'aymah. Sai da ya sake tabbatar da komai ya zauna sannan ya fito yay musu sallama akan insha ALLAH da sassafe zai dawo yaga jikin nata. Idan kuma sunga da wata matsala komai dare su kirashi.
     Sun masa fatan alkairi da godiya ya tafi.

_★__★_

      Baba malam bai shigo gidan ba sai kusan goma saura, dan ya tsaya sunyi karatu ne. Sashen Hajjo ya fara shiga ya duba Nu'aymahn. Har sannan barci take, dan haka ya ɗauka file ɗin nata ya fice da shi zuwa sashensu.
      Duk abinda Umm take masa bata fasaba. Yanda kuma bai mata magana akan Nu'aymahr ba itama batace da shi ƙala ba har suka kwanta.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
WASHE GARI
_______________

          Alhmdllh Nu'aymah ta tashi jikinta da sauƙi, kuma kamar yanda kowa yay fata bata manta da komai ba kamar yanda Doctor yayta jin tsoro. Hajjo ce ta taimaka mata tayi wanka. Yusrah ta kawo mata abinci tama zauna da kanta ta ringa bata. Ta ɗanci babu laifi, dan Yusrah lallaɓata ta dingayi ita da Hajjo.
     Kamar yanda kowa na gidan yazo ya dubata da safen haka Baba Malam da Umm ma sukazo suka dubatan. Sunji nutsuwa sosai a zukatansu ganin jikin nata Alhmdllh. Sai dai kowansu bai nunaba a fuska, sunma haɗe mata gabas da yamma.
    Hakan ba ƙaramin sake ɗaga hankalin Nu'aymah yay ba, harta kasa haƙuri ta shiga tambayar Yusrah ko wani abu ya faru bayan barinta gida ne? Dan ita tayi zaton idan ta dawo zataga kowa na murnar dawowar tata. Amma saita samu saɓanin hakan, sai ma kalaman baba malam na jiya keta mata kaikawo a cikin rai.
    Ƙasa Yusrah tayi da kanta hawaye na cika mata idanu, haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Nu'aymah ɗin mai tsanani. “Yusrah dan ALLAH kimin bayani mana? Ina Yah Ab da Adawiya duk bamma gansu ba”. Nu'aymah tai maganar cikin sanyin murya na alamun rashin jin daɗin jiki.
     Saurin miƙewa Yusrah tayi ta juya mata baya zata bar ɗakin. Nu'aymah ta riƙe hannunta itama da sauri. Hannu Yusrah tasa ta goge hawayen dake rige-rigen sakko mata a kumatu batare data juya ta kalli Nu'aymah ba.
     Dai-dai nan Hajjo ta shigo tare da Doctor da yazo sake zuwa ganin jikin nata.
         “Kai lafiyarku?”.
Hajjo ta faɗa ganin Nu'aymah da Yusrah duk suna hawaye.
         “Ba komai Hajjo”. Yusrah ta bama Hajjo amsa tana zare hannunta daga cikin na Nu'aymah. Kamar hajjo zata sake magana sai kuma tayi shiru suka bama Doctor damar duba Nu'aymahn. Yaji daɗin ganin jikin nata normal, sai dai yanason mata allura yana tsoron rikicinta da zasu kwasa. Nu'aymah ta mugun tsanar allura a rayuwarta, indai akace za'ai mata allura to lallai an taro match kuwa. Dan sai kowa yaji a gidan harma makwafta.
     Kallon hajjo yay murya ƙasa-ƙasa yace, “Hajjo ko za'a kira mana su Ahmad ne kusa. Allura zan mata kinsan kuma sai ansha yaƙi”.
       Sosai hajjo ta waro idanu waje. Taɗan kalli Nu'aymah data kwanta idonta na kallon fanka dake juyawa a hankali. Sake kallon Doctor tayi, itama a hankali tace, “bara dai a dubamin cikin iyayen nasu tunda duk basu fita ba”.
    Kansa ya ɗaga mata ya tashi ya fita falon dan ya haɗa allurar. Itama Hajjo biyosa tayi.

      Kusan mintuna biyar da fitar tasu duk suka dawo harda Baba malam dake cikin shirin fita. Batare da yayi maganaba ya kama Nu'aymah da kansa ya tayar zaune. Kallonsa take cike da so da ƙaunar mahaifin nata. Amma yanda yay kicin-kicin da fuska sai yake ƙara tsoratata. Ganin yanda ya jata jikinsa ya rungumene ya saka ƙirjinta bugawa. Dan tun tana yarinya inhar taga ya mata irin wannan rungumar to lallai allura za'a mata. Saurin ɗagowa tai ta kalli Doctor daya ɓoye hannunsa a baya. Jikinta ne ya fara tsuma, zatai magana Baba malam ya balla mata hararar da ta sakata maida kanta jikinsa ta kwantar.
      Rikici sosai akasha kafin Doctor ya mata allurar, ba ita kanta ba har baba malam da hajjo masu riƙetan saida ta tarama gajiya. Doctor kam har ƴar zufar wahala yakeyi a goshi, a ransa yana sake jinjina daru irin na Nu'aymah.
        Tunda baba malam ya maidata ya kwantar ajiyar zuciya kawai taketa faman saukewa hawaye na zirarar mata da gudu. Hajjo ta zauna inda baba malam ya tashi ta ɗago kan Nu'aymah ta aza bisa ƙafarta tana shafa mata dogon gashinta.
       Sauran magungunanta Doctor ya ajiye yayma hajjo sallama suka fice shi da Baba malam.
        Hajjo ta jima tana lallashin Nu'aymah kafin ta samu tayi shiru barci ya saceta. Amma har cikin barcin tsabar rikicinta ajiyar zuciya taketa faman saukewa a jajjere. Haka dai hajjo ta lallaɓa ta kwantar da ita da gyara mata kwanciya ta tashi ta fice.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
______________
DUBAI
________

              Amarya Adawiya da ango Abdallah sun isa ƙasar dubai lafiya, sai dai gaba ɗaya ya canja tsarin daya shiryama kansa da Nu'aymah. Ya dai kama musu babban hotel kuma a ɗaki ɗaya. A randa suka isan kuma ya sace wayar Adawiya ya ɓoye batare data saniba.
     Ita dai duk abinda yake mata bai ɓata mata rai, haɗe fuska da ƙin mata magana tunda suka taho baisa taji haushinsaba balle sonsa ya ragu mata a zuciya. Saima ƙaruwa da ya sakeyi tanajin kamar ta haɗiyesa.
     Gadon ya bata ta kwanta shi kuma yasa bargo a ƙasa yay kwanciyarsa. Da asuba ya rigata tashi, yay wankansa yay shiri tsaf. Sai da ya kammala komai sannan ya tadata. Mamaki ya kamata matuƙa ganinsa cikin shirin fita, sai dai kuma babu fuskar tambayarsa.
       Murya a shaƙe yace, “Duk abinda kike buƙata ki kira zasu kawo miki”. Daga haka bai sake tofa komaiba yay ficewarsa daga ɗakin yaja mata ƙofar. Ta jima zaune a wajen tamkar wata gunki har gari yay haske sosai kafin ta sakko jiki a sanyaye taje tayo alwala. Duk da hakan da yay mata babu daɗi sai bataji haushinsaba. Haushin Nu'aymah nema ya kamata, dan a ganinta zaman dataine cikin zuciyarsa yasa baya ganin kowa da gashin mutunci sai ita. Aiko ta ɗauki alwashin sai ya manta wata banza Nu'aymah a zuciyar tasa har abada balle kuma wata Yusrah da tasan bata a gabansa.

“Hajiya Adawiya, ke dai kike kiɗanki kike kuma rawarki🤣😏”.

               Haka ta yini ita kaɗai, daga kallo sai cin abinci da kwanciya. Gashi ta nema wayarta ta rasa, sai kawai tunaninta ya bata kota barta a gidane kokuma ta yaddata a jirgi Yah Abdallah ya ɗauke mata. Ta barsa akan idan ya dawo zata tambayesa.
         Abdallah bai dawo hotel ɗinba sai kusan 11 na dare, harkokin kasuwancinsa ya yini yi hankalinsa kwance. Baiyi zaton iske Adawiya ido biyu ba. Amma a mamakinsa sai ya sameta zaune dirshen tana kallo. Sannu da zuwan data masa kawai ya amsa ya ɗauke kansa. Ya ɗauka kayan barci ya nufi bathroom. Tana nan zaune ya fito tsaf da shi. Nanma bata ishesa ko kalloba ya zauna a ɗaya daga rukunin kujerun ɗakin yay kira a kawo masa tea. Babu jimawa akai knocking ƙofar. Adawiya ta miƙe jiki na ɓari zataje ta buɗe ya ɗaga mata hannu. Da kansa ya tashi yaje ya amso ya dawo yay zaman sha bayan ya kunna laptop.
       Sunja tsahon lokaci zaune, Adawiya nata faman kallonsa kamar ta samu television, shiko aikinsa yakeyi tamkarma ya manta da ita a cikin ɗakin.
      “Uhhm Yah Ab dan ALLAH ko kaga wayata?”. Cak ya tsaya daga aikin da yake yana sake tsuke fuska batare da ya kalleta ba. Ba komai ya jawo hakanba sai Yah Ab datai kiransa da shi. Dan Nu'aymah itace ta fara kiransa da suna har kowama ya ɗauka. itace kuma ke kiransa hakan a koda yaushe. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya girgiza mata kansa kawai ya cigaba da abinda yakeyi.

★★★★

        Haka suka cigaba da tafiya a kwanakin da duk suka gabata na barinsu ƙasarsu. Adawiya duk a takure take, dan Abdallah kullum da sassafe yake fita, bazai dawoba kuma sai sha ɗaya. amma soyayya ta rufe mata idanu ta kasa jin zafin hakan da yake mata.
     Shiko gaba ɗaya ya ɗauketa yasa a kwandon shara ya maida hankalinsa ga kasuwancinsa kawai, dan a maimakon kwana goma da ya shirya yi a ƙasar ya maidashi kwana shida zasu wuce.

         Tun a randa Nu'aymah ta dawo gida yay mafarkin hakan da daddare, aiko tunda asuba yay kiran Number Ahmad. Cike da farin ciki Ahmad ɗin ya sanar masa komai, dan dama shima yana da shirin kiran nasa, so yake kawai jikin Nu'aymah aga yanda zai kasance a washe garin.
            Karan farko da tun faruwar al'amarin nan Abdallah yay sassanyan murmushi hawayen farin ciki na cika masa ido. Jiyake tamkar an tsundumasa aljanna yau. Yana katse kiran ya kira Momy itama. A lokacin dawowarta kenan daga sashen hajjo taje ta duba Nu'aymah itama.

        Bayan sun gaisa cike da so da ƙaunar juna irin ta ɗa da uwa, ya tambayi lafiyar kowa a gidan sannan cike da zumuɗi yace, “Momy ashe Nu'aymah ta dawo?”.
       Jimm tayi kamar bazata amsa masaba, sai kuma tace, “Uhmm! ta dawo jiya”.
        “Kai Alhmdllhi Momy, yanzu zanje na saya mana tickets kuwa mu dawo, in ALLAH ya yarda wannan karon bazan sake ta sake kuɓuce minba Momy, a yau ɗin nan ina durowa koda magriba ne sai an ɗaura mana aur......”
         “Kai! Shashasha dakata min. To idanma mafarki kake maza ka farka ka dawo hayyacinka. Wai kai Abdallah wane irin sakaran banzane halan? Ka fita idanuna tunkan na rufesu da kai a ciki wlhy. Bara makaji na maka mai kankat. Wlhy tallahi idan naga ƙafarka a ƙasarnan batare da ni nace kazoba ALLAH ya isa ban yafe maka ba.....”
         “Momy!!” ya faɗa cikin tsananin tashin hankali.
     “Yes! Abinda kaji shi na faɗa. Idan zakai haƙuri da waɗanda aka baka kayi. Hauka akeyi da za'a manna maka mata har uku ƴan family ɗaya uban ƴan son zuminci? Itama Yusrahn ina nan ina nema maka hanyar barinta wlhy. Adawiyar dai ta tsira tunda ALLAH ya sota ka baro ƙasar da ita da wuri. Idan suma sunada nasu zaɓin nima inada nawa ai, amma aka nunamin fin ƙarfi da ƴan uwantaka. Kai kuma shashasha da yake baka kishina hakan ko damunka bayayi. To wlhy kama cire wannan tunanin a ranka. Kuma ko a waya ka kira wani cikin iyayenku kace a ɗaura maka aure da Nu'aymah shima ban yafe makaba. Idan wannan maganar tasa ka kirani karka sake kirana”.
    Ta katse wayar batare da ta jira cewarsa ba.

      Sosai jikin Abdallah ke tsuma. Haƙoransa har wani bada sautin ƙara suke saboda rawar da bakinsa keyi. So yake ya faɗi sunan Momy amma ya kasa haɗa kalmar waje guda dan tsabar rikicewar da yayi.
      “Yah Ab lafiya kuwa?”. Adawiya ta faɗa tana ɗaura hanunta saman kafaɗarsa. A fusace ya ɗago ya hankaɗe hannun nata tai taga-taga ta faɗa saman kujera. Ko kallonta baiyiba yay wurgi da wayarsa ya nufi bathroom da sassarfa. Yana shiga ya sakarma kansa shawa ruwan na saukar masa a jiki batare da ya cire kayaba.
     Kalmar ALLAH ya isar Momy ce keta masa kai kawo a zuciya har kana hango sama da ƙasan da ƙirjinsa keyi na.

       Adawiya kam tana ganin ya shige ta miƙe idanunta cike da hawaye. Da ƙyar ta ɗangyasa ƙafarta data buge da centre table ta isa inda yay wurgi da wayarsa. Addu'a take ALLAH yasa babu lock. Cikin sa'a kuwa babun, sai dai hoton data fara cin karo da shi a fuskar wayar ne yasata jin wani irin zafi tamkar an soki zuciyarta da mashi.
       Hoton Nu'aymah ne da sukayi ranar walimar gama makarantarsu. Tayi masifar ƙyau a hoton, dan ɓakar doguwar rigar data saka na Material ɗinkin yay masifar zama mata a farar fatarta. Ga idanun nan sun bala'in fitowa cikin kwalli har wani ƙyalli suke saboda haske. Tayi ɗan murmushinta loɓar kuncinta data gemunta ta fito raɗam. Sosai Adawiya ke faman taunar lips da ƙarfi tamkar zata hudasu, duk da tasan hoton tunkan shi Abdallah ma ya gani hakan bai hanata jin zafi mai tsanani ba. Da kyar ta iya danne ranta ta shiga dan son ganin dawa yay waya. A fili tace, ‘Momy!. To mita gaya masa daya fusatashi haka har yake neman karya ni a banza?’. Bata da mai bata wannan amsar, gashi kuma batasan inda wayarta takeba balle ta kira wani ta tambaya. Tanajin tsoron yin amfani da tasa kuma yazo ya kamata. Da sauri ta ajiye wayar inda ya jefar jin za'a buɗe ƙofar bayin.
       Tsaye yay cak a ƙofar bayin yana binta da kallon tuhuma fusatar zuciyarsa na daɗa bayyana saman fuskarsa.............✍

   
        Kuyi haƙuri, jiya man kaina ne ya tsiyaye tas yasin na kasa typing😖.


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

No. 7

................Sosai gazawar Umm take ƙoƙarin bayyana ga kowa. Dan gaba ɗaya yinin yau da Nu'aymah ta yisa a ranta. Tun tana kukan zuci kamar yanda ta saba har hawaye suka kai ga fara sakko mata daga idanu. 
        Wajen misalin biyu da rabi na rana Baba malam ya shigo gidan. Kamar yanda al'adarsa take inhar ya dawo daga wajen aiki sai ya fara zuwa sashen Hajjo yaga lafiyarta. yauma haka ne. Zaune ya isketa a falo Imran na tausa masa ƙafa yana kumbura baki dan ta sakashine dole.
     Murmushi Baba malam yay da zama a ƙasa gefenta kaɗan da ajiye mata ledan kayan fruits idonsa akan Imran ɗin da shi sam hankalinsa bai kai kansa ba.
           “Imran ya naga fuskar a kumbure? Ko dai aikin innah ne ba'a son yi?”.
     Kallonsa Imran yay da sauri, sai kuma ya saki ƙafar Hajjo ya nufi baba malam ɗin yana sake tunzura baki gaba. “Baba sannu da dawowa”. Kafin Baba malam ya bashi amsa Hajjo ta katsesa. “Dan gidanku dawo ka cigaba, inba hakaba kasan ALLAH nasan ta inda zan rama mai ƙwalelen ƙeya kawai”.
      Dariya Baba malam yayi yana kallon yanda Imran ɗin ya cika yay fam, sai kuma ya kalli Hajjo da itama ta kumbura farar fuskarta da duk tai tamojin tsufa tana zubama Imran ɗin harara......
       “Ni wlhy na gaji Hajjo, kumafa Momy jirana take zan mata aika”.
     “Oh! Uwarka ta fini kenan?..”
Baba malam yay saurin haɗiye dariyarsa da matsawa kusa da ita gab ya kama ƙafar tata ya aza saman ƙaramin filon kujera. “Kinga Inna manta da shi kinji, idan shima yana tsoron ɓatama mamarsa nima ai gani tare dake ko?”.
         Murmushi tayi kamar ba itace da fuska a kumbure ba. Sai kuma ta watsama Imran ɗin harara tana faɗin, “Tashi ka fitarmin a falo to kirikun banza, indai nice ai inada ranata yaro”.
     Tashi Imran yay da sauri dan ganin Hajjo ta kwakuso filon kujera da alama dukansa zatayi. Sai da yaje bakin ƙofa sannan ya juyo. “Ai dai gobe idan ALLAH ya kaimu zamuyi komawarmu Abuja.......”
     Kafin ya rufe baki ta tilla masa filon, kwasa yay da gudu ya fice yana ƙyalƙyala mata dariya.
        “Wlhy Ɗan malam ƴaƴanku sun fetsare musamman ma ƙarshe-ƙarshen nan. Kaga akace maka Imran da Muhammadu da Jafar sunfi kowa rainanima a gidannan”. Hajjo ta faɗa a ƙufule.
      Cike da girmamawa da lallashi baba malam yace, “To kiyi haƙuri inna zan musu faɗa kinji, yanzu dai ƙafar ciwo take miki ne?”. 
        “Kaɗan take ciwon dai, na neman man zafin daka siyomin shekaranjiya na rasa inda yake, na tabbata cikin ƴaƴanku wani ya ɗaukesa. Ƙilama Zainabu c.......” sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa saboda tunawa da tai Nu'aymah ma bata gidan. To ita kaɗaice ke mata yanda ta gadama a cikin jikokinta a zauna lafiya a gidan. Dan suna mugun ɗasawa da Nu'aymah saboda duk aikin da ta sakata yimatashi take. Hatta da wanki Nu'aymah ce kema Hajjo. Hakama gyaran sashenta. Sai ko Adawiya itama sunaɗan shiri, amma ƙa'ida kullum sai sunyi faɗa.
      Ɗan murmushi baba malam yayi mai ciwo, dan shima a kullum ɗiyar tasa tana a ransa. Ya sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Karki damu innah insha ALLAH zansaka Abubakar ya saya miki idan zai baro company. Sannan zanma Doctor Kabir magana yazo ya duba ƙafar, idan kuma asibitin zamu koma to”.
      Jikinta a sanyaye ta ɗaga masa kanta, harya miƙe bata iya sake cemasa komaiba. Sai da yaje gab da fita sannan ta kira sunansa. “Ɗan malam!”. Juyowa yay da sauri yana ƙoƙarin haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi da amsawa da “Na'am Innah”.
         “Har yanzu babu labarin Zainabu dai ko?”.
     Murmushin yaƙe yay mata wanda yafi kuka ciwo, ya ɗan girgiza mata kansa da faɗin, “Innah tasan inda taje ta ɓoye kanta ai. Randa ta buƙaci ganinmu da kanta zata nememu, ki kwantar da hankalinki wannan yabar damunki”.
     Bata iya cewa dashi komaiba yanzuma. Dan damuwa ƙarara ta hango a saman fuskarsa da cikin idanunsa. Amma dan ƙarfin hali sai yay mata murmushi sannan ya juya ya fita.

          Tamkar wanda aka zarema lakar jiki haka ya isa sashensa. Da tsarabar da yayo ta fruits ya fara cin karo a falo alamar driver baiga kowaba ya ajiye a nan. Ya ɗanbi ledojin da kallo kafin ya ida shigewa cikin corridor ɗin da ɗakunan barcin su Umm suke. Kansa tsaye ɗakinta dake can ƙarshen dogon corridor ɗin ya nufa, yay sallama kusan uku a ƙofar ɗakin babu amsa, sai kawai ya tura ƙofar ya shiga da sallama.
       Tsaye yay cak a ƙofar ɗakin riƙe da handle ɗin kofar yana kafe Umm dake zaune a saman gado, Muh'd na kwance ya aza kansa bisa cinyarta yana barci. Kan yaron take shafawa a hankali, kanta na kallon p.o.p idanunta na tsiyayar da hawaye. 
         Haɗiye tasa damuwar yay ya ƙarasa cikin ɗakin sosai. Harya zauna a bakin gadon kusa da Umm bata motsaba. Ya ɗaura hannunsa saman nata dake shafa na Muh'd. Nannauyan numfashi ta sauke da ɗago kanta. Kallon ido cikin ido sukaima juna ita da baba malam ɗin. Sai tai azamar saka hannunta na haggu ta share hawayen fuskar tata tana maye gurbinsa da murmushi.
       “Sannu da zuwa Abban Nu'aymah. Yaushe ka shigo ban saniba? Gaba ɗaya na gajine shinefa nace bara nazo na.........” hannunsa yay saurin ɗorawa akan bakinta alamar tayi shiru. Yasan ba wani abune ya saka wannan kame-kamenba sai dogon gargaɗin daya gindaya mata akan karta sake masa maganar Nu'aymah koda da wasa ne. Umm macece ita mai biyyaya da gudun ɓacin ran mijinta, duk abinda ya nuna bai masaba ƙoƙarinta shine dainashi tai masa wanda zai sakashi a farin ciki koda ita zai cutar da tata zuciyar kuwa. Wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya ƙara mata kima da daraja a gareshi, tare da sake girmama soyayyarta a ranshi.
     Miƙewa yay ya ɗauki Muh'd a hankali ya matsar dashi can gefe ya kwantar. Ita dai tana binsa da kallone har ya dawo ya zauna kusa da ita sosai. Kamota yay ya kwantar da kanta a ƙirjinsa. A tare suka sauke nannauyar ajiyar juciya. Hawayen da taketa ƙoƙarin karsu zubo suka ziraro a guje suna sauka bisa jikinsa.
        Idanunsa ya lumshe tare da sake kwantar da ita jikin nasa da ƙyau, ya zame ɗan kwalinta yana shafa kanta dake cike da gashi dogo mai yarfin furfura ɗai-ɗai alamar girma ya fara kamata. Sake kwanciya tai sosai da cigaba da hawayenta.
    Sunja tsahon lokaci a haka har saida akai kiran sallar la'asar sannan. Itace ta ɗagashi da sauri. Hakan yasa ya farka daga barcin daya figesa shima. Tunda abinnan ya faru bai sake yarda sun kwana ɗaki ɗayaba tun randa ta kwana babu lafiya. Hakan yasa suke tsananin kewar ɗumin junansu. Matsar da fuskarsa yay gab da tata ya sumbaci goshinta da dogon hancinta.
     Ɗan murmushi tamasa da sadda kanta a ƙasa na alamar jin kunya. Shima yay murmushin yana sauke ƙafafunsa ƙasa. Batare da yace mata komaiba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “Ki tada Muh'd yay alwala mu wuce massallaci”.
       “To” ta amsa masa tana binsa da kallo.

__________________________________ 

              Ana shiga sallar la'asar jar motar na shigowa cikin layin. Parking yay a ƙofar ƙaton gate ɗin gidan yana kallon gate ɗin massallaci. Kafin kuma ya maido dubansa kan Nu'aymah dake a gefensa hannu da idanunta da baki a rufe tana gyangyaɗi.
       Ɗauke kansa yay ya kashe motar gaba ɗaya. Bai fitaba, saima kwanciya yay jikin kujera ya lumshe idanunsa dake a cikin baƙin glasess ɗinsa.
       Kusan mintuna uku da tsayuwarsu Nu'aymah ta farka. Sai dai kasancewar idanunta da bakinta a rufe suke sai bazaka fahimtaba. Addu'a kawai take jerawa a ranta na nema agajin UBANGIJI. Sai da aka fito massallaci mutane suka gama shashsharewa, sai hayaniyar yara ƴan islamiyya dake cikin harabar massallacin. Kusan biyar na yamma Baba malam ya fito daga cikin massallacin shi da wani maƙwafcinsu suna magana. Saurin tashi yay zaune da kallon Nu'aymah, yay azamar saka hannu ya ɗaye mata salataf ɗin da suka rufe mata baki da shi. Ƴar ƙarar azaba ta saki tana faɗin, “Mugu kawai, ALLAH zai sakamin”. Bai kulata ba ya kwance mata idanunta da hannunta suma. Wani irin farin cikine ya saukar mata a rai ganinta a ƙofar gidansu. Tana zumuɗin fita ya dakatar da ita.
      “Malam ɗauki akwatinki ki wuce da shi”.
     Juyiwa tai da sauri tana kallonsa batare da ta saki handle ɗin ƙofarba. “Bansan kallo, ki ɗau akwatinki nace”.
          “Minene abin kallo a jikin naka banda baƙin hali da zalunci. Ni dai nasan banbar gidanmu da akwati ba mizaisa kuma na ɗauka na shiga da shi...”
        “K!!!” ya daka mata tsawa a fusace. Hakan ya sakata dakatawa daga ƙoƙarin sake buɗe ƙofar ta juya tana watsa masa harara da manyan fararen idanunta masu yalwar gashi. “Minene namin tsawa malam?”. Maimakon ya bata amsa sai ya ɗaga mata yatsun hanunsa biyu dake a cikin safa yana faɗin, “Kinada zaɓi biyu. Koki ɗauka akwatin nan kokuma wlhy na maidake inda muka fito, kuma wannan tafiyar itace zata zamemiki ta har abada keda gida”.
     Kafinma ya rufe baki ta miƙa hannu baya ta sungumi ƙaramin akwatinta ruwan hoda mai ƙyau. Batare data sake jira yace uffan ba ta buɗe murfin motar ta fice abinta.

         
          Sosai gaban baba malam ya faɗi, yabi Nu'aymah dake jan akwati zata shiga gida da kallo harta tura ƙofar ta shiga, kafin ya maido dubansa ga motar data ajiyeta. Akan idonsa mai motar yay reverse yabar anguwar.
    Duk yanda yaso danne ransa suci gaba da magana da Alhaji Mani hakan ya gagara. sai kawai yay masa sallama akan yayi haƙuri anjima zasu ƙarasa maganar.
       Da mamaki Alhaji Mani yabi baba malam da shi harya shige gida da kallo.. Ya ɗanyi shiru alamar tunani. Ganin bai hasaso komaiba sai kawai ya girgiza kai shima ya juya ya shiga nasa gidan da masallaci ya raba tsakaninsu da nasu Baba malam.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

__________________
__________________

             Nu'aymah na isa tsakiyar gidan ta yadda akwatin ta kwasa da gudu zuwa ciki tana ƙwala kiran sunan Umm da Hajjo, dan gani takema tafiyar ɓata mata lokaci takeyi na isa garesu.
        Ba Umm da Hajjo kaɗaiba kowa ma na gidan sai da ya fito, yaran ne kawai da suka wuce islamiyya babu. Samarinma yawancinsu sun dawo daga wajen aiki da makaranta ga waɗanda ke jami'a.
         Wani irin tsalle Nu'aymah tai ta ɗane wuyan Umm dake tsaye a ƙofar sashenta tamkar wata gunki. Hakan yayi dai-dai da shigowar Baba malam gidan a matuƙar fusace.
         “K!! Nu'aymah! K!! Nu'aymah kina ina?”. Baba malam dake shigowa tun daga gate ya fara kwala ma sunanta kira kamar zai haɗiye harshensa.
       Da sauri Nu'aymah ta saki Umm jikinta na wani irin rawa, dan abin yazo mata a yanda batai zatonsa ba. Akwatinta dake yashe a ƙasa ya shura da ƙafa yana faɗin, “Zoki ɗauka ki koma inda kika fito kafin harshena ya furta miki abinda har ki ƙare rayuwarki zai zame miki musiba”.
        Idanu sosai Nu'aymah ta zaro waje jikinta na sake ɗaukar tsuma. Muryarta na rawar fitar kuka tace, “Abba......” Katseta yay a tsawace yana nuna mata hanya da yatsansa. 
     Ba'ita mai laifin kawai ba, kowama yayi tsuru-tsuru a gidan hatta dasu Abba Rudwan sun kasa magana, dan sunsan ran yayan nasu a matuƙar ɓace yake. Hajjo ce kawai zata iya sakashi ko hanashi a irin wannan yanayin. Gashi kuma bata fitoba, ƙila wanka takeyi.
        “Ba dake nake magana ba ne?!!”.
Fashewa da kuka Nu'aymah tayi ta durƙushe ƙasa. “Abbah wajen waɗanda suka sacenin kakeson na koma?”. Tsaki yaja mai ƙarfi, dan yama ɗauka maganarta raini da iya shege.
          “Lallai Nu'aymah kin girma! Ashe wayonki da iya tsara abubuwa har ya kai haka ƙarfi? Ki sanar mana kinbi saurayi saboda kar a aura miki Abdallah sannan ki dawo mana da wani sabon rainin wayon saceki akayi?. To idan saceki akayi uban wanene ya rubuta saƙwannin da kika barmana? Wanene kuma ya sacekin? Wanda naga ya ajiyeki yanzu shima wanene?. Duk sai ki bamu waɗanan amsoshin muna saurarenki?”.
       Kai Nu'aymah ta shiga girgizawa tana hawaye. “Wlhy Abbah bansan komaiba akai. Bansan su wanene ba? Bansan wanene wanda ya ajiyeninba nima? Sannan ban ajiye saƙon komaiba ga kowa wlhy”.
       “Nu'aymah!!!”. A tsananin tsawace baba malam ya kira sunanta. Sai da hantar cikin kowa ta kaɗa da tsawarsa. Itama tai baya ƙasa wanwar jikinta na ɓari na tsabagen tsorata. Dan bata taɓa ganin fushin mahaifinta irin hakaba duk da tasan yanada zuciya.
           Nufarta yay tamkar wani mayunwacin zaki, sai famar huci yakeyi jikinsa na tsuma.
      Da sauri Abban Abdallah da Abba Mustapha suka sha gabansa yana gab da isa ga Nu'aymahn. Kareta sukayi yanda bazai ko iya ganinta ba balle ya taɓata.
         Sake ɓaci ransa yay, ya kallesu da jajayen idanunsa da ƙwalla suka taru a ciki. kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa, ya juya zai zagayesu ya damƙeta.
      Caraf aka riƙe masa hannu. Dan haka ya tsaya cak batare da ya shiryaba. Hajjo data fito yanzun nan saboda tsawarsa da taji ta kalli hannunsa data riƙe da tana sake tamke fuska batare da tayi magana ba.
        A take dukkanin jikinsa yay sanyi laƙwas, sai wata irin zufa data shiga tsatstsafo masa a goshi. Sun kai kusan mintuna biyar a haka ana kallon kallo tsakanin duka ƴan gidanma. yayinda Umm tunda Baba malam ya shigo ta sulale ta koma ciki tana hawaye. 
         Da idanu Hajjo tai masa magana da yaren da tun yana yaro ya haddace sa, kafin ta saki hannunsa a hankali ta nufi Nu'aymah dake durƙushe ƙasa tana kuka har yanzun. su Abbah zagaye da ita suma har yanzun suna bata kariya daga baba malam. Kamata hajjo tai ta miƙar da ita ta rungumeta a jikinta. Nu'aymah ta ƙanƙame Hajjo sosai tana jan numfashi da ƙyar. A hankali kuma sai idanunta suka fara lumshewa, kafin kowa ya farga tama sume.
         Hajjo da taji ta mata nauyi tai ƙoƙarin ɗagota amma ta kasa. Gabantane ya faɗi tace, “Kai Mustapha zoku duba yarinyarnan kamarma bata da rai”.
      Ai kafinma ta rufe baki sun kama Nu'aymah da hanzari. Yaraf tai baya jikin Abban Adawiya alamar dai da gaske bata numfashin. Sake tashi hankalin kowa yayi, duk sauranma suka matso suna ambaton Innalillahi....
      Ɗaukarta Abban su Adawiya yay ya nufi sashen Hajjo sauran biye da shi. Yana kwantar da ita bisa kujera Ahmad na miƙo ruwa daya ciro a fridge. Amsa Abban su Abdallah yay ya zuba a hannu sannan ya shafama Nu'aymah a fuska. Ko motsi bataiba balle ai tunanin farfaɗowar ta. Sake tashi hankalinsu yayi. Ahmad da Malam ƙarami suka durƙusa da saurin kama ƙafafunta suna murzawa, suma su Abba hannayen Nu'aymah suketa faman murzawa. Amma abin tashin hankali ko motsi bataiba har lokacin.
          A yanzu kam kowa ya fara tunanin ciwon Nu'aymahr ne ya motsa, dan haka Abba Musbahu da bai jima da shigowa gidanba yay saurin faɗin, “Inaga a kira Doctor ɗinta, kamarfa ciwontane ya motsa”.
        Cikin kuka Hajjo tace, “Kirashi Musbahu, dan ALLAH ka kirashi da sauri. Innalillahi......... Zainabu karki mutu ki barmu kinji”. Kukan Hajjo ba ƙaramin sake ɗaga hankalinsu yayiba, matan ma sai faman share hawaye sukeyi.

        Duk abinda ke faruwa akan idanun Baba malam ne dake tsaye a jikin daga ƙofar falon Hajjo yana kallonsu. Kallo ɗaya zakai masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali. Nu'aymah zuciyarsa ce, yana dannewa ne kawai, amma bazai yuwu ya bari son da yake mata ya hanashi hukuntata akan kuskurenta ba, dan yasan icce tun yana ɗanye ake tanƙwarashi, idan ya bushe karyewa yakeyi.

      Sun cigaba da ƙoƙarin ganin ta farfaɗo kafin Doctor ya iso, sai dai fa ko motsi babu wani sashe na jikinta dake nuna alamar zaiyi ma...........✍
      

Tashin hankali😪, kumuje zuwa.


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

No. 9

.................Sosai Adawiya ta tsorata da mugun kallon da Abdallah ke jifanta da shi. Jan jikinta ta farayi baya a hankali ganin ya fara takowa yana nufota. “Y...y..Yah Ab wlhy babu abinda nayi da wayarka, Please dan ALLAH karka dak......”
     Ta kasa ƙarasawa saboda kiran wayar da akayi. Shima cak ya tsaya daga bin nata yana kallon wayar. (Sweet Momy) ya hango ɓaro-ɓaro yana yawo akan fuskar wayar kamar yanda yay saving. Iska mai zafi ya busar daga bakinsa yana lumshe idonu. Tsinkewa wayar tayi aka sake kira. Yanda bai motsaba haka ma Adawiya ta kasa motsawa. Kallon wayar take kawai daga nesa tamkar yanda yake kallonta shima. Sai ka ɗauka gamo sukai da bomb.
      Sai da Momy ta jera ma Abdallah kira har biyar bai ɗaga ko guda ɗaya ba a ciki. Daga ƙarshema saiya nufi wayar a fusace ya takata da ƙafarsa. A take screen ɗin ya shiga bada sautin fashewa.
        Baya Adawiya tai da sauri tana mugun waro idanu da buɗe bakin mamaki. Al'amarin bai ƙara firgitataba sai da taga ya ɗauka wayar ya zare sim card ɗin ya karyashi biyu. ya kuma nufi toilet ya jefashi yay flushing a take.
     Da sauri Adawiya ta koma inda take da ta tsaya zuciyarta na mata wani masifar bugu, ga wani irin tsoron Abdallah daya sake shigarta mai ƙarfi. Sam batai tunanin yanada zuciya irin hakaba. Duk da tasan ƴan gidansu kowa yanada wannan shegen zuciyar amma tazata tashi mai sauƙice ganin yanda bata cika ganin fushinsa ba. Ta gabanta yazo ya fice ko kallon inda take bai sake yi ba. Ya bugo mata ƙofar da ƙarfi har saida ta zabura jikinta na karkarwa........

*_NIGERIA_*

             Cike da mamaki Momy ke kallon wayar tata tamkar idanunta zasu zubo ƙasa. A ranta take raya ‘To miya samu wayar Abdallah? Ta shiga bai ɗagaba, daga ƙarshema wayar ta jita a kashe’.
       “Momy lafiya?”. Omar daya shigo falon ya faɗa idanunsa akan Momy dake tsaye tana ta faman juya waya.
     Saurin ɗagowa tai ta kallesa, sai kuma cikin sanyin murya tace, “Omar yayanku ne wlhy, ya kirani bana kusa inaga ko cikin su Amal wani ya ɗaga, shine yanzu dana fito naga alamar ya kira an ɗaga saina kirashi. Amma har missed calls biyar na jera masa bai ɗaga minba, yanzu daga ƙarshema wayar a kashe take”.
        Murmushi Omar yayi yana zama da faɗin, “Oh Momy ƙila to baya kusa ne, kinsan hidimar Yah Abdallah ba ƙarewa takeba. Nasan zai kiraki shima”.
       Kai Momy ta girgiza masa, “Omar ba rashin ɗaga kiran bane damuwata, jin wayar a kashe bayan kuma duka kiran danai sun shiga”.
       “Momy Please ki kwantar da hankalinki, nasan insha ALLAH babu wata damuwa. Koma baida cajine kokuma network”.
    Kamar zata sake magana sai kuma tai shiru taɗan jinjina kanta. Tashi tai ta maida wayar a caji dan fama cajin ta saka ta shiga kitchen tun ɗazun. Yanzuma tana maida wayar a caji saita koma kitchen ɗin suka cigaba da aiki ita da masu aikinta su biyu tabar Omar daya kwanta cikin kujera yana canja chennal a falon. Sai dai kuma abin yaƙi barin ranta sam.

        Har dare Momy na jiran kiran Abdallah shiru, ta kuma sake nemansa itama amma har lokacin wayar switch up. Tun tana danne damuwarta harta bayyana fili. Abbah da tun ɗazun yake kula da yanayinta ya tambayeta ko lafiya?. Batai nauyin bakiba tai masa bayanin abinda ya faru.
     Shi dariyama ta bashi ganin yanda duk tai wani iri kamar ance Abdallahn ya rasu ne, dan haka yaɗan murmusa yana girgiza kansa, batare da ya ce mata komaiba ya cigaba dacin tuwonsa. 
        “Abban Abdallah dan ALLAH ko zaka kira min shi da wayarka?”. Sake kallonta yayi da ƙyau, sai kuma yay gyaran murya da ɗauke idonsa. “Khadija ki rage ruɗiyarnan taki, yanzu dan ALLAH Abdallah ƙaramin yarone halan? Maybe baida caji ne kokuma ya shiga wata sabgar. Kiyi haƙuri kiga zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu idan bai kiraki ba”.
       A sanyaye tace masa “to” kawai badan hakan ya mata daɗiba. Sai ma ta tattare kwanikan daya kammala cin abincin ta fice da su. Saida takai kitchen sannan ta nufi ɗakin su Amal. Zaune ta iskesu suna karatu, Amal na ƙarama su Imran. Duk shiru sukai suna kallonta. Itama kallon nasu takeyi.
      “Amal wanene a cikinku ya ɗaga kiran yayanku ɗazun?”.
      “Kira kuma Momy? Wlhy bansan Yayah ya kira wayabama ni, dan tun ɗazun danace miki zanje na sake duba Nu'aymah ina can wajenta ɓangaren Hajjo ni da Yusrah. Amma wani abune ya faru?”. Kai momy ta girgiza mata tana kallon su Imran suma. Da ɗai-ɗai suka shiga bata amsar suma duk basu baneba.
     Kanta taɗan dafe zuciyarta na neman faɗawa a ruɗani, lallai yaran sunada gaskiya, dan idanma tai dubi da lokacin da Abdallah ya kira ai duk basa gidan ma suna islamiyya. Kasancewar yau lahadi sunayin harta safe zuwa uku a tashesu, to indai suna garin suma yaran suna zuwa anan ma. Kuma tunda safen duk suka fita. Amal ce kawai batajeba saboda ta tashi da ciwon mara, daya ɗaga matane tace zataje ta duba Nu'aymah. Sai da ta fita da kusan awa ɗaya ma Abdallah ya kira.
      Ficewa tai taja musu ƙofar tanason tunano ko wani ya shigo a wannan lokacin, to amma kuma babu wanda ya shigo ɗin, daga ita sai ƴan aikinta. Abba ma baya nan, Omar ma ganin datai masa bayan kiranne ya shigo gidan, dan tare suka fita da baba malam tunda safe.

              Momy da taga tunaninta na kaita wasu nazari daban sai kawai ta ajiyesa gefe, ta barsa akan uzirine yayma Abdallah yawa. Waya kuma ƙila sanda yake kira cikin sauran ƙannensa yaran gidan wani ya shigo ya gani ya ɗaga. 
     Washe gari da safe batabi takan kiran Abdallah ba ta cigaba da hidimominta kamar yanda ta saba. Abin mamaki kuma har dare bai kirantanba, sai itace dai da dauriyanta ya gaza ta nemesa kusan taƙwas na dare. Switch up dai ɗin yauma.
            Ganin yanda ta zuba tagumi yasa Abba jin tausayinta. Wayarsa yasa ya kira Abdallahn, amma sai yaji layin a rufe. maida kiran yay a ɗayar Number Abdallah ta business. Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Bayan sun gaisa yace masa ga Momy.
       Jimmm Abdallah yay kamar bazaice komaiba, sai da Abbah yace, “Nace ga Momynku ko bakajiba?”.
         “Amm sorry Abbah network ne, bata to”.
      Miƙama Momy Abbah yayi, ta amsa zuciyarta na mata sanyi, dan tana matuƙar ƙaunar Abdallah sosai a cikin ƴaƴanta, sai dai tana ƙoƙarin dannewa gudun saka ruɗani a tsakanin ƴaƴanta.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________

            Da ƙyar Abdallah ya danne zuciyarsa ya gaida Momy da fuskarta ke shimfiɗe da murmushin farin cikin jinsa. Ta amsa masa cike da kulawa tana tambayarsa yaya suke? Ina Adawiya?.
           Muryarsa a ɗan cinkushe yace tayi barci, shima shirin kwanciya yakeyi.
           “To Alhmdllh tunda dai lafiya kuke. amma jiya miya samu wayarkane? Na kira har sau biyar baka ɗaga ba, daga baya kuma saima naji switch up”.
           Ba ƙaramin haushine ya kama Abdallah ba dajin maganar Momy, bayan sharaɗin data gindaya masa mai ƙarfi akan abinda yake tsananin so shine kuma zata kirasa?, yanzu kuma dan taga tana kusa da Abbah take nuna kamar batai komaiba. To mizata faɗa masa bayan wanda ta faɗa masan kuma?............ 
       “Abdallah lafiya kuwa?”. Momy ta katse masa tunani. “Babu komai Momy, wayarce ta faɗi a cikin ruwa bayan mungama waya jiya shiyyasa”.
         “Abdallah ai ni bamuyi way.......”
Zare wayar Abba yay daga kunnen Momy yana faɗin, “Haba Khadijah tunda kinji lafiyar tasu ya isa haka. Bakiga dare yayiba ne? Yanzu kuma Abdallah yanada iyali”.
          “Afuwan Abban Abdallah na shafa'ane wlhy. Ni saima naji muryarsa kamar wanda bayajin daɗi”.
      Kallonta Abba yay sosai, sai kuma ya matsota jikinsa ya gwargwaɗa mata magana a kunnenta. Idanu ta ɗan zaro waje, sai kuma tai saurin miƙewa tana kare fuska da hannu alamar maganar tasa ta bata kunya.
     Murmushi Abba yay yana binta da kallo harta shige toilet. Yaɗan girgiza kansa yana gyara kwanciyarsa.

________________

          Jikin Nu'aymah yayi sauƙi sosai Alhmdllh, sai dai har yanzu bata koma sashensu ba tana sashen hajjo. Tana dai zuwa ta gaishesu da safe, ta kuma taya Umm aiki kamar yanda aka horesu. Babu wanda yay mata maganar Yah Ab a gidan, itama tayi ƙoƙari ta danne tana jira taji daga garesu kamar yanda Yusrah ta bata shawara data dameta da tambayar yanda akayi.

       Kwana biyu da samun lafiyar Nu'aymah su Momy sukai shirin komawa Abuja saboda karatun yara. A wannan karon Nu'aymah jitai batason tafiyar su Yusrah da Amal, dan suna ɗauke mata kewar Adawiya sosai. Tasan kuma idan suka wuce zata koma ita kaɗaine babu wani abokin ƙiriniyarta kamarsu a gidan, daga yayu sai ƙanne sai iyaye.
        Babu yanda ta iya, a washe gari su Amal suka fara wucewa Lagos da safe. Da yamma kuma su Yusrah. Nu'aymah harda hawaye. Hajjo da taji tausayinta har tayi tunanin ko Nu'aymah tabi cikinsu Yusrahn, sai kuma ta tuna ashe akwai shirin zuwa ganin Doctor da sukeyi. Zama tayi taita lallashinta harta saki jikinta, yayinda su Hajarah da sukazo sashen Hajjon suka ɗan rage mata kewar tafiyarsu Amal ɗin.

★★★★★★

           Kwanaki sun shuɗa, jikin Nu'aymah yayi garas, gidan ya koma kamar da sai su kaɗai. itama harma ta tattara ta koma ɗakinsu ita da Adawiya dake a sashensu. Sosai takejin kewar Adawiya, musamman ma idan tazo kwanciya ko zata shiga toilet. Dan ƙa'idane kullum sai sunyi faɗa akan bargo da filos, hakama shiga wanka sai sunyi faɗa. Haka sabo yake turken wawane.
       A yanzun kam sai Muhammad ƙaninta ya zame mata abokin hira. Daya dawo makaranta koda yaushe suna tare, duk da dai ta dage wajen maida hankali a karatunta na islamiyya itama. Dan a ɗan tsakanin nan ba ƙaramin ƙoƙari takeyi akan haddar Qur'aninta ba. Ga sauran littatafai ta dage sosai suma.
      Wannan karatun shine ya ɗauketa busy matuƙa. Tunma rashin sakewar da su Umm suke mata yanzu yana damunta har abin ya fara raguwar mata a rai. Dan tasha tambayar Umm ɗin kota musu wani laifine?. amma sai Umm ta shashantar da zancen taƙi bata amsa, haka shima Baba malam baya cemata komai akan hakan. A yaran gidan ma duk wanda taima tambayar ina Adawiya taje? Sai suce mata makaranta, Yah Ab kuma ya koma Saudia.
      Takanyi shiru taita tunanin miyasa  za'akai Adawiya makaranta ita kaɗai a barta? Bayan kuma tunda suka taso komai tare sukeyi, makaranta da komai da komai tare ake sakasu, kuma tare ake musu komai. Wannan tafiya makaranta da taji na Adawiya saida ya sakata kuka, daga ƙarshe ta haƙura da fatan ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Tana kewar Yah Ab sosai a zahiri da baɗini. Gashi yanzu bata da waya, ta kuma kasa aron ta wani ta kirashi koda ta Umm ce. Dan da idan tanason suyi magana wayarta babu caji data Umm take amfani. Shima daya kira yaji bai sametaba zai kira Hajjo ko Umm a bata. Amma a wannan karon ganin shima ko sau ɗaya bai nemeta ba sai al'amatin ke ɗaure kanta da bata mamaki. Da taga dai zuciyarta na neman ƙuntata sosai sai taje ta tsare Hajjo da tambaya tana kuka.
       Hankalin Hajjo ya tashi sosai. Ta zauna tana lallashinta amma Nu'aymah sai taƙi saurarenta. Tana cikin darzar kukan Baba malam ya shigo sashen hajjon da daddare bayan ya taso daga wajen karatu a massallaci.
         Tsawa yayma Nu'aymah amma ba wadda zata sakata firgitaba. Tai saurin nutsuwa hawaye na sake rige-rigen sakko mata a kumatu.
       “K wai kin koma jaririyane a gidan nan yanzu? Da zaki zauna kitama mutane kukan banza da wofi. Ki fita idanuna Nu'aymah tunkan na saɓa miki. Bake kika zaɓama kanki hakanba da kanki? To daga yau na baki sati biyu kima shi wanda kika gudu dominsa magana ya turo iyayensa”.
         Cikin tashin hankali Nu'aymah ke kallon Baba malam. Bakinta na rawa tace, “Abbah wlhy ban guduba, dan ALLAH ka saurareni na faɗa maka yanda akayi”. “Bana buƙatar jin komai daga gareki Nu'aymah, dan saƙwannin da kika bar mana sun isheni dukkan amsa. To kin samu yanda kikeso. Kinso tozartamu ALLAH kuma ya hana faruwar hakan ya rufa mana asiri. Abdallah ne dai kince baƙyaso, ALLAH kuma ya canja masa da waɗanda suka fiki alkairi, sai kima wanda kikeson magana ya fito a aura masa ke kuje ku ƙarata”.
      “A....Ab....Abbah!” ta kira sunan Baba malam bakinta na rawa da jikinta. Sosai kalamansa suka nema zautata. ‘Yah Ab ɗinta ne yay aure da wata ba itaba?. Kai ina bazai yuwuba ma’. Tai maganar a fili tana kallon Hajjo dan baba malam tuni yay ficewarsa ma.
      Kamota Hajjo tayi ta rungume tana lallashinta. Tausayinta na ratsata. “Hajjo dan girman ALLAH kimin bayani, wlhy na kasa fahimtar kalaman Abbah gaba ɗaya. Da gaske yake Yah Ab yayi aure? Ya auri wata ba ni Nu'aymah ba?. Hajjo faɗamin dan ALLAH, taimakeni ki faɗain dan girman ALLAH hajjo”.
          “Ya isa haka Zainabu. Ki nutsu na miki bayanin komai to kinji”.
     Da sauri Nu'aymah ta shiga ɗaga mata kai tana share hawayenta da hannaye biyu. Hajjo ta ruƙo hanun nata, cikin nutsuwa tai mata bayanin komai daya faru a ranar bayan an wayi gari babu ita a gidan. Saƙwannin data ajiye musu akan ita ta tafi batason Abdallah sai Ameer.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________

                 “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Mike shirin faruwa dani ni Nu'aymah? Hajjo wlhy kinji na rantse miki bani nabar saƙon nanba. Kuma Ameer da ake magana akansa ni babu abinda ya taɓa haɗani da shi sai sako da Yah Abdallah ke bashi yana kawomin. Rabon kuma dana sake ganinsa wlhy anfi wata huɗu Hajjo”.
        “Ah ah! To amma shi kuma Abdullahin yace bai san Ameer ɗinba, bai kuma taɓa aiko wani wajenki ba sai Ahmadu”.
           “Bai taɓa ba Hajjo? Shi Yah Ab ɗin da kansa yace haka kuma?”.
          “Sosaima kuwa, a gaban kowama ya faɗa a randa al'amarin ya faru. Amma kwantar da hankalinki, Zainabu nima dai al'amarin nan ya ɗaure min kai matuƙa, yanda nasan kike da Abdullahi tayaya zaki aikata wannan abun? To amma iyayenki duk sun kasa fahimtar akwai wani ɓoyayyen al'amari daya faru a wannan ranar, musamman ma ɗan malam daya ɗauki zafi sosai akan al'amarin”.
         “Hajjo dan ALLAH ki taimakeni, wlhy inason Yah Abdallah fiye da yanda kowa yake tunani, dan ALLAH ku tausaya mani karna rasashi hajjo. Idan na rasashi mutuwa zanyi......”
        “Bazaki mutuba Zainabu kinji, ki kwantar da hankalinki muyita addu'a ALLAH na nan, yana sane da komai kuma shine maiyin maganin komai”.
       Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajjo dake share mata hawaye, ta kwantar da kanta a jikinta saboda kanta dake wani irin bala'in sara mata kamar zai tsage. “Hajjo kaina”. Hankalin hajjo ne ya sake tashi, dan sam ba'ason ciwon kai ga Nu'aymahr, daboda ciwonta. Saurin tada ita tayi daga jikinta ta kwantar da a kujerar tana faɗin, “Ina zuwa, bara na amso miki maganinki kisha”. 
        Hajjo da kanta ta nufi sashen su Nu'aymah dan yaran duk basu shigoba daga ita sai Nu'aymah ne kawai. Baba malam da Umm suna zaune a falo ta shigo, Muhammad na gefe yana homework.
        Da sauri suka shiga tambayarta ko akwai abinda take buƙata?. Fuskarta babu ko ɗigon walwala tace su bata maganin Nu'aymah kanta ke ciwo. Ba ƙaramin faɗuwa gaban Umm yayi ba, amma saita danne ta tashi taje ɗakin Nu'aymahn ta ɗakko ɗan box ɗin da magungunanta ke a ciki ta kawoma Hajjo. Tanason taje taga mike faruwa da ɗiyar tata amma tanajin nauyin hakan. Ga baba malam yay kamar abin bai damesabama, ya cigaba da shan fruit salad ɗinsa hankali a kwance.
     Hajjo dai batabi takansuba ta amsa tai ficewarta. Da kanta ta bama Nu'aymah maganin, sannan ta kamata ta kaita bedroom ɗinta ta kwantar. Cikin amincin ALLAH babu jimawa barci yay gaba da ita.

          Washe gari da zazzaɓi Nu'aymah ta tashi ga ciwon kai. abinda ya tada musu hankali Doctor ɗinta yayi tafiyar da yace, gashi kuma basu nema wancan likitanba. Andai kaita asibiti wani likitan daban ya dubata, yaɗan mata abinda zai iya ya turasu asibitin dawanau. Kamar koda yaushe Baba malam yaƙi yarda a kai Nu'aymah dawanau, dan acewarsa yarinyarsa ba ciwon hauka take ba. Yasan dai ance tanada matsala a ƙwaƙwalwa. Hakan yasa ya ɗakko file ɗin Nu'aymah da shirin neman wancan Doctor ɗin. Amma abin mamaki da al'ajabi babu takardar da Numbers ɗin take. Anyi ɗai-ɗai da file ɗin babu ko alamar takardar. Kamar wasa aka bincike littatafan baba malam dake tare da file ɗin tas babu takardar dai.
     Wannan al'amari ba ƙaramin ɗaure kan kowa yayiba a gidan. Musamman da ya zam agaban kowa Doctor ya bada takardar da file ɗin. Wannan al'amari ya sake ɓata ran baba malam matuƙa, amma jarumar fuskarsa taƙi nuna hakan. Sai Hajjo ce keta masifa kamar zata haɗiye harshenta. Dan wannan ɗauke takardar ya sake tabbatar mata da akwai mai yin ƙulle-ƙulle a gidan da gaske. Sai dai yanda kowa ya nuna damuwarsa akan al'amarin baka isa nuna zarginka kai tsaye akan wane ne ɗin ba.

_____★_____

               “Maganar gaskiya al'amarin gidannan ya fara bani tsoro Abban Nu'aymah. Anfa daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, dolene a wannan karon nasan wanene ke mana SARAN ƁOYE. Tunda har aka iya toshe hanyar neman lafiyar Nu'aymah lallai za'a iya kashe mana ita ma”. Umm tai maganar hawaye na zuba mata masu zafi.
          Zama baba malam daketa kai kawo a ɗakin yay kusa da Umm, ya kafeta da idanunsa da sukai jajur shima saboda damuwa. “Jannat idan munce zamu ɗauki mataki, akanwa zamu ɗauka? Akan kuma mi?”.
       “Amma Abbah Nu'aymah karka manta musabbabin ciwon Nu'aymah fa faɗo da ita akai daga kan gado tun tana jaririya, kanta ya bugu ta samu ciwo a ƙwaƙwalwa. Badan ALLAH ya taƙaita wahalaba da zata tashine cikin halin rashin hankali kamar yanda Doctor ya sanar mana. Addu'a da hikimar UBANGIJI ce ta cigaba da jagorancin lafiyar Nu'aymah hartakai wannan lokacin cikin hankalinta, sai dai idan ciwon ya motsa tasha wahala. Tun Nu'aymah batasan ma'anar magani ba ake ɗura matashi a ciki, kanaji kwanaki badan ALLAH yasa Doctor ya farga ba hantarta fa harta harbu da ciwo saboda yawan shan magani. Abban Nu'aymah baka tunanin game da al'amarin aurenan akwai wani abu da bamu hasasoba kuwa?”.
           “Kiyi haƙuri Jannat karmu zargi kowa akan al'amuranmu, mu daure mucigaba da ɗaukar komai akan jarabawa ne. Duk abinda yay farko nasan zaiyi ƙarshe. Da ALLAH na dogara game da lafiyar Nu'aymah nasan kuma shi mai jine mai kuma ganine. Indai bamu da haƙƙin kowa ALLAH bazai bama kowa damar shiga haƙƙinmu ba. Ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU zan sake samo Number likitan nata, dan mantawama nai nace masa idan ya tafi ya kiramu”.
           Kanta ta jinjina masa hawaye na cigaba da sauka mata. Ya saka hannu ya share mata yana murmushin da shima iyakarsa laɓɓansa ne kawai. Shi kaɗai yasan mi yakeji a ransa. Yana dai ƙoƙarin dannewane dan yasamu Umm ta kwantar da nata hankalin kodan hawan jininta............✍


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

No. 11
________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* 

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

___________________

   ................Kamar bazata juyaba sai zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncine shiɗin, 
       Abun mamaki babu kowa a wajen,  sai dai an sauke glass ɗin motar kaɗan alamar tanan koma wanene ya isar da saƙon nashi. Jitai zuciyarta ta sake hawa sama fiye da da. Ta yunƙura da nufin nufar motar gayun nan suka sake mata zobe. Kallonsu tai sama da ƙasa a wulaƙance da faɗin, “Wlhy idan baku matsamin ba ɗaya bayan ɗaya saina muku fashin goshi da dutsen nan”.
    Babu wanda ya motsa a cikinsu, da alama ma basa fahimtar yaren datai maganar, dan kallonta kawai suke tamkar wasu zakaru. Dutsenta da har yanzu ke a hannu ta sake ɗagawa zata bugama wani again. Da sauri yay baya da ɗana kunamar bindigarsa yana huci. Nu'aymah ta taɓe baki tamkar bata fahimci abinda yake shirin yiba, ta sake ɗaga dutsenta ta makama na gefen hannun haggunta a goshi cikin rashin tsamanin hakan daga garesa.
     Ƙara ya saki da duƙewa ƙasa bindigarsa na faɗuwa dan abun yazo masa a bazata, babu yanda za'ay kai tunanin shiɗin zata bugamawa. Ƙafa ɗaya daga ciki ya saka ya taɗeta tai baya zata faɗi cikin security ɗin gidan marayun da suka iso yanzun wajen yay saurin tareta. Ai tanajin bata kai ƙasaba tai wani irin ɗagowa da sauri ta wulwula dutsin nata sai akan motarnan dai ta ɗazun data fasama glass, kuma a gaba ya sauka, dan haka glass ɗin ya ƙara tsatstsagewa fiye da ɗazun.
         A yanzunkam bodyguards ɗinsa sun tabbatar bazasu iya haƙura da tsagerancin yarinyarnanba, sai sun ɗauki mataki duk da ogansu bai basu damar yin hakan ba. Hannu ɗaya daga ciki ya ɗaga zai kwasheta da mari iya ƙarfinsa, sai dai ganin za'a buɗe ƙofar motar ne ya sakashi dakatawa da nufar motar da sauri ya ƙarasa buɗewa yana saurin cewa, “Sorry Sir”..
           Banji an amsashi ba, sai dai motsin da naga anyi daga cikin motar ya bani tabbacin wanda ke a ciki zai fitone. Ba Nu'aymah kaɗai ba, harsu Yusrah sun zuba idone suga mai fitowar.
        Ƙafarsa dake cikin baƙin takalmi mai shegen ƙyau ta fara bayyana, kafin farin wandonsa. A hankali ya dire sandarsa ƙasa itama tare da ɗayar ƙafarsa ya fito gaba ɗayansa. 
     Koni mai ɗaukar rahoto saida na furta ‘masha ALLAH’ a zuciyata. Zuƙar iskar yammaci data fara kaɗawa yay a hankali cikin hancinsa ya fesar yana sake tamke farar fuskarsa dake zagaye da baƙin gashin saje siɗik, dan a rayuwarsa ya tsani kallo. Baiko kalli ko sashen dasu Nu'aymah da guards ɗinsa sukeba ya nufi inda su Nanah suka rufu kan yaron tare da securitys ɗin gidan marayun. Hannun Malika dake a saitinsa ya kama ya matsar da ita gefe, hakanne ya sakasu farga da isowarsa duk suka dawo cikin hankalinsu daga kallon ƙurullar da suke masa. Baice dasu uffanba yay wani ɗan dirƙuson gayu gaban yaron tare da kai yatsunsa biyu saitin hancinsa, yakai kusan sakan goma kafin ya janye, sai kuma ya maida kan jijiyar wuyansa dake a saitin kunne. Nanma ya kwashe sakan goma da ɗoriya sannan ya ɗauke. Miƙewa yay tsaye, idanunsa dake cikin baƙin glasess akan ƙaton symbol ɗin da aka rubuta sunan gidan marayun, kafin ya janye ya maida dubansa ga guards ɗinsa da har yanzu suke zagaye da Nu'aymah kamar wata ɓarauniyarsu. Da hannu yay musu nunin su barta, tare da yin wani salo da yatsunsa biyu wanda shi da su ne kawai sukasan ma'anar yaran nasa.
    Cike da takaicin rashin ɗaukar mataki a kanta sukaja baya kowanne na zuba mata harara a ƙasan ido da huro hanci. Gaba ɗayansu garesa suka nufo. Ɗaya daga ciki ya matso sosai inda yake, A hankali ya furta maganar da babu wanda ya iya jinta a cikinsu Nu'aymah, dan kuwa jajayen laɓɓansa ne kawai suka motsa kaɗan.  Ganin haka ya saka Nu'aymah nufosu da sauri itama. Yana ɗaga ƙafarsa zai bar wajen tana isowa tasha gabansa.
      “Kai malam dakata mana! Shin babu zuciyane a ƙirjinka kokuwa kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?”.
        Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin glasess ɗinsa, batare da yama nuna alamar ya fahimci yaren da take maganar da shiba ya raɓata zai wuce abinsa. Hanzarin riƙo sandarsa tai ƙoƙarin yi Yusrah ta riƙeta. Cikin magana raɗa-raɗa tace, “Aymah calm down Please, kalla kiga”.
       Sai da ta zubama bayansa harara kafin ta kalli abinda Yusrah ke nuna mata. Securitys ɗin gidan marayun ne tare da guards ɗin nasa uku dasu Nanah ta hango harsun kusa shigewa cikin Orphanage ɗin ɗauke da yaron a hannun ɗaya daga cikin guards ɗinsa. Juyawa tai da sauri ta kalli inda yake shima sai ganin motocin uku tai har sunyi reverse suma da alama gidan marayun zasu shiga.
             “Zuciyarki tayi sanyi ko? Iya masifa! ALLAH wataran sai kinsa an maidamu kwalta Nu'aymah, jibesu tamkar wasu bajiman zakuna su da ogan nasu. Da ganinsu kasan ba hausawa baneba ma, ke koma tsoro baƙyaji”. 
        “Mtsoww! Ina ruwana da rashin kasancewarsu Hausawa, inda banyi musu hakanba ai guduwa zasuyi dan tsabar rashin sanin darajar ɗan adam. Ko dabba suka bige ai ta cancanci su fito suga lafiyarta balle mutum, shegu masu suffar baƙaƙen aljanu”.
      Dariya Yusrah ta kwashe da ita tana faɗin, “Amma dai banda wannan Handsome ogan nasu ko? Dan wlhy dai kam komai yaji zammm anan kema kin sani”.
        “Ke kikaga wannan”. Nu'aymah ta bata amsa tana fisge hannunta dake cikin na Yusrahn ta tsallaka titi ta barta tana dariya. Dan ta kula bori kawai Nu'aymah keyi itama tasan gayen ya haɗu masha ALLAH, sai dai yanayinsa sam bai mata kama dana Musulmai ba, dan askin kansa kawai da ƙaton sarƙan Cross na diamond dake a wuyansa, da ɗan kunne guda ɗaya manne a kunnensa ya isa amsar hakan a garesu.
      Hango Nu'aymah har zata shige cikin Orphanage ya sakata saurin tsallaka titin itama ganin babu mota tabi bayanta.

       Nu'aymah da har yanzu keta faman jan tsakin takaicin mutanen ta nufi clinic ɗin gidan kanta tsaye, tasan dai bazai wuce can suka nufa da yaron ba. Kasancewar tafiyar tata sai a hankali, ba wani sauri ta iyaba kuma akwai tazara tsakanin gate ɗinma da clinic ɗin saiga Yusrah harta isketa. A tare suka ƙarasa batare data kula Yusrah daketa son taga ta sakko ba. Tsaitsaye suka iske su Nanah a reception da guards ɗin mutumin, sai bah-bah hindatu ɗaya daga cikin masu kula da yaran, da kuma Abban Adawiya da ashe tun ɗazun yana a cikin gidan marayun su Nu'aymah basu saniba.
      Waige-waigen inda zataga gayen ta farayi, sai dai babu ko mai kama da shi a wajen. Wani takaicine ya sake dirar mata a zuciya, cikin ranta ta ayyana ‘Wato shi yamafi ƙarfin shigowa kenan? To ai idan yasan wata baisan wataba’. Ta nufi hanyar fita tana surutunta a zuciya.
     Yusrah da tunaninta ya bata Nu'aymah zata iya zuwa ta sakemusu ɓarna a motoci tai saurin riƙo hannunta tana faɗin, “Ina kuma zakije?”.
          “Yusrah sakeni, bakiga wannan mai shegen taurin kan bai biyosu ba”. “Oh ALLAH, to minene idan bai shigo ɗinba, baga guards ɗinsaba, nasan ai zasu wakilcesa. Ki tunafa ba shine ya buge yaron ba ma, cikin guards ɗin nasane tunda shi yana a motar tsakkiyane, sannan ba shinefa ke tuƙinba”.
         “Wannan matsalarsace kuma, ai wanda ya bige ɗin dai yaronsane ko? To ya zama dole shina ya kasance a wajen wlhy dan ya ja masa matsala”.
       Kafin Yusrah ta samu damar mata magana sai gashi ya fito daga ɗaya a cikin ɗakunan clinic ɗin, Dr Safwan biye da shi a baya, taku yake cike da nutsuwa irinta zaratan samari masuji da lokacin ƙuruciya da kwanciyar hankali. Handglop ɗin dake a hannunsa taga yana zarewa ya jefa cikin shara. Har yanzun dai idanun nasa a toshe suke da Google ɗin, kuma fuskar a tamke, tana ƙoƙarin janye idanunta daga kallon nasa caraf suka sauka bisa kan ƙatuwar sarƙar Cross ɗinsa da aɗazun masifa baisa ta ganta ba.
      Cikin suɓutar baki tace, “Ashe Arne ne shiyyasa baida imani”. 
     Karaf wannan magana a kunnensa. Sai dai yanza yazo ya gittata ya barta da ƙamshin turarensa mai sanyin daɗi batarr da ko kallon inda takeba ne, zaka fahimci da wahala ace yamaji mitace, maybe ma bayajin hausar sam. 
          Wajen Abbah dake zaune ya ƙarasa, suna ɗan nesa dasu kaɗan shiyyasa bazasu iya jin mi suke faɗa ba. Ta taɓe baki da nufar Dr Safwan tana tambayarsa yaya jikin yaron?.
       “Jikinsa Alhmdllh, ai bama wani ciwo yaji sosai ba, yadai bugune a kansa da hannunsa na haggu, insha ALLAH kuma fatan komai zaiyi normal da wuri”.
      Duk da taji daɗin hakan sai bataji ranta ya huce daga haushin mutuminda ita kanta shaidace tasan ba shine ya aikata laifin ba. ‘Amma kuma ai ogan wanda ya aikata ɗinne’ ta raya a cikin ranta cike da gamsuwa da jawabin zuciyarta.
         Ɗakin da yaron yake kwance suka nufa suka dubashi duk da ansa masa ruwa barci ya ɗaukesa. Lokacin da suka fito basu iske mutanenba har motocinsu. Hakan ya bama Nu'aymah tabbacin sun wuce kenan.
         Suma nufar hostel ɗin yaran sukai suna sake tattauna abinda ya faru, tare da yin gulmar mutumin dako sunansa basu saniba. Nu'aymah dai uffan bata cewa, dan ita takaicima suke ƙara mata a kanshi kawai.
        
                 

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________

        Tunda suka baro cikin Orphanage ɗin ya kwantar da kansa jikin kujera yay shiru idanunsa dake da cikar baƙin gashi da gira a sama suna a lumshe. Sai faman juya glasess ɗinsa dake a hannunsa na dama yake tamkar zai karyasa. Gaba ɗaya abinda ya farune ke dawo masa cikin zuciya daki-daki. Ya yarda yaran Arewan nan basajin magana tamkar yanda yakeji ana shan faɗa. Jibafa yanda ƴar yarinya ƙarama sa'ar ƙanwarsa Victoria ta tsaya agaban bindiga tana musu raini tamkar wasu sa'anninta. A karan farko yaja ƙaramin tsaki da furzar da iskar daya cika baki da ita yana maijin takaicin komai a ransa. A hankali ya buɗe idanunsa ya kai dubansa ga glass ɗin gaban motar tasa da Papansa yasa maƙudan kuɗi wajen siya masa. Yau shine hawansa na farko da motarma gaba ɗaya, dan sati biyu da suka wuce papa ya bashi ita a birthday ɗinsa matsayin gift. Amma sai gashi cikin sakanni an mata walmakalifatu, kamar Mom tasan hakan zai faru tace bata yarda yazo kano a mota ba daga Abuja, shi kuma gashi yanada uzirin da bazai yuwu ya fasa tafiyarba, dan dama zaibi jirgine kamar yanda ya saba sai akace jirgi bazai tashiba dan yanayi babu ƙyau yau. Shinefa ya zaɓi tahowa a mota duk da Mom bataso hakanba. Sake rumtse idanunsa yay da shegen ƙarfi da cije lip ɗinsa na ƙasa sosai tamkar zai hudashi da haƙori.
        Duk abinda ya keyi drivernsa na kula ta cikin mirror, hakanne ya saka zuciyarsa sake zafafa da abinda yarinyar tai musu shima, ya kai hannu ya shafa inda Nu'aymah tai masa rotse da dutse aka saka masa bandage, wlhy yau badan oga ya hanasu ba da yarinyarnan saidai uwarta ta haifa wata. Shiyyasa shifa a rayuwarsa yay mugun tsanar ƴan Arewa ɗin nan musamman hausawa, ƙauyawa dasu ko karatu basayi sai rashin mutunci. (Humm malam driver naka tunanin kenan, amma ƴan Arewa sun wuce da sanin duk wani gurɓataccen tunaninka ai🙄😏). Shi yanzu babban tashin hankalinsa ma mi zasuce da Madam ɗinsu akan wannan al'amarin daya faru?, dan kowa yasan yanda family ɗin gaba ɗaya ke masifar so da ƙaunar ogan nasu tamkar wani tsoka ɗaya a miya.
      Haka dai suka cigaba da tafiya kowa da abinda yake saƙawa a cikin rai. Gashi mahaukacin gudu sukeyi kai kace Lagos suka nufa ba Abuja ba.
       Tunda 6pm tayi kiran Mom ya fara shigowa a wayarsa, sai dai ko sau ɗaya bai amsa mataba ya share, sai ma kwanciya daya gyara cikin lallausar kujerar motar ya cigaba da latse-latsen laptop ɗinsa har yanzu da takaicin Nu'aymah a ransa.

*_ABUJA_*

          *_09:30pm_*  Dai-dai suka shiga garin Abuja saboda holdup daya riƙesu a madalla zuwa Kubwa expres, da ƙyar suka fita a jigace, dan kafin su iso Asokoro ji yay tamjar ya fasa ihu dan gajiya, shi dama can mutum ne da baida jimirin tafiya mai nisa a mota, duk da tafiye-tafiye sun kasance cikin ginshiƙin aikinsa kuwa.
         Anguwace da bata da maraba da a cikin turai saboda rashin hayaniya da haɗuwarta. Ko ina ƙwanyar yake da wutar nepa tamkar rana, duk da dare baiyi nisaba babu abinda kakeji sai haushin karnuka. Motocin uku suka tsaya dai-dai saitin wani ƙaton baƙin gate da zaka iya hango cikin gidan daga waje kasancewarsa tamkar net. Horn sukai, da gudu sai ga wani dake cikin Blue Uniform ya iso da sauri ya buɗe musu.
     Tunkan su gama dai-daita parking idanunsu suka sauka akan Madam Chioma dake ta faman kai kawo ta barandar saman bene. Sai dai ganin shigowar motocin tuni tabar wajen da alama zata fitone.
       Tuni Securitys ɗin gidan kusan su goma sha biyar suma sukayoma motar caaa. Buɗe masa akai da sauri, sai dai kafin ya fito Madam Chioma harta iso. Da kanta tasa hannu ta fiddosa a motar, tai saurin rungumesa tana magana cikin yarensu. “Yarona miya sameka? Ina kuka tsaya? Miyasa kaki ɗaga kiranmu?”. tashiga jero masa tambayoyin batare data bashi damar amsa ko guda ɗaya ba daga ciki. 
           “Relax Maa! i'm okay”. “Ka tabbatar?”. Ta faɗa tana ɗagosa daga jikinta hannayenta duka biyu akan kwantaccen sajensa tana shafawa, sai kuma tabi jikinsa da kallo daga sama har ƙasa. Ganinsa dai lafiya lau saita sake rungumesa tana faɗin, “Thanks God”.
           “Ɗan uwa sannu da zuwa”. Wata murya ta faɗa daga bayansu cikin harshen nasara. Sakinsa Madam Chioma tai suka juya suna kallon mai maganar. Matashin saurayine da bazai wuce 22years ba, sai kuma wasu dake bayansa su kusan bakwai. Kallonsu yay ɗaya bayan ɗaya kafin ya buɗe masu hannayensa sukazo duk suka rungumesa suma suna masa sannu da zuwan. Sai da duk suka gama sannan ya amsa musu da “Thanks you”. a jimlace.
      Har sun nufi babbar ƙofar shiga ainahin cikin gidan ɗaya daga cikin yaran cikin harshen turanci tace, “Jesus!! Miya faru da motarka Brother?!”.
     A tare duk suka juya suna kallon motar, amma banda shi dama yay gaba abinsa tamkar baiji mi Joy ɗin ta faɗa ba.
       Cike da firgici Madam Chioma ta shiga ƙwala kiran sunan guards ɗinsa ɗaya bayan ɗaya. Aiko jikinsu har rawa yake suka nufota ransu cike da tsoron amsar da zasu bata akan abinda sukasan dole su amsa tambayoyinsa dama.
          Aiko a jajjere ta shiga jero musu tambayoyin ko bari su bada amsa batayi. Sai da ɗaya a cikin yaran da zatama iya kai sa'ansa tace, “Mom ki shiru haka mana su bamu amsar miya faru?”. Zata sake magana budurwar tai saurin sake faɗin, “Please Mom”. Shiru tayi badan taso hakanba. Ta maida hankali ga guards ɗin da saima yanzune ta kula da masu fasashshen goshi biyu a cikinsu. Babban ne ya shiga mata bayanin duk abinda ya faru tsakanunsu dasu Nu'aymah daga farko har ƙarshe. A take takaici da baƙin ciki suka sake rufeta ta shiga zagin Hausawa da kiransu da sunaye marasa daɗin ji. Sai da tayi iya iyawarta kafin ta bar wajen tabi bayansa. Suma sauran yaran bayan nata sukabi suna zagi.

        Shikam yana shiga ƙaton babban falon gidan dake ɗauke da set ɗin kujeru biyu mabanbanta kala baiko tsaya ba yay saurin hayewa sama inda sashensa yake. Baya buƙatar kowa ya biyosa, dan haka yay saurin maida ƙofar corridor ɗin sashen nasa ya rufe, sannan ya ƙarasa nasa madaidaicin falon daya gama haɗuwa, yanata wani tattausan ƙamshi mai daɗin shaƙa da kwantar da zuciya. murza ma ƙifar falon key yayi sau biyu sannan ya shige. dispencer dake acan gefen dining mai ɗauke da madaidaicin d/table ya nufa, ya ɗauki glass cup dake cikin wani showglass mai ƙyau da ɗaukar hankali ya matsi ruwa. Tas ya shanye wanda ya ɗiban, ya ajiye kofin saman d/table ɗin ya baro wajen zuwa wata ƙofa dake a cikin falon. Nan ɗinma dai corridor ne, sai dai ƙofa biyu ce kawai a cikinsa, ƙofar ƙarshe ya nufa yana zame baƙar jacket ɗin jinsa tunkan ya buɗe. Ya riƙeta a hannu ɗaya sannan ya ƙarasa ya murda handle ɗin ƙofar ya tura ya shiga.
       Fes ɗakin yake shima, yanata tashin ƙamshin fresheners data haɗe da turaren da yake amfani da shi. Jefa jacket ɗin yay saman gadon ya ƙarasa gaban mirror yana ƙoƙarin cire sarƙar cross ɗin wuyansa. Ya ratayeta jikin wani ɗan hangar ƙarami mai ƙyau dake cike da sarƙoƙin kala-kala a  ajiye saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban madubin yanata faman yamutse fuska dan yunwa yakeji, sai da ya cire takalman ƙafarsa da safar, farar ƙafarsa dake fes ta bayyana kafin ya miƙe kansa tsaye ya nufi wata ƙofar da ko ba'a faɗaba kasan toilet ne.
     Yana shiga aka fara knocking ƙofar falonsa, amma sai ya share ya cigaba da abinda yake a ciki. Anyi kusan sau uku sannan aka bari. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe Milk color. Hannunsa riƙe da ƙaramin towel yana tsane sumar kansa da kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tana masifar lasar kuɗaɗe kodan ƙyawun da take dashi ga mai kallo a ido balle kuma wanda ya taɓa.
         “Yoohan! Buɗe min ƙofa”. Ya tsinkayo muryar Mom tana faɗa cikin yarensu da ɗan buga ƙofar yanda tasan bazai takurasa ba. Gefe ya karyar da wuyansa yana yamutsa fuska da yarfar da hannayensa duka alamar shifa an takura masa. Fuskarsa cike da takaici yaje ya buɗe mata tare da juyowa a binsa batare da ya tsaya saurarenta ba.
     Ƴar dariya tayi abinta, dan ko kaɗan hakan bai dametaba, tasan ya gajine matuƙa, shikuma idan ya gaji to lallai sannan baƙin ransa ke ƙara hauhawa, kowa kuma yimawa yakeyi har ita da Papa. Ƙarasawa tai inda yake tsaye a gaban mirror yana cigaba da tsane kansa. Kama hannunsa tai ta zaunar, ta amshi towel ɗin ta cigaba da goge masa kan tana kallonsa ta cikin mirror fuskarta washe da murmushi.
     Shiko ya ciskule tasa kamar zai fasa ihu. Sai da ta tsane masa kan tas kafin tajawo hand dryer ta jona a jikin soket ta fara busar masa da shi. Ajiye dryer ɗin tayi da jan hancinsa tana faɗin, “Nasan wannan fushin bana komai bane sai yunwa da gajiya my boy. Taso kaje kaci abinci ka kwanta ka huta”. Tai maganar da turanci
          Yana shirin miƙewa danya shirya akai knocking ƙofar, jiyay tamkar ya fasa ihu dan takaici, shiyyasa sam bayason zaman gidan nan wani lokacin, dan ana hanama rayuwarsa shaƙatawa da hutawa. A hakanma gwara nan, abinda yafi tsana shine zuwa ƙauyensu, dan anfi cika masa ciki da takaici acan fiyema da nan Abuja. Mom ce tai magana, shiko tuni ya miƙe ya koma wajen kayansa. Ɗaya daga cikin ƙannensa ce mai suna Victoria. Tarkacen kayansa ne daya bari a mota cikin guards nasa ya kawo tun ɗazun, shine yayta masa knocking lokacin daya shiga bayi, da yaji ba'a buɗeba ya koma dasu ya bama yaran akan idan ya fito saisu kawo masa.
          Zubesu tai akan table ɗin gaban gadon, ta juya garesa zatai magana ya ɗaga mata hannu da sauri tare da nuna mata ƙofar fita. Baki ta kumbura ta juya ta kalli Mom nasu dake murmushi sannan ta fice tana buga ƙafafu da ƙananun kukan taɓara.
      Miƙewa Madam Chioma tayi itama tana faɗin, “Ina jiranka kai maza ka fito”. Kansa kawai ya ɗaga mata ya cigaba da abinda yakeyi...........✍


Read more har bakwai yau?.😳😵😓🚶🏻.


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_Typing📲_*

No. 10

________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* 

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai *ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE*  domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*
     _________________________

.............Yau Nu'aymah ta tashi jikin nata daɗan dama, sai dai rashin ƙarfin jiki. Tunda Ahmad ya tafi raka Hajjo asibiti ganin Doctor saboda ƙafarta saita dawo sashensu ta kwanta. Barci tai sosai dan har sai gab da azhar ta tashi tai wanka. Shiri tai da ɗan sauri-saurinta ta fice zuwa ɗakin Umm, dan wani irin maitan awara takeji. Babu kowa a ɗakin, sai gyara da yasha yanata uban ƙamshi. Tai murmushi da faɗawa saman gadon ta kwanta tana mai sake shaƙar turaren wutar da ƙyau cikin hancinta. Tana masifar son ƙamshi a rayuwarta. Shiyyasa turare kwana kaɗan yake mata ya ƙare. Ga baba malam da Yah Ab sun mugun ɗaure mata ƙugu wajen siya mata. Sam basa gajiyawa. Kafin wani ya ƙare an saya mata wani. Ga khumra da Umm itama take bata ita da Adawiya. Tun Adawiya bata damu da ƙamshiba harta fara biyema Nu'aymah saboda yanda take bulala musu shi a cikin ɗaki kamar shagon saida shi.........
          “K! Kuma yaushe kika shigo nan?”. Umm ta faɗa tana kallon Nu'aymah dake kwance a kan gadonta idanu a lumshe. 
     A hankali ta buɗesu akan Umm dake kallon yanda tai rama cikin kwanaki kaɗan. Tai ɗan ɓata fuska kamar zatai kuka. “Umm dan ALLAH awara zanci”. Kai Umm taɗan girgiza da nufar gaban mirror ɗinta ta ɗauki ƙaramar wayarta da tazo ɗauka. “Indai banda fitina ni ina naga awara yanzu Nu'aymah? Ke dai inhar kikai zazzaɓi sangarta iri-iri kin iyata mara dalili, ko Muhammad baya iya shegenki a gidan nan”.
              “Umm Please!”. Ta sake faɗa cike da shagwaɓa kamar zatai kuka. Zama Umm tai a bakin gadon kusa da kanta. Taɗan shafa goshinta a hankali,  “Nu'aymah banson rigimar nan, yanzu dai kinsan baza'a samu awaraba ko? Sai ki bari sai anjima, bara dai na bama Saude takai kuɗin gidan ƴan awaran”.
      Kai Nu'aymah ta ɗagama Umm tana murmushi, sai kuma ta tashi zaune ta rungumeta tana ƴar dariya. Zame hular kanta Umm tai ƙoƙarin yi. Da sauri Nu'aymah takai hannu zata riƙe dan tasan mi Umm ɗin zata duba. “Umm kainafa ke ciw.....”
        “Ƙaniyarki keda ciwon kan, wai Nu'aymah bazaki daina wannan shegen ƙazantan nakiba na rashin son ƙitso? Kalla kiga fa kanki gashinki duk ya lalace saboda rashin kula. Tashi maza ki wuce wajen Adda ta kama miki kai kafin na ɓata miki rai”.
         Ƙwalla cike da idonta ta kalli Umm, “Umm dan ALLAH ba yau ba”. “Kin rainani ko?”. Umm ta faɗa tana ɓata fuska.
      Muhammad dake ƙoƙarin shigowa ya ƙyalƙyale da dariya yana faɗon, “Umm ALLAH fa ta rainaki, inba rainiba ya zakice taje kitso ta zauna shagwaɓa......”
    Filo Nu'aymah ta ɗauka ta wurgama Muhammad ɗin. Ya goce yana dariya. “Wlhy idan na kamaka a gidannan saina tsiyayar maka da man kai tas. Umm ki faɗama yaron nan nifa ba sa'arsa bace”. Yanda tai maganar idanunta cike da ƙwala ya saka Umm yin ƙaramar dariya itama, tai saurin saka hannu ta rufe bakinta tana haɗiyeta ganin hawayen harsun sakko a guje.
      “Uhghumm!” Umm tai gyaran murya tana haɗe fuska da wurgama Muhammad harara. Hannayensa ya haɗe waje guda fuskarsa da murmushi yace, “Am Sorry aunty N”. Ya ƙare maganar da mata gwalo kaɗan. Harara ta zuba masa ta koma ta kwanta da juya masu baya shi da Umm ɗin.
       Hannu Umm ta bashi suka tafa, kafin ya haye gadon yana faɗin, “Banace kiyi haƙuri ba Noorunnisa”. Juyowa tai fuskarta ɗauke da murmushi ta dungure masa kai tare da ja masa hanci tana faɗin, “Yaro 1-0”.
      Dariya sukayi a tare. Umm ta miƙe tana murmushi ta bar musu ɗakin.

★★★★

       Sashen Addah Umm ta nufa, dan tanason su tattauna game da al'amarin nan na Nu'aymah tun jiya, sai dai rashin lokaci yasa bata shigaba. Tasan itama Addahn bata shigo bane saboda taga baba malam ya wuni a gida jiya, yauma ya daɗe bai fitaba.      
         Kubrah kawai ta iske a falon tana  yankan ƙumba. Ta gaidata cike da girmamawa kamar yanda suka saba. Dan bayan mahaifiyarsu Umm itace mace ta biyu a gidan da suke ɗauka tamkar mahaifiya. Fuskar Umm ɗauke da murmushin itama ta amsa mata, “Ɗiyata saike kaɗai a gidan kenan?”. “Eh Wlhy Umm, daga ni sai Addah kawai. Hajarah da su Jafar sun fita aika”. “To ALLAH ya maidosu lafiya. Ina Addan?”. “Umm tana ɗaki ki shiga mana”.
     Kafinma Umm ta amsa mata Addah ta fito daga ɗaki. “Haba nifa ince kamar muryar Umm, ashe kuwa kece?”. “Ƙyaface haka mana, tun jiya rabon danaga idonki a gidannan Addah. saboda kinga ƴarki ta samu lafiya”.
               “Wacefa lafiya Umm, anason a ganmin bayanta”. Addah ta faɗa cikin ɓacin rai. Murmushi Umm tayi da kama hannunta, dan tasan Addah dama bata barin saita kwana sam. “Kinga nidai muje sarkin hawa”. 
           “Bazaki ganeba Umm. Daga jiya zuwa yau naje sashenki yafi sau a ƙirga amma sai na iske Baba malam na nan. Wlhy na kwana tamkar na ciji kaina dan baƙin ciki. Gaskiya Umm wannan al'amarin bai kamata mu zuba masa idanuba a wannan karon, yanzu dan ALLAH minene na ɗaukar Number wayar likita idanba zalunci ba? Lafiyarta ne ba'ason anema kenan ko minene?”.
          “Humm Addah wlhy nama kaina wannan tambayar yafi sau dubu tsakanin jiya zuwa yau. A a daren jiya har musabbabin ciwon Nu'aymah sai da ya dawomin a rai. Bansan minene laifin yarinyar nanba akeson rayuwarta ta salwanta. Ni harma na rasa wane kalar tunani zanyi Addah, wanene? Miyasa? Mi mukai masa?......”
            “Umm nidai tsakanina da ALLAH na fara zargin jama'ar gidan nan fa, idan har mai aikata wannan abubuwan ba'a gidan nan yakeba to daga ina yake zuwa? Nifa dagama jiya na fara tantama akan barin Nu'aymah gidan nan akan maganar aurenta. Shiyyasa ni dama tun farko ban yardaba. ni dama tun jiyan wani shawarace tazomin akan yanda zamu saka ido akan motsin kowa, na tabbatar insha ALLAH a hankali zamu samo bakin zaren”.
                Kai Umm ta ɗaga mata cikin alamar nuna gamsuwa. Addah ta matso kusa da kunnen Umm ta gwargwaɗa mata hanyar daya kamata subi. Ɗari bisa ɗari Umm ta amince, suka ɗaura da addu'ar dacewa. Daga nan suka cigaba da tattauna al'amarin suna ƙarama juna haske. Umm bata bar sashenba sai da lokacin salla yayi. Ta koma sashenta tana jin daɗi a ranta, koba komai zuciyarta ta rage nauyin da tai mata. Shiyyasa akoda yaushe take sake godema ALLAH daya haɗasu aure gida ɗaya ita da aminiyarta. Su kashe su rufe matsalolinsu babu maiji sai ALLAH.
            
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
_____________
*_DUBAI_*
________

                 Tun randa Abdallah yay waya da wadda yake zaton Momynsa ce ransa ya sake dagulewa gaba ɗaya. Wani lokacin ji yake tamkar ya naɗama Adawiya mugun duka ya cillata jirgi ta koma Najeriya. Sai dai tsoron fushin iyayensa ke sakasa dannewa.
         A maimakon kwanaki bakwai ɗinma da yay niyyar suyi a kwana na huɗu yasa suka wuce Saudia. Adawiya sai jin daɗi takeyi dukda bata ganin koda murmushinsa. Ita kasancewa da shi a ƙarƙashin inuwa ɗaya kawai ya wadatar da ita a cewarta.
       Ba wannan bane karonta na farko zuwa ƙasar saudia, sai dai yanda tazo a wannan karan yanada banbanci da sauran zuwanta na baya. Shiyyasa take wani jin kanta a sama. Wanda kuma takeyi dominsan ma baisan tanayiba. Tunda suka iso gidan da zasu zauna ya nuna mata ɗakinta bata sake ganin koda ƙeyarsa ba. Tsalle ta dingayi bayan fitarsa, dan ɗakin yayi matuƙar ƙyau da tsari. Sai dai kalar komar zaɓin Nu'aymah ne, harda ma manyan frames ɗinta guda uku da aka manna a bango, sai na Abdallah guda biyu shima. Dukansu sunyi masifar ƙyau. Ta taɓe baki da jan wawan tsaki, stool ɗin mirror taja duk ta juya na Nu'aymah dan har cikin ranta ta tsani ganinta, tunda itace sanadin hana tabbatar farin cikinta, saboda Nu'aymah yah Abdallah yaƙi sake mata, saboda Nu'aymah ta gagara daraja a garesa matsayinta na matarsa. Saboda Nu'aymah saboda Nu'aymah..... Komanta yaƙi dai-daita kamar yanda tai fata, tabar na Abdallah kawai tana faman kuka kashirɓan da zagin Nu'aymah da batasanma tanayiba.

           Rayuwarsu ta saudia tana kadaran kadahan ne, baya shiga harkarta bakuma ya takura ma rayuwarta. Sai dai har yanzu ya hanata wayarta, idanma zata gaisa da Addah da Abbanta ko wani a ƴan gidan nasu saita wayarsa. Kuma yay tsaye a kanta har saita gama ya amshe abarsa. Hakanna bata haushi, amma sonsa da tsoronsa ya hanata ta nuna masa koda a fuska.
      A haka suka kwashe watanni biyu a gidan. Shirye-shiyen makarantarta ya gama kammaluwa ta fara zuwa. Da farko bata shiga harkar kowa ta maida hankalinta a karatu kamar gaske. Tana wata na biyu da fara karatunta tai ƙawa mai suna Abida, sai da ana kiranta Maman Aaida, itama matar aurece harda yaranta biyu, asalin Mamana Aaida itama ƴar Nageriya ce, amma yanzu iyayenta na nan Saudia. Ta girma Adawiya da kusan shekara uku zuwa biyar, dan itakam zatai 22years. Maman Aaida irin matan nanne masu shegen iyayi dason gayu, ga Ƙwanƙwanin tsiya kamar jikar ƙaruna, kullum cikin bama Adawiya labarin mijinta take a zatonta Adawiya budurwa ce. Adawiya dataga iyayin Maman Aaida yayi yawa saita fito ta nuna mata itama ai tanada auren. Sosai Maman Aaida tayi mamakin hakan, danta tabbatar saita shirya zuwa gidan Adawiya a wani weekend. Babu wani ja'inja Adawiya ta bata address ɗinta. A kuwa ranar Alhamis saiga Maman Aaida har gida ita da maigidanta da yaransu biyu, da yake Abdallah na gida sai har mijinma ya shiga. Abdallah dai bai wani sake musu ba, bai kuma wulaƙantasuba aka gaisa da ƴar hira suka wuce, bayan tafiyar tasu kuma bai cema Adawiya komaiba akan zuwan nasu ba duk da yasan ya dace ace yayi hakan.
           Sanadin haɗuwa da Maman Aaida fa idanun Adawiya ya ƙara buɗewa. Dan tunda Maman Aaida ta bigi cikinta taji yanda akai aurenta da Abdallah sai ta shiga ɗorata bisa wasu hanyoyi da zata ringa jan hankalin Abdallah, ciki harda abubuwan irinsu turaren jan hankali da sauransu. Tun Adawiya najin tsoron yin hakan harta fara hawa kan network da sha'awar fara gwadawa ko zata dace Abdallah ya manta da Nu'aymah.
      A ranar farko da ta fara buɗe jikinta da turare Abdallah bai kwana gidanba, yamayi tafiya bata saniba. Da yake sai ya gadama take ganinsa sai bata fahimci baya nanba, washe gari ta wuce makaranta. Data dawoma bata gansaba bata kawo komai a ranta ba har dare, lokacin kwanciya ta sake shanana turare ta nufi ɗakinsa. Sai dai kuma wayam. saida ta leƙa har toilet sannan ta lurama ba'ai amfani da toilet ɗinba ma kwata-kwata. A take kuma sai tsoro ya kamata duk ta tsure, leƙe-leƙe ta shigayi cikin gidan kamar wata zararriya. Data ga dai lallai babushi a gidan saita fara kuka, ta koma ɗakinsa ta ƙulle ƙofa ta ƙudundune a bargo. Ta kusa awa guda a haka sannan ta fara jin motsin za'a buɗe ƙofa. Sake rikicewa tayi da kuka catake wanine ya shigi. Cike da mamaki Abdallah daya shigo yake sauraren kukan nata dan baiyi zaton ganinta a ɗakin nasa ba. Ƙarasawa yay gaban gadon ya yaye bargon. Tako dage zata kwarara masa ihu dan ruɗewa ya hanata nutsuwa taga wanene. Saurin hayewa gadon yayi ya rufe mata baki ruf da hannunsa yana kallon yanda jikinta ke rawa. 
        A take yanayin nata ya juye masa tamkar na Nu'aymah, dan duk lokacin da abu ya tsoratata haka zakaga jikinta na rawa duk ta fita hayyacinta, daga haka kuma saita suma. Yanda zuciyarsa ke ƙawata masa Nu'aymah sai tunaninsa ya gushe zuwa gareta harya rungume Adawiya batare daya fargaba. “K malama ki nutsu nine?”.
         Sosai Adawiya ta sake maƙanƙale masa dan a rikice take sosai, amma taji daɗi da taji shine.
            Tun Abdallah na shaƙar ƙamshin turaren data saka matsayin ƙamshi kawai harya fara canja masa yanayi. Hancinsa ya ɗaura bisa wuyanta yana shinshina da lumshe idanu, kafin a ɗauki tsahon lokaci jikinsa ya fara tsuma, sai ya sauya salon riƙon da yay mata. Anan nefa Adawiya ta dawo hankalinta da ƙyau. Da farko nishaɗin abinda yake matan ta farayi. Sai dafa taji al-amarin bawai wasan yara bane sannan ta fara kuka da roƙo da magiya. Da al-amari yay zurfi saiga hajiya malama mandiya ƴar ƙwalisar soyayya Adawiya na tsinema Maman  da jamata ALLAH ya isa🤣😂🤣.
     Oho, Abdallah baisan tanayiba, morewarsa yakeyi dai-dai gwargwado, yama manta dawa yake tare. Iya wahala ya bama Adawiya batare da tausayawaba, kafin ya koma gefe ya barta ko numfashin kirki bata iya yi.

      Tun daga wannan ranar Abdallah ya maida Adawiya abar hutawarsa. Daya samu biyan buƙatarsa kuma ya watsar da ita tamkar bai taɓa sanin daga inda ta fitoba. Sam ta gagara gane kansa balle inda ya dosa. Komai nasa yana yinsane da kulawa da lura. Abincinta dama kam bai taɓa ci ba, zai dai ajiye mata duk abinda ta buƙata ya kuma bata kuɗi. Amma babu wani farin ciki da kulawa kamar yanda Maman Aaida ke faɗa mata. Duk iya dabarun Maman Aaida cikin gwadasu take ga Abdallah amma saiya yi kamarma baisan tanayiba. ba shiga ɗakinta yakeba, ko abu zai bata sai dai yay knocking ta fito ta amsa. Idan yana buƙatar moranta ma zai mata knocking ne idan tana ɗaki yace ta samesa nasa ɗakin. 
     A haka rayuwar auren nasu ke tafiya tare da karatun Adawiya da ta fara saka shiririta saboda damuwarta kawai itace Abdallah ya sota a yanzu.

*_NAJERIYA_*

            Rayuwa ta shuɗa, kwanaki nata gangarawa, inda ake neman watanni na takwas kenan da lalacewar auren Nu'aymah da Abdallah. Tana cikin tsananin damuwa da begensa, kullum dare sai tayi kuka, tana sonsa matuƙa, dan ta rayune da son nasa. Yawan damuwar da take a cikine ya haifar mata da yawan yin ciwo, saboda ciwonta bayason damuwa sam. A duk sanda ta takura kanta da tunani da damuwa yakan yawaita motsa mata akai akai, tana kuma matuƙar shan wahala. 
        Gaba ɗaya a awatannin nan lafiya taƙi wadatarta, haka taketa fama yau fari gobe tsumma. Gashi baba malam kullum cikin mata jan ido yake akan ta kawo Ameer yay musu aure. Tayi kuka tayi rantsuwar akan Ameer ba saurayinta bane amma sam yaƙi ya saurareta. Umm kanta wannan al'amari na tada mata hankali. Amma babu yanda ta iya ta zuba musu ido kawai taga iya gudun ruwan mijin nata. 
    
      Burin Nu'aymah cigaba da karatu a yanzun, amma Baba malam yay banza da maganar karatun nata, bayan kuma kowa a gidan yasan burinta a rayuwa shine ta zama likita ko Nurse tun tana yarinya. Addu'arta kullum itace Baba malam ya haƙura a sake nema mata makaranta kafin ALLAH ya dawo da hankalin Abdallahnta gareta, dan ita duk ɗaukarta Abdallah fushi yake da ita akan ta gudu ran aurensu, shiyyasa yaƙi nemanta koda a wayama. Ta dage da azumin litinin da alhamis da sallar dare tanata gayama UBANGIJI kukanta.
      Ana cikin wannan yanayin su Baba malam suka gama shirya gagarumar walima na saukar Al-Qur'anin yaransu na gidan marayu, tare da aurar da waɗanda suka samu mazan aure. Wasunsu anan cikin gidan suka dai-daita kansu. Wasu kuma a waje suka samu mazajen aure da mata.
    Shirye-shirye ake babu kaman hannun yaro, dan shinema ya ɗauki Baba malam Busy sosai ya samawa Nu'aymah lafiya daga takurar zancen fiddo mijin aure. Duk da dama dai yana matane kawai dan hukuntata ta cikin ruwan sanyi akan abinda ya faru. amma ta ƙarƙashin ƙasa neman hanyar ganin likitan nan kawai yakeyi da nema mata makaranta batare da ko Umm ta san da hakan ba.  
      Ana saura sati ɗaya su Yusrah suka iso, washe gari kuma su Amal. Hakan ba ƙaramin daɗi yayma Nu'aymah ba, koba komai ta rage kaɗaicin da ta tsinci kanta a cikin a waɗannan watanin ai. Abinda ya ƙara faɗaɗa farin cikin natama shine Amal da Yusrah bazasu komaba, dan zasu zaunan zana jarabawar ssce anan. Cikin kwana biyu kacal da dawowar tasu ta fara komawa cikin walwalarta. 
       Tuni suka fara addabar gidan da ƙiriniyarsu da bata ƙarewa, sauƙinma babu Adawiya, amma hakan baisa sun fasa abinda suka saba yiba. tun ana saura kwana uku suka saka Hajjo ta roƙa musu baba malam komawa cikin gidan marayu har sai an kammala komai. Dan yawancin ƴammatan da za'aima auren duk ƙawayensu ne, duk da dai a shekaru gaskiya zasu girmesu da kusan shekara bibbiyu ko ɗai-ɗai.
     Bai hanasu ba, dan gidan marayun nan nada matuƙar muhimmanci a garesa dama family ɗin gaba ɗaya. Yanda suke ƙoƙarin dagewa akan tarbiya da karatun yaransu haka suke dagema yaran gidan marayun nan suma. Shiyasa suma yaran suna tsananin ƙaunar wannan family, su suke ɗauka danginsu da komai a rayuwa.

★★★★★

             “Wai wannan akwatin da kika lodama kaya duk na miye Nu'aymah?”. Umm data shigo ɗakin Nu'aymah ta faɗa tanabin Nu'aymahr daketa shirin kaya da kallo.
     Ɗagowa tai ta kalli Umm cike da ɗoki, “Umm yo na bikine mana, sati guda zamuyi a can”.  “To lallai, ashema kune iyayen bikin kenan?”. Dariya Nu'aymah tayi dajin zancen Umm, Umm kam daga haka bata sake cewa komaiba ta ajiye mata magungunan ta tana faɗin, “Gasu nan, saura kije kita wasa da shansu Nu'aymah, dan ALLAH ki kula da kanki, duk abinda kikasan zai zame miki matsala ki kujesa, ku kuma riƙe mutuncin kanku, na kira Baba Habi a sashenta zaku zauna kafin Hajjo ta iso gobe idan ALLAH ya kaimu, saura naji wani abu mara ƙyau na shegen tsiwanki, ALLAH saina ɓata miki rai”.
        “Umm insha ALLAH bazakiji komaiba ma”. “ALLAH yasa”. Umm ta faɗa tana juyawa ta fice daga ɗakin..

          Bayan sallar azhar su Nu'aymah sukai sallama da kowa suka wuce, Yah Abubakar ne ya kaisu. Da yake shima irinsu ne ɗan taraliya saida ya kaisu sukai shopping sannan ya wuce dasu gidan marayun.
     Ƙaton gaske ne, sannan an ƙawatashi ta ko ina babu makusa. Akwai makaranta da asibiti da duk ma abinda masu rayuwa da iyayensu suke samu. Makarantarsu ta fara tun daga noziri har zuwa sakandire. Ana koyar da boko da arabic, idan kaji yanda yaran ke larabci da turanci sai kasha mamaki da al'ajabi. Rayuwarsu suke cike da farin ciki da jin daɗi wadda ko wasu masu iyayenma basa samu. Gasu da tarbiyya abin birgewa. 
     Ɓata lokacine zama bayyana muku yanda gidan marayun nan ya ginu da tsari mai ƙyau, kusa a ranku kawai ya haɗu. Dan sosai su baba malam ke samu taimakon manyan mutane dama masu mulki game da riƙe gidan. Ga kuma suma kansu masu nemane basu zauna jiran na sadakaba. Kaso mafi yawa na ɗunbin dukiyarsu yana tafiyane wajen tattalin rayuwar marayun nan da kulawa da su. Shiyyasa Alhmdllh da wahala ace sun nema abu sun rasa. Sai dai ace yau da gobe sai ALLAH, komai arziƙinka dama wani abun sai ya gagareka.
       A yanda su Nu'aymah suka sami tarba zai tabbatar maka da sanannune a gidan, kuma ba wannanne farkon zuwansu su kwanaba. Dan rigima aka shigayi musamman ga sa'anninsu, kowa na faɗin sashinsu su Nu'ayma zasu sauka. Bayan ansha taƙaddama dai kowa ya haƙura zasu zauna a sashen da amare suke, wato sashen baba habi da Umm ta faɗama Nu'aymah tun a gida.
        A yau kowa ya kalli Nu'aymah yasan tana cikin farin ciki sosai, haƙoranta sun kasa rufuwa. Tsiyarsu sukaita tsulawa uwa ba kwaɓa uba babu tsanani, dan suna son suga sunzo gidan nan, shiyyasa wani lokacin baba malam da kansa yake cewa suzo suyi weekend ɗinsu anan, dama anan duk yaran gidansu ke karatunsu tun daga noziri har zuwa sakandire, shiyyasa sukeda shaƙuwa sosai da yaran gidan marayun fiye da zaton mai tunani.

     Washe gari Nanah tace suma gasunan zuwa ita dasu Suhailat, hakan yasa bayan sallar la'asar ana tsaka da musu ƙunshi dan ranar itace suka saka ranar ƙunshin, Nanah ta kira wayar Yusrah ta sanar musu gasu a bakin titi suzo su shiga dasu dan baza'a barsu su shigaba kai tsaye.
        Nu'aymah da Yusrah da biyu cikin ƴammatan gidan suka fita shigowa da su Nanah dansu ƙunshinsu harya bushe sun wanke, Nu'aymah ce kawai bata wanke nata ba amma ya bushe. da ƴar tafiya tsakanin gate da gidajen yaran, amma haka suka taka a ƙasa suna hira har suka iso. suna a gab da fitane suka haɗu da yaran gidan maza da bazasu gaza shekaru sha biyu ba kusan su bakwai wai wajen ball suka tilla ƙwallon waje ta katanga shine zasu zagaya ɗakkowa. Security ɗaya ne tare dasu zai rakasu. A tare suka fita dasu Nu'aymah da zasuje tarbar su Nanah.
       Gidan marayun yana akan babban titine, shiyyasa sam ba'a barin yaran fitowa ko ina su kaɗai koda hakan ta kama sai da security.
      
        Dariya Nu'aymah tai ganin su Nanah acan ɗayan tsallaken basu tsallakoba, tasan Nanah matsoraciyace akan tsallaka titi dama, shiyyasa yanzuma abun ya bata dariya data tuna. Su Yusrah ma dariya suka sanya famhimtar dariyar Nu'aymah da sukayi. Bayan sun kalla ɓangare biyu na titin babu mota suka sa kai zasu tsallaka. Da sauri security ɗin daya rako yaran nan yasa hannu ya fisgo Nu'aymah dake ƙarshen tafiya saboda tahowar wasu motoci guda uku a jere cikin masifaffen gudu.
        Ta juya zataima security ɗin masifar taɓatan da yayi dukda tasan hakan na halinsu bane sukaji razananniyar ƙarar ɗaya daga cikin yaran wanda motar farko ta kwashesa yana ƙoƙarin ɗakko gyalen Nu'aymah daya zame ya faɗi lokacin da security ɗin nan ke ƙoƙarin maidota baya.
         “Ƙuuuuuwww!!!” motocin suka bada sautin taka birki a tare, yayinda mai napep dake bayansu ya bugi motar ƙarshe shima.
      A tare su Nu'aymah suka fasa ƙara da rumtse idanu kunnuwansu a toshe da hannayensu, sai da sukaji tsitt sannan suka bubbuɗe ido dan son ganin yaya akayi.
       “Innalillahi.... Suka shiga ambata kusan a tare saboda hango yaron a kwance ƙasa cikin jini. Sunma manta a titi suke, suka tafi da gudu kansa suka rufu masa. Sunkai mintuna uku akan yaron nan suna kuka da jujjuyashi amma ko mutum ɗaya bai fito daga motocin nan uku ba balle kai tunanin sunsan ma abinda suka aikata. Cikin tsananin fushi da zafin zuciyar gado Nu'aymah ta rarumi wani dutse dake a gefen titin ta nufi motar tsakkiya dake a saitinta, wadda kuma tafi kowacce haɗuwa da ƙyau ta buga dutsen jikin glass ɗin. 
      Ko gezau glass ɗin baiyiba, dan haka ta koma na gaba wanda tasan insha ALLAH zata dace ta sake bugawa da iya ƙarfinta. Aiko a take ya shiga tsatstsagewa. Ta sake ɗagawa zata buga aka riƙe mata hannu. Fisge hannun nata tai ƙoƙarin yi ta kasa, dan haka ta juyo bakinta cike da tsiwa.
      Ido huɗu tayi da manyan garada masu suffar ƴan dambe cikin baƙaƙen suit da glasess zagaye da ita su shidda, daka gansu kaga cikakkun marasa imani dan babu alamar sunsan ma minene dariya a rayuwarsu, babu tantama kuma zasu iya halaka mutum batare da sunji koda ɗar ba.
        A mamakinsu sai gani sukai ta ɗaga dutsen ta bugama wanda ya riƙe mata hannu a goshi. Saurin sakinta yay ya dafe goshinsa daya fashe a take ya fara zubda jini.
        Kusan a tare suka fiddo bindigu suka nunata da shi. Duk da Nu'aymah tasan zasu iya harbin nata ta mutu kuma, amma sam cikin idanunta babu tsoronsu, saima masifa dake cinta. Haka take ita sam batasan tsoroba. Idan kaga tsoro ga Nu'aymah to duhu ne ko tsawa, ko allura.
       Ɗasss! Ɗasssss!! Ɗassssss!!!
Sukaji sautin buga yatsu a bayansu. Gani tai duk sunja baya daga kusa da ita amma basu sauke bindugunba, sundai risinar da kawunansu ƙasa na alamar girmamawa ga koma wanene mai buga yatsun.
        Kamar bazata juyaba sai zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncine shiɗin...........✍

Nidai nama rufe idona bazan gansa ɗinba😎🚶🏻.

Yau dai ga dogon page nan ku more harda na jiya na haɗa muku. Saura kuma naji wata tace bai isheta ba😚😏😣🚶🏻🚶🏻🚶🏻


__________________________________
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_Typing📲_*

No. 12

________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* 

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

___________________

................Sai da ya kammala ƙalular shirinsa cikin kayan barci wando 3quarter da riga Armless sannan ya zura slippers masu taushi ya fita. Kusan su shidda ya iske a falon kowa da hidimar da yakeyi. Wasu kallo wasu danna waya wasu surutu.
     Da sauri Miracle ta ɗauki remote ta rage ƙarar television ɗin dan tasan ya tsani hakan. Shikam baimabi takan kowaba ya nufi d/table. Kafin ya ƙarasa Miracle ta rigashi isa, yana ɗaura hannunsa saman kujera zai jata baya ta ɗora nata akan nashi. A take fuskarsa ta sake tsukewa, ya ɗago fararen idanunsa ya zuba mata wani banzan kallo. Maimakon ta janye hannun saita kashe masa ido ɗaya tana murzawa a hankali. Kallon hannun yayi cike da tsantsar fushi. Duk da tsoronsa dana yanayinsa a yanzu ke ratsata bata fasaba, saima karta zaƙo-zaƙon faratan ta ta farayi tana matsawa da hannunta gaba akan nashin cike da salon iskanci.
          Ita da kujerar ya haɗa ya wancakalar gefe, kafin takai ƙasa ya bita da halbi, sai gata ƙasa wanwar. Ƙarar data firgita kowa a gidan ta ƙwalla tana faman ihu kamar wadda aka yanka. Dukansu kanta sukayo, yayinda Yoohan ya sake ɗaga hannu zai ƙwaɗa mata mari Gebrail ƙaninsa yay saurin riƙesa, fisgewa yay yayi ƙwallo da kujerar kusa da shi ta dining ɗin ya juya fuuu kamar wani kumurci ya nufi sama. Da sauri Mom data fito daga wani ƙofa yanzu saboda jiyo ihun Mira ta shiga ƙwala masa kira da turanci. “Yoohan! Yoohan!! Yi hakuri zo kaci abinci”.
      Baiko waiwayeba balle tai tunanin samun amsa. Da gudu ta bisa tana haɗa steps ɗin da bibbiyu. Kafin ta ƙarasa har ya tura ƙofar ya maida ya rufe. Bugawa Mom ta shigayi tana kiransa cike da lallashi “Yoohan! yi haƙuri kaji, kar kayi fushi zo kaci abinci Please”. Duk da yaransu take maganar, amma yaƙi buɗe mata. Shi tunima yabar jikin ƙofar harya shige bedroom ɗinsa.
        Zuciyarsa cike da matsanancin ƙunci ya faɗa saman gadonsa ya kwanta a rufda ciki. Ji yake gaba ɗaya duniyar ta masa masifar ɗaci, yaja filo ya danne kansa da shi da ƙarfi.

      A falo kam Mom data sakko a ranta a ƙuntace ta ƙarasa inda Mira ke faman kuka har yanzu, cikin faɗa tace, “Miracle bance ki fita hanyar Yoohan bane? Kin riga da kinsan halinsa baya son wannan banzan halayar amma ke kam bazaki kama kankiba. Ki cigaba, wataran idan ya karyaki ko ya miki mugun dukan da za'a gaza ganeki zaki kiyayesa ai”. Batare da ta saurari amsa daga Mira ba ta wuce ɗakinta cikin fushi itama, dan a rayuwarta ta mugun tsanar ganin an ɓatama Yoohan rai a gidan. Tana masifar son yaronta fiye da sauran ƴaƴanta.
          Kuka Mira ta sake ɓarkewa da shi iya ƙarfinta su Joy na lallashinta, da ƙyar suka iya ɗagata dan tanada jiki sosai bawai siririya bace, sannan a shekaru sai dai suyi sa'anni ma da Gebrail ƙanin Yoohan ɗin. 
      Da taimakon su Joy Miracle taje ɗakinta, sai da suka kwantar da ita a gado Gebrail ya kalleta shima cike da takaicinta. “Mira idan baki fita hanyar Brother ba na tabbatar shine zai maidaki gurguwa kafin ki koma gidanku, nasha faɗa miki shifa a rayuwarsa yanda ya tsani shan giya haka ya tsani harka da mata. Wanda yay kashi biyu cikin ukun rayuwarsa a turai matan can basu sakashi ya iskance ba ta yaya kike tunanin ke ƙaramar ƙwaruwar Najeriya zata iya sakashi aikatawa? Ƙilama dakin kama kankine zai soki kamar yanda kikai fata, amma a haka ina tabbatar miki tsanarki yake ƙarayi dan baya ɗaukar lamarin ta fuskar soyayya, idan kinji shawarata sai ki kiyaye”. Yana gama faɗa ya juya yay ficewarsa, kafin duk suma sauran su fito a barta daga ita sai Joy da take kusan sa'arta itama. Dan twins ne ita da Gebrail ɗin. Hawayenta ta share tana danna ƙafarta data buge, da yarensu tace, “Joy wai miyasa Brother ɗinku bashi da kirki?, gashi duk iskancin da wulaƙancin da yakema mutane su Mom sai sudinga goya masa baya basa son ɓacin ransa, kamar sunajin tsoronsa ma......” da sauri Joy ta rufema Miracle baki da hannu tana girgiza mata kai, sai da ta tabbatar tayi shiru kafin ta saketa, ƙofa ta nufa da sauri ta leƙa, ganin babu kowa saita maida ta rufe sannan ta dawo wajen Miracle ɗin. Daf da ita ta zauna cikin magana raɗa-raɗa tace, “Ni kaina na daɗe inason yin maganarnan da Wani Mira, kinga dai su Mom duk su suka haifemu, amma idan kika lura sunfi son Brother Yoohan, ko yaya suka gansa a damuwa sai kiga sun rikice, sannan duk abinda yakeso shi ake masa. Kiga dai yanda kike sonsa yana wulaƙantaki a gidan nan amma basu taɓa nuna masa rashin dai-dai akan hakan ba. Kowafa tsoronsa yakeji anan gidan har Mom ɗin”. Mira dake sauraren Joy kamar mai ɗaukar karatu tace, “Yayi kuɗi ne shiyyasa ai”. Kai Joy ta girgiza mata da faɗin, “Sam ba haka bane Mira, ki tuna tuntuni suke masa wannan gatan na fitar hankali, makaranta saida ya zaɓa ya darje mai mugun tsada a ƙasar waje, har sai da ya cika burinsa na zama babban likitan da yakema duniya aiki bama Najeriya kaɗaiba, amma kina gani ni da Gebrail a 9ja muka fara karatunmu, sai yanzune da shi yace zai fita damu sannanfa suka yarda”. “Hakane Joy. to ammafa kinsan Yoohan yanada bala'in ƙwaƙwalwa, dan sister Divine tace min sanda suna primary yafi kowa hazaƙa da ƙoƙari a ajinsu, yanzu za'a karanta masa yanzu zai ɗaukesa a kai. Ni yanda ya tsaya yay karatun ya birgeni, dan masu irin shegen kaifin ƙwaƙwalwar nan tasa basu da yawa a cikin mutane, zakiga kuma mafi yawansu sunfi yarda su zama mugaye fiye da mutanen kirki, balleshi daya tashi ɗan gata ma. Amma kigafa shi a ma tsarinsa baya shan komai har giya da ba komaiba, baya neman mata, abinda kawai ya sani a rayuwarsa shine aikinsa da Family ɗinsa. Gaskiya ina masifar son gayen nan Joy, komai nashi yana birgeni”. 
        Dariya Joy tayi sosai, ta wani juya idanunta cike da yanga, “Ai bake kaɗaiba Mira, koni da yake Brother ɗina sonsa nakeyi, haka ƴammata da yawa suke haukacewa a kansa, shiko babu wacca ta ishesa koda kallo ma, Mom tace tunda suke da shi bai taɓa ce musu ga budurwarsa ba. Ke nifa da ƙanwa zata iya auren yayanta da Brother Yoohan zan aura fa”. Baki Mira ta taɓe cike da kishi ta ɗauke kanta batare data bama Joy amsaba. 
     Joy data fahimci kishi Mira keyi saita kwashe da dariya ta miƙe, amma ita tasan har cikin ranta son Brother ɗinta take da gaske. Kuma harga ALLAH tana kishin ganinsa da wata mace har Mira ɗin, dan yau sosai taji daɗin mazgar da yayma Miracle.

🤣Joy kedai muguwace to.

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka karanta idan baka biyaba, karka kuma yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________

               A tsarin gidan dolene duk safiyar duniya ka fito babban falo inda suke taruwa su duka har ma'aikatan gidan suyi addu'oinsu. Yoohan ne dama sai ya gadama randa ta raya masa yake fitowa idan har ya kwana a gida, dan yafi ganema yayi tasa a ɗaki shi kaɗai baisan hayaniya, garama idan Papa ya takura masa.
      Yauma kamar kullum duk sun hallara, har ƙananan yaran duk an tasosu, Papa da yay tafiya ne kawai babu sai Yoohan da kowa yasan yau bazai fitoba tunda jiya da haushin Miracle ya kwanta. Amma duk da haka sai da Mom taje ta buga masa ƙofa.
      Yana jinta sarai, dan tashinsa kenan yana zaune a kan gadonsa ido a rufe yana addu'ar shima. amma yay mata banza, sai da ta gaji dan kanta ta haƙura. Sauka yay a gadon fuskar nan kamar kullum a cinkushe, amma hakan bai hana ƙyawunsa da ALLAH ya azurtasa dashi bayyana ba (damma babu hasken bautar UBANGIJI a cikinsa Yoohan daya zarce hakan ga mai kallo😭).
        Slippers ya zura ya nufi toilet, ya kusa mintuna goma a ciki sannan ya fito, da alama dai ba wanka yayi ba, dan kayansane a jikinsa bai canja ba. Ficewa yay daga ɗakin gaba ɗaya ya fito falonsa, a mamakina sai naga ya ɗaga labulen bangon gabas, sai ga ƙofa a wajen ƙatuwa ta glass. Danna wani abu yay a bangon ta zuge da kanta ya shiga. Ƙaton ɗakine da aka cika da kayan motsa jiki kala-kala. Gaba ɗayansa kuma da glass aka yisa, ta ciki kana iya hango harabar gidan dama cikin anguwar gaba ɗayanta. Zama yay ya ɗaura takalma a ƙafarsa batare daya canja kaya ba ya fara motsa jiki a style kala-kala. Yana a kusan mintuna hamsin da farawa amintaccen yaronsa da Nu'aymah ta fasama kai jiya ya shigo ta wata ƙofa ba wadda shi ya shigoba. Madaidaicin tiren hannunsa ya ajiye kan wani table dake can gefe gaban kurera doguwa guda ɗaya kacal dake a ɗakin, sannan ya dawo inda Yoohan ke cigaba da ɗaga ƙarfe yace, “Good Morning sir”. Sai da ya furzar da zufan dake sakko masa har kan laɓɓa sannan yace, “Morning” a taƙaice. 
            Ajiye ƙarfen yay ya miƙe ya sake komawa kan wani machine ɗin, sai da ya fara batare daya kallesa ba yace, “Solo! Aikin dana saka ka fa?”. Kan Solo a ƙasa yace, “Sir komai ya kammala, yanzu haka ma nasan sun kama hanyar tafiya dan tunda daddaren na sanar masa, ya kuma tabbatar min za'a haɗa komai tun a daren, a yau su tafi kaiwa”.
       “Good” ya faɗa a taƙaice yana kallon agogon dake manne a bango ƙato. Lumshe idanunsa yay ya buɗe yanata faman fidda numfashi da sauri-sauri. Sajensa kansa ɗigar da zufa yakeyi balle murɗaɗɗen jikinsa dake sharkaf tamkar wanda yayi wanka. Sauka yay daga saman machine ɗin ya amshi ƙaramin towel dake a hannun Solomon ya fara goge fuskarsa zuwa wuya.
        Da sauri Solo ya ɗakko tiren daya shigo dashi shima. Iska Yoohan ya furzar kafin ya ɗauka babban kofin glass dake cike da tatattun kayan marmari da babu koda suga a ciki akan tiren dake hannun Solomon. Barin wajen yay da kai kofin bakinsa yana sha, ya ƙarasa kujerar nan ƙwara ɗaya ya zauna da ɗaura ƙafa ɗaya a kan ɗaya ya ɗauka remote ya kunna television dan akwai program ɗin da yake kallo a NTA kullum safiya a irin wannan lokacin a duk inda yake, inhar kaga bai kalli wannan shirinba to sai dai inda yake babu wutar nefa kuwa.
             Dawowa Solo yay gefensa ya tsaya suna kallo a tare, yana shan lemonsa suna magana jefi-jefi akan tafiyar da zasuyi yau har aka kammala shirin, dan minti ashirin ne dama. Ajiye kofin yayi ya miƙe bayan ya cire takalman yabar Solomon na gyara ɗakin da maida kowane abu inda yake.

      Kusan 9am ya fito daga ɗakinsa cikin gayunsa dake rikita ƴammata, sai baza ƙamshi yake kamar wani gonar turare. Sai dai tamkar kullum fuskar dai babu fara'a. Sajen nan da gashin sunsha uban gyara na ɗaukar hankali kamar dansu kawai aka yosa duniyar.
        Tunda ƙarar takunsa ta fara bayyana garesu falon yayi tsitt, kowa ya zubama hanyar benen idanu duk da sunsa wanene ɗin mai tahowar kuwa.
           Kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa yana sake tamke fuska musamman da yaga Miracle zaune. Mom ce cike da farin cikin ganinsa ta miƙe tsaye tana buɗe masa hannayenta alamar yazo. Fuskarsa ya ɗan saki amma ba murmushi ba, ya nufeta ya ɗan rungumeta a gefe saɓanin ita da ba haka take buƙatar yi masaba, ta fison ta jisa sosai a jikinta, sai shi kuma sam baiso. yace, “Good morning Mom”. “Good Morning my boy, ka tashi lafiya?”. Kansa kawai ya gyaɗa mata. Tai murmushin jin daɗi tana kama hannunsa cikin nata.
       “Good morning Brother”. Suka haɗa baki wajen faɗa yaran suma, amma banda Mira data haɗe rai wai ita a dole fushi take da shi. Kallonsu yay sosai da fararen idanunsa ɗaya bayan ɗaya kafin ya amsa musu da muryarsa mai amo. Ya ɗaura da tambayar lafiyarsu kamar yanda ya saba cike da kulawa da sonsu. Dukansu fuska a washe suke amsa masa, dan sunsan yana ƙaunarsu. Idan dai baƙin halinne ya motsa ba sani ba sabo yakema kowa a gidan.
        A tare suka ƙarasa d/table shi da Madan Chioma, ta zaunar dashi da kanta ta shiga zuba masa abincin da tasa akai masa na musamman. “Thanks” ya faɗa a saman laɓɓa ya ɗauka cokali ya fara ci. dai-dai misali yaci, dan badan ma tafiya da zaiyiba bazai karyaba a irin wannan lokacin. Dan shi mutum ne mai ƙa'ida da tsari. Komai nasa a tsare yake tamkar wani bature😜 (mudai munsan ALLAH shike tsara rayuwa ba mutum ba😁).
         Cikin damuwa Mom daketa kallonsa tace, “Badai ka ƙoshi ba?”. Idanunsa ya ɗan lumshe mata alamar amsawa. Tai saurin kamo hannunsa tana girgiza masa kanta. “Jiyafa bakaci abinciba ka kwanta, shine yanzu kuma......” “Shiiii!!” ya faɗa yana ɗora ɗan yatsansa akan bakinta, “Mom ya isheni haka”. Badan tasoba ta barsa. Yasa tissue ya goge bakinsa sannan ya miƙe, “Mom zan wuce Lagos, zata iya yuwuwa daga can bazan dawo nanba zanje ƙasar Kenya. Cike da damuwa take kallonsa, har yanzu ta kasa sabawa da waɗannan tafiye-tafiyen nasa, dan ko kaɗan batason yay nesa da ita, a koda yaushe tafison taita ganinsa tare da su.
        Kansa yaɗan girgiza dan yasan miyasa jikinta yay sanyi. Ya kama hannunta da yasha farce zaƙo-zaƙo, murya a tausashe yace, “Mom kimin addu'a mana, baƙyaso na cigaba da taimakon mutane ina samun lada?”. Da sauri tai murmushi, “Inaso sosai Yoohan, sai dai aikin nan ya maka yawa, gaba ɗaya baka da wani lokacin kanka kai saina wasu. ALLAH yasa kaje lafiya ka dawo lafiya”.
     “Amin” ya faɗa da yin kissing hannun nata.

      Gaba ɗayansa suka fito domin masa rakkiya har wajen da motar da zai shiga take, cikin girmamawa guards ɗinsa da securitys gidan suka iso ɗaya bayan ɗaya suna gaishesa. Kamar yanda ya saba musu alkairi idan zai yi tafiyar kwanaki haka yauma duk ya bisu da shi ta hanyar Solomon dake da kusan ci dashi fiye da kowa, dan duk inda zaije tare suke tafiya, sannan komai nasa shi yake sakawa. Dan haka yasan sirrinsa sosai da halayensa fiyema dasu iyayensa. A tare suka shiga masa addu'ar fatan alkairi, ƙannensa kowa na masa shagwaɓar zaiyi missing ɗinsa. Babu dai dariya a fuskarsa, amma duk yana binsu da kallon kulawa. Kafin ya bisu ɗai-ɗai yay kissing nasu a kumatu, banda Miracle dako kallon inda take bayayi. Gebrail ya buɗe masa mota ya shiga, shima ya zagaya ta ɗayan gefensa ya shiga dan zai masa rakkiya airport ne.
         Ɗaga fararen idanunsa yay ya kalli Mom da duk fuskarsa tai kalan damuwa. Yatsunsa biyu yasa a gefen bakinsa yay mata alamar *_Smile_*. Murmushin kuwa ta saki har haƙoranta na bayyana kafin ta ɗaga masa hannu. Shima yatsunsa biyu ya ɗaga mata daɗan motsa laɓɓansa kaɗan yay maganar da shi kaɗai yaji kayarsa. (Dan nidai banjiba🙄😏).
      
      Ganin motocin sun fice Madam Chioma ta sauke ajiyar zuya, yayinda Miracle ta share hawaye masu zafi da suka gangaro mata batare data shirya hakanba. 
     Juyawa sukai suka koma ciki, dama yaran sun wuce school su tun ɗazun.

__________________
*_NU'AYMAH_*
_________________

           Tunda garin ALLAH ya waye kaikawonsu suketayi na hidimar walima a cikin gidan marayun. Da safe kusan goma Hajjo ta iso tare dasu Hajarah. Su Umm kuma sai zuwa anjima.
         A babban harabar farkon shigowa cikin gidan marayun aka kafa manyan rumfuna tare da kujeru masu yawan gaske. Sai babban munbari da malamai zasu gabatar da lectures insha ALLAH.

     Nu'aymah harkokin gabanta take kawai, tama manta da wani faɗa da tayi da wasu jiya. Haka take, akwai saurin fushi da tsiwa akwai kuma saurin sauka da mantuwa. Itadai wuyarta ace ta rama kota maida murtani, daga haka kuma ta manta sai wata ta taso.
      Wajen misalin sha biyu saura ta kammala shirinta cikin baƙar jallabiya datasha adon manyan jajayen duwatsu masu ɗaukar ido. Itace shigar da gaba ɗaya ƙawayen amare zasuyi a wajen walimar. Tayi ƙyau sosai, ta sake gyara gashinta da saida akasha dagama kafin ta yarda aka tsefe aka wanke mata shi. Tanada gashi gwargwado dan yana sauka mata har kan kafaɗa, amma ta tsani kitso, gashi ta zama budurwa amma batabar kukan kitso ba har yanzu. Tsifar kai ma kuka take masa da wankewa balle kuma kitso.
      Jan veil ɗinta madaidaici ta naɗa, kalar saita sake bayyana ainahin hasken fatarta da kwarjininta da ƙuruciya. Ga jambakin data saka kaɗan a laɓɓa ya sake ƙawata madaidaiciyar kwalliyar tata. Sauri take taje kiran da baba malam ya aiko ai musu yanzun nan tana wanka. Tasa turare kaɗan ta fito da ɗan hanzarinta.
     Tare suka tafi ita da Amal da Yusrah, dan su ukun ya aiko kira. Suma sunsha ƙyau cikin kalar rigar da Nu'aymah tasa iri ɗaya komai da komai. Akwai tazara tsakanin office ɗin baba malam zuwa sashen gidajen yaran, amma haka suka taka cikin nutsuwarsu suna ƴar hira har suka isa. Sai da aka nemar musu iso sannan suka shiga.
      Baba malam ya ɗan kallesu ya ɗauke kansa, a ransa yanajin daɗi da godema UBANGIJI daya azurtasu da kamilan yara da yayi. Basu izinin zama yay kafin su gaidashi. Ya amsa musu kamar yanda ya saba. Sannan ya lissafa musu aikin da zasuyi a wajen walimar. Sai dai ba komai ya saka Yusrah a cikiba kasancewar tanada aure ita. 
     Suna shirin miƙewa zasu fita security yay knocking ƙofar office ɗin dayin sallama. Amsa masa sukayi, baba malam ya bashi iznin shigowa. Cike da girmamawa yace, “ALLAH gafarta malam saƙone wani bawan ALLAH ya aiko dashi”. Baba malam dake saurarensa yace, “To aike kuma Rufa'i. Nami kenan?”.
       “Kayan abincine dai mota guda gasu can a waje”. Baba malam bai sake cewa komaiba ya miƙe. Shi ya fara fitowa sannan su Nu'aymah a bayansa.
     Mota ce ta kamfani, dan haka baba malam ya ƙarasa suka gaisa da drivern cikin mutuntawa. “Malam ko zan iya sanin saƙo daga ina haka?”. Baba malam ya faɗa cikin fara'a da mutuntawa. Murmushi drivern yayi, shima cike da girmamawar yace, “Ranka ya daɗe wlhy nima bansan daga wa kayan sukeba, amma dai wani bawan ALLAH ne ya saya a kamfaninmu ya kuma bada wannan address ɗin a kawo tare da wannan”. Ya ƙare maganar da miƙa masa leda madaidaiciyar ruwan ƙasa.
       Sai da baba malam yay ɗan jimm kafin ya amsa, dan su gidan marayunsu nada tsari, ba komai suke amsa kai tsayeba babu bincike saboda gudun abinda zaije ya dawo. “Idan bazaka damuba ko zaka bani Number ɗin Manager ɗinku?”. “A babu damuwa ranka ya daɗe, dan dama shima yace na baka idan nazo”. “To Alhmdllh”.
      Wucewa sukai tare office ɗin baba malam ɗin, inda suka bar su Nu'aymah nan tsaye suna kallon kayan cike da jin daɗi da jan addu'ar alkairi ga wanda ya aiko ɗin. Suna a wajen tsaye baba malam da drivern nan suka sake figowa, a yanda sukaga fuskar baba malam ɗin yanzun sunsan ya amshi kayan shima. Umarni ya bama security ɗin nan akan a raka drivern har jikin store ɗin Orphanage ɗin a sauke kayan................✍


_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
_ANNUR PERFUMES: GIDAN KAMSHI KENAN.! WANI KAYA SAI AMALE! HAKAN TAKE, INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGATATTUN KAYAN TURARE NA GIDA DANA JIKI DANA KAYA NA MAIDUGURI? KU MATSO KUJI! NESA TAZO KUSA, ANNUR PERFUMES. KAMFANIN TURAREN MAIDUGURI NE DA RESHEN SA KENAN JIHAR KANO. MUNA DA KOWANE IRIN SAMFURIN KAYAN KAMSHI KAMAR SU; TURAREN WUTA NA KAYA DANA JIKI DANA TSUGUNNO, MUNA DA KHUMRAH, KULACCAM GANGARIYA DA ALMISKI(THAHARA/AYSHA/BAKI DA JA) MUNA DA DECORATIONS NA TSINTSIYA DA SAURAN SU, AKWAI KAYAN MATA INGATATTU MAI SA KISHIYA KWAFA, BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNADA KAYAN MATSI YAN GASKE, NAMU BA IRIN NASU BANE. _

_DUKA WADANNAN JERIN TURARUKA MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYI ‘DAI DAI. ADIRESHEN MU; MUNA KANO, UNGUWAR GAIDA, LAYIN MASALLACIN IMAMU MALIK. LAMBOBIN TARHON MU: 07086341096/07069036534. MUNA AIKA KAYAN MU KO’INA A FADIN NAJERIYA, KAMSHI RAHAMA NE YAN’UWA, MUSANMAN KAMSHIN ANNUR PERFUMES DAKE SANYA NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI. GA ARHA GA LAGWADAR KAMSHI SAI ANNUR PERFUMES_

____________________________

13

.................An gudanar da gagarumar walimar aure da saukar alkur'anin marayun ALLAH da waɗanda son zuciya ta saka iyayen nasu ajiyesu saboda gudun abin kunya. Sai kuma UBANGIJI mai rahama yay musu gata ta hanyar waɗanda basusanma sanda kikaje kika aikata ɓarnanrba.
     An sha wa'azi mai ratsa jiki ga manyan malamai, tare da addu'oi ga waɗan nan yara. Sai ƙyaututtuka daga manyan mutane ta hanyoyi da dama. Al'amarin dai sai muce Alhmdllh. Sosai su baba malam da ƙannensa da Hajjo harma da iyalansu suke cikin dunbin farinci da zagayowar wannan rana a garesu, dan kuwa ba itace ta farko ba, dan wannan shine karo na bakwai da zasu aurar da yara a cikin wannan gida. Al'amarin kam ya burge mutane matuƙa, inda wasu sukaji inama sune da wannan ƙyaƙyƙyawar zuciyar haka irin tasu baba malam. Yayinda wasu kuma suka ɗauki ɗammarar shigowa cikin tawagar a dama dasu da iya abinda ALLAH ya hore musu suma. Komai ya ƙaytar, dan ya tafi cikin nutsuwa, sarki ya bama waɗanan yara ƙyaututtuka, hakama Gwamna daya turo wakilinsa dan shi bai samu damar zuwaba ya dai bada tashi ƙyautar ga waɗannan angwaye da amare.
          Su Nu'aymah ansha kaikawo, dan kuwa sunyi tiɓis kamar sune amarorin. Bayan an tashi daga walimar da ƙyar suka rarrafa masaukinsu suna maida numfashin wahala. Su dai su Umm sunbi mazansu sun koma gida kamar yanda sukazo tare. Su Nu'aymah d Hajjo kuwa suna nan sai sunga ƙwal uwar daka.

________________________
  
           Bayan sallar isha'i baba malam ya tattara ƴan uwansa su duka uku a falonsa. A tare sukaci abincin dare, tare da tattauna yanda walima ta tafi cikin aminci da farin ciki babu wata matsala. Sunyi godiya ga UBANGIJI da ya zamemusu garkuwa, sannan baba malam dake tsaye akan komai.
     Ɗan murmushi kawai yayi batare da yace dasu komai akan hakanba. Kafin cikin nutsuwa ya nuna musu leda ruwan ƙasa da aka kawo ɗazun kafin walima tare da kayan abinci. Kasancewar bai samu zama dasu ba ɗazun sai bai sanar dasu komaiba ya bari sai sun dawo gida suyi maganar a tsanake sannan su duba abinda ke a ciki.
     Abba Musbahu da ya kasance ƙarami shi baba malam ya mikama ledan yana faɗin, “Musbahu buɗe muga minene a ciki, dan shi manager ɗin kamfanin da aka kawo kayan ta hanyarsu yace dukkan bayanan da muke bukata zamu samu anan. Amma mu kwantar da hankalinmu wanda ya bada ɗin baiyi da wata manufa ba, kuma shi yayine badan musan wanene shi ba, idanma muna tsoron wani abune to duk abinda mukaga be kwanta mana a raiba ko wata matsala ta biyo baya to mu nemesa shi, zai kaimu ga mai saƙon idan buƙatar hakan ta taso”.
      A tare sukace masha ALLAH, ALLAH ya sakanka masa da alkairi, ya biyasa da sakamakon abinda yafi wanda yayi. Shima ALLAH ya faranta masa fiye da yanda ya farantama mabukata.
      “Amin". baba malam ya amsa musu, yayinda Abba Musbahu ya fiddo abinda ke naɗe cikin leda mai ƙyalƙyali. Buɗe ledar yayi sai ga madaidaicin kwali ya bayyana. ya buɗe kwalin shima. Sun sami envelope guda biyu, ta farko check na kuɗi da suka basu mamaki fiye da zato. Dan a irin wannan halin da ake ciki mai bada ƙyautar irin waɗanan kuɗi masu yawa haka ai dole a jinjina masa. Sai zungureriyar wasiƙa, wadda bayanan cikinta ke magana akan su bada sunan yara talatin na gidan marayun da suka ƙare sakandire, ya ɗauki nauyin karatunsu na jami'a harsu ƙare, maza 15, mata 15. sai sunan kuma wasu ashirin din, maza 10 mata 10 sukuma waɗanda suka kare karatun zai nema musu aiki. Daga ƙarshe yace yana roƙonsu alfarmar sakashi cikin jerin mutane da zasu dinga hidima ga wannan gidan marayu gwargwadon ƙarfinsa.
         dukansu ajiyar zuciya suka shiga saukewa na mamaki da al'ajabin wannan mai saƙo. Kafin su shiga ja masa dogayen addu'oi, daga ƙarshe suka tattauna sosai akan lamarin. Sun yake shawarar faɗama UBANGIJI akan lamarin. Idan alkairine kuma mai wannan ƙudiri bada niyyar cuta musu ya zoba ALLAH yay riƙo da hannayensu gaba ɗaya. Idan kuma da wata manufa tattare da shi ALLAH yay musu maganinsa tunkan ya samu damar shiga jikinsu balle ya cutar da bayin ALLAH.
     Daga haka suka tashi akan zasu mikama UBANGIJI kukansu tsahon kwanaki uku, inda zuciyarsu ta karkata akan al'amarin zasu ɗaukesa a matsayin shine zaɓin da ALLAH yay musu, saisu yanke hukunci akan hakan. zasu cire kuɗaɗen daya rubuta ɗin a maidasu asusun gidan marayun.  bayan an gama ƙurar ɗaurin auren gobe idan ALLAH ya kaimu kuma saisu tantance yaran daya buƙata game da cigaban karatunsu da kuma waɗanda za'a nemarwa aiki.

*_ABUJA_*

               Bayan tafiyar Yoohan da kamar awa biyu sai ga papa da tawagarsa shi kuma ya dawo gida. Dama sunje taron manyan fastocine daya gudana a jihar Lagos, yau kwanansu biyar kenan a can. Ya samu tarba daga iyalansa da ma'aikatan gidansa, inda madam Chioma ke maƙale da shi har sashensa tai masa rakkiya.
       Bayan ya ƙimtsa ya fito sukai zaman yin lunch su duka a dining, sosai suka cika falon da surutu kamar ba abinci suke ciba, kowa na bama papa labarin abinda ya faru da baya gida. A cikin surutun nasu ne Abraham ke faɗama papansu an fasama Brother Yoohan motarsa a kano.
     Cak Papa ya tsaya daga cin abincin yana kallon Abraham ɗin, kafin ya maida kallonsa ga Madam Chioma da a lokaci guda ɓacin rai ya mamaye fuskarta. “Mi naji Abraham na faɗa Darling?”. Kanta ta jinjina masa tana ɗan karta cokalin hannunta akan filet ɗin abincinta, “Hakane Honey, jiya da yaje Kano abin ya faru, dama jira nake ka dawo asan matakin daya dace a ɗauka, shiyyasa bance masa komaiba dan karya ce bayaso ayi komai dan kasan halinsa dai”.
      Ɗan dukan table ɗin papa yayi da ture kofin da aka zuba masa lemo ya faɗi. A tare yaran duk suka zabura dan tsorota. Ya miƙe a fusace yana faɗin, “Miyasa tun a jiyan baki sanar minba, Gebrail ka tattaramin guards ɗin Yoohan gaba ɗayansu yanzun nan”.
            Cike da jin daɗi Gebrail ya amsa ma papa yana miƙewa. Dan shima burinsa a ɗauki matakin dama.

      Cikin mintuna ƙalilan guards ɗin Yoohan suka taru a falon, kallo guda zakai musu ka fahimci hankalinsu a matuƙar tashe yake. Musamman da suka shigo falon suka iske Papa nata kai kawo rai ɓace, kai kace gadin wani abu ya keyi. Sunkai tsayuwar mintuna goma kansu a ƙasa kafin ya kallesu da jajayen idanunsa.
         “Inaga baku da wani amfani game da tsare lafiyar Yoohan, zamu sallameku mu canzaku da waɗanda zasu iya, dan na inhar kune zaku cigaba da kulamin da yaro wataran sai an masa yankan rago kuna kallo baku iya yin komaiba akai”.
     Cikin ƙololuwar tashin hankali suke bashi haƙuri da roƙonsa. Suka ɗora da faɗin, ba laifinsu bane suma, boss ɗin nasune ya hanasu kowanne irin yunƙuri akan yarinyar. Kuma suna isowa sukaima Madam bayanin komai da ya faru....
      Tsawa papa ya daka musu wadda ta sakasu yin shiru lokaci guda. “Idan ya hanaku ɗaukar mataki miyasa bazaku kirani tun a lokacin ku sanar mini ba?! Tunkan ku fara aiki ban sanar muku duk randa kukayi kuskure wani abu ya faru da yarona abakin aikinku ba?”.
        Ka faɗa mana sir. Suka bashi amsa kowanne rai a dagule a tsorace kuma. 
     Hannu yasa ya bugi kujerar gabansa, “Oh shine kuma baku tuna wannan dokarba?!!”.
         Madam Chioma dake bayansa ta kama hannunsa ta riƙe cikin nata tana ɗan murzawa alamar lallashi, dan bata buƙatar a sallami guards ɗin, itama suna mata nata aikin ne daban. “Darling relax, kasan halin Yoohan ɗin namu ai, kai musu afuwa su kiyaye gaba kawai. Sai kuma musan abinda ya dace a ayi, idan aikawa za'ayi a kamo mana yarinyar shikenan, dan bana goyon bayan a barta”.
        Iska ya furzar daga bakinsa, ya zare hannunsa daga nata ya zagaya cikin falon sosai ya zauna a kujera. Kwalba dake a saman ƙaramin tray ya ɗauka ya tsiyaya abinda ke a cikinta a kofin glass ɗan ƙarami da shima yake a kan tray ɗin. Gaba ɗaya ya juye a baki yana ya mutsa fuska, kafin ya ajiye kofin ya kallesu ɗaya bayan ɗaya.
        “A ina abin ya faru?”.
“A ƙofar gate ɗin wani orphanage ne sir, kuma muna ƙyautata zaton yarinyar itama ƴar gidan ce, dan ciki boss yasa muka shiga akai treatment ɗin yaron”.
        “Daga nan zuwa safiyar gobe ku tabbatar wannan yarinyar tana nan cikin abuja, inba hakaba a bakin aikinku”.
        A tare suka saki murmushin jin daɗi, dan koba komai suma dama ƙulle suke da yarinyar, da kuma takaicin hanasu ɗaukar mataki da Yoohan yayi jiya. Yanzukan sun sami damar cin ubanta dai-dai gwargwado. Cike da girmamawa da alƙawarin yin abinda papan ya sakasu suka amsa. kafin ya basu izinin barin falon.

      Ko cikakken mintuna ashirin basu ƙaraba a gidan suka ɗakko hanyar kano duk da kuwa a lokacin ƙarfe ɗaya na rana ya gota. 

      Tofa, ana wata ga wata kenan😳😳 .

_____________________
*_NU'AYMAH_*

            A ɓangaren su Nu'aymah suma a washe garin wannan ranar bayan sakkowa sallar juma'a a massallacin aka ɗaura auren yara talatin da shida dake a gidan marayu na ƊAN JIBIYA FAMILY. Inda bayan kammala ɗaurin auren aka rakasu da addu'oin fatan alkairi kuma. 

         Da yamma su Nu'aymah suka ɗanyi shagalinsu iya mata a sashen matan, suma mazan anguna sukayi nasu a sashensu tare da sauran angunan da ba'a gidan marayun suke ba suma. Bayan sallar la'asar kusan ƙarfe biyar da tai dai-dai da isowar tawagar guards ɗin Yoohan gidan marayun aka kwashi amare gaba ɗayansu aka miƙasu ɗakunan mazansu, bisa rakkiyar iyayensu su baba malam. bayan doguwar nasiha da sukasha daga garesu tamkar yanda mahaifa kema ƴaƴansu idan zasu miƙasu gidan miji.
        Duk wani jan ido da barazanar Guards ɗin Yoohan securitys sun hanasu shiga cikin Orphanage ɗin, acewarsu sai dai su faɗi miya kawosu anan gate, idan sunga da damar barinsu su shiga shikenan, idan sunga babu damar hakan kuma sai dai su juya. Ran guards ɗin ya ɓaci matuƙa, sunji kamar su harbesu kowama ya huta. amma sai suka danne sukai musu bayani akan abinda ya kawosu, tare da tabbatar musu suna tare da ƴan sanda.
      Duk da securitys ɗin gidan marayun sun gane wa ake nufi da kuma miya faru jiya sai suka nuna bama su ganesuba, dan a ganinsu bai kamata su bada damar da za'aci zarafin ƴa ɗaya tilo ga wanda bai taɓa gajiyawa wajen musu hidimaba. Sun kaɗasu dambu taliya sunce basu gane Nu'aymah ba, su bama susan anyi wani abuba.
     Ran guards ɗin yayi ƙololuwar ɓaci, sai dai ɗaukar mataki ya gagaresu, dan suma securitys ɗin gidan marayun bawai kanwar lasa bane. Sun san taɓasu babban bala'ine ga ogan nasu papa balle su ɗin karan kaɗa miya. Dan haka suka bar orphanage ɗin ransu a ɓace, akan zasuje su sake shiri gobe su dawo.
     Hotel suka kama, kafin su kira papa su sanar masa da komai daya faru.

★★★★

         Su Nu'aymah da basusan wainar da ake toyawaba ana kammala miƙa amare baba malam yasa Yah Ahmad ya tattara masa su aka wuce dasu gida badan sunso hakanba. Dan so sukai sukam sai sunyi sati ɗai-ɗai a gidan kafin su koma gida. Sai dai baba malam ya ɓata musu shirinsu.
     Aiko koda suka koma gidan sai suka dinga fushi da kumbure-kumbure. Kayan biki da baba habi ta haɗa musu ma sunƙi kulawa. Babu wanda yabi takansu a gidan, saisu Kubrah ne ma ke musu dariyar tsokana suna sake ƙulal dasu dan duk suna sashen Hajjo ne da suka dawo tare.

____________________

     
         Gaba ɗaya ran guards ɗin Yoohan a ɓace yake, tunda suka iso hotel ɗin da suka kama basu zaunaba, sai faman ƙulle-ƙullen yanda zasu sami Nu'aymah da matakin da zasu ɗauka a kanta sukeyi. Kai kace wata babbar ƴar ta'adda suke bibiya.
      Sun ƙulla yafi sau hamsin suna warwarewa. Suna tsaka da sake ƙullawa saƙo ya iso garesu daga hannun ɗaya daga ma'aikatan hotel ɗin. Number wayace daga wani, ya basu damar su kirashi idan suna buƙatar sanin inda wadda suke nema take..  
             Da yake burinsu kenan jiki na ɓari suka kira kuwa. Ba'a ɗagaba har sai da ta kusan tsinkewa. Ƙinyin magana akayi. sai da ɗaya daga cikin guards ɗin ya fara magana. 
      “Duk da bamusan ko wanene ba, mun maka alƙawarin inhar ka sanar mana inda yarinyar take zamu biyaka da kuɗi masu nauyi, oganmu ma zai maka ƙyauta ta musamman”.
       Batare da an basu amsaba aka yanke wayar. Kallon juna suka shigayi tambayoyi fal ransu. Kafin ɗayansu ya iya furta wani abu sai ga saƙo ya shigo. Da sauri suka buɗe ganin Number da suka kira ɗince. Ba komai bane a saƙon face cikakken address ɗin gidansu Nu'aymah, da sunanta harma da hotonta.
    Daɗine yay mugun kamasu, dan kuwa sun sake tabbatar da itaɗince, dan haka jiki na rawa suka sake kiran wanda ya tura musu ɗin. Yanzun ma dai baiyi maganaba, sai sune suka buƙaci ya turo musu accaunt details nashi ko nata zasu tura masa ladan aikinsa. Ƙitt aka yanke wayar batare da ance komaiba. Mintuna kaɗan kuwa saiga accaunt Number an turo. A take suma sukaima papa massege bayan sun kirashi sun sanar masa komai. 
             
     Har a lokacin cike yake da ɓacin ran abinda ya faru, dan yaje yaga yanda akaima motar bugu na fitar hankali, shiyyasa ransa ya sake ɓaci, ya kuma tabbatarma kansa ko ɗiyar uban wacece yarinyar sai ta yabama aya zaƙinta.
           Babu ko tantama ana turo masa accaunt details ɗin ya antayama maishi kuɗi masu tsoka, dan a ganinsa bukatarsa ta biya. Mizaisa yaji ciwon biyan wanda ya taimakesu.

________________________________
*_NU'AYMAH_*

               Yau sama-sama Nu'aymah ta wayi gari, dan ta tashi da ciwon ƙafa alamar zuwan period ɗinta. Ita dama takan fara da ciwon ƙafane, randa yazo kuma zataita amai har saita jigata. Kafin daga bisani ta koma normal sai shegen ƙwaɗayi kamar taci mutum ɗanye.
      Tunda Umm ta shiga tadasu sallar asuba ta lura batajin daɗi, dan maimakon kwance saita isketa zaune ƙasa a bakin gado kan kafet ta kife kanta a kan gadon. Yusrah da Amal nata barcinsu a kan gadon su. Ita ta fara tadawa kafin su Amal, har zata juya ta fita sai kuma ta dakata ta kalli Nu'aymahn data maida kanta ta kife tsakanin ƙafafunta.......
      “Ke kuma lafiya?”. Da ƙyar Nu'aymah ta ɗaga kai ta kalli Umm, sai dai gudun kar ace ta shirya aje asibiti a mata allura sai ta daure tace, “Umm lafiya lau, kawai gajiyace tasa ƙafafuna ciwo”.
      Ɗan ƙura mata idanu Umm tayi na wasu mintuna, kafin ta janye tai ficewarta batare data sake cewa komaiba. Yusrah ce ta ƙaraso wajen Nu'aymah ɗin ta durƙusa. “Baby ƙarya kikaima Umm wlhy, daga gani baki da lafiya”.
    Yamutsa fuska Nu'aymah tayi kaɗan tana maida ƙwallar data cika mata ido. “Ƙafafuna ke ciwo wlhy Yusrah, nasan kuma period ɗinane zaizo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ko anjima”.
         Amal dake fitowa daga bayi tace, “To miyasa kikaƙi faɗar gaskiya?”. Yusrah data harbo jirgin Nu'aymah tai saurin cewa, “Allura”. A tare suka kwashe da dariya ita da Amal. Nu'aymah kuma tai tsaki idonta cike da ƙwalla ta miƙe. Da ɗingishi ta shiga bayi batare data kula dariyar dasu Yusrah ke mataba har yanzun.
  
       Bayan sun idar da salla Yusrah da Amal suka fice taya iyayensu aiki, Nu'aymah kam saita koma saman gado ta kwanta. Babu jimawa barci yay gaba da ita.

     Umm da duk ta gama fahimtarta bata nemeta ba, dan tasan zata gama zagayenta ne tazo ta nemeta. Bayan sun kammala breakfast ita da ƴan aiki ta shirya na baba malam da sauran ƴan uwansa a falonsa da kanta kamar yanda ta saba inhar duk suna gari, dan tare sukecin abincin safe da dare. Na rana ne dai bai zama dole su dukansu suna a gidaba shiyyasa. Garama idan ta kama juma'a ace dan duk basa zuwa ko ina a wannan ranar sai massallaci.
        Sai da taga komai ya mata yanda takeso sannan ta saka turaren wuta ta leƙa bedroom ɗinsa. Yana wanka, sai kawai ta buɗe Wadrobe ɗinsa ta zaɓo masa kayan da zai saka, saboda yau zasuje taron wani wa'azi a jihar katsina. Bayan ta ajiye masa duk abinda tasan zai buƙata ta fita zuwa ɗakin Muhammad danta taimaka masa yayi shirin makaranta shima.

*_08:15am_*

       Kusan takwas da kwata su baba malam suka hallara a falonsa shi da sauran ƴan uwansa domin karyawa. Sun sake gaisawa cikin girmamawa kamar yanda suka sabama kansu. Kafin su zauna su fara karyawa abin cike da birgewa.
     Sunyi nisa da cin abincinsu sukaji sallama. A tare suka amsa idonsu akan ƙofar. Ƙarasawa ciki falon Abbas da yay sallamar yayi. Ya durƙusa har ƙasa ya gaidasu. kafin cikin damuwa yace, “Abba ƴan sandane ke sallama”.
       “Ƴan sanda kuma Abbas? Lafiya dai ko?”. Baba malam dake kallon Abbas babu ko ƙyaftawa ya faɗa.
       “Abba ban saniba wlhy, amma sun nuna wai an turosu su tafi da Nu'aymah ne”. 
       Ran Abban Adawiya a ɓace yace, “Wace irin Nu'aymah kuma? Miya haɗata da ƴan sanda banda shashanci irin naka Abbas?”. “Wlhy Abba haka sukace, dan hotonta ma suka nuna”. Miƙewa sukai su duka huɗun, sai dai su uku suka fara fita, kafin baba malam yabi bayansu..............✍

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.b



________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* 

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

_______________________________

14

.................A tare suka fito harabar gidan, inda suka iske matan gidan da sauran samarin da basu kai ga ficewa sabgoginsu ba duk sun fito suma. 
      Suna ƙarasawa ga ƴan sandan Nu'aymah da Amal taje ta kira itama sai gata ta fito tana ɗan ɗingisa ƙafa. Sanye take da siket da riga na atanfa, sai ƙaramin hijjab da Umm ta sabar mata da sakawa a cikin gidan saboda samarin gidan tunda ba muharramanta bane ba.
       Tunda su Baba malam suka fito jikin wasu a cikin police ɗin yayi sanyi ganin dai da gaske an turosune gida mai daraja kamar wannan dan suyi abinda basu da tabbacin faruwarsa tunda ba'a gabansu akaiba. To amma yaya zasuyi, d.p.o ne da kansa ya sakasu zuwa su kama Nu'aymah, ga kuma kuɗaɗe da sukaci har kashi biyu daga Papa da kuma guards ɗin Yoohan na toshiyar baki. (Ya rabbi ka tsaremu cin rashawa da bada ita. Amin🙏🏻😭).
        
     Sun gaisa dasu Abba cikin girmamawa, kafin su sanar musu daga station ɗin da aka turosu da kuma abinda zasuyi. Kusan a tare su Abbah duk suka juya suna kallon Nu'aymah. Baba malam ne kawai kansa a ƙasa yana ɗan murmushi. Batare da yace komaiba ya nufi inda jama'ar gidan ke tsaitsaye suma suna kallonsu hankali a tashe.
       Hannun Nu'aymah ya kama batare da yacema kowa uffanba. Itama kuma babu musu ta bisa har wajen ƴan sandan. Ya miƙama macen hannun Nu'aymah yana faɗin, “Itace wannan?”.
        Kallon hoton dake a waya babban nasu yayi, kafin ya kalli Nu'aymah. “Eh itace ALLAH ya gafarta malam”. Ya faɗa cike da girmamawa ga baba malam. Murmushi baba malam yay musu yana nuna masu Nu'aymah dake kallonsa kamar wata sokuwa. “Gata nan, zaku iya tafiya da ita”. Da sauri Abban su Abdallah ya yunƙuro zaiyi magana baba malam ya ɗaga masa hannu fuska a ɗaure. Cak ya tsaya hankalinsa a ƙololuwar tashe. Hakama su Abban Adawiya hankalin nasu a tashe yake da hukuncin da baba malam ya shirin yankewa. A ganinsu ai basai anje station ba, zasu iya tsayawa su tattauna anan, musamman ma shi Abban Adawiya da yana cikin Orphanage randa abin ya faru. Kuma an sanar masa komai akai.
        Godiya ƴan sanda sukai tare da juyawa da Nu'aymah zasu tafi. Tirjewa tai tana kallon Baba malam daya ɗauke kansa gaba ɗaya daga garesu tamkar baisan mi akeyiba. Hannunta ta fara ƙoƙarin fisgewa idanunta na cika da ƙwalla. “Abba wlhy bansan mina musu ba”. Tai maganar muryarta na rawa. 
     Juyawa baba malam yayi zai bar wajen batare daya kula maganar Nu'aymah ba. Sai da yay taku biyu uku sannan ya tsaya tare da juyawa ya kalli ƴan sanda da Nu'aymah data fisge zata dawo. Cikin tsananin kaushin murya yace, “Idan bazata biku da arziƙiba ku ɗauketa!!”.  
     Tsayawa Nu'aymah tayi cak tana kallon baba malam ɗin. Sai kuma ta kalli inda su Umm suke. Sake dawo da idonta tayi kan ƴan sandan da suma ita suke kallo. kunyar baba malam ce kawai ta hanasu fara cin ƙaniyarta tun anan. Tsaf ta haɗiye kukanta. Ta juya cikin ɗingishi ta nufi ƴan sandan. Basuce mata komaiba suka tasa ƙeyarta gaba suka fita waje inda motarsu take.
      A gaban ƴan anguwa daketa kai kawo aka sakata a motar ƴan sanda. Gaba ɗaya hawayen da Nu'aymah ta fara ɗazun sun ƙame ƙaf. Ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta tai shiru. Sai faman cije baki kawai take saboda zugi da ƙafarta ke mata. Har suka isa police station ɗin bata ɗagoba. Sai da ƴar sandar ma ta taɓata sannan ta san sun iso. Ɗago kanta tai a hankali ta kalli station ɗin, sai kuma ta juya ga ƴar sandar dake mata kallon tausayi. Dan ita yanda taga mutanen na hanƙoro akan yarinyar ta zata ma wata tsohuwar macece, ashe yarinyace ƙarama. Itace ta taimaka mata ta fito, ta kama hannunta ganin kamarma ta kasa tsaiwa. A haka suka shiga cikin station ɗin da taimakon ƴar sandar. 

  
         “Amma Yaya ka.......” hannu baba malam yay saurin ɗagama Abban su Adawiya dake son masa bayanin ainahin abinda ya faru. Ya kallesa fuskarsa babu wasa, “Banason jin komai akan hakan Mustapha. Kaje ka shirya mu wuce banason yazam mu ake jira”.
     Kai kawai Abban su Adawiya ya kaɗa masa. Kafin ya kalli su Abba Musbahu ya bar wajan jiki a sanyaye. Da sauri su Abban Abdallah suka nufi mota da nufin bin bayan su Nu'aymah, sai kawai a bazata suka tsinkayi muryar Baba malam na faɗin, “Na haramtawa kowa bin bayanta a cikin gidan nan, idan kuma wani ya aikata koda ban saniba zai fuskanci fushina”.
     Cak suka tsaya daga yunƙurin shiga motar, kowannensu goshinsa na tara zufa. Babu wanda ya iya sake cewa komai har Baba malam ya shiga sashensu ya fito cikin shirin fita. Ta gabansu ya wuce zuwa sashen Hajjo data sha maganin mura tun ɗazun ta kwanta. Duk wainar da ake toyawa bata saniba dan barci takeyi. Baifi mintuna biyarba sai gashi ya fito.  Yanzunma bai kalli sashen da kowa yake ba ya nufi inda motar da zasu tafi take, sauran motocin uku da ɗalibansu zasu shiga da ƴan agaji kuma duk suna a harabar massallaci. 
     Suna kallo motar ta fice batare da ko mutum ɗaya ya iya cemasa a dawo lafiya ba, shima kuma bai nuna ya damu da hakan ko jiran cewar tasu ba.

      Umm ce ta fara sulalewa ta koma ciki, kafin sauran suma su fara zare jiki ɗai-ɗai suna shigewa sashensu. Addah dai bayan Umm tabi tana share hawayen da ke sakko mata batare data farga da fitowarsu a cikin idanunta ba.

_____________
*_ABUJA_*

        Tunda labarin kama Nu'aymah ya isa kunne Papa farin ciki ya mamayesa shi da Madam Chioma, breakfast da suke shirin zamanyi ma su kasawa sukayi, sai kai kawo sukeyi zuciyoyinsu fes kamar an basu rabin duniya. 
    Dolene yasa a koyama yarinyar hausawan nan hankali, dan shi a rayuwarsa idan da abinda yafi tsana a rayuwarsa to ƴan yankinta ne. Ya tsani yarenta fiye da mutuwarsa, a cewarsa babu abinda suka iya sai haihuwa, ƴaƴan nasu kuma babu tarbiyya sam, daga ƴan bangar siyasa sai masu bara. Sam mutanen da yankinsu basu masaba, inda ace zai iya zama shugaba, sai ya shafe yankin ko tarihinsu baza'a sake aji ba. (hummm Papa, a ringa sara dai ana duban bakin gatari).
           Abinda papa ya keta faman rayawa a ransa kenan yana murmushi. Waya ya sake ɗagawa yay magana da d.p.o ɗin akan yanzunan a bama guards ɗin Nu'aymah su taho masa da ita Abuja. Shi kuma d.p.o ya turo da accaunt Number ɗinsa yanzu zaiji alert.
        Cike da farin ciki d.p.o ya amsama papa. Babu ko tunanin komai a ransa ya aika da accaunt details nashi, ya kumayi zaman shirya takardar ƙarya akan laifin da bashi Nu'aymah ta aikataba.

(Humm! Ya ALLAH ka shiryemu ka shiryi shuwagabannin mu da jami'anmu. Ka tsame bara gurbin cikinmu, idan masu shiryuwane ka shiryesu. Idan bazasu shiryuba UBANGIJI kafimu sanin miya dace dasu, mun barka dasu😭🙏🏻).

________________
*_LAGOS_*

         Fitowarsa kenan daga ɗakin theatre a matuƙar gajiye. yanda yake tafiya kawai zai baka wannan amsar. Tare yake da likitoci uku da suka tayasa aikin, sai Nurses suma guda uku. Dai-dai sun ƙaraso ƙofar wani office nurse ɗin dake a gefen damarsa ta miƙa masa tasar hannunta ya jefa hand gloves ɗin daya cire daga hannunsa ya jefa a ciki, hannu ya ɗaga musu kawai alamar su dakata anan ya tura ƙofar ya shige.
       Basu damu ba, dan kowa yasan Dr Yoohan haka yake, mutum ne mai ƙoƙari akan aikinsa da himma, ga tausayi sosai musamman ga marasa ƙarfi. Bashi da yawan magana, sannan baida fara'a. Wanda bai fahimcesa ba zaita ɗauka kamar kullum shi cikin ƙuncin rayuwa yake, kokuma girman kaine bisa ga ɗaukakar da ALLAH ya basa. Idan kuma ka fahimcesa zaka gane cewa haka halayyarsa take, shi kawai aikinne a gabansa ba shiririta da shashanci ba. Akance likitoci mafiya yawansu sunada son mata, sai dai ga Dr Yoohan sam ba haka baneba. Duk yanda matan ke binsa da soyayya shi bama su ishesa kalloba, shi fa a rayuwarsa damuwarsa kawai shine aikinsa, sai ko family ɗinsa da taimakon marasa ƙarfi. Idan ya shiga cikin musulmi bazaka taɓa cewa shi ba musulmin bane, musamman daya ajiye ƙasunba da yanda yake gudanar da al'amuransa sak halayyar musulman ƙwarai. Sai dai fa idan kaci karoda sarƙar Cross a wuyansa da akoda yaushe baya fashin sakawa ne zaka gane daga ina ya fito. ALLAH ya ɗaukakashi a duniya a dalilin ƙwaƙwalwar aikin likitanci daya azurtashi da ita, likitane shi da kota wane fanni zai iya gunar da aikinsa akan mara lafiya, sai dai abinda ba'a rasaba kam, dan UBANGIJI shine mai komai da kowa.

         Office ne daya amsa sunansa office. Bakajin komai sai sassanyan ƙamshin turarensa dana ac. Wanda ke zaune a rikunin kujeru uku dake can gefen office ɗin yana aiki ya miƙe yana masa barka da fitowa cike da kukawa.
     Kansa ya ɗaga masa fuska a yamutse na alamar gajiya. kafin ya ƙarasa ga kujerar zamansa yaja wani file dake a jiye ya fara singing.
      Tasowa Richard yay da sauri garesa yana murmushi, ya ajiye files ɗin hannunsa gaban Dr Yoohan ɗin yana faɗin, “Doctor akwai mutane biyu da zaka ganifa yanzun kafin ka tafi hutun awa uku da rabi, idan lokaci ya cika zaka sake shiga theatre room, na mutane biyu da suka rage suma”. Da sauri Yoohan ya ɗago yana kallon Richard fuska a marairaice kamar zai fasa kuka. Richard yay saurin haɗiye dariyar dake neman kufce masa dan yasan shima da gaske Yoohan ɗin ya kai iyakar gajiya, amma sai ya fiske yace, “Da gaske nake Yoohan, gama files nasu na kammala dubawa”. 
          “Rich.. Please, wlhy na gaji, sai dai kai ka dubasu” ya faɗa yana sauke numfashi da miƙewa ya nufi wata ƙofa. 
      Murmushi Richard yayi yana binsa da kallo harya shige. Ya ɗan girgiza kansa da kwasar files ɗin ya fice daga office ɗin zuwa nashi shima.
         ALLAH ne ya haɗashi da Yoohan tun a secondary school, a farkon haɗuwarsu sam basa shiri, dan abokan faɗan junane a aji. Ba komai yasa rashin jituwa tsakaninsu ba sai kasancewar su duka sunada matuƙar ƙoƙari, kafin Yoohan yazo school ɗin shike ɗaukar na ɗaya a ajinsu, amma Yoohan na zuwa ya amshe wannan matsayin. Kafin zuwan Yoohan ɗin kuma kowa sonsa da girmamasa yake a ajin, hasalima shine Monitor, ƴammatan ajin ji suke tamkar su haɗiyesa kuma. Amma Yoohan na zuwa nanma komai ya canja, kan ƴan ajin ya rabu biyu, wasu na ɓangaren Yoohan wasu Richard. Dan haka aka zama abokan dabin juna, duk da sam Yoohan baya kula duk haukarsu. Rashin kulawar Yoohan ɗin tasa a koda yaushe shi da tawagarsa suke ɗauka Yoohan matsoracine, dan babu wanda ya taɓa ganin faɗansa. Sai fa wataran da suka kaishi bango yayma Rich dukan mutuwa, da ƙyar aka karɓesa a hannunsa dan Yoohan akwai zuciyar tsiya. Tun daga wannan duka da Yoohan ya masa suka koma abokan juna, tun sauran ɗalibai na ƙalubalantar abotar tasu har suka fahimci ta gaskiyace suma sukabi. Shi da Yoohan duk burinsu ɗaya ne akan karatu, dan haka haɗewarsu waje guda ta ƙara musu himma da ƙwazo. Koda suka kammala secondary kuma cikin amincin ALLAH iyayensu suka amince musu tafiya karatu tare. A gaba ɗaya rayuwarsu tare ta gudana, sai daga bayane Yoohan daya cigaba da wasu kwasakwasai (Courses) ne suka ɗan rabu, danshi ya amshi aikin da aka bashine a ƙasar London bayan zamowarsu cikakkun likitoci, saɓanin Yoohan daya ƙi amincewa.
     Daga baya Yoohan ya kuma samun ɗaukaka fiye da tashi, danshi ya ƙara faɗaɗa wasu karance-karancen daya bashi damar iya duba marasa lafiya ta kowane fanni, aikinsa ya zam zai iya yinsa a kowacce ƙasa kuma. 
       Bayan shekara ɗaya da fara wannan gwagwarmayar Yoohan ya fahimci bazai iya shi kaɗaiba sai da taimakon Richard, dan haka yaje ya dabaibayesa da daɗin baki har saida ya amince suka sake curewa waje guda suke gudanar da aikin a tare. Yanzu haka shekararsu ta biyu kenan da fara aiki, suna ɗaya daga cikin manyan matasan likitoci da duniya ke alfahari dasu bama ƙasarsu ko yankin Africa kawai ba.
    A yanzu haka dai shi Richard ana shirin aurensa ma da wata baturiya, shiko Yoohan yaƙi motsawa sam, a cewarsa shi bama zaiyi aure yanzuba sai nan da wasu shekarun daya tsara.

           Ɗakine madaidaici dake ɗauke da kayan ɗaki complete, shima sai ƙamshi yakeyi kamar ba'a cikin asibiti ba. Kansa tsaye toilet ya nufa yana faman lullumshe idanu dan barci yake matuƙar ji. Tunda ya iso Lagos a daren jiya bai hutaba, dan ya iske patients da yawa da sukai booking ɗin ganinsa. Tun a jiyan yay dauriyar zaman duba files ɗinsu, waɗanda yasan akwai mafita ya rubuta musu Doctors ɗin da zasuje su gani ya turama Rich. Waɗanda kuma yasan sai shine zai duba ya sanar da Richard ya sanar musu time ɗin da zasu gansa ta hanyar text messeges.
       A safiyar yau tun ƙarfe huɗu na asuba ya baro gida, tunda yazo kuma aiki yake bai hutaba. Bayan ya gama duba adadin daya ƙayyade ya shiga theatre akan matsaloli daban-daban kuma, yanzunma ba ya gama baneba, yanada loacin hutawa ne na awa uku da rabi kafin ya koma ɗakin theatre ya ƙarasama mutane biyu dake a ƙasa kamar yanda Rich ya faɗa. Bayan ya kammala dasu zai ƙara hutun awanni uku jirginsa ya ɗaga zuwa ƙasar Kenya inda wasu patients ɗin ke jiransa canma.
            Bayan wasu mintuna ya fito daga toilet ɗin sanye da rigar wanka Blue, sai hular wanka data kare gashinsa daga jiƙewa, da alama dai baya buƙatar jiƙawar. A bakin gadon ya zauna yana mai furzar da iskar daya cika bakinsa da ita, yajawo wayarsa dake a drowar gefen gadon a jiye ya cireta a silent. Dan ya sakata a silent ɗinne tun lokacin dazai shiga theatre room. Solomon ya kira, sai akai rashin sa'a ya samu wayarsa a busy.
        Kume fuska ya sakeyi alamar baiso hakanba, ya ajiye wayar. ɗayar ya ɗauka itama ya cireta a plane mode daya sakata. Kamar jira ake ya cire ɗin sai ga kira ya shigo, kafin ya amsa kuma akai knocking ƙofar. Rasa wanne zai farayi yayi. Ɗaga wayar? Kokuwa buɗe ƙofar?.
       “Yoohan!” ya tsinkayi muryar Richard na kiransa. Duk da yayi tunanin akan maganar patients ɗin da Rich ɗin yay maganar zai dubane hakan bai hanashi tashi ya buɗe masa ƙofaba, sai dai ya sake haɗe fuska alamar da gaske ya gaji baison takura.
      Yana buɗe ƙofar yace, “Rich plea.....”
          Saurin katsesa Richard yay da faɗin, “Yi haƙuri ba wancan maganar bane, akwai damuwa Yoohan, matar da kaima aiki a kano yanzun nan Doctor Sa'ad ke sanar min an samu matsala”.
       “What?!” ya faɗa hankali tashe. Shima Richard da hankalin nasa ke a tashe ya shiga jinjina masa kai. Juyawa cikin ɗakin yay da sauri, yama manta da wata gajiyarsa. Wayarsa ya ɗauka domin neman Dr Sa'ad. Ganin ashe shinema ya kirasa ɗazun lokacin da Richard ke knocking ya sakashi kiransa. Bugu ɗaya kuwa Dr Sa'ad ɗin ya ɗaga. 
       Ko gaisuwa basuyi zaman yiba Dr Sa'ad ya shiga masa bayanin dukan abinda ya faru, da halin da matar ke a ciki yanzun.
        Hannunsa dafe da kansa cikin tsagwaron damuwa yace,  “Dr Sa'ad ta yaya hakan ta faru? Ince duk yanda ya kamata a bata kulawa na sanar muku. Miyasa kuke da sakaci akan rayukan mutane!!?” ya ƙare maganar da ɗan kaushin murya.
        Dr Sa'ad da maganar Dr Yoohan tai masa zafi ya buɗe baki zaiyi magana cikin ƙoƙarin danne fushinsa, amma sai Yoohan ɗin ya kuma dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Bana buƙatar jin komai please, zan turo maka hanyar da zakubi wajen fara bata taimako yanzun, nima ina hanyar tahowa”. 
       “Okay Sir” Dr Sa'ad ya amsa masa daga can cikin wata irin murya mai cike da ɗaci da takaici. Yaro ƙarami dashi yana juyasu dan kawai ALLAH ya basa baiwar da tafi tasu, tabbas idan ba kawar da Dr Yoohan sukaiba a duniya rayukansu da hanyar cin abinsu na a cikin garari. 
      (Ni dai nace Humm).

      Shi Yoohan baima saurari amsawar Dr Sa'ad ɗinba, dan tuni yayi wurgi da wayar saman gado cike da takaicin likitoci irin Dr Sa'ad, da a kullum basu da kishin ƙasarsu da jama'arsu, burinsu sudai kuɗi kawai da taƙama da aikinsu. Da hanzarinsa ya fito ainhin Office ɗin yana faɗin, “Rich Please ka bincika min idan akwai jirgi mai tafiya kano daga nan zuwa mintuna talatin”.
       Da sauri Richard ya fita daga office ɗin zuwa nasa, dan yabar wayarsa a canne. Shi kuma Dr Yoohan yaja Laptop ɗinsa dake saman tebirin daga tsaye ya shiga dannata da sauri sauri cikin ƙwarewa. A haka Solomon ya shigo ya samesa, batare daya tsayaba yay saurin shigewa bedroom ɗin domin fidda masa kayan da zai saka dan Richard ya sanar masa halin da ake ciki, kuma shi Dr Sa'ad ya fara samu a waya kafin Richard ma.
         Dr Yoohan na kammala tura abinda zai aikama Dr Sa'ad ya nufi ɗakin shima. bai wani damu da tsayawa duba kayan da Solomon ya ajiye masanba ya ɗauka ya fara ƙoƙarin sakawa, shi kuma Solomon ya fito ya bashi waje.
        Shirin yake ransa duk a jagule da takaici, yana kammalawa ya fito jacket ɗin suit ɗinsa a hannu, necktie ɗinma haka. Gashinsa kansa yau sama-sama ya samu gyara. Haka yake shi, a kullum matsalar al'umma itace tashin hankalinsa da damuwarsa. Da kaga damuwa a idanunsa to patient ɗinsa na cikin matsala ne. Baiko kalli inda Solomon ke tsaye da jikkarsa a hannuba ya nufi hanyar fita fuskarnan babu alamar wasa.
      Kusan cin karo sukai da Richard dake ƙoƙarin shigowa ya sanar masa an samu jirgi, kuma cikin amincin ALLAH zai tashi nan da mintuna goma sha bakwai ne, da ƙyar akama samu ticket ɗin guda biyu. A yanda Dr Yoohan yasan garin Lagos da yammaci irin haka yasan kafin su isa airport ma lokacin tashin jirgin ma ya wuce, dan haka ya yanke shawarar su tafi a Ambulance kawai zasufi samun hanya da sauri.
       Rich kansa yayi na'am da wannan tunanin na Yoohan, dan haka yama yanke shawarar kaisu da kansa ko Yoohan ɗin zai kuma samun nutsuwa.............✍

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________    
   *_SAUDIA_*

     .............Kai kawo taketa faman yi a falon nasu dake wadace da sanyin ac da ƙamshi kai kace safa da marwa take gudanarwa. Ta canja sosai, dan komai na jikinta ya ƙara girma da cika. Daman can duk tafi su Nu'aymah girman jiki kasancewar ta ɗakko jikin Addah. Yanzu kuma darajar aure saita sake bata damar buɗewa tamkar ba ƴar shekara goma sha takwas ba.
    Tabbas tana samun ci da sha da sutura duk irin wadda ta buƙata, sai dai a watanni tara kenan da aurenta da Yah Abdallah babu wata rana da zata ware ta dangantata da farin cikinta. Idan har ta samu kulawarsa to na wasu awoyine da zai biya buƙatarsa. Baya son zaman gidan sam, ita kanta har mamaki take da al'ajabin ina yake zuwa bayan makaranta da harkar kasuwancinsa?. 
         Duk yanda taso fahimta ko gano hakan ya gagara, babu kalar dabaru da maman Aaida bata koya mataba duk kuma ta bisu daki-daki amma ta gaza samun haske. A yanzu haka wata ƙura ta fahimta baibaye da ita game da mijin nata shine dalilin kaiwa da kawowar tata. 
       Tun daga randa Abdallah ya fara kusantarta ba'a cikin hayyacinsa ba a washe gari ya haɗata da wasu ƙwayoyin magani guda biyu. Daga haka kuma duk sanda zai kusanceta sai ya batasu ta sha. Tun bata taɓa kawo komai a ranta game dasu ba harta fara zargar wani abu. Ba komai ya kawo mata zarginba kuma sai haihuwa da akullum maman Aaida ke kawaɗaita mata ta sanadinta zata iya samun soyayyar Abdallah, tunda sunyi dukkan wasu dabaru yaƙi hawa network. Da farko Adawiya batason ta haihu yanzu, amma da taji wannan magana daga maman Aaida sai taji ƙwaɗayin hakan itama dan tana masifar son Yah Ab. To amma sai me? Har yanzu babu ciki babu alamarsa a gareta, har zuwa asibiti tayi a ɓoye aka dubata Doctor ya tabbatar mata inhar bata daina sha maganin hana ɗaukar cikiba bazata taɓa samun ciki ba.
      Wannan magana ta daki zuciyarta, dan a ɗan hasashenta ta fahimci kenan maganin da Yah Ab ke bata kullum na hana ɗaukar cikine? Duk da zuciyarta taƙi aminta da hakan sai taji tana ƙwaɗayin dubawa ta tabbatar. Wannan shine dalilin kai kawonta tana nazarin hanyar data dace tabi wajen binciken maganin a ɗakinsa batare daya saniba ko ya ganta. Saboda haka taƙi zuwa makaranta yau ta zauna gadin fitarsa. Sai dai kuma har yanzu bataji ko motsin alamar zai fitoba balle tayi tunanin fitar tasama kamar yasan mi take shirin yi....

(Humm muje zuwa baby Adawiya😉😂).

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

_______________________
________________________

          Dr Yoohan ya bama matar da yazo kano dominta dukkan gudumawar data dace har ALLAH ya bashi nasarar dai-daita komai da taimakon Dr Aysha. Sai dai fa Dr Sa'ad yasha masifa dan tabbas harda sakacinsa. Ba komai ya sashi sakacinba kuma sai kasancewar matar talakace, hasalima Dr Yoohan shine ya biya mata kuɗin aikin dukda kuma shine yayi aikin. Ya kuma bama marayun ƴaƴanta wasu ƴan kuɗaɗe tare da buƙatar takardun makarantar babban yayansu dake riƙe da gidan da ƴar sana'arsa ta saida ruwa a cikin kasuwa. ALLAH ya taimakesa tun mahaifinsu nada rai ya haɗa diploma ɗinsa da ƙyar da siɗin goshi. Wannan alkairi nasa a garesu ya sakasu cigaba da jera masa addu'oin fatan alkairi da nasara a rayuwarsa. Tare da fatan ALLAH yasa yanada rabo cikin addinin islama.
      Tunda Dr Sa'ad yaga Dr Yoohan ya wuce sai ya fara sakaci da kula da matar yanda ya kamata saboda takaicin ƴarta data bijire masa tun farko. Da farko shine zaima matar aiki akan matsalarta, ya buƙaci kuɗaɗe masu nauyi daga wajensu na aikin amma suka tabbatar masa basu dasu. Sunta roƙonsa ya taimakesu ko rabi su bada kafin ta warke sai su cika ya nuna bazai iyaba, sai kuma ya koma ta bayan fage ya nema yarinyar matar akan inhar zata bashi kanta shiko zaima mahaifiyarsu aiki ƙyau bama sai sun biyaba. Itako tace bazata aminceba, dan ran mahaifiyarsu a hannun ALLAH ya ke, sun kuma dogara da shi.
       Wannan shine farkon matsalar. Lokacin da Dr Sa'ad ke bibiyar yarinyarnan saiko karaf a kunnen Dr Aysha, hakanne yasa ta koma a ɓoye ta kira Dr Yoohan da roƙon ya taimaki yaran inhar yanada halin yin hakan. Da yake tasan yana Abuja yana hutun kwanaki uku. Sanin ƙyaƙyƙyawan halin Dr Aysha ya saka Dr Yoohan yarda ya baro Abuja ta mota ya nufo kano. Da taimakonta sukaima matar dukkan hidima, ya tafi yabar amanar kulawarta a hannunta ita da Dr Sa'ad. dan Dr Aysha ta ɓoyema Yoohan sunansa dan kare masa mutuncinsa.
         Da Dr Sa'ad ya fahimci Dr Aysha ta ɓoyema Dr Yoohan sunansa da ainahin gaskiya sai yay shirin ɓata aikin da akaima matar saboda jin zafin rashin haɗin kai da bai samuba na yarinyarta. Dr Aysha dake taimaka musu kuma data fahimci hakan ta tabbatar masa saita sanarma Dr Yoohan ɗin komai. Wannan shine yay masifar tada hankalinsa kafin ta sanarɗin shi ya kira ya sanar.
      
          Yunwa da gajiya taima Dr Yoohan rumusu zuwa yanzun, haka ya fito a matuƙar wahale Dr Aysha biye dashi tana masa bayani akan nasarorin da suka samu game da sauran aikin da yayi a wancan zuwan kafin yima wannan matar aiki. Sosai yaji farin ciki a ransa, dan haka ya biye mata suka shiga zagaya ɓangarorin da marasa lafiyar suke yana dubasu.
     Duk inda ya gitta addu'a ake binsa da shi, duk da wasu da an masa addu'ar zakaji sunce. Arne ne fa. Jin hakan kansa wasu jikinsu yay sanyi. Wasu kuma suce dan arne ne baza'a masa addu'a ba bisa ga ƙyautatawarsa?.
     To shidai baimasan sunayiba, dan farincikine shimfiɗe a ransa ganin nasara na kuma ziyartar aikinsa a koda yaushe. Amma duk da wannan farin ciki sam babu fara'a kota sisin kwabo a fuskarnan tasa saboda halittarsace haka rashin fara'ar.
        Suna kammala zagayawa ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa. Ganin yaci a wanni uku a cikin uku da rabi na hutunsa ya sauke ɓoyayyen ajiyar zuciya. Bashi da tabbacin samun jirgi mai komawa Lagos yanzu, dan haka ya yanke shawarar nufar Abuja a mota kawai, sauran patients ɗinsa kuma sai dai Richard ya dubasu.
     Da wannan tunanin yayma su Doctor Aysha sallama ya fito batare da ko office ɗinsa yay tunanin shiga ba. Amma duk da haka sai da Doctors ɗin dake matuƙar yinsa suka firfito suka gaishesa, sannan suka yo masa rakkiya zuwa wajen guards ɗinsa da basuyi tunanin fitowar tasa ba a yanzun. Dan Solomon suke ta bama labarin abubuwan da suka faru game da kama Nu'aymah da aka turosu yi.
         
         Cike da farin ciki Solomon ke wata shegiyar dariya, ya ƙyalƙyale da ita yana faɗin, “Inason kafin kuje abuja da ita kuci ubanta a hanya ta ƙarasa da ƙafa ɗaya. Kai bama nason taje da numfashi gaba ɗaya. ku kaita da rabin rai yanda oga zai ƙarasata da kun isa, dan bana fatan kafin mu dawo Abuja boss yaji koda ɓurɓushin labarin abinda ya farune. Kunsansa ɗan hana ruwa gudu ne. Shi a dole masoyin ƙ..........”
         Da sauri Solomon ya haɗiye sauran maganarsa jin ƙamshin turaren Dr Yoohan ya cika wajen. Yay azamar juyawa kamar yanda suma sauran duk suka juya a tsorace.
     Ganin yana maganane da Doctors ɗin da sukai masa rakkiya ya sakasu sauke ajiyar zuciya. Dan sun tabbata baiji komaiba.
           Dr Yoohan yay sallama da abokan aikinsa kafin ya shiga motar da aka buɗe masa yana nai ɗaga musu hannu hamar yanda suke ɗaga masa. A haka motocin suka fito daga cikin asibitin.
        “Sir! Zamu koma airport ne?”. Cewar Solomon fuskarsa ɗauke da murmushin jin daɗin kama Nu'aymah da har yanzu ya gaza barin fuskarsa.
      Shiru Yoohan ya musu tamkar bai jiba, yama maida hankalinsa kan files ɗin daya fiddo a jikkarsa yana dubawa. Sake maimaitawa Solo yayi. 
     Nanma sai da yaja wasu sakanni kafin yace, “Police station”.
        Ji kake ƙiyyyyy!!! Driver ya taka wani uban birki a firgice, tare da haɗa baki shi da Solomon waje. faɗin, “Police station kuma sir?!”.
         (🙄🙄😏An yanka ta tashi ko masu gadi?).

       Idanu ya zuba musu na wasu sakanni fuska a matuƙar ɗaure. Sai kuma ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Ganin gaba ɗaya wutar kansu ta ɗauke a fusace ya sake kallonsu “Kona canja yaren da nai maganar da shi ne bakuji wannan ba?”.
         Da sauri suka shiga bashi haƙuri, driver ya ƙarama mota gudu zufa na keto masa ta ko ina a sassan jikinsa. Kai kace motar babu ac. kallo ɗaya zaka fahimci tsagwaron tashin hankali da ɓacin rai tattare da su. Driver bashi da wata hanyar daya wuce ya ɗauki hanyar police station ɗin da suka bar Nu'aymah. Acan kuma ƙasan ransu shi da Solomon tunanin mafita sukeyi.
    Sunci rabin tafiya wani dabara yazoma Solo a rai, dan haka ya ɗauka wayarsa ya rubuta text ya turama Madam Chioma. Mintuna uku ba'ayi cikakkuba sai ga kiranta ya shigo wayar Yoohan.
     Idanunsa ya ɗago daga abinda yakeyi ya kalli fuskar wayar. Duk da yaga sunan Mom ɓaro-ɓaro a jiki sai ya ɗauke kansa ya cigaba da abinda ya keyi. Kiran ya yanke wani ya sake shigowa. Yanzun kam maimakon kallon wanene sai ya lumshe idanunsa ma, sai da sukai kusan sakan goma a rufe sannan ya buɗesu akan su Solomon dake a gaba suna addu'a da fatan ya ɗaga wayar kafin su isa station ɗin.
       Lip ɗinsa na ƙasa yaɗan lasa da harshe ya sake maida idanunsa ya lumshe bayan ya kife wayar alamar dai bazai ɗaga ɗinba..
        “S...S sir ana kiran wayarka fa”. Solomon ya faɗa da rawar baki.
        Tamkar yayi magana da dutse, dan Yoohan yi yay kamarma bai jisa ba, kuma sarai yaji miya faɗa ɗin.

       A haka suka iso station ɗin, bai fitaba sai da yaja wasu mintuna, ta cikin motar ya gama ƙarema station ɗin kallo har su Solomon da suka fita suka buɗe masa. Solomon yay ƙasa da kansa ganin banzan kallon da Dr Yoohan ɗin ke masa. Batare da yace da shi uffanba ya zuro ƙafafunsa ƙasa ya fito. Gaba yay suka take masa baya kowanne zuciya babu daɗi.
            Duk da ƴan sandan basusan wanene shi ɗinba shigarsa da waɗanda suka rufa masa baya ya sanar dasu ogan gayunne gaba ɗaya. Suda ya kamata ya fara gaidawa sai gasu suke masa tarba cikin tsantsar girmamawa kai kace wani babbane a cikinsu.
           Ransa dake a ɓace da guards ɗinsa ya sakashi ɗaga musu hannu kawai batare da ya cire ko baƙin glasess ɗin idonsaba ya buƙaci a kaisa office ɗin d.p.o. Guards ɗinsa zasu magana da nuna masa sunada power ɗin shiga kai tsaye basai an nema masa isoba yay saurin ɗaga musu hannu suma cikin fushi. Tsitt sukayi kuwa kowa kai a ƙasa.
            Maida dubansa yay ga ƴan sanda ya sake sanar musu su nema masa iso office ɗin d.p.o. Babu musu suka amsa masa cike da girmamawa, yayinda ɗaya a cikinsu ya nufi Office ɗin d.p.o ɗin domin sanar masa. 
         “Ranka ya daɗe yace ka shiga”. Ɗan sandan ya faɗa da harshen hausa yana ɗan risinawa. Ko motsi Yoohan baiyiba. bai kuma nuna yaji mi ɗan sandan ya ceba. Wani cikinsu dake acan gefe daya fahimci Yoohan baya jin hausa yay saurin sake maimaita abinda ɗan uwansu ya faɗa da turanci. Sai lokacin ne Yoohan ɗin ya motsa tare da ɗaga musu hannu.

          Da sauri Solomon ya buɗe masa ƙofar office ɗin ya shiga. D.p.o yay azamar ajiye biron hannunsa yana mai miƙewa cike da tsagwaron mamakin ganin wanda baiyi zato ko tsammani ba. Shi kansa Yoohan ɗin tsaye yayi kawai yana kallonsa, a ransa yana raya ashe papa yayi amfani da wanda ya sanine shiyyasa ya nuna ƙarfin ikonsa.......
          D.p.o ya katse tunaninsa da faɗin, “Oh God! Dr Yoohan!”. Hannu Yoohan ya saka ya zare glasess ɗin idonsa, batare da ya amsa d.p.o ba ya zuba masa idanu kawai kamar mai nazari. Har inda yake d.p.o ya ƙaraso shi, ya nuna masa kujera cike da girmamawa yana faɗin Please Sir ka zauna, ka taimakeni ka zauna”.
     Kamar bazai zauna ɗinba, sai kuma miya tuna oho masa sai ya zauna a kujerar da d.p.o ya gyara masa tare da harɗe ƙafafu ya ɗora glasess ɗinsa saman table ɗin.
    D.p.o daya koma tamkar ya mance da matsayinsa da kansa ya buɗe fridge ya ɗakko ruwa da lemo da kofi ya ajiye saman table ɗin. Abin mamaki duk ya wani rikice.
    
          Nu'aymah na zaune a office ɗin ta cusa kanta cikin ƙafafunta dake mata wani irin ciwo taji takun shigowar mutum office ɗin. Yanda taji D.p.o na magana ba ƙaramin takaici ya bataba. A ranta rayawa take ‘Shin sai yaushene wai ƙasarnan tamu zata gyarune? Sai yaushene jami'an tsaronmu da duk wasu ma'aikatunmu zasu daina fifita masu hannu da shuni akan talaka? Ta taso gidan da Alhmdllh akwai arziƙi da wadatar zuci, akwai kuma kima da daraja na babban gidan. Dan haka duk inda suka tsinci kansu da wuya kiga ba'a girmamasu, sai dai idan ba'asan su ɗin su wanene ba. Ta tabbata wannan d.p.o ɗin inda ace bahaushene da babu yanda za'ai ya kasajin kunyar tura yaransa har gidansu ɗakkota, koda kuwa za'ace an basa kuɗin toshiyar baki. To amma yanda akema talaka na sosa mata zuciya da ruhi. A yanzu haka shigowarta station ɗin nan taga abubuwa kala-kala da suka sosa zuciyarta duk kuma an yisune akan talaka’. Batare data saniba tsaki ya kufce mata, cikin zafin zuciya da takaicin d.p.o ta ɗago dan taga wane shashasha ne yazo ake masa wannan tarbar tamkar wani IG ko gomnan kanon ma gaba ɗaya.
          Akan bayansa ta sauke idanunta, dan ya juya mata bayane bata ganin fuskarsa, ta zuba ma bayan nasa harara duk da bawai ta gane wanene ba.

    Yoohan da baisan Nu'aymah nayiba ya kalli d.p.o fuska babu walwala yace, “Inason ka saki yarinyar da papa yasa aka kawo nan”. “Sir amma.....” hannu Yoohan ya ɗaga ma d.p.o da sauri. “Emanuel! Haka kawai nake buƙatar ayi”. 
       “Za'ayi yanda kakeso sir, sai dai nima ka saurareni ko kaɗanne Please ”. Shiru Yoohan ɗin yayi alamar ya bashi dama. D.p.o daya fahimci hakan sai ya gyara zama, cikin kwantar da murya yace, “Ka taimakeni ka kira Pastor ka sanar masa kaine ka bada umarnin a saketa kar yaga kamar na saɓama umarninsa rayuwata ta shiga garari.
     Lumshe idanu Yoohan yayi, wani irin takaici da ƙunci na daɗa faɗaɗa a cikin ransa. Yanajin zafi da matuƙar damuwa idan yaga yanda mutanensu ke masifar tsoron papa. Yakan rasa minene dalilin hakan? Dan kawai yana pastor ne ko me? Kodai akwai wani abu da bai saniba game da mahaifin nasa ne? K........’
      “Please sir!”. Maganar d.p.o ta katse masa tunani. Maimakon ya amsa zai kira Papa, sai yace, “Ina yarinyar take?”. Da hannu D.p.o yay masa nuni da Nu'aymah dake bayansu ta sake duƙar da kanta saboda ƙafarta. Kafin Yoohan yace wani abu d.p.o ya bata umarni akan ta taso. Ko motsi bataiba dan abinda ya dameta shine matsalarta ba tsawarsa ba. Yunƙurawa ɗaya daga cikin yaransa yay a fusace zaije gareta Yoohan ya ɗaga masa hannu. Komawa yay ya tsaya inda yake cike da takaici.
     Nu'aymah da duk tana jinsu bata motsaba, sai da ƙafarta ta lafa mata. Ƴar sandan da suka ɗakkota a gidace ta shigo bisa umarnin d.p.o ɗin ta taimaka mata ta miƙe. Miƙewar tata tayi dai-dai da ranƙwafawar Yoohan da ya miƙe yana faɗima d.p.o “Police ɗin da suka ɗakkota su maidata, su kuma bama iyayenta haƙuri da wanketa, inba hakaba Emanuel kaine zaka ɗauki laifin”. Da sauri d.p.o ya ɗaga masa kai zufa na keto masa. Yoohan ya ɗauki glasess ɗinsa ya juyo zai saka a ido. karaf suka sauka akan Nu'aymah dake tsaye tana binsa da wani shegen kallo na fusata, dan ko kaɗan batai tunanin shiɗinne yasa a kawota nan wajenba, saboda sam bata wani gane guards ɗinsa ba, hasalima ta manta da shi da abinda ya faru tsakaninsun.
     Nunashi tai da ɗan yatsa babu alamar koda tsoro tattare da ita, “Kai ne dama kasa a kawoni nan wajen?” tai maganar fuskarta ɗauke da murmushin takaici, sai kuma ta haɗe fuska da maida dubanta ga d.p.o. “Yallaɓai ai bani na cancanci zuwa nanba wannan mai suffar ƴan damben ne, dan haka nima yanzu na kawo ƙararsa”.
      Kafin d.p.o yace wani abu ta fisge hannunta daga na ƴar sandar ta fice a office ɗin da ɗan sauri duk da tana ɗingishi. Saurin bin bayanta d.p.o da ƴan sandan da ke office ɗin sukai, yayinda Yoohan ya lumshe idanu da saka glasess ɗinsa da ganinta ya hanashi sakawa ɗazun shima yabi bayansu.
     Isowar su d.p.o yayi dai-dai da furucin Nu'aymah dake tsaye gaban ƴan sandan dake wajen kanta  . “Yallaɓai na kawo ƙara”.
      A tare suka kalleta, ɗaya a cikinsu yace, “ƙarar wa? A kanmi kuma?”. Juyawa tai inda su d.p.o ke tsaye cike da al'ajabi da mamakinta, dai-dai kuwa da fitowar Dr Yoohan daga lungun da office ɗin d.p.o yake ta nunasa da faɗin, “Ƙarar wannan mai siffar ƴan damben na kawo”............✍

😂Wagga ɗiya kina da tsaurin ido aradu😚🚶🏻.
       
          
Barka da juma'a😘😍🤗.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
________________________
*ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE* 

       *_KAJI shahararrun kuma mandiyoyin ƴan ƙwalisar kawo kayan kitchen masu tafiya dai-dai da zamani. Idan nace nadaban ina nufin suɗin nadabanne wajen kaya ƴan gaske dake ƙawata kitchen ɗin amarya harma dana uwargida ƴar ƙwalisa. Ka siya ka tabbatar ka saya ɗin ko a gaban tsaranka sai ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. sunan kayansu sa kishiya cin bashi🤣, dan tana ƙyalla ido taga kitchen ɗinki tsarin amerikawa tuni zata fara ƙwafa da tunanin zuwa gidan delu dillaliliya mai saida kwanika. Sai dai kuma kama da wane akace bata wane, dan haka ku maza ku garzaya ZEESMART KITCHEN UTENSILS AND MORE. domin samun naku kuma. Suna kawo kaya daga ƙasashen ƙetare akan farashi mai sauƙi da rahusa. Suna order ɗin products kamarsu, dukan kayan kitchen na zamani, bedsheets, shoes dade sauransu, products ɗinsu pre-order ne dake zuwa akan lokaci batare da mai kaya ya ƙosa da jira ba ko samun matsala. Zaku iya samunsu a Number waya kamar haka ko Location nasu. Phone number: 08102393622. Location Gombe. Amma Zasu iya turawa kowani gari dake a lungu da saƙo na ƙasarnan. Sayen nagari maida kuɗi gida. Ku garzaya kar ayi babu ku. Da ƙyar nasha yafi da ƙyar aka kamani inji masu iya magana😉😘😘😍😋._*

_______________________________

15

.................Kaɗan ya rage su makara a hanyar zuwa airport, ALLAH dai ya taimakesu suka isa gab. Sai da Richard ya ga tashin jirgin sannan ya bar Airport ɗin yana mai kiran Dr Sa'ad ya sanar masa ga Dr Yoohan nan ya taho su kwantar da hankalinsu.
      Duk da Dr Sa'ad baiso hakanba sai ya amsa masa harda addu'ar isowarsu lafiya. A ƙasan ransa kam ji yake kamar zuciyarsa zata babbake da wuta dan takaici da tsanar Dr Yoohan ɗin da bai taɓa tare masa komai a duniyaba bayan nusar dashi ya san kansa kawai.
     Yana sauke wayar daga kunnensa kiran Madam Chioma na shigowa. Ɗagawa yay da hanzarinsa, dan yasan dai bai wuce ta kira Number Yoohan ɗin bata shigaba ko bai ɗagaba. Ya gaidata cikin girmamawa kamar yanda ya saba, kafin ya ɗora da faɗin, “Mom lafiya dai ko?”. Daga can tace, “Eh Richard, lafiya, amma na kira abokinka sau uku bai ɗagaba, nayi zaton ko yana akan aikine idan ya kammala zai kirani, sai dai har yanzu banga kiransaba. Na kuma nemesa yanzu da kaina wayarsa bai tafiya. Shine nace ko lafiya?”.
       Murmushi yay yana ƙara jinjina ƙaunar wannan uwa da ɗa a zuciyarsa. Cike da kulawa yay mata bayani yanda zata fahimta, sai dai yanda tai azamar katsesa jin ya ambaci kano sai abin ya nema firgitashi. Kafin ya samu damar tambayarta dalili harta yanke kiran.

*_ABUJA_*

       Hankalin Madam Chioma a tashe tai kiran Guards ɗin Yoohan dake shirin tahowa da Nu'aymah Abuja. Cikin azalzala ta sanar musu karsu taho su ajiye Nu'aymah a police station ɗin maza su nufi airport su tarbi Yoohan gashi nan ya taho da ga Lagos. Tai mugun basu gargaɗi akan inhar wani abu mara ƙyau suka bari ya faru da Yoohan ɗin yau to su tabbatar a bakin aikinsu kenan, bayan horo mai tsanani da zasu fuskanta kuma.
              Sanin Madam Chioma zata aikata fiye da abinda ta faɗa inhar akan Yoohan ne ya saka guards ɗin Yoohan bin dukkan umarninta. Har an fito da Nu'aymah da ko harara babu wanda yay mata a station ɗin, hasalima tana a office ɗin d.p.o tunda aka kawota suka sanarma d.p.o halin da ake ciki game da umarnin mahaifiyar uban gidansu.
       Babu musu ya amince da ajiye Nu'aymah har suje su dawo, su kuma suka shiga motocinsu suka bar station ɗin zuwa airport ɗakko Dr Yoohan da suka san nanda mintuna ƙalilan ne jirginsu zai sauka.

      Murmushi Nu'aymah tayi tana mai buɗe tafin hannunta ta kalli ƴar takardar da baba malam ya saka mata lokacin daya kamo hannunta. Takardar ta sake buɗewa ta karanta addu'ar dake ciki tana murmushi, wata irin ƙaunar mahaifinta da tausayinsa na ratsata a zuciya da ɓargo. A yau ta ƙarajin ƙwarin gwiwa akan shirin mahaifin nata. Wanda daga ita sai shi sai ALLAH daya hallicesu sukasan da shirin. Amma ko Umm yaja mata gargaɗi mai ƙarfi akan karta bari ta sani, bakomai yasashi yin hakanba sai wani dalilinsa da itama yace ba yanzu zai sanar mataba sai nan gaba.

 ______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 Wannan littafi SARAN ƁOYE na kuɗine, yana ɗaya daga zafafa biyar, idan kana buƙata kaima waɗanan numbers ɗin magana ka biya kuɗinsa naira 300 kacal dan girman ALLAH. Karka yaɗa dan ALLAH idan ka gani😀🤝🏼.

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

______________________★
  
          Gaba ɗaya Yoohan ji yake kamarma jirgin baya wani sauri, duk bayan mintuna sai ya kalli agogon hannunsa yayi ƙaramin tsaki da Solomon ne kawai ke jinsa, yay masifar ƙosawa yaga sun sauka. A yanda hankalinsa ke a tashe har sai da Solomon yaji tausayinsa ya kamasa. Yana mamakin yanda Dr Yoohan sam babu wani ƙyashi ko ƙabilanci a ransa, game da aikinsa bai taɓa banbanta kai ɗan wane addini bane ko kai ɗan wane yankine. Kansa tsaye yake ƙoƙarin sa, shiyyasa a kullum ALLAH ke sake ɗaukaka darajarsa, dan kullum bayin ALLAH cikin masa addu'oi suke a zahiri da baɗinin zuciya.
          Duk da burinsa nason jirgin yay saurin sauka ahakan bai hanashi fita cikin nutsuwa ba lokacin da jirgin ya taɓa ƙasa. Yanda yake tafiya kawai ya isa abin kallo ga mutane. Duk da fuskarsa kullum a cinkushe take hakan bai hana ya ɗauki hankalin masu kallonsa daga maza har mata ba.
         “Welcome sir”. Yaji an faɗa Lokacin da suke isowa wajen masu taxi shi da Solomon dake a bayansa. Kamar zai share sai kuma dai ya juya. A bazata idanunsa suka sauka akan guards ɗinsa waɗanda baiyi zato ko tsammanin ganiba.
     Da sauri suka ƙaraso gabansa zuciyarsu na dukan ɗari-ɗari ganin kallon da yake musu na tsagwaron mamaki da tuhuma, cike da girmamawa suka shiga gaishesa ɗaya bayan ɗaya, kafin su ɗora da masa bayanin Mom ce tace suzo su tarbesa.
      Duk da akwai magana a bakinsa game da ganin nasu a kano sai ya share bai yiba. Ya nufi inda ɗaya daga cikinsu ya buɗe masa mota ya shiga.
       Sai da suka fito da ga airport ɗin gaba ɗaya suka hau kan titi sannan ya jefama driver da Solomon ke kusa da shi tambaya a bazata.
     Cikin harshen nasara yace, “Miya kawoku kano?”. Cikin faɗuwar gaba driver ya kallesa ta madubi. Sam bama kallonsu yake ba, hankalinsa nakan waya yana dannawa. Cikin ɗan rawan baki na rashin gaskiya driver ya bashi amsa da faɗin, “Sir M... Madam ce ta aikomu”. “Yin me?”.Yoohan ya faɗa da ɗago fararen idanunsa ya zubama drivern cike da nazari. Sosai kallon ya firgitashi, dan anyi sa'a lokacin da Yoohan ɗin ya ɗago idanu yayi dai-dai da ɗagowar driver shima ya kallesa. 
     Saurin riƙe sitiyarin yayi jin zai ƙwace masa, dan har motar sai da tayi ɗan tangaɗi kaɗan. “I am sorry sir” driver ya faɗa da sauri ƙirjinsa na dukan tara-tara ganin yana neman zubar dasu a ƙasa. Shiru Yoohan bai tanka ba, hasalima ya ɗauke kansa tamkar baiga wani abu daya faru ba. Sai ma ya ɗauka waya yay kiran Dr Sa'ad da kai hannu saman kunnensa ya gyara Bluetooth ɗinsa na fama dake a maƙale.

       Solomon da duk ya fahinci akwai wani abu dangane da zuwan ƴan uwanasa kanon ya haɗiye yawu da ƙyar shima yana satar kallon madubin, ganin hankalin Yoohan ɗin baya garesu sai yay saurin maidawa ga drivern. Ƙyaftama juna idanu sukai, alamar dai sun saba da yaran. Solomon ya ɗan gyaɗa kansa yana gyara zama.
     A haka suka isa asibitin batare da kowa ya sake magana ba. Tun kafin a buɗe masa shi harma ya buɗe ya fice abinsa. Da yake yau zuwan bazatane Dr Sa'ad kawai ya san zaizo sai Dr Aysha, sauran Doctors ɗin basu fito sun tarbesa ba kamar yanda suka saba.
    Sai dai tun shigowar motocinsa wasu daga ma'aikatan asibitin suka fahimci shine. Yayin da gefe guda kuma da ya zama abin kallo ga mutane. Musamman ma yanda yake tafiya Guards ɗinsa na take masa baya. Waɗanda suka sanshi nata faɗin, “Dr Yoohan yay zuwan bazata, yaukam za'asha masifa musamman akan ma'aikatan dakeda sakaci akan aikinsu. 
     Duk da ya fahimci yanda wasu a cikin ma'aikatan ke ta guje-gujen sanarma iyayen gidansu zuwansa basuko ishesa kalloba. dan abinda ya kawosa shine kawai a gabansa ba su da shirmensu ba.

     Tunda su Solomon sukaga shigewarsa sai yaja hannun ɗaya daga cikin Guards ɗin suka fito, sauran kuwa na tsaye ƙiƙam tamkar an dasasu gadin duniya🙄😏, sai zazzare idanu suke sun hana masu kai kawo ta wajen sukuni. Ba marasa lafiya da ƴan uwansu kawaiba, hatta ma'aikatan asibitin a takure suke. Masu sanya da aikinsu duka sun dage saboda jin zuwan Dr Yoohan. (ALLAH ya ƙyauta. Bazakaji tsoron UBANGIJIN daya halicceka ya baka amanar wannan aikin a ranka ba sai wani shasha mutum irinka, ba kuma komai ke kawo tsoronsa ba sai gudun karka rasa aikinka🤦🏻, ya salam. Musulmai ina muka ajiye gaskiyar tamu? Ina muka ajiye koyarwar addinin namu? Ina muka ajiye tausayi dajin ƙan da aka san mumini da shi?. Ku dubafa Dr Yoohan ba musulmi bane, baɗan yankinku bane, ba yarenku bane? Amma yana nuna fushinsa akan sakaci da cigabanku, yana nuna damuwarsa akan ƴan uwanku, yarenku addininku, yayinda ku son zuciya da burin tara duniya ya rufe jinku da ganinku. Kaje asibiti kaga ana wulaƙanta marasa ƙarfi dan kawai sunzo neman lafiya. Babban abin takaicinma yafi yawa a ɓangaren mata masu haihuwa. Kaga ma'aikatan asibiti nacin zarafinsu dan kawai sun kasance ƙauyawa ko talakawa. Haba ƴan uwana, wannan aikinfa da kike cin zarafin wasu dashi tamkar mabuɗine na gida guda biyu. Wuta ko aljannah, ya rage naki/nak ka zaɓama kanka wanda kafi buƙata. ALLAH ya shiryar damu dai, ya rabbi kai riƙo da hannun ma'aikatanmu masu ƙyawawan zukata domin rahamarka da alfarmarka🙏🏻😭).

__________________________

             Tunda Addah ta isko Umm a ɗaki basu iya cema juna uffan ba. Kowa ya zabga uban tagumi ne yana saƙa mai fishshesa. Sun kwashi tsahon mintuna sha biyar a haka kafin Addah ta katse shirun nasu da faɗin, “Ni nama rasa abin faɗa wlhy akan wannan al'amari, har nawa Nu'aymah take da ƴan sanda zasuzo su tafi da ita? Mi ma to tayi musu? Sannan miyasa yaya malam zai yanke wannan hukuncin mai tauri haka?”.
          “Wannan sune tambayoyin da nake taima zuciyata Addah, amma sam na gaza samo amsar ko guda a ciki. Ina ƙyautata zaton a tafiyarsu bikin nan koma miye ya faru acan ya faru, dan........”
           “Haba Umm miyasa zakice haka? Naga dai su a cikin Orphanage suke? To mima zata aikata da har ace mu bamujisa ba?”. 
      “Addah yaran nan kafa haifesu ne amma baka haifa halinsu ba, minenema bazasu aikataba tunda basa ganin idon kowa. Ballema Nu'aymah da batajin magana sam, wuyarta dai ta samu sakewa ne kawai, shiyyasa sam banason ko gidanmu tace zataje ta kwana ko wani waje wlhy, danni bansan ina ta ɗakko wannan halin nata na tsiwa da rashin kunyaba”. Yanda Umm tai maganar cikin ɓacin rai yasa Addah saurin faɗin. “Dan ALLAH karki tsaurara harshenki akan wannan abun, mudaibi komai a sannu muji inda matsalar take. Nu'aymah har yanzu yarinyace, kuma sanin kankine duk rashin ji da tsiwar Nu'aymah batayinsa ita kaɗai sai da gudunmawar su Adawiya dama, tunda halin nasu ai duk ɗaya ne.....”
       “Humm Addah kema kinsan indai gaskiya zaki faɗa Nu'aymah ta fisu kaifi, dan duk abinda zasu aikata itace jagora”. “To kowa ya zauna akan ra'ayinsa danni bawai yarda zanyi ba, inaga dai bara nakira su Yusrah muji minene ya faru?”. Umm dai batace komaiba, tanata kuma ƙoƙarin danne damuwar dake cizon ranta da kukan dake yunƙuro mata a rai. Duk da Alhmdllh zuwan Addah a gareta ya sanyaya mata fushinta bakamar sanda ta shigoba.

        Sallamar Yusrah da Amal ce ta saka Umm da Addah ɗagowa suna kallonsu. Basai an faɗaba, daga gani kukama sukeyi. Hakan da Umm ta gani sai ya sake karya mata zuciya, tai ƙasa da idanunta tana karanto7 addu'ar neman sauƙi da sassauci wajen UBANGIJI.
     Zama su Yusrah sukai kansu a ƙasa suna sharar ƙwalla. Addah tace, “Kuka ba shi bane mafita Amal da Yusrah, ku sanar mana mikuka sani game da hakan dan musan hanyar data dace mu kama wajen amso ƴar uwarku”.
      Share hawayensu duk sukai, cikin nutsuwa sukaima su Umm bayanin abinda ya faru aranar ƙunshi, sai dai sun ɓoye cewa Nu'aymah ta fasama guards ɗin kai, sundai ce ta wulwula dutse bisa tsutsayi ya daki glass ɗin motar. Hakan da tayine kuma ya saka mutanen tsayawa amma da guduwa zasuyi. 
      Shiru babu wanda ya iya cewa komai tsakanin Umm da Addah, sai da kusan mintuna uku Addah ta sallamesu suka tafi.

         “Umm! Inaga lokaci yayi da zamu fara aiwatar da shirinmu a gidan nan gameda waɗanan abubuwan. Na kula al'amarin ƙara zurfi yakeyi kullum”.
       Murmushi Umm tayi idanunta akan Addah, ta ce, “Addah wannan ai babu saka hannun kowa a ciki, itace ta jama kanta. Ni wlhy a yanzuma naji bana sha'awar sanin wanda ke aikatawar.........”
        “Me yasa?”
Addah ta faɗa da mamaki.
     Murmushi Umm ta sake yi har haƙoranta na bayyana, tace, “Addah to minene amfanin sanin? Babu abinda sanin zai amfanar sai fitina. Idan a gidan nan yake zai zama sanadin lalacewar zumincin da aka gina bisa haƙuri da juriya. Idan kuma a waje yake za'a jawo masa tsana daga mutane a tozarta iyalansa. Addah hakan baida wani amfani a gareni, dan wlhy bana fatan kwana da wani musulmi a cikin raina koda na kwana ɗaya ne, dan bani da tabbacin wayar gari. Koma wanene UBANGIJI ya rufa masa asiri na tsahon lokaci, ya kuma fimu sanin hikimar yin hakan. To mu haƙura kawai mu barsa da UBANGIJIN ya ishesa komai”.
     Ba ƙaramin ƙurama Umm ido Addah tayiba, har sai da takai Umm ɗin ta taɓata da faɗin, “Ina kika tafi kuma?”. Murmushi Addah tayi da sauke ajiyar zuciya. Tace na tafi duniyar mamaki ne da tsarkake sunan ALLAH, Umm ki godema ALLAH ya azurtaki da ƙyaƙyƙyawar zuciya wlhy........”
     “Kema ai ya azurtaki da ita Addah, dan ina koyi da wasu ƙyawawan halayene daga gareki. Hakan yasa ƙaunar da nake miki ta dabance a zuciyata wlhy, fatar bakima bazata iya kwatantawa ba, kun bani gudunmawa ke da Baba wadda har na koma ga ALLAH bazan gazaba wajen roƙa muku rahama da yardarsa”.
       Hawayene ya cikama Addah ido kamar yanda ya cikama Umm itama, suka kama hannun juna suna murmushi cike da ƙaunar juna da ta ginu tun ƙuruciya..............✍

(ALLAH ya bar ƙauna Umm da Addah😅😘🤗)
              
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
   *_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
    *_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
       *_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
     *_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
   *_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

Mo. 18

..............Ran papa na zafi da ƙuna ya ajiye wayar, hakan da yay ya sake fahimtar da Madam Chioma cewar akwai damuwa.
     “Lafiya Daddyn Yoohan?”. Ta faɗa da yarensu cike da zaƙuwa. Banza yay mata kamar bazai tankaba, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya sanar mata yanda sukayi da Yoohan ɗin. Itama abin ya sosa mata rai, amma saita bama mijin nata shawara akan ya barshi kawai. Karkuma su sake ɗaukar kowanne irin mataki akan yarinyar har sai Yoohan ɗin ya manta da zancen sannan.
     Wannan shawarar ta masa daɗi sosai, harya kai ga jawota jikinsa ya rungume yana kissing ɗin wuyanta. Fakar idanunsa tai ta zuba masa harara tana yamutse fuska daɗan turesa daga jikinta irin kamar da wasa ɗin nan.
         Shikuma yaƙi ya bari saima ƙara wuta yakeyi. “Darling!” ta faɗa tana fisge jikinta da ɗan fushi, ganin ya saketa kuma saita ƙyalƙyale da dariya tana miƙewa ta nufi ƙofa da gudu tana faɗin wai ta masa wayo. Miƙewa yay zai bita ta ida ficewa da gudu taja ƙofar ta rufesa a ciki.
        Haɗe fuska tayi tamkar an aiko mata da saƙon wani ya mutu yanzun nan tana harar ƙofar. Jitake a ranta lokaci yayi da zata fitar da abinda ke ranta tsahon shekaru. Taja gajeren tsaki tana barin wajen ta nufi ƙasa inda take jiyo hayaniyar su Miracle dake casar rawa a falon sun ƙure kiɗan daya karaɗe gidan.

________________________
            *_SAUDIA_*

       Shirin Adawiya ya saka suka wuni cikin daɗin rai yau ita da Abdallah. Dan dakansa ya sakata tai musu girki kamar yanda tai masa alƙawarin yimasa irin girkin da Nu'aymah tafi iyawa kuma tafi so. Shiko ya biye mata harda binta kitchen sukai aikinma tare. 
     Bayan sun gama kuma ya jata ɗakinsa sukai wanka tare, dukda babu abinda yay mata irin na nuna soyayya ga ma'aurata ɗinnan hakan baisa ta damuba. acewarta ai yanzun aka fara wasan. Dan haka ta ƙara ƙaimi wajen saka masa sunan Nu'aymah akan duk abinda zasuyi.

      Zuwa dare bayan tayi barci a ɗakinta shima yana nasa sai ya shiga dogon nazari akan shawarar Adawiyan. A yanda ya ƙiyasta zaiyi amfani da yarinyar wajen dawo da martabarsa ga Nu'aymah kamar yanda ta faɗa masa. Duk da yayi saurin ɗago dabararta nayin hakan game da sakko Nu'aymah a lamarinsu, sai yaga ai shima wata damace a hannunsa da zai dama ya yadda ƙwallon mangwaro kuma ya huta da ƙuda.
    Dan haka ya kammala shirinsa tsaf game da yanda zai bida Adawiya akan Nu'aymah har haƙarsa ta cimma ruwa ya mallaki abar sonsa su gina rayuwar da yagama tsara musu tun asalin fara mallakar hankalinsa.
    Da wannan ƙwarin gwiwar yay barci ranar. Washe gari kuwa tunkan ya tashi Adawiya harta shirya masa breakfast wai acewarta irin abincin da Nu'aymah tafi ƙauna kenan. Yakoyi farin ciki, a ƙasan ransa kuma yana mai mata kallon ƙuruciya da wauta. Zama yay yaci sosai ya ƙoshi, ya kuma taimaka mata suka gyara gidan sannan suka fita tare ya kaita makaranta kafin shima ya wuce tasa.

        Ba ƙaramin farin ciki Maman Aaida tayi da labarin da Adawiya ta bataba. da kuma abinda ta gani da idonta na kawo Adawiya da Abdallah yayi school, rabonda hakan ta faru tun randa ta fara zuwa da kwanaki ukun da suka biyo baya. Daga haka yace ta cigaba da zuwa ai zata gane hanya. Sai gashi yau ya kawota da kansa cike da farin cikinsa.
      Haka taita walwala a majaranta har lokacin tashi yayi. Abin mamaki kuma sai gashi ya sake dawowa ya ɗauketa. Suna isa gida kuma ya miƙa mata kwalin waya sabuwa fil harda sim card a ciki. Wani uban tsalle ta buga ta ɗaresa tana masa tagwayen kiss a wuyansa da fuska. Daga haka ya biye mata ya kwashi gara sanan ya sake wanka ya fice gidan ya barta da murnar waya.

         Wani irin ji Adawiya tayi kanta na yawo a sama. Ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta cike da nishaɗi da yabama tunaninta da shirinta. ‘Yo ashe nice na zauna shashanci akanka Yah Ab, ashe kawai wata ƴar gajeriyar hanyar da zan bi da kai na samu nasarori a kanka bama nasara gudaba, amma na zauna ɓata hawayena da lokacina wajen tunani da baƙin rai. To yanzu kam saika shirya, dan Adawiya tayi alƙawari da alwashin sai kayi nadamar cin kashin dakai mata akan wata shasha Nu'aymah. Kaida Nu'aymah kuwa sai dai gani a hoto, dan lokaci zaizo da ko gaisuwar waya sai kun tsani kanku wajen dinga yinta balle ta zahiri. Ni Adawiya Mustapha Hashim Jibiya, ni kaɗaice matar da zata mallakeka a duniya da komai naka. Kuma Nu'aymah bazata taɓa samun wanda ko ya kama ƙafar matsayin Slippers ɗin wankan kaba Yah Ab. Dan saina sakata kuka da baƙin ciki kwatankwacin wanda ta sakani a baya saboda zazzafar ƙaunarka da begenka inhar niɗin jinin Fauza ce (Addah).

Tofa Adawiya anya baki ɗebo da zafiba kuwa🤔🤥🤐?.

___________________________________

        Nu'aymah da batasanma Adawiya nayiba tana can durƙushe gaban Umm da Baba malam tana mai basu haƙuri akan ɓacin ran data assasa musu a safiyar jiya game da abinda ya faru. Dan jiya gaba ɗaya ƙin kulata Umm tayi. Baba malam kuma basu shigo gidaba sai gab da magriba. Yana zuwa yay alwala ya wuce massalaci ko Hajjo bai leƙaba. Bai kuma shigo gidanba sai goma saura kamar yanda ya saba. Zuwa lokacin kuma Nu'aymahr ta gama jigata da aman da taita kwarawa na ƙa'idar zuwan jininta hartasha magani tai barci. 

       Ƙinyin magana Baba malam yayi har sai da Umn ta gama yima Nu'aymah faɗa sosai akan shegen tsiwarta kamar zata daketa kafin ta koma nasiha kuma. 
        Bata bartaba har sai da taga tana sharar ƙwalla, dan Nu'aymah fa batason faɗa a rayuwarta, sai dai kuma babu yanda ta iya dan iyaye nagari suke saurin tsawatawa yaransu idan sun gansu akan dokin kuskure. Bayan Umm ta gama nata shima bana malam ya murje nasa idanun yay mata tas fiye da wanda Umm ɗin tai matama. Kafin shima daga baya ya koma nasihar da nuna mata illar rashin kunya ga ɗiya mace.
     Tasha kuka da neman gafararsu sosai, dan har saida Muhammad ya sulale sashin hajjo ya sanar mata tazo ta ƙwaci Nu'aymah a hannunsu sannan suka barta. Duk da dai itama Hajjo ba ƙyaleta taiba sai da ta mata nasihar itama.

      Haka Nu'aymah ta wuni ranar cikin halin ciwo da takaicin Yoohan da Guards ɗinsa da duk ta tattara laifin a kansu saboda faɗan da akai mata. Bata da riko sam idan akai mata abu. amma sai gashi yau Yoohan ɗin da tarkacensa sun kasa barin ranta harma washe gari da shima dai haka ta yini babu walwala saboda jinin nata.
     
      Da haka kwanaki suka cigaba da  ƙara shurawa, baba malam yana cigaba da ƙoƙari neman hanyar haɗuwar Doctor da Nu'aymah batare da kowa ya saniba. Sai dai kuma har yanzu dai ba'a dace ba kam. Har gasu Yusrah sunyi nisa a zana jarabawarsu, wadda a dalilinta baba malm ya dakata da nemawa Nu'aymah makaranta. A cewarsu idan sun kammala sai a nema mata ita da Amal, tunda ita Yusrah zatabi Abdallah ne taje itama tayi nata karatun kamar adawiya.
        Cikin wannan tsukun takardun da bawan ALLAH nan da har yanzu basusan ko wanene ba suka gama kammala. Daga na neman aiki harna karatun yaran daya buƙata. Haka suka tattarasu aka aika masa ta hanyar daya faɗa.
    Kamar wasa kuwa sai ga saƙon ɗaukar aikin nata zuwa ɗaya bayan ɗaya. Hakama na masu shiga makaranta ba'a ƙulla sati uku ba ya turo da kammaluwar komai da makarantun da duk zasuje ɗin.
     Wannan al'amari yayi masifar yima baba malam da duk ahalinsa daɗi. har takai ya shirya family meeting na musamman ya roƙa duk yaran da iyayensu akan su ware dare guda wajen mikama UBANGIJI addu'aoinsu na alkairi akan wannan bawan ALLAH da basusan wanene ba ɗan kuma wane yankine. Kowa ya aminta da wannan tukuyci, sunkuma ɗauki alwashi da ɗamnarar gudanarwa insha ALLAH.
       Yanda Nu'aymah taga mahaifinta yana farin ciki da al'amarin ita bayanma ƙiyamullaili da tayi harda azumi ta tashi washe gari, dan a duniya babu abinda ke sakata nutsuwa da maɗaukakin farin ciki irin ganin iyayenta a farin ciki.

     Kamar yanda Baba malam ya roƙama wannan bawan ALLAH addu'a ga iyalansa haka ya roƙama masa a massallaci, ya kuma roƙa masa a gidan marayun da alkairin yazam duk a kansune. Dan bayan wancan aiken duk ƙarshen wata sai an kawo mota guda ta kayan abinci gidan daga wannan mutumi da basusan ko waneneba. Wani abin mamakima harda yankakkun kaji lafiyayyu ake hado musu yanzun ko ɗanyen kifi ko jan nama.

______________
*_SAUDIA_*

        Tunda Adawiya ta samu waya shikenanfa harka ta buɗe mata. Kullum cikin kiran ƴan uwanta takeyi suna shargallensu. duk da Nu'aymah bata da waya a hannu yanzu haka Adawiya ke addabama Umm kira akan ta bata. Kokuma wayar Amal ko Yusrah, kai harta hajjo kira take a haɗasu.
        Duk hakan tanayinsane danta birge Yah Abdallah ya yarda da gaske tanason cika masa alƙawarinsa na maido Nu'aymah rayuwarsa. Shi kuma duk da yasan dalilin yin hakan bai taɓa nuna mata ya fahimta ɗinba. Haka ya cigaba da biye mata akan ƙuruciyarta da wauta. Sai dai yanajin farin cikin yanda yakejin muryar sahibarsa kullum sama da sau biyar a rana. Duk da har yanzu bai taɓa amsar wayar sunyi maganaba koda kuwa a gabansa ne Adawiya zatai fira da Nu'aymah.

         A gefe kuma abinda Abdallah bai taɓa fahimtaba shine Adawiya ta daina shan maganin da yake bata. Duk sanda zai batan bata musawa wajen amsa, sai dai fa cikin dabara da wayon da ALLAH yay mata zata zirar dashi cikin riga tayi kamar tasha. Sai ta faki idanunsa ta watsa cikin wani abun da tasan idonsa bazai kaiba. A haka suka cigaba da shurawa ƴar shaƙuwar dake tsakaninsu kafin aure tana dawowa a dalilin saka Nu'aymah da sukayi a tsakkiyar lamarinsu.

★★★★★

        A ranar da Adawiya ta fara kiransu a waya suka gaisa Nu'aymah tasha kuka a ɓoye, dan har Umm sai da ta gane tayi kuka. Dan haka ta jata a jikinta sosai cikin hikima taita lallashinta harta ware. Daga nan kullum Adawiya ta kirata bayan sun gama hirar da ƙyar take iya danne zuciyarta. Dan tunkan ai nisa ta fara fahimtar kamar da biyu Adawiya ke kiranta tana gasa mata magana a fakaice kan Abdallah.
     Duk da ƙuruciya da yarinta dake tattare da ita hakan bai hanata zama ta harhaɗa wasu abubuwan cikin rantaba gameda abinda ya shuɗe na rayuwarta da Abdallah harma lalacewar aurensu da har yanzu an gaza gano musabbabin sa a gidan. Kuma har yanzu wasu basubar kallonta da tabon guduwaba a ranar auren nata. Yayinda sukeji a ransu rashin dawowar Ameer gareta butulcine da alhakin Abdallah.

        A wayar da Adawiya takeyi da ita kowa yana kallonta a matsayin shakuwar da sukayice da ɗunbin soyayyar dake a tsakaninsu. Amma kuma a baɗini Nu'aymah ita kaɗai tasan mike faruwa tsakaninta da Adawiyar. Ta kuma shanye a ranta duk da yana damunta bata taɓa nunama kowa a fuskaba koda kuwa su Yusrah ne balle Umm.

★★★★

      Rayuwa ta cigaba da shurawa, inda alkairin wannan bawan ALLAH keta sake faɗaɗa ga gidan marayunnan. Ga azumi nata gabatowa gamai yawancin kwana kuma. Kowa nata shirye-shirye da abinda ALLAH ya hore masa dan farantama iyalansa da bayin ALLAHn da basu da shi.
             A gefe kuma babban gida irin na malamai su baba malam sunata shirye-shiryen tafsir da hidimar da suka shiryama marasa ƙarfi wanda suke jiran sakamakonsu a gurin UBANGIJI al'arshi.
     Duk shekara su duka huɗun suna gudanar da wa'azi a mabanbanta garuruwan da suke rayuwa. Abba Mustapha dake tare da baba malam anan kano shine keyi anan masallacin ƙofar gidansu. Yayinda shi kuma baba malam keyi a massallacin gidan sarki duk shekarar duniya.
      To a wannan shekararma sun kammala shirinsu tsaf daga gidajensu har gidan marayunsu. Ta wani ɓangaren kuma taimakone keta ɓullowa ta hanyoyi daban-daban zuwa gidan marayunsu. Amma duk da haka baba malam bai gazaba wajen tsayuwar daka akan tantance daga ina komai ya fito da ingancinsa ga lafiyar yaran da mutuncinsu.

             Alhmdllh an shiga watan azumin ramadan cikin rahamar UBANGIJI da yardarsa. Kowanne musulmi na ƙwarai yana cike da murnar shigar wannan wata mai tarin falala dake zuwa mana a cikin watanni goma sha biyu na shekara sau ɗaya kacal ya wuce.
    Randa aka kai azumi na goma Baba malam ya gama shirya maganar Umrah da Hajjo kanje a duk shekarar duniya idan wata ya raba. A ƙa'ida kuma takanje da yara biyune cikin ƴaƴan gidan. Namiji babba sai mace budurwa guda ɗaya. Sau ɗaya a wata shekara dasu Nu'aymah suka tada billi ita da Adawiya aka tafi dasu su biyu. Aiko Hajjo ta shawo wahala da su, tun daga lokacin ta rantse bazasu sake bintaba sai sunyi hankali. Sai dai idan wani zaije cikin iyayensu mata su bishi.
         To a wannan karon koda Baba malam yay mata magana a mamakin kowa sai tace da Nu'aymah zataje. Babu wanda hakan bai bashi mamaki ba. Amma sai babu wanda yace wani abu tunda dama itake zaɓar abokin tafiyartata.
        Amsar passport ɗinsu baba malam yay ya bama Ahmad yay musu komai su biyun, sai shi Ahmad ɗin da zaije a wannan karon tare da hajjon.
     Haka kawai sai Nu'aymah ta tsinta kanta da rashin jin ɗokin zuwan, duk da kuwa tana matuƙar son rayuwa a ƙasar saudia saboda dalilan data ginu dasu a cikin rai game da ƙasar.
     Ta samu hajjo a ɓoye ta roƙeta akan ta canja ta da ko Amal ko Yusrah, ita batason zuwa batajin daɗin jikinta. Harara Hajjo ta watsa mata tana taɓe baki. Batare da tace mata cikankiba a zancen ta ɗauke kanta ta maida ga lissafin atamfofin salla da ƴaƴanta kan siya mata danta rabama ƴan uwa da abokan arziki. To da yake bata dawowa sai a daren salla  sai yazam take rabasu kafin ta wuce.
       “Hajjo dan ALLAH mana”. Nu'aymah ta faɗa cike da shagwaɓar data saba yima hajjon tana kwanciya mata a gefen kafaɗa.
      Ture mata kai hajjo tayi tana faɗin, “K da ALLAH jacan shashasha, yo ko shi uban naki wama yake da suna (ba faɗafa zatai ba burgace sabida ɗan farine🤣) bai isa sakani ko hanani abinda nai niyyaba bareke haihuwar jiya jiya Zainabu. Dukfa take-takenku ina sane dasu. Yanzu bautar UBANGIJI ce ma baƙyason zuwa saboda Abdullahi nacan ko yaya? Ke koma ɗokin ganin ƴar uwarki da duk ta addabi kanta da ƙulafucinki a watannin nan baƙyayi? Ni na tausaya mukune dan kuga juna ke da ita shiyyasama na zaɓi tafiya dake. duk da nasan wahalarku da rashin arziƙi zaku jazamin acan kamar yanda kuka saba”.
     Baki Nu'aymah ta sake kumburawa tana faɗin, “Ada kenan, sai akace miki kullum zama zamuyitayi jiya iyau Hajjo, yanzu fa munsan kanmu”.
    Baki Hajjon ta riƙe tana ƙyaɓewa, “Oho to lallai sannu uwata Ɗaharatu, keni dalla tashimin a falo koma kizo na aikeki gidan marigayi malam Aminu kikai waɗannan zannuwan na marayun ƴaƴansu”.
       “Ni wlhy hajjo bani da lafiya, ki aiki Amal kosu Muhammad ai basa azumi”.
       “To wlhy ko zakiyi mushe a gidannan kece zaki aikarnan, kuma Umrah babu fashi sai kinjeta. Dan ALLAH idan kunga juna ke da Abdullahin ku babbaka juna saboda takaicin kanku da kukeji. Tunda shima ya zama babban hotiho ya ɗauki fushi da mutane shi mai zuciya. Toni namaga kuturu ƙarewa zuciyar banzarku da kuka gada wajen malam”.
         Nu'aymah bata sake tankawaba, dan ita ɗaya tasan damuwar da take ciki da matsin da take fuskanta daga Adawiya akan Yah Abdallah ta waya. A ganinta suna a nesa da juna kenan inaga sun haɗu, tunda ta tabbata babu fashi a gidan zasu sauka. Tayi imani da ALLAH harta mutu son Yah Abdallah bazai bartaba, ƙilama shine zai zama ajalinta. Kafin ta san matsayin Yusrah da Adawiya a garesa tana fatan ko bayan shekara nawane idan ya gama fushin ya dawo gareta. Amma kuma zuwa yanzun ta haƙura koda sonsa zai halakata. Badan bazata iya zama dasu bane, sai dai kawai tanason tayi sadaukarwa a garesu dukda tasan ta fisu buƙatarsa. 
         Tanaji a jikinta inhar ta matsama kanta saita mallaki Yah Ab kamar yanda ta rayu da wannan burin a ranta to lallai zumincin gidansu da aka gina tunkan samuwarsu yana gab da tsinkewa ya tarwatse ta dalilinsu. Dan kuwa Adawiya da gaske take nuna mata zata iya yaƙi da kowa akan Yah Abdallah a yanzun har ita kanta Nu'aymah. Tana ƙaunar Adawiya har yanzu a ranta, duk da SARAN ƁOYEN da take mata batare da kowa ya saniba daga ita sai ALLAH. Wannan dalilan guda biyu kawai zaisa ta sakama ranta salama da haƙuri. Sai dai kuma haƙura da Abdallah yana nufin harta koma ga ALLAH bazatayi aureba. Shiyyasa ta duƙufa addu'ar ALLAH ma yasa kar a samu likitan da ake fatan ta silarsa ciwonta zai barta. Dan a yanzu bata buƙatar kowacce irin lafiya kuma, tafi buƙatar ta rayu a haka harmai kasancewa ta kasance a gareta. Idan da rabo zasu hadu da yah Ab ɗinta a gida mafi tsada shine Aljannah.
     Da wannna tunani ta ɗauki aikan Hajjo ta fice bayan ta shiga bedroom ɗinta ta ɗakko hijjab dan akwai kayanta anan sashen hajjon.

*_ABUJA_*

          “Wai nikam Khadijah mike damunkine haka kwanakin nan? Ina lura dake kullum walwalarki da farincikinki ƙara nisantar rayuwarki da mu'amularki sukeyi. Ko baki da lafiya ne?”.
      Idanun Momyn Ab cike da ƙwalla take kallon mijin nata. Ta matso hawayen nata suka gangaro saman kumatunta tana girgiza masa kai.
    Tausayintane ya sake kamashi, dan tsaf ya fahimci damuwar tata akan Abdallah ne da a yanzu ko kiranta a waya baya sonyi sai idan shine ya kirashi ya balbalesa da faɗa. “Khadijah!” ya sake kiran sunanta cike da taushin murya.
    Kanta ta sake ɗagawa ta dubesa. Sai kuma ta duƙar tana fadin, “Na'am”.
         “Mike damunki? Ki faɗamin dan ALLAH?”. Jin ya ambaci ALLAH ya sakata sake fashewa da kuka, cikin rawar harshe irin na mai kuka tace, “Abdallah ne, gaba ɗaya Abdallah yaƙi sauka daga fushin rashin Nu'aymah. Kuma nama lura yanzu fushin nasa duk a kaina ya tattarashi bansan miya saka ba?. Bayason kirana sam yanzun, sannan ƙiri-ƙiri yaki yazo ko sau ɗaya mu gansa. Idan wancan karon yana ganin baida iyali rashin zuwansa bai damemuba ai yanzu yana dasu, ita kanta tana buƙatar ganin nata iyayen ai Adawiyan. Kuma wancan karan a rana sai muyi waya sau uku hardama video call. Yanzu kam kaga inma bakai ka kirasa ka baniba sam ya manta dani?”. ta ƙare maganar da rushewa da kuka mai ban tausayi.
     Jawota jikinsa yayi kasancewar darene sosai ansha aruwa. Dan sunama zaune ne sun kammala ƙiyamullaili suna jiran lokacin sahur ya ƙarasa su tashi yaran suma.
      Bayanta ya rinƙa shafawa a hankali shima yana jin ɗacin hakan a maƙoshinsa. dan bama ita kaɗai Abdallah kema hakanba, kowama yana masa. Sai dai su da sauƙi saboda harkar business na shiga tsakaninsu akai-akai. Amma ko ranar sai da baba malam da kansa yay wannan ƙorafin na banza da kowa da Abdallah yayi tun tafiyarsa.
    Baki ya buɗe a hankali yace...........✍

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
   *_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
    *_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
       *_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
     *_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
   *_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________
No. 19

..............“Khadijah tabbas kin cancanci ki damu, amma karki manta nima fa ina cikin damuwarne har kashi biyu. Ta shi da taki kema, dan farin cikinki shine nawa dana sauran yarana. Akasin haka duk a wani hali zaki sakamu. Ko yau ke baki lura da yanda Omar ya yini sukuku ba saboda yanda yake ganinki?. Kofa makaranta bai fitaba sai da nai masa magana”.
       Zaune ta tashi sosai tana share hawayenta. “Kayi haƙuri to na daina, amma kodan Adawiya ka sakashi ya biyo Hajjo idan zata dawo suzo suyi salla a gidan dan ALLAH itama iyayensu su ganta, sannan musan yaya zaman nasu yake tafiya”.
        Ɗan murmushi yay mata da shafa kumatunta. Yace, “Karki damu zanyi ƙoƙarin hakan insha ALLAH, nima gobe idan ALLAH ya kaimu zanje kanon, inaga Omar ne zaiyi tafsir ma gobe idan ALLAH ya kaimun insha ALLAH”.
    Kanta ta jinjina masa da addu'ar fatan ganin wayewar garin lafiya.

_____________________________

          Washe gari Abban su Abdallah ya nufi kano domin yin sallama da hajjo da suke shirin wucewa nan da kwanaki biyu. Yako isa da wuri, dan sanda ya shigo gidan ma duk ƴan uwansa na nan, baba malam yanama barci bai tashiba tun ɗazun daya ɗan kwanta. Yaran sun baibayesa da oyoyo kamar yanda suka saba a sashen hajjo, kowa na tambayar ɗan uwansa da suke sa'anni. Yayinda shi kuma yake tambayarsu azuminsu nawa-nawa.
     Ya jima yana biyema shirmensu kafin ya nufi ɓangarensu da babu kowa a ciki, sai dai zuwan nasa Hajjo ta saka Amal da Nu'aymah zuwa su gyara duk da yace ba kwana zaiyi ba. Wanka yaɗanyi ya kwanta kafin azhar ya samu ganawa dasu baba malam, dan yama iske Abba Musbahu yana wajen tafsir danshi na safe ya keyi.

         Bayan gama gaisuwa da Abban su Abdallah Nu'aymah ta nufi sashensu ranta duk a cinkushe, ko kaɗan bata sha'awar wannan zuwa Umrah duk da tana buƙatar hakan fiye da komai a ƙasan ranta. To amma fitinar da take hangoma kanta a tafiyar ta fahimci sai tafi daɗin yawa.
      “Lafiyarki kuwa Nu'aymah? Kina tafiya kamar hankalinki baya jikinki?”. Umm dake zaune a falo tana duba littafin KITABUT TAUHID ta faɗa tana kallonta.
       Zama Nu'aymah tai kusa da ita, tare da ɗora kanta gefen kafaɗar Umm ɗin. “Umm azuminne fa yau nikan tun yanzu na fara jinsa ALLAH, ni koma wajen tafsir bazanjeba yau barci zanje nayi”. Shiru Umm tai kawai tana kallon Nu'aymah, dan gaba ɗaya a watannin nan tana kula da ita kamar akwai abinda ke damunta. Ta zaunar da ita yafi a ƙirga tana tambayarta amma sai tace mata babu komai. Da yake ta san akwai damuwar Abdallah tattare da ita har yanzu sai take danganta yanayin Nu'aymahn da hakan. Shiyyasa ta duƙufa gayama ALLAH akan lamarin. Idan da rabon aure a tsakaninsu ALLAH ya kawo mafita ayi, idan babu kuma ALLAH ya saka musu salama su duka itama ya bata miji nagari.
    Jin Umm batace komaiba itama sai bata sakeyin magana ba, tama lumshe idonu kamar mai barci. 
           Sun jima a haka, kafin Umm da taji Nu'aymah ta mata nauyi a kafaɗa taɗan ɗago ta kalleta, numfashi take saukewa a hankali na barci. ta girgiza kai kawai da ɗagota a hankali ta gyara mata kwanciya a kujerar tare da ɗaura kanta saman cinyarta. Aiko kamar jira take saita sake gyara kwanciya da ƙyau a cinyar Umm ɗin.
        “Ita wannan lafiya take kuwa?” Baba malam da Umm bataji fitowarsa da isowarsa wajenba ya faɗa yana ɗaura hannunsa saman goshin Nu'aymahn. Ɗago ido Umm tai ta kallesa dai-dai ya janye hannun ya sake maidawa a gefen wuyan Nu'aymah.
       “Lafiya lau take, barcine kawai”. Janye hannun yay yana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “To Alhmdllh, bara na leƙa massallaci Mustapha yasanar min da zuwan baƙi”.
    Kanta ta jinjina masa cike da girmamawa, tare da masa addu'ar dawowa lafiya. Da amin ya amsa yay gaba. Harya kusa ficewa a falon sai kuma ya tsaya tare da juyowa. “Banji motsin Muhammad ba, shi yana inane?”.
        “Inaga yana ɓangaren Hajjo, dan tun isowar Abbansu na Abuha ya fice”. Umm ta bashi amsa. “Oh Rizwan ɗin yazo ne?”. Yay maganar yana ficewa batare daya saurari amsa daga Umm ɗinba. Itama ganin ya fice ɗin sai batace komaiba ta maida hankalinta ga kallon tafsir ɗin da takeyi yanzun a WISAL HAUSA.

________________________

            Kasancewar baba malam da anyi magriba yasha ruwa yake barin gidan sai suka yanke shawarar ganawa bayan sallar zuhur shi da sauran ƴan uwansa biyu dan Abba Musbahu yana Lagos.
    Bayan ya kammala da baƙin da sukazo ganinsa bai shigo gidanba dan lokacin salla yayi. Sai da suka idar da salar zuhur ɗin sannan suka shigo gidan a tare ta ƙaramar ƙofa abin sha'awa. Kansu tsaye sashen mahaifiyarsu suka nufa. Inda suka isketa ita kaɗai sai Kubrah dake fashin salla tana barci a kujera. Sallamarsu kuma ta sakata farkawa. Sai ta koma bedroom ɗin hajjo ta kwanta bayan ta gaishesu.
       Duk a ƙasa suka zauna suka zagaye mahaifiyarsu, dan wannan al'adarsu ce inhar suna wajenta basa zaman kujera sai dai ƙasa. Sun gaisheta ta amsa cike da farin cikin ganunsu kamar yanda ta saba. Harda ɗan barkwancinta akan autanta. “Kunzo duk kun zagayeni babu autana”. Dukansu murmushi sukayi, Abbansu Abdallah yace, “Inna ai tunda kin gammu kin gansa”. Dariya taɗanyi irin tasu ta manya. Tace, “Gara dai shima na gansa ɗin dai yaji ɗumina”.
       Dariya suke mata cike da ƙaunarta. Kafin su tsagaita su fara tattauna abinda ya tarasu game da abinda suke tsarawa na hidima bayan tafiyarta. Sun shafe kusan awa ɗaya suna ƙulla abubuwa masu muhimmanci da amfani. A cikin maganganun nasu ne Abbansu Adawiya ke kawo shawarar ya kamata su gayyato bawan ALLAH nan daketa hidima a garesu shan ruwa idan a cikin kano yake inhar yanada halin zuwan.
         Baba malam da shawarar taima daɗi sosai yace, “Mustapha kaga kuma fa kazo da shawara mai ƙyau gaskiya. Dan wlhy bazan ɓoye mukuba inajin matuƙar son ƙwaɗaituwa da ganin wannan bawan ALLAH. Akwanakin nan kodan na saka lamarinsa cikin raina sai nakanta mafarki da shi duk da ban taɓa ganinsaba. Sai dai yanda mafarkin nasa ke zuwamin sai abin yakan zauna cikin raina sosai. Shiyyasa nakeson mu ƙara ƙaimi wajen masa addu'ar fatan alkairi, idanma wani al'amarine ke damunsa ALLAH ke nunamin ta hakan ALLAH ya warware masa”.
       Duk da sun fahimci mafarkin akwai abu mara ƙyau a ciki sai basu takura kansu nason saniba, suka shiga addu'a a garesa da alƙawarin sakashi a duk ibadunsu insha ALLAH. Sunja kusan awa biyu da rabi a wajenta sannan suka fito dan la'asarma tayi. Basu koma ciki ba sai suka nufi massallaci kawai.

________________★

        Shirye-shiryen tafiyar hajjo da Nu'aymah da Yah Ahmad Umrah ya gama kammala tsaf, insha ALLAH gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce. Ta kama dai-dai da cikar azumi kwana goma sha biyar kenan.
       Duk hanyoyin da Nu'aymah zatabi nason ganin tafiyar bata yuwu da itaba tabi amma bata samu mafita ba. Hakan yasa taci kukanta ta haƙura ta barma UBANGIJI ikonsa, dan ta miƙa kukanta wajen ALLAH akan wannan tafiya har batasan iyakaba. Ganin al'amarin ya kasa gagara saita ɗaurasa a mizanin hakan shine mafi alkairi a gareta shiyyasa.

      Zaunar da ita Umm tayi tai mata doguwar nasiha akan wannan tafiya, tare da tunatar da ita manyan ibadu da idan taje zata maida hankali a kansu ba shashanci ba. Tsaf Nu'aymah ta riƙe komai a ranta, tareda ƙarfafa ranta akan insha ALLAH zata zama mai himma. Saboda ma ta gujema abinda take gudun ganin daga Adawiya da Yah Abdallah saita ƙudiri niyyar shiga ittiqafin idan sun isa.
      
        Washe gari ƙarfe biyu na rana jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki ita da Yah Ahmad da Hajjo. Ta tafi cike da kewar Umm da Muhammad harma da baba malam da sauran jama'ar gidan. Musamman ma su Amal da badan basu ƙarasa jarabawarsu guda biyu data rageba da tare zasu tafi.

To Nu'aymah a sauka lafiya. Duk da muna tare dake dan muji yaya wasan zai kaya ke da Adawiya da Yah Abdallah🤔🤗🚶🏻.

_______________________________
            *_DOCTOR YOOHAN_*

     Kwance yake acan cikin garden ɗin gidan nasu daya ƙawatu da korayen ciyayi da furanni kala-kala, tare da ƴaƴan itatuwa da ALLAH yayma bayinsa ni'ima da su. Kwanakinsa biyu kenan a Abuja ya ɗauki hutu na kwanaki goma ne saboda jikinsa daya ɗan motsa masa. 
        Fuskarsa a cinkushe take matuƙa, dan rashin walwalarsa ta yau ta ɗara ta kullum ma. Sosai zuciyarsa ke a matuƙar ƙuntace, shiyyasa ma ya waro kansa daga cikin gidan ya dawo nan cikin garden ɗin a gaban swimming pool dake gefe ya kwanta. Haka yake, a duk lokacin da abin nasa ya motsa yakan tsinci kansa cikin wani irin ƙunci da takuruwa. Komai na rayuwa yakan koma masa baƙiƙƙirin. Yaji ya tsani komai da kowa har aikinsa na taimakon al'umma da yake matuƙar so fiye da komai. Idan yana a wannan halin ko magana baya sonyi da kowa ciki harda iyayensa kuwa. Shiyyasa da ya motsa sai yay wuf ya ɗauki hutu domin samun damar zuwa ya keɓance kansa batare da ya shiga haƙƙin wani ba.
     Duk yanda iskar garden ɗin dana ruwan pool ɗin ke kaɗawa da ƙamshin furanni masu daɗi sam bayajin wani nishaɗi tattare da shi. Hasalima yazo wajen ya zaunane badan yay farin cikiba ko yaji daɗi. Hannayensa da yay filo dasu ya sake gyarawa yana yamutsa fuska kaɗan. Sai kuma yaja tsaƙi tamkar wanda akaima wani abu.  
       A haka Solomon ya shigo cikin garden ɗin a ɗarare, dan yafi kowa sanin idan ogan nasu na irin wannan yanayin babu mai raɓarsa a gidan har iyayensa, suko wani lokacinma sallamarsu yake daga gidan gaba ɗaya ma.......
       Duk da Yoohan yaji motsin mutum a wajen baiko motsaba, har sai da Solomon yay magana cike da rawar baki, “O...Oga good everning, dama saƙone aka kawo maka daga hannun manager ɗin com.......” kasa ƙarasawa yay saboda yanda Yoohan ɗin ya buɗe fararen idanun nan nasa da suka rine suka koma jajaye a kwanakin nan uku da ciwon nasa ya motsa.
       Yanda yake jifansa da kallon ba ƙaramin tayar masa da hankali yayiba, ya ɗanja baya kaɗan dan yana shawarar juyawane kafin abinda baiyi zatoba ya afku yanzun nan. 
      Yoohan da duk yake kallonsa ta ƙasan ido ya maida idanunsa ya lumshe batare da ya nuna alamar yama san da zaman Solomon ɗin a wajen ba. Juyawa Solo yayi da sauri yabar garden ɗin, dan zuciyarsa ta bashi shawarar gwara ya juya yaje ya ajiye masa saƙon a ɗaki idan ya gadama ƙila ya duba daga baya.

         Shigowar Solomon falon ya saka madam Chioma dake cike da tsantsar damuwar halin da Yoohan ɗin ke a ciki ta ɗago tana kallonsa. Risinawa Solomon yay ya gaidata yana nuna mata abinda ke hannunsa da faɗin, “Ma'am zan ajiyema oga wannan a ɗakinsa”.
        Muryar Madam Chioma a cinkushe tace, “Yana ina?”. “Yana garden kwance Ma'am” ya bata amsa cike da girmamawa. Batace komaiba sai miƙewa da tai ta nufi ƙofa, shi kuma Solomon ya nufi sama dan ajiyewa.

       A yanda Solomon ya tafi ya barsa haka Madam Chioma ta shigo garden ɗin ta iskesa itama. Duk da tana tsoron abinda zai iya biyo baya haka ta ƙarasa garesa cikin sanɗa. A gaban kujerar da yake kwance irin wadda ake ajiyewa a gaban swimming pool ɗin nan ta tsugunna saitin kansa. Duk da a yanzunma yanajin motsin sarai bai buɗe idanunsa ba harta kai hannunta kan sumarsa dake a hargitse yau tamkar ba itace ke masifar ɗaukar gyara ba. ta ranƙwafa kanta saman fuskarsa tamkar zatai masa kiss. yanda takai bakinta gab da nashi ya sakashi saurin saka hannunsa ya ɗaura saman bakinsa yay musu katanga. Sannan ya sake saka ɗayan hannunsa da sauri ya riƙe nata data tura cikin gashin kansa, ya buɗe jajayen idanunsa sosai a kanta. A take taga wani fushi na tattaruwa saman fuskarsa mai saka bantsoro ga duk mai kallonsa. Saurin girgiza masa kai ta shigayi cike da kame-kame tana faɗin, “Relax my baby”. Tai maganar jikinta har ɗan rawa yake na tsorata da yanayinsa dan tayi zaton barci yakeyi da farko.
           Batare da yace mata komaiba ya miƙe zaune tare da sakin hannunta daya damƙe, sai kuma ya miƙe ya saka Slippers ɗinsa yabar garden ɗin gaba ɗaya batare da ko waiwayarta yayiba.
     Binsa tai da kallo idanunta na cika da ƙwalla, babu abinda zaka iya hanga a gareta sai tsantsar damuwa da tashin hankali. Kasa tashi tai a wajen har tsahon wani lokaci. Sai da tai kuka sosai kafin ta iya miƙewa tabi bayansa.

      Yoohan da tuni ya shige ciki yana shiga sashensa ya maida ƙofar ya kulle tare da barin key ɗin a ciki dan karma Mom ɗin tace zata biyosa. Kai tsaye ɗakin motsa jikinsa ya shige ya farayi da wani irin yanayi maiban tsoro. Dan komai yana aiwatar da shine fiye da yanda yakeyi idan yana cikin nutsuwarsa. 
      Tsahon lokaci ya kwashe a ɗakin, duk da yanda yay bala'in fita hayyacinsa saboda wahala ya kasa bari ya huta. Sai da yay wujiga-wujiga da shi, daga ƙarshema ya yanke jiki ya faɗi. 
             A take wasu hawaye masu zafi suka shiga gangaro masa a fuska, ya shiga taunar lip ɗinsa ƙirjinsa na sake zafafa, abinda ke kusa da shi ya rarimo yay wurgi da shi, ya sake ɗaukar wani ya ƙara wurgawa. A haka yayta jefe-jefe da kayan ɗakin yana hawaye cike da jin ɗacin da fushi mara dalili.

           Hankalin madam Chioma yay masifar sake tashi fiye da farko. Tunda Yoohan ya fara jefe-jefen nan akan kunnenta ne, taje ta kira su Solomon amma kowa na tsoron shiga ɗakin. Waya ta ɗauka ta kira papa shima. Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Da kukanta shaɓe-shaɓe ta sanar masa da duk abinda ke faruwa.
     Duk da papa yasan da yanayin na Yoohan sai hankalinsa ya sake ƙololuwar tashi fiye da da can. Wannan al'amari na Yoohan na bashi tsoro. Sunyi addu'oin a church, sunyi maganin, sunyi na aaibitin amma abu yaƙi barinsa. Tunda suke basu taɓa gamo da mai kalar matsalar Yoohan ba. Shi ciwon nasa bawai wani waje ne ke masa ciwo a jikinsa ba, likitocima kansu sun sanar musu su basa ganin kowacce irin matsala tattare da Yoohan ɗin, ƙwaƙwalwarsa lafiyarta lau. 
          UBANGIJI shine yasan gaibu game da matsalar Yoohan. Dan haka kawai yake tsintar kansa da kasa yin barci. Sai ya jera kwanaki sama da biyar bai rintsaba koda kuwa yanajin son yin barci, ada sanda abin ya fara masa sai ake yimasa allurar barci mai shegen ƙarfi, a kuma haɗa masa da magani. Idan har akai haka yakan samu barci kona awa ɗaya zuwa biyune ya farka. A hankali kuma yana ƙara girma matsalar na hauhawa, sai yazama kobabu ciwon ma baya iya barcin sai yasha maganin ko anyi allura, kuma baya wuce awa biyu zai tashi. Al'amarin sosai ya fara neman taɓa masa rayuwa da karatu, amma da yake yanada ƙwazo sai akaita lallaɓawa.
     A lokacin da karatunsa na likitanci ya fara zurfi sai ya fahimci shan maganin barci da yin allurar barci illace a lafiyarsa da hankalinsa da kuma aikinsa dake cikin manyan burikansa na rayuwa. Ballema da ALLAH ya taimakesa shaye-shaye baya cikin abin sha'awarsa, dan ya jima da fahimtar inhar zaiyi shaye-shaye koda na giyane to bafa zai kai labariba akan burin zamansa likita, sai kuma Asthma da yake da ita, itama ta taka rawar gani wajen sakashi ƙyamatar bushe-bushen hayaƙin samarin zamani. A ɗan tsakanin da ya daina yarda amasa allura, ya kuma daina shan maganin barci yasha matuƙar wahala, komawa yay tamkar wani ƙaramin mahaukaci, (kunsan rashin barci matsalane). Ya koma babu abinda ya keyi sai baƙin rai, abu kaɗan zai hau fushi, baya walwala sam, baison hayaniya, magana ma sai yaso ya keyinta. Karatunsa ma sai ya fara neman yin tangal-tangal. 
     Baya son zuwa aji, akoda yaushe yafi buƙatar zamansa a hostel shi kaɗai, idan kuma ya fito sai ya koma can gefe guda ya zauna inda mutanema basa gilmawa. Duk da wannan tashin hankali da Yoohan yake a ciki yana nan akan bakansa na daina yarda ayi masa allurar barci ko yasha magani, ya yarda zai jure duk wani matsi da rayuwa zatazo masa da shi dan ya samu ya sai-saita rayuwarsa kodan samun cikar burinsa. Aikam ya jigatu, dan a tsakanin badan Rich ba da ƙwaƙwalwarsa ma zata iya taɓuwa.
      A cikin wannan yanayin da ya tsinta kanshi a wata ƙasa suka sami hutun sati biyu. A wannan karon sai ya haɗa kaya yace shi zaije gida 9ja hutu. Rich yayi mamaki matuƙa, dan yasan burinsu shine bazasu taɓa zuwa gidaba sai sun kammala karatu. Duk yanda yaso tunama Yoohan wannan alƙawarin yaƙi saurarensa sam, haka dole ya barsa ya shirya ya taho Najeriya. Da yazo Najeriyar ma bata canja zaniba. Dan sai addu'in coci da kullum papa yake kan kaisa ai masa bayan nashi, sai kuma masu magani da basu maraba da a kirasu da matsafa kowa na gwada tasa fasahar.
        Ahaka ya kusan cinye hutun babu wani ci gaba, saima gaba al'amarin yakeyi dan yanata ƙara nisanta kansa da zama cikin mutane, ya kuma daina fara'a sam balle walwala. Cikin amincin ALLAH ana saura kwana biyu zai koma makaranta ALLAH ya haɗa shi da wani bawan ALLAH da wani yammaci, ya ɗauka mota ya ɗan fita daga gida suka kusayin taho mu gama da motar mutumin. Hankali a tashe waɗanda suke a waccan motar suka fito, amma shi Yoohan sai yaƙi fita yay zamansa a mota yana cika yana batsewa. Su duk zatonsu wani abun ya samesa, sai da suka buɗe motarsa dansu duba sai suka samesa lafiya lau. Sai dai kuma mutumin kallo guda yayma Yoohan ɗin ya fahimci yana tare da damuwa sosai, duk da wani kallon banza dana takaici da Yoohan ke musu sai yay murmushinsa daya ƙarama kamilar fuskarsa kwarjini, cikin kwantar da murya ya kama hannun Yoohan ya fiddosa a motar, ya saka drivernsa ya ja motar gefe dan a tsakkiyar titi suke. Danma titine na anguwa babu yawan shiga da fitar motoci.
     Da farko Yoohan yaso bijirewa, sai dai kwarjinin mutumin ya cika masa idanu har yaji bazai taɓa iya masa musu ba. Can gefe bawan ALLAH nan yasa suka zauna, ya amshi ruwan da yasa drivern sa ya ɗakko masa a mota ya bama Yoohan yace ya sha. Nanma sai bai musaba ya amsa yasha kusan rabin robar yana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da ya huta na wasu mintuna sannan mutum nan ya shiga masa tambayoyi cike da nutsuwa da kulawa. Wasu Yoohan ɗin na bashi amsarsu, wasu kam sai yay masa shiru.
             Duk da bawan ALLAH nan ya fahimci Yoohan ɗin ba musulmi bane sai ya dubesa cike da kulawa yace, “Idan na baka wani magani ka gwada zaka amsa kasha?”. Kallonsa Yoohan ɗin yayi na wasu mintuna yana nazari, kamar bazai amsaba sai kuma can ya ɗaga masa kai alamar “eh”. Murmushi wancan mutumin yayi a wancan lokacin, ya ɗauka goran ruwan da Yoohan ɗin yasha ya rage yay addu'oi a ciki ya bashi. Yoohan ya jima yana kallon ruwan kamar bazai sha ba, sai da yaja lokaci mai tsayi sannan ya kafa baki ya shanye. Murmushi mutumin ya sakeyi, ya kama kan Yoohan yay masa addu'oi ya tofa masa. Daga haka yace masa ya koma gida ya kwanta, insha ALLAH yau sai an gaji da dogon barcinsa a gidansu an tadashi. Da izinin ALLAH kuma indai matsalar barcice ya daina fuskantarta sai dai idan hakan yana cikin doguwar ƙaddararsa.
      A lokacin Yoohan ya tashine kawai ya bar wajen amma ko godiya baima mutuminba dan bawai ya yarda da zancensa bane, tunda shi yasan faɗi tashin da iyayensa keta famanyi akan matsalar. Shi kuma mutumin bai damuba sai kallo kawai ya bisa da shi a ransa yana fata da sakankancewa UBANGIJI zai amsa masa addu'arsa tai tasiri akan Yoohan ɗin.............✍
      
     

_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
   *_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
    *_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
       *_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
     *_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
   *_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

No. 20

..............Aiko ALLAH ya amsa masa, dan cikin amincinsa Yoohan na komawa gida bai rufa awa ɗaya ba wani irin barci mai daɗi da saka kwanciyar hankali yay awan gaba da shi. Sai ga Yoohan da ya kwanta tun kusan shida na yamma bai farkaba sai goma na safiyar washe gari.
     Wannan al'amari ya bama Yoohan da su Papa mamaki, suka shiga masa tambaya akan yaya akai yay barci jiya?. Bai ɓoye musu komaiba ya basu labarin haɗuwarsa da mutumin da bai sani ba, bai kuma san inda zai sake samunsa ba a yanzun. Duk da sunji daɗin hakan sai suka nuna rashin damuwarsu da sanin wanene mutumin ko inda zasu samesa, saboda kawai sun fahimci musulmi ne. Yoohan ɗin kuma ya koma inda suka haɗu da mutumin har kusan sau huɗu bai samu koda mai kama da motarsaba ma balle shi ɗin. Haka ya haƙura badan yasoba ya koma makaranta.
      Wannan shine dalilin samun sauƙi sosai daga matsalar Yoohan, ya koma yana barcinsa lafiya lau kamar kowa, sai dai lokaci-lokaci abin nasa kan buga, idan kuma ya juyo yana tsintar kansane cikin mawuyacin hali na baƙin rai da fushi da tsangwamar kansa. Dama gashi dalilin hakane sanadin maidashi mutum mara fara'a da son hayaniya.
     To a yanzu gashi al'amarin nasa ya sake motsawa, duk da yakan jima baiyiba ma. Yau kwanakinsa uku kenan da dawowa ƙasar, amma ko barcin mintuna goma ya kasa ɗaukarsa. Yanda yake ganin rana haka yake ganin dare. Ya mugun fita hayyacinsa a kwana ukun nan, ya daina magana da kowa, abincima ya masa yajin aiki sai abinda ba'a rasaba yake ɗanci idan yaji yana neman halaka a banza. 

★★★★

       Cikin murya mai cike da lallashi papa ke kiran sunan Yoohan ta jikin Window da suke a tsaye shi da Madam Chioma. Duk da yana jinsu bai fasa wurgi da abinda duk yaci karo ba a ɗakin, har wani sashe na gilas ɗin dake zagaye da ɗakin ya tsage, dan ya jefa ƙarfe ne ya bigi gilas ɗin dake a matsayin bango ɗakin.
      Sai da ya jigata dan kasan sannan ya zube a ƙara yana wani irin sauke ajiyar zuciya mai ƙarfin daban tsoro.. Duk da hankalinsu ya ɗan kwanta ganin yabar jefe-jefen basu daina kiran sunansa da roƙon ya buɗe musu ƙofarba cike da lallashi. Shi kuma yayi banza dasu tamkar baisan da zaman nasu a wajenba.  
       Papa ne ya tuna da extra keys ɗin sashen nasa, dan haka yabar wajen Window da sauri zuwa bedroom ɗinsa. Mintuna ƙalilan sai gashi ya dawo cike da farin cikin samo keys ɗin. Hakama Madam Chioma saboda daɗin da taji har kiss taima papa tare da rungumesa. Zagayawa sukayi domin buɗe ƙofar, sai dai kuma key ɗin yaƙi shiga alamar yabar wani key ɗin a ciki. Ransu duk a jagule suke bin ƙofar da kallo, madam Chioma har hawayenta sun dawo kwarara.
     Solomon ne ya kawo shawarar bin ƙofar can baya dake sada mutum da ɗakin motsa jikinsa kai tsaye. Su ruɗewama ta sakasu mantawa da ƙofar. Da sauri suka zagaya tacan, cikin amincin ALLAH kuwa suna gwada key ɗin da suketa kokwanton ba nata bane sai gashi ya buɗe musu.
       Har rige-rigen isa garesa kuwa sukeyi. Duk da yana jinsu bai motsa ba, sai da sukasha fama, dan Yoohan akwai taurin kai dama, da ƙyar ya yarda suka tadashi zuwa ɗakinsa. Madam Chioma da kanta ta shiga toilet ta haɗa masa ruwan wanka mai ɗumi sosai. Kafin ta dawo inda papa ke rungume da shi yanata faman lallashinsa da masa magana mai daɗin gaske, wadda ko ba'a faɗaba da alama tana tasiri ga Yoohan ɗin.
     Zama tai kusa dasu itama, ta miƙa hannu ta riƙo na Yoohan ɗin tana murmushin jin daɗin ganin ya nutsu,  matsawa tai jikinsa sosai zata rungumesa kamar yanda papa yay masa, sai ya ƙwace hannunsa ya miƙe zumbur. Cike da basar da abinda ya fahimci zatayin ya nufi toilet yana ɗingishi, dan da alama yaji ciwo a ƙafar tasa ne.
    Duk binsa da kallo sukai ita da papa, yayinda ranta ya sosu sosai akan yanda Yoohan ɗin keyi mata a duk lokacin da ta nufi yimasa makamancin waɗan nan abubuwan. Tarasa dalilinsa na yimata hakan, ‘shi kodai ya fara tunanin.......’ sai kuma ta kasa ƙarasawa ta girgiza kanta alamar ba haka bane. Dariyar papa ta sakata saurin kallonsa. Ya ɗage mata gira da matsowa shi ya rungumeta yana faɗin, “Ɗanki fushi yakeyi dake yau, kinga yamaƙi yarda ki rungumesa. ni zo na rungumeki”.
         Fuskarta a yatsine taɗan turesa, cike da salon yaudara ta matsa baya da juya masa keya irin maganarsa ta ƙara mata haushin nan. Shiko ya sake matsowa jikinta ya rungumeta ta baya yana dariya ƙasa-ƙasa. “Wasa nake miki Momyn Yoohan, shima nasan yanayin da yake cikine kawai ya sakashi aikata miki hakan”.
          Duk da haushin da take ciki sai maganar papan taɗan sanyaya mata rai, dan ita ada tunaninta ba haka yake kawo mata ba. Juyowa tai idanunta cike da ƙwalla, muryarta na rawa tace, “Darling! Anya kuwa bazamu nema mutumin nan daya taɓa yimasa maganiba shekarun baya da suka wuce sannan muna farko-farkon zuwa Abuja?”.
        Papa dake kallonta ya ɗan ɓata fuska yana nazarin maganarta, sai da yaja tsahon lokaci kafin ya amsa mata. “Shawaranki mai ƙyaune momyn Yoohan, sai dai kuma a ina zamu samesa? Shi kansa Yoohan ɗin bana tunanin zaima iya ganesa idan ya gansa ai”.
     Kafin ta samu damar bama papa amsa Yoohan ya fito daga toilet ɗaure da towel, dan duk zatonsa sun fita. Turus yaja ya tsaya yana kallonsu fuska a turɓune.
        Ahankali madam Chioma ta sauke idanunta akan buɗaɗɗen jikin yaron nata dake ɗauke da wata lafiyayyar farar fata mai santsi da ɗaukar idanun mai kallonsa. Basai an faɗaba a kallo ɗaya zaka fahimci shi ɗin ya tashi cikin kulawar rayuwa da jin daɗi, dan sam babu alamar rama tattare da shi......
       Jikinsa ya fara ja da baya yana ƙara tamke fuska, hakan yasa Mom saurin tashi tsaye har tana neman faɗuwa, da yarensu tace, “Ina zaka kuma yaro na? Kaga zo na shafa maka man ma da kaina idan bazaka iya b.....”
          Kafin takai ƙarshen maganarta harya maida ƙifar bayin ya rufe, jingina yay a jikinta ya lumshe idanu zuciyarsa na ƙara ƙarfin bugu. Duk da yanda take buga ƙofar a hankali tana kiran sunansa bai motsa ba, sai ma wani haushi dake sake ziyartarsa. Sam bayason wannan halin da Mom take masa, a ganinsa bai daceba, yakamata tasan da ba yanzu bane, yanzu fa ya girma, shekararsa talatin har da biyu a duniya, miyasa bazata daina masa kallo kamar ɗan shekara goma ko ƙasa da hakaba?. bawai yana saka abinda take masan a wani mizani daban bane, dan yasan soyayyar da suke masa mai yawa ita da papa ne ya jawo hakan, amma ya kamata ta fahimci yanzu ya wuce ta dinga masa wasu abubuwan kanta tsaye ai......
         A hankali ya buɗe kumburarrun idanunsa dake cike da barcin da baisan ranar yinsaba, ya sake lumshesu yana sauraren yanda Papa ke lallaɓa Mom akan su fita su bashi waje ya shirya, idan yaso saisu dawo daga baya. 
     Badan madam Chioma taso hakanba ta yarda suka fita ɗin ranta na mata ƙuna.

       Yoohan najin sun fita shima ya fito, dan dama a gajiye yake da tsayuwar saboda ƙafarsa wani bala'in zogi take masa. Sai da ya leƙo ya tabbatar babu kowa sannan ya fito. Bai kalli ko inda Mirror ɗinsa yake ba balle ai tunanin shafa mai ya nufi wajen kayansa kawai. Dogon wando ash mai taushi da farar t-shirt data kama jikinsa ya saka. Ya taka zuwa gaban gadon yana cije baki, zama yay yana mai kallon ƙafarsa data ɗan kumbura dai-dai idon sawu. Hannu yasa ya taɓa wajen yana yamutsa fuska, duk da zafin da yaji haka ya daure ya kama ƙafar yaja da ƙarfi. Siririyar ƙarar azaba ya saki tare da sakin ƙafar itama.
     Har rige-rigen shigowa ake tsakanin papa da Mom da Richard da yazo gidan yanzu babu jimawa. Sai Solomon da Miracle dake ƙoƙarin shigowa falon suma Joy biye dasu tare da masu aiki dake ɗauke da abincin Yoohan ɗin.
      Yanda sukagansa a kan gadon ya saka hankalinsu sake tashi, suka zagayesa da tambayoyin yaya akai?. Duk da surutun nasu haushi yake sake bashi sai ya tashi zaune, ganin Rich tare da su ya sakashi miƙa masa ƙafarsa. Kallon ƙafar Richard yayi da ƙyau, kafin ya jawo stool ɗin mirror ya zauna yana tambayarsa garin yaya yaji ciwon?.
     Bai tanka masa ba, dan haka Rich ɗin ya kama ƙafar kawai ya hau ja masa. “Jesus!!!” ya faɗa da muryar nan tasa mai amo data haɗu da damuwa a yanzun. Saurin zama Momy tai a kusa da shi ta amshe filon daya damƙe ta maye gurbin filon. Caraf kuwa ya kama hannunta ya damƙe cikin nasa da masifar ƙarfi, dan har sai da ta saki ƙara itama.
     Yanda jikinsa ke rawa zufa na fito masa sai duk tausayinsa ya sake kamasu, Miracle tai saurin zama ɗaya gefensa tare da kwanciya a jikinsa tana hawaye. Sai da Rich ya tabbatar ƙafar tayi yanda ya kamata sannan ya barsa. Sai faman jera masa sorry sukeyi.
      Duk da yaji mutum kwance a jikinsa bai motsaba sai da zafin ƙafar ya daina sosai, a lokacin ƙamshin turaren Miracle dana Momy suka tabbatar masa sune nanuƙe da shi. A hankali yasa hannu ya ɗaga Miracle dake lafe a jikin nasa, kafin itama Mom da tunda ta farga da Mira take zuba mata wani kallon ƙasan ido na gargaɗi, shi dai ya zare hannunsa daga cikin nata, jan jikinsa yay baya ya haye gadon sosai batare da yace uffanba duk da sannun da suketa faman yimasa har yanzun.
         Cike da kulawa Rich ya basu shawarar ya kamata su fita abar Yoohan ɗin ya huta, dan ya kula da yanda Yoohan ya sake cika tamkar zai fashe, hakan kuma yanada nasaba da zamansu a ɗakin, dan shi ɗin shaidane akan yanda Yoohan yay mugun tsanar jin kowanne kalar motsi a kusa da shi idan har yana cikin wannan yanayin.
        Papa da ya gamsu da shawarar Rich ɗin sai ya tarkatasu suka fice duk da uwar gayyar Mom bataso hakanba ita. Bin bayansu Richard yay shima dan yana buƙatar ɗakko wani abun da yake son gwadawa Yoohan ɗin ko zai aminta wannan karon yasha.

           Yoohan na zaune yanda suka barshi idanu a lumshe Richard ya dawo ɗauke da ƙaramin tray mai ƙyau. Duk da Yoohan na jinsa bai buɗe idanu ba balle ya motsa, Rich ya jawo ƙaramin table glass dake gaban sofa zuwa gaba gadon. Trayn dake ɗauke da kwalbar barasa da kofuna biyu, sai ƙanƙara a wani bowl ya ɗaura a kai yana kallon Yoohan ɗin. “Mr-x!”. Ya faɗa yana ƙoƙarin buɗe kwalbar barasan.
      Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali batare da ya amsama Rich ɗinba. Rich ya ɗan murmusa, dan bai damu da rashin amsawarba, barasan ya zuba rabin kofi, ya ɗiba ƙanƙara ya zuba a ciki yana murmushi. Ɗagowa yay ya miƙama Yoohan dake kallonsa ta ƙasan ido kofin.
     Ɗauke kai Yoohan yayi fuskarsa na nuna ƙarin ɓacin rai, dan yasan Rich ɗin yafi kowa sanin shi baya shan giya...........
          “X-Man! inhar bazaka yarda na maka allurar da zata taimakeka kayi barci ba to ka daure kasha wannan, na tabbatar ita zata saka ka barcin koda na awa ɗaya ne. Kai fa likitane, kasan illar wannan matsalar da yanda take maida rayuwar mai fuskantarta a ƙarshe. Idan kana tunanin ƙin shan giya ne dan karta shiga maka rayuwar aiki yanzu ai ba'akan aikin kake ba, sannan don neman lafiyarka ne”.
         Shiru kamar Yoohan bazai kulasa ba, dan har Rich ɗin ya fidda tsammanin samun kulawarma. Sai ya tsinkayi sautin tsakin Yoohan ɗin a hankali. Kallonsa Yoohan ɗin yake cikin ido da jajayen idanunsa dake a kumbure, murya a daƙile yace, “Rich! a wajenka ya kamata mutane su ƙara sanin halina akan idan nace bazanyi abuba bazan taɓa yinsa ɗinba, dan haka karka sake tunanin zansha barasa koda ba yau ba”.
        Yanda yay maganar cikin kaushin murya ya saka Rich saurin cemasa “I'm very sorry”. Batare da Yoohan ɗin ya sake cewa komai ba ya maida idanunsa ya lumshe duk da yasan barcin ba ɗaukarsa zaiyi ba.

     Haka suka cigaba da zama a cikin ɗakin shiru, Richard da ya sha barasar da Yoohan yaƙi sha har ya fara barci a gefen sa, shiko idanunsa biyu amma suna a lumshe. Lokaci-lokaci hawaye kan ziraro masa ta gefen ido. Yana sauraren yanda Momy da Papa keta faman zaryar leƙowa ɗakin, sai dai ɗauka suke ko Rich ɗin yaci nasara yasha giyar barci ya ɗaukesa, shiyyasa hankakinsu yaɗan kwanta suketa faman jin daɗin yanda duk shigowar da sukeyi suna samun Yoohan ɗinne a kwance.
   
       Wajen misalin goma na dare Yoohan ya gaji da kwanciyar, tashi yay ya sauka daga gadon yana bin Rich dake barcinsa hankali kwance da kallo, bayi ya shiga ya watso ruwa. Bai jimaba ya fito sanye da bathrobe. a bakin gadon ya zauna tare da jingina da fuskar gadon. Ya kai hannu zai kashe fitilar gefen gadon idanunsa suka sauka akan farar envelope, cak ya tsaya yana kallon rubutun jiki, janyewa yay kamar zai share, sai kuma yasa hannu ya ɗauka tare da buɗewa ya zaro takardar dake a ciki.
     Rubutun bashi da wani yawa sosai, amma a tsare yake gwanin sha'awa, sannan yanda aka tsara kalaman cikin rubutun da harshen turanci sunyi matuƙar jan hankalinsa har yana ɗan lumshe ido. Sai da ya maimaita takardar sau biyu sannan ya ninketa ya maida cikin envelope ɗin ya jawo drawer ya ajiyeta yana juya abinda ta ƙunsa a cikin ransa.......

________________________
        *_SAUDIA_*

       Duk da fushi da zuciyarsa keyi ga duk zuri'ar gidan tasu hakan bai hanashin jin ɗokin zuwan hajjo da Ahmad ba, dan baisan harda Nu'aymah a tafiyarba. shiri yay tsaf ya wuce airport domin tarbosu batare da ya saurari Adawiya da tace zata bishi ba, dan tana wanka ma ya siɗaɗe ya fice daga gidan.

       Cikin sa'a kuwa yana isa airport ɗin jirginsu Nu'aymah na taɓa ƙasa. Lumshe idanu tayi tana karanto addu'oi da fatan cika alƙawarin da taima iyayenta akan kama kanta batare da wata fitina ta ɓullo ba. Hajjo na lura da duk motsinta, amma sai batace da ita komaiba har sukabi ayarin masu fita. Sanye take cikin wando blue na jeans da farar rigar fakistan da tsahonta yake har gwiwar ta, an ma rigar ado da blue ɗin duwatsu manya da ƙanana, sai farin veil da ta naɗa a kanta wanda ya sake fidda ƙuruciyarta da ƙyawun da ALLAH ya bata. Farar ƙafarta da kalar wandon ya haska tana sanye cikin blue ɗin takalmi da yay masifar mata ƙyau dan bata da babbar ƙafa sam. Sai ƙaramar jakarta itama dai blue ɗince.
     Kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tai lokacin da suke ƙoƙarin sakkowa daga jirgin, ta ɗan yamutse fuska tana sauke hannun a hankali da kai dubanta can ɗan nesa dasu. Wani irin bugawa ƙirjinta yayi saboda hango Abdallah dake tsaye jikin motarsa sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau, ya ƙara ƙiba da ƙwarjini a idanun mai kallo kamar ba azumi ake ba. A take wata kasala ta saukar mata, tafiyarta ta sake raunana fiye da farko. Dan sai da Hajjo ta kama hannunta ta ida sauka da ita ma.
      Abdallah da ya yunƙuro saboda hango Ahmad dake a gabansu da yay yaja ya tsaya cak lokacin da idanunsa suka sauka akan Nu'aymah da bai zato ko tsammaanin gani ba.. Wata irin hajijiya-hajijiya ya faraji tana neman ɗibarsa a wajen, ya kasa motsi balle ɗauke ido daga kallonta har suka ƙaraso inda yake.
    Hajjo datai tamkar bataga halin da suka shiga ba ta mangare masa ƙeya tana faɗin, “Kurwata kur dan gidanku”. Firgigit yay da sauke nannauyan ajiyar zuciya, sai dai ya kasa ɗauke idanun nasa daga kan Nu'aymah da ta ɗauke kanta gefe tamkarma batasan da zamansa ba a wajen. Hannu yakai ya shafa inda Hajjo ta tallaresa kafin ya janye idanunsa da ƙyar ya maida kan hajjon data wani ƙyaɓe fusaka tana zuba masa harara.
      “Yanzu dan ALLAH daga zuwanki mina miki zaki tallemin kai?”. Ya faɗa yana ɓata fuska da kallon Hajjon. Watsar dashi tai taƙi magana, saima hannun Nu'aymah data kamo suna shirin barin wajen.
    Dariya Ahmad yayi, ya matsa ya rungume Abdallah, “Oh Yaya kaifa kai da Hajjo sai a slow, manta da batunta kayi tani da ƙanwarmu kawai”. Murmushi Abdallah yay tare da rungume Ahmad ɗin shima. Kafin su saki juna kowanne fuskarsa da murmushi jin daɗi. Abdallah ya sake kai dubansa ga Nu'aymah sannan ya kalli Ahmad.
     Kai Ahmad ya ɗan jinjina yana murmushi, amma baice komaiba sai ƙyafta idanu da yayma Abdallahn. Ab ya kaɗa kansa kawai da nunama Ahmad hanya alamar suje to.

         Nu'aymah da Hajjo na baya, yayinda Ab da Ahmad ke gaba. Hajjo ce kawai ke magana a motar Ahmad na tayata, dan mafi yawan maganar tata duk tsiya takema Abdallah, shi kuma Ahmad ɗin na karesa.
      Abdallah kam rabin hankalin na'a tuƙi ne rabi akan Nu'aymah da a yanzuma ta ɗauke kanta tamkar bata gansa ba. A haka suka iso madaidaicin gidan nasa mai ƙyau da tsari. Sai da ya faka motar inda ta dace kafin su fita shi da Ahmad, Ahmad ya buɗe na Hajjo, ya taimaka mata ta fito, Nu'aymah kuma ta buɗe da kanta ta fito tana kallon gidan dama anguwar gaba ɗaya, a baɗini kuwa zuciyarta har wani zallo take saboda ganin Yah Ab ɗinta, duk yanda tai tunanin zata daure sai ganinsa ya canja dukan ƙudirin nata lokaci guda. Sai dai kamar yanda ya fiske itama haka tai ƙoƙarin fiskewar.

         Abdallah ne a gaba lokacin da zasu shiga gidan, Ahmad da Hajjo biye da shi, sai Nu'aymah a ƙarshe tana karanto duk addu'ar da tazo mata a baki domin samun sassauci daga abinda takeji akan ganin Abdallahn.
        Falon tsaf yake ko ina a gyare, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi da sanyin ac. Sallamar Abdallahn da karaɗin Hajjo ya saka Adawiya data cika da haushin tafiyar Abdallah batare da ta saniba ta fito. Sam idanunta basu kai a kan Nu'aymah ba, dan haka ta daka tsalle cike da ihun murna ta ɗane Hajjo, saurin riƙota Ahmad yayi yana faɗin, “Ke malama karki ƙarasata ki jamin tsiya wajen su Baba malam”. Sakin Hajjon tai tana dariya ta juyo ta rungume Ahmad ɗin shima tana tsale.
          “Wannan matar taka bata da man kai sam Yah Abdallah ”. Ahmad ya faɗa yana janye Adawiya daga jikinsa. Murmushi yaƙe Abdallah yayi yana kama hannun Hajjo ya zaunar a kujera. Hakan yay dai-dai da ɗagowar Adawiya zataima hajjo magana idanunta suka faɗa akan Nu'aymah dake tsaye gefe tana kallonsu.
      “What?!!!!” Adawiya ta faɗa da sauri tana waro idanu waje, a take ta sarƙe da yawu kuwa ta hau tari.
       Karan farko Nu'aymah ta saki wani lallausan murmushi da har ya bayyana fararen haƙoranta waje, ta taho da wani irin ɗoki ta rungume Adawiya dake tari tamkar zata amayo harshenta.
     Dakatawa Abdallah da Ahmad da suka miƙe saboda ƙwarewar Adawiyar sukai. Nu'aymah ta ƙanƙame Adawiya jikinta tana matso ƙwallar da suka taru mata a ido akan dalili biyu. Ganin Abdallah, da kuma kewar Adawiyan. 
      Da wani irin sauri Adawiya tasa hannu biyu ta tura Nu'aymah, jikinta na wani irin rawar tashin hankali............✍

🤔Tofa, hajiya Adawiya yaya dai?🤗🚶🏻.


Barka da juma'a😍😘😍🤗


_______________________________

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
   *_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
    *_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
       *_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
     *_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
   *_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________






No. 21

.................“Adawiya!!” hajjo ta faɗa a ɗan tsawace. Yayinda Ahmad da Abdallah ma sukai wani zallon mamakin abinda Adawiya tayi suma.
     Kallonsu tai a firgice idanunta na tara ƙwallar takaici da jin zafin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Ta buɗe baki zatai magana a zafafe sai kuma ta tuna abinda ta nema mantawa. Saurin sauke numfashi tayi tana fashewa da kuka, tare da juyawa ta kalli Nu'aymah dake tsaye dafe da kujerar data taimaketa ta hanata faɗuwa lokacin da Adawiyar ta turata.
       “Nayi fushi wlhy Aymah, yanzu dama dake za'azo amma kikaƙi sanarmin saboda ke yanzu kinma daina sona?”. Adawiya ta faɗa cike da makirci da waskewa. 
     Ajiyar zuciya Abdallah da Ahmad suka sauke, dan duk zatonsu Adawiya da gaske da faɗa tayi abinda tayi. Hajjo dai bata motsa ba, amma ta kafesu da kallo su duka huɗun tana nazarin kowa. 
     Jin abinda Adawiya tace ne ya saka Nu'aymah sakin murmushi, dan tsaf ta fahimci Adawiya canja hanya tayi, inkuwa hakane ai itama tanada wayonta, dan wani abun ma sai dai ta koyama Adawiyar duk da kuwa ta girmeta da wasu wattani. Sake tahowa tai da ɗan gudunta ta rungume Adawiya tana faɗin, “Afuwan habibiya, surprise nai niyyar miki shiyyasa na hana kowa faɗa miki”.
        Leɓe Adawiya ta cije dan ta juyama su Hajjo bayane, itama cike da ɗacin zuciya ta rungume Nu'aymahn tana magana cikin kuka, “ALLAH saina hukunta ki tunda kika sani kuka”. Nu'aymah tai dariya hawaye na sakko mata itama, ta ɗago Adawiyan daga jikinta tana durƙusawa gabanta da riƙe kunnuwanta, “Afuwan hassanata, kaina bisa wuya Please”.
    Karan farko Adawiya ta saki dariya, itama sai ta durƙusa kamar yanda tayi sunama juna kallon ido cikin ido, Nu'aymah murmushi takeyi, Adawiya kam ta haɗe fuska ganin su hajjo basa ganinta. “Kin haƙura kenan?” Nu'aymah ta faɗa tana wani ɗage ma Adawiyar gira ɗaya da sakin mata lallausan murmushin da yay mata tsaye a maƙoshi.
      Kasa magana Adawiya dake mata kallon tsantsar takaici da haushi tayi, sai kawai ta rungumeta a jikinta tana gyaɗa kai........
       Gyaran Murya Yah Ahmad yay yana faɗin, “Kunga malamai ya isheku haka, ku barmu mu ƙarasa ƴar yunwar azuminmu da sauran yawu a baki dan ALLAH, idan akasha ruwa komaima sai kuyi zamu tayaku da sulhu”.
         “Faɗa musu dai”. Abdallah ya faɗa a wani irin yanayi yana komawa kusa da hajjo ya zauna. Ƙaramar dariya Hajjo tayi kawai tana ɗauke kanta, sai kuma ta kalli Abdallah tana faɗin, “Kaga Audillahi kaini ɗakina na huta kaji, bazan iya luguden laɓɓa ba da azumina a baki”.
        Fuskarsa ƙawace da murmushi ya miƙe tare da taimakama hajjon itama ta tashi. Har ɗakin da zata zauna ya rakata, tana zama Nu'aymah na shigowa itama. Duk kallonta sukai shi da Hajjon, ta ajiye jakarta tana zama a kujerar dake a ɗakin ƙwaya ɗaya tal, batare data kalli Abdallah ba tace, “Yah Ab! Ina yini?”. Kallonta yay a karon farko suka haɗa ido, sai ta ɗauke nata gefe tana komawa jikin kujerar ta jingina.
    “Kunzo lafiya?”. Ya amsa mata shima cike da basarwa, dan haka kawai yanzu yakejin zafin abinda ta aikata a ranar ɗaurin aurensu. Ƙin sake tanka masa tayi, hajjo kuwa tamayi kamar bata a ɗakin.
      Ƙofa ya nufa dan kai Ahmad nasa masaukin yana faɗin, “Ki taso ki koma ɗakin Adawiya, ita hajjo sai ta zauna anan...”. Kafinma ya rufe baki cikin sauri tace, “A'a zan zauna anan tare da Hajjon”.
     Da ga Hajjo har Abdallah kallonta sukai, amma saita ɗauke kanta tana ɓata fuska danma kar Hajjon tace dole sai taje. Shima har zai sake magana sai kuma ya fasa ya fita kawai.

     “Miyasa bazakije can ɗinba? Bayan ƴar uwarki na cike da ɗokin ganinki?”. Hajjo ta faɗa bayan ficewar Abdallah.
        Nu'aymah dake ƙoƙarin cire kayan jikinta tace, “Babu komai Hajjo, nafison kawai na zauna da ke kodan himma akan ibadar da mukazoyi, sannan nifa ma ittiqafin zan shiga insha ALLAH”.
      Murmusawa Hajjo tayi kawai tana ɗauke kanta batare da ta sake cema Nu'aymah komai ba, itama Nu'aymahn sai ta shige bayi abinta batare data jira amsar hajjon ba.

★★★
     
        “Kuturun ubancan kayyasa! Yanzu wane algungumine mai wannan shirya tafiyar a gidanmu?”. Adawiya daketa faman zagaye ɗakinta ita kaɗai ta faɗa tana cizar laɓe kamar zata hudashi. Ganin babu mai bata amsa ta rarumo waya ta fara neman maman Aaida. Bugu biyu kuwa ta ɗaga. Harta fara tsokanarta Adawiyan ta katseta da faɗin, “Maman Aaida yanzu ba lokacin wasa bane, ko kinsan sister ɗin nan nawa da zata auri Yah Ab da, ta biyo kakarmu sunzo Umrah tare?”.
      Da ƙarfi Maman Aaida tace, “Na shiga uku, da gaske dan ALLAH?”. Adawiya da ranta ya ƙara dugunzuma tace, “Wlhy kuwa. Bama zuwan nata bane tashin hankalina Maman Aaida, kinga kuwa yanda Yah Ab duk ya susuce, gashi kakarmu ɗin nan shegen sa idone da ita wlhy”.
       “Tab, lallai aiki ya samemu, dan kuwa wlhy mukai sanya to ki tabbatar nanda wata ɗaya ko sati biyu ma mijinku zai koma na mata uku....”
     “ALLAH ya kiyaye” Adawiya tai saurin katse Maman Aaida hawaye na ziraro mata a idanu. Takaicin maganganun maman Aaida ya sakata katse kiranma gaba ɗaya tai wurgi da wayar kan gado.
     Abdallah dake ƙoƙarin shigowa ɗakin yace, “Lafiyarki kuwa kike wurgi da waya? Kamar ba kuɗi akasa aka saya ba!”. Da sauri tasaka hannu ta share hawayenta, kafin ta nufesa ta rungume da ƙarfi. Saurin tureta yay yana faɗin, “Haba Adawiya, shin wai kina mantawa muna azumi ne? Duk hanyar da zaki raunanama mutum azumi kin santa”.
        “Kayi haƙuri Yah Ab, wlhy ɗokin zuwan Nu'aymah ne ya sakani yin hakan”.
      “Umyim! Kina ɗokin zuwan natane kika barta tafiya ɗakin da Hajjo zata zauna ta sauka”. Kamar zatai kuka ta kallesa, acan ƙasan ranta kuma tamkar ana babbaka wuta, cikin shagwaɓa tace, “Damafa jira nake kazo na kawo maka ƙararta ALLAH, nayi-nayi tazo mu zauna anan taƙi, wai batason shiga haƙƙinmu”.
        Kafeta yay da idanu kamar mai nazarinta, sai kuma ya ɗauke kawai yana ƙaɗa kansa ya fice batare daya bata amsa ba.
      Harara ta raka bayansa da shi harya fice, taja gajeren tsaki, ‘Wlhy tunda aka munafunceni sai yarinyarnan ta gwammaci kiɗa da karatu a gidan nan, ni kama ƙaramin haske akan dawowarta ɗakin nan Yah Ab, dan wannan itace babar damar da zan riƙe wajen tarwatsa zuciyarta, saina maidata mahaukaciyar gaske idan da ƙaramin haukane a kan nata mtsoww!! Aikin banza kawai’.

         
      Oho, ita Nu'aymah ma batasan tanayiba, dan bata sake leƙo falonba har lokacin shan ruwa ya ƙarasa, itama Adawiya bata shiga inda sukeba ta maƙale akan shirya kayan shan ruwa takeyi. Duk da kuwa ba ita ta girkaba. Fita Abdallah yay ya musu order ɗin komai daya dace, dan yasan Adawiya bazata iyaba ita kaɗai tunda sunada yawa. Bai kuma kamata asa Nu'aymah shiga kitchen ba daga zuwansu.
      Aikin da Adawiya tayi kawai shine shirya abincin a tsakkiyar falo, wanda saida Abdallah ma ya tayata suka tsara komai a inda ya dace.

            Koda aka kira salla ruwa da dabino kawai suka ɗanci, sannan suka gabatar da sallar magriba. Daga hajjo har Nu'aymah basu zaƙeba akan abincin, sukai zamansu gefe suna tsumayen tayi daga Adawiya. Itako hankalinta ma baya garesu, tana can tana ƙullama zuciyarta abinda zata aikata a wajen shan ruwan idan an zauna danta cusama Nu'aymah takaici. Shiyyasa ta fara ƙoƙarin shiryama Abdallah nashi tunkafin su shigo.
           “A'a Hajjo ya naga baku fara buɗa bakin ba?”. Abdallah da ke ƙoƙarin ƙarasowa cikin falon sosai ya faɗa idonsa akan Nu'aymah dake danna waya. Wando da rigane marasa nauyi a jikinta, sanin basu kaɗai bane ya sakata ɗoro hijjab a sama wanda yaje mata har gwiwa.
      Murmushi hajjo dake kallon Adawiya cike da nazari tayi, sai kuma ta maida kallonta ga Abdallahn tana faɗin, “Ku muke jira mana, dan zaifi daɗin ci ai”. Cike da jin daɗi ya kama hannunta ya sumbata, kafin ya zauna kusa da ita yana gaisheta da mata barka da shan ruwa. Nu'aymah dake a ɗayan gefen Hajjo itama tace, “Barkanku da shan ruwa”. Ahmad dake ƙoƙarin zama kusa da Abdallah ne kawai ya amsa, sai hajjo data ƙwace wayar tana harararta da faɗin, “Sai yanzu kika san damu?”.
            “Waini miyasama na biyoki?”. Nu'aymah ta faɗa cikin haushin amshe mata waya tana tura baki cike da shagwaɓa. Hajjo da Ahmad sukai dariya, hajjo tace, “Tambayi kanki mana, ja'ira kawai”.
       Adawiya da abun sam bai burgetaba, ta kalli Abdallah da gaba ɗaya hankalinsa akan Nu'aymah yake.  Haushine ya sake turniƙeta, murya a cinkushe tace, “Yah Ab ga abincinka”. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. “Gasu hajjo da suke baƙi baki haɗa musuba sai ni da ko shigowa banyiba........?”
           Katseshi Hajjo tai da faɗin, “Kaga barta, ai abincinma so nake a haɗesa a babban tray mu haɗu tare mu sami ladan juna”.
       ‘Tabɗi jan’ Adawiya ta faɗa a ranta tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki, a fili kuwa sai ta kafe Abdallah da ido a zatonta ko zaice wani abu. Duk da ya ganta sarai baice uffanba, saima ɗauke kansa yay abinsa.
     Hajjo da duk take lura da motsin kowa tace, “Zainabu zuba abincin, ki haɗe da wanda Adawiya ta zuba duk a haɗu kowa ya saka hannunsa”.
         Murmushi Nu'aymah tayi a karon farko, ta gyara zamanta tana faɗin, “Angama Hajjaju uwar masu gida, uwar gida ran gidan malam Hashimu ɗan jibiya”.
        Sosai Abdallah, Ahmad da Hajjo suka sanya dariya da kirarin na Nu'aymah. Hajjo ta ranƙwasheta akai tana faɗin, “Ja'ira”. Adawiya kam wani baƙin cikine ya kumeta a rai, harta kasa daurewa ta miƙe.
       Abdallah yace, “K kuma ina zaki?”. Da ƙyar ta iya haɗiye kukanta tace, “Zan ɗakko abune a kitchen”. Bata jira amsarsa ba tai gaba. 
     Wani shegen murmushi Hajjo da Nu'aymah suka saki, wanda kowa da manufar nasa. 

        Hawaye sosai Adawiya tayi a kitchen, sai dai gudun kar wani ya biyota yasata saurin wanke fuskarta ta ɗakko ruwa ta fito.
    Koda ta dawo babu wanda ya tanka mata, saima ƙoƙarin kai abinci suke a cikinsu. Yayinda Abdallah duk Motsin Nu'aymah na gunada ne a idonsa. Itama Nu'aymahr dai hankalinta na a kansa. Sai dai tana ƙoƙarin fuskewa ita babu mai ganeta.

     A haka dai suka kammala buɗa bakin, yayinda kowa yaci komai dai-dai misalin da bazai cutu ba. Duk da akwai gajiya tattare dasu haka suka rarrafa zuwa massallaci sukai isha'i da asham. Kafin su dawo kowa ya nema makwanci.
         Abin mamaki sai ga Adawiya tayi shiri ta tafi kwana ɗakin Abdallah.

(😂ta wajena Adawiya gara ki dage ki samu kan, gaskiya fa, dan naga su o'e anzo saudia da shirin Snatching mijin mutane.😎🙄🚶🏻)

_______________________________
             *_NIGERIA_*

     “Wai tunanin mi kiketayi ne haka da zurfi Darling? indai akan Yoohan ne na samo mana mafita”.
     Da sauri Momy ta juyo tana kallon papa da ke maganar da yarensu, bakinta har ɗan rawa yake wajen tambayarsa wace irin mafita ya samo?.
     Sai da ya rungumeta kafin yace, “Mu lallaɓashi ya auri Miracle kawai”. A wani irin zumbur ta miƙe zaune tamkar wadda maciji ya sara. Ta nuna Papa da yatsa tana faɗin, “Kasan mi kake faɗ kuwa Darling? duka-duka shekarar Yoohan ɗin nawa da kake maganar yay aure? Indama son Miracle ɗin yake to da sauƙi, amma kana ganin yanda yake mata a gidan nan ai ko”.
     Tsuru papa yay yana kallon yanda matar tasa ke masifa kamar zata haɗiye harshenta, sai da takai ayar zancenta tana wani huci sannan yay saurin jawota jikinsa yana girgiza kansa. “Ki fahimceni mana, idan Yoohan yay aure matarsa zata dinga ɗebe masa kewa a duk lokacin da ya shiga irin wannan damuwar, kum.......”
         “Kaga nifa bani da lokacin wannan maganar, ka barni barci nakeji”. Ta faɗa ranta a ɓace da ƙwace jikinta taje gefen gadon ta kwanta. Da kallo kawai ya iya binta har na tsahon lokaci, kafin shima ya kwanta ɗin yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. A cikin ransa kuwa ya ƙudiri aniyar lallaɓata ita da Yoohan ɗin har sai sun amince da ƙudirinsa.

*_WASHE GARI_* safiyar lahadi, tunda safe jama'ar gidan suka shiga hada-hadar shirin fita church, dan papa ma tun da sauran duhun safiya ya fice shi.
      Rich daya fito wanka ya kai dubansa ga Yoohan dake zaune kan sofa, ƙafafunsa miƙe akan table, ya jingina bayansa kansa na kallon sama. Duk da idanunsa a lumshe suke ya tabbatar ba barci yake ba.
      “Doctor ya kamata ka tashi kai shiri mu shiga church ko? Idan mun fito sai mu ɗan zaga gari danni yau da yamma zan koma Lagos”.
      Shiru Yoohan bai motsaba, duk da kuwa sarai yanajin Rich ɗin. Sai da ya ɓata wasu mintuna kafin ya buɗe idanunsa da sukai wani irin kumburowa, fatarsu tayi jaa sosai alamar jin barci tattare da shi, hakama fuskar tayi jajur sosai abin tausayi. Miƙewa yay batare da yayi magana ba, ya wuce toilet yana ɗan ɗingisa ƙafarsa da bata gama sakiba, sai dai hakan kuma sai ya bama tafiyar tasa wani style daban kamar mai tafiyar izza.
        Baija dogon lokaciba ya fito ɗaure da towel ruwan gwaiduwar ƙwai. Babu kowa a ɗakin dan Richard ya gama shirinsa ya fice. Ya ƙarasa gaban mirror, shafe jikinsa yay da mai da kayan ƙamshi tamkar yanda ya saba, kafin ya nufi wajen kayansa. Fararen suit ya ɗakko yana ɗan yamutsa fuska da kallonsu. Sai kuma yabar wajen dasu zuwa gaban gado. Tsaf ya shirya a cikin suit ɗin da sukai masifar zama masa a jiki, tare da fiddo surarsa mai jan hankalin mata dama mazan kansu. Necktie ɗin ya ɗauka a hannu tare da jacket ɗin suit ɗin, dan shi kam har yanzu ɗaura tie na masa wahala. Gaban mirror ya sake komawa ya feshe kansa da kalolin designers ɗin turarurrukansa, kafin ya ɗau sarƙa ɗaya a cikin sarƙoƙinsa na Cross da taji zallar diamond tanata ɗaukar idanu ya saka. Ya ɗauki agogo ya ɗaura tare ɗan wani abin hannu na gayu ya ɗaura a ɗayan hannun, ya kuma manna ɗan kunnensa a kunne ɗaya. Yayi ƙyau sosai, duk da kuwa fuskar a turɓune take matuƙa. Amma yanda yau ya gyara kansa da sajensa sai yay ɗas da shi kamar ka suresa ga gudu.

        Tun fara sakkowarsa daga benen Mom da Rich, Solomon dake a falon duk suka zuba masa idanu, sake ɗaure fuska yayi yana ƙarasa sakkowa. Saurin tararsa Solomon yay da kofin coffee daketa turiri akan tray, yace, “Good Morning sir”. Kansa kawai ya ɗaga masa yana gyaɗa kai, tare da ɗaukar coffee ɗin ya nufi Mom da ta tsatstsaresa da idanu tun sakkowar tasa, sai dai fuskarta sam babu walwala. Tayi ƙyau sosai abinta tamkar zata gasar sarauniyar ƙyau. Necktie ɗin hannunsa ya miƙa mata batare da yayi magana ba, saima kofin coffee ɗinsa da yakai baki yana curɓa kamar bayaso.
     Tsaye ta miƙe, duk da ya fita tsaho, amma da yake tana kan tudun dining ne saita samu damar kaiwa wuyansa cikin sauƙi. Ɗaura masa tie ɗin tayi, tare da amsar jacket ɗin ta koma bayansa. Hannunsa guda ya miƙa mata ta saka masa, ya sake miƙa ɗayan ma ta saka, sannan ta zagayo gabansa tana gyara masa da ƙyau.
        Ta ɗan saki murmushi tana masa wani narkakken kallo, kafin takai hannunta saman fuskarsa ta shafa kwantaccen sajensa dayin magana ƙasa-ƙasa kamar mai raɗa. Ɗanja baya yay yana zame hannunta, murya a cinkushe yace, “Thanks Mom”.
         Kafin ta samu damar yin magana ƙannensa dake fitowa cikin nasu gayun suma suka shiga gaishesa ɗaya bayan ɗaya. Hannu kawai yake iya ɗaga musu yana cigaba da shan coffee ɗinsa cike da basarwa.
     Ganin yanda Mira ke binsa da wani shu'umin kallone ya sakashi miƙama Solomon kofin duk da bai ƙarasa ba, batare da yayima kowa magana ba ya nufi hanyar fita abinsa cike da takun nutsuwa da ƙasaita sai kace wani jinin mulki.
        Dukansu baya suka take masa, yayinda Gebrail yay saurin kaiwa inda yake yana riƙo hannunsa. Batare daya kallesaba yace, “What happend?”. Murmushi Gebrail yayi yana susar kai, cikin ɗan in ina yace, “Brother Yoohan kuɗi nakeso Please”.
            Yoohan baice komaiba, ya zare hannunsa daga cikin na Gebrail ɗin, ƙarasawa yay jikin motar da yaga Rich tsaye yana waya. Da sauri ɗaya a cikin Guards ɗinsa ya buɗe masa yana gaishesa. Hannu kawai ya ɗaga mar ya shige. Richard ma shiga yay ta ɗayan gefen, Solomon da driver ma suka shiga. Cike da ɗoki Gebrail da yasan matsalarsa ta yanke ya shiga motarsa shima tare da su Mira da taso bin motar Yoohan ɗin. Sai dai ganin Rich datai tunanin ba a gidan ya kwanaba da, ya sakata haƙura ta shiga ta Gebrail ɗin ita da joy.

       Motocin na gama fita a gidan Yoohan ya zaro wayarsa dake cikin aljihu, transfer ɗin kuɗi masu yawa yayma Gebrail tamkar baisan ciwonsu ba, kafin ya ajiye wayar gefensa ya maida kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa.
         Har motocin suka tsaya a katafaran church ɗin da papa ke riƙe da shi Yoohan bai motsaba, duk da kuwa Rich na masa bayani ne akan wata harkar business ɗinsu da sukeyi tare.
      Katafaren church ne mai girman gaske, wanda akaima gini na ƙawa da ɗaukar hankali, dan a gaba ɗaya gaban church ɗin da idanuna ke iya gani anyisane da zalkar glass. Yayinda akasa ƙaton tambarin Cross da akayisa da golden ɗin abu. Tun a farkon shigowar titin zaka faracin karo da muryar papa dake lecture. Gaba ɗaya titin wajen sun kashesa babu maibi saboda motocin da duk akai parking masu tarin yawa. Securitys ɗin church ɗin da sauri suka shiga bama motsocin su Yoohan ɗin hanya cike da tsantsar girmamawa. Sai da sukai parking a waje na musamman da aka tanada domin motocin nasu dama sannan aka shiga buɗe musu suna fitowa.
     Yoohan ne ƙarshen fita, dan sai da ya gama jan ajinsa kafin ya ziro sandarsa ta gayu sannan ya fito gaba ɗayansa. Gebrail da tun a hanya yaga alert yay saurin ƙarasowa ya rungumesa yana godiya. Baice dashi komaiba sai shafa masa baya da yay kaɗan.
           Yanda securitys ke basu kariya da tsantsar kulawa sai ka ɗauka dajin sambisa zasu shiga🤥🙄, suna zagaye dasu har ta ƙofar da take ta musamman domin iyalan papan kawai da shi. Tanan suka shiga cikin church ɗin dake a cike maƙil da mabiya kamar zai fashe.
        Duk suka zuba musu idanu suna miƙewar girmamawa a garesu cike da sha'awa da ƙauna. Sai da suk suka ɗaga musu hannu banda Yoohan da ko kallon basu ishesa ba sannan suka ƙarasa wajen zamansu na musamman dake a gaba duk suka zauna.
    Papa dake a gaban wani glass mai ƙyau da aka ƙawata da golden ga abin magana kusan huɗu a jiki yay murmushi yana ma iyalan nasa barka da zuwa, kafin ya cigaba da zubo bayani cikin kwakwazo da karaɗin da aka san fastoci da shi, ko haɗiyar yawu bayayi😕.
          A hankali sai hayaniyar ta fara takurama Yoohan, duk da kuwa tunda ya zauna yana jingine ne da kujera idanunsa a lumshe kamar mai barci. Siririn tsaki yaja yana yamutsa fuska. Ya shafa kunnensa na dama dake manne da Bluetooth yana cizar lip. Sai kuma ya buɗe ido da motsawa zai miƙe Rich yay saurin riƙe masa hannu. Ransa a ɓace ya kallesa, sai dai baice komaiba.
       “Please ka daure” Rich ya faɗa cike da marairaicewa dan kar Yoohan ɗin ya bijire. Siririn tsaki ya kuma ja kaɗan ya maida kansa ya sake kwantarwa ya rufe idanu.

     Kusan awa guda Yoohan nata sake daurewa duk da kansa ya fara masa wani azababben ciwo. Kiran daya sake shigowa a wayarsa ne a karo na babu a dadi ya sakashi yamutsa fuska, duk kiran da ake masa bai amsa ko guda ɗaya ba, amma yanzu sai yaji buƙatar amsawar. Miƙewa yay zai fice Rich yay saurin sake riƙosa. Nuni yay masa da Bluetooth ɗin kunnensa batare da yayi maganaba. Hakanne ya saka Rich sakinsa yana gyaɗa kai.
         Sama-sama ya amsa mutumin dake gaishesa, kafin yay shiru yana sauraren bayaninsa da magiyar da yake masa akan buƙatar mutanen da kimarsu ta wuce ace Yoohan ɗin yaƙi buƙatarsu.
        Ajiyar zuciya Yoohan ɗin ya sauke a karon farko, batare da ya amsaba ya yanke kiran kawai. Wayarsa ya ciro yay ɗan typing ya tura abinda shi kaɗai ya sani. Mintuna uku ba'a rufaba saiga reply an naido masa. Buɗewa yay ya gani, batare da yayi maganaba ya maida wayar aljihu yana ɗan dube-dube kamar mai neman wani abu. Sai kuma ya sake zaro wayar ya sake yin wani abun.
    Yanzu kam ya kai tsahon mintuna biyar yana jiran reply ɗin kafin a turo masa. Shiru yay yana ɗan kallon wayar kamar mai nazari, kafin ya gyaɗa kansa da nufar inda motocinsu suke da wasu a cikin guards ɗinsa tsaye a wajen.
    Batare da yayi maganaba ya miƙama drivernsa hannu da masa nunin ya bashi key. Kamar driver zaiyi magana sai kuma ya haɗiyeta da sauri ganin kallon da Yoohan ɗin ya zuba masa. Saurin bashi key ɗin yayi, shi kuma ya buɗe motar da kansa ya shiga mazaunin driver yay mata key tare da yin reverse ya bar wajen securitys nata risina masa cike da girmamawa.............✍      

To ɗan dabe ina zuwa kuma🤥🤐?.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_INA MASU NEMAN INDA ZASU SAMU INGANTATTUN:_*
*_HERBALS APHRODISIAC NA GARGAJIYA BANA HADIN BATURE BA MAI SIDE EFFECT..?_*

*_TO KU SAURARA KUJI, DOMIN NESA TAZO KUSA.._*

*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!_*
*_ZEE HERBALS APHRODISIAC!!!_*

*_MUNZO MUKU DA INGATTTUN KAYAYYAKI WANDA ZASU GYARA CIKI DA WAJE_*
   *_MUNADA SUPPLEMENT MASU GYARAN JIKI DANA FATA, WANDA ZASA SAKI KIYI SHEKI FATAR KI TAYI LAUSHI. TAYI LUWAI! LUWAI! TAMKAR TA JARIRAI_*
    *_AKWAI SUPPLEMENT NA KAYAN MATA WANDA ZASU GYARA KI, KIJI KI TAMKAR BUDURWA, SUPPLEMENTS DINMU BASU DA SIDE EFFECT, DOMIN AN HADO SU NE DAGA INGATTATTUN ITATUWA, WATO NATURAL PRODUCTS NE ACIKI._*
       *_KAI BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA, MUNA DA INGATTUN KAYAYYAKIN MATA WANDA KESA KISHIYA KWAFA, WANDA DUK INDA SARAUNIYA TAKAI KIN WUCE, WANDA ZASU TSATSO MIKI MARTABAR KI DA KIMAR KI_*.

*_AKWAI INGATTATTUN MAGUNGUNA, NA CUTUTTUKAN DA SUKA SHAFI DAN ADAM DAMA JINNU.. KAI DAMA WANDA BAMU AMBATA BA.. ZEE HERBALS APHRODISIAC (MASARAUTAR INGATTATTUN MAGUNGUNA KENAN)_*
     *_KYAU, ARHA, INGANCI, RAHUSA... SAI ZEE HERBALS APHRODISIAC_*
   *_MANHAJOJIN MU NA SOCIAL MEDIA: KAMAR INSTAGRAM DA WHATSAPP DAMA NAMBAR TARHON MU: DOMIN SHIIGA KUGA IRIN KAYAYYAKIN MU TUNTUBE MU TA_*

_INSTAGRAM LINK DIN MU:_
www.instagram.com/zeeherbalsaphrodisiac

_WHATSAPP LINK DIN MU:_
https://Zeeherbalsaphrodisiac.whats.bz

_NAMBAR TARHON MU_
08169380189

*_KARKA BARI A BAKA LABARI GWARA KA BAYAR.. KIZO A DAMA DAKE YAR UWA, KI ZAMO DAYA DAGA CIKIN KASAITATTUN MATA MASU AJI.. MUNA GARIN KATSINA, SANNAN KAYAN MU MUNA BADA SU AKAN FARASHIN SAYA ‘DAI DAI KO SARI.. MUNA TURA KAYANMU A KO’INA A FADIN NAJERIYA._*

__________________________________

No. 22

...............Hankali tashe guards ɗinsa ke kallon juna, kowa nama ɗan uwansa tambaya da idanu dan bakunansu sun musu nauyi har Yoohan yabar sashen church ɗinma gaba ɗaya.
    Jigum-jigum sukai da fatan ALLAH yasa ya dawo da wuri kafin madam Chioma ko papa wani ya fito daga cikin church ɗin.

     Sai dai kuma addu'ar tasu bataci ba, dan bayan kamar mintuna ashirin da barin Yoohan wajen Rich da ya ga bai dawoba ya miƙe ya biyo bayansa bisa umarnin Madam Chioma. Yanda yaga Guards ɗin sunyi diri-diri da idanu lokacin da yake tambayarsu ina Yoohan ya sakashi daka musu tsawa. Sake rikicewar sukayi, kowa na inda-indar bada amsa. A haka Madam Chioma itama data biyo bayan Rich ɗin ta samesu. Sake ruɗewa sukayi, dan sunsan idanma azaba ce tafi papa akan Yoohan, ga Rich shima ɗan babu sauƙine.
    Da ƙyar driver ya iya dauriyar faɗa musu yanda akayi, jikinsa har rawa yakeyi. Yanda Madam Chioma ta rikice sai ka rantse yaronta ɗan shekara biyu ko uku ne ya ɓata. A take ta birkice lissafin Guards ɗin Yoohan da securitys ɗin church ɗinma kansu. Ta kuma tabbatar musu nanda awa biyar idan Yoohan bai dawo ba saisun gane kuransu.
      Ana a cikin wannan dambarwar ne aka tashi daga church ɗin. Mutane suka fara tururuwar fitowa suna nufar inda ake rabon abinci. gudun kar ai abin kunya Rich ya shiga lallaɓa madam Chioma akan ta kwantar da hankalinta maybe Yoohan gida ya nufa, tunda duk sunsan a yanayin da yake baya buƙatar kowanne kalar hayaniya. Zata iya yuwuwa ya ƙosa ne da zaman shiyyasa. Da wannan ya samu yaci ƙarfinta suka koma ciki inda suka tarar duk wanda zai fita sai yaje ya jefa kuɗin baikon sa tare da karɓar wani abu da papa ke saka musu a baki sannan mutum ya fice.
     Matsawa madam Chioma tai kusa dashi tai masa magana a kunne, kansa kawai ya gyaɗa mata yana murmushi. Ita kuma ta juya ta fito yaranta da su Mira na biye da ita. Koda suka fito sai manyan mata suka zagayeta anata miƙa gaisuwa ga matar Pastor, harma da mazan da matasa kowa burinsa ya gaisheta. Yayinda wasu keta tambayar ina Yoohan dan sun riga duk sun gansa ɗazun. Da yake shi dama zuwan nasa bawani sosai bane saboda yanayin aikinsa sai yazam duk sanda yazo sai su maidashi tamkar wani tauraro mai fitowa a daren sha biyar.
      Cike da yaƙe madam Chioma ke basu amsa da cewar wani uzirin gaggawa ya sakashi tafiya, amma wani satin zai tsaya yay gaisuwa da kowa. 

      Da ƙyar ta samu kanta daga wajensu, gashi rabin hankalinta duk yana ga Yoohan da Rich keta faman kira yaƙi ɗaga waya. Daga ƙarshe ma wayar bata shiga.
     Tun shigowar motocinsu ƙaton harabar gidan suka fahimci Yoohan ba gida ya zo ba, dan babu ko mai kama da motar da ya shigo acikin jerin mitocin dake gidan. Sai da suka gama fita sannan Madam Chioma ta ƙwalama maigadi kira cikin ƙaraji. Jikinsa na ɓari ya ƙaraso gareta cikin cika umarni.
            Kafinma takai ga jefa masa tambaya Miracle ta rigata. Mai gadi yay saurin basu amsa da cewar Yoohan baizo gida ba. Gaba ɗayansu hankalinsu sake tashi yayi, kowa ya fiddo waya suka shiga nemansa..........😒

🙄😏Mufa an ishemu kamar wani ɗan gwal🤕😤.

_____________________________
                
          Koda Yoohan yabar gidan wani ma'aikata ya nufa, duk da kuwa da ƙyar yake jan motar saboda nauyin jiki dana zuciya da rashin baccin ya haddasa masa.
        Yana tsaida motar a inda ta dace ya ɗan kife kansa a sitiyarin motar na wasu sakkani, zuciyarsa ce keta faman masa kai kawo akan abinda yake shirin aikatawa. wani ɓangaren na ƙarfafasa akan dai-dai, wani kuma na raunana masa niyyar tasa. A haka dai ya kwashe mintuna har biyu kafin kiran daya shigo masa waya ya maidashi cikin hankalinsa. Ɗagowa yay a hankali yana yamutsa fuska, ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa tana gab da tsinkewa.
          “Na shigo” ya faɗa kawai cikin harshen nasara. Bansan amsar da aka bashiba. ya dai yanke kiran tare da buɗe motar ya fita.
       Wani matashin saurayi da zasu iyayin sa'anni ya fito daga cikin ginin ma'aikatar fuskarsa ɗauke da murmushi. Kallo ɗaya zakai masa ka shaida shiɗin musulmine, dan yana sanye cikin shadda bara sol dataji ɗinkin tazarce, ga ƙaton tambarin salla a goshinsa ya kuma murza baƙar dara mai taushi.
           Tunda ya tunkaro Yoohan ɗin kallonsa yake ta ƙasa ido cike da nazari. amma ba kowa zai fahimci yana kallon nasaba musamman idan akai dubi da yanda yay wata tsayuwar basarwa yana busar iskar dake kaɗawa ta hantsi mai gauraye da ɗumin rana.
         “Ina fatan dai baƙo nane?”. Saurayin yay maganar fuskarsa ɗauke da fara'a duk da kuwa tun daga nesa ya gama shaida Yoohan ɗin ba musulmi bane.
     Duk da Yoohan yana mu'amulat da musulmai batun yanzuba, a mabanbanta ƙasashe da yarurruka kuma, baya iya sakin jiki da su. Dan shi kullum yana cikin yin taka tsantsanne karsu cutar da shi kamar yanda aka ɗorasa a hakan tun ƙuruciya. Ya dai yarda zai ƙyautatama mai buƙatar taimakonsa ko a wane irin yare yake ko addini, zai kuma gudanar da aikinsa da gaskiya ga kowa. Amma bai aminci da yayi dogon aminci da musulmin ba.
      Sai dai kuma gashi yau a karan farko na tarihin rayuwarsa matsashin saurayi ya burgesa, harma da shigar kamalar dake a jikinsa. Duk da babu ɗigon fara'a kota sisin kwabo tattare da shai sai ya jinjina kansa cikin lumshe ido yana mai miƙama saurayin hannu.
        Saurayin ya sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi yana faɗin, “Ina godiya ƙwarai da amsa wannan gayyata tawa da banyi zaton zata karɓu ba. Sunana Hamza Ibrahim khalil, manager mai aiki a wannan kamfani namu mai albarka”. Yanda matashi Hamza yay magana da harshen ingilishi haka Yoohan dake binsa da kallo kwarjininsa na sake cika masa ido shima ya mayar masa da murtani cikin harshen nasaran. “Dr Yoohan Goshpower”. Ya faɗa a hankali kamar bayason maganar, sai dai hakan bai hana voice ɗinsa mai amo fita da ƙyau ba. “Ina sake godiya da amsar gayyata ta a karo na biyu Doctor”.
       “Karka damu” Yoohan ya faɗa a taƙaice. Hamza Ibrahim da kansa yayma Yoohan jagora har cikin office ɗinsa dake a haɗe masha ALLAH, dan babban kamfanine dake fidda kayan masarufi masu ingaci da lafiya ga jikin al'umma.
    Sai da Yoohan ya zauna kafin Hamza Ibrahim ya kawo masa lemo, ya tsiyaya a cup tare da ajiye masa gabansa a kan table ɗin. Godiya Yoohan ɗin ya masa. Hamza Ibrahim ya sake yin murmushi yana gyaɗa kansa tare da yima kansa mazauni shima. 
     Sun sake gaisawa a karo na biyu. Yoohan ya sake bin ba'asin kiran da ya samu daga garesu. Babu wani ɓoye-ɓoye Hamza Ibrahim yay masa bayani cikin nutsuwarsa, tare da miƙa masa envelope yana faɗin, “Wannan itace takardar da suka aiko da ita a baka, abinda yasa ban badata kai tsaye taje garekaba saboda gudun ha'incin mutane, zata iya yuwu akai takardar amma taƙi isa gareka. Shiyyasa na buƙaci dama nazo ni gareka da kaina na kawo maka. Sai ma kace min zakazo da kanka.
       Yoohan daya gama duba takardar ya ɗan ɗago kansa yana kallon Manager, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya haɗiye abinsa a rai yana ƙoƙarin maida takardar cikin envelope ɗin.
         Duk da Hamza yayi mamaki da ganin Yoohan ɗin a matsayin wanda yaketa faman hidimtawa bayin ALLAH haka ya haɗiye mamakinsa, dan yayi imani da UBANGIJI na fidda rayayye a cikin matacce, kuma ana samun mutanen kirki a cikin kafiranma, wanda wasu musulman mu sukan gaza gyara zukatansu su zama haka duk da addininmu ya koyar damu komai. cikin hikima irinta masu ilimin addini dana zamani yace, “Yallaɓai ina fatan dai zaka amsa wannan gayyatar? Dan suma mutanene masu karamci da mutunci kamar kai, na tabbata alkairinkane kuma yake sake girmamarsu shiyyasa suka shirya wannan liyafar a gareka domin nuna girmamawarsu a kanka”.
      Karan farko a rayuwar Yoohan da kalaman hikima sukai masa daɗi a rai, har yay wani ɗan motsi da laɓɓansa mai kama da murmushi amma ba murmushin bane ba. Idanunsa ya ɗan lumshe na wasu sakanni yana nazari. Ba zuwan bane matsalarsa, ciwonsane damuwarsa. Bayason kowacce kalar hayani, ba kuma ya buƙatar shiga cikin kowanne irin mutane gudun ƙuntatama wani. To amma kuma maganar Manager tai tasiri a ransa harma da tunaninsa. 
     Buɗe idanunsa yay a hankali ya ɗan gyaɗa kansa, “Babu damuwa zanje ɗin, sai daifa ka shirya ayi tafiyar tare da kai”. “Ni kuma Doctor?”. Manager ya faɗa yana ɗan waro idanu. “Indai kace bazakajeba nima kam zan fasa, dan saboda kaine dama zanje. Banyi musu komai dan su damu da sanina ba, sannan wanna shine karo na farko da aka buƙaci yimin karamcin da bai shafi aiki na ba ko yarena ko addinina ba. Shiyyasa nakeson na halarta ko zai shiga tarihin farko da ƙarshe na rayuwata”.
         Manager ya gyaɗa kai a ransa yana faɗin ‘daga ganin wannan a Christians ɗinma inaga ɗan ɗariƙar Catholic ne, ALLAH yasa ina ɗaya daga mutanen da zasu jagoranci duhunsa ya samu haske’ a zahiri kuma sai yay murmushi da faɗin, “Babu damuwa, indai kana buƙatata a tawagar masu rakkiya bazan ƙi ba”.
    Hannu Yoohan ya miƙa masa tare da yin godiya, kafin ya miƙe alamar zai wuce dan yasan hankalin families ɗinsa nacan a tashe da rashin ganinsa.
     Har mota Manager yay masa rakkiya yana ƙara masa godiya sosai, dan yana cikin mutanen da ayanzu company ɗin ke jin daɗin shigowarsu cikin manyan Customers.

★★★

         Lokacin da Yoohan ya iso gidansu ya iske kowa a birkice, dan har papa ya baro church yayo gida. Harma yana shirin kiran police station yay report.
     Tun a harabar gidan ya fuskanci akwai abinda ke faruwa a gidan, dan yaga baƙin motoci da yake ƙyautata zaton na Uncles nashi ne. Sannan yanda yaga Guards ɗinsa da sauran securitys ɗin gidan na sauke manya-manyan ajiyar zuciya yasan da walaki. Amma kowa bai tankamawa ba ya nufi ƙaton ƙofar falon nasu na glass da yaja manya kuɗaɗe masu nauyi koda ba'a faɗaba.

      Wani ihun farin ciki Miracle ta kurma dan itace ta fara ganinsa, kafin ta kwaso a guje tazo zata ɗane masa jiki. Sai dai yanda ya wani uban tsumewa ya sakata jan birki a gabansa ta kama hannunsa kawai ta ƙanƙame a ƙirjinta. A take sauran yaran gidan da baƙin ƴammata da samari yaran Uncles ɗinsa suma duk suka taso kansa. Basubi takan tsumewar tasaba sukam duk suka rungumesa.
     Da ƙyar madam Chioma ta samu suka sakesa, itama ta matsa ta rungume abinta tsam yanda takeso hawaye na gangaro mata akan fuska. Hannunsa yasa ya ɗan buga bayanta kaɗan tare da ɗagota yana mamakin hawayen na miye? Batare da yace komaiba ya ciro handkherchief a aljihunsa ya share mata hawayen.
          Ƙarasowar su Papa da Uncles nashi uku yasa madam Chioma matsawa suma duk suka rungumesa, hakama matansu. Shikam dai kansa sake ɗaurewa ya keyi, dan haka ya tambayesu wai ko lafiya?.
     Basu bashi amsaba sai da Madam Chioma data kama hannunsa ta kaisa har saman kujera, Victoria ta kawo masa ruwa dan kowa yasan yafi ƙaunarsa sama da kayan zaƙi. Bai musaba ya amsa yasha kusan fin rabi, sannan ya sake binsu da kallo da sake tambayar yaya akayi wai?.
       Gebrail ne ya sanar masa da komai. Hakan ya saka Yoohan ɗin dafe kansa dake sara masa kaɗan-kaɗan yana ɗan lumshe idanu. Shi abin nasuma takaici ya bashi sosai. Amma sai baice komaiba. Sanin bazai ceɗinba yasa babu wanda ya damu da jiran sai yace ɗin. Saima ringuɗa da sukai Dining domin yin breakfast ɗin da suka kasa yi tun ɗazun.
        Shi dai Yoohan duk a takure yake matuƙa, amma sanin baƙar masifar Uncle Zamani yasa shi haƙura ya zauna akai breakfast ɗin da shi, wanda shi sam ma baici wani abin kirki ba. Bayan sun kammala sukai sama shida sa'anninsa su uku, sai Rich daya dawo daga nemansa. Amma duk masifar da yay masa akan ɗaukar mota ya fita shi kaɗai a wannan halin da yake ciki sai bai kula Richard ɗinba. Shima bayan gama masa masifar sai ya watsar dashi ya biyema su Osen kawai da suka baje a falon Yoohan ɗin suna kwasar dariya da hirarsu ta shaƙiyanci akan ƴammata.
      A haka Solomon ya shigo da kwalaben barasar da sukai Order, sai kofuna da ƙanƙara. bayansa cikin ma'aikatan gidanne ɗauke da tray da aka shiryo gasashen naman kaji a cikinsa wanda zasuyi amfani dashi wajan shan barasan.
     Sai da suka jera musu komai yanda ya dace kafin su fice su barsu. Miƙewa Yoohan yay zai shige bedroom dan ya rage kayansa. Da sauri Godwin yace, “Mr-x ina zuwa?”. (Dan haka duk abokansa ke kiransa da shi, Rich kawai yafi kiransa da Doctor) Yamutsa fuska Yoohan yay yana hararsa, dan dama abokin bugawarsa ne, kawai dai dan yau baya cikin good mood ne. “Ina zuwa” ya bashi amsa a taƙaice yana shigewa.
           “Wai mike damun Boss ɗinka ne?”. Joseph ya faɗa yana kallon Richard.  Cikin damuwa Rich yace, “Matsalarsa ce dai ta rashin barci ta motsa, nayi-nayi yasha barasa ko nai masa allura yaƙi”.
         Godwin ne yace, “Shegen taurin kan Mr-X ai ba ƙarewa yakeba, ni wlhy sonake wataran na samu wata na biyata tai disvirgin ɗin gayen nan kozai ware yaji daɗin rayuwarsa. Duniya ai sai da jin daɗi, amma shi yabi ya wani ƙanƙame kansa kamar wanda bai wayeba ko ba'a turai yay rayuwa ba. Minene a giya? Dama da shanta kawai nishaɗine, kuma tunda munada aikin yinmu sai fa lokaci- lokaci muke shanta, ba kuma mai cutarwa ba.......”
     Katsesa Joseph yayi da faɗin, “Kaga G. Ka barsa, Mr-x tsarinsa kenan shi da ra'ayinsa, koka manta tun muna secondary shi dama komai nasa da ƙa'ida ya keyi. so ni banga abin damuwa da har zaku shiga masa rayuwa da yawaba, kubarsa ya tsara ma kansa yanda yake buƙatar ya rayu Ok?”.
           Richard yace, “Hakane Joseph, amma idan ka lura shima fa bawai jin daɗinne baya buƙata ba, kawai shi dai ya ɗauki burin duniyane ya ɗaura akan aikin nan namu, a tunaninsa duk abinda zai sha zai iya shagaltar da shi akan aikinsa, sannan mata ma zasu iya takura masa su hanashi yin rayuwarsa da ƙyau, kunsan mutum namu ɗan hutune, ko mace bata faɗa masa son jiki ba”.
     Dariya suka kwashe dashi gaba ɗaya suna mai haɗa kofunan da suka zubama barasa a ciki alamar chssss.
       Hakan yayi dai-dai da fitowar Yoohan daga ɗaki, ya canja kayansa zuwa wando da riga duk blue na kamfanin adidas. Duk da hayaniyar tasu bai sonta haka ya zauna a cikinsu dan gaba ɗayansu childhood Friends ɗinsa ne, kuma ƴan uwansa na jini dan duk ƴaƴan ƙannen papa ne, sai Osen ne kawai ɗan aboki shima kuma iyayen nasu sun zama kamar ƴan uwa, sai kuma Richard shi kuma abokinsa. Amma tare sukai secondary school dukansu, hasalima duk ajinsu guda.
     Osen ne ya miƙa masa cup duk da yasan ba sha zaiba. Aiko Yoohan ɗin ya yamutse fuska da girgiza masa kai tamkar mai ƙyanƙyamin giyar ma. Dariya suka sanya masa suna zuba masa shaƙiyancin da suka saba, tare da labarin daɗin da ƴammatansu ke jiyar dasu harma da karuwai dan dukansu ji suke da ƴan kuɗaɗe a aljihu. iyayensu kuma sun tara, sanna suma ɗin gwasaken kansune sosai. Shiyyasa suke zuba tsiyarsu a garin Abuja da Lagos kamar babu gobe.
         Duk abinda sukeyi saboda Yoohan yaji haushine yay budurwa, dan har maganar ƴammatansa dake bala'in sonsa suke kawowa harda Miracle, tare da koɗa ƙyawunta dama na sauran ƴammatan da Yoohan ɗin shi yake nuna kullum basa gabansa.
         Joseph yace, “Mr-x daga yau ka fara taka tsantsan da G-boy, dan ya shirya yanda za'a maka fyaɗe, kaga sai kasan zaman da zakai da shi”.
    Mangare ƙeyar Joseph Godwin yayi yana faɗin, “Munafiki, halan giyan ya fara kai maka karo zaka haɗani da shi”. Dariya suka kece da ita duka. Yoohan dake harar Godwin ɗin yace, “Barma wani kare kanka naji sanda kake faɗa ai, an faɗa maka ni irinka ne da baida damuwa saita kwana da mata. Please, try and change your habit kaima”.
     Nanma dariya suka sanya, dan sunsan kam G-boy shege ne akan mata, duk yanda zai yaudareki ya biya buƙatarsa ya sani. Rich yace, “Calm dawn my Doctor, duk randa ya aikata maka haka zuwa zakai kawai ka tona masa asiri wajen babien sa, dama gata da shegen kishi kamar taci wuta a cikinta.......”
        Osen dake ƙoƙarin yagar nama yace, “Ashe ka ganota, nifa haushi take bala'in bani, amma G-Boy sam baya ganin laifin hakan da take masa, da kayi magana saiya nuna cewar son da take masa ne”.
       Ajiyar zuciya Yoohan da warin giyar ya fara hawar masa kai ya saki, ya miƙe a hankali ya ɗauki basket ɗin da aka zubo musu kwalaban giyan ya nufi hanyar fita. Da sauri suka shiga kwala masa kira akan ya kawo musu abinsu, amma baiko juyoba ya fice yama kullesu ta baya ya sauka ƙasa. Canma iske su Papa yay suna ɗora tasu suna hira da dariya harda su Momy suma sha suke. Sosai ransa ya sake sosuwa, sai kace ba yanzu papan ya gama wa'azi a church ba. Tsaki yay ciki-ciki ya wucesu batare da ya tanka musu ba yana ƙwalama Solomon kira. 
       Da gudu ya shigo kuwa, ya miƙama masa basket ɗin kawai babu bayanin komai ya fice a falon. Garden ya nufa. Sai dai kuma yana shiga ya hango su Miracle a cikin swimming pool suna wanka. Cike da farin ciki duk suka zuba masa idanu, kowacce kwaɗayinta a kansa na fitowa fili saman fuskarta. sai dai kuma tuni ya juya yana jan wani tsakin takaici. Wannan taron yasa sam bayason zama gidan ranar lahadi, yanzu haka zuwa anjima gidan sake cika zaiyi da wasu baƙin kuma. Solomon ya bama key ɗin ƙofar sashensa daya kulle su Rich, yace yaje ya buɗesu, shi kuma ya fice gidan a ƙafa duk da kuwa rana ta fara ɗagawa kuma akwai ɗan zafi............✍

Amin afuwa jiya ciwon kai ya hanani sukuni na kasa typing ɗin🤦🏻.

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: No. 23

................Tun sakkowar Yoohan daga sashensa Momy tai saurin ajiye kofinta na barasa, dan Yoohan ya daɗe da hanata shan giya, kuma ta masa alƙawarin dainawa. Sai dai wani lokacin damuwar da take ciki kansa tasha abinta musamman da daddare idan zata kwanta barci. duk da dama wani mai yawa take sha ba. Binsa tai da wani shegen kallo tamkar idanunta zasu faɗi ƙasa, yayinda fuskarta ma ta nuna shauƙi sosai fiye da yanda suke zaune. Yunƙurawa tai zata tashi amiyarta madam Monecca tai saurin riƙe mata hannu tana girgiza mata kai cikin hikima. Duk da bataso hakanba saita koma ta zauna tana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciyar da harsu Papa da fira ya ɗaukema hankali basusan da wucewar Yoohan ɗinba suka juyi suna kallonta. 
          “Lafiya Darling?” papa ya faɗa cike da kulawa a gareta. Murmushi yaƙe ta masa da cewar “Babu komai, bara naɗan rage kayana dai sun fara min nauyi”. Murmushi yay mata da aika mata kiss daga inda yake. Ta miƙe tana fadin, “Thanks Honey”.
       Rakata da idanu yay cike da so da ƙauna harta haye sama sashen bedrooms ɗinsu. Sai da ta wuce da kusan mintina goma kafin Madam Monecca ta miƙe itama tana neman excuse ɗin zuwa toilet. Duk da kowa yasan dama amintarsu tafi zuwa ɗaya da madam Chioma babu wanda yay zargin komai a sauran matan. Sai ma maida hankalinsu ga hirar mazajen su da sukayi kawai.

        A bakin gado Madam Monecca ta iske Momy zaune ta dafe kanta. Ta ƙarasa kusa da ita ta zauna, cikin harshen nasara take tambayarta damuwarta?.
         Ɗagowa Madam Chioma tai idanunta cike da hawaye tana kallon ƙawarta, tace, “Monecca! Ina cikin damuwa sosai akan Yoohan, gaba ɗaya ya sake canjamin, ɗan kusancin da nake murnar ya ƙara shiga tsakaninmu a yanzu neman hanyar kakkkaɓar da shima ya keyi. Rungumarsa ma yanzu bayason yaga nayi, sai kiga ya kama ɗacin rai. Nifa na gaji da ɓoye-ɓoyen nan, dan gashi Honey harya fara tunanin wai yay masa maganar aure.…..”
       “Aure!?” Monecca ta faɗa cikin tashin hankali.
       “Ki bari kawai, jiya da yay maganar naji kamar na bindige shegen nan nama huta da wahalansa, Monecca zan fitoma Yoohan a mutum kawai da buƙatata, duk da kuwa nasan shegen taurin kansa”.
        Cikin sauri Madam Monecca tace, “Karkiyi haka, dan zaki samu babbar matsala. kidai bari muyi tunani akai. Wai ita Mira bazata koma gidansu ba ne. sai naga kamar itace ke ɗauke masa hankali?”.
        Cikin dariyar da Madam Chioma batai niyyar yiba tace, “Miracle fa? An gaya miki kalloma ta ishesa ne a gidan nan. Dama fa Zamani ne keta son ganin Yoohan ɗin ya aureta. kuma ni na gama fahimtar shima akwai tasa manufar akan hakan, shi kuma Yoohan ɗin duk da ƙyan Miracle ɗin bata gabansa shiyyasa nima zamanta a gidan bai taɓa damunaba”.
     Ɗan taɓe baki Monecca tayi tana hararar Madam Chioma a kaikaice. a ranta kuwa rayawa take duk rintsi saita bi hanyar mallakar Yoohan ɗin, dan itama wani Masifaffen sonsa take, tana dannewa ne a gaban ƙawar tata kawai. Sun tattauna sosai ta yanda suke ganin ya dace a samu Yoohan ɗin a hannu. Kafin su fito wajen sauran ƴan uwansu a cigaba da hira.

      Haka gidan ya cigaba da karɓar baƙi har dare, dan yau ranace ta ziyara a garesu, musamman ma gidan papa daya kasance babban mutum a wajensu.
     Yoohan bai dawo gidanba sai yamma lis, ya samu giyar dasu Osen suka sha ta ɗan sakesu, harma sun fito daga sashensa Solomon ya shiga ya gyara. Duk suna harabar gidan zaune dan wasu abokan nasu sun ƙaru saboda jin Yoohan ɗin na gari, shima sai kawai ya zauna a wajensu duk da ba firar yakeba sosai.

______________________________
                *_SAUDIA_*

     Duk da Adawiya na ƙoƙarin ɓoye halayenta hakan bai hanata sakin layi a wasunl lokutan, dan babu abinda ke sakata takaici da ƙunar zuciya kamar yanda Nu'aymah taƙi nuna damuwarta akan duk abinda take mata. Gaba ɗaya Nu'aymahr ma ta maida hankalinta ga ibada ne kamar yanda ta ɗauro niyya tun daga gida.
     Tayi mugun yin watsi da shirmen Adawiyar dan ta gama karantarta tsaf akan lamarin nata, to dama tasan tun suna secondary ma Adawiya tasha haɗata faɗa da ƙawayensu, ta kuma koma ta noƙe ta nuna ba ita tayiba. Amma sai bata taɓa nuna mata ta gane komaiba akan hakan, dan duk sanda taje ta sanarma Umm Adawiya ta mata kaza sai Umm ta lallasheta da nasiha da nuna mata muhimmancin haƙuri da ɗan uwa. Hakanne ke daƙile Nu'aymah daga ramuwa ga Adawiyar gashi har hakan ya zame mata jiki.
         A wannan tsukun kuma data fahimci Adawiya ta canja sabon salon halaye sai itama ta canja takunta a kanta tana binta da gashi cikin ruwan sanyi, a ranta tana zargin kenan dama Adawiya na son Yah Ab komi?. A duk sanda tai wannan tunanin takanyi ƙoƙarin ganin ta ƙaryata zuciyarta, dan bata taɓa ganin alamar hakan ba ga Adawiya a dacan baya. A ganinta yanzu dai daɗin aurene yasa take ganin tafita kusanci da Abdallahn shiyyasa take shirya yaƙarta a kansa.

       Yau ma kamar kullum Nu'aymah na ɗan yin barcin rana a falo, dan da daddare tafi maida hankalinta ga ibada ne, Abdallah ya shigo gidan. Adawiya ta wuce makaranta. daga hajjo sai Nu'aymah. Da tare suke da Hajjon a falo zaune suna ɗan hira sai barci ya kwasheta, itama hajjon saita nufi ɗaki ta kwanta danta huta.
         Kafe Nu'aymah da idanu Abdallah yayi ko ƙyaftawa ba yayi, ya ƙaraso inda take yay tsaye kanta yana cigaba da kallonta tamkar mai nazarin wani abu. Cikin barci Nu'aymah taji alamar tsayuwar mutum a kanta. A ɗan firgice ta buɗe idanu saboda barcin nata baiyi nisaba sosai. Ganin Yah Ab tsaye a kanta ya sakata sake zabura tana binsa da kallon tuhuma itama. Sai kuma ta kumbura baki tana ɗauke kanta cike da takaicinsa.
        Fuskarsa a haɗe ya zauna a kujerar da take kwance, hakan ya saka Nu'aymah saurin miƙewa sosai tana faɗin, “Yah Ab minene haka wai?”. 
        “K kika cancanci wannan tambayar ai?”. Ya faɗa shima yana miƙewa yasha gabanta fuskarsa a haɗe, ya cigaba da faɗin, “K harkin isa ki dinga wulaƙantani akan wani banza can Nu'aymah? Kinzo inda nake amma sai wani basar dani kikeyi”.
       Cikin rashin fahimta take kallonsa, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta raɓashi zata wuce. Sake shan gabanta yayi yana mazurai, “Nabaki izinin tafiya ne?”.
     Idanunta cike da ƙwalla tace, “To idan na zauna mizan maka? Kodan kaga nazo na zauna a gidanka kakeson ƙuntata rayuwata?”. Hannu ya ɗaga tamkar zai ƙwaɗa mata mari sai kuma ya fasa ya dunƙulesa yana taune lip ɗinsa jikinsa na tsuma. Yace, “Uban wanene Ameer?”.
           Cike da takaici Nu'aymah ta kallesa ta watsar, kamar karta bashi amsa sai kuma mamakin abin nasa yasa ta kallesa da ƙyau. “Ban gane mikake faɗa ba Yah Ab?”. A hasale yace tayaya zaki gane mara mutunci. Nu'aymah wai harni zaki iya gudammawa a daren aurenmu saboda wani jaki? Kinsan baƙya sona miyyasa kika yarda aka saka mana ranar aure?”.
        Sallamar Adawiya da batai zato ko tsammanin Abdallah zai dawo gidan a wannan lokacinba ya hana Nu'aymah da mamaki ya kume bashi amsa. Turus Adawiyan tayi tana kallonsu, dan wanda bai saniba zai ɗauka ne wata maganar arziƙi sukeyi da juna.
     Binsu take da kallo tamkar idanunta zasu zubo ƙasa, Abdallah yay ƙaramin tsaki yana barin wajen ya nufi ɗakinsa. Har Nu'aymah ta cira ƙafa itama zata bar wajen Adawiya ta dakatar da ita ta hanyar riƙo mata hannu. Juyawa tai tana kallonta fuska a haɗe sosai, “Malama sakeni”. Nu'aymah ta faɗa a hasale.
      “Anƙi a sakekin, idan kin isa kiyi duk abinda zakiyi. miya haɗaki da mijina?”. Kallon tsantsar mamaki Nu'aymah kema Adawiya, sai dai kuma a fili saita saki lallausan murmushi da har ya bayyana haƙoranta. Tace, “Tunda kinsan mijinkine mizai hana shi kije ki tambayesa miya haɗashi dani? Inaga kamar hakan zaifi birgewa a gareki shashasha kawai”. Ta ƙare maganar da fisge hannunta tai gaba tabar Adawiya da huci.
        Hajjo data hango tahowar Nu'aymah saita saki labulen cikin ɗakin ta zauna a bakin gado. A haka Nu'aymah ta shigo ta sameta. “Hajjaju kin tashi ashe?”. Nu'aymah ta faɗa tamkar babu wani abu daya faru. Murmushi Hajjo tayi tana kallonta, “Ba dole na tashiba tunda kin gaza zuwa ki tadani mu wuce massallaci”.
     Kusa da ita ta zauna tana dariya, “Ho hajjonmu, yanzu kuma dana tadakin cazaki ban barki kin rintsa ba, gara mu maidake da ƙwarinki karsu Abba suga kin sake rugurgujewa”.
      Duka Hajjo ta kaima Nu'aymah da filo. Hakanne ya sakata tashi ta shige bayi da gudu tana dariya. Cike da tausayinta Hajjo ta sauke ajiyar zuciya, a ranta kuma tana ƙulla abubuwa da dama game da rayuwar Nu'aymahr

           A falo kam Nu'aymah na shigewa Adawiya ta nufi ɗakin Abdallah a fusace, babu ko sallama ta tura ƙofar ta shiga. Sai dai ganinta yay kawai a kansa kamar an jehota. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Hakan ne ya sake hasala mata zuciya, sai ta fashe masa da kuka. “Yanzu Yah Ab abinda kakemin kana ganin adalcine? Ni dake matarka baka da lokacina amma kanada lokacin dawowa gida da wuri dan ka kasance da Aymah? Badan ALLAH yasa yau na shigo gidan da wuri ba bama zansan hakan na faruwaba tsakaninku. Shin wai da mi Nu'aymah ta fini ne? Wlhy sai ALLAH ya sakamin duk cin amanata da akeyi, kuma ni na gaji zan kira baba malam na faɗa masa komai tunda naga ita hajjo goyon baya take baku ma, ƙilama wataran a gabanta zaku shiga ɗaki ku rufo bazata tankaba saboda tana tsoronku......”
        Wani wawan mari ya sauke mata a fuska da saida taga stars na mata kaikawo, balle dama ga azumi. A take ta zube ƙasa da sakin wata ƙarar kuka data kai har kunnen Hajjo.
        “Kai Abdillahi lafiya kuwa? Mike faruwa hakane nakejin kukan Adawiya?”. Ta ƙare maganar tata dai-dai lokacin da take ƙarasowa cikin ɗakin. Ganin Adawiya kwance ƙasa dafe da kunatu ya saka hajjo zaro idanu, “Mikai mata Abdullahi?”.
     Cikin ɓacin rai yace, “Hajjo barni da ƴar iskar nan kawai, wlhy tai wasa wataran saina karya ƙasusuwanta a gidan nan tunda ita kamar dabba take”.
            “Ya isa haka”. Hajjo ta faɗa tana ɗago Adawiya dake ƙasa tana cigaba da sakin gunjin kuka. Saida ta zaunar da ita saman kujera sannan ta sake tambayar Abdallah miya faru?. Faɗa mata komai yayi amma banda tsayuwarsu da Nu'aymah, baisanma ita taji komaiba.
     Cikin ɓacin rai Hajjo tace, “Adawiya dama baki da wayo haka? Ita ƴar uwar takice kuma tazama abar kishi a gareki? Har kike jifansu da wannan mummunan lafazin ita da mijinki? Adawiya yaushe kika bari ƙawayen banza suka canja miki tarbiyya ne? Har haka. To wlhy ki shiga hankalinki, idan kuma ba hakaba ni bazan ɗauki wannan banzan halayen a cikin zuri'ata ba, saina ɓatama kowa rai a cikinku har iyayen naku ni babu ruwana. Bandama iya shege kowa na fama da ibadar ALLAH a baki ke kina biyema sheɗan yana ɗoraki akan dokin zuciya. To idan na sakejin makamancin wannan zancen lallai sai kinyi nadama shashasha kawai. Banda ƙaddara da yanzu ita wadda kike cin zarafin ba itace matsayin matar tasa ba”.
        Haka Hajjo taima Adawiya tas sannan ta fito ta barsu. Duk abinda akeyi Nu'aymah najinsu, sai dai ko tari bataiba balle a fahimci ta sani ɗin. Daga ƙarshema sukai shiri suka wuce massallaci, suda gidan kuwa sai anyi sallar asuba kuma.

      Tun daga wanan ranar Adawiya ta shiga fishi da kowa a gidan. Daga gaisuwa bata sake tankama wani. Ahmad yamata nasiha harya gaji ya watsar da ita shima. Bayan kwana biyu da yay dai-dai da cikarsu kwanaki biyar da zuwa, ashirin kuma ga watan azumi Nu'aymah ta tattara inata-inata ta koma massallaci zaman ittiqafin.
       Abdallah yaso hanata, sai dai Hajjo tace ya barta tai ibadarta yamafi zaman nata a gidan aita fitina. Badan yasoba ya haƙura, dan yaso a wannan zaman suyi magana ta fahimta da Nu'aymahr ya samu ya lallaɓa hajjo dasun koma a ɗaura musu aure.
        Bayan barin Nu'aymah gidan sai ga Adawiya ta saki jikinta, ashe dama Nu'aymahr ce natsalar rayuwarta. Babu wanda yace mata komai. Saima hajjo ce taima Abdallah magana akan su shirya shi da Adawiyan dan tare zasu wuce Najeriya ayi bikin salla. Kai tsaye Abdallah ya nuna cewar bazaije ba, sai dai Adawiya, dan shi bai manta ALLAH ya isan da mahaifiyarsa tai masa akan zuwan nasaba. 
      Balbalesa da masifa sosai hajjo tai dan ita batasan dalilinsa na bijirewarba. da taga dai ya tirje ɗin saita kira baba malam ta faɗa masa komai. Shine ya kira Abdallahn cikin bada umarni ya sanar masa ya shirya suzo salla gida tunda suna samun hutu a wannan lokacin.
          Abdallah ya shiga tsaka mai wuya sosai akan hakan, dan yasan dai umarnin mahaifiyarsa dana baba malam babu wanda yake da damar tsallakewa a ciki, dan duk sunada daraja da kima a idanunsa da rayuwarsa.

_________________________
            *_NIGERIA_*

      A kwanaki biyun nan abubuwa sun sake tsamari akan Yoohan, gaba ɗaya neman birkicewa yake saboda rashin samun barci, tun daga jiya zuwa yau yaƙi magana da kowa a gidan, yama kulle kansa a ɗaki ya hanama kowa ganinsa. Momy tayi kukan tayi roƙon amma yaƙi buɗewa. Hakama su Gebrail sunyi nasu ƙoƙarin ya sharesu.
      Amma saboda ƙarfin hali da burinsa nason cika alƙawari sai gashi a safiyar yau talata yayi shirin tafiya kano. Tunda safe ya bama Solomon umarnin faɗama guards ɗinsa su tafi kano. Su kuma ya nema musu ticket guda uku. Solomon nason tambaya akan hakan yanajin tsoro, dan haka yaja bakinsa yay shiru yaje dai ya cika umarninsa

           Kusan ƙarfe huɗu na yamma sai gashi ya sauka ƙasa cikin shigarsa ta suit blue mai haske. sun masa bala'in ƙyau duk da yana a yanayin da a kallo ɗaya zaka fahimci akwai damuwa tattare da shi.
      Momy ce kawai zaune a falon sai Victoria da Abraham. Cikin girmamawa a garesa yaran suka shiga gaishesa. Hannu ya ɗaga musu kawai tare da ƙarasowa inda suke duk ya shafa kansu batare da yayi magana ba.. 
     Ya maida dubansa ga Momy da idanunta suka kumbura saboda kuka, ɗauke kanta tayi ita a dole fushi take da shi. Baice komaiba ya ƙaraso inda take ya tsaya a gabanta tare da riƙe kunnuwansa da hannayensa alamar ban haƙuri.
     Bata iya dogon fushi da Yoohan ɗinta. Dan haka tai murmushi tare da miƙewa ta rungumesa. Yau dai ya daure bai tureta ba, sai da ta gaji dan kanta ta sakesa sannan, ta amshi tie ɗin hannunsa ta ɗaura masa tana faɗin, “My Boy nikam yaushe zaka fara saka necktie da kanka?”.
     Bai bata amsaba, sai dai ya sake ɓata fuska alamar shagwaɓa. Da ƴar dariyarta ta shafa masa kwantaccen sajensa da yasha gyara yau, ya kama hannun nata ya sumbata kaɗan.
       “Ina zakaje ma wai?”. Ta tambaya tana tsatstsaresa da idanunta manya. Da ƙyar ya buɗe baki wajen bata amsa da “Kano”. “Kano!! kuma Yoohan? Mizakayo a kano kaida kake cikin wannan halin? Badai aiki ba?”. Kansa ya girgiza mata, batare daya bata wani ƙarin bayani ba yace mata, “Bye” yana nufar ƙofa.
        Saurin binsa tai tana kira, amma sai yaƙi tsayawa, saida ta haɗa daɗan gudu ta cimmasa, duk da kuwa tafiyarma ba wani sauri yakeba saboda rashin ƙwarin jikinsa. Yanda ta riƙosanne ya sakashi waigawa ya kalleta. Tace, “Ina tambayarka mizakayo acan amma ka taho baka kulaniba Yoohan”.
      Kansa dake faman masa ciwo ya dafe kaɗan, kafin cike da ƙosawa yace, “An gayyaceni ne” danshi baison yin ƙarya a rayuwarsa, kamar yanda ya tsani kuma saɓa alƙawari. Yana gama faɗa ya zare hannunsa zai juya ta kuma riƙewa. Yanzunkam bai juyoba sai da yaja wasu sakanni. Muryarta da damuwa ta zagayo gabansa tana magana. Amma maimakon ya bata amsa sai ya saka yatsansa akan baki yace “Shiii!!!”. 
       Shirun kuwa tayi tana kallonsa, ya ɗaura yatsunsa saman baki yay mata alamar *_Smile_* kamar yanda ya saba mata aduk sanda ya ganta a damuwa tun yana yaro. Duk da batason yin hakan saita murmusa. Yay mata jinjina yana ɗan lumshe idanunsa dake a kumbure sosai.
      Tanaji tana gani ya shiga mota driver ya jasu shi da Solomon suka bar gidan, gashi Papa bayama ƙasar jiya sukai tafiya shi da Uncle Zamani.

★★★★★

        Airport driver ya kaisu. inda acan suka haɗu da Manager Hamza Ibrahim yana jiransu. Sun gaisa cikin mutunta juna Hamza na mamakin ganin Yoohan ɗin a ƙunci fiye da waccan ranar. Ga idanunsa da fatarsu tai jajur hakama farar fuskarsa. Haka kawai yaji a ransa akwai abinda ke damun Yoohan ɗin. amma sai baiyi magana ba suka nufi ciki.

       Ƙarfe biyar da rabi jirginsu yabar Abuja zuwa birnin dabo kodami kazo mun fika🤗😜.
       Kamar yanda Yoohan ya iske Guards ɗinsa na jiransa haka suka iske motoci biyu na tarbarsu kuma. Hakan ya sai ya sake birge Yoohan matuƙa, dan haka bai shiga tasa motarba ya shiga wadda aka aiko musu, Guards ɗinsa kuma suka bisu a baya.............✍
 
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: No. 24

...............Baba malam daketa kaikawo na ƙoƙarin ganin komai ya kammala yanda yake buƙata ya nufi sashen nasa a karo na babu adadi. Yanda ya hana kansa sakat akan tarbar baƙonsa haka ya hana Umm sakat itama, dan baiwar ALLAH nan tun ƙarfe biyun ran take a kan ƙafafunta tana hidima. Sauƙinta ma Addah ta shigo tana taimaka mata, ga kuma mai aikinta. 
           Omar ne biye da shi, dama yafi shaƙuwa da shi a samarin yaran gidan fiye da kowa, duk da dai ada kam sunfi shaƙuwa da Abdallah, amma daga baya da Omar ɗin yafi Abdallah zaman kano sai shaƙuwarsu ta zarce ta tsakaninsa da Abdallah ma. Dan shi Omar yarone mai tsananin ƙwazo da biyya ga iyayen nasa, sannan baba malam shine babban malaminsa na addini fiye da kowa, shiyyasa koda yaushe yana kano bai cika son zaman Abuja ba shi.
     Kai tsaye kitchen suka nufa, inda suka iske Umm da Addah suma dai kamar su tsinke nasu ran, dan tare suke aikin daya rage ɗin. Bayan Baba malam yay sallama baima bari an amsa masaba yace, “Umm Muhammad yaya kun kammala?”.
     Ɗagowa Umm tai taɗan kalli mijin nata, sai kuma ta maida akan aikin gabanta tana cewa, “Abban Nu'aymah wlhy nikam dai zakama sake rikitamu gaba ɗaya, insha ALLAH muna gab da kammalawar, dama zuwa kai kayi wanka dan magrib ta gabato”.
     Murmushi shimfiɗe a fuskarsa ya ƙaraso yana amsar abinda take tace lemon mangwaron daya rage su haɗa. “Ke dai kawo na taimaka miki ki kammala kawai, dan yanzu haka an wuce ɗakkosu fa”.
     Dariya Umm da Addah da Omar sukai, ya ƙaraso wajen baba malam ɗin yana faɗin, “Abba kawo ni nayi basai kayi da kanka ba. Dan nikam yau namafi kowa zumiɗin son ganin wannan baƙo mai daraja a wajenku Abba, dan naga gaba ɗaya hankalinku na kan son ganin an ƙyautata masa, yau kota abincin buɗa bakinmu bakwayi sai na baƙo”.
        “Kace ido ka saka mana? Hakama malam ƙarami (baban yaron Addah) sai da ya gama ƙorafi kafin ya wuce airport ɗakkosu”. Ita dai Umm da Addah dariya sukayi musu kawai, ta matso suka ƙarasa haɗa komai ita da baba malam ɗin. yayinda Omar da Addah kuma suke ɗorawa tray. Omar ne ya ƙarasa kwashewa ya kai komai can sashen kakansu  inda za'a sauke baƙon. Hakan kawai ya isa kasan an daratta baƙon sosai, dan duk baƙon da su Baba malam zasu kai da shigo dashi cikin gidansu to lallai ya isa kuwa.

     Sai da yaga an fita da komai sannan ya sauke ajiyar zuciya, tare da ficewa domin aiki da shawarar Umm ta farko. Cike da gulma irin ta aminai Umm da Addah suka kalli juna, sai sukai murmushi kawai dan Baba malam ɗinne ya basu dariya.
    Ficewa sukai a tare suma zuwa sashen da aka shirya abincin, suka ƙara gyara komai tare da saka turaren wuta da kuma Air Fresheners masu ƙamshi. Kamar Umm ta sani har zasu fito saita yanke shawarar fita da kaskon turaren, acewarta kar ko a baƙin asamu mai Asthma ya cutu. Ta ɗan ɗaga labulen Windows ɗin kaɗan hayaƙin turaren ya ragu sosai. Cikin sa'a ma sai gashi Omar yaje ya tada Genretor. Ac suka kunna tare da sake duba komai suka tabbatar yayi dai-dai sannan kowa ya nufi part ɗinsa Umm nama Addah godiya.
      Dan tasan badan itaba da aikin baiyi sauriba sam. Mama amaryar Abba Musbahu kuwa dama ita sai a hankali ce, San jikinta bai bari tama kula da sashenta ba balle taimakon wani kuma, komai ƴan aikine keyi, kodan taga mijin ba mazauni bane oho.

         Motocin na shigowa anguwar ana fara kiraye-kirayen sallar magriba. Yoohan na kwance shiru a jikin kujera idanunsa a lumshe. Baisan inda ake shiga da fita ba har saida motocin suka tsaya a ƙofar katafaren gate ɗin. Hakan sai yayi dai-dai da fitowar baba malam da Abban su Adawiya, sai Malam ƙarami da Omar da sauran samarin gidan da yara amma iya mazan kawai.
       Duk da yanda guards ɗin Yoohan suka firfito suka zagaye motar da yake a ciki hakan bai saka fuskokin su baba malam sauyawa daga fara'ar dake tattare da suba. Akan idonsu Hamza Ibrahim ya fita. Kafin Yoohan da Solomon ya buɗemawa shima.
     Shima a gaban idanun nasu ya fito, bayan ƙafarsa kuma da sarƙar Cross ɗinsa suka fara cin karo kafin cinkusashshiyar fuskarsa. Abinda zai baka mamaki a tare su baba malam sukayo caa a kansu. Cikin ƙyaƙyƙyawan tsari na masu ilimi da baiwar hikima suka tarbesu. Wani iri Yoohan yaji a ransa shima duk da kuwa dama ya fahimci masu gayyatar tasa musulmai ne, amma sai ya dake ya basar.
           Duk yanda yaketa faman musu shan ƙamshi da cika da batsewa babu wanda ya canja yanayin nasa, saima sannu da zuwa da suka shiga jera musu tare da basu hannaye suna musabaha har guards ɗin. Kafin baba malam ya bama Malam ƙarami da Omar damar shiga da Yoohan ɗin ciki. Danshi Hamza Ibrahim ya buƙaci a inda zaiyi alwalane kai tsaye.
      Yoohan dai baiyi musu ba yabi bayan su Omar, sai dai idonsa da zuciyarsa nakan hasaso masa a inda ya taɓa sanin fuskar baba malam a rayuwarsa. Guards ɗinma bin bayansu sukai. Omar zaiyi magana baba malam ya girgiza masa kai alamar ya barsu.

          Tun a farkon shigowa gidan Yoohan yasan masu gidan sun wuce raini, dan babu abinda nasu gidan zai nuna masa sai dai kayan ƙawa da ƙyale-ƙyale, nasu baba malam ma yafi nadu girma sosai. A haka su Omar suka kaisa har falon, guards ɗinsa biye da dasu kamar wasu jela ko suna ganin za'a cutama Yoohan ɗinne oho musu. Sai da sukaga ya zauna suka ajiye masa ruwa da lemo kozai buƙata sannan sukai masa sallama suka fito, duk da basuji ya amsa musu da ƙyau ba. Dan Solomon ma tunda ya fahimci inda suka kawo kansu sai takaicin ogan nasa da buɗaɗɗen ra'ayinsa ya shiga masa zafi a rai. Dolene yay saurin sanarma Madam Chioma kafin a bama Boss ɗin nasu wani abin yaci a tsafesa.
        Yana cikin shawara da zuciyarsa ta yanda zai silalo daga cikin falon ya kira madam ɗinsu sai ga sallamar su Baba malam, da alama ana idar da sallar magrib basu zaunaba suka shigo gidan. Aiko takaici kamar ya kar Solomon, amma duk da haka saida yayi dabarar turama Momy text message ko za'a dace wayar na a hannunta ta gani.

         Koda suka shigo Yoohan na'a zaune yanda yake baiko motsaba, sai dai yana binsu da kallo ne ta ƙasa ido. Abban Adawiya da suka taɓa haɗuwa a orphanage ranar da suka buge yaron nan sai ganin Yoohan ɗin ya sakashi matuƙar jin mamaki. Duk da ya jima a ransa yana zargi da hasashen kodai shine mai musu wannan ɗawainiyar. Rashin tabbas ɗin hasashen nasa yasa bai taɓa yin magana ba sai yanzu ya ɗan gwargwaɗa ma baba malam cikin harshen larabci.
     Murmushi kawai baba malam ɗin yayi, cike da kulawa ya maida hankalinsa akan Yoohan da suka fahimci a takure yake da kasancewarsa a wajen. Basu damuba, dan sunyi gamo da waɗandama suka fisa taurin kai da aƙida amma cikin amincin UBANGIJI sun sami nasarar canjasu. To balle shi kuma dama suka fahimci zuciyarsa nada rangwame tunda har ya iya kasancewa maison ƙyautatawa marayu.
     Duk da baba malam yaga saɓanin abinda yay tammani daga Yoohan hakan baisa ya canja komaiba daga ɗokantuwa da mutunta baƙon nasu. Hakam ɗan uwansa da ƴaƴansu basu nuna wani mamakinsu a fili ba ko ƙyanƙyamin su Yoohan ɗin, kowa ya shanye a ransa. Ba Yoohan kawai ba, dai-dai da guards ɗinsa an mutuntasu fiye da zatonsu, dan suma ca akai su zauna ayi buɗa bakin dasu. Duk da suna noƙewa saboda boss ɗinsu haka baba malam ya matsanta musu. Ganin Yoohan kuma bai tanka musu ba, yamayi kamar baisan mi akeyiba sai suka saki jiki aka kwashi gara da su, a ransu kuma suka koma zuba santi dajin kimar mutanen musamman yanda aka nuna musu suma mutanene masu daraja ba bautace kawai aikinsu ba.

      Yoohan kansa da keta noƙewa da farko tuni baba malam ɗin ya tsaresa sai yaci, harda nuna masa idanfa baici da hannunsaba shi zai basa da kansa to, kuma ɗura zai masa. Karan farko a rayuwata da ni kaina mai ɗakko muku rahoto naga murmushi a fuskar Yoohan yau. Dan shi kansa a bazata ya saki lallausan murmushin ga baba malam ɗin.
      Baba malam yace, ‘Masha ALLAH’ a ransa, duk da yau ya fara ganin Yoohan sai yaga murmushin yay bala'in masa ƙyau. Haka dai suka gudanar da buɗa baki cikin nishaɗi da farin ciki. Guards ɗin Yoohan dake ɗar-ɗar harda Solomon mai hasashen banza sai gasu sun kwashi gara suna washe baki dajin farin ciki a ransu.
    Kiran sallar isha'i ya saka su baba malam ficewa massalaci akabar Yoohan da tawagarsa. Sai dai kuma bayan fitarsu babu jimawa shima sai ya miƙe da nufin ɗan yin tattaki ko cikinsa zai sauka. Shi kansa yasan ya jima a rayuwarsa baiyi irin wannan cin abincinba, ballema a ɗan tsakanin nan da yake cikin halin ha ula'i. Ta ƙaramar ƙofar da yaga su baba malam ɗin sunbi shima ya bi, kai tsaye ta kaisa ƙatuwar harabar massalacin kuwa. 
         Ko'ina ƙwanyar yake da haske tamkar rana. Ga mutane maza da mata harma da yara cike da massalacin harda mata. Yoohan yay tsaye jikin katanga yana kallonsu cike da nazari har aka tada salla. Ba massallacin kawai ba hatta anguwar kanta sai yaji ta ɗauki shiru gaba ɗaya, babu abinda kakeji sai sautin karatun salla da baba malam keyi. Lokacin da ya kammala karanta fatiha mamu suka amsa da “Amin!!!!” sai gaba ɗaya tsigar jikin Yoohan ta tashi, zuciyarsa tai wani bala'in tsargawa har saida ya rumtse idanunsa.
        Baisan dalilin daya hanashi komawa ciki ba, haka ya cigaba da tsaiwa har sukai ruku'u. suka sake ɗagowa sukai sujida. Tsigar jikinsa sake tashi tayi a karo na biyu, dan yanda sukai sujidan gasu a sahu nagartacce dolene ko musulmin ya gani yaji ƙarin imani a ransa balle wanda bai taɓama yin sujudar ga UBANGIJI ba.
      A hankali Yoohan ya ɗaga ƙafafunsa ya fara ja baya da ƙyar harya fice a harabar massalacin ya koma cikin gidan. Haka ya cigaba dajan jiki harya isa falon da aka saukesu da ƙyar. Tsitt guards ɗinsa daketa faman surutun santin abincin da sukaci sukayi ganin ya shigo kamar a birkice. Da sauri duk suka miƙe tsaye domin girmamawa. Solomon ya taimaka masa ya zauna.
     Sai kuma duk hankalinsu ya tashi, amma yanda baiyi maganaba suma sai basuyiba sukai dai masa tsaye cike da tsoron kodai an cutar dasu ɗinne kamar yanda sukai hasashe tun farko?.

        Har aka idar da sallar asham Yoohan bai dawo hankalinsa ba. Baba malam da ayau baije tafsir ba dama ya ɗauki alfarma suka sake shigowa. A yanda yaga Yoohan ɗinne ya saka hankalinsa tashi. Tambayar guards ɗin ya shigayi a ruɗe. Nan sukai masa bayanin abinda suka sani kawai. na cewar Yoohan ya fitane shan iska sai ya dawo musu a haka, dama kuma bashi da isashen lafiya, bama suyi zaton zai iya zuwa nan lafiya lau hakaba.
       Ɗan shiru Baba malam yayi cike da nazarin bayanin da Solomon yay masu na rashin yin barcin Yoohan, kafin ya zauna kusa da Yoohan ya janye hannunsa daya dafe kansa da shi ya maye gurbinsa da nasa, addu'oi ya fara masa yana tofawa, ya kuma saka Abban Adawiya yin wasu addu'oin a ruwa ya miƙo masa. Kamar Solomon zaiyi maganar karsu bashi sai dai ya kasa saboda nauyin da bakinsa yay masa da kuma kwarjinin mutanen. 
       A gabansu akaba Yoohan ruwan addu'ar yasha. baba malan ya zuba a hannunsa kaɗan ya kuma shafa masa a fuska. A take ya fara sakin tagwayen ajiyar zuciya a jajjere. Ya buɗe baki da ƙyar yace, “Thanks”. Murmushi baba malam yayi kawai, kafin yace, “inaga ya kamata a kaiku masauki ka huta, dan da alama idanun nan naka barci sukeji”. Cike da mamaki Yoohan ke kallon baba malam, duk da dai ya kasa yarda su haɗa idanu da ƙyau dan bala'in kwarjini baba malam ɗin ke masa shikam. Sake murmusawa baba malam ɗin yayi. Ya ɗauke kansa ya maida gasu Omar. 
      “Farukh a kaisu masauki ko”. Da sauri Omar yace, “To Abba”..
      
      Da gaske Yoohan barci yakeji fiye da zatonsa, dan haka ya kasa musama baba malam duk da kuwa shi a yau yaso su juya zuwa Abuja shi da Solomon da Manager, guards ɗinsa kawai yay shirin bari su kwana a kanon da safe suma su wuce. Amma sai yaji babu abinda yafi buƙata kamar kwanciya a yanzun.
          Su Malam ƙarami sun kaisu gida mai ƙyau matsakaici dake gaba da gidansu kaɗan, inda nanne masaukin da su baba malam ɗin kan sauke baƙi daman. Tsaf yake gidan, saima uban ƙamshi mai saka kwanciyar hankali da ya keyi. Duk da babu wutar nefa nanma an tada gen.....
     Abin mamaki sai ga Yoohan kamar bugagge, suna shiga wajen kwanciya ya buƙata. Yana ganin gado kuwa ya zube akai yana sauke ajiyar zuciya abin tausayi.
     Takalma da necktie ma sai Solomon da Manager ne sukai 
dabarar zare masa. Hakama jacket ɗin suit ɗinsa. Sai suka barsa da shirt ɗin da dogon wando kawai.      

    Manager ne ya kwana tare da Yoohan duk da shi Solomon baiso hakaba. Bawan ALLAH nan yanda ya kwana bautar UBANGIJI haka ya ja doguwar addu'ar samun haske daga Yoohan ɗin. Hakama su baba malam, ranar mafi yawan addu'oinsu akan Yoohan suka yisu da ga su har iyalansu. Da asuba aka kawoma Hamza abin buɗa baki, daga Yoohan har guards ɗinsa barci suke kwasa masu a lokacin.

★★★WASHE GARI★★★

             Washe gari sai ga kowa ya tashi banda Yoohan, barci yake cike da kwanciyar hankali, dan haka baba malam daya zagayosu har sau kusan uku ya hana a tadashi. 
      An kawo musu lafiyayyen breakfast sukaci suka ƙoshi, wajen sha biyu ma aka sake kawo musu abinci nanma. Ganin har ɗaya saura bai tashiba Solomon ya bama sauran ƴan uwansa shawara akan su tafi, shima zaije ya sayoma Yoohan kaya ya kuma nema musu ticket. .  
     Basu musama wannan shawara ba, suka shirya suka tafi harda Solomon ɗin, dan sai da suka kaisa ya kammala uzirinsa kafin su sake maidosa gida, sukaje sukai sallana da baba malam da yake a lokacin sun samesa tsaye a ƙofar gidansa ya dawo daga orphanage ne..
       Baiso tafiyar tasuba, amma sai bai hanasuba tunda ƙila sunada uziri. Ya musu godiya sosai tare da basu tsaraban da aka shiryama Yoohan ɗin dan suyi gaba da ita, suma kuma aka basu tasu. Yanda su baba malam ke musu godiyar sai duk abin ya ɗaure musu kai da saka jikinsu yin sanyi akan a ƙidarsu. Har suna hasashe a ransu dama haka musulmai keda kirki da karamci amma ake aibantasu da nuna musu suba mutanen kirki bane? To su dai gashi jiyane karon farko da sukai mu'amula da musulmai hausawa mai tsaho amma sai basuga hali mara ƙyau ɗin da ake faɗar suna da shiba saima alkairi da ƙyawawan halayya abin koyi.
     Sun tafi da wannan alkairai da akai musu cikin rai sosai.

     Bayan wucewarsu baifi da mintuna talatinba Yoohan ya farka. Yayi matuƙar mamakin ganin inda ya kwana, manager ya taimaka masa da ruwan wanka, Solomon zai shiga gabatarma Yoohan ɗin da kayan daya siyo masa sai ga malam ƙarami da kaya sabbi fill ya kawo. Sai kuma abinci da aka shiryoma Yoohan ɗin tunda sunsan bai karyaba shi.
         Haɗa kayan Solomon yay gaba ɗaya ya kai ɗakin ya ajiye. Ya juya zai fita Yoohan ya fito. Dakatawa yay ya gaidashi cike da girmamawa. Yoohan da kejin kansa sakayau kamar ba shiba ya amsa masa idanunsa nakan kayan da Solomon ɗin ya ajiye masa. sai dai baiyi maganaba sai shi Solomon ɗinne yay masa bayani.
           Zama yay ya gyara jikinsa tsaf, ya buɗe kayan duka, na Solomon ƙananun kayane, nasu baba malam kuma shaddace ruwan zuma da akaima ɗinki mai ƙyau kuma dai-dai shi kamar an gwada. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa saka kaya makamanta hakaba. Duk da kuwa suma a nasu yare suna ɗinka shigensu amma shi bai taɓa sha'awar yin hakanba. A yau kam sai yaji sun birgesa har yay sha'awar sakawa. Haka ya warwaresu ya saka.
      Baisan lokacin daya furta kalmar ‘Woow!’ ba a fili yana sake kallon kansa a mirrorn ɗakin. A haka manager da shima yay shiri tsaf a kayan da aka kawo masan ya shigo ya samesa. Sosai yake yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan shima, sai ko Yoohan ɗin ke sanar masa shi bai taɓa sakawa ba sai yau. Hamza yayi mamaki sosai, duk da daga jiya zuwa yau ya fahimci su Yoohan sunada tsauri ko a cikin Christians ɗin ma, dan ya karanci yanda guards ɗinsa suka ringa gudanar da al'amiransu.

       Sun fito falo Yoohan yaci abinci, bayan ya kammala babu jimawa sai ga Abba da Baba malam sun shigo. Su kansu bakinsu bai iyayin shiru ba sai da suka yaba ƙyawun da Yoohan yayi a kayan. Ya duƙar da kansa ƙasa saboda kwarjinin da suke masa yana godiya a garesu, musamman yanda suka sakashi yay barci jiya bayan kwanaki tara daya kwashe baiyi ba.
     Cikin hikima ta masu ilimi baba malam ya nuna masa basune ba, UBANGIJI ne yay ikonsa, su nasu kawai roƙone cike da yaƙinin samu. Duk da Yoohan bawai ya fahimci maganar tasu bane sosai saiya gyaɗa kansa kawai. Sun ɗanyi hira kaɗan, duk da Yoohan dai bai saki jikiba sosai. Hamza ne ke biyema su baba malam ɗin, Solomon ma baya saka baki. Wannna ɗan zaman nasu ya saka Yoohan ɗin sake jinjina mutuncin mutanen da sanin darajar ɗan adam ɗinsu. Sai da su baba malam sukayi sallar la'asar sannan sukai musu rakkiya har airportda kansu suna sake roƙon Yoohan ɗin yazo musu bikin salla harma da Manager.
     Yako amsa zaizo kodan yay gaisuwa da yaran orphanage.

________________

      Guards ɗin Yoohan sun iske madam Chioma ashe bata gari tayi tafiya zuwa ƙauyensu mamarta babu lafiya, saƙon kuma ya risketa bayan wucewarsu kano babu jimawa. Dan haka ta wuce hardasu joy da Gebrail. Su Victoria ne kawai da ƴan aiki suma saboda makaranta ne.
      Sun shiga da tsaraban cikin gida suka ajiye har boss ɗinsu ya iso. Aiko zuwa biyar na yamma sai ga kiran Solomon yace suje su ɗaukesu a airport.

        Su Abraham sunyi murna sosai na dawowar yayansu, sunata kallon kayan jikinsa mamaki na cinsu. Sai dai sun kasa tambaya dan babu fuska. Shi kuma bayan yaji komai na ciwon kakar tasu sai ya shige sashensa yay kiran momy.
     Sun tattauna sosai ya basu shawarar ɗakkota a taho da ita nan Abuja ya dubata, dan ashe dama tun jiyan suke neman layinsa amma bai shigaba. Bayan sun ajiye wayar sai yay kwanciyarsa. Wani barcinne ya sake ɗaukarsa mai nauyi yauma. Bai kuma farkaba sai gabannin asuba.

Washe gari tun kusan goma na safe su Momy suka iso abuja, sun iske Yoohan ɗin ya gama shiryawa tsaf game da jikin kakar tasu. Suna isowa kuwa ya dukufa kanta. Cikin amincin UBANGIJI sai gashi tun aranar jikin nata ya fara sassautawa.
        Wannan hidimar jinya ce ta mantar da madam Chioma sake bin ba'asin zuwan Yoohan kano har ma hutunsa ya ƙare yabar abujan.

*_A KWAN A TASHI_*

       Babu wahala wajen UBANGIJI, dan gashi yau saura kwana biyu kacal salla, kowanne yanki na musulmi suna cikin shirye-shiryen ta da yin bankwana da azumin watan ramadhan😢.
      Yayinda su Nu'aymah ƴan saudia keta shirin dawowa suma a ranar sallar...........✍



_____________________
SAHFAT PREORDER!
______________________

        Wani kaya sai amale ka ɗauka🤗.

SAHFAT PREORDER maida tsohuwa yarinya.

Kaji masu kawo kayan adon gida dana jiki ƴan gaske.

*_Ina mata masu ƴan bana bakwai? ko uwargidar da ake shirin kawoma ƴar bana bakwai?. Kai hardama matan gayu ƴan ƙwalisa masu son sabunta gida da kayan ado ƴan waje masu sauƙin farashi da nagarta!._*

_To ku garzayo dama ta samu, dan SAHFAT PREORDER sune na ɗaya a wannan fanin. Idan kayan kitchen kikeso masu ƙyau da nagarta a farashi mai sauƙi kuma zaki samu a Sahfat preorder. Idan kayan sakawa kikeso na manyan mata ƴan gayu suma akwaisu babu ƙayarya. Jaka ko takalma na nunawa tsara suma ba'a barsu a baya ba harma da mayafai. Hakama kayan ɗaki basu da tsara_.

Ni shaidace domin dukkan kayana ta hannunsu nake samu nima. Ku garzayo kuma a dama daku dan nasan zakuyi alfahari da hakan insha ALLAHU.

Kiyi magana ta wannan Number 08142957548 insha ALLAH zaki samu ƙarin bayani ƴar uwa.

*_Siyen nagari😇, maida kuɗi gida😉 sai SAHFAT PREORDER🤗🤗😘😍😋_*

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: Alhmdllh, barkanku da salla. Barkanmu da dawowa filin daga.

    Da farko zan fara da baku haƙuri akan ɓacewata ɓat tun kafin azumi. Uzirine babba kuma mai ƙarfi da bazan iya ajiyesaba ya riskeni. Amma Alhmdllh komai ya daidaita. Na kuma gode sosai da haƙurin da kukaimin.

Kufara da wannan kafin gobe idan ALLAH ya kaimu.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biyaba ki haƙura domin ALLAH🙏🏻☺️_*


No. 25

...............“Hajjo nikam mizai hana tunda kince bayan salla da sati uku za'ai bikin su Hajarah mu bari sai lokacin bikin muzo ni da Adawiya? Abinda zaki duba abune bana kusa ba, kuma gashi mu duka karatu mukeyi, musamman ma ni da nake gab da kammalawa. Idan har nace zan ringa jeka ka dawo zan iya samun matsala wlhy”.
         Hajjo da ke sauraren yah Abdallah ta jinjina kanta cike da nazarin maganganun sa, ta sauke numfashi da gyara zamanta saboda ƙafarta mai mata ciwo. “Gaskiya kam Abdullahi ka fimu gaskiya daga ni harsu ɗan malam, duk da nasan suma ɗin kansu, abinda yasa wannan tunanin baizo musu ba, saboda ba'a gama dai-daita maganar su Kubrah ɗin bane ba. Na kula kamar shi mai auren Hajarah keson kawo wani tsaiko akan batun shiyyasa suka jinkirta harni na koma. Amma yanzu inaga ka barni dasu, zanyi magana ta fahimta da ɗan malam insha ALLAH”.
        “Nagode sosai Hajjo, ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai mai amfani. Ki daɗe kiyi ƙarko hajjajun mu”.
     Murmushi kawai hajjo tayi da shaƙiyancin jikan nata. Daga haka suka cigaba da firarsu har zuwa wani lokaci ya fice ya barta tana ƙarasa shiri, dan Nu'aymah nacan ta tare a massallaci tana ibadar ALLAH.

           Cike da farin ciki Abdallah ya faɗa saman gadonsa yana murmushi, insha ALLAH indai su baba malam suka amince zuwan nasu ya koma sai bikin su Kubrah yanada yaƙinin samun cikar burinsa. Dan babban fatansa shine shirinsa akan mallakar Nu'aymah ya tafi dai-dai, shima ranar ɗaurin auren su Kubrah a ɗaura nasa da masoyiyarsa, farin cikin rayuwarsa.
       Wayarsa ya jawo dake a gefensa, ya shiga ma'adanar hotunansa yana kallon hotunan da yaytama Aymah a wannan zuwan nasu batare da ita kanta tasan yana ɗaukarba. Ya jima yana kallon hotunan kafin barci yay awon gaba da shi a wajen
            Barcin nasa bai kai mintuna ashirin da ɗaukarsa ba Adawiya ta shigo gidan ita da maman Aaida. Ganin ɗakinsa a buɗe ya sakata nufar can tana faɗima maman Aaida, “Aminiya zauna ina zuwa, naga kamar Yah Ab yana gida ma”.
     Ɗan murmushi maman Aaida tayi da bata amsa cike da zolaya. “To adaibi a hankali azumi ake hajjaju”. Batare da Adawiya ta bata amsa ba ta shige tana dariya.

          Hajjo da dariyarsu ta sakata farkawa da ga ɗan barcin daya figeta itama ta fito dan taji ba muryar Adawiya bace kawai. “Baƙuwa mukayi a gidan?”. Ta faɗa lokacin da take fitowa falon. Maman Aaida dake latsa waya ta ɗago idanunta ta sauke akan Hajjo. Sai kuma tace, “Barka da fitowa hajiya”.
      Hajjo dake mata kallon sani tace, “Barka dai ƴar nan, gashi kuma kamar na sanki”.
     Da sauri maman Aaida ta zaro idanu waje da mamaki, sai kuma ta tuna maganar hajiya datai mata gargaɗi tun farko akan zuwa gidan, amma yau tsabar taurin kai sai gashi ta biyo Adawiya data dinga mata daɗin baki..........
      “To ko dai kamanni ne?” 
Hajjo ta katse mata tunani. Da sauri maman Aaida tace, “Eh gaskiya hajiya inaga hakane, dan ni ƴar nance”. Cike da nazarinta Hajjo tace, “Oh to ALLAH sarki, kinsan idon tsufa ƴar nan. To barka da zuwa, halan ke ƙawar Adawiya ce?”.
      “Eh hajiya”. Maman Aaida ta bata amsa a ɗarare, dan tasha jinin jikinta da kallon ƙurulla da hajjon ke binta da shi...

         Ɓangaren Adawiya kam tana shiga ɗakin Yah Ab sai ta iske yana barci, ga wayarsa ajiye saman ƙirjinsa kamar wanda ya rungume mace. Harta juya zata fita, sai kuma zuciyarta ta ƙwaɗauta mata wani abu daban. Dawowa tayi da baya a hankali ta ɗauka wayar, kasancewar ta jima da sanin password ɗinsa sai batasha wani wahalar buɗewa ba. Gabanta yay bala'in faɗuwa saboda cin karo da hoton Nu'aymah da tayi, ta kafe hoton da idanunta da suka ciko da ƙwalla, sai kuma ta kalli Abdallah dake barcinsa hankali a kwance batare da yasan tanai ba. Harararsa tayi kamar idanunta zasu faɗo, mikuma ta tuna oho mata, saita ajiye wayar a inda ta ɗauka ta fito a ɗakin.
     Karo da taci da hajjo ta fito suna ɗan hira da maman Aaida yasata haɗiye damuwarta ta zauna tana gaisheta.

WASHE GARI

        Washe gari ya kama ranar salla, a kuma ranar Nu'aymah ta fito daga ittiqafi bayan sakkowa sallar idi. Duk da tayi ƴar rama sai gata ta ƙara haske saboda yanayin zafinsu da kuma zama cikin ac a koda yaushe. Tayi mamakin ganin Abdallah yazo ɗaukarta. Da farko taso taƙi binsa, amma ganin rana zatayi saboda yau zasu wuce sai ta haƙura ta bisa.
      Motar tayi shiru babu mai magana a cikinsu har suka isa ƙofar gidansa. Tana ƙoƙarin buɗe ƙofar yay saurin saka lock. Juyowa tai tana kallonsa fuska a ɗaure, shima sai ya ɗaure tasan, batare da ya kalleta ba yace, “Inason muyi magana da ke a yau”.
    Kamar bazata tanka masaba, sai kuma tace, “Yah Ab maganar mi? Dan ALLAH ka cire komai a ranka kamar yanda na cire nima, bana buƙatar wata sabuwar fitina dan girman ALLAH”.
        Cikin zafin rai yace, “Saboda kin samu wanda ya fini? Nu'aymah minai miki ne a rayuwa har kika zaɓi sakamin da waɗanan abubuwan? Mina rasa irin na sauran maza ne.....?”
      “Baka rasa komaiba Yah Ab, sai dai ka sani mu wannan itace ƙaddarar mu, UBANGIJI kuma shine yasan hikimar dake cikin yin hakan. ALLAH shine shaidata ban gujeka ba, ban kuma daina sonka ba. Sai dai wata katanga mai tsauri tariga da tayi gicci a tsakanin ƙaddarar mu. A ganina kuma babu amfanin maida yanda akayi domin bakin alƙalami ya riga da ya bushe.........”
        “Sai dai idan kece kika busar da shi Nu'aymah, idan har kin amince inason a wannan karon mu cika burinmu na mallakar juna, na yadda da kaifin wuƙar data datse zaren ƙaddarar mu a wancan karon, sai dai a yanzu na sake ɗaura ɗammarar ɗaure zaren domin mu zama abu guda kamar yanda mukai fata”.
     Murmushi mai ciwo Nu'aymah tayi, ta gyara zama tana fuskantar Yah Ab, cikin raunin murya tace, “Yah Ab, karka manta a yanzu kai ɗin mijin Adawiya da Yusrah ne, tayaya kake tunanin zan yarda ka sake ƙulle wancan zaren ƙaddarar da kaifin wuƙa ya datsa ta. A ganina muyi haƙuri kawai da yanda yau tazo garemu, domin kuwa jiyanmu ta wuce sai labari. Muyi haƙurin fuskantar gobenmu sai muzama masu cin riba. Wlhy Yah Ab bazan taɓa iya haɗa zaman kishi da Adawiya da Yusrah b.........”
     Da sauri ya saka hannu ya rufe mata baki, cikin matuƙar ɓacin rai yace, “Hakan ya zamemiki dole kuwa Nu'aymah, idan kuma kikace zakimin taurin kai, wlhy a yanzu sai kunbar ƙasarnan da Adawiya tare da takardar sakinta ɗai-ɗai har uku kuwa”. Yana gama faɗar haka ya cire lock ɗin motar tare da ficewa a fusace.
           Nu'aymah da tun farkon fara maganarsa akan su Adawiya ta ɗaura hannu a ƙirji da faɗin, “Na shiga uku ni Zainab! Yah Ab mi kake faɗi haka?”. Bai saurareta ba ya shige gida, da sauri itama ta buɗe motar ta fito ta bisa da ɗan gudu tamkar zata faɗi.

          Adawiya dake a ƙwance bayan motar tai saurin cire hannunta data toshe baki, dan daƙyar tai control ɗin kanta lokacin da Abdallah ya furta zai sakesu inhar Nu'aymah bata amince da buƙatarsa ba. Motar ta buɗe ta fito itama da sauri tana faɗin, ‘Tabɗi jan, ashe lokacin yin yaƙin duniya na uku ya gabato kenan, lallai yanzune za'a fara wasan na gaske wlhy’. Ta ƙare maganar hawaye masu zafi na gangarowa a kumatunta.
    Tun lokacin da taji Abdallah na sanarma Hajjo shine zaije ɗaukar Nu'aymah bayan an idar da sallar idi ta ƙudiri aniyar binsa a ɓoye. Dan haka kawai taji a ranta akwai manufa a zuwa ɗaukar, dan ta gama fahimtar take-taken Abdallah tun lokacin dasu Nu'aymah suka zo ƙasar. Shinefa ta lallaɓa taje ta shige motar ta ɓoye sannan ya samama hajjo inda zatayi sallar idi a massalacin, shi kuma batare dayin wani tunani ba yana zuwa yaja motar ya wuce. Kuma harya ɗakko Nu'aymah hankalinsa bai kai akan Adawiya dake lafe a ciki ba. wadda ko sallan idi ita batayi ba.

        Tana shigowa cikin gidan duk a falo ta iskesu har Nu'  Abdallahn. Duk suka bita da kallon mamaki dan sunta nemanta bayan idar da salla basu gantaba, shine Ahmad yace suyi tahowarsu tunda ita ɗin ƴar garice ai. 
      “Ke kuma dama ba gidan kika dawo ba?”.
Abdallah ya faɗa cikin kaushin murya dan har yanzu ransa a ɓace yake. Kamar bazata tanka masa ba, dan ranta a bala'in cinkushe yake, ji take kamar ta burmama Nu'aymah wuƙa ta mutu kowama ya huta. Amma komi ta tuna oho mata, sai tai kalar tausayi tana haɗiye ƙududun daya tokare mata maƙoshi. “Eh na biya nan maƙwafta wajen Umm-Farukh, dama wasu kayane mukai da ita zan amsarma su Aymah to kuma ma dai anyi rashin sa'a basu isoba, dama daga Mexico ake kawo matasu”.
       Ɗauke kansa yay bai tanka ba, sai Ahmad ne da Hajjo sukai magana. Nu'aymah da tasha jinin jikinta akan yanda Adawiya ke magana ma bata tanka ba, sai dai a ƙasan ranta bata yarda da itaba sam.

★★★

      Duk yanda Abdallah yaso sake keɓewa da Nu'aymah dan su sake cimma matsaya akan zancensu taƙi basa dama har suka wuce Nigeria bayan awanni huɗu da sakkowa idi, dan kobi takan bikin sallar da ƴan saudia ke gudanarwa basuyi ba, dama Adawiya ƙin dafa komai tai saboda takaici. Abdallah zaiyi magana kuma Hajjo ta hanashi, acewarta su da zasu tafi yanzu mizasuyi da wani abincin salla bayan nasu nacan na jiransu a ƙasarsu.
         
      Sun sami ƙyaƙyƙyawar tarba kuwa daga su baba malam, dan ana sakkowa daga sallar juma'a (da yake ranar sallar ta kama juma'a ne) suka nufi airport domin tarbar mahaifiyarsu tamkar yanda suka saba. Babu kunya Nu'aymah taje ta rungume Baba malam, dan harga ALLAH tayi kewarsa shi da Umm da Muhammad. Kai dama ƴan gidan duka.
     Fuskar baba malam ɗauke da murmushi ya shafa kan ƴar tasa yana faɗin, “Ja'ira, duk ga iyayenku cike da wuri bakiga kowaba sai ni ko?”. Fuskar Nu'aymah washeda murmushi tace, “Abba nayi kewarka ne sosai, kuma ALLAH kullum sai nayi mafarkinka kai da Ummuna”.
     Baice da ita komaiba sai murmushi kawai daya sakeyi, dan shi mutum ne mai tsananin kawaici ga yaransa, yanama ƴan uwansa kara sosai. Dan haka suma a kullum suke ƙoƙarin koyi da ɗabi'unsa akan nasu ƴaƴan.
          Bayan Nu'aymah ta ƙarasa ta gaida sauran iyayenta uku suma cike da girmamawa. Suma suka amsa mata da tsananin kulawa sai suka runguɗa gaban mahaifiyarsu suna jera mata sannu da zuwa. Cike da kulawa da kewa take dubansu, fuskarta faɗaɗe da murmushi. Ta kama hannun Abba Musbahu tana faɗin, “Wayyo autana duk ka faɗa, ko azuminne?”.
     Dariya Nu'aymah da Ahmad sukayi, Malam ƙarami da Omar na tayasu kuwa. Hakama su baba malam sunata murmushin akan diramar autan nasu da mahaifiyarsu.

            Lokacin da suka iso gidan nasu sun iskeshi da dangi da yaransu na ma'auri duk anzo tarbar hajjo da kuma yawon salla. Inda gidan ke wadace da tarin abinci kala-kala da kowanne sashe ya tanada. An gyarama hajjo sashenta tsaf an kuma kai mata abinci daga kowanne sashe an ajiye mata. (Dama haka suke mata).
            Motocin na gama tsayawa Nu'aymah bata tsaya sauraren masu tarar tasu ba ta shige sashensu da gudu tana ƙwalama Umm kira. Da sauri Umm dake ƙoƙarin fitowa taja baya dan kaɗan ya rage suci karo da Nu'aymah.
        Faɗawa jikinta tai ta ƙanƙameta tana faɗin, “Wayyo Ummuna, nayi kewarki wlhy”. Umm dake murmushi ta amshi ɗiyar tata da hannu biyu ta rungumeta itama, sai da ta tabbatar sunji ɗumin juna kowa na sauke ajiyar zuciya kafin ta ɗagota da ga jikin nata. “Nu'aymah! Yaushe ne zakiyi hankali kisan kin girma ne? Bakisan yanzu ba da bane, shekararki goma sha bakwai fa kina shirin shiga sha taƙwas”.
     Cike da shagwaɓa ta saka kanta a kafaɗar Umm tana faɗin, “Umm ni indai ina gabanki wlhy jaririyace sabuwar haihuwa, nayi kewarki ne sanyin idaniyata. Ina Muhammad yake?”.
          “Nayi cinikinsa” Umm ta bata amsa tana janyeta daga jikinta ta fice domin shiga tawagar masu tarbar surukar tasu.        
      Baki Nu'aymah ta tura gaba, ta ɗaga ƙafa zata biyo Umm tajiyo muryar Muhammad a bayanta yana faɗin, “Marhaban biki Aunty na”. Saurin juyowa tai garesa, sai kuma ta nufe da sauri kamar yanda yake nufota suka rungume juna cike da kewa da ɗoki.

        Haka gidan ya kasance a hargitse ranar saboda shagalin bikin salla, Nu'aymah bataje ko inaba, dan bayan tayi salla taɗanci abinci sai ta shiga ta gaida kowa na gidan, kafin ta koma ɗakin Umm tai kwanciyarta, duk wanda yazo musu yawo a ranar bai samu ganinta ba, dan ta ɓoye kanta a cewarta saita huce gajiyarta da ƙyau tunda dai tasan zasu zaga gari yawon sallar gobe idan ALLAH ya kaimu ai.

___________

           Kiran sallar la'asar ne ya tada Nu'aymah dake kwasar barcin gajiya. Ta miƙe da ƙyar dan jikinta ko ina ciwo yake faman mata. Wanka ta farayi, ta saka ɗaya daga cikin kayan sallarta. Tayi ƙyau sosai cikin shaddarta ruwan hoda, taji aikin stones da yay ƙyau sosai. Kayan sun mata ɗas ajiki, tare da sake fiddo haskenta saboda ƴar ramar da tayi.
         Lokacin data fito Umm kanta sai da tace, “Masha ALLAH”. Hakama ƴaƴan yayun Umm ɗin su uku da sukazo mata yawon salla duk sai da suka yaba ƙyawun da Nu'aymahr tayi. Ta zauna fuskarta da murmushi tana gaidasu cike da girmamawa. Dan dukansu matan aurene, kuma duk suna da yaransu. Cike da kulawa suke amsa mata, kowanne na mata ƙorafin rashin zuminci, musamman babbarsu.
       Nu'aymah tace, “Lah Aunty Zulfah wlhy ba rashin son zuminci bane, ni abinda yasa banason zuwa gidanki wannan ƙanin mijin naki takuramin yake wlhy. ya cika shegen kallo kamar ɗan daudu”.
      Dariya suka sanya gaba ɗayansu, aunty Zulfah tace, “To kwantar da hankalinki, indai Fa'iz nema aurensa zaiyi, tunda ke kinƙi. Kinga nima dakin yarda ai dana samu ƴar uwata kusa dani ko.......”
      Da sauri Nu'aymah ta katseta da faɗin, “Taf, aunty daina faɗa dan ALLAH, wlhy ya cika iyayi, banason namiji yayta gwalli kamar wani mace, shiba ɗan daudu ba shiba mata maza ba”.
           “Amma Nu'aymah baki da kirki wlhy, kin gama ɗebema ƙanin mijin aunty Zulfah albarka gaba ɗaya”. Aunty Rafi'a ta ta faɗa tana dariya. Ita kanta Nu'aymah dariyar takeyi, Umm dai batace musu komaiba. duk da kuwa tana zaune tana jinsu.
       Sai da suka tsagaita da dariyarne Nu'aymah ta miƙe tana faɗin, “Umm yunwa nakeji, ALLAH yasa akwai waina dai?”.
         “Kin kuwa makaro, dan su Basira na ɗeboma ita gaba ɗaya, kinsan zakici wainar kikaƙi ɗiba ki ajiye?”. Kamar Nu'aymah zatai kuka tace, “Kai Umm! ALLAH yanzu kin daina sona, amma yanzu duk wainar dana gani ace ta ƙare? Su su aunty Basiran miyasa basu zauna sunci a sashen Addah b.......”
       Harar da Umm take jefo matane ya sakata yin shiru, dan su Basiran ƙannen Adda ne. “ALLAH ya shiryeki to, to ance miki sune kaɗai suka cinye. Ga yayunki nan suma duk ita sukaci, sannan Abbanku da yay baƙo duk da baya a gidan shima ita yace akai musu kafin ya iso gidan”.
         Komawa tai ta zauna kamar zatai kuka, su Aunty Zulfah nata tsokanarta wai ta amshema Muhammad guri tana shagwaɓa bayan shine auta.
     Umm tasan yanda Nu'aymah keda jarabar son waina, dan haka ta dubeta sau ɗaya ta ɗauke kanta tana faɗin, “ki wuce sashen hajjo idan bata ƙareba”. Aiko zumbur ta miƙe, a ranta tana fatan ALLAH yasa ta samo.
      Duk da takalman data gani na maza a ƙofar falon na hajjo kusan ƙafa biyar bata damu ba, sallama tayi kawai, kafimma su gama amsa mata ta shige dan duk zatonta yayunsune a ciki, tunda tasan duk suna gidan. A shagwaɓe ta buɗe baki zatai magana. sai dai cin karo da fuskar da batai zato ko tsammanin gani ba ta sata waro manyan fararen idanunta waje cike da al'ajabi.
      Yoohan dake zaune shima cikin Suit ruwan babypink kallon nata yake cike da mamaki, a ransa faɗi yake, ‘Dama yarinyarnan ba'a cikin Orphanage ɗincan take ba? No wander ɗazun baiga komai kama da itaba a cikin yaran’. A fili kuwa sai ya ɗauke kansa cike da shan ƙamshi kamarma irin bai ganta ba ɗin nan shi.......
        “Lafiya wai kika tsayama mutane ƙerere a kai Zainabu?”. Maganar Hajjo ta katse mata tunaninta. Juyawa tai inda hajjon take, har yanzu mamakin ganin Yoohan ɗin bai barta ba, “Hajjo wannan mutumin kuma ina kika sanshi?”.
     “Wa ɗin?”. Cewar Hajjo tana kallon inda Hamza Manager, Yoohan dasu baba ƙarami ke zaune.
        Maimakon Nu'aymah tai magana sai ta je ta zauna kusa da hajjon, matsar da bakinta tai dai-dai kunnen Hajjo tace, “Hajjo arne ne fa wlhy”. “Aina sani” Hajjo ta bata amsa cikin nuna halin ko in kula. 
     Sosai mamaki ya kume Nu'aymah, tai tsai tana kallon Hajjon, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta sake maida dubanta ga Yoohan daya maida dukan hankalinsa kan wayarsa.
       “Wai lafiyarki kuwa? Kina ganin mutane baki iya gaisuwa bane? Sai shegen kallo malama”. Yah Ahmad ya faɗa idonsa akan Nu'aymah. Sai da taɗan tura baki kafin ta duba Hamza manager data wuce da dukanin imaninsa tace, “Ina yini”. Cikin narkakkiyar murya da shi kansa baisan ta fitaba ya amsa mata da “Lafiya lau ƙanwarmu, kinyi salla lafiya?”. Kai ta gyaɗa masa kawai, dan duk sai taji kuma ta takura da kallon da yake mata. Ganin bata gaida Yoohan ba ya saka Malam ƙarami hararta, yace, “Shi kuma fa?”.
       Yanzun kam baki ta kumbura sosai, ta kalli Yoohan ɗin da yay tamkar baisan da zaman kowaba a falon tace, “Good evening.
          Sarai yajita, amma sai ya share baiko motsaba. Sai da Hamza ya ɗan taɓasa da faɗa masa ana gaishesa sannan ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke a cikin nata. Karan farko da sukaima juna kallon ido cikin ido. Kusan lokaci guda kowanne gabansa ya faɗi. Nu'aymah tai saurin fara janye nata da ƙoƙarin juyawa daga saitinsa.
      Shima ɗan lumshe nasa yay ya buɗe (dan hakan ya zame masa kamar wata ɗabi'a) cikin muryarsa mai amo ɗin nan yace, “Kina lafiya?”.
       A mugun razane Nu'aymah ta sake waigowa inda yake, har taune harshenta take wajen faɗin, “What?! Dama kanajin hausa?”. 
      Yanda tayi tambayar sai da ya saka su hajjo yin dariya. Hakan sai ya ƙarama Nu'aymah takaici, musamman ganin yanda Yoohan ɗin ya wani yamutse fuska, tare da miƙewa saboda wayarsa da aka kira, dama shi baiyi dariyarba. Sai da yazo daf da ita a hankali yace, “Yeyye girl”. 
       Kafin wani ya sake magana a cikinsu, ko ita ta bashi amsa Abban su Adawiya da Abban Musbahu suka shigo falon da sallama. Shi kuma ya fice yana amsa wayar.
       Daurewa tai ta shiga gaishesu tana ɗan harar ƙofar da Yoohan yabi ya fice ta gefen ido, a ranta kuwa sai cewa take, ‘Oh ALLAH, amma dai gayen nan akwai munafurci, dama yanajin hausa amma duk sanda suka haɗu yake nuna mata bayaji, jibesa da wani shegen aski kamar kan zakara, sai kuwa yaga yeyye kafin yabar gidan nan yau’.
      Duk kallon harar Yoohan da take Manager yana kallonta ne ta gefen ido shima, sai da Abban Musbahu ya kira sunansa ne sannan ya maida hankalinsa garesa, a ransa yana mamakin yanda alamu suka nuna akwai sanayya tsakanin Yoohan da wannan Zuƙeƙiyar budurwar data gama tafiya da dukkan imaninsa a kallo ɗaya. 
        Ita kam Nu'aymah da batasan yanayi ba sai ta lallaɓa ta fice dan jitai tama fasa cin wainar, yau duk yanda za'ai sai taji dalilin shigowar wannan kahirin cikin gidansu, harma falon kakarsu...........✍

😜Kina ruwa Aymah😸.



______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/28, 3:14 PM] Queen Meenali👑: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta_*.


No. 26

..............Cike da jin haushin Yoohan Nu'aymah ta fito daga sashen hajjo. Hakan yayi dai-dai da shikuma Yoohan ɗin zai koma dan ya kammala wayar.
         Karo sukayi, goshin Nu'aymah ya bugu da sarƙar Cross ɗinsa. Da sauri tai baya saboda azaba. Shima bayan yaja kaɗan yana wani yamutsa fuska idonsa a kanta. Kasancewar Nu'aymah bata taka ɗan step ɗin ƙofar falon hajjon dai-dai ba lokacin da tai baya sai ta sake yo gaba zata faɗi.
           Yoohan ya tabbatar idan ya barta ta faɗi zataji mugun ciwo ne, dan haka da saurinsa kuwa ya tarota ta faɗo jikinsa. Sai kuma ta firgice saboda tsoratar da tai najinta kwance a ƙirjinsa, ta wage baki zata tsala ihu yay azamar ɗora lallausan tafin hannunsa saman bakin nata ya rufe ruf.
         Cikin tashin hankali Nu'aymah ta fara mutsu-mutsun kwatar kanta, jikinta sai rawa ya ke yi. Shikuma yaƙi sakinta dan ya tabbatar yana sakin nata faɗuwar daya gudar mata a farko sai tayi wadda ta fita a yanzu, cike dajin haushi ya daka mata tsawa, dan jiyayma kamar ya saketa ta faɗin ma yaga ƙarshen rashin kunya.
          Duk da tsawan da yay mata bata nutsuba, sai ma cigaba dayin mutsu-mutsunta nason ƙwacewa takeyi, tuni hawaye kuwa sun fara bimata kumatu, dan a rayuwarta da hankalin kanta kuma hakan bai taɓa faruwa da itaba. Ko hannu bata yarda samarin gidansu wani ya riƙe mata balle akai ga runguma irin haka. Sai gata yau kwance a ƙirjin ƙaton kahiri, da ko yayunta basu taɓa aikata haka a gareta ba. gashi ya rufe mata baki babu damar magana. Kuma ƙarfi ba ɗaya ba.........
       Jin ya manneta da bango sai tashin hankalinta ya ƙaru, dan ta zata wani abun kuma zai aikata mata, ta kasa nutsuwa ta fahimci taimakonta yayi. hannayenta duka biyu ta saka tare da dukan ƙarfinta tana ƙoƙarin ture masa hannunsa daya rufe mata baki da shi. Ko gezau baiyiba, saima wani shegen kallo da yake binta da shi tamkar ya manta a inda suke, ga fuskarsa a matuƙar ɗaure balle kai tunanin da biyu yay hakan, sai dai shima zuciyarsa wani irin harbawa take da sauri-sauri.
      “Ouch!!” ya faɗa da sauri yana janye hannunsa da ya toshe mata baki da shi, dan kuwa daddagewa tayi ta gasa masa cizo a tafin hannun. Yaja da baya yana yarfe hannun nasa da faɗin, “Are you mad?!”.
       Nu'aymah da har yanzu jikinta bai bar rawa ba ta galla masa harara tana share hawayenta. “Eh banda shi. ALLAH ya isana kuma, wlhy ka sake gigin taɓani saina fasa maka kai, danni ba ƴar iska baceba!”.
      “Silly girl! Waye ɗan iskan?” ya faɗa da turanci kamar yanda ta faɗa itama yana galla mata harara tare da cafkota, iya ƙarfinsa ya fisgota tayo baya ta sake faɗawa jikinsa. Mannata jikin bangon ya sakeyi, ya toshe mata baki da ɗayan hannunsa. kafin ya ɗago ɗayan hannun ya kalli inda ta cije sa, yamutse fuska yay ganin yanda shatin haƙoranta suka fito masa, ba wajen data ciza ɗin kawaiba, tafin hannun gaba ɗaya yayi jaa abinka da ba'asan wahala ba...
       Nu'aymah ta rikice iyakar rikicewa yanzun kam, dan ta yarda a ranta da gaske Yoohan son cutar da ita yake. Ƙilama abinda ya kawosa gidan kenan. Sake kaima ɗayan hannun cizo tayi. Yayi saurin janyewa ya maye gurbin hannun nasa da bakinsa. Shi kansa baisan yaya akai hakan ta faru ba, ya tsinci kansa ne kawai da haɗe bakin nasa da nata ya shiga kissing ɗinta.
       Yanda take kuka da turesa da yakushinsa ne ya sashi janyewa daga gareta da sauri. Duk da halin daya ganta na ƙololuwar shiga ruɗani da tashin hankali hakan bai hanashi kallonta ba, tare da zazzaro mata manyan idanunsa da suka sauya kala zuwa ja.
      Harga ALLAH Nu'aymah ta tsorata yau kam, dan ta tabbatar tunda har ya iya mata wannan abun a cikin gidansu to lallai zai mata duk abinda yazo masa rai. Tunda tasan su basu ɗauki keta mutuncin mace a komai ba. Amma tsabar ƙarfin hali irin na mutuniyar taku ana sakar mata baki sai ko ta murguɗa masa bakin da sake zuba masa harara. iya ƙarfinta ta turashi dan har yanzun yana manne da ita ne a bangon, amma ko gezau baiyiba balle tasa ran samun hanyar kuɓuta. Waige-waige take gudun kar wani ya fito ya gansu a haka, tana kuma hawaye, cike da tsiwa cikin harshen turancin data san yafi fahimta sosai tace,
        *_“Dama ku babu abinda kuka iya sai son taɓa mata da ɓata musu rayuwa, ALLAH ya isana ɗan iska kawai. shiyyasa wanda baya salla an haramta ma sa jin daɗin duniya. Sannan zai gamu da wahalhalu a wurare guda huɗu: A nan duniya, da ranar mutuwa, da cikin ƙabari da ranar hisabi. A duniya ana ɗebe ma sa albarka, a cire ma sa kwarjini daga fuska, a sa ma jama'a ƙyamar sa. A ranar mutuwa zai mutu da wulaƙanci da yunwa da ƙishirwa. A cikin kabari ALLAH zai ƙuntata ma sa, a hura ma sa wuta a cikin sa, a aika ma sa kumurci a tsakanin fatar jikinsa da namansa. A ranar hisabi za a baƙanta fuskarsa, a yi masa hisabi dalla-dalla, sannan a haɗa shi da zabaniyawa da za su wurga shi cikin wuta. Lallai, sallah ita ce ginshiƙin addini. Idan kaƙi gaskiya zaka faɗa ɓata. Idan ba ka ji nasiha ba, zaka yi da-na-sani. Wanda baiji bari ba ya ji hoho!......”_*
     Ta ƙare maganar da sake turashi da ƙarfi. Yanzun kam da kansa ma ya matsa ya bata hanya, da gudu tabar wajen kuwa tana kukanta har yanzun.
         Cike da takaicin kansa ya rumtse idanusa da ƙarfi, tare da ɗora hannunsa a goshi yana murzawa da abaton “Oh lord!, mina aikata?!”.

★★★★

         A wani ɗan lungun sashensu Nu'aymah ta maƙale tana sauke tagwayen shashshekar kuka, har zuwa yanzu jikinta baibar rawa ba, sai faman waige-waige take tamjar ance mata Yoohan ɗin biyota yayi.
       Ta ƙanƙame jikinta lokacin da abinda ya farun ya sake dawo mata a rai, yanda gashin jikinta ke wani mimmiƙewa zai tabbatar maka da tsigar jikinta tashi takeyi.
     Da sauri ta saka hannu tana share hawayenta saboda jin tahowar mutum. ‘Na shiga uku ya biyo ni’ ta faɗa a fili zuciyarta na wani irin zallo tamkar zata faso ƙirjinta ta fito........
       “Nu'aymah lafiya na ganki anan? Mi kikeyi ne haka?”. 
      Duk da ganin Aunty Kubrah ce ba Yoohan ɗinba hakan bai hana Nu'aymah sake rikicewa ba, ta shiga inda-inda jikinta na tsuma. “A..Aunty babu ko.. Komai”.
       Kubrah data kafeta da ido taɗan murmusa, sai kuma ta juya bayanta tana faɗin, “Ki kwantar da hankalinki ai ba biyoki yayi ba, na tabbatar kuma babu wanda ya ganku a gidan nan”.
        Wani muguwar faɗuwa gaban Nu'aymah ya sakeyi daboda jin furicin Aunty Kubrah. Cikin rawar harshe Nu'aymah tace, “Aunty Kubrah wlhy ni.......”
       “Kinga kwantar da hankalinki Nu'aymah babu maiji, indai nice ko Hajarah baza taji wannan zancenba balle wani a gidan nan. Amma inason ki faɗamin gaskiya, yaushe kuka fara wannan abun ke da shi?”.
       “Innalillahi! Aunty wlhy bamu taɓa yiba, yau ma na rantse shin......”
       “Kinga ya isa. Share waɗan nan hawayen idan baso kike ki tonama kanki asiri ba da kanki”.
       Nu'aymah duk ta sake rikicewa, tama rasa fahimtar inda maganganun Aunty Kubrah suka dosa saboda tashin hankali. Duk da ta share hawayen sun gaza tsayawa. Hannunta Kubrah ta kama har lokacin fuskarta da murmushin da Nu'aymah ta gaza fahimtar na minene. “Kinga muje sashenmu, idan ba hakaba Umm sai ta fahimci abinda ya faru, ko kinfi buƙatar hakan?”.
     Da sauri Nu'aymah ta shiga girgiza mata kai, “A'a wlhy Aunty, banason Umm ta sani dan zata kasheni, dan ALLAH karki faɗa mata, wlhy kuskurene ba kuma laifina bane ba, na rantse da ALLAH Aunty ban taɓa yiba, ko hannuna Namiji bai taɓa riƙewa ba”. Ta ƙare maganar da rushewa da wani irin kuka maiban tausayi.
     Komai Kubrah bata sake cewaba ta kama hannun Nu'aymah suka nufi sashensu. Ta ƙofar baya tabi da ita, dan ƙannen Addah su Aunty Basira suna falo zaune dasu Addah suna hira. Batare data bari sun gansu ba ta shige da Nu'aymah bedroom ɗinsu. Zaunar da ita tayi sannan itama ta zauna a kusa da ita. Har lokacin kuma Nu'aymah kuka takeyi, zuciyarta na ƙarajin tsanar Yoohan matuƙa........
         “Ko shine Ameer ɗin Saurayinki?”. 
     Da sauri Nu'aymah ta ɗago tana kallon Kubrah, sai kuma ta shiga girgiza mata kai, “Aunty dan ALLAH ki yarda dani, wlhy Ameer ba saurayina bane. Wannan kuma bama musulmi bane ba, baƙone yau na fara ganinsa”.
        Haɗe fusaka Kubrah tayi tamau tana kallon Nu'aymah ɗin. “Karkimin ƙarya Nu'aymah, inba hakaba wlhy na fasa rufa miki asirin, a yau da daddare zan sanarma Hajjo da Baba malam da Umm komai. Ki faɗamin tun yaushe kuke tare? Sau nawa kuma yay amfani da ke?”.
       Duk sai Nu'aymah ta sake daburcewa, dan tama rasa wace amsa zata bama Aunty Kubrah, gaba ɗaya ta kasa fahimtar manufar Kubrah.......
     Kamar Kubrah tasan tunanun da Nu'aymahn keyi, sai ta sassauta fuskarta tana gyara zama. Ta ɗan rage kaushin muryarta kuma ta koma magana cikin lallashi. “Nu'aymah kinsan dai yaya nake a gareki, duk abinda zan iya gani gasu Hajarah raina ya ɓaci idan nagani daga gareki dolene naji zafi, ɗiyar ƴar uwar mahaifiyata ce kuma ke, dan kuwa Umm tamkar ƴar uwar Adda take, tamafi min wasu ƴan uwan Addan. Yanzu Nu'aymah da wani ya ganki a gidannan ƙaton banza yana lalubeki mikike tunanin zai faru?, idan ma iskancin zakiyi ai gara kuyisa can a waje wani bai gankiba ko, amma a cikin gidanku? Babban gida mai daraja irin wannan? Wane kallo kikeson aima iyayenki maza damu kanmu Nu'aymah?”.
          “Dan ALLAH kiyi haƙuri Aunty Kubrah, wlhy bazan sakeba wannan ma ƙaddara ce da kuma kuskure”.
      “ALLAH yasa hakane to”. Kubrah ta faɗa tana wani ɗauke fuska da ƙyaɓe baki.
             Nu'aymah na kuka tace, “Wlhy da gaske nake Aunty. Dan ALLAH ki yarda dani”.
         “Nu'aymah idan ban yarda da ke ba minene amfanin musawar to?, tunda idan kunbar gabanmu ALLAH kaɗai yasan mi kuke aikatawa, masu iya magana fa kance rana dubu ta barawo, ɗaya tak ta mai kaya. Yau ɗinma ai bakiyi tunanin zan ganku ba”.
          Ƙasa Nu'aymah ta zube tana kuka tamkar ranta zai fita, ‘Ita mizata faɗama Aunty Kubrah ta fahimceta ne wai? Wane rantsuwa zatai mata danta yarda ba da yardarta kafirin nan ya aikata hakanba a gareta?’.
       Sai da taci kuka sosai, Kubrah na zaune na kallonta kafin ta ɗagota ta rungumeta, “Kukan ya isa haka, aina yarda ba laifinki bane. Na miki hakane kawai dan kisan baki dai-dai ba”.
         “Na gode da kika fahimceni Aunty, kuma namiki alƙawarin hakan bazata sake faruwa ba insha ALLAHU”.
     Ɗagota Kubrah tayi ta share mata hawayen tana murmushi, “Shikenan naji, kuma na miki alƙawarin babu maijin zancen nan a gidan nan kinji, kije bayi ki wanke fuskarki kizo ki sake shafa hoda dan karma wani ya zargi wani abun kuma kinji ko. Ki kuma saki jikinki inba hakaba Umm zata gane, kuma kinsan halinta. Zatabi duk hanyar data dace dan tasan gaskiyar abinda ya sakaki kukan”.
           “Insha ALLAHU bazan bari ta gane ba Aunty, bara ma na wanke”. Ta ƙare maganar tana miƙewa da sauri ta nufi bayin su dake cikin ɗakin. Tana wanke fuska tana kallon bakinta a mirror. Wasu hawayen sai sake ƙoƙarin zubowa suke tana dannesu da ƙyar. A fili tace, ‘Na tsaneka mugu ɗan iska mai suffar samudawa, bazan taɓa yafe makaba wlhy”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
     Taja kusan mintuna biyu tana kukan kafin ta wanke fuskar ta fito. Fitowar tata tayi dai-dai da shigowar Hajarah da wayar Kubrah a hannu. Da mamaki Hajarah take kallon Nu'aymahn, dan ita dai bataga shigowarta sashen ba.
       “Nu'aymah yaushe kika shigo ne? Gashi kamar kinyi kuka?”. Da sauri Nu'aymah ta girgiza mata kai, sai kuma ta kalli Inda tabar Aunty Kubrah dan tana zaune a wajen, tana jinsu kuma amma ko kallonsu taƙi tayi balle ta nuna alamar tasan mi sukeyi ma. “Babu komai Aunty Hajarah, kaina ne kawai ke ɗan ciwo”.
      Ƙarasawa inda Nu'aymahn take Hajarahn tayi, ta ɗago fuskarta cike da nazari........
       “Wai miye hakane? Tace miki babu komai kanta ke mata ciwo miye na damunta ne kuma?”.
       Baya Hajarahn taja kanta a ƙasa tace, “Kiyi haƙuri Aunty Kubrah, ga wayarki dama Alhaji ne ya kiraki”. Ta matsa inda take cike da girmamawa ta bata wayar.
      Tana amsa ta nuna mata ƙofa da ido. Da sauri kuwa Hajarahn ta fice. 
     Kubrah ta maida dubanta ga Nu'aymah dake a tsaye har yanzu. “K kuma ki bada himmar tonama kanki asiri kinji ko, ki wuce ki shafa hodan, idan kuma sokike wani ya sake shigowa to”.
        Gaban Mirror Nu'aymah ta ƙarasa. Ta shafa mai da hoda harda kwalli, duk da dai hakan fuskar dai babu walwala.
     Amma sai Kubrah batace mata komaiba suka fito falo inda su Hajarah ke hira tare. Zama tayi kamar yanda Addah dake kallonta ta Umarceta. Su Aunty Basira nata tsokanarta da faɗin ina tsarabarsu ne?.
       Tun tana noƙewa dai harta ɗan ringa amsasu, amma ta gaza sakin jikinta yanda ya kamata sosai. Duk motsinta Hajarah da Addah na lura da shi, sai dai babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu. 
      

___________________________
    
          A ɓangaren Yoohan kuwa duk yanda su Hajjo sukaso ya zauna jiran dawowar baba malam ya gaza hakan. Yace musu zai dawo da safe yanzu yanada wani uziri.
      Badan hajjo taso ba ta barshi. har ƙofar gida su Yah Ahmad sukai masu rakiyya shi da Manager. Inda su Solomon ke jiransa a mota. Kasancewar basu iske baba malam ba yasa bai shiga dasu cikiba. Yace su jirashi a waje. Dan da ƙyarma Su Ahmad suka lallaɓashi ya shiga cikin gidan. Da farko ya ce zai koma tunda baba malam ya fita. Dan dama yaso yin surprise ɗinsa ne shiyyasa bai sanar masa shigowarsa kanon ba ma.
         Har drivern sa ya tada mota ya tsaidashi. Kuɗi ya ciro a cikin jakarsa rafa guda na ɗari biyar sabbi ƙal ya miƙama malam ƙarami yana faɗin, “Please a bama yarinyar nan barka da salla. Na manta ban bata ba”.
       Malam ƙarami da ya fahimci Nu'aymah yake nufi sai yay murmushi. bai musa ba ya amsa yay masa godiya, dan suma daya basu sukaƙi amsa a ciki ɓata rai yayi, wai basu ɗaukesa ɗan uwansu ba. Hakanne ya sakasu amsa tunda yace barka da salla ce.
         Duk abinda ke faruwa Solomon na saurarensu. Dama cike yake da haushin sake zuwa wannan gidan. Ya kuma ɗauki alwashin suna komawa wannan karon sai ya sanarma madam Chioma. Dan tsaf ya fahimci waɗan nan mutanen zasu iya jan hankalin Ogan nasu tsaf, musamman yanda suke masa hidima kamar wani sarki. Yanzu haka a gabansa aka saka babbar leda a booth wai kayan barka da salla ne aka bama Yoohan ɗin a cikin gida. Ya cije bakinsa yana satar kallon Yoohan daya kwantar da kansa jikin kujera ya lumshe idanu kamar mai barci ta mirror.
    
      Babu abinda kema Yoohan kai kawo a zuciya da ruhi sai kalaman Nu'aymah. Kalaman sunyi masifar tasiri a ransa fiye da zaton mai karatu. Sai faman tisasu yake dalla-dalla kamar mai bitar karatu. Duk da ac dake aiki a motar bai hana zufa tsatstsafo masa a goshi ba. Mafarkin da yayi shekaran jiya da baba malam ya kuma sake maimaita shi yau da safe ya shiga tariyowa shima.        
       ya sauke wani irin nannauyan numfashi yana sake tariyo mafarkin nasa da yayi a karo na biyu kenan,
        *Ya kanga kansa a mafarkin a gaban wani kogo ƙaton gaske, cikinsa akwai wani irin wuta dake ci mai ban tsoro, dan duk iya hasashensa ya kasa kamanta ƙarfin wutar da zafinta a zahiri. Aduk lokacin da yake a gaban wannan kogon dake zuwa masa a mafarki, ya kan tsinci kansa cikin matsanancin mawuyacin hali da ruɗu, sai dai kuma abin mamaki sai ya ga baba malam acan gefensa cikin shiga ta kamala, a wasu irin korayen ciyayi masu bada ni'imtaccen yanayi yana masa murmushi da miƙa masa littafin nan na musulmai (Al-Qur'ani), yakan ringa ce masa_______* 
        *_“Yoohan wannan shine zancen ALLAH, littafi dake ƙunshe da kowane irin sirri, littafin da aka aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) da shi. kanada sauran daman riƙo dashi domin ka samu tsira daga wannan narkon azabar dake gabanka. Kazo gareni, zan nuna maka hanyar sanin UBANGIJINA kamar yanda ya aiko MANZONMU ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) a garemu ya nuna mana muma, ya kuma koyar damu. Ni Sooraj bin Hashim, na rantse maka da ALLAH, babu wani addini na gaskiya sai musulinci, babu wata hanya ƙyaƙyƙyawa sai ta bin UBANGIJI, babu wani abin taƙama da riƙo sai MANZON ALLAH. Inhar kabi ALLAH, kai koyi da koyarwar MANZON ALLAH, ka riƙe gaskiya da amana, ka tsare gangar jikinka daga saɓama ALLAH, ka nema dukiyarka ta hanyar halak, kaji tsoron zalintar mutane, ka kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ALLAH bazai jarabceka da shiga wannan taskar azabar dake a gabanka ba. Domin UBANGIJI ya tanadi gidaje guda biyu, WUTA DA ALJANNAH, ya kumayi alƙawarin cikasu da mutane. Dan haka Yayha kazo gareni, kazo ka karɓi kalmar LA'ILAHA ILLAH, MUHAMMADURRASULULLAH (S.A.W)._*
          A wancan ranar da yay wannan mafarki ya wayi garine a yanayin sanyin jiki, da tunane tunane kala-kala. Ya kuma yini zuciyarsa na rinjayarsa da amsa wannan kira. Sai dai daya tuna wani gagarumin al'amari sai yay azamar ƙwaɓar kansa harma da alƙawarin nisanta kansa da su baba malam ɗin. Dan yau ɗin nanma da ƙyar manager ya lallaɓa shi sukazo nan ɗin. duk da kuwa yana a cikin kanon yau kwanansa biyu kenan ma.

       Kafin su ƙarasa hotel ɗin daya sauka sosai ya tsinta kansa cikin ruɗanin kalaman Nu'aymah da mafarkinsa. Sai ɗunbin takaici da dana sanin abinda ya aikata ma yarinyar yakeyi, wanda sam ba halinsa bane yin hakan, amma yasan ita da duk wanda zai iya ji ko ganinsu a lokacin bazai taɓa yarda da shi ba. Ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa da ƙarfin tsiya, ƙirjinsa na sake masa zafi.
     Motocin na tsayawa baiko jira an buɗe masa ba ya buɗe da kansa ya fice. Daga Solomon har sauran guards ɗinsa tsaye kawai sukai suna kallonsa cike da mamaki da tsoron yanayin nasa. Da sauri Solomon yabi bayansa shima dan yasan ba lafiya ba dai. Gashi key ɗin ɗakin Yoohan ɗin yanama a hannunsa ne.
     Ɗan gudun da yayine ya sakashi cimmasa. Dan haka suka ƙarasa ƙofar ɗakin tare. Solomon ya buɗe masa tare da matsawa ya bashi hanya dan ya shiga. 
        Batare da yace masa komaiba ya shige, shi ma Solomon ɗin sai ya bisa yana faɗin, “Sir lafiya kuwa?”.
        Cak Yoohan ya tsaya da ga yunƙurin shiga Bedroom ɗin da ya keyi, batare da ya juyoba ya ɗagama Solomon ɗin hannu da masa alamar ya barsa.
      Da baya-baya Solomon ya rinƙa tafiya harya fice da ga ɗakin, yaja masa ƙofar a hankali gabansa na faɗuwa da yanayin ogan nasu.............✍

🤔🤔🚶🏻Tofa, Dr Yoohan yaya dai?🚶🏻



_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.



[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta_*.


No. 27

............Zubewa Yoohan yayi a saman gadon tare da saurin dafe kansa dake barazanar rabewa biyu, sai kuma ya ɗan naushi gadon da faɗin, “Noooo!!!”. Da ƙarfi kamar mai magana da wani.
    Tashi yay zaune zumbur yana huci, so yake abinda ya faru yabar ransa, amma tamkar ana ƙara kusanto masa da hotonsa ne a zuciya. Da ya rufe ido babu abinda yake gani sai yana kissing ɗin yarinyar da ko sunanta baima sani ba. Miƙewa yay daga gadon ya shiga toilet ɗin dake cikin ɗakin, ko takalman dake ƙafarsa bai cireba balle kuma kaya, ya ƙarasa gaban shower ya tsaya, tare da kai hannu ya murza makunnar da ƙarfi, tamkar itace tai masa laifi.
     Shaaa!!! Ruwa ya fara sauka masa bisa gyararren gashinsa yana gangarowa fuska. Lokacin da ya gangara cikin jikinsa ya wani saki sassanyar ajiyar zuwa tare da lumshe idanunsa ya dafe bangon da hannunsa duk biyu. A haka ruwan ya cigaba da sauka a kansa, kafin wani dogon lokaci ya gama jiƙewa sharkaf. Sai da yay kusan mintuna ashirin a haka sannan ya kashe shower ɗin yana sauke numfashi a jajjere, kafin ya ƙarasa saman toilet sit ya zauna yana mai riƙe kansa da hannu biyu....

_______________________

          Duk yanda Nu'aymah taso sakewa a sashen Addah ta kasa hakan. Gani take kamar kowa yasan abinda ya faru tsakaninta da Yoohan. Kamar an tsikareta ta miƙe daga zaunen da take kusa da Kubrah. Dukansu da kallo suka bita har suna rige-rigen tambayarta lafiya.
    Sai da taɗan saci kallon Addah da tai banza dasu kafin ta amsa musu cike da in-ina. “Um.....u.... Zanje su Aunty Zulfah na jirana”. Bata jira amsar su ba tai wuf ta nufi ficewa da ga falon tamkar zata kifa dan sauri. 
     Karo suka kusan ci da Malam ƙarami da ke shigowa. Tai saurin komawa da baya tana faɗin, “Yi haƙuri Yaya, bansan ka taho ba”.
     Murmushi ya mata da cewa, “Karki damu Aymah. Ashe dama kina nan naje nemanki wajen Umm”. Ɗan kallonsa tayi kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ya sake faɗaɗa murmushin sa, “Dama ba wani abu bane, baƙon da kika ganmu tare a sashen Hajjo ne ya bada barka da salla a baki. Shine naje kai miki na Iske baƙya nan. Amma na bama Umm ta ajiye miki”.
      Tunda ya ambaci baƙo gabanta ya sake tsananta faɗuwa. Ta tsaresa da manyan idanunta dake wani mar-mar na rashin gaskiya. Sai kuma ta ɗan juya ta kalli sashen da su Addah suke. Su dukansu hankalinsu na wajen. Sai taji hankalinta ya sake tashi. Tai saurin faɗin, “Ni banaso Yaya”.
    Kafin yayi magana ta fice da gudu daga falon. Shi malam ƙarami ma dariya abin nata ya bashi. Hakama su Hajarah. Dan haka suka shiga ƙyalƙyala dariya banda Kubrah da tai shiru tana kallon wani waje daban.
     Hajarah ce ta fara farga da yanayin Kubrah, dan haka ta tsagaita da tata dariyar tana faɗin, Aunty Kubrah ALLAH dama nasan ba ciwon kai Nu'aymah keyiba. Inagafa sabon siriki ta samo ma su Addah shine duk take a ruɗan nan”.
    Uffan Kubrah batacema Hajarah ba. Sai ma mikewa tai ta bar falon tana wani ɗan murmushin da su duka basu fahimci ma'anarsa ba......

Nidai nace, “Humm”.

        “K lafiya? Kika shigoma mutane tamkar wadda aka koro!”. Umm ta faɗa a tsawace tana kallon Nu'aymah data shigo falon a guje.
      Duƙar da kai tayi ƙasa tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ke son zubo mata. Cikin rawar murya tace  “Umm babu komai fa, zanje toilet ne”. Bata jira amsar kowa ba a cikinsu ta shige ɗakinta da sauri.
      Dariya su Aunty Zulfah sukayi, sai dai banda Umm da tabi Nu'aymahn da ido dan sam bata yarda da abinda ta faɗa ba.

            Tana shiga toilet ɗin ta maida ƙofar ta rufe harda murza key. Jingina tayi da ƙofar ta fashe da kuka maiban tausayi. A ranta tana faɗin yaya zatai da wannan abin kunya da takaici da mutumin nan ya aikata a gareta? Ita namiji yayma kiss, namijinma kafiri da baya bautama ALLAH. Baisan idan ya saɓama UBANGIJI ba ya nema gafara. Baisan haramci ba baisan halacci ba, balle yasan hukuncinsu. Bakinda bai taɓa ambaton ALLAH ba sai shan giya da zina, bakin dake ambaton wanin ALLAH (Shirka) shine yau akan nata. ‘ALLAH ya isa bazan taɓa yafe makaba’. Ta faɗa a fili tana sake rushewa da kuka. ‘Na shiga uku ni Zainab, ni.........’
       “Nu'aymah!”. Muryar Umm ta hanata ƙarasawa. Saurin toshe bakinta tayi dan kar Umm taji shashshekar kukanta.
      “Nu'aymah wai baƙya jinane?”.
Umm ta sake faɗa tana matsowa jikin bayin.
      Da sauri Nu'aymah tai gyaran murya. Kafin ta miƙe da sauri gaban tap ta fara wanke fuskarta, kallo ɗaya taima mirror tasan idan Umm ta ganta a haka akwai matsala, to amma kuma bata da wani ikon ko dabarar yin wanka tunda yanzu nan tayi sa. Towel tasa ta tsane fuskar tata sannan ta buɗe ƙofar a hankali ta fito.
      Haɗa ido sukai da Umm da ke a tsaye tana jiran fitowar tata. Tai saurin kauda idanunta zuwa ƙasa da faɗin, “Umm yi haƙuri, ALLAH toilet ne”.
         “Toilet ko kuka?”. 
Da sauri ta ɗago ta kalli Umm ɗin. Muryarta na rawa tace, “Umm toilet ne ALLAH”.
      “Toilet ɗin ki kai ma kuka kenan?”.
Baki taɗan tura gaba, “To Umm gudawa fa ce”.
        “Mtsoww! K dai bansan randa zaki bar wannan shashancin ba wlhy. Idan gudawan ne bazaki iya zuwa ki amshi magani ba”.
         “Kiyi haƙuri Umm”.
Juyawa Umm tayi ta fice batare data tanka mataba. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya tanabin mahaifiyar tata da kallo. Ta tabbatar yau da tasan mita aikata da saita fasa mata baki. Dan Umm tana da zafi idan aka ƙureta, sam bata ƙaunar halin banza.
         Duk da tana buƙatar kaɗaici haka ta daure ta sake gyara fuskarta sannan ta fito falon. Dan bata fatan wani ya gano halin da take ciki. Musamman ma Umm data kasance mace mai saurin fahimta akan rashin gaskiyar yaranta. Ba komai ya jawo hakanba kuwa sai saka musu ido da takeyi a duk motsinsu kwarai da gaske. (Iyaye ya kamata mu kasance haka. muzama kowanne motsin yaranmu nakan idanunmu da zukatanmu kodan gudin yin tufƙa da warwara akan tarbiyyarsu. ALLAH ya kare mana su dai damu baki ɗaya).
     Tana zama aunty Rafi'a tace, “Hummm! Aymah ina kika samo wannan turaren mai shegen daɗi haka?”.
     Gaban Nu'aymah yay mugun faɗuwa. Ta ɗago da dauri tana kallon aunty Rafi'a. Sai taga har Umm ma ashe kallonta take tamkar yanda su Aunty Zulfah duk suka xuba mata idanu. Ta buɗe baki zatai magana su Nanah suka shigo cikin uhun sallama.
       Wata muguwar ajiyar zuciya Nu'aymah ta sauke a ɓoye. Tare da saurin miƙewa zumbur ta nufi su Nanah ta rungume.

           Zuwan su Nanah gidan ne ya shashantar da maganar turare. Amma ga Umm sam abin yaƙi barin ranta. Dan sai da tai duk dabarar da uwa ta gari ya dace tayi wajen shaƙar ƙamshin a jikin Nu'aymah. Ta kuma jisa, ta tabbatar duk gidan kuma batasan kowa da wannan ƙamshin ba. Amma sai bataima Nu'aymah maganar ba. Dan tuni su Nanah sun janyeta ma sun fice su da su Amal daga gidan.
       

____________________

       Ya jima zaune matuƙa akan toilet sit kafin ya miƙe ya fara zame jiƙaƙƙun kayan jikinsa. Wanka yayo, ya fito sanye da Bathrobe fara mai ɗan tsaho. Dan ta wuce gwiwarsa kaɗan. Towel ƙarami ya riƙo a hannu ya fito yana goge fuskarsa da sumarsa.
        Kallo ɗaya yayma Solomon daya kasa haƙuri ya dawo ɗakin duk da korar da yay masa ya ɗauke kansa. Kan Solo a ƙasa yace, “Kamin afuwa Sir, bazan iya nutsuwa ba bayan kai kana cikin wani hali”.
       Yanzun ma uffan baice masa ba. Ya dai gitta ta gabansa ya wuce zuwa gaban kujeru biyu dake a ɗakin. Zama yay cikin ɗaya ya ɗora ƙafafunsa saman table ɗin dake a gabansu tare da naɗe towel ɗin hannunsa saman kansa ya jingina bayansa da kujerar ya lumshe idanu.
     Shi dai Solomon na tsaye yana cigaba da kallonsa cike da damuwa. A can ƙasan ransa kuwa zargine fal ciki akan su baba malam. Gani yake kamar yau rashin bin Yoohan cikin gidan yasa aka cutar da shi........
       “Ina buƙatar coffee”. Ya katsema Solomon tunaninsa cikin yin magana a daƙile.
    Da sauri Solo ya dawo hankalinsa. Ya amsa da “Okay sir” yana matsawa inda telephone ɗin ɗakin take yay kira domin yin order ɗin coffee ɗin da Yoohan ya buƙata.
      Ba'afi mintuna uku zuwa huɗu ba kuwa sai ga cikin ma'aikatan yay knocking. Solomon ne ya je ya buɗe ya amso. Ya dawo inda Yoohan ɗin ke zaune ido a lumshe ya ajiye tray ɗin ƙasa dan ya ɗaura ƙafarsa akan table ɗin. Saida ya tsiyaya masa, tare da saka sukari ƙwara ɗaya kamar yanda yasan Yoohan na buƙata sannan ya miƙa masa.
      “Gashi Sir” ya faɗa da yarensu.
Buɗe ido Yoohan yay a hankali. Sunyi jajur alamar baya cikin nutsuwarsa. Baice komaiba ya amsa tare da yima Solomon alamar yaje. Badan Solo yaso hakanba ya fito yana waigensa. A falo ya maƙale dan bazai iya zuwa ko inaba yabar Yoohan ɗin a haka, kodan gudun ɓacin rai mai tsanani da zai iya fuskanta a gurin madam Chioma da Papa.

         Yoohan da baisan Solomon bai fitaba ya fara shan coffee ɗin a hankali zuciyarsa na cigaba da kai kawo akan abubuwa masu yawan gaske. A haka ya shanye ya sake zubama kansa. Yanzu kam ko sugan ma bai sakaba a haka ya sha kayansa. Koda ya gama kuma nan ya cigaba da zama har tsahon lokaci.
       Zuwa can kuma tamkar wanda aka mintsina sai ya miƙe, duk da rigar wanka ce a jikinsa bai damu ba, a haka ya buɗe ƙofar ya fice bayan ya zura Slippers. Tsaye yayi yana kallon Solo dake gyangyaɗi a falo, kansa ya ɗan girgiza ya nufi ƙofa batare da yayi magana ba.
         Can ya fita harabar hotel ɗin da ko ina ke ƙwanyar da haske, mutane nata kai kawo tamkar ba dare ba. Mafi yawansu mazane dake shigowa da mata. Wasu kuma matan su kaɗai ke shigowa alamar masu jiran nasu suna ciki su. Wasu mazan kuma su kaɗai ne suma, dan wasu matafiyane ba sheɗancin ne ya shigo dasu ba.
         Watsar da komai yay dan shi baya matsama kansa shiga hurumin da banasa ba. Can wajen kujerun da aka tanada dan hutawa ya nufa. Babu mutane sosai a wajen, dan haka ya samu ɗaya ya zauna, tare da sake tsunduma cikin abinda ke masa kai kawo a zuciya da ruhi tun ɗazun.
       A cikin tunanin nasa ne hankalinsa ya fara karkata ga abinda na kusa da shi ke saurare a wayarsa. Duk da ya saka ƙarar can ƙasa sosai hakan bai hana Yoohan ji ba saboda dare ya fara nisa. Wajen da suke kuma wajene da sam babu hayaniya, dan hotel ɗin dama bana ku bayi bane, na manya ne masu ji da ƴan canji, inda aka ginasa ma kawai ya isa baka amsa. 
          Lecture ce da ga bakin Sheikh Fantami yake saurara. Kasancewar da turanci ne sai komai yake shiga kunnen Yoohan raɗam. Buɗe idanu yay a hankali ya kai dubansa ga mai sauraren wa'azin. Matashin saurayine tamkarsa, sai dai kallo ɗaya zakai masa kasan kaga ustaz. yayi shiru a wajen tamkar baisan da motsin kowaba yanata sauraren wa'azin sa. 
      Tsintar kansa yay shima da sake nutsuwa sosai yana saurare. ya shagala sosai da sauraren wa'azin nan mutumin ya miƙe, batare da yayi tunanin wani na tayasa ji ba ya kashe tare da barin wajen ya koma ciki dan ya kwanta ya huta.
       Ko kaɗan Yoohan baiso hakan ba, dan anzo wata gaɓa da duk mai sauraren wa'azin zai so jin ƙarshensa. Bin mutumin yayi da kallo harya ɓacema ganinsa. Ji yay tamkar ya bisa ya roƙe ya basa ya ƙarasa ji. Dan jikinsa wani irin tsuma ya keyi, gashi duk ya mimmiƙe masa. Komai ya sake birkice masa, duk yanda yake tunanin tasirin mafarkinsa da maganganun Nu'aymah sai lecture ɗin nan daya saurara ta sake faɗaɗa rauninsa zuwa ƙololuwar rikicewar tunani da gushewar wani duhu daya fahimci ya jima a cikinsa. Tunanin bin bayan mutumin ya sakashi kallon agogon hannunsa, ya ɗan waro idanu waje dan bai ankaraba sai yaga agogo ya nuna ƙarfe ɗaya saura.
         Sake maida idanunsa yay ya lumshe tamkar baiga mi agogon ya nuna masa ba. Sai ajiyar zuciya daya dinga saukewa a jajjere. 
         A haka Solomon daya sake shiga ɗakin nemansa bai gansaba ya fito a rikice nemansa ya iske sa. Duk da wayar dake a hannunsa da alama ta nuna wanine akan layin sai da ya sauke ajiyar zuciya . 
         “Ashe kana anan sir?!”. Solo yay maganar yana sake sauke numfashin ruɗanin da yake ciki na rashin ganin nasa da farko.
         Yoohan da tun isowar Solomon wajen yana kallonsa ta ƙasan ido ya buɗe idanunsa ya watsa masa wani shegen kallo mai cike da gargaɗi.....
        “I'm sorry sir. Madam ce”.
        Kafesa da ido sosai yayi, duk da kuwa yasan Momy Solomon ɗin ke nufi. Bai amshi wayarba, bai kumace komaiba ya miƙe yabar wajen. Solo dake binsa da kallo yay saurin bin bayansa hankali a tashe.
         Koda suka koma ɗakin bai gajiya ba sai da ya sake maimaita masa maganar amsar wayar sannan ya miƙa masa hannu alamar ya bashi. Yana amsar wayar ya nunama Solo toilet da hannu.
     Duk da bai fahimcesa ba haka ya nufi toilet ɗin dan ya duba. Shi kuma ya ɗora wayar saman kunnensa muryarsa mai amo da kauri ɗin nan ta fara fidda sauti. “Hello Mom”.
    Ajiyar zuciya mai ƙarfi madam Chioma ta sauke da ga can, kafin cikin ƙasa da murya sosai tace, “My boy!”.
       “Humyim”.
Ya faɗa a hankali cikin maƙoshi.
      Murmushi mai sauti ta sake da ga can tana mai ƙanƙame filo a ƙirjinta da lumshe idanu. Cikin sake narke murya tace, “Mike damunka?”.
      Shiru yay na wasu sakanni. kafin ya furzar da ɗan huci yana sauke idanunsa da ga table ɗin. “Ba komai Mom, bakiyi barci ba?”.
           Sake narke murya tayi kamar zatai kuka. Tace, “My Boy tunaninka ya hanani barci. Kai kasan muna tsananin buƙatar ganinka tare da mu ni da papan ku dama ƙannenka gaba ɗaya. Amma duk da ɗokin dawowarka da mukeyi wannan karon, bayan tsahon sati biyu da ka ɗauka bakanan shine kai wucewarka wani gari batare da ka fara sauka Abuja mun ganka ba”.
         “Am so sorry Mom”. Ya faɗa a taƙaice kawai.
     Matse filo ta sakeyi sosai a ƙirjinta. Dan ji take jininta na wani masifar yamutsawa tamkar zaiyi tsartuwa ya fito. Kafin ta samu damar sake magana ta sake tsinkayar muryar Yoohan na faɗin, “Mom goodnight, zan kwanta”. Ƙitt ya yanke wayar.
      “My b......” tai yunƙurin faɗa sai kuma taji ƙitt. Da sauri ta ciro wayar daga kunnenta ta kalla. A take fuskarta tai masifar tsukewa hawaye na taruwa mata cikin idanu. Filo ta sake jawowa zata ƙanƙame papa ya shigo ɗakin nata.
       “Wai lafiya kika maƙale anan bayan inata jiranki a can?”.
     Wani irin takaici da baƙin ciki ne ya kumeta a zuciya. Ta ɗan hararesa a kaikaice tana maijin wani irin zafinsa da ɗaci a ranta. Amma a zahiri sai tai ɗan murmushi da cewa, “Ka bari kawai. Solomon ne ya kirani wai yaga kamar John a damuwa. Shine fa nasa ya haɗamu dan wayoyinsa duk basa tafiya. Amma yaron nan sai ya amsa ni sama-sama. daga ƙarshe ma ya yanke wayar”.
      Ƴar dariya Papa dake hawowa gadon yayi. ya jata jikinsa ya rungume yana faɗin, “Kema kinsan halin yaronki ai. Minene zai ɓata miki rai a ciki. Maybe yana buƙatar hutawa ne shiyyasa ya kashe”.
    Kafin ta samu damar basa amsa ya haɗe bakinsu waje guda. Duk yanda taso ta ƙwace kanta ya hanata wannan damar. Dan dama inhar ALLAH ya bashi sa'a a kanta baya wasa da damarsa. Saboda duk lokacin da zai buƙaci kasancewa da ita sai sunsha uwar rigima, wani lokacinma ƙarfi yake nuna mata ya samu nutsuwa. Yakan rasa miyasa take masa hakan tunda shi dai yasan auren soyayysa sukayi. ada can kuma sam bata masa wannan halin sai a shekarun nan da bazasu gaza goma zuwa sha ɗaya ba.
    To komadai minene yau ya moreta da ƙyau. Daga ƙarshe ya koma lallashinta sabida kuka da take masa tamkar wanda yay mata fyaɗe. Da ƙyar ya samu kuwa tai shiru sukai barci duk da shi ya rigatayi kafin itama ya sacetan.

         Yoohan kam koda ya yanke wayar sai yay jifa da ita saman kujerar dake gefensa. ya sake maida kansa jikin kujerar ya lumshe idanunsa tamkar ɗazun.
     A haka Solomon da ya kammala tattare kayan da Yoohan ɗin ya baza a toilet ya fito ya samesa. Baiyi magana ba, ya lallaɓa kawai ya ɗauki wayarsa ya fice da ga ɗakin. Duk da Yoohan najinsa bai motsaba, haka ya cigaba da zama a wajen har tsahon lokacin da shima kansa baisan ya kai ba, dan barci ne mai nauyi ya kwashesa a wajen, tare da faɗawa cikin nannauyan mafarki maiban tsoro da al'ajabi a garesa.
           Gabannin asuba ya farka a firgice, da ƙyar ya iya motsa wuyansa da ya ƙage, cikin dauriya da jarumta ya shiga jujjuyasa yana matse fuska saboda zafi. Sai da yaji ya ɗan sake masa sannan ya miƙe tsaye yana sauke tagwayen ajiyar zuya. Duk da a zuciyarsa yayi mamakin barcin da yay a zaune na kusan awa huɗu sai baiyi magana ba ya taka a hankali zuwa gaban Window. Idanu ya rufe zai fara addu'a kamar yanda sukeyi a addininsu sai kuma yay saurin buɗewa. Hannu ya saka ya buɗe Window ɗin. Sassanyar iskar asubahi ta feso masa, tare da ƙwala kiran sallar farko da ga wani massallaci da alamu suka nuna yana gab da hotel ɗine ko kuma a cikin hotel ɗinma yake . Wani wawan numfashi ya sauke tare da lumshe idanunsa. Haka kawai sai ya tsinci kansa a wani irin nishaɗa na musamman..............✍



_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 28

............Sake buɗe idanun yay ya saukesu bisa giza-gizai dake yawo cikin hasken sararin samaniya na yanayin asubahi. Karan farko a rayuwarsa da zuciyarsa ta tafi wajen tunanin da girmama UBANGIJI da ya halicci sammai, gata dai babu icce ko ɗaya daga kowacce kusurwa ta duniya da zakai zaton ta riƙeta. Sannan babu wata sarƙa ko ƙarfe da suma suke amsa sunan ginshiƙi a gareta. Da rana hasken *_Rana_* ya mamayeta. Da dare hasken *_Wata_* ya ƙawata ta da adon taurari. da *_Damuna_* na _Giza-gizai_. Lokacin asubahi takan canja kala zuwa sky blue da wasu ado masu ban mamaki da al'ajabi. Hakama da yammaci lokacin faɗuwar rana takan ƙawatu da kalar sky blue da na yanayin faɗuwar rana. Duk wannan hikima da rahamar akan azurtamu da sune babu ko naira ɗaya. Babu kuɗin haraji babu na ƙarshen wata. To miyasa wanda ya azurtamu da ita bai taɓa jiran mu biyasa da ko taro ba?  ‘saboda shi ɗin *_(SARKI NE GAGARA MISALI DA BAUTA KAWAI AKE KAƊAICE SA)’_* 
         Wani yanki na zuciyarsa ya bashi wannan amsar.
       Samun kansa yay da sake lumshe idanu ya sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya saboda wata kalma data faɗo cikin kunnensa daga massallacin da aka kira salla dan sun saka tafsir ne.. (Kana son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?). Furicin ya fito daga bakin Sheikh Sooraj Hashim jibiya (Baba malam) dan sun saka tafsir ɗin nasa ne. 
         ‘Tabbas ina son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?’. Ya amsa tamkar shi ɗin akeyima tambayar kai tsaye. yana mai cigaba da kallon yanda wata keyin ƙasa cikin giza-gizai alamar lokacin faɗuwarsa yayi, zai bama rana guri itama tazo ta cika umarnin ALLAH (S.W.A) akan aikinta.
        Tabbas wannan tambaya ta tsayama Yoohan a zuciya. Dan da ita ya ƙarasa sauran daren daya rage masa. Akan kunnensa har aka kira assalatu akai salloli a massalatai. Sai da gari yay haske sosai sannan ya iya barin jikin Window ɗin zuwa toilet.
     Ji yake a ransa bazai taɓa samun nutsuwa ba sai ya dangane da gidan baba malam a safiyar nan. Dan tabbas yana buƙatar sanin (Hanyar fahimtar ni'imomin dake cikin addinin musulinci? A yau).

       A gaggauce ya gudanar da komai. Kamar ko yaushe yay shirinsa cikin ƙananun kaya. Blue jeans da farar shirt mai gajeren hannu. Sai ya ɗora suit jacket fara tas itama. Yau dai bai saka necktie ba, maɓallin shirt ɗinma ba duka aka rufe ba. Cikin ƙamshinsa ya baro cikin hotel ɗin batare daya nema inda su Solomon suke ba.
         Safiya ce sosai a garin, hakan yasa da ƙyar ya samu keke napep, shima da mutum ɗaya a ciki. Bai damu ba, duk da kuwa wannan shine karan farko a tarihin rayuwarsa da zai shiga napep ɗin. Lokacin da mai napep ya tambayesa ina zasa? Da ƙyar ya iya haɗa hausan ya bashi amsa da sunan baba malam kawai. Dan dama bawai ya iya hausan bane yana dai jin abubuwa sosai saboda mu'amula da mutane marasa lafiya akan aikinsa. Sai dai bai iya maidawa, bayan gaisuwa sai abubuwan da baza'a rasaba suma ɗai-ɗai ne.
     Sai da aka fara ajiye wanda ya tarar a ciki kafin shi a kaisa. Kusan dubu uku ya miƙama mai napep ɗin. Da mamaki shiko yake kallonsa, yama rasa mizai ce masa dan ya fahimci hausa ba isarsa tayi ba. Sake miƙo masan da yayne ya saka mai napep ƙoƙarin haɗa ɗan turancinsa ya sanar masa naira ɗari da hamsin ne kuɗinsa. Duk da dai turancin bai haɗu da ƙyau ba Yoohan ɗin ya fahimci mi ya faɗa. Dan haka ya ajiye masa kuɗin a jiki yana faɗin, “Na baka ne duka”. Yanda yay maganar da hausa abin dariya, harma mai napep ya kasa haƙuri sai da ya dara.
       Yoohan baibi takansa ba ya nufi ƙofar gate ɗin su baba malam kansa tsaye, kai kace gidansa yazo.
               Sau uku yay Knocking sannan maigadi ya buɗe ƙaramar ƙofar ya leƙo yana tambayar “Wai wanene haka da farar safiyar nan?” dan yasan su Baba malam ta ƙaramin gate sukaje massallaci yau.
     Bai gane Yoohan ba. Dan duk zuwan da yay har sau biyu bashi kaɗai ya shiga ba sai da jagorancin masu gidan. Sai da ya gama ƙare masa kallo sama da ƙasa kafin yace, “Samari lafiya kuwa? Mikake nema ko buƙata anan?”.
        Sam Yoohan bai fahimta ba, bayan kalmar (lafiya da wasu ɗai-ɗai) babu abinda ya gane a zancen maigadi. Sai yay shiru yana kallonsa cike da nazarin miya kamata ya ce da shi. Maigadi da haushi ya kama ya sake maimaita masa tambayar?. Nan ɗinma dai ba fahimtar yayi ba. Sai ma ya jefa masa tambaya da turanci shima.
      “To bakajin hausa kenan?”. Maigadi ya faɗa a hankali. Sai kuma ya kalli Yoohan yay masa alama da hannu (wai yana zuwa). Kafin Yoohan ɗin yace wani abu maigadi ya koma ciki. Saurin yunƙurowa Yoohan ɗin yayi zai tsaidashi sai dai tuni ya rufe ƙofar.
      Cike da damuwa ya dafe kansa. Sai kuma ya juya yana kallon titin anguwar. babu mutane sosai, sai tsilli-tsilli dake fitowa cikin massallacin. Sai kuma sautin karatun yara da shima alama ta nuna daga harabar massallacin ne.
       Nufar gate ɗin massallacin yayi, kasancewar shi a buɗe yake sai ya samu damar shiga kansa tsaye. Sai dai bai kai tsakkiyaba wani cikin almajiran malam ya tsaidashi da sauri, dan kallo ɗaya zai tabbatar maka Yoohan ɗin ba musulmi bane.
      Anyi sa'a almajirin malam najin turanci, sannan kuma duk zuwan da Yoohan yayi gidan sau biyu ya gansa. Ba ƙaramin daɗine ya kama Yoohan ba jin cewar almajirin malam najin yaren da shima yake ji. Cikin sauƙi suka gaisa ya sanarmasa wajen malam yazo. Kuma yana cike da ƙaguwar san ganinsa domin dalilin babban uziri.
         Duk da almajirin malam yayi mamaki hakan bai hanashi yarda zaima Yoohan ɗin iso ba. Dan haka ya nuna masa wani ɗan dakali alamar ya zauna ya jurasa. Shi kuma ya juya cikin massallacin inda yasan malam na zaune yana karatu da azkar kafin ya fara karatu ga magidantan anguwar dakan ɗauki karatun safe da baya wuce zaman awa guda.
   
      Yoohan bai zauna ba. Sai ma faman bin massallacin yake da kallo. A ransa yana sake jinjina ƙoƙarin da su baba malam sukai wajen ginashi. Dan ƙaton gaske ne, kuma ya ginu da gini mai ƙyau. Gashi an shafesa da farin fenti yanata ɗaukar ido tamkar ba'a shiga cikinsa, sai shukoki da suka sake ƙawata shi suma. Ko ina kuma a tsaftace yake. Daga wajen da yake tsaye yana shaƙo daddaɗan ƙamshin dake fitowa daga massallacin wanda kullum safiya da maraice Nu'aymah ke zuwa ta sharesa ta saka turaren wuta da kalolin Air Fresheners masu daɗin ƙamshi..........
     Kukan wani yaro ne ya katse masa tunanin nasa. Ya ɗan juya inda yake jiyo kukan. Hakan yayi dai-dai da fitowarta daga cikin ajin da take koyarwa riƙe da bulalar dorina. Sanye take da dogon hijjabi mai hannu fari tas dan har yana jan ƙasa. Hannunta na dama riƙe da Al-qur'ani, na haggu kuma bulala. Yanda take jijjiga bulalan tana magana da nuna yaron ne ya sakashi shagala da kallonta. A ransa ya raya, ‘Ashe kowa ma masifa take masa?’. Jiba dai yanda takema yaro ƙarami duk da kuwa bayajin mi take faɗa. Amma yanayinta ya nuna faɗa takeyi dan tama saka yaron kneeling ne a ƙofar ajin.........
       “Yahya! kai ne da safen nan?”.
Maganar baba malam ta katsesa daga kallon Nu'aymah daya shagala yi. Numfashi ya sauke tare da juyowa ga baba malam ɗin. Baba malam daya juya yana kallon abinda Yoohan ɗin ya shagala kallo shima ya ɗauke kansa ya maido garesa. Sake mai-maita masa tambayar yayi a karo na biyu.
         Yoohan da ya sunkuyar da kai ƙasa yace, “Uncle, inason sanin minene ni'imomin dake a cikin addininku na musulinci?!”.
        Ba baba malam da yayma tambayarba, hatta Abban su Abdallah dake fitowa daga massallacin sai da ya taka wani uban birki.
      Baba malam da jikinsa ya hau tsuma yace, “Yoohan sake maimaitawa naji”.
     Babu musu Yoohan ya kuma faɗin,
               “Ina son sanin ni'imar dake cikin addinin musulinci?!”.
    
الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .
Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat.
        Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika.
اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.
Alhamdu lillahi ala kulli halin
        Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali.

        Sai ya durƙusa a ƙasa yay sujida hawaye na sauka masa a fuska.
      Yoohan dake binsa da kallo yay saurin duƙawa shima yana zaro manyan idanunsa a waje. durƙushewa yay gwiwa bibbiyu yana kallon malam harya ɗago daga sujidar da yay.
     Fuskarsa ɗauke da murmushi ya kama Yoohan suka miƙe tare, sai kawai ya jawosa jikinsa ya rungume.
     Duk da ba yaune karan farko da aka fara yima Yoohan irin wannan rungumar ba sai yaji ta yau ɗin kamar daban ce a rayuwarsa. Kamar ba irin wadda Papa da sauran mutane ke masa bace. Kamar girman ta yau ɗin na musamman ne.
     Baba malam ya ɗagosa da sauri tare da riƙe hannunsa. Yace, “Lallai yau zaka fara sani da ga rahamar UBANGIJINA, domin kuwa, *HASKE da RAHAMAR UBANGIJIN* al'arshi ta bayyana a zuciyarka da harshenka Yahya!. Sai dai bazaka taɓa fahimtar tarin ni'imomin dake cikin musilinci ba daga wajensa har sai ka shigo cikinsa”. 
       Yoohan da bai fahimcesa ba yay shiru yana kallonsa ƙasa-ƙasa. Sai kusan seconds goma ya ɗago kaɗan ya kalli baba malam ɗin da ƙyau, sai kuma ya sake maida kansa ƙasa. “Uncle ban gane mikake nufi ba”.
     Murmushi baba malam yayi, ya sake gyara tsaiwarsa cikin harshen turancin da suke magana yace, “Ina nufin bazaka taɓa fahimtar ni'imomin dake tattare da wannan addini mai daraja ba har sai ka kasance musulmi Yoohan. Ta wannan hanyar ne kawai zaka ƙwanƙwaɗi madarar ni'imar UBANGIJI fiye da zaton hasashen ka”.
        Babu ko tantama Yoohan yace, “Inhar zan sani ɗin ta wannan hanyar zan biya ko nawane na shiga addinin naku dan na sani, dan na tabbatar idan ban sani ɗinba natsuwa zata cigaba da yin nisa da ni har abada”.
       “UBANGIJI kai ne gagara misali a tunanin hankali ko hasashen zuciya. Tabbas kai mai ikone ga wanda kaso, a kuma lokacin da kaso. Yahya shiga addinin musilinci ba'a biyan ko sisi. *_ALLAH maɗaukakin sarki ya halicci halitta ne domin su bauta masa, kuma ya sawwake musu abinda zai taimaka 
musu na arzikinsa, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
      _“Kuma ban halicci aljan da mutum ba sai domin kawai su bauta mini. Bana neman wani arziki daga gare su kuma bana bukatar da su ciyar da ni. Lalle ALLAH shi ne kaɗai mai azurtawa kuma ma’abocin karfi sosai”._ Suratuz Zariyat, aya ta:56-58.
        *_Mutum a halittar da ALLAH ya yi masa zai bautawa ALLAH ne shi kaɗai inda za’a bar shi, ya zama mai son ALLAH ya na bauta masa ba ya yi ma sa shirka, sadai abinda ya 
ɓata wannan (dabi’ar) kuma yake karkatar da ita shi ne abin sheɗanun aljanu da na mutane su ke ƙawata mata na abinda sashin su yake yi wa sashi wahayi na ƙawatacciyar Magana kawai don ruɗi, shirka wata aba ce da ta zo daga baya kuma ta kutsa kai ga halittar da ALLAH 
ya yi wa mutum, ALLAH maɗaukakin sarki yana cewa:_*
      _“To, ka tsayar da fuskarka ga wannan addini kana mai kaucewa shirka, halittar ALLAH wacce ya halicci mutane a kan ta, babu mai canza halittar ALLAH”._ Suratur Rum, aya ta: 30.
   *Kuma Ma’aikin ALLAH (S.W.A) ya ce: “Dukkan abin haihuwa ana haihuwarsa ne akan musulunci, to iyayan shi ne su ke yahudantar da shi, ko su Nasarantar da shi (kiristan da shi) ko su majusantar da shi”. Bukhari da Muslim ne su ka ruwaito.*
       Dan haka Yahya UBANGIJI baya buƙatar ko sisi da ga gareka face amsa kalmar *_La'ilaha illallah......._*”.
       Sosai abin ya bama Yoohan mamaki da wannan bayani na baba malam. dan haka ya gyaɗa kansa yana mai gyara tsaywarsa da faɗin, “Na shirya amsar wannan kalma Uncle”.
       Murmushi sosai ya sake faɗaɗa a fuskar baba malam, batare da ya sake cewa komai ba ya kama hannun Yoohan sukabi ta ƙaramar ƙofa zuwa cikin gida. Abban su Abdallah na biye da su zuciyarsa fal tunanin inda ya taɓa sanin mai kama da Yoohan ɗin a wasu shekarun baya..
        Sashen mahaifinsu kai tsaye suka nufa, ko ina fes yake dan ana gyarawa saboda sukan zauna a ciki musamman randa sukaso nishaɗi. Duk hidimar bikin salla ma jiya a ciki sukayita su huɗun. Sai da duk suka zauna, Yoohan da Abban Abdallah kowa nama ɗan uwansa kallon sani baba malam ya katsesu da faɗin.
     *_“Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai ALLAH, Kuma Muhammadu MANZON ALLAH ne”_*.
       _“Waannan kalmomin shahada guda biyu, sune ƙofar shiga musulunci, sune kuma rukuninsa mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musulusncin mutum, sai da furuci da su, da kuma aiki da abin da suka ƙunsa, da wannan ne kuma kafiri yake zama musulmi._
       1-Ma’anar kalmar shahada: Ma’anar shaidawa da cewa babu abin bauta da gaskiya sai ALLAH, shi ne yin furuci da ita tare da sanin ma’anarta, da kuma yin aiki da abin da ta ƙunsa, zahiri da baɗini, malamai sun haɗu akan cewa furuci da kalmar shahada, ba tare da sanin ma’anarta ko yin aiki da abin da ta ƙunsa ba, ba shi da amfani, kai sai dai ma ta zama hujja a kansa, kuma ma’anar (La Ilaha Illallah) shi ne babu abin bautawa da gaskiya sai ALLAH shi kaɗai matsarkaki maɗaukaki.
       _Rukunan wannan kalmar (shahada) sune: (korewa da tabbatarwa), wato kore haƙƙin bauta daga wanin ALLAH, kuma tabbatar da shi ga ALLAH shi kaɗai ba shi da abokin tarayya. Haka kuma wannan kalmar ta ƙunshi kafircewa ɗagutu (shi ne dukkannin abin da ake bauta masa wanda ba ALLAH Maɗaukaki ba, ko da kuwa ya kasance mutum ne (tare da yardarsa da bautar da ake masa), ko dutse, ko bishiya, ko son zuciya, ko sha’awa), da nuna masa ƙiyayya da yin kuɓuta daga gare shi._
        *_Wanda ya faɗi wannan kalmar (shahada da bakinsa) amma bai kafircewa abubuwan da ake bauta 
musu wanin ALLAH ba (a aikace), to tamkar bai faɗeta ba. ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Kuma abin bautarku abin bauta ne guda ɗaya. 
Babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi. Mai rahama Mai jin ƙai”.(Baƙara: 163)._* 
       *_Kuma Maɗaukaki ya ce: “Babu tilastawa game da (shiga) addinin 
(musulunci), haƙiƙa shiriya ta bayyana daga ɓata, saboda haka wanda ya kafirce wa ɗagutu kuma ya yi imani da ALLAH, to haƙiƙa ya riƙi igiya amintacciya, (wadda) ba ta yankewa. ALLAH kuwa Mai ji ne, Masanine”._* (Baƙara: 256) 
           _Kuma kalmar (Ilah) tana nufin abin bautawa da gaskiya, duk wanda ya ƙudurci cewa abin da ake nufi
da kalmar (Ilah) shi ne: Mai halitta, Mai arzutawa, ko wanda yake da ikon ƙirƙira, kuma ya ƙudurci cewa yin 
imani da wannan kawai zai wadatar, ba tare da kaɗaita ALLAH da ibada ba, to haƙika faɗin kalmar (La Ilaha 
Illallahu) ba za ta amfane shi ba, a nan duniya wajen shiga Musulunci, kuma a Lahira ba zata kubutar da shi ba daga azaba madawwamiya._
         ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Ka ce (da su): “Wane ne yake arzuta ku daga sama da ƙasa? ko kuma wane ne yake mallakar ji da gani?, kuma wane ne yake fitar da mai rai daga matacce, ya kuma fitar da matacce daga mai rai? Wanene kuma yake tsara al’amura?” To za su ce: “ALLAH ne”. To ka ce (da su): yanzu ba za ku ji tsoronsa ba?” 
(Yunus: 31). 
         *_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Ko wane ne ya halicci sammai da ƙassai, ya kuma saukar muku da ruwa daga sama, sannan (da wannan ruwan) muka tsirar da (shukokin) gonaki 
masu ƙayatarwa, ba kuwa za ku iya tsirar da bishiyoyinsu ba?, shin akwai wani abin bautawa tare da ALLAH, A’a, su dai mutane ne da suke kauce wa (gaskiya)”. (Naml: 60)._*
         Kuma ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Kuma lallai idan ka tambayesu, “Wanene ya halicce su?, Lallai za su ce: “ALLAH ne” To, yaya ake juyar da su (daga bauta wa ALLAH)?” (Zukhruf: 87).

           *_“Ma’anar Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
        _Ma’anar shaidawa lallai (Annabi) Muhammadu 
MANZON ALLAH ne shi ne a yi masa biyayya cikin abin da ya umarta, da gaskatashi a kan abin da ya ba da 
labari, da nisantar abin da ya hana kuma ya yi tsawa a kansa, kuma ba za a bautawa ALLAH ba sai da abin da ya 
shar’anta._
       *_Tabbatar Da Shaidawa Lallai MUHAMMADU MANZON ALLAH ne:_*
      _ MANZON ALLAH ne: Shaidawa lallai (Annabi) Muhammdu Manzon 
ALLAH ne tana tabbata ne da yin imani da cikakken yaƙinin cewa lallai (Annabi) Muhammdu tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawan ALLAH ne, kuma Manzonsa ne ya aiko shi zuwa ga Aljanu da mutane gaba ɗayansu, kuma lallai shi ne cikamakin Annabawa da Manzonni, kuma shi Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi bawa ne makusanci a gurin ALLAH ba shi da komai daga siffofin ALLAH, kuma (wannan shaidar tana tabbata ne) da yi masa biyayya da girmama umarninsa da haninsa, da lazimtar 
sunnarsa a baki, a aikace, kuma a ƙudurce._
       *_ALLAH ya ce: “Ka ce: ya ku mutane lallai ni MANZON ALLAH ne 
zuwa gare ku gaba ɗaya” (A’araf: 158). _*
     _Kuma ya ce: “Ba mu kuma aiko ka ba face zuwa ga mutane baki ɗaya, kana mai gargaɗi da bushara” (Saba’a: 28)._ 
       _Kuma ya ce: “(Annabi) Muhammadu bai kasance uban ɗaya 
daga mazajenku ba, sai dai (shi) Manzon ALLAH ne kuma cikamakin Annabawa” (Ahzab: 40)._ 
         _Kuma ya ce: “Ka ce tsarki ya tabbata ga Ua
UBANGIJINA, ni ba 
kowa ba ne face mutum kuma Manzo” (Isra’i : 93)._
      Wannan (tabbatar da shaidawa Annabi Muhammadu Manzon ALLAH) ya ƙunshi al’amura kamar 
haka:
       Na farko: yarda da Manzoncinsa da ƙudurceshi a ɓoye cikin zuci. 
      Na biyu: yin furuci da haka da harshe a bayyane. 
      Na uku: koyi da shi da yin aiki da abin da ya zo da shi na gaskiya, da barin abin da ya hana na ƙarya. 
        *_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Sai ku yi imani da ALLAH da Manzonsa, Annabi Ummiyyi¹, wanda yake imani da ALLAH da kalmominsa, kuma ku bi shi don ku shiriya” (A’araf:
158)._* 
      Na huɗu: gaskatashi a kan dukkan abin da ya ba da labarinsa. 
   Na biyar: Mutum ya so shi sama da son kansa da dukiyarsa da ɗansa da mahaifinsa da mutane baki ɗaya; domin shi MANZON ALLAH ne, kuma haƙiƙa sonsa yana daga cikin son ALLAH, da so saboda ALLAH Haƙiƙanin son MANZON ALLAH shi ne yi masa biyayya wajen bin umarninsa da nisantar haninsa da 
taimakonsa da jibintarsa.
         *_ALLAH ya ce: “Ka ce: idan kun kasance kuna son ALLAH, to ku bi 
ni, sai ALLAH ya so ku, ya kuma gafarta muku” (Ali Imran: 31)._*
           Kuma ANNABI tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi ya ce: “Ɗayanku ba ya zama mumini har sai ya soni fiye da mahaifinsa da ɗansa da mutane gaba ɗaya” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi daga hadisin Anas ALLAH ya yarda da shi. 
       *Kuma Allah Maɗaukaki ya ce: “Saboda haka waɗanda suka yi imani da shi, suka kuma girmama shi, suka kuma taimake shi, suka kuma 
bi hasken da aka saukar a tare da shi, to waɗannan su ne marabauta” (A’araf: 157).* 
       Na shida: Ƙudurce cewa sunnarsa asali ce ga shari’ar musulunci, kuma ita sunnar kamar Alƙur’ni mai girma take (wajen dogoro da aiki da ita), saboda haka ba a saɓa mata domin hankali ya ci karo da ita. 
       Na bakwai: yin aiki da sunnarsa da gabatar da maganarsa a kan maganar kowa, da miƙa wuya zuwa 
gare shi, da yin hukunci da shari’arsa da yarda da ita. 
        *_ALLAH Maɗaukaki ya ce: “Na rantse da girman UBANGIJINKA ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba su sami 
wata ƙunci ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su kuma miƙa wuya gaba ɗaya” (Nisa’: 65)._*...............✍ 

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 29

.............“Na faɗaɗa maka muhimmanci kalmar shahada ne domin kasan addinin musilinci ba abin wasa bane, sannan bautama UBANGIJI shi kaɗai bashi da abokin tarayya shine cikakken imani. Gujema shirka babba da shirka ƙarama domin dawwama da tsira wajen bautama ALLAH shi kaɗai da tabbatar da soyayyar MANZONMU a zukatanmu wajibine. Zaka karɓi kalmar shaha yanzun nan Yahya, da ga haka ka tabbatar kabar kafircema ALLAH har abada, ka tsarkake ranka da zuciyarka cewa babu wani sarki sai ALLAH, ANNABI MUHAMMADU kuma MANZON ALLAH ne”.
     Kai Yoohan ya jinjina a hankali, zuciyarsa na wani irin tsitstsinkewa, tsigar jikinsa na tashi batare da yasan dalili ba. Hakama jininsa gudu yake a cikin jijiyoyinsa da sauri-sauri. Wannan yanayin sai ya saukarma jikinsa da kasala da wani rauni da bai taɓa tsintar kansa a ciki ba. 
     Baba malam na faɗar kalmar shahada yana maimaitawa, suna kai ƙarshe sai kawai hawaye suka ɓalle masa tamkar an buɗe fanfo. Ya sakko a kujerar da yake zaune a hankali ya durƙushe ƙasa jikinsa na wani irin rawa. A matuƙar mamakin su baba malam sai gani kawai sukai ya kai goshinsa ƙasa yayi sujda.
       Ɗan yatsa baba malam ya saka ya ɗauke hawayen da suka sakko masa gefen ido kaɗan. Hakama Abban Abdallah sai da hawaye suka cika masa idanu, sai jin wata irin ƙauna da soyayyar Yoohan ɗin suke tana nunkuwa a zukatansu. Kamar yanda shima ƙaunarsu ke sake masa ninƙaya a zuciya. 
       Koda ya ɗago da ga sujudar da yayi kamar yanda yaga baba malam yayi ɗazun sai kawai ya matsa ya rungume baba malam ɗin yana cigaba da hawaye. Sunja tsahon lokaci a haka kafin baba malam ya ɗagosa yana murmushi, yace,
          “Yahya ina tayaka murna. akwai ayyuka sosai a gabanka. Amma kafin su yanzu zakayi wankan shiga musulinci”.
      Cikin lunshe idanu dajin wata nutsuwa ta musamman Yoohan ya gyaɗa masa kai.

       Bisa jagorancin baba malam Yoohan ya gabatar da wankan shiga musilinci, tare da tsaftace wasu najasosi dake jikinsa, kamar tarin gashin kansa, an ragesa, amma ba sosai ba, dan baba malam ya shaida masa barin gashi ado ne, sannan koyine da MANZON ALLAH (S.A.W), bama ason ayi aski tas-tas ɗin nan kai na ƙyalli. Yanke masa ƙunba. Duk da shi bama mutum bane mai tarata, tare da sauran abubuwan da suka dace su kasance a tsaftace ga ƙa'idar musilinci.
     Bayan ya shirya tsaf cikin sabuwar suturarsa farar ɗanyar shadda tas, da taji ɗinkin da yay masa ɗas a jiki baba malam suka rungumesa suna sake masa marhaban da shigowa addinin gaskiya, sannan suka sake zama da shi a karo na biyu domin masa bayani akan SALLAH.
      yanzu kam harda su Abba Musbahu suma sun shigo tawagar. Bayan an kawo musu breakfast sunci tare su biyar abin sha'awa. Bayyana muku irin farin cikin da nutsuwa da Yoohan ke ciki a wannan lokaci ɓata lokaci ne.
     Shiru falon ya ɗauka duk suna sauraren baba malam dake zuba bayani cike da nutsuwa da ƙwarewar ilimi da sanin da ALLAH ya azurtashi da shi.
       Yoohan! Sallah na nufin addu'a.
Amma a shari'ance ibada ce ma'abociyar karatu da ayyuka Keɓaɓɓu, da ake fara ta da kabbara a kuma rufe ta da sallama, sallah ita ce rukuni na biyu a cikin Addinin Musulunci bayan kalmar shahada, wato *_(ASH'HADU AN LA ILAHA ILALLAHU WA ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH)_* sai ita. kuma ita ce kashin bayan addini, saboda girmanta da matsayinta ALLAH bai aiko mala’ika da ita ba sai ALLAH Madaukakin Sarki Ya kirawo ANNABI (SAW) a daren Isra’i da Mi’iraji ya bashi ita. Yana daga girman sallah ambatonta da ALLAH Madaukakin Sarki Yayi sau hamsin da takwas (58) a cikin Alkur’ani, kamar inda yake cewa:
{وَأَقِيمُوا الصَّلَوةَ} [البقرة: 43] 
Ma'ana: "Ku tsaida sallah"
{قُلْ لِعِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا يُقِيمُوا الصَّلَوةَ}[إبراهيم: 31]
Ma'ana: "Ka fada (Ya Muhammad S.A.W) ga bayina da suka yi imani su tsaida sallah".
Da sauran wurare a cikin Alqur'ani da dama.
       Annabi (SAW) yana cewa: “Bainar rajuli wabainal kufri tarkus salati” (Rawahu Muslim).
      Ma’ana: “Tsakanin mutum da kafirci shine barin sallah”. Kuma ana umartar karamin yaro da yin Sallah tun yana dan shekara bakwai, kuma in ya kai shekara goma a doke shi in ya ki yi.
     Sallah bata yiwuwa sai da alwala.

  ALWALA:
Ubangiji Madaukakin Sarki yana cewa:
"يأيها الذين ءامنوا إذا قمتم إلى الصلوة فاغسلوا وجوهكم وأيديكم إلى المرافق وامسحوا برءوسكم وأرجلكم إلى الكعبين وإن كنتم جنبا فاطهروا وإن كنتم مرضى أو على سفر أو جاء أحد منكم من الغائط أو لامستم النساء فلم تجدوا ماء فتيمموا صعيدا طيبا فامسحوا بوجوهكم وأيديكم منه ما يريد الله ليجعل عليكم من خرج ولكن يريد ليطهركم وليتم نعمته عليكم لعلكم تشكرون" المائدة: 6.
"Ya ayyuhal lazina aamanuu izaa kumtum ilas salati fagsilu wujuuhakum wa’aydiyakum ilal maraafiki wamsahuu biru’uusakum wa’arjulakum ilal ka’abayni wa’in kuntum junuban faddahharuu wa’in kuntum marda au alaa safarin au ja’a ahadun minkum minal ga’idi au laa mastumun nisa’a falam tajidu ma'ana fatayammamu sa’idan dayyiban famsahuu biwujuuhikum wa’aydiykum minhu maa yuridul Laahu liyaj’ala alaykum min harajin walakin yuridu liyudahhirakum waliyutimma ni’imatahu alaykum la’allakum tashkuruun”. Alma’ida: 6.
         “Yanzu zamuje kaga yanda ake alwala kafin salla”. Baba malam ya faɗa yana miƙewa. Gaba ɗaya suka biyosa ƙofar toilet ɗin dake cikin falon. Yayinda Yoohan da baba malam suka kasance daga ciki.
       *YADDA AKE YIN ALWALA SHINE:*
      1-Da farko yin niyya a zuci sannan ka ce: “Bismillahi” sannan ka wanke tafukanka na dama da na hagu kowanne sau uku(3).
     2-Sannan ka debo ruwa ka kurkure bakinka ka zubar da ruwan sau uku(3).
     3-Sannan ka debo ruwa ka shaka a hanci ka fatar shi ma sau uku(3).
      4-Sannan ka debo ruwa ka wanke fuskarka gaba dayanta sau uku(3), a lura cewa wanke fuska yana farawa ne tun daga farkon goshinka har izuwa karkashin haba wato kusa da makoshi a tsayinta kenan, a fadi kuma tun daga gefen kunnen dama zuwa gefen kunnen hagu. 
     5-Sannan a wanke hannu tun daga tafuka har zuwa gwiwar hannu na dama da na hagu shima uku(3).
      6-Sannan a ɗebo ruwa a yi shafar kai wato a tafin hannu a shafo tun daga farkon goshi har a kai ƙeya sannan a sake dawowa farkon goshi.
       7-Sannan shafar fatar kunnuwa na dama da na hagu.
     8-Sannan a wanke kafafu na dama da na hagu tun daga tafin kafa har izuwa gwiwar kafa.

          *ADDU’A BAYAN KARE ALWALA:*
"أشهد أن لا إله إلا الله وحده لا شريك له وأشهد أن محمدا عبده ورسوله" رواه مسلم.
"سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك" رواه الطبراني.
“Ashhadu an Laa ilaha illal Lahu wahdahu laa sharika lahu wa’ashhadu anna Muhammadan abduhu warasuluhu”. Muslim ne ya rawaito.
        Ko kuma ka ce;
“Subhanakal Lahumma wabihamdika Ashhadu an Laa ilaha illa anta astagfiruka wa’atubu ilaika”. Dabarani ne ya rawaito.

       “Wannan itace alwala Yahya. Da ita ake gabatar da bautar ALLAH, idan babu ita babu salla. Akwai abubuwan da suke warwareta, amma zamu ajiyesu zuwa nan gaba a neman ilimi zaka sansu. A yanzu muna tsinkayar jiran shigar lokacin azhar ne, dan a ƙa'ida ko wanne wuni musulmai na gabatar da salla sau biyar ne. Akwai nafiloli da mutum kan ƙara dasu domin samun kusanci ga UBANGIJI. Amma da waɗan nan biyar dazan lissafa maka sune wajubabbu. Wanda ya barsu ko yayi sakaci dasu, haƙiƙa bai cika cikakken musulmi ba.
       *SALLOLI  WAJIBABBU:*
Ya zo a hadisin Dalhatu bin Ubaydullah cewa:
"أن أعرابيا قال: يا رسول الله ماذا فرض الله عليَّ من الصلاة؟ قال: «خمس صلوات في اليوم والليلة.. الحديث… 
Ma'ana: "Cewa wani Balarabe ya ce: Ya Ma'aikin ALLAH me UBANGIJI (SWT) ya wajabta a garemu na daga sallah? Sai ANNABI (SAW) ya ce: Salloli biyar a cikin (kowane) wuni da dare".
       Salloli wajibabbu guda biyar sune: 1-Asubah, 2-Azzahar,  3-La'asar,  4-Magriba,  5-Isha'i.
   
       *LOKATAN  SALLAH  DA ADADINSU:*

ASUBAH: Sallah ce da ake yin ta raka'a biyu, Lokacin yin ta kuma shine bayan bullowar alfijir na gaskiya. Sannan ana yin karatunta a bayyane, Fatiha da sura a kowacce raka'a sannan a yi tahiya ayi sallama.

AZZAHAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacin yin ta yana farawa idan rana ta bar tsakiyar sama ta karkata zuwa mafadarta. Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.
Amma a ranar Juma'a sallar Azzahar tana zamowa sallar Juma'a a inda take komawa raka'a biyu kuma ana yin karatunta a bayyane, bayan liman ya kare khuduba.

LA'ASAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta na farawa daga inda inuwar abu tayi daidai da tsayinsa. Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

MAGRIBA: Sallah ce da ake yin ta raka'a uku, lokacin yin ta shine idan rana ta fadi a mafadarta (a nan Najeriya fuskar yamma). Sannan ana yin karatun raka'o'i biyun farko a Fatiha da sura amma a bayyane, sai a zauna a yi tahiya sannan a mike a yi raka'a daya ta karshe a karanta Fatiha kawai a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

ISHA'I: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta yana farawa ne idan shafaki ya buya (wato dan jaja-jajan nan na bayan faduwar rana idan gari ya fara duhu). Sannan ana yin karatunta raka'o'in biyun farko Fatiha da sura a bayyane, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.

*KIRAN SALLAH:*

الله أكبر الله أكبر
أشهد أن لاإله إلا الله 
أشهد أن لاإله إلا الله
أشهد أن محمد رسول الله 
أشهد أن محمد رسول الله 
حى على الصلاة 
حى على الصلاة
حى على الفلاح
حى على الفلاح
الله أكبر  الله أكبر
لا إله إلا الله 
Allahu Akbar,
Allahu Akbar, 
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah,
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah, 
Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah,
Hayya alas-Salat,
Hayya alas-Salat,
Hayya alal-falah,
Hayya alal-falah, 
Allahu Akbar 
Allahu Akbar
La’ilah aillall-lah.
Wannan shi ne lafazin kiran sallah. An so ga wanda ya ji kiran ana kiran sallah ya maimaita abin da mai kiran sallar yake fada shi ma, sai a wajen fadin "HAYYA ALAL SALAT" da kuma fadin "HAYYA ALAL FALAH" a madadin ka maimaita su idan mai kiran sallah ya fade su, sai ka ce "LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAH".

*YADDA AKE YIN SALLAH:*
- Da farko sai ka fiskanci alkibla (Saitin inda Ka’aba take, anan arewacin Najeriya ana cewa Gabas domin nan ne saitin inda Ka’aba take daga nan) sai a yi ikama, ga yadda lafazinta yake:
        Allahu Akbar, Allahu Akbar, Ash-hadu an La’ilaha Illal-lah, Ash-hadu anna Muhammadar-Rasulullah. Hayya alas-Salati. Hayya alal-falahi. Kad-kamatis-salatu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, La’ilah aillall-lahu.
       Sai ka daga hannuwanka daidai kafadunka ko daidai kunnuwanka sai ka yi Kabbara wato ka ce: “Allahu Akbar”.
       -Sai ka dora hannunka na dama akan hannunka na hagu a kirjinka (kabalu), ko kuma ka sake su (sadalu), duk wanda ka yi daidai ne.
      -Sai ka karanta karatun bude sallah a asirce ake yinta ita ce:
“Subhankal Lahumma wabihamdika watabaraka ismuka wata’ala jadduka wala’ilaha gairuka”
        ko kuma ka ce: “Allahumma ba’id baini wabaina hadayaya kama ba’adta bainal mashriki wal magribi, Allahumma nakkini min hadayaya kama yunakkal saubul abyadi minad danasi, Allahumma agsilni bil ma’i wassalji wal baradi”.
        -Sannan a karanta Fatiha zuwa karshenta.
      -Sannan a karanta abinda ya sauwaka na daga Alkur’ani sura ko wani sashi na sura daga Alkur’ni.
       -Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” ayi ruku’u, a cikin ruku’u ana iya karanta: “Subhana Rabbiyal Azim Wabihamdihi” ko a karanta “Subbuhun Kuddusun Rabbul Mala’ikati Warruhu” gwargwadon abinda ya sauwaka.
      -Sai a dago daga ruku’u ana fadar "Sami'al Lahu Liman Hamidahu" idan an dago an tsaya kafin a tafi sujjada sai a ce: “Allahumma Rabbana walakal hamdu” ko ka ce “Rabbana walakal hamdu”
        -Sai kuma ayi kabbara “Allahu Akbar” a yi sujjada ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjada gwargwadon abin da ya sauwaka a (a lura cewa sujjada ana yinta akan gabobi guda bakwai, goshi tare da hanci, tafuka biyu, guiwoyi biyu da kuma kafafu biyu).
       -Sai ayi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada a zauna akan kafar hagu ko duwawun hagu, a dora tafuka akan cinyoyi ana fadin “Rabbigfirli” ko kuma “Allahumma Igfirli”.
     -Sannan ayi kabbara “Allahu Akbar” a koma sujjada ta biyu ana fadin “Subhana Rabbiyal A’ala wabihamdihi” a cikin sujjadar gwargwadon abin da ya sauwaka.
-Sannan a yi kabbara “Allahu Akbar” a dago daga sujjada ta biyu, yayin mikewa zuwa raka’a ta biyu (idan an zauna dan kadan kafin mikewa raka’a ta biyu ba laifi, ana kiran wannan dan zama kadan “jalsatul istirahati”).
   Sai a sake kawo raka’a kamar yadda aka yi wannan ta farko, amma idan an dago daga sujjada ta biyu a raka’a ta biyu sai a zauna kamar irin zaman da aka yi na dagowa daga sujjada ta farko a dora hannaye akan cinyoyi, sannan hannun dama ayi nuni da dan yatsa manuniya a yi karatun tahiya a wannan zama, karatun tahiya shine:
       “Attahiyatu Lillah, Azzakiyatu Lillah, Addayyibatus Salawatu Lillah, Assalamu alaika ayyuhan Nabiyu Warahmatullahi Wabarakatuhu, Assalamu Alaina wa’ala ibadil Lahis Salihina, Ash’hadu an La’ilaha illal Lahu Wa’ash’hadu anna Muhammadan Abduhu warasuluhu”. 
      Haka ya zo a (Muwadda Malik, lafazin Umar bn Khaddab).
  Idan sallar mai raka’a biyu ce, kamar sallar Asubah sai ka cikasa karatun tahiyar anan da salati Ibrahimi. Shi ne kamar haka:
      “Allahumma salli ala Muhammadu wa’ala aali Muhammad kama sallayta ala Ibrahim wa’ala aali Ibrahim innaka Hamidun Majid, Wabarik ala Muhammad wa’ala aali Muhammad kama barakta ala Ibrahim waala aali Ibrahim Innaka Hamidun Majid”. 
       Sai kayi sallama, ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah”. Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.
       Idan kuma sallar mai raka’a uku ce kamar Magariba ko raka’a hudu kamar Azahar da La’asar da Isha’i, idan kayi kashi na farko na karatun tahiya sai ka tashi ka cikasa ragowar raka’ar da ta rage ko daya ko biyun (a lura cewa a ragowar raka’ar da ta rage bayan biyun farko Fatiha kadai za’a karanta ban da sura ko wani sashi na sura) sai ka sake zama na tahiya a karo na biyu ka cikasa tahiyar har zuwa sashi na biyu na salati Ibrahimi sannan ka yi sallama ka ce “Assalamu Alaikum Warahmatullah” Ko kuma ka yi sallamar bangaren damanka da kuma hagunka.

        *BAYANIN SHARADAN SALLAH
Sharadan sallah sune:-*
1.Musulunci. (ba ta inganta ga wanda ba Musulmi ba).
       2.Hankali (ba ta inganta ga mara hankali).
     3.Tsarkin dauda: Shine tsarkake jiki da tufa da bugire na mai sallah tun daga farawa har kammalawa.
    4.Tsarkin Hadasi: Shine duk abin da ke warware alwala, shima tun daga fara sallah har zuwa kammalawa. Ana bukatar wadannan tsarki a cikin kowace irin sallah ma’abociyar raku’i da kuma sujjada kai har ma wanin nan nata.
        5.Shigar lokacin sallah.
6.Niyya.
     7.Sitirce al’aurar namiji tana kamawa ne daga cibiya har zuwa gwiwa. Ita kuwa mace baki dayan jikinta al’aurane ga ajnabinta sai dai fuskarta da tafukan hannuwanta.
     8.Fuskartar Alkibla; Sai dai in a halin rincabewar yaki ko nafila a tafiyar da ya halatta ayi kasaru kuma mutum ya zamo mahayi ne kan abin hawa.
     Wanda ya yi sallah yana kallon watan alkibla ba yana mai mantawa ko rashin sani har sai da ya yi sallama, to ya saketa har abada, sai dai malamai sun yi sabani a cikin wannan hukunci, haka hukuncin ya ke idan ya zamo bai yi sani da alkiblar ba ko ya ganganta yin sallar ba a alkiblar ba.

       “Yahya musulinci yana da ƙa'idoji da tsare-tsare ga komai na rayuwa musamman ma ibada. Wannan kaɗanne daga ciki nake tsakuro maka a yanzu, kafin kayi ninƙaya cikin taskar ilimi ka fahimci manufata. Inaga yanzu mataki na gaba da zamuje domin gabatowar Azhar shine karantar fatiha daga littafin ALLAH, wato Al-qur'ani. Sauran abinda zai biyo baya zamu bisa daki-daki mu tsara yanda zaka samu karantarsu. Dan zamu sake komawa baya muyi cikakken bayani akan tsarki a muhimmancin sa. Ina fatan kana fahimtar duk abinda mukeyi”.
         Cikin raunin murya da sanyin gaɓoɓi Yoohan ya amsa da, “Ina fahimtar komai Uncle, ina kuma cikin ɗunbin farin ciki da kasancewata cikin wannan addini dake cike da tarin hikimomi da ƙa'idoji ababen birgewa da ƙayatarwa. Tabbas tun a yinin farko na fara cin karo da ni'imomin musulinci, ina fata da addu'ar cigaba da karo dasu har ƙarhen numfashina. A yau ina jina tamkar wani sabon hallita, tamkar ba Yoohan Goshpower ba, lallai babu abinda ya kai addinin musulinci nutsuwa da kwanciyar hankali. Ya ALLAH na gode maka da wannan ni'ima taka, ina roƙon ka cigaba da tabbatar da ita a gareni batare data yanke ba koda a sakan guda ne na rayuwata”.
      Cike da farin ciki su Baba malam suka amsa masa. Handkherchief Yoohan yasa ya ɗauke hawayen da suka ciko masa idanu. Kafin ya durƙusa har ƙasa yana godiya gasu baba malam da suka zamewa rayuwarsu sandar jagora wajen jawosa daga DUHU zuwa HASKE. 
      Saurin ɗagosa baba malam yay ya runmesa. “Yahya bamu bane ALLAH ne, mu kawai mun kasance ne daga cikin ƙaddararka ta alkairi, ALLAH yayi maka albarka, ya share hawayenka, ya yaye maka damuwarka, ya karɓi tubanka, ya shafe zunubanka damu baki ɗaya”.
      A tare suka sake amsawa da amin.

__________★★★★__________

                A hotel kam hankalin su Solomon a matuƙar tashe yake da rashin ganin Yoohan. Gaba ɗaya sun tada hankalin ma'aikatan hotel ɗin da barazanarsu. Saboda maigadi ya tabbatar shi baiga fitar Yoohan ba. Hakama wanda yake a reception yace baiga fitarsa ba. Ga kuma motocinsu duk suna ajiye alamar Yoohan bai fitaba a fahimtarsu.
        Ganin ƙaramar magana na neman zama babba Solomon ya kira papa ya sanar masa halin da ake ciki. Cikin matsanancin tashin hankali papa yace su kira layin Yoohan ɗin mana.
         “Sir! Duk wayoyinsa na nan cikin ɗakin, shiyyasama muka fahimci bada kansa ya fitaba kenan”. Solomon da jikinsa har tsuma yake ya bama papa amsa murya na rawa. Wata wawiyar tsawa papa ya sake daka masa daga can, tare da sakin wani irin ihu tamkar zai fasa gidan.
       “Solo!!!!!! Inhar yarona ya shiga wani hali na rantse muku da ALLAH duk sai na kasheku da hannuna, na baku awa biyar kacal akan nemansa. Idan har kuka bari na iso kano kuyi kuka da kanku!!....”
    Ƙit ya yanke wayar batare da ya bari Solo yay ko ƙwaƙwaran numfashi ba.

        Sosai hankalin Solomon ya sake ƙololuwar tashi, hakama na sauran ƴan uwansa. Dan sunsan wanene Pastor Goshpower, sun san kuma abinda zai iyayi, musamman ma akan Yoohan da duk duniya bai haɗa sonshi dana kowa ba.
       Suna cikin tashin hankali da tararrabin mafita sai ga ƴan sanda kusan mota uku sun iso hotel ɗin bisa jagorancin D.p.o Emanuel.
     Su masu hotel babban tashin hankalinsu kar sunansu ya ɓaci. suko su Solomon sune sukasan babban tashin hankalin da zai iya samunsu da su kansu masu hotel ɗin indai har ta tabbata anyi kidnapping ɗin Yoohan a hotel ɗin ne, kamar yanda kowa yake tunani da hasashe.............✍
[5/18, 6:00 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



No. 30

................Lokacinda su Solomon ke acan cikin tashin hankalin tsoron cikar lokacin da papa ya basu akan sanin inda Yoohan yake, shi yana nan suna shirin tafiya massallacin juma'a shi da su baba malam.
      Kowa ya kalli baba malam ɗin a yau zai fahimci yana cike da tsantsar farin ciki. A cikin nishaɗin daya shiga da shi cikin gidan nasa ya sake fitowa shi da Umm data taimaka masa yay shirin massallaci.
    Ƴar tsokanar da ya kema Umm yasa Nu'aymah dake zaune a falon tana gyaran fruit ɗin da Umm ta sakata ɗagowa tana kallonsu. Cikin washe baki tace, “Abbah yau dai kana cikin farin ciki ALLAH, naga tun safe fuskarka sai annuri takeyi”.
      Da ga Umm har baba malam dariya sukayi, ya matsa kusa da ita tare da kai hannu ya shafa kanta. “Tabbas yau ina cikin farin ciki mamana, saboda wannan farin cikin yau har ƙyauta ta musamman na shirya miki ke da Muhammad, dan haka kafin na dawo ki shirya faɗa mini abinda kike so”.
         Sosai farin ciki ya sake kamata. Ta shiga jera masa godiya da addu'ar fatan dawowa lafiya. Daga shi har Umm amsa mata suke cike da kulawa. Kowannensu najinta a ransa sosai, dan daga Umm har Baba malam ba ƙaramin so sukema Nu'aymah ba. Suna dannewane kawai saboda ƙarfafama kansu tarbiyarta. Ga ɗunbin tausayinta dake mamaye da ruhinsu game da matsalarta. Dan har yau da muke ɗin nan baba malam bai gajiya ba wajen cigaba da neman likitan nan, yana kuma gayama UBANGIJI da neman taimakonsa a kowane daƙiƙa.

     Bayan Umm tama baba malam rakkiya ta dawo. A inda tabar Nu'aymah nan ta sake isketa tana ƙalular gyara fruit ɗin.
      “Nikam naga takaina da wannan hali naki Nu'aymah! Mutum yayta abu sanyi-sanyi tamkar bazai ƙaresa ba. Yanzu maimakon ki zauna kiyi aikin nan a kitchen shine kika taho nan kuma dan salon neman ɓata guri?”.
       Baki ta tura gaba tana ɓata fuska, “Yoni Umm idanfa na zauna a kitchen wlhy Rabi damuna zatayi da surutun ta, kin sani dai ko redio haka ta ganta ta ƙyale akan zanc........”
      Bammm!. Umm ta make mata baki, hakanne ya hanata ƙarasa faɗa. Da sauri ta saki wuƙar hannun nata hawaye na taruwa mata a ido. Umm dake hararta tace, “Saunawa zan faɗa miki karna sake jin wannan maganar banzan a bakinki Nu'aymah? Rabi bata girmeki ba? K wai yaushe ne zaki bar tsiwa da rashin kunya? Itaɗin sa'arki ce?”.
       “Kiyi haƙuri Umm bazan sakeba ALLAH ”.
      “Kima sake mana, mara wayau kawai”. Umm ta faɗa tana hararta da barin wajen. Harta kusa ƙofar sashen baba malam ta juyo. “Kiyi ki tashi a wajen nan kuma kafin na fito, ga man-shanu can a kitchen ki ɗauka ki kaima Addah, kuma idan kinje ki zauna shiririta karki dawo ki ƙarasa aikin dana sakaki kinji ko”.
        Sake ɓata fuska Nu'aymah tayi hawaye na zirara mata. Sai dai batace komaiba har Umm ta shige ciki. Dan zuciyar gadon tazo mata wuya.
      
       Duk yanda Umm tace tayi haka tayi, sai dai data shiga kitchen Rabi tasha harara, dan a ganinta saboda itane Umm ta Mammangare ta. oho ita batama san tanaiba, dan aikinta takeyi koda ta shigo bama ta kalli inda Nu'aymahn takeba tunda tasan basa doguwar magana lafiya sai sunyi faɗa. 
       Manshanun ta ɗauka zuwa sashen Addah. Sai da tai sallama kusan sau uku kafin a amsa mata ciki-ciki. Bata damuba ta shige tana ɗaure fuska dan har yanzu akwai haushin faɗan Umm tare da ita. Kubrah kawai ta iske zaune a falon, tunkan ta ƙaraso ciki take jefo mata harara.
       Jitai kamar ta juya dan haushi, amma sai ta daure ta ƙarasa da faɗin, “Aunty Kubrah Umm ce ta aikoni wajen Addah?”.
     Banza tai mata tamkar bata jitaba, har Nu'aymah ta fara yanke shawarar juyawa sai ga Hajarah ta fito daga ɗakinsu hannunta ɗauke da Al-qur'ani.
       “A'a Aymah ce a wajen namu?”.
Ajiyar zuciya Nu'aymah tayi da maida kallonta gareta. Fuskarta da ɗan damuwa tace, “Aunty Hajarah Umm ce ta aikoni wajen Addah. Amma ina tambayar Aunty Kubrah tamin banz.....”
           Kafin ta ƙarasa taji saukar duka a bakinta, Kubrah da tai dukan ta nunata da yatsa cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “K dan uwarki ni sa'arki ce ko?”.
       “Kai haba Aunty Kubrah daga tambaya, yanzu dan ALLAH mita miki zaki dakar mata baki? Minene abin laifi anan to?”. Hajarah ce mai maganar dai-dai tana ƙarasowa inda suke ta kama hannun Nu'aymah dake hawaye, dama bakin bai gama mata zafiba akan dukan da Umm tai masa yanzu. Ga kuma Kubrah ta ƙara mata wani.
    Cikin masifa Kubrah ta kalli Hajarah, “Kozaki rama mata ne?”.
     “Bazan rama mata ba, amma ALLAH zai saka mata. Tunda duk wanda ya zalinci wani ALLAH na kallonsa. Nu'aymah jeki Addahn na ɗakinta kinji ko”.
      Kai Nu'aymah ta ɗagama Hajarah tana share hawayenta. Batare datace komaiba ta nufi ɗakin Addah zuciyarta na mamakin yanda Aunty Kubrah kejin zafinta a ƴan kwanakin nan, duk da dai dama ita babu wani shaƙuwa sosai tsakaninta da ita tun da can. Sai dai bata taɓa nuna mata banzan hali irin na wannan karonba. Tana gab da shiga ta tsinkayo muryar Kubrah na faɗin, “Ƴar iskar yarinya ki taka a sannu dan a tafin hannuna kike wlhy, inba hakaba saina tona asirin iskancinki a gaban kowa yasani a gidan nan”.
     Sosai gaban Nu'aymah yay bala'in faɗuwa, dan tasan inhar Kubrah ta faɗi abinda ta gani tsakaninta da Yoohan ranar tata ta ƙare. Da ƙyar ta iya haɗiye kukan daya taho mata. 
        Da mamaki Hajarah ta kalli Kubrah, “Haba Aunty Kubrah wace irin maganace haka? Wai nikam minene ya haɗaki da Nu'aymah mai zafi a kwanakin nan dan ALLAH?”.
      “Ki shaƙeni in faɗa miki mana”. Kubrahn ta faɗa a harzuƙe. 
      “ALLAH ya baki haƙuri”. Hajarah ta faɗa tana barmata wajen ranta fal tunane-tunane kala-kala akan ƴar tsamar yayar tata da Nu'aymah data gaza fahimtar tushenta a kwanakin nan sam.

       Sai da Nu'aymah tai sallama Addah ta bata izinin shiga sannan ta shiga ɗakin. Tsaye ta isketa tana ninke abin salla alamar sallar ta idar. Ganin Nu'aymah na sharar hawaye yasa fara'ar fuskar Addah gushewa lokaci guda. “Lafiya Nu'aymah? mi akai miki?”.
       “Babu komai Addah, Umm ce tace na kawo miki wannan”.
    Sam Addah bata yarda da maganar Nu'aymah ba, dan haka tai shiru tana cigaba da kallonta kawai batare data amshi man-shanun ba. “Nu'aymah bana son shirme, faɗamin gaskiya mi akai miki?”.
      “Addah wlhy aunty Kubrah ce ta dakar mata baki dan hawai tacemin ta tambayeta kina ina ta mata banza”. Hajarah dake shigowa ɗakin ta bama Addah amsa.
      Cikin ɓacin rai Addah tace, “Kubrah?!”.
       “Eh wlhy Addah, ni bama dukan ya ɓatan rai ba, bakiji yanda take faɗama Nu'aymahr maganar banza ba. A kwanakin nan dama na kula tana matsama yarinyar nan a gidan nan, haka ɗazun a islamiyyar asuba dan kawai Nu'aymah ta fiddo Fahad ɗin maman Sadiya daga aji saboda suna faɗa da wani yaro wlhy bakiga abinda tai mataba. Alhalin baikamata taima Nu'aymahn maganaba tunda yaran duk ƴan ajintane, ta fita sanin halin kowa a cikinsu”.
      Kama hannun Nu'aymah Addah tayi suka fito ranta a ɓace. Hakan yasa Hajarah biyo bayansu da sauri itama. 
         “Kubrah!!”. Addah ta ƙwala mata kira ganin bata a falon.
    Da sauri ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da plate ɗin abinci. 
     “Ubanmi Nu'aymah tai miki kika daketa?!”.
        Sake tsuke fuska Kubrah tayi, ta kalli Nu'aymah data duƙar da kai tana hawaye har yanzun. Wani ɗan murmushin mugunta tayi kafin ta kalli Addahn. “Addah catai na daketa?”.
       “Ni na faɗa ba ita ta faɗaba, tunda a gabana akai komai”. Hajarah ta bata amsa kafin Addah tai magana.
      “Mtsooow!! Munafuka kawai. Addah ni ban daketa haka kawaiba, rashin kunya zataimin shiyyasa........”
     “To amma shine zaki ce mata ƴar iska, kuma sirrinta a tafin hannunki yake. Idan kinso zaki tona mata asiri agaban kowa”.
       “Wlhy Hajarah zan sauya miki kamanni, wai ni sa'ar wasanki ce?”.

         “Kai!! Ya isheni haka, banason rashin mutunci. Bazan ɗauki wannan wawancinba kunji na faɗa muku. Shin kuɗin yaran goye ne da kullum baku da wani buri sai na samin ciwon kai? Kusani daga yau na sakejin makamancin wannan banzan al'amarin wlhy sainayi ƙololuwar ɓatama mutum rai a gidannan. Banda k kullum girma kike kinacin ƙasa Nu'aymah ce kuma ta zama abar tozartawarki Kubrah? To daga yau na ji wani abu ya sake fitowa makamancin wannan zakiyi nadama a gidannan kinji na faɗa miki”. Ta ƙare maganar da matuƙar zafin rai tana sake yima Kubrah gargaɗi da hannu.
   Sai kuma ta juya ga Nu'aymah dake sauke ajiyar zuciya a jajjere. “Nu'aymah jeki wanke fuskarki kinji  kuma kar naji wannan maganar a wani waje, kiyi haƙuri”.
     Kai Nu'aymah ta jinjinama Addah, babu musu ta shiga toilet ɗin dake a falon ta wanke fuskarta ta fito. sallma tai musu ta fice batare data sake yarda ta kalli sashin da Kubrah take ba. Harga ALLAH hankalinta a tashe yake matuƙa da kalaman Kubrah.
           Koda ta koma sashensu ɗakinta ta shige ta shiga raira kuka, Nu'aymah yarinyace da bata da tsoro sam. Amma yanda tai matuƙar damuwa da faruwar abin nan na jiya daya kasa barin ransta saita baka tausayi. Tasan tabbas wannan laifin na jiya yasha banban da kowane irin laifi, kuma duk wanda zaiji abinda ya farun sai yayi ALLAH wadai da ita, ƙilama baba Malam da Umm su tsine mata albarka. 
     Sake rushewa tai da kuka kamar zata shiɗe wajen jan zuciya. A haka ta tsinkayo muryar Umm na ƙwala mata kira. Da sauri ta miƙe ta shiga share hawayen, harta nufi ƙofar fita sai kuma tai saurin dawowa. Toilet ta shiga ta sake wanke fuska tazo gaban mirror tasa hoda da kwalli sannan ta fita.
         Zaune ta iske baba malam da Umm a falo. Cikin raunin murya taima baba malam sannu da dawowa. Duk kallonta sukai shi da Umm, baba malam yace, “Lafiya kuwa? Naga idonki kamar wadda tai kuka? Mamana!”.
    Kafin tayi magana Umm dake hararta tace, “Saboda namata faɗa akan rashin kunyar data iya”. (dan ita tazata faɗan datai matane ya sakata fushi har yanzun). 
      Baba malam baice komaiba sai maida kansa da yay ga tv kawai. Fuska a ɗaure Umm ta nuna mata trayn dake a kan centre table. “Ki ɗauka ki kaima baƙo a falon baba”.
     Kai kawai ta jinjina mata ta koma ɗakinta ta ɗakko hijjab. Batare datai maganaba ta ɗauka tiren ta fice. Sai da ta fice gaba ɗaya sannan baba malam ya ɗauke kansa daga kallonta. maidawa yayi ga Umm da itama take kallon nata.
       “Addu'a ya kamata ki cigaba da mata bawai nuna fushinki da zafi fiye da kima ba. Har yanzu Nu'aymah yariyace ƙarama, sannan kinsan lalurar dake tare da ita sam bata buƙatar yawan takura. Ki fahimci ita wannan tsiwar itace tata ƙuruciyar”.
        “Amma Malam ka tunafa ƴa mace ce ita. Gidan wani fa zataje. Bandama ƙaddara daba yanzu tana ɗakin miji ba. Wlhy sam bana son tsiwarnan tata, bansan a ina ta kwaso wannan banzan halinba nikam”.
     Murmushi baba malam yayi yana miƙewa, “To ayi haƙuri zata daina insha ALLAH, nima zan zauna da ita anjima ALLAH ya huci zuciyarki”.
       Yanda yay maganarne ya saka Umm yin murmushi, dan ta sake tabbatarwa yau mijin nata yana cike da nishaɗi sosai kam, musamman data san yafi kowa ƙin jinin tsiwar ɗiyar tasu.

★★★★★★

             Murya a sanyaye tai sallama a ƙofar falon har kusan sau uku. jin shiru ba'a amsaba ya sakata tura kanta ciki da haushi. Takaicin rashin amsa mata sallamar da ba'ayiba ne ya sakata ƙin kallon baƙon ma balle tasan wanene. 
      A gabansa ta dangwarar da trayn, murya a cinkushe batare data kallesa ba tace, “Ina yini”.
       Shiru yanzuma ba'a amsaba, wani sabon takaicin ya sake lulluɓe ta. Har tayi niyyar dubansa ta sauke masa takaicinta saita tuna yanzufa Umm ta gama mata faɗa harda duka akan tsiwa, sannan kuma bai kamatama tayi wani abun rashin hankali ba tunda batasan wanene baƙon nasu ba. Zata iya yuwuwa babban mutumne sa'an baba malam ko cikin yayunta. Haɗiye haushinta tai ta nufi hanyar fita zata bar falon.
          Yoohan da tun shigowarta idonsa nakan wani littafi da baba malam ya bashi ya duba ya ɗan ɗago kansa dan sam baiji sallamarta ba balle shigowartaba ma shi, sai gilmawarta kawai ya gani yanzu da take ƙoƙarin fita. Cikin tsautsayi ta bigi ƙaramar jakkar dake gefensa da ƙafa. baya tai taga-taga zata faɗi cikin sa'a yay saurin saka mata ƙafa dan son kareta bisa tsautsayi sai gata a cinyarsa ɗare-ɗare.
     Duk da ya canja kayan jikinsa mayataccen ƙamshin turarensa na nan manne da shi. Shaƙa ɗaya Nu'aymah tayi tai azamar ɗagowa cikin tashin hankali da tsantsar takaici.
       Idanunsu ne ya shige cikin na juna, cike da firgici Nu'aymah ta sake waro masa idanunta da kware baki zatai ihu saboda harga ALLAH ta tsorata da ganinsa.  Saurin saka tattausan hannunsa yay ya rufe mata bakin ruf yau ma, tare da sake manneta a jikinsa sosai shima a cikin ɗan firgice.
        Wani irin mugun bugawa ƙirjinta ya sakeyi, jikinta ya hau ɓari tamkar wadda aka jefa cikin garwashin wuta ko akan wayar lantarki. Ta shiga mutsu-mutsun ƙwace kanta tana kai masa duka.
          “Oh my God! Just relax. Please calm dawn”. Ya faɗa yana janye hannayensa duka daga jikinta.
       Cikin rawar jiki hawaye na zirara ta miƙe, sake bigewa tai da kujera ƙafarta ta tuzguɗe ta sake yin gaba kuma zata kifa yay azamar riƙo mata hannu ta sake dawowa jikin nasa.
      “Wayyo Abbana ɗan isk.........” ta wage baki da iya ƙarfinta zata faɗa yay azamar saka hannu ya sake toshe bakinta da manneta sosai a jikinsa yanda bazata iya ko motsawa ba.

        “Wa'iyazubillah!! Iskancin naku da rashin tsoron ALLAH yau har a falon malam?” Kubrah data shigo falon tamkar an jehota ta faɗa hannu bisa kai tana mai waro idanu waje..    
          Tashin hankali, tsabar ruɗewa Nu'aymah harda guntun fitsar ta saki a wando, batama san ta saka gwiwar hannunta ba ta kai ma Yoohan duka. Sai ko ya sauka a gefen cikinsa.
      Saurin sakinta yay yana faɗin “Ouch!!!” dan harga ALLAH yaji zafi. Yay saurin ɗoura hannun nasa bisa cikin ya riƙe yana watsa mata mayun idanunsa masu haske da cikar gashi.
       Nu'aymah dake ja da baya tana hawaye da kallonsa da kallon inda Kubrah take tsaye tace, “Ɗan iska kawai, ALLAH ya isa ban yafeba. Wlhy daga yau ka sake ƙoƙarin taɓamin koda hannu sai na illata maka wannan fuskar taka mai kama da jan ƙosai, na tsane ka wl........”
        “Hhhhhhh! K! Ƴar iska bar wani pretending kinji!”. Kubrah ta faɗa tana ƙarasa shigowa cikin falon sosai.
      Nu'aymah dake kuka tamkar ranta zai fita tace, “Aunty Kubrah wlhy ba abinda kike tunani bane. Wlhy tallahi kinji na rantse by mistake ne hakan ya sake faruwa yau ma, shine fa y.....”
        “K dalla saurara mani! Mahaukaciya kika maidani irinki komi? Na ganki da idona saman cinyarsa kuna tsotsar bakin juna sannan ki hau mini wani rsantse-rantsen banza. Kinsan ALLAH, inhar kika sake faɗin tak saina kwarara ihu yanzun nan kowa yasan halin da kuke ciki”.
     Ƙasa Nu'aymah ta durƙushe tana ƙara sakin kuka maiban tausayi. Yayin da Yoohan da sam bai fahimci mi Kubrah ke faɗa ba ya zuba musu idanu kawai yana kallonsu.
     Juyowa Kubrah tayi garesa, sai dai wani shegen kwarjini da cikar haibarsa tai bala'in cika mata idanu. Muƙut ta haɗiye maganar tata ƙirjinta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Cikin suɓutar baki ta firta ‘Tsarki ya tabbata ga ALLAH’.
         Sake ɗaure fuska Yoohan yayi fiye da da, dan a rayuwarsa ya mugu-mugun tsanar kallo, musamman ma irin wanda Kubrah ke masa na ƙurulla a yanzun. Duk da ma bawai yaji mi take faɗaba ne ɗazun, sai dai ya fahimci ba magana mai daɗi takema Nu'aymah ba. Dan haka ya watsa mata wani mugun kallon da manyan idanunsa yana miƙewa.
     Ganin ya nufita ya sata saurin zabura tai baya, sai dai kuma a mamakinta yama ɗauke kai daga gareta gaba ɗaya, raɓata yay ya nufi Nu'aymah dake durƙushe har yanzu tana kukan tashin hankalin datasan a yau babu makawa sai Kubrah ta tona mata asiri.
        Handkherchief ya ciro a aljihunsa tare da tsugunawa gabanta, murya ƙasa-ƙasa yace, “Hello!”. 
      A razane Nu'aymah da batasan da isowar tasaba ta ɗago danjin maganarsa gab da ita. Ta waro idanu waje sosai da saurin duban inda Kubrah ke tsaye tana kallonsu kamar ta samu television.
       Kamo hannunta yay, da sauri ta dawo da dubanta garesa tare da fisgewa da ƙarfi. Sai dai ko gezau baiyiba balle tai tunanin ƙwacewar. “Kai wane irin......”
         Yatsansa ɗaya ya ɗaura akan baki. “Shiiii!!!” ya faɗa cikin katseta da zazzaro mata idanunsa sosai.
         Ruf. Tai saurin rufe bakin kuwa. Dan wani irin shakkarsa da tsoronsa da bata taɓa fuskantaba daga gareshine ya shigeta yau ɗin. Ga wani irin kwarjini mai bala'in cika idanu da yay mata. Batare da yayi magana ba ya saka mata handkherchief ɗin cikin tafin hannunta tare da matso da fuskarsa gab da tata cikin wata irin raunanniyar murya yace, “Silly girl”.
       Baya taja jikinta, dai-dai da sakar mata hannu da yayi ya miƙe shima. Batare da ya kalli ko inda Kubrah take ba ya ɗauka jikkar da Nu'aymah tai tuntuɓe ya fice abinsa. Ya tabbata idan ya cigaba da zama a falon to lallai zai iya aikata abinda shi kansa bazai yafema kansaba. Dan duk da baiji mi Kubrah ta faɗaba ya fahimci ba abune mai daɗi ba musamman yanda Aymah take kuka.

          Yana ficewa Kubrah ta bi bayansa da sauri. 
      “Aunty Kubrah!” Nu'aymah ta faɗa da hanzari tana miƙewar itama. Amma sam Kubrah batako jiyoba balle ta nuna zata saurareta ta ficewarta.
             اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.
Ya Allah! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki.
         Nu'aymah dake jin wata hajijiya na neman zubar da ita ƙasa ta faɗa tana mai dafe kanta da sauri. Da ƙyar ta iya kai hannu domin lalubar bango. Sai dai kuma ina bai kai ga bangonba wani duhu ya mamaye idanunta. a take ta zube ƙasa jikinta na karkarwa saboda wani bala'in sara mata da kanta yayi lokaci ɗaya..............✍


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


[5/21, 9:18 AM] +234 816 133 8078: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 32

............Tun isowarsu asibitin aka fara bama Nu'aymah dake a sume taimakon gaggawa. Sai dai harsu baba malam suka isa asibitin bata farfaɗo ba. Hakan sai ya sake ɗaga hankalinsu. musamman ma Hajjo dake ta faman sharɓar hawaye. Cike da kulawa baba malam ya zauna kusa da ita duk da kunyar ɗan fari dake tsakaninsu. Murya a tausashe da nuna ɗunbin kulawa da ladabi ya fara lallashinta da faɗa mata kalamai masu taushi da nutsuwa irin na masu ilimi. Ya nuna mata koda rasa Nu'aymah sukayi su zama masu haƙuri da godema ALLAH. Dan lokacin da ya basu ita baiyi shawara da suba. A yansu kuwa idan ya karɓeta ya fisu bukatarta ne. 
     Haka ya cigaba da mata nasiha harta samu nutsuwa tai shiru. Abba Musbahu yazo gabanta ya durƙusa tare da saka handkherchief ya share mata hawayen.
     Ana haka Doctor ya fito daga ɗakin da aka sanya Nu'aymahn. Ya buƙaci ganin ɗaya daga cikinsu cikin nuna girmamawa a garesu. Abban Abdallah da Abban su Adawiya ne suka bisa office. Dan baba malam ya nuna kawaicin nasa da ya saba kamar ko yaushe. Amma zuciyarsa cike take da tsoro da rauni. Yana ta dai ƙoƙarin danneta ne da ambaton ALLAH wajen ƙarfafa imaninsa.

       A office ɗin likita kuwa ya nutsu ne wajen rubuce-rubuce a wata takarda kafin ya maida hankalinsa gasu Abbah.
       “ALLAH ya gafarta malam zan fara da muku albishir ɗin farfaɗowarta. Sai dai kuma kamar yanda kuka sani raunin dake a cikin ƙwaƙwalwarta shine ya motsa mata. Kuma gaskiya a bincikenmu yarinyarnan tana matuƙar buƙatar son ganin babban likita. Idan ba hakaba a koda yaushe zata iya fuskantar gogewar komai na ƙwaƙwalwar ta. saboda tana ƙara girma ciwon na daɗa faɗi. Musamman ma daya kasance kamar tana sakama kanta abubuwa masu nauyi a cikin rai. A duk kuma lokacin data shiga ƙunci ciwon na mata kuɗa a cikin kanta, ba dan ma tana samun kulawa da kuma addu'oi ba da gaskiya bana zaton yarinyarnan zata kai wannan shekarun batare data tsinci kanta a ciwon hauka ba. Duk da komai na ALLAH ne, babu wani bawa daya isa canja ƙaddarar wani bawa daga yanda tazo a littafinsa. Amma a wannan karon ayi himmar sadata da likitan daya dace da matsalarta, munan taimako kawai muke bata na dakatar da raɗaɗin a gareta a lokacin daya taso. Amma matsalarta sake hauhawa takeyi gaskiya”.
       Su Abba da duk jikinsu yay sanyi sukaima Doctor godiya sosai. Tare da tabbatar masa insha ALLAHU a wannan karon zasuyi abinda ya dace.
     Yaji daɗin hakan sosai. Ya sake ɗan musu wasu bayanan da suka dace akan yanayin kula da Nu'aymahn kafin ALLAH yasa a dace da samun Doctor ɗin daya faɗa. Dan ya basu note dazai taimaka musu samun ganin makusancin likitan da lokaci-lokaci yake shigowa cikin kano. Baya kuma duba marasa lafiya a ko ina sai a General hospital. Dan haka ya basu abinda zai taimaka musu ganawa da wata likita dake aiki a General hospital ɗin, wadda yake da tabbatacin ta hanyarta zasu iya ganin Doctorn.
     Godiya sukai masa sosai, sannan suka fito. Sai dai basu ma su baba malam bayanin komaiba, a ƙoƙarinsu nason yin wani hoɓɓasa akan jinin yayan nasu da a kullum hidimarsa ke ƙarewa a kan su da nasu iyalin. Suma wannan karon sunason nuna tasu bajintar akan ɗaya daga cikin jininsa guda biyu da ALLAH ya bashi.

________★★

          Ganin lokacin sallar la'adar ya gabato Yoohan ya buƙaci kaɗaicewa dan ya huta. Hakanne ya saka papa fita ya barsa shima ya nufi ɗakin da aka kama masa.
      Yoohan ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana miƙewa. Zuwa yay ya sakama ƙofar ɗakin key. Kafin ya nufi bayi yayo alwala kamar yanda baba malam ya koya masa. Duk da zuciyarsa na kwaɗayin zuwa massallaci yay salla cikin jam'i kamar yanda suka gabatar ɗazun a massallacin juma'a haka ya haƙura ya daure yin tasa shi kaɗai a cikin ɗakin kamar yanda aka koyar da shi.
     Bayan ya idar da sallar a tsanake yay addu'a gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa. Waya ya jawo yay kiran baba malam. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗaka. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke wadda har baba malam ya jiyota.
        “Banyi zaton zaka ɗagaminba Uncle. Nazata zakayi fushi dani bisa kuskuren papa”.
         Baba malam da fitowarsa kenan daga massallacin cikin asibiti sun idar da salla kiran ya shigo masa yay sassanyan murmushi, ƙaunar Yoohan ɗin da ƙyawawan ɗabi'unsa na sake dulmiyasa a ƙaunar yaron. Cikin kulawa yace, “Haba Yahya! Mizaisa nayi fushi da kai? Ai koshi bazanyi fushi da shiba dan ya fini gaskiya. Da farko ina fatan dai ka gabatar da sallar la'asar. Na biyu kuma ina fatan babu wata matsala tsakaninka da mahaifinka a dalilin ganinka da yay a wajena?”.
       Lumshe idanu Yoohan yay a hankali yana jingina bayansa da kujera, cikin so da ƙaunar baba malam dake ratsashi shima yace, “Alhamdulillahi Uncle. Yanzun nan na idar da salla, sai dai banje massallaci ba, ina fatan hakan ba laifi baneba. Dan nayi hakanne saboda ahalina, banason su fahimci ni musulmi ne tun yanzu dan zasubi hanyoyi da dama wajen kaini ƙasa. Amma idan na sami wadataccen ilimin addini musulinci duk ta inda suka ɓullo zan kare kaina”.
          Baba malam dake murmushi ya sauke ajiyar zuciya. “Tunaninka mai ƙyau ne Yahya. Sai dai salla cikin jam'i tanada matuƙar muhimmanci, dan haka kar kayi sakaci da samun ladan dake cikin jam'i kaji”.
       “Zan kiyaye Uncle”.
“Alhamdulillahi haka ake so. Mahaifinka fa?”.
        “Karka damu da shi Uncle. haka yake da zafi, amma da an fahimtar da shi yanada saurin fahimta. Munyi magana da shi ya kuma fahimceni, kafin ma ya wuce zai shigo wajenka yacemin”.
         Hakan ya bama baba malam mamaki matuƙa. Amma sai bai nunama Yoohan ba ya amsa masa kawai. Sannan sukai sallama.

         Lokacin da Yoohan ke waya da baba malam a can papa ma yana ɗakinsa suna waya da Uncles ɗin Yoohan ɗin su Uncle Godwin. Ba akan komai suke wayarba sai akan baba malam. Kamar yanda papa ya girgiza da ganin Yoohan da farko haka suma suka girgiza dajin Yoohan a wajen baba malam. amma daga baya sai bayanin da Yoohan yayma papa ɗin yaɗan sanyaya musu rai.
     Uncle Mike yay wata dariyar mugunta yana faɗin, “Wannan ɗan nakafa shegen kansane, inaga akwai aikin da yakema turawan nan ta ƙarƙashin ƙasa shiyyasa kullum bai damuwa da lamarin kowa sai wannan aikin nasa. A da ba ƙaramin haushi yake baniba akan hakan, amma jin wannan maganar ta yau sai naji ƙaunarsa da son haɗa tafiya da shi. Sai dai matsalar ɗaya ce yaron yanada taurin kai, nasan bazai taɓa yarda musan cikinsa gaba ɗaya ba. Amma ni a ganina mizai hana muma muyi namu aikin akan wannan hausa man ɗin, dan fa multi millions ne. Kawai dai baya nunawa ne”.
         Papa ya kwashe da wata dariya, kafin yace, “Mike! tunaninmu ɗaya, dan haka ku bari sai na shigo Abuja mu tattauna da ƙyau. Yanzu dai matakin farko zanbi shawarar Yoohan zanje har gida na bashi haƙuri. Daga haka na ƙulla alaƙa mai ƙarfi da shi. Sauran bayani kuma sai mun zauna a tebirin shawara”.
    Duk sunyi na'am da hakan suma. Dan haka yay musu sallama ya kashe wayar cike da zumuɗi a ransa. Kaɗan-kaɗan sai ya ƙyalƙyale da dariya. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta gama tsara masa yanda komai zai kasance.

______________★★

         Bayan Baba malam sun shiga sun duba Nu'aymah dake barci suka bar Hajjo da Abba Musbahu a asibitin. Koda suka iso gidan sai su Umm suka shirya su kuma suka tafi duba Nu'aymah. Wanka yayi ya zauna a falonsa yaci abincin da Umm ta shirya masa kafin su wuce. Abincin kawai yake ci a zahiri, sai dai zuciyarsa sam bata tare da duniyar mutane. Yayi zurfi matuƙa gaya a tunanin Pastor Goshpower (Papa). Ba komai ya kaisa ga tunaninba kuwa sai mamakin dama Papa nada babban ɗa a duniya kamar Yoohan? Ga shi dai a zahiri akwai kamanni tsakaninsu, sai dai baisan miyasa zuciyarsa ke kawo masa wani al'amari mai kama da kokwanto a cikin zuciyaba. Musamman da zuciyar tasa ke tariyo masa wani shuɗaɗɗen al'amari daya faru a shekarun baya tsakaninsa da Papan.
       Haka yayta saƙawa da kwancewa har lokaci yaja bai farga ba. Sai da Abban Abdallah ya shigo dubasa sannan ya fahimci yayi zurfi sosai a tunani ashe. Alwala yayi suka fice massallaci dan lokacin sallar magriba ya gabato
    Suna fitowa su Umm na dawowa gidan. tambayar jikin Nu'aymah sukayi. Suka sanar musu har yanzu tana barci, batama san sunje ba balle tahowarsu.
        Baba malam yabi Umm da kallo harta shige. tausayinta mai tsanani ne ke sake shigarsa. Tanada haƙuri da kawaici matuƙa, shiyyasa yake tsananin ƙaunarta fiye da zaton mai hasashe. Yanzu haka inba shi daya gama sanin kayarsa ciki da bai ba bazaka taɓa fahimtar tanada damuwa ba a fuskarta. Ta dake ta shanye komai, baka ganin komai akan fuskarta sai tsananin jarumta da tarin haƙuri da juriya.
     Haka ya tafi massallaci da wannan tunanin na Umm. 

         Bayan idar da sallar isha'i suna shirin zaman karatu kamar yanda suka saba ɗaya daga cikin ƴan agajin massallacin ya shigo ya sanar masa cewar yayi baƙi.
    Jimm yayi alamar tunanin baƙi daga ina a wannan lokacin? Bai gama kaiwa ƙarshe ba ya hango Yoohan dake ƙoƙarin shigowa massallacin. Bai tashi ba, sai ya jira harya ƙaraso inda suke. Yoohan da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci damuwa da rashin walwalarsa kamar ko yaushe ya ɗan bama na kusa da shi hannu sukai musabaha kafin ya ƙarasa inda baba malam ɗin yake. Cike da girmamawa ya risina ya gaishesa. Amma sai baba malam ɗin ya kamo hannunsa cikin nasa sukai musabaha kamar kowa. Cike da jin nauyi Yoohan yay masa bayanin tare yake da baƙi, wannan ya saka baba malam miƙewa bayan ya bama ɗalibansa haƙuri ya barsu da Abbansu Abdallah shi kuma suka fito.
       Duk da dai yayi mamakin ganin papa ne sai baice komaiba. Da kansa yay musu iso gidan saukar baƙinsu. Sannan ya kira Umm ta bada abinda ke akwai a gidan cikin su Omar wani ya kawo. 
         Papa dake ta waya tun ɗazun ya ajiye yana kallon baba malam da murmushi, shima bai gazaba wajen maida masa murtani. A ƙasan ransa kuwa yana neman tsarin ALLAH da ga kowanne irin sharri papan ke tare da shi ko yake shirin ƙullawa. Duk da shi mutum ne mai ƙyautatama mutane zato zuciyarsa ta kasa ƙyautata zaton akan papa, dan shi shaidane akan sanin papa bayahude ne na gaske, sai dai bai saniba ko yanzu ya canja daga yanda ya sanshi a da ɗin.
         Hannu ya bashi suka gaisa, hakan yay dai-dai da shigowar Omar ɗauke da basket da Umm ta shiryo abincin motsa baki. Sai da ya gaida Papan, suka gaisa da Yoohan da alamar sanayya tsakaninsu sannan ya fice. Papa ya gyara zamansa yana wani ɗan basarwa, fuskarsa da murmushi har yanzu ya duba baba malam da faɗin, “Kayi haƙuri da kuskurena na ɗazun, ina fatan zaka dubesa akan rashin sani na aikata. Bansan alaƙarka da yarona mai daraja bace irin haka sai bayan mun barka ne yaymin bayanin da har na fahimta, ina fatan zakamin afuwa”.
      Sosai mamaki ya kama baba malam, dan duk zatonsa Yoohan ya ma mahaifinsa bayanin ya musulunta ne. dan haka ya ɗan dubi Yoohan ɗin. Da sauri Yoohan ya girgiza masa kai yanda papa bazai fahimtaba, hakanne ya saka baba malam fahimtar akwai abinda Yoohan ya sanarma mahaifinsa daban kenan. Sai kawai ya murmusa abinsa ya fuskanci papan shima.
       “Karka damu komai ya wuce. Dama kuma ni ban ɗaukesa wani abuba. A inda ya faru anan na zubar da shi, nima ina fatan kaimin afuwa ka kuma fahimci alkairine ya haɗani da Yahya ba sharriba. Sanin shi wanene kuma bazaisa na taɓa cutar da shi ba insha ALLAHU. Saɓanin dake tsakanina da kai kuma bana fatan ya zama sanadin ɓata alaƙata da shi, dan sanin kai ne mahaifinsa bazai canja komai ba daga yanda na ɗaukesa a raina”.
       “Naji daɗin haka, na kuma gode sosai da wannan girmamawa”. Papa ya faɗa yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushin mugunta.
     Daga haka dai suka ɗan taɓa hirar da bawani tsaho taiba, shi dai ma Yoohan ba saka musu baki ya keba, yama maida dukkan hankalinsa ne ga wayarsa kamar baya falon. Kusan awarsu ɗaya da rabi sukai masa sallama suka fito inda su Solomon suke. Sai da baba malam yaga barin motocinsu anguwar sannan ya shiga cikin gida ransa taf da wasiwasi akan wannan ziyara ta Pastor Goshpower, amma sai ya bar abinsa a zuciya bai faɗama kowa ba, ya ma maida hankalinsa wajen kwantarma matarsa hankali akan damuwar ciwan ɗiyarsu.

WASHE GARI.

          Washe gari papa ya matsa akan sai Yoohan ya bisa sun koma Abuja. Badan yaso hakanba ya amince zai bisa, dan dama yau ɗinne zai kammala abinda ya kawosa kanon. Yaso komawa wajen baba malam dansu tattauna game da neman iliminsa amma papa ya tsare ko ina ya hanashi matsawa ko nan da can. Asibiti ma binsa yay sukaje tare, ya kuma zauna a office ɗinsa har sai da ya kammala komai suka fito.
      Da ga asibitin airport suka tafi kai tsaye, sai da jirginsu ya ɗaga sannan guards ɗinsa suka ɗauki hanya suma a motocin.

      Baba malam na asibiti wajen duba jikin Nu'aymah da jikinta Alhmdllh saƙo ya shigo masa. Buɗewa yay ya duba ganin Yoohan ne. Murmushi baba malam yayi saboda ganin abinda saƙon ya ƙunsa, a ransa kuwa yana tsananin tausayi da ƙaunar Yoohan, insha ALLAH yayi alƙawarin zai taimaki yaron nan har ya zama HASKEn da zai zama HASKE ga waɗansu.
    Ajiye wayar yay ya maida hankali ga Nu'aymah da Hajjo take lallaɓawa taci abinci amma sai shagwaɓa take ita ta ƙoshi. Ya ɗan murmusa tare da kamo hannunta cikin nashi. “Mamana daure kici ko kaɗanne kinji, inba hakaba fa kinsan Doctor yace allura zai miki, idan kuma kin fison allurar to sai a kirashi kawai”.
     Da sauri ta shiga girgiza kanta idanunta cike da ƙwalla. “Abba dan ALLAH a'a banaso”.
      “To ki daure kici abincin sai kisha magani ki kwanta ki huta. Kinga kince dama kanki na ciwo har yanzu, Doctor kuma yace kina buƙatar hutune sosai”.
      Kanta ta sake jinjina masa. Hajjo da batace musu komaiba ta miƙama baba malam abincin. Babu musu ya amsa ya fara bata da kansa. Batafi spoon huɗu ba su Ahmad suka shigo ɗakin bayan sunyi sallama an basu izini. Ba Nu'aymah kawai ba hatta Hajjo da baba malam da ɗunbin mamaki suke kallon wanda ya shigo tare da su Ahmad ɗin. Ba kowa bane face Nasir jikan yayar Hajjo.
     Babu kunya idonsa fes akan Nu'aymah da mamakin ganin nasa ya sakata masa kallo mai nisan zango. Hajjo ce ta katse su da faɗin, “Naseru yaushe a gari? Inji maƙi baƙo?”.
          Goshinsa yaɗan sosa najin kunyar kallon da baba malam ke masa. Kafin yace, “Hajjo yanzun nan muka iso”.
       “Kuka iso? To kai da wa kuma?”.
Kansa tsaye yace, “Rufaidah”.
      Baba malam da tun gaisuwar daya amsa musu baice komai ba sai yanzu yace, “Lafiya dai ko Naser? Yau ka tuna damu a duniya”.
        “Ayi haƙuri Kawu, ni ɗin mai laifine kam, mun tahone saboda ga biki nata gabatowa, ganin mun sami hutun makaranta mu duka sai kawai nace bara mu taho maɗan huta ai”.
      “Oh to masha ALLAHU, ALLAH yayi jagora to”.
     A tare suka amsa da amin. Nu'aymah dai bata tanka ba, tama ɗauke kanta tamkar batasan mi akeyiba. Sai da Naser ya tambayeta yaya jikin sannan ta gaidashi batare data kallesanba yanzun ma. Shiko yanata so su sake haɗa ido ko zaiji ɗan sanyi a ransa da ruhinsa.
     Miƙewa baba malam yayi yana faɗin, “To ni bara naje gida hajjo, dan ina saka ran zuwan wasu baƙi ɗan anjima kaɗan idan ALLAH ya kaimu. Idan sun wuce insha ALLAHU zan dawo muji ko zasu bamu sallama, banason zama asibitin nan sam”.
      Amsa masa hajjo tayi tare da binsa da addu'a. Nu'aymah ma ma dasu Ahmad sukai masa sallama ya fice. Hajjo ce ta sake cigaba da bama Aymah abincin, badan yana mata daɗi ba take amsa, sai dai mayataccen kallon da Naser ke mata duk ya sake takureta matuƙa, sannan ya tuno mata da wasu shuɗaɗɗun abubuwa dake tdakaninsu a lokacin ƙuruciyarta, hakan yasa taketa cuno baki gaba da ɓata fuska duk da ƙasan ranta cike yake da mamakin ganin nasa ya dawo bayan barinsu na tsahon shekaru da yayi akanta. 
          Idan bata manta ba shekara kusan takwas kenan rabonsa da kano. Dan tunda tace masa ita Yah Abdallah ne zaɓinta yay zuciya saboda goyon baya da Hajjo ta bama Abdallah a wancan lokacin. Anyi bukukuwa kashi-kashi a gidansu shi kaɗai ne baya zuwa sam.
    Ta ɗan sake satar kallonsa da jijjina ƙyawun daya ƙara da cikar kamala tamkar ba Yah Naser ɗin data sani ba a shekarun baya. Kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yanzu kam kuɗi sun zauna a garesa da hutu, dan sai ɗaukar ido yake kamar gasashshiyar kazar gidan gona.

    *_Naser yaro ne wajen Alhaji Kabeer Usama dake a garin katsina. Jikane ga Yayar hajjo da suke uwa ɗaya uba ɗaya, dan aurene ya kaita katsina ta zuba zuri'a kuma a can mai albarka. Ita kaɗai kuma ta ragema hajjo a yanzun, shiyyasa take ɗaukarta tamkar uwa. Naseer ya zauna a gidan su Nu'aymah sosai, dan rashin yara a gidan lokacin da su Abdallah sukai Accident yasa hajjo ɗakkosa. A wajensu yay primary ɗinsa har secondary. Jami'a ce kawai ta maidashi garin jos. Yaso nu'aymah shima tun tana ƙarama, dan lokacin takara suka dingayi da Abdallah a kanta duk da kowa bai furta ba saboda ƙuruciya. To sai kuma yazam sanda suka furta ɗin ya zam lokaci guda, sai dai Abdallah ya riga Naser. Dama kuma ya fisa nuna damuwa da Nu'aymah. Hakan ya haddasa rigima sosai tsakaninsu, da Hajjo taga lamarin zai girmama ne tai musu shari'a a tsakani da shaidar cewar Abdallah ya riga Naser ɗin. Wannan shine sanadin yin zuciya ya tattara komansa yabar kano ya koma gidansu. Bai kuma sake zuwa ba sai yau ɗin nan da suka gansa tsulum. Har yanzu kuma baiyi aure ba._*..........✍

      To ga dai Naser tsohon masoyin Nu'aymah a kano bayan gudun hijira na shkara takwas da yayi. Ko da wane shiri ya dawo yanzun kuma? Dan da alama kam akwai motsawar tsohon tsumi tattare da shi dama ita kanta, sai mu cigaba da binsa muji YAYA TAKE NE?!!🤗.

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/21, 9:18 AM] +234 816 133 8078: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 31

..............Ta ƙaramin gate Yoohan yay ficewarsa. Hakan yasa Kubrah data biyo bayansa ta rasa ina ya nufa. Har babban gate taje bayan ta gama dube-dube a harabar gidan bataga wata baƙuwar mota ba duk saina ƴan gidan.
             Yanda ta iso gate ɗin a rikice tana tambayar maigadi sai abin ya bashi mamaki. Amma sai kawai ya bata amsa da cewar babu wanda ya fita.
       “What?! Yama zakace dani babu wanda ya fita a gidan nan? Bayan nasan tabbas idan ba fitaba babu inda zai nufa”.
       “Hajiya Kubrah wlhy babu wanda ya fita kamar yanda na sanar miki. Shin kodai ɓarawo ne ya shigo gidan ban sani ba?”.
      Wani takaicine ya sake tuƙe Kubrah, batare data bashi amsaba ta bar wajen tana zuba masa harara. Shima tsit yayi bai sake magana ba, sai dai zuciyarsa fal saƙe-saƙe.

★★★★

            Yoohan na fitowa waje yay turus dan mamakin ganin motocin gidansu da alamu suka nuna tsayawarsu kenan. Dan yanzu suke ƙoƙarin fitowa. Mamaki yay masifar sake kamashi ganin papa harda d.p.o Emanuel da yaransa. Tsuke fuska ya sakeyi ya nufesu ganin yanda suka tafi kai tsaye ga gate ɗin gidan dan su basu ganshi ba.
       “Papa!” ya faɗa dai-dai lokacin da papa ya kai hannu zaiyi knocking gate ɗin. A kusan tare duk suka juyi garesa domin shigar muryarsa mai amo da kauri cikin kunnuwansu.
        Wata wawuyar ajiyar zuciya suka shiga saki a jajjere, musamman ma guards ɗin Yoohan da suka san suna a cikin gagarumin tashin hankali inhar ba'a samesa anan ɗinba.
       Papa har yi yay tamkar zai kifa dan saurin zuwa ga Yoohan ɗin. Yay wani bala'in rarumosa jikinsa ya rungume yana faɗin, “Thanks you lord. my son are you okay?      
       “Yes Papa! What is happening? Mi kakeyi anan? Miya kawoka kano?”. Yoohan ya jerama papa tambayoyin yana zare jikinsa daga nasa tare da bin guards ɗinsa da ƴan sandan dake zagaye da su da kallon tuhuma suma.
       Sake jawosa jikinsa papa yayi, batare daya bashi amsar ko ɗaya daga tambayoyin ba, ya shiga duba jikinsa sama da ƙasa kamar mai tunanin an masa wani abu. Sai kuma ya kama rigar shaddar jikinsa yana faɗin, “Yoohan minene wannan?”.
      Wani irin luuuu da idanu Yoohan yayi tare da huro iska daga bakinsa. Cikin ƙosawa da abinda ke faruwa yace, “Papa kaya ne mana. Wai mi kukeyi anan wajen ne? Miya kawoka kano?”.
             Cikin tsananin nuna ɓacin rai papa yace, “John! Yau kaine da kayan hausawa a jiki? Mike damun kanka da tunaninka?”.
      Sake shiga wani takaicin shima Yoohan ɗin yayi, dan a take fuskarsa ta sake nuna fusata. Tayaya yana tambaya amma batare da an basa amsaba papa kuma na masa wasu tambayoyi mara kangado sai kace wani ƙaramin yaro. A tsawace ya kalli su Solomon da faɗin, “Mi kukazo yi anan nace?!!”.
       Yanda ya daka tsawar basu Solomon kawai ba, hatta Emanuel da yaransa duk da suke ƴan sanda saida suka razana. Balle kuma ƴan anguwa da suka fara taruwa kallo. Gashi Yoohan yayi maganar ne da yare.
       Solomon ne cikin rawar jiki data baki ya fara masa bayani,
      “Sir! Dama mun zata ko wani abu mara ƙyaune ya sameka. Tunda muka tashi muka fahimci baka a cikin hotel ɗin. Gashi an duba ko ina amma babu alamarka. Ma'aikatan kuma duk sun tabbatar mana basuga fitarka ba, ga kuma wayoyinka mun samu baka fita dasu ba. To shine mukai tunanin ko anyi kidnapping ɗinka ne shine muka kira boss muka sanar masa.......”
        “To da kuka kawosu nan, sune sukai kidnapping ɗin nawa kenan?”. Yoohan ya faɗa cikin katse Solomon.
    Kasa bashi amsa Solomon yayi, dan harga ALLAH ba ƙaramin gulma da munafincin su baba malam sukai wajen papa ba akan gaba ɗaya sun janye ra'ayin Yoohan ɗinma, amma sunyi bakin ƙoƙarinsu suga tun a zuwan farko bai sake zuwa gidanba sai dai hakan ya gagara. Kuma jiya a yanda suka bar gidan yana cikin wani yanayi yasa sukai suspecting ɗin kosu baba malam ɗinne suka turo aka saceshi. Shiyyasa papa na isowa maganar gidan suka fara faɗa shiyyasa yace su kawosa.......

★★

           Baba malam da Kubrah kusan a tare suka shiga falon. Shi ya fitone wajen Yoohan ɗin dan yanason su tattauna ta yanda ya kamata Yoohan ya fara neman ilimin dazai taimakamasa wajen bautar ALLAH. A tunaninsa zuwa lokacin ya kammala cin abincin da Nu'aymah taje kai masa. Dan rashin dawowar tata baisa sun zargi komaiba da ga shi har Umm. A tunaninsu ko bayan takai masan ta shiga sashen Hajjo ne ko kuma Addah.
       Da sauri ya ƙarasa ga N'aymah daya hango ƙasa wanwar, ga kuma falon babu alamar Yoohan ɗin sai ƙamshin turarensa kawai. Tiren abincin data kawo yana a ajiye a inda ta ajiyesa.
       “Ya ALLAH! K lafiya kuwa mamana? Mikikeyi kwance anan haka?!”. Baba malam ya faɗa yana kai hannu ga Nu'aymahn. Da sauri ya zabura dan jin jikinta yayi sanyi ƙalau ya saki. Yay azamar maida yatsunsa biyu wajen ƙofar hancinta. ‘tabbas bata numfashi’ ya ambata a zuciyarsa yana ɗagota gaba ɗayanta.
     Hakan yayi dai-dai da ƙarasowar Kubrah da tun shigowar baba malam tana biye da shi, sai dai shi bai gantaba sai yanzun data ƙaraso garesu da dauri tana faɗin, “Abbah lafiya? Miya faru da ita ne?”.
       Cikin tashin hankali baba malam yace, “Ban saniba nima Khadijah, kinga miƙo ruwa dan bata numfashi”. 
    A hanzarce ta ɗakko masa ruwan da Yoohan yasha ya bari, ya miƙa hannu ta tsiyaya masa. shafama Nu'aymah yay a fuska. sai dai ko motsi batayiba balle ai tunanun zata farko. Hankalin baba malam ne ya sake tashi matuƙa. Ya ɗago idanunsa da sukai jajur ya kalli Kubrah.
        “Khadijah maza kiramin Ahmad ko malam ƙarami ko Omar. duk wanda kakaci karo dashi cemasa ya fiddo mota”.
      Amsawa tai da to tana fita da sauri. Sai dai maimakon ta wuce aiken da akai mata saita samu waje ta laɓe abinta tana wani taɓe baki da sakin murmushin mugunta. Zuciyarta fes take akan halin da Nu'aymahr ke ciki. Ita ta mutu kota rayu hakan ba damuwarta bace a yanzu. Dan ita kaɗai tasan miyasa take bala'in jin zafin yarinyar.

      Baba malam da baisan Kubrah bata tafi aikansa ba ya ɗakko Nu'aymah gaba ɗayanta ya fito. Da sauri Kubrah data hangosa ta sake maƙewa tana zaro ido waje. dan batai tunanin baba malam zai fito da Nu'aymah ba yanzun, a tunaninta ko saita kira ɗaya daga cikin wanda ya aiketan.
    Oho shi hankalinsa ma bai kai gareta ba. Jikinsa na tsuma bakinsa na ambaton ALLAH ya nufi harabar gidan. cikin sa'a kuwa sai hakan yay dai-dai da fitowar malam ƙarami daga sashin su Kubrahn hannunsa ɗauke da leda da key ɗin mota.
      “Abba lafiya? Miya sameta?”. Malam ƙarami ya faɗa a ruɗe yana nufo baba malam dake ɗauke da Nu'aymah.
      Da sauri baba malam ya bashi amsa da, “Maza buɗemin mota malam ƙarami, yanzu ba lokacin sanin mafari bane ba”. Cikin sauri malam ƙarami ya cika umarnin baba malam. ya karasa ga motarsa ya buɗe. Baba malam na ƙoƙari sakata a ciki Kubrah ta ƙaraso wajen. Tamkar an kira Hajjo sai gata itama ta fito daga sashenta ita da Husnah da alama ma fita zatayi.
      A rikice ta nufesu tana tambayar ba'asi. Dan taga yanda baba malam ya saka Nu'aymah a motar tamkar bata da rai. Babu yanda baba malam ya iya dole yayma Hajjo bayani a taƙaice. Kubrah na ƙoƙarin shiga motar dan a tafi da ita Hajjo ta tureta gefe ita ta shi. Yayinda Husna ta ƙirƙira cikin gidan da gudu tana ƙwalama Umm kira tana kuka. Dan ita a zatonta Nu'aymah kota mutune. Yarinyace ƙarama bata wuce 9years ba. Itace autar amaryar Abbah Musbahu.
         Fara fitowar mutanen gidan saboda ihun Husna yay dai-dai da ficewar motar da aka sakata daga gidan. Sai dai suna fitowa idon Baba malam ya sauka akan su Yoohan. Da mamaki ya tsaida malam ƙarami dake ƙoƙarin hawa titin layin. buɗe motar yay ya fita yana faɗin, “Malam ƙarami kuje asibitin ina zuwa. da alama wajen nan babu lafiya dan kamar Yahya ne”.
         Daga malam ƙarami har Hajjo dake baya riƙe da Nu'aymah tana faman jijjigata da tofa mata addu'a basu fahimcesa ba. Sai malam ƙaramin yabi umarni. 
         
        Cikin nutsuwarsa ya ƙarasa garesu tare da yin sallama duk da alamarsu bai nuna na waɗanda ya dace yayma sallamarba. Sai bai saniba ko akwai musulmai a cikinsu. Ai ko cikin sa'a sai gashi wasu daga cikin ƴan sandan sun karɓa masa. Harda ma risinawa suna gaishesa dan darajar da ALLAH yay masa ta babban mutum kuma jagora.
      Ya amsa musu ne idonsa akan Papa da sukema juna kallon sani. Kusan a tare papa da baba malam suka ambaci sunan juna.
     “Pastor Goshpower!”.
“Sheikh Sooraj Hashim!”. 
       Sai kuma kawai sukaga Papa ya kece da dariya yana tafa hannu. Ya sake nuna Baba malam yana faɗin, “Da gaske Sheikh Sooraj nake gani anan?”.
       Kafin baba malam dake kallonsa fuskarsa babu yabo babu fallasa ya bashi amsa Solomon yace, “Sir! Ai shine mutumin da.......”
      Malalacin kallon da Yoohan ke masane ya hanasa ƙarasawa, yay saurin duƙar da kansa ƙasa yana haɗiye sauran maganar.
      Kallon Yoohan baba malam yayi. Sai kuma ya sauke wani lallausan murmushi. Cikin halin dattako irin na masu ilimi da sanin ya kamata yace, “Yahya ka sanshi ne?”.
      Kai Yoohan ya jinjinama baba malam, kafin a hankali yace, “Mahaifina ne”.
         Sosai alamar mamaki ya bayyana ga baba malam, dan fuskarsa ta nuna ƙuru-ƙuru. Yace, “Yahya da gaske?”.
      Kafin Yoohan yay magana Papa da yay matuƙar tsuke fuska ya matso gaban baba malam ɗin yana faɗin, “Mizaisa ya maka ƙarya?”.
      Kamar baba malam zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana sake dai-daita nutsuwarsa. Kusan sakanni goma kafin yace, “Okay! Alhmdllh. Inaga to muƙarasa ciki tunda yau gashi kazo gidana.....”
        “Never!”. Papa ya faɗa cikin saurin katse baba malam ɗin.
     Da sauri Yoohan yace, “Papa saboda mi?”.
     Kallonsa papa yayi da tsananin ɓacin rai. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya sake maida kallonsa ga baba malam dake murmushi.
        Baba malam yace, “Kayi haƙuri, dan kai yau sunanka baƙona. Ka cancanci na karramaka da masauki da abin ci da sha. Dan koba komai kazo ƙasata ne, yankina, gidana kuma”.
       Tsaki papa ya ja. Tare da kallon d.p.o Emanuel yace, “D.p.o kama shi, inason sanin dalilin alaƙarsa da yarona”.
      “What!!?” Yoohan ya faɗa a zabure yana ƙarasowa gaban papan. Cikin nuna fusata yace, “Papa mi kake shirin yi haka? Dammi zakasa a kamashi bayan ba'a cikin gidansa ka ganniba. Sannan ba tare da shi ka ganni ba”.
        “Rufema mutane baki!!. Karna sake jin bakinka anan. Wannan wasane tsakanin manyan daji guda biyu. Ka shiga mota yanzun nan zamu koma Abuja da kai”.
       “Babu inda zanje papa. Domin aikina ne ya kawoni nan. Banga kuma dalilin dazaisa na barshi ba akan dalili mara tushe. Ku kuma (ya faɗa yana nuna police ɗin) duk wanda yay gigin matsowa koda kusa da shi ne na rantse da ALLAH sai ya rasa aikinsa. Idan kunji ƙarya zaku iya gwada hakan kuma”.

      Tashin hankaline ƙarara ya bayyana a fuskar d.p.o Emanuel. Dan shi kam an sakashi a tsaka mai wuya. Matsayin papaa a garesa ya wuce duk yanda mai karatu zaiyi hasashe. Sannan ɗansa Yoohan basai an faɗaba, yanada faɗa aji ga gwamnatin kowacce jaha saboda rawar da yake takawa akan harkar lafiya dama matsayinsa na babban likita da duniya gaba ɗaya ke ji da gani a yanzu. Dan tabbas yaron yana lokaci da lokacinsa.
          “Yahya! Iyaye nada matuƙar daraja ga ɗa. Ka daina tsaurara harshenka ga mahaifinka kaji. Karka damu da tsakanina da shi, dan a yau a yanzu ya fini gaskiya tunda a wajena ya sameka. Ba'a wasa da iyaye. Dan haka karka sake maida masa magana kaji”. Baba malam ya faɗa idanunsa akan Yoohan dake ta faman haɗiyar zuciya da sauri-sauri.
     Kai kawai ya ɗaga ma baba malam, dan zuciyar tazo wuya bazai iya magana ba. Ya watsama guards ɗinsa wani shegen kallo. Kafin ya raɓa papa da baba malam ya bar wajen batare da yayima kowa maganaba.
             Papa da yasan minene fushin Yoohan yay saurin bin bayansa yana kiransa. Amma ko kallonsa baiyiba balle ya saka ran amsawa. Ya buɗe murfin motar a fusace ya shiga baya, shima Papa ɗayan gefen ya zagaya ya shiga yana cigaba da kiran sunan sa. Hakanne ya saka drivern sa da Solomon saurin shiga suma, sauran guards ɗinsa da su Emanuel da suka sami mafita suma suka nufi nasu motocin batare da suncema baba malam komaiba.

             Nannauyan numfashi baba malam ya sauke lokacin da mitocin suka harba kan titi. Yayinda can ƙasan zuciyarsa ke mamaki da jinjina al'amarin UBANGIJI. ‘Yoohan ɗan Pastor Goshpower ne da gaske? Lallai UBANGIJI mai yin yanda yaso, a lokacin da yaso, ga kuma wanda yaso’. Baba malam ya faɗa a fili. Yasan tabbas UBANGIJI shike fidda rayayye a cikin matacce, ya kuma fidda matacce a cikin rayayye. Amma al'amarin akwai ɗunbin ban al'ajabi a cikinsa, dan yasan abubuwa masu yawa game da papa tun shuɗaɗen lokaci kafin yakai haka.
       Da wannan tunanin baba malam ya koma cikin gidan, inda ya tadda duk jama'ar gidan sun fito sunata tararrabin abinda akace ya faru da Nu'aymah. Su Abban Abdallah ma shirin shiga mota suke zasubi bayansu asibitin.
    Ganin baba malam ya sakasu dakatawa, duk suka nufesa hankali tashe suna tanbayar yaya Nu'aymahn.
        Tausayinsu ne ya kamashi. dan haka cikin taushin murya ya kwantar musu da hankali, tare da sanar musu shima yanzu zai bisu. Basu zauna ɓata lokaciba suka ɗunguma a mota ɗaya Omar ya jasu, akabar su Umm a gida na binta da addu'a.

       Yoohan da tunda suka tafi ya ƙi kula papa daketa so yayi magana yay kwance jikin kujera hannunsa dafe da goshinsa cike da tsananin takaicin abinda ya faru tsakaninsa da Nu'aymah yauma. Yarasa mike jan hankalinsa ga aikatama yarinyar nan wannan banzan ɗabi'ar?. Abinda ba halinsa ba amma yana ƙoƙarin ɗabi'antar da shi a gareta. Saima yaji na yau yafi masa zafi a rai fiye da na jiya.
      Da sauri ya kwanto jikin papa saboda wata hajijiya-hajijiya dake neman kwasarsa. Sake rikicewa papa yayi. A matuƙar ruɗe ya shiga girgiza Yoohan kai kace gani yay baya numfashi.
        Sosai takaici da hayaniyar papa ta sake rufe Yoohan ɗin, amma sai ya daure cikin taushin murya da sanyayata yace, “Papa Please relax. Ina lafiya fa”.
       Da sauri ya rungumeshi yana sauke numfashi a jajjere. Su dai su Solo suna kallon ikon ALLAH daga gaba. A haka suka ƙarasa hotel ɗin da har yanzu akwai sauran yaran Ema... Da taimakon papa Yoohan ya fita, shine ya kamasa har ɗakin da yake. Su kuma su Solomon suka dakata wajen manager ɗin hotel ɗin suna musu bayani akan anga Yoohan ɗin su kwantar da hankalinsu.

         Papa na zaune kusa da Yoohan dake kwance idanu a lumshe, hannunsa har yanzu dafe yake da kansa. Yama rasa wane kalar tunani ya dace yayi akan matsalarnan guda biyu. Alaƙalar Papa da Baba malam. Abinda ya aikatama Nu'aymah a karo na biyu. Buɗe idanunsa yay a hankali kan papa da yay shiru shima yana wani tunani can daban, sai da yay masa kusan kallon sakan goma kafin cikin nuna kulawa ya kamo hannunsa cikin nashi da faɗin, “Papa!”.
       Firgigit ya dawo hankalinsa tare da kallonsa. Yoohan ya sake lumshe idanu ya buɗe a kansa. “Papa dama kasan malamin nan ne?”.
     “Yoohan! Wannan tambayar taka bata da muhimmancin samun amsa. Kai ya kamata nasan minene alaƙarka da shi?”.
       Kamar Yoohan ya faɗi ainahin gaskiya sai kuma wata zuciya ta gargaɗesa dayin hakan. Yunƙurawa yay ya tashi zaune sosai ya jingina da fuskar gadon. Hannunsa ya sake maidawa cikin na papansa, cikin kwantar da murya yace, “Papa akwai abinda nake buƙata a wajensa, shiyyasa na kwantar da kaina nake binsa a sannu harna cimma burina. Sai dai kuma gashi kai kazo cikin mintuna goma kacal kana shirin rusamin shiri na. Miyasa zaka biyema su Solomon da shirmensu? Ai koda suka sanar maka na ɓata ko tunanin inda za'a'a sameni kamata yayi ka jira harna dawo kaji ta bakina. Haba papa da girmanka a ƙasarnan amma kake abu tamkar wani mara.......”
      Saurin katsesa papa yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. hakanne ya saka Yoohan haɗiye sauran maganar tasa. Papa ya gyara zamansa sosai da cewa, “Naji nayi kuskure, amma kaima harda laifinka. Miyasa tun tuni baka sanarmin ba, bayan kasan niɗin mai baka goyon bayane akan kowanne irin business naka musamman a wannan yakin”.
       “Nima naji nayi kuskure to. Amma ina da dalilin ɓoyewar ai. Da ace na sanar maka mi nake shirin yi zaka iya ɓatamin aiki dan kanada gaggawa papa. kai kafi son komai da zafi-zafi a lamarinka. Hakan kuma na taɗiyeka daga nasarorinka. Yanzu da ace bakazo ba da cikin satin nan zan kammala aikina. Amma yanzu kaga ka kawo min togaciya dan zai fara kokwanto a kaina. Kaga kenan saina sake sabon ginin da zai ƙara yarda dani hundred percent kamar farko”.
     Cikin tsananin jin daɗi papa ya rungume Yoohan yana faɗin, “I am sorry my sweetheart, kai ɗinne ba'a gane kanka sai kaso. Yanzu dai na maka alƙawarin da kaina zan gyara abinda na ɓata a yau ɗinnan kaji”.
        Ɗagowa Yoohan yay da sauri, yace, “Papa da gaske kakeyi?”.
     “Ƙwarai kuwa my dear son”.
Wani lallausan murmushi Yoohan ya saki najin daɗi. Dan ya fahimci lallai sai ya nunama papa akwai manufa a tafiyarsa da baba malam sannan zai samu nutsuwar samun damar fahimtar ilimin addinin islama da zai kare kansa anan gaba a wajensu dama duk wani dake a cikin ahalinsa da yasan zai kawo masa togaciya. Amma a yanzu yasan duk yunƙurin da zaiyi sai sun taɗesa saboda rauninsa na kasancewa sabo cikin addini mai ɗunbin haske irin musulinci. A yau kawai daya kasance a ciki jinsa yake tamkar sabon mutum. Tamkar darajarsa ta ƙaru. Duk wani nauyin zuciya da ƙunci da yakan tsinta kanshi a ciki a baya yau sai yaji tamkar ansa kwano an kwashesu tas.
       Jikin papa ya sake lafewa tare da lumahe ido. Papa ma dake jin daɗin Yoohan ya fara ɗaukar huɗubarsa ya shiga shafa kansa cike da jin daɗi da annashuwa. Dan shima har zuciyarsa ta gama shirya masa babban aiki akan baba malam tsaf............✍

Tofa masu karatu. Yanzu za'a fara wasan😎 dan haka kumuje zuwa filin daga😉😱🚶🏻.
       


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/23, 10:10 AM] +234 816 133 8078: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


*_BARKA DA JUMA'A. ALLAH yasa muna cikin bayin da zasu sami gafara a cikinta😭🙏🏻_*


No. 33

..........Koda suka isa can ɗinma wasu jerin motocinne sukazo tarbarsu tare da bodyguard ɗin papa. Haka suka nufi gida zuciyar Yoohan sam babu daɗi.
     Sun sami tarba da ga ahalin nasu, musamman ma Yoohan da ya jima dama baya ƙasar. Shima yaji daɗin ganinsu sosai, musamman kakarsa data haifi Papa da ƙannen papan su uku mata da yaransu da ya gani sunzo musu, ga kuma kakarsa data haifi Mom itama dai bata komaba har yanzun.
     Madam Chioma sai tattalinsa take kamar ta haɗiyesa dan farin cikin ganinsa, gashi taga ya wani ƙara mata ƙyau da kwarjini da cikar haiba kamar wanda akaima wankan iji. 
     Haka dai ya daure yana biye musu sama-sama dan kamar ko yaushe fuskar dai babu walwala. Ƙasan ransa ma basusan cike yake da tashin hankalin ganin yanda suka cika gidanba tamkar masu biki, musamman da ya san baƙar ƴar tsamar dake tsakanin kakanninsa guda biyu. A yanzu ma haka ya tabbata wannan zuwan na kakar tasu yanada nasaba da zaman mama Deborah Abujan.
     Da ƙyar ya iya zaman mintuna goma a falon ya gudu sama a cewarsa zai watsa ruwa ya dawo. Yana shiga ya ja tsaki tare da dafe kansa. Zama yay cikin kujerar dake ɗakin ya zaro wayarsa a aljihu, sai faman yamutse fuska yake dan har yanzu ransa a ɓace yake akan dawowar dole da papa ya sakashi yi. Wayar ya shiga sarrafawa cike da ƙwarewa. Kansa tsaye yay kiran number baba malam dan yana buƙatar yin magana da shi. Cikin sa'a kuwa bugu uku ya ɗaga. 
           Sai da suka gaisa Yoohan yace, “Uncle mun iso gida, amma nifa gobe zan dawo kano”.
       “Alhamdulillahi, barkanku da hanya. Amma mizaisa ka dawo Yahya?”.
        Fuska ya ɓata kamar yana gaban baba malam ɗin, cikin nutsuwarsa da taurin kai irin na samari masu ji da lokacinsu yace, “Uncle ina buƙatar neman sani akan addinin musulinci. Ta wannan hanyarne kawai zan iya yaƙar duk wani ƙalubalen da nake hange da ga ƴan uwana. Ta hanyar neman ilimin ne kuma kawai zan bautama UBANGIJINA. Ba tsoro nake duk wanda ya sanni yasan na zama musulmi ba. Kawai ina buƙatar kwankwaɗar madarar ilimine nima cikin kwanciyar hankali”.
     Sosai baba malam yay murmushi har Yoohan na jiyo sautinsa. “Yoohan karka damu kaji, bama sai ka dawoba, inason kabi komai a hankali kamar yanda ka faɗa. Akwai ƙanina dake anan zaune abujan amma yana nan basu koma bikin salla ba, dama na shirya masa magana kawai zaka ringa ɗaukar karatu a wajensa tunda anan kafi zama fiye da nan kano, kaga zaifi maka sauƙi ko kuwa?”.
          Ɗan jimm Yoohan yayi alamar tunani, bawai hakan bai masa baneba. A'a tunaninsa shine yanayin aikinsa, dan ya tabbatar a nan abujar ma ba samun zaman yake ba. Yanzu haka kwanaki biyar kawai zaiyi ya wuce Lagos. daga can kuma zai shiga Maiduguri. Yana da tabbacin kuma da wahala ya ƙulla wata guda bai sake barin ƙasarba ma........
       “Yahya ko akwai damuwa ne?”. Baba malam ya katse masa tunaninsa.
    Ajiyar zuciya ya sauke, tare da miƙewa ya taka jiki a sanyaye zuwa bakin gadonsa ya sake zama. “Uncle babu komai. Kawai dai ina duba yanayin aikina ne da baya barina zaman waje ɗaya, sai nake gani kamar hakan zaiyi wahala a gareni. Inba dai ajiye aikin zanyiba kawai na fuskanci karatun.....?”.
       “A'a Yahya bazai yuwuba, duk da bansan ya aikin naka yake ba bazan baka shawarar ajiye aikinka ba. Dan mu musulinci addini ne dake son mutum mai neman na kanka. Ta hakane zaka kare mutuncinka da tarbiyyarka, ka kuma nema halalinka harka tausayama na ƙasa da kai da marayun ALLAH. Yahya karka manta kaifa bawan ALLAH ne mai yawan hidima, sannan bayane goya marayu. Idan ka ajiye aiki yaya masu jira daga garekan zasu kasance kuma?. Kaf Annabawan ALLAH tun daga farkonsu har zuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gareshi, tarihi ya nuna mana nauyin dake kansu na yaɗa kalmar ALLAH baisa sun rayu a rashin neman na kansuba, balle ai tunanin zama daga jiran na wani ko taskar masu mulki. Dukansu sunada sana'oinsu. To inhar mutane masu daraja irinsu sun yi gwagwarmayar neman halalinsu mu su wanene da bazamu tashi munema na kanmu ba”.
       Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Murya a sanyaye yace, “Hakane Uncle. Tunanin hakan baizo min a rai ba shiyyasa”.
        “Karka damu ALLAH yana tare da mu. Insha ALLAHU mafita zatazo daga UBANGIJIN rahama da jinƙai”.
      “To shike nan Uncle nagode sosai. ALLAH ya ƙara lafiya da tsahon rai. Bara na barka ka huta dan yanzu na sami nutsuwa, ɗazu kam hankalina a tashe yake sosai”.
     Ƴar dariya baba malam yay masa sukai sallama ran Yoohan fes. Da ƙarfin zuciyarsa kuwa ya miƙe ya fara zame kayansa dan son watsa ruwa.

★★★

         Tunda suka ajiye wayar baba malam ya shiga dogon nazari, harga ALLAH yana jin son Yoohan cikin ransa. hakan har mamaki yake bashi wani lokacin. Duk da yasan UBANGIJI kan jefa soyayyar wani a zuciyar wani batare da wata alaƙa ba a tsakaninsu 
      Har yanzu baisan abubuwa da yawa ba dangane da Yaron ba, amma sai ya keji zuciyarsa na tsananin ƙyautata masa zato akan abubuwa da dama na rayuwar yau da gobe. Haɗuwarsu ta uku kenan kacal. Amma ya fahimci wasu ƙyawawan halayya da ko a cikin musulman ma ba kowane ke da su ba. Ga ƙyauttawa da yarda da yaron ke bashi ɗari bisa ɗari.
    Numfashi ya ɗan sauke wani gefen zuciyarsa na sake ƙarfafa masa gwiwa akan alkarin da yake shirin aikatawa. Yayinda can kuma wata ke gargaɗarsa musamman akan ahalin da Yoohan ɗin ya fito.........
         “Malam lafiya kuwa ka zurfafa a tunani haka?”. Umm data shigo tun ɗazun tanata sallama bai jiba ta faɗa tana mai katsesa.
    Ajiyar zuciya ya sauke da sauri tare da kallonta. Gefensa ya nuna mata da hannu alamar ta zauna. Batare da tayi musu ba ta zauna kuwa idanunta a kansa. Hannunsa ya saƙala cikinnata yana ɗan sake furzar da huci. “Jannat wani al'amarine yanzun nan UBANGIJI ya saƙaminshi a cikin tunanina akan yaron nan dana sanar miki jiya ya musulunta. Sai dai kuma wani sashi na zuciyar tawa yana gargaɗina dason jefani a kokwanto game da al'amarin”.
      “Tom nidai a nawa tunanin sai naga kamar shaiɗanne Malam. mizai hana ka bama al'amarin wani ɗan lokaci haka, sai ka duƙufa neman zaɓin ALLAH akan yuwuwarsa ko barinsa”.
     “Eh tabbas kinzo da shawarar hankali Jannat. Insha ALLAHU kuma zanyi amfani da ita. Amma kema inason ki tayani dan ALLAH”.
      “Insha ALLAHU zan tayaka Abban Nu'aymah, ALLAH ya tabbatar mana da alkairinsa”.
      “Amin ya rabbil-alamin”. Ya faɗa cike da jin nutsuwa da gamsuwa akan shawararta”.
    

______________★★★

             Kwanakin Nu'aymah uku a asibiti aka sallamota. Alhmdllh jikinta yayi ƙyau sosai, sai dai haɗarin da Doctor ya tabbatarma iyayenta tana a ciki akan iya fuskantar loosing mamory shine ya jefasu a cikin matuƙar damuwa.
       Yayinda ita kuma da batasan mike faruwa ba sai tata matsalar ta zama Naser. Dan a kwanaki biyun nan daya ɗauka da zuwa gaba ɗaya ya takurama kowanne irin motsinta. Duk da daga gaisuwa babu abinda ke sake haɗasu sai magana kamar kowa. Amma kallon da yake jifanta da shi da tarewa a asibiti da yayi ya tabbatar mata cewar zuwan nasa akwai manufa.
      Tun bayan dawowarsu gida Umm ta taimaka mata tai wanka taci abinci da magungunanta ta kwanta danta huta. Shine ta samu damar yin tunani akan Naser ɗin. Kamar daga sama ta dinga jiyo hayaniya na tashi a gidan, sosai mamaki ya kamata, duk da ta tabbatar hayaniyar bata faɗa bace tasan wannan ba ɗabi'ar mutanen gidansu baceba hakan. ‘To minene ya faru?’ ta faɗa a fili cikin sake zurfafa mamakinta. 
     Kusan mintuna ashirin sai kuma taji hayaniyar ta lafa. bata ko motsa ba balle ai tunanin zata fita ta ganoma idanunta, haka ta cigaba da kwanciyarta tun tana tunani har barci mai nauyi ya ɗauketa saboda a maganin nata akwai na barci daman.

        Kiran sallar magriba ne ya saka Umm shigowa ɗakin Nu'aymah ta tadata. Da ƙyar ta samu ta tashi dan barcin nata yayi nisa sosai. Taimaka mata tayi tai alwala kafin tai yunƙurin fita zata barta.....
     “Umm wai hayaniyar mi naji anayi ɗazun?”. Ta faɗa cikin katse hanzarin Umm dake ƙoƙarin fita.
       Batare da Umm ta juyo ta kalleta ba tace, “Su Abdallah ne, sunma shigo dubaki kina barci”.
      Sosai gaban Nu'aymah ya faɗi, sai dai kafin ta sake cewa wani abu Umm ta fice abinta. Shiru tai tsaye hannunta riƙe da hijjab, dan zuciyarta cike take da tambayoyin miya kawo su Yah Ab ɗin gida a yanzun bayan kuma shine da kansa yacema Hajjo sai bikin su aunty Hajarah daya rage saura kwanaki ashirin cif yau ayi. Ganin bata da mai bata amsarta sai ta saka hijjab ɗinta ta kabbara salla kawai.
       Koda ta idar bata fitaba tai zamanta a ɗaki, sai da tai sallar isha'i da shafa'i da wutiri sanna ta fito falonsu danta ɗansha iska. Umm kawai ta tarar zaune. Ta zauna kusa da ita tare da ɗora kanta a gefen kafaɗarta.
     Ɗan kallonta tayi, kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta ɗaura hannunta a wuyanta. Jin jikinta babu wani zafi ya saka Umm sauke ajiyar zuciya da janye hannunta.
      “Umm nafa warke”. Nu'aymah ta faɗa tana murmushi dajin ƙaruwar ƙaunar mahaifiyar tata a cikin rai. Itama Umm Murmushin tayi, ta shafa kumatun ɗiyar tata da faɗin, “Ai haka muke fata Nu'aymah, ALLAH ya ƙara miki lafiya dai damu baki ɗaya”.
      “Amin Umm”. Ta amsa mata zuciyarta cike da damuwa. tasan iyayenta suna cike da damuwar halin data tsinci kanta, basu da damuwa sama da lafiyarta, basu kuma da burin da ya wuce su wayi gari suga ta warke.........
      Sallamar Adawiya ta katse tunanin Nu'aymah. Ta ɗan ɗago daga kafaɗar Umm tana amsawa. Sai dai ganin harda Yah Abdallah ya sata maida kan ta sake kwantarwa zuciyarta najin zafin kishi a kansa.
     Rungumeta Adawiya tayi cike da munafincin data saba nunawa idan suna a gaban mutane. Itama sai Nu'aymah ta tarbeta fuskarta fes. Umm dai cike da jin daɗi take dubansu. Yayinda Abdallah kam kallonsu kawai yakeyi. 
     Bayan sun gaisa da Umm, Nu'aymah ta gaida Abdallah batare data yarda sun haɗa ido ba duk da kuwa shi hakan yake buƙata tun ɗazun. A tunaninta zasu tafi ne, amma sai taga sunyi zamansu sunata hira da Umm. Kusan mintuna talatin basu da ko niyyar tafiyar, takaici ya cika Nu'aymah, dan haka kawai yau itama sai takejin zafin Adawiya akan Abdallah. Shiyyasa hirarma bata saka baki, tana lafe jikin Umm tamkar wata mage.
      Basu bar sashen ba har sai da Baba malam ya shigo gidan, dama shi suke jira. Zama kuwa yay suka gaisa a ransa yana mai jin daɗin ganin yanda Adawiya ta kwantar da hankalinta. Yanda tai ƙiba ta ƙara ƙyau kawai ya isa fahimtar da mai kallonta hankalinta a kwance yake sosai. Barci ne ya sake kwashe Nu'aymah har suka bar sashen bata saniba. Koda Umm datai tunanin anan Adawiya zata kwana amma taga saɓanin hakan sai da ta tashe Nu'aymahr ma ta rakata ɗakinta saboda barcin da tayi.

       Washe gari Nu'aymah ta tashi ne duk a takure. Ba komai ya jawo hakanba sai zuwan su Yah Ab da zaman Naser a gidan. Maƙalewa tayi a sashensu taƙi fita har rana. Sai da Umm ma ta takura mata ɗaukar abincin Hajjo ta kai mata sannan ta fita badan taso ba.
       Tunda taga takalma birjik a ƙofar Hajjo taji kamar ta juya. Amma gudun kar Umm tai mata faɗa sai ta daure tayi sallama. Sai da aka bata izinin shiga sannan ta shiga da wata sallamar a bakinta. Duk samarin gidanne a she. Sai Rufaida da Hajjo. Nu'aymah ba wani shiri sukeyi da Rufaidah ba itama, dan ta girmesu, gata kuma da shegen son girman tsiya, shiyyasa take ganin sai dai su bita. Ita kuma Nu'aymah tsiwa. 
      A tare kawai tace dasu “Ina yinin ku”. batabi takan dawa-dawa ya amsa ba ta nufi Hajjo daketa binta da kallon jin daɗin ganin jikinta ya sake warwarewa.
     “Hajjo barka da gida. Ga abinci inji Umm na”.
     “To takwara sannu kinji, yaya jikin naki?”.
     “Naji sauƙi Hajjo”.
   “Alhmdllh ai haka akeso dama. Tun ɗazun nake tsumayen ganinki amma shiru. Tashi ki duba a firiji na ajiye miki fura”.
     Sosai daɗi ya kanata. Cike da ɗoki ta nufi fridge ɗin hajjo ta ɗakko kofin furar tana sakema hajjo godiya. Har zata fice Naser ya kirata. Badan tasoba ta amsa tare da juyowa tana kallonsa. Ya sakar mata sassanyan murmushi tare da miƙewa ya nufo inda take tsaye. Bayare da yay magana ba yay gaba da mata alamar ta biyoshi.
      Bataso hakanba, amma sai ta bisa kawai gudun kar yaga kamar ta masa wulaƙanci. Ɗaya daga rumfar bunun da aka jera guda uku a harabar gidan ya nufa. Nu'aymah ma dai na biye da shi. Kujera ya ja mata baya yace ta zauna. Nanma bata musaba tayi yanda yake buƙata. Sai da ta zauna sannan shima yaja wata ya zauna. 
     Yana zama Abdallah na isowa wajen kamar daga sama. Daga ita har Naser kallonsa sukai. Yayi kicin-kicin da fuska tamkar zai fasa ihu. Batare da yace dasu uffanba yaja kujerar ɗanyan gefen Nu'aymahn ya zauna suka sakata a tsakkiya.
       ‘Ikon ALLAH ’. Nu'aymah ta faɗa a cikin ranta tana kallonsu da mamaki. 

     “Alhaji lafiya kuwa?”. Naser ya faɗa a lalace yana kallon Abdallah. Murtani Yah Ab ya maida masa cike da dizgi. “Itace ta kawo haka”.
      “Humm!” Naser ya faɗa yana ɗauke kansa daga garesa ya maida ga Nu'aymah da mamaki ke cigaba da nuƙurƙusarta a zuciya.
      “Kayi haƙuri ka bamu waje magana nakeson yi da ita Abdallah”.
     “Wannan isar ce kuma baka yiba. Duk abinda zaka faɗa mata inhar kasan ba mara ƙyau bane ka faɗa a gabana mana”.
       “Mtsoww! Ai kasan baka isa sakani yin abinda banyi niyya ba. Nu'aymah tashi muje can...”
       Batayi niyyar binsaba a yanzu. Tayi niyyar kawai tabar musu wajen. Sai dai tana yunƙurawa zata miƙe Abdallah ya daka mata tsawa. “Koma ki zauna kona mareki!!”. Ya faɗa yana ɗaga hannun tamkar zai maketa.
       Ɓata fuska sosai tayi tamkar zata fasa kuka. Dan ita kam sun sakata a tsaka mai wuya. 
     A fusace Naser yace, “Abdallah karka bari nakai bango da kai, wai shin ina ruwanka dani ne? Naga dai Nu'aymahr nan ba matarka bace balle kace zakama mutane iko. Idan ada kayi ikon saboda akwai alƙawarin aure a tsakaninku yanzu saika tuna babu wannan. Ita ɗin allura ce cikin ruwa mai rabo ka ɗauka........”
     “Nine mai rabon kuma insha ALLAHU!!, dan haka ka kama kanka karka bari a jimu da kai Naseer”. 
       “Hhhhhh! Abin dariya. Sannu Abdallah ubana mai bani umarni. ai ka sani kayi sake tun a farkon dama, a yanzu kuma ta suɓuce maka har avada. A da canma dan ba'a bata dama bane akaso mata auren dole da kai, amma sai UBANGIJI yay dubeta ya hana hakan.....”
        “Naser!!!” 
Abdallah ya kirashi cikin ƙaraji da fusata tare da dunƙule hannu tamkar zai kai masa naushi. Ƴar zabura baya Naser yayi kamar irin yaji tsoro ɗin nan. Sai kuma ya kwashe da dariya ya kuma ɗaure fuska duk a lokaci ɗaya. “Oh to ko dukan nawa zakayi ne?!”.
          Bai gama rufe baki ba kuwa Abdallah ya kai masa naushi. Da sauri Naser ya duƙe naushin yabi iska. Ya sake kai masa wani Baba malam da ke bayansu shi dasu Abbah ya daka musu tsawa.
      “Kai!! wane irin shashanci ne haka kukema mutane a cikin gida da hankalinku?. Ko kunya bakujiba kuka zauna faɗa a gaban ƙaramar ƙanwarku, wannan ai rashin hankaline da sakarci”.
         Duk ƙasa sukai da kawunansu kowa na huci. Abban su Adawiya yace, “Ku wuce muje ciki. Kema Nu'aymah shige”.
        Sum-sum ta wuce tana danne dariyar dake cinta a rai tun fara rigimar yayun nata. Tana shiga falonsu kuwa ta fashe da dariya. Da sauri Umm da Rabi dake a kitchen suna aiki duk suka leƙo.
     “K lafiyarki kuwa kike wannan dariyar ta rashin hankali?”.
      Hannu Nu'aymah tasa da sauri ta danne bakinta, da ƙyar ta haɗiye dariyar tata sannan ta kalle su. “Wlhy Umm su Yah Ab ne suka bani dariya”.
     Batare da Umm ta tsaya jin ba'asi ba tai tsaki ta koma kitchen. Rabi kam sai ta nufota tana tambayarta wai miya faru?. Da sauri Nu'aymah ta haɗe fuska tare da zuba mata harara tabar wajen. Itama Rabin da harara ta raka Nu'aymahn, a ranta kuwa faɗi take, ‘Zaki gane shayi ruwa ne yarinya, shegiya mai kama da ƴaƴan aljanu’.
      Oho Nu'aymah batasan tanai ba. Dan tuni ta shige ɗakinta. Sai dai itama a ranta tana matuƙar mamakin munafunci irin na Rabi. amma sam Umm ta kasa fahimtar akwai wani abu a zuciyar Rabi, dan ita ta jima da fahimtar hakan, harma a ranta tana zargi Rabin da ɗaukar sirrin Umm tana fitarwa. Dan akwai ranar data taɓa ganinta bayan ɗakinsu tare da wanda bata fahimci namiji ne ko mace ba suna magana. Sai dai kafin ta zagaya taga wanene ta iske sunbar wajen Rabin ma harta shigo ciki. Tun daga lokacin ta saka mata kahon zuƙa. Taso fahimtar da Umm amma saita hauta da faɗa akan batason wannan halin banzar, dan Rabi a haife ta haifi Nu'aymah harma wanda ya fita. Kuma tun Nu'aymah na ƙarama suke tare ita bata taɓa ganin wani abu mara ƙyau daga gareta ba.
    Tsaki tayi kawai da kauda zancen Rabi a ranta ta koma tuno su Abdallah. Haka kawai takejin al'amarin nasu na sakata nishaɗi. Ba sai an faɗa ba kowa yasan tana tsananin son Abdallah, ƙaddara ce kawai ta shiga tsakanin al'amarinsu. Amma a yau sai kawai yanda Naser yay sai shima ya birgeta. Har takeji zata iya aurensa duk da zuciyarta bawai tana sonsa bane ba. Amma tunda ta haƙura da Yah Ab zata iya maye gurbinsa da Naser ɗin. Sai dai fa tasan lallai akwai ƙura a cikin faruwar hakan kuma.

★★★

      A ɓangaren su Abdallah kuwa faɗa sosai su Baba malam sukai musu akan abinda suka aikata. Dan a gabansu mafi yawan rigimar ta faru shiyyasa basu bi takan jin yanda akai ba. Sai da baba malam ya tabbatar jikinsu yayi sanyi sannan ya ɗora musu da nasiha kuma, ya kuma sakasu bama juna haƙuri sannan suka sallamesu.
        Suna fitowa kowanne ya wurgama ɗan uwansa harara da jan tsaki.............✍

Kuyi manage Please, inada baƙi😒🚶🏻.



_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.




[5/22, 10:26 PM] +234 809 502 2953: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 34

............Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana na neman zama babba. Dan kuwa dai rikici sosai ke wakana a tsakanin Abdallah da Naser akan Nu'aymah. Amma sai suka canja taku yanda iyayensu bazasu fahimta ba. A duk sanda Naseer yasa aka kira masa Nu'aymah sai Abdallah yazo ya tsare. Hakama duk lokacin da Abdallah ya buƙaci ganawa da Nu'aymah sai Naser yazo ya hana hakan ta hanyar zama tsakaninsu kamar yanda Abdallahn keyi.
      Hajjo da mafi yawan rigimar a sashenta akeyi tana kallonsu amma tai kunnen uwar shegu da su kamar bata ganiba. Wani lokacinma da biyu take sakawa a nemo mata Nu'aymah ta zauna a sashenta dan tasan nanne wajen zaman su Naser ɗin musamman da daddare.
       Duk kuma wannan abun dake faruwa Adawiya bata nan, dan kwanansu biyu da zuwa sukai tafiya biki ita dasu Hajarah dangin kakarsu maman su Addah. Da Addah ta ƙarrafa ayi tafiyar da Nu'aymah ma. Sai dai yanayin jikinta yasa Hajjo hanawa. Shiyyasa suka tafi su uku harda Kubrah sai Addahn da sauran ƴaƴanta na ma'auri.
        
      Da farko rikicin nasu Naser nishaɗi yake saka Nu'aymah, amma ganin al'amarin na sake ɗaukar zafi sai hankalinta ya fara tashi. Dan neman birkita mata tunani sukeyi har takan rasa wanene yafi cancanta ta mallakama kan nata?.
     Al'amarin bai sake tada hankalin kowaba a gidan sai randa Hajjo take cema Abdallah dama ya haƙura ya barma Naser Nu'aymah. Tunda shi a yanzu gashi yana auren su Yusrah. A fusace yace, “Indai su Yusrah ne zasu masa katanga da mallakar Nu'aymah to lallai zai rusa katangar”.
     Babu wanda ya ɗauki furucin nasa da muhimmanci a lokacin da yayisa. Sai dai ga mamakinsu bayan sallar isha'i sai gashi da zungureriyar takarda har guda biyu yazo ya dire gaban hajjo.
      Kallonsa tayi fuska a yatsine. “Kai wannan takardun kuma na miye ka ajiyemin kamar wani ɗan saƙon kotu?”. Fuska a turɓune yace, “Hajjo sakamakon katangar da kika tabbatar min zata shiga tsakanina da Nu'aymah ne a ciki. Kinga yanzu sai ki daina min baki ko”.
        Sam hajjo bata fahimci zancen nasa ba, amma sai ta saka Omar dake zaune tare da ita ya duba mata. Ɗaukar ɗaya yay yana murmushin diramar kakar tasu da yayansu. Da sauri ya fesar da ruwan da ya ke sha yana faɗin, “What!?” saboda abinda yaci karo da shi a rubuce.
       A rikice hajjo tace, “Miya faru Umaru?”. Jikin Omar na ɓari ya ajiye kofin ruwan tare da ɗaukar ɗayarma ya buɗe. Nanma dai abinda ke cikin ta farkon ce a ta biyu, ai baima san lokacin daya furta, “Hajjo wlhy Yah Abdallah ya haukace! ko kuma ya fara shaye-shaye ku bincika!. Hajjo sakin Yusrah da Adawiya fa ya yi.....”
      “Saki kuma?!!” Hajjo ta faɗa itama tana miƙewa zumbur.
     “Wlhy kuwa Hajjo gashi a rubuce saki ɗai-ɗai”.
      “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Abdullahi!!. A wlhy gaskiyarka kuwa Umaru Abdullahi ya haukace. Ni Zainabu na shiga uku. Kaga kiramin ɗan malam duk inda yake yazo gida”.
        Ɗan jimm Omar yayi alamar tunani, sai kuma ya dubi Hajjo da ranta ke a matuƙar ɓace. Cikin lallashi yace, “Amma Hajjo inaga kamar dai kiyi haƙuri har ya dawo gida. Kinga yanzu bamusan wane uziri yake kan yiba, kiran da za'ai masa zai iya dagula masa tunani, amma idan kince a kirasan dai sai na kirasa ɗin”.
      “Hakane Umaru! Kaima kayi maganar hankali, amma lallai sai na saɓama Abdullahi fiye da zato a gidan nan. Wane irin wawancine wannan? Ashe hankalin da ake ganinsa da shi da girma bashi da shi ɗin?”.
      “Kiyi haƙuri Hajjo, ALLAH ya huci zuciyarki. Ni kaina ban taɓa zaton hakan daga garesa ba. Kinga wannan ai tushen ɓata zuminci ne, idan iyayen namu basu kai zuciya nesa ba sai kiga al'amarin ya kawo ɓacin rai. Sannan su kansu yaran an saka wani abu a zuciyarsu gurɓataccen. Dan zasu iya tsanar Nu'aymahr da yace dominta yayi, hakan kuma bashi da amfani”.
      Ƙwafa kawai hajjo tayi ranta da zuciyarta na ƙara mata suya da ɗaci. Omar dai yayta lallashinta har sai da yaga ta ɗan kwantar da hankalinta sannan ya fice cike da jimami. Sashensu ya nufa, yaje ya faɗama Momy duk abinda ya faru.
      Sosai itama ta rikice hankalinta ya tashi. Dan ta tabbata Abbansu dama wasu a mutanen gidan bazata fita da ga zarginsu ba, musamman ma da akasan taso ya auri ɗiyar ƙanwarta. Waya ta ɗauka ta shiga neman Abdallah. Sai dai harta tsinke bai ɗagaba. Bata gajiya ba wajen cigaba da jera masa kira, amma yaƙi ya ɗaga.

        Hajjo, Omar, Momy sun yi yinin yau ne cikin tashin hankali da damuwar ɓarnar da Abdallah ya tafka. Duk da sun ƙagara Baba malam ya dawo gidan ransu cike yake da fargabar sakamakon da zai biyo baya kuma.
       Sai bayan sallar la'asar baba malam da Abban Abdallah suka dawo gidan. Dan dama tare suka fita. Sunje wani ƙauyene akan maganar wata katafariyar gona da zasu saya. Sunason gyarata su maidata gidan gona a zuba dabbobi kala-kala na kiwo a ciki. Wannan ma ne dalilin da yasa har yanzu shi da Abba Musbahu basu koma ba. Suna son sai komai ya kammala sannan su ɗauka iyalansu su koma inda suka fito sai kuma biki.
       Kamar yanda al'adarsu take ta fara shiga sashen mahaifiyarsu yau ma hakan suna fitowa daga mota can suka nufa. Yanda suke tafe suna firarsu kowanne fuska ɗauke da fara'a dolene su matuƙar burgeka. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin shaƙuwa da ƙaunar juna dake a tsakaninsu.
     Sai da sukai sallama Hajjo da ke zaune cikin ɓacin rai har yanzu ta amsa musu da basu izinin sannan suka shiga. Kallo ɗaya sukai mata suka fahimci tana cikin damuwa. Kusan da sassarfa duk suka ƙarasa gareta kowanne na tambayarta tana lafiya?.
       Batai magana ba, sai wajen zama data nuna musu. Sai dai maimakon su zauna a kujerun sai suka zauna ƙasa tamkar yanda suka saba. Gaisheta sukayi, sannan suka sake jero mata tambayoyi akan yanayin nata.
      Ƙwallar da suka cika mata idanu tasa bakin ɗan kwalinta ta share. Hakan sai ya sake tada musu hankali.
     “Inna dan ALLAH ki faɗa mana minene ke damunki? Mune mukai muki laifi? Ko matan mu? Kokuwa a cikin yaran nan ne wani yay miki wani abu?”.
        Sake share hawayen data matso tayi da cewar, “Ni babu abinda kukai min ɗan malam, Abdullahi ne kawai keson watsa mana gida”.
     Hankali a tashe baba malam da Abban su Abdallah suka kalli juna. Cikin ƙarfin hali baba malam yace, “Innah mi Abdallahn ya aikata?”.
       Takardun da Abdallah ya rubuta ta ɗakko ta miƙa musu. Amsa sukayi kowanne ya buɗe guda ɗaya gabansa na faɗuwa. A tare suka ɗago a razane suka kalli juna da ambaton sunan ALLAH. Baba malam har yana tsallaken kalma wajen faɗin, “Innah shi Abdallah ɗinne ya rubuta wannan takardar?”.
           “Shine ɗan malam, shine da kansa ya rubutasu ya kuma kawo mani. Wai dan kawai jiya na bashi shawarar cewar yay haƙuri ya barma Nasiru Zainabu tunda shi yanzu yana da matansa har biyu. Shine fa yau ya kawomin takardar sakinsu Adawiya wai gashinan ya rushe katangar dana ce masa tana tsakaninsa da Zainabu”.
     Abba da ya gaza cewa komai tun ɗazun yace, “Innalillahi..., wai inna kina nufin su duka biyun ya saka?”.
      “Eh mana Lurwanu, baga takardun nan ba duka biyu na baku”.
      Da sauri baba malam ya amshi ta hannun Abba, shima ya karɓa ta hannunsa. Da gaske kuwa su duka biyun ya saki. A take tsananin ɓacin rai ya sake bayyana a kan fuskokinsu. Abba ya miƙe a fusace zai fice. Kiransa baba malam ya shigayi amma ina zuciyar gadon ta motsa. Dan haƙuri kawai ya bashi batare da ya juyoba ya fice.

          Momy na zaune cikin damuwa da fargabar jiran dawowar mijinta Abba ya shiga. Jiki a sanyaye ta dubesa dan ko sallama baiyi ba 
     Takardun guda biyu ya watsa mata a jiki. “Da saninki ɗanki yay wannan aika-aikar ko?”.
      Gaban Momy na faɗuwa ta ɗauki takardun ta karanta, hawayen da taketa faman dannewa tun ɗazun suka zubo mata a saman kumatu. “Wlhy Abban Abdallah ban sani ba. Nima ina zaune Omar yazo yake sanarmin. na kirashi yafi sau hamsin amma ya ƙi ɗagamin waya ma, kai........”
    Baki ya buɗe zai daka mata tsawa Omar da ya shigo basu sani ba yace, “Abba wlhy babu ruwan Momy, hasalima batasan komaiba akan al'amarin nan sai da nazo na sanar mata. Abba ko kasan dama tunda Yah Abdallah ya dawo gidannan baiyi zaman minti biyar da Momy ba. Da ya shigo ya gaidata da safe bazata sake ganinsa ba sai washe gari. Fushi yake da ita babu gaira babu dalili. Ta sakani na tambayesa amma yacemin idan na sake zuwa masa da zancen Momy sai ya ɓatamin rai. Ita kanta nace zan sanar maka abinda ke faruwa amma ta hanani, wai mu bashi lokaci kozata fahimci abinda ke damunsa”.
        Jikin Abba ne yay sanyi, dan tabbas kuwa ya kula tunda Abdallah ya dawo ƙasar nan bai taɓa ganinsa zaune da Momy ba, da farko yaso tambayarta sai kuma yayi tunanin ƙila sai ya fita suke zaman. Wannan ya sakashi yin shiru duk da kuwa yasan yanda matar tashi take da ƙulafucin ƴaƴa musamman Abdallah.
    Nannauyan numfashi ya sauke tare da zama yana cire hular kansa ya ajiya.....

           A ɓangaren baba malam kuwa Abba na fita waya ya zaro ya shiga neman layin Abdallah. Sai dai kuma abin mamaki switch off. Ajiye wayar yayi ya maida hankali ga Hajjo da ke sharar hawaye har yanzun. Kwantar mata da hankali ya shigayi da bata haƙuri. Yace, “Inna ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, insha ALLAHU mu dai wannan bazai kawo mana rabuwar kawuna ba. Duk inda Abdallah ya shiga kuma na tabbata zuwa dare dole ne ya dawo gida ya kwana ai, insha ALLAHU a daren nan sai ya maidasu su duka biyun”.
        “Ɗan malam bazaka gane abinda nake nufi ba, amma duk yanda kake tunanin sauƙi a al'amarin nan da wahala ya kasance hakan. akwai abinda na sani wanda kai da sauran ƴan uwanka baku san da shi ba a gidan nan. Ina barin masu aikatawar ne kawai kafin ranar da zan masu bankaɗa da tonon silili a gaban kowa. Ni dai abinda zan sanar maka yanzu shine da ga Abdullahi har Nasiru ka zaunar da Zainabu ta zaɓi wanda tafi so tunda abin ya zama haka. Kokuma ta auri wani bare can a zauna lafiya. Sannan inason ka nutsu kayi tsai da hankalinka a wannan karon game da kowa a gidannan, koda baka fahimci duka abinda na fahimtaba zaka fahimci wasu daga ciki. Dan kai ne uba a gidan nan, duk da dama nauyi da girman ya rataya a wuyankane tunbayan rasuwar mahaifinku, ina kuma alfahari da yanda ka riƙe hakan, amma sai randa ƙasa ta rufe idanuna zaka sake tabbatar da girman dake bisa kanka da tarin fituntunun da ke kwance a cikin gidannan wanda ALLAH ne kawai hanasu fallasuwa saboda rahamarsa da ikonsa da kuma ƙarfin addu'ar mahaifinku da har yanzu take biye da ku. Kai dai ALLAH ya ƙara maka haƙuri da juriya kawai. Tashi kaje ka huta, ka kumayi ƙoƙarin tausar sauran ƴan uwanka akan duk ma abinda zai iya biyo baya game da wannan gagarumar fitinar da Abdullahi ya ɗaɗɗago mana”.
       Kasa cewa komai baba malam yayi. Cike da ruɗanin maganganun Hajjo ya jinjina mata kansa kawai da miƙewa ya fice zuwa nasa sashen. Bai iske kowa a falon ba sai Muhammad dake karatun Al-Qur'ani na haddar da aka basu a islamiyya. Yaron bai dakata daga karatun da yakeyi ba, shima kuma bai masa magana ba ya wuce ɗakinsa. 
        Komai tsaf a gyare kamar yanda ya saba zuwa ya iske, ga ƙamshi mai daɗi. A ɗaya daga kujerun ya zube hankalinsa har yanzu baya tare da shi. Dan ransa da zuciyarsa cike suke da tarin ruɗanin kalaman mahaifiyar tasu. Shi kansa yasan akwai abubuwan dake kwance a gidan nan ƙwarai da gaske. Waɗanda da yawansu shi da iyalinsa sun cutu matuƙa a cikinsu. Koma yace suna kan cutuwa. Ya kumayi imani da ALLAH babu wani baƙon ido daga waje da zasuce yana aikata su, dolene mai aikatawar a cikin zuri'arsu yake. Yasha yin tunanin tsananta bincike, amma sai zuciyarsa ta gargaɗe sa da yin haƙuri, sannan yana mai tsananin jin tsoron wanda sakamakon ɓarnar zata tabbata a garesa. A ganinsa gara kawai a cigaba da tafiya a lulluɓen dan UBANGIJI mai ji ne kuma mai ganine akan kowa da komai..........
        Taɓa shin da akayi ne ya saka tunaninsa katsewa. Duban Umm da tun ɗazun take masa magana yay. Fuskarta cike da damuwa tace, “Malam lafiya kuwa? Wane irin zurfafa tunanine haka? lna fatan dai lafiya ko?”.
         “Humm! Jannat lafiyar nan da dauƙi”.
      Saurin zama tayi hannunta riƙe da kofin data zuba masa ruwa tana faɗin, “Miya faru?”.
      Ruwan ya fara karɓa ya sha, ta sake ƙara masa ya shanye sannan ya ajiye kofin ya labarta mata duk abinda ya faru, harma da zancen da Hajjo tai masa.
         Duk da itama ta jima da ji a ranta duk abinda Hajjo ke zargi a kwaishi a gidan hakan bai hanata jin tashin hankali ba. Ita kanta tanason sanin mai aikata musu SARAN ƁOYE a lokuta da dama. Sai dai tsoron wanda zata gani yana aikatawar ke sakata sama ranta haƙuri da barin komai hannun UBANGIJI.

★★★★
    
           A yau dai har dare Abdallah bai dawo gidanba duk jiran da su baba malam sukai zaman yi masa. Dole suka haƙura suka kwanta al'amarin nacin ransu da zuciya.
        Washe gari bayan fitowa sallar asuba baba malam da sauran ƴan uwansa suka hallara gaba ɗaya a sashen mahaifiyarsu. Bayan sun gaisheta suka sake haɗuwa gaba ɗaya wajen bata haƙuri akan abinda Abdallah yayi, suka kuma tabbatar mata insha ALLAH zasu dai-daita komai ba sai yayi tsamari ba.
       Batace da su komaiba dai, sai dai ta musu addu'ar nasara da nemawa Abdallah dama sauran yaran shiriya gaba ɗaya.

       A wannan yinin maganar sakin ta shiga kunnen kowa dake a gidan ciki harda Addah da yaranta dake can suna shan biki. Aiko ba ƙaramin rikita musu lissafi Adawiya tayi ba. Dole babu shiri suka tattaro suka nufo kano zuciyar kowa babu daɗi.
       
      Tunda saƙon saki ya isa kunnen Yusrah kuwa sai wani tarin farin ciki ya kamata. Bama tasan lokacin data shiga dirga tsalle akan gadon ɗakinsu ba. Kafin ta sakko da sauri ta shiga bayi ta ɗauro alwala. Salla tayi raka'a biyu na godiya ga ALLAH daya kawo ƙarewar wannan aure da ko tarewa batayi ba a cikinsa. Dama tunda su Adawiya suka diro ƙasar bata da wani sukuni. Shiyyasa ta koma yinin makarantar Tahfiz ɗin gidansu dan kawai ta gujema ganinsa. Hakan kuwa akayi, dan tunda suka iso sau biyu ta haɗu da shi. Ɗaya da daddare ya shigo sashensu wajen Abba. Na biyu kuma a sashen hajjo taje kai mata abinci. Duka a haɗuwar tasu gaisuwa ce kawai ta shiga tsakaninsu. Yanda baya sakar mata fuska itama bata shiga sabgarsa sam, dan baya wani nuna alamar akwai ko ɗigon haƙƙinta daya rataya a kansa ma. Hakan kuma bai dameta ba, to gashi cikin amincin ALLAH komai ya zama yanda taketa fata a kullum. Ba ƙaramin azumi da ƙiyamullaili tayi ba akan auren nan a cikin watannin nan. Dan ita kaɗai tasan dalilin rashin son auren.

        Duk wannan ruguɗai da akeyi Nu'aymah batasan anai ba ita kam, dan Umm da baba malam babu wanda ya sanar mata. Sashen Hajjo kuma yanzu ba wani shigarsa takeba sosai saboda takurawar Nasir da Abdallah da suka maida sashen hajjo wajen zamansu. Ta gwammaci taita zama a sashensu, idan Muhammad na gidan susha shirmensu, idan kuma ya fita makaranta tayi kallo idan akwai wuta ko su zauna hira da Umm. Wani lokacin kuma tai barcinta dan Doctor ya ce ta dinga yawan barci, shiyyasa ma ya saka mata maganin barci a magungunanta.
           Yauma tana a ɗaki tasha barcin rana har su Adawiya suka dawo bata saniba. Ta fito wanka tai sallar la'asar, shiri ta farayi da ƙudirin zuwa islamiyya yau dan tanajinta Alhmdllh. Tana tsaka da saka kaya ta jiyo kururuwar kuka kamar muryar Adawiya kuma. Saurin ƙarasa saka kayan tayi ta fito, a mamakinta duk ma sai ta iske ƴan gidan a tsakar gida kowa ya fito an rufu kan Adawiya. Gabantane ya faɗi da tunanin ko Accident sukayi a hanya. Da sauri ta shiga bin kowa da kallo sai taga kowa ma yana nan, harsu Aunty Aysha ma basu wuce gidajensu ba nan sukayo.
     Kallon Jafar dake kusa da ita tayi tace, “Jafar miya faru wai?”.
      “Aunty Nu'aymah ban saniba nima. Kawai dai naga Aunty Adawiya na kuka tana cewa wai indai aka rabata da Yah Ab zata mutu”.
       Kafesa da kallo Nu'aymah tai tana son fassara kalaman nasa amma sunƙi fassaruwa. Dubanta ta kai ga Umm dake lallaɓa Adawiya taje sashensu amma taƙi, hakan ya sake tabbatar mata da lallai ba lafiya ba kuwa. Baba malam daya shigo gidan yanzunne ya dakama Adawiya tsawa. Jiki na rawa ta miƙe tsaye.
      “Wane irin rashin hankaline wannan tun daga wajen gate anajin muryarki, tona mana asiri zakiyi da shirme ko mi?. To wlhy bara kuji bama ita ba duk wanda na sakejin bakinsa a wannan maganar saina ɓata masa rai, naga dai Abdallahn a ƙarƙashin ikonmu yake shima, dolene kuma yabi abinda mukeso inhar yana buƙatar gamawa da rayuwarsa lafiya. Kowa ya shige ciki”.
        Jan ƙafa kowa ya shigayi zuwa sashensa. Kubrah ta kama hannun Adawiya suka shige tare. Inda suka bar Addah da bata fitaba nan suka isketa zaune. Babu wanda taima magana a cikinsu har suka zazzauna kowa na ƙannun magana. Batace musu komaiba dai har lokacin, saima jingina da tai da kujera ta lumshe idanu.

          Nu'aymah suna shiga sashensu ta shiga tambayar Umm abinda ke faruwa. Dan ita harga ALLAH bata fahimci komaiba dai har yanzun. A taƙaice Umm ta faɗa mata, sai ko ta zabura a matuƙar razane. “Ya salam. Umm Yah Ab kuwa yana da hankali?! Wannan ai gogama mutane sharri ne da zai ce saboda ni ya aikata saki ga matansa”.
         “Wannan sakaki a cikin da yayi shine ya sake tada mana hankali muma Nu'aymah. Dan zai iya zama wata fitina daban wadda ba'asan iyakar inda zata tsaya ba a gidan nan. Yanzu dai Abbanku ya gano inda yake, ya kuma bashi daga nan zuwa kwana uku idan bai dawo gida ba zai haɗu da ɓacin rai mai tsanani daga garesu”.
         “Ai gara yazo ya kwance wannan ƙullin da yay min nikam, a dalilin mi zai sakani tsakkiya, a barni da abinda ya damenima nikam ya isheni Umm”. Tai maganar tana fashewa da kuka.
        Tausayinta ne ya kama Umm sosai, ta ruƙo hannunta ta sakata jikinta tana lallashi............✍


😩 Yah Ab ya zaka mana haka ne?🤦🏻‍♀️🙆🏻‍♀️
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/24, 12:25 PM] +234 806 269 3623: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


Ina fatan ansha weekend lafiya? ☺️🤝🏻😘


No. 35

.............Kamar da wasa sai ga Abdallah ya shanye kwanaki ukun da baba malam ya bashi babu shi babu mai kama da shi. Ran baba malam da sauran ƴan uwansa ya sake ɓaci matuƙa, amma duk sunta ƙoƙarin dannewa. Dan hatta Hajjo ranta a ƙololuwar ɓace yake.
          Hankalin Nu'aymah ne ya sake ta shi. Dan koba komai har yanzu tana son Yah Ab, bazata so bari ya cigaba da munana a idon iyayensu ba akan shima son da yake mata. Tunda duk abinda yake aikatawa na laifi a garesu a kanta ne.
          Kuka sosai Nu'aymah tasha akan wannan al'amari. Musamman ma da itama tai kiransa da wayar Umm amma yaƙi ya ɗaga tun a ranar. 
        Yau ma wayar ta sake ɗakkowa ta Umm ta kirasa, sai dai bai ɗaga ɗin ba. Haƙura tayi da kiran, sai dai kuma bayan kamar awa guda kamar an tsikareta ta sake zuwa ta aro wayar again. Test massege ta tura masa, bakinta cike da addu'ar ALLAH yasa ya duba.
    Bayan kamar mintuna biyar kuwa sai ga reply ɗinsa. Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta duba.

       *_“Zan iya amsar gayyatarki akan dalili guda ɗaya, idan kin amince da shi ko yanzu zan iya dawowa gida na fuskanci iyayenmu”._*
        _Dalilin kawai ki amince a ɗaura mana aure ranar bikin su Kubrah._

       Wani irin mugun bugawa ƙirjin Nu'aymah yayi, tai mugun waro manyan idanunta waje hawaye masu zafi na rige-rigen fitowa. A fili cike da karyewar zuciya ta furta, ‘Anya kuwa Yah Ab bai fara shaye-shaye ba jama'a? Na shiga uku ni Zainab, wane irin tsaka mai wuya bawon ALLAHn nan yake ƙoƙarin jefani a gidan nan?’. 
        Kuka sosai ta kuma sha fiyema dana ɗazun, dan sai da taji kanta ya fara sara mata sannan ta haƙura. Har bayan anyi sallar isha'i bata fitaba ta cigaba da zama a ɗaki. Wayar Umm ma da Muhammad ya shigo aran littafinta na *Ahdhari* ta bashi ya kai mata. Yunwa ce ta fara takura mata, dole ta miƙe ta shiga bayi, wanka tayo ta fito, tai shirin cikin wando da riga na barci masu taushi. Tanajin yunwa amma bata jin cin abincin kuma, sha'awar shan lipton ne yazo mata a rai. Dan haka ta miƙe ta ɗauka hula ta saka a kanta sannan ta fito.
      A falo sukaci karo da Rabi ɗauke da ƙaramin jug da alama ma ɗakinta zata. Baki Rabin ta washe ta na faɗin, “A'a uwar ɗakina kin tashi ashe? Kamar kinsan kuwa zoɓon nan zan kai miki dama ko zaki ɗansha dan na sanki da son zoɓo”.
      Ɗan lumshe idanu Nu'aymah tayi ta buɗe akan rabin tana ɓata fuska kaɗan. “No bar zoɓon nan ma dai baba Rabi. Idan ban takura miki ba dan ALLAH haɗamin lipton kaina ciwo yake min”.
       Da sauri Rabi tace, “Ah wlhy babu wani takura uwar masu gida. Kinga zauna bani mintuna biyar kacal, barama nai miki amfani da ganyen shayin baba malam, ina dai kina so ko?”.
        Kai kawai Nu'aymah ta gyaɗa mata dan surutunta ya isheta. A ƙasan ranta kuma tana mamakin yanda Rabin ta amsa dafa mata shayin ɗin babu ko musu balle sukai ga faɗan da suka sabayi kullum.

        Ɗakin Umm Nu'aymah ta nufa kafin Rabi ta kammala, sai dai ta iske tana wanka dan haka ta fito akan idan ta gama zata koma. Fitowarta dai-dai da fitowar Rabi da ga kitchen ɗauke da kofin shayi dake ta turiri. Sai da tai mata godiya sannan take tambayarta ko baba malam ya shigo?.
       “A'a bai shigoba, dan naji Muhammad na faɗin kamar yayi baƙi ne ma”.
     “Okay”.
   Kawai Nu'aymah ta faɗa tare da ɗaukar kofin ruwan zafin ta kai bakinta tana ƙoƙarin kunna television da hannunta na haggu.
      Sosai shayi yayma Nu'aymah daɗi, harta shanye wanda Rabi ta zuba mata itama ta sake zuba sauran wanda ya rage a butar shayin. Tana cikin shan wanda ta zuba ɗinne Umm ta fito...
         “Oh dama kin tashi?”.
“Eh, nama shiga ɗakin na tarar kina wanka. Umm kaina ke min ciwo ALLAH”.
        Cike da kulawa Umm dake dubanta tace, “Ba dole kanki yay ciwoba Nu'aymah, kukan da kikayine ai. Halan ma da kika tafi ɗakin ba barcin kikayi ba?”.
         “Umm barcin nefa bai zoba. Amma yanzu naɗan fara ji, sai dai zan jira Abba ya shigo sannan naje na kwanta”.
          “Wayasan sanda zai shigo, ki tashi kije ki kwanta banason sakarci. Miyasa ke wai sam baƙya tattalin lafiyarkine? Kin fison kullum ki ganmu hankali a tashe”.
      “Kiyi haƙuri Umm ba haka baneba wlhy, dama dan yau duk bamu haɗu da Abba bane shiyyasa. Amma bara nasan insha ALLAHU da safe zamu haɗu. Sai da safe”.
      “Ki tabbatar kinyi addu'a kafin ki kwanta”.
     “To Umm”. 
Nu'aymah ta faɗa tana nufar ɗakinta badan taso hakanba. Kamar jira tana kwanciya sai barci mai nauyi ya kwasheta batare da ko addu'ar da Umm ta gargaɗeta yi ba tayi ɗin.

★★

       Sai wajen sha ɗaya baba malam ya shigo gidan. Koda ya tambayi Nu'aymah Umm ta sanar masa ta kwanta sai ya nufi ɗakinta. Yayi sallama kusan sau uku babu amsa, dan haka ya juyo falo yana faɗin, “Nayi magana shiru, inaga tayi barci ma”.
        “Dama tace barci takeji, amma tsabar fitina wai zata zauna jiranka dan yau duk bata gankaba”.
     Murmushi kawai baba malam yayi, amma baice komaiba.

          Kusan ƙarfe sha biyu saura Nu'aymah ta farka da wani Masifaffen ciwon ciki. Juye-juye ta shigayi a kan gadon tana kiran sunan Umm. Tun abin na mata sama-sama harya fara fin ƙarfin tunaninta. Yunƙurawa tai da ƙyar ta tashi zaune tana ambaton ‘Innalillahi.....’ da ƙyar ta iya sakkowa da ga saman gadon. Sai dai yanda ƙafafunta da mararta suka riƙe sam bazata iya takawa ba. 
       Ƙasa ta durƙushe hannunta ɗaya riƙe da cikinta, ɗayan kuma ta dafe gado da shi tana matse idanu da cije baki. Cikin azabar data isheta ta fara ƙwalla kiran sunan Umm da baba malam tana roƙon suzo su taimaketa zata mutu. Yanda zufa ta jiƙeta sai ka ɗauka ruwa aka watsa mata. Wata gigitacciyar ƙara ta saki lokacin da idanunta ke sauka akan Windown ɗakinta. Gilmawar mutum ta gani, wanda alama ta nuna ya jima a wajen tsaye koma waye. Ai sai kawai ta daddage ta fasa ƙarar da tafi ta farko badan taji tsoro ba sai dan wani irin kartawa da mararta tayi tamkar numfashinta zai bar ganar jikinta a lokacin.......

        A rikice baba malam da Umm da barci ya fara ɗauka yanzun suka farka. Har rige-rigen fitowa sukeyi dan ƙarar Nu'aymah sun jitane tamkar a tsakkiyar ƙwalwar kansu.
    Kwance suka isketa a ƙasa wanwar tana numfashi da ƙyar. Baba malam yay saurin kunna fitilar ɗakin mai haske, Umm kuma ta nufeta tana kiran sunanta. Sai dai ina Nu'aymahn ta suma. Sake rikicewa Umm tayi, ta fashe da kuka itama tana girgiza Nu'aymahn.
       Baba malam daya nufosu shima a rikice yay sauri ja da baya jin ƙafarsa cikin wani abu mai ɗumi. Kallon inda ya taka ɗin yayi. gabansa yay bala'in faɗuwa ganin jini. Cikin rawar jiki ya durƙusa da kai ɗan yatsansa ɗaya yaɗan dangwalo. Tabbas jinine kuwa. Dan haka yace, “Jini kuma?”.
     Saurin kallonsa Umm tayi itama. Tace, “Jini kuma malam? A ina?”.
      Da hannu ya nuna mata, sosai zuciyarta tai masifar harbawa. Tabi jinin da kallo har jikin Nu'aymah da alamu suka nuna daga nan yake fita. Kafin ta iya cewa wani abu sai ga Hajjo da Addah da Momy sun shigo a rikice. dan duk wanda yake a gidan yaji ihun Nu'aymah saboda dare yayi. Sai kuma ga matan Abba Musbahu su maman Yusrah, suma Samarin gidan duk sun shigo sai dai sun dakata a a falo.
       Hankalin kowa ya tashi da ganin wannan jini. Ga dare ya fara.
    Hajjo tace, “Mafita ya kamata mu nema ba wai koke-koke ba. Ya kamata a tado su Ahmadu dan a tafi asibiti”.
       Addah data maida Nu'aymah jikinta ta share hawayen da ke ziraro mata itama da faɗin, “Hajjo inaga a kira Doctor Sale tunda nan kusa yake shi. amma yanzu ko asibiti akaje zaiyi wuya a samu likitan kirki. Gashi yarinyar nan tana ciki wani hali”.
       Dukansu sunyi na'am da zancenta. hakan ya saka Abban Abdallah fita dan ya kiran Doctor Sale a waya. A falo ya wuce samarin gidan tsaitsaye jigum-jigum. Kusan a tare suka shiga tambayarsa mike faruwa?.
       A taƙaice ya basu amsa yana ƙoƙarin kai waya kunnensa.

         Cikin mintunan da basu gaza talatin ba Doctor Sale ya iso. Malam ƙarami ne yaje ya shigo da shi, yay masa iso har ɗakin Nu'aymah. Zuwa lokacin su Momy nata ƙoƙarin saka abu ana kwashe jinin da har yanzu bai dai na zuba da ga jikin Nu'aymah ba. Su baba malam kuma sun koma da ga ƙofar ɗaki. 
      Ko gaisuwa bai tsaya sunyi ba ya shiga. Su Umm duk suka fito aka barsa da Addah da Umman su Yusrah a ciki. Ƙoƙarin tsaida jinin ya farayi, kafin ya fara bama Nu'aymah taimakon gaggawa.
     Kamar wasa sai da ya kwashe awa guda domin ƙoƙarin ceto ta, Umman Yusrah nata gyara wajen, Addah kuma na riƙe da Nu'aymahn har yanzun. Jinin an samu ya tsaya, harma an saka mata ƙarin ruwa bayan an samu ta farfaɗo. Fita yay ya basu waje dan su ƙarasa gyara mata jikinta.
  
         Yana fitowa duk suka yo kansa suna tambayar yaya jikinta. Doctor Sale ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, “Alhmdllh malam ku kwantar da hankalinku. Komai ya dai-daita, sai dai kuma anyi asarar cikin da ke jikinta. Nayi iya ƙoƙarina na ganin cikin bai dalwantaba amma hakan ya gagara, sai dai haƙuri”.
     Ga ba ɗayansu wani irin kallon rashin fahimta suke masa. Cikin ƙarfin hali Hajjo tace, “Kai ɗan nan bamu fahimci zancenka ba. Miya haɗa Zainabu da ciki kuma? Ko kuwa kana nufin wani ciki dai bana haihuwa ba?”.
        Shima ɗin dai kallon mamakin yake mata, kafin cike da son fahimtar da ita yace, “Mama ina nufin ciki na haihuwa mana, ko bakusan tana da shi ba ne?”.
        Kallon juna suka shiga yi ƙirjin kowa na bugawa da sauri-sauri musamman ma Baba malam da Umm da Hajjo. Da rawar harshe Umm tace, “Ya zakace ciki a jikin Nu'aymah?”.
          “Ikon ALLAH! Hajiya wlhy ciki ne da ita ɗan sati shida ma kuwa”.
       Umm zata sake magana baba malam da zufa ke karyo masa ta ko ina a sannan jikinsa yay saurin katseta da faɗin, “Doctor yanzu wane hali take ciki ita?”.
        “Ah Alhmdllh malam, yanzu haka tama farfaɗo, na kuma saka mata ruwa da zai sakata barci, zuwa da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo na sake dubata sai na taho da magungunan da ya kamata tai amfani dasu. Zuwa da yamma idan taji ƙarfin jikinta za'a kaita asibiti dan na sake dubata da ƙyau, a kuma yi mata wankin ciki, dan gaskiya ɓarin yazo mata da matsala kamar”.
      “To shikenan, mungode sosai Doctor, ALLAH ya saka da alkairi”.
      “Amen” Doctor Sale ya amsa saboda jin daɗin addu'a daga babban malami irin baba malam. Daga haka yay musu sallama ya tafi ya barsu da ruɗani.

      Tun fitar Doctor Sale kowa ya kasa yin ko motsi. Sai ma Umm da hajijiya ke ɗauka kaɗan-kaɗan ce ta ɗan zauna jin zata faɗi. Cikin ƙarfin hali Hajjo ta shiga ɗakin Nu'aymahr, ta iske su Addah sun kammala kimtsata harma sun lulluɓa mata bargo, ga ƙarin ruwan da aka saka mata yana tafiya dai-dai.
       “Kunga kuje ku kwanta dare na ƙara nisa. Tunda ALLAH yasa ta samu barci. Suma sauran ku sanar musu suje su kwanta”.
      Babu musu sukai mata sallama suka fita. Su da basusan mike faruwa ba sai suka shiga sake kwantar musu da hankali akan jikin Nu'aymahn da sauki. Hajjo ma tace kowa yaje ya kwanta.
        Su Abban Adawiya ne kawai sukace Alhmdllh, amma babu wanda yay yunƙurin tafiyar sai da Baba malam yay magana. Har kowa ya gama ficewa da ga sashen baba malam da Umm basu iya motsawa ba. Sai bayan kusan mintuna goma sannan ya kama Umm ta miƙe da ƙyar. Ɗakin Nu'aymah suka shiga. Hajjo dake zaune ta zubama Nu'aymah ido ta ɗago tana kallonsu.
     Saurin yin ƙasa da kai Umm tayi, dan sai yanzu me wasu zafafan hawaye suka sami damar ziraro mata. Har ga ALLAH zuciyarta ta shiga cikin matsanancin ruɗanin bayanin Doctor Sale. Wani sashe yana gaskatawa wani sashe na ƙaryatawa. Hakama baba malam a matuƙar ruɗanin yake. Amma da yake shi namijin duniya ne sai ya shanyeshi tsaf dan a ganinsa yana buƙatar lokacin yin tunani akan hakan..........
      Hajjo ce ta katsesu da faɗin, “Ban yarda da wannan maganar ta likitan nanba, duk da kuwa koni jinin ya matuƙar tsoratani tunkan bayaninsa. Sai dai hakan bashine ke nufin mu amince da cewa ciki a jikin Zainabu ba. To ta yayama hakan ta faru? A ina kuma? Yaushe kuma?”.
      Kan baba malam a ƙasa, muryarsa a matuƙar cinkushe da tashin hankali yace, “Inna bazamuyi saurin ƙin gaskatawaba, tunda kinga ai aikinsane hakan”.
      “Duk da aikin nasa ne ban yardaba. Sai an nemo wani likitan ya sake dubata tukunna. Kokuma muje asibiti da safe idan ALLAH ya kaimu”.
       Basu iya mata musu akan hakanba da ga shi har Umm da bata iya furta komai ba har yanzun. 

WASHE GARI

         Da safe Doctor Sale ya dawo gidan zuwa 8:30 kamar yanda yay alƙawari. A lokacin Hajjo ta gyara Nu'aymah da kanta. Yayinda Rabi ta sake tsaftace ɗakin ita kuma.
       Ya dubata yanda ya kamata, ya kuma tabbatar musu komai Alhmdllh dan UBANGIJI ya sauƙaƙa al'amarin. Ita dai Nu'aymah ba wani fahimtarsu take ba, dan batasan ainahin abinda ya sameta ba bayan ciwon cikin da zata iya tuna tayi kafin gushewar hankalinta.
     Ya bada magungunan da zatay amfani da su, da waɗanda bashi da su za'aje a sayo. Daga haka yay musu sallama akan da yamma zai dawo ya sake dubata idan ya taso aiki. Godiya baba malam yay masa. Hajjo da Nu'aymah dai basuce komai ba. Hakama Umm da tun daren jiya da hankalinta yabar jikinta har zuwa yanzun bai gama dawowa ba.

        Baba malam baiso maida hankali akan maganar hajjo na nemo wani likitanba. Amma ganin ta matsa sai ya bi umarninta suka kira wani Doctor Faisal abokin Ahmad. Wajen ƙarfe goma na safen shima ya iso, a lokacin an maida Nu'aymah sashen hajjo.
      Shima dai sun bashi dama yayi aikinsa yanda ya kamata. Kafin daga bisani yay zaman basu bayanin daya matuƙar tada musu hankali akan result ɗin shima. Ya tabbatar musu da gaske Nu'aymah ɓarin ciki tayi ɗan sati shidda da wasu kwanaki, amma babu wata matsala tattare da ita, magunguna kawai zataita sha jikinta zai koma normal.
      Har ya kai karshen bayaninsa babu wanda ya iya motsawa a falon, sai hajjo ce tai ƙarfin halin masa godiya.
     Bayan wucewar Doctor hajjo ta sake tabbatar musu shima bata yarda da nashi aikinba. Duk yanda baba malam yaso fahimtar da ita tace bata yarda ba. A yanzu sai su ɗauki Nu'aymah suje asibiti kawai, kuma na gwamnati take so.
    Ɗari bisa ɗari su Abba Musbahu sun yarda da maganar hajjo, dan suma zukatansu sam basu aminta da maganar ɓarin cikin Nu'aymah ba sam. Sunfi baba malam yawa, dan haka dole yay shiru ya barsu. Amma a ƙasan zuciyarsa bai son sake fitar maganar kuma dan hakan tamkar tonama kansu asirine sukeyi, tunda yasan ba duka likitocinne zasu iya barin maganar a cikinsu ba duk da yasan basusan Nu'aymah bata da aure ba.
           

_____________________

         Bisa matsawar hajjo suka ɗauki Nu'aymah da sam jikinta babu ƙarfi zuwa asibiti. Kasancewar su manyan mutane da ake girmamawa basu wani sha wahalar ganin likita ba, a yanzu kam mace ce ma Doctor Halima. Itama ɗin dai ta gunar da aikinta cike da ƙwarewa. Bayan kamar awa biyu ta basu samako dai-dai dana su Doctor Sale. Dan ta sake tabbatar musu da Nu'aymah tayi ɓarin ciki ɗan sati shida da wasu kwanaki dai, harma ta ɗora da faɗin Nu'aymahr na buƙatar hutu sosai da yawaita cin abinci mai inganci saboda jinin data zubar.
        Ba ƙaramin tashin hankali suka sake tsintar kansu ba a wannan karon kam. Dan ko masu tatsuniya sunce Ƙurun ƙus, anzo ƙarshe. Hajjo mai gardamar bata yardanba a yanzu sai bata iya cewa komai ba. Haka suka tattaro suka taho, dama ita da Ahmad da Naser da Abban su Abdallah da Addah ne suka je. 
        Ganin Hajjo na sharar hawaye Nu'aymah da ke magana da ƙyar saboda rashin ƙarfin jiki ta matsa da son jin mike damun kakar tasu?. Banza tai mata, hakan yasa tunanin Nu'aymah ko hajjo bataji ba ne sai ta sake maimaitawa.
        Tsawar data sakata ɗinke bakinta Hajjo tai mata, ta kuma ja mata dogon gargaɗi akan ta barta taji da abinda ya dameta. Shiru kawai Nu'aymah tai tana kallon hajjon, a ƙasan ranta ko fal tambayoyin mike faruwa ne?.
    Koda suka iso gida Addah ce ta taimakama Nu'aymah zuwa sashen hajjo, inda suka iske Abdallah da ya dawo gidan tare da sauran samarin gidan suna zaman jiran tsammanin dawowarsu.
         Kowa ransa babu daɗi ya shiga yima Nu'aymah sannu, yayinda Yah Ab ya kafeta da idanu kawai yana kallo. Itama dai kallon nasa takeyi. a ƙasan ranta kuma tanajin daɗin dawowarsa gidan. 

      Basuyi zaman mintuna biyar ba baba malam da sauran ƴan uwansa suka shishshigo harda Umm ma da sauran matan gidan dan Hajjo ce ta aika kiran kowa. Sai dai babu yaran gidan da ƴammata. Yaseer ma dake falon zaune tun ɗazun korashi waje akayi, Abba Musbahu yace yaje ya tattara yaran su wuce islamiyya.
         Shiru falon yayi kowa na jiran mi hajjo zata faɗa, Nu'aymah da ganin ita ba'ace ta tashi ta fitaba taita binsu da kallo a ƙasan ido tana mamakin yanda fuskar kowa ke ɗauke da ruɗani da tashin hankali........
       Maganar Hajjo ce ta katsema Nu'aymah tunani.
        “Alhamdulillahi, kamar yanda na buƙaci zuwa asibiti dan tabbatar da abinda zuciyata ta kasa gaskatawa ga shi munje mun kuma dawo. Sai dai abin razanin da tashin hankalin shine babu banbancin magana tsakanin likitocin farko da wadda ta duba Zainabu a yanzu. Itama ta sake tabbatar mana cewar Zainabu ɓarin ciki tayi ɗan sati shidda........”
       “What?!!!”.
Nu'aymah ta katse hajjo a zabure tana miƙewa zaune zumbur tamkar ba itace kejin kamar iska zata ɗauketa ta faɗi ba yanzun. Jikinta na matuƙar rawa tace, “Hajjo ban ganeba dan ALLAH! Wace Zainabu kike magana badai ni Zainab ɗinba?”. 
     Matsananciyar tsawa baba malam ya daka mata, ai bama tasan ta koma ƙasa rib ba ta zube a carpet saɓanin kujera da take kwance a kai ɗazun. Baba malam ya nunata da yatsa yana faɗin, “Zainab!! Wlhy tallahi kinji na rantse, inhar na sakejin bakinki batare da an baki izinin magana ba sai kinyi nadama”.
      Babu wanda ya iya ko motsi, dan jin ainahin sunan Nu'aymah a bakin baba malam ya tabbatar musu da lallai magana tazo iyaka. Ita kanta jin sunan daya kiratan ya saka zuciyarta ƙara gudu da tsitstsinkewa lokaci guda, wani bahagon tsoro da ruɗani suka da ɗa mamaye dukanin gaɓɓanta.
      Hajjo data juyo tana kallonta tace, “Zainabu bama buƙatar wani ja'inja ko rantse-rantse, nan gurin duk zuri'armune babu wani bare a ciki. ki daure ki faɗa mana wanda ya aikata miki wannan ɓarna. Shin da ganganci ne kokuwa fin ƙarfinki aka y? Wanene uban cikin nan da ya salwanta jiya?”.
          Sake rikicewa Nu'aymah tayi, jikinta na rawa tace, “Wlhy hajjo, na rantse da UBANGIJIN al'arshi ban taɓa aikata abinda kuke tuhumata da shi ba. ALLAH shine shaidata ni banda ciki.........”
         Wuƙa sharɓeɓiya Abba Musbahu ya fiddo ya nunama Nu'aymah, sai ƙyalli take da ɗaukar ido, mai kallo daya ganta yasan ta cancanci a kirata da suna GAYAWA JINI NA WUCE.
       “Nu'aymah kinga wannan wuƙar ko?”.
      Kai ta ɗaga masa da sauri jikinta na cigaba da rawa.
       Ya jinjina  kansa da cigaba da faɗin, “Inhar kikace zaki mana wasa da hankali to nan tsakkiyar falon nan zansa su Abdallah su kwantar min dake na yankaki kamar yanda ake yanka ragon layya. Ke dawa kuke aikata wannan shaiɗancin anan gidan.....?”
      Kai Nu'aymah ta shiga girgizawa tana kuka tamkar ranta zai fita. Bakinta kuwa sai wani irin karkarwa yakeyi kamar laɓɓanta zasu zubo ƙasa. Ta buɗe baki zatai magana sai kuma ta sake rushewa da wani sabon kuka.
     
     Kamar daga sama sukaji a bayansu ance, “Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku..........”✍

😱😱To wane majanunun ne kuma wannan?.



______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/25, 3:17 PM] +234 703 121 9749: No. 36


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


_KAWATA INA KIKA KOYO HADADDUN CAKES DA GIRKUNA NE HAKA? KINGA ABINCIN NAN NAKI DA NAYI TAKE AWAY BABAN AMEER BAKIGA YADDA YAKE SANTIN SABA, KWANA BIYU INA GIRKI AMMAN NAKI DAI YAKE TA SANTI, YACE LALLAI KAFATA KAFARKI KI RAKANI INDA KIKA KOYO_

_TAB! LALLE MAMAN SUDEIS AN BARKI A BAYA,  AI WAJEN *UMMU AYMAAN’S KITCHEN*!NA KOYO HADADDUN BIRTHDAY CAKES, SNACKS, DA ABINCIN YAN GAYU KE HARDA NA NAHIYAR KETARE.. BIKIN ADAMA KANWATA MA ITA NA BAWA ORDER TAYI MANA NA MUTANE DARI BIYAR.._

_LALLE AN BARNI A BAYA, WAI.. YANZU YA ZANYI NA KOYA DAN ALLAH?_

_SHA KURUMIN KI MATAR MIJIN TA.. UMMU AYMAANS KITCHEN TA SAKE DAWOWA DA KOYAR DA BIRTHDAYS CAKES AND DECORATIONS WANDA ZATAYI A KWANAKI 2, PRACTICAL CLASS , AMMA IDAN KINASON KOYA TA ONLINE NANMA ZATA KOYA MIKI._

_WAYYO ALLAH NA DADI..! YANZU YAUSHE ZAAI WANNAN BONANZA? KUMA NAWANE KUDIN?_

_NAIRA DUBU 6 KACAL WALLAHI, DUK ABUNDA YA SHAFI HARKAR BIRTHDAY CAKES AND DECORATIONS ZATA KOYAR_

_BA’ANAN TA TSAYA BA, AKWAI_ CAKE PARFAIT, 
CUPCAKES
SAMOSAS
SPRING ROLLS
MEAT PIE DA DOUGHNUTS.

_DUKA TANAYIN NA SHAGULAN BUKUKUWA, TARON SUNA, DANA CI A GIDA DAN MOTSA BAKI, KE HARDA GIRKUNAN DA KIKESON KI KOYA NA NAHIYAR KETARE DANA NAMU GIDA NIGERIA._

_KAI NAGODE KAWATA, AWANE GARI TAKE NE?_

_FARKO DAI GA NUMBER WAYAR TA :08032964266_

_SANNAN TANA NAN KANO, UNGUWA UKU, LAYIN MAI FATA, ZARIA ROAD KANO._

_CLASSES DIN ASABAR DA LAHADI NE KAWATA WATO 5 DA 6 GA WATAN JUNE DINNAN. MAZA FADAWA SU UMMI DAKE KADUNA KICE ZATA KOYAR A ONLINE MA.._

_KAI AIKO NAGODE DA SANARWARKI KAWATA. SHIN TANA INSTAGRAM?_

_Eh SUNANTA:_
@Ummu_aymaan_kitchen.

_TANA TURA KAYANTA A KOINA A FADIN KASAR NAN, INGANCI, KYAU, RAHUSA, LAGWADA GA CIKA CIKI DON DADI SAI UMMU AYMAANS KITCHEN AND CATERING SERVICES_


No. 36

.............“Malam nine kawai zan iya baku wannan amsar idan ita ta gaza baku. Amma kuyimin afuwa idan ya kasance na shiga hurumin da ba nawa ba”.
        Gaba ɗaya suka juya suna kallon bakin ƙofar har Nu'aymah data fara ganin dishi-dishi cikin idanunta. 
     Ba kowa bane mai maganar face ɗaya daga cikin amintattun almajiran baba malam mai suna Hamisu. Hamisu ɗan anguwar su Nu'aymah ne, hasalima maƙwaftan junane. Mahaifin su baba malam yayi zaman mutunci da girmama juna da kakansu Hamisu, dan takai harda ɗaukar nauyin karatun mahaifin Hamisun a wancan lokwcin. Sai dai ALLAH bai masa tsahon rai ba, dan ya rasu tun su Hamisu suna ƙanana sosai. Wannan dalilin ne ya saka zuri'ar gidan su Hamisu ta dawo ƙarƙashin kulawar zuri'ar ɗan Jibiya bisa wasulcin da ya barma ƴaƴansu su baba malam. 
     Tabbas baba malam ya cika wannan wasiyya, dan babu irin ɗawainiyar da bayayi da gidan su Hamisun, har takai Hamisu yana ɗaya daga cikin amintattun almajiransa da sukasan abubuwa masu yawan gaske da ya shafesa, kuma Hamisu har cikin gidan yakan shigo bisa yarjewarsa musamman akan aiko da wani abu cikin gidan idan babu ɗaya daga yaran gidan a tare da shi...

        A fusace Yah Ab ya miƙe yana nunasa da yatsa. Har tdallaken kalma yake wajen faɗin, “Amma kasan wannan matsalace ta family da bata shafekaba ko malam. To ta yayama akai kai kasan cewar ana wannan zancen a gidan nan? da har zaka wani shigoma mutane tsulum batare da neman izini ba sai kace wasu sa'anninka. Wannan ma ai raini ne da keta haddin mutane”.
        Nasir da shima baƙin ciki ya lulluɓe ya miƙe a fusacen yana cewa, “Tabbas maganarka gaskiyace Abdallah, mi zaisa ya.........”
      “Kunga ya isa haka” baba malam yay saurin dakatar dasu ganin yanda Hamisu duk ya muzanta abin tausayi. Ya cigaba da cewa, “Tabbas yayi kuskuren shigowa kai tsaye, amma ina ganin mu bashi dama ƙila mu sami bakin zaren matsalar tamu. Hamisu ya akai kasan da wannan issue ɗin?”.
        “ALLAH ya gafaeta malam ka gafarceni, tabbas nima a yanzu na fahimci nayi kuskuren shigowa babu izininku. Ba komai ya jawo hakanba kuma sai ɗunbin ruɗanin dana tsinci kaina a ciki. Abinda yasa kukaji zancen nan a gareni jiya da daddare na dawo daga inda ka turani kai saƙo. Duk da dare yayi sai naga ya dace nazo na kawo maka saƙon koda ban samu damar maka bayani ba. Da ƙyar ma na samu maigadi ya barni na shigo, to a lokacin dana shigone na samu duk jama'ar gidan a sashenka, na iskeku cikin tashin hankali shine na juya da saƙon gidanmu, sai da safe na dawo kawowa nakejin abinda ke faruwa bisa fahimtar da nai daga maganganun ku. Har fitarsu asibiti akan idonane, wlhy da farko naso ɓoyewa nima, sai dai tashin hankalin danaganka a ciki ne naga ya cancanci na bayyana abinda na sani kodan ka samu nutsuwar warware al'amarin yanda ya dace, ku fita daga ruɗani kuma”.
         Duk da sun gamsu da jawabinsa Naser da Abdallah sai zabga masa harara sukeyi. Baba malam ya bashi izinin ƙarasowa ciki. Da ga ɗan gefe ya durƙusa, ya miƙama Abban Adawiya dake kusa da inda yake Envelope ɗin dake a hannunsa.
    Amsa Abban su Adawiya yayi, batare da ya buɗe ba ya miƙama baba malam. Nuni baba malam ɗin yay masa daya buɗe kawai. Abban su Adawiya ya buɗe Envelope ɗin ya ciro hotuna dake a ciki guda uku. Ba ƙaramin razana yayi ba matuƙa, har ta kai yana dubawa hannunsa na rawa.
      Hoton Nu'aymah ne da Yoohan, a ranar farko da tsautsayi ya saka shi taimaka mata lokacin da zata faɗi a ranar salla, har ta kaisa ga kissing ɗinta saboda baki data wage zata masa ihu. Sai rana ta biyu itama ranar daya musulunta. Saina ukun shima dai a ranar farko ne, ya ranƙwafa a kanta suna kallon juna.
       Yanda baba malam yaga ɗan uwan nasa ya shiga wani haline ya sakashi zare hotunan daga hannunsa. A take jinsa ya ƙauracema kunnensa. Hakama ganinsa neman kuɓucema idanunsa yake neman yi. Saurin fara ambaton UBANGIJI yayi yana ƙoƙarin ajiye hotunan Abban Abdallah ya amsa. Shi kam ma na farko kawai ya iya kallo ya miƙama hajjo. Itakam ta jima tana kallon hotunan ko ƙyaftawa batayi, ta haka ne Nu'aymah da ke gani dishi-dishi ta samu damar ganin hotunan gaba ɗayansu a hannun hajjo. 
       Babu wanda ya lura da ita. Sai ganinta kawai sukai kwance ƙasa wanwar. A take falon ya sake rikicewa gaba ɗaya. Duk suka rufu a kanta banda Baba malam da Umm da ko motsi basuyi ba da ga inda suke. Hajjo ma da bata tashiba sai ta maida hotunan a Envelope ɗin batare da ta sake bama kowa ba. Sai ma miƙewa tai ta shiga bedroom ɗinta da su. Babu jimawa ta fito lokacin anata ƙoƙarin zubama Nu'aymah ruwa dan son aga ta farfaɗo. Sai dai kuma ko motsi batai ba balle suyi tunanin dacewa.

      Gidan ya sake cakuɗewa fiye da farko, sai da baba malam ya musu magana sannan suka ɗan nutsu. Tamkar bai damu da halin da Nu'aymah ke a ciki ba ya kalli Hamisu dake zaune tsuru-tsuru yana zare idanu. “Hamisu su waɗanan hotunan ina ka samesu ne haka?”.
      Kansa a ƙasa yace, “Baba malam nine na ɗaukesu da waya gaba ɗaya”.
      “Hakan na nufin komai ka gani kenan Hamisu? Ina nufin duk abinda ke a cikin hotunan nan a gaban idonka aka yisa?”.
        “Eh wlhy duk na gani”.
“To miyasa baka taɓa sanar minba kuma?”.
     Jimmm Hamisu yayi kafin yace, “Wlhy ina tsoron ɗaga maka hankaline, tare da gudun abinda zai iya zuwa ya dawo malam. Amma ka gafarceni nayi kuskure ”.
        Nannauyan numfashin baba malam ya sauke. kafin a sanyaye yace, “Shike nan jeka abinka. na gode sosai”.
     Godiya shima Hamisu yayi ya tashi ya fita.

      Hajjo da duk kejin komai na neman kufce mata tace, “A kaita asibiti, koma minene sai a yisa da ga baya, ciki kuwa harda neman yaron shima. Da yawan mutane wannan suke tsoro ga taimako, shiyyasa bahaushe ke faɗin kasa mutun inuwa ya saka rana. Ko a fuska bazaka taɓa tunain yaron nan zai aikata makamancin hakanba duk da kuwa a farkon shigarsa jikinmu kafiri ne. Ashe ya lulluɓe mune kawai yazo jikinmu ya cutar damu, da alama dama yarinyar nan ya biyo bawai alkairin da muke tsammani daga garesa ba. To kansa yay mawa, ALLAH kuma ya saka mana da gaggawa indai muna da haƙƙi a kansa”.
       A tare duk suka amsa mata da amin. Banda baba malam da yay wani ɗan murmushi ya ɗauke kansa kawai. Abdallah ne ya ɗauki Nu'aymah dake a sanƙame ya fita da ita bisa umarnin Hajjon.

_________________

        An musu ƙarɓar gaggawa saboda halin da Nu'aymah ke a ciki. Musamman ma da suka sami mace ce Doctor ɗin dake dutyn lokacin.
      A yanda suka ga likitocin na kai kawo ɗakin da aka saka Nu'aymah hankalinsu ya daɗa tashi sosai. Duk kuma sanda wani ya fito suka tambaya baya basu amsar komai yake wucewa da sauri. Tun suna ɗaukar al'amarin ƙarami har suka fahimci yanada girma sosai, dan Doctors har uku sun ƙaru bayan ta farko. Sai faman yin ƙus-ƙus kuma sukeyi a tsakaninsu.
     Cikin ƙarfin hali Abba Musbahu ya dubesu yana faɗin, “Bayin ALLAH inaga idan yarinyar nan ta rasa ranta ne ya kamata ku sanar mana, dan kunata sake ɗaga mana hankali da rashin cewarku komai da kai kawon nan naku”.
     Ɗaya da ga cikin likitocin ne ya sadda kansa ƙasa cikin girmamawa yace, “Ai mana afuwa malam, ba muna ɓoye muku komai baneba. Kawai muna akan aikine shiyyasa, amma insha ALLAHU zakuji komai nanda ƴan mintuna kaɗan”.
       Shiru wajen yayi babu wanda yace komai, sai dai a zukatansu sam basu gamsu da zancen likitan ba.

★★★

        Tunda aka fita da Nu'aymah asibiti baba malam ya koma sashensa. Zaune yake a study room ɗinsa saman wata kujera da ke ɗan lilasa idan yana kanta. Duk da rana ce ɗakin yayi duhu sosai kasancewar bai ɗaga labule ko guda ɗaya ba a ɗakin. Bai kuma kunna fitila ba sai ɗan hasken da ake gani kaɗan kasancewar na hasken rana. Kwance yake a jikin kujerar idanunsa a lumshe ya faɗa duniya mafi nisan zango a tunani.
         Tun daga daren jiya har zuwa yanzun zuciyarsa a ruɗani take. Ruɗani irin wanda ƙwaƙwalwa bata iya rarrabe gaskiya da ƙarya, fari da baƙi, haggu da dama........
        Motsin da yaji a kusa da shine ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar. Umm ce ya gani cikin ɗan hasken da ɗakin ke da shi. tsaye take a gefensa dafe da kanta alamar tana a cikin matsala. Zumbur ya miƙe ya riƙota ganin tana layi, ga hakki tanayi kamar wadda tayi gudu a cikin sahara.
      Kujera doguwa dake a ɗakin ƙwara ɗaya kacal ya nufa da ita, ya kwantar da ita jikinsa sai tsuma ya keyi. “Jannat miya sameki?”. 
       Duk da halin da take a ciki itama sai da tausayinsa ya kamata jin a yanda yay magana. Tasan ƙarfin hali kawai ya keyi tun jiya akan al'amarin nan, amma shima a ruɗanin yake. Hannunsa ta kamo da ɗayan hannunta, ɗayan kuma na akan ƙirjinta da ke mata azabar zafi tamkar zai buɗe.
         “Sooraj inaji a jikina mutuwa zanyi, a wannan karon zuciyata bazata iya ɗaukar wannan al'amarinba. Abban Nu'aymah akwai ruɗani a cikin zancen nan, amma ni kaina na kasa banbance mai gaskiya tsakanin ƴarmu da likitocin nan. Idan da ace likita ɗaya ne ya faɗa sai muce ko haɗa baki akayi da shine, amma kaga harsu uku, ɗayan ma bamu santa ba tunda asibiti suka sameta. Sannan Sooraj a kwanakin cikin nan da aka ambata ya kasance jikin Nu'aymah ban taɓa ganin wani alama na mai ciki tattare da yarinyarta ba, babban tashin hankalina kuma shine tabbas watan da ya shige na azumi banga Nu'aymah tayi jini ba har suka wuce saudia, wancan watan kuma a farkon wata tayisa. Kasan dai ita jininta baya ɓoyuwa a gidan nan saboda lalurar da yake zuwa mata da shi. Sooraj na shiga ruɗani wlhy”. 
      Ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
       Shima sai ya ji hawaye na ziraro masa batare da ya shirya yin hakan ba. Dan zuciyarsa ta karye gaba ɗaya. Ya rungumeta a jikinsa sukayi mai isarsu kafin ya ɗagota yana kallon yanda take faman dafe ƙirjin nata har yanzun.
        “Jannat bazaki mutuba, bana fata ki tafi ki barni cikin wannan tarnaƙin, nima zuciyar tawa ba iya ɗauka zatai ba. Ki daure dan ALLAH muyi imani da ƙaddara. Amma kamar yanda kike cikin ruɗani a wannan al'amarin wlhy nima haka nake a ciki. Na ƙiyasta duka zuwan Yoohan cikin gidan nan gaba ɗaya ban iya tunano ta yanda har ya samu keɓancewa da Nu'aymah ba. Wlhy zuciyata ta kasa yarda Nu'aymah da Yoohan zasu aikata wannan ɓarnar. Idan kuma nace ban amince sun aikata ɗinba yaya xanyi da waɗan nan hujjojin bayyanannu kuma Jannat? Ya ALLAH ka bayyanar da gaskiyar al'amarin nan koda a cikin Zukatanmu ne ya Rabbi”.
      Haka sukaita hawaye har sai da baba malam ya fahimci Umm na neman rasa numfashin ta. Sake ruɗewa yayi ya shiga girgiza ta jikinsa na rawa. Yama rasa miya kamata yay mata, kiran sunanta kawai yake iya yi da iya ƙarfinsa.
       Hakanne ya jawo hankalin su Hajjo da ke zaune jigum-jigum suna jiran jin halin da Nu'aymah dake a a sibiti take a ciki. Har rige-rigen shiga sashen sukeyi, gashi duk mazan gidan sun wuce asibiti tare da Nu'aymah, dama baba malam ɗinne kawai ya rage. 
         A hankali inuwar mutum dake a jikin windown tana kallon su baba malam ta kafar labule ta janye daga wajen. Hakan yay dai-dai da fara shigowar matan gidan. Babu wanda hajijiya bata kusan kwasa ba ganin da gaske Umm bata numfashi, ga baba malam yau duk jarumtarsa da kawaici yana zirar da hawaye............

_____________★★★

             A asibiti bayan sallar la'asar Doctors ɗin suka buƙaci ganin wasu a cikin su Abba. Su duka ukun suka shiga office ɗin, aka bar su Abdallah kawai a waje.
     Sai da aka nuna musu wajen zama kafin likitar mace tai ɗan gyaran murya tana kallon sauran ƴan uwanta uku likitocin. Kawuna suka ɗaga mata alamar bata damar magana. Ta amsa musu da kai itama tana sake gyara zamanta. 
       Cike da girmamawa a garesu tace, “Dama munason muku bayani ne akan abinda ke faruwa idan bazaku damu ba”. Babu wanda ya iya ce mata komai a cikinsu. Dan haka ta cigaba da faɗin, “Maganar gaskiya yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali, duk yanda mukaso ceto rayuwarta ma mun gagara, dan aikin yafi ƙarfinmu. Amma a yanzu dai abinda muka iya kawai shine jawo numfashin ta da wasu na'urori kafin a samu mafita. Muna da likitan da zai iya duba matsalarta, sai dai kuma ganinsa shine tashin hankalin musamman da ya kasance yau kwanakinsa goma sha ɗaya kacal da barin nan, sannan aikinsa yana da ƙa'ida bana waje ɗaya bane balle muce muku kai tsaye ga inda zaku iya samunsa. Amma yanzu dai in taƙaice zance matsayinku na iyaye a garemu masu daraja da kima bazamu iya ganin matsala a gareku ba mu kauda idanunmu, dan haka munyi ƙoƙarin nemansa dan muji ko zai iya mana alfarmar ganinsa amma bai ɗaga wayar ba, sai dai mun kira amintaccen sa da ke a garin Lagos a yanzu haka ya tabbatar mana zai bincika mana shi, idan har ya amince zaizo zamu iya ganinsa a koda yaushe. idan bai aminceba yana da wani uzurin kuma shi zaizo ya ga yarinyar ko zai iya bada wata mafita akan matsalar tata dan shima babban likita ne”.
          Cike da gamsuwa da bayaninta duk suka karɓa mata da “ALLAH yasa a dace” tare da musu godiya sosai akan wannan taimako da sukai musu. Daga haka suka tashi suka fito kowa yana addu'ar dacewa a cikin ransa da jin tausayin ɗiyar ɗan uwan nasu dama ɗan uwan nasu shi kansa fiye da ko yaushe a yau.

        Kamar da wasa sai ga su Abbah sun shafe fin awanni bakwai amma babu labarin likitan da ake tsumayen jira. Su kuma likitocin basuce musu komaiba. Haka suka cigaba da zama jugum-jugum suna addu'oi a zukatansu har tsahon wani lokaci. Shigar lokacin sallar la'asar ne ya sake tadasu suka nufi massallaci, bayan an idar da salla suka sake fitowa suka sake zaman jiran tsammani.
       Wata cikkakkiyar awa biyu suka sake sharewa gangariya, Abban Abdallah na ƙoƙarin miƙewa zuwa office ɗin Doctor ɗin nan mace mai suna Doctor Ai'sha yaji yaya ake ciki? sai ya hangota tana fitowa da ga office ɗin nata fuskarta washe da murmushi.
      Kafin ya samu damar mata magana yaga ta nufi ƙofar fita da hanzarinta. Kamar zai bita sai kuma ya fasa, ya cigaba da tsaiwa a wajen yana jiran ganin ko zata dawo. 
          Tsayuwar tasa tayi dai-dai da shigowarsa cike da takunsa na ƙarfi da lafiya, wanda idan baka saniba zaka iya ɗauka tsabar isa ce da izza ke ɗawainiya da shi. Amma sam ba haka baneba, halittar tasa ce kawai haka.
       Kansa duƙe yake sakamakon file ɗin Nu'aymah da ke a hannunsa yana dubawa. Ya ɗan rame, hakan ya saka sake fiddo hasken fatarsa da ƙyawun da ALLAH yay masa. Ga wani annuri na hasken ibadar ALLAH tattare da shi, wanda ya sake ɗaukaka ƙwarjininsa da cikar haiba kai kace farin watane ɗan daren sha biyar. Kamar kullum sanye yake cikin suit, na yau ɗin sun kasance Coffee color, sai farar shirt da ke a ciki babu necktie, dan maɓallan Shirt ɗinma kusan uku a buɗe suke.
        Doctor Aysha na daga gefen damarsa duk da yaɗan zartata kaɗan a tafiyar kasancewar ya fita tsayi, da alama bayani take masa akan matsalar. Sai Solomon dake ɗauke da jikkarsa a hannu, da Doctor Sa'ad da wasu likitoci biyu da Nurse kusan huɗu na biye da bayansa. Har suka zo suka gitta Abban Abdallah bai ga fuskarsa da ƙyau ba, dan har lokacin kan nasa a sunkuye yake ga file ɗin. A dai-dai ƙofar ɗakin da Nu'aymah ke ciki suka ja birki, su Abdallah da duk suka zuba nusu ido duk suka miƙe, sai dai kafin wani cikinsu yace wani abu. Ya tura ƙofar ɗakin ya shige har lokacin hankalinsa nakan file ɗin.
        Iya shi da Doctors ɗin suka shiga, yayinda Solomon da Nurses ɗin suka ja birki a bakin ƙofar.
      Sai da ya ƙarasa gab da gadon da Nu'aymah ke kwance sannan ya ajiye file ɗin ya kai dubansa gareta, bai ganeta ba sam, saboda na'urar da aka saka mata mai taimakama numfashinta fita. Ya ɗan ranƙwafo kanta kaɗan ya kai hannu ya zare na'urar mai haɗe da oxygen. Ba ƙaramin tsirgawa zuciyarsa tayi ba, amma saboda son sake gaskta abinda yake tunanin sai ya zare Glasses ɗin idonsa da ya ƙara ƙawata fuskar tashi. ‘Kamar dai itace’ ya ayyana a zuciyarsa cike da kokwanto. 
        A fili kam sai yay saurin maida mata na'urar saboda ganin yanda ƙirjinta ke sama da ƙasa da sauri-sauri ga jikinta na vibration har gadon kansa na motsawa. Luuu ya ɗanyi da idanunsa ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta. murya a cinkushe ya dubi Doctor Aysha a ɗan faɗace ya ke faɗin, “Anyi matuƙar sakaci da lafiyar yarinyar nan da har take neman shiga matakin ƙarshe, ina mamakin yanda mutane suke abu tamkar basu san muhimmacin lafiya ba. Mtsoww!!. Su Iyayenta fa?”.
      Dr Sa'ad ne ya bashi amsa da “Haka suke wlhy Doctor, sai kuma an mutu suce likitoci ne da sakaci bayan tun farko sune da matsalar su.........”
         Cikin sauri Dr Aysha ta katse Dr Sa'ad ɗin dan bata son ya sake tunzura Dr Yoohan, “Ayi haƙuri sir, duk family nata suna waje, duk da kasancewarsu manyan mutane suna tare da ita tun ɗazun fiye da awa tara wlhy”.
      Baice komaiba, ya dai sake kai dubansa ga Nu'aymahn, sai kuma yay azamar ɗauke kansa batare da nasan dalilin yin hakan ba. Juyawa yay zai fita. Doctor Aysha tai saurin ɗaukar file ɗin da ya ajiye su ka sake bin bayansa ita da su Doctor Sa'ad da ke ta faman cika yana batsewa saboda haushin kare dangin Nu'aymah da tayi.
       Yanzun ma bai duba kowa ba a cikin su Abdallah yay wucewarsa. Duk da kallo suka sake binsa suma, yayinda Abban Adawiya yaso gane sa, sai dai baiyi magana ba jin suma su Abban Abdallah basu ce komai ba.
        Da ga shi sai Solomon suka shiga office ɗinsa, komai ƙal yake, dan tunda Dr Aysha ta tabbatar da zuwan nasa ta saka aka sake tsaftace office ɗin duk da dama ƙa'ida kullum sai an share an goge. Ƙaramin ɗakin hutun dake cikin office ɗin Solo ya ƙarasa. Ganin nanma komai dai-dai yake yanda yasan Yoohan ɗin na buƙata sai ya ajiye jikkar ya fito. 
      Tsaye ya iske sa yana ƙoƙarin zame rigar suit ɗinsa, har Solomon ɗin ya kai ƙofar fita ya tsinkayi muryarsa ya na faɗin, “Kiramin Dr Aysha”.
       “Okay sir”.
     Solo ya faɗa da sauri yana ficewa. Hanging ɗin rigar yayi bayan kujerarsa ta zama, sannan ya fara ƙoƙarin kunna Computer ɗin da ke a saman desk ɗin na sa. Yanda yay matuƙar zuba idanunsa ga Computer ɗin zai tabbatar maka abunda yake yi a ciki yana da matuƙar muhimmanci. A haka Dr Aysha ta turo ƙofar bayan tayi knocking ta shigo, dan tasan ba lallai ta samu amsa ba musamman a irin wannan lokacin da ta tabbatar hankalinsa gabaki ɗayansa nakan patient ɗin da ke jiran taimakonsa.
      Batare da ya ɗago ya kalleta ba yace, “Matsalar yarinyarnan babba ne, sai dai zan mata wani ƙaramin theatre yanzun, dan haka ku shiryata zuwa theatre room”.  Ya miƙa mata file ɗin gabansa yana cigaba da faɗin, “Wannan mahaifinta zai saka hannu anan, ko mahaifiyarta ko mijinta. Kuma dole ɗaya da ga cikinsu ake buƙata kawai”.
      Ɗan jimm Dr Aysha tayi. sai kuma komi ta tuna oho, ta gyaɗa masa kai da faɗin “Okay sir”. Daga haka ta fice shi kuma ya miƙe ya nufi ɗakin da ke a cikin office ɗin.........✍

          
______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/26, 3:26 PM] +234 806 269 3623: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 37

............A tsaitsaye ta iske su Abba gaba ɗaya yanzun kam. Cikin girmamawa ta ƙarasa garesu. Fuskarta ɗauke da murmushi tace, “Congratulations, mun samu nasara babban likitan da ganinsa ke da matuƙar wahala ya amshi gayyatarmu”.
     Cike da jin daɗi suka shiga faɗin Alhmdllh.
       Da ga haka ta buƙaci magana da su Abbah. Babu musu suka bita office. Bayani tai musu akan ƙa'idar saka hannu da Dr Yoohan ya sanar mata, Abba Musbahu ne ya nuna ai suma iyayen Nu'aymah ne idan sun saka hannun babu damuwa, tunda yayansu baya a kusa, gashi kuma tace za'a shiga aikin ne da gaggawa........
     Ita dai kasa ce musu komai tayi dan suna da girma da kima a idonta, sannan kuma ta tabbatar tunda Dr Yoohan yace a cikin ukun ɗaya ake buƙata dolene hakan za'ayi. Ganin shirun da tayi ne ya saka Abban Adawiya fahimtar akwai matsala, dan haka sai ya kalli ƴan uwansa, “Inaga kawai mu kira Yayan kamar zaifi fa'ida, dan sun fimu sanin muhimmancin sharɗanta hakan”.
    Duk sun gamsu da bayaninsa. Abban Abdallah ya ciro waya yay kiran Baba malam. Kirannasa ya shiga wayar baba malam ɗinne dai-dai lokacin da Umm da Hajjo ta shafama ruwa a fuska ta kawo nannauyan numfashi alamar dama suma tayi. Kusan a tare duk suma suka sauke numfashin, musamman ma baba malam da ke jin kamar an tsundumasa a aljanna.
    Ba ƙaramin faɗuwa kuma gabansa yayiba ganin kiran ɗan uwansa, amma sai yay ƙarfin halin ɗagawa ya saka a kunne. “Rudwan ta rasu ko?”.
    Da dauri Abban Abdallah yace, “A'a Yaya tana da ranta”. Da ga haka yayma baba malam bayanin halin da ake ciki. Kamar baba malam bazaice komaiba. sai kuma ya nisa kaɗan da faɗin, “Shike nan ina zuwa”.

★★★★
    
             Bayan saka hannun baba malam Yoohan da wasu likitocin biyu sai Dr Aysha ta uku suka shiga theatre room da Nu'aymah da ko maƙiyinta ya ganta a wannan lokacin sai ya tausaya mata.
     Tun suna irga mintuna har suka koma awanni, dan anyi sallar magrib har isha'i su Yoohan basu fitoba. Duk jikinsu ya kumayin sanyi. amma saboda ƙarfin hali irin na baba malan haka ya bama matan da samarin ƴaƴan nasu umarnin suje gida su huta haka nan. Basu da ikon masa musu akan hakan, amma a kallo ɗaya zaka fahimci ba haka suka so ba, dan Abdallah kasa daurewa yay kansa a ƙasa yace, “Abba da ku kuje kawai, ni zan zauna har su fito insha ALLAHU”.
     Da sauri Naser shima yace, “Abba nima ina nan harsu fito dan ALLAH”. Ta ƙasan ido Abdallah ya ballama Naser harara, amma dai baice komai ba.
       Shiru kawai baba malam yay yana dubansu, dan shi harga ALLAH tausayi suke bashi. Kafin baba malam yace wani abu Hajjo tace, “Ai mu duka ma tafiyar tamu bamai yuwuwa bace ba, dan ya kamata muga fitowarsu ko ma tafi da ɗan ƙwarin gwiwa. ALLAH dai ya bata lafiya”.
      Duk da Amin suka amsa mata. Daga haka kuma babu wanda ya sake cewa komai, suka sake cigaba da zaman jiran tsammani.

       Sai kusan ƙarfe tara na dare dai-dai su Yoohan suka fito, duk su baba malam suka miƙe tsaye don son jin yaya ake ciki?  Su Doctor Aysha ne kawai suka tsaya musu bayani, dan Yoohan yana ɗakin bai fito ba tukunna.
      A tare suka shiga faɗin Alhmdllhi, Koba komai sunɗan sami kwanciyar hankali duk da ba cewa akai Nu'aymahn ta tashi garas bane ba. 
        Su Dr Aysha da suma fuskokinsu ke nuna alamar nutsuwar jin daɗin yanda aikin ya kasance suka sanar da su zasu iya tafiya gida. Dan Doctor yace babu wanda zai iya ganin Nu'aymah a yanzu, hasalima ba'a buƙatar kowa a gareta.
          Duk da ba haka suka so ba sun gamsu da bayanin Doctor Mubarak ɗin, dan haka baba malam yace su wuce ɗin kawai, dama gashi sun baro Umm ita kaɗai a gida sai su Hajarah da ke a tare da ita. 

          ★★★★‡★★★★

      Kamar jiya yau ma baba malam ba shine yaja salla a massallaci ba, hakama bayan an idar bai zauna wajen karatu ba ya shiga gida. 
          Tun a daren jiya ya gama yanke shawarar da ta dace akan wannan al'amarin, dan haka koda ya shigo gidan waya ya ɗauka, ya rubuta gajeren text massege ya tura. Umm na zaune na azkar tana kallonsa. Yanda baice mata komaiba itama batace ɗinba har sai da ya kammala ya ɗago yana kallonta.
      Ɗan Murmushin ƙarfin hali tai masa ta duƙar da kanta. Shima sai ya ɗan murmusa cike da jarumta ya kirayi sunanta a hankali. ɗagowa tai ta sake kallonsa. Muryarsa a sanyaye yace, “Ki ƙara haƙuri Jannat kinji, nasan kina cutuwa matuƙa, amma inason ki ɗauki komai matsayin jarabawa, kinsan ita duniya dama UBANGIJI bai yita dan ta kasance abin jin daɗin ɗan adam ba a kullum”.
         Ƙwallar da suka cika mata idanu ta haɗiye da ƙyar, ta maida kanta ƙasa dan karya gani tana faɗin, “Insha ALLAHU, ALLAH ya bamu ikon cinyewa”.
       “Amen ya rabbi” ya amsa mata shima.
        Shiru ɗakin yayi kowa na nazari a zuciyarsa, a haka har gari ya ƙarasa wayewa tangaran. Duk da Umm bazata iya aiki ba haka ta fita cikin dauriya ta lissafama Rabi abinda zatayi. Ita kuma ta koma ɗakin baba malam inda ta tarar zai shiga wanka. 

★★★

       A ɓangaren Abdallah kam tun a daren jiya ya karɓa Number Yoohan a wajen Ahmad. Babu irin tambayar da Ahmad ɗin bai masa ba akan mizaiyi da Number amma yaƙi faɗa masa. Dan haka ya ƙyalesa kawai yay kwanciyarsa.
        Tun a daren ya fito harabar gidansu ya kira wani abokinsa SSS, bayani ya kora masa akan taimakon da yake son yay masa, babu musu kuwa ya amsa zaiyi. ya buƙaci Number Yoohan a take ya tura masa ita da ƙara jaddada masa dan ALLAH zuwa gobe yake buƙatar result.

       A safiyar yau kam kusan ƙarfe bakwai da kwata sai ga kiran abokin nasa. Bayan sun gaisa da ɗan tsokanar juna kamar yanda suka saba ya sanar masa aikinsa ya kammala, yaya yakeso ayi?.
       “Wow gaskiya na gode matuƙa Mahmood, amma nayi mamakin jin mai Number wai yana a kano, kasan a yanda naji Abuja yake da zama”.
       “Eh to, zata iya yuwuwa kanon yazo, dan a yanzu hakama sai da na sake tabbatar da yana a inda muka gansa jiya sannan na kiraka, dama wannan shine amfanin tracing ɗin ai”.
         “Gaskiya kam, aiko nagode sosai. Abu nagaba shine zanzo mu haɗu yanzun, dan ina buƙatar a kama min shi ne”.
      Dariya sosai Mahmood ya keyi, yace, “Shegen sama mi yayi maka ne? Halan wata harƙallar kuka ƙulla ya doje?”.
        “Ai harƙallar dake tsakanina da wannan shegen ta wuce duk yanda zakai tunani wlhy Mahmood, kai dai faɗamin inda kake nazo na sameka kawai”.........

      
   ★∆∆★

          Sai ƙarfe shida da wasu mintuna ya farka na safiya. ya tashi a ɗan firgice bakinsa ɗauke da addu'ar barci da ALLAH ya bashi ikon riƙewa a lokaci ƙanƙani kamar yanda baba malam ya koyar da shi. Tunda ALLAH yasa ya musulinta yau ne karan farko da zaiyi sallar asubahi a makare. Dan alarm yake sakawa gudun karya makara. Sannan kuma baba malam duk asubahi sai ya kirasa ya tadashi. Hakan na masa daɗi, yana kuma ƙara masa ƙwarin gwiwa. Dalilin makarar tasa ta yau ma dan bai kwanta da wuri bane, dan tun bayan fitowarsu theatre ya duƙufa ne akan binciken matsalar Nu'aymah. Dalilin binciken nema ya sakashi kwana a asibitin, Solomon ne kawai yaje Hotel ya kwana.
        Bayi ya shiga ya ɗauro alwala ya fito, ya buɗe jakka ya ciri sallaya da yanzu bai rabo da ita a kayansa duk inda zaije, shimfiɗawa yayi sannan ya zura jallabiya ya tada salla. Yana idarwa saƙo na shigowa wayarsa, sai dai baibi takai ba ya miƙe ya fita dan yana son duba patient ɗinsa. 
       Kusan mintuna ashirin ya ɗauka a ɗakin da Nu'aymah take sannan ya fito ya koma office. Yanzunma baibi takan wayarba dai ya shiga wanka. Bayan ya fitone ya ɗauka wayar saboda ganin screen ɗin yana haske. Missed calls ne har uku yaci karo da su duk na Mumynsa. Bai kirata ba sai ƙoƙarin duba saƙon da ya gani yay cike da mamakin ganin baba malam ne.
         Yana gama duba saƙon yay ƙoƙarin kiran baba malam ɗin. Cikin sa'a kuwa ya ɗaga. Tamkar yana a gabansa haka ya rissina da girmamawa ya gaida shi, shima kuma da ga can baba malam ya amsa masa da kulawa tamkar yanda ya saba.
       “Uncle dama naga massege ɗinka ne, ina fatan dai lafiya?”.
      “To Alhmdllh Yahya, kawai dai inason ganinka ɗinne, ina fatan bazan shiga aikinka ba?”.
        “A'a Uncle babu damuwa, dan yanzu hakama ina cikin kano, insha ALLAHU zuwa anjima zan shigo”.
        “Masha ALLAH, ALLAH ya nuna mana”.
    Daga haka sukai sallama Yoohan na cigaba da mamakin ganin nasa da baba malam ke buƙatar yi, dan ya ƙara fahimtar kiran nasa nada muhimmanci sosai. Bai kira Momy ba sai da ya shirya cikin ƙanun kaya. Daga wandon har riga duk baƙaƙe ne, sai suka sake fito masa da ainahin farar fatarsa daketa ƙyalli da ɗaukar idanu. Yaɗan saka turare tare da gyara gashinsa da a yanzu yake ɗauke da aski na mutunci, sai sajensa dake kwance luf masha ALLAH.
        Jin motsi a office ɗin nasa ya sakashi ɗaukar p-cap ɗinsa jaa ya ɗora a kai, sannan ya zauna bakin gado ya saka takalmansa suma baƙaƙe da ɗan kwalliyar ja kaɗan.

          Harya ƙaraso cikin office ɗin da aka gyara tsaf yana zuba ƙamshi Solomon na kallonsa ta ƙasan ido, a ransa kuwa yaba iya ado da kwalliya irinta ogan nasu ya keyi, sai dai yana mamakin ganin a ƴan kwanakin nan gaba ɗaya ya daina saka sarƙa, hakama ƴan kunne baya sakawa. Saurin katse tunaninsa yayi cike da girmamawa ya miƙe tsaye yana faɗin,
      “Good Morning sir”.
A taƙaice Yoohan yace, “Same”. Yana zama a kujerarsa. Ɗan kallon Solomon ɗin yayi ya ɗauke kansa da faɗin, “Bani Coffee”.
       Solomon na cikin haɗa coffee ɗin akai knocking ƙofar. Izinin shigowa ya bada idonsa akan file ɗin Nu'aymah daya tattara na binciken jiya. Dr Aysha ta shigo hannunta ɗauke da basket. Saman table ɗin ta ɗora tana faɗin, “Good morning Doctor”.
        Kaɗan ya kalleta ya ɗauke kansa zai maida ga file ɗin, sai kuma ya sake dubanta ya dubi basket ɗin yana faɗin, “Morning. How are you?”.
     “Alhmdllh sir” ta faɗa tana sake faɗaɗa murmushinta ganin yanda yake kallon basket ɗin data ajiye. A taƙaice tace, “Breakfast. ban saniba ko zaka iya cin jagwalgwalon hausawa”.
      Ɗan lumshe idanu yay ya buɗe yana maida kansa ga abinda yakeyi da faɗin, “Thanks” a taƙaice.
     Bata damuba, sai ma murmushi da ta sakeyi tana amsa gaisuwar da Solomon ke mata fuskarsa a murtuke kamar ma shine boss ɗin. Coffee ɗin daya haɗa ya ajiye gaban Yoohan. 
        Nanma “Thanks” ɗin Yoohan yace masa batare da ya kallesa ba. Sai da yaja wasu sakanni sannan ya rufe file ɗin ya gyara zamansa da ƙyau yana ɗaukar kofin coffee ɗin da ɗan kallon Dr Aysha da har yanzu take a zaune.
       “Matsalar yarinyarnan babbace, ina buƙatar magana da mahaifinta”.
      “Sir kana nufin aikin da akai mata jiya ba shine na ainahin matsalarta ba kenan?”.
        Sai da ya kurɓa coffee ɗin sannan ya girgiza mata kai, “No ba shi bane dai kai tsaye, dan tana da matsala a ƙwaƙwalwa, wanda shine musabbabin yawaita haddasa mata matsalar saurin suma da wasu matsalolin da akai mata aiki a kansu jiya”.
     Cike da tausayawa Dr Aysha tace, “ALLAH sarki, ALLAH ya bata lafiya, gata yarinya ƙarama dan da alama bata wuce 17years zuwa 18 ba”. Yoohan baice komai ba dai. Ganin haka Dr Aysha ta miƙe dan ta bashi damar cin abincin idan yana so. “Bara naje to Doctor, zan duba ko wani cikin ƴan gidan nasu ya shigo”.
     Kansa kawai ya ɗaga mata. Ta juya ta fita itama tana jinjina hali irin na Dr Yoohan a ranta. Amma ita duk da haka sam baya ɓata mata rai, sai ma birgeta da ya keyi.
      Da harara kuwa Solomon dake can gefe ya raka bayanta.

       Dr Aysha na fita su Abdallah na isowa bakin ƙofar office ɗin Yoohan su biyar, dan bayan Abdallah akwai Mahmood da yaransa su uku, sunbar biyu a mota kuma. Mahmood ya ɗaga wayarsa yana faɗin, “Nan shine alama ta nuna, kuma da alama shi ɗinne” ya ƙare maganar yana nuna masa rubutun dake a saman office ɗin mai ɗauke da sunan *_Dr Yoohan Goshpower_*.
       Wani Murmushin mugunta da jin daɗi Abdallah yayi, batare da ya jira sunyi knocking ba ya tura ƙofar office ɗin kawai ya shige.

         Duk da a yanda aka buɗe ƙofar Yoohan baiko motsaba balle yabar abinda yakeyi. Sai Solomon ne ya miƙe zumbur yay magana cikin daka tsawa. Cikin harshen nasara yace, “Kai wanene zaka shigo nan babu neman izini?”.
      Wani banzan kallo Abdallah yayma Solo, sai kuma ya maida idonsa ga Yoohan da har yanzu bai ɗago ya kallesu ba, baima nuna alamar yasan da shigowar tasu office ɗin ba. Hakan sai ya sake fusata Yah Ab, shima a tsawace yace, “Tsaya matsayinka na bodyguard yaro, dan ubangidanka ne dai-dai da ni”.
      Solomon zaiyi magana Yoohan da har yanzu ɗin bai ɗago ba ya ɗaga masa hannu alamar kar yace komai. Shirun kuwa Solo yayi ransa na masa ƙuna da takaicin rashin sauran ƴan uwansa.
        Cike da ƙasaita Yoohan ya ɗago fuskarsa da ada p-cap ta rufe kusan rabi saboda kansa da ke a duƙe. Manyan idanunsa ya sauke akan Abdallah, sai kuma ya maida kansu Mahmood da ke tsaitsaye suma. Batare da yayi magana ba yay musu nuni da wajen zama cike da basar da yanayin da ya ga fuskokinsu.
      Abdallah ne yaja tsaki da ƙarasawa gaban table ɗin Yoohan ɗin, cike da kaushin murya yace, “Ba zaman shan ac da kallon syringe ya kawomu ba, munzo arresting naka ne”.
     Ɗan jim Yoohan yayi kamar bazaiyi magana ba, sai kuma ya motsa laɓɓansa a hankali yace, “For......?”. A takaice cike da rainin wayo
        A hasale Yah Abdallah ya jefa masa farar envelope ɗin hannunsa.
      Da farko Yoohan baiyi niyar dubawa ba, sai dai ganin tsantsar kamannin Abdallah da su baba malam ya sakashi ɗaukar Envelope ɗin, hotunan ciki ya fiddo. A karon farko ƙirjinsa ya ɗan buga saboda cin karo da abinda baiyi tsammanin gani ba. Da kafin ya musulinta ne akazo masa da wannan hoton da yake kissing ɗin Nu'aymah bazai nuna ya damuba, amma a yanzu yana matuƙar sake ƙyamatar wannan ɗabi'ar, idan kuma ya tuna ya aikata akan kuskure yana jin matuƙar takai ci. Kallon na biyu da na ukun yay su ma, amma duk da haka sai ya dake, ya sake tsuke fuska fiye da yanda suka sameta yana jifan Abdallah da yake masa kallon tsana da ƙyama shima da kallo wulaƙanci.
     Kafin wani a cikinsu ya samu damar cewa wani abu Dr Aysha ta shigo office ɗin ita da Dr Mubarak, dan sunyi knocking har sau biyu basuji ya amsa ba. A zatonsu ko yayi busy ne shiyyasa suka shigo kawai tunda sunsan babu wani mara lafiya da zai duba bayan Nu'aymah kamar yanda ya sanar musu tunkan yazo.
      Da mamaki suke bin su Abdallah da kallon tsoro, sai kuma suka kalli Dr Yoohan ɗin shima. Ganin yanda ya tsuke fuska ya sakasu kasa masa tambayar dake a bakunansu, sai Dr Mubarak ne ya kalli Solomon da ya gama tsumewa da baƙin ciki. “Solomon mike faruwa anan ne?”.
       Solomon zai basu amsa Yoohan ya katsesa da faɗin, “Mi kuke buƙata?”. Shiru Solo yayi dan ya fahimci Yoohan ɗin baya buƙatar ya faɗa. Suma jin hakasai duk suka sake maida kallonsu garesa, cike da ƙarfin hali Dr Aysha tace, “Dama mahaifin yarinyar ne ya zo, shine nace a shigo da shi?”.
      Kansa kawai ya gyaɗa mata, sannan ya maida dubansa ga su Abdallah “Zaku iya fita ga ƙofa ko”. Ya faɗa cike da tsantsar rainin hankali. Abdallah zaiyi magana Mahmood ya matso da sauri yana nunama Yoohan I'd card ɗinsa. Hakan yayi dai-dai da shigowar Baba malam office ɗin bisa jagorancin Dr Aysha.
        Mahmood da ya fara faɗin, “Muɗin jami'ai ne daga hukumar s......” ya kasa ƙarasawa saboda tozali da baba malam. Yoohan ma mamakin ganin baba malam ɗinne ya sakashi sakin hotunan hannunsa saman desk ɗin.
         Baba malam kuma da duk ke binsu da kallon mamaki ya sauke idanunsa kan Yoohan a ƙarshe. Takawa yay a hankali zuwa gaban tebirin, ya kai hannu ya ɗiba hotunan dan tun daga inda yake yana hango komai na cikinsu. Ɗauka yay ya sakasu cikin envelope ɗin. Kafin ya samu damar faɗin wani abu saboda nauyi da bakinsa yay masa Abdallah yace, “Abba munafukin nan ashe likita ne anan, dan hak.......”
       Baba malam yay saurin girgiza masa kai, mamakinsa na sake bayyana sosai da ganin Yoohan ɗin wai matsayin likita. Koda wasa bai taɓa kawo hakan a ransaba shikam, hasalima ya ɗauka Yoohan ɗan kasuwa ne kawai.
        Yoohan dai ya gaza yin magana, kallon baba malam ɗin kawai ya ke ko ƙyafta ido bayayi. Baba malam ya ajiye envelope ɗin yana duban su Mahmood. “Zaku iya tafiya abinku mun gode”. Kamar Abdallah zaiyi magana sai kuma yayi shiru, sai ma alamar su Mahmood suje ɗin kawai yay musu da kai. Batare da Mahmood yace komaiba ya nunama yaransa hanyar fita suka fice badan ransu yaso hakanba.
         Bayan fitar tasu babu wanda ya iya sake yin magana a office ɗin har tsahon kusan mintuna biyu, sai Abdallah ne keta antayama Yoohan harara, Solomon kuma na hararsu gaba ɗayansu. Dan duk haushi suke bashi.    
       Cikin ƙarfin hali Yoohan ya duba Dr Aysha da Solomon. Murya a sarƙe yace, “Kuje zan neme ku”. Babu wanda yay musu a cikinsu suka nufi hanyar fita kowanne da abinda yake kissimawa a cikin zuciyarsa.
         “Dama kai likita ne Yahya?”.
  Kai Yoohan ya jinjina ma baba malam da yay tambayar, yace, “Eh Uncle”.
    Murmushi baba malam yayi a karo na farko, yace, “Masha ALLAH, ALLAH ya sanya albarka, yay riƙo da hannunka wajen aikata alkairi ga al'umar MANZON ALLAH ”.
     Cike da jin daɗi Yoohan ya amsa da “Amin” kansa a ƙasa dan ya kasa kallon baba malam ɗin, harga ALLAH kwarjini yake masa matuƙa, musamman ma yanzu da yaga hotunan nan duk da bai tabbatar da alaƙar dake tsakanin baba malam ɗin da yarinyar da har yanzu shi ko sunanta ma bai saniba.
          Cike da takaici Abdallah yace, “Abba mutum nan fa shineya lalata rayuwar Nu'aymah, ta yaya zamu cigaba da fiskantarsa kamar munajin tsoronsa?”.
        Da turanci Abdallah yay maganar, dan haka Yoohan yaji komai, ya kuma fahimci komai. Sai dai kafin yace wani abu baba malam ya kalli Abdallah fuskarsa na nuna ɓacin rai, sai dai kuma baice komai ba. Yanzun ma shiru Abdallah yay badan yaso hakanba, sai dai yanda yake sauke huci zai tabbatar maka cewar zuciyar ƴan mazan a wuya take.
       Fuuu ya fice a fusace da ga office ɗin. Da ga baba malam har Yoohan duk binsa sukai da kallo............✍

______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[5/27, 2:14 PM] +234 806 269 3623: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 38

.............Duk yanda su Abdallah sukaso a tuhumi Yoohan tun a asibiti game da zancen Nu'aymah baba malam ya hana, hakama su Abba basu bada goyon baya ba.
      Zuwa yanzu dai Yoohan ya fahimci alaƙar baba malam da patient ɗinsa. Ya kuma gane Nu'aymah. Sai dai taka maimai abinda bai gama fahimta ba shine hotunan da Abdallah ya kawo masa da tsantsar ɓacin ran da yake ganni tattare da samarin gidan su baba malam ɗin gaba ɗaya harsu malam ƙarami da ya fara sabo da su.  

        Bayan samun damar shiga ɗakin da Nu'aymah ke kwance da sukayi ɗai-ɗai suka dubata duk da bata farfaɗo ba baba malam ya tattarasu su duka suka bar asibitin. Dan Yoohan ya tabbatar musu ba'a buƙatar wani mai jiyya tattare da ita har sai ta farfaɗo.
      Suna tafiya baifi da mintuna talatinba shima ya amshi key ɗin motar Dr Mubarak Solo ya jashi zuwa gidansu baba malan ɗin. Kamar yanda yay tsammani ya iske kowa a gida da alama ma zaman jiransa sukeyi. Omar ne ya fito yay masa iso har sashen Hajjo. Hajjo ce kawai a sashen sai su baba malam su duka. Omar ma yana shiga da shi fitowa yayi.
      Duk da Hajjo najin haushin Yoohan sai ta danne ta amshesa da fara'a kamar ranar salla dasu Ahmad suka shigo da shi wajenta. Ta kuma kawo masa ruwa da lemo. Yaji daɗi kuwa sosai, tare da sake jin ƙaunar ƴar tsohuwar har cikin ransa.
     Bai iya sakin jiki ya sha ruwan yanda ya kamata ba, ya ajiye kofin tare da sake nutsuwa yana jiran ji daga garesu. 
     Bayan shuɗewar shiru na wasu mintuna Abba Musbahu yay gyaran murya idonsa akan Yoohan da kansa ke a rissine. Ba bu wani kwalo-kwalo ya shiga zayyano masa duk abinda ke faruwa.
            Sosai mamaki ya kusa kashe Yoohan, ya sake tsuke fuska yana girgiza kansa. Idanunsa da suka kaɗa sukai jajur ya ɗago ya duba baba malam, “Uncle ni a rayuwar turai da nayi ma ba taɓa aikata haka da wata mace da yardarta ba ma balle anan ƙasata. Nasan anyi hakane kawai don shiga tsakanin alaƙarmu, ko kuma kasancewata musulmi a yanzu. Sai dai kuma ko wanene bai samu nasara ba, dan babu wani ɓatanci da za'aimin koda yafi wannan da zai girgiza zuciyata daga barin bautama UBANGIJINA shi kaɗai. Ban musulinta domin kowa ba, ba kuma zan fita domin wani ba. Nasan zaku yarda da ni, Tunda har kuka yarda da dani alokacin da ba addininmu ɗaya ba ma, dan kuɗin nagartattun mutanene masu ƙyawawan zukata. Zan faɗa muku ainahin gaskiyar abinda ya faru”. Cikin nutsuwa da ɗacin rai ya bayyana musu tun daga haɗuwarsa da Nu'aymah ta farko har zuwa ranar da ya musulinta. Bai iya ƙarya ba tun yana kafirinsa, balle yanzun da ya ƙara sanin muhimmancin gaskiya a harshen ɗan adam. dan haka ko kissing ɗin Nu'aymah da yayi bai ɓoye musu ba ya faɗa. Ya ɗora da faɗin, “Zan koma asibiti yanzun insha ALLAH, na muku alƙawarin bincike akan cikin da akace itama ya zuba a jikinta, dan sam ni dai banga wannan matsalar tattare da itaba saboda ba akanta na fuskanci matsalarta ba. Amma zan kawo muku hujja a yanzu da yardar ALLAH”.
      Gaba ɗaya sun gamsu da bayaninsa har Hajjo da Abba Musbahu ke fassarama maganar Yoohan ɗin dan da turanci yay bayaninsa.
       Baba malam ya ɗanji nauyin zuciyarsa ya ragu sosai da bayanin Yoohan, a yanzu kuma hankalinsa ma yafi kwanciya da binciken Yoohan ɗin fiye da na likitocin farko. Sannan tunaninsa ya fara karkata akan wani abu da ban kuma.
    Ko mintuna goma Yoohan bai ƙara a gidanba ya fice ya koma asibiti. Sam baiji zafin su baba malam ba akan wannan maganar. Sun ƙarama mutunci a idanunsa ne, haka yake son iyaye su kasance akan ƴaƴansu. Ya sake fahimtar addinin musulinci addinine abin koyi, domin yana ƙyamatar abinda wasu addinan su a wajensu ado ne, Wayewace. Hasalima zuciyarsa wani hasashe take masa daban akan wannan ƙullin da akai musu. Duk da bai tabbatar ba amma zuciyarsa na kinsa masa papa.

           Tare suka koma asibiti da su Abdallah da har yanzu su dai basu wani gamsu da Yoohan ɗinba. 
     Shi da Doctor Aysha suka gudanar da duk wani bincike akan Nu'aymah da har yanzun tana cikin halin sumar allurar da sukai mata. Dr Aysha ta tattara komai zuwa lab ta danƙama wanda ta aminta da shi. Daga haka ta dawo ta sanarma Yoohan.
     Kansa kawai ya iya ɗaga mata, dan yana lafe jikin kujerarsa ne idanunsa a lumshe. Fuskar nan tasa kuwa a tsuke take matuƙa. yana cigaba da nazarin komai dalla-dalla. Babu abinda ya iya taɓukawa a wannan yinin sai zuwa salla idan lokaci yayi da leƙa Nu'aymah da suke tsumayen farfaɗo warta a kowane irin lokaci.
       Misalin ƙarfe biyar saura na yamma Dr Aysha ta kawo masa duk results ɗin bincikensu. Ko buɗewa baiyi anan ba ya miƙe da shi ya fito, su Abdallah da suka zame masa bodyguard shi da Nasir da Ahmad biye da shi. 
      Har zuwa yanzun su baba malam duk suna gida suna jiransu. Yanzun dai saɓanin ɗazun, duk mazan gidan ne suka taru banda ƴammatan da yaran da su Umm, dan hajjo ce kaɗai mace ma a cikinsu. A maimakon Yoohan ya buɗe yanzun ma sai ya bama Abdallah damar buɗewa dan ya tabbatar musu zai gane.
            Tun a result ɗin farko Yoohan yaji saɓanin abinda yay tsammani. Hakama sauran ƴan gidan, aka tafi na biyu dana uku, Abdallah baima ƙarasa na ukun ba Yoohan ya miƙa hannu a hankali ya zare file ɗin da takardun results ɗin ke a ciki yana binsu ɗai-ɗai da kallo. Tabbas babu ƙarya dai-dai Abdallah ke faɗa. Dan kuwa duk Results ɗin sun nuna Nu'aymah tasan ɗa namiji, ta kuma ɗauki cikin sati shida da wasu kwanaki, cikin kuma tayi ɓarinsa kwana biyu kenan.
      Dimmm kan Yoohan yayi na ɗan wani lokaci, sai kuma ya sake duba duka takardun sannu a hankali. Su baba malam dai babu wanda yay magana sunata binsa da kallo. Sai Abdallah ne da Naseer ke jifansa da wani mummunan kallo tamkar zasu hau kansa da duka.
       A harzuƙe Abdallah yace, “Yanzu kuma wace ƙarya zakai mana dan ka kare kanka?”. Yay maganar yana riƙo rigar Yoohan.
        “Abdallah!!!!” Abbansa ya daka masa tsawa yana miƙewa. Ransa a ƙololuwar ɓace yace, “Sake sa”.
        Kamar Yah Ab ya kashe Yoohan haka yakeji, amma kasancewar an musu tarbiyyar jin maganar magabatansu sai ya saki Yoohan ɗin da shi sam hankalinsa ma bawai yana tare da su baneba. Dan gaba ɗaya zuciyarsa ta shige a wani sabon nazari ne. Ɗan hankaɗashin da Abdallah yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ɗagowar da zaiyi sai idanunsa suka sauka jikin Windown falon hajjo. Inuwar mutum ya gani, yay ma wajen kallon kusan seconds goma kafin wanda ke a tsaye ya farga ana kallonsa yay saurin barin wajen.  A take kan Yoohan ya kawo masa wuta kasancewarsa mutum mai kaifin tunani da basira.
      Kallon sashen da baba malam yake yayi, ya ɗanyi luuuu da idanunsa da haskensu ya ɗan sirka yana wani bahagon murmushi, kamar zai lumshe su sai kuma ya ɓuɗesu a hankali. Cikin muryarnan tasa mai kauri da amo data hadu da ɓacin rai a yanzun yace, “Uncle wannan tatsuniyar akwai marubucinta kusa da mu daf. Amma mizai hana ka bani damar yankar ticket ɗin fara game da shi? Dan ni bana wasa a saman ruwa tunda ba masinci bane. Nafi yarda da shiga ƙarƙashin ruwan kasancewata mai yawan bincike akan ma'adanai. Kasan masu iya magana kance idan ka hango biri bisa tsumagiyar reshe ba gangancine ya kaisa ba, tsabar ƙwarewa ce a iya hawan bisa. Ko zaka amince ka bani aurenta idan ta girma?”.
         Kowa a falon sai da ya zaro idanu waje, harma da masu zabura. Nasir da Ya Ab kam ai dingangan suka tsaya akan ƙafafunsu tare da hassalowa lokaci guda kamar zasu haɗiye Yoohan da ko kallo basu ishesaba. Sai dai kafin su ƙarasa Abban Adawiya ya daka musu tsawa. Tilas suka ja burki badan rayukansu sunso hakanba.
         A karon farko baba malam yay tattausan Murmushin da har haƙwaransa sai da suka bayyana. idanunsa ƙyam akan Yoohan. zamansa ya gyara da ƙyau yabi duk jama'ar falon da kallo, su Abban Adawiya ma duk murmushin sukeyi, hadda hajjo da malam ƙarami ke fassarama maganar yoohan ɗin. 
          Murmushi baba malam ya sakeyi a karo na biyu, kafin yace, “Yoohan maganar aure ba abin wasa bace a musulinci, dan haka bazan iya baka amsar bukatarka a yanzun kai tsaye ba. Amma kaje zanyi magana da ƴan uwana, duk hukuncin da muka yanke zamu sanar maka insha ALLAHU”.
         Duk da Yoohan yaso samun amsar baba malam take a wajen sai kawai ya jinjina masa kai alamar ya amince da hakan. dan haka ya miƙe yay musu sallama ya fice abinsa yana jifan Naser da Abdallah da wani irin kallon na ban ƙyaleku ba kuma, kamar yanda suma suke binsa da kallon kishi da tsana.

       A yanzun kam zamu iya cewa komai ya harmutse musamman a gidan su Nu'aymah. Dan tun bayan barin Yoohan gidan baba malam ya kasa zaune ya kasa tsaye da fashin baƙi akan kalaman yaron mai hikima. Kai kawo kawai yake a bedroom ɗinsa tamkar mai safa da marwa. Hakama Abdallah da Naser hankalinsu a matuƙar tashe yake, dan su dukansu suna tsananin son Nu'aymah har cikin ransu. Umm kam da hajjo bama a maganar halin da suka tsinci kansu a ciki. Umm ba maganar wa Nu'aymah ya kamata ta aura bane damuwarta. Abinda likitocin keta tabbatarwa ga ɗiyarta shine tashin hankalinta. Itace ta haifi Nu'aymah, itace tai mata tarbiyya, sannan a gabanta ta tashi har zuwa yanzu da ake akan rikicin. Tunda take da yarinyarta bata taɓa kamata da kuskuren sauka akan turbar tarbiyyar data ɗorata ba. To tayaya za'ace hakan ta faru?  Kanta ya kulle gaba ɗaya, tama rasa wazata gaskta tsakanin likitoci da Nu'aymah. Dan zuciyarta taƙi aminta ƴarta zata aikata haka, to sukuma likitocin mizaisa su musu ƙarya? Ta yama zasu musu ƙarya bayan sun kasance daban-daban?.

        A ɓangaren Yoohan kam yana fita yaci karo da Solomon. Bai wani zaman tunanin yanda akai ya biyisaba ko inda ya samo motar da yazo ɗaukarsa kawai ya shiga kusa da mazaunin driver. 
       A tsorace Solomon ya dubesa, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. saurin zagayawa yay mazaunin driver ya tada motar suka bar anguwar. Har suka isa hotel babu wanda yace uffan a tsakaninsu. Solo yay masa rakkiya har ɗakin da ya kama masa. Yana ganin ya shiga shi kuma ya koma da baya. Wayarsa ya zaro yay kiran papa. Bugu biyu kuwa Papa ya ɗaga saboda muhimmancin da Solo yake da shi a wajensa. Cikin girmamawa ya gaishe da shi, kafin suyi magana mai tsajo wadda bilyn ku bataji saboda da yare Solo ke magana. Sun kusa mintuna talatin sannan Solomon ya yanke wayar yana wani cizon lips da yin ƙwafa.

          Ƙarar waya ce ta saka Yoohan dake zube saman gado idanu a lumshe ko takalmi bai cire ba buɗe idanunsa. Kasancewar ring ɗin daya sakama iyayensa da banne yasa ya fahimci papa ne. Sai da wayar ta kusa katsewa sannan ya ɗaga. Ya saka a kunne batare da yayi maganaba.
       Daga can Papa yace, “Yoohan kana lafiya?”. “Uhhm!” Yoohan ya amsa a taƙaice. Papa da keta ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Ni bansan lokaci daka fara zama maƙaryaci ba. Ni nasan dagajin muryarka akwai matsala ai, dan an kirani daga asibitinku an sanarmin duk abinda ke faruwa”. Kamar Yoohan zaiyi magana sai kuma yay shiru abinsa yana sake tsuke fuska. Takaici ya kuma kume papa, yace, “John kana jina kuwa?”. Yanzunma kamar bazai amsa ba, sai kuma ya nisa muryarsa a harɗe yace, “Papa inason nayi aure! Kuma ɗiyar Sheikh Sooraj Hashim jibiya zan aura, sai dai yarinyar ta cika ƙankanta”.
      Wani irin bugawa ƙirjin Papa yayi a lokaci guda. Tamkar wanda aka ƙwaɗama guduma a saman kai ya miƙe zumbur da faɗin, “What?!. John! Are you Mad?!!”. Yanda papan yay maganar da tsananin tsawa ne ya saka Yoohan janye wayar daga jikin kunnensa yana matse idanu tam-tam. Sai kuma kawai ya yanke wayar yay wurgi da ita ta tarwatse ƙasa kamar wani zararre. Harya ɗan zabura zai miƙe sai kuma ya koma baya ya sake zubewa a gadon yana ambaton addu'ar da Manager Hamza Ibrahim da a yanzu suka sake zama abokai sosai ya koya masa. Ita ya shiga maimaitawa a cikin ransa. Cikin amincin UBANGIJI a hankali yaji ƙirjinsa ya fara rage nauyi, sai kuma wani irin barci ya fara fisgarsa a hankali.

        Gaba ɗaya papa ya haukace a gaban abokansa da ƙanninsa. Dan suna a tare lokacin wajen wani meeting ɗinsu na manyan ƙauyensu, dan dama yaje ƙauyensu ɗinne tun jiya da daddare saboda meeting ɗin mai muhimmanci ne suka shirya yi.
     Uncle Godwin ne ya kama hannunsa ya zaunar da shi yana faɗin, “Hah Friend. Please calm dawn ”. 
            Papa ya furzar da wani zazzafan huci jikinsa na wani irin tsuma, ya doka sandar hannunsa a ƙasa yana cizar lip ɗinsa na ƙasa da masifar ƙarfi. Da turanci yace, “Tayaya kake tunanin hankalina zai kwanta Godwin? Ko nauyin faɗamin Yoohan baijiba wai zai auri ƴar arewa, ɗiyar hausawa masu sallah?”.
         Da sauri Uncle Mike yace, “Ah!Goshpower wani lokacin kana abu kamar ƙwaƙwalwarka baya aiki da kyau. kai nefa ka sanar min yaron nan ya sanar maka yana da manufa akan duk abinda ya keyi. Mizai hana ka amince masa ya aureta ɗin. Muma wata damace tazo hannunmu akan mahaifinta.....”
     A fusace papa yace, “Sai kuma akace muku da ɗana kawai zamu iya samun wannan damar? Salon suje su maidashi mai salla, to ni......”
     Saurin ɗaga masa hannu wani da suke kira Chief yayi da sauri. Ya juya maganarsa zuwa yarensu da ayanzuma bilynku bataji ba😪. Magana ya farayi kamar zai haɗiye harshenshi cikin maida gaba ɗaya hankalinsa ga papa. A mamakina kuwa sai naga gaba ɗaya papa ya nutsu yana saurarensa tamkar ƴan uwansa. A hankali na ga fushin papa ya fara sauka daga fuskarsa. Saima ya koma sakin wani mugun murmushi yana gyaɗa kai. Kafin ya miƙe cike da wani irin farin ciki ya rungume Chief ɗin. Suma sauran duk tsantsar farin cikinne ya bayyana a fuskokinsu. Da alama dai shawarar Chief ta zauna da ƙyau a zukatansu.
     Tashi papa yay ya shiga neman Number Yoohan. Sai dai kusan kira goma bata shigaba. Canja akalar kiran yay ga Solomon.
        Yoohan na kwance har yanzu a gadon Solomon yay knocking. Bai motsaba balle ya amsa masa. Shikuma Solo jin yayi har kusan sau huɗu babu amsa sai kawai ya tura ƙofar ya shigo. Ƙarasawa yay inda Yoohan ɗin ke kwance cike da tsoro da girmamawa yace, “Am sorry sir. Boss ne yace na baka waya”. Kamar Yoohan bazai tankaba ya watsar da shi. sai kuma zuwa can ya miƙa masa hannu alamar ya basa wayar. Yana bashi ya fice abinsa. Yoohan ya ɗora wayar a kunne batare da yayi magana ba.
     Cikin sanyin murya papa daga can yace, “I am so sorry my son. Raina ne kawai ya ɓaci dan ina tsoron su canja min kai su cuceni. Amma kuma sai nayi tunani da sake tuna bayanin da kaimin kwanaki sai na fahimci kaima ba ƙaramin abune mai muhimmanci zai saka yin hakan ba. yanzu yaya kaso ayi to?”.
        A karon farko Yoohan yayi wani munafukin murmushi ya kai hannu ya shafi sumar kansa har zuwa sajensa. Idanunsa ya buɗe a hankali ya sauke bisa frame ɗin da akai adon ɗakin hotel ɗin da shi. Magana ya farama papan nasa da yare cikin taushin murya. 

To su dinɗin dinkum balkisu saina koma gehe kawai ina zare idanu dan anzo dai-dai wajen. Turancinma da yaya nake haɗosa nake masa fassara🙄😜🚶🏻.

       Papa da Yoohan sun ɗauki lokaci mai tsaho suna waya. Dan har sai da na ƙosa kafin su kammala. Yanda naga Yoohan ɗin ya ɗan rage buyagin nasa ne ya sakani fahimtar maybe har sun gama tsara wani abune. 

★★★★★
   

          Kusan ƙarfe tara na dare Nu'aymah ta farfaɗo. Dr Sa'ad dake tare da ita dan duty ɗin dare ne da shi yay azamar kiran Dr Yoohan da har yanzu yana a hotel ɗin bai kuma waiwayar asibitin ba.
      Cikin kuwa mintuna ƙalilan ya shigo asibitin. Tsabar yanda ransa ke a jagule sai ya toshe idanu da baƙin Glasses da yay masifar sake fiddo masa ƙyawun fuskarsa da kwarjinin hasken musilinci dake mamaye da shi. Tunda ya shigo asibitin baiyi magana da kowa ba. Ko gaidashi da Nurses suke da sauran ma'aikatan  hannu kawai ya dinga ɗaga musu kansa a ƙasa ya rufe rabin fuskar da p-cap bayan glasess ɗin. Shi dai Solomon na biye da shi kamar jela.
       Ɗakin da Nu'aymah ke a kwance ya tura a hankali ya shiga da sallama ƙasa-ƙasa. Dr Sa'ad da Nurses guda biyu dake a tare da shi suka amsa suna ɗagowa. Da girmamawa Nurses ɗin suka risina suna gaishesa. Batare da ya amsa musu ba suma ɗin ya ɗaga musu hannu kawai. Kafin ya miƙama Dr Sa'ad hannun sukayi musabaha shi kuma. 
          A hankali ya juya kansa zuwa ga sashen da kan Nu'aymah ya ke. Ya ɗan ranƙwafa kanta ƙaɗan ya janye wani igiyan na'uran dake a gefen kanta gab da kunne. 
      Yanda ƙamshin turarensa ya buga mata hancine ya saka ƙirjinta harbawa. Buɗe idanun nata tayi da ƙyar saboda bala'in nauyin ciwo da sukai mata. Dai-dai Dr Yoohan ya dubeta shima yana ƙoƙarin zare glasess ɗin idonsa. Kallon ido cikin ido sukaima juna, duk da ita ɗin dishi-dishi take ganinsa hakan baisa ta gagara ganesa ba.
           Wani irin juyawa kanta ke mata, daga ciki tanaji kamar ana karta mata ƙarfe, zabura tayi, ta yunƙura zata tashi Sai kuma tai saurin dafe kan nata tace, ‘Aushhh kaina!’.
         Yoohan da shima zuciyar tasa ke wani irin harbawa, da sauri ya wani ɗauke idanunsa daga kanta cike da basarwa, tamkar bai fahimci halin da take a ciki ba. 
      Yanda jikinta ke wani irin ɗan karkarwa ga kanta data riƙe da duka hannayenta tana jujjuyawa ya saka Nurses ɗin nufarta da sauri tare da Dr Sa'ad. Yoohan dai na tsaye baiko motsaba. Sai dai yana kallonsu ne ta ƙasan ido. Yanda duk sukaso Nu'aymah ta nutsu hakan ya gagara, dan ganin Yoohan ɗin ya sake dawo mata da komai cikin memory ɗinta, wanda hakan ke mata barazana cikin kanta tamjar ƙwanyarta zata tarwatse.
        “Ku barta” ya faɗa a hankali tamkar ba shine yay maganar ba. Baya Nurses ɗin suka ja domin cika umarninsa, amma tausayin Nu'aymah fal ransu. Dr Sa'ad kam sai ƙoƙarin son riƙo hannun Nu'aymah data riƙe kanta da shi gam ya keyi. A bazata yaji an riƙe masa hannun lokacin da yake gab da ɗorasa saman nata..............✍



Ni dai nace ‘Hummm’.😶 inji mai tsoron gulma.


__________________________
ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


BARKA DA JUMA'A


No. 39

.............Ba Dr Sa'ad ba hatta Nurses ɗin da Dr Aysha dake ƙoƙarin shigowa da drip a hannu sai da suka kalli Dr Yoohan ɗin. Amma a mamakinsu ya fiske abinsa tare da sake tsuke fuska tamkar ba shine ya aikata ba. Sai tura tattausan nasa hannun yay ƙarƙashin kan Nu'aymah da dogon gashinta ke a tsefe duk ya baje a saman filon.
     Da sauri ta sake buɗe idanunta, dan kusancin da suka samu gaba ɗayansu neman haifar da barazana yake a bugun Zucikatan su, cikin rawar jikinta daya ƙaru ta sake buɗe baki zatai magana, sai dai kuma hakan kamar da wuya a gareta. Dan saɓanin yin maganar sai hawaye sharrrr!! Suka fara bin kumatunta. Yanda damshin ruwan hawayen nata suka sauka bisa fatar hannunsa ne ya sakashi lumshe idanu yana wani jan numfashi da sassarfa. Sai kuma a hankali ya janye hannun nasa daga cikin kanta dama jikinta gaba ɗaya ya ɗan matsa baya kozaiji sauƙin yamutsawar da dukan gaɓɓan jikinsa ke masa.
        Da sauri Dr Aysha tace, “Doctor akwai matsala ne?”.
    Shiru mai amsa mata ba. Sai idanu da ya zubama Nu'aymah da jikinta ke vibration a hankali, har zuwa yanzun kuma riƙe take da kan nata da duka hannayenta tana ɗan mirginashi bisa filon. Kusan mintuna biyu yana kallon nata, kamar yanda su Doctor Aysha ke kallonsa a tsorace, kafin ya ɗauka file ɗin Nu'aymah yaja da baya daga gaban gadon. jikin Window ya koma tamkar halin da take ciki bai damesaba. Ya shiga buɗe shafukan takardun dake a ciki file ɗin  yana bin rubutun ciki daki-daki da nazari a nutse.
       Su Dr Sa'ad kam duk sun rikice, sai dai sun kasa fahimtar wane taimako ya dace su bata ne. Dawowar da yay gaban gadon riƙe da file ɗinne ya sakasu zuba masa idanu su duka. Ya ajiye file ɗin a saman drawer'n gefen gadon da take sannan yay magana a ɗan kausashe yana kallon Aymah. “Malama ki nutsu”.
       Ai maganar tasa tamkar zuga Aymah ma ma tayi, dan gani kawai sukai tayi wani irin masifar zabura zata miƙe. Cikin sassarfa Dr Aysha ta ƙaraso ta tareta. Da ƙyar ta iya dannata saman gadon ta kwantar, duk da hakan kuma fisge-fisge takeyi har yanzun. Batare da Yoohan ya ƙara magana ba ya matsa jikin makunnar wutar ɗakin ya kashe. a take duhu ya mamaye ko ina. Wata razananniyar ƙara da ta amsa duka Word ɗin Nu'aymah ta ƙwalla. Duk firgita su Dr Aysha sukayi, dan haka suka shiga lalube a cikin duhu kowa na neman wajen ɓuya. Shiko yana tsaye ko gezau, duk da kuwa ƙarar tata jiyay tamkar zata tarwatse masa kayan cikin kansa. Lumshe idanu yayi ya buɗe a hankali sannan ya kunna wutar. Baiko kalli inda su Dr Sa'ad suka maƙalƙale ba ya taka zuwa ga Nu'aymah dake yashe a ƙasa alamar faɗowa tayi ƙasa.
      Duƙawa yay yasa hannu biyu ya ɗauketa cak ya maida saman gadon, a kallo ɗaya zaka fahimci batama yin numfashi. Sai da yaja bargo ya lulluɓa mata sannan ya maida mata duka na'urorin da ke manne da kanta ɗazun. Juyawa yay yayima su Dr Aysha alamar su fita. Suna gaba yana biye dasu riƙe da file ɗin Nu'aymah.

★★★★★

            Tun barin Yoohan gidan su Nu'aymah babu wanda ya sake samun nutsuwa. Musamman ma Naseer da Abdallah. Dan furicin Yoohan akan Aymah ba ƙaramin girgiza musu zukata yayi ba.
        A yanzu hakama Naser ne zaune can bayan sashen samarin gidan. Waya ce mane a kunnesa alamar magana yake da wani. Muryarsa cike da rauni yace, “Ananah wlhy ina sonta, dan ALLAH karku bari wannan karon na rasata. A wancan karonma na haƙura ne saboda duk kun goyama Abdallah baya. Ni kuma banason abinda zai kawo rikici a cikin zuminci ta dalilina. Amma a yanzu wlhy babu abinda zai sakani na janye, dan ALLAH kizo kano, nasan Hajjo duk abinda kikace zatayi, dan kece ke sakata tayi abu koda bataso matsayinki na babbar yayarta”.
      Shiru ya ɗanyi yana sauraren abinda take cewa daga can. Sai kuma naga ya saki lallausan murmushin daya sake ƙawata ƙyawun fuskarsa ta jinin katsinawa, ya kai hannu ya shafi kwantaccen sajensa da faɗin, “Na gode sosai Ananah, furucinki ya koremin dukkan damuwata da tashin hankali, wlhy ba cikiba ko ƴaƴa goma Zainab ta haifa ina sonta a hakanta, kema kuma shaida ce akan hakan Ananah”. Ya sake jim na saurare sannan yace, “To nagode sosai, sai kun iso”. Daga haka ya yanke wayar yana sake faɗaɗa fuskarsa da murmushi. Yanaji a ransa insha ALLAHU a wannan karon ya gama mallakar farin cikin rayuwarsa Nu'aymah ya gama, musalta irin son da yakema yarinyar ɓata bakine, amma wlhy ko rantsuwa yay babu kaffara a cikinta yafi Abdallah son Nu'aymah.

(To masu karatu kun yarda😉😂?).

            A can sashen su Abdallah kuwa Abdallah ne zaune a gaban Momy a karo na farko tun dawowarsa gidan, dan daya gaisheta baya ƙara ko minti ɗaya yake barin wajen. Tun tana damuwa da hakan harta zuba masa ido kawai da kaima UBANGIJI kukanta. A yau kan tun bayan watsewar kowa daga falon hajjo bai zame ko inaba sai sashen iyayen nasa. Momy na zaune a bedroom ya sameta. Ganinsa kawai tai a gabanta ya ɗora kansa bisa cinyarta yana hawaye.
     Cikin tsoro da mamaki tace, “Abdallah lafiya kuwa?”. Da muryar kuka yace, “Momy wannna karonma zasu rabani da ita. Wlhy ina sonta, dan ALLAH karki bari su rabamu, itama tana sona Momy”. “Ikon ALLAH Nu'aymahr dai?”. Da sauri ya gyaɗa mata kansa, kafin ya shiga bata labarin duk abinda ya faru yanzu a falon hajjo.
      Cike da al'ajabi Momy tace, “Nikam wannan lamari da ɗaure kai, har raina zuciyata ta kasa aminta da zancen likitocin nan akan Nu'aymah. To amma yanda duk bakin nasu yake zuwa ɗaya ne zai sakama kowa ruɗani, sannan shi kuma yaron yanzun yazo da batun cewa zai aureta. Kodai....? Kai ina ba haka bane, hakanma bazata taɓa faruwa ba”. Ta ƙarasa faɗa tana girgiza kanta.
     Abdallah yace, “Momy wlhy koma hakan gaskiyane ni inasonta a hakanta, ƙilama fyaɗe yay mata”. Murmushi Momy tayi a karon farko, tace, “Humm Abdallah zuciyata na hasashen abubuwa da yawa a gidan nan, sai dai bazan furtaba har sai zargina da zatona sun zama gaskiya a idanun kowa”.
       “Momy kamar ya?”. Abdallah ya faɗa da sauri yana kallonta. Kanta ta girgiza masa. “No, bazaka ganeba share kawai. Yanzu kai da kake batun auren Nu'aymah su Adawiya daka yima aika-aika fa? Kasan kowa a gidan nan ciki yake da kai harni wlhy. Abinda ya hana ace maka komai wannan tashin hankalinne kawai. Abdallah kodai ka fara shaye-shaye ne bamu sani ba?”.
        “Momy shaye-shaye kuma? Ni ban fara shaye-shaye ba wlhy. Kawai dai na rushe katangar da sukace itace zata hanani mallakar burina ne, kema kin sani momy Nu'aymah farin ciki nace, da sonta na fara sanin kaina, tayaya lokaci ɗaya za'ace za'a ruguzashi. Itama tana sona. Batason a rabamu”.
        “Nasan duk haka Abdallah, shawarar da zan baka kawai kabi komai a hankali, ka kuma saka a ranka wani ramin rijiyar yafi gaban tsallakawa saboda faɗin baki, a kuskure kaɗan zaka iya afkawa ciki ka halaka. Zan tayaka da Addu'a, insha ALLAH kai da Nu'aymah sai kunyi farin ciki. Daga ni har mahaifinka kuma sai inda ƙarfinmu ya ƙare wajen ganin ka mallaki Nu'aymah a wannan karon kodan samun farin cikinku kai da ita”.
        Sosai yaji daɗin kalaman mahaifiyar tasa. Yay mata godiya sannna ya fice daga sashen cike da ƙwarin gwiwa.

________★★★________

           Baba malam na zaune a falonsa hannunsa riƙe da Littafin gawurtaccen barubucin malamin addinin nan Sheikh: Salihu bn Fauzan bin Abdallahil Fauzan yana dubawa, sai dai sam hankalinsa bama ya tare da fahimtar abinda littafin ya ƙunsa. Karantawa kawai ya keyi. Kiran da akaima wayarsa ne a karo na biyu ya saka Umm dake kwance cikin kujera idanunta a rufe an cire mata drip ɗin da aka saka mata kallonsa. Ganin sam bama yajin kiran wayar ya sakata miƙewa a hankali zaune. Hannu ta miƙa ta taɓashi.
     Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke da juyowa ya kalleta da sauri, sai kuma ya maida ga wayarsa data nuna masa da hannu. Sake sauke numfashin yayi, ya gyarama Muhammad dake kwance jikinsa yayi barci kwanciya, sannan ya ɗauka wayar dai-dai ta tsinke. Ganin wanda yay kiranne ya sakashi kiransa babu jinkiri. Sai dai kuma bai ɗaga ba harta tsinke shima, tana tsinkewa kiransa ya sake shigowa wayar baba malam ɗin. A karon farko baba malam yay ɗan murmushi, wannan ɗabi'ar Yoohan ce, baya taɓa yarda baba malam ya kirashi sai dai shi ya kira. Koda kuwa baba malam ne ya fara kiransa zai bari har sai ta katse sannan shi ya kirasa.
     Kamar yanda ya saba cike da ladabi yayma baba malam cikkakkiyar sallama da harshensa da baya fita da kyau. Baba malam ya amsa masa da kulawa tamkar yanda ya saba, bazaka taɓa cewa wani abu ya faru tsakaninsu ba. Gyara zama sosai Yoohan ya sakeyi a kujerar office ɗinsa kafin ya farama baba malam ɗin bayani a nutse.
         “Uncle Alhmdllh patient ɗin ta farfaɗo, sai dai kuma.......” Sai yay shiru kuma. Cike da dauriya da kawaici irin na baba malam yace, “Yahya! Sai dai me? Karkaji komai kai min bayani akan duk halin da Nu'aymah take, domin UBANGIJIN daya jarabceta a wannan yanayin ya fimu sanin dalilin hakan, ita rayuwa da ƙaddara duk suna cikin kundin jarabawa ne, mai ƙarfin imani da ƙwaɗayin rahama ne kuma kawai ke iya juriyar cinyesu komai tsanani da zafin da sukazo masa da shi. UBANGIJI ya fimu sonta ai, bai kumayi shawara damu ba sanda ya bamu, idan ya ƙarɓeta a yanzu sai dai mu gode masa da ni'imar da yay mana na samunta tsawon shekaru sha bakwai a gabanmu. Dan haka faɗamin kawai”.
       Baki Yoohan ya cika da iska ya fesar, zuciyarsa da ruhinsa na ƙarajin ƙauna da son baba malam har cikin jini. A komai nasa yana fatan yin koyi da baba malam. Cikin harshen turanci yace, “Uncle tanama da ranta, sai dai dama bawai mun mata aikin ainahin matsalarta bane kamar yanda nai maka bayani ɗazun kafin mu taɓata. Aikin da mukai mata zai bata taimakone kawai wajen hana ƙwaƙwalwarta goge komai da take barazanar yi, sannan zai sassauta mata raɗaɗin da takeji a duk lokacin da matsalar ta motsa, insha ALLAHU zai hana ta iya rasa hankalinta. Nayi tunanin aikin zai bata kariyar da zamu iya ɗaukar kamar watanni biyar kafin ai mata aikin gaba ɗaya, dan dole sai an fita da ita waje, a ƙasarnan bamu da isassun kayan aikin matsalarta, koma muna dasu zaka samu bana zamani bane tunda shuwagabannin namu bawai hankalinsu nakan abinda ya dace suyi bane. To a yanzu dai matsalar dana fahimta dolene ai gaggawar yimata aikin koda nan da wata ɗaya ne insha ALLAH, inba hakaba zata iya loosing memory ɗinta a koda yaushe”.
     Ɗan rumtse idanu baba malam yay yana ambaton sunayen ALLAH, muryarsa da ƙoƙarin jarumta yace, “Shikenan Yahya, duk yanda kake ganin ya kamata akai kayi tunda aikinka ne, yanzu zamu iya zuwa mu ganta?”.
       Ɗan jimm Yoohan yayi, kafin yace, “Eh to amma karkuzo da yawa dai”. “Babu damuwa”. Baba malam ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya.

         Batare da kowa ya saniba a gidan Umm da baba malam da Hajjo suka tafi asibiti duba Nu'aymah. Yoohan da yake wani irin jin kunyarsu da nauyinsu ne yay musu rakkiya har ɗakin da Nu'aymah ke kwance. Ba ƙaramin tashi hankalinsu yayiba ganin yanda aka jajjone kan Aymah da na'urori, Hajjo da Umm harda hawayensu. Basu wani jimaba suka fito. Office ɗin Yoohan suka sake komawa. Inda ya sake musu bayanin komai dalla-dalla a nutse. Sosai suka gamsu da bayaninsa, wanda a take duk murmushi ya baibaiye fuskokinsu, suka shiga saka masa albarka da jera masa addu'oin fatan alkairi. Har wajen mota ya rakosu, sai da yaga tafiyarsu sannan ya koma ciki, dan yau a asibitin zai sake kwana saboda Nu'aymah zata iya farkowa a kowane irin lokaci.
            Zamansa babu jimawa Solomon ya shigo ɗakin ɗauke da takeaway da yayo masa acan hotel ɗin da suke sauka. Dan idan yazo kano abincin can kawai yake ci, sai ko yanzu da suka haɗu da su baba malam. Ganin yana waya ya saka Solomon komawa gefe ya tsaya yana sauraren yanda Yoohan ɗin ke wayar a nutse.
        Magana suke da wani likita abokinsa dake a ƙasar Canada. Yana buƙatar a aiko masa da wasu allurai ne masu matuƙar tsada da zaima Nu'aymah amfani da su. Kuma yana buƙatar sune da gaggawa daga nan zuwa yammacin gobe idan ALLAH ya kaimu. Shine suke maganar ta yanda za'a kaisu airport ɗin ƙasar a damƙawa wani abokinsa matuƙin jirgi da Yoohan ɗin yasan kayan zasu iso yanda yake fata. Sai da suka kammala maganarsu har Yoohan ɗin yayma Dr Androi transfer ɗin kuɗaɗen allurar take anan masu yawa daga asusunsa sannan ya ajiye wayar.
               Solomon dake kallonsa cike da takaici da mamakin ganin kuɗin daya biya na alluran tamkar baisan ciwonsu ba yay saurin faɗin, “Good evening sir! Ga abinci na amso maka, naga bakaci komaiba tun breakfast ɗin safe”.
     Ɗan luuuu da idanu Yoohan dake miƙewa yayi, kamar zai lumshesu sai kuma ya buɗe su akan Solomon ɗin. “Karka damu banajin yunwa. Haɗamin coffee kawai is ok for me”.
     Ganin yanda ya tsuke fuska sosai ya saka Solo amsa masa da “To” kawai. Cikin bin umarni yayi masa yanda ya buƙata, acan rukunin kujerun office ɗin daya koma yana aiki a lap-top yaje ya kai masa coffee ɗin. A hankali yace, “Thanks”. Shiru office ɗin yayi na wasu mintuna, Yoohan nata aikinsa da shan coffee kamar ya manta da Solomon. Sai kuma ya ajiye kofin ya ɗago yana kallon solo ɗin. “Kaje ka kwanta, basai kazo nan da safe ba, inaga zuwa dare zamu wuce Abuja, sai ka mana booking ɗin jirgi”.
         Cike da girmamawa yace, “Okay sir”. Daga haka yay masa sallama ya fice.

       Solomon na isa hotel ɗin wayar Papa ya fara kira. Ba a ɗauki lokaciba kuwa ya ɗaga. Bayani ya shiga yimasa da yarensu wanda sam ban fahimci akan minene ba. Sunja lokaci mai tsaho suna wayar sannan ya kira madam Chioma itama. Itama ɗin dai magana sukai ta tsahon lokaci da wani yaren ba irin wanda sukai da papa ba. Batun yau ba na fahimci Solomon najin yare ba ɗaya ba. Kamar yanda na kula shima Yoohan ba yare ɗaya kawai yake jiba bayan turanci. Shiyyasa a lokuta da dama nakan gaza banbance shin su wane yarene wai?.

*_WASHE GARI_*

          Washe gari da safe ƴan gidan su Nu'aymah sukaje asibitin suka duba Nu'aymah data sake farfaɗowa. Sai dai har suka gama abinda zasuyi suka taho basuga Yoohan ba. Yana office yana duba marasa lafiyar da suke da tsananin buƙatarsa duk da da da farko baiyi niyyar hakanba.
       Suna dawowa gida kuma suka iske baƙin da basu san da zuwansu ba. Kakar Nasir data haifi babansa ce tazo daga katsina mai suna Hajiya Hassana. Sai dai suna kiranta Ananah, yayar Hajjo ce uwa ɗaya uba ɗaya, wadda ita kaɗai ce ta rage mata a duniya. Hajjo na tsananin girmamata dan itama tana ƙaunar hajjon, batason abinda zai taɓa hajjo da zuri'arta, ta zame mata tamkar uwa da uba. Itama ta tsufa sosai fiye ma da Hajjo, sai dai da yake ALLAH ya basu lafiya sosai ga jin daɗin rayuwa, ko ina suna zuwa, garama hajjo tana fama da ciwon ƙafa. Ananah kuma idanuntane dan sai da galashi take gani da ƙyau.
       Tare take da jikokinta da yaranta biyu ƙannen mahaifin Nasir ɗin mata. Dama duk babbar salla anan take salla kano, ita kuma hajjo sai gab da azumi take zuwa mata can katsina tai kamar wata guda. Hakan na sakasu farin ciki sosai.

‘To yanzu kuma Nasir ya ɗaɗɗago Ananah akan batun Nu'aymah. Ko yaya zata kasance?. saimu bisu muga wane mai rabo ne zai ɗauki wannan allurar ta cikin ruwa😉?’.

         Ba ƙaramin farin ciki hajjo dama duk jama'ar gidansu Nu'aymah sukaiba da zuwan Ananah. Dan yanda take son kowa a gidan haka kowa ke sonta da ƙaunarta har surukan Hajjo. Take gidan ya rikice da murna dan duk tunaninsu ta iso da wurine saboda bikin su Kubrah nan da kwanaki goma. Ciwon Nu'aymah ne ma yaɗan sanyaya shirye-shiryen da akeyi.
       Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya abinci gabansu kala-kala daga kowanne sashe. Da mamaki Ananah tace, “Wai ni banga ƙawalliyata ba ita?”. Kowa yasan Nu'aymah take nufi. dan suna shiri sosai-sosai da Ananah, saboda Nu'aymah nada sunan hajjo ma take cemata ƙawalliya.
        Rufaidah ce tai caraf ɗin cewa “Ananah tana asibiti babu lafiya” a rikice Ananah take tambayar, “Asibiti kuma? Miya sameta ni Hassana ɗiyar malam Haruna”. Shiru kowa yayi ya gaza bada amsa. Sai hajjo ce tai ɗan murmushi da cewar, “Ciwonta ne ya motsa, amma Alhmdllh da sauki ma”. 
      Cikin jimami Ananah ta share ƴar ƙwallar data taru mata a ido, tace, “Kai duk wanda yay sanadin shigar wannan yarinya a bala'innan yayi asarar rayuwarsa wlhy, ALLAH ya saka mata, ko wanene kuma ALLAH ya hanashi farin cikin duniya dana lahira”.
      Kusan a tare duk falon suka amsa da amin.

★★

          Bayan sallar magriba Ananah sukaje asibiti suma suka duba Nu'aymah, a lokacin Yoohan yaje airport amso saƙon da aka aiko masa daga ƙasar canada. Hakan yasa har suka kammala suka wuce yanzunma basu haɗu da shi ba. Sai bayan wucewarsu da kamar awa guda ma ya dawo.
            Kansa tsaye ɗakin da Nu'aymah take ya nufa. Solomon biye da shi ɗauke da wata madaidaiciyar bag. A ciki ya samu Nurse ɗin data gama gogema Nu'aymah dake barci jiki. 
     Da girmamawa ta gaida shi, Solomon kuma ya ajiye bag ɗin ya fice. Matsawa yay gaban gadon lumsassun idanunsa akan Nu'aymah da fuskarta tai wani irin fayau. Sai uban haske data ƙara tamkar mai yaron ciki. Ya kafe Laɓɓanta da sukayi wani irin jajur gwanin sha'awa, gashi taɗan tsuke bakin ya sake komawa mitsitsi.
         Huci ya ɗan furzar ya janye idanunsa daga kallonta, yana faɗin ‘Bakin tsiwa’ a zuciyarsa. ya gyara kujerar gefen gadon ya zauna tare da ɗaukar bag ɗin da Solo ya ajiye ya buɗeta. Madaidaicin abu ya fiddo cikin kwali mai kama da kula, ya buɗesa sai ga ƙanƙara a sama tanata huci. a ƙasan ƙanƙarar ya zaro kwalaben alluran kusan guda guda bakwai ƴan ƙananu, yanda kwalaben suke ƴan mitsitsi sai ka ɗauka wani tarkacen banza ne. Nanko kuɗaɗene masu shegen nauyi zaune da ƙafafunsu. Sai da ya gama duba takardar dake a cikinsu kafin ya maidasu ciki ya fiddo ɗaya kawai.
    Miƙama Nurse ɗin dake a ɗakin yayi, murya a daƙile yace “Kiyi mata allurar nan yanzun nan”. Amsa tayi da girmamawa. A gabansa ta buɗe syringe ta kwashe ɗan ruwan allurar da ko ganinsa bama ayi sosai cikin syringe ɗin. Shine ya nuna mata a inda zatayi. (A raina nace da idon Aymah biyu sai anyi ƙaramin yaƙin duniya na uku kafin ayi allurar na kuwa🤣).
           Mintuna uku ba'a rufa dayin allurarba wani irin mahaukacin zufa ya fara tsatstsafowa a kowacce ƙofar gashi ta jikin Nu'aymah. Kafeta da kallo Yoohan dake zaune ƙafa kan ɗaya ya harɗe hannayensa a ƙirji yayi. Yanda take wani irin mutsu-mutsu kamar macijiya mai tsohon ciki ne ya sakashi sakin wani tattausan murmushi daya ƙawata cikar haibarsa da kwarjinin bautar UBANGIJI. Ya ɗan lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta yana jan ajiyar zuciya.............✍

‘Saura naji wani yace ɗan kaɗan ne😣😒. Da gobe saina ƙara rage mudu🚶🏻😑😚’.


______________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


*Ga breakfast nan aci a hankali har dinner ɗin gobe idan ALLAH ya kaimu sai ku ɗumama😎😁⛹🏻‍♀️*.


No. 40

............Ƙarfe sha ɗaya na dare Yoohan da Solomon suka bar kano zuwa Abuja. Tafiyar da bata kulle awa guda ba jirginsu ya sauka. Sun iske guards ɗinsa tuni suna a airport ɗin ma, dan haka basu ɓata lokaciba wajen wucewa gida.
         Kamar yanda yay tsammani ya iske gidan nasu shiru, alamar duk sun kwanta, madam Chioma kawai suka iske a falo zaune cikin kwalliyar riga da wando da sukai mata ƙyau sosai. Yanda ta zubamasa ido haka shima kallonta yake babu yabo babu fallasa. Cikin takun nasa ya ƙarasa gareta, itama sai ta miƙe tana mai buɗe nasa hannayenta alamar yazo gareta.
       Gabanta yaje ya tsaya batare da ya shiga jikin nata yanda ta buƙata ba. Ya kamo hannunta ɗaya yana ɗan shagwaɓe fuska kaɗan. Cikin sanyin muryar da tabbatar da agajiye yake, da yarensu yace, “Mom na girma ni”.
         Ɓata fuska tayi itama cikin wani yanayi, muryarta na harɗewa wajen fita tace, “Please my boy”. Karan farko ya saki lallausan murmushin da ya nema sumar da ita a wajen. Ya ɗora hannunsa na haggu saman tattausan sajensa ya shafa yana ɗan kauda idonsa daga gareta zuwa ƙafar benen dake a falon inda Miracle ke tsaye cikin kayan barci, ƙirjinta rungume da madaidaicin teddy bear ta wani kafesa da idanu tamkar zata haɗiyesa ta huta.
        A hankali ya janyesu gareta yay wani luuuu da su kamar zai rufe sai kuma ya buɗesu yana sakin hannun Mom yaja baya. Hannayensa duka biyu ya ɗaga mata da faɗin “Sweet mom gudnit”. Kafin tace wani abu harya fara hayewa upstairs ɗin da ɗan sauran kuzarinsa batare da ya sake duban Miracle ba ya raɓa ta gefenta ya wuce.
     Su duka da kallo suka bisa harya ɓacema ganinsu, mira ta share ƙwallar data cika mata idanu ta juya da gudu zuwa ɗakin barcinsu ita da joy. Wata malalaciyar harara Mom ta raka Mira da ita. Kafin ta taune lip ɗinta na ƙasa da ƙarfi zuciyarta na ƙuna fiye da yanda gangar jikinta ke tsuma.

          Yoohan daya iske ɗakinsa kamar yanda yay fata komai fes bai wani zauna ba ya shige toilet. Bayan wasu mintuna masu ɗan tsaho ya fito jikinsa na ɗigar da raɓar ruwan wanka. Da sauri yaja ya tsaya ganin Mom zaune bisa sofa. A ɗan daburce yace, “Mom lafiya kuwa?”. Saurin ɗago idanunta dake akan wayarta tayi ta dubesa, dai-dai shi kuma yana ƙoƙarin saka farar t-shirt ɗin daya ɗauka. Miƙewa tai ta nufosa tana wani sakin tattausan murmushi, ta ɗauka ƙaramin towel ɗin daya fito da shi a hannu ta nufi sumar kansa alamar zata tsane masa gashinsa dake ɗigar da ruwa. Da ɗan hanzari yaja baya kaɗan yana tsuke fuska.
       “Mom!!” 
   Ya faɗa aɗan tsawace. Jin a yanda yay maganar ne ya sakata tsayawa cak daga yin abinda tai niyya. 
         Da ɗan shagwaɓa yace, “Haba Mom! Miyasa kike son maidani baya ne kullum? Nifa ba Abraham bane ko Victoria Please”.
        Ƙanƙance mayatattun idanunta tayi tana ɗan matsosa, cikin muryarta dake wani irin rawa tace, “Kaine kake ɗaukar kanka babba John! Ita uwa ɗanta kullum yaro ne a gareta. Ina sonka Yoohan fiye da yanda kake tunani, kai ɗin farin cikinane fiye da sauran ƙannenka”.
        Ɗan lumshe idanu yay ya buɗe a kanta, ya ɗan sassauta muryarsa da fuskarsa dake a tsuke. Dan shi harga ALLAH bai fassara maganarta da komaiba face soyayyar ɗa da uwa. “Na sani Mom, nima ina sonku da ƙaunarku fiye da zato ke da papa da ƙannena. Amma Please ki ringa rage cewa zakimin wasu abubuwan. Bama ni ba ko Abraham ɗan shekara goma ba komai zaiso kimasa ba yanzun. Mun rigada mun girma, hidimar da kikai mana muna ƙanana ta wadatar uhmyim?”.
         Yanda yay maganar cike da lallashi ne ya sake narkar da ita a wani irin yanayi mai wahalar fassara. Ta buɗe baki zatai magana aka turo ƙofar aka shigo. Gaba ɗayansu ƙofar suka kalla. Papa ne cikin kayan barci da alama ma ya fara barcin tashi yayi.
      Cikin ƴar shagwaɓa Yoohan yace, “Yauwa papa Please kwashi matarka ku wuce dama ta sakani a gaba nikam”.
       Papa dake bin Mom da wani irin kallo ya haɗiye yawu da yin guntun murmushi yana maida idonsa akan Yoohan ɗin da ya sake ƙwaɓe fuska. Muryarsa da alamun barci ya tashi yace, “Yaushe ka dawo?”.
         Mirror Yoohan ya nufa yana faɗin, “Yanzun nan babu jimawa nazatama baka gida ai”.
     Komai papa bai ceba ya kama hannun Mom suka fice yana faɗin, “Huta abinka sai da safe”. Suna fita Mom ta fisge hannunta da ga na papa tana kumbura kumatu. Baice mata komaiba yay gaba abinsa dan jin Yoohan yana sakama ƙofarsa key. Yasan ko mi zatayi bazai sake buɗe mataba kuma. A ransa kuwa mamakin yanda Matar tasa ke nuna tsananin so ga ƴaƴansu yakeyi. shi bai taɓa ganin mahaifiya mai ƙulafucin ƴaƴa irin Madam Chioma ba.
   
        Yoohan kam koda ya kammala kimtsawa falo ya fito ya haɗa tea ya koma bedroom ɗinsa. Zaman sha yay zuciyarsa da tunaninsa duk na wajen Nu'aymah. Ji yay yana buƙatar sanin yaya take yanzun, dan haka yaja wayarsa ya nema Dr Aysha a karo na farko a rayuwarsa.
      Ita kanta Dr Aysha ba ƙaramin mamaki tayi ba ganin kiran Dr Yoohan a wayarta. Abinda bai taɓa faruwa ba. Jikinta har tsuma yake wajen saurin ɗauka. Ta kara a kunne murya a narke tace “Hello! Doctor good evening”. Maimakon ya amsa mata sai cewa yay “Assalamu alaiki”. Idanu taɗan zaro waje jin sallama yayi, saɓanin da da sai dai ya ce maka hii. Itafa dama gaba ɗaya a wannan zuwan nasa abubuwa da yawa taga idan yanayi tamkar ba shiba. Shekaranjiya ma har ganinsa tai kamar ya fito massallaci......
     Sallamar da ya sake maimaita matace ta katse mata tunaninta. “I'm sorry sir. wa'alaikissalam. Kunje lafiya?”.
       “Humm” 
ya faɗa a taƙaice yana lumshe idanu da kai kofin tea ɗin bakinsa. Sai da ya kurɓa ya haɗiye kafin yace, “Ya yarinyar nan ta farka ne?”. Ta gane Nu'aymah yake nufi, dan ita kaɗaice patient ɗin daya kwantar dai. Cikin sanyaya muryarta tace, “A'a har yanzu tana barci, amma an saka mata drip ɗin daka ce ɗin yanzun babu jimawa”. “Okay night” ya faɗa a taƙaice da yanke wayar batare da ya ƙara komai ba.
       Nannauyan ajiyar zuciya Dr Aysha ta sauke tana ɓata fuska kamar zatai kuka. Akan laɓɓanta ta furta, ‘Ɗan wulaƙanci’.
     Oho baimasan tanai ba, dan shi tea ɗinsa ya ƙarasa sha kafin ya miƙe ya nufi toilet. Alwala yayo. Ya saka sallayarsa sabuwa da baba malam ya bashi ya tada salla kamar yanda ya keyi yanzu a kowanne dare. Idan har ya samu dama yakan fara daga ƙarfe ɗaya ko biyu, zuwa uku sai yaɗan kwanta kafin asuba.
   

*_WASHE GARI_*

    
           A gidan su Nu'aymah kuwa a safiyar yau bayan kammala breakfast ɗunguma sukai asibiti suka duba jikin ta, kamar ko yaushe basu duka aka bari suka shigaba. Baba malam ne kawai dasu Abba Musbahu. Sai hajjo da Ananah. Umm dama batajeba dan tanason zuwa gidan Gwaggo mahaifiyarta. Daga can zata biya asibitin tare da Gwaggon.
      Basu jima a asibitinba suka dawo gidan, baba malam da ƙannensa uku da hajjo sai Ananah a falon hajjo suka yada zango domin tattaunawa. Sunyi zaman kusan awa guda sannan Abba Musbahu yay kiran Abdallah da Naser a waya. Ba a rufa mintuna biyarba kuwa sai gasu dan dama duk suna gida. Zama sukai inda Ananah ta nuna musu kowanne kansa na a ƙasa..
        Fuskar baba malam a ɗaure ya dubi Abdallah, “Abdallah zan fara ta kanka, dan karka zata shirun da mukai maka kamar mun ƙyalekane bisa abinda ka aikata mana. Gani ga ƴan uwana ga Hajjo harma da Ananah. Inason ka faɗa mana dalilinka na aikata abinda ka aikata. Shin bamu da daraja a idanunka ne mu da muka baka auren yaranmu kokuwa raini ne dan kaga ka girma?”.
       Cikin sauri Abdallah ya ɗago yana kallon baba malam ɗin da girgiza kansa. “Wlhy sam ba haka bane ba Abbah. Kuna da darajar da bayan MANZON ALLAH babu mai ita a idona a duk faɗin duniya sai ku”.
        “Ban yarda ba Abdallah, inda ace munada wannan darajar da bazaka aikata abinda kayi ba. Mu aura maka yara ka sake mana su akan wani banzan dalilinka mara amfani”.
        “Abba ku gafarceni, amma wlhy ina son Nu'aymah, son da zaku iya rasani idan kuka hanani mallakarta. dan ALLAH a wannan karon karkuce mani a'a”.
         “Ba maganarta nai makaba ni ai, maganar yarana daka saki nake maka”.
       Shiru Abdallah yay zuciyarsa na masa ƙuna da zafi mai raɗaɗi, sai faman haɗiyar zuciya yake kamar budiddigin ƙwaɗo. Ganin yaƙi cewa komai hajjo ta amshe zancen da cewa, 
       “In banda zancen banza taya dan kawai nayi maka magana zakaje ka aikatama yara wannan wautar, ina iliminka yake? Ina wayonka yake? Kaine fa babba a gidan nan, kuma ka tabbatar abinda ka aikata da shi na ƙasa da kai zasuyi koyi. Ta hakane zaka iya zama jagora uba garesu a randa ƙasa ta lulluɓe idanunmu mu da iyayen naka?”.
      “Kiyi haƙuri hajjo”. 
Ya faɗa muryarsa na zuga.
       “Idanma banyi haƙuri ba dukan ka zanyi Abdullahi. Yanzu dai ka maida matanka, batun Zainabu kuma gaka ga Nasiru yanzun, sai ku sasanta kanku dan babu mai shiga a wannan karon. Duk wanda ya sameta a cikinku mu abin farinciki ne a garemu, kuma zamu saka albarka. Sai kuje ku nema yarda daga gareta, wanda duk ta zaɓa magana ta ƙare”.
       Hukuncin hajjo yayma kowa dai-dai, sai dai banda Naser da Abdallah. Dan a kallo ɗaya zaka hango tsantsar tashin hankali cikin idanunsu. Lokacin da suke ficewa daga falon har tafiya suke kamar zasu kifa, musamman ma Abdallah.

   
*_ABUJA_*

          Aɓangaren Yoohan kam yau da azumi ya tashi kasancewarta al-hamis. Azumin litinin da alhamis yana ɗaya daga cikin ibadar da tun bayan musulintarsa ta fara zame masa jiki. Bayan ya idar da sallar asubahi yay zaman yin azkar kamar yanda baba malam ya koyar da shi ta bidiyo kol da sukeyi a kullum. Sai dai kasancewar bai gama haddacesu ba sai yake karantasu a littafin. Sai da gari yay haske kamar yanda shari'a ta koyar sannan ya miƙe zuwa ɗakin motsa jikinsa.
      Kamar yanda ya saba ya farayi yana haɗa uwar zufa, kasancewar kwana biyu bai samu damar yin na kirki ba a kano sai yau yaji jikinsa yay masa ɗan nauyi. Hakan ya sashi zarta lokaci kaɗan, dan har Solomon ya shigo masa da tatattun kayan itatuwa (fruit) bai kamalla ba. 
        “Good morning sir” 
Solo ya faɗa yana ɗan risinar da kansa tire a hannunsa.
    A taƙaice Yoohan dake ɗan hakki ya share zufar goshinsa da cewa “Same”. Da ga haka ya cigaba da abinda yakeyi. Shigowar Solo da kusan mintuna sha biyar sannan ya kammala, lokacin har an fara gudanar da program ɗinsa a NTA. zama yay Solo ya miƙo masa juice ɗin. Kai ya girgiza masa yana goge zufar dake tsiyaya masa da ƙaramin towel, yace, “Barsa kawai”.
       Sosai Solomon yayi mamaki. dan a watan nan ya fara lura da wani abu daga ogan nasa. Duk monday and Thursday da wahala kaga yaci wani abu har yamma. Kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru. Shima Yoohan ɗin bai sake tankawa ba, sai ma maida hankalinsa da yayi ga television ɗin gaba ɗaya. Ana kammala program ɗin ya miƙe, anan yabar Solomon na kimtsa ɗakin.
        Tsaf ya tadda ko'ina Solo ya gyara, sai ƙamshi da sanyin ac dake ratsa ko ina. Toilet ya nufa yay wanka, ya ɗan jima a ciki kafin ya fito. Bashi da sha'awar fita ko'ina yau ɗin nan, dan haka body spare kawai ya saka da boxer ya haye gadonsa ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya. Cikin mintuna kaɗan barci kuwa yay gaba da shi.

         A falo kam koda su madam Chioma suka haɗu dan yin breakfast kakarsa data haifi papa ce ta saka Destiny wai taje ta kira Yoohan ɗin. Sosai Destiny ta waro idanu waje. cikin yare tace, “Granny inajin tsoro gaskiya. Brother John baya son mutane”. Harara mama ta zuba mata, cike dajin haushi ta duba Madam Chioma. “Ai ga wadda ta watsa shi nan bai ganin kowa da gashi sai ita data haifesu. Yaro sai masifar taurin kai”. Banza Momy tai mata, sai mamanta ce ta karɓe zancen da faɗin, “Inma a bauɗen yake ai ba ita kaɗai ta bauɗar da shiba harda ɗanki. Debora ki daina sakama yarinyata baki akan rayuwarta fa, ni dama nasan masiface ta kawoki ba komaiba. dan kawai kinga nazo, yanda kikejin gidan ɗankine nima gidan inlow ɗina nen ai”.
      Ai kafin kace kwabo sun hargitse da cacar baki kamar wasu kaji. Su dai jikokin duk idanu suka zuba musu kawai suna kallo da ƙannen papan dama momy ɗin kanta. Abun nasu zattakaici da dariya. Basuyi shiru ba sai da papa ya fito yay musu magana cikin damuwa.
     Daga haka suka koma harar juna suna huci kamar wasu zakuna. Daga ƙarshe basuci abincin a Dining ɗinba sai dai kowa masaukinta ta koma aka kai mata nata.

      Yoohan da baisan sunayi ba kam sai wajen sha biyu ya farka. Wanka ya sakeyi yay shiri cikin ƙananun kaya. Blue jeans da t-shirt fara ƙal an rubuta HERO da kalar blue a gaba. Ya gyara sumarsa da sajensa yanata zabga ƙamshi. Slippers masu taushi ya saka dan ba nisa zaiyi ba. Ya ɗauka wayoyinsa ya fito.
      Da sauri Favour ta ɗauki remot ta rage kiɗan da suka saka a sifiku kamar zai tsaga falon lokacin da yake sakkowa. Fuska a matuƙar tsuke ya dubesu, baiko amsa gaisuwar da suke jera masa ba yace, “Wannan kiɗan da kuka cikama mutane kunne da shi fa?”.
       Cike da tsoro Victoria tace, “Brother sai da nacema Favour karta kunna bakason ƙara da yawa, amma tace sai......”. Wani irin zabura Favour tayi ta danne bakin Victoria dan karta ƙarasa faɗa. Ba komai ta tuna ba sai marin da ya taɓa kashe fuskarta da shi ranar X-max ɗin last year da sukaje a ƙauye ya iske ta samu ciki. Cikin rawar murya tace, “Ƙarya take Uncle John, na rantse bance komai ba”.
      Shi baimabi takansu ba ya fice abinsa saboda jin kakarsu data haifi papa na ƙwala masa kira da alama sunansa dasu Victoria suke ambata ta jiyo.
       Da ƙafa ya fice a gidan bayan ya gaisa da ma'aikatan gidan a tsaitsaye. Can bayan layinsu ya nufa, inda yake ganin wani masallaci. Acan ya gabatar da sallar azhar, koda aka idar ya dawo gidan garden ya wuce kai tsaye. Babu kowa a ciki, sai sassanyar iskar dake kaɗawa daga ni'imar itatuwan cikin garden ɗin. Anan yay zamansa har la'asar tayi, kasancewar yanada alwalarsa massallacin ya sake komawa yayo sallar la'asar, ya cigaba da zamansa a ciki har zuwa biyar sannan ya fito.
       Daya dawo ma bai shiga ciki ba, duk da kuwa Solomon ya sanar masa Momy nata zuwa nemansa tun ɗazun. Aika solo ɗin yay ya ɗakko masa key ɗin mota a ciki. Tare suka dawo da Miracle. Koda ta gaishesa sau ɗaya ya amsa ya ɗauke kansa, cikin damuwa ganin zai shiga motar tai saurin fada masa Momy tace yazo yaci abinci. Bai amsata ba sai da ya shiga motar mazaunin driver, dan ya hana kowa binsa. Kallonta yay sau ɗaya ya ɗauke kansa. “Ki sanar mata ina azumi”. Daga haka yay reverse ya fice a gidan.
         Koda ta koma ta sanar ma madam Chioma sosai sukaita mamakin azumin mi Yoohan ɗin keyi? dan sunsan dai su azuminsu yanada lokutansa a addininsu. Ganin basu da mai basu amsa suka haƙura harya dawo gidan.

       Yoohan kam koda ya fita wajen Hamza Ibrahim ya nufa, can suka haɗu gidan wani haɗaɗɗen abinci daya gaji da ƙawatuwa. Sun ɗan zauna kusan na mintuna talatin kafin a kira sallar magriba. Zuwa sukai sukayo salla suka sake komawa gidan abincin, anan Yoohan yay musu order ɗin abincin buɗa baki dan shima manager axumin ya keyi. Da wannan damar sukai amfani wajen sake faɗaɗa hirar tasu da duk ta kasance akan abinda ya faru a kano, wadda dama duk ya sanar masa ta waya. Hasalima shine ya bashi shawarar kawai yacema baba malam zai auri Nu'aymah ɗin koda a yanzunne. Shi kuma aranar bai wani ja zancenba ya amince da shawarar duk da a idanunsa yana ganin Aymah tayi ƙanƙanta da aure. 
      A fahimtar manager dai anya dama Yoohan ɗin ba ya na son Nu'aymahn bane kuwa?. Da yake baida mai bashi amsa sai ya watsar da zancen.
      Duk yanda ake gudanar da bikin aure a musulinci da hidimar da hausawa keyi a al-adance manager ya sanarma Yoohan, dan haka basu rabu ba sai kusan goma na dare.
      Koda Yoohan ya dawo a harabar gidan ya iske papa nashan iska. Zama yay a wajen suka tattauna abinda ya shafesu. Sai kusan ɗaya saura suka shiga cikin gida. A hakanma Yoohan ɗinne ya nuna ya gaji.

*_BAYAN KWANAKI UKU_*

        A kwanaki ukun nan kullum sai Yoohan dake a birnin ikko yanzun sai ya kira Dr Aysha yaji yanayin jikin Nu'aymah da suka maida sumammiya, dan tunda ya bar kano a yanayin barci take, sai dai drip da ake ƙara mata a koda yaushe da allurai a ciki. Haka suke buƙata ta sami isashen hutu. Allurar kuma daya sa aka kawo masa daga canada tun wadda akai mata randa aka kawo ba'a sakeba. Dan ƙa'idar allurar sai bayan sati ɗaɗɗaya za'ayita, hakan yasa bai bama kowa ba ya ajiyeta a office ɗinsa a waje mafi sirri. Dan daga Lagos nan kano yake fatan dawowa ya duba Nu'aymahn. Kamar yanda ya sabarma kansa kuma kullum sai ya kira baba malam sun gaisa safe da maraice.

       A gidan su Nu'aymah kuwa shirye-shiryen biki ake babu kama hannun yaro, dan yau saura kwanaki shida kacal a ɗaura auren su Hajarah. Da Abban su Adawiya yace a ɗaga har sai Nu'aymah ta samu sauƙi. Amma sai baba malam ya hana hakan. Ya ce babu abinda za'a fasa ALLAH zai bata lafiya itama.
         Yayinda aketa shirin biki Abdallah da Naser ƴar tsama a tsakaninsu kullum sake faɗi da tsauri takeyi akan Nu'aymah. Gashi sun maida asibiti wajen yininsu duk da ita wadda sukeyi domintama batasan sunayi ba ma. Duk sunbi sun tashi hankulansu akanta. Yayinda Adawiya ita nata hankalin yafi nasu tashi. Dan har yanzu Abdallah yaƙi maida auren nasu. Su baba malam kuma babu wanda ya sake cewa da shi komai akan hakan.
      Sosai Adawiya ta rame, kamar ba itace suka dawo ta zama lukuceciya ba. Tabi ta ɓoye kanta a gidan babu mai ganinta sai ƴan sashensu. Ita kuma Addah tayi kamar bama tasan halin da Adawiya ke a ciki ba. Dan tun lallashin datai mata na farko taki saurarenta saita watsar da ita bayan ta babbanka mata zagi da yi mata kaca-kaca.
       Ƴan uwantane kawai da Umm ke tausayinta, dan Hajarah tamafi kowa damuwa da halin da Adawiya ta jefa kanta. Har kwatance take mata da yanda Yusrah tai kamar komai bai dametaba tanata harkokinta ita. Hakama Nu'aymah lokacin da aka rabasu aka bashi aurensu. Amma sam Adawiya taƙi fahimta. Sai bin hanyoyin da zatai magana da Abdallah takeyi shi kuma ya toshesu ya hanata kowacce dama. Gaba ɗaya ya maida hankalinsa ga takarar neman yardar Nu'aymah da take a rabin duniya da barzahu.

       A washe garin da Yoohan ya cika kwanaki huɗu da tafiya su Papa sukazo kano shida ƙannensa da abokansa uku. Babu wanda yasan abinda ya kawosu. Shi kuma baba malam bai faɗama kowa ba sai ƴan uwansa da Hajjo da Ananah kawai. 
     Amma yanda Papa da gayyarsa suka koma ransu a ɓace zai baka tabbacin zaman baiyi daɗi ba. Dan shima baba malam ɗin dai ranar yini yayi babu walwala tattare da shi. 

★★★★

        Ana saura kwanaki huɗu ɗaurin auren su Kubrah Yoohan dake a birnin ikko har yanzu ya kira Dr Sa'ad ya sanar masa su tsagaita da yima Nu'aymah allurar barci haka nan, idan ta farfaɗo a kowanne lokaci a kirasa a sanar masa.
      Haka kuwa akayi, ƙarfe kusan sha biyu na daren rar Nu'aymah ta farfaɗo............✍


_________________________


        ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.      





I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 42

.............Wani irin zabura Yah Ab yayi tamkar wanda yay gamo da mala'ikin mutuwa. A tsananin razane yace, “Nu'aymah kina nufin Naseer?!!”.
        Fashewa tai da wani sabon kukan tana jijjiga masa kanta. “Yah Ab kayi haƙuri, yanzu shine ya fi cancanta da hakan a gareni, kai ma dan ALLAH ina roƙonka ka maida matanka. Dan ALLAH ka kare mutuncin danginmu, karka bari wannan ya zama sanadin rusa zuminci ko saka ƙiyayya a tsakaninmu. Kayimin afuwa mu rungumi ƙaddara, UBANGIJI ya fimu sanin hikimar dake a cikin hakan. Dan........”
        Da sauri ya ɗaga mata hannu jikinsa na wani irin tsuma na yunƙurowar zuciyar tasu ta gado. Ya duba iyayensu da duk sukai tsit suna kallonsu tamkar babu su a cikin falon. Sai kuma ya duba Naser dake ta zuba murmushi idanunsa a lumshe bakinsa na motsawa alamar addu'oin godiya ga UBANGIJI yake jerawa. Batare da yace komai ba ya juya zai fice.
         “Abdallah!”.
Baba malam ya kirashi cikin muryar rashin wasa.
     Cak ya tsaya, sai dai bai iya juyowa ba. Cikin bada umarni Hajjo tace, “Dawo ka zauna”. Hawayen da suka cika masa idanu ya share. Kafin ya juyo a hankali ya dawo inda yake da, ya sake zama batare da yayi magana ba.
           Kallon Nu'aymah dake kuka hajjo tayi. “Zainabu tashi kije mun gama da ke. Ki kuma share waɗan nan hawayen ki kwantar da hankalinki, dan munsan abinda mukeyi”. Kai kawai ta jinjina mata tana miƙewa. Batare da ta sake duban inda su Abdallah suke zaune ba ta fice a falon jikinta duk a sanyaye. Zuciyarta kuwa wani irin zafi take mata tamkar ana gasa mata ita bisa garwashin wutar gasa balangu.

     ★★<>★★

  Tun wannan zama da akayi Nu'aymah bata sakeji daga bakin kowa ba a gidansu. Dan zuwa yamma ma gidan sai ya sake cika maƙil da baƙi dake ta sake ɓullowa ta kowanne irin kusurwa saboda walimar da za'a gabatar daga ƙarfe huɗu. Hakama su Yah Ab bata sake ganin kowa ba a cikinsu, harma iyayen nasu. Garama Abba Musbahu taji muryarsa bayan la'asar ɗin ya shigo suna magana dasu hajjo a falo.
          Ana idar da sallar la'asar mafi yawan mutanen dake cikin gidan suka fice wajen walimar. Anguwar tayi tsit bakajin komai sai karatun alkur'ani Muhammad ƙaninta ke rairawa cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗi. Lamo tai a kan gadon hajjo dan bata da sha'awar fita wajen walimar. Fitar tata zai iya fama mata ciwuka masu yawa da suka zame mata gyambo a zuciyarta. Hakan yasa ta zaɓi cigaba da zamanta tunda daga nanma tana iya jiyo komai da ake faɗa tamkar tana a wajen.
            A wajen walima kam bayan Muhammad ya gama karatu baba malam ya buɗe taro da addu'a ga amare da angwayensu dama al'umar musulmai gaba ɗaya. Daga nan aka fara abinda ya tara mutane. 
       Duk yanda akaita ragargaza wa'azi mai ratsa jiki a kunnen Nu'aymah ne, duk ba itace amaryarba sai da ta taya su Aunty Hajarah hawaye. Lokacin sallar magrib nayi akaje akai salla aka sake dawowa. Sake ɗorawa da wasu nasihohin sauram manyan malamai abokan su baba malam sukayi. Daga haka akaci aka sha kowa yay haniƙan, aka kuma raba abubuwa kamar yanda suka saba duk lokacin aurar da yaransu ko yaran gidan marayunsu. 

       Lokacin da aka tashi tuni Nu'aymah data koma sashensu tai barci a falon baba malam. Umm bata sani ba, dan tana can wajen taimakawa baƙin da zasu kwana a sashenta samun wajen kwana. Sai da baba malam ya shigo wajen sha biyu sannan ya ganta kwance a doguwar kujerar falonsa ta naɗe waje guda alamar sanyi takeji. Zama yay a kujerar gefen da kanta yake yana kallon ƙyaƙyƙyawar fuskar ɗiyar tasa mai tsananin kama da mahaifiyarta abar sonsa da ƙaunarsa. Ɗan murmushi yayi tare da shafa kumatunta sannan ya miƙe. Batare daya tadata ba ya cire babbar rigarsa ya lulluɓa mata. Yana jinta ta sauke ajiyar zuciya, tare da gyara kwanciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya ɗauka remote ɗin ac ya rage mata shi sosai sannan ya wuce bedroom ɗinsa cike da tausayinta.

*_JUMA'A_*

          Da asuba baba malam bai wuce massallaci ba sai da ya tada Nu'aymah. Bayan an idar da salla bai jimaba ya dawo dan yau basuyi zaman karatu ba daman. A falo ya iske Nu'aymah inda tai salla tana karatun Al-qur'ani. Zama yay kallonta da sauraren zazzaƙar muryarta da a yau take fita da sanyi matuƙa. Yayi kusan mintuna arba'in sannan Umm ta shigo falon da sallama. Tray ɗin hannunta ta ajiye a gabansa tana kallon Nu'aymahn da mamaki. dan ita dai bataga wucewarta ba. Kallon baba malam tai, ya sakar mata lallausan murmushi tare da maida idanun nasa shima kan Nu'aymah da batasan sunayi ba.
      Zama Umm tai a kusa da shi. Cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “Yaushe tazo nan?”. Murmushin ya sakeyi kamar bazaice komaiba, sai kuma ya ɗan sauke numfashi yana riƙo hanun Umm cikin nasa. Cikin wani irin yanayi yace, “Anan ta kwana. Nima na dawo wajen walima na sameta anan da alama bama taje wajen walimar ba”.
           Guntun numfashi Umm ta furzar, batare da tace komaiba ta zare hannunta cikin nasa. Shayin daya saba sha duk irin wannan lokacin ta shiga haɗa masa. Yayinda Nu'aymah keta karatunta batare da tasan mi sukeyi ba. Sai dai tana ɗan jin motsinsu kaɗan-kaɗan, dayake hankalinta baya a tare da sune yasa batajin mi suke faɗa.

        Duk hidimar da ake a gidan da sake cika da yake yi da baƙi Nu'aymah tana sashen baba malam taƙi fitowa. Yau tare da shi ma sukai breakfast. Sashen nasa ma itace ta gyara masa yau. Bayan yayi wanka ya fito ta shiga ta gyara masa bedroom ɗinsa tsaf, ta dawo falo inda yake zaune shida ƙannensa da huhunan goro dana alawa da aka shigo da su, magana suke ƙasa-ƙasa alamar tattauna wani abu mai muhimanci a garesu. Cike da girmamawa ta gaidasu, duk suka amsa mata da kulawa tare da tambayarta yaya ƙarfin jikinta.
     Har zata fice baba malam yace ta koma tai wankan a bathroom ɗinsa tunda mutane sunyi yawa a gidan. Daɗi taji sosai, dan haka ta juya cike da ɗoki ta koma bedroom ɗin baba malam ɗin.

      Tsaf Nu'aymah tai shiri da kayan da Umm ta kawo mata ɗakin baba malam ɗin. Lass ne ɗan ubansu sky blue da akaima ɗinkin riga da zani. Ya zauna mata ɗas a jiki tare da haskaka farar fatarta daketa ƙyalli. Ƴar ramar da tayi sai ta sake fiddo ainahin dogon hancinta da manyan idanunta masu matuƙar haske da cikar gashi. Turaren baba malam dana Umm dake a bedroom ɗin babu wanda bata fesa ba. Hakan yasa take zuba uban ƙamshi tamkar tayi wanka da turare. Gashi cakuɗasun da tayi sai ya bada wani irin shu'umin ƙamshi mai narkar da zuciyar mai shaƙa. Ɗan kwalin ta ɗaura bisa gyararren gashinta da hajjo ta matsa jiya Yah Omar ya kaita wajen wankewa tare da su Amal. Ta saka sarƙa da sauran kayan adon sannan ta ɗauki blue gyalen da aka haɗo mata da shi ta ɗora a kafaɗarta. ta zira flat shoes ɗinta suma blue. Tayi ƙyau sosai tamkar ka saceta ka gudu. Kamar yanda Umm ta gargaɗeta akan idan ta shirya ta fito ta gaisa da baƙi batayi musu ba ta nufi sashen Umm ɗin bayan ta kulle falon baba malam ta taho da key ɗin a hannunta.

       Tunda ta fito jama'ar dake zazzaune a falon Umm keta ambatar masha ALLAH. Ita dai cikin ɗan jin nauyin wasu daga cikinsu ta shiga risinawa tana gaishesu. Masu tsokanarta kuwa ta kasa maida murtani. Saɓanin da da kowa yasan Nu'aymah bata barin saita kwana ga abokin wasa. da kace kule take cewa cas. Amma yau sai ga bakin ya mutu murus sai ɗan sassanyan murmushi kawai take musu a taƙaice.
      Har bedroom ɗin Umm ta shiga inda ƙanen Umm da yayunta ke cike da shi. Nanma gaidasu ta shigayi. Sukam sunata amsawa cike da ƙaunar ɗiyar ƴar uwar tasu. Aunty Hibba dake cin abinci ta jawo hanunta ta zaunar kusa da ita tana faɗin, “Zauna kici abinci. Ni wannan ramar taki sam banason ganinta dota”. A ɗan shagwaɓe Nu'aymah tace, “ALLAH na ƙoshi Umma, munyi breakfast tare da Abba, kuma naci sosai ki tambayi Umm ma kiji”.
     “Eh breakfast ai tun ɗazunne, kusan awa uku kenan, wannan abincin rana ne. Ke dama nasani da masifar son masa”. Duk yanda Nu'aymah taso zamewa sai da Aunty Hibba ta dinga bata masar a baki tare da naman. Sai gashi kuwa taɗanci babu laifi ta kuma shanye ƙaramar roban zoɓo data ɗauka.

★★★★

        A ɓangaren su baba malam kuwa duk sun ɗunguma massallacin juma'a inda za'a gudanar da ɗaurin aure bayan sallar juma'a insha ALLAHU.
      Massallacin ya cika danƙam da manyan mutane daga kowacce kusurwa ta Najeriya harma da wasu ƙasashen ƙetare. Tun daga kan malamai, ƴan kasuwa, harma da masu mulki. Sai abokan arzuƙa da ƴan uwa na kusa dana nesa. gayyar anguna dana jama'ar gari da girma da kimar su baba malam ɗince ta tarasu a wajen.
       Bayan kammala sallar juma'a akai ɗaure-ɗauren aure ciki harda na ƴaƴan su baba mala su Aunty Kubrah. Ana kammalawa manyan baƙi suka ɗunguma babban hall ɗin da aka kama domin gudanar da ƙwarya-ƙwaryar walimar cin abinci.
      Walimar ce ta jasu har sai bayan la'asar sannan suka koma gida da wasu tawagar baƙin da ba'a ranar zasu wuce gida ba.

     Zuwa yanzun kam gidan su Nu'aymah ya sake cika danƙam da mata, dan yau ne Addah ke nata yinin bikin. Hayaniya akeyi sosai babu maijin wani. Dan tun bayan ɗaurin aure su Omar sukaje gidan da labarin yanda komai ya kama.
    Nu'aymah na tsakkiyar dangin Umm har yanzu. Sun sakata a tsakkiya anata hirar zuminci cike da farin ciki. Wata Gwaggon su Umm ce, data kasance kaka ga Nu'aymah ta shigo ɗakin tana guɗa. Da mamaki duk suke kallonta har suna rige-rigen faɗin, “Gwaggo an ɗaura ne?”. 
       “Ƙwarai da gaske an ɗaura. Yanzun ma haka ƴan ɗaurin aure sun dawo, kuma harda sabon albishir na ƙarin amarya”. 
        Aunty Fareeda tace, “Ƙarin amarya kuma Gwaggo? A cikin yaran gidan dai?”.
       “Ƴarku ma kuwa” ta sake basu amsa tana cillara wata sabuwar guɗar. Kafin su gama fita daga ruɗani su Nanah suka shigo suna ƙwala kiran “Nu'aymah amarya”.
     Dakatar dasu Aunty Hibba tayi. “Kai mufa kuna sake ɓatar damu, Gwaggo wai mike faruwa?”.
    Da sauri “Raudah tace, “Momy baku san Nu'aymah ma an ɗaura mata aure ba yanzu tare da su Aunty Hajarah. Yanzun ƴan ɗaurin aure da suka dawo suke faɗa ai”.
        A take ɗakin ha harmutse da murna da taraddadin wanene angon? Miyasa kuma aka ɓoye musu, dan su dai basusan da auren ɗiyar ƴar uwar tasu za'ayi ba. Duk sunzone yima Addah baici kasancewar zumincine mai ƙarfi da kowa ya sani a tsakanin Umm da ita. 
       Tunda aka fara wanan kace nace Nu'aymah ta ɗora hanunta saman kai ta riƙe. Cusashi tai a tsakanin cinyoyinta jikinta na wani irin tsuma. Ga kanta ya fara sara mata sama-sama. Duk yanda taso ta daure ta kasa. Dan haka cikin ƙarfin hali ta shiga laluben wanda ke a kusa da ita. Cikin sa'a ta damƙo hanun Aunty Magajiya yayar Umm. Hankali tashe Aunty Magajiya ta dubeta, sai kuma yanda taga jikin Nu'aymahr na karkarwane ya sakata ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ da ƙarfi.
     Kusan mafi yawan ƴan ɗakin sai hankalinsu ya dawo wajen. A take kuma sai duk sukai tsitt tare da zabura kan Nu'aymah......

          Gwaggo Ramma ce ta hana ɗaga maganar mawuyacin halin da Nu'aymah ke a ciki a gidan har lokacin da su baba malam suka dawo. Dan Umm ma bata fasa kai da kawowar da takeyi tsakanin sashen Addah da sashentaba saboda son ganin baƙi kowa ya samu abinci. Yin komai takeyi cike da ƙarfin hali. Sai ta fakaici idon mutane take share hawayen dake cika mata idanu. Duk da kuwa ita tasan da maganar auren. Kuma tana cikin masu goyen bayan ɗaurashi a yau ɗin saboda wasu dalilainsu ita da baba malam da hajjo.
    Key da baba malam bai gani bane a inda suke ajiyewa ya sakashi kiran wayarta. Cikin sa'a kuwa wayar tana a tare da ita. Dan haka ta ɗaga ya sanar mata gashi ya shigo amma baiga key ba. Ta kira masa Nu'aymah ko ta canja masa waje.
      “To” kawai tace masa ta yanke wayar.
       Ɗakinta ta fara shiga inda danginta ke zaune jigum-jigum da Nu'aymah shimfiɗe bisa gado tana fidda wahalallen numfashi tamkar mai Asthma. Aunty Juwairiyya sai shafa mata ruwa take a fuska wasu kuma na tofa mata addu'oi. Wani Key ɗin ta ɗauka a drawer ta fita batare da tace musu komaiba ta fice.
         A kallo ɗaya baba malam ya fahimci akwai matsala. Tunkanma ta buɗe ya shiga jero mata tambayoyi akan mike damunta?. Sai da ta buɗe ƙofar suka shiga sannan tai masa bayani. Shima hankalinsa ne ya tashi, dan haka yace taje su maido Aymah sashensa, karsu bari kowa kuma ya fahimci halin da ake ciki. Bara ya kira Doctor.

        Tunda aka dawo da Nu'aymah sashen baba malam ALLAH ya bata ikon ganinsa saita damƙe hannunsa tana cigaba da jujjuya kanta da fisgar numfashi a wahalce. A hankali take magana wadda idan ba'a kusa da ita kakeba ma bazakajita da ƙyau ba.
        “Abbah kaina, kaina zai fashe Abbah. Kamin addu'a kaina zai fashe, Abba kamar ana kartamin ƙarfuna a ciki. Innalillahi... Abbana zan mutu..”
        Cikin rawar harshe baba malam yake girgiza mata kansa da haɗiye abinda ke cinkushe masa maƙoshi da ƙyar. “Bazaki mutuba Mamana kinji, daina magana kiyita addu'a a ranki insha ALLAH ga Doctor nan zuwa kinji”. Ya ƙare maganar da saka ɗan yatsa ya ɗauke hawayen da suka tsatstsafo masa saman fatar ido. Hajjo da Ananah ma hawaye sukeyi. Haka su Abban Abdallah ma duk zukatansu suya suke da tausayinta.
       Sallamar da akayi a bakin ƙofarne ya sakasu duk kallon ƙofar tare da amsawa. Ahmad ne ya fara shigowa, yana sanye cikin tattausan farar shadda harda babbar riga. Har yazo tsakkiyar falon sai kuma ya ɗan juya ganin wanda suke tare bai biyosa ba. “A'a Doctor shigo mana”.
      Kusan seconds biyar kafin a ɗaga labulen ya shigo bakinsa ɗauke da tausasa kalaman sallama. Sanye yake cikin wata shegiyar bugaggiyar shadda getzner kalar royal blue. Wando da riga harda babbar riga. Sai hular zanna daya murza itama royal blue data samu nutsatstsiyar saƙa. Hatta da agogon dake a tsintsiyar hannunsa kalar blue ne. Wanda bai saniba sai ya ɗauka wannan ɗin itace shigarsa dama can tun fil azal. yayi ƙyau harya gaji a cikin kayan. sun sake fidda masa kwarjini da cikar haiba da kamala. Farar fatarsa ta sake haskawa tamkar wata ɗan daren sha biyar. Yanda sajen fuskarsa da kwantaccen gashin kansa dake baƙi siɗik kwance a ƙeyarsa suke ɗaukar ido babu tababa zaka iya sakashi a jinsin larabawa. Idanba faɗa maka akaiba bazaka taɓa yarda Dr Yoohan ɗan gidan Papa da Madam Chioma ne ba wanda ko hausar bai gama fahimtar inda ta dosa ba balle akai ga larabci.
      A hankali ya cigaba da tako ƙafarsa dake sanye cikin baƙar safa cikin falon, dan ya cire takalman a ƙofa. 
         Tunda yay sallama  Ananah da Hajjo suka zuba masa idanu cike da jin daɗin isowarsa a kan lokacin da ya dace. Umm kam kallo ɗaya tai masa ta maida idanunta ƙasa tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Cikin girmamawa ya gaida su Hajjo. Suma sun amsa masa da kulawa harda ƴar tsokana. Kaɗan gefen bakinsa ya motsa alamar murmushi. Dan bayan gaisuwar baiji mi suka faɗa ba sam tunda da hausa sukai magana.
      Baba malam da ya tashi daga inda yake zaune ne ya nuna masa alamar ya zauna anan. Bai musaba ya zauna idanunsa akan Nu'aymah da har yanzu take riƙe da kanta. Sai da yay mata kusan kallon minti ɗaya da wasu sakanni sannan ya ɗago. Ɗan kallonsu yayi sai kuma ya sake maida idanun nasa kan Aymah.
      Da sauri Ananah tace, “Ɗan nan ko akwai matsala ne?”. Ya ɗanji wani abu daga zancen nata. Sai dai bai iya haɗasu a jimlace yanda zai fahimta ba. Hakanne ya sakashi kallon Ahmad dake ɗan murmushi. Faɗa masa abinda tace yayi, hakan yasa Yoohan cewa, “No babu damuwa Mama. Sai dai a ringa kula, indai zata ringa shiga irin wannan yanayin akwai matsala. Aikinmu zai dinga komawa baya”.
         “Yoni yaro bafa jin wannan yaren naku na masu jajayen kunne nake ba, kai Amadu fassara mana mi yake cewa”. Ananah ta faɗa da iya gaskiyarta.
      Gaba ɗaya su baba malam murmushi sukayi dajin zancen Ananah. Umm ma saita nufi ƙofar fita ita dai tana nata murmushin. Cike da ƴar tsokana Ahmad yace, “Gaskiya Abba kubani kwangilar maida Hajjo da Ananah makaranta, dolene su fara jin turanci kwanan nan”.
     Daƙuwa Abban Adawiya yay masa. Yayinda Hajjo ta talle masa ƙeya tana faɗin, “Kaci gidanku Ahmadu. Yo turancin banza turanci wofi. tunda munajin yaren da ALLAH yayimu a cikinsa muna kumajin yaren dayafi kowanne daraja, yaran MANZON ALLAH larabci ai mungama nasara. Kune kuka ɗauki amanar kanku kuka miƙama masu jan kunne shiyyasa gashinan kullum sai hanyoyin wajiga rayuwarmu suke ƙara ƙirƙirowa. Shima Yahaya ɗin kwanan nan dan gidansu sai ya fara iya hausar”.
      Duk da Yoohan bajin abinda ta faɗa yay ba, baisan sanda murmushi ya kufce masa ba ganin yanda take masifa akan Ahmad tana duddungure masa kai hularsa har tana matsawa baya. Su Baba malan kuwa sai zuba murmushi sukeyi. Sosai abin nasu sai ya birgesa, musamman daya tuna nasa kakannin da kullum babu abinda sukafi ƙwarewa sai masifa da faɗa kamar kajinaye.......
    Hannunsa da Nu'aymah ta riƙo ne ya sakashi saurin juyawa gareta. Cikin yanayin ciwo ta sake matse lallausan tafin hanun nasa cikin nata tare da ɗorasa bisa kanta, “Abbah ka riƙemin zai fashe”.
       A hankali Yoohan ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. Baiyi magana ba, bai kuma janye hannunsa data ɗora akanta ba ta danne da hannunta kuma.
       “Inaga mu bara mu barka kayi aikinka”. Ya tsinkayi maganar Abban Abdallah a cikin kunnensa. Janye idanunsa yay daga kallon da yakema Aymah, sai dai kafin ma ya ɗago su duk sun fice. Hajjo da Ananah da Ahmad kawai aka bari.
    Baice komaiba sai hannunsa da yay ƙoƙarin janyewa daga kanta. Amma sai ta sake riƙesa da ƙyau tana faɗin, “Abbah Please karka tafi ka barni, kaimin addu'a kaji Abbana”.
      Sosai tausayinta ya sake lulluɓe su Hajjo. Yoohan ya ɗan matsar da kansa kusa da nata kaɗan, a hankali yace, “Ki daina magana zan baki magani yanzu zai daina insha ALLAH”.
       Tabbas taji muryar ba Abbahn ta bane, amma halin da take ciki bai bata damar banbance wanene ɗinba sam.  
       Kallon Ahmad Yoohan yayi, yay masa nuni da box ɗin da suka shigo yana faɗin, “Brother Please ko zaka iya haɗamin allurar nan?”. “Yes! Doctor babu damuwa”. Ahmad ya bashi amsa yana jawo box ɗin.
      Wata irin zabura Nu'aymah da zancen ya shigarma kunne tayi, batare da sun fargaba suka ganta tsaye bisa ƙafafunta jikinta na rawa. “Bana son allura, Abbah! Abbah! banason allura...” ta faɗa a wahale tana riƙe kanta da hannu biyu duka tai baya luuuu zata zube.
        Cikin zafin nama Yoohan ya miƙe tsayen shima, hakan yasa Nu'aymah faɗawa jikinsa nata jikin na wani irin karkarwa. Saurin riƙota yayi shima yana faɗin, “Relax, Please calm dawn!” 
      Ina batama san yana faɗa ba, kanta kawai take jujjuyawa a ƙirjinsa da faɗin, “Banason allura, Abbah banaso”. 
       “Okay shike nan, kinga baza'ai mikiba, ya isa ki daina magana, tana sa miki ciwo kai”. Yay maganar da ɗaukarta gaba ɗayanta ya maida a kujerar zai kwantar. Sake ruƙunƙumesa tai, sautin muryarta na ƙara fita da ƙarfi wajen faɗin, “Abbah karka bari sumin allura dan ALLAH ” ta ƙare maganar da fashewa da kuka.
     Su dai su Hajjo duk wannan drama dake faruwa suna tsaye ne suna kallonsu, Ahmad dake murmushi yace, “Hajjo kumuje kawai mu barsa da ita, nasan zaiyi duk dabarar data dace yay mata insha ALLAH ”.
     Cike da gamsuwa suka amsa masa. Allurar ya matsa ya miƙama Yoohan da Aymah ta kanannaɗema jiki kamar mage ta samu katifar audiga. “Gashi, bara mu baka waje kai aikinka Doctor ”.
       Yoohan zaiyi magana Ahmad ya ajiye syringe ɗin da sauri yabi bayan su Hajjo da har sun fice abinsu............✍


Likita bokan turai😉😜.


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.




I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 43

............Ajiyar zuciya ya sauke a hankali jin yanda Aymah take sake tura kanta cikin ƙirjinsa. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akan dogon gashinta dake ta uban ƙamshi ga ƙyallin mai daya sha masha ALLAH. “Silly girl!” ya faɗa a hankali yana kai bakinsa dai-dai kunnenta. Batare da ya jira amsarta ba ya sake miƙewa da ita ɗauke a hannunsa. Zama ya farayi saman kujerar sannan ita kuma ta koma saman cinyarsa da ƙyau batare da tasan mi takeyi ba. Syringe ɗin da Ahmad ya ajiye ya ɗauka, ɗan guntun ruwan allurar dake ciki ya kalla, ya ɗan yamutsa fuska kaɗan da zare hular kansa ya ajiye gefe. Ya sake kallon Aymah ya girgiza kansa, cikin ƙwarewa da sanin makamar aiki ya kuma turata jikinsa da ƙyau tare da ranƙwafowa ya ɗaura bakinsa akan kunnenta. Wata irin sassanyar iska ya shiga hura mata cikin kunne a hankali, yayinda can kuma hannunsa ke saita inda zai mata allurar batare da ta saniba.
        A hankali ta saki wani irin nannauyan ajiyar zuciya da sake shigewa jikinsa, saboda ƙamshinsa na sake jan hankalinta. Hakane ya bashi dama tsira mata allurar dai-dai inda ya dace. Da masifar ƙarfi ta zabura tare da fasa ƙara ta sake damƙesa da ƙyau jikinta na wani irin karkarwa.
     Zare allurar yay yana sakin wani lallausan murmushi daya sake fidda annurin fuskarsa. “I am sorry”. ya faɗa a hankali cikin kunnen nata.

        Ihun Nu'aymah duk sai da ya shiga cikin kunnen su baba malam. Duk rumtse idanu sukayi tausayinta na tsargama zukatansu. Sai dai babu wanda yay yunƙurin shiga cikin falon.
       A ɓangaren Yoohan kuwa idanunsa ƙyam akan Aymah dake ta juyi a jikinsa tamkar wata macijiya, sai zufa dake ta faman tsatstsafo mata a goshi. Handkerchief ɗinsa fari ƙal ya fiddo cikin aljihun gaban rigarsa ya shiga share mata zufar, tsahon mintuna biyar suna a haka kafin ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere, a hankali kuma sai jikinta ya fara saki alamar barci. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Kwanciyar ya gyara mata a cinyarsa yanda zataji daɗi sosai, sai kuma ya kai hannu saman gashinta daya barbaje ya tattaresa cikin hannunsa. Ribbon ɗin ya ɗauka ya ɗaure mata shi a tsakkiya ya nannaɗesa da ƙyau yanda bazai takura mata ba. Baya yayi ya kwanta jikin kujerar shima, ya lumshe idanunsa da sakin sassanyar ajiyar zuciya.
        Shirun da su baba malam sukaji babu motsinsu har tsahon wasu mintuna ne ya saka Ahmad faɗin, “ALLAH yasa dai lafiya naji shiru”. Ɗan murmushi baba malam yayi, ya kalli Ahmad ɗin yana faɗin, “Ai tunda kaji mamana tabar kwakwazo na tabbatar anyi alluran”.
       Kusan a tare duk suka murmusa. Hajjo tace, “Raguwar amarya ba, sai tsiwa a baki amma cikinta fal tsoro, gashi kuma ta zama matar likita sai su ƙarata ai”. Yanzun kam duk dariya suka ɗanyi. Ananah tace, “Ai irinsu dama hakane, zakiga akwai tsiwa amma matsoratane a bugun farko. Ahmadu leƙa kagani”.
      Da to Ahmad ya amsa yana nufar falon. Sallama kusan uku yayi baiji an amsa masa ba. Hakane ya sakashi tura ƙofar a hankali ya shiga. Sai dai daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonsu. A take murmushinsa ya sake faɗaɗa.
       Buɗe idanu Yoohan yayi a hankali tare da ɗagowa zaune sosai yana kallon Ahmad ɗin. Sai kuma ya yunƙura ya ɗaga Aymah cak daga cinyarsa zai miƙe.
      Da sauri Ahmad yace, “No Doctor, kayi zamanka dama na leƙone kawai naga idan komai lafiya. To ashema har tayi barci”. Yoohan daya ƙarasa miƙewa baice komaiba, sai da ya shimfiɗe Nu'aymah a kujerar da ƙyau ya gyara mata kwanciya sannan ya ɗauki hularsa ya maida bisa kai yana bama Ahmad ɗin amsa. “Barrister wannan ƙanwar taka ta cika raki da ragwantaka, saboda allura kawai duk ta jigatani tamin Squeezing ɗin kaya”.
        Ƴar dariya Ahmad yayi yana ƙoƙarin tattare syringe ɗin da komai da sukai amfani dashi. Yace, “A'a Doctor karmuyi haka da kai. Ni na tabbatar maka sai kazo wataran ka sanarmin Aymah jarumace, ballema itama likita zata zama insha ALLAH ”.
      Idanu Yoohan yaɗan waro yana gyara zaman rigarsa, yace, “A hakanne zata zama likita tana tsoron allura tamkar bindiga ɗin? Tab za'aga likitoci kam”.
   
       Da haka suka fito Ahmad na dariyar zancen Yoohan, shiko Yoohan ya fiske abinsa tamkar ba shine yay maganar ba.
       Kusan duk a tare su Abbah ke tambayar jikin Nu'aymahn. Ahmad yace, “Ku kwantar da hankalinku ita harma ta tafi duniyar barci. Dama ihun na allura ne”.
     Duk kallon Yoohan sukai cike da farin ciki, suka shiga jera masa sannu da godiya. Shi dai kansa a ƙasa yake faɗin, “Uncle karku damu aikina ne ai. Insha ALLAH zata tashi kamarma komai bai faruba dan amfanin allurar kenan. Sai dai a dinga kula dan abu kaɗan ita yanzu zai iya birkita ta, ruɗanin kuma shine ba'a so dan zai maida cigaban da ake murnar samu bayane. komai a ringa mata shi da lallashi”.
      “Insha ALLAHU za'a kiyaye. ALLAH ya saka maka da alkairi, ita kuma ALLAH ya bata lafiya yasa kaffara ne”.
      A tare suka amsa da amin, harsu hajjo da Ahmad ya fassara musu abinda Yoohan ɗin ya faɗa.

         A cikin gida kuwa dai hidimar bikinsu suke tayi, babu wanda yasan abinda ke faruwa da Nu'aymah sai shaƙiƙan Umm da suke a bedroom ɗinta kawai. Suma kuma tunda Umm taje ta sanar musu likitan da zai duba Aymah yazo duk sai suka samu kwanciyar hankali.
       Bayan wucewar Yoohan duk suka shiga har falon baba malam suka ganta. Hakan ya ƙara musu nutsuwa sosai, dan haka suka dawo ɗakin Umm suka cigaba da hirarsu ta zuminci tare da tattaunawa akan auren na Aymah.
       Koda suka koma can baba malam da kansa ya ɗauki Nu'aymah dake barci hankali kwance ya maida bedroom ɗinsa. Sannan ya fito shi da ƴan uwansa suka fice massallaci gabatar da sallar magriba. 
       
         Biki yayi biki masha ALLAH, dan Addah ta samu alkairi sosai daga wajen abokan arziƙinta. Hakama sauran matan gidan bisa al'adar biki da kowa ya sani suma sun samu rabonsu ga abokan arziƙansu. Harma da Umm da kowa sai yanzu yasan harda gudan jininta. Ana idar da sallar isha'i kuma aka shiga shirya amare. Hajarah da Kubrah. Nu'aymah dai babu wanda yay magana maybe ba yau ba kenan. 
      Kamar yanda kowa ya sani baba malam shike raka duk ƴaƴansu gidan aure. Babu wani gayyar ƴan kai amarya. Duk wanda yake da buƙatar ganin ɗaki yakanje da rana bayan ɗaurin aure ko washe gari idan amarya ta kwana a gidanta. To gasu Hajarah ma tsarin bai canja ba. Dan ana idar da sallar isha'i su baba malam duk suka shigo gida. Sashen Hajjo aka kai amaren, Hajarah nata kuka kamar zata shiɗe. Kubrah kam idanunta ƙyar cikin lifayar da aka naɗa musu. Sai uban ƙamshi suke kamar gidan turare.
      Duka iyayensu da shaƙiƙan ƴan uwa suka taru a sashen Hajjo aka shiga musu nasiha. A yanzunma dai Hajarah kuka take, Kubrah kam kanta dai a ƙasa tana saurarensu. Bayan nasihar da akai musu da gargaɗi mai ratsa jiki akai musu doguwar addu'a da fatan alkairi sannan aka fito dasu. Da motoci uku kacal za'a kai amaren. Motar farko amaren ne a baya sai baba malam da Omar da zaiyi driving. Mota ta biyu iyayene mata na ɓangaren Addah su huɗu, sai yayun Umm biyu, su kuma Malam ƙarami ne zai jasu. Sai motar ƙarshe da Yah Ahmad zai ja ita kuma tsoffin iyaye ne dangin su baba malam a ciki su biyu, sai Umm da momy da amaryar Abba Musbahu. Motar ƙarshe, Abban Abdallah, Abba Musbahu, Abubakar da zai jasu, Uncle Kabeer mahaifin Nasir, sai Uncle Babangida shima dai shaƙiƙinsu ne. 
     Haka suka fita a jere ana bin amare da addu'ar tafiya a sa'a. Dama mafi yawan ƴan biki na kusa duk sunata guduwa suma. Zuwa goma na dare sai hayaniyar gidan ta ragu sosai, wasu sunyi barci, wasu sun tafi.
    

★★★

        Su baba malam sun fara miƙa Hajarah ne dan itace ƙarama. Gidanta mai ƙyau da tsari a anguwar GRA, kowa ya yaba da addu'ar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Sun sami tarba ta mutuntawa daga dangin ango su bakwai da sukazo tarbar amarya daga can gidan surukan Hajarah. Kasancewar sunsan dokar su baba malam ɗin suma cikinsu harda maza uku. Bayan sun ɗan zauna a falo akai addu'a baba malam ya kama hannun Hajarah har cikin Bedroom ɗinta ya kaita, zaunar da ita yay a bakin gado yay mata addu'a da saka mata albarka. Ya juyo zai tafi ta riƙe hanunsa. Tsayawa yay tare da juyawa jikinsa duk a sanyaye yana dubanta. Haka yake shi, yanada son yara, shiyyasa har ƴayan ƴan uwan nasa ƙaunarsu yake har cikin ɓargonsa. Duk kuma sanda yay irin wannan rakkiyar sai yayi ƙwalla dajin ɗacin rabuwa da yaran nasu ta dalilin aure ƙanin mutuwa.
     Hajarah data buɗe fuskarta ta share hawayen dake silalo mata. Cikin dasashshiyar muryarta tace, “Abbah dan ALLAH inason in roƙeka wani abu”. Kansa ya jinjina mata, yace, “Komi kikeso zan miki inhar baifi ƙarfina ba Hajarah, dan haka faɗamin koma miye kinji”. Sake share hawayenta tayi tana jinjina masa kai. “Abbah dan ALLAH idan yah Abdallah yace bazai maida aurensa da su Adawiya ba karku takura masa”. Jimmm baba malam yay yana kallonta. Sai kuma yace, “Uhm Hajarah miyasa kika buƙaci hakan? Bayan kinsan shi ɗin mai laifine”. “Abbah zan faɗa maka dalilina amma ba yanzu ba, dan ALLAH kuyi mani wannan alfarmar, suma su Abba zan kirasu duk na roƙesu har Hajjo”.
       Numfashi baba malam ya ɗan sauke, sai kuma yace, “Karki damu zan duba na gani, kibar kukan nan haka karya saki zazzaɓi. ALLAH ya baku zaman lafiya”.
    Daga haka ya fita ya barta tana cigaba da rabzar kukanta.
      Daga gidan Hajarah saina Kubrah. Itama dai gidan ya haɗu masha ALLAH. Sai dai ita tana da abokiyar zama harda yaranta uku. Amma kowa da sashensa dan gidan babbane. Itama dai an tarbesu da mutuntawa. Baba malam kuma ya rakata har nata ɗakin ya ƙara mata addu'a sannan ya fito suka wuce gida kowa aka barsa da halinsa kuma.

____________________

           A ɓangaren Yoohan kam tunda suka baro gidan su baba malam sai ya koma Hotel ɗin da su papa suka yada zango. Babu yanda baba malam baiyiba akan su sauka a ɗaya daga cikin gidajen baƙinsu amma papa ya ƙi fir. Wajen ɗaurin aurenma da yake jirgin 12 suka shigo suna isowa ana idar da sallar juma'a, hakan yasa saida ma aka ɗan jirasu kafin su iso wajen ɗaurin auren daga airport. Yoohan ne kawai yazo tun goma na safe. Bayan an ɗaura auren aka ɗunguma har dasu hall ɗin da su baba malam ɗin suka tanada domin gudanar da walimar cin abinci. Anan akaci aka sha cike da farin ciki. Babu wanda zai kalli baba malam da papa yace akwai wani abu na rashin jituwa a tsakaninsu. Suma su papan sun sake sosai a cikin mutane bazaka taɓa cewa ga daga addini ko ƙabilar da suka fito ba. Musamman ma daya kasance a cikin manyan mutanen ƴan ɗaurin aure akwai waɗanda suke da alaƙa dasu sosai musamman ma ƴan siyasa. Wasuma papan ya sake gayyatarsu bayan gayyatar da baba malam yay musu.
      Bayan an kammala walimar ne mafi yawan baƙin suka kama gabansu, su kuma su papa da tawagarsa suka nufi hotel bayan sunƙi amsa tayin baba malam. Hakan yasa yanzun acan Yoohan ya iskosu. Sai dai kasancewar jirgin ƙarfe bakwai da rabi zasu bi zuwa Abuja duk ya iskesu sun fito shi ma suke jira. Basu wani zauna zaman ɓata lokaci ba duk suka shiga motocinsu. zasu kaisu airport ɗinne su dawo su kwana da safe suma su ɗauki hanya. Dama da safe suka taho kafin su papan.
          Ko mintuna goma cikakku basuyi da zuwa airport ba jirginsu ya lula birnin tarayya abuja. Inda a canma dai ɗaukarsu akazo akayi. Abokan papa kowa ya nufi gidansa, papa da Gebrail, Richard, Joseph, Godwin, Osin, Uncle Marcel, Uncle Anthony, kuma suka nufi gidan papan. Sai Solomon jelar Yoohan😂.
     Sun iske gidan a hargitse da rikicin da suka bari su Mama Debora nayi akan auren Yoohan ɗin. Faɗa mai lasisi sosai akasha tsakanin tsofin biyu. Kuma duk akan sufa basu yarda jikansu ya aure bahaushiya mai salla ba. Momy da papa ya gama sanar mata komai akan manufar auren tanata ƙoƙarin fahimtar da su duk da kuwa jitake kamar tafi kowa shiga tashin hankali, amma sun ƙi fahimta. Sai kiran dangi suke na nesa a waya suna sanar musu. Miracle kam yanke jiki tayi ta faɗi a sume dama tunkan su Yoohan su wuce. Akace kuma ya dubata ya tsallake yay ficewarsa batare daya ko tanka musu ba.
    Hakan daya aikatane ya sake fusata kakanninsa sabon wutar bala'i ya ƙara ruruwa. Sai asibiti aka kai mira bayan wucewarsu ɗaurin auren.

        Tunda Yoohan ya shigo idonsa ya sauka akan kakannin nasa sai ya sake tsuke fuska fiye da yanda take. Ɗauke kansa yayi ya nufi upstairs duk da yaga yanda suka miƙe zumbur suna kallonsa cike da wutar masifa.
     Cikin yare, mama Debora ta shiga ƙwala masa uban kira kai kace gidan zata fasa. Ko waiwayensu baiyiba ya buɗe ƙofarsa ya shige bayan ya amshi babbar rigarsa a hannun Solomon dake biye da shi a tsorace. Ruf ya rufe ƙofar ya murza mata key yama barshi a ciki dan kar wani yay tunanin amfani da wani key ɗin.
       A falo ya zube yana sauke numfashi da jan dogon tsaki. Jin an fara buga ƙofar tasa da ƙarfi ana masifa ya kuma jan wani tsakin ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa. Bai zaunaba anan, kayansa dake ta zuba ƙamshinsa dana Nu'aymah ya cire yanata faman lumshe idanu. Dan a matuƙar gajiye yake. Babu abinda yake buƙata a yanzu sama da kwanciya. Ya gaji harma baisan tataya zai faɗa ba a tausaya masa. Ga ihun su Mama debora da yake jiyowa sama-sama yana neman saka masa ciwon kai. ‘Nasan maganinku ai. Kwanan nan zaku bar gidan nan ku koma inda kuka fito’. Ya faɗa a fili yana harar ƙofar kamar sune wajen tsaye.
       Daga haka ya shiga yay wankansa kamar yanda ya saba. Ya jima bai fitoba daga bayin kamar mai naƙuda🙄😏. Sai kuma gashi ya fito a yanayin gajiyar da yake ciki. Sama-sama yay shirin barci cikin tausasan kayan barci, yana fesa turare wayarsa tai ring. Kallon wayar yay, ganin Richard ne sai ya basar ya cigaba da hidimarsa. Sai da Rich ya sake kira bayan ta katse sannan ya ɗaga. A dakile yace, “Kana damuna fa”. A fusace daga can shima Richard yace, “An damekan, shine dan tsabar wulaƙanci ka wani kullema mutane ɗaki? Da ace babu wasu ɗakunan ina kake tunanin zamuje mu kwanta?”.
      “Oho muku” Ya faɗa a taƙaice da yare.
      “Zakace oho kuwa tunda mun gama maka wahala, mtsoww! Ka wani saka mutane zuwa cikin.....” Katse wayar Yoohan yayi batare da ya bari Richard ya ƙarasa ba. Ya taɓe bakinsa yana cilla wayar saman gado. Yanaji Rich ya sake kira bai kulaba. Sai da ya kammala shirinsa tsaf yay sallar magriba da isha'i da shafa'i da wutiri da addu'oinsa sannan ya mike ya haye gadon. Wayarsa daya cillar gefe ya ɗauka. Number baba malam ya lalubo yay dailing. Ring uku kuwa ya ɗaga. 
     Tamkar Yoohan yana gabansa haka ya risina cikin girmamawa yana gaishesa. Daga can kuwa baba malam na amsa masa da kulawa.
      “Abba mun iso babu jumawa. Ina fatan jikin nata babu wani matsala zuwa yanzun?”.
     Murmushi baba malam yayi da duban Nu'aymah da Umm ta gama canjama kaya zuwa na barci. Ya ɗauke kansa yana sauke numfashi. “Alhmdllh Yahya. ALLAH ya huta gajiya, ya kuma saka albarka. Dama yanzun nan muka gama waya da baban naka shima ya kira ya sanarmin isar taku. Mamana kuwa har yanzu barci ma take batako farkaba tun bayan allurar”.
       Sassanyan murmushi Yoohan yayi babu shiri, yace, “Alhmdllh Uncle, insha ALLAH zuwa da safe zata farka normal, ALLAH ya ƙara lafiya. Bara na barka ka kwanta sai da safe”.
     “To Yahya ALLAH ya huta gajiya”.

    Daga haka sukai sallama. Baya yay ya kwanta ƙafafunsa a ƙasa yay filo da hannayensa. Idanunsa ya lumshe a hankali ya faɗa duniyar tunanin da shi kaɗai yasan akan abinda yake yi.

__________★★★★_________

            *_To masu karatu sace shin ina Abdallah da Nasir😱🤗?._*

       Tam nima dai tsayawar wannan tambayar a raina ce taja ra'ayina shiga bulayin nemansu a cikin gidansu Nu'aymah. Sai dai na karaɗe ko ina da ina tsaf babusu babu mai kama da su ɗin. Sai acan bakin su Omar dana tsinkayi yana faɗama Momynsu yanda ɗaurin auren ya kasance naji.
         Ashe faɗan da Abdallah da Naser suka tafka ne a daren shekaran jiya daya bama kowa tsoro yajawo su baba malam canja shawara akan zaɓin Nu'aymah. Ananah da hajjo sukai dogon nazari da shawarar canja komai. Dan yanda abubuwan ke nan canja salo tabbas zumincinsu zai iya girgiza akan matsalar Naseer da Abdallah. Dan haka suka kira su baba malam a wannan daren tare da Abban Naseer daya iso suka tattauna. Abban Nasir shine ya bada shawarar hana Abdallah da Nasir gaba ɗaya. Ya kuma bada shawarar aurama Yoohan kamar yanda ya bukata dan a samu zaman lafiya. Hakan zai kawo masalahar Abdallah ya maida matansa. Nasir kuma yaje ya auri wata.
     Kowa yayi na'am da wannan tunani na Abban Naser. Babu ɓata lokaci ko jinkiri suka kira Yoohan suka sanar masa. Yoohan kuma bai ɓata lokaci ba wajen sanarma papa. Sai dai yayi matuƙar mamakin ganin yanda Papa ya bashi goyon baya babu wani ja inja ko ƙalubalantar lamarin, ya kuma gargaɗesa karya sanarma Momynsa (Madam Chioma😸) shi zai sanar mata.
       A wannan daren papa ya bada akai masa invitation na layin waya aka turama duk wanda yake da buƙatar gani a wajen ɗaurin auren ɗan nasa. Washe gari kuma ya ƙarasa dukan kai kawo da yake buƙata tare da bincikar duk yanda al'adar auren hausawa yake. Duk abinda ake buƙata sai da papa ya saya aka shiryasu a mota.

     Anan kuwa kano su Abdallah basusan wace wainar ake toyawa ba. Kowannensu dai ya ɗauki alwashi akan ɗan uwansa tsakanin shi da Nasir. Hakan yasa sukaje ɗaurin auren kamar kowa cikin kwalliya ta musamman. Sai dai kuma ganin Yoohan da tawagar ƴan uwansa da abokai ya basu matuƙar mamaki. Gashi waje ya ƙure balle su tambayi iyayen nasu. Basu fita daga ruɗanin ganin Yoohan ba aka fara ɗaurin auren. An fara ɗaura na Kubrah da angonta Al-ameen yuseef durɓi, sai Hajarah da angonta Dawood Sulaiman Rano. Naseer na jiran yaji shi da Nu'aymah sai yaji Zainab Sooraj Hashim jibiya da Yahya Goshpower”.
     Turƙashi zance ya girma. Ba Nasir kawaiba ne a ruɗani, Abdallah kansa hajijiya yaji tana ɗibarsa. Hakan yasa Omar dake kusa da shi ya taimaka masa suka fito daga cikin hayaniyar ya kaisa mota. Shima acan Nasir sai Ahmad ne ya kamashi ya fito da shi. Sun koma sanarma su baba malam, Abdallah ya tada motar da Omar ya sakashi ciki ya bar wajen batare da kowa ya sani ba. Nasir kam da ƙafa ya bar wajen shima a birkice.
       Daga wannan tafiyar ne har yanzu babu wanda yasan ina suke. Su baba malam sunyi neman a waya harsun gaji. Dan duk wayoyinsu a kashe suke. Halin da suka ahigo suka iske Nu'aymah a gidane ya sakasu yin shiru da zancen rashin su Abdallah ga kowa. Duk da kuwa Hajjo nata tambayarsu bataga Abdallah da Nasir ba.

WASHE GARI..........✍



ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 44


*_IDAN kaji ƙi gudu sai in sa gudu bai shigo wajen ba. Ƴan uwa abokan tafiya, gafa magani A GONAR YARO. domin tabbas idan kaji gangami akwai labari_*.

*_Ina masu wahala kullum cikin neman maganin sanyi (imfection) amma babu biyan buƙata. Kinyi na asibiti har kin gaji babu canji, na gargajiyarma taɓawa kike babu wani ƙyaƙyƙyawan sakamakon. Tofa kakarku ta yanke saƙa. Domin kuwa ga dama a tafin hannunku. Munada maganin NI'IMA, maganin GYARAN HIPS (mai gida bye bye😉). Muna da maganin BOOBS (mai gida welcome🙈). Maganin BASIR mai hana sakewar zama. Duk ku garzayo domin samunsu akan farashi mai sauƙi da rahusa, ga kuma inganci domin an samosu ne daga tsaftatacciyar hanya mai nagarta._*👇🏻

*AISHA S BAYERO TRADITIONAL MEDICINE AND HERBAL RESEARCH CENTER...*

_KUNJI SUNAN KO? CENTER CE TA MAGUNGUNAN GARGAJIA, WANDA DUK WANI DAMUWA DAKE DAMUNKA IDAN HAR KAZO WAJEN S BAYERO TA KARE DA YARDAR ALLAH.. KADAN DAGA MAGUNGUNANTA SUN KUNSHI:_

_MAGANIN SANYI_
_MAGANIN NI'IMA SET_
_MAGANIN NANKARWA_
_MAGANIN KIBA BABBA DA KARAMI_
_MAGANIN HIPS_
_MAGANIN GYARAN NONO_
_MAGANIN RAGE KIBA_
_MAGANIN SAKA FEELING_
_MAGANIN CIDA KWAI_
_ZUMA YAR ASALI_
_MAGANIN BASIR KOWANNE IRI_
_HODAR NI’IMA_
_MAGANIN MALLAKA_
_GUMBAR NONON RAK’UMI_
_GUMBAR MADARA_
_TURAREN FARIN JINI_
_KAZA MARA KWAI_
_TURAREN MALLAKA 3 STEP_
_HAD’IN MATAR MINISTER 1_
_KAZA ME KWAI_

_STEP 2:_

_TURAREN MALLAKA ME KWALBA_
_ME KUNAMA DAN MATSI_
_TURAREN GOSHI_
_TURAREN QIRJI_
_TAUWADAR MATA_
_MEMORY_
_KAHON MALLAKA_
_YAJIN MAZA_
_TEA  DIN MAZA_
_DAMBUN MATSI_
_MAN AYU_
_MAN DAMO PURE_
_KWALLIN IDONKA IDONA_
_GARIN SHA DAKA ME KYAU_
_KUBEWAR MATA_

_DUKA WADANNAN INGATTUN MAGUNGUNA NA GARGAJIYA HAJ AISHA NA DASU GANGARIYA.. HERBAL MAGUNGUNA NE MASU KYAU DA INGANCI.. TAFIYAYYU NA KASAR CHAD. CHADIAN HERBAL MEDICINE AND RESEARCH CENTER.. KYAU, INGANCI.. RAHUSA... SAI MAGUNGUNAN *AISHA S BAYERO TRADITIONAL MED AND HERBAL RESEARCH CENTER....*_

_NUMBER WAYAR WHATSAPP: 08121491609 KO KIRA TA NUMBER 08145873617._

_ADIRESHI: KUNTAU KARSHEN KWALTA KAN A KARASA YAN TIFA, DAIyDAI GADON KAYA CEMENT.._


Sai kunzo😘😘🤝🏻
_________________________


No. 44

..........WASHE GARI normal Nu'aymah ta tashi kamar yanda kowa yay fata. Sai dai rashin ƙarfin jiki da damuwar maganar auren da ta sake tabbatar an ɗaura mata shi. Dan bayan baba malam ya dawo daga massallaci zaunar da ita yay ya ringa mata nasiha mai ratsa jiki da ɓargo. Tun tana hawayen zuci, harta koma na zahiri. Hawaye suka dinga kwarara mata daga ido suna sauka saman fuska.
       Fuskar baba malam ɗauke da murmushi ya kai hannu ya share mata hayen. Ya kamo hannayenta duka cikin nashi yana sake kwantar mata da hankali. “Kukan ya isa haka kinji mamana. Duk abinda kikaga ya shigo cikin rayuwarki saɓanin tunaninki ki ɗauka hakan shine mafi alkairi a gareki. Idan kuma har kika rasa abinda ke shine burinki da fatanki, ki saka a ranki UBANGIJI bai baki shi bane saboda ba naki bane, hanakin kuma shine yafi alkairi. Akwai abubuwa da yawa dana san suna damunki a cikin rai. Amma inason ki ɗaukesu ki watsar da su acan nesa, ki kuma manta da su ki shafe babinsu a tunaninki. Dan jiyanki ta wuce, kina cikin yau ɗinki ne. Kinga yafi kamata ki maida hankali wajen hangen gobenki. ALLAH yay miki albarka. Ya yaye miki damuwarki. Ya share hawayenki. Yay riƙo da hannunki. Yay miki jagora a gobenki da jibinki”.
       “Amin Abbah na gode, ALLAH ya ƙara maka lafiya da tsahon rai”.
     “Amin mamana nima na gode. Kije ki kwanta ki sake hutawa kinji. Sai dai ki zama cikin shiri dan zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu kema za a miƙaki gidan mijinki”.
      Kanta kawai ta ɗaga masa. kamar zata tambayesa waye mijin nata sai kuma tayi shiru. Ɗago idanunta dake jajur tai ta kallesa. Muryarta na rawa tace, “Abba dan ALLAH ka yafemin dukan abinda kake ganin na maka a sanina ko saɓanin haka. Sannan wlhy kaji na rantse ban aikata abinda likitocin nan suka tabbatar ba. Abinda ke a cikin hotunan nan kuma ya farune bisa ƙaddara........”
    Duk abinda ya faru a waɗan nan ranakun biyu sai da Nu'aymah ta sanarma baba malam. hatta da farkon haɗuwarta da Yoohan. Sosai baba malam ya gamsu da dukan bayaninta. Dan duk abinda Yoohan ya faɗa shine ta maimaita. Inda sukai saɓani kawai shine ita tana ganin da gangan ya aikata mata. Shi kuma ya sanar dasu baba malam duk akan taimakonta zata faɗi komai ya faru. Ya san Nu'aymah tun tana yarinyarta da wahala kaji tamaka ƙarya akan abu. Koda kuwa za'a daketa idan tai laifi aka tambayeta saita faɗa.
       “Na yarda da ke Mamana. Insha ALLAHU kuma zamu ƙara sanin gaskiyar daga ina zancen ya fito. Dan wasu kalaman mijinki akan maganarnan suna nan tsaye bisa ƙwalwata ina musu fashin baƙi a hankali. Kuma lallai da gaske na fara ganin haske a ciki”.
       “Abba na gode daka fahimceni”. Ta faɗa tana kuka da dariya lokaci ɗaya. Shima Murmushin ya keyi cike da tausayinta. Daga haka suka fara cin abincin da Umm ta shirya masa na breakfast shi da ita. Tana bashi a baki shima yana bata abin sha'awa.
      Janyewa inuwar dake jikin windown tayi, baba malam da sai yanzu ya farga yay tsai yana kallon jikin Window ɗin cike da mamaki da al'ajabi. Sai dai kuma a zahiri ya maida hankalinsa ga Aymah ne. Daga can wani gefe na zuciyarsa yace, ‘Taya zakai zargin an muku laɓe ne bayan gidan cike yake da baƙi. Maybe wanine ke wani abu a wajen dai’. Ɗari bisa ɗari ya gamsu da hakan har cikin ransa. dan haka ya sake maida hankalinsa ga ɗiyarsa da tausayinta ke cike taf da ransa.

        Bayan baba malam ya shirya ya fita Nu'aymah ta koma sashen Umm. Ƙannen Umm ɗin da yayunta duk suna nan. Breakfast ma sukeyi. Sai wasu daga ƴan uwan Adda da suma anan suka kwana. Cike da jin daɗin ganinta ras duk suke kallonta. Ta risini ta gaidasu. Daga haka ta fito sashen hajjo. Nanma sunyi farin cikin ganin ta tashi lafiya kamar ba ita ba. Gaishe da baƙin dake a sashen tayi sannan ta shige bedroom ɗin hajjo. Acan tai wankanta tsaf, Yusrah data shigo taje ta amso mata kaya. Bayan ta shirya tare da Yusrahn suka fito. Hakan yayi dai-dai da shigowar Adawiya falon hannunta ɗauke da bokiti ruwan goro.
        Tunda sukazo ƙasar wannan shine gani na uku da Aymah tai mata. Adawiyan duk ta rame, tayi duhu kamar ba itace sukazo tayi ɗam da ita kamar zata fashe ba dan ƙyau. Ɗauke kanta tayi tamkar bataga Aymah da Yusrah ɗinba. Ta ƙarasa gaban Ananah ta ajiye bokitin tana faɗin, “Ananah gashi inji Addah na ƴan katsina ne da zasu wuce yau”.
      “To. To masha ALLAH, ALLAH ya sanya alkairi yasa albarka. Kice mata angode ALLAH yayi albarka”.
    “Amin” ta faɗa tana ƙoƙarin gitta su Nu'aymah zata fice. Murmushi Aymah tayi, tare da cewa, “Adawiya an tashi lafiya?”. Da mamaki Adawiya ta juyo ta kalli Nu'aymah. Kamar bazata amsaba sai kuma tace, “Alhmdllh”. Daga haka ta fice abinta.
     Yusrah tace, “Humm ALLAH ya ƙyauta. Wlhy lamarin Adawiya har mamaki yake bani Aymah. Ita yanzu dai abinda take nunawa ta raba zuminci damu. Nifa tunda sukazo ƙasarnan batamin magana. Idan na mata kuma saita amsani kamar wata kashi. Koda yake kema da kuka shaƙu da ita fiye da kowa tana ɗaga miki hanci bare mu”.
      Murmushi kawai Aymah tayi, amma batace komaiba. Daga Ananah har hajjo duk suna jinsu suma. Amma sai sukai kamar basujinba. 

      An ƙarasa gudanar da shagalin biki yau. Zuwa bayan azhar sukaje gidan amare akai buɗan kai. duk baƙi masu tafiya daga can suka kama gabansu. Sai ɗai ɗai kune suka dawo nan gidan waɗanda su sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Nu'aymah dai tana gida bataje ko inaba. Cikin ranta kam fal damuwa dason sanin wanene ita aka ɗaura mata aure da shi?. Anya kuwa Naser ne datai fata? A ganinta idan shine yaci ace ta gansa ai. Amma tunda ta tashi daga Naseer har Abdallah bataga kowa ba a cikinsu. Kuma duk sauran samarin gidan ta gansu.

_________★★★★_________ 

    *_FCT ABUJA_*

            A birnin tarayya kam taƙaddama ake bugawa sosai tsakanin Yoohan da kakanninsa. Harma da wasu a cikin ƴan uwansa da suke nuna borensu akan auro Nu'aymah da yayi. Hayaniyarsu da haukarsu duk bata damesa ba. Yamayi kunnen uwar shegu da su tamkar baiji akan mi sukeyi ba. Babban tashin hankalinsa da damuwarsa kawai halin da Momynsa ke a ciki.
     Dan tun daren jiya jininta ya hau sama sosai saida ya danna mata allurar barci, har kuma yanzun bata farka ba saboda mai ƙarfi sosai yay mata. Su Richard ne kawai da suma suka so tasashi gaba da magana akan auren yay azamar taka musu burki. Dukansu sunsan halinsa, idan rashin mutuncinne da buyagi duk ya fisu iyawa. Sannan suma ɗin kowanne allazi da nasa amanu ai. Kuma babu wanda sirrinsa ba'a tafin hanunsa yake ba. Haƙuri suka bashi akan masa katsalandan ɗin da sukayi. Suka kuma nuna masa zasu basa goyen baya tunda yana son matarsa.
    Uffan baice da su ba daga haka. Su kuma duk suka tashi suka fice suka barsa. Fita sukai daga gidan duka, sai da sukasha gulmarsu iya iyawa a waje kafin su tattauna akan shagalin biki da suke son shirya masa tunda auren nasa yazo musu da salo na daban ba irin nasu ba.

        A cikin gida ma bayan su mama Debora sun turza sun turza akan Yoohan ɗin sunga babu mafita sai suka sakko dan kansu akan zasu amince da auren, sai dai da sharaɗin duk sun dawo da zama gidan papa. dolene kuma Nu'aymah ta zauna itama a gidan Yoohan bazai kaita ko ina ba.
        Sai dai a mamakinsu sai sukaga Yoohan yayi murmushi tare da lumshe idanunsa ya buɗe a kansu. Sai da yay musu kallon tsaf na wasu mintuna kafin ya miƙe cike da basarwa yace, “Na amince”. A ransa kuwa dariya ya tafi yana musu, dan yasan indai nu'aymah ce sun sami dai-dai dasu.
     Kusan duk a tare sukai wata irin zabura. Dan sam sun zata zaice bai yardaba su kuma su sake tada wani billin. Sai gashi sunga saɓanin tunaninsu. Kafin su gama dawowa hayyacinsu ya dawo falon ɗauke da takarda.  A tebirin dake tsakkiyar falon ya ajiyeta. Ya bisu da kallo fuska a murtuke yana faɗin, “Wannan takarda ce ta agreement tsakanina da ku. Zaku cigaba da zama a gidan nan, matata ma zata zauna. Sai dai da sharaɗin duk randa na kama wani da laifin mata koda maganar banza a cikinku ko cikin yaranku sai mutum yabar gidan nan koda ace kuwa cikin su Gebrail ne. Itama kuma na muku alƙawarin bazata shiga rayuwarku ba bayan mutuntawa da girmamaku”.
        Cike da wani mamakin suke kallonsa. Zasuyi magana papa yay saurin faɗin, “Wannan tsarin na John yayi dai-dai. Dan shine zai kawo mana masalaha da kwanciyar hankali a zuri'ar mu. Mukuma sake tabbatar da kowannenmu nada ƴancin aikata abinda bai saɓamana ba”.
      Babu wanda ya iya sake cewa komai. Sai singing ɗin da Yoohan ya fara yi ya basu suma duk sukayi. Ɗaya ya ɗauka ya basu ɗaya. Ɗayan copy ɗin kuma da aka saka cikin frame ya nufi bangon falon daga kusurwar d/table ya kafesa jikin ginshiƙin wajen daya zama kwalliya.
     Wannan abu da Yoohan ɗin yayi ya kuma girgiza su matuƙa. Gashi babu damar magana dan ya tsuke fuskar fiye da ɗazun.

     Wannan takardar Agreement itace ta zama makullun rufe bakin duk wanda keda ƙarfin faɗa a ji a family ɗin su Yoohan. Sai ma zaman shirya biki sukai dan nuna bajintarsu ga gudan jininsu tamkar yanda akema kowa.
       Shi dai Yoohan bai tanka kowa a cikinsu ba akan shirin bikin, ranarma yini yayi a asibiti shi da Richard. Basu dawo ba sai dare. Gajiyar da sukayi ce ta sakasu ko zaman hira basuyi ba Yoohan ya shige sashensa. yau ma tsabar wulaƙanci hana su Rich shiga yayi. da sukai magana yace shi yanzu yayi aure baya buƙatar su a sashensa. Suje can su ƙarata a sashen baƙi suyita loda kwalaben barasarsu.
      Aiko sun hayayyaƙo masa tamkar zasu cinyesa. Ya fice yana murmushi bayan ya musu gwalo.

______★★★_______

       *_KANO_*

  A kano kam tunda garin ALLAH ya waye yau da shirye-shiryen tahowar su Nu'aymah aka tashi. Dan zasu taho abuja gidan su Abdallah. washe gari sai a miƙata ɗakin mijinta daga nan gidan. Saboda ma baba malam baya buƙatar ayi wata gayya jirgi zasu biyo.
        Jin abuja zasu wuto yasa Nu'aymah fara tunanin ko dai yah Ab aka ɗaura mata aure da shi? Ko burinsu na mallakar juna ya tabbata ne? To amma idan har hakane mizaisa a ringa ɓoye mata?. Har yanzu babu wanda ya sanar mata wanene mijinta. sai dai kowa na zaunar da ita yay mata nasiha dai-dai gwargwadon saninsa. Haka ne yasa yau taci kuka harta godema UBANGIJI. Mai ƙunshi ma da Addah tasa aka kawo da ƙyar Aymah ta yarda akai mata. Hakama da za'a kaita gyaran jiki sai da baba malan ya saka baki wajen lallashinta sannan ta amince. Ai ko sai gata tayi ɗas tamkar ka saceta ga gudu. ƴar ramar da tayi saita sake ƙara fiddo mata da ƙyawunta da haskenta. Sai dai a kallo ɗaya kaɗai ya isa ka tausaya mata duk tayo laushi kamar ba Nu'aymah tsiwa ba. Duk ta zama shiru-shiru, ta kuma nanema Umm taƙi barinta sukuni.
       Lokacin da aka idar da sallar la'asar Ananah tazo har sashensu tajata dan taje a kimtsata tunda jirgin 5:30pm zasu bi saita saka musu sabon rikici. Babu wanda bai lallasheta ba amma taƙi tai shiru. Sai da baba malam ya fito yay mata jan ido da nuna mata ɓacin ransa sannan. Aiko tana kuka tana sharɓar hawaye. Koda ta fito ma sai Aunty Kulu yayar Naser ce tai mata kwalliya ka ɗan dukda kuwa ba wai gidan su Yoohan ɗin zata sauka kai tsaye ba.
     Tsaf ta sakata ta shirya cikin atamfa lass ƴar ubansu, ɗinkin zani da riga. Kasancewar atamfar baƙa ce da kwalliyar golden sai tai bala'in zama mata a jiki tamkar ka saceta ka gudu.
            Iyayenta sun sake taruwa a kanta sun mata nasiha da gargaɗi mai faɗi akan rayuwar da zata fuskanta ta aure mai cike da ƙalubale. Dan aure ibadane. Ita kuma ibada a koda yaushe tana a cike ne da jarabawa kala-kala. Daga haka aka miƙata wajen Umm tai mata sallama. Ba Umm da Nu'aymah kawaiba, hatta duk wanda ke a wajen sai da ya matse hawayen tausayinsu. Da ƙyar aka ɓanbare Aymah jikin Umm. Hakama Muhammad dake taya yayar tasa kuka abin tausayi. Daga haka aka kaita kowane sashe tai musu sallama sannan aka shiga da ita ɗaya daga cikin motocin da zasu musu takkiya zuwa airport. Abban Abdallah da duka yaransa duk sun fito dansu daga haka zasu koma kenan sai kuma anyi hutun makaranta. Sai matan Abba Musbahu duka biyu da zasu mata rakkiya. Sai Ananah da Aunty Kulu. Aunty Aysha, Sai ƙanen Umm biyu da yayarta ɗaya. Sai Yusrah da Adawiya da taso tirjewa bazataje ba. Sai da Hajjo ta zageta tas sama da ƙasa sannan ta yarda da binsu badan taso ba. Sai Nanah, da Rufaidah autar su Naser.

      Tunda motocin suka ɗauki hanyar airport Aymah ta kwantar da kanta jikin Aunty Hibbah ta cigaba da raira kukanta a hankali. Aunty Hibbah dai nata shafa bayanta cike da lallashi amma batace uffanba.
     Basu wani ɓata lokaci ba a airport ɗin jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja. Tafiyar mintuna ƙalilan kuwa ta kaisu. Anan ɗinma dai tarbarsu akazo akayi, daga gani dai daga company ɗinsu ne masu tarbar. Zuwa yanzun jikin Nu'aymah yayi zafi zau da zazzaɓi, hakan yasa suna isa Momy ta kama hanunta zuwa ɗakinta, sai da ta sakata tai sallar magriba da aketayi lokacin da suke shigowa gida, tana idarwa ta haye gado ta kwanta Momy ta lulluɓa mata bargo saboda rawar sanyin da taketa faman yi.
         Ganin yanda rawar sanyin nata ke ƙaruwa Momy taje ta sanarma Abban su Abdallah dake shirin fita massallaci sallar isha'i. Biyota yay suka dawo ɗakin tare. Shima sai hankalinsa ya tashi jin yanda jikin Aymah yay masifar zafi. Ga rawar sanyin na ƙaruwa harma tana roƙon a ƙara mata wani bargon.
       “Khadijah inaga bara na dawo masallaci sai a kira Yahya zaifi, dan yayi gargaɗin bata magani kai tsaye. Nasan yanzu kuma a duk inda yake yana ƙoƙarin yin sallar isha'i ne tunda kiji gashi can za'a tayar”.
       “Eh gaskiya, hakan zaifi Abbansu. Bara nayi sallar nima kafin ku shigo”. 

     Bayan an idar da sallar isha'i Abba ya shigo gida. Kai tsaye waya ya ɗauka yay kiran Yoohan. Sai dai harta katse bai ɗaga ba. Ya sake kira nanma bai ɗaga ba. Ajiye wayar yayi yana faɗin, “Maybe baya kusa. Amma idan ya gani nasan zai kira”. Kai Momy ta jinjina masa kawai.
       
       A lokacin da Abbah ke kiran wayar Yoohan yana massallaci, wayar kuma na mota, dan suna wani hotel tun kafin magriba shi da su Joseph akan dinner ɗin da za'a gudanar gobe idan ALLAH ya kaimu bayan kawo amarya. koda ya fito kuma wajen nasu ya koma dan dama yace musu ne kawai yana zuwa, sukuma tsare-tsaren da sukeyi ya ɗauke hankalinsu basubi ta kansa ba akan inda zaije ɗin.
      Kujerar daya tashi ya ja ya zauna yana harar Osin da aka ajiyema kwalbar giya da yayi oda. Bai dai ce komaiba, sai Osin ɗinne yay murmushi yana faɗin, “Duk iya hararka dai ba ƙinsha zan ba. Kaima koda ɗura gobe sai ka shata domin farin ciki, koba komai kaji daɗin cin soyayyarka da amryarka”. Dariya suka kwashe da ita gaba ɗaya. Richard yace, “No, bazai shaba a wajen dinner sai ya koma gida, so kake y......” bammm kakeji Yoohan ya dokema Rich baki da bayan hannu kafin ya karasa faɗa. Aiko mizasuyi inba dariya ba. Tsabar mugunta Godwin har faɗuwa yake ƙasan korayen ciyayin da akaima wajen shimfiɗa da su. Richard daya ɓata fuska yace, “Mr X da zafi fa”. “So..” Yoohan ya faɗa a wani salo yana ɗage kafaɗa. 
        “Aiko na rantse sai kaji a jikinka yau” Rich ya faɗa yana rarumo kwalbar giyar da Osin bai kai ga buɗewa ba. Da gudu Yoohan ya tashi yana dariya shima saboda yasan mi Richard ke shirin aikata masa. (a karan farko dana taɓa ganin dariyarsa mai faɗi irin haka). Suma gaba ɗaya dariyar sukeyi, dan Rich bin Yoohan ɗin yayi shima da gudu. Mota Yoohan ya buɗe ya shige ya saka lock yana yima Rich dake ƙoƙarin ganin ƙofar ta buɗe daƙƙuwa. Da ɗan ƙarfi yace, “Stupid boy”. “Same to you”. Shima Rich ya faɗa yana masa daƙƙuwar.
     Gwalo Yoohan ya sake masa yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake haske. Da mamaki yake kallon sunan wanda yay kiransa har 3missed call. Bai kula Rich dake masa knocking glass ba ya shiga ƙoƙarin dailing Number Abban Abdallah.
      Bugu biyu kuwa ya ɗaga. Kamar yanda yake gaida baba malam da girmamawa haka ya gaida Abbah. Shima Abba sai ya amsa da kulawa, sannan yayma Yoohan ɗin bayanin abinda ke faruwa. Ɗan lumshe idanunsa yayi ya buɗe a hankali tare da kwanciya jikin kujera. “Uncle bara nazo na dubata kawai”.
     Cikin jin daɗi Abba yace, “To shikenan ALLAH ya kawoka lafiya. Ai kana da address ɗin gidan ko?”.
      “Eh Uncle inada”.
Daga haka suka yanke wayar. Glass ɗin motar ya sauke yana kallon Rich da ke jiransa ya kammala wayar. Da ƴar damuwa yace, “Sorry Rich ina zuwa, bazan jimaba insha ALLAH ku cigaba kawai”.
        Richard yace, “Lafiya dai ko?”.
  “No, babu damuwa dear, wani ɗan uzirine idan na dawo zan maka bayani”.
        “Ban yardaba gaskiya muje tare kawai”. Richard ya faɗa yana buɗe motar ya shigo shima.
    Yoohan ɗin baice da shi komaiba, sai waya daya ɗauka yay kiran Godwin, yana ɗagawa yace, “G-boy muna zuwa Please, just 30minutes”. “Okay no prob..” ya amsa masa da salon iya shege na gayu.
      Motar ya tada suka fice daga hotel ɗin. Yanda yake driving ɗin a hankaline ya sa Rich faɗin, “X-man are you ok?”. Ɗan murmushi Yoohan yayi kawai bai ce komaiba.

        Tafiyar mintuna ƙalilance ta kawosu gidan. Sun iske Omar tsaye a bakin gate da alama zuwan nasu yake jira. har ciki Yoohan ya shiga da motar. Da ga shi har Rich bin gidan suke da kallo dan kuwa ya haɗu. A ransa kuwa ayyanawa yake lallai su baba malam sunada ƙuɗi. Sai dai sun iya takunsu dan basu da fariyya akan ni'imar da ALLAH ya basu.
        Ƙofar da zata sadasu da cikin gidan suka nufa. Omar na gaba suna biye da shi, shi dai Rich ransa fal mamaki dan baisan ina suka zo ba. Su Aunty Hibbah na baje a falo zasuci abincin da Omar ɗin ya fita yayo musu takeaway suka shiga da sallama.  Cikin girmamawa Yoohan da yay musu kallo ɗaya yay ƙasa da kansa ya shiga gaishesu. Hakan yasa shima Richard da ke binsu da kallon tsaf ya gaida su. Daga haka suka wuce falon Abba dake zaman jiransu.

       Aunty Aysha ce tai ƴar dariya bayan shigewar su Yoohan. Duk kallonta sukai na alamar tambaya. Tace, “Wannan angon namu dai akwai kunya, abokinsa yay mana ƙuri da idanu, amma shi ya kasa kallon ko sashen da muke”. Aunty hibbah ta karɓe da cewa. “Sai kace jinin hausawa, inma ba faɗa maka akaiba bazaka taɓa cewa ba bahaushe bane wlhy. Musamman wanda yasan yanda ƙabilun nan suke da shegen tsaurin ido”.
      Haka suka cigaba da hirarsu ƙasa-ƙasa akan Yoohan. Har Umm tazo ta wuce ta fito da Aymah zuwa falon Abbah basu lura ba. Adawiya ce kawai da Amal babu a falon. Adawiya dai ƙin fitowa tai, tunda suka iso gidan ta shige ɗakin Amal bata sake leƙo waje ba. Amal kuwa kanta ke ciwo shiyyasa tasha magani ta kwanta tana idar da sallar isha'i.

         Tunda Momy dake riƙe da Aymah data langaɓe mata a jiki tai sallama duk suka ɗago kansu. A hankali Richard ya furta ‘Woow kaga wata ƙyaƙyƙyawar halitta’. Akan laɓɓansa ba tare da kowa ya jisa ba. Dan Yoohan ma dake kusa da shi zaune hankalinsa gaba ɗaya akan Aymah data takure cikin kujerar da Momy ta ajiyeta ya ke. Cikin rawar sanyi tace, “Momy Please ki bani bargo sanyi”.
     Kafin Momy tai magana Abba dake kallonta da tausayawa ya duba Omar da shima duk yay wani iri da tausayin ƙanwar tasa. “Omar kaga rage gudun ac nan”. Da sauri yace, “To Abba” yana ɗaukar remote ɗin.
     Murya ƙasa-ƙasa Rich ya cema Yoohan, “X-man who is she?”.
     Fuska Yoohan ya ɗan tsuke tare da ɗauke kansa batare da ya bama Rich amsa ba, saima maida hankalinsa yayi ga Abba da ke faɗin ga Nu'aymah ɗin nan. Yana gama faɗa ya bar falon Momy biye da shi. Har Omar ya juya zai fita shima Yoohan yace, “Excuse me Fharook”.  Dawowa Omar yayi fuska ɗauke da murmushi yace, “Yayah kana buƙatar wani abu ne?”.
       Ɗan murmushin kaɗan shima Yoohan yayi, yace, “Kaɗan samo mata tea tasha first”.
     Kai Omar ya gyaɗa ya fita.
Yana fita Rich ya bugi kafaɗar Yoohan da yare yace. “Kaifa banza ne! Ina tambayarka kana basar dani. Ina ka kawomu nan, gidan ƙyawawan mutane wai?!”.
     Dariya yaba Yoohan, amma sai ya gimtse bai yiba. Da gatse yace, “Gidan kidnappers ne” tare da zuba masa harara. Hakan yayi dai-dai da dawowar Omar falon ɗauke da ƙaramin tire an ɗoro mug dake ta turiri.............✍



ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.



I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.



No. 45

............Hararsa shima Richard ɗin yayi, amma sai Yoohan ya watsar da shi ya miƙe yana nufar kujerar da Aymah ke kwance a kai. Omar dake murmushi ya ƙarasa inda suke ya ajiye tiren a copy table ɗin dake gefen kujerar. Hakanne ya saka Yoohan dake tsaye yana kallon yanda take rawar sanyi zama kan hannun kujerar kaɗan shi kuma.
      “Thanks you” ya faɗa a hankali yana kallon Omar. Murmushi kawai Omar yayi shi dai. 
      Da hannu Rich ya yafito Omar, hakanne ya sakashi nufarsa. Tambayarsa yay wacece Aymah? Dan shi harga ALLAH ya gama rikicewa. Cikin ƴar dariya Omar ya faɗa masa amaryarsu ce mana.
       Sosai kuwa Rich ya waro idanu waje yana faɗin, “Are you serious?”. kai Omar ya gyaɗa masa alamar sake tabbatarwa.
       
       Shi dai Yoohan na jinsu, amma sai bai ko waiwaye ya dubesu ba, sai ma hannu da ya kai a hankali ya janye bargon Abba da Momy ta ɗakko ta lulluɓawa Aymah. Zabura tai da sauri ta cafke hannunsa tana ƙwaɓe fuska zatai kuka. Dan a tunaninta Momy ce ma ita. Tace, “Momy Please karki cire sanyi nakeji”.  
          Hannunsa yay ƙoƙarin janyewa daga cikin nata amma ta riƙe gam, hakanne ya sakashi barin hannun kujerar ya dawo ta gabanta ya tsugunna. Sosai ƙamshin turarensa ya daki hancinta yanzu. Tai azamar buɗe idanunta da sukai mata nauyi, sai ko a cikin nashi. 
       Zabura tai da sauri tana saki masa hannu tare da wancakalar da bargon har yana rufe masa fuska. Hannunsa yasa ya janye bargon a hankali tare da saurin riƙota dan tana ƙoƙarin barin kujerar ne. Hannun taja zata fisge. Fuska a murtuke yace “ALLAH idan baki nutsu ba allura zan miki”.
       Ai babu shiri tai saurin komawa ta zauna hawaye na zubo mata saman fuska da uban gudu. Ta bashi dariya amma sai baiyiba ya gimtse abarsa. Sai dai hakan bai hana lips ɗinsa motsawa ba kaɗan. 
     Duk da halin da take a ciki sai da ta zuba masa harara ga hawaye na zirara kuma. Dariya Richard dake kallonsu tamkar ya samu television yayi. Juyawa Yoohan yayi yay masa daƙƙuwa yana danne tasa dariyar. Sai kuma ya mike daga tsugunnon da yay a gabanta ya koma kujerar da take zaunen daf da ita, dan tazarar dake tsakaninsu kaɗance. Harara Aymah ta kuma zuba masa tana maƙurewa gefe. Shi dai bai kulataba ya ɗakko kofin shayin ya miƙa mata.
         “Ban sha” ta faɗa tana kuma matse jikinta a cikin bargon. Sake tsuke fuskarsa yayi da ƙyau sannan ya kalleta, dan duk da da hausa tayi maganar sarai ya jita. Sake mika mata kofin yay tare da matso da fuskarsa gab da tata. Yace, “Silly girl! Koki karɓa ko ki sha allurai a bom-bom ɗinki yanzun nan”.
        Duk da tsoratar da tayi sai da tace masa ɗan iska a zuciya, saboda kalmarsa ta ƙarshe-ƙarshe. kofin ta amsa tana hawaye da tunzura baki gaba. Shi dai bai kulata ba, sai hararar Rich da kema su Osin gulmar haɗuwar matar Yoohan ta waya da yare yayi. Richard yi yay kamar bai gansa ba ya cigaba da rattafa bayani dalla-dalla.
          Nu'aymah bata son shan shayin amma tana tsoron allura, hakan yasa ta daure ta shanye duka tana hawaye. Amsar kofin yayi yana sakin wani shegen Murmushin gefen baki. Aymah kanta sai da Murmushin ya daki zuciyarta, dan tunda ta sanshi a rayuwarta bata taɓa ganin yayi murmushi ba sai yanzun. Saurin riƙe bargon da take neman rufama har kanta yayi. 
      “Ban gama da ke ba”. Yay maganar a hankali tamkar mai yin raɗa. Cikowa idanunta sukai da sabbin hawaye. Ta ture hannunsa dake riƙe da bargon tana faɗin, “Bana shanye ba, nifa ka takuramin da yawa, yanzu ba da bace inada aure ka daina taɓani banaso”.
       Da ɗan wani salo yace, “Oh really? Smalley! Waye mijin to?”.
             Sosai rawar sanyin nata ya fara raguwa, sai ma wata zufa dake taruwa mata a goshi, hakanne ya saka bakin tsiwar tata sake fitowa fiye da sanda suka shigo. Tai masa wata irin harar da ta saka tsigar jikinsa tashi tana murguɗa baki, “To ina ruwanka shugaban masu shishshigi. Idan ka gama abinda ya kawoka zaka iya tafiya”.
        Bakinsa ya taɓe ya ɗauke kai tamkar bai ji mita faɗa ba. Sai ma aljihun jeans ɗin jikinsa daya laluba ya zaro ledar daya ɗakko daga mota. Wani ɗan kwalin magani ne ƙarami ya zaro. Ya fiddo maganin ciki ƴan kanana, a gaban idonta ya ɓalli ɗaya, sai taga ya rabashi biyu ya maida rabin a ramin daya ciro ya liƙe tare da sakawa a kwalin. Miƙewa yay zuwa inda Rich ke zaune har yanzu yana waya, ya halbi ƙafarsa sannan ya ɗauki gorar ruwa ɗaya cikin waɗanda aka ajiye musu ya bar wajen batare da ya kula Rich daya riƙe ƙafarsa da yaji zafin halbin da yay masa ba.
       Duk abinda suke Aymah kallonsu, har addu'a tayi a ranta ALLAH yasa Richard yace sai ya rama koda sun fita ne. Cikin katse mata tunanin muguntarta ya miƙa mata maganin dake cikin hanun nasa. Baki ta buɗe zatai magana yay saurin ɗaura yatsansa kan baki yace, “Shiiii!! bana son musu malama, ki karɓa inada abinyi jirana akeyi”. Da mugunta tasa yatsu biyu zata ɗauki rabin maganin dake cikin lallausan tafin hannunsa da jini keta kai kawo tamkar zai tsillo waje. Saita haɗo da fatar hannun ta mintsina da ƙarfi. Duk da yaji zafi sai baiko motsa ba balle ya nuna yasan mi tayi. Tai masa harar gefen ido tare da jefa maganin a bakinta tana faɗin, ‘Sai shegen dauriya wai shi jarumi, ai ko baka nunaba nasan wlhy kaji zafi’ ta ƙare zancen zucin nata da jefa maganin cikin baki. 
       Shi dai yana kallonta ne ƙasa-ƙasa. Ya miƙa mata ruwan hannun nasa, babu musu ta amsa ta tuttula cikin baki tana yamutsa fuska tamkar zata fasa ihu. Dan shima maganin bawai tana ƙaunarsa bane ba. amma dai yafi mata sauƙi-sauƙi akan allura.
     Goran ta miƙa masa, ya amsa tare da ranƙwafowa ya kama bargon ya rufa mata a jikinta yana magana kamar baya so. “Kwanta”. Bata musaba ta zame ta kwanta tare da lumshe idanunta masu cikar gashin gira dana ido.
         Tasowa richard daya gama gulma a waya yayi yana gaisheta da jiki. Batare data buɗe idanunba ta amsa masa sama-sama alamar barcine mai nauyi ke fisgar idanunta.

      Jin motsi a bayansu yasa duk suka juya. Momy ce ta fito akan ko zasu buƙaci wani abu. Kai Yoohan ya risinar, cike da girmamawa yace, “Aunty mu bara muje, insha ALLAH barcin da zatayi yanzu zai taimaka mata zazzaɓin kuma zai sauka, shima sanyin zata bar ji”.
      Fuskar Momy da fara'a tace, “To Alhmdllh Son, mun gode sosai”.
       Kansa kawai ya jinjina mata sukai mata sallama suka fice tare da Omar dake zaune a ƙofar corridor ɗin Abban yana jiransu dama. Su aunty Hibbah duk sun shige kwanciya saboda gajiya. Hakan yasa suka fice abinsu babu wata gargada

      Tunda suka bar gidan bakin Richard ya kasa yin shiru wajen yaba ƙyawun Aymah, da tambayar Yoohan ya akai ya samota? Bayan yasan hausawan nan basa son bama kowa ƴaƴansu sai yarensu kawai. Tun Yoohan na sharesa harya gaji ya ɗauki Bluetooth ya maƙala a duka kunnensa alamar baya bukatar cigaba da jin surutun na Rich. Kai tsaye Hotel ɗin suka koma. Inda a canma Rich yay zaman bama su Joseph labarin matar ta Yoohan, sai dai a cewarsa ƴar karamar yarinya ce.
         Ko sau ɗaya Yoohan bai saka musu baki ba, gefe ma ya koma yasa aka kawo masa coffee dan su Godwin sun cika wajen da warin giyar da suka sha harda sigari. Dan dai ita sigarin ana mata shan gayune kara ɗaya ko biyu shikenan. Giyar ce dai aka maida ruwa😖.

WASHE GARI

         Washe gari da safe company ɗin da aka bama kwangilar kayan Nu'aymah suka isa gidansu Yoohan bisa address ɗin da aka basu. Wannan al'amari ya bama dangin Yoohan mamaki, dan su dai basu saba ganin hakaba. A saninsu miji shike kayan gida. Amma sai gashi su an kawo musu. Da alama kuma babban company ne.
              Kiran baba malam. Yoohan yayi yana roƙonsa akan basai sun saka komai ba, shi zaiyi komai insha ALLAH. Amma sai baba malan ya nuna masa sam bazai yuwuba. Mu hausa fulani hakan al'adarmu ce, yayi haƙuri ya barmu muyi. Yanajin nauyin baba malam da kimarsa. Shiyyasa dole ya bari aka kwashe kujerun falonsa da kayan gadon dake a ɗayan ɗakin, harma dana karamin falonsa na hutawa da sai ya bushi iska yake shigarsa duk suka fidda. A wani sashe na cikin gidan aka maida kayan, su kuma suka shiga aikinsu cike da ƙwarewa. Kayane ƴan ubansu masu shegen tsada. Dan sai dama suka bama Yoohan ɗin zaɓin waɗanda yake so ta hanyar pictures sannan suka koma company suka ɗakko akazo aka shiga hadawa.
       Zuwa lokacin kuma gidan nasu ya fara ɗaukar baƙi na nesa. Dan sosai Papa da su Gebrail sukai gayya, hakama su Richard sun bala'i-bala'in gayyato abokansu kamar hauka. Harda na ƙasashen ƙetare. Shi angonma baisani ba, iya waɗanda kawai ya gayyata ne yasan da zuwansu.

        Anan gidansu Abdallah ma ragal Aymah ta tashi, sai dai rashin ƙwarin jiki da ƴar fargabar tunanin wanda ya kasance mijin nata. duk da ranta yafi bata Yah Ab, ganin an kawota gidansu ne na nan abuja.
     Gari na fara haske Aunty hibbah ta fara mata gyaran jiki na musamman, hakan yasa bataga idanun su Adawiya ba. Koma nace Adawiya kawai dan su Yusrah da Amal suna nane da ita.
           Ji tai duk kewar su Umm ta gallabeta, ta amshi wayar Yusrah tai kiran baba malam, ALLAH yasa lokacin yana gida bai fita ba. Shima yaji daɗin jin muryarta, dan Abba ya sanar masa jiya tayi zazzaɓi sai da Yoohan yazo ya dubata. Sai dai kuka data saka masa ne ya sashi fara mata faɗa, daga ƙarshe kuma yay mata nasiha mai haɗe da lallashi. Yace bazai bama Umm wayarba sai idan ya kirata anjima yaji bata kukan. daga haka ya yanke kiran itama ta ajiye tana sharar ƙwallan da har yanzu sun ƙi tsayawa. Sosai Yusrah da Amal ke tausayinta. Shiyyasa duk sai suka zama shiru-shiru suma. 

________★★★★________

         Kasancewar su dai basusan da zaman dinner ɗin da gidansu Yoohan ke shiryawaba ƙarfe huɗu suka shirin miƙa amarya ɗakinta. Dan jirgin 8pm zasubi ya maidasu kano. Anayin sallar la'asar kuwa aunty Aysha ta tsaya akan Aymah sai da taga ta shirya tsaf cikin lifaya fara da kwalliyar golden. Tai mata ƴar kwalliya duk da ta nuna bataso. Kowa ya ganta sai ya ambaci masha ALLAH, ga uban ƙamshi da take zubawa kamar gidan turaren (miss xoxo😚lol). 
       Kamar yanda tsarin yake ga duk amaryar da za'a miƙa gidan miji a gidansu haka itama akai mata. Dan kuwa Abba ne yay mata rakkiya gidan aurenta sai su Momy dasu Aunty Hibbah. Su Adawiya ma Abba cayay bazasu je ba sai gobe idan ALLAH ya kaimu dan bandasu za'a koma kano dama. Zasu ɗanyi kwana biyu a nan.

         An tarbesu yanda basuyi zato da tsammani ba, ba kuma komai ya jawo hakanba sai dogon gargaɗin da papa da Yoohan ɗin sukayi, sai kuma sauran matan su Uncle Mike suma sunsha gargaɗi wajen mazajen nasu. Shiyyasa suka zama gaba-gaba wajen ƴan amsar amarya basu bari su mama debora sun kwafsa ba. Koba komai dangin Nu'aymah sunji ƴar nutsuwa, sai dai har cikin ransu sunji tausayinta na zama cikin waɗan nan gurguzin kahiran da idanunsu ke buɗe da wayewar karatu dana kuɗi. Amma sun rigada sunyi imani da cewar UBANGIJIN daya ƙaddara shigowarta cikinsu, yafisu sanin alkairi da hikimar yin hakan. Sun sake mata nasiha sosai, tanata kuka dai duk da bata fahimci ina aka kawota ba. 
         Duk da tarin abinci da kayan sha da aka kawo musu basu taɓa komaiba, sai ma miƙewa da sukayi da zummar tafiya bayan sun leƙa ko ina na sashen nata sukaga yanda company ya tsarashi gwanin birgewa. Ƴan gyare-gyaren da suka ƙara mata ba wasu masu yawa baneba, shiyyasa basu jasu lokaci ba.
      Ganin suna shirin tafiya kamar yanda Abba daya fita tuni suna tare da papa a harabar gidan papa yace ya zasu tafi bayan ana shirin yin taro suma anan.
     Murmushi Abba yayi, yace, “Ai su anjima kaɗanma zasu koma kano, muna musu fatan alkairi dai”. Yoohan da duk ke saurarensu yay saurin cewa, “Uncle Please ka barsu, na maka alƙawarin insha ALLAH zasu sami jirgin safe saisu wuce. Itama zata damu idan taga babu family nata a wajen”.
      Ɗan jimmm Abbah yayi yana nazari, yasan gaskiya Yoohan ɗin ya faɗa, duk da dai su ba ɗabi'arsu bace yin wannan bidi'oin, to amma a yanzu basu da iko akan Aymah tunda sun kawota gidan mijinta. Basu da ikon kuma cewa su Yoohan bazasuyi nasu shagalinba tunda shi aure rahama ne, yin shagali a cikinsa kuma ba aibu bane. Abinda kawai ba'a bukata wuce gona da iri da yin almabazaranci da dukiya. (Wadda a yanzu hakan ne yafi yawa a bukukuwanmu. shiyyasa tun a filin bidi'oin ake zazzage daraja da albarkar auren atafi da gayyar sheɗanu😪🤦🏻).
       Kansa ya ɗan jinjina da faɗin, “Tom shikenan. Amma bara na fara kiran Yaya (baba malam) na sanar masa tukunna”. Wannan ɗabi'ar tasu na birge Yoohan matuƙa. 
       Bayan Abbah daya koma gefe ya gama waya da Baba malam ya dawo yana faɗin, “Shikenan zasu zauna ɗin, amma yanzu su fito muje idan lokacin yayi sai a kaisu can. Idan mun koma sai ƴan uwanta suzo su tayata zama su yanzun”.
       “Muna godiya Uncle, ALLAH ya ƙara girma”.
    Murmushi kawai Abbah yayi, hakama Papa fuskarsa kamar gonar auduga.

★★★★★★

             Tun bayan magriba mai kwalliya tazo yima Aymah. Amma saita tubure akan sai tayi sallar isha'i. Dole aka haƙura akan hakan, duk da su ƴan bikima harsun fara wucewa inda za'a gudanar da shagalin. Duk yanda taso su Amal su sanar mata wanene mijin sunƙi. Dan Amal da Yusrah da wasu ƙawayen Amal ɗin biyu maƙwaftansu suna nan tare da ita. Adawiya kam batazo ba wai kanta ke ciwo tasha magani sai anjima zata biyo su Aunty hibbah. Hakan bai wani damu Aymah ba, dan ita mantawa take ma da babin wata Adawiya yanzun.
      Bayan an idar da sallar isha'i aka rangaɗama amarya Nu'aymah kwalliyar garari. Dan ko makaho ya taɓa saiya jinjina. Hakama su Amal an musu tasu. Momy daketa danne zuciyarta bisa shawarar ƙawartace da kanta ta kawoma Aymah rigar da zata saka wadda garariya garara har ƙasan amuruka akaje sayota daga aljihun papa da umarninsa.
      Nu'aymah taso yin gaddamar sakawa. Amma yanda Momyn ke mata da lallashi ita da ƙawarta ya sakata amsa ta saka ganin rigar akwai hannu a jiki. Ammafa ta bala'i-bala'in haɗuwa sai ɗaukar ido takeyi. Farace tas sai kwalliyar furanni pitch color data ƙawata rigar. Hakan yasa dogon takalminta da shi kansa abin kallone ya kasance pitch. Sarƙa ɗankwali duk pitch. Humm lamarinfa ba'a cewa komai. Ita da kanta Aymah tasan ta haɗu, sai dai zuciyarta a raunane take, dan ta tabbatar ba Yah Ab ɗinta bane angonta. Musamman data san danginta basa irin wannan shirmen bidi'ar, kuma tasan ba Yah Naser bane shima, dan da ace shine katsina za'a kaita. ‘Ni Zainab wanene iyayena suka bama ni’ ta faɗa cikin zuciyarta tana kukan zuci, a fili kuwa idanunta sun cika da ƙwalla. Tayi jarumta sosai wajen ganin basu zubo ba.

      Tare suka tafi dasu madam Chioma a mota ɗaya, dan shi ango yana acan hotel ɗin da za'ayi dinner ɗin, acan suke zaune da abokansa da baƙi da shi kansa wasu ma baisan da zuwan nasuba sai da sukazo ɗin. Dan ba ƙaramar gayya su Rich suka yo ba. Harda abokansu tunna secondary skull.
      Lallai biki yayi biki kam, dan tun a ganin zuƙa-zuƙan motocin dake cike da harabar hotel ɗin har waje zaka san eh lallai manya ne ke lokacinsu. Ga ƴan jarida da ƴan sanda a wajen harda soji. 
        Momy da ƙawarta ne kawai suka fita. Aymah kam zata jira angonta. Su Yusrah ma dake motar bayansu duk sun fito suna tsaye. Ba'a rufa mintuna biyarba sai ga Doctor Yoohan mai zamani ya fito tare da gayyar abokansa. Tab, lallai kam ita ranar aure ta musamman ce ga kowa. Duk da shigar suit ɗabi'arsa ce sai yau tafi ta kullum. A kallo ɗaya zaka gane cewa kuɗaɗe masu nauyi aka zuba wajen sayen kayan. Fararene tas shima sai shirt ɗin ciki ce kaɗai ta kasance pitch. Gashin kan nan nasa da saje sunsha gyara sai walƙiya da ɗaukar idanu sukeyi. Duk da fuskar babu murmushi a sake take bai ɗaure ta ba. Hakan ya saka ƙyawunsa sake fita da ƙyau, ga wani irin kwarjini na angwanci dana ruwan alwala daya fara bin ƙofofin gashinsa na ɗawainiya da shi. Duk da ƙyawun da abokansa sukayi suma duk sai ya damasu ya shanye saboda darajar hasken musilinci.
        Solomon yay saurin buɗe masa motar da Aymah ke a ciki zaune tanata haɗiyar zuciya. Baice komai ba sai matsawa da yayi jikin motar. Ya ɗan ranƙwafa kaɗan yanda zai iya ganinta da ƙyau. A tare hancinansu suka shaƙar musu ƙamshin turaren juna. Kowanne zuciyarsa ta harba kaɗan, musamman ma Yoohan da ƙyawun da Aymah tayi ya nema zarar da shi a tsaye. Amma a fili sai ya fuske abinsa ya miƙa mata tattausan tafin hannunsa, cikin harshensa da baya fita da ƙyau yace, “Bismillah”.
        Wani irin harbawa da ƙarfi ƙirjin Nu'aymah yayi a karo na biyu, duk da kuwa dama ta tsargu tun jin ƙamshin turarensa. Amma sai bata kawoma ranta shiɗinne ba..... Kafin ta fahimci ruɗanin da take neman afkawa taji ya saƙala hannun nasa cikin nata. 
      Da sauri taja zata fisge jikinta na wani irin tsuma. Riƙesa yayi da ƙyau tare da matso fuskarsa gab da tata. A cikin kunnenta yace, “Wlhy kina min tsiwankin nan sai wannan ya shiga jikinki, garama ki nutsu mubar wajen nan lafiya”. Yay maganar yana nuna mata syringe da batasan daga ina ya cirosa ba.
        ‘Innalillahi....’ Aymah kawai ke iya maimaitawa a cikin zuciyarta. Kanta ya sake shigewa a ruɗani har batasan lokacin daya fiddota waje ba, ta dai ganta akan ƙafafuntane kawai dake sanye da dogon takalmi. Sauƙinta ma ta iya tafiya dasu dama can, amma da ansha kunya yau.
        Gaba ɗaya ta zame masa mutum-mutumi, binsa kawai take duk yanda ya juyata. Ƴan jarida da abokansa da duk suka rikice sai zuba musu hotuna suke tako ina. Hasken camaras kawai kake gani babu ƙaƙƙautawa.
       Duk da a cikin abokansa wasu na ganin Nu'aymah tayi kanƙanta hakan bai hanasu taya abokin nasu murna ba da mamakin inda ya samo wannan ƴar shilar. Yoohan dai ya fuske abinsa, dan bayason yayi wani ɗan sakaci da Aymah zata birkice masa a wajen nan. A haka suka shiga cikin hall ɗin daya haɗu harya gaji, decoration ɗin wajen ma komai fari ne da kwalliyar pitch kaɗan-kaɗan. Gashi komai a tsare babu wani hayaniya ko shirme, ga uban haske tako ina tamkar rana. Ko allura ka yadda zaka ɗauka abarka. Kowa yana zaune a inda ya dace da shi. Ita dai kanta na a ƙasa ne bata yarda ta kalli kowa ba duk da uban tafi da ake musu, ga wata waƙar na tashi a hankali cikin hall ɗin. Bayan an musu rakkiya inda ya dace su zauna kowa ya nema wajen zama. Papa ya gudanar da addu'a a wajen da kansa, shidai Yoohan yayi tasa a cikin rai. Nu'aymah ma sunayi tanayin tata cike da takaici. Ita abinda yafi birkitata shine su baba malam basu san Yoohan arne bane suka aura mata kenan? (Kusanfa ita batasan Yoohan ya musulinta ba) wannan bahagon tunanin ne yake neman zauta mata ƙwalwar kai. Shiyyasa tai shiru bata sake koda wani ƙwaƙwƙwaran motsi ba har aka fara gudanar da abinda ya tara mutane. Ita dai komai a shirme ma take kallonsa, sai dai ta ɗanji sanyi a ranta lokacin data ɗaga kai idonta ya sauka akan ahalinta su aunty hibbah da sukazo wajen daga baya. Amma saboda girmamawa a garesu sai aka kawosu gaba inda aka tanadar musu tebiri biyu dama. A yanzunma bataga Adawiya ba tare da su.
       Lokacin da akace su yanka cake tasha uban takaici. Dan ƙin basa tayi. Idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta ganin yanda hall ɗin yay tsit kowa ya zuba musu idanu. “Kinason muji kunya wajen waɗan nan ɗunbin mutanen da suka taru saboda mu ko? To idanfa kinƙi yin yanda akace ALLAH saina miki abinda sai kin kasa fita hall ɗinnan da kafafunkin nan”.
      Gabantane ya faɗi. dan tasan zai iya aikatawar. Tunda har baiji nauyi ko shakkar mata kiss a gidansu ba. Sai da taɗan hararesa ta gefen ido sannan ta ciri cake ɗin da suka yanka ɗin, batare da ta yarda ta kallesa ba takai hannunta bakinsa. Hannun ya kama da nasa hannun ya ƙarasa da cake ɗin cikin bakinsa. Ɗan kaɗan ma ya gutsira ya juya hannun nata dake riƙe a cikin nasa wajen nata bakin. Badan ta so ba ta buɗe kaɗan itama danta ɗan gutsirar sai ya tura mata shi gaba ɗaya tsabar neman rigima. Saurin ɗagowa tai a ɗan zabure, hakan yasata gullewa tai gefe zata faɗi yay azamar riƙo ƙugunta ta dawo kan ƙirjinsa. Tuni tsiwar mutuniyar taku ta motsa, ta ɗago birkitattun idanun nan nata da suka sake girma ruwan hawayen da suka taru a ciki suka sasu wani kala ta musamman. Cikin nasa manyan idanun suka shige caraf, ya sarƙeta da su yanda ya hanata koda motsi suka cigaba da tsaiwa a haka tana a jikinsa idanunsu sarƙe cikin na juna. Gaba ɗaya tama rasa wane kalar bore zatai masa yasan halin da take ciki akan ganinsa matsayin wai miji a gareta. A hankali ta motsa laɓɓanta zatai magana. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓansa. a hankali yace, “Shiiii!!!”. Kasa yin maganar kuwa tayi batare da tasan dalilin hakan ba. Sai ma wata iriyar kasala data saukar mata da bala'in kwarjininsa da bata taɓa ganiba cikin idanunsa.
         Kusan a tare hall ɗin ya ɗauki dariya, sai uban hasken camaras kake gani nata walwala su. Dan yanda suke a tsayen dolene su birge mai kallo, musamman ma'abota son soyayya.
      Saurin yin ƙasa da kai Madam Chioma tayi tare da saka handkerchief ta share hawayen da suka cika mata idanu, badan shirin da suka ƙulla akan yarinyar nan ba ita da ƙawarta da tun a wajen nan saita halakata ta huta akan yaronta da takejin tsananin kishi. Miracle ma tsaki tayi ta miƙe ta fice daga cikin hall ɗin tana kuka, daga nan sai gidan barasa, dan tana buƙatar sheƙe wasu kwalabe ko zata sami nutsuwa. Hakama sauran ƴammatansa da baisan da zamansu ba abun yamusu takaici, ko joy da take ƙanwarsa sai da ranta ya sosu duk da kuwa sun birgeta itama.
        Da sauri Nu'aymah data dawo hayyacinta saboda maganar mc tai saurin saka hannayenta ta ɗan turasa. Sakinta yay badan yaji turawar datai masa ba, sai dan kawai muguntar da tazo masa a cikin rai. Baya ta sakeyi zata faɗi ya riƙo hannunta da sauri ta kuma dawowa jikin nasa. Ya ɗan tsuke fuska kaɗan yana faɗin, “Silly girl”. Sannan ya saketa a hankali. Baki ta murguɗa masa kaɗan tana gyara tsaiwarta zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri. Kallo ɗaya taima sashen dasu Ananah suke ta maida idonta ƙasa ta duƙar saboda tsananin jin kunyarsu data lulluɓe ta.

       Haka dai taro ya tashi lafiya bayan anci an sha kamar ba'asan ciwon kuɗi ba. liƙi kam sai kace basu sa zafin nema ba. Dan ƴan dubu-dubu ne sabbi ƙal keta farfar a ƙasa. Musamman lokacin da ango da amarya suka fito filin rawa. Sai dai sunyi tsayene babu wanda ya motsa, dama can kowa yasan Yoohan baya rawa, to bare Aymah da basa samun wannan sakewar a nasu gidan dama.
     Su Osin abokan ango dai dasu Gebrail ƙannen ango an cashe gwargwadon iko. Mawaƙan da sukayi wasa a wajen sun kwashi kuɗi kam gwargwadon iko. Ƙarfe ɗaya dai-dai aka tashi.
      Wasu sun nufi gidajensu ne, wasu kuma anan hotel ɗin, sai masu komawa gidansu Yoohan da amarya. Su Amal dai binsu Aunty Ananah sukayi suka koma gidan Abbah kamar yanda Omar ya tasasu a gaba............✍



ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 46
__________

_INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._

_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._

_”Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_

_”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_

_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻‍♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼‍♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._

“_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi..  Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_”

_”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a  faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_


____________


No. 46

.............Washe gari ƴan biki duk suka kama gabansu. Ciki kuwa harda ƴan kano su aunty hibba. Dan cikin sa'a sun sami jirgin safe. Sun tafi kuma da ɗunbin alkairi daga Yoohan. Sai dai kuma zukatansu cike da tausayin Nu'aymah da ƙaddarar aure ta kawo tsakkiyar waɗan nan mutane. Amma zasu cigaba da tayata da addu'ar zama mai nasara a cikinsu.

         Nu'aymah kam bama tasan wainar da ake toyawaba a cikin gidan.  Babu wanda ya nemeta a jama'ar gidan, itama kuma bata damu da son ganin kowa ba ma. Dan kukan data raba dare tanayi jiya ne ya ja mata komawa barci mai nauyi yau da safe. Bata farka ba sai wajen sha ɗaya. Haka ta tashi jikinta zau da zazzaɓi. Cikin dauriya tai wanka da ruwa mai zafin gaske. Tana fitowa anayin knocking ƙofar. Sai da ƙirjinta ya ɗan harba kaɗan, dan zatonta ko Yoohan ɗin ne. Jin an sake knocking ɗin ya sakata rumtse idanunta da sukai mata nauyi, hijjab ta ɗauka ta zira, sannan tazo ta buɗe ƙofar tana faman cin magani.
      Victoria ce tsaye da tray a hannu, Destiny a bayanta ɗauke da flask ɗin shayi madaidaici. Ganin yanda yaran keta washe mata fuska ya sata sassauta fuskarta data ɗaure. Baki suka haɗa wajen faɗin, “Good morning Aunty!”.
       A taƙaice Nu'aymah tace musu, “How are you?”. 
       “Fine Aunty, dama Aunty Blessing ce tace mu kawo miki breakfast”. (Kukun gidan).
        Matsa musu tayi suka shiga cikin ɗakin batare data sake cewa komai ba. Ɗakin sukebi da kallo cike da sha'awar yanda ya haɗu. Bayan sun ajiye Destiny da bakinta baya iya yin shiru tace, “Aunty ɗakinki yayi ƙyau”.
     “Thanks you”. Aymah ta sake faɗa a taƙaice. Dan ta kula shegen surutu yaran zasu dameta da shi idan ta basu fuska. Ilai kuwa sai Victoria ma ta buɗe baki zatai magana aka turo ƙofar ɗakin. Basai an faɗa ba, ƙamshin turarensa ma kawai ya isa amsa garesu. Da sauri suka miƙe daga zaman da sukayi akan sofa. Cikin ɗan rawar baki suke gaishesa. Janye idanunsa yayi akan Nu'aymah data ɗauke kanta bayan ta masa kallo ɗaya ya maida garesu. A taƙaice ya amsa musu yana cigaba da takowa cikin ɗakin. Saurin nufar ƙofa sukai suka fice.
       Duk abinda sukeyi Nu'aymah na kallonsu ta cikin mirror, sai dai ta basar tanata shafa mai a ƙafarta kamar batasan da zamasu ba. Sai dai a ranta ji take kamar taje ta shaƙesa. Amma zata daure taga iya gudun ruwansa na yinin yau kawai......
      Yanda bata tanka masa ba shima bai tanka matanba. Wayar dake a hannunsa yana latsawa ya matsa ya ajiye mata saman mirror ɗin, batare da yace komaiba ya juya zai fice. Cike da jin haushi Aymah ta bisa da kallo, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa ta murguɗa baki da harar bayansa.
        Shiko haushin ƙin gaidashin da batayi bane ya sakashi ƙinyi mata magana. Duk da daman dai yau ya tashi ne da rashin ƴan son maganar saboda barci dake cike da idanunsa. 
       Yana ficewa Aymah ta maida dubanta ga wayar tasa mai azabar ƙyau, baki ta taɓe, harta ɗauke kanta sai kuma ta sake duban wayar. ba komaine yazo mata a rai ba sai kiran su Umm. Kwana ɗaya kawai har taji kewarsu, ji take kamar ta shekara babu su tare da ita. Sannan koba komai tanason sanar musu abinda take ganin basu sani ba, dan ta tabbata akan rashin sani iyayenta sukai wannan gamin gambizar. Ita dai tasan mutumin nan da aka aura mata kafiri ne, kuma tana da tabbacin iyayenta bazasu aura mata arne ba tunda sunsan haramunne a musulinci. Shin ko dai ya ɓoye musu ainahin kansa ne? Tabbas Aunty Kubrah ta cutar da ita, tunda har ta ɗauki hoton abinda ya faru a kuskure ta bama Hamisu ya kawo gidansu, (dan harga ALLAH tasan Kubrah ce ta saka hamisu yin hakan, sai dai shi tarasa miyasa ya amince ya aikata?)  gashi nan ta silar hakan taja an aura mata kafirin da baisan ALLAH ba, danginsa mushiri kai. Dolene a yau tai gaggawar sanarma baba malam abinda ke faruwa..
          Hawayene masu zafi suka sake gangaro mata, harga ALLAH ta gwammaci zaman gidansu akan wannan gidan da babu komai sai shirka a cikinsa. Gashi bazata ɓoyeba tana son Yah Ab har gobe a cikin zuciyarta. Tana danne soyayyarne kawai dan gudun shiga tsakanin alkairin iyayensu da zumincinsu. Taji daɗin ganin wayar babu wani lock. Daga Number baba malam harta Umm da hajjo a cikin kanta suke tsaf. Dan haka babu wani shan wahala ta saka Number Umm ta kira. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ba. Ta sake kira nanma ba'a ɗaga ɗinba. Ta baba malam ta saka. Tunkan ta karasa ma *Uncle S* ya bayyana. alamar da haka yay sebin lambar kenan. Cikin sa'a kuwa bugu biyu aka ɗaga. Jikinta har rawa yake najin daɗi. Hawayen da take maƙalewa suka sake silalowa jin muryar Abbanta ya rangaɗa sallama da muryarnan tasa mai tarin kamala.
        “Abba na!” ta faɗa kukanta na ƙwacewa da sauti.
      Murmushi baba malam yayi daga can, cike da tsokana yace, “Anya mamana bata girmi kuka ba yanzun?”. 
     Ai kamar ya sake zugata ma, saita ƙara sautin kuka nata. Baba malam daketa ƙoƙarin danne kewar ƴar ɗiyar tasa yace, “Tom ya isa haka kuka. Inba hakaba kuma zan yanke wayata.....”
        “A'a Abbah, dan ALLAH karka kashe. Ina kwana?”.
       Murmushin ya sakeyi sannan ya amsa mata. Bayan sun gama gaisawa ta tambayi kowa da kowa na gidan nasu. Ya tabbatar mata da duk lafiya suke harsu Ananah da tuni sun isa gida.
       “Amma Abbah shine basu sake zuwa nan ba?”.
      “Ai kinga da safe sosai suka taho mamana, kinga idan sunce sai sunzo nan zasu makara. Mijinki ne ma da kansa yaje ya kaisu airport”.
       Hawayene suka sake ziraro mata. A ranta tace, ‘Mugu shine yaki tashina muje tare’. a fili kuwa sai ta saka hannu ta share hawayen nata. Murya na rawa tace, “Dama na kiraka ne muyi magana Abbah”.
               Zamansa ya sake gyarawa da ƙyau yace, “ina jinki mamana”.
    “Abbah dan ALLAH ka fahimceni, wlhy ba ƙazafi nake masa ba. Mutumin nan fa kafirine, ya ɓoye muku ne kawai har kuka bashi aure na.......”
         “A'a Mamana shi ba kafiri baneba a yanzu. Ki nutsu ki saurareni za miki bayani yanzun nan kinji”.
     Kanta ta ɗaga masa tamkar tana a gabansa. cikin nutsuwa baba malam ya sanar mata komai game da musulintar Yoohan, ya kuma nuna mata muhimmancin zama da shi da dalilin aura mata shi dansu raba gardama tsakanin Abdallah da Naseer gudun kar zuminci ya samu giɓi. Itama kuma zata huta idan tayi nesa da su. Harga ALLAH taji daɗin jin cewa Yoohan ɗin yanzu musulmi ne, sai dai bawai hakan na nufin zata so shi bane ba, zataima iyayenta biyayya har lokacin da UBANGIJI zai iyakance mata zama tare da shi. Dan bataji zata iya rayuwar dindindin ta aure da shi ba balle waɗan nan dangin nasa masu kama da ojuju.
       Baba malam ya mata doguwar nasiha mai ratsa jiki da ɓargo. taji kuma tayi ɗammarar yin amfani da ita, amma bata ɗauki alƙawarin haƙurin zama da Yoohan ba tabbas. A ƙarshen wayar ta roƙa baba malam a kawo mata koda ƴar aiki ce daga nan kano. hakan zaisa ta samu abokin hira kafin ta saba da jama'ar gidan. 
        Baba malam baiƙi karɓar alfarmar tata ba. Dan koba komai yasan hakan zai bata nutsuwa ta ɗan kwantar da hankalinta yanda yake bukata da fata. Sai dai yace sai mijinta ya amince sannan.

        Koda suka ajiye wayarma tashi tai tana sharɓar hawaye. Batare data cire hijjabin data zumbula ba balle ta nema kayan sakawa ta faɗa saman gado ta cigaba da kukanta da batasan na minene ba. Jitai zazzaɓin na sake lulluɓe ta. Taja lallausan bargon dake saman gadon ta kudundune zuciyarta fal ƙunci.
      
       Yoohan dake can ɗakin Momy da itama babu lafiyar bayan ya lallaɓata tasha tea ya saka mata ƙarin ruwa. Sai da yaga barci ya ɗauketa ne ya zare hannunsa dake cikin nata a hankali ya lulluɓa mata bargo ya fito. A corridor yaci karo da Miracle. Kallo ɗaya yay nata ya ɗauke kansa saboda shegun kayan barcin dake a jikinta bata da maraba da tsirara. Da alama ma yanzu ta tashi barci. Cike da kishi tace masa “good morning”. Batare daya amsata ba ya wuce abinsa ya barta da ƙamshinsa.
      Sashen sa ya koma. Inda ya iske Solomon a falo yana goge-goge. Gaidashi yayi cike da girmamawa kamar yanda ya saba.
       Amsa masa yayi yana tura ƙofar ɗakin Nu'aymah ya shiga. Solo ya rakashi da kallo tamkar idanunsa zasu zubo ƙasa. Oho baimasan yana yi ba, danshi tuni ya shige.
           Shashshekar kukanta daya faracin karo da ita cikin kunnuwansa ne ya sashi lumshe idanunsa a hankali ya buɗesu a kanta, cigaba da tsaiwa yayi a bakin ƙofar kawai yana kallonta kamar ya samu television. Ita kam bama tasan da shigowarsa ba, dan gaba ɗaya hankalinta da tunani yana kan ta yanda zata samu mafita akan wannan auren ne. Sai ɗunbin kewar iyayenta da ƴan uwanta dake gaba-gaba wajen tunzura kuka nata.
        A hankali ya sauke numfashi da zura duka hannayensa cikin aljihun baƙin wandonsa. Ya fara taka farar ƙafarsa dake fes babu wani datti a jikinta saboda tsabar saka kwaba shu da yake a koda yaushe ya ƙarasa har gaban gadon dai-dai saitin inda fuskarta take. Har fuska ta rufa bargon. Kaɗan yaja gajeran tsaki a maƙoshi, a ransa ko rayawa yake, ‘Sai shegen tsiwa a bakinta da ƙuruciya’. A fili kam sai ya ɗan ranƙwafo da zare hannunsa daga cikin aljihu ya yaye bargon daga fuskarta. Bai kai ga kaishi kafaɗa ba ta riƙe gam. Idanu ya zubama farar fuskarta da tai jazur musamman saman hancinta da idanunta. Dai-dai da ɗago nata kumburarrun idanun ta zuba cikin nashi. Sai dai sam kwarjininsa ya hanata iya cigaba da kallon tsakkiyar idanun nasa. Hakan ya sakata azamar janyewa tana kumbura baki fal da iska. “Malam ka daina shigamin rayuwa bana so”. Cikin yin ƙasa da murya yanda bazaiji ba tace, ‘Haka kawai a ringa shigoma mutum kai tsaye babu neman izini’.
      Baiji maganar data faɗa ba a ƙarshe dan da hausa tayi, ta farkoce dai tayi da turanci. Amma a yanda tai maganar yaji a jikinsa rashin kunya ce a ciki. Amma sai ya shareta bai kulata ba, sakin bargon yayi ya ɗora yatsunsa biyu a saman goshinta saboda ganin yanda jijiyar kanta tai ruɗu-ruɗu.
     Saurin ja baya tayi hawaye na sakko mata, “Nifa a daina taɓa ni bana so”. Ta faɗa tana hararsa ta ƙasan ido da murguɗa baki kaɗan.
       A karan farko da abin nata yaso bashi dariya, dan haka ya ɗanyi luuu da idanunsa tamkar zai lumshesu amma sai ya buɗe yana kauda kai gefe da sakin murmushi. Barin gaban gadon yayi batare da ya sake magana ba. Abincin da aka kawo mata ya bubbuɗe. Irish ne da ƙwai, sai farfesun kayan ciki, da gasashshen burodi da yaji haɗin salad a tsakkiya. Maidawa yay ya rufe sannan ya miƙe ya fita. 
       Nu'aymah da duk tana kallon abinda ya keyi ta raka bayansa da harara tana faɗin, ‘Mutum babu abinda ya iya sai son taɓa jikin mutane dan kwartanci’. (Hhhhhh🤣 Aymah tamu ta mutunci, mutum ya sauke sadaki ki kirashi kwarto dan ƙarfin hali irin naki😂).

          Bai fi mintuna huɗu da fita ba ya dawo hannunsa ɗauke da kofin tea ruwan hanta, yanda turiri keta fita ta samansa zai baka tabbacin shayi ne..
     A gefen gadon ya zauna daf da ita. Hakanne ya sakata matsawa da sauri. Baki yaɗan taɓe, batare da ya kalleta ba yace, “Oya tashi”. “Na maka mi?” ta bashi amsa tana satar kallonsa. Kofin tea ɗin kawai ya miƙa mata batare da ya sake cewa komai ba.
       “Tab, toni nace maka zansha tea ne? Na ƙoshi”.
       “Silly girl” 
ya faɗa yana hararta a karo na farko. Ya sake tsuke fuska da faɗin, “Malama tashi kiyi breakfast kona juye miki shayin nan ta hanci”.
         Tuni idanun Aymah suka ciko da ƙwalla, cikin rawar sanyin da yake ƙaruwa mata tace, “To ana dole ne? Nace na ƙoshi ba sai ka barni ba”. Komai bai sake ce mataba, sai dire kofin yayi a saman bedside drawer ɗin ya miƙe. Fita yay da ga ɗakin. Da sauri Aymah tace, ‘ALLAH ya hanaka ikon dawowa mai zubin masu jajayen kunne, da wani kansa kamar sheƙar angulu’. (Wlhy ke da shi Aymah ni dai ba ruwa na😂).
              Ganin abinda ya dawo da shi a hannu ya sakata miƙewa zumbur jikinta na rawa. Shiko ko kallon inda take ya ƙiyi sai ƙoƙarin ɓare syringe ɗin daya shigo da shi ya keyi. Ya sake zama a bakin gadon yana ɓalle bakin kwalbar maganin, tare da saka kan allurar jikin syringe ɗin ya zuƙe ruwan allurar da ya kusa rabin syringe ɗin. Ajiyewa yay a gefenta bayan ya gama, sannan ya ɗakko kofin shayin ya miƙa mata batare da yace komai ba. 
        Da iya gaskiyarta take ziraro da hawaye, zuciyarta sai bugawa take da sauri-sauri. Tabbas a rayuwarta allura na ɗaya daga cikin abinda take tsoro fiye da hasashen mai karatu, sai kuma duhu. Waɗan nan abubuwan ko a tunani batason tunasu suna tayar mata da hankali. Hakan yasa hannunta har karkarwa yake wajen miƙa hannu ta amshi kofin shayin. Nanma baice da ita komai ba ya sakar mata. Tiren kayan breakfast ɗin ya ɗakko gaba ɗayansa ya ajiye saman gadon a gabanta. Bayan ya buɗe mata koma ya ɗago ya kamata tana jan allurar daya ajiye alamar so take ta ɓoye.
       Da ƙyar ya iya danne dariyar data zo masa a maƙoshi. ya sake tsuke fuska yana balla mata harara. “Idanma kin ɓoye inada gomanta a ɗakina, kinga kenan kinyi na banza. Na baki 20minutes kacal naga tray ɗin nan empty”.
        Hannu tasa ta sake share hawayen da suka ciko mata idanu, cikin ƙunƙunin da bazaijiba tace, ‘Tunda ga jaka rumbu uwar zira lauma an kawo maka ko’. A fili kuwa duƙar da kai ƙasa tai kamar ta ALLAH😂.
     Hannunsa ya ɗora saman nata da har yanzu ke riƙe da syringe ɗin ya zare abarsa. Gefensa ya ajiye tare da gyara filos ɗin dake birjit a saman gadon ya kwanta rigingine. Wayarsa ya ɗauka ya hau dannawa tamkar ya manta da ita a ɗakin.
     Ɗagowa goma Aymah zatayi harara ashirin take antaya masa. Baƙar magana kuwa da gorin hawa mata gado da yay tayi yafi sau ɗari babu ɗaya tana tunzura baki gaba. Daka ganta kasan tsoro ne fal ranta kawai da neman faɗa da tafi ƙwarewa a yi. Shi dai bai sake bi ta kanta ba duk da yana jin ƙunƙunin da takeyi da harar da take masa. Sai dai kasancewar hausa takeyi bai damu da abinda take cewarba. Da yake dama yunwar ta keji sai gashi ta shanye tea ɗin duka dan ya mata daɗi. Harko da ayyanawa take a ranta ‘Wai buzun nan ashe ya iya haɗa shayi’ (Kai wagga ɗiya ta baba malam ALLAH dai ya gyara😆😂). A sauran abincin kuwa bread kawai taci, dan yanda aka haɗashi ya mata ƙyau a ido da daɗi a baki. Wai saida ta gama ci kuma sai cewa tai, ‘ALLAH dai yasa ba arnakun nan suka yishiba na wage baki ina turawa kamar a haɗiɗiya’. (Ke dai kika sani🤣).
          Ganin ta kammala Yoohan ya miƙe zaune sosai yana ajiye wayar hannunsa. Trayn ya sauke ƙasa, batare da ce mata uffan ba ya matso daf da ita sosai har suna jin saukar numfashin juna. Zabura tayi da sauri zata matsa ya riƙota. Baya buƙatar hayaniyarta a yanzu saboda jikinta yay masifar zafin zazzaɓi, shegen taurin kanta ne kawai ya hana bakinta da bai rabo da tsiwa yin shiru. Baki ta buɗe zata fara masa tijara ya mannesa da nashi tare da sake jawota ya matseta a jikinsa tsam. Ƙarfin ba ɗaya bane, hakan yasa duk mutsu-tsunta ko gezau baiyiba balle tasaran kubuta. Syringe ɗin daya ɗura ruwan allura ya ɗauka, batai auneba sai jin shigarta tayi cikin tsokar jikinta. Tabbas da bakinta baya cikin nasa ba ƴan gidan kaɗaiba har maƙwafta sai sunsan ta kwana a gidan yau. Dan allurar malaria ce daya fahimci shike saka mata zazzaɓin yay mata, allurar kam tana da azabar zafi, dan saita ratsa kowacce kafar magudanar jini da ɓargon mutum kafin a hankali ta fara bashi nutsuwa.
      Wani irin mugun ƙanƙamesa tayi jikinta na rawa. Harma ya zare allurar yana murza mata wajen bata dawo hayyacinta ba. Bakinsa ya janye a cikin nata a hankali yana sauke wani wahalallen numfashi da gajerun ajiyar zuciya a jere. Itakam kuka ta fashe da shi jin ta samu bakinta, sai ƙara ƙanƙamesa take kamar zata koma masa ciki saboda yanda zafin allurar ke gauraye duk jikinta. Haɓarsa ya ɗaura saman kanta yana ɗan murmushi da lumshe idanunsa. Hannayensa a bayanta yana shafawa a hankali alamar lallashi.
     Sun sami tsahon mintuna biyar a haka sannan ta tureshi da ƙarfi tana janye jikinta baya. Cikin kuka kashirɓan tace, “Wlhy sai ALLAH ya mana hisabi da kai tun a duniyarnan tasa. tunda ai cakai idan naci abincin bazaka minba shine ka karya alƙawari. Na rantse saina faɗama Abbana” ta goge bakinta da bargo tana cigaba da faɗin, “Ƙazami kawai mayen bakin mutane”.
        Shi dai komai baice mataba. Kallonta kawai yake da narkakkun idanunsa masu cikar gashi da haske. Tana cigaba da masifarta da goge baki yaga ta fara ajiyar zuciya da lumshe idanu alamar gyangyaɗi. Basuyi mintuna bakwai ba a haka ta ɓingire barci. Kansa yaɗan girgiza kawai. A kan laɓɓansa ya furta “Yeyyey girl, mai bakin tsiwa”.
      Sauka yay daga kan gadon ya zagaya ɗayan gefen gadon data koma tun turesa da tayi. Kwanciyar ya gyara mata, ya fara ƙoƙarin zare hijjabin jikinta. Amma kasancewar barcin baiyi nisa ba, sai ta shiga ture masa hannu cikin kasala irin ta mai barci. Durƙusawa yay gaban gadon ya riƙe hannun nata cikin nasa. idanunsa ƙyam akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta da komai ya dace da ita. Bata zare hannun nataba daga cikin nasa tabbacin barcin ya fara nauyi. Sai ajiyar zuciya da take faman saukewa a jajjere. Sai da ya ƙara bata mintuna kusan uku kafin ya kai dubansa ga hannunta data matse nasa. Zanen ƙunshin ya ringabi da kallo yana ɗan murzawa da babban yatsansa a hankali, abin ya masa ƙyau sosai, sai dai a ƙasan ransa tunani yake badai tattoo bane ba?. Jin ta ɗan motsa ya juyo ya kalleta. Yanda ta wani taɓe baki a cikin barcin kamar zatai kuka sai abin ya so bashi dariya. A fili ya furta “Trouble maker” yana lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta.
       Gudun kar hijjabin ya shaƙeta ne ya sashi cire mata shi cikin dabara. Sai kuma yaci karo da bata da riga sai zani data ɗaura. Kallo ɗaya yay mata ya janye idanunsa yaja bargon ya lulluɓa mata.
       Oho, ita dai duk batasan yanayi ba, barcinta take zazzaɓin na sauka mata a hankali. Sai da ya gama bin ɗakin da kallo tsaf sannan ya fice a ransa yana yaba ƙoƙarin iyayenta. Dan ko kujerun da aka zauba musu a falon yasan kuɗi sosai aka zuba wajen sayensu.
    
________★★★_______

       A kano ta dabo kam baƙi sun isa gida lafiya da shatara ta arziƙin da suka samu. yanzun kam gidan ya koma shiru duk baƙi sun kama gabansu, hakan yasa suma duk basu wani yi zaman awa bibbiyu ba a gidan duk suka tafi. Sai Ananah kawai da ba yaune ranar tafiyar tataba ita. Amma jikokinta da sauran ƴaƴanta duk sun koma katsina tun jiya...........✍


_Kuyi manage da wannan bajin daɗin jikina nakeba, mura tamin ram🤦🏻_.


Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 47


________

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p.

     INA MA’ABOTA KARATUN LITTATTAFAN HAUSA? WANDA ZAI NISHADANTAR DAKU, YA FADAKAR, YA KUMA TSUNDUMA KU A KOGIN LOBAYYAR KAUNA? TO KU MATSO KUSA... DOMIN MUNZO MUKU DA ALBISHIR DIN WANI GANGARIYAR LITTAFI.. DAYA NE TAMKAR DA DUBU.. YAZO DA WANI SALO NA DABAN WANDA ZAI SANYAYA ZUKATAH.._

_LITTAFIN *UNCLE NE...* LITTAFI NE FIRST OF ITS KIND, DA YAZO A WANNAN SHEKARA TA 2021. AN BAJE KOLIN BASIRA A BOOK DIN UNCLE NE.._

_”Wait... Dakata hafsat Rano, Kina nufin NIMCYLUV, dai shararriyar murubuciyar nan itace tazo da wani salon rubutun..?..”_

_”Kede bari Billyn Abdul.. Tsaya kiji kanun labarin a tak’aice..*NIMCYLUV* Tace book din a ta’kaice labarin *UNCLE NE* ne yana tafe:_

_Da farko yana mata kallon uwa wacce ta haife shi kuma jigon rayuwarsa, ashe itace silar rushewar rayuwarsa😢yarinyar da yakewa kallon ƙanwa uwa ɗaya Uba ɗaya ita aka wayi gari ta zama MATAR SA🙆🏻‍♀️ ƙaddara ta haɗashi da (Ahlil kitab) kiristan ya bata farin ciki, kulawa, soyayya, harya samu ta musulunta, Dalilinta sbd al'ƙawarin aure da yyi mata,ashe ba sonta yake ba🤔yaje birnin NUFAR domin kai masu tayin Muslunci, sun amince da hakan amma sharaɗin dole ya kwanta da ƴarsu,🤦🏼‍♀️gashi bashi da cikakkiyar lfy mazantakarsa bata aiki😫 ashe mahaukaciya ce ta haife shi.._

“_Kai lalle akwai runguntsumi acikin wannan littafi..  Ba za’ayi babu ni ba, Domin Za’a sha lagwadar romon dadi. shin tayaya ake biya Hansatu?_”

_”Ai ta Abdul..LITTAFIN *UNCLE NE* Naira 300 ne, Idan kuma kana son vip inda za'a ake posting sau biyu a rana kuma za'a baku littafan data rubuta na kuɗi sai ka bada 600 mai ma kon 1k.. number asusu wato bank account details: 0116886423 : account name sulaiman Na’ima S. Bank name: unioun bank: Sai a tura shedar biya ta 08119237616... A nuna mata ƙauna ta hanyar turowa ta account🤲🏻kamar yadda Za’a  faranta maku a littafin UNCLE NE_
_(Best romantic love story of the year//Had’adden labarin kauna na shekarar 2021)_



No. 47

...........Sosai Nu'aymah tasha barcinta. Dan sai gab da la'asar ta sake farkawa. Yanzun kam Alhmdllh garas take jinta, sai dai jinta take wata fiyau tamkar iska zata ɗauketa ta yada saboda rashin nauyi. Wanka ta fara yowa da alwala. Tazo tai salloli sannan ta kimtsa ɗakin duk da bayyi wani datti ba. Tunda ta buɗe kwanikan dake saman tray ɗin da ke bisa centre table sau ɗaya bata sake ba. Sai ƙunƙuni da ta dingayi akan ita bazataci wannan jagwalgwalon abincin ba yasin. Dan duk da uban naman dake cikin miyar baiko birgeta ba.
         Tsaf tai shiri cikin riga da sket na atanfa. Kayan sun mata ƙyau sosai. Tana cikin saka turare aka turo ƙofar. Saurin juyawa tayi danjin babu wani knocking balle a kai ga sallama. Haushi ya tuƙeta ganin Yoohan ne. Ta ɗauke kanta tana ɓata fuska. 
        Yoohan da waya ke manne a kunnensa alamar magana ya keyi da wani shima ɗin dai kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa, zama yay a kan sofa ya cigaba da sauraren abokin wayar tasa dake masa bayani daga can. Ita Aymah ma harta fara tunanin ko wani sabon wulaƙancine ba wayar yake ba. Dan ya kusan mintuna sha biyar wayar na kunnensa amma baice komaiba.. Dai-dai ta ɗago ta kallesa taji ya ɗan sauke numfashi, sai kuma ya fara magana a hankali cike da nutsuwa. Harga ALLAH bazata ɓoye ba muryarsa na mata daɗi. Ita bata buɗe yanda zaka tsorata mai sauraro ba, ba kuma ta sirance kamar ta mata ba. Tana fita da kauri da amo musamman daya kasance shi ma'abocin magana ne a nutse.
       Haka ta dinga satar kallonsa harya kammala wayar. Ya cire daga kunne yana ɗago idanumsa kanta. “Am sorry, Assalamu alaiki”. Ya faɗa yana janye idanun kanta lokaci guda. Amsa masa tayi fuska a tsuke, kamar zata ɗauke kanta sai kuma ta sake dubansa. “Nifa yunwa nakeji”.
       Da mamaki ya kalleta, sai kuma ya duba tray ɗin dake a jiye a wajen. Tabbas bana safe bane. Kulolin ya buɗe batare da yace mata komaiba. “Shi wannan abincin kuma fa?”. Ya faɗa yana kallonta. Baki ta kunbura tana wani sake tsuke fuska, “Yoni bazanci wannan abincin ba, dan ban iya cinsa ba”.
       Shiru ya ɗanyi yana kallon abincin shima. Eba ne da wata miya da suke kira Abak Atama soup (miya ce da mutanen Akwa ibom state suke yinta) taji uban nama sai ƙamshi takeyi. Tabbas yasan da wahala ta iya ci ɗin, tunda abincine irin nasu. “Mi zaki ci to?”. Yanda yay maganar a daƙile ne ya sakata sake jin haushinsa, tai masa harar gefen ido. Kamar bazata faɗa ba sai kuma tace, “Noodles”.
            Batare da ya ƙara kallonta ba ya ɗauka waya yay kiran Joy. Ring biyu kuwa ta ɗaga. Ko gaisuwar datai masa bai amsa ba yace, “Dafa min Noodles”. Daga can tace, “Okay Brother, and egg?”. Bai amsata ba, sai duban Aymah da yayi, wadda ya tabbatar tana jinsu tunda a Hans free ya saka. Kanta kawai ta ɗaga masa ta ɗauke idonta daga garesa. Amsa ya bama Joy ɗin da faɗa mata inda zata kawo ya yanke wayarsa.
        Daga haka ɗakin ya ɗauki shiru, shi dai wayarsa ya keta latsawa, ita ko tana zaune a stool ɗin mirror ne kawai tana kallonsa ta ciki fuska a kumbure. Ba komai ke cinta ba sai kewar gida da yunwa. Damuwace fal ranta, a kallo ɗaya kuma zaka tabbatar da hakan.
      Knocking ɗin da akayi ne ya sakashi faɗin “Shigo” a taƙaice batare da yako ɗago daga abinda yakeyi ba. Gabansa Joy taje ta ajiye tiren batare data kalli inda Aymah take ba, “Broth gashi, nikam inata mamaki, wai kai ne da cin Noodles yau a gidannan?”.
       Wani mugun taɓe baki Aymah tayi ta ɗauke kanta daga kallonsu, a ranta kuwa rayawa take saita saita kan joy ɗinnan a layi idan har tace zatai mata hauka. Dan duk da ta girmeta sosai ai ita yanzu matar yayanta ce dan ƙaniyarta. (Madam son girma😚lol).
          Yoohan kam da ya gama sauraren Joy a taƙaice yace, “Thanks”. kawai. Duk da Joy tasan halinsa, ba kuma yau ne farauba sai na yau ɗin yay mata zafi saboda agaban Nu'aymah ne. A hasale ta nufi ƙofa tana harar inda Nu'aymah take. yanda ta fisgi ƙofar ɗakin da zata rufe ne ya sakashi ɗagowa, sai dai kafin yace komai ta bar wajen da gudu.
        Shiru yay baice komaiba, sai idanunsa daya maido kan Nu'aymah. “Kizo kici zamuje ki gaida Momy da Papa”. Batare data dubesa ba tace, “Badai mai wancan zaƙo-zaƙon farcen bace ta dafa min ko?”. Yanzun kam sosai Yoohan yake kallonta, a ransa yake faɗin, ‘Yarinyar nan muguwar ƴar matsala ce wlhy’. A fili kam fuska ya ƙara tsukewa yana tsatstsare ta da idanu. “Kina ɓatamin lokaci malama, inada abu mai muhimmanci a gabana”. Kanta ta maida gefe tana ƙyaɓe baki, cikin ƙunƙuni da hausa tace, ‘Da waye ya gayyatoka anan balle ka ɗagan hanci’. Ta ƙare maganar tana tasowa inda yake. dan harga ALLAH wata shegiyar yunwa kecin hanjin cikinta.
         Shikam baima sake bi takanta ba, ya cigaba da sabgar gabansa a wayar. Ba ƙaramin danne zuciya Aymah tayi ba wajen zaman cin indomie ɗin nan. Dan babu abinda ke zuwa mata a cikin rai sai farcen dake a hannun Joy zaƙo-zaƙo da tarin gashin dokin da akai mata kitso da shi kamar jikar bammali. Ko rabi kuwa bataci ba ta ture gefe.
         Kallonta yay fuska a tsuke, cike da ƙosawa yace, “Wazai ci miki wannan ɗin?”. “To oho, ni dai na ƙoshi, yama zaka saka wancan mai farcen da Attachment ɗin kamar ɗiyar bammali taimin girki. Wanda naci ma da wahala ya zauna dan amai nakeji dana tunota. Ga uban bleaching tayi sai ƙarni takeyi”.
         Sosai yaji zafin abinda take faɗa akan ƴar uwarsa, amma sai yake mata uzirin ƙuruciya ce kawai ke ɗauwainiya da ita. Watsar da ita yay bai sake duban ko inda take ba har tsahon mintuna uku. Kafin ya miƙe yana zura wayarsa a aljihu. “Muje” ya faɗa a taƙaice yana yin gaba abinsa.
        ‘Tab! Wai kaji haushi ne dan na faɗa abinda ke raina? Aiko aiki ya sameka, dan bazan ga abin maganaba nai shiru bakina yay wari. Da wani kansa kamar mulmulen furar hajjo’. Tai maganar tana miƙewa. Dan itama zaman ɗakin ya fara isarta kuma. Tanason taga gidan yaya yake?. gyale ta ɗauka da yay dai-dai da atanfar ta biyosa. A falo ta samesa tsaye, batare da yayi magana ba yay gaba ta bisa a baya suka fice.
    
       Tun daga bakin ƙofar sashesa take ƙarema gidan kallo, babu ƙarya gidan ya haɗu, musamman idan kana sama kake kallon tsarin falon ƙasa. Hakama idan kana a ƙasa kake kallon upstairs ɗin. Ga koma tsaf babu wani datti alamar dai ana kula da tsaftar gidan yanda ya kamata. A yanzu haka ma'aikatan gidan daketa shara da goge-gogen yamma sai risinawa suke suna gaishesu. Shi kaɗai yake amsawa. Ita kam binsu kawai take da kallo da takaicin ganinsu ƙattan maza.
            Ta saman upstairs ɗin suka nufi sashen Momy dake jikin na papa. Corridor ne mai ɗan faɗi da ƙofofi uku a cikinsa. saɓanin Nasu da zaka iske falo. Knocking ɗin ƙofar tsakkiya yayi. Daga ciki wata murya ta amsa. Juyowa yay ya ɗan kalleta sannan ya tura ƙofar. Ita dai biye take da shi. Yanda taji yace, “Excuse me” itama Excuse me ɗin tace a hankali.  
       Murmushi madam Chioma dake waya da ƙawarta tana bata wasu dabaru ta saki saboda ganin rabin ranta. A yau ɗin nan duk da zafin zazzaɓin nan da takeji sai taji a ranta garama da take yinsa. Dan koba komai a dalilin zazzaɓin ta samu kusanci da lokacin yaronta mai tsaho tare da ita. A gaba ɗaya yinin yau sai zirga-zirga ya keyi a kanta da son ganin jikinta ya dai-daita. Ɗazuma da taita langare masa yafi awa biyu zaune tare da ita.
       A hankali kuma sai fara'ar fuskar tata ta fara gushewa saboda ganin abinda ke a bayansa.......
       “Masha ALLAH Mom sauƙi yazo sosai” ya faɗa yana zama a gefen gadon nesa da ita kaɗan batare da ya lura da canjawar fuskar tata ba. Nu'aymah kam dake mata kallon ƙasan ido taga komai da madam Chioma tayi, murmushin farko da canja fuskarta da tai saboda ganinta. Dai-dai Aymah na zama bisa sofa ɗin ɗakinne Momy ke bama Yoohan amsar maganarsa. “Ƙarfin haline kawai my boy, dan dana tashi ma kamar zan kiraka kazo ka sake dubani sai nayi tunanin ko baka a gidan ne?”.
      Ɗan murmushi kawai yayi batare da yace komai ba, saboda gaisheta da Nu'aymah keyi. Shiru tayi kamar bazata amsaba, ita kuma Aymah daga gaisuwar nan guda ɗaya bata sake wata ba.
     “Mom tana gaisheki fa”. Ya faɗa yana kallonta. Daburcewa ta nema yi, dan batai zaton zai saka baki ba. Cikin kame-kame tace, “Oh Daughter Am sorry, hankalina nakan Son, kina lafiya?”. Cike da mamakinta Aymah tace, “Alhmdllh” daga haka taja bakinta tai tsit fuska babu walwala. Itama Madam Chioma bata sake bi takan Nu'aymah ba. Gaba ɗaya hankalinta naga Yoohan. Sai takalarsa da zance take yaƙi magana ƙwaƙwƙwara, daga guntun murmushi sai um sai a'a. Ita Aymah ma abin dariya yaso bata. A ranta sai gulmar ɗan da uwar takeyi tana kwasar dariya. A fili kuwa fuskarta babu ko ɗigon walwala a cikinta. Ta tsume abinta kamar tama manta da su a ɗakin.
             Sosai Yoohan yake lure da ita, amma idan ba shiba bazaka taɓa fahimtar hankalinsa na gareta ba. Agogon hannunsa ya kalla yana faɗin, “Momy bara muje ta gaida Papa nasan ya shigo yanzun”.
        “A to muje sai na rakaku ai” ta faɗa tana miƙewa. Da sauri Yoohan yace, “Haba Momy, keda ke fama da kanki”. “Karka damu ai da sauƙi” ta faɗa tana bin bayan Aymah da tunda ya ambaci tafiyar har ta kai ƙofa. Bayansu kawai yabi yana mamakin halin Momynsa. 

        Koda suka fito Aymah tsayawa tai baya suka wuce gaba tunda sune ƴan gida. Sun shiga sashen papa dake da falo babba, dan har yafi nasu girma ma. bata cuci kanta ba, koda suka zauna sai da ta ƙarema kowace kusurwa ta falon kallo lokacin Momy ta shige bedroom ɗin papa dan basu sami kowa a falon ba. Yoohan kuma yanata latsa waya.  
         Lokacin da suka shigo shima papan ta ƙasan ido ta gama ƙare masa kallo tsaf. Shima ƙyaƙyƙyawa ne kuma fari, dan suna kama da Yoohan, sai dai Yoohan ya fisa ƙyau da ƙwarjini da ƙuruciya. Da alama dai Yoohan ɗin ya kwaso kamannin wanu bayan shi. Papa na zama Aymah ta zamo ƙasa ta zauna. Ba Yoohan ba har Madam Chioma hakan da Nu'aymah tayi ya bata mamaki. A ranta kuwa ayyanawa take, ‘Wato ni wannan ƴar shilar yarinyar ta raina kenan?, ina zaune sama tana zaune itama a ɗakina’.
       Maganar papa ce ta katse madam Chioma. Cikin fara'a sosai yake amsa gaisuwar da Aymah ke masa, harda haɗawa da ƴar tsokanarta. Itako tanata zuba murmushi kanta a ƙasa. Tambayoyi ya rinƙa mata dake nuna kulawarsa a gareta. Hakan ne ya sakata ɗan sakin jiki da shi tana bashi amsar da duk ya buƙata.
     Shi dai Yoohan ma abin sai ya bashi mamaki, dan koshi bata sakin jiki da shi kamar hakan. Papa daketa murmushin jin daɗin yanda Aymah ta saki jikinta da shi ya dubi Momy yana faɗin, “Darling a tattaro min duk members na gidan nan da masu aiki, zan gabatar musu da daughter in-low ɗina. Itama na gabatar mata da su.
         Cikin ɗan yatsine fuska madam Chioma ta miƙa hannu ga wayar landline dake a table ɗin jikin kujerar da suke zaune ita da papan ta hau danne-danne. Kira tayi, bayan an ɗauka daga can tace, “Joy, ki sanarma kowa na gidan nan yazo Master parlor yanzun nan”.
        “Okay maa!” 
Joy ta amsa daga can tana ajiye wayar.

       Cikin mintuna ƙalilan kowa ya shigo falon, hatta da maigadi bai zaunaba, kulle gate ɗin yayi ya taho. Shi dai Yoohan kamarma baya cikin falon. Babu wanda ya damu da shariyar tasa tunda sunsan halinsa kenan. Victoria ce ma uwar surutu taje jikinsa zata zauna ya harareta. Da sauri ta canja mazauni tana tura baki gaba na shagwaɓa.
       Sai da kowa ya nutsu sannan papa ya fara magana. “Na taraku anan ne domin na sake tabbatar muku da ƙaruwar member da family ɗinmu ya samu duk da nasan kun sani. Karku ganta ƴar ƙarama kuce zaku ɗauketa ƙasa da ku, har wani raini ko abu mara ƙyau ya faru a tsakaninku. Duk wanda ya aikata hakan zan saɓa masa da saɓawa mafi ciwo. Dolene kowa na gidannan idan ka cire su mama da Darling dake matsayin kakanni a gareta da Uwa kowa ya bata girmanta. Saboda mata ce ita a wajen John, kowa kuma yasan a gidan nan bayan ni John shine uba, dan shine babban ɗana abin alfaharina. Sunanta Zainab, amma ana kiranta Ayimah. My daughter ko ba haka bane?” ya ƙare maganar yana kallonta. Murmushi Aymah tayi, batare data ɗagoba ta gyara masa da cewar, “Nu'aymah”. 
       Sake maimaitawa yayi duk da dai yanzunma bai faɗa dai-dai ba. “Nasan dai baku manta da sharaɗin John ba. Zainab ɗago kanki zan nuna miki kowa da sunansa anan kema”.
     Babu musu kuwa ta ɗago, dan ganinsu cike da falon baisa taji ko ɗarba a ranta saboda tun fil azal ita ALLAH yayita mutum mara tsoro. “Wannan itace mamana sunanta Mama debora. Itace ta haifeni tare da ƙannena. Maza mu uku, mata su biyu. Gasu nan”  ya nuna ƙannensa biyu mata dake zaune a wajen. Maman Favour, da maman Destiny. “Akwai maza biyu suma zan nuna miki su idan sunzo. Sai wannan itace Maman Darling. Momyn John kenan gata nan” ya nuna madam Chioma da mamanta. Daga haka ya dawo kansu Joy, Gebrail, Abraham, Victoria ƙannen Yoohan kenan. Sai Miracle ɗiyan ɗan uwansa Uncle Mike. Sai Aunty Blessing kuku, daga haka ya koma kansu Solomon daki-daki da ayyukansu a gidan duk ya sanar mata har zuwa kan maigadi.
      Cikin murmushi tace, “Nayi murnar haɗuwa da ku duka”.
        A tare suma duk suka amsa mata da hakan, duk da dai da yawansu ba har cikin zuciya bane ba. Sun faɗane kawai saboda tsoron Yoohan da duk abinda sukeyi yayi kamar baya falon. 
  
       Sallamar ma'aikatan gidan ya farayi, kafin ya sake duban family nasa ya shiga musu nasihar zaman lafiya (Su papa kenan😂lol). Daga haka ya sallami su Miracle ma daketa antayama Aymah harara ta ƙasan ido ita da joy. ya rage daga shi sai su mama debora da su maman Destiny. A gabansu ya fiddo keys ɗin mota guda biyu ya miƙama Nu'aymah ɗaya.
      “Dota wannan shine wedding gift ɗinki daga ni. Kai ma John ga naka. ALLAH ya sanya muku albarka a cikin aurenku”. Da hannu biyu Aymah ta amsa bayan taje gabansa ta durƙusa. Tai masa godiya sosai. A ranta kuma tana addu'ar ALLAH ya shiryesa idan yana da rabo, idan baida kuma ALLAH yay maganinsa. Shima oga Yoohan ya amshi nasa. Tare da rungume papansa yana mai nuna masa jin daɗinsa da waɗannan ƙyaututtuka shi da matarsa. Buɗe masa hannaye madam Chioma tayi wai itama ya bata hug.... Kafaɗa ya maƙale mata yana faɗin, “Sai kin bamu naki gift ɗin sannan”.
       Kusan a tare duk falon akai dariya. Banda Aymah da sam abin ita bai birgeta ba. Dan haka kawai madam Chioma duk da mahaifiyar mijin nata ce batai mataba ko kaɗan. Su mama debora ma duk sun bama Yoohan ƙyauta, amma basu bama Aymah ba. Ko a jikinta ita kam, dama bata buƙata. Ganinma lokacin salla yayi saita miƙe tana faɗin ita zataje tai salla lokaci yayi.
        Papa ne kawai ya amsa mata. Sai Yoohan da ya bita da kallo saboda ganin yanda tai maganar kanta tsaye babu wani inda-inda a ciki. Harga ALLAH ta birgesa, dan da watace sai tai ta nuku-nuƙu musamman data san su ɗin sun rinjayeta a gidan.
       Ko kallon inda yake bataiba tai ficewarta, dan tasan zata gane hanya abinta. Acan downstairs ta hango su Miracle sun baje suna kallo, ta girgiza kai da taɓe baki tana faɗin, ‘ALLAH ka rabamu da gafalalliyar rayuwa dai’.
       Sai da ta tsaya a falon ta gamai masa kallon tsaf tana jinjina yanda ya haɗu, da jin ƙaunar iyayenta. Ganin zata makara salla ta nufi hanyar bedroom. Tana buɗe ƙofar zata shiga aka buɗe ta falon. Kallon inda ƙofar take tayi, ganin shine ya sakata ƙarasa shigewa batare data nuna alamar tasan da shigowar tasa ba. A fili ta furta, ‘Ai nazata tuban mazuru kayi, bazaka taso kayi sallan ba’.
         Oho, shidai baisan tanayi ba. Dan ɗakinsa shima ya shige kai tsaye dan gabatar da sallar, tunda an ja masa makara bai tafi massallaci ba.

________★★★★________

          “Wai nikam murmushin mi kike tayi hakane Jannat? Tun jiya ina lura dake Murmushin nan ya kasa barin ƙyaƙyƙyawar fuskarnan taki”.
      Murmushin Umm ta sake yi tana kallon mijin nata da take ɗunbin so da ƙauna. Sai da ta miƙa masa kofin ruwan data zuba masa kafin tace, “Wlhy idan na tuno Nu'aymah tabar gidan nan sai naji wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali. Duk da ina fargabar inda ta tsinci kanta kuma a yanzu. Sai dai inaji a raina bazata bari a cuta mataba acan tunda tasan suɗin su wanene. Amma a gidan nan da bakasan wanene mai SARAN ƁOYE ba tayaya zakai taka tsantsan da al'amarinsa. ALLAH ya ƙarama Hajjo tsahon rai da nisan kwana. Dan nasan ita ɗin babbar garkuwa ce a garemu a gidan nan. Kaga yanzu saimu gani, yarinyarmu ce ba'a buƙata a gidan? Komu kanmu ne?”.
       “Gaskiyarki Jannat, koni inajin nutsuwa ta musamman a zuciyata tun bayan ɗaura auren mamana. UBANGIJI shine masani akan wannan auren na Yahya da mamana ya ƙumsa. Dan maybe da ɗaya daga cikin su Abdallah ta aura salamar da muke mata fata bazata taɓa samunta ba. Sai ma wasu sabbin fitintunu ne zasu cigaba da bayyana ƙilama har sai mun rasata gaba ɗaya. Amma kinga a yanzu aurenta da yaron nan zan jefa tsuntsu uku ne da dutse ɗaya”.
       “Tsuntsu uku kuma Abban Nu'aymah?”.
     “Ƙwarai kuwa Jannat. Na farko zan ƙara ƙarfafa gwiwar Yahya akan musulinci, zata taimakesa akan dukkanin ilimin da yake buƙata na sanin musilinci. Na biyu Mamana zatayi ibadar aure, ta kuma samu lafiya da kulawa mai inganci akan lalurarta. Na uku zataimin wani aiki da zuciyata ta kasa daina min kokwanto a kansa. Maimakon inji na ajiye batun, kullum sai sake jin ƙwaɗayin tabbatar da gaskiyarsa nakeyi”.
        “Ikon ALLAH, Abban Nu'aymah minene shi kuwa wannan al'amari?”.
       “Zan faɗa miki shi Jannat, ki bani lokaci na gama neman zaɓin UBANGIJINA akansa sannan”.
        “To UBANGIJI yayi jagora Abban Nu'aymah, ALLAH kuma ya tabbatar da alkairi a cikin al'amarin”.
       “Amin ya rabbi Umm-Muhammad. Yanzu yaya batun mai aikin da mamana ta buƙata?”.
        “Karka damu za'a nema insha ALLAH, bandama rigima irin tata mizatayi da wata ƴar aiki tunda nasan can gidan bazasu zauna babu ma'aikata ba”.
           “Eh duk da haka dai a nema mata. Koba komai zata samu yarenta a cikinsu, ko wani abinne ya dameta ta faɗa mata kafin mu mu sani. Shiyyasama nake ganin ko haƙura zakiyi ki bata Rabi'atu, tunda kinga ta saba da ita sosai, akwai shakuwa tsakaninsu sannan itaɗin ba yarinya bace zata taimakamata da shawarwarin zaman rayuwa”.
         “To banƙi ta taka ba Abban Nu'aymah. Sai dai kasanfa ko sanda Nu'aymah na gidan nan ba shan inuwa ɗaya sukeyi da Rabi ba. Inaga ka fara tambayarta idan tanason a bata ita sai taje. Idan bataso sai a aika mata wata ɗin. Dan kasan halin butsutsun yarinyarka ɗin nan ba man kai ne da ita ba sam”.
         Dariya baba malam yay tayi da zancen matar tasa. Daga haka suka cigaba da firarsu duk kusan kashi biyu na firar akan Nu'aymah ne. Da kaji kasan cike suke da kewar ɗiyar tasu da begenta. Sai dai dattakonsu ya danne komai suna binta da fatan alkairi a zuci da fatar baki.....

*_ABUJA_*

            Nu'aymah bata sake ganin Yoohan ba ko wani a jama'ar gidan har washe gari. Dan tunda ta shiga ɗakinta bayan barowa wajen su papa saita kulle harda murza key. Littatafan ta na islamiyya da aka zubo mata cikin kaya ta ɗauka taita dubawa a hankali har lokacin barcinta yayi ta kwanta.
          Washe gari tunda tayi sallar asuba bata koma ba. Gyara ɗakinma tayi har toilet, rashin sabo da zaman ya sata sha'awar fitowa falon shima dan ta ɗan gyara ko ta ƙarajin ƙarfin jikinta ta kuma ɗan rage kewa. Tana buɗe ƙofar ɗakin nata shima yana buɗe tasa ƙofar............✍
     
      
yanzu haka an kusa kai ƙarhe, gamai buƙata zai iya garzayawa ya biya😋😋😋.

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

NO. 48

___________________

I'm on Instagram as yerwaincense_and_more. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ayfowzb2ah8k&utm_content=6k8ur6p

_YERWA INCENSE AND MORE _
_(Masarautar K’amshi)_

_We’ve got you covered with our balsamic scented products.. Yerwa scents last longer and linger.. Ba kauri irin na wa’ensu turaren, Chadian kamshi ne na gaske, Kowane irin samfurin turaren wuta munayi, traditional and modern. _

_Akwai Khumrah’s kala kala. Kulaccams, Turaren wanka dana wanki dana mopping, Da tsugunno, Jiki da kaya duk muna dasu. Domin mallakar naki tuntub’e ta number shafin dake kasa, Ko kuma Ki duba shafin mu na manhajar Instagram ta: @yerwaincense_and_more. _

_Kyau, arha, inganci , sai yerwa incense. Muna tura kayanmu ko’ina a fadin nigeria da waje.. Ayi following, Da liking dinmu a Instagram handle dinmu dake sama._


No. 48

..............Kallo ɗaya tai masa ta kauda kanta. Dan daga shi sai wando gajere fari dako cinyoyinsa bai gama rufewa ba. Sai singlet kalar gwaiduwar ƙwai hannunta mai faɗi fiye dana singlet data sani. Shikam dai kansa tsaye yake ƙare mata kallo cikin kayan barcin wando da riga pink masu taushi. Duk da basu kama mata jiki ba sun mata ƙyau, musamman daya kasance kanta ko hula babu. Gashin dake a ɗaure a tsakkiya duk ya zazzame a gaba ya tashi. 
      Cike da ƙosawa da kallon ƙurillar da yake matan tace, “Good morning”. Kamar dama abinda yake jira kenan. Ya janye idanunsa daga kanta yana sakin handle ɗin ƙofar da faɗin, “How are you feeling now?”. “Alhmdllh”. Ta amsa dai-dai lokacin da yake tura glass ɗin dake bangon kudu a falon ƙofa ta bayyana. Ita duk zatonta ma an sakashine kawai domin ado. Amma sai taga ya shige ƙofar ta koma da kanta ta rufe. Shiru tayi tana ta kallon wajen kamar wata sokuwa.......
       “Good Morning Maa!”.
   Aka faɗa a bayanta. Da sauri ta juyo danjin muryar gardi. Solomon dake ta wani ɓata fuska yay saurin sunkuyar da kansa ƙasa bayan ya gama ƙare mata kallo tun shigowarsa. Wani irin mugun takaicine ya turnuƙe Nu'aymah, taya ƙaton banza da shi zai shigo musu babu wani neman izini. Lallai dolene ta saitama ma'aikatan gidan nan zama, dan bazata ɗauki wannan iskancin ba sam. Da ƙyar ta iya haɗiye bala'in dake a harshenta. Murya a daƙile tace, “Ince dai lafiya?”. “Yes maa! Zanyi sharane. Dan nine mai yima oga gyara”. ‘Zan saita muku layi kai da ogan ai’ ta faɗa da hausa tana zuba masa harara kamar idanunta zasu faɗo. Shi dai Solomon bai ji mita faɗa ba, amma yana kallon harar da take zuba masa. Kuma harga ALLAH sai yaji wani irin shakkarta da ganin ta cika masa idanu da kwarjininta duk da kuwa inda aure yayi sai ya haifi wadda ta fita ma.
       “Kaje bana buƙatar sake ganinka ka shigo mani nan, ka ajiye min kayan sharan hannuna zai iya yin komai”.
      “Okay maa! I'm sorry”.
Banza tai masa, sai harar da taketa cigaba da antaya masa hannayenta riƙe da ƙugunta kamar mai shirin yin dambe. Kamar walƙiya Solo yabar falon. Ta dafe goshi cike da takaici. ‘Shegu dangin ƴan sama jannati, duk saina muku sabon kaciya tunda idonku bai iya daina kallon mutane. Yanda kasan mayu, suyi maka ƙuri da idanu’.
          Haka taita banbamin jaraba ita ɗaya kamar wata zararriya. Ta gyara falon tsaf harma kitchen da ba komai aka taɓa yi aciki ba. Ta kwaso turarenta na ƙamshi haɗin da miss xoxo tai mata ta baje ko'ina da su, (Da gaske masoya, duk mai buƙatar turarurrukan su khumrah da makamantansu ya tuntuɓemu zai samu. Kuma a kowane gari kake muna aika kayanmu insha ALLAH) sannan ta ɗora da Air Fresheners ɗin data gani. Yanda gidan ke tashin ƙamshi tuni zai saka ka barci baka shirya yi ba. Yunwan da takejine ya sakata nufar inda taga an shirya kayan tea cikin wata drawer glass dake a dining ɗin. Sai da ta gama ƙarema kayan shayin kallo da su biscuits dake ciki kala-kala, sai su cornflakes, gyaɗa soyayya a cikin kwalabe, dabino, zuma, kayan ciye-ciye ne dai iri-iri wasuma ko ganinsu bata taɓa yiba. ‘Oh ALLAH, amma guy ɗinnan mugun makwaɗaici ne yasin. Kaga yanda ya haɗa kayan ƙwalama kamar wani sa'an Muhammad. Amma dai anji jiki yasin’. Tana mita tana zagurar waɗanda ta gani a buɗe tana jefawa a baki (makwadaitan sun ƙaru kenan😂lol).
      
★★

         Sosai Solomon yaji zafin abinda Aymah tayi masa, ya kuma ɗauki alwashin sai ya saita ta a layi duk da matar ogansa ce. Da wannan takaicin yaje kitchen ya amshi tatattun kayan itatuwan Yoohan ɗin a wajen Blessing data kammala haɗawa. Ta waccan ƙofar yabi ya shiga Gym ɗin. Inda ya tarar Yoohan ko rabin motsa jikinma baiyi ba. “Good Morning sir”. Ya faɗa ransa har yanzu najin zafin Aymah. “Morning?”. Yoohan ya amsa masa yana dubansa da tunanin ko baida lafiya ne. Yanzun ma cike da ɗacin murya yace, “I'm Good sir”. Komai Yoohan bai kuma ce masa ba. Ya cigaba da harkokin gabansa har ya kai lokacin da yake tsayawa. Towel Solo ya miko masa. Amsa yay yana furzar da huci ya ƙarasa kujerar zamansa ya zauna. Solomon ya karaso ya miƙa masa juice ɗin. Sannan ya ɗauka remote ya kunna television.
       Sai da Yoohan ya sha kusan rabin juice ɗin, hankalinsa nakan program ɗin yace, “Ka bama su SJ kayan dana ce?”. “Sir wane kaya? Bansan ka ajiye kaya na basu ba ai”. Da mamaki Yoohan ya juyo ya ɗan kallesa, sai kuma ya maida ga television ɗin yana faɗin, “Baka gyara min ɗaki ba kenan?”.
        A take abinda Aymah tai masa ya dawo masa a rai. Murya a cinkushe yace, “Sir naje zan gyara Madam ta hanani. ta kuma min gargaɗin ma karna sake shiga sashen gaba ɗaya”.
      “Madam? Wace madam?”. 
Yoohan yay maganar da tsatstsare sa da idanu. Kan solo a ƙasa yace, “Madam Nu'aymah”. A take ya zayyane masa duk yanda sukayi da Aymah kafin yazo nan wajensa. Ya zata zaiga ɓacin rai tattare da ogan nashi, dan ya saka aiki aƙi masa ko wani ya hana a masa yana ɗaya daga cikin abinda ya tsana, ko madam Chioma ce sai ya nuna ɓacin ransa koda ba zaiyi magana ba. Amma a mamakin Solo sai yaga Yoohan ɗin yayi wani ɗan munafukin murmushi yana ajiye kofin hannunsa. Batare da yace komaiba ya shiga zare takalman ƙafarsa. Yana kammalawa kuma ya miƙe ya fito solo na binsa da kallon tsoro dan ya wuce na mamaki kam.

          Har yanzu Aymah na a falon, dan tsabar ƙwarewa a ƙwaɗayin da take cema wani yana yi ita kofi ma ta ɗakko ta haɗa madara da zuma da yawa, tasa ruwa ɗan kaɗan. Ta kwaso biscuits kala-kala kusan shida tazo ta zube a dining tana faman ci da lumshe idanu. Dan babu ƙarya biscuits ɗin duk sunyi uwar haɗuwa.
     Cak Yoohan dake ƙoƙarin fitowa ya tsaya kawai yana kallonta da maɗaukakin mamaki da al'ajab. Yayi tsayuwar kusan mintuna uku yana kallonta da ita da falon da ƙamshinsa ke neman saukar masa da kasala kafin ya cigaba da takowa a hankali ya iso inda take. Kamar zaiyi magana sai kuma ya wuce a binsa zuciyarsa fal mamakinta. Ya tabbatar ta gansa amma ta basar.
       Tunda ya tura ƙofar ɗakinsa yaga yanda ya barsa haka yake sai ya juyo bai shiga ba. Wajen Aymah dake cigaba da party ɗinta ya dawo. Yanzun kam a bisa tsautsayi ta ɗago kanta, dan batai tunanin shine ya dawoba duk da taji ƙamshinsa sai suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi tana tura biscuit cikin baki.
       Shikam yana tsaye hanayensa duka cikin aljihun wandonsa, cikin ƙasa da murya sosai, kamar baya son yin maganar yace, “Hy Smally, tuda kin korarmin maimin aiki sai ki je ki min dan bana iya wanka a toilet ba'a wanke ba”.
         Kamar Aymah zata sharesa sai kuma ta kasa, dan yanda yay maganar ƙasa-ƙasa da kiranta sumoli yaja hankalinta wajen son maida masa murtani. Sai dai kuma tana ɗagowa ta sami fuskarsa a tsuke mayun idanunsa kuma ƙyam a kanta kamar zasu haɗiyeta. Kumbura baki tayi da faɗin, “Wlhy niba smally bace, dan ko a yanzu dai shekarata goma sha bakwai da wata tara”.
        A ransa yace, ‘Ai fa sai sha bakwai ɗin’. 
      Ta cigaba da faɗin, “Kuma da kake cewa na korar maka mai aiki, ta yaya zanbar wannan ƙaton gardin yana tsayamin a kai kamar wani mala'ikin dake tsaron ƙofar wuta. Baga ƙannenka nan ba wani yazo ya gyara maka”.
         Harga ALLAH maganarta ta bashi dariya, amma sai ya danne. Takawa yay gab da ita. Hakan yasa ta miƙe zumbur tana ajiye ledar biscuit ɗin hannunta, ta tura kujerar baya danta samu hanyar guduwa. Caraf ya riƙo hannunta ta faɗo jikinsa. Duk da yaji ɗan zafin yanda ta faɗo masa bai damuba. Sai ma hannunsa daya ɗora akan ƙugunta ya sake matsota ta manne masa sosai. 
        “Ouch!! Wannan muguntar fa?”. Ta faɗa tana ƙoƙarin ɗago fuskarta dake saman ƙirjinsa gab da haɓarsa, dan har ɗan gashin gemunsa na gogar gashin kanta. Kallon ido cikin ido sukaima juna. Tana ƙoƙarin son kauda nata amma ya hana, da wani irin yanayi yace, “Miyasa ke bakinki baya iya daina magana? Kowacce amsa kinada ita?”.
          “To sai in zauna a ringa cutata, ku mutane ai kunason mutum ya zama banza ku dinga takashi kamar wani tiles kuna wucewa”.
        Shi sam bama ya fahimtar mi take faɗa, hankalinsa gaba ɗaya yana kan bakinta ne da idanunta da suka ciko da ƙwalla. Hakan yasa baice mata komaiba, sai saukar babban ɗan yatsansa taji akan gefen bakinta. Saurin kauda fuskarta tai ƙoƙarin yi tana zaro ido. yayinda shi kuma ya ɗaga mata yatsan yana nuna mata ɓurɓushin biscuit daya goge mata. Haɗiye abinda zata faɗa ɗin tayi da ƙoƙarin san zamewa daga jikin nasa. Babu musu ya saketa kuwa.
     Daɓar ta faɗa saman kujerar da take zaune da. “Wayyo Abbana!”. Ta faɗa saboda zafi da taji.
      Dafe tebirin yayi da hannu biyu ya ranƙwafo kanta har tanajin saukar numfashinsa. Cikin kunnenta yace, “Silly girl, wannan shine maganin masu bakin magana kamar akku”.
         Hawaye na silalo mata akan fuska ta sa hannu kan damtsen hannunsa ta turesa. Fuskarsa ɗauke da murmushin mugunta ya riƙe hannunta, “Tashi muje ki gyaramin ɗaki kona sake ɗagaki sama na dire a kujerarnan har sai........ ” Sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba
          Zatai magana ya ɗora yatsansa saman bakinta yace, “Shiiii!!!!”. Sai kuma yaja hannunta dake cikin nasa ya miƙar da ita. Tanaji tana gani ya jata har ɗakinsa. Ganin ya nufi hanyar da take ƙyautata zaton toilet ne ta tirje da faɗin, “Nifa bana shiga toilet babu ɗan kwali”.
       Baice komaiba, sai sakin hannunta da yay ya nufi Wadrobe ɗinsa, sai gashi riƙe da babban handkerchief. Gani tai kawai ya warwaresa yay masa linkin ɗankwali ya ɗora mata bisa kai. Tsaf ya ɗaura mata shi kuwa duk da bawai ya buɗe bane da ƙyau yanda ya kamata, amma dai ya rufe gashin. Sake kama hannun nata yay zuwa cikin toilet ɗin. 
      “Ki fara wanke nan, wanka zanyi na fita”. Daga haka ya saketa ya fita. 
       Dubansa tayi kamar zatai magana sai kuma tai shiru dan harya gama ficewa. Tsaf ta gama bin toilet ɗin da kallo, dan babu ƙarya ya haɗu, gashi an zuba kayan toilet ɗin irin kalar, garai-garai ɗin nan kamar ƙanƙara, sai dai sunfi ƙanƙara duhu dan sunyi ɗan kalar ash da fari-fari. Komai tsaf a tsare inda ake buƙatar ganinsa babu wani dattin da yake faɗa akansa bazai iya wankan ba. Da yake neman aikin yin take saboda jikinta da yay mata nauyi sai gashi ƙara gyarashi tsaf, kamar taje ta ɗakko turaren toilet ɗin da miss xoxo ta haɗa mata mai shegen ƙamshi na wanke toilet sai kuma ta fasa. A cewarta kada ta cika zaƙewa ya ɗauka ya sameta ne a ɓagas.
      Fitowa tai riƙe da ƙugu alamar ta gaji, Yoohan dake zaune a kujerar dake tebirin karatunsa ya ɗago yana kallonta jin tana nishi. Dan shi a zatosa ko faɗuwa tayi a toilet ɗin ma. “lafiya?”.
         Baki ta kumbura gaba da faɗin, “Na gaji ne, bayana kamar zai ɓalle”.
     “Kaɗanma kenan, tunda kika koramin mai mini ai”. Ya faɗa yana ɗauke kansa daga gareta ya maida ga lap-top ɗin gabansa da yake aiki a ciki. Haushin maganar tasa ya hanata tanka masa, ta ƙarasa ga makeken gadonsa ta faɗa a kai tana faɗin, “Wash Umm na gaji, nima bara na rama hawar min gado da kayi”.
      Miƙewa yay idonsa a kanta. Batare da yace mata komaiba ya nufi bayi yana wani murmushin daya zo masa babu shiri. Harga ALLAH ta burgesa da tai aikin, dan baiyi zaton zatayin ba saboda sanin tsiwarta. Iyawarma baiyi zaton ta iya ba. Amma daya shiga bayin sai yagama gyaran natama yamafi na Solomon ɗin.
        Sai da taja kusan mintuna uku a kwance tana shaƙar ƙamshinsa daya manne bedsheet ɗin, kafin ta miƙe ta fara gyarawa duk da harga ALLAH ta gaji da gaske. Amma batason ya fito ya isketa. Kuma tanama buƙatar zuwa tayi wanka itama dan cikinta dam yake da ciye-ciyen da tayi.

       Tana tsaka da mopping kuwa ya fito. Kallo ɗaya tai masa tai azamar maida kanta ƙasa ta duƙar tana ƙunƙunin wai mara kunya ne mutumun nan. Yasan da ita amma ya fito da towel.
        Oho shi baimasan tanai ba. Dan mirror ya nufa bayan shima ya mata kallo guda ya dauke kansa. kansa tsaye yake komansa duk da kuwa yasan tana cikin ɗakin. Ta gama tana fesa fresheners data gani shi kuma ya ɗakko kaya zai saka. Juyowar da zatayi idonta ya sauka a kansa yana ƙoƙarin ƙwaye towel ɗin. Cikin subutar baki tace, “Babbar bala'i a gabana?”. Kafinma ya fahimci mitake nufi ta jefar da roban freshener ɗin ta kwasa da gudu ta fice.
       Da kallo ya bita ransa fal tunanin lafiya kuwa? Sai kuma yay saurin kallon hannayensa biyu dake riƙe da gefe-gefen towel ɗin. Ai baimasan sanda ya fashe da dariya ba. Ya saki towel ɗin yana zama bakin gadon har sannan dariyar yake hannayensa riƙe da kansa. Pant ɗin dake jikinsa fari ƙal ya shafa yana faɗin, ‘Silly girl, an gaya miki zan fito gabanki babu pant’. 
           Oho Aymah tuni takai ɗakinta ita dai, ta faɗa toilet tana hakki idanunta a rufe kamar ance gashi gabanta. Taja kusan mintuna biyu sannan ta sami nutsuwa, ta ɗan dafe kanta a ranta tanajin da sakamakon abinda zata gani kenan da bata biye masa tai wannan shararba. Dan dama tayine kawai saboda an koya musu biyayya gana gaba dasu, sannan nasihar iyayenta a gareta tana nan daram cikin ranta babu abinda ta manta a ciki. Daga haka itama ta zame kayanta ta hau yin wankan.

        Ta kammala shirinta kenan cikin baƙar doguwar rigar jallabiya data ji stones ya shigo. Saurin juya masa baya tayi tana ɓata fuska. Kansa ya girgiza kaɗan ya cigaba da takowa cikin ɗakin. A kan laɓɓanta ta furta, ‘Mayen suit ’ dan tsaf ta gama ƙare masa kallo ta cikin mirror ba tare da ya sani ba. Shima ɗin dai kallonta yake daga sama har ƙasa dan rigar ta mata ƙyau sosai. Idonsa akan dokin wuyanta da kananun gashi ke kwance luf-luf yace, “Ni zan wuce porthercout, sai gobe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”.
      Da sauri ta juyo tana kallonsa idanu a buɗe, tace, “Ni kuma ka barni a ina?”. 
       Da mamaki yace, “A ina kike anan?”. 
      “Gidanku”.
ta bashi amsa kansa tsaye. 
      “Oh to anan zaki zauna kenan, tunda kinsan ni dai aiki zanje ko”. Yanda yay maganar a dakile ne ya bata haushi. Cike da tsiwar tata data motsa tace, “He'em. Wlhy to nima ka kaini gidan Abbah dan bazan zauna ni ɗaya ba. Sannan kuma nama Abbana maganar ƴar aiki daga can kano yace babu ruwansa saika amince. Please ka kirashi kace ka yarda”.
           Necktie ɗinsa dake rike a hannu da rigar saman suit ɗin ya gyarama zama yana tsatstsare ta da idanunsa, “Duk waɗanan masu aikin dake gidan nan su menen amfaninsu da har sai an kawo mai aiki daga kano?”. “Toni bana buƙatar aikinsu, ni dai kawai a akawomin YARENA ADDININA hankalina zaifi kwanciya. Amma ta ina zan yarda waɗan nan garadan na shigomin kai tsaye gasu da shegen kallo kamar ƴaƴan mayu”.
        Ƙala baice da itaba, dan shima ya tafi wani kuma tunani daban. A ganinsa zaiyi amfani da wannan damar wajen binciko abinda yay alwashi. Dan dole kam ya yarda sai sun sami kusanci da wani ɗan gidansu Aymah anan sannan zai fahimci abinda yake zargin. Kuma ya tabbata idan aka kawo mai aikin duk wanda yayma Nu'aymah wancan ƙullin zai haɗa alaƙa mai ƙarfi da wanda za'a kawo musun saboda samun bayanai akanta. Shi kuma wannan shine mabuɗin bincikensa...........
           “Na shirya” data faɗa ne ya maidosa hankalinsa. Yay saurin dubanta da ƙyau yana bin handbag ɗin hannunta da kallo da ƙaramar leda. ‘Lallai kan yarinyar nan da motsi’ ya ayyana a ransa yana ɗauke idonsa a kanta. Duk da take masa kallon ba bahaushe ba duk yanda al'adunsu da dokokin musulinci sai da Hamza manager ya bashi haske a kansu daki-daki. Shi kuma ya ɗauki ɗammarar bi da ita akansu kodan ta samu nutsuwar zama da shi.
      “Karki ma ɓatama kanki rai dan babu inda zakije. Idan abokan hira kike bukata gidan nan cike yake da mutane”. “To ni........” ta kasa ƙarasawa saboda matsota da yayi. “Ke me?”. Ya faɗa yana tsuke fuskarsa da ƙyau. Bata sake magana ba dan kwarjinin da yay mata da cika idanu. Ga kuma zuciyar ta gado ta yunƙuro tazo gab da maƙoshi ta tsaya. Harya juya ya fita bata sake magana ba sai hawayene da suka cika mata idanu. Yana rufe mata ƙofar kuwa ta matsosu suka zubo.

       Duk da yaji tausayinta a ransa haka ya fice daga sashen nasu, a falo ya iske duk a halin gidan suna breakfast a babban dining ɗinsu. Cike da girmamawa yaran duk suka shiga gaishesa. Ya amsa sau ɗaya shima yana gaida su Momynsa dake binsa da wani irin kallo da ya kasa bama fassara. Da yake tasan kullum itace ke saka masa necktie indai yana gida saita taso. Amsa tayi ta saka masa, tare da taimaka masa ya ɗora rigar saman itama. Yanda batai magana ba shima sai baiyi ba. Sai da ta gama saka masa sannan yace, “Mu an daina bamu breakfast ne a gidan Momy?”.
       Da sauri tace, “No my boy, dama na sanarma Blessing ne takai muku tunda har yanzu kaga dota tana tare da baƙunta”.
       Idanunsa yaɗan lumahe ya buɗe a kanta. Hakan ba karamin sumar da ita yake ba, dan tana masifa-masifar son wannan salon da ya zame ma ɗan nata ɗabi'arsa. Yace, “Wasa nake nima Momy, ga amanar matana nan na bar miki, ni zanje porthercout ne, amma zan dawo gobe”.
      Da ƙyar ta danne zafin da takeji a zuciyarta. Ta kai hannu bisa tattausan sajensa ta shafa tana lumshe idanu, “Babu damuwa My Son, kaje lafiya ka dawo cikin nasara”. Hannunsa yasa ya janye nata daga fuskar tasa. Ya sumbaci bayan hannun yana jinjina mata kai da faɗin, “Thanks you sweetheart”.
        Daga haka ya juya ga kakaninsa. Fuska ya tsuke da ƙyau yana kallonsu. “Granny's na dawo gareku, dan nasan kunfi kowa tarin matsala a gidan nan yanzun. Baku barma kanku ba balle wani. Ga matata nan zan bari, idan na dawo naga ko ƙwarzanen damuwa a fuskarta nasan maganinku”.
     Cike da hayaniya Momy Debora ta hayayyaƙo masa cikin yarensu, dan dama da yare yay maganar shima. Itama Mama miƙewa tai tana zazzaga masa nata. Bai kulasu ba ya duba kannensa suma yay muau nasa gargaɗin da idanu, sannan ya duba ƙanen papa su Momy Destiny. A girmame yace, “Auntys kuma na baku amanar matata, karku bari waɗanan tom and jerry ɗin su mata ko kallon banza”. Cike da kulawa suka karɓa masa. Dan sukam har cikin ransu suna ƙaunar ɗan ɗan uwan nasu, musamman daya kasance Yoohan tsaye yake akan bukatunsu na yau da kullum harma da ƴaƴansu.
       Har mota ƙannensa da Momy sukai masa rakkiya, Gebrail ma motar ya shiga zai bisa har airport dan yanason ya tambayi kuɗi a wajensa. Solomon dai nata faman cin maganin da shi Yoohan ɗinma bai san yanayi ba. Sai da motocin suka fice sannan suka koma cikin gidan.

      Hawaye sosai Aymah ta dingayi dan kewar gidace sosai ta dawo mata sabuwa fil. Daga ƙarshe ma sai ta koma gado ta kwanta abinta. Tun tana tunanin mafita akan wannan auren har barci yay awon gaba da ita batare data shirya hakanba.
       Barcin kusan awa guda da rabi tayi kafin ta tashi, koba komai taji sakayau bakamar ɗazunba. Ganin lokacin walha ya wuce sai kawai ta shiga toilet tai uzirinta ta fito. A ranta take ayyanawa bazatai zaman takura kai ba, gara ta fitama ta zagaya gidan kar masu gidan su ɗauka ko tsoronsu takeji su sami nayi a kanta. A falo taci karo da breakfast da Blessing ta kawo mata tun ɗazun. Ta matsa gaban tray ɗin tana buɗe kwanikan. gasashen plantain ne, sai miyar ƙwai da ruwan tea da farfesun kifi. Ba yunwar take jiba. dan haka ta ɗauki gasashshen plantain ɗin guda biyu tasa miya a gefe ta zauna taci, koda ta gama saita ɗauka trayn gaba ɗaya ta fito da shi.
      Tunda ta fara sakkowa daga steps ɗin benan duk suka zuba mata idanu. Babu wanda bai yaba ƙyawunta ba a cikin ransa. Tare da ganin dacewarta da Yoohan ɗin nasu. Miracle ce ta fara jan tsaki tana kauda kanta gefe. Karaf kuwa a idon Aymah dake sakkowa. Wani ɓoyayyen murmushi ta saki a ranta tana ayyana ‘kece zaki fara ɗaukar lesson kenan ƴar lukuta’. A fili kam saita dubi Blessing data hangota tazo wajen da saurin domin amsar tiren hannunta. Yanda Blessing ɗin ta gaidata da girmamawa haka itama ta amsa mata da girmamawa tana miƙa mata tiren..
          Cikin falon ta ƙarasa fuskarta ɗauke da ɗan murmushi, ta zauna a kujerar data rage. Su mama debora ta fara gaidawa, suka amsa mata fuska a ɗaure. Bata damuba ta gaida Momy, ita dai babu yabo babu fallasa ta amsa. Daga haka ta gaida su Momy Favour da suka amsa mata sukam da fara'a, har suna tambayarta ya baƙunta?. ko kallon inda su Joy suke batai ba, sai da su Victoria na gaisheta ne ta amsa musu da kulawa tana tambayarsu ya school?.
       Wani wawan tsoki Miracle ta sake ja tana miƙewa tana wani fifita fuska da hannu alamar wulaƙanci dai. 
     Tana zuwa saitin Aymah tasa ƙafa ta taɗeta batare da kowa ya lura da yanda akai ba, sai ganin Miracle sukai a ƙasa wanwar bakinta ya daki gefen centre table aiko ya fashe.............✍

Tofa, mutuniyarku zata fara taro mana world cup a gidan Pastor goshpower😱😣😂.


yanzu haka an kusa kai ƙarhe, gamai buƙata zai iya garzayawa ya biya zafafa kar agama shanye romo babu shi😋😋😋.

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍


*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 49

_____________

_Ina ma’abota karance karance littafin hausa? Wanda ke nishadantar wa ya fadakar? Kana ya tsunduma ku a kogin lobayyar kauna..?_

_*REAL FEEDO* hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: *BA AMO...!* *BA AMO* wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani irin salo na daban..._

_Labarin *BA AMO* ya faru akan wata yarinya da d'an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne...Baban su yana auri saki ya tara 'ya'ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT... Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da 'ya'yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta.... wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak'i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d'an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma'aikata, 🧚🏻‍♂️😍cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma'aikata sai aka daura ita Khairat d'in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d'in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura.._

_Tab rungutsumi din fa kenan🤮Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d’aya? Ya rabbi😢 labarin kauna yayi.. Amma fa Za’a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito🥺Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana.._

_BA AMO::::: (Ba Labari...)_

_DOMIN MALLAKAR NAKI/‘NAKA sai ku baza idanu domin free ne yana nan yana yawo a kowane group_😘😘


___________

No. 49

............Kusan duk falon sai da kowa ya miƙe saboda uban ihun da Miracle ta ƙwallo. Hannunta ɗaya riƙe da baki ɗaya riƙe da ƙafarta data bugi kujera. Duk kanta suka nufa cike da tashin hankali. 
       Banda Aymah data wani ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tamkar ba itace ta aikata tsiyar ba. Cikin mintuna ƙalilan bakin Miracle ya suntume, gashi an ɗagata ta kasa taka ƙafar sai faman ihu take tana kiran Jesus. Tayi yare tayi turanci hawaye shaɓe-shaɓe da fuska. 
        Abu kamar wasa sai ga jikin Miracle ya rine da zazzɓi dan harga ALLAH taji faɗuwar musamman data kasance a bazata tazo mata. Gata masha ALLAH tanada jiki. Ko a kwalar rigar Nu'aymah, dan saida ta gama shan ƙamshinta sannan ta ɗan matsa gab da Mira da aka kwantar a doguwar kujera dake kusa da inda Aymah take zaune ana jiran Doctor yazo ya dubata. Da wani salon iskanci tace, “Ayyah Aunty Orrobo sorry yeah, wannan baki haka kamar shantu? Gobe kam ya sake yin tsaki batare da ya tantance inda zaiyi ba”. Babu wanda yaji mita faɗa a maganarta ta ƙarshe bayan sannu da taima Mira. Dan kuwa da hausa tayi, yanda kuma ta kwaɓe fuska sai ka ɗauka duk tausayin Mira ɗinne takeyi.
      A gefe kuma suna ganin Aymah ba wani turancin kirki takeji ba shiyyasa ta ƙarasa sannu wa Miracle ɗin da hausa. Haka suka cigaba da zama har isowar Doctor, ya duba Miracle ɗin sai ga sakamakon targaɗe a ƙafar data buge. Dole yace su shirya a kaita asibiti dan a duba ƙafar da ƙyau, a kuma yimata ɗinki a gefen bakinta da ya shafce. 

        Tun bayan wucewar su Miracle da Gebrail da Joy suka tafi rakawa asibiti Aymah ta koma sama dan lokacin sallar zuhur yayi. Dariya ta dinga sheƙawa tunda ta shigo kamar wata zararriya. Sai da tayi mai isarta sannan ta ɗauro alwala tana faɗin, ‘Duk wanda ya shirya match dani ai ya sani nima da shirina nake. Babu ta yanda za'ayi na zauna mushirikai su hau kaina suci tuwo. Wasa kam yanzu aka fara a wanga gida dan na kula basusan wacece Zainabu jikar Hajjo ɗiyar baba malam ba’.
           Sallarta ta gabatar a nutse, tana idarwa ta ɗauki Al-qur'ani ta hau karatu cikin zazzaƙar muryarta. Blessing ce ta shigo kawo mata lunch, sai dai a falo ta ajiye bata shigoba. Ta matso jikin ƙofar danta sanar mata ga abinci nan kunnenta ya jiye mata zazzaƙar muryar Nu'aymah na raira karatun littafi mai tsarki. Tsayawa cak tayi daga yunƙurin knocking ɗin tana sake matsar da kunnenta dan taji sosai. Kamar wasa sai gashi ta share mintuna kusan goma tana saurarenta. Sai da taji tsoron kar wanu ya shigo ya ganta ne sannan tai saurin barin sashen.
      Oho, Aymah batasan tanayiba. Karatunta ta sha na kusan awa ɗaya sannan tai addu'a ta miƙe. Sosai takejin kewar ahalinta, musamman ma Muhammad abokin dambenta. Gudun kar damuwa taima ranta yawa yasa ta fito falon danta ɗanyi ko kallo ne. Sai da ta fara duba abincin da Blessing ta ajiye, duk da taga shinkafa da miya hakan bai sata jin zataci ba. Itafa gaskiya bazata jura cin abincinsu ba. Ya dawo zata faɗa masa ita zatana girkintane kawai. Da wannan tunanin ta maida kulolin ta rufe. Saurarrakin biscuits ɗin data ci ɗazun ta ɗebo. ta dawo cikin kujera ta kunna tv a ranta tana mamakin yanda koda yaushe suke cikin wutar nepa. A maimakon kallon ma sai tai ta Searching tashoshi tana duba masu amfanin da riƙe Numbers ɗinsu a kanta. Hakan ya jata lokaci mai tsayi har aka kira la'asar. Salla taje tayi, ta sake wanka. Tsaf ta fito tana baza ƙamshi ta sauka ƙasa.
       Yanzunma duk a falin ta iskesu an dawo da Mira data sha ɗauri a ƙafa da hannunta data kulje, kunburin bakin kam ya ƙara faɗi dan ya kusa shanye rabin kumatunta. Batare da Nu'aymah ta duba ko inda take ba tacema su Destiny suzo su rakata taga gidan. Harara mama debora ta zuba musu da musu gargaɗi da idanu. Amma duk sai suka maƙe kafaɗa suka miƙe. Tsaf Aymah na lura da komai, dan haka tai murmushi kawai (Mama debo karfa kizama next level🤣lol).
           Suna fita Joy tace, “Yarinyar nan na kula da rawan kai ta shigo gidan nan, wlhy ni sai nagama kamar itace ta sama Mira ƙafa ta faɗi fa?”.
      Gebrail da ya bi Aymah da kallo kamar idanun zasu zubo ƙasa yay saurin waigowa yana duban Joy ɗin. “Hy madam banda ƙarya fa, dan kawai tana rayuwanta kai tsaye sai ace tana rawan kai?. Kufa ɗazun kuke gulman hausawa bagidadawa ne. Sai kuma gashi ita ta ƙaryataku yanzun tunda ta nuna kanta a buɗe yake. Da kun sone ta ƙunshe kanta a ɗaki komi? Mtsoww amebo girl”.
       Zumbur Joy ta miƙe kansa, Momy ta daka musu tsawa. Dan ciwon kai suke neman ƙara mata bayan wanda take ciki. Saboda akan idonta Aymah ta sakama Miracle ƙafa. Amma tai shiru saboda wani dalilinta. Tsaki Joy taja da yima Gebrail alamar zasu haɗune da yatsunta. Shima sai ya ɗage kafaɗa da taɓe baki irin na I don't care ɗin nan.
      Wani irin tafasa zuciyar mira ta ringayi, ga abin faɗa a bakinta amma babu damar cewa. Ita kanta yanzu maganar Joy ta sakata ƙara tariyo a yanda ta faɗin. Tunda tasan lafiyar ALLAH take tafiya babu kuma komai a gabanta. Aiko tabbas saita damalmala kan yarinyar nan bisa tiles ɗin gidan nan bara ta warke dai.
       Su mama debora nata cancana maganar da Joy ta faɗa akan tunanin Aymah ce ta kada Mira. Yayin da su Maman Favour keta ƙoƙarin kare Nu'aymah ɗin akan Joy ɗin ta faɗi dai son zuciyarta ne kawai.
      Oho, Nu'aymah batasan sunayi ba, tana can sunata zagaya lungu da saƙo na gidan ita da su Victoria. A ƙarshe suka yada zango cikin garden ɗin gidan da yay mugun tafiya da tunanin Aymah. Musamman ma swimming pool ɗin da ruwan cikinsa sky Blue da keta ɗaukar idanun mai kallo. Sun ɓata lokaci sosai a garden ɗin, dan har sai da duhun magriba ya fara rufa sannan suka fito.
     Yanzun kam babu kowa a falon kowa ya shige, sai masu aiki biyu maza dake gyarawa. Sashenta tai wucewarta suma su Favour suka nufi ɗakinsu.

___________★★★__________

            A kano kam shiru kakeji babu wani abu daya sake faruwa bayan jin labarin inda su Abdallah suke. Ashe Abdallah saudia yay komawarsa, Naseer kuwa yana anan cikin garin kano sai a yau yazo gidan. Kowa yayi mamakin ganinsa hankali kwance saɓanin yanda sukayi tunanin samunsa.
            Dominma ya ƙara tabbatar musu da hankalin nasa a kwance yake sai da ya shiga kowanne sashe yay musu bangajiyar biki. Da yamma su Abba Musbahu zasu koma Lagos harda shi cikin ƴan rakkiya airport.
     Bayan ya dawo ne shi da malam ƙarami da suka kaisu ya samu gaisawa da baba malam daya shigo. Yanda babu wanda ya tambayesa ina yaje cikin su hajjo haka baba malam ma baice masa komaiba. Sai dai a ƙasan ransa mamakin yanda babu wata damuwa tattare da Naseer ɗin yakeyi. ‘To mi hakan ke nufi?’ ya tambayi kansa acan ƙasan zuciya. babu mai basa amsa, dan haka yaja bakinsa ya tsuke ko Umm baima wannan maganaba. Bai san itama abinda Naseer ɗin yayi yana cikin ranta ba, tayi shiru ne kamar yanda kowa yayi ne kawai itama.

___________★★★★__________

        Lafiya lau Nu'aymah tai barcinta a sashen ita kaɗai batare dajin ko ɗar ba na tsoro. Dan haka sam dama ba ɗabi'arta bace ba kowa ya sani. Abinda kawai yayta cimata rai shine kaɗaici da kewar ahalinta. Gashi bata da ko ƴar waya balle ta kirasu taji koda muryarsu. Sai damuwa akan waɗan nan mutanen gidan data fahimci sam babu mai ƙaunarta a cikinsu. Sai dai kowa da nasa salon kallon data lura yana mata. Yaran nan su Victoria ne kawai babu ruwansu, sai su maman Destiny. Amma har masu aikin gidan tana fahimtar kallon ƙyama da suke binta da shi duk da kuwa duk suna mata gaisuwa da girmamawa. Lallai kuwa dolene ta ɗaura ɗammarar zama mara jin magana, inba hakaba wahala zata sha tunda ta fahimci shi daya ajiyeta bamai zama bane. Yazama lallai kenan itace zataima kanta yaƙi da kanta basai ta jira daga wurinsa ba. Da waɗan nan tunane-tunanen tai barci a wannan daren, hakan yasa washe gari bata fita a sashen nata ba sai bayan sallar zuhur.
       Yau kam babu kowa a falon sai Abraham kawai yana kallon cartoon, yanda yaron bai tanka mata ba haka itama bata kulashi ba tai ficewarta. Kai tsaye garden ta nufa abinta. Shiru wajen babu komai sai kukan tsuntsaye da iska mai daɗi dake kaɗawa. Ta zauna a bakin pool ɗin tare da zira ƙafafunta ciki tana lumshe idanu saboda sanyin ruwan. Haka ta zauna tsahon lokaci a wajen rabin hankalinta duk yana ga tunani, kamar ance ta waiga sai idanunta caraf akan Gebrail da ita kanta batasan adadin lokacin daya ɗauka a wajenba. Kanta ta ɗauke daga dubansa tana sake tsuke fuska. Yayinda shi kuma ya shiga takowa inda take yana wani rangaji irin na gayu marasa jin magana. A mamakinta sai kawai ganinsa tai ya zauna daf da ita shima ya zura ƙafafunsa cikin ruwan.
          Kallonsa tai da wani irin takaici, shiko ya saki murmushi. Kafin ya furta maganar dake bashinsa taja baya ta fidda ƙafafunta tana jan wani shegen tsaki........ Da sauri yace, “Ayya sorry my aunty, i......”
      Wani shegen kallon da tai masa ne ya sakashi haɗiye abinda ke bakinsa. Ta zira takalmanta ta fice daga garden ɗin gaba ɗaya. Ta kula yaron nan yana son shigar mata hanci, to lallai zata fyatoshi kuwa da gaggawa tunda shi ɗan bunsuru ne.
      Gebrail kam da kallo ya bita a wani irin yanayi yana lashe laɓɓansa, harga ALLAH tun ganin Aymah a wajen dinner ya rikice, dan yarinyar da shekarunsa ta dace bawai yayansa ba.

         Takaicin da take ciki na Gebrail yasata ko ganin hanya batayi take tafiya kawai ta bayan garden ɗin. Dan jitai sam batama buƙatar shiga cikin gidan balle ta sake karo da wani takaicin kuma. Cak ta tsaya saboda jin ana magana ƙasa-ƙasa kamar cikin tashin hankali. Tai saurin komawa baya kaɗan ta maƙe jikin rassan flowers ɗin da suka sarƙe wayar garden ɗin. Ƙafafunsu kawai take gani banda fuska saboda karewa da bishiyan ayaba tayi, saboda da turanci suke haɗawa a maganar ya bata damar jin wani abu a ciki.
     Wanda ke maganar yace, “Boss! Nima ganin hoton nan ya matuƙar tadamin hankali, dan bamu saniba koma bashi kaɗai baneba, tunda wannan ma a tsakkiyar file ɗin nan na companyn na samesa”. Cikin tsananin tashin hankali taji wanda aka kira boss ɗin ya fara magana da yare, kafin ya kuma dawo yi da turanci kamar zai haɗiye harshensa. “Tabbas akwai damuwa idan hoton nan ya shiga idon wani, dan zai iya zama silar buɗewar ɓoyayyen sirrina da babu wani mahaluki daya sanshi bayan mutum huɗu, suma ɗin ba komai suka saniba akai sai abinda na sanar musu. SB kayi gaggawar ɓatar da hoton nan, sannan dolene a cikin watannan mubi kaf takardun nan mu bincikesu dama gidan gaba ɗaya, sai mun tabbatar da babu wani makamancin irin wannan hoton sannan hankalina zai kwanta, zan shigo Lagos ɗin nima amma bari sai tafiya mai tsaho ta sam....”. Sai kuma ya sake komawa yin maganar da yare wancan na amsa masa.
       Gani tai ɗaya na takowa alamar zai fito. Tai azamar sake maƙewa a wajen dan taɗau alwashin sai taga kosu ɗin su wanene?.
       Har yayo nisa taji wancan ya tsaidashi, da turanci yace, “Kaga bani hoton nan kar a sami kuskure, zan ƙonashi ni da kaina kawai”. Batare da wancan ɗin yayi musu ba ya miƙa masa yana faɗin, “Okay sir”. Daga haka ya juyo zai fita. 
       Da kallo Aymah ta bisa harya ɓacema idanunta, bata sanshiba, dan babushi a cikin duk waɗanda aka nuna mata a cikin gidan. Jin ana takowa za'a fito ya sata sake komawa da sauri ta maƙe. Wani irin waro idanu tayi ganin Papa ne ya fito. Ta bisa da kallo zuciyarta na wani irin motsi a ƙirjinta. Sai da ta hangi ya shige cikin falon gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fito a wajen zuciyarta na mamakin wane sirrine yake iƙirarin babu wani mahalukin daya sani sai mutane huɗu?. Miyasa yace sanin zai iya zama sanadin buɗewar sirrinsa? ‘Sirrin mi to?’ ta ayyana a fili cikin jimami.
     Wata zuciyace tace, ‘Ke ko Aymah ina ruwanki, ko shishshigi da son asani. Hakane fa’. ta sakke ayyanawa a ranta tana barin wajen. Daga nan ma sai ta koma cikin gidan itama.

      Kamar wasa sai ga tattaunawar papa da baƙonsa ta kasa barin ranta. Duk yanda taso yakicewa abin sai sake tisa kansa yake a zuciyarta. Haka kawai takejin ƙwaɗayin son ganin hoton nan. Sai dai idan tacema zata gani a ina zata gansan? Tunda yace ƙonawa zaiyi. Koma bai ƙonaba tayaya zata iya shiga ɗakinsa binciken hoto?.
       Waɗan nan tambayoyi sunta mata kaikawo a zuciya har lokacin Yoohan ya shigo gidan bata sani ba. 

       Yoohan da ƙarfe takwas na dare da wasu mintuna jirginsu ya sauka sun iske guards ɗinsa na jiransu a airport, basu wani ɓata lokaci ba suka nufo gidan. Lokacin da suka shigo basu iske kowa ba a falon sai Blessing dake shirya dinner. Itace ke sanar musu ai su Momy duk sunje church. Baice komaiba yay gaba Solomon na biye da shi har ƙofar sashensa. Cikin in-ina da rawar harshe Solomon yace, “Sir! Ga kayan inaga ni basai na shiga ba?”. Da ɗan mamaki Yoohan ɗin yay masa kallo ɗaya ya ɗauke fuska a tsuke, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru yana miƙa masa hannu alamar ya bashi kayansa dake a hannunsa. Saurin miƙa masa yay da faɗin, “Am sorry sir ba laifina bane dokar madam ce hakan”. Shi dai Yoohan baice masa komaiba ya amsa ya rufe ƙofar. Harga ALLAH shi Solomon ma dariya yaso bashi. jin ko ina shiru yayi tunanin kota kwanta ne? Ya ɗan kalli ɗakin sai ya wuce nasa kawai. Wanka kawai yayi ya fito dan sai da yayi salla tunkan su taho. Abincin dake kan dining ɗin ya nufa ya buɗe, shinkafa ce dafa duka da taji haɗin kayan lanbu tanata ƙamshi, sai gasashshen nama kaza da haɗin salad a gefenta. Zama yay ya zuba abincin kaɗan yasa salad ɗin da yanka ɗaya na naman dan yunwa yakeji, rabonsa da abinci tun breakfast saboda aikin daya sha masa kai.
        Baifi lauma uku ba aka turo ƙofar aka shigo babu ko knocking. Yasan Momy ce kawai ke masa wannan halin a gidan, ilai kuwa itace sanye cikin skirt da riga na lass, taci uban gashin Attachment da kallo ɗaya zai baka tabbacin mai tsadane dan sai walƙiya yake da ƙyalli. Bible ɗin hannunta ta ajiye saman tebirin taja kujerar kusa da shi ta zauna tana shafa masa kai. “My Boy duk yunwarce tasa ko kallon mutane ba'ayi?”. Tun shigowarta sai yanzu ya ɗago ya dubeta yana wani sake ɓata fuska. “Momy ai ke ɗince sam baƙyama mutane knocking sai dai ki....” Da sauri ta katsesa da faɗin, “To naji sarkin ƴan ƙorafi, kai kullum magana ɗaya baka gajiya zan gyara”.
         Haka kullum take faɗa masa idan yayi magana, kuma bazata gyara ɗinba. Hannunta data ɗora saman sajensa tana shafawa da faɗin, “To kayi murmushi mana” ya janye da cewa “Niba fushi nayi ba yunwa nakeji”. Jin yace yunwa yakeji duk sai ta rikice kamar ba abincin ta samu yana ci ba. Amsar spoon ɗin tayi daga hannunsa ta ɗiba takai bakinsa. Zaiyi magana tai saurin faɗin, “Hahh! Kona maka ɗura na rantse”. Yasan idan baiyi yanda take so ɗinba ba barinsa zatai ba. Dan haka kawai ya shiga buɗe bakin tana bashi. Data kai hannu saman jikinsa kuma zai ture.
      Nu'aymah da tun shigowar madam Chioma surutunta yaja hankalinta ta fito ta kuma ƙyaɓe baki a karo na babu adadi. Barin jikin ƙofar tayi ta fito tsakkiyar falon sosai tana wani ɗan munafikin tari data ƙirƙiro.
       Da sauri duk suka juyo suna kallonta, ganin ta cigaba da tarin Yoohan ya zare hannunsa dake cikin na Momy ya ɗauki glass cup ɗin dake cike da ruwa ya nufota. Yanda madam Chioma ta tsuke fuskane murmushi yaso suɓucema Aymah, sai ko yawu ya sarƙeta ta shiga yin tari na gaskiya. Tuni Yoohan ya manta da Momynsa dake a falon, ya riƙota da sauri ya zaunar bisa centre table da ke kusa da su. A gabanta ya durƙusa ya saka mata kofin a baki. Da sauri ta ɗora hannayenta duka biyu a saman nasa da ke riƙe da ruwan suka karasa da kofin bakinta a tare. jikinta sai rawa yake hawaye na zirara dan taji sarƙewar sosai. Ɗayan hannunsa ya ɗora a gadon bayanta yana shafawa. Kusan rabin ruwan tasha sannan ta janye, ta maida hannayen nata ta riƙe kumatunta tana ɗan murzawa da sauke wahalallen numfashi irin na wanda ya sarƙe. Cigaba yay da shafa mata bayan yana jera mata sannu.
        Kanta a duƙe ta tokare gwiwar hannunta da cinyoyinta ufan bata iya cemasa har tsahon mintuna kusan biyu. Sai a sannan ne madam Chioma ta taso inda suke. Hannunta ta ɗora akan nasa dake shafa bayan Aymah ta ɗan bubbuga ta wuce batare da tacema Nu'aymah sannu ba. Binta yay da kallo harta fice. Haka kawai ya samu kansa dajin haushin abinda tayin. A ganinsa ya dace ace tama matarsa sannu tunda a gabanta komai ya faru ai. Wannan halin na Momynsa ya fara damunsa shi kam. Ya kula batason kowace mace ta raɓesa a rayuwa daga ita sai ƙannensa. Kai su kansu ƙannen nasa wani lokacin fuskarta nuna ɓacin rai takeyi........
       Hannunsa da Nu'aymah ta janye a bayanta ne ya maidosa hankalinsa, saurin riƙota yay ganin zata tashi. “Ina kuma zakije?”.
      Cikin ɗan sanyin muryar da sarƙewar taja mata tace, “Zanje in kwanta barci nakeji”. 
     “Da miya fito dake nan ɗin?”.  
Baki ta tunzira masa da faɗin, “To bahar na kwanta ba surutunku kai da Momynka ya tasheni”.
     “K ba momynki bace?”.
       “Bayan bata sona”. Ta faɗa da iya gaskiyarta. 
      Tsatstsare ta yayi kawai da idanu ya kasa cewa komai. Ganin zata miƙe ya sake ruƙota, “Kinga muje kici abinci kafin kije ki kwanta ɗin”. 
   “A'a ni na ƙoshi”. 
“Mi kika ci?”.
      “Babu komai, kawai dai na ƙoshi”.
“Silly girl, kodai sauran kayana kika tattare kika cinye?”.
        A yanda yay maganar sai yaso bata dariya, amma saita gimtse abinta batayi ba, ta zare hannunta kawai daga cikin nasa tana miƙewa, “ALLAH ni barci nakeji ka barni na kwanta”. 
        Bai sake ce mata komai ba ta raɓa ta gefensa ta wuce. Kallo ya bita da shi harta shige ta maida ƙofar ta rufe. Idanunsa yaɗan lumshe da sauke ajiyar zuciya sannan ya miƙe. Shima jiyay baya buƙatar cigaba dacin abincin, dan haka yay kiran Blessing ta telephone ya sanar mata tazo ta kwashe. Yana cikin haɗa tea a kofi Blessing ɗin ta shigo, ta tattare komai ta fice da shi, shi kuma ya nufi ɗakin Aymah da kofin shayin da biscuit guda ɗaya. Zaune ya sameta a gaban mirror tana ɗaure gashinta, ta canja kaya zuwa wando da riga na barci. Wandon ɗan fit ko cinya bai gama rufe mata ba, sai rigar itama dai babu wani girma da siririn hannu. Rikicewa tayi sosai dan batayi zaton shigowar tasa ba. Yanda taketa budum-budum ɗin neman hijjab ne ya bashi damar kallon abinda take ƙoƙarin son rufewar.
        Sosai ƙirjinsa ya harba. Ya ajiye shayin a kan mirror da biscuit ɗin yana faɗin “Gashi nan kisha kafin ki kwanta”. Daga haka yay ficewarsa dai-dai da ita kuma taja hijjab ɗin sallarta data samu nasarar gani a yanzu ta ƙudundune jikinta.

         Koda Yoohan ya fita da sassarfa ya rufe ƙofar falon ya kashe komai ya nufi nasa ɗakin shima. Ƙofar ya maida ya rufe ya jingina a jikinta da rumtse ido da ƙarfi. Tsaf Nu'aymah ta shiga dawo masa cikin idanu. ‘Ƴar 17years ce da wannan surar?, ko ina ya kai yanda ya kamata?’. Ya ayyana a ransa tsigar jikinsa na wani yamutsawa................✍

😜Ƴar yarinyace fa Dafta, ka bari sai ta girma kawai🤣🙄.


_______________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.




*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 50

____________

_Ina ma’abota karance karance littafin hausa? Wanda ke nishadantar wa ya fadakar? Kana ya tsunduma ku a kogin lobayyar kauna..?_

_*REAL FEEDO* hazikar marubuciyar nan ta zo muku da wani gangariyar littafi mai suna: *BA AMO...!* *BA AMO* wani nazartaccen littafi ne daya zo da wani irin salo na daban..._

_Labarin *BA AMO* ya faru akan wata yarinya da d'an sarkin garin su, yarinyar gidan su gidan yawa ne...Baban su yana auri saki ya tara 'ya'ya da mata da yawa. Tirqashi! To ita yarinya sunan ta KHAIRAT... Tun farko dangin mahaifin su sun tsani mahaifiyar tasu,Bayan ya auro ta, Ta haifi yara mata zallah suna kiran ta da uwar mata kuma kwata-kwata basa kaunar ita da 'ya'yan nata. To ita yarinya ta gama karatun ta.... wato KHAIRAT.. shekarun ta 22 matan gidan nasu suna mata gorin tayi kwantai tak'i aure. Kwatsam wata rana yarinyar ta samu labarin d'an sarkin garin su ya bude sabon company ya fara daukan sabbin ma'aikata, 🧚🏻‍♂️😍cikin ikon Allah ta zuwa ta samu aiki. Ta fara zuwa aikin ta, a karshe su kansu da suka fahimci kwazan ta da nutsuwar ta samu karin matsayi. To a lokacin ne kuma Yarima da PA dinsa suka sami matsala aka kore ta a ma'aikata sai aka daura ita Khairat d'in a matsayin P.A dinsa. Tafiyar tasu batama yi nisa ba! Aka yi makiya suka yi masu sharrin wai karuwar sa ce, har labarin yaje gun mai martaba. Itama Khairat d'in labarin yaje ga mahaifin ta har ya nemi korar ta daga gidan sa, da kyar aka lallashe shi ya hakura.._

_Tab rungutsumi din fa kenan🤮Ya zata kaya ne ga YAREEMAH GA KHAIRAT..a roof d’aya? Ya rabbi😢 labarin kauna yayi.. Amma fa Za’a sha rikici.. Karku manta khairat daga gidan yawa tafito🥺Ga basuda wani hali.. Shin sarki zai yadda da Khairat amatsayin personal assistant din yareemah ko kuwa.? Duk wannan ruguntsumi n REAL FEEDO ce kadai zata iya warware mana.._

_BA AMO::::: (Ba Labari...)_

_DOMIN MALLAKAR NAKI/‘NAKA TUNTUBE MU TA:_ +227 81 73 10 21


________________

No. 50

............Ya jima tsaye a jikin ƙofar wutar kansa a ɗauke. Kafin ya ja ƙafa da ƙyar zuwa saman gadonsa. Duk yanda yaso barci ya ɗaukesa hakan ya gagara, har kusan 2, daga ƙarshe dai ya miƙe zuwa toilet, ruwa ya sakarma kansa kafin ya ɗauro alwala ya fito. Daga haka yay nafilfilin daya saba, ganin ya kai har asuba saiya bari sai da yay sallar asuba ɗin sannan ya haye gadon ya kwanta ko azkar yau bai iya kammalawa ba saboda barcin dake cike da idanunsa.

          A ɓangarrn Aymah kuwa kanta ta dafe tare dayin jifa da hijjabin tana ballama ƙofar harara, sai kuma ta zabura ga ƙofar ta murza mata key wai karya dawo. Addu'a ta komayi akan ALLAH yasa bai ganta da ƙyauba, idanko ya ganta to bata yafe ba (dan ƙari😂). Da ƙunƙuni ta koma gaban mirror ɗin inda ya ajiye tea ɗin, babu kunya ta zauna ta sha dan dama ƴar yunwa na cinta ƙasa-ƙasa, alwashin data ɗauka na daina cin abincin gidanne kawai ya sata cewa ta ƙoshi. Sai da ta shanye tsaf taci rabin biscuit ɗin sannan taje ta sake yo brush tazo tai kwanciyarta.

★★★★

        A ɓangaren madam Chioma kam ta fitane da wani irin jin zafi da takaicin Aymah, dan ita duk a tunaninta da biyu tayi abinda tayi. Batasan ita Nu'aymah ko tarin farko da tayi, tayine kawai dan neman tsokana bawai danta kawo wani abu a ranta game da zaman nasu ba, tunda tasan sudai basu ɗauki taɓa jikin juna komaiba musamman ma ita dake a matsayin mahaifiyarsa. Ko kallon Victoria da Abraham dake rigima akan camara batai ba ta shigewarta ɗakinta ta banko ƙofa. Zama tai kan sofa zuciyarta tamkar zata tarwatse dan tsanar Aymah. Waya ta ɗauka kamar zata kira ƙawarta sai kuma ta fasa, a ganinta gara ta bari su haɗu a church jibi lahadi zasufi yin maganar yanda ya kamata ai.
      Hular gashin dake a kanta ta tuge ta ajiye, cirkuɗaɗɗen ainahin nata dake guntu ya bayyana. Fitowa ta sakeyi daga ɗakin zuwa sashen Papa. Baya falo, dan haka ta nufi bedroom ɗinsa kai tsaye. Saurin tura hoton hannunsa da lighter da zai ƙonashi yayi ƙarƙashin gado dan yazata cikin yaransa ne wani ya shigo masa. Amma ganin matarsa ne sai ya ɗan sauke ajiyar zuciya. Sai dai hakan baisashi sake ɗakko hotonba duk da itama tasan wani abu akan hoton.
     Ita sam bama ta lura da abinda yayi ba, ta zauna a bakin gadon kusa da shi tana hawaye. Duk rikicewa yayi, ya shiga jera mata tambayaoyi da rungumota jikinsa. Bata iya bashi amsaba sai da tai kukanta ta more sannan ta labarta masa abinda ya faru. Murmushi yayi dan shi baiga wani abin fushi ba anan, a fili kam sai yace, “Uhm-uhm Darling cool down, ke mima ya kaiki sashensu yanzu? Kin sanfa yanzu yana da mata, duk kulawar da kike tunanin baya samu yanzu akwai mai masa”. Ɗan turesa tai ta tashi zaune sosai. Ya ƙyalƙyale da dariya yana riƙo hannunta, “Ah son ƴaƴa yamiki yawa Madam, karfa kice zaki ringa irin halin su mama akan matar John Please, dan indai kina nuna mata ƙi bazamuci nasara akan burinmu ba zaki rusa mana aiki”.
           “Honey yarinyar nan bata da kunya, ciwon da kaga Mira taji fa itace ta saka mata ƙafa ta faɗi saboda ta mata tsaki”. Idanu papa ya zaro waje sosai da faɗin, “Da gaske?”. “Na rantse maka kuwa Honey, abinda yasa nai shiru banyi maganaba saboda itama Miracle ɗin shegiyan kanta ne, danni tama isheni a gidan nan, ya kamata ta koma gidansu hakanan tunda ta kammala karatun ai”.
       Da sauri Papa yace, “No baza'ayi hakaba Darling, kawai dai zan mata gargaɗi karta sake shiga rayuwar matar John, inba hakaba kuwa shine da kansa zai koreta a gidan nan tunda tasan halinsa”. Wani shegen kallo Madam Chioma kema Papa mai cike da tuhuma. Amma sai ya basar kamar bai ganta ba. “Humm” ta faɗa tana haɗiye abinda ke a ranta. a ganinta inma hakanne ai zata saka idanu ta tabbatar. “Naji, yanzu dai inason kaima John magana, dolene idan yana garin nan ya ringa fita church bawai dole sai Sunday ba. Idan bamuyi hakaba yarinyar nan zata iya sakashi ya fara salla. Gara mu saka masa ido sosai itama kanta duk Sunday ya sata tana binmu tunda akwai addu'oin da ake masa, tunda kuma yanada mata kaima kasan a ƙa'ida dole saita ringa kasancewa a wajen”.
        “Eh maganarki gaskiyane kam, zan zauna da shi sai muyi magana”.
      Kanta ta jinjina masa alamar gamsuwa. Daga haka suka cigaba da hirarsu har ya manta da batun ƙona hoto ma.

*******

      A ranar gaba ɗaya Nu'aymah wasan ɓuya ta dingayi da Yoohan, gaba ɗaya taƙi yarda su haɗu har yamma duk da dai ya daɗe bai tashi a barci bane, sai gab da azhur ya tashi, yana yin wanka kuma yay shirin massallaci ya fita. A lokacinne ya isketa a falo tana kallo. Amma tanajin motsinsa ta tashi da gudu ta shige ɗakinta harda mirza key. Shi dariya ma ta bashi a lokacin, amma sai ya gimtse baiyiba yay ficewarsa dan ya kusa makara.

          Sai bayan sallar la'asar ya dawo massallaci ne ya ritsata ta fito zataje garden. Karo sukayi a bakin ƙofa, tai baya da sauri tana tura baki gaba da dafe goshinta. Uffan baice mata ba, sai idanu daya kafeta da shi. Dan doguwar rigar atamfar jikinta ta mata ɗas, daka ganta kaga cikkakkiyar bahaushiya ƴar arewaci.
        Jin yaƙi cemata sannu ta sake tura bakin tana tara hawayen ƙarya, ita a lallai dole taji zafin bigewar da tayi. Raɓashi tayi zata wuce yay azamar riƙo hannunta ya dawo da ita gabansa. “Kin gama gudun?”. Ya faɗa a hankali kamar bayaso. Yanda yay maganar muryarsa a sanyaye ne yasa kallonsa da sauri, kallon ido cikin ido sukaima juna, ya ɗan lumshe nasa dake da ja a ciki, gashi sun ɗan kumbure ya sake buɗewa a kanta.
      Samun kanta tai da faɗin, “Baka da lafiya?”. Kansa ya ɗan jinjina mata da yamutse fuska, kafin yace, “Kaina ke min ciwo”. Ya bata amsa yana sakin hannunta dake cikin nashi. 
     A bazata yaji tace, “Dama likitoci na rashin lafiya?”. Tai maganar da waro idanunta manya waje sosai. A karan farko ya saki murmushi yana ƙoƙarin raɓata zai wuce, sai da ya shige falon sosai sannan yace, “Shi likita ba mutum bane?”.
         Harta buɗe baki zatayi magana sai ta fasa saboda hango Papa na sakkowa daga sama waya a kunnensa. Sai dai kuma idanunsa na kansu da ga ita har Yoohan ɗin. Juyawa tai ta fice abinta.

_______★★★★________

  *_KANO TA DABO_*

        Kamar yanda baba malam yayma Umm bayani akan ƴar aiki da Aymah ta buƙata daga nan, itama Hajjo ya sameta da zancen, Ɗari bisa ɗari hajjo ta bada goyon baya, sai dai tace ya kamata a tuntunɓi Yoohan idan ya amince, idan bai aminceba a haƙura kawai, a hankali zata saba da waɗanda ƙadadara ta kaita zama da su. Harma suna mata fatan cin riba akan hakan. 
       Duk da baba malam ya riga da yayi magana da Yoohan akan maganar tun kwana biyu daya wuce sai ya amsama hajjo da cewar insha ALLAH a yau zai tuntuɓi Yoohan ɗin, yanda sukayi kuma zataji. A ransa kuwa da biyu yaƙi faɗa mata gaskiyar yanda al'amarin zai kasance. Ba komai ya jawo hakaba sai laɓe daya fahimci anai musu shi da Umm kwana biyun nan, inuwarnan daya gani a ranar da za'a kai Aymah Abuja. Sai kuma ya sake ganinta randa yakema Umm bayani akan wayar da sukayi da Nu'aymah. Sai dai yayi shiru da bakinsa ko Umm ɗin bai sanarmawa ba. Sai Yoohan da shima yay masa zancen ganin mutum a randa akai maganar cikin nan na Aymah,  dan randa Nu'aymah tai masa maganar mai aiki daga nan kano ya kira baba malam sunyi doguwar waya.
      A yanzu haka fatansa ALLAH yasa maganar da sukayi da hajjo an laɓe musu ɗin. Dan duk mai aikata musu SARAN ƁOYEN zaiso ace koma wace ƴar aiki za'a turama Nu'aymah ya samu dangantakar da zai ringa samin bayanai akan Aymah.
      Baba malam ya jima a wajen Hajjo da tunanin ko zai sake ganin inuwar mai laɓen nan. sai dai harya ƙaraci zamansa da kallon windows babu ko ƙyallin mutum balle wata inuwa. Hakan ya bashi mamaki amma sai ya share dan baya buƙatar hajjo ta fahimci komai tun yanzun, sai sun kammala ɗana tarkunansu tsaf sannan.

         Washe gari baba Malam ya sake samun Hajjo da maganar cewar Yoohan ya amince da maganar mai aikin. Fuskar Hajjo faɗaɗe da murmushi tace, “To to Alhmdllhi, madalla da ɗan albarka Yahya. Kaga bara na shiga nan gidan Iyami da kaina sai na mata bayanin a samo mai hankali ba yarinya irin Zainabu ba. Dan bazai yuwu a irin wannan zaman a haɗa ƙuruciya da ƙuruciya ba. Sai dai wadda taɗan tasa idan taga ba dai-dai ba ta nusar da ita”.
       “Eh gaskiya ne inna, hakan yayi kam. Dan mamana halinta kam sai ita, inba mai ɗorata a hanyar aka samoba sai aita samun matsala dan har yanzun hankali bawai ya gama isarta bane”.
          “Ai karka damu ɗan malam, wlhy duk abinda kaga Zainabu nayi nima nayisa, babu abinda ta bari na ƙuruciyata. Malam yasha fama dani bana wasa ba. Amma kaga ina fara haihuwa duk saina rage nawa. Garama Zainabu ai a shekarun da akai mata aure ta tasa fiye dani. Tunda ni ina sha uku aka aurama babanku ni, itako sha bakwai fa harda wasu watanni”.
          Baba malam dai kansa a ƙasa yanata ƙoƙarin haɗiye dariyarsa. Dan shima kafin mahaifinsu ya rasu ya taɓa bashi labarin ƙiriniyar da Hajjon tayi a gidansa. Da yake shi haka yake, duk randa ƴan labarin nasa ya motsa sai ya zaunar dasu yayta basu tarihin gwagwarmayar da yayi ta rayuwa harma da ƙuruciyarsu. Wannan ɗabi'ar ta mahaifinsu tana ɗaya daga cikin abinda basa iya mantawa a rayuwarsu su duka.

        Kamar yanda Hajjo tai alƙawari da yamma kuwa sai ta shiga gidan su Hamisu wajen mahaifiyarsa Iyami. Sosai Iyami ta dinga haba-haba da hajjo duk da kuwa kasancewar su maƙwafta. Amma da yake ba ɗabi'ar shige-shigence da suba inba da ƙwaƙwaran dalili ba, sai yazam duk randa akaga juna kamar baƙi.
       Bayan sun gaisa hajjo tasha ruwan da Iyami ta kawo mata duk da ba ƙishin take jiba, sai dai a cewarta ruwan zuminci yafi zuma garɗi. “Yauwa Iyami nasan kinata mamakin ganina da maraicen nan. To dama ba wani abune ya sani fitarnan ba ta gabannin magriba sai takwarata ƴar jikalleta Zainabu da aka kai Abuja”.
        Iyami dake murmushi tace,  “Oh ALLAH sarki Nu'aymah amarya zaki cemin, inadai fatan suna nan lafiya ko?”.
          “Ah lafiya lau suke sai alkairi kam. Mijin ne dama ya kira wai a nema mata mai aiki daga nan, shine nace to bara nazo da kaina wajenki ƙila ta hanyarki a samo wata mai hankali. Danni ƴan aikin gidan nan namu yanzu tsoro al'amarinsu ke bani wlhy Iyami. Kuma kinsan duk deluwa ce dama take kawo manasu gashi ALLAH yay mata rasuwa”.
        “To hajjo babu damuwa. Tunda har kika zaɓeni nikuwa insha ALLAH zan samoma Nu'aymah mai aiki ƴar gaske wadda baza'ayi kuka da ita ba. Duk da dai yanzu kinsa al'amarin mutanen namune sai dai addu'a. Baka fiya ganin abinda ke cikin zuciyar mutum ba a fuskarsa. Sai dai muce ALLAH ya datar damu”.
        “To amin dai Iyami. Lamarin bani adama kam na wannan rikitaccen zamani sai godiyar ALLAH kawai. Yanzu dai sai a bincika mana ɗin daga nan zuwa kwana biyu. Amma sai a samo mana ƴar babba ko tunda kinga ba'a haɗa Zainabu da sha katafi irinta ba. Wadda dai idan tayi ba daidaiba za'a tsawatama yaro a kuma ɗorasa akan hanyar data dace”.
       “Eh gaskiya kam hajjo, aiko indaima hakane bari zuwa anjima idan cikin su Hamisu wani ya ya shigo sai na saka su kira min Uwaliya idan zatayi, ƴar wajen yafendona ce acan wudil, mijinne ya tafi da ita can kudu da yake ɗansanda ne ya gama wajigo rayuwarta shine fa ya turota da takardar saki har uku. Shekara biyu kenan wani auren ya gagara abu kamar na magani”.
       Hajjo daba cika son irin waɗannan ƙananun maganar tayiba ta miƙe tana faɗin, “Ai ɗan adam sai ki barsa kawai Iyami, ALLAH dai ya ƙyauta ya shiryrmu mu da halinmu”.
       “Amin dai to”.
Iyami ta faɗa badan taso firar ta tsaya iya haka ba. Daga haka hajjo tai mata sallama ta dawo gidan dan anata haramar fara kiraye-kirayen sallar magriba ma.

_________★★★★_________

*_SUNDAY MORNING_*

         Washe gari ta kama Sunday. Gaba ɗaya ahalin gidan sun tashi ne da shirin tafiya church kamar yanda suka saba. Papa ya riga kowa fita shida bodyguard ɗinsa. Aymah da batasan hidimar da sukeyi ba tana tsaka da mopping a falo akai knocking ƙofa. Batare da ta damu da sanin wanene ba ta nufi ƙofar zata buɗe. Dan akwai hijjab ƙarami a saman kayan barcin jikinta. 
       Momy ce cikin shiga ta alfarma, anci uban kwalliya kamar zataje gasar ƙyau. Abraham biye da ita shima cikin gayunsa. Kamar zata shareta karta gaisheta sai kuma tace, “Good Morning”. Bata saurari amsarta ba tai gaba abinta. Haka kawai itadai Madam Chioma batai mataba, badan mahaifiyar Yoohan bace ba da lallai zamansu a waje ɗaya zai iya haifar da matsaloli, dan a rayuwarta ta tsani wulaƙanci koda a wajen babba ne.
        Da harara Momy ta raka bayan Aymah data koma kan aikinta batare da ta sake bi takansu ba. Ɗakin Yoohan kai tsaye ta nufa Abraham biye da ita. Sai dai koda ta tura ƙofar suka shiga sai taga wayam. Jikin ƙofar toilet taje nanma babu wani motsi, ta tura ƙofar ta leƙa babu kowa a ciki, amma dai da alama anyi amfani da shi babu jimawa. Tunanin ko yana ɗakin motsa jikinsa ne ya sata fitowa ta nufi can. Lokacin Aymah tana dining tana aikinta ko kallonsu batayi ba. Canma babu Yoohan, babuma alamar yau ya shigo wajen dan komai tsaf yake.
        “K ina my son?”. 
   Nu'aymah taji muryar Momy a bazata. Ɗago dara-daran idanunta dake saka tsigar jikin Momy tayi tana kallonta. A yanayin halin ko-inkula tace, “Nima ban gansa ba tunda na tashi”. Daga haka ta ɗauki botikin ruwan mopping ɗinta ta nufi ɗakin Yoohan ɗin danta gyara tunda taji baya a ciki.
       Cike da takaici Madam Chioma ta bita da harara, kafin taja hannun Abraham su fice. Fita tai harabar gidan, dan sauranma duk sun fita harma sun shishshiga motoci.
       Guards ɗin Yoohan ɗin ta shiga tambaya ko sunga fitarsa?. Solomon ya bata amsa da cewar ya fita tun ɗazun ma, sunce zasu bisa yace baya buƙata. Ranta a ɓace tace, “Baku da hankali, sau nawa nake jaddada muku kubar barinsa yana fita shi kaɗai?. Da wace motama ya fita tunda naga duk ga motocinsa?”.
       Kan Solomon a ƙasa yace, “Sorry maa. Babu yanda banyiba koni kaɗaima na bisa amma yaki, a mashin ya fita kuma”.
        Wani shegen ihu ta buga tana ambaton “Jesus!!. Da wannan uban iskan safiyan kuka barshi ya fita a mashin dan ku kidahumai ne? idan Asthma ɗinsa ya tashi fa?”. Duk yanda sukaso ta fahimci ba laifinsu bane sam taƙi. Ihunta sai da yasa harsu Gebrail da suka shiga cikin mota duk suka fito. Nu'aymah kanta dake can sama sai da ta jiyo, hakan yasata buɗe Window ɗin bedroom ɗin Yoohan tana leƙosu. Ba ƙaramin dariya madam Chioma ta bataba yanda taketa faman tsalle da bala'i harta yadda takalman gayun nata saboda jarabar da takema guards ɗin Yoohan. Dariya sosai Aymah tasha harda hawaye, a ranta tana sake jinjina hauka da rashin kangado irin na waɗannan mutanen. Danma batasan akan mi madam Chioma ke bala'in bane😂.

         Jin gidan yayi tsitt bayan gama bala'in madam Chioma da wucewarsu  sai tunanin maganar hoto ta dawo mata a cikin rai. Tabbas wannan shine lokacin da take da shi akan hakan tunda taga duk sun fice kamar maigadi ne kawai aka bari. Sai dai bata sani ba ko hadda duk masu aikin gidan. Sannan kuma bataga Miracle ba ma a amasu tafiyar.
     Ɗakinta ta koma tai wanka a gurguje. Shiryawa tai cikin doguwar rigar jallabiya blue. A falo ta zauna danta karya saboda yunwa dake cinta. Jiya tayi barci da wuri bataci abinci ba, duk da ma har yanzun ta kasa sakin jiki da abincin gidan sam. Ta gwammace zaman cin kayan ƙwalam ɗin da Yoohan ya ajiye. Aiko dukta kusan ganin ƙarshensu batare da ya sani ba.
       Yanzun ma madara ta haɗa da kauri tai zaman shan Cornflakes hankalinta kwance. Tana sha tana tunanin hanyar shiga sashen papa ɗakko hoton nan, a gefen zuciyarta kam cike da fargabar ALLAH yasa bai ƙona ɗin ba. Wannan tunanin ne ya saka cornflakes ɗin fita mata a rai ma. Ta ture bowl ɗin gefe tana miƙewa. Bedroom ɗinta ta koma ta leƙa harabar gidan ta Window, sai da ta tabbatar babu motsin kowa sai maigadi kawai sannan ta rufe glass ɗin a hankali.
         A falon gidanma bataga motsin kowa ba, hakama sama ko ina shiru ƙofofin bedrooms ɗin duk a rufe. Duk da haka batayi gangancin yin komai kai tsaye ba. Ta sauka downstairs ɗin ta shiga kitchen kamar zata ɗakko wani abu. Babu kowa a kitchen ɗin tabbacin da Blessing aka tafi. Ƙofar da zata kaika bayan gidan ta buɗe ta kitchen ta fito, nanma shiru babu kowa. Ta sake dawowa cikin jin daɗi ta haye upstairs ɗin. Ɗakin da take da tabbacin nasu Miracle ne ta nufa, tunkan ta ƙarasa jikin ƙofar sosai tajiyo minsharin Miracle dake barci. A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta leƙa kanta. Kan gado ta hangota a cikin bargo, ga kafarta data sha ɗaurin bandage taɗan leƙo, key ɗin ƙofar dake ta ciki ta zaro a hankali, sannan taja ƙofar ta kulle mira ta waje.
      Lumshe idanu tayi a hankali tana karanto addu'oin neman nasara. Daga haka ta nufi sashen papa da addu'ar ALLAH yasa a buɗe yake. Cikin sa'a kuwa tana tura ƙofar sai gashi ta buɗe. Nannauyan numfashi ta sauke da turawa gaba ɗaya ta shiga corridor ɗin. Ƙofar falon ma ta sameta buɗe, nanma ta shige cike da ɗoki. 
      Koda wasa batai tunanin tsayawa a falon ba, dan tasan yanda papa ya nuna muhimmancin hoton nan bazai yarda ya ajiyesa anan ba sai dai bedroom. Bedroom ɗinma dai a buɗen ta samesa. Da alama ma ko gyara bai samu ba dan gadon duk a curkuɗe yake. Bata damu da wannan ba. Ta fara buɗe-buɗen bedside drawer farko tana ɗaɗɗaga abubuwan ciki. A duka biyun bata sami hotonba. Dan haka tabar nan ta juya kan Wadrobe ɗin kaya. Sai dai koda ta buɗe ma sai ta rasa da ina ya kamata ta fara?.  Sunan ALLAH ta shiga ambata tana ɗaɗɗaga duk abinda taci karo da shi. Amma babu alamar wannan hoto. Harta sare da tunanin kodai ya ƙona. Sai idanunta suka sauka kan wani ɗan kanta dake can gefe da tarin littatafai da takardu. Nanma zuwa tai tanata ɗagawa ɗaya bayan ɗaya sai dai babu anan ma.
      Kanta ta dafe hawaye na ciko mata idanu dan takaici, tabbas yanzu kam tama yarda ya riga da ya ƙona kenan?.  Zuciyarta ce ta ayyana mata ƙasan gado. Saurin nufar gadon tayi. sai dai tana ɗora hannunta a kai tajiyo dariyar Papa a falo yana faɗin, “Kai! Kai kai gaskiya kamin bazata Andrew, da alama ka matsu da kayan nan kam gaskiya”. Dariya wanda ya kira Andrew taji yayi shima, cikin harshen turancin yake faɗin, “Mr Goshpower bazaka ganeba ne, kuɗi masu nauyi ne na hango mana shiyyasa zuciyata ta kasa zama waje guda duk da nasan kana church a irin wannan lokacin”.
        Wata shegiyar dariya Papa ya kece da ita yana nufar hanyar bedroom ɗinsa, “Ai kai indai akan kuɗine zakama iya saka kanka a kowane kalar haɗari, shiyyasa kaga bana wasa da al'amarinka”. Ya ƙare maganar yana ƙarasa tura ƙofar bedroom ɗin da Aymah ke a ciki ya shi🙆🏻............✍

  Hannuna ya firgita ya gaza aikinsa😱🙆🏻.

         

_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 51

____________

_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._ 

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_

_____________

No. 51

............Tun fara jin dariyar Papa Aymah ta rintse idanunta da ƙarfi, ko ɗar bataji a rantaba na tsoro. Sai dai bata fatan ya ganta a ɗakin. Harta yunƙura zata ɗaga katifar da zaton ba shigowa zaiyiba sai taji sautin takowarsa. Da sauri ta saki tana waige-waigen ina ya dace ta shiga ta ɓuya. ‘Toilet ’ zuciyarta ta bata amsa a taƙaice. Da gudu ta nufi toilet ɗin dai-dai da murɗa handle ɗin ƙofar bedroom ɗin da papa yayi. Yana shigowa tana turo ƙofar bathroom ɗin. 
       Da sauri ya kalli ƙofar toilet ɗin danjin ta ɗanyi ƙara alamar rufewa. Yay tsaiy yana kallonta zuciyarsa fal mamaki. Shi dai yasan baiyi tsammanin ganin kowa a ɗakinsa ba. Musamman daya san duk ahalin gidan ya barsu a church ne. Shima harya fara lecture sai ga baƙonsa mai muhimmanci Andrew yazo. Dole ya baroma Uncle Mike shikuma yazo yaji da baƙon nasa dan yafi lecture ɗin da zaiyi a church ɗin muhimmanci. 
       Duk da yasan babu kowa ɗin dai, sai ya sami kansa dason tabbatarwa. Dan haka ya nufi toilet ɗin yana zancen zuci. 
       ‘Ya ALLAH!’. Nu'aymah ta faɗa a zuciyarta tana rumtse ido da ƙarfi jin kuma ya nufo toilet ɗin. Da sauri ta koma ta jikin bayan ƙofar, yanda idanma ya buɗe bazai gantaba sai dai idan shigowa yay ya rufe.
     Ƙofar kuwa ya tura ya leƙa kansa yana bin ko ina da kallo. Baiga alamar akwai wani motsi ba saboda numfashi Aymah ta ɗauke gaba ɗaya. Yay guntun tsaki ya jawo ƙofar ya rufe ransa na raya masa abarda ya shace a daren jiya bata gama sakinsaba kawai.
        Yana maida ƙofar ya rufe Aymah ta saki wani nannauyan numfashi, hannunta toshe da bakinta, idanunta kam har sun kaɗa sunyi jajur dan wahala. Da sauri ta matsa tana leƙensa ta kafar makulli. Ta zaro idanu waje da saurin sake toshe bakinta jin zatai suɓutar baki saboda ganin Papa daya danna wani ɗan abu a jikin Wadrobe ɗinsa. A hankali Wadrobe ɗin ta zuge kanta gefe, bangone sosai kamar yanda kowa ya sani ya bayyana. Amma a mamakinta sai taga yasa hannu yana shafa bangon a hankali, yanayi yana kallon ƙofar shigowa bedroom ɗin. Da alama tsoro yake ƙila kar baƙon nasa ya biyosa. Gani tai ya sake danna wani abu a jikin bangon, sai ga wani ɗan loko kamar drawer ya bayyana. Sai dai shi wannna murfinsa na ƙarfene. Key ya ɗakko a samansa ya buɗe, bata ganin abubuwan dake ciki saboda murfin ya tare ta. Wani madaidaicin jakka ya fiddo a ciki ya ajiye a kan gado, ya cigaba da ɗebo abubuwan da ba fahimta takeba yana lodasu a jakkar. Yana ƙoƙarin rufewane farar envelope ta faɗo. Gani tai ya duƙa ya ɗauka yana jan ƙaramin tsaki, ya ɗanyi magana da yare sai kuma ya ajiye envelope ɗin a saman gadon itama sannan ya maida Wadrobe ɗin yanda take ya ɗauki jakkar ya fita yana gyara wuyan rigarsa.
         Da sauri Aymah ta fito tana haɗa gumi, ta ɗauki envelope ɗin jikinta na tsuma ta buɗe. hoto ta gani, duk da bata iya zaman kallon wanene a hoton ba haka kawai zuciyarta ta bata hoton da take nema ne tabbas. zaresa tayi a cikin envelope ɗin, ta buɗe bedside drawer data ga invitation a ciki ta zaro ɗaya ta saka a envelope ɗin. Shi kuma wanda ta ɗauka ta ɗaga rigarta ta saƙa ciki sannan ta gyara ta nufi ƙofa cikin sanɗa. Leƙasu ta farayi ta kafar makulli, hakan yay dai-dai da tasowar papa ya sake nufo ɗakin. Da sauri ta shige cikin labulen window tana rumtse ido, dan harga ALLAH yanzu kam zuciyarta bugawa take da dauri-sauri. 
        Jinin ɗan adam ya wuce wasa a waje, dan haka papa sam zuciyarsa ta kasa gaskata masa babu mutum a ɗakin. Ƴan kalle-kalle ya farayi a ɗakin, idonsa ya tsaya ƙyam a inda Aymah take cikin labule. Duk da bawani nuna alamun tana wajen labulen yay ba, saboda yanada kauri da cika, sai ya nufi wajen. Baƙaramin bugawa ƙirjin Nu'aymah ya keyi ba a wannan lokacin, zuciyarta ta buɗe sosai kamar zata faso ƙirjinta ta fito ta toshe bakinta da ƙyau tana rumtse idanu da ƙarfi, dan tama rigada ta sallama sai ya ganta.
        Yana ɗora hannunsa saman labulen wayarsa nayin ring. Tsaki ya ja tare da ja baya, ya zaro wayar  yana sake jan wani tsakin. Sai dai ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa da sauri yasa wayar a kunne.
        A hankali Nu'aymah ta sauke numfashi da buɗe idanunta ta sake buɗewa a hankali hannunta dai-dai saitin zuciyarta. Kobi takan wayar da papa keyi bataiba, sai dai jin ƙauri yasata ɗan buɗa tsakkiyar labulen ta leƙa. Hoton nan taga yana ƙonawa yana cigaba da amsa wayar. Sai da hoton ya kammala ƙonewa tsaf a cikin envelope ɗin dabai ciresa ba sannan ya ɗauka abinda ya shigo ɗauka ya fice yana cigaba da wayar. 
       Saurin fitowa tai daga cikin labulen, dan ta fahimci dolene tabar sashen nan kafin baƙon papa ya tafi.. Komawa ta sakeyi jikin ƙofar yanzunma ta leƙa. Hangosu tai gaba ɗaya hankalinsu nakan centre table da alama wani abu suke lissafawa. Buɗe ƙofar tayi a hankali, ALLAH ya sota ma bata ƙara, ta ziro ƙafarta ta dama tana ambaton sunan ALLAH, ɗayar ta sake zirowa ta fito gaba ɗayanta batare data rufe ba. da sauri ta duƙe ganin baƙon papa zai ɗago, ta fara tafiya da rarrafe har zuwa bayan kujerar da papa yake.
         Ganin yanda Andrew ke kallon ƙofar bedroom ɗin kamar baya fahimtarsane ya saka papa tambayarsa ko lafiya?.
       Kai tsaye Andrew ya tabbatar masa tabbas mutum ya gani ya fito a ɗakin. Zabura Papa yayi ya miƙe,  hakan ya bama Aymah damar rarrafawa da sauri tai gaba hanyar ƙofa, ta buɗe ƙofar da gudu ta fita. Gudunta ya sakasu juyowa da saurin suma, sai dai ta rigada ta fice. Biyota sukayi dan sunajin sautin gudin nata. Suna fitowa tana maida ƙofar sashensu data sami damar shigewa ta rufe. A falo sukaci karo da Yoohan da shigowarsa gidan kenan shima, jin babu motsinta a sashen ya sakashi leƙawa ɗakinta ko barci takeyi. Sai ya sami ɗakin wayam.
      Sam baiga daga ina ta fitoba. Jinta kawai yay a jikinsa a bazata, hakan ya sakashi yin baya suka faɗa a kujera a tare, yana ƙasa tana a samansa. Riƙeta yay da ƙyau yana matse ido dan yaji zafi a kafaɗunsa, in kuma ya saketa zata faɗi, itama a firgicen da takene ya sakata mamuƙesa yanda ya kamata, har yana jiyo yanda zuciyarta ke gudu akan ƙirjinsa. Kusan mintuna uku suna a haka, sai da ya tabbatar bugun zuciyarta ya dai-daita yanda ya kamata sannan ya tura hannunsa cikin gashinta, gyalen jallabiyar ya zame. Saurin yunƙurawa tai tana ƙoƙarin ture masa hannun. “Nikam minene haka kuma?”. Ta faɗa tana kumbura fuska.
      Bai kulata ba, ya cigaba da tura hannunsa har sai da ribbon ɗin data ɗaure gashin ta fita gaba ɗaya gashin ya baje. Ƙara yunƙurawa tai da zafin nama zata raba jikinta da nasa ya maidata suka sake mannewa. Zatai magana yay saurin faɗin, “Shiiii!!”.  Bata fuskar ta sakeyi da cewa, “Toni ka sakeni na tashi”.
        Batare da ya saketanba yace, “Daga ina kike haka?”. 
     “Babu ko ina, tsoratani akayi”. 
Ta bashi amsa tana ƙoƙarin sake tashin, maidata yayi fuskarta gab da tashi har hancinsu na gab da gogar na juna. Duk yanda taso yin tsiwar tata sai ta gaza. Dan yanda ya sarƙeta da mayun idanunsa, ga numfashinsa da yake busa mata yana zuƙar nata shima sai taji kamar ya wani ɗaɗɗauretane da igiyoyi, ga wani shegen kwarjini da yay mata da cika idanu. A takema ta fara jin kasala na saukar mata.
         Ƙofar falon da aka buɗe ne ya sakasu sauke ajiyar zuciya a tare, ido huɗu sukayi da papa daya shigo da gani kasan a rikice yake. Nu'aymah tai azamar yunƙurawa zata tashi daga jikin Yoohan. Shima sakinta yay saboda ganin a yanda papan ya shigo.
       Papa ko da kallo ɗaya yay musu ya ɗan kauda kansa sai ya sami kansa da sauke numfashi. dan a yanda ya gansu kawai ya tabbatar masa ba ɗaya daga cikinsu bane ya shigar masa ɗaki kamar yanda yay zargi daga farko.
       “Papa lafiya kuwa?”. Yoohan ya faɗa yana sauke Aymah dake ƙoƙarin barin jikinsa a hankali”. Da sauri papa yace, “No Son karka damu, kuyi haƙuri na shigo muku babu knocking ”.
       “Babu damuwa papa. Amma inji dai ba wani abune ya faru ba ko?”. dafe kai papa yayi dan duk ya shiga ruɗani. Yace, “John ni nama kasa fahimta gaba ɗaya, mune a ruɗe kokuwa abinda mukai tunanine a gaske?. Kawaifa muna zaune da baƙona sai mukaga kamar mutum ya fito a bedroom ɗina. Mun duba ko ina na gidan nan kuma amma babu alamar kowa. Maigadi ma ya tabbatar mana shi baiga kowa ba sai kai daka shigo tun ɗazun”.
       Kafin Yoohan yay magana Aymah tai saurin faɗin, “Yes papa nima naga mutum, ina kitchen zan dafa noodles naji gudu an sakko daga downstairs, shinefa na tsorata na shigo da gudu na zatama ɓarayine ko aljanu”.
       “Daughter da gaske?”.
    “Eh papa, da gaske naga mutum ya fita da gudu”. Tai maganar tana satar kallon Yoohan ta ƙasan ido.
       Daga Yoohan har papa sun yarda da zancen Aymah, hakan yasa duk suka fito har ita da keta faman maƙalewa bayan Yoohan wai a dole tsoro takeji (😂wagga ɗiya ko).
       Tsaf Nu'aymah ta saka papa da Maigadi da Yoohan da Andrew zagaye gidan nan duk faɗinsa. Tana kuma biye dasu kamar jela. Sai dai babu ko alamun wani yama shigo gidan balle maganarta ta tabbata.
         Dafe goshi Yoohan yayi yana faɗin, “Papa wannan shi nake faɗa maka a koda yaushe. Ka daina saka guards ɗin gidannan gaba ɗaya tafiya church, taya za'ace maigadi ne kawai za'a bari a gida bayan wasu su irin wannan damar suke nema. Dolene a sake tsari dan wannan tsarin baiyiba na shigo mana da kowa cikin gida”. Ya ƙare maganar da kama hannun Nu'aymah suka shige ciki.
       Daga papa har Andrew dake lasar baki tun ganin Aymah da kallo suka bisa. Kasa haƙuri kuwa Andrew ɗin yayi, ya shiga tambayar papa ina suka samo wannan ƙyaƙyƙyawar young lady ɗin haka?. Duk da takaici daya kama papa sai da ya bama Andrew amsa da cewar daughter in-low ɗinsa ce. Da yake baisan Yoohan ɗin yayi aureba, dan papa bai tura masa invitation ba. Kai duk ma abokan harƙalarsa ta bayan fage bai gayyacesu wajen taron ba.
      Ciki suka koma ya sallami Andrew dan maganganun Yoohan ne ke neman masa tasiri a cikin zuciya. Idan har ya fahimta dai-dai Yoohan yana zargin wani shirine da Andrew kenan? Maybe shine ya shigo da wani batare da shi ya sani ba saboda wani dalilinsa. Wannan tunanin da yay masa tasiri ne ya sakashi bincike tun daga bedroom ɗinsa har falon gaba ɗaya. sai dai baiga wata alama ta wani abunda zarginsa ke a kai ba. Amma duk da haka bazai sakankance ba kai tsaye. Dan haka ya canja password ɗin kwaba ɗinsa ta sirri yama ƙara mata wasu securitys ɗin.

           Aymah kam suna shiga ta zare hannunta cikin na Yoohan ta kwasa da gudu zuwa bedroom ɗinta tana faɗin, “Fitsari nakeji”. 
      Da kallo kawai ya bita harta banko ƙofar, ya ɗan girgiza kansa da ƙarasawa cikin falon ya zube akan kujera yana furzar da iskar ɓacin ran kwashe-kwshen papa. Baisan daga ina kuma ya kwaso musu wannan mai suffar marasa imanin ba.

          Koda Aymah ta shiga ɗaki bata iya tsayawa a bedroom ɗin ba, dan tunaninta Yoohan zai iya biyota nan. Toilet ta shiga ta maida ƙofar ta rufe da murza key har sau biyu. Sai da ta tabbatar tayi gam sannan ta ɗaga rigarta ta zaro hoton da duk ya lanƙwashe. Bata damuba, sai tsuramasa idanu da tayi ko ƙyaftawa babu. Ba kowa bane a hoton face papa yana ɗanyen matashi jagab, sai ƙyaƙyƙyawar balarabiya mai tsananin kama da Yoohan a gefensa da shekarunta bazasu wuce sha tara zuwa ashirin ba. Da cikinta tsoho wanda yay mata ɗas a jiki. Hannunta dana papa duk akan cikin suna murmushi. 
      A take wani gumi ya fara karyoma Nu'aymah, ta nuna balarabiyar da ɗan yatsa bakinta nason furta magana amma ta kasa. Sai a zuciyarta zantuttukan keta kaiwa da kawowa na mamaki, al'ajabi, ruɗani, harma da firgici. ‘To mi hakan ke nufi?’. Ta ambata a fili da ƙyar.
      Harga ALLAH man kanta fa yana neman kwararewa a ƙasa, dan haka ta jingina da ƙofar tana furzar da huci mai zafi tare da sharce gumin daya taru mata a goshi. ‘Tabbas akwai magana kenan. Wacece wannan tare da babansa? Sannan kenan wannan matar dake a gidan itace ta haifesa da gaske? Kokuwa yaya abin yake?’. 
       Waɗan nan tambayoyi suke sake rikitar da ita da hautsina mata man kai da ruwan kwanya awaje guda.....
      Maganganu take ɗanji sama-sama kamar a cikin ɗakinta, hakanne ya sakata leƙawa ta kafar mukulli bayan ta zaresa a hankali. Momy ce ke magana a faɗa-faɗa. “My Son wai yaya ma zaku yarda da zancen yarinyarnan cewar wai taga wani. Sai dai idan itace da kanta ta shiga take neman raina muku hankali. tayaya idan ba ita baceba za'a kulle Miracle ta baya bayan kuma Joy ta tabbatar mana bata kulleta ba, ita kuma gashi tace babu key a cikin ɗakin”.
        Idanu Aymah ta zaro waje, tai saurin kallon yatsanta da key ke maƙale wanda bana ko ina bane sai na ƙofar ɗakin su Mira data kulle. Gaba ɗaya tama manta da shi a hannunta. Kanta ta dafe dan ganin key na neman jiƙa mata aiki bayan ta tsalake rijiya da baya........
         Cikin ɗacin murya da Yoohan ya fara magana ya katsema Aymah tunaninta...  “Momy Please, banajin daɗin irin waɗanan maganganun naki akan matata. Taya zakice itace? Idan kince ita ɗince ma mita sani akan gidan nan da har zataje sashen papa kuma harma cikin bedroom ɗinsa? Mima zatayi acan?”. 
           Dariya sosai ya bata ganin yanda ya haƙiƙance akan abinda bai saniba wai shi nan mai mata. Taima ƙofar gwalo tare da jefa key ɗin cikin toilet tai flushing ɗinsa, sannan ta cire rigarta ta naɗe hoton a ciki ta hau yin wankanta hankali kwance. A ranta tana addu'ar ALLAH ma yasa kar a samu key ɗin buɗe Mira. Tun tana cigaba da jiyosu sama-sama har taji tsit. Ɗauraye jikinta tayi taja rigar wanka ta saka. Dama ta ƙirƙiri wankan ne dan batason fita ta haɗu da madam Chioma.

       Koda ta fito bata samesu a ɗakin ba, hakanne ya bata damar ɓoye hotan sannan ta sake sabon shiri ta fita dan yunwa takeji batayi breakfast ɗin ƙwarai ba ta tafi ɗaukar magana.
        Duk da hangosa da tayi a saman dining ɗin bata fasa nufar can ba. Sarai shima ɗin yaji motsinta amma ya basar yana cigaba da danna waya. ayaba da gyaɗa a gabansa. Bowl ɗin data haɗa madarar ɗazun ta ɗauka takai kicin, zubashi tayi a ƙaramar tukunya ta ɗora kan gas, tana tsaye sai da ya tafasa sannan ta juyosa ta fito. Inda ta barsa nan ta sake taddashi. Yanzun kam duk yanda taso haɗiye maganar dake bakinta ta kasa sai da ta tanka. ƙasa-ƙasa tace, ‘Yau ina ganin ƙazanta, wai ayaba akeci da gyaɗa’.
          Shi dai baima jitanba balle yasan da shi take tunda da hausa tai maganar. Itama daga haka bata sake tankawaba ta zauna ta fara shan madarar data dafo. Kansa ya ɗago ya kalleta a karo na farko, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida kansa ga wayar.
          Gyaran murya ta ɗanyi, hakanne ya sakashi ɗagowa ya sake kallonta. Ta wani ɓata fuska irin bata son wargin nan. Shi dai baice uffanba. Lura da tai ba magana zaiyiba yasata faɗin, “Uhhm ni dai gaskiya zan dinga girka abincina anan ni kaɗai, dan ban iya cin waɗan nan abincin naku ba”.
        Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, batare da yace komaiba ya maida kansa a kan wayarsa. A ƙufule tace, “Dan ALLAH Yah Yoohan”.
       Duk yanda yaso basarwa hakan ya gagara. Karon farko a rayuwarsa da yaji sunansa a bakinta. Sannan yasan a hausance kalmar Yaya dai girmamawace ga wanda aka kira da ita. A hankali ya lumshe idanunsa ya buɗesu a kanta, yana binta da wani narkakken kallo data gagara fahimtar ma'anarsa. Kamar mai ciwon baki yace,
       “Naji”
           Ya bata amsa a taƙaice, dan har yanzu ransa a ɓace yake da zantuttukan Momy. Ita kuma mutuniyar taku da yake babu man kai ta kasa fahimtar ransa a ɓacen yake.
       Shine ya fara bar mata wajen bayan ya cinye ayaba da gyaɗansa. 

_________★★★★

          Bayan sallar la'asar tana a ɗaki kwance tanata faman ƙullawa da kwancewa akan yanda zata ɓulloma Yoohan da tambaya game da sanin matsayin Momy a garesa ya shigo. Harya ƙaraso gaban gadon bata sani ba. Sai da ya zauna ne jikinsa ya taɓa mata hannu sannan tai firgigit. Da sauri ta miƙe zaune tana cika baki da iska. Bakinsa ya taɓe da kauda kansa yana lumshe idanu. 
       “Ki shirya muje”
Ya tari numfashinta ganin zatai magana. Shi kuma baya buƙatar surutun sam. Haka yake idan abu ya ɓata masa rai, sai ya wuni yana ɗacin rai. Hakan yasa mafi yawan lokaci ƴan gidan suke gaza gane kansa. Ita kanta Aymah ganin har yanzu fuskar tasa a tsuke kamar ɗazun duk sai taji shakkar masa tsiwar tata. Duk da ma dai har ranta taji daɗin jin fita zasuyi.
       Fita yay alamar bata damar shiryawa. Aiko cike da ɗoki ta shiga neman kayan canjawa. Tana cikin zarowa Yoohan na sake shigowa ɗakin. Kallonsa tayi da sauri, zatai magana sai dai ta kasa saboda cin karo da fuskarsa dake a matuƙar tsuke. Cikin kaushin murya yace, “Idan kin shirya ki sameni a waje”.
           Kanta ta ɗaga masa dan bataga fuskar yin wargi ba. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya. A ranta duk sai taji babu daɗi, dan tasan abinda ya saka masa ɓacin ran dai da gaske ta aikata, amma yanata ƙoƙarin kareta a wajensu har yana saka kansa a ɓacin rai irin haka.
        Da ɗan hanzarinta tai shiri cikin wata doguwar rigar jallabiyar, amma yanzu baƙa. Taji adon blue stones sai ƙyalli da ɗaukar idanu takeyi. Bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta saka hula da naɗa madaidaicin blue gyalen daya shiga da adon stones da akaima rigar. Taɗan gyara fuskarta tasa takalma ta fito tana ƙamshinta mai sanyi.
         A sashen ta fito gaba ɗaya tana karanta:
        
اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرورِهِمْ .
Allahumma inna naj'aluka fee nuhoorihim wana'oothu bika min shuroorihim.
            Baƙi sosai ta samu a falon ƴan ziyarar Sunday. A taƙaice tace musu “Good Afternoon” dan taga akwai manya. Batare data jira sanin waɗanda suka amsaba tai ficewarta. A harabar gidanma dai duk baƙin fuska taita cin karo da su. Wasu ta gaishesu wasu tai wucewarta. 
     Da sauri Gebrail dake jikin motar da Yoohan ke a ciki ya buɗe mata ƙofa yana wani rissinar da kai kamar gaske. A ranta tace, ‘Munafuki dan ka gansa a wajen kake wani acting like mutumin ƙwarai. Zanyi maganinka ne ai, bara na gama da na sama da kai’.
       Tana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da leƙowa. a marairaice yace, “Please Brother na shigo muje tare?”.
               Wata banzar harara Yoohan ya watsa masa. Saurin barin jikin motar yay yana ɓata fuska. A ransa kuwa wani irin wutar son Aymah ce ke ruruwa masa a zuciya tare dajin zafin Yayan nasa mai share kukansa a koda yaushe wajen magance masa bukatunsa. Da ƙyar ya iya nufar garden inda abokansa suke zaune da giyar da zasu sha ransa duk a ƙuntace. Dan tabbas yanaji a ransa bazai iya haƙuri ya barma Yayan nasa zuƙeƙiyar yarinyarnan datai dai-dai da burinsa ba. Shi musilincinta ko yarenta duk ba damuwarsa ba. Itaɗin yake so, so irin wanda ke shiga ɗin nan farat ɗaya a zuciya batare da yayi shawara da mai zuciyar ba. Dan a kallo ɗaya da yayma Aymah a wajen dinner tai masa shigar corona virus a zuciya. Bakuma tayi sanya ba wajen mamaye dukan zuciyarsa da ilahirin jikinsa. Dan haka koda bala'i sai ya mallaketa, sai ya ɗanɗani zumarta, sai ya ɗanɗana mata tashi kuma. Yanaji a ransa zata soshi fiye da Brother Yoohan inhar ya bayyana masa abinda ke cikin zuciyarsa game da ita..............✍

😸Wa yaga kwamatsala ɗan Nageriya da mulkin Amuruka😜. 


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 52

_________________
_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._ 

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_


______________

No. 52

............Motar tayi shiru, bakajin komai saina fitar sassanyan ac da sautin karatun al-qur'ani daya saka can ƙasa. A hankali yake tuƙin kamar baya so. Fuskar nan babu ko alamun yasan minene ma murmushi. Duk da Aymah tasan shiɗin ba mutum bane mai fara'a aɗan zaman da sukayi, sai duk tajita a takure da yanda yay matuƙar tsuke fuskar.
       Sake lafewa tai abinta cikin kujera ƙamshin motar da sanyin ac na kuma saka mata kasala. A zahiri zakace idanunta a rufe suke, sai dai sam ba haka bane. Ta ƙasan ido take ƙare masa kallo daki-daki kamanin balarabiyar nan ta hoto na sake bayyana tattare da shi. A ranta kuwa rayawa take, ‘Dolene kayi ƙyau, ashe kanada alaƙa da larabawa. Ga papan ma duk da kasancewarsa ɗan African, Africa ɗin ma Najeriya, Najeriyarma kudanci shiɗin ƙyaƙyƙyawa ne tabbas’.
      Yoohan dake ji a jikinsa kallonsa akeyi ya ɗan juyo ya kalleta. Duk da idanunta a rufe suke ya fahimci ba barci take ba. Dan inba ita ɗinba babu wanda zai kallesa tunda a mota suke, motarma mai tinted glass. Baice komaiba ya cigaba da tuƙinsa kamar baya son suje inda zasu ɗin. 
          Sun isa haɗaɗen shagon sayayyar da Abujawan da kansu keji da shi, (bazan faɗi suna ba, danni na dainama masu shaguna talla yanzun🙄, duk maison a ringa saka sunan shagonsa a littafi yazo ya biya kuɗi koda baturene😎😏). 
            Sai da ya gama dai-daita fakin ya buɗe motar zai fita sannan Nu'aymah ta buɗe idanu. Batasan wannan cinkushe fuskar dan haka cikin neman tsokanar data iya tai saurin faɗin, “Ni dai gaskiya bazan shiga da kaiba wani yazata kidnapping ma'aikatan mukazoyi”.
        Jin abinda ta faɗa ɗinne ya hanashi zura ɗayar ƙafar da yay niyya dan har ya sauke ɗaya a ƙasa. Juyowa yay yana kallonta. Ta cika kumatu da iska tana tura baki. “Yoni ka daina kallona da waɗan nan idanun iya gaskiyata na faɗa. tayaya dan ALLAH zan bika, kaga fuskarka kuwa? Yasin kamar ta shekau na dajin sambisa. Dan haka yi gaba zan biyoka a baya”.
      Duk yanda yaso daurewa ya gaza, ya kauda kansa gefe murmushi na suɓuce masa. A ransa yana jinjina rashin jin yarinyar nan da rashin tsoro. A fili kam sai ya ƙarasa fita  yana faɗin, “Silly girl sakko, kafin in jehoki ƙasa”. 
         Baki ta murguɗa tana buɗe ƙofar ta fito. Cikin ƙunƙuni tace, “Kaima dai nakusa fara kiranka Silly boy ɗin nan daka ishi mutan da shi”. Ta ƙare maganar tana ƙarasawa inda yake tsaye yana gyara p-cap ɗin da a yanzu itadai ta gansa da ita. Dan da suka fito kansa babu hula. Kallonsa tai ta ɗauke kanta, a ranta kuwa tana yaba yanda p-cap ke masa ƙyau idan ya sanya. Musamman a yanzu da komai na jikinsa ya kasance baƙi, hularce kawai fara. 
        “Malama kallon da kikemin ya isheni”. Taji maganarsa a bazata. Sai dai yayi gaba kamar bashine ya faɗa ba. Murya taɗan ɗaga kaɗan yanda zai jita tace, “Kai da wane idon kasan ina kallonka?”.
         Tsayawa yay tare da juyowa gaba ɗayansa. Ita kuma ta riga da tazo gab da shi sai tai ƙoƙarin yin baya ganin zasuyi karo. Tako tafi gaba ɗayanta zatasha ƙasa. Da sauri ya bita ya tallafo ƙugunta ta dawo jikinsa. A yanda ƙirjinta ke bugawa ya tabbatar masa taji tsoron faɗuwar sosai. Samun kansa yay dajin dariya na taho masa. Ya ɗanyi kamar zai saketa, tai wani uban tsalle ta mamuƙesa zata saki ihu yay azamar danne bakin da ɗayan hannunsa yana kallon yanda tsirarun mutane dake shiga da fita cikin wajen suna kallonsu. Wasu na dariya wasu na gulma.
      Idanunsa ya rumtse da sauri yana faɗin, “Shikenan kin tara mana mutane hankalinki ya kwant...” Ai baima kai ƙarsheba ta fincike jikinta tana turesa. Sai kuma tai saurin komawa bayansa ta ɓuya ganin da gaske kallon nasu akeyi. Gaba ɗaya kunya ta dabaibayeta kamar ta nutse ƙasa takeji.
        “ALLAH ne ya rama min”. Ya juya da wani salo yana yin manar a cikin kunnenta kamar bashi ya faɗa ɗin ba. Da sauri tabi bayansa tana tura baki gaba. Sai dai da alama bakin tsuwar ya mutu kam. 
       Kamar yanda ƙa'idar shiga wajen take sai da akai bincikesu sannan suka shiga, sai dai yanzu kam a jere suke tafiya gwanin sha'awa. Batare da ya kalleta ba yace, “Mizaki saya?”.
     “Duka shagon”. Ta bashi amsa itama batare data kallesa ba.
      Shima da yake ya iya baƙar maganar sai cewa yay, “Okay sai muje a saidama Shekau ɗin da kikace Kano muzo musai shagon da kuɗin”. 
       Babu shiri taja birki harda riƙe ƙugu. Shima tsayawar yay ya tura duka hannayensa cikin aljihun yana kallonta fuska a ciskule. “Ai wlhy sai dai a saida garinku, dan kano tafi ƙarfin shekau”.   
       “Trouble maker”. 
Ya faɗa yanayin gaba. Bayansa tabi tana ƙunƙuni, sai dai bajin abinda take faɗan akeba. A haka suka shiga wajen kayan ƙwalam da maƙulashe. Irin kalolin biscuits da kayan ƙwaɗayin dataga ya tara a gida yaketa ɗiba yanzun ma, hakan yasa ta dinga binsa da kallo kawai tana gulmarsa a cikin zuciya, (wai maƙwaɗaici ne🤣).
       Sai da ya kusan cika keken sannan ya kalleta. “Kifa ɗeba naki, dan ba ƙara cimin nawa zakiyi ba yarinya”. Idan ba ita datasan shine yayi maganarba babu yanda za'ai ace shi yayita. Dan ya ɗauke kansa ya cigaba da harkar gabansa.
       Leɓe Aymah ta ciza, a ranta take raya ‘zakaga mugunta kuwa yau ɗan balarabe’ komawa baya tayi itama ta jawo nata keken. Ta shiga lodar chocolates da kayan ciye-ciye iri-iri. Wanima ko saninsa batayiba balle tasan zaiyi daɗi ko bazaiyiba. Saida ta cika kwandon nan dam da kayan ƙwaɗayi kawai har tana turawa da ƙyar tsabar mugunta. Tana a layin ƙarshe zata ɗauki wani roban chewing gum taji ƙamshin turaren da ya sakata waige-waige da sauri. Cikin kwandon ta jefa chewing gum ɗin tai saurin fitowa a lungun tana leƙe. Babu ko mai alamarsa, sai dai tabbas wannan ƙamshin shi kaɗai ta sani da shi. Duk da zuciyarta na ayyana mata wanine bashi ba ta kasa aminta. Sai ƙara kutsa kai take kowanne layi dan dubashi. Wani irin mugun bugawa ƙirjinta yayi jin an riƙo mata hannu. Ta waigo da sauri sai taga Yoohan ne. 
       “Miye kike nema haka?”.
   Yay maganar babu wasa a fuskarsa. Sannan muryarsa a kausashe kamar wanda yake cikin fushin da ɓacin rai. Kanta ta girgiza masa tana ƙoƙarin maida ƙwallar da suka cika mata ido. Bai sake cemata komaiba yaja hannun nata suka bar wajen. Duk da taga bai maidata wajen kayanta data bariba, ba tai magana ba. A mamakinta saita hangi kayan can wajen bada kuɗi ana loda musu a ledoji. Suna isowa matar fuskarta faɗaɗe da murmushi tace, “Doctor ATM”. Zarowa yay a wallet ya miƙa mata batare da yace komaiba. Ta amsa idanunta akan Nu'aymah dake sake waige-waigen ko zata gansa anan. 
      “Amaryar Doctor Good evening ”. Maganar matar ta maidota hankalinta. A taƙaice ta amsa mata duk da ta fahimci akwai sanayya tsakaninta da Yoohan ɗin. Ta ɗan dubesa lokacin da ma'aikatan wajen ke kwashe ledojin zasu kai masu mota. Har yanzun fuskarsa babu sauƙi. Gashi ya wani riƙe mata hannu gam kamar za'a saceta. ATM ɗin ya amsa yaja hannunta suka fita.
           A can wajen motar da sukazo taga anata loda kaya harma da wanda bataga sanda aka sayaba ita dai. Batayi magana ba dan bataga fuskaba. Saima buɗe mata murfin yayi yay mata alamar ta shiga. Tana shiga ya maida ƙofar ya rufe mata. Ta mazauninsa ya zagaya, taga ya buɗe lokar motar ya ciri kuɗi ya maida ya rufe. Batasan waya bamawa ba, sai dai bai jimaba ya dawo suka fice a wajen.
      A lokacin anata kiraye-kirayen sallar magriba. Gudu yake yanzu sosai, kai tsaye anguwar su Abban Abdallah ya nufa. Daɗi ya kama Aymah sai dai ta haɗiye abinta a ciki har suka isa. Anata hada-hadar shiga sallar magriba a massallacin ƙofar gidan. Horn ɗaya kuwa yayi maigadi dake ƙoƙarin fitowa zaije salla yay murmushi yana komawa ya buɗe musu. Shiga Yoohan yay da motar har ciki yay fakin Aymah nata mamakin ƙarfin halinsa.
      “Kije ciki zanje nai salla”. Yay maganar yana buɗe motar ya fita. Ai tuni ma ta rigashi fitar. Sai hangota yay ta tsilla da gudu hanyar shiga cikin gidan. Da kallo kawai ya bita harta buɗe ƙofar falon ta shige. 
      Ya ɗan lumshe idanunsa ya buɗe yana nufar hanyar fita gate ɗin da hanzari jin za'a tada salla.

       Da uban ihu Nu'aymah ta shiga tana ƙwalama su Amal kira. Aiko kamar jira suma sai gasu da gudun sun fitowa suna ihun murnar ganinta. Momy na salla take jiyo ihun nasu. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka sarara. Ɗakin Amal ɗin suka nufa inda Yusrah da Adawiya dataƙi fitowa suke hutunsu da basusan dalilinsa ba balle ranar komawa kano.
         Duk da idon Aymah ya ga Adawiya dake kwance a kan gado tana danna waya sai tai tamkar bata ganta ba ta cigaba da biyema su Yusrah dake mata sherin wai ta canja saboda daɗin aure ko sun sami baby ne?. Shaƙiyanci sukaitama juna suna sheƙa dariyar dake sake ƙullar da Adawiya. Dan suma su Amal ɗin ta ishesu. Kullum haka take yini a gidan cikin ɗacin rai, bata shiga sabgarsu basa shiga tata. Momy tayi faɗan harta gaji ta zuba musu idanu. 
           Sallar suma sukayi, kafin su idar Adawiya tabar ɗakin ta koma falo. Bayan sun idar cikin dabara Aymah take tambayarsu Amal yaushe Yusrah zata tare tunda taga Yah Ab bai koma ba. Da mamaki sosai Amal tace, “Yah Ab ɗin da ya koma Saudia tun randa aka ɗaura miki aure. Kuma Yusrah ai tace bazata tare a gidansa ba saboda fitinar Adawiya”.
          Bayanin Amal ya matuƙar ɗaure kan Aymah, dan ita dai tabbas-tabbas tanaji a ranta da Yah Ab sukai gamo a inda suka baro. Sai dai batasan dalilinsa na ɓoye mata kansa ba. Danne wannan tunanin tayi a zuciyarta ta fuskanci Yusrah datai kamar bataji mi suke magana a kai ba. 
         “Yusrah! Miyasa baƙya son zama da Yah Ab wai dan ALLAH?”.
       Murmushi Yusrah tayi tana ƙoƙarin miƙewa daga wajen gaba ɗaya, Aymah tai saurin maidata ta zauna. “ALLAH babu inda zakije sai kin amsamin tambaya ta”. 
        “Humm Aymah kenan, ba amsa tambayarki bace mai wahala, hujjar amsata. Ni bancema kowa bana son Yah Ab ba ai. Kawai dai zaman aurene banason yi da shi. Fatan da nakeson muyi ni da ku kawai shine ya maida Adawiya ɗakinta. Indan ba hakaba kuwa tsugunne bata ƙareba a family ɗinmu wlhy. Adawiya na son Yah Ab sosai duk da nasan tabbas Nu'aymah kin fita sonsa. Amma ke yanzun wannan babin ya shafe a gareki dan dama ƙaddarace tazo muku da wannan yanayin”.
          “Amma Yusrah.…..”
“No Aymah karki sake cewa komai dan ALLAH. Mu ajiye wannan maganar haka kawai. Ku tashima muje dan ga kamar momy can ta fito”.
      Badan Nu'aymah taso ba tai shiru. 

  A falo kam zaman Adawiya babu jimawa Abba da Yoohan suka shigo falon Omar biye da su. Ɗago kanta tayi da nufin yima Abba sannu idanunta ya sauka akan Yoohan da shi koma kallon inda take baiyi ba. Ganin har zasu wuce batai magana ba Abbah yace, “Adawiya baki iya gaisuwa ba ne? Ko bakiga mijin ƴar uwarkiba Nu'aymah?”.
       Da gaske gaban Adawiya sai da ya faɗi. Bakinta na rawa ta gaida Yoohan. Sau ɗaya ya amsa tare da mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa. Binsa da kallo kuwa ta cigaba da yi harya shige falon Abbah. 
       A fili tace, ‘Dama Aymah ba ƙabila akace ta aura ba? Naga kuma balarabe?’. Bata da mai bata wannan amsar dan haka tai shiru tana saƙe-saƙenta a cikin zuciya har Momy ta fito tana tambayarta ihun mi takeji ɗazun. Tana cikin sanar ma Momyn ne su Aymah suka fito. Zuwa Nu'aymah tai ta rungume Momy cike da murna.
       Momy dake dariya tace, “Ja'ira, an girma ba'asan an girma ba”.
         Dariya ta sakeyi su Amal na taya ta. Adawiya dai tai muƙuy kamar bata falon abin duniya ya gama isarta a rai game da ganin mijin Nu'aymah..
          Tura Amal momy tayi ta kira Uwaliya mai aikin da aka kawoma Nu'aymah daga kano. Ashe dama ita suka biyo ɗauka batare da Yoohan ya sanar mata ba. Ba wata tsohuwa bace ba. Zata iya kai kimanin shekaru talatin da bakwai dai. Sun gaisa da Nu'aymah momy tai musu bayanin juna. Har cikin zuciya Aymah taji son zama da Uwaliya kuwa. Dan haka cikin jin daɗi ta miƙe domin zuwa falon Abbah ta gaidashi shima.

          Basu bar gidanba sai goma saura. Sun tafi da Uwaliya. Su Amal ma sun mata alƙawarin zuwa next week dan dama Abbah ne ya hanasu wai karsuje su tada mata hankali. Amma yanzu daya ganta babu wata damuwa yace zai barsu suje ɗin amma sai weekend insha ALLAH.
          Papa kawai suka samu a harabar gidan zaune. Sai su Solomon da suma ke tasu hirar acan gehe. Ita dai tana gaida papan ciki suka wuce da Uwaliya. Shi kuma ya nufi inda papan yake zaune.
         Basu sami kowa a falon ba. Gidan ma shiru alamar duk sun kwanta. Ta fahimci ɗabi'arsu ce barcin wuri, musamman ma yaran saboda makaranta. Da kuma su ɗin kansu daya kasance duk suna fita aiki da safe. Uwaliya nata kalle-kalle ita dai har suka ƙarasa sashensu. Sarai Aymah taga Momy acan ƙofar sashenta zaune. Amma sai tai kamar bata ganta ba suka shige abinsu.
        A falo suka yada zango. Kusan zaman mintuna ashirin sai gashi ya shigo tare da su Solomon da suka kwaso kayan. Anan tsakkiyar falon duk suka zube komai suka fita suna musu sai da safe.
      Batare da Yoohan ya zauna ba ya dubi Aymah yana faɗin, “Ki kaita ɗakin kusa da sashen nan anan zata zauna”. Kamar Aymah zatai magana sai kuma tai shiru ganin ya juya abinsa ya nufi hanyar ɗakinsa. Ta fahimci har yanzu ransa a ɓace yake dai, kamarma an sake tunzurashi ne yanzu da suka shigo. Tashi tai ta raka Uwaliya ɗin, ɗakine babba da katifa a ciki da kwabbot na kaya da toilet ɗinsa kamar kowane ɗaki. Hakan yasa hankali Aymah kwanciya. Itama Uwaliya sai faman washe haƙora takeyi ganin ita da aka kawo tai aiki amma irin wannan aljannar duniya haka.

_________★★★★_________

              Washe gari da yamma tana ɗakinta bisa gado ta baje littatafan ta na islamiyya tana dubawa ya shigo. Batare data ɗago ba ta amsa masa sallamar da yayi. Sai da ya zauna a bakin gadon tare da ɗaukar littafin gabanta na SAHIH AL-BUKHARI da take dubawa sannan ta ɗago. 
      Idanu ta ɗan zaro tana kallon abinda ya ke ci. Ta tsuke fuska iya gaskiyarta tana faɗin, “Tab wannan ai chocolate ɗina ce, naga kaine kace kowa yaci abinda ya sayo ai ɗazun da safe ko?”.
          “Oh ashe babu daɗi hajjaju, ni da kika tasamin biscuits a gaba kika cinye banyi maganaba, sai ni danna sha wannan chocolate ɗin da ko wani daɗi babu”.
       Ture buks ɗin tai gefe ta miƙa hannu zata warce a hannunsa. “Tunda babu daɗi bani abuta”.
        Hannun ya riƙe yana wani kafeta da narkakkun idanunsa. Yayinda yake ɗan motsa bakinsa a hankali yana cinye wadda ya gutsira. Ƙara matsowa tai tasa ɗayan hannun zata warce again, dai-dai zai kai bakinsa.
      Fisgota yay gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa. Yay baya shima suka faɗa saman gadon. Zabura tai tana faɗin, “Malam kana shigarmin hanci da yawa wl......”
        Bai bari ta ƙarasa ba ya juyata ta koma ƙasa shi ya koma sama. Sai dai rabin jikinsa ne a kanta, a hakanma bai sakar mata nauyinsa ba dan a ganinsa bazata iya ɗauka ba. Amma tsabar ragwantaka na Aymah sai ta wage baki zata masa ihu. Hannu yay saurin ɗorawa akan bakin nata yana ɗan waro idanunsa waje. “Idan kikai ihun nan na ratse sai na haɗiye bakin kinnan yanzun nan”. 
         Hannu tasa ta ture nasa hannun tana faɗin, “Tunda kai maye ne basai ka haɗiye ba mugani”. 
       “Kema zaki koma mayyar ai”
Yay maganar yana saka idanunsa cikin nata yanda ta kasa magana ta kuma kasa janye nata idanun saboda tsabar yanda ya sarƙeta da nashi.
        Cikin wata irin kasalalliyar murya yace, “In sammiki chocolate ɗin?”.
       Duk yanda taso buɗe baki tayi magana ta kasa. Dan yanda yay maganar gab da fuskarta, ga idanunsa cikin nata sai taji kamar ya mata wani ɗaurine da igiyoyi. 
          Chocolate ɗin ya kai bakinsa ya sake gutsira kaɗan, har yanzu idanunsa na a cikin nata bai janye ba. Ya sake matsar da bakinsa gab da nata. A hankali cikin maganar raɗa yace, “Buɗe bakin”.
       Kamar wadda ake juyawa da remote Aymah ta motsa laɓɓanta kaɗan idanunta dake cikin nasa na cikowa da ƙwalla. Bata ankara ba taji laɓɓansa akan nata, a tare suka lumshe idanu, sai dai ita wasu hawaye da batasan na minene ba suka shiga silalo mata saman kumatu da gudu. Yayin shi kuwa Yoohan yake juye mata narkakkiyar chocolate ɗin daya narkar da yawunsa......

    (Kai zafafa fans wannan bada cakuleti na Yoohan yafi ƙarfina, bara naɗan fita na barsu su sarara😱. Amma zan leƙa muku ta kafar mukkuli🏃).

         Gaba ɗaya Nu'aymah ta kasa fahimtar kanta balle abinda Yoohan yake mata. Shi kansa da yake aikatawar yayi masifar shafa'a da wadda yake tare. Sai da labari ya nema canja salone ƙwaƙwalwarsa ta fara aikin masu hankali. Da ƙyar ya iya janyewa daga jikinta ya koma gefenta ya kwanta rufda ciki. itama saurin juyawa tayi ta koma can gefe taja bargo ta ƙudundune jikinta na wata irin karkarwa.
         Sunja tsahon mintuna goma a hakan kafin Yoohan ya buɗe idanunsa dake a rufe da ƙyar. Ya cija lip ɗinsa na sama tare da sake lumshe idanu ya sake kuma buɗewa akan Aymah dake a cikin bargo har yanzun. Tsaf yanayin ya shiga dawo masa a cikin kai. Duk da cikinsa daya ƙulle hakan bai hanashi tashi zauneba da sauri jin ajiyar zuciyar da Nu'aymah ke saukewa. Ya matsa inda take tare da jan bargon data kudundune a ciki har kanta.
     Cikin muryar da bata taɓa saninsa da itaba yashiga kiran “Zeeynab! Zeeynab!”.
        “Hasbunallah” tai saurin ambata akan laɓɓanta jin zuciyarta na neman faso ƙirjinta ta fito waje. duk da ba yaune karan farko da aka kirata da wannan sunanba sai taji tamkar na yau ɗin ya banbanta dana kullum. musamman daya faɗa a saitin kunnenta kuma cikin wata irin shu'umar murya. Gashi da wani irin style ɗin daya banbanta da harshen duk masu kiranta da sunan saboda hausa bata ishi nasa harshen ba.
          Ganin duk yanda yaso yaga fuskarta ma taƙi yarda ya sakashi ƙyaleta, dan cikinsa ya ƙulle matuƙa. Idan kuma ya cigaba da zama a ɗakin za'a samu matsala. Da ƙyar yace, “Okay na fita”.
        Duk da tana jinsa batako motsaba. Amma muryarsa ta sakata jin tsoro. Dagaji kasan baya cikin ƙoshin lafiya. Ƙarar rufe ƙofa kawai taji, daga haka bata sake jinsaba sai da daddare wajen sha ɗaya saura ya shigo lokacin tana ƙoƙarin hawa gado ta kwanta.
          Tanajin ƙamshin turarensa tai saurin ƙoƙarin jan bargo zata lulluɓa. Sai dai tayi rashin sa'a dan harya rigada ya shigo. Ta bashi dariya amma sai ya gimtse. Bakin gadon ya ƙarasa saitin inda ta saka fuskarta. Ya ajiye ledar hannunsa yana faɗin, “Ga wayarki nan, da sassafe zan wuce UK. Please banda jan faɗa wa kowa”.
         Duk da tana jinsa bata motsaba. Sai dai tana kallonsa ta cikin ƴar ƙofar data bari kaɗan kasancewar bata kashe wutar ɗaki dama ita. Daga haka bai sake cewa komaiba ya juya ya fita. Da kallo ta bisa tana mamakin yanda duk yay wani laushi duk da fuskar a matuƙar tamke take ma fiye da yanda ta sani.
      Tanajin ya fita ta yaye bargon da sauri. Mikewa tai tsaye a saman gadon ta dirgo ƙasa. Ta nufi ƙofar da gudu ta murza key kamar ance mata zai dawo. Sai da ta tabbatar tayi gam sannan ta dawo wajen wayar da yace. Ledar ta buɗe cike da doki, sai ko ga waya mai azabar ƙyau ta kamfanin Apple ta bayyana ƴar yayi. ai batamasan ta dirga wani uban tsalle da ihu ba ta ɗane gadon. Sai kuma ta miƙe ta hau rawa duk a saman gadon harda kwaso shoki ta manna a ido duk tana kallon kanta ta mirrorn ɗakin dake kallon gadon.
       Sosai Aymah tasha rawarta da ihun daɗi akan wannan waya kafin ta zauna ta fara dubawa. Komai na cikin wayar yana akwalin dan sabuwace fil. Sai dai a mamakinta anyi caji full, sai dai sim card guda biyu duk suna jikin ƙashinsu bai ɓalleba. Ta ɗauki ƴar guntuwar takardar dake ciki ta karanta abinda ya rubuta.
         _Ki shirya Gebrail zai kaiki kiyi register ɗin layukan duk sanda kike buƙata. Zanyi kwanaki goma ne ko sati biyu. Please banda tsokana, dan an tabbatar min kece kika karyama Miracle ƙafa ranar._
        Da sauri ta zaro idanu waje tana faɗin, ‘La'ila wane shugaban ƴan sherin ne ya faɗa masa? Tab ashe gidan bayan masu shegen kallo da rawan kai akwai magulmata ma. Indai suna son karna shiga harkarsu nima karsu shiga tawa. inko ba hakaba na rantse da gemun baba malam nata karya ɗiyan jama'a a gidannan ana kaima likitoci ɗorinsu’.
     Daga haka ta murguɗa baki tana miƙewa taje ta kashe wutar ɗakin ta dawo ta kwanta tana ƙanƙame wayar a hannunta. Tace, ‘Tab, ai wlhy dake zanyi barci ko sauron ɗakin nan sai dai yayi shawagi a bayan hannuna ya wuce’.
       Da wannan shiriritar tai addu'a tai barci...............✍

          
ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenm*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 53

_________________
_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._ 

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_


__________________

No. 53

...............Kamar yanda Yoohan ya faɗa da safe basu haɗu da Aymah ba, dan sammakon barin gidan yayi saboda tafiyar tasa ta gaggawa ce. Zasuyi aikine wa wani shararren ƙusa a gwamnatin UK da aka shaƙama poison a wani taro da yaje ƙasar China. Shima tafiyar tazo masa ne a gaɓar da bai so ba. Dan dama yana shirin ɗaukar hutune saboda fita da zaiyi da Nu'aymah wajen nata aikin itama. Ya kuma ƙiyasta zai ɗauki tsahon wata guda kafin komai ya dai-daita yanda yake buƙata a yanda yay fata. To sai gashi kuma an ɓata masa budget. Dolene kuma yaje wannan nema, sai dai idan ya dawo ya sake sabon tsari.
           
             Da safen koda Aymah ta fito domin yin gyara sai taita laƙe-leƙe a ɗarare. Sai dai taji ko'ina tsit alamar dai baya gidan. Badai ta saki jikiba harta kammala aikin gyara sashen. Ganin bai fitoba ya sata rumtse idanu ta leƙa ɗakinsa. Shiru babu kowa sai kayansa daya cire na barci a saman gado. Da wasu ƴan abubuwan da baza'a rasaba da ya bari saboda saurin karsu makara.
        Ajiyar zuciya ta sauke a hankali duk da ita bawai taji farin ciki a tafiyar tasa bane. Sai dai koba komai ta samu rangwamen kunyar daya aza mata a yammacin jiya da har a yanzu idan ta tuna ita kanta kunyar kanta takeji dan bai taɓa mata irin kalar k... Ɗinnan ba.
        Ɗakin ta gyara masa, ta tattare kayan cikinsa daya tara alamar bai samu damar wankewa ba tana tura baki. Kamar ta bar masa kayansa sai kuma ta tuna ya saya mata waya. Baki cike da iska tace, ‘Wlhy badan halinkaba dai. Dan kar ace banda kirki ka saimin waya mai tsada ni kuma naƙi maka wanki, da a haka zan barmaka abunka’.
           Fitowa tai da su takai toilet ɗin ɗakinta ta ajiye da nufin sai anjima zata haɗa da kayanta data cire ta wankesu. 

★★★-----★★★

          Yau satin Nu'aymah biyu kenan a gidan su Yoohan matsayin matarsa. Yayinda Uwaliya keda kwana biyar. Zuwan Uwaliya ya sake bama Aymah damar fahimtar halayyar mutanen gidan sosai. Sannan tana samun abokiyar ɗebe kewa. Dan sosai suka saki jiki da juna ita da Uwaliya. Uwaliya nada wayewar kai sosai saboda yawon da suka ɗanyi da tsohon mijinta kasancewarsa ɗan sanda, tanajin turanci kuma. hakan yasa rashin Yoohan a gidan bai cika damunta ba tunda dama bawani zaman arziƙine ke haɗasu ba da shi a kwanakin da suka kasance tare.
        Yanzu tanayin abinci a sashenta, dan haka babu ruwansu da abincin gidan. Sai dai idan akayi wani abu na musamman a gidan Blessing bata gajiyawa wajen kawoma Aymah. Dan ita dai haka kawai ALLAH ya jefa mata son Nu'aymah. Wani lokacinma dan kawai tazo sashen nata take ƙirƙirar yin abu. Wannan shigowa jikinta da Blessing keyi yaɗan saka sabo tsakaninta da Aymah har tana samun wasu bayanai akan gidan da tsarin zamansa.
       Kamar yanda akeyo cefane wa mutanen gidan haka itama ake kawo mata nata cefanan dan dama dai Yoohan ne maiyi. Tunda ya fara aiki ya saukema papa wannan nauyin. TA yanzu ma tunda Momy takai masa ƙarar Aymah nayin girki a sashenta sai maimakon ya hana kamar yanda madam Chioma taso, sai gani tai washe gari Blessing da Sj sun dawo kasuwa da uban cefane har kashi biyu. Sj yakai nasu kitchen ɗinsu Blessing ta nufi kaima Aymah.
     Tsaidata Momy tayi tana tamabar ina zata dasu?. Cikin girmamawa Blessing taima madam Chioma bayanin cewar Yoohan ya kirata tare da turoma SJ kuɗin cefane kashi biyu. Ayi nasu, akumayima Nu'aymah itama.
       Ba ƙaramin sosa ran Momy wannan al'amari yayiba. Dan haka da kanta ta nufi sashem Aymah. Lokacin suna falo Uwaliya na mata kitso dan kanta ya isheta sai ƙaiƙayi yake mata saboda rashin kitson duk da basonshi take ba. Ko sallama babu ta banko musu ƙofar. Uwaliya ce kawai ta zabura gefe jikinta na rawa. Dan ita harga ALLAH tsoron madam Chioma takeyi. Nu'aymah kam fuska ta haɗe tamau ta cigaba da game a wayarta da har yanzu taƙi bin Gebrail ya kaita tayo register layin da Yoohan yace. Sai ka rantse da ALLAH bataji shigowar Momy ba.
       Wannan shariya ta sake tunzura zuciyar madam Chioma. Da matuƙar masifa tace, “K! Bakiji shigowata bane ba?”. 
        Sake watsar da ita Aymah tayi tsahon sakanni kafin ta ɗago idanunta tana ajiye wayar tata da Momy kebi da kallo kamar idanunta zasu faɗo ƙasa. “Momy a ƙa'ida babu wani addini daya yarda da shiga waje babu neman izini. Sai dai bansan a al'adunku ba ko baku da wannan tarbiyyar. Dan haka a matsayinki na babba gareni, ni ya kamata nai wannan kuskuren kimin gyara, ni kuma idan su Victoria sunyi na gyara musu”.
       Wani irin mugun gurnani madam Chioma tayi, a ranta tana raya ‘Dolene taci uban yarinyarnan la'ada waje’. A fili kam saita zuba mata wani mummunan kallo da a tunaninta zai razana Aymah. sai dai ko gezau a idon mutuniyar taku. Saima tsatstsare ta da idanu data sakeyi tana karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga sharrinta a zuciyarta.
         “Yarinya basai kin ƙara tabbatar min ƴaƴan hausawan arewa baku da tarbiyya ba. Ba akan wannan nazo nanba. So nake naji dalilinki na saka my son yo miki cefane ke ɗaya bayan gaba ɗaya ake girki a gidan nan da kowa”.
         Baki Aymah ta taɓe tana zama saman kujera. Kanta taɗan dafe kafin ta sake duban Momy. “Oh my GOD! Ƴaƴan hausawa ginin ALLAH. To momy wannan kuma ai tsakanin mata da mijinta ne. Yanzu a gidan nan ko Mama debora ta isa jin tsakaninki da papa ne?. Inaga ki kirasa zakifi jin komai daga bakinsa yanda ya kamata kamar”.
     Ta ɗauke kanta tana maidawa ga Uwaliya da kanta ke a ƙasa ita da Blessing dake can bakin ƙofa. Saika rantse ba itace tai maganarba. “Uwaliya Please zomu ƙarasa kitson nan inada abinyi, inba hakaba na banbance tarbiyyar hausawa data aljihun baya dan wlhy ni babu ruwana da matsayin kowa gidan nan”.
       Baki Momy ta buɗe a matuƙar hasale zatai magana dan da turanci Aymah ta faɗa, Papa ya shigo falon. Tsawa ya daka mata cikin yare yake magana a fusace batare da Aymah da Uwaliya sunji mi yake faɗa ba. Ita kanta Blessing batajin yaren dan su papa sunajin yaruka kusan uku ne.
     Gani sukai kawai yaja hannun Momy sun fice tana kumfar baki kamar zata haɗiye harshenta. Su Blessing dai basu motsaba, Aymah kam da uwar harara ta raka bayansu tana jan tsaki. Daga ƙarshema ta tashi ta shige bedroom kitson da ba'a ƙarasaba kenan.

     Washe gari da safe papa ya aiko Abraham kiran Aymah. A yanda yaron ya shigo musu babu sallama babu gaisuwa yana magana a gadara ne ya bata haushi. Tako tashi ta tallare masa ƙeya da kama kunnensa ta murɗe tana faɗin. “Kai dan ƙaniyarka ƙaracin tarbiyya yasaka banbance na gaba da kai ne? Ko Muhammad ɗina ya girmeka amma kake neman saka kanka a filin yaƙin da ko uwarka tamin ƙaɗan wajen gwajin ƙwanji”.
       Kuka Abraham ya fasa. Aymah ta sake talle ƙeyar tana nuna masa hanya. “Ficemin anan kafin na maka ɓalli-ɓalli a waɗanan shegun kumatun samfarin gurasar kano”.
       Da gudu yaron ya fita yana kuka. Itakuma ta juya bedroom ɗinta tana bambamin masifa akan wlhy dai-dai take da ƙugun duk wanda yace shi shegene a gidan. Babu mai sakama rayuwarta kahon zuƙa ya tsira. Dan zuru bata cin zuru sai dai a haɗu ai zuru-zuru. 
       Itadai Uwaliya binta kawai tai da kallo tana jinjina ƙarfin zuciyarta da tsaurin ido. Sam yarinyar bata da tsoro kamar dangin ifiritu. A fili tace, ‘Koda yake tun kina ciki an gama tsumeki da addu'oi shiyyasa’.

         A falon papa ta iske Momy na banbamin jaraba ga Abraham na sharɓar kuka. Dama ta wuto su Joy na nasu masifar a downstairs kuma tasan duk akanta ne. Kallo ɗaya papa yayma fuskarta shi kansa yaji shakkarta. Duk da kasancewarta ƙaramar yarinya kwarjinita na tada masa hankali dan kallon mahaifinta yake mata. Zama tai tana gaishesa batare data kalli ko sashen da Momy take ba. Ya amsa mata da kulawa.
       “Daughter miya haɗaki da ɗan ƙanin nakine?”.
      Zuciyar Aymah ta gado a ƙirji take. Dan haka tama manta da matsayin wani papa. Cikin ɗacin rai da rufewar idanu tace, “Papa har wannan ɗan mitsitsin yaron yakai girman da zai dinga kawomin raini a gidan nan? Tunda nake bai taɓa gaidani ba. Hakan yasa sam bana shiga sabgarsa. Shine tsabar rainin wayo yanzu yaje yana min magana a tsaitsaye kamar wata sa'arsa, shiyyasa naga ya dace na fara koya masa tarbiya idan wadda aka bashi bata ishesa ba, dan.........”
         A wani irin harzuƙe Momy ta katseta. “Yaƙi ya gaishekin? Ke kina girmama nagaba dake ɗinne?”.
        “Tabbas ina girmama nagaba dani Momy, sai dai fa inhar shi wannna na sama dani ɗin ya nunamin shekaruna da nasa babu banbanci to wlhy zan bi na taka shima na koyar dashi tarbiyyar daya rasa tun ƙuruciya. Kuma wlhy inhar Abraham baya gaisheni a gidannan, koya sake rainani saina sakasa a makarantar jiki magayi a gidanan a kuma gabanki”.
       Ba Momy ba hatta papa lamarin Aymah tsoro ya ƙara bashi. Sai faman jinjina kai yake yana magana da zuciyarsa. ‘Like Father like daughter. Lallai John ya ɗakko mana shugabar ƴan boko haram a gidan. dan kuwa tabbas jinin Sooraj dama bazai kasance na banza ba’. A fili ko sai yaya saurin dakatar da Momy da taso yin magana. “Ya isa Darling. Bakiga yarinya bace ita. bai kamata ki biyetaba. Kuma tama fimu gaskiya. shi Abraham ɗin miyasa baya gaisheta?”.
      Nanfa ya shiga yima Abraham faɗa sosai, ya kuma sakashi bama Aymah haƙuri dole. Itama Momy akan abinda ya faru jiya yay mata sulhu da Nu'aymah. Yasa Aymah bata haƙuri, ya kuma jama Momy gargaɗi akan shiga sabgar Nu'aymah inhar ba wadda ta kasance ƙyaƙyƙyawa ba.
      Hakan ya sake cima Momy rai akan yarinyar. Amma sai tayi shiru saboda maganar da suka tattauna da papan a daren jiya gameda shirinsu akan mahaifin Aymah dama ita kanta da zasu raba da ɗansu nanda lokaci ƙanƙani.
     Daga haka ya sallameta ta tafi. A wannan yinin kaf Nu'aymah tayisa cikin ƙunci ne a gidan. Tare da ɗaukar alwashi kala-kala ga duk jama'ar gidan. Dan ta rantse da gemun baba malam duk sai ta gasa musu aya a hannu. Papa ne kawai zai tsira a cikinsu shima idan yaso.
                 Dalilin wannan rikici Nu'aymah ta sake tsumewa kowa a gidan. Bata da abokin hira sai Uwaliya sai ko Blessing dasu Destiny dake fakar ido idan su mama debora basa falo su shigo mata. Ko kuma idan ta fita harabar gidan shan iska. Dan yanzu da gadara ma take fitowa har falon ƙasan ko harabar gidan ko garden ta zauna tana latse-latse a wayar da babu sim card a ciki koda kuwa suna zaune a wajen. Kota duba buks ɗinta na boko kona islamiyya. Kosu zauna da Uwaliya suyi hira idan sun gama aiki tunda yazam aikin nasu bawani mai wahalarwa bane ba. Komai tare sukeyi da Uwaliya, ɗakin Yoohan ne dai bata taɓa bama Uwaliya damar ko taɓa murfinba. ɗakinta ma itace ke gyara abinta, sai dai wani dalili yakai Uwaliya ciki amma badan aiki ba. Abinci ma kusan Aymah keyin abinta, sai dai Uwaliyan na tayata.
      Kullum sai tayi waya da Umm da Baba malam da Hajjo a wayar Uwaliya. Yoohan kam basu taɓa waya ba tunda ya tafi, ita harma mantawa take da lamarinsa. sai dai duk sanda zata sha chocolate sai abinda ya faru tsakaninsu akanta ya faɗo mata a rai. Haka kawai abin kan sakata murmushi, kokuma taita ƙunƙuni tana kiransa ƙazami mayen baki.
          Bata taɓama kowa zancen hoton data ɗakko a ɗakin papa ba, tundama ta ɓoyesa bata sake waiwayarsa ba. duk da kuwa batunsa na nan damar cikin zuciyarta. A dalilin hakannema ya sata mugun sakama duk wani motsi na madam Chioma da papa a gidan idanu. Tanason ta gano ainahin gaskiyar abinda ranta ke raya mata game da madam Chioma ba itace mahaifiyarsa ba. Abinda Aymah ta fara fahimta shine akwai wani haramtaccen business da papa keyi a ɓoye da Yoohan baisan da shiba. Dan inhar Yoohan yana a gari komansa yakan zama taka tsan-tsan. Amma yanzu da baya nan sai take ganin wasu baƙin halaye muraran ga papan duk da bawai yana fitowa fili yanayi bane, sai idan ka kasance mai lura sosai kamar ita data saka masa idon mikiya ne zaka fahimta.
      Wannan ne ya saka ƙaramin tunaninta sake faɗaɗa, harta kasa haƙuri suna waya da baba malam take faɗa masa ita lamarin papan Yoohan na bata tsoro. Da yake dama baba malam ɗinne yay mata tambayar akan papan cikin hikima. Koda ta faɗi hakan dariya kawai yayi, bai tambayeta mita gani ba ko dalilinta nacewar hakan sukai sallama.
          Daga ranar kuma baba malam bai sake takalar Aymah da zancen papa ba. Itama kuma bata sake masa ba ta cigaba da hidimarta.

__________★

          Yau ta kasance asabar. Kusan ƙarfe sha biyu sai ga su Amal Yah Omar ya kawo mata su. Wayyo zokaga murna kamar zata tashi sama danjin daɗi. Hatta Adawiya da Abbah ya tilastama biyosu dan dole Aymah sai da ta rungumeta. Ranar dai ƴan gidan sunsha kallo dan duk suna gida. Gebrail le kawai yanacan gantalinsa da abokai tunda babu makaranta.
        Jama'ar gidan sun sake yarda Nu'aymah bata fito a ƙaramin gida ba, dan motar da Omar ya kawo su Yusrah a ciki kawai ta isa shaida. Ga uban tsaraba da suka shigo dashi kamar sunzo daga wani garine. Nasu daban na Aymah daban kuma.
        Adawiya dai nata kallon makeken gidan da aka kawo Aymah a ciki, musamman sashen Aymah daya tsaru da irin burinta da buƙatarta. Tasan iyayensu nada kuɗi sosai, dukda ta taɓa jin ƙishin-ƙishin a gidansu akan kaso biyu na dukiyar gidansu mallakin baba malam ce. Amma sai taji kamar Aymah ta sake samun matsayine sama dana gidansu duk da tana a tsakkiyar waɗan nan mutanen da babu ALLAH a ransu. 
      Kayan ƙwalam da maƙulashe ta ɗebo musu sukaci iya cinsu suna kwasar hira cike da farin ciki. Adawiya ce dai data saka kanta a uku bata cewa komai. Suko sun watsar da ita sunata sabgoginsu.
     Bayan sallar la'asar Aymah tace su shirya su rakata mtn office tayo register layinta ta ɗora a wayarta da suketa faman santi saboda haɗuwarta. Dan ganin wayarnan sai da ya saka idanun Adawiya cika da ƙwallar baƙin ciki. Duk abinda taima kanta buri da fata sai taga Aymah ta fara samunsa kafin ita. Yah Ab ne kawai tayi nasar ƙwace mata. Shima gashi ya suɓuce mata a daidai lokacin da Nu'aymahr ta samu wanda ya fisa komai. Dan ƙyaƙyƙyawar nasaba ce kawai Abdallah zai bugi ƙirji yace yafi Yoohan da ita.
         Kan Nu'aymah tsaye taje ta sanarma drivern gidan zai kaisu anguwa. Duk da tsoron madam Chioma dake a ransa haka ya amsa mata saboda uban kwarjinin datai masa a idanu. Itako bama ta damu da halin da yake a cikiba. Ta miƙa masa ɗaya daga cikin keys ɗin motar Yoohan data ɗakko a ɗakinsa. Idanu ya zaro sosai cikin rawar jiki yake, “Madam ai ko oga sau biyu kawai ya taɓa shiga motarnan, kuma da kansa yay driving, duk guri kuma na musamman yaje a ciki”.
       Wani shegen harara ta zuba masa tana kallonsa a iskance. “Kai dokar ogan ta dama. Dalla amshi key muje banason ƙananun magana. Motar wofi makamin mutuwa da har za'a wani zauna yin tsarin shigarta. Koshi ogan naka ya zama mota hawa zanyi na zaga duniya nai kallo mtsoww!”.
        Amsa yayi dole dan yasan jarabar Aymah tafi gaban naƙi. Masu gidanma ba raga musu takeba balle shi da yake cin arziƙi. Sai dai kuma abinda Nu'aymah bata saniba shine suna fita guards ɗin Yoohan suma suka bisu a baya. Dan dokar Yoohan ɗince haka a garesu. Bata farga da su ba sai da sukaje har sukayo register ɗin suka fito. Aymah tasa aka kaisu wani wajen shan ice-creem dasu shawarma. Sai gab da magriba suka taso zasu tafi idonta ya sauka akan guards ɗin Yoohan ɗin. Wannan abu ya baƙanta mata rai. Amma sai bata tanka ba. A cewarta da ubangidan nasu zatayi shine dai-dai da ita. Sukam basu kai martabar ji daga gareta ba.

        Sanda suka iso gidan har an idar da sallar magriba. Sun iske Omar ya dawo ɗaukar su Yusrah. Aiko ya balbalesu da faɗa musamman Nu'aymah da Yoohan ya tabbatar ma Omar a waya cewar baisan da fitarsu ba. Shima guards ɗinsa ne kawai suka kira suka sanar masa gata sun fita yasa su bi su.
      Sai da ya ga tayi laushi da faɗan da yay mata sannan ya koma mata nasiha. Ya miƙa mata ATM yana faɗin, “Gashi inji Abbah. Zaki iya fitar da kuɗi yanzu a bank accaunt ɗinki. Saura kuma kiyi musu sukuwar salla kinji ko?”.
     Baki ta tunzura gaba. “To ni indai ba saka kati ba a waya mi zanyi da su Yah Omar. Sai kuma idan inason shan ice-creem ne”.
      Bugu ya kaima bakinta yana faɗin, “Oh maganar shegen ice-creem ɗin nan bazai bar shegen bakinkin nan mai kama dana tsutsa ba kenan”.
     Saurin kaucewa tai tana sake kumbura fuska, ta kwasa da gudu batare da taga tafiyar tasu data so ganiba. Aiko Yusrah da Amal sai kwasar dariya suke daga cikin mota. Duk wannan abu a gaban idanu Joy da Miracle da Gebrail dake can gefe ya faru. 
             Cike da mamaki Gebrail yace, “Wai wannan ɗan yarinyar aka bama damar ciran kuɗi a bank yanda ta gadama. Amma mu ga Brother Yoohan ya hana a zuba mana kuɗin daya haura dubu hamsin tsabar ya rainamu”.
         Joy tace, “Shegiyan yarinyar nan family ɗinta kudine da su shiyyasa takema mutane iskancin data so. Ni dama muyi joining ɗinta mu cinye kuɗin”.
         Tsaki Gebrail yaja yana faɗin, “Mumu! Ance miki bata da basira ne kamar ke. Bayan kun nuna bakwa sonta sai ta yarda daku yanzu. Yaran arewa ɗin nan fa shegen wayone dasu more especially yaran Hausawa ɗin nan. Balle wannan mai aiki da aljanu ɗin nan, dan idanunta kamar na Google suke a gidan nan”.
         Masifa Joy ta fara masa saboda yace mata Mumu. Nan take suka harƙume faɗa Miracle data tsunduma duniyar tunanin akan zancen kuɗin Nu'aymah ta shiga rabasu daga zaune dan har yanzu ƙafarta batai garau ba sosai. Ga tabon fashewar da tayi a baki akai mata ɗinki nan raɗam ya zame mata tambari😜😂.

_____________

        Oho, Aymah bama tasan sunayi ba. Dan tana can ta ɗora layinta a waya tana jiran awannin da suka bata ta fara kira da shi su cika ta kira Umm da baba malam da hajjo dan tsabar zumuɗi. Kota Yoohan da ya sai wayarma ba'ayi bawon ALLAH😪.
        Ganin dai lokacin yayi dare dole ta haƙura sai da safe. Tana kuwa idar da salla sai ga massege ya shigo mata. Ɗaukar wayar tayi ta duba. Ɗaya daga kamfani ɗaya kuma credit card ne aka lodo mata harna dubu biyar. Basai ta nema ba'asi ba, dan ta ga sunansa ne. Amma maimakon tai tunanin nemar lambarsa ta fara kiransa sai ta kira Umm ɗinta. Dan tasan baba malam kam yanzu yana massallaci bai fito ba.
         
★★★

        Yau kwanaki biyu kenan da zuwan su Amal gidan, ranar litinin bayan sallar la'asar momy da su mama debora suka tafi church. Blessing taja Uwaliya suka tafi kasuwa cefane. Su joy kuwa suna school. Hakan yasa gidan yin shiru dan da alama ma Nu'aymah ita kaɗaice. Bata damuba dan ko tsoro bataji. sai ma ta buɗe data ta shiga cheating da su Yusrah dan yanzu duk ta koma harkokinta na yanar gizo numbers ɗin ƴan gidansu da ƙawayensu kuwa duk su Amal sun tura mata har ƴan orphanage. Hakan yasata sake samun abubuwan ɗebe kewa tanata hidimarta hankali kwance kamar bata da damuwar kowa a ranta.

        Shiru babu wanda ya dawo har magriba ta rufa. Aymah dake ɗanjin ƙafarta na mata ciwo sama-sama tun a daren jiya ta miƙe da ƙyar tana yamutsa fuska dan tasan dai period ɗintane ke nuna alamun ya kusa zuwa. Alwala taje tayi tazo tai sallar magriba. Tana idarwa ta miƙe ta fito waje saboda motsi da taketa faman ji tun tana salla. ita a zatontama ko Uwaliya ce suka dawo. Sai dai a mamakinta sai bataga kowaba a falon, batare data damu ba ta juya ta koma cikin bedroom ɗinta bayan taje ta rufo ƙofar falon data gani a buɗe.
       Tana shigowa ɗakin aka kashe fitila duhu ya mamaye ɗakin Tare da rungumota aka matse. Tashin hankali da ba'a saka masa rana. Duhu shine abu na biyu da Aymah ta tsana a rayuwarta bayan allura. Gashi yana mugun yin tasiri akan lalurarta. Aiko a take ta daddage ta ƙwalla wani irin gigitaccen ihu da sai da muryarta ta amsa kowanne kusurwa da bango da ke a cikin gidan...........✍

😱Tofa, wane hege ne zai ɓallo mana ruwa kuma Aymah?🙆🏻. Ga Dafta yayi nisan kiwo🤦🏻😫.



_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.u😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 53

_________________
_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._ 

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_


__________________

No. 53

...............Kamar yanda Yoohan ya faɗa da safe basu haɗu da Aymah ba, dan sammakon barin gidan yayi saboda tafiyar tasa ta gaggawa ce. Zasuyi aikine wa wani shararren ƙusa a gwamnatin UK da aka shaƙama poison a wani taro da yaje ƙasar China. Shima tafiyar tazo masa ne a gaɓar da bai so ba. Dan dama yana shirin ɗaukar hutune saboda fita da zaiyi da Nu'aymah wajen nata aikin itama. Ya kuma ƙiyasta zai ɗauki tsahon wata guda kafin komai ya dai-daita yanda yake buƙata a yanda yay fata. To sai gashi kuma an ɓata masa budget. Dolene kuma yaje wannan nema, sai dai idan ya dawo ya sake sabon tsari.
           
             Da safen koda Aymah ta fito domin yin gyara sai taita laƙe-leƙe a ɗarare. Sai dai taji ko'ina tsit alamar dai baya gidan. Badai ta saki jikiba harta kammala aikin gyara sashen. Ganin bai fitoba ya sata rumtse idanu ta leƙa ɗakinsa. Shiru babu kowa sai kayansa daya cire na barci a saman gado. Da wasu ƴan abubuwan da baza'a rasaba da ya bari saboda saurin karsu makara.
        Ajiyar zuciya ta sauke a hankali duk da ita bawai taji farin ciki a tafiyar tasa bane. Sai dai koba komai ta samu rangwamen kunyar daya aza mata a yammacin jiya da har a yanzu idan ta tuna ita kanta kunyar kanta takeji dan bai taɓa mata irin kalar k... Ɗinnan ba.
        Ɗakin ta gyara masa, ta tattare kayan cikinsa daya tara alamar bai samu damar wankewa ba tana tura baki. Kamar ta bar masa kayansa sai kuma ta tuna ya saya mata waya. Baki cike da iska tace, ‘Wlhy badan halinkaba dai. Dan kar ace banda kirki ka saimin waya mai tsada ni kuma naƙi maka wanki, da a haka zan barmaka abunka’.
           Fitowa tai da su takai toilet ɗin ɗakinta ta ajiye da nufin sai anjima zata haɗa da kayanta data cire ta wankesu. 

★★★-----★★★

          Yau satin Nu'aymah biyu kenan a gidan su Yoohan matsayin matarsa. Yayinda Uwaliya keda kwana biyar. Zuwan Uwaliya ya sake bama Aymah damar fahimtar halayyar mutanen gidan sosai. Sannan tana samun abokiyar ɗebe kewa. Dan sosai suka saki jiki da juna ita da Uwaliya. Uwaliya nada wayewar kai sosai saboda yawon da suka ɗanyi da tsohon mijinta kasancewarsa ɗan sanda, tanajin turanci kuma. hakan yasa rashin Yoohan a gidan bai cika damunta ba tunda dama bawani zaman arziƙine ke haɗasu ba da shi a kwanakin da suka kasance tare.
        Yanzu tanayin abinci a sashenta, dan haka babu ruwansu da abincin gidan. Sai dai idan akayi wani abu na musamman a gidan Blessing bata gajiyawa wajen kawoma Aymah. Dan ita dai haka kawai ALLAH ya jefa mata son Nu'aymah. Wani lokacinma dan kawai tazo sashen nata take ƙirƙirar yin abu. Wannan shigowa jikinta da Blessing keyi yaɗan saka sabo tsakaninta da Aymah har tana samun wasu bayanai akan gidan da tsarin zamansa.
       Kamar yanda akeyo cefane wa mutanen gidan haka itama ake kawo mata nata cefanan dan dama dai Yoohan ne maiyi. Tunda ya fara aiki ya saukema papa wannan nauyin. TA yanzu ma tunda Momy takai masa ƙarar Aymah nayin girki a sashenta sai maimakon ya hana kamar yanda madam Chioma taso, sai gani tai washe gari Blessing da Sj sun dawo kasuwa da uban cefane har kashi biyu. Sj yakai nasu kitchen ɗinsu Blessing ta nufi kaima Aymah.
     Tsaidata Momy tayi tana tamabar ina zata dasu?. Cikin girmamawa Blessing taima madam Chioma bayanin cewar Yoohan ya kirata tare da turoma SJ kuɗin cefane kashi biyu. Ayi nasu, akumayima Nu'aymah itama.
       Ba ƙaramin sosa ran Momy wannan al'amari yayiba. Dan haka da kanta ta nufi sashem Aymah. Lokacin suna falo Uwaliya na mata kitso dan kanta ya isheta sai ƙaiƙayi yake mata saboda rashin kitson duk da basonshi take ba. Ko sallama babu ta banko musu ƙofar. Uwaliya ce kawai ta zabura gefe jikinta na rawa. Dan ita harga ALLAH tsoron madam Chioma takeyi. Nu'aymah kam fuska ta haɗe tamau ta cigaba da game a wayarta da har yanzu taƙi bin Gebrail ya kaita tayo register layin da Yoohan yace. Sai ka rantse da ALLAH bataji shigowar Momy ba.
       Wannan shariya ta sake tunzura zuciyar madam Chioma. Da matuƙar masifa tace, “K! Bakiji shigowata bane ba?”. 
        Sake watsar da ita Aymah tayi tsahon sakanni kafin ta ɗago idanunta tana ajiye wayar tata da Momy kebi da kallo kamar idanunta zasu faɗo ƙasa. “Momy a ƙa'ida babu wani addini daya yarda da shiga waje babu neman izini. Sai dai bansan a al'adunku ba ko baku da wannan tarbiyyar. Dan haka a matsayinki na babba gareni, ni ya kamata nai wannan kuskuren kimin gyara, ni kuma idan su Victoria sunyi na gyara musu”.
       Wani irin mugun gurnani madam Chioma tayi, a ranta tana raya ‘Dolene taci uban yarinyarnan la'ada waje’. A fili kam saita zuba mata wani mummunan kallo da a tunaninta zai razana Aymah. sai dai ko gezau a idon mutuniyar taku. Saima tsatstsare ta da idanu data sakeyi tana karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga sharrinta a zuciyarta.
         “Yarinya basai kin ƙara tabbatar min ƴaƴan hausawan arewa baku da tarbiyya ba. Ba akan wannan nazo nanba. So nake naji dalilinki na saka my son yo miki cefane ke ɗaya bayan gaba ɗaya ake girki a gidan nan da kowa”.
         Baki Aymah ta taɓe tana zama saman kujera. Kanta taɗan dafe kafin ta sake duban Momy. “Oh my GOD! Ƴaƴan hausawa ginin ALLAH. To momy wannan kuma ai tsakanin mata da mijinta ne. Yanzu a gidan nan ko Mama debora ta isa jin tsakaninki da papa ne?. Inaga ki kirasa zakifi jin komai daga bakinsa yanda ya kamata kamar”.
     Ta ɗauke kanta tana maidawa ga Uwaliya da kanta ke a ƙasa ita da Blessing dake can bakin ƙofa. Saika rantse ba itace tai maganarba. “Uwaliya Please zomu ƙarasa kitson nan inada abinyi, inba hakaba na banbance tarbiyyar hausawa data aljihun baya dan wlhy ni babu ruwana da matsayin kowa gidan nan”.
       Baki Momy ta buɗe a matuƙar hasale zatai magana dan da turanci Aymah ta faɗa, Papa ya shigo falon. Tsawa ya daka mata cikin yare yake magana a fusace batare da Aymah da Uwaliya sunji mi yake faɗa ba. Ita kanta Blessing batajin yaren dan su papa sunajin yaruka kusan uku ne.
     Gani sukai kawai yaja hannun Momy sun fice tana kumfar baki kamar zata haɗiye harshenta. Su Blessing dai basu motsaba, Aymah kam da uwar harara ta raka bayansu tana jan tsaki. Daga ƙarshema ta tashi ta shige bedroom kitson da ba'a ƙarasaba kenan.

     Washe gari da safe papa ya aiko Abraham kiran Aymah. A yanda yaron ya shigo musu babu sallama babu gaisuwa yana magana a gadara ne ya bata haushi. Tako tashi ta tallare masa ƙeya da kama kunnensa ta murɗe tana faɗin. “Kai dan ƙaniyarka ƙaracin tarbiyya yasaka banbance na gaba da kai ne? Ko Muhammad ɗina ya girmeka amma kake neman saka kanka a filin yaƙin da ko uwarka tamin ƙaɗan wajen gwajin ƙwanji”.
       Kuka Abraham ya fasa. Aymah ta sake talle ƙeyar tana nuna masa hanya. “Ficemin anan kafin na maka ɓalli-ɓalli a waɗanan shegun kumatun samfarin gurasar kano”.
       Da gudu yaron ya fita yana kuka. Itakuma ta juya bedroom ɗinta tana bambamin masifa akan wlhy dai-dai take da ƙugun duk wanda yace shi shegene a gidan. Babu mai sakama rayuwarta kahon zuƙa ya tsira. Dan zuru bata cin zuru sai dai a haɗu ai zuru-zuru. 
       Itadai Uwaliya binta kawai tai da kallo tana jinjina ƙarfin zuciyarta da tsaurin ido. Sam yarinyar bata da tsoro kamar dangin ifiritu. A fili tace, ‘Koda yake tun kina ciki an gama tsumeki da addu'oi shiyyasa’.

         A falon papa ta iske Momy na banbamin jaraba ga Abraham na sharɓar kuka. Dama ta wuto su Joy na nasu masifar a downstairs kuma tasan duk akanta ne. Kallo ɗaya papa yayma fuskarta shi kansa yaji shakkarta. Duk da kasancewarta ƙaramar yarinya kwarjinita na tada masa hankali dan kallon mahaifinta yake mata. Zama tai tana gaishesa batare data kalli ko sashen da Momy take ba. Ya amsa mata da kulawa.
       “Daughter miya haɗaki da ɗan ƙanin nakine?”.
      Zuciyar Aymah ta gado a ƙirji take. Dan haka tama manta da matsayin wani papa. Cikin ɗacin rai da rufewar idanu tace, “Papa har wannan ɗan mitsitsin yaron yakai girman da zai dinga kawomin raini a gidan nan? Tunda nake bai taɓa gaidani ba. Hakan yasa sam bana shiga sabgarsa. Shine tsabar rainin wayo yanzu yaje yana min magana a tsaitsaye kamar wata sa'arsa, shiyyasa naga ya dace na fara koya masa tarbiya idan wadda aka bashi bata ishesa ba, dan.........”
         A wani irin harzuƙe Momy ta katseta. “Yaƙi ya gaishekin? Ke kina girmama nagaba dake ɗinne?”.
        “Tabbas ina girmama nagaba dani Momy, sai dai fa inhar shi wannna na sama dani ɗin ya nunamin shekaruna da nasa babu banbanci to wlhy zan bi na taka shima na koyar dashi tarbiyyar daya rasa tun ƙuruciya. Kuma wlhy inhar Abraham baya gaisheni a gidannan, koya sake rainani saina sakasa a makarantar jiki magayi a gidanan a kuma gabanki”.
       Ba Momy ba hatta papa lamarin Aymah tsoro ya ƙara bashi. Sai faman jinjina kai yake yana magana da zuciyarsa. ‘Like Father like daughter. Lallai John ya ɗakko mana shugabar ƴan boko haram a gidan. dan kuwa tabbas jinin Sooraj dama bazai kasance na banza ba’. A fili ko sai yaya saurin dakatar da Momy da taso yin magana. “Ya isa Darling. Bakiga yarinya bace ita. bai kamata ki biyetaba. Kuma tama fimu gaskiya. shi Abraham ɗin miyasa baya gaisheta?”.
      Nanfa ya shiga yima Abraham faɗa sosai, ya kuma sakashi bama Aymah haƙuri dole. Itama Momy akan abinda ya faru jiya yay mata sulhu da Nu'aymah. Yasa Aymah bata haƙuri, ya kuma jama Momy gargaɗi akan shiga sabgar Nu'aymah inhar ba wadda ta kasance ƙyaƙyƙyawa ba.
      Hakan ya sake cima Momy rai akan yarinyar. Amma sai tayi shiru saboda maganar da suka tattauna da papan a daren jiya gameda shirinsu akan mahaifin Aymah dama ita kanta da zasu raba da ɗansu nanda lokaci ƙanƙani.
     Daga haka ya sallameta ta tafi. A wannan yinin kaf Nu'aymah tayisa cikin ƙunci ne a gidan. Tare da ɗaukar alwashi kala-kala ga duk jama'ar gidan. Dan ta rantse da gemun baba malam duk sai ta gasa musu aya a hannu. Papa ne kawai zai tsira a cikinsu shima idan yaso.
                 Dalilin wannan rikici Nu'aymah ta sake tsumewa kowa a gidan. Bata da abokin hira sai Uwaliya sai ko Blessing dasu Destiny dake fakar ido idan su mama debora basa falo su shigo mata. Ko kuma idan ta fita harabar gidan shan iska. Dan yanzu da gadara ma take fitowa har falon ƙasan ko harabar gidan ko garden ta zauna tana latse-latse a wayar da babu sim card a ciki koda kuwa suna zaune a wajen. Kota duba buks ɗinta na boko kona islamiyya. Kosu zauna da Uwaliya suyi hira idan sun gama aiki tunda yazam aikin nasu bawani mai wahalarwa bane ba. Komai tare sukeyi da Uwaliya, ɗakin Yoohan ne dai bata taɓa bama Uwaliya damar ko taɓa murfinba. ɗakinta ma itace ke gyara abinta, sai dai wani dalili yakai Uwaliya ciki amma badan aiki ba. Abinci ma kusan Aymah keyin abinta, sai dai Uwaliyan na tayata.
      Kullum sai tayi waya da Umm da Baba malam da Hajjo a wayar Uwaliya. Yoohan kam basu taɓa waya ba tunda ya tafi, ita harma mantawa take da lamarinsa. sai dai duk sanda zata sha chocolate sai abinda ya faru tsakaninsu akanta ya faɗo mata a rai. Haka kawai abin kan sakata murmushi, kokuma taita ƙunƙuni tana kiransa ƙazami mayen baki.
          Bata taɓama kowa zancen hoton data ɗakko a ɗakin papa ba, tundama ta ɓoyesa bata sake waiwayarsa ba. duk da kuwa batunsa na nan damar cikin zuciyarta. A dalilin hakannema ya sata mugun sakama duk wani motsi na madam Chioma da papa a gidan idanu. Tanason ta gano ainahin gaskiyar abinda ranta ke raya mata game da madam Chioma ba itace mahaifiyarsa ba. Abinda Aymah ta fara fahimta shine akwai wani haramtaccen business da papa keyi a ɓoye da Yoohan baisan da shiba. Dan inhar Yoohan yana a gari komansa yakan zama taka tsan-tsan. Amma yanzu da baya nan sai take ganin wasu baƙin halaye muraran ga papan duk da bawai yana fitowa fili yanayi bane, sai idan ka kasance mai lura sosai kamar ita data saka masa idon mikiya ne zaka fahimta.
      Wannan ne ya saka ƙaramin tunaninta sake faɗaɗa, harta kasa haƙuri suna waya da baba malam take faɗa masa ita lamarin papan Yoohan na bata tsoro. Da yake dama baba malam ɗinne yay mata tambayar akan papan cikin hikima. Koda ta faɗi hakan dariya kawai yayi, bai tambayeta mita gani ba ko dalilinta nacewar hakan sukai sallama.
          Daga ranar kuma baba malam bai sake takalar Aymah da zancen papa ba. Itama kuma bata sake masa ba ta cigaba da hidimarta.

__________★

          Yau ta kasance asabar. Kusan ƙarfe sha biyu sai ga su Amal Yah Omar ya kawo mata su. Wayyo zokaga murna kamar zata tashi sama danjin daɗi. Hatta Adawiya da Abbah ya tilastama biyosu dan dole Aymah sai da ta rungumeta. Ranar dai ƴan gidan sunsha kallo dan duk suna gida. Gebrail le kawai yanacan gantalinsa da abokai tunda babu makaranta.
        Jama'ar gidan sun sake yarda Nu'aymah bata fito a ƙaramin gida ba, dan motar da Omar ya kawo su Yusrah a ciki kawai ta isa shaida. Ga uban tsaraba da suka shigo dashi kamar sunzo daga wani garine. Nasu daban na Aymah daban kuma.
        Adawiya dai nata kallon makeken gidan da aka kawo Aymah a ciki, musamman sashen Aymah daya tsaru da irin burinta da buƙatarta. Tasan iyayensu nada kuɗi sosai, dukda ta taɓa jin ƙishin-ƙishin a gidansu akan kaso biyu na dukiyar gidansu mallakin baba malam ce. Amma sai taji kamar Aymah ta sake samun matsayine sama dana gidansu duk da tana a tsakkiyar waɗan nan mutanen da babu ALLAH a ransu. 
      Kayan ƙwalam da maƙulashe ta ɗebo musu sukaci iya cinsu suna kwasar hira cike da farin ciki. Adawiya ce dai data saka kanta a uku bata cewa komai. Suko sun watsar da ita sunata sabgoginsu.
     Bayan sallar la'asar Aymah tace su shirya su rakata mtn office tayo register layinta ta ɗora a wayarta da suketa faman santi saboda haɗuwarta. Dan ganin wayarnan sai da ya saka idanun Adawiya cika da ƙwallar baƙin ciki. Duk abinda taima kanta buri da fata sai taga Aymah ta fara samunsa kafin ita. Yah Ab ne kawai tayi nasar ƙwace mata. Shima gashi ya suɓuce mata a daidai lokacin da Nu'aymahr ta samu wanda ya fisa komai. Dan ƙyaƙyƙyawar nasaba ce kawai Abdallah zai bugi ƙirji yace yafi Yoohan da ita.
         Kan Nu'aymah tsaye taje ta sanarma drivern gidan zai kaisu anguwa. Duk da tsoron madam Chioma dake a ransa haka ya amsa mata saboda uban kwarjinin datai masa a idanu. Itako bama ta damu da halin da yake a cikiba. Ta miƙa masa ɗaya daga cikin keys ɗin motar Yoohan data ɗakko a ɗakinsa. Idanu ya zaro sosai cikin rawar jiki yake, “Madam ai ko oga sau biyu kawai ya taɓa shiga motarnan, kuma da kansa yay driving, duk guri kuma na musamman yaje a ciki”.
       Wani shegen harara ta zuba masa tana kallonsa a iskance. “Kai dokar ogan ta dama. Dalla amshi key muje banason ƙananun magana. Motar wofi makamin mutuwa da har za'a wani zauna yin tsarin shigarta. Koshi ogan naka ya zama mota hawa zanyi na zaga duniya nai kallo mtsoww!”.
        Amsa yayi dole dan yasan jarabar Aymah tafi gaban naƙi. Masu gidanma ba raga musu takeba balle shi da yake cin arziƙi. Sai dai kuma abinda Nu'aymah bata saniba shine suna fita guards ɗin Yoohan suma suka bisu a baya. Dan dokar Yoohan ɗince haka a garesu. Bata farga da su ba sai da sukaje har sukayo register ɗin suka fito. Aymah tasa aka kaisu wani wajen shan ice-creem dasu shawarma. Sai gab da magriba suka taso zasu tafi idonta ya sauka akan guards ɗin Yoohan ɗin. Wannan abu ya baƙanta mata rai. Amma sai bata tanka ba. A cewarta da ubangidan nasu zatayi shine dai-dai da ita. Sukam basu kai martabar ji daga gareta ba.

        Sanda suka iso gidan har an idar da sallar magriba. Sun iske Omar ya dawo ɗaukar su Yusrah. Aiko ya balbalesu da faɗa musamman Nu'aymah da Yoohan ya tabbatar ma Omar a waya cewar baisan da fitarsu ba. Shima guards ɗinsa ne kawai suka kira suka sanar masa gata sun fita yasa su bi su.
      Sai da ya ga tayi laushi da faɗan da yay mata sannan ya koma mata nasiha. Ya miƙa mata ATM yana faɗin, “Gashi inji Abbah. Zaki iya fitar da kuɗi yanzu a bank accaunt ɗinki. Saura kuma kiyi musu sukuwar salla kinji ko?”.
     Baki ta tunzura gaba. “To ni indai ba saka kati ba a waya mi zanyi da su Yah Omar. Sai kuma idan inason shan ice-creem ne”.
      Bugu ya kaima bakinta yana faɗin, “Oh maganar shegen ice-creem ɗin nan bazai bar shegen bakinkin nan mai kama dana tsutsa ba kenan”.
     Saurin kaucewa tai tana sake kumbura fuska, ta kwasa da gudu batare da taga tafiyar tasu data so ganiba. Aiko Yusrah da Amal sai kwasar dariya suke daga cikin mota. Duk wannan abu a gaban idanu Joy da Miracle da Gebrail dake can gefe ya faru. 
             Cike da mamaki Gebrail yace, “Wai wannan ɗan yarinyar aka bama damar ciran kuɗi a bank yanda ta gadama. Amma mu ga Brother Yoohan ya hana a zuba mana kuɗin daya haura dubu hamsin tsabar ya rainamu”.
         Joy tace, “Shegiyan yarinyar nan family ɗinta kudine da su shiyyasa takema mutane iskancin data so. Ni dama muyi joining ɗinta mu cinye kuɗin”.
         Tsaki Gebrail yaja yana faɗin, “Mumu! Ance miki bata da basira ne kamar ke. Bayan kun nuna bakwa sonta sai ta yarda daku yanzu. Yaran arewa ɗin nan fa shegen wayone dasu more especially yaran Hausawa ɗin nan. Balle wannan mai aiki da aljanu ɗin nan, dan idanunta kamar na Google suke a gidan nan”.
         Masifa Joy ta fara masa saboda yace mata Mumu. Nan take suka harƙume faɗa Miracle data tsunduma duniyar tunanin akan zancen kuɗin Nu'aymah ta shiga rabasu daga zaune dan har yanzu ƙafarta batai garau ba sosai. Ga tabon fashewar da tayi a baki akai mata ɗinki nan raɗam ya zame mata tambari😜😂.

_____________

        Oho, Aymah bama tasan sunayi ba. Dan tana can ta ɗora layinta a waya tana jiran awannin da suka bata ta fara kira da shi su cika ta kira Umm da baba malam da hajjo dan tsabar zumuɗi. Kota Yoohan da ya sai wayarma ba'ayi bawon ALLAH😪.
        Ganin dai lokacin yayi dare dole ta haƙura sai da safe. Tana kuwa idar da salla sai ga massege ya shigo mata. Ɗaukar wayar tayi ta duba. Ɗaya daga kamfani ɗaya kuma credit card ne aka lodo mata harna dubu biyar. Basai ta nema ba'asi ba, dan ta ga sunansa ne. Amma maimakon tai tunanin nemar lambarsa ta fara kiransa sai ta kira Umm ɗinta. Dan tasan baba malam kam yanzu yana massallaci bai fito ba.
         
★★★

        Yau kwanaki biyu kenan da zuwan su Amal gidan, ranar litinin bayan sallar la'asar momy da su mama debora suka tafi church. Blessing taja Uwaliya suka tafi kasuwa cefane. Su joy kuwa suna school. Hakan yasa gidan yin shiru dan da alama ma Nu'aymah ita kaɗaice. Bata damuba dan ko tsoro bataji. sai ma ta buɗe data ta shiga cheating da su Yusrah dan yanzu duk ta koma harkokinta na yanar gizo numbers ɗin ƴan gidansu da ƙawayensu kuwa duk su Amal sun tura mata har ƴan orphanage. Hakan yasata sake samun abubuwan ɗebe kewa tanata hidimarta hankali kwance kamar bata da damuwar kowa a ranta.

        Shiru babu wanda ya dawo har magriba ta rufa. Aymah dake ɗanjin ƙafarta na mata ciwo sama-sama tun a daren jiya ta miƙe da ƙyar tana yamutsa fuska dan tasan dai period ɗintane ke nuna alamun ya kusa zuwa. Alwala taje tayi tazo tai sallar magriba. Tana idarwa ta miƙe ta fito waje saboda motsi da taketa faman ji tun tana salla. ita a zatontama ko Uwaliya ce suka dawo. Sai dai a mamakinta sai bataga kowaba a falon, batare data damu ba ta juya ta koma cikin bedroom ɗinta bayan taje ta rufo ƙofar falon data gani a buɗe.
       Tana shigowa ɗakin aka kashe fitila duhu ya mamaye ɗakin Tare da rungumota aka matse. Tashin hankali da ba'a saka masa rana. Duhu shine abu na biyu da Aymah ta tsana a rayuwarta bayan allura. Gashi yana mugun yin tasiri akan lalurarta. Aiko a take ta daddage ta ƙwalla wani irin gigitaccen ihu da sai da muryarta ta amsa kowanne kusurwa da bango da ke a cikin gidan...........✍

😱Tofa, wane hege ne zai ɓallo mana ruwa kuma Aymah?🙆🏻. Ga Dafta yayi nisan kiwo🤦🏻😫.



_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 54

_________________
_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._ 

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_

_______________

No. 54

............Ihun Nu'aymah yayi dai-dai da shigowar motocin guards ɗin Yoohan da sukaje taryosa a airport batare da kowa na gidan ya san da dawowar tasa ba. Ba ƙaramin faɗuwa gabansa yayi ba. Ya ɓalle murfin motar da hanzari batare da ya jira an buɗe masa ba ya fice. 
       A dai-dai wannan lokacin kuma su Momy ma suka dawo daga church. Ihu na biyu da Nu'aymah ta sake ƙwalawa ya sake shiga kunnuwansu suma. Har rige-rigen fitowa suke a mota kowa na zare idanu da kiran Jesus.

         A ciki kuwa, tun a ihun farko da Aymah tayi Gebrail ya ruɗe. Yay saurin sakinta daga rungumar da yay mata jikinsa na ɓari. Faɗuwar da tayi a kan hannunta ne yasata sake ƙwalla ƙara ta buyu a take ta sanƙame a sume.
        Da lalube ya buɗe ƙofar ya fito, kirif ya kife ƙasa a cikin falon. Goshinsa ne ya bugi tiles sai ga jini. Bai damu ba, ya miƙe da sauri zuciyarsa kamar zata zubo ƙasa saboda firgici da tashin hankali. Ya kai hannu ya murza key ɗin data sakama ƙofar falon, zai buɗe ƙofar kenan aka turo. Da sauri ya koma bayan ƙofar ya maƙale fitsari na zubo masa a jiki dan jin ƙamshin turaren Yoohan, hannu yasa ya danne bakinsa da sauri.
      Kasancewar Yoohan a rikice ya ke hankalinsa bai kai ga Gebrail ba, ɗakin Nu'aymah kawai ya tasarmawa yana ƙwala kiran “Zeeynab! Zeeynab!! Where are you?!”.
         Da wannan damar Gebrail ya fita a guje zuwa ɗakinsa hannunsa tare da goshinsa dake zubda jini. Akan idanun Uwaliya dake shirin fitowa daga ɗakinta Gebrail ya fito daga sashen Aymah. Sun dawo suma babu jimawa. Sai dai ganin lokacin salla na ƙara wuceta ya sata nufar ɗakinta da nufin sai tayi sallar sannan taje ta sanarma Aymah sun dawo. Blessing kuwa tana can backyard tana tattaro shanyar da tayi kafin su fita. Ihun Aymah kawai taji hakan yasa suka shigo falon kusan a tare da su momy da suka dawo church.
            Gaba ɗaya Yoohan yama rikice, ya rasa miya kamata yayi saboda ganin duhu a ɗakin Nu'aymah daya shiga. Da ƙyar ya iya lalubar makunnar fitila ya kunna. Ganinta yashe a ƙasa ya sakashi zabura kanta yana sake ƙwala mata kira da wata irin razananniyar murya data sake rikita su Momy Destiny da ke shigowa sashen.
           Gaba ɗayanta ya ɗago zuwa jikinsa, ya sakata a ƙirjinsa yana bubbuga fuskarta da cigaba da kiran sunanta. Fahimtar da yay numfashinta yayi nisa sosai ya sakashi miƙewa da ita gaba ɗaya zuwa gado. Su dai su Momy sunyi cirko-cirko kowa yana tambayar kansa miya sameta?. Babu mai basu amsa, dan haka suka cigaba da kallonsa.
       Shimfiɗeta yay a gadon ya shiga murza tafin hannunta. Sai kuma ya koma ƙafafunta. Babu dai alamar zata motsa. Kansa ya dafe yana ambaton sunan ALLAH. Ya kai tsahon seconds sha biyar kafin ya koma ƙasa gaban gadon ya durƙusa saitin fuskarta. Bakinsa ya ɗora saman nata ya toshe mata hanci da yatsunsa biyu ya shiga jawo numfashinta cike da dabararsu ta likitoci. Kusan tsahon seconds ashirin kafin ta kawo wani irin dogon numfashi tare da zabura ta saki wahalalliyar ƙara saboda sakin mata baki da yayi.
         Zabura tai ta haye jikinsa dan ya dawo bakin gadon ya zauna yana sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin ta farfaɗo. Ta ƙanƙamesa tana faɗin, “Duhu Umm. Banason duhu ki samun fitila. Umm ki kiramin Abbana banason duhu Yaya Yoohannnnn!!”.
         Idanu Yoohan ya lumshe a hankali saboda jin yanda taja sunansa akan harshenta, ya saka duka hannayensa ya rungumeta a jikinsa da ƙyau dan jikinta wani irin karkarwa yakeyi. A haka ya ɗora bakinsa saman kunnenta ya shiga hura mata iska a ciki. Hannayensa kuwa na shafa bayanta. A hankali ta fara sassauta surutan da takeyi, rawar jikinta na raguwa. Sai kuma ta koma sauke ajiyar zuciya hawayenta dake fita masu ɗumi na saukar masa a ƙirji.
       A haka ta sake sumewa, Hankalinsane ya tashi da wannan sumar, dan sumace da yake da tabbacin mai haɗarice a gareta. sai ji yay ta masa nauyi kawai. Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na babu adadi, hankalinsa na ƙara afkawa cikin ƙololuwar damuwa. Ya buɗe idanunsa da suka rine da ja yana kallo ahanlinsa dake zagaye da su a cikin ɗakin. Baice komai ba, dan bayason susan komai ɗin, sai kwantar da ita da yayi a hankali yaja bargo ya rufa mata, tare da ɗaukar remote ɗin ac dake a durowar gefen gadon a ajiye ya ƙara gudunsa saboda sanyin da yasan tafi buƙata a yanzun.
       Sake maida hankalinsa yay gasu Momy yana musu alamar suje waje. Babu wanda yace komai duk suka fara fitowa shima ya biyo bayansu yaja ƙofar ya rufe mata dan dolene yaje ya nema mafita.
      Dukansu babu wanda baibi jinin Gebrail daya fasa kai ba da kallo. Yoohan da yay ƙarshen fitowa ya jinjina kansa kawai yana kallon jinin da tunani barkatai a ransa.
      Momy Favour ce ta fara faɗin, “Wai miya sameta ne haka John?”.
       Kansa ya girgiza. Muryarsa na nuna alamun damuwa yace, “Aunt ban saniba nima. Ihunta kawai naji dai-dai muna shigowa gidan nan. Sai dai da alama wanine ya shigo ya tsoratata da duhu dan batason ganin duhu”.
               Kallon-kallo suka shigayi a tsakaninsu. Momy tace, “Amma babu kowa a gidan nan sai ita da su Blessing. Dan muma shigowarmu kenan daga church muke. Joy da Gebrail suna school. Miracle kuma bata dawo daga wajen aiki ba har yanzu da alama”.
       Batare da Yoohan yace wani abuba ya dubi Blessing da Uwaliya. Cikin sauri Blessing tace, “No Sir. na rantse da ALLAH muna bamusan miya sameta ba. Dan bamufi 5minutes da shigowaba mukaji ihunta. Ni inama backyard ina kwashe kayan dana shanya danai wanki ɗazun. Uwaliya kuwa tacemin zataje tai salla sai dai ban saniba ko.......”
       “Wlhy nima salla na shigayi banje wajentaba saboda ganin zan makara”. Uwaliya tai saurin tarar numfashin Blessing ɗin.
      Hannu Yoohan yasa a goshinsa yana ɗan murzawa. Sai kuma ya furzar da huci mai zafi. Batare da ya sake magana ba ya nufi ɗakinsa kawai.
       Suma duk jan ƙafafu sukai gwiwa a sage suka fita harsu mama debora da suka gaza cewa komai. Su Victoria kam dama sunsan idan Yoohan na magana da iyayensu baya buƙatar cewarsu, shiyyasa basu tofa ko ‘A’ ba a maganar. Daka gansu dai kasan tausayin Nu'aymah ya cika musu zukata.

        Kowa ɗakinsa ya nufa, sai dai Momy na shiga nata taci karo da Gebrail cikin toilet yana leƙo kansa. Yanajin motsin za'a buɗe kofa yay saurin komawa zai rufe ƙofar. Da sauri momy tace, “Kai waye anan?”.
      Jin muryar momynsa ne ya sakashi fitowa jikinsa na rawa. Yay saurin faɗin, “Momy shiii!! Karkiyi magana Please”.
      Sosai gabanta ya faɗi ganin yanda jikinsa ke ɓari. Ga jini ya jiƙe handkerchief ɗin daya ɗora a goshinsa inda yaji ciwo garin gudu. Saurin ruƙo masa hannu tayi suka koma cikin toilet ɗin itama nata jikin yana rawa. Ta maida ƙofar ta rufe tana magana a matuƙar tashin hankali. “Gebrail! Badai kaine ka aikata ba?”.
        Hawaye na zuba masa a idanu jikinsa na karkarwa yace, “Momy idan Brother John yasan nine kasheni zaiyi. Na rantse tsautsayine momy kuma ban mata komai ba. Na rungumeta ne kawai na kashe wutar ɗakin shine tamin ihu”.
      Kai momy ta dafe tana faɗin “Oh my lord”. Sai kuma ta kama kafaɗun Gebrail ta shiga girgizawa. “Gebrail baka da hankali. matar John? Bayan kasan halinsa a gidan nan”.
        “Momy na rantse tsautsayi ne, ina sonta da gaba ɗaya zuciyata. Amma nasan Brother Yoohan zai halakani idan ya sani, kasheni zaiyi da hannunsa momy, ki taimakeni karki bari ya gane nine momy”.
     Kuka yake sosai jikinsa na karkarwa. Jansa tayi jikinsa ta rungume duk da itama harga ALLAH a mugun tsoracen take. Dan tasan shirun da Yoohan yayi tabbas bazai zama na banza ba. Sai da taji bugun zuciyar Gebrail yaɗan dai-daita sannan ta ciresa a jikinta ta zaunar akan bathtub. Fita tai ta ɗakko First aid box ta dawo toilet ɗin bayan ta murzama ƙofar bedroom ɗinta key. Zuwa tai tai masa dressing wajen. Ta miƙe tana faɗin, “Kayi wanka zanje na ɗakko maka kaya a ɗakinka, dolene kabar gidanann a daren nan Gebrail. Kaje ka kama hotel koka koma cikin hostel ɗin makarantarku har sai wannan ciwon da kaji ya warke. Inba hakaba sai Yoohan ya gano kaine dan kowa yaga jinin daka zubar a sashen. Ka kuma san shi mutumne mai tsanani basira akan duk abinda ya ƙwafa”.
     Kansa ya ɗaga mata yana faɗin, “Thanks you momy, thanks you so much”.
      Bata sake cemasa komaiba ta fita tana tunanin yanda zata shiga ɗakinsa ta ɗakko kayan cikin dabara ba tare da kowa ya fahimta ba.

           ★★★★

              Tabbas yau Gebrail ya sako Aymah cikin mummunan matsala. Musamman daya kasance a irin wannan lokacin ana lallaɓa lafiyar tata ne, domin aikin da Yoohan keta kaikawo wajen ganin da shine za'ai mata shi saboda haɗarinsa. Sai dai Alhmdllh, isowar Yoohan ɗin akan lokaci ya zama rahama a gareta. Duk da shima kuwa dawowar tasa bata lafiya bace ba. Ciwonsa ne na rashin barci ya dawo, yau kwanakinsa uku kenan baya iya barci, koya ɗaukesa saboda addu'a da yake yi baya gaza mintuna ashirin yake farkawa. Ganin al'amarin nasa na ƙara faɗine ya sakashi tattarowa ya taho gida. Sai gashi kuma ya iske wani tashin hankalin da shima ya nema birkita tashi ƙwalwar kan.
     Duk yanda yake tunanin bama Nu'aymah taimako da kansa anan kafin wa'adin da za'ai mata aikin ya fahimci babu mafita. Dole ya yabar ƙasar nan da ita a gobe idan ALLAH ya kaimu, dan inhar ta wuce awa saba'in da wani abu komai zai iya faruwa da ita. Shi a yanzu hakama ya rasa wane taimako zai bata. Duk wata basirarsa ta likitanci ta kufce, man kansa ya tsiyaye tas. Waya ya ɗauka ya shiga nema wata abokiyar aikinsa Dr Shukurah dake anan General hospital na Abuja. Dan itama likitace mai ƙwazo da sanin makamar aiki. Gata babbar mace kuma dan momy ma Yoohan ke kiranta ita kuma tana cemasa Son. Tun ganinta da shi na farko lokacin an turasa bautar ƙasa a asibitinsu kamanninsa da yaron ƙanwarta yaja hankalinta. Ta kuma kasa haƙuri sai da tai maganar kamannin nasu. Sai dai shi Yoohan har yanzu bai ɗauki abin da muhimmanci ba, saboda bai taɓa ganin wancan datake faɗin suna kamar ba. Amma tayi alƙawarin wataran sai ta haɗasu dan wancan duk da ba'a Najeriya yake ba.
       Duk da Dr Shikurah ta tashi da ga aiki yanda taji muryar Yoohan ɗin sai yay matuƙar tada mata da hankali. Dan haka ta nema alfarmar mijinta akan zataje. Da yake mutumne shi mai sauƙin kai sai ma yace bara ya kaita da kansa tunda darene duk da bawai can sosai ba.
        Kasancewar tasan gidan su Yoohan ɗin dama basusha wani wahalar neman address ba. Cikin mintuna ƙalilan sai gasu sun iso. Solomon ne yay mata iso cikin gidan. Har lokacin su momy na tsaye a ƙofar sashen cirko-cirko kowa da abinda ya damesa. Dan da farko basu ɗauki al'amarin da zafi ba. sai da sukaga yanda Yoohan ɗin ke a birkice ne yanata shige da fice suka sanfa aiki ne babba kenan.
       Sama-sama ya iyayma Dr Shikurah bayani akan matsalar Nu'aymah. Itama sosai hankalin nata ya tashi ta shiga faɗa akan dan miyasa za'ai gangancin sakata a duhun? Bayan kuma yana cikin abunda zai iya burkita ƙwaƙwalwar ta a lokaci ɗaya babu jinkiri. A yanzu hakanma basu da tabbacin ba'a samu matsalar da suke tsoronba. Shi dai Yoohan ma ya gaza cewa komai. Sai dai idanunsa sun sake kaɗawa jazur. Yana tsananin tausayin yarinyar nan fiye da tunani. Shiyyasa yake ta lallaɓa yanayin nata har kwanakin da zasu wuce ai mata aikin su cika. Amma dan tsabar zalunci an samu wani yazo yana neman ƙwaɓe masa aiki. Dolene wanda ya aikata wannan ya fuskanci mummunan hukunci daga garesa a gidan nan koda kuwa wanene. Amma a yanzu bashi da lokacinsu sai matarsa ta dawo hankalinta insha ALLAHU.
         Dukkan wani taimako daya dace Dr Shikurah ta bama Aymah, dan yau ko allurar nan da yake mata biyu akai mata, dama uku ce ta rage. Ta kuma tunatar dashi akan dolene kafin nan da awanni saba'in aimata aikin da ya sanar mata sun gama booking.
     Kansa kawai ya iya jinjina mata, tare da godiya akan ƙoƙarinta. Daga haka yayo mata rakkiya ta wuce. 
      Sai a lokacinne yacema su Momy ya kamata suje su kwanta abinsu tunda da sauƙi. Dama a ƙage Momy take da kowa ya shige ɗin. Dan har yanzu Gebrail na ɗakinta neman hanyar da zai gudu take bukata.

           Dole ranar a ɗakin ya kwana. Dama gashi ba barci yake iya yi ba. Sai dai saɓanin baya da yake kwana cikin ƙunci da baƙin ciki yanzu ba haka baneba. Zuciyar tasa kam a ƙuntacen take, ga ciwon kai mai tsanani. sai dai kuma ya raya kaso biyu bisa uku na daren ne da nafilfili yana miƙama UBANGIJI kukansa. Sauran kaso ɗayan kam duk akan duba na'urorin da aka sakama Aymah ne lokaci-lokacin domin duba yanayin tafiyarsu, sai kuma neman hanyar da zai matso da maganar aikin da za'ai mata kafin waɗanan awannin su cika. Alhmdllh babu wata damuwa har suka wayi gari. Bayan yayi sallar asuba toilet ɗinta ya shiga yay wanka. Sannan yaje ɗakinsa yay shiri ya sake dawowa. Wayarsa ya ɗauka kamar zai kira baba malam sai kuma ya fasa bisa wani tunani da yayi.
            Dubata yayi, ya tabbatar kozata iya farkawa sai nan da wasu awa kamar huɗu. Insha ALLAH kuma zuwa sannan zai kammala usirinsa ya dawo. Hannunta ya kama a hankali ya sumbata, kafin ya shafi kumatunta yana mai mata addu'ar samun lafiya mai ɗorewa. Daga haka ya fito. A falo ya iske Uwaliya na gyarawa. Ta gaidashi da girmamawa tana tambayarsa mai jiki. A takaice ya amsa mata. Tare faɗa mata ta ajiye aikin taje ta zauna a ɗakin Nu'aymah. Ta amsa masa da to, ta ajiye kayan sharar ta nufi ɗakin shi kuma ya fita.
       Masu gidan duk suna ɗaki, ma'aikatanne kawai ke aikin gyara gidan. Papa baya nan yayi tafiya shima. 
         Har Yoohan ya nufi downstairs yana amsa gaisuwar da ma'aikatan gidan ke masa sai kuma ya dawo. Ɗakin Momy ya nufa kai tsaye. Ya tsaya a bakin ƙofa yay knocking. Sai da ta bashi izinin shiga sannan ya shigo. Rikicewa tai, dan a bazata ta gansa. Duk zatonta su Victoria ne sukazo mata sallama zasu wuce school. Ta tura wayar da take amsawa ƙarƙashin filo cike da rashin gaskiya. Shi dai da yake hankalinsa ba a jikinsa yake ba yanda ya kamata baima fahimci halin da take ciki ba. Ya gaidata da girmamawa kamar yanda ya saba. Sai dai yanda ta amsa masa murya na rawa da kuma kamar a daburce ne ya bashi mamaki.
       “Mom are you ok? Hope you are well?”.
       “Y..yes yes Son. It is Okay. Mika gani?”.
        “No, dama banga Gebrail bane tunda na dawo. Where is he?”.
           Ba ƙaramin bugawa ƙirjin momy yayi ba, harda taune harshenta saboda a bazata tambayar tazo mata. Ta shiga girgiza kanta tana faɗin, “Uh...Uhm ai yayi tafiya ne?”. Tai maganar da sosa ƙeya tana wani washe haƙwara.
        “Tafiya? Where did he go?”. Yay maganar yana tsuke fuska da ƙyau.
     Sosai Madam Chioma ta ƙara rikicewa. dan gani take kamar Yoohan ɗin ya shinshino wani abune. da ƙyar ta iya control ɗin kanta tace, “Ban sani ba Yoohan. Dama inason ka dawo na zauna da kai akan lamarin Gebrail. Rashin jinsa ya fara yawa. Tunda suka shiga University ɗin nan ƙara kangarewa yakeyi”. Yanda ta ƙare maganar ne tamkar zatayi kuka ya saka Yoohan sassauta muryarsa yana sauke nannauyan numfashin ɓacin rai. Ya cije lip ɗinsa yana miƙewa daga zaman da yayi. “Babu damuwa ki barni da shi. amma Mom kema harda laifinki. Kece ke zama da yaran nan fiye da kowa. Amma miyasa idan kinga irin haka ta fara faruwa bazaki sanar min ba. Yanzu daban tambayaba maybe harna sake barin ƙasar bazaki sanar minba. Zanci ubansane. Tunta bayaji zaiko cigaba da karatu a Nageria”.
         Daga haka ya fice batare da ya sake bata damar cewa wani abuba. Itama daɗin hakan taji, dan inhar suka cigaba da zama a haka zata tonama kanta a siri, zata kuma iya aikata abinda ke ranta game da yaron nata. Dan a yanayin da yake na sanyi-sanyi yau sai ya wani tada mata tsuminta. Ji take kamar tai.....
       Ta matse idanu da ƙarfi tana faɗawa saman gadon batare data iya ƙarasa ruɗaɗɗen tunanin nata ba. Oho shi Yoohan ma baisan tanayiba. Dan har sun fice daga gidan shi da guards ɗinsa.

__________________

       Tunda Yoohan yabar gidan yaketa faman shigi da fici. Duk da azabar ciwon kai dake damunsa haka ya jure yanata kai kawo ko takan breakfast bai bi ba. Baima tunawa da yunwar duk da kuwa jiya ko buɗa bakin kirki baiyi zaman yiba tunda ya kai azumi.
       Sai wajen sha biyu saura ya kammala duk abinda ya dace. Ta office ɗin Abban Abdallah ya biya. Suka tarbi juna cike da girmamawa da surukuta. Anan ne Abba ya fahimci kamar baida lafiya. Sai dai bai tambayesa kai tsayeba sai a cikin hikima. Yoohan ɗin bai ɓoye masa ba ya sanar masa.
       Kai kawai Abba ya dinga jinjinawa. cike da damuwa yace, “Yahya anya kuwa a lamarinka babu sihiri?”. Yoohan bai fahimci abinda Abba ke nufi ba. Dan haka ya ɗago rinanun idanunsa yana kallonsa. Kai Abban ya sake jinjinawa. Cike da tabbatarwa yace, “Tabbas akwai sihiri a wannan al'amarin. Amma karka damu zanyi magana da Yaya. Insha ALLAH komai zai wuce. bara yanzu nai maka kamu sai na rubuta addu'oin nan idan kaje gida mamana ta zauna tayisu dan duk ta sani. Ka fara shansu su zama kamar ruwa a gareka”.
      Godiya Yoohan yay masa. amma sai ya sanar masa ma ai zasu wuce da Nu'aymah ne a yau da daddare dan jikinta ya motsa. Sai dai bayason baba malam ya sani da wuri har sai sun isa can dan karya tada hankalinsa.
        Cikin tsananin damuwa Abbah ke jera mata addu'oin samun lafiya. Ya ɗora da faɗin, “Duk da nasan Yaya bazai shiga ɗimuwar da kake hasashen ba na goyi bayan a ɓoye masa ɗin har sai kunje. Amma insha ALLAH muma zamu biyo bayanku ko zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu ne. ALLAH ya ƙara muku lafiya damu baki ɗaya”.
      Da amin Yoohan ya amsa masa.
Baibar Office ɗinba sai da Abba yay masa addu'oi sosai, har a cikin ruwa ya bashi ya sha sannan yay masa sallama ya wuce yana maijin ƙaunar waɗanan bayin ALLAH har cikin ƙasan zuciyarsa.

★★

        Daga wajen Abbah gida ya koma. Inda ya iske farkawar Nu'aymah kenan kamar an auna da dawowar tasa. Uwaliya kawai ya iske a ɗakin kamar yanda ya gargaɗeta karta bar kowa ya zauna dan ba'a bukatar yin hayaniya komin kanƙantarta. Hakan yasa ƴan gidan duk wanda yazo ya dubata sai ya fice baya zama.
         Saurin ƙarasawa yay cikin ɗakin. Hakanne ya saka Uwaliya dake riƙe da hannunta tana jera mata sannu saurin matsawa baya ta bashi waje. Zama yay a bakin gadon kusa da ita. Ya cire duk na'urorin dake manne da kanta da kunne. Yanayi yana addu'ar neman nasara ga UBANGIJI.
          Batayi maganaba, sai dai hawaye dake silalo mata a kan fuska a hankali. Sake matsawa yay sosai kusa da fuskarta, ya dafa hannayensa a gefe da gefenta yana mai tsurama hawayen nata ido. Da ƙyar ya haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi, ya ɗan furzar da iska yana lumshe idanu da sake buɗewa akan fuskartata. Hannunsa ɗaya ya ɗaga ya ɗaura akan lallausan fatan kumatunta yana share mata hawayen. Kafin ya ƙara ranƙwafowa kanta sosai fuskarsa gab da tata yay magana a hankali kamar mai raɗa. 
        “Please banason kuka Zeeynab. Idan zaki iya buɗe idanunki kaɗan-kaɗan na gani”.
       Uwaliya dai na tsaye a gefe tana kallonsu a wani yanayi.
       Duk maganar da Yoohan keyi Aymah na jinsa, dan haka taɗan shiga motsa idanun nata kaɗan-kaɗan. Tana buɗesu a sannu-sannu harta buɗe kusan rabi a kansa. Murmushin ƙarfin hali ya sakar mata yana lumshe nasa idanun da a kallo ɗaya zaka fahimci shima lafiyar ba isasrsa tayi ba.
         “Alhmdllh” ya sake faɗa a hankali yana kamo hannunta cikin nashi. Sake maida idanunta tai ta lumshe itama. Daga haka ɗakin ya ɗauki shiru. Yaja wasu mintuna uku haka kafin ya juya ya kalli Uwaliya. Saurin yin ƙasa tai da kanta tamkar dama ba kallonsu take ba. Bai wani damuba duk da ya fahimci yanzu ne ta duƙar da kan. Shi gulmar ƴan aiki ba irin wadda bai haddace ba. 
        “Haɗomin ruwa mai ɗumi a roba, tare da towel”.
      “Okay sir”. Uwaliya ta faɗa da girmamawa tana nufar toilet ɗin Nu'aymah.
        Kansa yaɗan dafe yana yamutsa fuska, dan dauriya ce kawai ya keyi iya jarumta. Cikin mintuna ƙalilan Uwaliya ta dawo da abinda ya buƙata. Tana ajiyewa tace, “Sir ko za'a haɗa mata wani abinci haka?”. Towel ɗin data ajiye ɗin ya ɗauka. Batare daya kalleta ba yace, “Ki duba abu maiɗan ruwa-ruwa haka da kika fahimci tana so sai ki haɗa muga ko zata sha”.
       “Okay sir”.
Miƙewa yay yabi bayan Uwaliya data fita. Ya murza key ɗin ƙofar sannan ya dawo yana zame baƙar jacket ɗin jikinsa mai ƙyalli kamar leda daya ɗora akan ƙananun kayan jikinsa. Inda ya tashi ya sake komawa ya zauna. Sake ranƙwafowa yay kan Nu'aymah yaɗan juyata kaɗan ya fara jan zip ɗin rigar jikinta ƙasa.............✍

😪Tabɗi, har words 3600. Kai yau gaskiya kun samu garaɓasa. To harda na gobe😖🚶🏻😒.



ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 55

_________________
_*HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION, HAJARA COLLECTION._*

_Ina mata masu son ingattun kayan kamshi: Na kece raini? Kayan mata masu sa kishiya k’wafa? Bikin dangin miji ba za’a baki yankan albasa ba da wankin tumatir? To matso kusa domin HAJARA COLLECTION ta kawo muku kayayyaki na gyara ciki da wajen mace, Wanda suka kunshi:_

_Khumrahs: Sudaniyya, Chadian, Dufr, Fara da brown, Kai harda masu flavours... _

_Akwai turaren wuta irin su sandal, Hawi, Alut, Gab gab da sauran su.._

_Akwai turaren tsugunno dana jiki original gangariya tafiyayye dan gaske_

_Hajara collection ta kawo muku air fresheners, Mopping sprays da turaren wanki..._

_Akwai herbal organic soap wato sabulun gyaran jiki na maida tsohuwa yarinya.._

_Sannan Hajia hajara collection tana gyaran jiki.. Tana kuma siyarwa da kayan gyaran jiki na dilke set, Fata tai luwai luwai kamar ta jarirai.._

_Akwai special bridal spa wato gyaran jikin Amarya... Duk Amarya mai son tadinga kamshi har bayan shudewar bikinta to ta nemi hajara collection.._

_Akwai duk wasu nau’in kayayyakin turare masu kamsasa unguwa baki d’aya, Ki mopping tiles suyi sati suna kamshi, Kayan Haj hajara collection akwai inganci sosai._ 

_Akwai page dinta a favebook mai suna *GIDAN KAMSHI* ga mai son zuwa ya duba hajarta, Ko kuma ya tuntubeta a number wayarta kamar haka: 09032069304_

_Adireshi: KANO NIGERIA, MARIRI dake Kan titin MAIDUGURI RD. KANO STATE.._

_TANA BADA KAYANTA AKAN FARASHIN SARI KO SAYA DAYA DAYA, SANNAN TANA TURA KAYANTA A KOINA AFADIN NIGERIA_

_AVAILABLE IN WHOLESALE/RETAILS. Nationwide deliveries. 100% tested and trusted...!!!_

_Kyau, inganci, Rahusa... Sai kayan HAJARA COLLECTION....!_

_idan anje siya ace daga zafafa biyar.. Akwai special package da Za’a hada maka masu kamshi🥰😍🧚🏻‍♂️_

_________________

No. 55

.............Sai da ya dire zip ɗin har ƙasa sannan ya maidata ya kwantar, hannun rigar ya kama ya cire, ɗayanma haka. Sannan ya cire rigar gaba ɗaya ya ajiye gefe. Idanu Aymah ta rumtse da ƙarfi jin zai zame skirt ɗinma. Bata da ƙarfin iya koda magana balle tace zata hanashi yin abinda taji yana ƙoƙarin aikata mata. Tanaji tana gani ya barta daga ita sai B&P. Ji take inama ƙasa ta tsage kawai ta zurma ciki. Sai dai tasan hakan bamai yuwuwa bane. Ta na sauraren ya idasa abinda ya fara sai taji baiyinba. Saima towel ɗin daya jiƙo da ruwan ɗumin nan ya fara goge mata jiki da shi a hakan batare daya cire sauran suturar tata ba. Taji daɗin hakan har cikin ranta. Sai kuma ya ƙara mata girma a zuciya. Ta tabbata shi ɗin ba mutum banza bane. Dan inda wanine duk da bata da lafiyarnan hakan wata damace a garesa. Amma shi tana kallonsa ta ƙasan ido aikin gabansa kawai yakeyi ko kallon ƙurilla bai tsaya mata ba.......
      Ajiyar zuciya ta saki a hankali lokacin daya ɗagota ya saka a jikinsa. Bayanta ya goge tsaf sannan ya ɓalle bra ɗinta. Batare daya ɗagota ba ya zare ya ajiye, a haka ya goge mata ƙirjinta tana a kife. Ɗagota yay zai kwantar ta ƙara narke masa alamar batason ɗagowar. Yoohan ya fahimci inda ta dosa. Dan haka yaɗan murmusa kaɗan cike da ƙarfin hali. “I'm sorry bazan kallaba na miki alƙawari”. Duk da tana jinsa taƙi yarda ya ɗagotan. Dole ya barta a yanda take son. Ya jawo bargo a haka ya lulluɓa mata sannan ta yarda ya kwantar da ita. Ta cikin bargon ya zare mata sauran kayan ya goge wajajen. Ya tattare kayan da kansa ya maida toilet. A washing machine ya saka ya wankesu. Ya shanya mata su bra ɗinta, kayan kuma ya barsu a boket idan Uwaliya ta shigo sai taje waje ta shanyo su.
       Sake dawowa ɗakin yayi ya ɗauka mata kaya. Rigace mara nauyi da kayan ciki waɗanda dai bazasu takura mata ba. Bai damu da yanda taƙi sake buɗe idanunba. Ya bita a yanda takeso ya saka mata kayan. Sannan ya yaye bargon daga jikinta yana sauke numfashi a hankali. gyara mata abinda baiyiba yayi ya ɗauketa cak zuwa bayi yana faɗin, “Muje kiyi fitsari nasan kinaji ko?”. 
      Kanta taɗan girgiza masa alamar a'a. Bai saurareta ba ya kaita, da taimakonsa tayi fitsarin da brush. Yana dawo da ita Uwaliya nayin knocking. Buɗe mata ƙofar yay ta shigo. Tana ajiye kunun gyaɗa data damo da soyayyan ƙwai dan aɗan zaman da tai da Aymah ta fahimci tana san soyayyen ƙwai.
         Zama yay da kansa ya bata cikin lallashi kamar ba shi ba. Da farko taso ƙinsha amma lallaɓatan da yake yine ya sakata daurewa tasha. Dan yanda takejin muryarsa duk sai taji babu daɗi..
        Idanun nata ta buɗe a hankali tana kallonsa. Yanda yaketa yawan kai hannunsa yana murza goshinsa ne yasata tunanin shima kamar baida lafiyan. Ga jijiyar kansa tayi ruɗu-ruɗu. A bazata yaji hannunta bisa goshinsa. 
        Saurin ɗago idanunsa yay yana kallonta. Daɗi yaji a ransa ganin ta ƙara buɗe idon harma yafi na ɗazun. Ya ɗora hannunsa shima akan nata data aza bisa goshinsa. “Kina buƙatar wani abu ne?”. Yay maganar a hankali yana kwantar da kanta a jikinsa.
      Kai ta girgiza masa. sai kuma ta sake ɗagowa tana kallonsa ƙasa-ƙasa sosai, da alama batason buɗe idanun saboda ciwon kai da ke addabarta. Cikin magana ƙasa-ƙasa sosai da shi kaɗai ke iya jinta tace, “Kaima kanka na ciwo ko?”.
         A bazata murmushi ya subuce masa. Ya sumbaci goshinta tare da sake maida kanta ya kwantar a ƙirjinsa yana shafa damtsen hannunta a hankali batare da ya bata amsar tambayar tata ba.
          Ƙare lafewa tai bata sake magana ba itama. Sai ma barci daya sake ɗaukarta a haka saboda allurar bata gama sakinta yanda ya kamata ba.

        Idanu ya tsura mata na kusan mintuna goma, a zahiri kallonta ya keyi. a baɗini kuwa ya tafi duniyar tunani mai zurfi. Ganin ta koma barcinne ya sakashi sauke ajiyar zuciya da sake maidata ya kwantar ya lulluɓeta. Fita yay dan yana son shirya abinda ya dace, ya kumayi sallama da jama'ar gidan. Dama ya kira Papa tun ɗazun sunyi magana. Papan ma yace zai samesu acan ƙasar Austria ɗin shima a randa za'aymata aikin.

________★★★_______

       Dukkan abinda ya dace Yoohan ya kimtsa akan tafiayarsu ya tattara. Yayi sallama da kowa na gidan. Momy dai nata baƙin rai dan tace zata bisu yace a'a. Ta bari idan papa ya dawo sai suzo tare.
         Bayan la'asar ƴan gidan su Abba suka iso, har dasu Adawiya. Duk ƙiyayyar da Adawiya kema Aymah yau sai da tai hawayen tausayinta kamar yanda su Yusrah keyi suma. Ƙarfe biyar dai-dai Ambulance da zata ɗauki Aymah ta shigo gidan tare da Dr Shikurah. 
     Yoohan ya ƙara duba komai na sashen nasu, ya tabbatar ya kashe duk wani kayan wuta, an kuma fidda duk abincin da zai iya lalacewa. Da kansa ya kulle ko'ina ya saka keys ɗin a jikkarsa. Duk ƴan gidan sun fito compound, babu dai wanda ke nuna jin daɗinsa da halin da Nu'aymahn ke ciki a zahiri. Sai dai a zuciya ALLAH kaɗai yasan karatun kurma. 
         Duk waɗanda zasu musu rakkiya airport sun shiga mota, harda Uwaliya da zata koma da zama gidan Abba sai su Aymah sun dawo. Haka motocin suka fita a jere waɗanda aka bari na binsu da addu'ar ALLAH yasa a dace.  
      Tafiyar mintuna kaɗan ce ta kaisu airport. kasancewar jirgin nasu na gab da tashi aka shiga da Aymah cikin jirgin, kafin suma su Yoohan da sauran passengers su shishshiga. su Abbah na binsu da addu'a kafin suma su taho. Basu bar airport ɗinba sai da jirgin ya ɗaga a samaniya ƙarfe biyar da rabi dai-dai.
           Sun sauka a Dubai, daga can suka shiga jirgin kaisu Austria.
        
________★★★_______

        Tun jiya Nu'aymah keta zuwama Umm a rai. Ta kira wayarta kusan sau uku kuma a kashe. Gudun karta saka abin yay mata tasiri a rai sai ta barshi akan Aymah bata da cajine maybe. Ko kuma ta kashe wayar a wajen shiriritan ta.
       Haka taita juriya har washe gari da baba malam ya dawo daga tafiya. Shine ya lura da yanayinta. Cike da kulawa ya shiga tambayarta ko lafiya?. Duk yanda taso dannewa kartace komai saita gaza. Muryanta a sanyaye tace, “Haka kawai taketa zuwamin a zuciya tun jiya. Na kirata kuma wayan nata a kashe. Na nema Uwaliya mun gaisa nace ta bata tace min wai barci takeyi. dana sake kira daga baya kuma itama wayan tata a kashe. sai nakeji a raina kamar ba lafiya ba”.
       Ɗan jimm baba malam yay yana kallonta. Dan Abbah ya kirashi bayan sallar magriba ya masa bayanin cewar jikin Nu'aymah ya motsa sosai harma sun wuce Austria yau da yamma. Murmushin ƙarfin hali yayi dason kwantar mata da hankali. Yace, “Babu komai insha ALLAH sai alkairi. Kimata addu'a kawai nasan zata kiraki idan ta kunna wayar. Nima tun jiya da safe bamu sake waya da itaba ma. Karki damu Jannat, ALLAH na tare da Zainab a duk inda take”.
        Yanda ya ambaci ainahin sunan Nu'aymah ya sake sakata jin wani iri. Amma sai ta danne dan karta sake ɗaga masa hankali shima. 
    Daga haka suka bar maganar, sai dai daren ranar daga farkonsa har ƙarshe akan sallaya Umm da Baba malam suka kwana suna mikama UBANGIJI kukansu akan lafiyar yarinyarsu. Duk da ita dai Umm batasan ainahin abinda ke faruwarba.

____________********___________

          Jirgin su ya sauka lafiya a babban birinin ƙasar Austria, Vienna International airport. ananma dai Ambulance ce tazo ta ɗauki Nu'aymah, Yoohan da Richard & Solomon kuma suka shiga taxi. Tafiyar mintuna kalilan ta kaisu katafaren babban asibitin Vienna daya haɗu harya gaji. Babu ta yanda za'ai ka ɗauka asibiti ne na gwamnati inba faɗa maka akaiba. Sannan abun zai matuƙar birgeka a yanda suka samu tarba. Ko hakan yanada nasaba ne da sanin Yoohan ɗin oho.
         Ɗaki na musamman inda sam babu hayaniya aka kai Nu'aymah. Da alama ma an tanajesane domin irin masu matsalarta. Wajen koda takalmi mai ƙara ba'a shiga. Kai ko key ƙaramin alhaki ba'a buƙata. Duk wani abinda ke'a sashen na amfani zaka samu na robane saboda tsabar sanin makamar aiki. (a raina nace hummm ya kaga irin haka a 9ja😁).
          Gaba ɗaya Aymah batasan a inda kanta yake ba, dan tun daga 9ja aka yo mata allurar data sakata doguwar suma saboda ba'a buƙatar duk wani motse-motse a kusa da ita.
         Sai da Yoohan ya tabbatar an ɗorata akan matakin farko sannan suka bar asibitin. Hotel ɗin da Yoohan yafi sauka idan ya shigo ƙasar suka nufa. Acan suka kama masauki. A kallo ɗaya zaka fahimci shima yana buƙatar kulawar, dan haka Rich ya matsa masa akan yay wanka yaɗan kwanta koda bazaiyi barcinba zai huta.
      Bai musaba yabi shawararsa. Shi kuma Rich ya fita zuwa nasa ɗakin. Bayan ya fito a wankan gorar ruwan addu'oin da Abba ya bashi ya fiddo, yay bismilla ya sha tare da shafe fuskarsa zuwa kansa sannan ya kwanta yana ambaton sunayen ALLAH da tuni ya gama haddacesu a kansa. Tun yanayi laɓɓansa na motsawa har ya komayi a zuciya. Cikin amincin UBANGIJI gagara misali sai gashi nannauyan barci yayi gaba da shi cikin lokaci ƙanƙani. Sai dai yayisa ne cike da mafarkin Nu'aymah. Hakan yasa bai wuce awanni uku ba ya farka. Alhmdllh ko yaya dai yaji sassauci ba kamar ɗazun ba. Ganinma lokacin salla yayi sai kawai yayo alwala yazo ya kabbara salla. Ko raka'ar farko bai ƙulla ba Richard ya shigo ɗakin domin son dubashi.
       A wani irin mugun shock yace, “Jesus!! Yoohan!! Salla ka komayi?”.
       Bai samu amsa daga Yoohan ba dan shi gaba ɗaya ma hankalinsa baya a nan kusa. ya nutsu sosai wajen bautar ALLAH.
      Ruɗani iya ruɗani Rich ya shiga. Dan a take gumi ya jiƙesa sharaf ya nata kaikawo da surutai kamar wani zararre.  
         Shi dai Yoohan bai katse sallarsa ba, sai da ya idar a tsanake yay addu'oin fatan samun lafiya ga matarsa sannan ya dubi Richard da ya kasa zaune ya kasa tsaye. A daƙile yace, “Lafiyarka kuwa?”.
         “Kai zan tambaya kana lafiya kuwa Yoohan?!. Salla fa naga kanayi?!”. 
      Idanu kawai Yoohan ya tsurama Rich dake maganar da yare tamkar zai haɗiye harshensa. 
     Ganin kallon da yake masa ne ya sake harzuƙa Richard ɗin, ya hayayyaƙo ma Yoohan da iya masifarsa, “Yanzu wannan ƴar yarinyar har takai ta canja ka ka bar addininka na gaskiya ka koma nata. John What's wrong with you? Are you mad? Are you............?”.
        Saurin katsesa Yoohan yayi ta hanyar ɗaga masa hannu.
      “please Richard!!. Ni ƙaramin yaro ne da zaka zauna kana min ihu a kai? Karka manta shekarata ɗai-ɗai har talatin da biyu. Kasan kuwa inada right ɗin zaɓama kaina abinda nasan ya dace dani ko?.......”
       “Yes! Kanada zaɓi, kuma shekarunka sun kai. Amma tabbas alamu sun nuna baka a cikin hankalinka ne. Shin ƙyawunta ne ya ruɗeka kokuwa kuɗin da mahaifinta ya mallaka? Sunan da yay? Kokuwa asiri sukai maka?”.
      A kanran farko Yoohan yay wani malalacin murmushi, sai kuma ya tsuke fuska tare da jan tsaƙi yana bin Rich da wani irin shegen kallon ɓacin rai da fusata. “Richard! Mubar wannan maganar dan ni ta shafa.......”
      “Nima ta shafeni Yoohan. Dan ka wucemin aboki kai ɗan uwana ne jinina da zan iya bama kariya a kowanne irin yanayi a kuma kowanne irin hali”.
        “Tunda kasan hakane sai ka bani lokaci dan ka fahimceni”.
        Baki Rich ya buɗe zai ƙara yin magana Yoohan yay azamar ɗaga masa hannu. 
        “Please Rich, kana ƙaramin headache. Ka bani lokaci zamuyi magana”.     
          Zama kawai Richard yayi batare da ya sake magana ba. Dan yasan Yoohan ɗin ya kai maƙura kenan. Idan ya cigaba da jan maganar komai zai iya faruwa a tsakaninsu. A ganinsa kuma yanzu na lokacin samun matsala bane. Kamata yay ya taimakama Yoohan ɗin ya dawo cikin hankalinsa dan ya fahimci an gusar masa da hankaline kawai ta hanyar asiri. Shiru ɗakin ya ɗauka har zuwa wasu mintuna kusan ashirin. Kafin Yoohan ɗin ya fara miƙewa ya ɗauka jacket ya ɗora saman ƙananun kayansa. Batare da yayi magana ba ya nufi ƙofar fita. Shima Richard ɗin miƙewa yay yabi bayansa suka fice daga hotel ɗin. a waje suka tari taxi dan komawa asibitin.

__________★★★★___________

*_WASHE GARI_*

       A yau data kama ranar da za'aima Nu'aymah aiki su baba malam sukaso tahowa shi da Abban Abdallah. Sai dai a bisa dalilin wani ɗan tsaiko hakan ya gagara. Tafiyar tasu ma ta tabbata sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu.
      Hakan baisa sun sare zaman jigum-jigum ba. Sai sukai zaman yin addu'oin samun nasara a aiki dan yanda Yoohan keta maimaita a tayasu da addu'a yana ƙara saka tsoro a zukatansu. Shi kansa sun fahimci a tsoratan yake. Saboda bai ɓoye musu ba game da haɗarin da aikin da za'ai mata ke da shi tun farko. Sai dai idan ALLAH ya amince sai ayi kaga kamarma bata taɓa shiga makamancin matsalar ba.
       Hajjo har abincin sadaka tasa akayi, aka kuma sayi abubuwan wasan yara da makamantansu aka rabama yaran gidan marayunsu don suyi farin ciki suma. Maybe darajar hakan ALLAH ya saka musu hannu a lamarinsu suma.

*_ƘASAR AUSTRIA*

          A nan kuwa Yoohan cike yake da fargaba. Sai dai yanata ƙoƙarin dannewa saboda kwarin gwiwa da Dr Liam Ke basa akan aikin. Dan shi da Rich sai a hankali. Ya ɗauki fushi dashi babu gaira babu sabar. Shi kuma sai hakan yay masa zafi ya tattarashi ya watsar. Ko game da harkar asibitin ya daina tuntuɓarsa da komai. Idan abu yake buƙata zaisa Solomon ne kawai yayi masa. Kai a yau ma gaba ɗaya baisa Richard ɗin cikin idanunsa ba har yanzun da suke shirin shiga da Nu'aymah ɗakin da za'ayi aikin.
         Baya buƙatar haɗama kansa damuwa da yawa. Shiyyasa ya ɗauki lamarin Rich ya ajiyesa gefe. Dan shi dai abinda ya sani bazai taɓa komawa abinda Richard ɗin ke buƙataba dan ALLAH ya nuna masa ƙyaƙyƙyawar hanya a yanzu mai cike da ɗumbin haske. Ai ko papa dake matsayin mahaifinsa bai isa sashi komawa kafiri ba balle Richard duk da kuwa yana sonsa har cikin ranshi.

        Sai da ya kammala shiryawa tsaf cikin kayan da zasuyi aikin. Ya gabatar da salla raka'a biyu sannan ya fito ya ƙarasa kimtsawa. Kasa shiga yay ɗakin da Aymah take domin fiddota zuwa ɗakin theatre ɗin. 
         Sai su Dr Sophia suka fiddota yana tsaye a ƙofar ɗakin. Cike da rauni ya bita da kallo samɓal akan gadon da aka turota tamkar gawa. Dan sun mata wata allura ne tun awa biyu da suka wuce. Wannan allura kuwa itace wasu da yawa masu irin matsalarta daga an musu ita suka tafi doguwar sumarnan shikenan har abadan. Ko an kammala aikin basa farfaɗowa. Wasu kuma koda sun farfaɗo sukan kasance komai sun manta na rayuwarsu ta baya. Sai an sake koya musu komai tamkar jinjiraye. Wasu kuma akan dace su tashi cikin rahamar UBANGIJI. 
       Wannan shine fatan su Yoohan akan Nu'aymah. Har aka shigar da ita hankalinsa yayi nisan kiwo wajen tafiya a dogon tunani. Sai da Dr Liam Yazo ya kama hannunsa ne ya kawo nannauyan numfashi. Lumshe idanunsa yayi ya buɗe a hankali akan ɗakin, Dole ne ya dawo da jarumtarsa jikinsa inhar yana son samun nutsuwa akan aikin nan duk da bashi kaɗaine zai gudanarba.
      Ya cija lip ɗinsa na ƙasa. Cike da ƙarfin hali da ƙarfafa kai ya nufi ɗakin zuciyarsa na wani irin bugu dai-dai da takunsa.
     “ALLAH ya bada nasara”.
Yaji an faɗa a bayansa. Cak ya tsaya tare da lumahe idanunsa ya buɗesu kafin ya juyo dan yasan Richard ne. Kallonsa yay kusan na sakon biyar cike da rauni. Sai kuma ya tako inda yake ya zo ya rungumesa idanunsa cike da ƙwalla.
      Bayansa Rich ya shafa cike da kulawa. “Zakayi nasara X-man, Please ka yarda da kanka”. 
     Ɗagowa Yoohan yayi suna kallon juna. Rich ya jinjina masa kai yana murmushi. “Ka yarda da ni, inaji a raina matarka zata tashi da yarda ALLAH, kodan taimakon mutane da yawa da kayi a rayuwarka a dalilin wannan aikin. Kaima ALLAH zai baka farin ciki akan matarka yau”.
      Yoohan yaji daɗin maganar Richard, dan haka ya sake rungumesa yana faɗin, “Thanks you Rich, I proud of you”.
      Sake shafa bayansa Richard yayi shima yana murmushi, dan har cikin ransa yana ƙaunar Yoohan, ba kuma zai iya dogon fushi da shiba komi ya zama, kai koda kuwa criminal ne shi zai iya cigaba da sonsa da taimakonsa. Yasan wanene Yoohan tun ƙuruciya. Ya tabbatar kuma bazaiyi abu kansa tsaye ba sai da dalili. shiyyasa yaga ya dace ya ajiye fushin da yake yi da shi ya bashi ƙwarin gwiwa akan abinda ya kawosu har komai ya dai-daita. Ya tabbatar zai masa bayanin dalilinsa na komawa mai salla. Wannan shine dalilin dawowarsa. amma da har masauki ya canja tun a daren jiya. Proud of you too”. Ya faɗa shima sunama juna murmushi.

       Koda Yoohan yazo shiga ɗakinma sai da yayi addu'a sannan ya shiga. Duk Doctors ɗin da zasu gudanar da aikin sun hallara, da alama ma shine kawai bai shigoba. Handglove ya cira ya sakama hannunsa. Ya zari Norse mask ma ya saka, duk abinda yakeyi idanunsa na akan ƙyaƙyƙyawar fuskar Aymah ne. Tayi wani irin ƙyawu fiye da wanda ya santa dashi. Fuskarta tayi fayau ɗan bakin tsiwarnan yana a tsuke. Ƙoƙarin maida ƙwallar data cika masa idanu yayi yana Murmushin tuno tsiwa-tsiwar data ringa masa tun daga haɗuwarsu har zuwa rayuwar aurensu ta ƴan kwanaki. Bai taɓa jin haushiba dan tana masa tsiwa. Hasalima wani lokacin yana takalarta ne dan kawai tayi masan. Saboda tsiwarta dake burgesa ko son ganinta shiru-shiru bayayi sam. Ya ƙarasa gaban gadon ya durƙusa a saitin fuskarta. Hannunta ya kamo cikin nashi ya riƙe, ɗayan kuma ya aza bisa kucinta na dama. Ya kafeta da kallo idanunsa na sake bayyana jan damuwa. Baice komaiba har tsahon mintuna biyu kafin ya miƙe yana haɗiyar zuciya da murmushin da baisan dalilinsaba shima. 

          Tunda suka fara aikin kuma sai jarumta ta baibaye Yoohan. Duk wani rauninsa da fargaba suka gudu. Ya maida hankali sosai akan abinda sukeyi da yaƙini da fatan samun nasara. Ko sau ɗaya baiyi saken addu'a ta ƙuɓucema zuciyarsa da harshensaba. Ambaton ALLAH yake tayi gwargwadon abinda ALLAH ya bashi ikon sani.
       Sun shafe tsahon awanni a cikin ɗakin. Solomon da Richard na zaune a waje idanunsa nakan ƙwan lantarkin dake a waje. Fatansu kawai suga ja ya koma green. Sai dai tun suna saran hakan a kusa har suka fara sarewa. Dan ba ƙaramin daɗewa su Yoohan sukai ba basu fito ba..

(Ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa😭🙏🏻).

★★★★

        Kamar yanda su Rich ke cike da fargaba acan Austria, anan gida Nigeria mas baba malam cike suke da fargaban. Sai dai sun miƙa lamuransu ga UBANGIJI akan koda rasa Nu'aymah sukayi haka ALLAH ya ƙaddara. Kuma sun tabbatar hakan shine mafi alkairi a gareta. Sai dai fatan ALLAH ya basu haƙurin hakan.
       Idan kuma ALLAH ya ƙara ƙaddara mata cigaba da wata rayuwar a gaba suna fatan nasara akan wannan aiki. ALLAH kuma ya hana samuwar loosing memory a gareta darajar Al-qur'ani izifi sittin dake haddace a cikin kanta da ƙirjinta.
  
         Duk bayan wasu awa guda baba malam kan kira wayar Yoohan yaji ko sun fito. sai dai ba'a ɗagawa. Hakan ke sakashi fahimtar basu fito ɗinba kenan. Ko yace ya haƙura bazai sake kira ba har sai Yoohan ya kirashi sai ya kasa haƙurin bayan shuɗewar lokaci sai ya ɗauka wayar ya sake kira ɗin. Tunfa yana saka ran ganin kiran Yoohan a kusa-kusa har lokaci mai tsayi ya shuɗe. Yana son shiga gida amma ya kasa dan bayason zuwa yaga halin da Umm take a ciki itama. Yasan suna tsananin son Nu'aymah, da wannan damarma maƙiyansu keyin amfani wajen azabtar da su, saboda sun gama fahimtar itace tarkonsu. Sai dai hakan bashi ke nufin bazasu iya haƙuri ba idan ALLAH ya amsheta. Dan dama ai shine ya basu batare da yayi shawara da su ba.

****
       A tare Richard da Solomon suka miƙe tsaye ganin jar wuta ta mutu blue ta kawo. Suka kafe ƙwayeyen uku da ido cike da tashin hankali. Rich likitane, yasan mi blue ɗin wuta ke nufi saɓanin green da sukai fatan gani. Shi kansa Solomon kasancewarsa tare da Yoohan a koda yaushe yasan ma'anar hakan. Cike da rauni suka kalli juna sai dai babu wanda ya iya furta komai.
      A hankali ƙofar ta zuge, wani irin mummunan faɗuwar gaba ta riski Solomon da Richard a lokaci ɗaya saboda ganin an fito da Yoohan a gadon da aka shiga da Aymah alamar dai suma yayi. Daɓar Richard ya koma ya zauna kansa na juya masa. dan fito da Yoohan a wannan halin kawai shine amsar dukan tambayoyinsu akan rasa Nu'aymah...............✍

*_Inason naja hankalin masu karatu anan. Wlhy kasancewar Nu'aymah matsayin jarumar littafin SARAN ƁOYE bashi ke tabbatar da bazata iya rasa ranta ba. Dan haka kar mu saduda akan wai dole labarin bazai tafi yanda ake buƙata ba sai tana raye. Wannan gurɓataccen tunani ne. Mutane nawane masu muhimmanci a rayuwarmu suka fita kuma gamu namu LABARAN basu daina tafiya bisa ƙaddararmu ba😭. Rayuwar Nu'aymah ba itace tabbacin fiddo da aynahin saƙon da SARAN ƁOYE keson isarwa ba. Dan haka Please karku saka rai, kar kuma ku sare, dan SARAN ƁOYE yazo muku ne da sabon salo da gasken gaske, dan haka mu daure wajen amsar salon da yazo mana da shi dan ALLAH😔😭🙏🏻🚶🏼‍♀️._*

ALLAH ka gafarta mana😭🙏🏻.      


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 56

.............A hankali Yoohan ya ringa buɗe idanunsa da ke ganin wanda ke zaune a gefensa dishi-dishi. Hannunsa ya ɗaga da ƙyar ya kamo na Richard wasu zafafa hawaye na silalo masa daga cikin idanu. Cikin rawar murya yace, “Da gaske ta na rasata ko Rich?”.
        Ƙasa Richard yay da kansa shima hawaye na ciko masa idanunsa. Ya zare hannunsa da ga cikin na Yoohan zai miƙe. Saurin riƙosa Yoohan yay yana girgiza masa kai. “Please Richard faɗamin gaskiya”.
      Kai Rich ya girgiza masa. “Basu ce mana komai ba har yanzun Yoohan. Tun da aka kawoka nan suka sake komawa ɗakin har yanzu basu fitoba kuma”.
        Da sauri Yoohan ya yunƙura zai tashi. Sai dai ya dafe kansa da hannunsa saboda tsananin sara masan da yayi. Saurin riƙosa Rich yayi yana faɗin, “Please cool down.
      “Bazan iya ba Richard, Karka damu dani, ina bukatar ganinta”.
       Duk yanda Rich yaso Yoohan ya haƙura yaƙi sauratensa sam. Dole ya taimaka masa suka fito a ɗakin yana dafe da kansa. Sai dai dole a ƙofar ɗakin suka tsaya dan dokace bazaiyi knocking ba ba kuma zai shigar musu kai tsaye ba. Yadai danna wani ɗan abu dake a jikin Computer ɗin dake maƙale a bangon ɗakin. Bayan kamar mintuna biyar ƙofar ta zuge ya shige.
         Da ƙyar ya iya ringa ɗaga ƙafarsa ya shiga saboda tsabar fargaba. A tare duk Doctors ɗin suka juyo suna kallonsa, fuskokinsu ya dinga bi da kallo ƙirjinsa na bugawa da sauri-sauri. Yama gama yarda ya rasata kawai. Dan haka ya juya zai sake fita hawaye na gangaro masa a saman fuska. a hankali Dr Sophia Tace, “Dr Yoohan!”. Cak ya tsaya da ga yunƙurin fitar tasa. Sai dai ya kasa juyowa. Sai da yaja kusan mintuna biyu sannan ya juyo a hankali yana kallon fuskokinsu da a yanzu suke ɗauke da murmushi.
     Kafin ya nema ba'asi Dr Liam Yace, “Smiles”. Yay maganar da ɗora yatsunsa biyu a gefen bakinsa alamar Yoohan yayi murmushin. Da gaske kuwa sai ga murmushin ya suɓuce masa ga hawaye. Ya tako da hanzari inda aka saka Aymah cikin wata na'uwar glass.
      Su kansu yanda yayi ɗin sai da ya basu tausayi da dariya, ta cikin Computers ɗin ya tabbatar da gaske Nu'aymahn sa nada ranta. Sai dai tana a halin suma haryanzu. Zuciyarta dai tana harbawa. Ƙafafuntane kawai a waje zuwa gwiwa, sauran jikin duk yana a cikin glass ɗin. Ya koma wajen ƙafafun ya riƙesu duka cikin hannunsa ya sumbaci tafinsu sau kusan uku-uku. Ga hawayen daɗi yanzu na sakko masa.
      Kamashi Dr Liam yazo yayi ya miƙar. Ya rungumesa yana masa Congratulations, aiki yayi kyau, sai kuma fatan farfaɗowarts da addu'ar kartai loosing memory ɗinta. Suma sauran duk sun masa Congratulations shima yayi musu, sannan suka tattaro suka fito dan sai zuwa nanda awanni goma sha biyu za'a fiddota daga ɗakin a maidata wani inda nanma zata share wasu awanni goma sha biyu daga nan ake fatan farfaɗowarta gaba ɗaya kuma.

        Su Yoohan na fitowa Rich ya nufosu, rungume juna sukayi yana tambayar tana da rai ne? Saboda ganin farin ciki tattare da Yoohan. Fuskar Yoohan washe da irin dariyar da shi kansa Rich ɗin bai taɓa gani ba yake tabbatar masa aiki yayi ƙyau. A take farin cikinsu ya ƙaru har Solomon. Dan shima Yoohan ɗin rungumesa yay.
        Baba malam Yoohan ya fara kira ya sanarmawa. sai kuma Papa dake tare da Momy dan ya koma Nigeria yau da safe. A wayar dai kam ya nuna murnarsa. amma yana katsewa yaja wani shegen tsaki mai nuna tsantsar takaici. ba haka ya soba sam. Dan game da aikin nan da za'aima Aymah a mutuwar da sukai fatan zatayi harsun gama tsara komai game da aikinsu akan baba malam.
      Ransa a ɓace ya ɗauki waya ya kira Dr Mateo. Domin kuwa sunyi da shi lallai Nu'aymah bazata tashi ba. Dan zaiyi duk abinda zaiyi su kasheta tun a wajen aikin. Sai dai har wayar katse Dr Mateo bai ɗaga masa kira ba. Maida kiransa yay ga Solomon. Shi kuma a lokacin suna tare da Yoohan da Richard shiyyasa ya kasa ɗagawa dan yasan dalilin kiran papan tunda a gabansu Yoohan ya kira ya sanar masa anyi aiki kuma an dace.

      Ba ƙaramin sake haukacewa Papa yayi ba kuwa. Ya ringa zazzaga bala'i Momy na tayasa itama duk da ba komai ta sani game da shirin papa ɗinba. To amma itama wannan ranar itace fatanta tun a daren auren Yoohan da Aymah da papa ya sanar mata matsalar Aymah da aikin da Yoohan zai fita da ita bayan auren. Wanda yana ɗaya daga dalilan yin auren da gaggawa. Shine dalilin sakankancewarta tabar Aymah miƙe ƙafa a gidanta tana zuba iskancin data gadama. To yanzu kuwa inhar Aymah bata mutu a wajen aiki ba lallai game ɗin zai canja salo kenan. Dan babu wata mace a duniya data isa raɓar Yoohan inhar tana a raye tana numfashi. Shiyyasa ma ta ɗauki mataki a kansa tun shekaru da dama ta kashe masa mazantakar tasa. Wannan yana ɗaya daga abinda ya sake assasa rashin damuwa da mata ga Yoohan, dan akan Nu'aymah ya farajin feeling makamancin hakan bayan shekarun farkon balaga da suka shuɗe masa lokacin yana farkon shiga University. Dan yanayinsa ya fara masa yanada ƙarfin sha'awa, amma ko a wancan lokacin yayi ƙoƙarin riƙe kansa dan shekararsa sha tara kacal, sai dai abin mamaki kafin suje level 2 sai yaji sam matanma basa burgesa. Kizo ki gama taɓararki a gabansa da nuna masa jiki ko a kwalar rigarsa bayajin komai ko a ɗanyatsan ƙafa kuwa. Rashin kula ta hanashi fahimtar akwai damuwa tattare da shi, sai ma sake ƙaimi da yayi akan harkar karatunsa fiye da farko. kuma shine dalilin saka masa rashin barci yake ɗaukar tsahon kwanaki, a dabarar bokan nata wannan galabaitar da zaiyi zai sakashi shan wani abu ya fita hayyacinsa. Ita kuma sai tai amfani da damar wajen kusanta kanta da shi har ta dinga biyama kanta buƙata.

     Sai dai kuma shi UBANGIJI alhakimu ne. dan hakan data aikata sai yazam kiyayewa ga Yoohan bai taɓa aikata zina ba. saboda tayi a sirin ne a dai-dai gaɓar da girmansa ya kai zai iya sha'awar kasancewa da macen.  Dalilin rashin barci kuma bai sakashi shan giya ko kayan maye ɗinba, abinda ma bata saniba ba aikinta bane ke hana Yoohan rashin barci. Wani kuma ƙullinne daban, ga wanda batai zatoba da ita kanta bata fahimtaba. Duk da kuwa tun yana yaro tasa akai masa wannan asirin.

To masu karatu sai muyi fatan samun lafiyar Aymah dan muga yaya wannan wasan zai kaya tsakanin madam Chioma, uwa ga Yoohana da   kuma Madam Nu'aymah mata ga Yoohana. Ga Papa ga baba malam, ga kuma Yoohan ga Abdallah dan tabbas idan mun tuna abinda ya faru ranar shopping  hakan na nufin akwai zazzafan wasa a ƙasa. Tsakanin Ayma da papa ma akwai game, hakama tsakanin Yoohan da family ɗin Aymah akwai game. Sai kuma Nasir da Abdallah. Tabb gyama-gyamanfa na da yawa. Kuma da alama samun lafiyar Nu'aymah ne kakar buga wasannin sai muje zuwa muga yanda za'a kafta wasannin😋😸😉🏃🏃.

________★★★★________

       Washe gari kamar haɗin baki su baba malam da papa a tare suka taho ƙasar Austria a jirgi ɗaya kuma. Suma basu fahimci hakaba sai da suka sauka kowanne yaga ɗan uwansa. Kallon kallo akaima juna tsakanin Papa da baba malam, Umm da madam Chioma. Sai dai baba malam ne ya fara kauda shirun da miƙama papa hannu. Itama Umm sai tai ɗan murmushi tana kallon madam Chioma da ke jinjina ƙyawu da kamalar mahaifiyar Nu'aymah. A ranata tace, ‘Ashe anan yarinyar nan ta ɗakko ƙyau kamar ƴar aljanu’.
      Itako Umm mamakinta yanda babu wani kamannin Yoohan da madam Chioma kamar yanda tai tunanin gani.
           Sun gaisa kowa yana ƙoƙarin danne abinda ke cikin ransa. Richard da Solomon dama sukazo ɗaukarsu, dan shi Yoohan sarai yasan a jirgi ɗaya zasu taho amma yaƙi sanarma kowannensu.
        Tun a wajen su Rich suka sakejin labari mai daɗi daya sake saka musu nutswa a zukata. Sai dai na papa da madam Chioma iya kan fuska ne kawai. Sai da aka fara kaisu masauki da Yoohan ya tanada musu, Rich yace su huta nanda awa uku zaizo suje asibitin dan ko sunje yanzu baza'a bari suga Aymah ba tunda ba'akai ga fiddota daga wancan ɗakin ba har yanzun. Duk da kodama sun fiddotan da wahala subar wani shiga inda take sai dai likitocin kawai.
       Su baba malam basu damuba. Dan mutanene masu tawakalli da kawaici. A ganinsu kuma tunda har suka iso ƙasar ai magana ta ƙare kuma.

        Papa dai kam bai zauna ba. Yana tabbatar da Rich sunbar hotel ɗin ta hanyar Solomon ya shirya shima ya fito zuwa inda sukai zasu haɗu da Dr Mateo, Sai da ya isa wajen shan coffee ɗin da kusan mintuna goma sannan Dr Mateo ya iso.
           Gaisuwar arziƙi Papa bai bari sunyi ba ya rufesa da jarabar miyasa yasan bazai iya aikinba ya amsa zai masa har kuma yama biyasa maƙudan kuɗaɗe?.
           Dr Mateo dake kallon papa a yatsine yace, “Na kula ƙwalwarka bata aiki da ƙyau Mr Goshpower. Wannan ƙasar tamufa ba irin africa ɗinku bane da kuka ɗauki ran mutum ba abakin komaiba. Sannan mutanenmu ba wawaye bane irinku da suke abu da ka babu wata ƙa'ida. Duk da aikine mai haɗarin gaske amma na gwada son ganin na aiwatar dan in faranta maka. Sai dai matsalar da aka samu bani kaɗai nayi aikinba. Kuma duk Doctors ɗin da mukayi aikinnan tare suna bala'i-bala'in ganin mutuncin yaronka Yoohan, dan yanada mutunci da karfi a wannan asibiti saboda yayi mana manyan ayyuka da ko gwamnatin ƙasarnan bazata manta da shi ba balle asibitin kansa. So Please kayi wani tunani akan kisan yarinyar ta wani hanyan amma ba wannan ba. Dan koni kaina yanda na fahimci Dr Yoohan nason yarinyar bazan iya kasheta ba dan ina girmama soyayya sosai”.
         A rikice papa yace, “Ban gane bazaka iya kasheta ba. Kana nufin kaci kuɗina a banza kenan?”.
       “A wofi ma kuwa Mr goshpower, dan na gwada maka aikin daka bani nasarace kawai ba'ayi ba, saboda yarinyar ƴar baiwa ce. Sannan ka yarda da shawarata kar kayi wani gangancin koda na saka wanine ya kasheta a cikin asibitin nan, asirinka zai tonu. Dan koshi ɗan naka bazai barka ka kuma zuƙar iska ba a duniya inhar ya fahimta. Ni kaina dasun fahimci nine naso ɓata musu aiki har Dr Yoohan ya tsorata ya suma da baka ganni anan gabanka ba. Abu na karshe dazan sanar maka kuma shine zagaye take da securitys ta ko ina saboda girmamawa ga Dr Yoohan akan hidimarsa. Dan tunda kowa ya fahimci matarsace kaf Doctors ɗinmu sun sake ninka kulawarsu fiye data farko a gareta. na barka lafiya”. Ya kare maganar da wani kaɗa masa yatsunsa da kashe ido yana wani shegen murmushi.
       Tamkar wani soko haka Papa yabi Dr Mateo da kallo harya tare taxi ya shige. Jiyay kansa ya masa wani irin shegen nauyi, ya ɗauki butar da aka zubo musu coffe a ciki ya tsiyaya a karamin kofi. Duk da turirin da yakeyi bai damuba haka ya kafa kansa ya hau kwankwaɗa yana ƙona masa baki da maƙogwaro. Wato lallai ya fahimci baturen likitan nan ɗan iska ya maidashi kawai. Duk yasan da wannan dokar amma ya amsar masa kuɗi ya kuma amsa masa zaiyi aikin?. Ɗaga kofin yayi kamar zai rotsa da ƙasa sai kuma ya fasa ya ajiye ya miƙe a fusace ya baro shagon shan coffe ɗin yana kumbura kamar wani kububuwa😁😜.

      Nannauyan numfashi Richard dake kujerar bayan su papa ya sauke, tsabar kaɗuwa da tattaunawar papa da Dr Mateo ta sakashi cire p-cap ɗin kansa ya hau fifita da ita. Miƙewa yay da ga shagon coffe ɗin shima ya fice zuciyarsa na bala'in masa kai kawo.

******

          A ɓangaren su Baba malam kuwa awanni uku na cika sai ga Solomon ya dawo ɗaukarsu. Ya iske papa baya nan dan haka ya tafi da su su uku tunda yasan inda papan ya tafi. Sun isa asibitin dai-dai da fitowar Yoohan daga wani aiki da sukai shi da wasu likitoci. Dan dama akwai yarjejiniya tsakaninsa da asibitin akan zasu taimakesa aima Nu'aymah aiki, shima kuma zai taimakesu wajen duba musu nasu patients ɗin da sukasan yanada basira a kai. Ya kuma amince zaiyi, dan haka bayan an kamalama Aymah shima ya maida hankali wajen cika musu nasu alƙawarin duk da kuwa duk abinda yakeyi hankalinsa na a kanta.
         Cike da murmushi ya tarbi su baba malam. Kamar yanda suma suke nasu ƙayataccen murmushi. Madam Chioma kam kallonsa take kamar ta hadiyesa. Ta buɗe masa hannayenta alamar yazo gareta. Daga shi sai ita ma baya iyawa balle yanzu akwai baba malam a wajen. Kafaɗarsa ya maƙe mata tare da cigaba da takowa zuwa gaban baba malam. Shi ya fara gaidawa da girmamawa. Baba malam ya riƙo hannunsa yana murmushi sukai musabaha. Daga haka ya gaida Umm itama data amsa masa cike da kunyar surukuta. Shima dai ya kasa dubanta da ƙyau dan tana masa tsananin kwarjini ainun.
       Juyawa yay ga Madam Chioma data cika tayi fam da takaici da kishi. Bai damu da yanayin nata ba ya kamo hannunta ya sumbata yana murmushi. Danne zuciyarta tai da ƙyar ta nuna masa kulawa da tambayarsa yaya daughter ɗinta. Cike da kulawa a gareta da nuna jin daɗi ya sanarmata suna fatan nasara ga farfadowar dota ɗin tata.
      Daga haka yay musu jagora zuwa zuwa ɗakin da aka maida Nu'ayma mintuna talatin da suka shuɗe. Basu shiga har inda takeba. Dan hakan dokar take ba'ason motsin komai a inda take. Hatta da takalmansu duk sai da suka cire suka saka na roba duk da kuwa ba ainahin ɗakin zasu shiga ba. Ta cikin glass ɗin daya raba tsakanin inda suke da dakin da Ayma ke a ciki suka lekata. Dolene mai imani ya ganta yaji tsananin tausayinta, dan bata da maraba da gawa a kwance, na'urorine kawai ke aiki a jikinta ta ko ina. Sun mata addu'oin samun lafiya a zukatansu suka baro wajen Umm na share hawaye. Baba malam ma dai dauriyace kawai da jarumta.
        Office ɗin da Yoohan yake suka koma, anan yay musu bayani sosai akan nasarorin da aka samu a wajen aikin da wanda suke fatan samu idan ta farka. Sunji daɗi sosai, sunata kuma godema ALLAH. Madam Chioma dai murmushi kawai take wanda yafi kuka ciwo. A haka papa yazo ya samesu shima.
       Shima dai sai da aka rakasa yaga Nu'ayma dan ya dage cike da nuna damuwa da alhini kamar har cikin zuciyarsa ne.
          Lokacin da zasu koma masauki tare suka tafi da Yoohan dan zaije yay hutun awanni biyar kafin ya sake dawowa asibitin.

★★★★★

           Ƙarfe takwas da rabi na dare agogon ƙasar su Yoohan suke saka ran farfaɗowar Nu'aymah. Amma sai bai sanarma su baba malam ba dan basu san mizai biyo baya ba. Yafi son sai sunga komai yanda suke fata kafin yay musu albishir. Daga shi sai Rich nema sukazo asibitin, Solomon ma sun barshi a masauki. Yauma sai da yay salla raka'a biyu da addu'ar neman nasara kafin su shiga ɗakin da Nu'aymahn take. Duk da ransa cike yake da tsoro haka yaketa ƙarfafa kansa suna ƙoƙarin janye duk wata na'ura dake tare da jikin ta.. Sai da suka cire komai aka barta da na'urar numfashi kawai kafin Yoohan ɗin da kansa yay mata wata allura. Daga haka suka koma gefe suka zubama sarautar UBANGIJI idanu kuma.
         Mintuna sha biyar da suke jira ta cika Aymah bata motsa ba. Suka sake ƙara biyar suma suka shuɗe shiru. Sha biyar suka ƙara nanma babu labari. Dukansu babu wanda tsoro da fargaba bata riskesa ba, musamman Yoohan da ruɗaninsa ke neman fitowa fili. Dr Sophia ta bada shawaran ko zasu sake mata allurarne dan dama ta fahimci jininta nada matuƙar ƙarfi. Duk sunyi na'am da hakan tunda sunsan ba illa bane. A ƙa'ida ma za'a iya yimata sau uku. Daga hakane idan bata farfaɗo ba sun tabbatar mutum ya mutu kenan.
         A yanzun kam Yoohan bashi yay alluranba dan bazaima iyaba. Koda suke maganarsu zaune kawai yake yana kallonsu bai saka bakinsa ba. Hakama har akai allurar bai motsa daga inda yake ba. Yanzu dai mintuna talatin suka bata na jira.
      Cikin amincin UBANGIJI minti ashirin da bakwai na cika tai wata irin mahaukaciyar zabura. Sai jikinta ya kama rawa har gadon kansa na jijjiga. Gaba ɗayansu suka rufu a kanta kowa na nuna farin cikinsa. dan kuwa dai ta wuce mataki na biyu kenan. Wanda kuma yafi kowanne haɗari dama a aikin. Matakin ƙarshe shine abubuwan dake a ƙwaƙwalwar ta zasu dawo ko zatayi loosing ɗinsu. Kasancewar ta yarinya ƙarama basu cika damuwa da wannan ba dan a ganinsu tanada sauran isashen lokacin da zata koya duk abinda ta rasa. Sai dai ga Yoohan sam baya fatan haka. Burinsa komanta ya kasance tare da ita musamman karatunta na addini koda kuwa zata manta da sauran abubuwan ciki harda shi kansa.
       Dukkanin taimakon daya dace shi suke bata cike da ƙwarewar aiki. A awa guda suka dai-daita komai Alhmdllh. Allurar barci aka sake mata da bama Nurse ɗin da zasu goge mata jiki dama. Amma sai Yoohan ɗinma yace su barshi. da kansa ya gogemata jikin ya canja mata kaya sannan aka maidata ɗakin da zatai jiyya.
          Farin cikine sosai tattare da Yoohan. Dan yanaga komai ya dai-daita tana sauke numfashin barci da ajiyar zuciya a kai akai sai ya fito ya koma masauki dan ya sanarma su baba malam wannan daddaɗan labari.

        Aiko basu kaɗaiba hatta da su hajjo ƴan Nigeria dake can cike da fargaba da alhini duk sun kaure da farin ciki da murna tamkar ance Aymah ta miƙe a kan ƙafafunta. Hajjo ta kuma sakawa akai abinci mai yawa akai sadaka da shi. suka kuma shirya ita da kaf ƴan gidan sukaje asibiti sukai ziyarar marasa lafiya da bama masu buƙatar taimakon tallafi.
      Suma anan daga su baba malam har Yoohan sunta nafilfiline suna nunama UBANGIJI godiyarsu akan wannan ni'ima da yay musu. Washe gari kuma suka tashi da azumi a bakinsu na sake jaddada godiyarsu ga ALLAH. Sun kuma je sun duba ta suma hankalinsu ya sake kwanciya da samun nutsuwa fiye da farko.
     Shi kansa Yoohan yau yini yay yana barci cike da kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya tare da daddaɗan mafarki.
          Su papa dai baƙin ciki fal ransu. Dan a ranarma sukace zasu koma tunda ta farfaɗo. Daga Yoohan harsu baba malam basu kawo komai a ransu ba game da hakan. Sai ma godiya da sukai musu tare da rakkiya har airport. Shima Yoohan ɗin a ganinsa zaifi samun sakewa da su baba malam ɗin a yanzu fiye da su papa na tare da su.

       Aiko hakance ta kasance. Dan suna dawowa daga rakkiyarsu Umm ta koma ɗaki, shiko shi da baba malam wani wajen hutawa suka zauna a cikin hotel ɗin suka shiga hira mai daɗi tamkar ɗa da uba. Dan idan ka gansu bazaka taɓa ɗaukar ba shine ya haifesaba. Yoohan yana bala'in sakin jiki da baba malam fiyema da papa da ke amsa sunan mahaifi a garesa.
         A haka Rich daya tashi a barci yazo ya samesu shima. Da farko ya zaunane kawai dan yanajin zafin baba malam da kuma son fahimtar ta wace hanya suka dilmiyar masa da ɗan uwa ya fara salla. Sai dai hirar batai nisaba Rich ya farajin nutsuwa da baba malam ɗin. Harma yake jin hirar na masa daɗi da basa wani irin farin ciki.
       Baba Malam kam tsaf ya fahimci Rich najin zafinsu tun isowarsu ƙasar. Sai dai baisan akan wane daliliba. Amma kasancewarsa mutum mai zurfin ilimi da hikima sai ya dinga mu'amulantar Richard ɗin cike da kulawa. Har i zuwa yanzun da suke zaune a tare. 
       Yoohan duk yana lura da yanda Rich ya fara sakin jiki da baba malam saɓanin farkon zamansa a wajen. Murmushi kawai yakeyi a cikin ransa, yana mai roƙon UBANGIJI ALLAH yasa abokin nasa nada rabon shiriya shima kamar yanda ALLAH ya cidashi ya tsamosa da ga DUHU zuwa HASKE.
        Sunja lokaci mai tsayi suna hirar kafin su koma ɗakunansu. Shi dai Yoohan shiri yay ya tafi asibitin dan akwai abinda zaiyi. Kuma lokacin gogema Nu'aymah jikima yayi

____________★

            Alhmdllh, yau kwanaki biyar kenan da yima Nu'aymah aiki. Sai dai zamuce har yanzun ba sanin inda kanta yake tai ba. Dan kullum a cikin barci take. A bisa ilimin likitanci ake bata taci ake bata ta sha ta allurai da sauransu.
       A komai Yoohan ne ke tsaye a kanta. Dan duk abinda ya dace shine kema matarsa da a kallo ɗaya zaka fahimci ɗunbin tausayinta da tsantsar kulawar da yake bata akan fuskarsa. A yau ne ake shirin barinta ta dawo hayyacinta gaba ɗaya. Dan haka tun sha biyu na daren jiya babu wata allura da aka ƙara mata. Duk wata na'ura dake tare da jikinta kuma an janyeta.............✍

*_Hummm. Ashe haka kuke da tsoron mutuwa dama? Tofa inhar a ranku kunajin jaruman littafi bai kamata su mutuba sai ku daina ƙalubalantar marubuta nasaka rayuwar littafii daya wuce kima. Idan kuma har kun shirya karɓar littafi dai-dai da zahirin rayuwa dolene ku shirya amsar ƙaddarar cikinsa itama dai-dai da zahirin rayuwa. Mutuwa dolece akan kowanne bawa. Dan haka jiya na tunatar da ku muhimmancinta dan shima littafin bazai zama kullum farinciki ba. inhar mutuwar jarumar littafi zata iya ɗaga hankalinku irin haka harda masu iya buɗe baki su zageni bayan sunama karantawa ne basu biyaba😂, to lallai ku ji tsoron zuwan mala'ikan mutuwa mai ɗaukar rai a zahiri ranar da babu tsumi babu dabara, sannan kuji tsoron cin haƙƙin abinda koda ɗaukarsa kuke ba komaiba. Muguji son ziciya dan ƙarshe ɓacin zuciya take zamarwa mai ita. Kai da karantawa kake kaji zafi a ranka dan an rubuta saɓanin abinda bashi kaso ganiba harka furta ALLAH ya isa. Mu kuma da muka ɓata awanni muna rubutawa kika fitarmana, ke kuma kika gani kika karanta da yaƙinin kin samu bati, bayan mun haɗaku da Girman ALLAH mi kake tunani koda bamuce da ku komai ba?. Kunbi kun ruɗar da kanku koma fahimtar bayanin nawa bayi kukaiba😸, nace karku sare, kar kuma ku saka rai, amma shine harda masu rusar kuka😂, da masu kirana suna kuka🤣, kai jama'a gaskiya jiya kun sani dariya kun kuma sakani hawaye saboda tausayin kammu, saboda tunawa da muma mutuwar nan tana tafe a garemu duk daren daɗewa, sannan wasu a cikinmu ma an zare mana mutane masu muhimmanci a rayuwarmu a yau babusu tare damu😭😭. ALLAH ka gafarta mana baki ɗaya. Wannan itace makarantar JIKI MAGAYI bisa gaskiyar zancen Nu'aymah_*😭🙏🏻.


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 57

________________

       *Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna *

https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg

*(YouTube link)👆🏾*

*This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing to you my latest films, And musical videos*


*NafisaKabdullahi* *Sabuwar ficacciyar jaruma ce data shahara wajen fina finai da kuma wakoki na siyasa, Masarautu da sauran su* 

*Ina masoya makaranta littafan zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora..*

*Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye.*

*DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba...*

*Akwai Facebook page dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi*

*Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: *

*08071172003*

*kada ku mance ko minene daya danganci wakokin al’adun hausa, Da ire-iren fina-finan mu na hausa, Nafisa zata dinga kawo muku shi a wannan sabuwar channel din nata, Saboda haka MASOYA a temaka aje ayi mata subscribing a kuma dinga kallan abubuwan data dora.*.


__________

No. 57

...........Ƙarfe goma dai-dai na safiyar wannan rana agogon ƙasar Nu'aymah ta farka a gaban Dr Yoohan da sauran likitocin da sukai mata aiki. Sai baba malam da Umm. Dan ana buƙatar tabbatar da ingancin lafiyar ƙwaƙwalwar ta da kuma tabbatar da idan bata manta komai ba.
         Gaba ɗayansu idanunsu cak akan yatsun ƙafarta dake motsawa. Har zuwa hannayenta biyu da suma ke motsin. A hankali gashin idanunta suma ke motsawa, sai numfashin ta dake sauya salon fita daga na barci zuwa na wadda take a farke. 
      Da farko bata ia ganin komai, ta cigaba da motsa idanun a sannu-sannu har ta fara ganinsu dishi-dishi. Idanun ta maida ta rufe tana matse fuska, babu dai wanda ya motsa a cikinsu harta sake buɗewar a hankali. Akan Dr Sophia ta fara saukesu, tayi kusan sakan goma tana kallonta kafin ta janye zuwa ga na kusa da ita. Shima dai tai masa kallo mai tsaho ta sake maidawa kan ɗayan likitan. Idanun ta lumshe ta sake buɗewa akan Dr Yoohan. Yanda take kallonsa haka shima yake kallonta cike da fargaba. Tafi tsayin mintu uku tana masa kallon ƙurullah da duk ya basu tsoro, dan tamkar tana hasashen wanene?. Ɗauke kanta tai a gareshi ta maida kan Baba malam dake a kusa da shi, sai kuma ta kalli Umm. Haka ta ringa raba kallo a tsakaninsu na tsahon mintuna.
      Gaba ɗaya jikinsu duk yayi sanyi har likitancin, dan da alama ta manta komai. A bazata sukaji ta fara magana da ƙyar,
      “Yah Yoohan da gaske su Abbana ne?”.
       Maganar da ƙyar take fita. Amma duk sunjita duk da a hankali ne. Rikicewa sukai da farin ciki. Yoohan yay azamar zuwa gabanta ya riƙe hannunta data dafe kai da shi saboda yunƙurin tashi zaune da taso yi.
       “Please relax koma ki kwanta”. 
Cikin rawar murya hawaye na zirara mata a idanu tace, “Kaina namin ciwo kamar zai rabe biyu”.
      “Okay, kiyi shiru ki daina magana”.
Ya sake faɗa yana maidata ya kwantar. Kunyar su baba malam da yakeji ne ya hanashi rungumeta dan farin cikin yanda komai yazo yanda sukai fata. Ya ja baya kaɗan dan bama su Umm damar ganinta da ƙyau. Idanunta a lumshe kuwa ta miƙoma su Baba malam hannu alamar suje gareta.
      Kallon Yoohan baba malam yay. Ya jinjina masa kai yana murmushi da sake matsawa baya yanda wajen zai ishesu. Ya kuma jawo musu kujeru su zauna.

      Tabbas Yoohan da su baba malam suna cikin ɗunbin farin ciki, hatta da Richard ma farin cikin da yaga ɗan uwansa a ciki shima sai yake tayasa. Duk da dai a yanzu shima jin wani girma da mutuncin baba malam ya keyi a ransa. Mutumin yana da wani kwarjini na musamman da iya mu'amula wa mutane.
      Hatta da Solomon duk da munafunci nacin ransa sai da ya nuna farin cikinsa. Kafin ya zagaye can baya yay kiran papa ya sanar masa halin da ake ciki. Aiko dai ba ƙaramin baƙin ciki papa ya shigaba. saboda karma Yoohan yay kiransa ya sanar masa farkawar Aymah sai ya sakashi a black list. Sai dai abinda ma bai saniba Yoohan sam bai nemesa ba a lokacin. Dan sunata shigi da fici akan Aymah daketa complain ɗin ciwon kai. Ko idanunta data ɗan buɗe da farko yanzu bata iya buɗesu. Tsoron kar matsalar ta shafi idanunta ya sakasu sake mata allurar barci na awa huɗu. Sunason suga ko barcin bai gama wadatar kanta bane jijiyoyin basu gama dai-daita ba.
         Da wannan damar suma su baba malam sukai amfani wajen komawa masaukinsu suka duƙufa addu'a a gareta a cikin tsaftataccen ruwan zam-zam da dama sunzo da abunsu. 
     
       A wanni huɗuu na cika Aymah ta sake farkawa. Cikin amincin UBANGIJI kuma an dace dan kuwa yanzu tana buɗe idanun, ciwon kan ma tace can ƙasa yake mata. Kowa yayi farin ciki da hakan. Yoohan ya bata ruwan zam-zam da su baba malam sukai mata addu'a aciki ta sha. shine abu na farko data fara sha. Ya kuma ɗiga mata a cikin ido kamar yanda baba malam ɗin ya sanar masa.
     Babu mai shiga inda take sai shi, saboda ba'a son mata hayaniya. Duk da tanata damunsa da ƙara son ganin su baba malam yana lallaɓata.

      A daren wannan ranar su Hajjo suka iso. Hajjo, Abban Adawiya, Abban Abdallah, Abba Musbahu. Sai Addah data takura akan sai tazo taga jikin Aymah ɗin. Duk da kuwa ance baza'azo da matan gidan da yara ko ɗaya ba. Su yi haƙuri har Aymah ta dawo tunda ance jikin Alhmdllh. Amma Addah ta nace, da kantama ta biyama kanta ƙuɗin jirgi. Dan ita dai a ganinta bai kamata a yanda suke da Umm ba ace batazo ta duba NU'AYMAH ba. Shaƙuwar tasu hajjo ta kalla tace a barta taje tunda tace zata biyama kanta. dan bazai yuwu a biya mataba sauran matan suga anyi son kai.

      Suma sunji daɗin ganin yanda jikin Aymahn yayi ƙyau sosai. Dan da taimakon Yoohan suka samu suka shiga wajenta. Alhmdllh kuma duk ta ganesu. Harma hajjo ta tsokaneta aka cuna mata baki. Dariya duk sukayi, Yoohan ya girgiza kai yana wani ɗan munafukin murmushi, a ransa yana faɗin, ‘Ta dawo duniya yanzu zata addabi kowa. Barema ni data gama rainawa’.
      Kamarko Aymah tasan mi yake rayawa. Dan tana can tana masa kallon ƙasan ido ganin yanda ya rame mata a idanu. Sai dai batai tunanin komai a ranta ba ta maida hankalinta gasu hajjo. 

      Bayan wucewar su hajjo Richard ya kawo abincin da zataci lokacin shan maganinta yayi da barcinta. Dan a yau ne zata fara cin abu mai nauyi bayan kullum da ake bata iya mai ruwa-ruwa kawai dan ba'a son ta tauna abu saboda jijiyiyin kanta dake tare dana haƙori.
       Cikin jin daɗi Yoohan ya amsa yana faɗin, “Thanks you Rich”. Ɗan hararsa Richard yayi da faɗin, “Dama akwai godiya ne tsakanina da kai Mr X”. Murmushi kawai Yoohan yayi amma baice komaiba. Shima Richard ɗin sai ya murmusa yana binsa da kallo. Sam baya iya dogon fushi da Yoohan. Ƙauna yake masa ta gaskiya kuma ta haƙiƙa har cikin ɓargonsa. Yanajinsa a jinin jikinsa tamkar ƴan uwansa da suka fito ciki ɗaya. Kuma shi harga ALLAH bai taɓa jin zafinsa akan auran Nu'aymah da yayiba duk da kuwa ta kasance Bahaushiya kuma musulma. Sai dai salla da Yoohan ya farayi yanzu yana matuƙar damun ransa. ya rasa wane kalar tunani zaiyi akan wannan matsalar, wazai tunkara su tattauna domin haɗa hannu wajen dawo da Yoohan cikin hankalinsa?. Da yayi yunƙurin sanarma wani sai yaji rauni da fargaba ta kamashi. dan haka ya barma ransa ko sauran abokansu su Joseph ya kasa faɗamawa....

           Yoohan dai tuni ya fice a office ɗin abunsa ya bar Rich da faɗawa dogon tunani. A waje yaga Solomon tsaye. Ya ɗan kafesa da kallon mamaki dan ganin yanda Solomon ɗin yay fakare kamar wanda ya tsorata da ganinsa. Bai dai ce da shi komaiba yay wucewarsa.
      Nannauyan numfashi Solo ya sauke yana rumtse idanunsa da wayarsa dake cikin hannu. Yau shikam ya shiga uku, yana fatan Yoohan baiji wayarnan da yakeyi da papa ba. Gaba ɗaya sai wani tsoro na tashin hankali ya kuma baibayesa. Barin asibitin yayi jikinsa na tsuma. dama zuwansa kenan shi da Richard.
          Yoohan da haka kawai yanayin Solomon yaso ɗarsa masa zargi a zuciya ya ƙarasa ɗakin da Aymah take yana wasiwasi. Kwance take akan gadon jiyyarta idanunta a lumshe. Har yanzu bawai jikin nata yayi ƙarfi baneba. Dan ko magana ma da ƙa'ida takeyinta. Kai duk ma sauran abubuwa komai zatayi da ƙa'idarsa saboda ƙwalwarta ana buƙatar ta samu isashen hutun da komai zai gama dai-daita. Dan yanzu dai su Yoohan sun tabbatar da komai Alhmdllh, sai dai zata ringa yawaita ciwon kai kafin wani tsahon lokaci da suma basusan adadiba. Sannan idanunta sun raunana zatake amfani da glass shima kafin zuwa wani lokaci. Bawai bata gani bane, tana ganin komai Alhmdllh, sai dai ba a yanda ya kamataba. Dan idan abu yayi mata nisa tana ganinsa bibbiyu ko dishi-dishi. Sannan sun tabbatar da zata rage yawan hayaniya yanzun.
        Ƙamshinsa da taji ya yawaita a ɗakinne ya sakata buɗe idanunta a hankali. A kansa ta zubasu, sai dai batai masa kallon sakan uku ba ta janye. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke. ya matsa gaban gadon sosai ya zauna, kama hannunta yay cikin nashi. Cikin magana ƙasa-ƙasa da ko kana a ɗakin bajinsu zakai ba yace,
        “How are you feeling?”.
   Hannunta da ke a cikin nasa taɗan motsa, idanunta a lumshe, cikin magana a hankali fiyema da tasa tace, “Alhamdulillah”.
         “Masha ALLAH”. ya faɗa da harshensa karyayye.
       Batare da yace mata komaiba ya kamata zai tayar. Buɗe idanun tayi sosai. A rashin sanin ita yake kallo suka faɗa a cikin nashi. Saurin kauda kanta tayi tana motsa baki kaɗan. Duk da ba magana taiba yasan tsiwarce ta motso, sai dai yanzu kam babu bakin yi yanda ya kamata. Filo ya saka mata ta jingina yanda zataji daɗi. Ya zauna a kusa da ƙafafunta dake a miƙe. Gaba ɗaya jitai ta gama takurewa a wajen. Ga ƙamshinsa yayi bala'in adabawa numfashinta. Shi dai da baisan tanayi ba, ya san dai tunda ta kasance jinin masoyinsa baba malam bazai taɓa gajiyawa wajen jinyarta ba tamkar yanda yasan iyayenta zasu kula da ita. takeaway ɗin ya buɗe yana fuskantarta. Duk da ya fahimci kallonsa takeyi sai bai nuna ya ganiba. Batare da ya kalleta ba yace, “Yau zaki fara cin abinci mai nauyi. Insha ALLAH yanda jikinki keyin ƙyau zamu samu sallama da wuri. Amma sai kin daure kin ringa cin abinci ko yaya ne. Dan yanzu zakiji ɗanɗanon sa sam baya miki wani daɗi. Sai a hankali ne ɗanɗanon harshenki zai warware”.
      Fuska kawai taɗan yamutsa. Dan harga ALLAH kam abincin ma ganinsa kawai da takeyi yanzu amai yake neman sakata, sai dai kuma itama tana buƙatar ganin an sallameta ta bar asibitin nan da duk take jinta a takure.
      Bai damu da rashin yin maganar tata ba. Ya ɗiba abincin a spoon ya nufi bakinta da shi. Har zata kauda kanta yay saurin faɗin, “No, Please!”. Daurewa tai ta buɗe bakin idanunta a rumtse. Ya zuba mata tausayinta na ƙara ratsasa. taja kusan minti biyu tana juya abincin a baki sannan ta haɗiyeshi da ƙyar. Sake ɗiba yayi ya bata. Nanma dai sai da ta ɓata lokaci. Da ƙyar ya samu taɗanci, sai dai sunja lokaci mai tsaho ana ƙaƙa nakayi, dan harda hawayenta shaɓe-shaɓe a fuska. Da ga ƙarshe dai ganin ta ɗanci ya haƙura ya barta. Tissue yasa ya goge mata bakinta da hawayen datayi. Yana ƙoƙarin tashi ta riƙo hannunsa. Kallonta yay kawai sai dai baice komaiba.
      A mamakinsa sai yaga ta ɗauki cokalin daya bata abincin ta ɗibo ta nufo bakinsa. ba ƙaramin harbawa zuciyar Yoohan yayiba. Duk da ba abincine daya cika damuwa da shi ba haka ya buɗe bakin kawai yana kallonta. Zuba masa tayi kuwa batare da ta yarda sun haɗa ido ba. Ta ƙara ɗebowa tana magana a hankali. “Ka rame da yawa. da alama kaima baka da lafiyar kuma bakacin abinci. Amma gashi ni kazo ka tsareni sai da naci. To kaima tsareka zanyi sai kaci”.
        Yanda tai maganarne a sakalce ya sakashi yin murmushi. ya fahinci kuma da iya gaskiyarta take faɗin abinda ke a ranta. Hannu ya kai saman fuskarta a hankali yana faɗin, “Thanks you”. Kallo ɗaya tai masa ta janye idanunta batare datace komaiba. Sai dai taji daɗin thanks you ɗin daya ce mata. Hannu tasa akan hannunsa dake saman fuskarsa ta janye, dan yanda yake mata a kumatu jitake tsigar jikinta na tashi. Murmushi ya kumayi yana cigaba da amsar abincin. itako taƙi yarda su haɗa idanu sam, sai danna masa abinci takeyi.
       A wannan yanayin Dr LiLiya shigo ya samesu. Da tsokana yake cewa, “Irin wannan soyayya haka bazasu bari a warke ba?”.
      Sosai Aymah ta waro idanu akan baturen likitan. Sai dai kuma batai magana ba. Ta ɗan harari Yoohan dake murmushi. Sai kuma ta ajiye spoon ɗin ta kwanta abunta da juya musu baya. Ƙaramar dariya Yoohan yayi har haƙoransa na bayyana sosai. Ƙasa-ƙasa ya cema Dr Liam “Kaga ka jamin an bar bani”.
       Dr Liam dariyar shima yayi yana haɗe hannaye waje guda alamar Sorry.
      Ita dai Aymah bata sake kulasuba. Da za'a bata magani ma ƙin yarda tayi ta kalli kowa a cikinsu. Tana sha kuwa ko mintuna goma cikakku batayi ba barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Sassanyar ajiyar zuciya Yoohan ya sauke. Ya kama hannunta data bashi abinci ya sumbata yana wani lumshe idanu. Daga haka suka fito suka bar mata ɗakin shi da Dr Liam

____________★★

            Yau kwanakin su Hajjo biyu da zuwa. gobe idan ALLAH ya kaimu kuma zasu koma harda su baba malam ma. Sunzo sun duba Aymah da jikinta keta ƙara warwarewa Alhmdllh. Sai dai batason cin abinci sai Yoohan yata lallashi da dabara. A hakanma bata yarda taci ita kaɗai. sai dai idan ya ɗeba spoon ɗaya ya bata itama sai ta ɗiba ta bashi. Ita a ganinta wayo takeyi dansu cinye tare ya rage mata aiki. shiko hakan ba ƙaramin shauƙi yake sakashi a ciki ba, da jinsa on top. Ta kai ko ruwan addu'arta ya bata tasha itama shima sai ta rage ta bashi ya sha. Dan harga ALLAH ramar da taga yayi kuma na damunta a cikin rai. Ta tabbatar koda rashin lafiya yayi to harda damuwar halin da take a ciki. Dan ta fahimci shi mutum ne mai tausayi sosai dama.

         Dr Yoohan da Dr Liam Sai Richard sun fito daga Ward ɗin dake gefen wanda Aymah take sai wayarsa tai ring. dakatawa yay domin ya amsa su kuma suka wuce. Papa ne, sun gaisa da maganar data shafesu ya maida wayar cikin aljihun farar rigarsa ta likitanci daya ɗora ya cigaba da tafiyarsa dansu Rich sun wuce. 
      Kamar da wasa sai yaji ana hausa ta lungun daya gitta. Duk da bajin hausar yake ba mu'amula da hausawa da yakeyi a yanzu tana ƙara sakashi fahimtar yaran hausa kaɗan-kaɗan. musamman zama da Nu'aymah duk da bawani jimawa sukai tareba. kawai dai shi mutum ne mai kaifin basira ɗaukar yare dama.
        Samun kansa yay da ɗan komawa da baya. Na daga ƙafa zan bisa nima na ɗakko muku rahoto xoxo da rano sukazo suka tsaidani da surutu🙄, wai su nan sunga wadda suka sani a ƙasar Austria, sunja mana rashin samun wannan rahoton. Dan ina gaisuwa da su ne hankalina nakan lungun da Yoohan ya shiga. Kafin mu gama sai gashi ya fito fuskarsa a tsuke. Kuma tamkar wanda yaga wani abun dayay matuƙar rikitashi ko ɗaure masa kai. Da kallo na bisa. batare dana tsaya munyi sallama da su Rano ba nai azamar binsa a baya. Suna ɗagamin hannuma ko saurarensu ban ƙaraba. Nai gaba ina faɗin, “Maƙalallu sun maƙalle a asibitin nan sun hanani ɗaukar rahoto”. Ina ɓullowa na hango Huguma da Mamu sun ɓullo suma. da alama tare suke dasu xoxo dinma dai. Washe baki suka fara irin su sunga wadda suka sani dinnan dai. saurin ɗauke kai nayi ina cuskule fuska na canja hanya kamarma ban gansu ba. Ina jiyo su Rano na basu labarin wai yanzu suma na gama musu yarfi dan ina tare da Dr Yoohan, Wai ai zamu koma Nigeria zan gane kurena, suma zasu rama ne😣😒.

        A office na iske Yoohan nata kaiwa da komawa. da alama dai tabbas abinda ya tada masa hankali ya jiyo ya kuma gano. Dan yanayin nasa yayi kama da wanda ke acikin ruɗani da al'ajab, harma da kullewar kai.
      To nidai bansan tayaya zanbi na san mi wannan bawa ya gano ba. Sai dai mu cigaba da bibiyarsa kuma kozamu fahimta anan gaba.

        Washe gari da safe su baba malam suka wuce Nigeria harda Richard. Akabar Aymah da Yoohan da Solomon kawai. (Jelar Yoohan😜). Kuka sosai Aymah tasha dan bataso wannan tafiya tasu baba malam ba. gudun samun matsala su Yoohan suka danna mata allurar barci data jata tsahon lokaci.
      Su kansu su Umm ɗin badan sunsoba suka taho, sai dai tunda jikin nata Alhmdllh gara su dawo kan harkokinsu suma tunda mijinta tsaye yake akan dukan lamuranta, ko a fuska basu taɓa ganin gajiyawa daga garesa ba. Hakan yasa ƙaunarsa ta ƙara shige musu zuciya da bargo sosai. Suna sake taya Nu'aymah murnar dacewa da tai da miji na gari mai kyawawan halaye. Hakan na nufin a haifeka cikin musilinci ka rayu da girma a cikinsa bashi bane ke nuna zakafi kowa kyawawan halaye. Balle har kayi tunanin samun lasisin hantarar wanda ya tuba daga baya da masa takama kai kaine mai addini. Shi wannan da kake kalubalanta da jifansa da kalmar tubabbe dan kawai ya shigo addinin islama daga baya sai kaga ya fika rabauta a wajen UBANGIJI. Ya fika ƙyawawan halaye nagartattu abin koyi. Mu kiyayi aibanta waɗanda suka shigo musilinci saboda mu an haifemu a cikinsa, dan wlhy mu hausawa munada wannan banzan halayen a rayuwar zahiri. ALLAH ka shiryemu dai.

       Sun iso Najeriya zukatansu cike dajin daɗin yanda suka baro jikin Aymah. Sun kawoma sauran ƴan uwa labari mai daɗi da saka kwanciyar hankali. Fatan kowa kuma ALLAH ya ƙara mata lafiya ya kuma maidosu gida lafiya.

_________★★★★__________

         Nu'aymah ta cigaba da jiyya da samun kulawa ga mijinta. Duk da kuwa bayan tafiyar su Umm taso rikita kanta da damuwa. Amma Yoohan yayta lallashi da lallaɓa harta haƙura ta cigaba da sakin jikinta da shi yanda ya kamata. Dan duk abinda ya fahimci tanaso shi yake mata. Wannan ya saka ƙara samun nasara sosai game da lafiyarta, wata shaƙuwa ta musamman kuma na sake shiga tsakaninsu. uwar ramar da tayi ta ɗan fara cikowa. Yakan kama hannunta yaɗan fita da ita su zagaya cikin asibitin dan tasha iska. Hakan kuma na sakata farin ciki da sake godema UBANGIJIN daya bata lafiya. Dan idan taga halin da wasu suke ciki zuciyarta na ƙara raunana. Taga ciwonta ba komai baneba ashe. 
      Haka rayuwar ta cigaba da gungurawa har ga su Yoohan da cika sati uku a ƙasar Austria, cikin birin Vienna. Alhmdllh yanzu kam jikin Aymah ko makiyi ya gani yasan an dace. Sai dai tana amfani da glasess ɗinta da yay mata wani masifar ƙyau kai kace na kwalliyane ma. Sai ko yar ramar da har yanzu bata gama cikowaba yanda ya kamata. An basu sallama a daren yau, tare da ɗorata a kan magunguna da zata sha na tsahon watanni biyu har komai ya karasa dai-daita. Sai allurai guda hudu da za'ai mata a kowanne wata sau biyu suma.
      Sosai Yoohan yake a tsananin farin cikin cikama baba malam burinsa na ganin lafiyar Nu'aymah. Hakama Solomon ya nuna jin daɗinsa. Uwar gayya Nu'aymah kam ai ba'a magana. Dan tsabar jin daɗi har rungume Yoohan tayi batare data farga da abinda tayi ba. Gaba daya saita sake sagar masa da gaɓɓan jiki. dan a yanda take masa abubuwa a asibitin nan gaba ɗaya rikita masa lissafin tunani takeyi. 
     Haka dai suka tattaro zuwa hotel ɗin da Yoohan sukai masauki. Bayan sun gumtsama ƴan 9ja labarin sallama. Masoyan su na gaske sun sake tayasu murna. Yayinda maƙiya kam sam ba hakan bane. Wasunsu ma sai shiri da suke musu na wasu bala'oin domin tarbarsu da shi. Dan a cewarsu babu abinda za'a fasa. Yanzu ne ma wasan zaiyi zafi.

Nidai nace, “Hummm”.

______________________________

            Tunda suka iso ƙayataccen Hotel ɗin daya gama haɗuwa da ƙawatuwa, Nu'aymah take jinjina girman UBANGIJI da rahamarsa. Hotel ne daya ginu, ginuwa mai ban mamaki da al'ajabi. dan wannan ba fasahar masu gini bace, wani ikone da rahamar UBANGIJI da hikinarsa. Ginine mai tsananin tsayi da ado, harma batasan yaya zata musalta gamai karatu ba. Mutane nata kaiwa da komawa duk da kuwa dare ne, maza da mata harma da iyaye da yaransu. Daka gani dai kasan wajene na hutawa, dan harda baƙakenmu tsilli-tsilli a wajen ana more rayuwa.
        Cike da neman tsokana Yoohan yace, “Kar dai kisa ace mana ƙauyawa hajjaju”. Hararsa ta ɗanyi, sai dai batace komai ba dan yanzu ba Aymahn da baceba. Sam bata cika son magana ba da hayaniya. Shiyyasa wani lokacin idan yaji shirun nata yayi yawa sai ya takaleta koda hararsan tayi. dan yanason yaga ta dawo kamar da ɗinta mai tsiwa abin na masa daɗi. Amma yasan sai a hankali. Koda kuwa zata koma kamar da ɗin ba hundred percent ba.
        Batare da tasan daga ina Solomon ya ɓullo ba ta gansa a gabansu. Cike da girmamawa ya risinar da kansa yana gaishesu da mata sannu da zuwa da taya murnar samun lafiya.
        Ta amsa masa kadaran kadahan. Dan mamakin irin wannan lamari takeyi, kenan a ko ina Yoohan yake suna tare da wannan mai gadin ko mi?. Bata da mai bata amsa dan haka ta hadiye abunta ta maida hankalinta ga sauraren bayanin da Solomon ke ma Yoohan akan ɗakin da zasuje, ya mika masa wani ɗan card. Nu'aymah ta fahimci da ba'anan suka saukaba kenan. A yau ne Yoohan ɗin ya saka suka dawo nan ko kuma yaya ai oho dai. Sai dai batasan minene dalilin yin hakanba, bakuma ta tambaya ba.
       Hannunta ya kama suka shiga har cikin hotel ɗin har masaukinsu. sai dai har suka iso ƙofar ɗakin tanata faman kalle-kalle. dan da gaske ta zama baƙauya. Duk da kuɗin gidansu iyayensu basa taɓa barinsu zuwa irin waɗanan wajajen koma tace ƙasashen. Iyakar yawonsu baya wuce Saudia shima Umrah ko aikin hajji ke kaisu. Sai ko mazansu da kan je harkokin kasuwanci dana karatu wasu ƙasashen. amma dai su mata ba'a barinsu sam. 
     Kati ya fiddo a aljihun green jeans ɗinsa ya saka a wani abu kamar na atm yay danne-danne ƙofar ta zuge kanta gida biyu. Zare katin yayi ya kalleta da mata nunin ta fara shiga. Bismilla tayi haɗe da sallama ta saka kafarta cikin ɗakin.............✍
        
_____________________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[6/22, 2:03 PM] +234 806 216 7027: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 58

............Wani irin ɗumi ne mai daɗi da saka nutsuwa ya ratsa mata jiki. Ga ƙamshi mai kwantar da zuciya na tashi. Ɗaki ne ƙaton gaske da yaji ababen more rayuwa da birgewa. Ga wasu irin ƙwayayen wuta dake bada kalar blue, green, an purpule ƙanana. Idan wannan ta kawo sai ta dauke wannan ta kawo. Hakanne ya ƙara ƙawata ɗakin da adon da akai masa na musamman daya tilasta Aymah nutsuwa tana kallon komai daki-daki.      
          Jinsa a bayanta ya sakata juyowa ta ɗan kallesa, ganin ita yake kallo tai saurin janye idonta. Kafarta ta ɗaga ta cigaba da takawa tsakkiyar ɗakin inda aka ɗaura wasu balan-balan da sukaja hankalinta masu zubin love, dan kamar sunanta take hange a jikinsu. 
          A hankali takai hannu kansu dan kuwa tabbas sunanta ne a jiki. Tana taɓawa suka shiga fashewa da kansu har taɗan zabura dan tsoro. A bazata sai jin abu na zubo mata a jiki tayi mai ɗan karan ƙamshi. Tanason ta kalla amma yanda yake zubowar ya hanata damar hakan. Dole ta tsaya a waje guda kawai ta lumshe idanunta abin na cigaba da sauka a kanta tamkar ana fesoshi.
      Tsahon mintuna biyu cif sannan ya daina zuba. Buɗe idanun tayi a hankali tana kallon ƙyawawan kalolin flowers ɗin dake zube a ƙasa alamar sune suka zubar mata a jiki. Samun kanta tai da tsugunnawa tasa hannu ta dumtsosu tare da kaiwa kan hancinta dan ƙamshinsu ya mata masifar daɗi..  
       Shaƙa tayi ta lumshe idanu wata irin nutsuwa na saukar mata. Ta buɗe a hankali tana ɗagowa ta kalli inda Yoohan ke taye jikin bango ƙafafunsa a harɗe. Hannayensa duka biyu cikin aljihun wandonsa yana mata wani irin kasallen kallo da lumshe idanu. Ga wani irin ƙyaƙyƙyawan murmushi akan fuskarsa. 
          Samun kanta tai da sakar masa wani lallausan murmushi itama batare data san kona minene ba. Ta miƙe a hankali tana takowa garesa har lokacin idonta dake cikin siririn farin gilashin na kansa. A fuska ta watsa masa fulawoyin cikin hannunta tana sakin siririyar dariya da fadin, “Kallon ya isa malami”.
       Murmushin daya bayyana haƙiransa ne ya subuce masa. Ya miƙe tsaye da ƙyau batare da ya zare hannayensa a aljihunba ya nufota. Baya ta fara ja a hankali tana wani marmar da idanu kamar maijin tsoronsa. Haka suka cigaba da takawa tana yin baya yana binta har jikin ɗan ƙarfe da akai kwalliyar ɗakin da shi, inda aka sakar mata flowers ɗin nan. Jin ta dangane da shi ya sakata saurin yinƙurin barin wajen. Ruff taji abu ya rufesu dan shima dai-dai da isowarsa gab da ita. Saurin daga kai tayi ta dubi sama. Abu ne tamkar net ya lulluɓesu, hannu ta kai a hankali jikinsa, tamkar taɓawar tata ake jira dama ya fara juyawa yana dunƙulewa tamkar kwalba.
       Idanunsa shima ya ɗaga yana kallon net ɗin tun daga sama harya sauke su a kanta a hankali. Ya tsatstsare ta da mayun idanunsa tare da ɗage hannayensa yana girgiza mata kai alamar shifa babu ruwansa. Dan wani irin kallon tuhuma take binsa da shai fuskarta a tsuke tabbacin ƴan tsiwar sun iso. 
         Taku biyu dake a tsakaninsu ya iso gabanta gab. Sosai ta matse bayanta da net ɗin ko nace kwalba a yanzu, dan daga wajema idan kana kallosu sai kace sun cikin kwalba kuma ruwa a ciki. laɓɓanta na motsawa kaɗan-kaɗan sai dai ta kasa cewa komai. Ya zare hannayensa daga cikin aljihu ya duƙa ya dimtso flowers ɗin shima. Ɗagowa yay ya watsa mata a fuska takar yanda tai masa. Baki ta tura gaba da share fuskarta, gefe da gefenta ya ɗora duka hannayensa biyu saman abun, saita koma tsakkiyar jikinsa. 
         Idanu sosai Nu'aymah ta zaro jikinta na wata irin tsuma da haɗe yawu da ƙyar. Saurin ɗago idanunta tai tana kallon nasa zatai magana........
           Da wani irin sallo yay luuu da nasa idanun yana faɗin “Shiii!!!” a saitin kunnenta dan ya ɗan ranƙwafota. Sai dai jikinsa har yanzu bai taɓa nata ba.
     Kasa maganar kuwa tayi, dan gaba ɗaya ya ƙure jarumtarta. Ba ƙaramin tasiri katangar da yay mata da jikinsa tayi a gareta ba. Ya shiga busa mata numfashinsa akan dokin wuya. Kafin ya fara magana a ahankali. “Inama ALLAH godiya, tare da taya kaina farin cikin samun lafiyar matata. Zeeynab ke ƴar baiwace......”
           Nu'aymah bazata iya jurewa da salon Yoohan ba. Dan jikinta yama fara rawa. A hankali ta sulale tai ƙasa tana matse hannayenta da jikinta waje guda batare data ƙarasa jin abinda ya faro faɗa ba saboda tsigar jikinta data mimmiƙe a dalilin salonsa. A hankali yay ƙasa da idanunsa shima ya bita da kallo. Samun kansa yay da zamewa ya durƙushe a gabanta kamar yanda tayi. Da wannan damar ta samu duƙe fuskarta saman cinyoyinsa dan bata son su haɗa idanun. Sassanyan murmushi ya sauke da ɗaura duka hannayensa akan bayanta. Cikin sake raunana muryarsa yace, “I love you Nu'aymah. I love you sooooo!! much”.
       Tabbas a bazata wannan kalma ta zoma Nu'aymah daga harshen Yoohan. Hakanne ya sakata ɗagowa a matuƙar razane, tare da idasa zama daɓat tana waro masa manyan idanunta tamkar wadda taji wata kalmar ban tsoro. Bakinta ta shiga motsawa a hankali, amma maganar ta gagara fita saboda tsabar firgici. Da wannan damar Yoohan yay amfani wajan matsar da fuskarsa gab da tata har suna shaƙa da busama juna numfashi. A bazata Aymah taji saukar tausasan laɓɓansa saman nata dake motsin son cewa wani abu amma hakan ya gagara.
       Ba ƙaramin rikicewa ta sakeyi ba. Sai dai ya hanata kowacce irin damar ƙwatar kai. sai ma hannaunsa daya ɗaura ya dafe net ɗin yanda bata da damar motsawa. Idanma tace zata motsa ɗin a takure suke cikin net ɗin dan haka babu wata dama. Wani irin sirrin sumbata yake mata da ke neman jirkice ƙwaƙwalwar daya gama cetowa a kwanakin da suka gabata. A take jikinta ya hau rawa ta kasa daurewa sai da ta ƙanƙamesa. Iya rikitarwa Yoohan ya ruɗama Aymah jiki da tunani. Sai da ya tabbatar da laushinta a hannunsa sannan ya danna wani abu acan ƙasan net ɗin yay sama daga inda ya sakko ya barsu a fili.
           Sunayen ALLAH kawai Nu'aymah ke maimaitawa da iya gudun fanfalaƙe da zuciyarta keyi, duk yanda Yoohan yaso ta ɗago ta kallesa ya tabbatar da sirrin tata zuciyar ya gagara. Dole ya ɗauketa cak ya kai bisa gadon da aka ƙawata da kayan ado ya kwantar. Yana ajiyeta ta kife da sauri batare data yarda tama kalli sashen da yake ba.
      Murmushi yayi yana wani lumshe idanu da buɗewa. Cikin muryarsa dake a dasushe yace, “Zan baki damar ɗorani a mizanin da kikaga ya dace da burin tunaninki da tsarinki. Bazan taɓa miki tilasba, sai dai ki sani bazan taɓa iya haƙura ba. Ina sake jaddada miki ina SON KI!, so kuma da zamanmu ne kawai zai tabbatar miki da shi ba fatar baki na ba. Nima ki So ni domin ALLAH”. Yay maganar a cikin kunnenta. yana gama faɗa ya ɗago daga ranƙwafowar da yay a kanta. 
      Yayinda ita kuma ta kuma takure kanta waje guda zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri.
        Gefen gadon ya koma ya zauna kawai yana kallonta, dan yanda ta cure jikinta waje ɗaya abin dariya. Ya dai daure baiyi dariyarba. Ƙarar door bell ce ta sakashi miƙewa yana gyara rigarsa da faɗin, “Oh God! ana jiranmu, taso muje”.
         Duk yanda take bala'in jin kunyar haɗa ko hanya da shi balle akai ga ido sai da ta ɗago. “Ina kuma zamuje?”. Tai maganar da ɗan tura baki da waro idonu.
       “Silly girl, taso kigani mana” ya bata amsa shima yana riƙo hannunta. Dole babu yanda ta iya haka ta miƙe tana gyara gyalen jallabiyar jikinta da ɗayan hannun. Ta gefen da take ɗauka labulene kawai ya kaita. Ya zaro handkerchief a aljihu ya zagaya bayanta. Ji kawai tayi ya ɗora mata akan ido alamar zai ɗaure. 
         “Wai kodai saidani zakayi ne?”.
    Tai maganar tana son ture masa hannu.
          Hannunta shima ya ture yana faɗin, “Kina ƴar tamilo ɗinan ko an saidaki namanki bazai ishi masu ci ba ai”.
      Da sauri tace, “To nama fasa”. 
   Shima saurin riƙe mata hannu yayi yana danne dariyarsa ganin bakin ya fara buɗewa. “Sorry kowa zaici ya ƙoshi, kuma zakiyi daɗi”.
       Shiru ta masa, sai dai bakin ya tashi sama alamar ta shaƙa. Shiko sai danne dariyarsa yakeyi dan bayason yayi ta birkice masa. Gani nayi ya danna wani abu sai ga labulen wajen dake bango guda ya zuge kansa ya koma gefe da gefe. Glass ya bayyana. Wanda ta cikinsa kake hango ainahin garin Vienna da ya gama haɗuwa da ƙayatattun gine-gine masu ban mamaki da al'ajabi. Kallonta yayi dai-dai ya sake danna wannan abun glass ɗin shima ya zuge ƙofar fita ta samu. Hannunta yaja suka fito ɗan barandan wajen dan ita dai ta zama makauniya.  
          Ni kaina sai da na ambaci masha ALLAH a zuciyata ganin yanda aka ƙawata barandar wajen domin hutawa kawai da ado na musamman, wanda a kallo ɗaya zaka fahimci tsarawa akayi dan wani dalili. Hannu ya saka ya kwance handkerchief ɗin daya ɗaura mata. glasses ɗinta daya cire ya ɗora mata duk da kuwa tana gani abunta ko babu shi, sai dai ba yanda ya kamata ba. Baki ta saki kawai tana bin wajen da kallo, kafin ta sami damar tambayarsa irin flowers ɗin ɗazun suka shiga zubo musu a jiki ita da shi, sai dai ƙamshin waɗanan daban suma. Atare suka lumshe idanunsa fulawoyin na cigaba da sauka musu. A bazata Nu'aymah taji tafi. Saurin waigawa tayi dan tafin yayi dai-dai da daina zubowar flowers ɗin a kansu. 
      Gaba ɗaya Doctors ɗin da sukai mata aiki ne. sai ƙarin mutum huɗu da bata saniba. Biyu mata biyu maza. Sai Solomon da Richard da batasan sanda ya dawo ba. Sai mutum biyu data taɓa gani a wajen dinner ɗinsu wanda take ƙyautata zaton abokansane ko ƴan uwansa ma.
      A taƙaice dai ƴar ƙwarƙwaryar liyafa ce su Rich suka shiryama Aymah da Yoohan na murnar samun lafiyarta da nasarar aiki. Sai dai basu samu damar zuwa Austria ɗin su duka ba. Sai Richard daya dawo, sai kuma Osin da Joseph. Ɗakin ma sune suka kama musu a hotel ɗin wai suyi Honeymoon na sati biyu Nu'aymah ta huta kafin su koma tunda hutu Yoohan ya ɗauka harna watanni biyu. 
       Gaba ɗayansu su goma sha biyu ne har Aymah da Yoohan. Hakan yasa komai ya gudana cike da birgewa da nutsuwa. Sunsha shagalinsu na awa ɗaya da rabi sannan aka tashi. Su Richard dai tun anan sukaima Nu'aymah sallama. Dan da safe zasu wuce ba lallai ta gansu ba.
           Godiya itama ta musu, ta shigo tabar Yoohan na ƙarasa magana da su. Bayan su Dr Liam sun wuce, Osin ya shige masaukinsu wai zaiyi toilet🤧. Solomon ma dai tafiya yayi can nasa masaukin inda suka fara zama da Yoohan. Hakan ya bama Yoohan da Richard damar kasancewa su kaɗai. Maganace a bakin Rich sosai gameda firar papa da Dr Mateo da yaji, sai dai baisan ta yadda zai tunkari Yoohan ɗinba kai tsaye tunda Papa mahaifinsa ne. 
       Ajiyar zuciya Yoohan dake ɗan nazarinsa yayi, “Rich kamar akwai magana a bakin nan naka tun kafin ka wuce kwanaki. Sai dai bansan miyasa ka gaza yiba. Duk da nasan dai bazai wuce akan komawata musulmi ba. Na yarda da kai Rich, dan baka taɓa cimin amana ba a tsahon shekaru goma sha shida da mukasan juna. Dan haka zan faɗa maka sirrin komawata mai salla a yanzu koda kuwa bazaka fahimceni ba”.
       Batare da ya jira amsar Richard ba ya shiga bashi labarin tun farkon haɗuwarsu da su Nu'aymah a ƙofar Orphanage. Fasa masa glass ɗin mota da tayi da tilasta musu shiga cikin Orphanage akan yaron da suka bige. Fara mu'amularsa da su baba malam har zuwa musulintarsa da aurensa da ita. Babu abinda Yoohan ya ɓoyema Rich. Sosai tsantsar mamaki da firgici ya bayyana ga Richard. Wani irin rauni da ƙwaɗayin shiga musulinci ya ringa kutse cikin ɓargon jikinsa da zuciya. Sai dai baice komaiba akan hakan sai magana akan ƙullin da akaima Aymah na maganar ciki.
        Ya janye hannunsa da ga dafe kan da yayi yana duban Yoohan da ke kallon wani waje da ban. “Ka yafemin Yoohan”.
      Juyowa Yoohan yayi yana dubansa. Cikin ɗan lumshe idanu yace, “Akan mi? Ni bakamin laifin komaiba ai”.
       “Niko na maka laifi X-man. Dan na zargeka akan abinda ba haka yake ba. Sannan na zargi in-lows ɗinka suma. Da ga yau na maka alƙawarin tayaka wannan yaƙin, zan taimakeka wajen cikama iyayenta alƙawarin daka ɗauka na bayyanar gaskiyar maganar cikin da suke zargin ta zubar”.
      Kallonsa Yoohan yake cike da so da ƙauna. Ya riƙo hannun Rich cikin nasa yana faɗin, “Nagode sosai Rich, kai ɗin na dabanne a gareni koda bakina bai furtaba”.
       “Ba nine na daban a garekaba Yoohan, kai ne na daban a gareni. Dan kamin abubuwa da yawa da ni kaina bansan hanyar da zan iya saka maka ba. Indai ni ɗin ɗan halak ne dolene na kasance a cikin yaƙin nan daka ɗauki alƙawarin yi. Sai dai zan baka shawara ɗaya zuwa biyu”.
        Numfashi Yoohan ya furzar da lumshe idanu ya buɗe akan Rich. “Ina jinka”.
       “Ka ajiye maganar ƙanƙantar matarka ka fara nuna mata ɗunbin soyayyar da kake mata. Waddama bata kaita shekaruba tana ɗaukar namiji balle ita dana fahimci tanada wayo sosai. Kaifa likitane, kasan sirrin mace duk da kuwa karatun likitancinka ba'a kansu kayisa ba. Amma na sanka da bincike, ta wannan hanyarne kawai kaima kanka zaka fahimci gaskiya ko akasin abinda Doctors ɗin suka faɗa a wancan karon, tare da naka gwajin, sai ka bita a sannu yanda kake buƙata.........”
      “Amma Rich.......”
“Karkace komai Mr X. Wai shin kai baka tunanin shekarunka ƙaruwa suke ba raguwa ba? Ya kamata kasan sirrin dake cikin wannan tafiyar. Ko dai baka da lafiya ne Yoohan?”.
       Harararsa Yoohan ɗin yayi kawai ya kauda kansa. Rich ya kwashe da dariya yana faɗin, “Kai ɗinne kana abu kamar dutsi oga. Ga dama ka samu a hannu amma kana son kasa damawa. Idan da kace kana ƙyanƙyami da gudun matan waje wannan dai matarkace ai ko.......”
      “To naji mai shegen surutun tsiya. Muje shawara ta gaba”. Yoohan ya faɗa yana talle ƙeyar Rich.
      Shafa ƙeyar Rich yayi da faɗin, “Mugu, ashe dai kanaso. Shawara ta ta biyu itace karku koma Nigeria da ita yanzu har sai na binciko maka duk yanda komai ya kasance”.
        “Taya zaka binciko abinda baka saniba. Sannan wannan abun nasu yayi kama dana family, kai da ma ko sakin jiki ka kasayi da Uncle ɗin kanata faman jin haushinsa”.
       Murmushi Rich dake kallonsa ya keyi, a ransa kuwa yanason hana Yoohan komawa Nigeria da Aymah ne saboda abinda ya jiyo a wajen papa a wannan komawar da yayi gida. Saboda hirar papa da Dr Mateo ta kasa barin ransa tun wancan karon. A wannan zuwan koda suka koma dasu baba malam a abuja ya sauka shi. Anan ya ɗanbi diddigin papa shine ya sakejin kwangilar kashe Aymah da ya bada ayi masa saboda wai ya ganta a cctv ta shigar masa ɗaki. Duk da basusan mitayiba a ciki saboda cctv ɗin iyakarta parlornsa ne, (Tab, kenan randa Aymah taje ɗakin papa. Ya salam🤦🏻‍♀️) Abinda yasa suka gaza gane mitayi su basuga komai a hannuntaba. To amma shi papa ya tabbatar ta ga sirrinsa shiyyasa yake buƙatar a kauda masa ita kafin bakinta ya faɗama wani. duk da yana zargin ta faɗama baba malam, yaso kuma ƙyaleta yabi a hankali harya gano abinda tayo a ranar amma su Uncle Mike sukaita tunzurashi aka ya kasheta kawai, shine ya bama Dr Mateo kwangilar kasheta a wajen aiki batare da an zargesaba, dan Yoohan ya sanar masa a inda za'ai aikin da masu tayasa. shine aikin ya gagara kuma.
       Wannan abu da Richard yajine ya sakashi zaunar dasu G-boy akan su haɗa kuɗi su saka Yoohan zaman Honeymoon a Austria. Sai dai su basu san dalilinsa nayin hakanba dan bai fito fili ya faɗa musu ba........
     Taɓashin da Yoohan yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ya sauke numfashi, cikin son kauda tambayar mi yake tunani da Yoohan yay masa yace, “Yoohan ka bani dama. Zanyi bincike nane iyakar likitocin da suka gwadata. Sai kuma ƴar aikin da kace an kawo muku tunda kace ka saka mata abin ɗaukar magana a ɗakin da kuka ajiyeta”.
       “Okay Rich, sai dai banason ka saka kanka a haɗari Please”.
      “Karka damu kamin addu'a kawai. Kuma ai tare zamuyi aikin ma da kai”.
      Murmushi Yoohan ɗin yay masa suka rungume juna cike da so da ƙauna. Daga haka Rich ya korashi wai yaje madam na jiransa shima zaije yay video call da tashi dan gobe ma wajenta ya nufa, tare zasu wuce 9ja daga can..........✍🏻


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[6/22, 2:04 PM] +234 806 216 7027: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 59
     
..............Sosai yanzu ta nutsu ta ƙarema lungu da saƙo na ɗakin kallo, dan an kashe waɗancan fitulun ansa ainahin fitilu da suka ƙarama ƙawata ɗakin. Lallai duniya budurwar wawa. Idan bakayi wasa ba irin waɗanan abubuwan tuni suke shagaltar da kai ma ga bautar ALLAH. Shiyyasa wasu mutanenmu dasun samu irin wannan damar sai kaga addininma an fara walagigi da shi. Zama tayi tana jiran shigowarsa dan taji wai yayama za'ayi? taga ɗaki daya ne. Nashi ne nan ko nata?. Dan kuwa dai ba yarda zatai su zauna a ɗaki ɗaya ba ehe.
        Tayi kusan zaman mintuna goma sha biyar sannan ya shigo ɗauke da ƙyaututtukan dasu Dr Sophia Suka bata. Yi tai kamar batasan ya shigoba. Shima kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Sai da ya ajiye kayan hannun nasa sannan ya nufo inda take. Zama yay a kujerar dake kallon tata ya zaro wayarsa dake ring ya sa a kunne fuska ɗauke da murmushi. Sun kwashe tsahon mintuna a haka yana waya tana satar kallonsa harya kammala.
        Kallonta yay ta kauda fuskarta gefe. ‘Yarinyar nan rigimanta yawane dasu' ya ayyana a ransa yana lumshe idanu da buɗewa a kanta. Ganin bazatayi manar daya fahimci takeson yiba sai ya mike ya shiga toilet ɗin ɗakin bayan ya ciri kayan barci a cikin kayansa da Solomon ya kawo ya ajiye rigar a saman gado ya ɗauki wandon kawai.
      Duk da Aymah najin sanda ya shiga bayin ta kasa ɗagowa. Haka ta cigaba da zama zuciyarta na tattaro mata abubuwa masu ɗunbin yawa a kansa, ga ɗokin son komawa gida da takeyi, dan wulaƙanci yau ma gaba ɗaya bai kira mata Baba malam ba kamar yanda ya saba.
        Duk daɗewar da yay a bayin a yanda ya barta haka yazo ya isketa. Da alama ma dai barci ta fara. Gaban kujerar ya matsa yana mai tsane sumar kansa ta gefe-gefe dan ba jiƙata yayi ba. Leƙa fuskarta yayi, hakan yasa ruwan da bai gama tsanewa ba a jikinsa ya ɗisar mata a gefen fuska. 
      Motsawa tai tare da buɗe idonta dan da gaske barci ta fara. Suna haɗa ido tai saurin jan gyalen jallabiyarta ta rufe fuska. “Oh God! Dama babyn nan mai bakin tsiwa tanada kunya ashe?. Tom tashi kije kiyi wanka”.
         Bata iya ta motsa ɗin ba sai da taji motsin barinsa wajen. Ta gabanta ya zagayo inda Wadrobe ɗin ɗakin take. Tabi bayansa dake raɓar ruwan wanka da kallo, dan dogon wandone kawai a jikinsa babu riga, sai towel ɗin dake a hannunsa ƙarami. harya buɗe Wadrobe ɗin da akwatin kayansa ke a ciki, harma da nata kayan a haɗe da batasan da zamansu ba idonta a kansa. Ajiyar zuciya taɗan sauke da mikewa ta nufi bayin dan tana buƙatar yin wankan da ruwa mai ɗumi ko zataji daɗin jikinta, taga alamar kuma guy ɗin nan ba kunyace da shi ba. Kaɗanma daga aikinsa yace a gabanta zai Shirya. Bara tai wankan sannan tazo taji yanda zasuyi akan zaman ɗaki.
        Lallai indai da ranka kallo baya ƙare maka ba. Dan toilet ɗin kansa ma wata aljannar duniyace. Tsabar ɗaurema ƙarya ƙugu harda television a ciki. Baki ta taɓe tana faɗin, ‘Kunga aljanu ai sun samu nayi. Kayi tsirara ga tv ana nunawa ai al-amari sai wanda kuma ido ya gani’. Da wannan mitar ta shiga wajen wankan na glass shima dake a mulmule. Wankanta tayi, sai da ta gama ne kuma tunanin kaya yazo mata a rai. Kanta ta dafe cike da damuwa tana faɗin ‘Oh Stupid  me. Miya shiga kaina ne?’. Fitowa tai gaban ƙaton mirror ɗin da aka shirya towels a wani ɗan drawern glass shima. Fatanta ta samu bathrobe. Cikin sa'a kuwa tana ɗaga ta farko sai taga rigace. Ajiyar zuciya ta sauke ta warwareta ta saka. Tako wuce mata gwiwa, hakan ya sata jin daɗi ta ɗaure igiyar sannan ta naɗa ƙaramin towel a kanta dan duk ta jiƙa gaban goshin da ƙeyar. Kayanta data cire da nasa daya ajiye ta jefa cikin washing machine ɗin ta wanke. Ta sakasu wajen busarwa ma ta busar sannan ta ninke abunta ta fito dasu a hannu duk da harga ALLAH tanajin nauyin fitar saboda Yoohan. Amma da yake bawani jikinta bane a waje sai ta fuske akan zata ɗakko kaya ta dawo toilet ɗinne ta saka.
           Zaune ta iskesa a bakin gado yana danna tab. Yana sanye da kayan barci farare ƙal. Baiji fitowarta ba saboda a hankali take tafiya da sanɗa, ita wayonta wai karya ganta. Sai ko akai rashin sa'a tana zuwa saitinsa ya ɗago ido ya kalleta. Cak ta tsaya tana cika baki da iska kamar zata fasa kuka. “Ni dai banason kallo”. Tai maganar da alama dai an ƙure mata gudu ne.
      Idanunsa ya lumshe yana sake buɗesu a kanta. Baki ta kuma cunawa gaba ta juya masa baya. 
       A hankali yace, “Silly girl!”. Yana maida kansa ga tab ɗin. 
          Cike da munafurci Aymah taɗan karkato ta kallesa. ganin ya maida kansa ga tab taci gaba da tafiyarta kai tsaye yanzun. Bayansa taje ta tsaya ta ɗayan ɓangaren gadon. Kamar zatai kuka tace, “Banda kayan sakawa ni fa”.
          Batare daya juyo ya kalleta ba yace, “Tom aro zan baki ne?”. 
       “Hu'um. Ƙato da kai tayaya kayanka zasumin. Kana kallon kanka kuwa a mirror? Sai kace ɗan dambe”.
         ‘Yarinyar nan ko’ ya faɗa cikin ransa yana juyowa ya kalleta. Saurin juya masa baya tayi dan itafa batason kallon. Shima ya fahimci kunya takeji, hakan ya sakashi yin murmushi. Wannan ɗabi'ar ta kunya tana abu na farko da yaren hausawa ke burgesa da shi. Ko abu ke damunsu sukazo gabansa matsayin likita sunta ƙunshe-ƙunshe kenan. 
         Miƙewa yay ya zagayo inda take. Ganinsa kawai tayi a gabanta. Hakkanne ya sakata zabura tai baya kamar wanda tai gamo da abun tsoro. Tai saurin sake juya masa baya a daburce.
      Hannayensa duka biyu ya tura cikin aljihun wandon kayan barcinsa yana faɗin, “Uhyim! Tom nama fasa bada aron kayan. Garama ki lallaɓani fa, koki kwana da bathrobe. idan kuma kinaso juyo ki kalleni”.
        Ji Nu'aymah tai kamar ta fasa ihu dan takaici, gashi harga ALLAH tana buƙatar aron kayan kuma da gaske. Dan bazata iya kwana da rigar wanka ba. Juyowa tayi a hankali idanunta a ƙasa ta kasa kallonsa. Yanda ta koma kamar wata munafuka ne ya bashi dariya. amma sai ya gimtse kayarsa baiyiba. Takowa yay gabanta ya tsaya gab. Yasa hannu a karɓi kayansu dake a hannunta tare da ɗora na damar a haɓarta ya ɗago fuskarta. Tsaf ta runtse idanunta kuwa. Baiyi magana ba, sai kallonta kawai da ya keyi musamman bakinta da arayuwa yake bala'i-bala'in ɗaukar masa hankali. Kodan shine yafi masa tsiwa oho. “Je gasu can a Wadrobe ki ɗauka badan halinkiba dai”.
      Batare data buɗe idanunba ta motsa laɓɓanta kaɗan tace, “Thanks you”. 
       Sakar mata fuska yayi ya matsa. Da sauri tabar wajen dan gaba ɗaya idan ya tsaya kusa da ita koya zauna jinta take a matuƙar takure, duk sai yay mata kwarjini. Tana buɗe akwatinsa dake a Wadrobe ɗin yana isowa wajen. A bayanta ya tsaya gab tare da zura hannunsa duk biyu ya ɗora akan nata dake ɗaga murfin trolly ɗin data buɗe. Jitai numfashinta na fita da ƙyar lokacin da ƙirjinsa ya mannu da bayanta duk da akwai kaya a jikin nasu. Taɗan rintse ido zuciyarta na harbawa. Kansa ya ɗora gefen kafaɗarta ya ajiye kayansu daya amsa a wajenta yana magana a hankali. “Ashe kin iya wanki?”. Kasa bashi amsa tayi, dan harga ALLAH ta matuƙar takuruwa. Shima fahimtar hakan da yayine sanadin numfashinta da yaji yana seizing ya sakashi sakar mata kiss a wuya yaja baya. Kaɗan ya hana fitsari zuboma Aymah. Ta sauke ajiyar zuciya da ƙyar sannan ta buɗe idanunta dake tara ƙwalla. Ɗaga kayan ta farayi ko zataga wanda zai ɗan mata, sai taga kayanta har kala huɗu ashema a ciki. juyowa tai taɗan kallesa da masa ƙaramar harara. Baisan tanayi ba, dan ya juya mata baya ne zai zauna a inda ya taso a bakin gado. Ƙunƙuni taitayi tana ciro kayan. Gaba ɗayansu ma kala huɗu ne. Na barci biyu, dogayen riguna biyu, sauran duk nasane suma dai basufi guda biyar ba, Sai kayan ciki datai fatan ALLAH dai yasa bashine da kansa ya ɗakko mata su ba. Dan wlhy daya gama da rayuwarta kam. Ɗaukar waɗanda zata saka tayi ta maida sauran. Ta haɗo harda wayarta data gani a ciki da Charger. Ta gabansa tazo ta wuce bayi, acan ta canjo kayan ta yafo mayafin jallabiyar data wanke dan dashi ta koma. Kayan bama wani kamata sukayiba, kuma basu fidda mata jikiba. Sai dai wandon iyakarsa gwiwar ta. Sannan hannun rigarma bawani babba bane can sosai. Amma bai mata yanda zataji kunya ba. A kwance ta samesa yanzun, idanunsa a lumshe suke amma batasan duk yana kallonta ba. Wajen Wadrobe ɗin ta koma, ta ɗauki turarensa data gani har biyu saman akwatin ta hau fesawa. Daga haka ta dawo wajen gadon tana kallonsa fuska a tsuke. 
          “Wai bazaka tafi ɗakinka ba ne?”. Tai maganar a hankali kamar maijin tsoro. Sarai ya jita, amma sai yay shiru abunsa kamar yayi barci. Idanuntane suka cika da ƙwalla. Dan gaskiya ita dai bazata iya kwana da shi a ɗaki ɗaya ba. Ta ɗan ɗaga murya fiye da ɗazun tace, “Kaji! Dan ALLAH kaje ɗakinka. Kokuma ni naje can sai na kwana”.
         Idanunsa ya buɗe a kanta. Yace, “Ohooo! Silly girl. Nan gidanki ne ma ashe ko? Dahar sai kin zaɓi ɗakin barci?”.
       “To amma ai kasan mu biyu ne sai ka kama ɗaki biyu”. Tai maganar da iya gaskiyarta. Fahimtar da yay yarintar tatace ta motsa ya sakashi gyara kwanciyarsa yana faɗin, “Wasa nake miki ga key ɗin ɗakinki anan zoki ɗauka”. Ya nuna mata bedside ɗin. Da iya yarda ta nufo wajen kuwa ita zata ɗauki key. Tana ɗora hannunta saman handle ɗin drawer ɗin kuwa ya riƙesa caraf.
          Bata ankaraba sai jinta tai a jikinsa ya fisgota ta faɗo. Duk da yaji zafi bai damuba, sai ma juyi da yay da ita suka koma tsakkiyar gadon sosai. Mutsu-mutsu take nason ƙwacewa ya matseta da ƙyau. Ga bakin ya kasa magana. Bargo ya jawo da hannu ɗaya ya lulluɓesu, kafin ya kai hannu  ga makunnar fitulin ɗakin duk ya kashe na barci suka kawo da kansu.
       Cikin kunneta yace, “Silly girl, ai kecema kike kama da ƴan damben. Garama ki nutsu muyi barci dan zaki gajiyar da kankine. A wancan karonma dana ƙyaleki akwai dalili. Yanzu kam ki fiddama ranki zamu cigaba da raba wajen kwanciya yarinya”.
          “Ni dai gaskiya bazan iya kwanciya da Namiji a ɗaki ɗaya ba”. Tai maganar tana kuka.
        Cikin kwaikwayon maganarta yace, “Nima gaskiya bazan iya kwanciya da mace ɗaki ɗaya ba”.
        Ɗagowa Aymah tayi tana kallonsa fuska shaɓe-shaɓe da hawaye. Ya ɗaga mata gira da kansa yana faɗin, “Kin zata kece kaɗai kika iya drama ɗin? Nima actor ne a film ɗin ai Trouble maker”.
       “Kaima Trouble maker ɗinne ai, Kuma sai na faɗaka da Abbana”.
          “Nima sai in faɗaki da Papa na. Kinga saisu haɗu su mana faɗa muyi-muyi mu kawo musu jikokinsu, dan ni nama ƙagara na ganki da ciki”.
         Da sauri Aymah ta maida kanta a ƙirjinsa saboda kunya. Ta dunƙule hannunta dake a bayansa tai masa ƙaramin dundu.
       Dariyar da bata taɓa ganin yayiba taji ya sanya mata yana riƙo hannun nata. Da ɗayan ta ƙara dukansa a ƙirji itama tana dariyar kaɗan-kaɗan. Matseta yayi gaba ɗayanta a cikin jikinsa yana ɗora haɓarsa bisa gashin kanta da hular ta zame duk ya mimmiƙe. Sumbatar kan yayi yana lumshe idanu har sannan da murmushi a fuskar tasa.
        “Yanzu fa idan nace zan rama sai ki kamamin raki ko? Kuma naji zafin dukanmin baya da kikayi”. 
      Da sauri tai ƙoƙarin ja da baya yay azamar riƙota cikin jikinsa yana mata magana a hankali. “Matsoraciya kawai, wasa nakeyi. Tashi kisha maganinki sai ki kwanta”.
       Itama luf tayi tana shaƙar ƙamshinsa, kusan mintuna biyu suna a haka kafin ya saketa dan yanayinsa neman fara sauyawa yakeyi. Jin ya saketa ta tashi zaune. Shima kunna fitilar ɗakin ya sakeyi ya tashi da kansa ya ɗakko mata maganin da ruwa ya kawo mata. Amsa tai tasha tana ɗan matse ido. Ta miƙa masa sauran ruwan batare data bari sun haɗa ido ba. Shima baice mata komaiba ya amsa ya juya. Da wannan damar ta tattaro filos ɗin gadon ta hau jerawa a tsakkiyarsu tana faɗin, “Kowa ya kwanta sashensa to gaskiya”.
         “Ai garama haka, ni karkimata ball da ni da waɗanan ƙafafun naki da basa zama waje ɗaya”. Yanda yay maganar yana kwanciya da juya mata baya kamar bashine yayiba ya sakata gallama bayan nasa harara. Itama bata tankaba ta kwanta ta juya masa bayan. Murmushi yayi dan yasan abin cewarne ya ƙare mata shiyyasa tayi shiru. Ba'afi mintuna biyar ba sai jin saukar numfashinta ya farayi a hankali alamar maganar ya fara aikinta har tayi barci. Juyowa yay a hankali yana kallon bayanta, musamman sumar kanta dake kwance luf a ƙeyarta har zuwa dokin wuya da ƙananu sukaima wajen ado mai ƙayatarwa bisa farar fatarta mai sheƙi da bawai ƙal-ƙal takeba irin ta turawa. Dan shi kansa ma ya ɗan ɗarata haske duk da farin fatar tasu ba iri ɗaya baneba sam.
       Hannu ya kai a hankali yana ciccire filos ɗin data jera musu a tsakkiya, sai da ya ciresu duka sannan ya matsa sosai jikinta ya sakata a nasa jikin yaja musu bargo. Ajiyar zuciya ya shiga saukewa a hankali, a ransa yana raya ‘Sarkin rikici’ tare da tura hannunsa cikin rigarta ya shafa cikinta dake lafe a jikinta kamar babu hanji a ciki. Lumshe nasa idanun yayi shima yana karanto musu addu'ar barci da ayanzu Alhmdllh ya haddace duka..

_________★★

         Alarm ɗin daya saka musu ne ya tadasu sallar asuba. Shine ya fara farkawa, sai da yayo alwala sannan yazo ya tada Nu'aymah da ƙyar. Ganin yanda take haɗa hanya alamar barcin bai saketa ba ya sakashi taimaka mata har ƙofar toilet ɗin. Bayan ta shiga ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya yasa abin salla ya kabbara raka'a-tainul fajir kafin ta fito.
        Itama koda ta fito doguwar riga ta cira a kayanta ta saka. sannan ta hau sallayan daya saka mata a bayansa tai tata nafilan raka'a biyu. suna zaune kowa na lazimi har lokacin sallan ya ƙarasa. itace ta bashi shawaran yay musu jam'i. Da farko ya nuna mata shi ina iliminsa ya kai da har zai musu jan salla. Ta masa taƙaitaccen bayanin da zai iya fahimtarta kafin ya jasu sallar asubahi.
        A mamakin Nu'aymah sai gani tai ya ɗakko Al-qur'ani ya dawo gabanta ya zauna. Kallonsa take kamar yanda shima nasa idanun ke a kanta.
     “Daga yanzu matata ce zata zama malamata kamar yanda Uncle ya bani shawara (baba malam)”. Sosai Aymah ta waro idanu waje, da faɗin, “Ni kuma Yaya Yoohan?”. 
      “Insha ALLAH kuwa. Dan duk abinda zanje nema a wajen wani malami na tabbata kinada kaso hamsin a cikinsa insha ALLAH. Karkiyi min wasa da damata Please Zeeynab, dan na yarda tun a farko UBANGIJI ya sakoki rayuwatane dan ki zamarmin fitila mai haska min hanya. So ni koda shekarunki basu kai hakaba zan zauna a gabanki na koyi abinda ban saniba. Cire duk wani kokwanto da shiriritanki nan wannan ba gaɓar wasa bane. Akwai manyan ƙalubale a gabana da dole sai da wannan ilimin zan tunkaresu”.
      Kan Aymah a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta jinjina masa kan. Cikin nutsatstsiyar murya tace, “Insha ALLAH zaka sameni yanda kake buƙata. Sai dai ka sani har yanzu ni ɗalibar ilimice, nima banje ko inaba a neman ilimin. Ko a gidanmu ƙaramin ajin yara nake koyarwa bawai manya ba”.
        “Bani da banbanci da waɗannan yaran nima ai Nu'aymah, domin abinda kike koya musu nima shi nake buƙata a yanzu ki koyar dani. Dukkan littatafan da zamu iya buƙata gasu Uncle yazo mani dasu. dan dama muna karatu da shi ta video call a kullum bayan sallar la'ar a duk inda nake. Da wannan ne na ɗan samu abin salla da addu'oin da kikeji a bakina”. 
      Sosai tausayinsa ya kama Aymah har idanunta suka cika da ƙwalla. Ya kuma birgeta matuƙa, dan ɗaukakarsa da girmarta da yayi, da matsayinsa na miji a gareta bata sakashi girman kai ba........
      “Please ki ceto rayuwata Zeeynab ”. Furicinsa ya katse mata tunani. Saurin ɗora hannunta tayi akan bakinsa saboda jin yanda yay maganar da rauni. Ta shiga girgiza masa kanta ƙwalla na sake taruwa mata a ido. “Ka daina roƙona, umarni kawai zaka bani a matsayinka na babba gareni kuma mij......”
      Sai kuma tai shiru ta kasa karasawa. Murmushi yayi da ɗaga mata gira. janye hannunta tai daga kan bakinsa ta hararesa. Yay karamar dariya da faɗin, “Hy karasa mana. Wai dama kinada kunya ashe?”.
      Harara ta kuma zuba masa tana kumbura baki, tace, “Silly boy”. 
     A tare suka fashe da dariya babu zato, dan ita kanta kalmar Silly boy ɗin datai saurin kiransa da shi kafin shi ya kirata ta bata dariya.. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka nutsu. Ya gyara zamansa yana faɗin, “Silly girl kin rainani wlhy”. Batace komaiba sai murmushi.
       Shima dai murmushi ne ɗauke a fuskarsa. Ya kara gyara zamansa. “Gashi Al-qur'anin ɗaya ne yaya zamuyi kenan?”.
     Murmushi ta kumayi mai kayatarwa tana lumshe idanu. Batare data kallesa ba tace, “Karka damu, ko babu Al-Qur'ani a hannuna zan iya ai”.
         “Woow masha ALLAH” ya faɗa yanajin wata ƙaunarta da girmanta a cikin zuciyarsa da bargo. Daga haka suka nutsu ya fara karanto mata iya inda ya tsaya da harshensa da baya fita sosai. Hakan yasa karatun nasa yay mata daɗi. Sai da ya tsaya ta dubesa da kulawa. “Zamu cigaba da yin Al-qur'ani. Amma ina ganin ya kamata ka fara koyan larabci hakan na taimakama mai karatun Al-qur'ani sosai wajen furta abinda ake buƙata”.
     Idanu ya lumshe a hankali ya buɗe a kanta. cikin muryarnan tasa mai amo yace, “Okay maa. Duk yanda kikace haka za'ayi”. Duk da ya bata dariya batayi ba, sai dai ta murmusa kawai. Cikin baiwar da ALLAH ya azurtata da ita na wadatuwa da ilimin addini ta fara ɗorama Yoohan karatun. Ba ƙaramin nutsuwa da shagala yayi a kallonta ba. Dan yaune karan farko da yaji yanda take raira karatun Al-qur'ani mai girma a fili. Wata irin nutsuwace ta ringa saukar masa. har ƙananun ƙwalla suka taru masa a cikin ido bai saniba. Sai da suka sakko a fatar idonsa kaɗan idanunsa sukai masa gizo sannan ya lura. Ɗan yatsa yasa ya ɗaukesu yana cigaba da saurarenta.
        Tabbas Yoohan ya saka a ransa zai nema ilimin addini babu wasa a ciki. Hakanne yasa UBANGIJI riko da hannunsa. Gashi kuma ya bashi Aymah a kusa da shi da har cikin ransa ya yarda itace zata zame masa malama kuma sirrin rayuwarsa. Dan haka basu tashiba a wajen sai da ta tabbatat ya fahimci abinda ta koyar da shi. 
       Bayan sun kammala abinci mara nauyi yaymata, order dan taci tasha magani kar lokaci ya wuce. Tunda shan maganin nata akwai ƙa'ida. Hatta da barcinta yanzu yanada lokacin yi da tashi har sai komai ya ƙarasa dai-daita yanda ya kamata. Tea kawai ta iya sha da cake kaɗan, dan ita dai wannan abinci na Austrian baya mata daɗi. Wanima ƙyanƙyami yake bata. Musamman da harshenta har yanzu ba komai yake masa ɗanɗano ba. A hakama cake ɗin sai da Yoohan ya tayata ci sannan. Tana kammalawa ya bata magani tasha ta shiga wanka. Shi kuma fita yay dan motsa jiki a gym ɗin hotel ɗin. Da kuma son ƙarasa magana da Rich.
         Aymah na fitowa kaya kawai ta canja sai kwanciya. Ko mintuna biyar bata rufaba kuwa barci yay gaba da ita.............✍


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


*_FEJI SATTIN😬_*

______________

*Sunana Nafisa k Abdullahi am a singer, actress.. wakokina are based on siyasa da kuma na sarakuna *

https://youtu.be/1VyZ6f1GTWg

*(YouTube link)👆🏾*

*This is my YouTube channel IN SHAA ALLH! I will be bringing to you my latest films, And musical videos*


*NafisaKabdullahi* *Sabuwar ficacciyar jaruma ce data shahara wajen fina finai da kuma wakoki na siyasa, Masarautu da sauran su* 

*Ina masoya makaranta littafan zafafa? Ku fito ga dama ta samu, Munason a nuna mana k’auna ta hanyar subscribing a sabuwar channel dinnan ta Nafisa mai suna a sama. 👆🏾A kalla a kuma danna kararrawa domin sauraron shirye shiryen ta a duk sanda ta dora..*

*Danna kararrawa domin kasancewa da ita da zarar ta dora sabbin shirye shrye.*

*DAN ALLAH! Ayi subscribing, Akuma dinga viewing, Inda hali ma ayi comment da sharing zuwa ga wanda basu sani ba...*

*Akwai Facebook page dinta mai suna: https://www.facebook.com/preetyfeenat.abdullahi*

*Domin karin bayani sai a tuntub’i Nafisa kai tsaye ta number ta: *

*08071172003*

*kada ku mance ko minene daya danganci wakokin al’adun hausa, Da ire-iren fina-finan mu na hausa, Nafisa zata dinga kawo muku shi a wannan sabuwar channel din nata, Saboda haka MASOYA a temaka aje ayi mata subscribing a kuma dinga kallan abubuwan data dora.*.


____________

No. 60

 ..........Koda Yoohan ya dawo ɗakin bayan awanni kusan biyu da fitarsa bai tada Aymah dake kudundune cikin bargo tana barci ba. Wanka yayi, yay shirinsa tsaf na fita asibiti. Turaren hannunsa ya ajiye dai da ring ɗin wayarsa. guntun tsaki yayi tare da ɗaukar brush ya nufo inda take yana kwantar da sajensa. Sai dai kuma ganin wanda yay kiranne ya sakashi ɗan waro idanu waje ya dafe goshinsa. Zama yay a bakin gadon dai-dai da katsewar kiran. Shine ya kirashi zuciyarsa fal takaicin tsakin da yayi. Koda baba malam yaga shigowar kiran da ga can murmushi yayi kawai ya ɗaga suna kallon juna da Umm dake a kusa da shi. Cike da girmamawa Yoohan ya shiga gaishesa. Shiko yana amsa masa da kulawa. Sunɗan taɓa hira da duk Yoohan ke ƙarajin ƙaunar Baba malam. Dan duk akan abinda zai amfani rayuwarsa ne suke tattaunawar. Daga bisani suka dawo da firar tasu akan Aymah. Hannu Yoohan ya kai ya janye bargon data rufe har fuskarta a hankali, dan ya gama fahimtar wannan ɗabi'artace na lulluɓa da bargo har kanta. Lumshe idanu ya ɗanyi ya sake buɗewa a kanta, dai-dai yana amsama baba malam da cewar, “Uncle babu wani damuwa yanzun kam. Gata nanma tasha magani tana barci. Sai nan da kamar awa uku zata tashi insha ALLAH”. Murmushi yayi mai ƙayatarwa saboda jin abinda baba malam ɗin yace daga can. Ya sake kai hannu akan girar idon Aymah ya shafa yana sakin murmushin da har haƙoransa suka bayyana. “Uncle ai zata daina watarana. Yanzunma ƙuruciya ce kawai, kowa dama da irin tasa. A dalilin aikin ma gashi yanzu tayi sanyi sosai. Duk ta zama shiru-shiru”. Faɗaɗa murmushinsa ya sakeyi sosai saboda amsar da baba malam ya sake bashi. Daga haka suka gaisa da Umm sannan yay musu sallama ya kashe.
        Ranƙwafawa yay akan Aymah ya sumbaci kuncinta da saman ido. Bargon ya sake gyara mata yanda bazata rufe fuskarba sannan ya miƙe ya karasa kimtsawa yaɗan mata short note ya ajiye mata da wayar ya fice. 

                    X★x*x★X
      
Sosai Nu'aymah tasha barcinta. Bata farka ba sai bayan a wanni uku da fitar Yoohan kamar yanda ya ambata. Taji daɗin barcin sosai. ta miƙe tanata faman ɓata fuska irin ta wanda ya tashi a barci. Wanka tayo da ruwa mai ɗumi. Ta buɗe Wadrobe zata ciri kaya tajita gam. mamaki ya kamata da takaici ganin rufewa yayi. ƙunƙuni ta fara tana faɗin, ‘Gaskiya wannan mai jajayen kunnuwan yama rainani. Nasan maganinsa ai ALLAH kuwa. Sai yasan yayi da ƴar Umm da baba malam’. Ta ƙare maganar tana huci kai kace wani uban laifi akai mata. Har ta nufi gado da fushi sai kuma ta dawo da baya. Ɗayan murfin Wadrobe ɗin ta buɗe. A mamakinta sai taci karo da akwatin nasu anan. Shi ta buɗe tana ƙwafa da faɗin, ‘Na rantse akan kayanka zan huce takaicina. Dan sakasu zanyi naita birgima a ƙasan ɗakin nan har sai sunsan niɗin Zainabu ce jikar Zainabu Abu hajjaju Hajjo matar malam Hashim ɗan jibiy.......’ ta kasa ƙarasawa sabida cin karo da wata leda da tayi a gefen akwatin. Ɗauka tayi ta buɗe ledar tare da zazzago kayan ciki. ‘Ikon ALLAH sai kallo. shiko wannan bawa mi yake nufi dani dazai ajiyemin waɗannan kayan kamar ɗiyar tsuntsuwar sama jannati? Shin wai nufinsa ni jikar ɗan jibiya ce zansa wannan a tsokani shari'ar komi?, dama shiyyasa yaƙi ɗakkomin kaya sai wani jallabiya guda biyu dan tsabar ya maidani doll’. Tai maganar tana ɗaga wandon da bazai wuce rabin cinyarta ba. Ajiyesa tai ta cigaba da ɗaga sauran ma. Duk da bawani na fidda tsiraici bane sun bata haushi. Dan ba saba saka irin waɗanan ƙananun kayan tayiba a gida. Wani lokacin ko wando da riga ta saka sai Umm ta korata ta ɗora after dress a sama inhar zata fita daga sashensu. Mansa ta ɗauka ta shafa tanata cika baki da iska. Sosai takema man shafawar matsar mugunta. Wai shima sai yaji a jikinsa tunda ya saya mata waɗanan fingalallun kayan kamar wata ƴar tsana. To wlhy tunda ya raina mata jiki saita ta narkar abinci ta zama ƙatuwa kafin subar ƙasar nan. Sai tama aljihunsa ɗibar karan mahaukaciya (Danƙari. To kaji Yoohan talautaka za'ai a ƙasar Austria🤣).
         Haka tasa kayan tana mita. ta ringa zazzagama jikinta turarensa wai shine target ɗin farko da zata fara. A gaban ƙaton mirror ɗakin taje ta tsaya tana kallon kanta. Ta wani riƙe ƙugu tana faɗin, ‘Woow na kumafa haɗu’ tai maganar tana jujjuyawa. ‘Yauwa nama tuna. Bara nayi yanda naga matar jiya tayi’ ta faɗa tana tattare ƙasan farar top ɗin tata ta ɗaure a gefe. Hakanne ya bama ɗingilis ɗin wandon nata kalar blue na jeans damar fitowa sosai. ‘Tab, wlhy su Umm an haifo baturiya ba'a saniba. Hummm inama zan haɗu da hajjo yanzun. Nunawafa zanyi bamma santa ba, dan saina gama folata irin nifa bamma san African ɗinnanba sannan’. Ita kanta abun sai ya bata da dariya. Ta ƙyalƙyale kuwa da ita kamar dai har yanzun kan da motsi😂.
         Haka taita shirmenta ita kaɗai harta gaji ta bari taje ta gyara gadon da kanta. A wajen gyaranne taci karo da note ɗinsa. Koda ta gama karantawa saita murmusa. Wayar daya ajiye ɗin ta ɗauka ta nufi ƙofar da taga sun fita jiya ta danna yanda taga yayi da zai rufe. a take kuwa labulen ya zuge. Ta sake dannawa ƙofar glass ɗin itana ta buɗe. Farar ƙafarta dake a cikin blue Slippers ta zira waje tana wani zuƙar daddaɗar iskan wajen. Barandan ta ɗakinne kawai, hakan yasa taji ta ta sake dan babu ruwan wani da wani. Sannan anyi iyakar da waɗanda ke maƙwaftaka da ɗakin bazasu gantaba, kamar yanda itama bata ganinsu sai ainahin birnin Vienna da kuma harabar hotel ɗin da ƙaton swimming pool yake. Shima sai idan ta miƙene a jikin ƙarfen barandar zata iya ganin masu hutawa na wanka, wasu kuma suna zaune a kujeru ana zuƙar drinks.
      A ɗaya daga cikin kujerar wajen ta zauna, ta ciro buk ɗaya dage cikin ɗan kantan wajen ta ajiye sannan ta hau ƙoƙarin kiran su Baba malam cike da ɗoki. Kamar kuwa jira sukeyi, tana kira ring baifi uku ba Umm ta ɗaga. Dan baba malam yana wanka a lokacin. Cike da ihun murna ta farama Umm magana. Itako daga can sai dariya take da jinjina wauta irin ta ɗiyar tata. Dan ita ta tabbatar ba kuruciyace kawai ke ɗawainiya da Aymah ba. Akwai tsantsar wauta tattare da ita. A dai ƙasar hausa mai shekaru irin nata ai budrwace cikkakkiya kowa ya sani. Biye mata tai ko tanata faman bata labarin haduwar hotel ɗin da suke, da gine-ginen garin Vienna. Harda cewa Umm bara ta katse ta kira video call wai dan ta gani. da sauri Umn tace, “A'a shugabar rawan kai na gode. Nima ai nazo na gani da idona”.
       “Yo Umm ai dai bakiyi yawoba” tai maganar cike da shagwaɓa. Dariya Umm tayi da faɗin, “ALLAH ya shiryeki Nu'aymah. Ga Abbanki nidai barni na hutama raina. Ga autana can kwance yana fama da zazzaɓi bara naje naji da shi”.
        A take kuma sai mood ɗin Aymah ya canja jin abokin faɗa babu lafiya. Duk sai ta marairaice kuma har ma abin ya bama Umm da baba malam dariya. Haka dai ya amsa shima ta zuba masa shiriritarta. Sai da yace ta kashe wayar haka karsu ƙararma Yoohan da kuɗi sannan sukai sallama bayan anbama Muhammad shima sun gaisa, duk da a kwance yake bayajin dadi. Daga haka Hajjo ta kira. Itama suka gaisa. Badan tasoba ta haƙura ta ajiye wayan ta ɗauki buk ɗin data ɗauka ta fara dubawa. 

         Haka Nu'aymah ta kasance ita kaɗai a wannan yini. Duk da gargaɗin karta zauna da yunwa da Yoohan yayta mata bataji ba, sau kusan uku ma'aikatan hotel ɗin na kawo mata abinci amma sau ɗaya taci. Da lokacin shan maganinta yayi kuma tasha kamar yanda ya rubuta mata a note ɗinsa. Novel ɗin data samu ne ya ɗauke duka hankalinta. Dan shi taita karantawa. Salla kawai ke sakata ajiyewa. Bata damu ba da rashin dawowar tasa. Tunda ya rubuta mata uzirinsa zaije ya ƙaraso yau gaba ɗaya shiyyasa. Kuma ya bata haƙuri akan barintan da zaiyi ita kaɗai ɗin. 
      Lokacin shan maganin darenta nayi taci abincin da aka sake kawo mata kaɗan tasha duk magungunanta tai wanka. Kwanciya tai tana cigaba da karatun buk ɗin har barci yay awon gaba da ita.

     A haka Yoohan ya shigo a matuƙar gajiye ya isketa. Ya zauna a bakin gadon yana kallonta. Hannu ya kai ya zare buk ɗin data rungume a ƙirji a hankali. Motsawa tai, tare da buɗe idanunta da ƙyar ta kallesa. Batare datayi maganaba tai luu dasu ta maida tarufe kayanta tare da gyara kwanciya. 
       Idanu kawai ya lumshe shima ya buɗe akan buk ɗin. Batare da yace komaiba ya ajiye ya miƙe domin yin wanka.
        Har ya kammala dukan hidimarsa Aymah nata barcinta. Bai tadataba kuwa yay shirin barci shima tare da sallolinsa da suka rage ya hawo gadon ya kwanta dan a matuƙar gajiye yake. Addu'ar barci yay musu ya rungume matarsa suka lula duniyar barci mai daɗi.

*_WASHE GARI_*

         Yau ma kamar jiya bayan sallar asuba sunyi zaman karatu. Koda suka idan tasha magani shi kuma ya fita motsa jiki. Da ya dawo ma ya sameta tana barcin. Wanka kawai yayi ya fiddo lap-top ya fita ƴar barandar Aymah ta jiya bayan yayi order ɗin abinda zaici. Acan ya shafe tsahon lokaci har Aymah ta tashi a barcinta. Ganin baya ɗakin tai tunanin ko ya fita. Wanka tayo tazo ta shirya cikin sauran kayan jiya. Yau dai wando ne ta saka yellow da black t-shirt. Tayi ƙyau yauma sosai, ta gyara gashinta tana ɗan yatsina fuska ganin yana bukatar wanki. Badai tayi maganaba dan bason a taɓa mata kai takeba daman. Kobi takan abincin data gani batayiba. Ta ɗauki buk ɗin jiya dake a durowar gefen gadon ajiye ta nufi wajen zamanta na jiya. Kasancewar ya rufe yasa bata fahimci yana a wajenba sai da ta fito.
        Yoohan dake zaune a kujerar ya ɗora ƙafafunsa bisa table ɗin, lap-top a saman filo daya sa kan cinyarsa yanata aikinsa ya ɗago idanunsa jin sabon ƙamshin turarensa data bunkuɗa a jiki. Suna haɗa ido ta turo baki gaba tana kauda fuskarta.
     Baiyi maganaba shi dai. Bai kuma daina mata kallon ƙurilla ba, dan kayan sun matuƙar mata ƙyau, kodan yau ne ya fara ganinta a cikin irinsu oho. duk da kuwa yana bala'in son yaga tayi shigar Hausawa dan tana masa ƙyau. Amma yauma dai tayi irin ƙyawun da yake buƙatar ganinta a ciki.
        Haɗiye abinda ya tsaya masa yay a maƙoshi yana furzar da nannauyan numfashi. Yanda yayi ɗinne ya saka Aymah dake tsaye kamar an dasata kallonsa. da alama kunyace ta hanata motsi kokuma ganin da tai masa a wajen a bazata. Saurin janye idanunta tai ganin har yanzun kallonta yakeyi. Harga ALLAH ita tanajin nauyin ganinsa da kaya irin waɗanan. Rigace armless fara tas a jikinsa, sai wando dako cinyarsa bai gama rufewaba oxblood. Duk da lap-top ɗin daya ɗaura bai hanata ganin farare cinyoyinsa da gargasa suka kwanta ba.. Cikin sanyin muryar da baisanta da ita ba tace, “Good afternoon”.
    Idanunsa yaɗan lumshe ya buɗe a kanta. Sai kuma ya maida ga lap-top ɗinsa yana faɗin, “Same, How are you?”. Hararsa tai ta gefen ido saboda jin yanda ya amsa gaisuwar. Da tamayi niyyar komawa ciki, amma yanda ya amsa matanne ya sakata takowa ta ƙaraso inda yake. Kujerar taja itama ta zauna tanata wani faman haɗe fuska irin batason wargi din nan.
      Duk abinda takeyi Yoohan na kule da ita. Sai faman ƙoƙarin danne dariyar dake taso masa a rai kawai ya keyi. Aikinsa ya cigaba da yi ita kuma ta karatun novel. duk da kuwa bama karatun takeba satar kallonsa kawai takeyi tana gulmarsa a zuciya. Tunda ya fahimci kallonsa takeyi shima sai ya kasa ci gaba da yin aikin. Saboda tsabar neman magana ya tura ƙafarsa ya tanƙwaɓe littafin nata ya faɗi. Ya kuma fiske abinsa yaƙi kallonta tamkar bashi ne ya aikata ɗin ba. 
      Ƙara tsuke fuska tayi tanabin buk ɗin dake yashe a ƙasa da kallo, ɗan bakin kuwa sai motsawa yake amma ta kasa magana. Cike da takaicin daya kumeta ta ɗauki filo ta maka masa a ƙafa harda cije baki.
       “Ouch!” ya faɗa yana saurin janye ƙafarsa. “Silly girl!. Wane mugunta ne haka? Mina miki?”.
        Harara ta balla masa. batare da tace komaiba ta duƙe zata ɗauki buk ɗinta. Sai dai kuma hannunta bazai kaiba dole sai tazo ta gabansa. Fitowa tai tazo har inda littafin yake. ta ɗauko harma ta miƙe zata koma inda take ya saka mata ƙafa. Sai ko gata a kan cinyarsa ɗare-ɗare.
        Mutsu-mutsun ƙwace jikinta ta fara ya saka hannayensa yay mata zobe. Duk yanda taso ta motsa kuwa sai ta kasa. Sake kumbura baki tayi da ƙyau, dan haka kawai ta tuno randa ya taɓa rungumeta a gidansu har Aunty Kubrah ta gansu.
          Kansa ya ɗora bisa kafaɗarta yana busa mata numfashinsa. Cikin magana raɗa-raɗa yace, Silly girl, K ba'a zama lafiya da ke sai kinja faɗa ko?”. Wani shegen mintsini ta bashi a cinya wanda ya sakashi sakinta babu shiri. Miƙewa tsaye tai daga jikinsa tana masa gwalo. Yanda ya ɓata fuska kamar zaiyi kuka ya sakata ƙyalƙyalewa da dariya tana nufa hanyar ƙofa. Yatsu biyu ta ɗaga masa, ɗayan hannunta riƙe da ƙugunta tace, “Wannan na yadda buk ne na maka. Saura na......”
     Ganin ya miƙe ya sata kwasa da gudu tai ciki batare data ƙarasa faɗaba. Baya ya rufa mata har cikin ɗakin. Nanfa suka shiga zagaye ɗakin. Duk yanda yaso kamata taƙi tsayawa, duk da dai da alama ya barta ne kawai. Ganin yanda yake hakki da nuna matuƙar gajiya ya saka taketa ƙyalƙyala masa dariya tana masa gwalo. Harda yin yanda yara keyi na tsokana. Tana saka yatsunta a kunne da jujjuyasu tana masa gwalo. 
      Shiko ƙara narkewa yake irin shifa ya gaza kamata. daga ƙarshe ma ya faɗa saman gado yana hakki da faɗin, “Silly girl”.
     Zuwa tai har inda yake kwance ta shuri ƙafarsa zata gudu. Dama tarko ya mata. Yako harɗota da ƙafar sai gata a jijinsa. Da dai taga da gaske an kamatan saita fara kukan ƙarya tana kai masa ƙananun duka a ƙirji. Dariya ya farayi ya haɗa duka hannayen ya riƙe tare da juyata akan gadon ya koma kanta. “Wana kama to yanzun?”. Ya faɗa yana busa mata iskar bakinsa a kan idonta dake hawayen ƙarya.
      Baki ta sake kumburawa tana matso hawaye. “To bakai ka fara tsokanata ba. Ni dai dana fita ai banma kulaka ba amma ka takaleni”.
       Ƙanƙance idanunsa yay da ɗage gira sama. Yace, “Yarinyar nan kin iya sharri. A yaushe na tsokanekin?”.
       “Na rantse da ALLAH kai ne ka fara tsokanata, kuma bazan ƙyaleka ba sai na rama”. 
      “Da gaske?”. Ya faɗa a hankali yana sake matsar da fuskarsa dab da tata har hancinsa na gogar nata. Cikin sarƙe idanunsa cikin nata ya sake faɗin, “Yaushe zaki daina rashin ji ne?”.
         Duk yanda taso bashi amsa ta kasa. Saboda goga mata lips ɗinsa da ya farayi akan nata. Tai ƙoƙarin kauda kanta gefe, yay saurin tarewa da nashi yana faɗin, “Uhmyim?. Faɗamin yaushe zaki san kin girma?”. 
     Ba ƙaramin harbawa zuciyar Aymah tayiba saboda jin a yanda yay maganar, kafin tai wani yunƙuri ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Tabbas yau kam tamafi ranar shan chocolate, dan Yoohan ya tabbatarma Aymah a matuƙar zalame yake dason kasancewa da ita. Duk yanda yaso sassauta mata ya gagara, sai da ya ɗora mata sabon salon karatunsa mai wahalar haddacewa.
       Gaba ɗaya kukan da taso masama sai ta nemesa ta rasa, sai wani irin tsoro da matsananciyar kunyace da bata taɓa karo da itaba a rayuwarta ta lulluɓe ta. Tunda ta samu ya barta ta tura kanta cikin filos bata sake yarda sun haɗa idanu ba. Sun kwashe mintuna talatin a kwance kafin taji ya sake matsota. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yayi ba jin ya kwanto a bayanta. Amma sai ta daure tana ambaton sunan ALLAH. 
         “Akwai matsala fa”. 
   Ya faɗa a cikin kunnenta yana tura hannunsa a rigarta. Saurin riƙe masa hannu tayi ta zabura zata matsa yaƙi bata space. Dole ta haƙura sai daifa mutuniyar taku tsorone fal cikinta. 
       “Kin jamin sai nayi wanka, kuma ni ban iya ba”.
        “Hu'um. wankan ne baka iyaba? Babu dai ƙyau manya na ƙarya”. Tai maganar da son jan jikinta. Saurin sake ruƙota yayi ya matse. A kunnen nata Yace, “Bafa normal wanka bane, Uncle ya sanarmin a addinin musilinci wanka ya kasu kashi da yawa. *_Fitar maniyyi kai tsaye, ta hanyar jin dadi daga mace ko namiji. 2. Ɓoyewar kan azzkari a cikin farji. 3. Idan mutum ya mutu ya wajaba ayi masa wanka, sai dai in shahiɗi ne. 4. Musuluntar kafiri ko wanda ya yi ridda. 5. Jinin al’ada. 6. Jinin biki (wato jinin haihuwa). 7. Wankan jumu’ah. 8. Wankan shiga harami (da hajji ko da umarah). 9. Wanka ga wanda ya yi wa mamaci wanka,  Wankan idi biyu (na zuwa karamar sallah da babbar sallah). 10. Idan mutum ya farfado daga hauka ko 
farfadiya. 11. Wankan shiga Makkah.
12. Wanka domin sallar kisfewar wata ko kuma rokon ruwa. 13. Wanka na mai istiha a kowacce sallah. 14. Ga kowanne jima’i an so a yi wanka._* &#0;kinga kenan yanzunma sai nayi fa tunda kin sakani na fitar da......”
     Wani irin wuntsilowa Aymah tayi ta dafe masa baki tana faɗin, “Na shiga uku ni Zainab, ni dai wlhy babu ruwana”. Ta fashe masa da kukan taɓara.
        Wani mugun dariya ne yaji yana taso masa. Amma sai ya danne da ƙyar dan karya ƙara tunzurata a samu matsala. Hannu yasa ya janye nata dake akan bakinsa. Fuskarta kuma har yanzu tana a ɓoye. “Okay yi haƙuri bake bace nine. Yanzu dai kisan yanda zakiyi dani lokacin salla yayi”.
        “To ni ya kakeso in maka?”.
   “Ki koyamin”.
Tamkar zata fasa masa sabon kuka tace,  “ALLAH ya sani nama fasa zaman hutawar ka maidani Nigeria kawai tunda na warke”.
      Shi dai dauriya yaketa yi dan kar yay dariya matsalar tafi haka. yace, “To naji, yanzu dai tashi muje ki koyamin yanda zanyi wankan”.
       “Ni dai babu inda zanje, idan kanaso na koya maka a haka kaje kayi abunka”. 
       “A'a gaskiya, sai dai fa kiyimin practical zanfi fahimtarki. Haka ake malami yayta ragema ɗalibi mudun koyarwa”.
       Shiru tayi taƙi motsawa, taki kuma tanka masa. ya tashi zaune yana faɗin, “Okay shikenan, bara kawai na kira Uncle saina sanar masa abinda ya faru daga nan ya koyamin yanda zanyi wank.......”. Zaune ta tashi dingangan ta ɗare masa jiki da danne bakinsa da hannunta tana waro idanun dake cike da ƙwalla.
       “Yanzu dan baka da kunya sai ka kira Abbana ka sanar masa wannan abun?”. Hannunta ya ture yana marairaice fuska shima. “To yaya kikeso nayi ne Sweet girl? Kinga dai babu damar nayi salla babu wankan nan? Kema kanki nasan fa sai kinyi”. Ya kai ƙarshen zancensa da kashe mata ido ɗaya. Filo ta jawo ta maka masa a hannu sannan ta sauka masa a jiki tana ƙunƙuni. Duk yanda yaso danne dariyarsa ta gagara sai da yayi abinsa. 
        Itako data sauka a gadon sai masifa takeyi a ranta tana sharar ƙwallan da babu tantama najin kunya ne. Shi dai Yoohan ganin ya samu yanda ya keso tasowa yayi ya biyota inda ta koma ta zauna akan sofa tana sharar ƙwalla. Ɗaukarta yay cak zuwa bayin tanata wantsala ƙafafu da faɗin ita ya sauketa. Tama fasa koyawar yaje yay Searching a Google ai zai gani. Ko jintama shi bayayi sai da ya direta cikin wajen wankan, zata gudu yay saurin kunna shower ɗin. A take tai musu jalab da ruwan data sheƙo. Ya jawo hannunta ta dawo saman jikinsa. Jin santsin ruwa zai jata ta faɗi dole ta rirriƙesa ruwan na sauka musu a jiki. Da wannan damar Yoohan ya kafe gaban rigarta daya jiƙe da ruwa komai ya fito yanda ya kamata da kallo. Bata fargaba sai da taji hannunsa a wajen. Ƙasa tai da sauri tana ture masa hannu. A ranta kuwa al'amarin sake firgitata yakeyi. ƙara ƙarfin shower ɗin yayi, hakan yasata tilas ta sake miƙewa tana sharce ruwar dake sakko mata a fuska ko gani da ƙyau yana neman hanata. Numfashi ma takai da baki take firzarwa. Shi kansa ruwan ya masa yawa. Amma saboda karta gudu yay haƙuri yana saka hannu yana sharcewa kamar yanda takeyi itama. Sai da ya tabbatar sunyi jagab sannan ya kashe shower ɗin. Ya koma hanyar ƙofar wajen wankan ya tsaya. A mamakinta sai gani tai ya fara cire rigarsa. Ƙasa tai da kanta gabanta na faɗuwa. Ganin wandonsa ya saɓulo ƙasa ta ƙara kiɗimewa. Da sauri ta juya bayanta. Hakan ya bashi damar matsawa ya manna bayanta da ƙirjinsa. 
      “Karki zama malama mai yima ɗalibanta rowar ilimi fa”. Yanda yake maganar yana yawo da hannunsa akan cikinta sai ya nema sake susutata. Tama rasa tunanin da zatayi akan wannan al'amarin nasa mai wahalar fashin baƙi. Tanaji tana gani yay amfani da ƙarfinsa wajen zame mata riga da wandon jikinta. Sai dai fa duk yanda yaso cire harna cikin taƙi yarda sam. daga ƙarshe ma sai ta saka masa kuka. Ƙyaleta yayi ganin dai ankai inda ma baiyi zatoba. A haka ta fara ƙoƙarin koya masa wankan duk dan ta samu ta kuɓuta daga wannan dabaibayin da yayma rayuwarta baki ɗaya.
      Sai da tai nisa a koyawarne ta fahimci ya iya, dama ashe kawai danya bata wahala da kallar mata jikine ya sashi cewa ta koya masan. Wannan haushin ya sakata harya ƙarasa wankan ya fita ya barta dan taki yarda tayi ita tana antaya masa harara. Duk da ƙaryar datai masa na cewar babu wani wanka daya hau kanta yana fita kuwa sai da tayisa. Dan duk wautarta tasan abinda takeyi tunda tanada ilimin addini. Aiko dai ansha ƙunƙuni. Tana cika baki da iska ta miko hannu akan ya bata Bathrobe da towel, dan yana a bayin bai fitaba. 
      Hand dryer ɗin hannunsa ya ajiye. Ya ɗauki rigar wankan ya kai mata sai dai babu towel. Hannun nasa ma sai da ya sha harara sannan ta amsa. Ganin babu towel ɗin kuma taita ƙunƙuni. Koda ta fito kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta ganin daga shi sai towel iya ƙugu zuwa gwiwa. Shiko gashinta dake ɗigar ruwa yabi da kallo. A cikin ransa dariya ya sanya mata yana faɗin, ‘Yarinya ashe kinada lafiya tunda saƙona ya isa inda na aikashi?’. A fili kuwa sai ya fuske abinsa. Tai saurin ɗaukar towel ta naɗe kanta wai dan karya gani.
      Ƙarasa hidimarsa yayi ya fito ya barta. Koda ya fito mai ya shafa yay shiri cikin ƙananun kaya. Baƙin wando da pitch color ɗin shirt mai dogon hannu. Yana fesa turare ta fito.  
       “Kiyi shirin fita”. Ya faɗa yana ajiye turaren.
     Bata tanka masaba. Tai tsaye har sai da ya matsa a wajen sannan ta buɗe akwatin nasu ta ɗauki jallabiya ɗaya. Bayi ta koma ta sanyo sannan tazo ya jasu salla. Suna idarwa yace ta ƙarasa shirin yana zuwa.
       Fita yay, ita kuma ta miƙe ta shafa mai, da ƙarasa kimtsawa. Tana gamawa kuwa yana dawowa. Zata fara feshi da turarensa ya amshe yana faɗin, “Silly girl ya isa haka dan ba tallanki nazo yima Austrian ba”.
     Ita dai bata tanka ba. Bakuma ta yarda sun kalli juna ba dan wannan fushin da takeyi tsabar jin kunyarsace kawai ke ɗawainiya da ita.
        Tsaf suka fito abinsu gwanin sha'awa. Tamkar ka sacesu ka gudu. idan ka gansu sai ka ɗauka ƙaramar ƙansawarsa ce ma. Yau dinma bata cuci kantaba sai da taita kalle-kalle har suka fito ƙaton reception ɗin hotel ɗin. Zuwa yay yayi signing kamar yanda dokarsu take. Daga haka yaja hannunta suka fito............✍


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 61

...........Da Solomon sukaci karo a jikin wata dalleliyar mota tsaye. sai baturen dake cikin Uniform ɗin hotel ɗin. Da girmamawa Solo yake gaisheta da sake tambayarta ƙarfin jiki. Cike da takaicin zamantowarsa tamkar jelar Yoohan ɗin ya sakata amsawa a taƙaice. Yoohan ya buɗe mata da kansa ya taimaka mata ta shiga. rufewa yay, ya zagaya inda baturen ya buɗe masa shi kuma ya shiga. Baturen ne ya shiga a matsayin driver, Solomon kuwa gefensa. wannan abu ya zafi Nu'aymah a rai. Kenan duk inda mijin nata yake dole wannan basamuden sai ya kasance da shi?. Dolene tasan matsayin wannan bibbinin kuwa. Galla masa harara tayi lokacin da drivern ke harba motar a titi suka fice daga harabar hotel ɗin.
        Idanu Yoohan ya lumshe da jingina kansa da kujera. Ya saki ajiyar zuciya, a ransa yana ayyana ‘hakan shine kawai mafita a gareni. idan ba ɗan fitar mukaiba bazan iya barin yarinyar nan ba. komai zan iya aikatawa kamar yanda zuciyarsa ke bani ƙwarin gwiwar game da ita’.
          Nu'aymah dai ta fahimci motar hotel ɗince ya ara. Sai dai batasan ina suka nufaba. Dan haka ta ware idanu da ƙyau tana sake kallon tsarin garin na Vienna da ya gama haɗuwa da ababen more rayuwa kala-kala. Duk da ranta cike yake da taikaicin tafiya tare da Solomon, kai harshi kansa Yoohan ɗin haushinsa takeji akan Solo.
         Sun fara zuwa wani haɗaɗɗen wajen Saloon, bata fahemci hakanba kuwa sai da suka shiga ciki. Ta kallesa tana yamutse fuska, “Mi zamuyi anan?”. Kallonta kawai yake shidai fuska a tsuke shima. Dan shi kaɗai yasan a halin da yake ciki. Sai dai yana mamakin miya ɓata mata rai haka? Ya fahimci tun fitowarsu cikin hotel ɗin wajensu Solo ta ciskule fuska, saɓanin farko da kunyarsace kawai tattare da ita.
      Bai bata amsaba, sai ma ma'aikatan wajen da sukazo musu tarba ta mutuntawa. Da Garman language yay musu bayanin abinda suke buƙata. Hakan yasa Aymah bataji komaiba. Saima mamakin dama yanajin yaren data fahimci mafi yawan ƴan garin sunfiyi kenan?. Bata da mai bata amsa, sai jan hannunta da ma'aikaciyar tayi zuwa sashen mata. Binsu yay har ciki, shine ya zaɓa duk abinda za'ai mata. Nu'aymah dai ta zubama sarautar ALLAH ido tana kallonsu. Shiko yaƙi yarda su haɗa idon. Yana gama zaɓa ya biyasu kuɗinsu. Sai shi kuma ya nufi na maza dan yana buƙatar gyaran fuska da yankan farce.
         Haushi ya hana Aymah yin magana har aka fara wanke mata kanta. Ganin babu kitso dai yasa bata damuba. An mata wankin ƙafa da gyaran farce, sannan aka kaita wani ɗaki wai na gyaran jiki ne. Nu'aymah dai taga abinda ya girmeta, har tsoron shiga waɗan nan injina ta ringayi, a ganinta idan aka ɗauke wuta mutum na ciki kuma ai shikenan labarinsa ya ƙare. ‘Kai wannan mutumin ba kawoni yay kuwa a markaɗeniba ma?’ ta aiyana a ranta tana ƙunƙuni da hausa. Su dai ma'aikatan ba jinta sukeba. Hakan yasa suketa aikinsu kawai. Anyi mata gyaran jiki na musamman da ita kanta tasan eh ta gyaru ƙwarai da gaske. Aka kuma kaita wani waje wai tausa nankuma za'ai mata. ‘Babbar bala'i’ ta faɗa a fili cikin suɓutar baki. ‘Amma wannan mai jajayen kunnen ya gama sakamin rayuwa a gaba. Yoni nace masa ina buƙatar duk wannan ne ko mi?’. Haka taita zuba mita ana mata tausa. gashi kuma sai faman lumtse idanu takeyi alamar tanajin daɗin jikinta. Bayan kammala tausan an maidata wajen gyaran jiki, daga haka aka ƙarasa gyara mata kanta. Haɗaɗɗun wando da riga aka kawo mata ta saka ƙyautar da shagon ke badawa kenan idan suka maka aiki mai tsada irin haka. Badan taso ba ta amsa ta saka. Ta yana gyalen jallabiyar ta akai suka fito inda Yoohan ke zaune yana jiransu. Dan shi tuni an kammala masa.
         A tare suka zubama juna ido. Kowanne yana zancen ƙyawun da ɗan uwansa yay masa a zuciya. Sake tashi hankalin Yoohan yayi matuƙa, wata sabuwar buƙata da tafi ta farko sai ƙara bijiro masa takeyi. Nannauyan numfashi ya furzar da yin luuu da idanunsa da launinsu na fari ya sirka zuwa ja. Sai da ya lumshesu sannan ya sake buɗewa akanta. Da ƙyar ya iya miƙewa tsaye zuwa gareta. Ita dai kanta a ƙasa tun kallon datai masa na farko da yaba ƙyawun da gyaran fuskar da yay yayi masa, dan an canja masa style ɗin sajensa. bata ƙara yarda ta dubesaba saboda kallon ƙurullar data ga shima yana mata. Hannu yasa a hankali ya zame gyalen daga bisa kanta yana kallon gyaran gashin nata. Ya kama jelar gashin dake ɗaure a tsakkiya ya murza cikin hannunsa tare da shaƙar ƙamshin da gashin keyi. Duk yanda yaso furta wani abu a harshensa ya kasa hakan....
        Maganar ma'aikaciyar wajen ce ta katsesa daga ƙoƙarin kamo fuskar Aymah da yayi niyyar yi. Ya juyo yana kallonta. Bag ɗin hannunta mai tambarin wajen nasu ta miƙama Nu'aymah fuskarta da murmushi tai musu godiya na zuwa masana'antarsu. Guntun murmushi Aymah tayi mata kawai ta amsa. Kallon jikkar yayi ya maida dubansa ga matashiyar matar. Yay mata tambayar da Aymah batasan ta minene ba, kai kawai ya gyaɗa mata da kama hannun Nu'aymah suka fito Reception, wata hanya sukabi bayan taga ya karanta rubutun wajen da ita dai ba ganewa takeba tunda ba turanci baneba. A shagon kaya ta gansu, yanda baiyi maganaba itama batayiba. Sai hannunta daya riƙe yanabin kayan da kallo. Yayinda ma'aikatan wajen ke musu barka da zuwa. 
         Kujera aka bata ta zauna shi kuma yana duba abinda yazo nema. Kallon shagon ya ɗaule mata hankali har batasan dami-dami ya ɗaukaba. Sai da yazo gabanta da riga a hannu ne ta kallesa. ya kamota ya miƙar tsaye yana magana a hankali. “A ƙasar mutane ma sai kin nuna ke bakanuwa ce?”..   
       Harararsa tayi dai-dai yana kamo hannunta ya zura mata hannun rigar coat ɗin ta mata data gama haɗuwa sai wani irin shegen ƙamshi takeyi. Bakinsa ya taɓe ya kamo ɗayan ma ya zura mata ya gyara mata rigar da ƙyau. Takai mata har gwiwa kuwa, hakan yasa ta rufe mata jikin yanda yafi buƙata, dan yaji a ransa bazai iya barinta yawo da kayan da wajen saloon ɗin suka bata ba.
      Ta ƙara ƙyau kuwa sosai masha ALLAH, shi kansa ya kasa ɗauke ido a kanta. Kuɗin abinda ya ɗauka ya biya suka fito a wajen. Inda suka bar su Solomon zaune a harabar wajen nan suka iskesu suna shan coffee. Solomon dake satar kallonsu ta gefen idi yace, ‘Yarinya sai shege ƙyau kamar aljana. Shiyyasa gaba ɗaya oga ya susuce a kanta’.
     Oho Aymah batasan yanayiba. Dan tuni ma ta buɗe mota ta shige ko jiran Yoohan ɗin ya buɗe mata yayi batai ba. Da kallo shima ya bita dan ya fara fahimtar kamar haushin Solomon takeji. Bai dai tabbatar ba, dan haka shima ya shiga motar. Su Solo ma duk shiga sukai suka bar wajen.
         A yanzunma da suka tafi kanta ta juyar tana kallon garin. Shi dai Yoohan nata kallonta ta ƙasan ido da nazarinta har suka ƙarasa wani garden ɗin hutawa. Wajene da masoya kawai ke kai kawo abin zaƙƙyau da burgewa. Sun bar su Solomon acan wajene, shi da ita kawai suka shiga ciki. Inda ya zazzagaya da ita wajejen abubuwan tarihi, sukai hotuna ta sha kallo kuma. Yoohan bai da kuzari gaba ɗaya. Yanata dauriyane kawai, dan a rayuwarsa bai taɓa jin matsananciyar sha'awa irin ta yau ba. Ji yake kamar idan bai akasance da mace ba zai rasa ransa. Itako Aymah gani take shegen miskilancinsa ne ya motsa kawai. Shiyyasa ta tattarasa ta watsar gefe. Ko abu ya faru sai dai taita ƙunƙuni a ranta da gulmarsa a zuciya. A waje sukai sallar la'asar, magriba da isha'i. Sun ɗanyi ciye-ciyensu da Aymah ke ganin wasu ƙazanta. Duk dan lokaci yaɗan ƙara ja sai da Yoohan ya bari tara na agogon ƙasar yayi sannan suka dawo hotel ɗin su.
        Masifaffen ciwon cikin daya taso masane ya sakashi cemata taje ciki yana zuwa zaije asibiti duba wani maralafiya. Bata damuba. Ta kwashi kayan da suka sayo tai ciki. Can ya samu ƙasan wani rumfar ya zauna dan dama babu asibitin da zaije. So yake taɗanyi nesa da shi ko zaiji sassaucin abinda ya keji game da ita. Sai dai kuma ina, rikicewa ma al'amarin ya sake neman yimasa saboda kaiwa da kawowa da matan turawan keyi ta wajen tamkar tsirara. Bai rufa mintuna ashirinba dole ya tashi a wajen ya nufi cikin ɗakin jikinsa na rawa.  

        Shigowarsa dai-dai da fitowar Nu'aymah da sanin bayama hotel ɗin gaba ɗaya ya sakata fitowa daga ita sai guntun towel iyaka cinya. Daga ita har shi turus sukayi. Aymah dai ruɗanin ganinsa babu zatone ya sakata ƙamewa waje guda ta kasa ko motsi. Shiko tashin hankalin halin da yake a cikine ya sakashi tsura mata idanu jikinsa na wani irin tsuma. Ya rasa wane kalar tashin hankaline yake ciki a yau shi kuwa?. 
     Sum-sum ta wuce gaban Wadrobe batare data ƙara yarda ta dubesa ba. Shima sai ya ƙarasa shigowa ya nufi bayin dan watsa ruwa ko zaiji sanyi a ransa da gangar jikinsa.
        Da sauri-sauri tai shirin barci. Sai dai doguwar riga ta saka ta tada salla dan basuyi shafa'i da wutiri ba. Tana yin sallamar shafa'i ya fito. Bata kallesaba ta miƙe zatai wutiri. Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa, “Jirani”.
     Da mamaki ta juyo ta kallesa. Sai dai tayi saurin ɗauke kanta ganin towel ne kawai a jikinsa shima. Jallabiya ya ɗauka ya zura a jikinsa yazo inda take. nuni yay mata data gyara tsaiwarta a bayansa. Zatai magana ya ɗan cije lip ɗinsa na ƙasa da girgiza mata kai yana yin luuu da idanunsa dake jajur kaɗan. Bata iya yin maganarba kuwa. haka ta bisa sukai salla raka'a biyu. Ya juyo ya dafa kanta yana karanta addu'ar da baba malam ya koyar da shi tun daren aurensu, kamar yanda kuma yay masa bayani dalla-dalla akan tsarin aure a musulince tun wancan lokacin,

اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.
*_Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh._*
       _Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa._
        Ya kuma ɗorawa da wasu addu'oin gwargwadon saninsa sannan ya miƙe yay shafa'i da wutiri da ƙyar. Itama wutirinta tayi. Bayan sun idar ne ta fahimci bashi da lafiya. Ƙulle masan da cikinsa yayine ya sakashi kwanciya ya ɗora kansa bisa cinyarta yana matse fuska. A rikice ta waro idanu waje tana tambayarsa, “Baka da lafiya ne?”.
        Bai iya ya bata amsaba. Sai hannunta daya riƙo ya matse cikin nasa jikinsa na ɗan rawa. Ruɗewa ta sakeyi ganin yanda yake zufa a goshi jikinsa na wani irin tsuma. Rungumo kansa tayi da ƙyau ajikinta ta fashe da kuka tana faɗin, 
      “Na shiga uku ni Nu'aymah. Yah Yoohan miya sameka? dan ALLAH ka tashi muje asibiti, ka tashi dan ALLAH ”.
        Duk da a halin da yake a ciki sai da ta bashi tausayi, yanda ta fashe da kukan kuwa har cikin ransa. Hannunta dake a cikin nasa ya ɗago da ƙyar ya ɗaura akan mararsa datai wani irin ɗaukar zafi dayin tauri ya danna. Zata ƙara magana ya manne bakinsa akan nata.
         Da farko Aymah tayi tunanin zafin ciwo ne ya sakashi aikata hakan. Dan jikinsa ƙara ƙarfin karkarwar data fi ta farko ya kamayi lokacin daya fara kissing nata. Sai dai fa ganin lamarin yana neman zarta wayonta ta fara ƙoƙarin turesa. Sosai hakan ya gagareta, ya bala'in birkice mata a namijinsa. Daga ƙarshema ɗaukarta yayi gaba ɗayanta zuwa gado. Duk kukan da take masa da son sauka a jikin nasa da alama ma bayajinta. Dan duk wanda ya duba Yoohan a wannan lokacin yasan sam baya a cikin hayyacinsa. Idanunsa kansu a rufe suke gam yama kasa buɗesu balle yaga halin ruɗani da tashin hankalin da Aymah take a ciki. Fincike kayan jikinta ya shigayi tana ƙoƙarin hanashi cikin kuka.
         Roƙonta shima ya shigayi cikin wata irin murya mai ban tashin hankali. “Please karkice a'a. Idan kika hanani kanki zan iya mutuwa Zeeynab. D....da....dan ALLAH N...u...ay...mah”. Duk da tashin hankalin da Nu'aymah take a ciki na fahimtar abinda yake shirin aikata mata sai da yanayinsa da yanda yake magana ya nema tarwatsa mata zuciya. Gaba ɗaya ya birkice mata kamar bashiba. Yanda take hawayen neman ceto da son ya barta haka shima hawayen neman agaji da taimakonta matsayin halalinsa ya keyi. A gefe kuma yana mata abinda tunda uwatata ta kawota duniya wani bai taɓa mata koda makamancinsa ba. Duk da ƙarancin shekarunta da shiririta tasan minene aure. Duk da bawai komai da akeyi a cikinsa ta sani gatse-gatse ba saboda yanayin tarbiyyar data tashi a ciki ta kulawar iyaye da rashin tarkacen ƙawaye.
        Duk da baya a cikin hayyacinsa sai da UBANGIJI ya bashi dama da ikon karanta,
         بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
*_Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana._*
     _Da sunan ALLAH. Ya ALLAH! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi._
        Kamar yanda aka koyar da shi. Lokacin da Aymah ta sake jin baƙon al'amarin da yafi komai gigitata fiye da duk abubuwan da yay mata a farko tuni sai numfashinta ya shiga neman shiɗewa. Kuka take iya ƙarfinta tana kiran baba malam da Umm suzo su taimaketa. Hajjo kanta da Muhammad sunsha kira. Kai duk ƴan gidansu ma babu wanda baisha kiran neman ceto ba hatta da Yah Ab da Nasir🤣, su Ananah kansu da su Gwaggo (kakarta data haifi Umm) sun sami nasu rabon. Tun tana haɗashi da ALLAH harta koma cemasa “Idan yana ƙaunar papa da Momy (Madam Chioma) yayi haƙuri, ta rantse tabar masa tsiwa bazata sake ba. Duk abinda ya keso zata dingayinsa. Ko ƴan gidansuma ta daina faɗa dasu, idan mutum ya mata abu zata barsa da ALLAH kawai😂😜. Na tabbata da ace Yoohan cikin hankalinsa yake babu abinda zai hanashi shan dariya da sumbatun shiriritar Nu'aymah. Tunma tana iya kukan da roƙo harta gaza bakin ya mutu ta tafi sumar wucin gadi........

Wannan lamari sai da tafiya hutun wucin gadi dan tausayin jikar ɗan jibiya😒😏🚶🏻.

*_ABUJA NIGERIA_*

     A firgice ta farka da ga razanannen mafarkin daya risketa cikin barcin daya ɗauketa bayan dawowarsu wani taron karammawa da akaima papa, kasancewar sa dattijon da akeji da shi a yankinsu. Sannan gashi babban Pastor da ba Nigeria kawaiba har wasu ƙasashen ƙetare yana baza komarsa. Wannan taron karammawa ya gudana ne a Abuja bisa jagorancin ƙungiyar Christians reshen catholic. An karamasu su bakwai. sai dai papa shine yafi kowa ɗaukar wannan jinjinar girmamawa.
       Ɗunbin gajiyar data samo acan ne ya saka suna shigowa gidan kaya kawai ta cire ta kwanta ko wanka bata iya samu tayi ba. A cikin wannan barcine tai gamo da mummunan mafarkin da ko'a labari bata fatan tabbatuwarsa. A zabure ta miƙe zuwa inda ajiyayyen asirinta yake na tsahon shekaru kusan goma sha uku. Rawa jikinta ya kamayi kamar mazari ganin ƙullin da akaima igiyar cikin tukunyar ya warware. Da sauri ta ajiye tukunyar a ƙasa saboda karkarwar da hannunta keyi gudun karta yaddata. Waya ta jawo a ruɗe tai kiran ƙawarta. Bugu biyu Madam Rebecca dake holewarta da wani yaro a gidanta dan mijinta baya ƙasar yana can harkar kasuwancinsa ta ɗaga tana riƙe hannun matashin yaron ɗan shekaru ashirin da uku daga sheɗancin da yakeyi a jikinta. 
     “Sorry Baby. just 5minutes”. Ta faɗa tana masa kiss da kai wayar kunnenta. Duk Madam Chioma tana jiyosu, ta riga tasan ƙawar tata kullum bata rabo da yara ƙanana tare da ita. Sai dai bama wannan bane damuwarta a yanzun. Damuwarta abinda taci karo da shi. Muryarta na rawa tace, “Rebecca! Tawa ta ƙare”.
       Cike da tsoron jin yanayinta da furicinta Madam Rebecca ta tashi zaune tana tambayarta miya faru?. Cikin kuka rurus Madam Chioma ta zayyane mata komai game da mafarkinta da kuma abinda ta gani a tukunyar tsafinta. Wani shegen murmushin mugunta Madam Rebecca tayi. A fili kuwa sai tace, “Kinga kwantar da hankalinki, bara na gama da babyn nan na gabana zanzo gidan”.
     Da matuƙar tashin hankali madam Chioma tace, “Haba Rebecca. ina miki maganar matsalata kina magana irin haka? ki tausaya min mana. Banason na rasa Yoohan a rayuwata ko cika burina ban samu nayiba”.
      “Hah!! Kinada matsala Chioma. Kema kinsan inaa wannan yanayin babu abinda zan iya miki koda nazo. Garama kiyu hakuri ki bani 1hour kawai”. Cike da matsanancin takaici Madam Chioma ta yanke wayar. Maida akalar kiranta tayi ga Number Yoohan. Sai dai harta yanke ba'a ɗagaba. Dan a lokacin bama wayaba har ita kanta dake matsayin uwarsa ya manta da ita a duniya. Nu'aymah kawai ya sani a yanzu, ita kaɗai kuma yake gani.
      Ta jera masa kira kusan biyar babu amsa. Hakanne ya ƙara rikitata ta koma kiran Solomon. shima dai akai sa'a bai ɗagaba. Dan a lokacin yayi barci saboda gajiyar yawon da sukasha, yana dawowa kuma ya samu wata ƴar baby suka shige da ga ciki. Ai saita sake haukacewa. A ruɗe ta fara haɗa kayan tafiya ƙauyensu Madam Rebecca, dama daga can aka yo mata aikin. Dan bazata iya kwana garin Abuja ba batare data san makomar abinda ta ganiba. Bayi ta shiga ta facaccala wanka ta fito. Yanda take komai a birkice sai ka ɗauka tama zare ne. Sai da ta kimtsa tsaf ta fito jaye da ƙaramin trolly da handbag. Sashen Papa ta nufa, kamar yanda tayi hasashe kuwa ta samesa a falonsa zaune shi da Uncle Godwin suna tattauna mai fishshesu. Da ƙyar ta iya ƙoƙarin control ɗin ruɗaninta suka gaisa da Godwin ɗin. Papa dake binta da kallo ya miƙo mata hannu alamar tazo garesa. Zuwa tayi ta zauna a jikinsa cike da dauriya, ta ɗora kanta a kafaɗarsa. Kiss ya bata a goshi da bakinta yana faɗin, “Are you Ok?”. Kanta ta daga masa. Murya a sanyaye tace, “Yes. I'm. Kirane ya sameni na gaggawa daga office ɗinmu, akwai wani taro wai da zamuyi a Lagos dama tun kusan sati biyu, anata ɗagawa kuma sai yau ne wai sukace gobe za'ayi, gashi yanzun an turomin saƙo ni akeson na halarci wajen wai kuma”.
       Tuni fara'ar papa ta ɓace a fuskarsa. Dan yana tsananin sonta, koda wasa bayason tanayin nesa da shi. Amma kuma bayason ɓacin ranta. Zai yi magana tai saurin ɗora yatsanta akan bakinsa tana faɗin, 
    “Please baby”.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali. Badan ransa nasoba yace, “Okay. Yanzu kina buƙatar wani abu ne?”.
       “No thanks you dear. Basai na ɗaura maka wata wahalaba ma”. 
       “Bakinta ya sake sumbata, da murmushinsa na yake yace, “Babu damuwa zan miki transfer ɗin kuɗin shan ice-creem ”.
       “Thanks you baby”. Ta faɗa tana sumbatar laɓɓansa da mikewa tsaye. Ta sake cewa “Bey”.
    Kusan a tare shi da Uncle Godwin sukace mata “Safe journey”. Daga haka ta fice tabar papa da jimami. Duk da shima hakan wata damace a garesa da zai shanama tashi rayuwar.
     Ko sallama batai da su mama debora ba ta fice abinta. Yaran kuwa suna can garden dama. Tana fitowa harabar gidan motar madam Rebecca na shigowa. Tsaki taja tare da nufar motar. Batare data yi magana ba ta buɗe gefen driver ta zauna. Reverse kawai Madam Rebecca tayi suka fice da ga gidan.
      Sai da suka hau titi suka fara magana. Madam Chioma ta dage akan a yau zata wuce dan bazata iya kwana cikin abuja ba. Lallaɓata Madam Rebecca ta shiga yi akan ta bari su sami jirgin da zai kaisu jihar River state. Dan tafiyar mota ba abune mai sauƙi a garesu ba. Da farko sam madam Chioma taƙi saurarenta. Sai da tai da gaske da tuna mata ka'idojin bokan sannan ta dawo hayyacinta ta amince zata kwana a gidan Madam Rebecca ɗin. Can suka wuce. Sai dai a ranar sukai booking ɗin jirgi. Tare da kiran bokan shima sukai magana da shi ya basu damar zuwa a goben. Da ga haka suka cigaba da tattaunawa akan lamarin Yoohan da Nu'aymah, dama basusan sunayi ba, dan su suna can a sabuwar duniya😉😎.........✍

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 62

............Iya wahala Aymah tasha a yau. Hatta shi kansa Sojan nata ya jigatu balle ita. Yama manta kansa matsayin likita, ya manta matsayin Nu'aymah ƴar shekara sha takwas kacal. Ya manta.. Ya manta... Da yawa. 
         Duk yanda yaso ɗaga ido ya duba halinma da take a ciki ya kasa. Wani irin azababben ciwon kai ne da jiri ke yawo da ƙwanyar kansa. ya yunƙura da ƙyar ya sauka a gadon yana layi. Toilet ya nufa. da laluben bango ya ƙarasa ciki, amai ya farayi babuji babu gani. Hannayensa duka biyu riƙe da kansa da yake neman tarwatsewa saboda azabar ciwo.
        Duk da halin da Aymah take a ciki tana jiwo kakarin aman nasa. Sai dai ko idanunta bazatama iya buɗewaba tsabar galabaitan da tayi. Kusan mintuna goma taji motsin fitowarsa. A yanzunma bata iya buɗe ido taga halin da yake a cikiba. Kunnenta dai na sauraren yanda yake fidda wahalallen numfashi, harya ƙaraso ya faɗa saman gadon yana ambaton sunan ALLAH. Hannunta taji ya kamo cikin nasa dake rawa. Ƙam ta ƙara matse idanunta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. 
         Haka suka kasance babu mai iya taimakawa ɗan uwansa. Ga shi kuma barci yaƙi ɗaukarsu su duka. Ga ciwuka sun musu rijif musamman Aymah da ko maganinta dama bata samu damar sha ba na daren, ga yunwa da take bala'in ji a yanzu haka.
       A hankali Yoohan da idanunsa ke a runmtse ya sake jan jikinsa kusa da ita. Muryarsa a ɗashe yace, “Baby. Are you ok?”. Hawaye ne masu ɗumi suka silalo mata, dan ita dai tasan she's not ok ɗin nan. Jin bata amsashi ba ya sakashi buɗe idanunsa da ƙyar yana taunar lip saboda azabar da kansa ke masa. Hannunsa ya ɗora bisa fuskarta ya shiga share mata hawayen dake ziraro mata. Cikin raɗar magana kamar ɗazun muryar a ɗashe yace, “I'm sorry. Forgive me Please Sweet girl”. Ya kare maganar da ɗora kansa jikin nata shima hawayen na tarar masa cikin ido na tausayinta. Dan jikinta ya ɗauki zafi sosai na zazzaɓi. Ga wani ƙaunarta mai zafi na sake ɗawainiya da zuciyarsa. Musamman da ya tuno sharrin da akai mata na zubar da ciki. Gashi shi kuma a yanzu ya sameta cikkakkiyar mace da ya zam shine namiji na farko daya fara ratsata. Hakan ya sake tabbatar masa da zarginsa akan gidansu.
        A hankali ta juyo dan son shigewa jikinsa ko zata sami sassaucin azabar da takeji. sai dai kuma wani zafi ne ya ratsata har cikin ƙwalwar kanta. Ta saki siririyar ƙara da fashewa da kuka. “Wayyo Abba ya kashe muku ni. Ummuna zan mutu”.
      A tsananin firgice Yoohan ya zabura. Ya riƙota jikinsa tare da saurin dafe kansa yana faɗin, “Achss! My head!. Baby Please i'm sorry, kibar kuka na roƙeki”. Sosai ta mamuƙesa tana cigaba da kukanta jikinta na rawa saboda zafin da takeji wajen na mata.
       Gaba ɗaya Yoohan sai ya sake ruɗewa. Duk da matsanancin halin da yake ciki haka ya ɗauketa cak zuwa toilet yana layi, sai jera mata kalmar ‘I'm sorry’ yaketa faman yi kamar shima zaiyi kukan. A wahalcen ya shiga bata taimakon da ya dace yasan kuma zai taimaka mata a irin halin da take ciki. Ya dai sha raki. Dan da azaba ta isheta hardasu ALLAH ya isa tai masa cike da suɓutar baki. Sambatu kuwa iri-iri wani abunma ita kanta batasan mitake faɗaba. Wanda tayi ɗazun yafi wannan, sai dai na yanzu da yake yana a hankalinsa sai yaji ransa duk a jagule. Yana jin haushin kansa akan gaza haƙurin da yay yama tausaya mata kodan ƙananun shekarunta. Yanda take rabzar kuka shima ƙwalla sai famar tarar masa suke a cikin idanu. Da ƙyar dai ya kammala kimtsata ya taimaka mata tasa bathrobe.
        Yanzun ma da ƙyar ya iya kawota falo ya kwantar saman sofa. Juyawa yay wajen gadon ya cire farin bedsheet ɗin dan ya ɓaci, sai dai bawani faca-faca ba. Jini ne ɗis-ɗis irin na macen data rasa budurci musamman mai ƙarancin shekaru irin nata. Har aransa yaji takaicin fara sanin matarsa a ɗakin hotel, da yasan hakan zata kasance shikam da gida suka koma abinsu. Amma duk da haka wannan bedsheet kam bazai ƙara yarda wani mahaluki ya kwanta a kansa ba. Inda ma yaji daɗi a ransa dama sabone aka saka musu kamar yanda al'adar hotel ɗin take. A washing machine dake toilet ɗin ya saka bedsheet ɗin ya wanke ya busar da shi. Sannan shina ya tsaftace nasa jikin ya fito.
         Kafin ya dawo gareta har barcin wahala yayi awon gaba da ita. Dan idanu ya rumtse sosai da cire tausayinta yay mata gashin ɗaya tamkar da dubu. Cike da dauriya yay order ɗin abinci dan yasan zataji yunwa. kuma ya tunama batasha maganinta ba. Ba'a rufa mintuna goma ba kuwa sai gashi an kawo musu. Lokacin yana ƙoƙarin canja musu bedsheet cike da ƙarfin hali dan jiri yake gani. Ga ciwon kai kuma. Zuwa yay ya buɗe ya amshi abinci ya koma ciki. Sai da ya gama kimtsawa tsaf sannan ya tasheta zaune. Kuka ta sanya masa duk da kuwa yanzu zafin ya ragu, sai dai zazzaɓi da jikinta da takejin na mata ciwo na bala'i. Kasancewar yunwa takeji sai gashi taci abincin daya bata da kansa. Ya bata maganinta daya tabbatar zai taimaka mata tunda zatai barci. Ayko bata rufa mintuna biyarba sai barci. Da ƙyar ma ya samu ya ta yarda ya saka mata kayan barci ya taimaka mata ta koma kan gadon. shima dai kayan barcin ya canja ya kwanta dan jikinsa sai karkarwar zazzaɓi ya keyi. Ga ciwon kai tamkar ana ƙara masa shi.
          Sai gashi ita Aymah ta samu barci mai nauyi, shiko dake rungume da ita ya kasa rintsawa. Ga zazzaɓi da ciwon kai. Sau biyu yana zuwa yay amai. Hakan yasaka shi sake galabaita fiye ma da farko.
          Yau ma Alarm ne ya tadasu, koma nace ya tada Nu'aymah dan shi dai Yoohan bama barcin yayiba. Garama gabannin asuba yaɗan fara figarsa sama-sama sai kuma ya farka. Daga haka bai sake komawaba har alarm ɗin ya buga. Sosai jikin Aymah da sauƙi dan zazzaɓin nata ya sauka ita. Sai dai rashin jin daɗi jiki da sabon al'amari ya haifar. Sai ciwo ƙafafunta dake mata. Jinta take fayau kamar iska zata ɗauketa ta kayar. Bakinta ko ɗaci, ɗan-ɗanɗanon data fara samu yana dawo mata ya sake guduwa. Yanda take tsananin jin kunyar Yoohan ɗinne ya sakata tashi zaune batare data yarda ta kalle sashin da yake ba, sai faman matse baki take dan can wajen kam da zafi har yanzun. 
        A hankali ta dinga tafiya tana hawaye har bathroom, Yoohan na kwance yana kallonta cike da tausayi, duk yanda yaso ya yunƙura ya sake taimaka mata ya kasa saboda ciwon da kansa ke masa ga zazzaɓi irin wanda shikam a rayuwarsa zai ce ya mata rabon da yayi zazzaɓi mai zafi irin wannan. 
       Aymah na shiga bayin ta fashe da sabon kuka mai sauti tana kiran baba malam da Umm suzo su taimaketa. Ta kai mintuna huɗu zaune a aɗan step ɗin hawa wajen bathtub ɗin kafin ta miƙe da sanɗa ta nufi madubi wani daɗi na ratsata na hango wayar Yoohan a jiye. Da alama dai a daren jiya ya manta da ita kenan. 
          Umm ta riga da ta mata tarbiyyar duk abinda ya sameta ita take fara sanarmawa, sai dai a yanzu abinda naga Aymah na shirin aikatawa ya sake tabbatar min da tsabar wautar dake a kanta, dan kuwa number ɗin Umm ta shiga lodawa cikin wayar tai dailing. Kuka ta sanya da dariya a lokaci ɗaya jin kiran ya shiga. 
       Daga can Nigeria kam Umm na idar da sallar magriba kiran ya shigo. Da mamaki take kallon Number dan bata kawo Aymah a rantaba. Tunda tasan indai zasu gaisa a wayar baba malam mijinta ke kira sai shi kuma ya bata su gaisa. Tana gab da tsinkewa dai tai ƙuru ta amsa, tare da kaiwa kunne tai sallama. Maimakon mutuniyar taku ta amsa sallanar sai kawai ta fashe ma Umm da kuka. Shiru kawai Umm tai tana saurarenta dan ta gane abarta. Sai da ta barta tayi kusan na minti ɗaya sannan tai gyaran murya. “Mike faruwa?”. Umm ta jefa mata tambayar.
     (Nazata bazata iya faɗaba fa😱) sai kawai Aymah ta gyara zama ta fara faɗin, “Umm dan ALLAH kuce ya maidoni gida. wlhy ban taɓa iskanciba. Na rantse da ALLAH Umm ba laifina baneba, sai da naita roƙonsa karyayi banaso, amma shi mugune sai da yayi. Gashi na kasa tafiya, wajen kamar zai fita, ciwo yake min, gashi inajin fitsari inajin tsoron yi Um........”
       Harga ALLAH dariya ta bama Umm, amma sai ta danne abinta tai saurin faɗin, “To ya isa zubaina sarkin magana. Wai nikam yaushene ranar hankalinki Nu'aymah?. Kai ALLAH na gode maka ni Firdausi. Yanzu shi mijin naki yana ina kike zubamin zance haka?”.
      Baki ta kumbura na haushin ba'a barta takai ƙarshen labariba tace, “Yanacan ɗaki bai tashi ba. Ni kuma ina toilet asuba fa tayi anan”. Ta ƙare maganar hawaye na silalo mata.
     Ajiyar zuciya kawai Umm ta sauke hawayen farin ciki itama na silalo mata. Koba komai dai ta fahimci yarinyarta takai mutincinta gidan aurenta. ALLAH ya ƙara wanketa a garesu ga ƙazafin da akai mata. Hawayenta ta share. Tace, “Ki shiga ruwan zafi kinji ko, ki daure duk zafinsa ya ratsaki sosai zakiji daɗi”.
       “Umm wlhy jiya daya sakani kamar zan mutu. Dan ALLAH ki faɗamin wani maganin sai nace ya sayo min zansha. Amma dan ALLAH kice Abbana ya kirashi ya kawoni gida yau”.
      “To naji, yanzu ki ƙara shiga ruwan zafin bazakiji zafin kamar na farkoba kinji ƴar albarkana”.
      Cikin jin daɗin sunan ƴar albarka da Umm ta kirata tace, “To Ummuna. In kiraki video call ki ganni, ƙila zakifi ƙarajin tausayina ma”. Da sauri Umm tace, “A'a jekiyi abinda na sakaki, kije kiyi salla lokaci na shigewa”.
        Fuska ta ƙwaɓe zatai wani sabon kukan, zatai magana Yoohan da shirunta ya sakashi a damuwa ya taso da ƙyar ya biyota yay azamar zare wayar daga hannunta dan yaji maganar video call da taima Umm, sai dai baisan amsar data bataba da ga can.
       Zabura tayi dan batasan da shigowar tasa ba. Shi kuma ya zaune a step din yana dafe kansa da faɗin, “Acshh!! Kaina”. Miƙewa ta nemayi duk da ganin yanayinsa ya bata tsoro, yay saurin damƙo hannunta ya maidata ya zaunar. Hannunsa dake akan goshinsa ya cire yana dubanta da idanunsa dake jajur. “Zeeynab baki da hankali wa kika kira? Ba dai Uncle ba?”.
          Tana cika kumatu da iska tace, “Ni ban kira Abba ba, Ummna na kira na faɗa mata abinda kaimin. Nace tasa Abbah yasa ka maidani gida”.
   Tuni ya manta da maganar ciwon kai, ya waro idanu waje yana faɗin, “Kin kasheni Zeeynab. Kika faɗa matafa kika ce?”.
        “To wa yace kayi? Gobe ma ka ƙara kaga idan bankira harda Hajjo da Abbana da Addah duk na faɗa musu ba ALLAH. Kai harma Ananah sai tasan halinka”. 
      Gaba ɗaya kunya ta lulluɓe Yoohan, ji yake tamkar yana a gaban Umm. cike da ƙarfin hali yace, “Yarinyar nan ALLAH har yanzu kanki da motsi, dole na sake maidaki wajen su Dr Liam”.
     Umm da duk take saurarensu da ga can ta yanke wayar tana dariya. Dama ta tsayane ta sake gaskata zancen Nu'aymah. Wayar ta ajiye tana faɗin, “Yaron nan kaga takanka indai Nu'aymah ce. Bayan motsin ciwo dake a kanta akwai ma na hali wlhy. Ni harma ka bani tausayi”.....
       “Waye ya bada tausayi?”. Cewar baba malam dake shigowa ɗakin. Dan dawowarsa kenan gidan. Juyowa tai tana cigaba da dariyarta. Ya zauna a bakin gadon ya riƙo hannunta. “Jannat da alama dai kina cikin farin ciki, zoki ɗan sammini nima muyi tare”. Sosai take ƙara faɗaɗa dariyarta. Ta shiga bashi labarin kiran da Nu'aymah tai mata da drama ɗin data gama ji tsakaninta da Yoohan a ƙarshe. Shi kansa baba malam sai da ya dara. 
      “Ai Jannat lamarin mamana sai ita. Yarinya tamkar goyon kaka. Amma koba komai ni hakan yamin daɗi tunda munji cewar dai sharri dai akai mata kamar yanda zukatanmu ke faɗa mana. Wannan shine amfanin ka bama yaro tarbiyya akan duk abinda ya shafesa ya sanar maka. ALLAH yay musu albarka su duka. Ya azurtasu da zuriya masu albarka da alkairi. Wadda zata zama maijin ƙai a garesu damu baki ɗaya”.
       “Amin ya rabbi. Sai dai kuma naji muryar mijin nata kamar wanda baida lafiya ma. Dan da ƙyar yake magana”.
        Ɗan jimmm baba malam yay yana sauke numfashi. Yace, “To inaga dai bara na sanarma yaron nan abokinsa shi sai ya nema wanda zaije ya duba halin da suke cikin, dan yanzu ni idan na kirashi a kunya zan sake sakashi tunda mamana ta ɓallo masa aikin data iya na wauta”.
     Dariya Umm tayi shima yana tayata. A take ya kira Richard dan yanzu yana da Number sa. Sai dai bata shiga ba. hakan na nufin Rich baya Nigeria kenan kokuma wayar a kashe. ya barsa akan zuwa anjima zai sake gwadawa kawai.

          A nan Austria kam Yoohan da ƙyar ya iya taimakama Aymah ta sake shiga cikin ruwan zafi. Sai dai yau batai rakin jiyaba. Hawayene dai kam tanata abunta. Baiyi maganaba dan shima takansa yakeyi, da alama ma yafita jin jiki yanzun. Tana ganin ya shiga wajen wanka tai alwala ta fice daga bayin tana ɗingishi. Yau ko jiransa ya jasu salla batayiba. Tana idarwa yana fitowa. Komawa tai kan gado ta kwanta.
      Bazai iya salla a tsayeba saboda jiri yake gani ga ciwon kai. Hakan ya sakashi yinta a zaune, yana idarwa shima gadon ya koma ya sake kwanciya. Wayar landline ya ɗauka da nufin kiran yima Aymah order ɗin breakfast saboda shan maganinta sai yaga wayarsa na haske. Hotel ɗin ya fara kira, kafin ya ɗauka wayar tasa dan silent take dama. Richard ya gani, cike da mamaki ya amsa kiran dan alamu sun nuna Rich ɗin yana a cikin Austria tunda da Number ƙasan ya kirashi. 
         Ko gaisawa basuyi ba Richard ya fara jera masa tambaya a rikice saboda jin muryarsa, cikin son kwantar masa da hankali Yoohan yace, “Ciwon kai ne kawaifa. Dama kana Austria?”.
       “Jiya da dare na iso, yanzu dai idan ba damuwa bara nazo ɗakin naku na dubaka hankalina zaifi kwanciya”. Murmushi kawai Yoohan yayi da faɗin “Okay”. Daga haka ya ajiye wayar ya juya yana kallon Nu'aymah data juya masa baya. Ta naɗe a cikin bargo alamar sanyi takeji. Maida idanunsa yay ya lumshe tunda yasan akwai kaya jikinta.

        Kusan a tare Richard da ma'aikaciyar hotel ɗin suka iso. Rich ya amshi abinci kawai sannan ya danna door bell. Miƙewa Yoohan yayi da ƙyar hannunsa dafe da kansa. Ya gyarama Aymah ɗan kwalin kanta daya zame sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. Saurin riƙesa Rich yayi ganin yanda yake layi, duk ya rikice masa da faɗan yaya zai zauna da ciwo irin haka baije asibitiba?. Amma yana faɗin wai ciwon kai ne kawai. Murmushin ƙarfin hali kawai Yoohan yay masa shi dai, ya zaunar da shi a kujera yana sake jera masa sannu.
       Kansa ya ɗaga masa yana magana cike da ƙarfin hali. “Shine zaka shigo baka sanar min ba?”. 
       Rich da damuwa duk ta baibayesa yace, “Manta da batun shigowata faɗamin mike damunka Please X-man”.
      “Kai dai ka cika ruɗiya. Ciwon kai ne kawai da zazzaɓi”.
     Hararsa Rich yayi da faɗin, “Shine bazakaje asibiti ba? Ina madam?”.
      Da idanu ya nuna masa gadon da cewa, “Gata can, itama bata da lafiyar”. 
       “Oh GOD. Miya faru haka?”.
Murmushi kawai Yoohan yayi baice komaiba. Hakan yasa shima Rich ɗin bai sake magana ba ya miƙe ya fita yana faɗin, “Ina zuwa Please”.
       “Okay” Yoohan ya faɗa da jingina jikin kujerar ya lumshe idanunsa. Yanason tashi yaje ya tada Nu'aymah data fara barci taci abinci amma jiri da yake gani ya hanashi motsawa. Har tsahon mintuna sha biyar Richard ya dawo da kayan magani. Sannu ya sake yima Yoohan ɗin sannan ya zauna yay allurai a cikin drip. Yana gamawa ya dubi Yoohan.
       “Ya kamata ka koma kan gado sai a saka drip ɗin”. Idanu Yoohan ya buɗe da ƙyar, batare da yayi magana ba yay ƙoƙarin tashi tsaye. Taimaka masa Rich yayi har kan gadon. Aymah nata barcinta batasan hidimar da sukeyi ba ita dai. 
       Ɗaura masa ruwan yayi, sai da ya tabbatar ya fara shiga jikinsa sannan yace, “Ita kuma yaya zamuyi da ita?”. Isaka Yoohan ya ɗan furzar idanunsa a lumshe yace, “Inaga ita barta kawai, dan allura ya kamata ai mata kuma bazata tsaya ayi da arziƙi ba. Dan bata ƙaunar allura sam”.
      “Okay, idan ka tashi kayi mata. Sai dai akwai alluran a wajenka ko sai an siyo?”. 
       “Sai an siyo”.
Ya bashi amsa a yanayin barcin daya fara fisgarsa. Sai kuma ya faɗama Rich ɗin sunan allurar da yake buƙata.
        Idanu Richard ya ɗan waro waje jin allurar da Yoohan ɗin ya faɗa. Cike da neman magana ya shuri ƙafar Yoohan ɗin yana faɗin, “Shegen sama, ashe kasan tsiyar daka aikata”.
       Shi dai Yoohan baice masa komaiba dan barcin ya fara masa Nauyi, Richard ya fice cike dajin daɗin ɗan uwansa ya zama babban mutum yau.
      
        Yanayin rashin jin daɗin jikin ya sakata kasa barci yanda ya kamata, ta buɗe idanunta a hankali kansa. Barci yake sosai yanzun. Ganin kamar ana ƙara masa ruwa ya sakata tashi aɗan zabure. Cike da ruɗewa ta kai hannunta ta ɗora a bisa kansa. Har yanzu kan nasa bai gama hucewa ba da zafi. Sosai damuwa da tausayinsa suka bayyana ƙarara a fuskarta. A fili tace, ‘Bawon ALLAH, ashe shima bashi da lafiya, shiyyasa ɗazun yaketa magana da ƙyar. Ɗan balarabe ALLAH na zata duk muguntar da kaimin ce ta sakaka komawa kalar tausayi ai’. Ta ƙare maganar da ɗora kanta bisa ƙirjinsa hawayena cika mata idanu ganin an saka masa allura a jiki. Dan itafa ba'a taɓa mata ƙarin ruwa cikin hankalinta dan bazata yardaba. Inhar yazam za'a ƙara mata ruwa to lallai sai an bata maganin barci ko an mata allurar barci saboda tsabar ƙiyayyar dake a tsakaninta da allura.
        Ta daɗe jikinsa kwance kafin ta tashi ta zauna, tagumi tayi hannu bibbiyu ta zuba masa idanu kaikace television ta samu. Ta shafe kusan mintuna talatin a haka kafin ta miƙe saboda fitsari da takeji. bayan ta fito kuma idonta ya sauka kan abincin. Yunwa takeji bana wasaba, dan haka ta zauna ta faraci dan ta fahimci natane dama. Tanaci tana kallonsa harta kammala dan kaɗan ma taci saboda rashin daɗin bakinta, cike da son ƙarfafa kanta da rashin daɗin da jikinta ke mata ya sakata ɗaukar magungunanta tasha kamar yanda taga yana bata kullum. Kasancewar barcin da suke sakata idan tasha ya sa ta ƙara ɓingirewa barcin a wajen.

★★★★

        A hankali Yoohan ya buɗe idanunsa saboda kaɗawar alarm alamar lokacin sallar zuhur yayi. Hakan kuma yay dai-dai da farkawar Aymah dake can kan sofa itama. Sai dai har Yoohan ya miƙe zaune ita ɗin bata tashinba tana kwancenta. Inda take ya kalla yana sake lumshe idanu da buɗewa. Sosai ciwon kan nasa yay ƙasa. Zazzaɓin ma kuwa duka ya sauka. Ya zare drip ɗin da kaɗan ya rage ya ƙare. Fuskarsa a yamutse na alamun wanda ya tashi a barci ya sauke ƙafafunsa ƙasa yana ambaton Alhmdllhi a cikin ransa. Sai da yay kusan minti uku a zaune sannan ya miƙe zuwa inda Nu'aymah ke kwance.
        Da sauri ta maida idanunta ta rufe, shikam batare da yasan idanunta biyu ba ya ɗora hannunsa saman kanta. Alhmdllh ya faɗa jin babu zafi. Ya taɓa wuyanta ma nanma sanyi ƙalau. Maganganun data sha ya dudduba yaga tashasu dai-dai, hakan ya sakashi miƙewa ya nufi bayi zuciyarsa sakayau da farinciki da nishaɗi. Jinsa yake tamkar wani sabon mutum a duniyar mutane. Aymah na ganin ya shige ta tashi zaune fuskarta a curkuɗe kamar zatai kuka. Gaba ɗaya jitake tama rasa abinda ke mata daɗi a duniya. Babu abinda tafi buƙata kamar ta ganta a gaban Umm ɗinta. Ta haɗiye ƙwallar daya cika mata idanu tare da zabga uban tagumi.
       A haka Yoohan ya fito ya sameta. Kallo ɗaya tai masa tai azamar maida kanta ƙasa saboda ganinsa da ga shi sai boxer da ƙaramin towel a hannu. Direct yayo kanta yana faɗin, “Kin tashi?”. Kunya ta hanata masa magana, sai kai kawai ta kaɗa masa. Bai damuba dan ya fahimci kunyarsa takeji. Ya zauna a hannun kujerar yana cigaba da goge wuyansa idanunsa a kanta. “Mike miki ciwo yanzun?”. 
     Murya na rawa tace, “Komai ma”.
A ransa yace, ‘Abin nemafa ya samu ga iya madam hajjaju malamar tsiwa da shagwaba'. A fili kam sai yace, “Oh so sorry Mrs Yoohan. Jekiyi wanka sai na duba wajen na gani”.
     Da sauri ta ɗago tana hararar sa kai kace idanun faɗowa zasuyi ƙasa. Gashi dama sun kumburo saboda kukan data sha sannan akwai ja a cikinsu. Da sauri ya kauda kansa gefe gudun kar dariya ta kufce masa ya ƙara laifi. Miƙewa tai tabar wajen tana ƙunƙunin da baisan mitake faɗaba a ciki saboda hausa takeyi. Ya ɗan lumshe idanu ya sake maidasu kanta. Sosai yanda take tafiya da ɗingishi ya ƙara masa tausayinta da ƙaunarta a cikin zuciya. Tana gama shigewa ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe..............✍




Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 63

............Ganin lokacin salla zai wuce ya sakashi mata knocking dan taƙi fitowa. “Sorry baby fito muyi salla kinga munata makara. Na yarda idan mun idar ki hukuntani koda bulalane ok”.
         Fitowa tayi, dan itama batason lokacin sallar ya wuce, dama ta sake  shiga ruwan zafi ne dan tanajin daɗinsa sosai. Ƙin yarda ta kalli inda yake tayi. Taje ta saka doguwar riga, shi kuma ya saka musu abin salla. Suna raka'a ta biyu Richard ya shigo ɗakin bayan yayi knocking yaji shiru. A zatonsa ko jikin nasu ne shiyyasa ya shigo abinsa. A hankali ya ajiye kayan hannunsa idanunsa a kansu. Tsigar jikinsa sai tashi take. Haka ya zauna yanata kallonsu tamkar ya samu television har suka idar. Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da Yoohan ya zubo masa harara. Da yare yace, “Shine bazaka jira a baka izinin shigowa ba zaka wani faɗoma mutane ɗaki?”. Jikin Richard duk a sanyaye yake, shiyyasa yace, “I'm sorry” kawai yana furzar da iska. Kauda kai Yoohan yayi ya maida ga Aymah dake jinsu sai dai ko ɗago kai batayiba dan itama shigowar Rich ɗin ta bata haushi. Dan tarbiyyarta ta koya mata shiga waje da sallama da kuma jiran bada dama. Yoohan ya fahimci shigowar Rich ta bata haushi. Dan aɗan zamansu ya fara fahimtar wasu daga halayenta. A hankali yace, “Kiyi haƙuri. Sai kin taimakeni wajen ceto rayuwar ɗan uwana da ga duhu zuwa haske”.
      Karan farko ta ɗago kai ta ɗan kallesa. sai kuma tai ajiyar zuciya da maida dubanta inda Rich yake zaune. Sai dai ba kallonsu yakeba yanzun. “Good Afternoon”. Ta faɗa da dasashshiyar muryarta datasha kuka.
     Miƙewa Yoohan yayi yana faɗin, “Ana gaisheka”. 
        Buɗe idanu Rich yayi yana kallonta, ya amsa cike da kulawa da tambayarta ƙarfin jiki. A taƙaice tace, Am better now”. 
         “Thanks God”. Ya faɗa shima yana miƙewa.  Fita yay ƴar barandar nan ya zauna, yayinda Yoohan kuma ya zauna inda ya tashi yana kiranta. Batare data tankaba ta miƙe ta nufesa. Gefensa ya nuna mata yana binta da kallo. Ita dai taƙi kallonsa sam. Abincin da Rich ya kawo musu ya buɗe. Gasashshen naman kaza ne da yasa akayisa na musamman domin Nu'aymah, sai haɗin salad da sauran tarkacen abincin Austrian daba gama haddace sunayensu tai ba itakam. Kamo hannunta yay ya matso da ita sosai jikinsa yana magana cike da lallashi. 
      “Ki daure kici wannan bakinki zaiyi daɗi sosai. Kuma zaki samu sauƙi insha ALLAH. Dan abincine da ya dace da buƙatar irin yanayin da kike ciki ok”.
       Idanunta cike da ƙwalla tace, “Toni bakina fa babu daɗi ALLAH”.
       “Eh idan kikaci wannan zai miki daɗi, idan kuma kinason na miki allura tom, ina dasu buhu-buhu a ɗakin nan. Ohya buɗe bakin”. Hawayen da take maƙalewa ne suka silalo, jin zancen allura ya sakata buɗe baki ya saka mata. Share mata ya shigayi yana faɗin, “Kefa yanzun babban mace ne, kin girmi harkar yara. Kona tayaki ci ne?”.
     Da sauri ta ɗaga masa kanta alamar eh.
    Yace, “Okay to dinga bani da kanki muyi maza mu mucinye kinga Rich yana jirana”. Babu musu ta dinga bashi shima yana bata. sai ko gashi sun cinye kazar tas harma suka ƙara da wani abun. Yana son ɗaukar allurar da Richard ɗin ya kawo amma bayason ɗaga mata hankali. Hakan ya sakashi ɗaukar ledar yabar wajen. Bata fahimci mizaiyi ba shiyyasa bata maida hankali kansa ba. Sai tattare kayan da sukaci abincin take.
       Batare data san mi yayoba yazo ya sake zama kusa da ita. Kallonsa tayi sau ɗaya ta janye idonta tana tura baki. “Ba kace jiranka akeba”.
        Wuyansa ya shafo yana gyaɗa mata kai. “Magani zansha sannan. Ɗakko min gasu can”. Kamar zata fasa masa kuka ta miƙe inda ledan maganin yake. Batason yin tafiya saboda zafin da takeji. Da kallo ya bita harta ɗakko ta juyo sannan ya janye idonsa. 
         Ledar data miƙo masa ya haɗa d hannunta gaba ɗaya ya jawota saman cinyarsa. kafin ta sami damar yin magana ya manne bakinsa da nata tare da saita allurar dake ɓoye cikin ɗayan hannunsa a inda ya dace. Tanajin shigar allurar ta nema fisge jikinta daya fara rawa dan abin yazo mata a bazata. Ya rumtse idanunsa da sauri saboda wani shegen mintsini datake masa a hannunsa. Allurar ya zare tare da bakinsa yana faɗin, “Ouch!!. sweet girl Zaki fasamin fata”.
        Lafewa tai a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere da shashshekar kuka mara sauti. Ga hawaye na zirara. Goshinta ya sumbata yana ɗan murmushi. Am sorry bazan ƙaraba huyim?”.
      Ita dai bata tankaba. Tanata hawayenta ne. Cigaba yay da shafa bayanta har sai da ta daina kukan sannan ya sauketa a kujerar, a gabanta ya durƙusa hannunta cikin nasa. Ya share mata hawayen da ɗayan hannun, a ransa yana dariyar rakinta akan allura. Sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa yanda ya kamata sannan ya duƙo ya sumbaci kumatunta da bakinta. “Bara inje inazuwa. Insha ALLAH wajen zai daina zafi kinji”. 
      Batace komaiba. Amma yasan tana jinsa. Ya sake sumbatar laɓɓanta sannan ya miƙe. da kallo tabi bayansa harya fice ƴar barandar nan. Sai ta maida idanun ta lumshe duk da ba barci takejiba kuwa.

       ★★★

  “Sai yanzu kagama lallashin?”
       Richard da ke danna lap-top ya faɗa cike da tsokana. 
           Hararsa Yoohan yayi, yaɗan sosa tsakkiyar kansa da cewa, “Ka samin ido da yawa fa”.
     Dariya Richard yayi kawai. Sai kuma ya juyo masa da fuskar lap-top ɗin yana sauke numfashi. “Brother lamarin zancen cikin nan fa akwai rikitarwa. Kasan gaba ɗaya Doctors ɗinan gaskiyar abinda suka gani suka faɗa? A iya bincikena babu wanda ya haɗa kai da su wajen bada result ɗin ƙarya, aikinsu sukayi a gaske”.
         Yoohan dake kallonsa yana ɗan taunar lip ɗinsa na ƙasa ya lumshe idanunsa da buɗewa a kansa. Da ɗan yanayin ruɗani yace, “Amma to miyasa sukaga haka? Yarinyar nan fa She's virgin wlhy”. 
       “Really?”.
“Kasan bazan faɗa maka abinda ba haka yakeba Rich. Amma lallai akwai abinda ke ɓoye da bamu sani ba. Minene sauran bayanin?”.
         Iska Rich ya furzar yana matso da kujerarsa kusa da Yoohan, ya gyara zaman lap-top ɗin. “Nabi diddigin duk abinda abin recording ɗin nan ya naɗa na mai aikinku. Ga su nan zaka iya samun lokaci ka saurara. Nata tunanin ta hanyar dazan samu wayarta, shine da mukai magana da kai kace nasa Blessing. A randa mukai maganar kuwa washe gari nasaka Blessing ta sato mana wayar har gidan Uncle ɗin madam ɗinka. Waɗanan sune gaba ɗaya Contacts ɗin wayarta. Na kuma bibiyesu dukansu da duk wayoyin da tayi da masu Numbers ɗin. Abinda na gano na farko shine kakar madam ɗinka kamar tana kan sani ta aiko yarinyar nan wajenku. Sai dai dalilinta nayin hakanne sam ban saniba gaskiya. Nabi duk hanyoyin dazan iya fahimtar wani abu ban samu dama ba”.
       Kai kawai Yoohan da ke saurarensa da kallonsa yake kaɗawa.
        Rich ya cigaba da faɗin, “Wannan itace Number datafi kira. Sannan da itanema mukafi samun bayanai. Sai dai matsalar da hausa language suke magana. Inaga dole sai madam ta taimaka mana. Wannan shine ainahin sunan da akai register ɗin layin da shi. *_Rabi'atu Halidu dauda_* kuma yanda alama ta nuna mana mai Number tana a cikin gidansu madam ɗinka. Sai dai bamu saniba ko anan take rayuwa, ko zuwa kawai takeyi”.
         “Gaskiyarka, dolene sai da taimakon Zeeynab zamu san wasu abubuwan kam. Tunda ita dai duk wanda ke cikin gidan ko shiga da fita ta sani”. Yoohan yayi maganar hankalinsa akan lap-top ɗin.
          “Tabbas wannan shine mafita, kuma itace hanya mai sauƙi. Dan inhar wannan Rabi ɗin tana a cikin gidan to itace first suspect ɗinmu, dan inhar aka samu nasarar kamata zamu iya samun bayanai masu yawa a wajenta”.
        “Okay ina zuwa” Yoohan ya faɗa yana mikewa. Ɗakin ya koma. Sai dai daga bakin ƙofar ya tsaya yay kiran Nu'aymah da ke zaune yanzun ta kunna television tana kallo. Babu musu ta taso inda yake dan bataga fuskar wasa tattare da shi ba. Kafin ta ƙaraso ya juya ya fito, hakan yasa itama biyo bayansa har wajen. Ya gyara mata kujerar kusa da shi ta zauna.
        Wayar da Richard ke dannawa ya ajiye ya ɗan kallesu, sai dai baice komaiba. Itama dai Aymah bata kallesa ba. Coffee ɗin da suke sha Yoohan ya nuna mata alamar ko tanaso?. Kanta ta girgiza masa. 
      Yace, “Okay, Please wani aiki zaki mana dama Sweet girl”. Kallonsa ta ɗanyi, sai kuma ta maida kanta ta duƙar. Shi dai Rich na jinsu amma bai saka baki ba. Sai ma latsa waya daya cigaba da yi yana turama Juliet ɗinsa text message.
          Lap-top ɗin Yoohan ya tura mata gabanta yana nuna mata Number Rabi da sunanta. “Kinsan wannan Number da sunan?”. Ɗan tsirama lap-top ɗin idanu Aymah tayi tana gyara glass ɗinta. Tai wani ɗan murmushi a bazata tana ɗagowa ta kalli Yoohan da shima ita yake kallo. “Sunan dai kam irin na mai aikinmu ne, sai dai ban riƙe Number ɗinta ba. Amma bara mu kira Umm sai ta turo mana”.
          Da ga Yoohan har Richard sunyi na'am da hakan. Yoohan ya mikama Aymah wayarsa alamar ta kira Umm ɗin. Number Umm ta saka tai dailing. Sai dai harta tsinke bata ɗagaba. Sake kira tayi, nanma har sun fidda ran zata ɗaga sai sukaji an daga. Zazzaƙar muryar Muhammad tai sallama. hakanne ya saka Aymah yin murmushi mai faɗi da cewa, “Uhm Auta kaine?”.
        Daga can yace, “Lah Aunty N dama ke ce?”. Murmushinta ya sake faɗaɗa. Sai da ya gaisheta ta tambayesa ya makaranta sannan tace masa ina Umm?.
      “Umm tana sashen Addah, amma bara na kai mata wayar”.
      Da sauri Yoohan ya girgiza mata kai. Hakan yasa itama saurin cewa, “A'a barta, amma ko zaka iya dubamin Number Rabi ka turo min yanzun?”.
       “Eh zan iya Aunty. Ranarma bani na tura miki Number Gwaggo ba da su aunty Zulfah”.
       “Yes, hakane my sweet Darling. Yanzuma ka turomin Please, amma ka nutsu ka ɗauki Number dai-dai kaji ko”.
        Amsa mata yay da to, sannan ta yanke wayar. Ko mintuna uku kuwa ba'ayi cikakku ba sai ga message ya shigo. Suna buɗewa sukaga Muhammad ɗinne ya turo. Number lap-top ɗin da wadda ya turo suka duba. Sai ko gata tazo iri ɗaya. A tare suka kalli juna. Cike dason jin dalilin zuwan Number wajensu Aymah tace, “Amma miya faru wai?”.
       “Karki damu zan faɗa miki. Saka earpiece ɗin nan ki saurari vn ɗin nan yanzu dai. Munason musan abinda ke ciki”. Babu musu ta amsa earpiece ɗin daya miƙo mata ta saka a kunne. shi kuma ya makala jikin lap-top ɗin yay mata playing na farko. 
       Shiru tayi tana mamaki cike da tsoro da al'ajabi, duk da ta daɗe tana zargin rabi na musu SARAN ƁOYE bata kawo abin ya kai har hakaba. Yana karewa ta zare earpiece ɗin daga kunnenta ta riƙe a hannu tana kallon Yoohan da duk suka zuba mata ido.
         Da damuwa tace, *_“Wai tana tambayarta ne yaya zamana yake a gidanku?. shine Uwaliya ta sanar mata ita dai bataga komaiba har yanzun, dan tunda muka shiga gidan na rakata ɗaki bata sake ganina ba har yanzu. Tanama ɗakin bata fitaba._* hakan na nufin kenan ranar farko da mukaje da Uwaliya gidan”.
      Sosai fuskar Yoohan ke a tsuke. Batare daya ce komaiba ya nuna mata ta maida earpiece ɗin. Sake mata playing na gaba tayi. Bayan ta gama saurare shima tai musu bayin, dan akan dai zaman gidanne. Na uku ma haka, har na randa Momy sukai hayaniya da Aymah. Sai randa kuma Gebrail ya shigarma Aymahn ɗaki wanda yay sanadin zuwansu Austria duk ta bama Rabi labari har suna kwasar dariya. Musamman ma Rabi har faɗi take ALLAH yasa Nu'aymah ta mutu acan wajen aikin, dan ta matuƙar tsanarta. Sannan ta godema Gebrail da yaba masa.
       A matuƙar firgice Yoohan yace, “Hasashena yana dai-dai kenan. Gebrail!! Gebrail!”. Yay maganar da dukan tebir ɗin gabansu da ƙarfi yana miƙewa. 
        Aymah da dama Gebrail ɗin ta zarga itama ta sauke numfashi da faɗin, “Na Gebrail ba shine important ba Yah Yoohan, tunda ALLAH ya kuɓutar dani. Bakuma sake yarda zanyi ya kuma samun damaba insha ALLAH. Wannan matar da kullum take nane da Umm ɗina tsahon shekaru itace abin duba. Bansan mi take buƙatar ji tattare da niba data addabi Uwaliya da tambaya kullum a kai na harda min fatan na mutu ta tsaneni. Sannan ita kanta Uwaliya kenan dama an kawotane dan ta dinga tattara bayanai akaina tana faɗa musu ko mi?. Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un”.
         Richard ne ya sauke nannauyan numfashi tare da kamo hannun Yoohan da ransa ke a ƙololuwar ɓace ya zaunar. “Cool down X-man. Maganar Madam nakan hanya. Na Gebrail mai sauƙine tunda a kusa da mu ya ke.......”
      A fusace Yoohan ya katsesa da faɗin. “Karku gayamin maganar banza mana Rich!!. Tayama zakuce nasa mai sauƙine shima? Ya shigarmin ɗakin mata sannan kuce mai sauƙi? Kenan raping ɗinta ya keson yi komi? Ni yaron nan zai shigarma ɗakin mata!!.....”
       Ba ƙaramin firgita Aymah tai da yanayin Yoohan ba. Dan tsantsar wutar masifa dake gauraye da kishi ta hanga cikin idanunsa. Gashin jikinsa duk ya mimmiƙe tsabar bala'i. Rich ya fahimci kishin ƴan maza ne ya motsa. Dan haka ya daga kafaɗarsa cikin lallashi yace. “Please ka fahimcemu. Gebrail bai ƙyautaba kam. Amma abinda zaka duba shi namune. Zamu iya hukuntashi a yau ɗin nan idan munso. Itako wannan fatama fa take Madam ta mutu. Kaga lamarin nata ya gawurta kuma akwai ban tsoro a ciki. Dan zata iya bata wani abunda zai halakata ma ba'a saniba........”
       Maganar Richard kam tamkar ta tsikari Nu'aymah ne. ta dubesa zuciyarta nason kawo mata wani tunani da sai yanzunne yazo mata a cikin rai ma ita. amma badai tace komai ba.
      Da ƙyar Richard ya samu Yoohan ya dawo hankalinsa akan zancen Gebrail suka cigaba da tattauna maganar Rabi.
       Ransa a dagule yace, “Wannan matar lallai akwai wanda takema aiki a gidan wannan ba basirarta bace ita kaɗai. Sannan akwai wanda ke laɓema mutane a gidan ta Window, kodai itace ɗin dai, kokuma yazam wanine daban shima”.
        Kallonsa Aymah tayi da sauri domin ƙara tuna abu na biyu. Tace, “Yah Yoohan kana nufin kaima ka taɓa ganin hakan a gidanmu?”.
      Kallonta yay da jinjina mata kai. “Tabbas nagani a randa naje gidanku game da pictures ɗin nan. Naga mutum a jikin Window ɗin Granny. Shinema ya bani haske akan lallai an ƙulla miki ne akan zancen ciki, kokuma akwai wani abu daban dasu Uncle su basu saniba. Amma kema kin taɓa ganine?”.
          “Na taɓa ganin inuwar mutum yafi a ƙirga jikin Windown ɗakina kona falonmu. sai dai ban taɓa kawo komai a raina ba dan bamayi zaton mutumu ɗin bane. Sai a daren da wannan abun zai farune lokacin cikina ya fara ciwo ina ɗagowa naga inuwar, sai kuma aka bar wajen shine dalilin zargin cewa mutumne a wajen”.
        Kallon juna Yoohan da Rich sukayi. Sai kuma duk suka dubi Aymah ɗin. Yoohan ya kamo hannunta cikin nasa da kulawa yace. “To waini abindama ya kamata tun wancan lokacin duk mu sani shine. Tayaya ma kika fara bleeding a waccan ranar?”.
        “Babu wanda ya taɓamin wannan tambayar, nima kuma ban taɓa tunanin bama wani amsarta ba,, duk da abin na'a cikin raina”. Tai maganar hawaye cike da idanunta.
     “Kiyi haƙuri, maybe kowama bai tuna bane, dan ana cikin tashin hankalin ciwonki shiyyasa. Amma na tabbata koda kowa baiso mikiba Uncle da Umm zasuyi tunanin miki ita. Yanzu ki sanar mana yaya abin ya faru?. Maybe mu samu wani evidence ta dalilin jin”.
      Hannu tasa ta ɗauke ƙwallar da suka cika mata idanu, Yoohan na shafa bayanta alamar lallashi. Cikin nutsuwa ta fara basu labarin tun daga fitowarta da gamo da Rabi datai ɗauke da zoɓo zata kai mata. Da shayi data sakata dafa mata har sauran abinda ya biyo baya ta suma. Sai da ta farfaɗo ne takejin sauran abinda ya farun a bakin Yusrah. Dan Umm bata taɓa mata maganarba har yanzu”.
      Matso da ita yay jikinsa ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa damtsen hannunta alamar lallashi, dan hawaye takeyi. Shi kansa sai faman sauke ajiyar zuciya yake a jajjere da taune lip ɗinsa na ƙasa. Richard kansa mamakin tsantsar salon makirci yake yi. Da ƙyar ya iya katse shirun nasu shi.
        “Wato idan na fahimta wannan matar itace ta bata abinda ya haifar da matsalarnan ta sha. To amma ni abinda ban ganeba anan, inhar da magani ta saka a cikin lipton ɗin ai dolene Doctors su gani? Su kuma san maganine ya haifar da bleeding ɗin. Amma kuma sai saɓanin hakan ma ya biyo baya kowa result ɗinsa na fita da zancen ciki. Kaina ya kulle gaba ɗaya”.
       Ita kanta Nu'aymah kanta ya kulle ɗin. Yoohan kam baice komaiba dan zuciyarsa a wuya take natuƙa. Ganin yanda har yanzu Nu'aymah ke hawaye ya saka Rich cewa, “Brother kaje da ita ta samu nutsuwa. zuwa dare sai mu ƙarasa magana dan dole na juya Nigeria da wuri. Akwai maganar da nake son nayi da ku kuma zuwa anjima daman”.
      Kai Yoohan ya jinjina masa kawai batare da yace komai ba.

       Bayan wucewar Rich sumbatar kan Aymah Yoohan yayi. A hankali yace, “Is ok. Kukan ya isa haka. Na miki alƙawarin insha ALLAH sai inda ƙarfina ya ƙare wajen amso miki haƙƙinki ga duk ma wanda keda hannu akan wannan al'amarin. Dan haka banason ganin hawayenki masu daraja na zuba akan azzalumai ok?”.
       Kanta ta jinjina masa. Ya miƙe riƙe da ita suka koma cikin ɗakin. A kujera ya zauna ya zaunar da ita saman cinyarsa. Zamewa tai a hankali ta kwanta dan jikin nata bawani ƙarfi yake mataba har yanzun. Ɗankwalin kanta ya zame ya sumbaci sumar kanta daketa ƙamshin gyaran jiya har yanzun. Cikin raɗa-raɗa yace, “Sweet girl!”.
       “Uhyim” ta faɗa kamar wadda barci ke shirin ɗauka.
     Ya tura hannunsa a rigarta yana shafa cikinta. Idanunsa a lumshe yace, “Bani labarinki, ina nufin yanda kika rayuwu a gidanku, da yanda kowama yake rayuwa a gidan”.
      Hannunta ta ɗora akan nasa dake shafa cikinta, sotake ta janye amma yaƙi yarda, sai ma jitai yayi sama da hannun. Ɗan zabura tayi da ɗaga kanta ta dubesa. Idanunsa a lumshe suke, sai dai yana kallonta. Hakan ya sakashi yin ɗan murmushi da ɗaga mata gira ɗaya.
      Tace, “ALLAH saima na fasa”.
Ƙasa yay da hannun nasa yana cigaba da murmushinsa bai dai ce mata komaiba. Itama sai ta saki numfashi a hankali, dan gaba ɗaya wuyar datasha jiyace ke dawo mata a rai. Kaudata tai a zuciyartata ta fara bashi labari tundaga asalin kakansu Malam Hashim ɗan jibiya har kawo yanzun. Yakan mata tambaya akan inda bai fahimtaba tai masa ƙarin bayani. A haka lokacin sallar la'asar tayi suka tashi suka gabatar. Bayan sun idan yace ta shirya suɗan fita tunda yaga jikin nata da sauƙi.
       Cike da ɗoki kuwa ta shirya. Sai da ta kammala yana fesa turare ta dubesa tana kumbura fuska. “Amma dai bada wannan jelan naka zamuba ko?”.
      Turaren ya ajiye yazo gareta, fuskar dai babu walwala. Hancinta yaja da faɗin, Silly girl waye jelana?”.
      “Wannan basamuden Solomon ɗin mana. I don't trust him bansan miyasaba”.
      Da mamaki yake kallonta, furicinta na masa yawo a zuciya. Yaɗan ranƙwafo ya sumbacin laɓɓanta da sukasha lipsgloss sunata walƙiya. “Sweet girl! Kinada rigima da yawa. Miye laifin Solo kuma?”.
    “Oho, nidai kawai I don't like him gaskiya”. Tai maganar da juya masa baya.
        “Alright. let go”.
“Indai da shine fa bazaniba”.
       “Trouble maker badashi ba ne” yay maganar yana raɓata ya wuce.
       Bin bayansa tai tana ƙunƙunin mita. Bai dai juyoba duk da yanajinta. Amma sai da yaɗan murmusa. Haka suka fice abin sha'awa. Yau dai taxi suka shiga bai amshi motar hotel ɗinba dan garau yake jinsa da sabuwar lafiya ma.

*_ABUJA NIGERIA_*

          A rayuwa madam Chioma zata iya cewa bata taɓa gamo da dare mafi tsayo irin na yau ba. Duk uwar giyar data kwankwaɗar ma cikinta a wannan dare baisa ta samu nutsuwar da take buƙata ba. Dan barcin kansa ma gagarar idanunta yayi. Ƙarfe huɗu na asuba na bugawa ta tashi tai wanka ta shirya duk da tana a cikin halin maye. Burinta kawai takwas tayi subar gidan dan jirginsu sai tara dai-dai zai tashi zuwa River state. Tana zaune wajen kallon agogo ta ɓingire barci. Hakan yama Madam Rebecca daɗi. Dan dama ta addabeta akan ta shirya. Sake kwanciyarta tayi tai barci, sai takwas ɗinma ta tashi tai wanka tai shiri. Tara saura kwata ta tada madam Chioma dake barci a kujera.
     Da wani uban ihu ta tashi saboda ganin abinda agogo ya nuna.
    “Hhheeyyyyy!!!! Heyyyy Jesus!!! Rebecca!.....”
     Da sauri Madam Rebecca ta dakatar da ita ta hanyar cemata “Please muje nidai karmu makara”. 
      Da yake tafiyar itace mafi girman damuwarta sai tai gaba jiki na rawa dan da gaske barci takeji yanzun. Amma da zaman wannan barcin gara ta ganta a gaban bokanta.
      Aiko sun kusan isa a makare, dan har an fara shiga jirgi. Anan madam Rebecca tabar motarta cikin airport ɗin ta riƙe Madam Chioma dake malangarin suka shiga suma. A cikin jirgin ma barci ta kamayi, koda suka iso kuma cikin mintuna ƙalilan sai da taimakon madam Rebecca ta fita. Taxi suka ɗauka ya kaisu can tashar da zasu hau motar kusa da ƙauyen. Nanma suka samu drop da ƙyar saboda rashin wadatuwar motocin............✍


*_Ga tsoron mutuwa ga son soyayya su o, e zafafa's fan🙄😉😜😂🏃🏃🏃._*

*_BARKA DA JUMA'A😍😍🤗_*


Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.

No. 64

............Motar ta ajiyesu a wani ƙauyene dan iya nan kawai zata iya shiga saboda uwar zaizayar ƙasar dake damun ƴan kudancin ƙasarmu duk ta cinye titunan. Ruwa mai uban sanyi na kwatami madam Rebecca ta samu ta sheƙama madam Chioma saboda sunyi-sunyi ta fita a motar ita da drivern madam Chioma da giya ke aiki a kanta taƙi fita.
      Firgigit ta kawo numfashi tana wani bada faɗi tamkar zata make mutum. Duk baya sukaja kam suka bata fili. Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta share fuskarta tana hararsu. 
     “Rebecca minene haka kuma?”.
Dariya Rebecca tayi tana miƙama yaron data ari roba a wajensa. “Inda ba hakan nai mikiba zaki tashi ne. Lokacin da ya bamu ya kusa cika kuma kinsan halinsa”.
      Zabura kuwa madam Chioma tayi ta wawuro handbag ɗinta tana ambaton Jesus. Haka yasa itama Madam Rebecca ɗaukar tata handbag ɗin suka zagaye zaftarewar ƙasar suka koma kan titi sosai. Suna tafiya suna ƙoƙarin tare mashin dake wucewa. Amma kowanne sai kaga da mutum. Sai da sukai tafiya mai nisan zango sannan suka samu mashin ɗaya. Badan zai ishesuba suka hau, dan madam Rebecca balaifi tanada jiki. Tafi madam Chioma ƙiba. Haka suka shirma cikin jejin da korayen ciyayi suka ƙawata suna nishin matsuwa. Tafiya sukai sosai kafin su isa wani ƙauye again. Anan mai mashin shima ya saukesu dan zasu hau kwale-kwale ne. Ga madam Chioma da tsoron ruwan masifa. Duk sanda sukazo wajen bokan nan a tsorace take. Shiyyasa wani lokacin tafi buƙatar Rebecca tazo mata sai ta biyata kuɗin da duk ta buƙata. Haka suka shiga kwale-kwale tanata faman ƙunshe kanta a cikin cinyoyi. Tafiyar mintuna ashirin ta kaisu gaɓar ruwan. Daga haka kuma suka kwashi ƙafafunsu suka nausa cikin jajenin da bazaka taɓa ɗauka akwai mutum mai numfashi a wajen ba. Amma da yake zukatansu sun bushe ko tsoro basaji. Sun iso ƙauyen da bokan yake a galabaice. Kamar yanda ƙa'idar shiga wajensa take suna isowa ƙofar fadarsa suka cire duka suturar jikinsu. Haka masu tsaron ƙofar suka basu hanya suka shiga tsirara haihuwar uwarsu (😱🤦🏻). Ba wannan ne ya firgitaniba. Dan su nasan komaima iya aikatawa zasuyi. Shigarsu wajen ne ya rikita tunanina da ɗarsa tsoron duniya a raina. Dan kuwa mutanene cike da wajen suna jiran layi kowanne tsirara yake. Abin kaico da takaici da ALLAH wadai harda musulmai a wajen, kai harma Hausawa saika samu ma'abota son duniya da ruguza lahirarsu. Manyan mutane ƴan siyasa da hasashenka bai taɓa baka ganin irinsu a wajenba sai gasu tumɓur suna zazzare idanu a fadar boka. Manyan mata masu neman duniya da gudun kishiya suma gasu nan ba'a magana. Wannan ya ƙara tabbatar min da sutura na rufawa bawa asiri a idanun mutane. Dan da yawan mutane munana ne idan ka gansu tsirara wlhy🙄.
        Sai da suka tsaya gaban wasu ƙartai akai musu wankan ƙa'ida kafin su ƙarasa su hau layi inda sauran suke. Suna nan zaune masu shiga na shiga suna fitowa har layi yaxo kansu suka shiga suma.
      ‘Wa'iyazubillah’. Ɗakin bokan cike yake da gumaka na dodannin tsafinsa ta kowace kusurwa. Suna shiga suka zube sukai sujida a gaban waɗanan gumaka. Kafin su miƙe zuwa wajen bokan dake hakimce a kujera sai kace sarki. Shima sujidar sukai masa sannan suka miƙe tsaye haihuwar tsoffinsu. Shima dai a tsirarar yake dama🤦🏻. Gashi ƙaton gaske mummuna baƙiƙƙirin matsiyacin sheɗani. Kallon madam Chioma yayi ya kece da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya haɗe fuska.
      “Yaron da kike tattali da burin mallaka yana neman ƙuɓuce miki ko? Hhhhhhhh!!!!. Ai tun farko kece kikai sakaci. Miyasa kika barsa yay aure?”.
      Kuka ta fashe da shi, “Bangaruta ba laifina baneba. Mijina nane ya cikani da daɗin baki akan ya yarda yaron ya aureta ne dan ya halakata da babanta. Shiyyasa na yarda ni kuma. Tunda nasan ka bani abinda bazai iya taɓa kallon mace da suffar mata ba”.
        “Hhhhhhh!!!!!. Yardarki kuwa ta zamar miki matsala. dan wannan yarinyar daya aura tafi ƙarfinki. A duk inda take tana zagaye da wani haske da ko iya ganinta ni kaina banayi. A yanzu haka bana iya ganin yaron ma kansa a ƙwaryar tsafina saboda kasancewarsu tare. Ke koma basa tare shima bana ganinsa a watannin nan gaba ɗaya.....”
      “Bangaruta ka taimakeni ta tsafemin shi. Na shiga uku shikenan tawa ta ƙare”.
       “Hhhhhhh taki zata ƙarene idan wannan aikin dazan miki yazam bai kamasu ba”. 
      Da sauri ta nutsu tana sharar hawaye. Ya kuna ƙyalƙyalewa da muguwar dariyarsa mara daɗin ji. Kamar yanda na faɗa miki tun farko aikinmu dake kansa bazai taɓa barinsa mu'amula da mataba sai ke. dan haka ki kwantar da hankalinki wannan kam tabbatacciyar maganace hakan bazai faruba. Yanzu zakiyi ƙoƙarin rabasa da yarinyarne kawai. gaba ɗaya hankalinsa zai dawo gareki a wannan karon dan bazamuyi masa da wasa ba”.
       “Nagode Bangaruta, sai dai kumafa igiyar nan ta tukunya ta kwance, wannan shine ya girmama tashin hankalina”.
     “Karki damu da kwancewarta, mu ta wajenmu tana nan a ɗaure. Dan bazai taɓa kwanciya da wata maceba sai ke. Cike dajin daɗi ta duƙe gabansa ta sakeyi sujida🤦🏻😭. A take ya haɗa mata duk abinda zatayi akan Yoohan da Nu'aymah. Ta dire masa maƙudan kuɗin daya buƙata sannan suka fito bayan itama Rebecca ta amshi nata aka abinda ya shafeta.
     A ranar suka sake juyiwa cikin River state a matuƙar galabaice. hotel suka kama zasu kwana sai zuwa da safe su koma abuja.

_____________________

     *_VIENNA AUSTRIA_*

     Su Yoohan da basusan wainar da ake toyawa ba sunacan hankalinsu kwance. Dan wani shagon cin ƙwalam da maƙulashe na kalolon chocolate da ice-creem ya kaita. Ko sha zumamu baya faɗama Aymah shan zaƙi ba. Tako dinga lodama cikinta cike da farin ciki. Duk gargaɗin da yake mata akan tabi a sannu saboda duk zaƙin da take danƙara zai tambayetane a wajen period bata sauraresaba. 
         Sun daɗe sosai a wajen, kafin su fito da ƙafa kamar yanda ta buƙata wai tanason taga gari da ƙyau. Aiko ta gani ɗin. Dan birnin Vienna ya matuƙar haɗuwa da gine-gine masu ƙayatarwa. Sai da ta fara hakkin gajiya sannan ya tsaida musu keken doki suka shiga ya maidasu masaukinsu.

        Suna isowa wanka Aymah ta shiga. Sai faman complain take wai ƙafafunta na ciwo.  Baice mata komaiba shi dai tunda itace ta ja musu shan wahalar ai. Amma da yake ta fisa baki shine take cewa shine.
    Wanka tayo ta fito tana ɗingisa ƙafa wai ciwo take mata. Da kallo kawai ya bita shi dai, ya ɗan girgiza kansa yana miƙewa da faɗin, Silly girl maganinki kenan ai”.
       Juyowa tai tana hararsa. Sai dai shi baimasan tanayi ba dan tuni ya shige toilet ɗin abinsa. Koda ya fito ya iske har tayi shirin barci. Sai dai bata kwanta ba. Tana kwance a sofa tana kallo. Shirin barcin shima yayi. Yana kammalawa wayarsa tai Ring. Miƙewa tai zata kawo masa sai taga ya nufota. Hakan yasa ta koma ta zauna harya ƙaraso. Yana amsa yaga Rich ne, sai ya maida kallonsa gareta. “Please sa hijjab muje mu ƙarasa maganarnan yana jiranmu”.
      “Okay” ta faɗa tana miƙewa. Ta ɗauki hijjabin sallarta ta saka tare da zura Slippers suka fito harabar hotel ɗin wajen swimming pool ɗin nan da mutane keta shanawarsu tamkar rana. Daga can gefen garden ɗin hotel ɗin suka koma. dan shima dai mutane ne keta hidimarsu. Aymah ta fahimci mutanen nan sam basa banbance dare da rana halan. Dan koda yaushe su dai hidimarsu suke hankali a kwance.
       Zama sukai inda suka iske Richard. Ta gaishesa da ƴar sakewa fiye da ko yaushe. Shima fuskarsa da murmushi ya amsa mata harda tsokanar wai ta ƙwace masa aboki. 
      Murmushi tayi kawai batare datace komaiba. Shi dama Yoohan bai saka bakinsa ba, sai dai ya bama Rich ɗin hannu sun gaisa.
      Bayan an kawo musu Coffee ɗin da yay musu order itama Aymah aka kawo mata lipton data buƙata sai suka fara tattaunawa akan yanda zasu ɓulloma lamarin. Suna gamawa da maganar gidansu Aymah Rich ya turama Joseph saƙo akan ya janye masa hankalin Yoohan.
     Haka kuwa akayi, ko mintuna biyu da tura saƙon ba'ayiba kira ya shigo wayar Yoohan. Ɗagawa yay suka gaisa da Joseph batare da ya tashi ba. Sai daga baya kuma ya miƙe saboda magana da Joseph ɗin yace yanason suyi.
           Yana barin wajen Rich ya kalli Aymah data ɗauke kanta daga garesu tana kallon wata mata da yaranta twins da babansu dake gefensu. Sai soyayyarsu suke zubawa da tattalin ƴan yaran nasu. jitai sun bata sha'awa sosai har tana kwatanta kanta da Yoohan ace yaran nasune wai (ƴar baba malam an fara hankali kenan🤣).
      Gyaran murya da Rich yayine ya sakata juyiwa taɗan kallesa. murmushi yayi shima dan haka kawai yay zargin abinda take tunani akan mata da mijin da yaransu. 
       “Inason muyi magana Please, sai dai tsakanina da ke ne banason Yoohan ya sani”.
      Cike da mamaki ta tsura masa idanun tana tsuke fuska. Saurin girgiza mata kai yayi yana murmushi. “Am sorry sister akan gidansu ne karki zargi komai”.
      Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye da ɗan shafa gefen wuyanta alamun taji kunya. Shima sai ya ƙara murmusawa dan ta birgesa. Hakan na nufin a duk inda take zata karema ɗan uwansa mutuncinsa. Wayarsa ya miƙa mata tare da miƙewa yabar wajen. Can ya koma inda Yoohan ke zaune yana waya dan ya fahimci shima hankalinsa na kansu.
      Binsa da kallo Nu'aymah tayi. sai kuma ta buɗe video ɗin data gani akan wayar, da alama shi Rich ɗin ke buƙatar ta gani. Ba ƙaramin bugawa ƙirjinta yayi ba, saboda cinkaro da kanta a ranar data shiga ɗakin papa ta ɗakko hoto. Sai dai iya falone. har shigowar Papa da Andrew falon. Shigarsa bedroom ɗin da fitowarsa da sake komawarsa. Harma fitarta da kayan harƙallar papa da suke magana akai shi da Andrew. Cocaine ce da wasu ƙwayoyi, sai abinda ke cikin ɗayar jikkar dai bai buɗeba, hakan yasa batasan minene ba. Hannu tasa ta sharce zufar data tarar mata a goshi. Ta ƙara playing ɗayan video ɗin dake a ƙasan wancan shima. Shi kuma papa ne da wasu mutane yana bada kwangilar a kasheta duk sanda suka dawo Nigeria. Randa aka kashetan kuma a kashe baba malam shima. ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ ta shiga maimaitawa tana kallon inda Yoohan da Rich suke zaune. Ganin Rich nata jan ra'ayinsa ga barin kallontane ya sakata kauda kanta tana taunar lip ɗinta. A ranta kuwa sake jinjina lamarin papa take da jin tsanarsa a ranta. Lallai saita tona dukkan sauran sirrin mutumin nan duk da kasancewarsa mahaifin mijinta. To amma shi wannan Richard ɗin mi yake nufi da bata video ɗin ta gani?.
     Kafin ta nemo amsar tambayarta taga sun miƙe sun nufota. Fita tai daga cikin folder ɗin da sauri ta ajiye masa wayarsa da ƙoƙarin control ɗin kanta dan kar Yoohan ya gane.
        Rungumeta Yoohan yayi cike da tsantsar farin ciki yana faɗin, “Oh my Sweetheart ke haske ce a rayuwarmu. Rich yace yanason zama musulmi”.
       Cike da razana Aymah tace, “What?!!”. Sakinta Yoohan ɗin yayi yana dariyar farin ciki da jinjina mata kansa. kafin yace wani abu Rich yace, “Tabbas abinda X-man ya faɗa ashine gaskiya Sister. Zama da mahaifinki ya ƙwaɗaitamin son kasancewa musulmi. Hakan ya ƙara tasiri ne a raina a ɗazun dana ganku kuna salla abin ya birgeni”.
      Kallonsa kawai Nu'aymah take cike da tuhuma. Dan gani take wani ƙullinne kuma yake shirin musu ta hanyar shiga musilinci.
     Fahimtar hakan da yayine ya sakashi girgiza mata kai idanunsa na kawo ruwan ƙwalla. “Na rantse da ALLAH ni Richard inason shiga musilinci ne da zuciya ɗaya bada wani daliliba. Ki yarda ke haske ce a garemu kamar yanda mijinki ya faɗa”.
        Numfashi Aymah ta sauke tare da furzar da iska ta lumshe idanunta hawaye suka gangaro mata a hankali. Sai kawai ta faɗa jikin Yoohan ta rungumesa tare da rushewa da kuka. “I love you so much Yah Yoohan”. Ta faɗa a bazata tana ƙanƙamesa da ƙyau. 
       Da sauri Yoohan ya ɗagota yana kallon fuskarta. “Cikin rawar muryar zuwan bazatan maganar yace, “Really? Please sake faɗa naji dan ALLAH”.
       “Babu ƙarya ko yaudara a maganata. Da gaske ina SONKA Yah Yoohan. Na rantse da ALLAH ina sonka da gaba ɗaya zuciyata”. Ta kuma rungumesa.
      Ai gaba ɗaya yama manta da wani Rich dake wajen. cikin sauri yaja hijjab ɗin jikinta ya shige ciki tare da zame mata fuskarta itama ta koma ciki. lalubar bakinta yayi ya manne da nashi. Duk da kunya da tsoron abinda ya faru dake cikin ranta hakan bai hanata tayasa abinda yakeyiba batare da tasan ta zurma ba.
        Dariya Rich ya sanya musu tare da miƙewa yabar wajen, can inda suka baro da Yoohan ya koma ya zauna yana kallon wani wajen daban, zuciyarsa fal da wani irin farin ciki da shi kansa baisan na minene ba.

         Da ƙyar Nu'aymah ta ƙwaci kanta daga hannun Yoohan da ke neman sakin layi. Ta sauka daga jikinsa tare  tabar wajen da gudu. Kasa motsawa yay saboda kasala data saukar masa. Ya kife kansa a table ɗin kawai yana sauke numfarfashi a jajjere.
      Ganin wucewarta da gudu ya saka Rich tasowa inda Yoohan yake. Damtsen hannunsa yaɗan buga da faɗin, “Mara mutunci, a gabana ma babu ɗaga ƙafa”.
        Gani kawai yayi Yoohan ɗin ya miƙe ya rungumesa yana faɗin, “Thanks you Rich, thanks you so very much. Gashi a dalilin gane gaskiyarka ta faɗamin kalma mai tsada dana fidda ran samu daga gareta. Wlhy ina sonta fiye da zaton mai hasashe Rich. ashe itama zata soni. ALLAH na gode maka. Rich ka zama sanadin farin cikina”.
      Dariya sosai Rich keyi ta jin daɗin ganin farin cikin Yoohan ɗinsa da yake tsananin so da ƙauna. Suka zauna kowanne fuska ɗauke da murmushi. Cikin ɗage gira Rich yace, “Dama makauniyar soyayya kakeyi kai ashe?”.
       “Makauniyar da ko idanu ba'a yanka mataba kuwa Rich, amma yanzu ta sanadinka gashi har numfashi ta samu”.
      “To Alhmdllh, dama ni na fahimci tana sonka wlhy. Kawai dai akwai yarinta tattare da itane. But ko dai yayane ma kun dace. Dan na jima banga masoyan da suka dace da junaba irin ku. Dan haka Mr Lover Congratulations joooh”.
        “Thanks you dear. Congratulations too. Nayi farin ciki da kai saurin gane gaskiya. Ya rabbi ka karɓi tubanmu ka gafarta mana”.
     “Emen dear. Yanzu nawane zan biya? A wajenwa kuma zan biya”.
     Fuska Yoohan faɗaɗe da murmushi yace, “Shi muslinci ba'a biyan komai a wajen shigarsa. Kalmar shahada kawai zaka faɗa. Amma bara na kira Uncle first”.
      Kai Rich ya jinjinama Yoohan. Ya ɗauka wayarsa yay kiran baba malam cikin sa'a kuwa ya ɗaga. Bayan sun gaisa yay masa bayanin komai cike da jin kunyar da Aymah ta sakashi a ciki tun ɗazun. Dan duk yau ma ya kasa kiran baba malam ɗin. Yanzun ma shaf ya mantane saboda ɗokin musulintar Richard.
        A take baba malam yace, “Ina mamana? Duk bayanin dazan muku itama zata iya yinsa insha ALLAHU Yahya”.
     Cike da jin kunya Yoohan yace, “Tayi barcine Uncle. Gashi kuma Rich ɗin zai dawo gida nan 9ja gobe. Idan kuma ya bari sai yazo wajenka to”.
        “A'a Yahya. Gara dai ya cikasa niyyarsa dan ranmu ai ba'a hannunmu yakeba. Nasan kaima zaka iya masa bayani akai. indai zaka iya tuna duk yanda kayi lokacin daka musulinta”. 
      “Insha ALLAH Uncle. Amma zanso kana saurarenmu”.
     Dama baba malam ya bashi. Dan haka Yoohan ya maida kiran video call. A take Yoohan ya bama Rich kalmar shahada. Bayan ya maimaita baba malam ya faɗaɗa masa bayanai masu muhimmanci tamkar yanda yayma Yoohan a wancan karon. Sai ga Yoohan da Rich suna hawaye. Sunja lokaci mai tsaho kafin baba   bashi zaɓin suna. A take Rich yace ya bashi dama ya zaɓa masa kowanne.
     Cikin jin daɗi Baba malam yace, “Akwai sahabban manzon ALLAH da sunayensu sukai fice a garemu, bara na lissafa makasu, tare da na Annabawan ALLAH da Yahya ya samu ɗaya daga cikin sunayensu shima”.
    A tare suka jinjina masa kai.
   “Abubakar, Umar, Usman, Aliy.......”
Kafinma baba malam ya ƙarasa Rich yay saurin faɗin, “Uncle inason Omar”.
        “Masha ALLAHU Son. Daga yau kazama Umar. ALLAH yasa ka zama mai koyi da ƙyawawan halayen Umar da gaskiyarsa da jarumtarsa harma da yawan ibada”.
       A tare suka amsa da amin.
Daga haka suka sake ɗan tattaunawa sannan sukai sallama da shi. Masaukin Rich suka nufa. Inda Yoohan ya koya masa wanka da alwala harma da salla. Daga haka ya barsa. Saboda gobe idan ALLAH ya kaimu Omar (Rich) ɗin zai koma Nigeria.
      Sun sake rungume juna suna hawaye da sake godema UBANGIJI. Sannan sukai nafila raka'a biyu a tare ta godiya ga ALLAH. Omar (Rich) yay sallar Magrib da isha'i dan lokacinsu bai gushe ba har sai alfijir ya keto. Musamman ma isha'i.
       Daga haka sukai sallama Yoohan ya nufi nasu masaukin cike da ɗoki da farin ciki.

      Nu'aymah dake kallo tanajin motsin buɗe ƙofar tai azamar kifewa rubda ciki dajan filo ta tura kanta ciki. Murmushi yayi yana ƙarasa shigowa dan ya rigada ya ganta. Television ɗin ya kashe tare da wutar ɗakin lokacin da yake ƙoƙarin hawa gadon. Cikin nutsuwarsa ya kwanto bayanta yana sauke ajiyar zuciya tare da saka hannu ya ɗauke filon data tura kanta a ciki. 
       “Wayyo Hajjo ƙaton nan zai ɓalla miki jika”. Tai maganar cike da rikicin kunya da nauyinsa daya sakar mata.
       Murmushi yayi da rage mata nauyinsa sannan ya birkitota. Da sauri ta kanannaɗe masa jiki dan batason su haɗa ido.
       Hannunsa ya tura cikin rigarta yana ɗora bakinsa akan kunnenta. Cikin raɗa yace, “I love kunyankin nan my sweet angel, my sweetheart my Heartbeat. My everything”. Ya ƙare maganar da ɗan cizar kunnenta kaɗan. 
       Kukan shagwaɓa ta saka mata tana murza ƙafafunta a jikinsa wai saita rama. yanda taketa masa mutsu-mutsu a jikine ya nema susutashi. ƙwaɗayin da yaketa dannewa tun da rana ya kasa dannuwa. Cike da kasala da tsumar jiki ya lalubi bakinta ya manne da nashi. Tun yana tunanin tsayawa iya kiss ya rage zafi har hakan ya nema fin ƙarfin ƙoƙarin nasa. Gaba ɗaya ya birkice mata. Tun tana biye masa da wauta harta koma masa kuka dan bata manta wahalar datasha daren jiyaba. 
        Duk yanda Yoohan yaso haƙuri ya bar Nu'aymah hakan ya gagara. cike da fita hayyaci ya fara sarrafata. Yau ma dai an maimaita na daren jiya, sai dai kukanta ya sakashi taƙaita tafiyar batai nisan zango kamar ta daren jiya ba ya tausaya mata dan yasan bata gama dawowa hayyacinta ba.
        A take kuwa jikinta ya ɗime da zazzaɓin wahala. Hardasu rawar sanyi. Yasan ya ƙara laifi mai girma. Dan haka yayta lallashi da ban haƙuri harya samu ya kimtsa mata jiki yau ma yay gashi dan yasan zataji ciwo a wajen balle gashi yayi fami ne.
       Da taimakonsa tayi wankan tsarki, shima yayo sannan ya taimaka mata suka fito. Lallaɓata yay tasha yogurt da maganinta, kafin ya ƙara mata shirin barci. Sai da ya sake kimtsawa shima sannan ya hawo gadon ya rungumeta dan harma ta fara barci. Irin allurar ɗazun da rana ta rage raɗaɗi yay mata. Kuka ta fasa masa jikinta na matuƙar rawa. Yay saurin haɗe bakinsu waje guda. Sai da ya janye allurar sannan ya janye bakin yana furzar da iska tare da rungumeta da ƙyau a jikinsa yana shafa bayanta da faɗin, “Am so sorry sweetheart. Please forgive me”.
         Luf tayi a jikinsa tana zirar da hawayen. A haka barci yay gaba da ita yana faɗa mata kalamai masu sanyi cikin kunne da hura mata iska mai daɗi. Jin ta fara sauke numfashi na alamar barci shima saiya shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Yana ƙara jin ƙaunarta mai tsanani tana ratsa masa zuciya da dukan jikin sama gaba ɗaya. Ta zama ta farko a zuciyarsa. Ta farko a sirrinsa. Ta farkon haskama rayuwarsa hanya. Ta farko.... Ta farko.... Da yawa harma baisan iyakaba. Insha ALLAH kuma itace zata zama ta farko har ƙarshen rayuwa🤗😍.

*_Muma ALLAH yasa mu zama na farko ta ƙyawawan hanyoyi ga mazajenmu har ƙarshen rayuwa my dear fans. Ba dole sai kin kasance matar farko ba zaki zama ta farko😋😘. Kota huɗu kikaje ƙyawawan halayenki zaisa ki zama ta farko😍. Uwar gida kema dage ki riƙe gam kar a ƙwace miki ta farko😉🤗😅._*

_________________

                  Washe gari haka Nu'aymah taita zubama Yoohan shagwaɓa da raki yana faman lallaɓata da lallashinta. Tasa dole ya kira mata baba malam da Umm da hajjo. Inda anan itama hajjon ta fahimci takwararta ta kai mutuncinta gidan aurenta. Hakan ya mata matuƙar daɗi harta kaita da yin sujidar godiya ga ALLAH. Cike da tsantsar alfahari da jin daɗi ta kira Ananah ta sanar mata. Sosai Ananah taji daɗi tana godema ALLAH daya wanke Aymah cikin sauƙi a garesu bisa hikimarsa da rahamarsa. Daga haka sukai gum da bakinsu suna jiran bayyanar gaskiyar ga kowama cikin hikimar UBANGIJIN al'arshi.
      Da ƙyar Yoohan ya samu yaje sukai sallama da Omar (Richard) da zai wuce Nigeria a yau. Daga haka ya dawo wajen ƴar amaryarsa sarkin shagwaɓa da shiririta. Haka suka kasance a gaba ɗaya wannan yinin cike da so da ƙauna. Dan itama tun tana nokewa da ƙunshe-kunshe harta saki jikinta duk da dai akwai kunyar tattare da ita, saboda ta kasance tarbiyyarta tun fil'azal...........✍



Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 65

..............A hankali soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi ta cigaba da shiga tsakanin ma'auratan masu banbancin yare da yanki cike da birgewa. Yayinda Aymah ke matsayin malama ga Yoohan a ɓangaren ilimin addini shima sai ya zame mata malami a ɓangaren sanin soyayya da rayuwa. Dan sosai yake yawo da ita a lungu da saƙo na ƙasar Austria har wasu jihohinma suna zuwa yawon buɗe ido.
      Tun tana tsoro da masa raki a shimfiɗa harta fara sakin jikinta da sabawa. Dan jarumin nata namijin gaskene babu wasa. Baya takura mata yanda zata wahala. ba kuma ya barinta ta shagala.
      Sai ga Nu'aymah tai wani irin murjewa da ƙibarta na dawowa, (kunsanfa wannan harkar na gyara wasu matan harma da mazan🙈, shiyyasa da yawa amare farkon aurensu zakaga sunyi ɓulɓul da su🏃). To ga Nu'aymah ma dai an dace. Balle abin ya haɗa da kwanciyar hankali data samu, babu mai hantararta babu mai damun rayuwarta. Abinci saita zaɓa. Kullum zatai waya ko video call dasu Umm. Ga lafiyar jikinta Alhmdllh sai ƙaruwa take ƙarayi dan tana shan maganinta da ƙa'ida kasancewar Yoohan tsaye yake akanta da tsantsar kulawa.
      Takanji yana waya da papansa da momynsa (Madam Chioma) sai dai yanda bai taɓa cewa gashi su gaisaba itama bata taɓa nuna sha'awar hakanba. Garama Momy ranar ta kira yana wanka har sau uku. Ganin wayar na wajenta ya sakata ɗagawa suka gaisa. Sai dai yanda Momyn ta amsa mata a daƙile ya sosa ranta. Dan ta fahimci har yanzu da sukai nesa da juna ba ƙaunarta takeyiba. Su Momy Destiny ne dai ta gaisa dasu kusan sau uku-uku harda su Victoria. Amma su tom and jarry mama debora ko yaya jiki basu taɓa aiko mata da shiba balle suce zasu gaisa da ita a waya. kuma taji ranar duk sai da suka gaisa da Yoohan. Gebrail nema ta lura idan ya kirashi baya ɗagawa, daga bayama sai taga ya sakashi a black list.
  
         Gaba ɗaya ta hana Solomon musu gadi. Dan yanzu duk inda zasuje tuburewa take akan itadai bazataba inhar sai Solomon ɗin ya bisu. Hakan yasa Yoohan ya yanke shawarar kawai ya sallamesa ya koma Nigeria, dan baiga amfanin kisan kuɗin da yake ba a dalilin zaman Solomon ɗin tare da su.
       Randa ya samu Solomon da maganar komawa Nigeria hankalinsa yayi matuƙar tashi. Ya kira iyayen gidansa ya sanar musu da hukuncin Yoohan ɗin. Hakan yasa papa kiran Yoohan ya nuna masa bai amince da dawowar Solomon gidaba. Dan bazai yarda ya barshi shi kaɗai yana yawo ƙasashen duniya a cutar masa da shi ba.
       Yanda Aymah ta tubure kuma akan indai Solomon zai cigaba da kasancewa da su sai dai ita ta koma Nigeria wlhy yasa kan Yoohan ɗaukar zafi. Yayima Aymah lallashin duniya akan tabar zancen Solomon tunda papa ya dage amma sam taƙi saurarensa. har takaisu dayin ɓacin rai ranar akai barci kowa na ƙarshen gado. Washe garima taƙi kulasa shima ya shareta. Sai daga baya yaso su shirya taƙi. (A raina nace hummm Yoohan bakasan kafiyar Aymah bane ba). 
        Wannan tuburewar tata ya ƙara bashi haushi. Harya yanke shawaran ta shirya ta koma Nigeria tunda bazataji lallashinsa ba.
      A mamakinsa kuwa sai yaga ta hau haɗa kayanta. Dan itafa tabbas tayi alƙawarin bazata sake zama inuwa ɗaya da Solomon ba. Dan tsaf ta gama fahintar wannan nanema Yoohan ɗin da yakeyi akwai wata a ƙasa. tabbas da gaske akwai abinda su papa suke ɓoyewa game da Yoohan ɗin. Inba hakaba minene na nana masa guard a duk inda yake. Sannan sau biyu tana kama Solomon na waya da papa. Na farko yare taji yanayi sai turancin daya saka kaɗan ya sakata fahimtar papa ne. na biyu kuwa da turanci sukai magana. Hakan ya sata jin komai akan duk wani motsinsu Solomon yana sanarma papa. Dan a ranar shi papan har maganar ya kamata ta koma Nigeria yayma Yoohan. Amma shi Yoohan ɗin ya nuna baya bukatar yana wani ƙasa matarsa na wata ƙasa. A ransa kuwa ya ɗau alwashin Aymah bazata ƙara zama a gidanba baya kusa saboda Gebrail. Dan ba ƙyalesa yayiba. ya ɗau alwashin duk randa ya dira Nigeria sai Gebrail ya yabama aya zaƙinta.
      Ganin da gaske shirin tafiyar take ya sakashi sakkowa daga fushinsa shi. Ya fara lallashinta amma taƙi saurarensa. Saima kuka da take masa mai cin rai. Daga ƙarshe dai dole ya kira baba malam akan dan ALLAH ya lallasar masa ita. Dan shikam a yaune ya kuma tabbatar da borin Aymah bana wasa bane. Dan ko abinci taƙi ci, taƙi shan maganinta. ta birkice masa ita kawai ya kaita airport ta wuce gida kokuma ta tafi da kanta.
       Murmushi baba malam yayi kawai yana girgiza kansa. kafin ya sauke ajiyar zuciya ya farama Yoohan nasiha. Daga ƙarshe ya koma masa faɗa akan sakacinsane ai ya saka Nu'aymahn iya bijirema umarninsa. Dan haka ya nutsu sosai wajen riƙe gidansa da ƙyau. dan su mata wani lokacin zuma ne sai da wuta. Sannan wutar kara ne sai da iji. Ba'a sakaci da su sannan ba'a musu tsauri da yawa. ana riƙesune tsaka tsaki sai a samu jin daɗin duniya.
     Sosai Yoohan yaji shawarar sirikin nasa. tare da ƙarajin ƙaunarsa a cikin zuciya da ɓargo. Daga haka ya haɗashi da Nu'aymah kamar yanda ya buƙata.
        Zata fara masa kuka baba malam yay mata jan ido. faɗa sosai yay mata akan tashiga hankalinta mijinta ba abin rainawarta bane. Idan batai wasabama sai yazo har Austria ɗin ya hukuntata. Sai da ya tabbatar tayi laushi sosai da faɗansa sannan ya koma yimata nasiha. Daga baya kuma ya buƙaci jin dalilinta na takurawa akan Solomon ya barsu.
           Kasancewar Yoohan yana koyon hausa a wajenta ya sakata yin amfani da manya-manyan hausa wajen yima baba malam bayani akan abinda ta fahimta da zaman Solomon tare da su. Ta kuma bashi labarin abinda ya faru akan maganar hoto, harma da videos ɗin da Omar (Richard) ya nuna mata kwanakin baya da suka shuɗe. shi kansa baba malam ɗin hankalinsa yayi matuƙar tashi. sannan zarginsa ya fara zama gaskiya kenan. Albarka ya saka mata sosai da faɗan rashin sanar masa zance hoton da tayi tun a wancan lokacin. Duk da ya fahimci mijinta take son bama kariya akan matsalar da gajeren tunaninta ya kasa faɗaɗa mata. Yace,
      “Mamana yanzu ina hoton yake?”.
Hawayenta ta share da jan majina. Tace, “Abba yana nan Nigeria a cikin kayana”.
       “Masha ALLAH. ALLAH yay miki albarka. Saka wani ya ɗakkosa bazai yuwuba. Dan haka zamuyi haƙuri har ku dawo ƙasar sannan musan ta inda zamu ɓuloma al'amarin. Batun Solomon kuma bata hanyar rikici zaki yakicesa a jikin mijinki ba. Cikin hikima da wayon da ALLAH ya baku na mata da tarbiyyar Umm ɗinki zakiyi amfani wajen sakashi ya sallamosa. Ko kin taɓa ganin muna rikici da Umm ɗinki ne a gidannan?”.
     Kanta ta girgiza masa tamkar tana a gabansa. Sannan tace, “A'a Abba”. 
      “To amma shine ke zakije kina rikici da mijinki. har yana taroki kina ƙwacewa? Wannan shashanci ne ai. Sannan kina zubar mana da kimar tarbiyyar da muka baki. Mu mazafa da kike gani munada wuyar sha'ani dason nuna mulki a gidajenmu, shiyyasa duk macen data fahimci haka ta iya zama damu mutane suke ganin kamar ta mallake mijintane  nanko ba haka baneba. juriyace kawai da iya zama da mijin tayi. Ki kula da ƙyau. Mahaifiyarki abin koyice a gareki akan zaman takewar aure. Babu wanda zaice ga Jannat da wata matsala a gidan aurenta. da daɗi babu daɗi ta jure ta shanye komai. Yaya muka kwana yaya muka tashi ta jurema ranta. har takai wasu na ganin tsorona takeji da yawa. Nanko ba hakan bane. Mune muka san sirrin kammmu fiye da duk wanda ke zagaye damu. Karna ƙarajin haka kinji ko?”.
       Nu'aymah na sharar ƙwalla tace, “Insha ALLAHU Abba bazaka sake jiba”.
       “To Alhmdllh naji daɗin hakan kuwa. ALLAH yay miki albarka keda mijinki damu baki ɗaya”.
      Cike dajin kunya ta amsa da amin. Daga haka suka ajiye wayar. Ta ɗan saci kallon Yoohan dake kwance ciki sofa idanunsa a lumshe tamkar mai barci. Tashi tai a hankali taje ta ajiye masa wayarsa a saman ciki batare datace komaiba.
     Shima buɗe idanu kawai yayi ya bita da kallo harta shige toilet.

_________★★

        Batare da tasan yaya zancen Solomon ya kasanceba washe garin da suke cika sati biyu. ta kama randa zasu bar ƙasar kenan. Bayan sun kammala shirinsu tsaf sukaje asibiti aka ƙara tabbatar da ingancin lafiyarta, sukai sallama da su Dr Sophia kuma. Yoohan ya ƙara siya mata sauran magungunanta suka nufi airport cike da kewar ƙasar Austria da garin Vienna. Harma da mutanen cikinsa.
           Yanzunma suna nane da jelar tasu Solomon. Sai dai kuma suna zuwa Airport ta fahimci Solo Nigeria ya nufa. ita da shi kuwa U.S zasu wuce dan Yoohan ya koma hutu. Zai kuma gudar da wani aiki a ƙasar United states ɗin, da wani taron manyan likitoci da zasuyi kuma insha ALLAH.
        Duk da basu shiryaba har yanzun ita da shi sai da ya ga farin cikin komawar Solomon 9ja a fuskarta. Shidai hakan na bashi mamaki. dan ya gaza fahimtar ƙiyayyar dake tsakanita da Solomon. Shi kansa Solo ɗin ya kula baison Aymah. Sai dai baya iya nunawa a gabansa saboda shakkarsa da yakeyi. shi kuma bai taɓa nuna masa ya fahimta ɗinba dan yanason aje inda zai taka masa birki akan matarsa.
      Shi kansa Solomon sai da sukaje airport ya fahimci Nigeria zai komai. Gashi babu damar kiran papa ko madam Chioma dan suna a tare. Sai dai zuciyarsa na ƙara jin zafin Nu'aymah. Dan ransa ya basa itace sanadin komawar tasa tabbas. Musamman da yaga yanda taketa faman moso. Dan ya fahimci kwana biyun nan daga ita har ogan suna cikin rikicine ko damuwa oho bai gama tabbatarwaba dai.
      Jirgin su Solomon ne ya fara tashi zuwa Dubai. daga can zai hau Jirgin Nigeria. Ya tafi cike da alkairin da Yoohan yay masa da takaicin Nu'aymah da tsana mai tsanani. Dan shi baimasan ina zasujeba a yanzu haka. Solomon na wucewa da kamar mintuna ashirin da biyar suma nasu jirgin ya ɗaga zuwa U.S. yana ta wajen Window tana gefensa a cikin jirgin. Sai dai ya ɗauke fuska a binsa gashi ya ɗaureta tamau. Daga ƙarshema saiya kunna lap-top da liƙa earpiece a kunne ya hau kallon film. Duk da ran Nu'aymah ya sosu saita fuske tai kamar bama tasan da zamansa a wajenba. Koda akazo tambayarsu mi zasuci catai bata buƙatar komai. Shi kuma yasa aka kawo masa coffee da biscuits.
         Lokacin da jirginsu ya sauka a U.S Nu'aymah barci takeyi. Hakan yasaka Yoohan shafa mata fuska. Sai dai tana buɗe ido ya ɗauke kansa tamkar bashine ya aikataba. Itama duk da ta fahimci shine ya tadata sai ta watsar da shi ta basar. Handbag ɗinta ƴar ƙarama kawai ta ɗauka tai gaba. Shi kuma ya jawo trolly ɗinsu sai lap-top bag ɗinsa a hannu. Yana biye da ita a baya. Sai dai da suka sakko dole ita ta koma bayan nasa dan ba sanin hanya tayiba. Da wannan damar ta ware ido tana kallon airport ɗin daya amsa sunansa airport. Sai dai ta haɗiye mamakinta a rai wai kar Yoohan ya rainata da ƙauyanci😂.
      Taxi ya ɗauka musu drop. Koda suka shiga nanma dai kanta naga Window tana kallon birnin da mutanen cikinsa. Daga haka suka isa wani haɗaɗɗen gida daya amsa sunansa gida. A tunaninta gidan nasa ne. sai dai batasan haya ya kama musu ba dan a yanzun baya buƙatar zaman hotel ɗin da ita. sannan yanason barinta anan U.S ɗinne dan yasan bazai yuwu yayta gantali da ita duk inda yakeba. Inba wajen daya san zai iya yin sati biyu kwana goma ko sama da haka ba. Amma kamar tafiyar kwana uku ko biyu zuwa sati ɗaya zai iya barinta yaje ya dawo. Inba dai buƙatar tafiya da ita taga duniya tasa suje tareba.
      Komai da zasu buƙata na gida akwaisa a cikin gidan. Shopping ɗin abinci kawai zasuje suyi da kansu saiko suturar sakawa da sukazo da kayansu. Harga ALLAH gidan ya matuƙar burge Aymah harta kasa ɓoye shauƙin hakan a zahiri.
       Duk da yaji daɗin yanda tai farin ciki sai ya basar bai nuna mataba. Ya fara shiga ko'ina ya duba gidan da ƙyau. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata tamkar yanda ya gani a yanar gizo daya kama gidan sannan ya shiga wanka.
      Yana fitowa Nu'aymah dake kwance a gado ta miƙe itama ta shiga dan wankan take buƙata itama saboda gajiya. Koda ta fito zaune ta samesa a bakin gadon yana musu order ɗin abincin ta wayar landline. Da alama dai gidan abincin yana kusa da sune, kokuma yanada alaƙa da masu gidan abincin dama can.
     Sai gashi kafin ta gama kimtsawa tai sallar magriba da lokacinta ya shiga an kawo abincin. Shine ya fita ya amso. Sai dai bai dawo bedroom ɗinba yay zamansa a falo. Sallama acan yay abinsa.
         Wani mahaukacin yunwa Aymah takeji. Hakan yasa bayan ta idar da salla ko hijjab bata cireba ta biyosa falon. Dan bazata iya basar da cikintaba ta halaka a banza a wofi. Turus tayi tana binsa da kallon mamakin ganin yanda ya baje yana ɗora abinci a cikinsa. Ta kumbura baki ƙwalla na cika mata idanu. Cike da fushin data koya kwana biyun nan ta juya zata koma bedroom ɗin. Sai dai kuma caraf taji an riƙi mata hannu. Ƙoƙarin fisgewa ta farayi hawayen da take riƙewa na zubo mata a guje saman kumatu.
      Ɗaukarta yay gaba ɗayanta ya dawo da ita a falon. duk yanda take watsal-watsal da faɗin ya sauketa bataso bai kulataba. Ya zauna cikin lallausar zagayayyar kujerar da aka ƙawata falon da ita kalar royal blue tana a jikinsa. Cikin hawayen da takeyi ta shiga kaimasa ƙananun duka a ƙirji da faɗin ita ya saketa bataso. Tunda yabar sonta yaje ta haƙura ta barma duniya dasu Miracle dake addabarsa da text massege kullum shi. 
         Zancen nata yaso bashi dariya. Dan haka ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa akanta yana ƙoƙarin riƙe hannayenta da take kaimasa duka a ƙirji. A ransa kuwa yana sake jinjina rikicinta. Duk da ransa na raya masa wani abu game da saurin fushinta na kwana biyun nan. Sai dai bai tabbatarba dan ya san inma shine to ƙaramine kuwa sosai.
     Bakinsu ya haɗe waje guda. Tun tana turesa harya samu nasarar maida mata jiki laƙwas ta fara bashi haɗin kai. Da ga ƙarshe ya ɗauki abarsa cak suka shige bedroom inda zaiyi lallashi ɗan gaske na zallar ƙauna da babu gaurayen algus a cikinta😵. Saiga mutuniyarkun muna funfun dake faɗin zata barma duniya dasu Miracle tai luf kamar bata gidan😏😧.
            (Su Aymah babu aji🏌😑)

Sai da suka gama wadata juna da farin ciki yanda ya kamata. Yoohan ya kalli Aymah dake lafe a jikinsa idanu a lumshe alamar barcin nata na ƙa'ida zai ɗauketa. Dan duk sanda hakan ta kasance a tsakaninsu sai tayi wannan barcin. Shiyyasa yake kiranta raguwa.
        Guntun murmushi yayi da lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta tare da ja mata hanci. “Silly girl! Babu abinda ta iya sai jan mutane faɗa”.
      Lumsassun idanunta da basu gama washewaba ta buɗe a kansa. Sai kuma ta tura masa baki tana maidawa ta rufe tare da tirza ƙafarta dake jikinsa tace, “Tab, kai wama ya kaika iya neman mutane faɗa”.
       Sake jawo bargon data zazzame da ƙafa yayi ya lulluɓesu da ƙyau yana ƙara sakata jikinsa. “Nine ma mai neman faɗan kenan?”. 
     “Sosai ma. Tunda ai kaine dai kasa akayi wannan faɗan”.
         Dariyar data bashi ce ta sakashin yin guntun murmushi. Ya sumbaci goshinta da laɓɓanta yana sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu. “ALLAH na gode maka daka mallakamin ƴar rigimarnan tawa. Tare da mai ramamin gashinan yazo”.
         “A ina?”.
Tai tambayar cikin yanayin barcin daya figeta.
        “Mi kikeci na baka nazuba, zaki gani ai”. Ya faɗa yana miƙewa zaune da ita a jikinsa. Cike da shagwaɓa tace, “Ni wlhy barci nakeji”.
      “To muje ayi wanka, sai kizo kiyi Sweet girl ɗin Yahya”.
      Da taimakonsa sukaje akayo wankan. Dan barcin da bataiba na bayan lobewa ne cike da idanunta. Suna fitowa kuwa ta zube a gadon ta fara. Kayan barci ya ciro mata yazo bakin gadon ya zauna yana kallonta na tsayin mintuna uku. Hannunta ya kamo ya na kallon tafin, kafin ya juya ya tsurama yatsun idanu suma na kusan minti ɗaya. Ya miƙe inda ƙafafunta suke ya durƙusa a gaban gadon yana kallon yantsun suma na tsayin mintuna. Sassanyan murmushi ya sauke da ajiyar zuciya, ya sumbaci ƙafafun duka biyu sannan ya dawo kusa da ita ya zauna. Sake tsirama fuskarta ido yayi na tsahon wasu mintunan cike da so da ƙauna, kafin ya ranƙwafa kanta yana sumbatar bakinta da kumatunta, idanun har wuya. (Ni mai ɗauka muku rahotonma sai yaban dariya. Dan na kasa fahimtar inda ya dosa😂😑).
      Kayan barcin ya sanya mata, ya gyara mata kwanciya, shikuma ya koma bayin ya ɗauro alwala ya dawo yay zaman karatun al-qur'ani. Dan tunda suka fara rigimarnan ta Solomon kota ɗora masa karatun ba fahimta yakeba da ƙyau. Haka yake kwata-kwata bayason damuwa. Koyaya irin haka ta faru da shi duk sai ya fita hayyacinsa. Ya jima yana duba al-qur'anin da sauran buks ɗin kafin ya miƙe zuwa fallo ya tattaro abincin da yaci ya rage dan yasan saita tashi cin abinci tunda yunwar takeji. Kwana biyun nan haka take, batama abinci sauƙi. Kodan jinyar da tasha ne oho. Sallaya ya hau ya kabbara sallar isha'i, bayan ya idan bai kwantaba ya ɗauki wayarsa da tun ɗazun yake ganin tana haske, ya tabbatar kuma kiransa akeyi dan a silent take.
      Ilai kuwa missed calls ne na papa har guda takwas, sai na Momynsa biyar. Sai na Omar (Richard) biyu. Sauran kuma duk ba important bane a garesa dan haka baibi takansuba dan harda mayyarsa Miracle.
        Kiran papa da Momy yasan bai wuce saukar Solomon Nigeria ba. Dan haka yay kiran Omar (Rich) kawai da shima yana Nigeria. 
       Sallama kawai Omar (Richard) ya amsa masa, ya shiga masa shaƙiyanci wai yanzu soyayya tasa sai ya gadama yake amsawa mutane kira a waya. Su G-boy ma jiya suka gama masa tsogumi a wajen birthday ɗin Osin da akayi a garin Lagos. Kai abokan suma da yawa sunyi wannan complain ɗin duk da dama sunsan shi Yoohan fa bai cika ɗaukar kiran da zuciyarsa ta raya masa mara amfani bane, saboda yanayin aikinsa da duk ya maidasa busy a gaba ɗayan rayuwarsa. Sai dai idan yana a cikin hutu da kansa yake bin abokan mu'amulat nashi masu muhimmanci ya kirasu su gaisa koda bazai zauna hira da kai ba. Musamman ma daya musulinta ɗin nan ya ƙara sanin darajar zuminci.
      Murmushi kawai yayima Omar (Rich) ɗin da cewa “Humm ka samin ido da yawa”. Dariya kawai Omar yayi da ga can. Dan ya fahimci ƴan miskilancinne a kusa yau. Ajiye maganar wasan yayi suka fara tattaunawa kamar haka.
       “X-man duk yanda muke tunanin aikinan bazai kasance mai sauƙiba. Amma dai na turo maka dukkan bayanan dake a hannuna yanzu ta Email ɗinka. Ni dai yanzu shawarar dana yanke, mizai hana mu sami wani amintaccen jami'in tsaro da zai taimaka mana akan case ɗin nan. Dan tabbas sai munyi kutse a cikin wayoyin mutanen gidan saboda fahimtar da nayi case ɗin babba ne dan yanada tushe”.
     Ajiyar zuciya Yoohan ya sauke yana bin Nu'aymah da ta tashi zaune da kallo. Ya juya harshensa zuwa yare. “Tunaninka mai ƙyaune Omar. Inaga kuma babu wanda zai iya taimakonmu akan aikin nan sai Dawood, sai yay mana hanyar ganin bawan ALLAH nan dana taɓa baka labarin ya taɓa buƙatar na duba matarsa akan matsalar cancer ɗin mahaifa da sukai zargin tana da ita, sai dai hakan bata samuba a wacan karon sai haɗasu nai da wani likitan.. So dole zan shigo Nigeria kwanan nan, tunda kaga akwai aikin da zanzo nayima anan Lagos. Kuma shi mutumin babban jami'i ne zaifi dawood tsaya mana sosai”.
         “To shikenan, sai mu bari sai kazo ɗin saimu tattauna, insha ALLAH madam ma zata dawo nextweek tunda kuna nan”. 
      “Idan kayi hakan kuwa zaka taimaka min, dan zaman Zeeynab a ƙasar nan yana buƙatar samun wanda zasu shaƙu. Inason samar mata admission ma ta fara karatunta insha ALLAH. Dan tanason karatu sosai na fahimta. Sannan tanada brain, sai dai shiriritanta yayi yawa wlhy”. Ya ƙare maganar yana satar kallonta, dan tana zaune ne tana cin abincin da yunwa ta hanata barcin nata yay tsaho.
      Dariya Omar yayi daga can yana faɗin, “Ai da sauranta ne. 18years fa. bandama hausawan nan babu ruwansu ina ƴar 18years ina aure. Sai dai kuma yanzu ni tsarinsu birgeni yake. Indai madam ta haihu min baby girl nima tana gama secondary zan mata aure”.
     Dariya zancen ya bama Yoohan. Dan haka ya murmushi yana bin Aymah da wani narkakken kallo. Itako ta zuba masa harara ta ɗauke kanta. Dan tana takaicin idan suna tare taji ya canja harshe yana magana. Sai taga kamar gulmarta akeyi🤣. Shiko tunda ya fahimta ma har yi yake danya takaleta suyi faɗan nasu.
            Cikin ɗauke kai yace, “Saina faɗa mata duk abinda ka faɗa”.
     “Kai! Kaifa baka da kirki wani sa'in dude. Ni karka ɓatamin suna wajen ƙanwata dan kaga dai tace yanzu nine yayanta, idan ka mata laifi zata kawomin ƙara na hukuntaka”.
       “Kai kuma kaji daɗi ko? Shege mai shiga hancin masoya sai anjima. Wuce ka tafi wajen Juliet ɗinka dare ne anan inan buƙatar ɗumin baby na”. Kafin Omar yace wani abu Yoohan ya yanke wayar ƙitt.
          Matsowa yay kusa da ita ya amshi spoon yana faɗin, “Wannan fake yayan naki yana takuramin da yawa Sweet girl”. Sai da ta buɗe baki ya saka mata abincin daya ɗebo sannan ta bashi amsa cike da kasalar barcin da takeji. 
       “Ai shine zai dinga saitomin kai idan ka birkice. Dan kaima rigimammene silly boy”.
        Goshinsa ya shafa zuwa saman ido yana murmushi. Ya cigaba da bata abinci batare da yace komaiba. Ta fahimci yau dai halinne ya motsa, shiyyasa itama tayi shiru ta cigaba da karɓar abinci da yake bata. Sai da ta tabbatar ta ƙoshi sannan shina ta amsa zata fara bashi. Cikin marairaicewa yace, “Na ƙoshi Sweet girl. Karkisa naita ƙaton ciki kizo kina kasa ɗaukata dama gaki da rakin tsiya”. 
      Murmushin da batayi niyyaba ta saki. Ta kwanto a gefen hannunsa tana lumshe ido da faɗin, “Duk ƙaton cikinka zan iya da kai malam”.
      “Oh wow!!. Da gaske?”.
    Miƙewa tai zata gudu yay saurin riƙota ta faɗo jikinsa. A cikin kunnenta yace, “Yarinyar nan kinfa ƙware wajen guduwa ba'a gama magana ba”. 
         Da sauri ta taune lip ɗinta na ƙasa tana dariya ƙasa-ƙasa. “Ni kaga barci nakeji ALLAH. Ka barni na kwanta kona maka barci a jiki”.
       “Ai jikinki ne baby”. Ya bata amsa yana miƙewa ɗauke da ita suka haura kan gadon. Fitilar ya rage musu yana gyara mata kwanciya a jikinsa da ƙyau. Kanta ya sumbata suka sauke ajiyar zuciya. Ɗagowa itama tayi ta sumbaci laɓansa da shafa kwantaccen sajensa. Cikin sauke murya sosai tace, “I'm sorry. Nayi alƙawarin bazan sake ba insha ALLAHU”.
       “Thanks you sweet angel. ALLAH yay miki albarka. Nima kiyi haƙurin ɓata miki rai da nayi. Insha ALLAH bazan ƙaraba humyim?”. Ya ƙare maganar da cusa kansa a wuyanta yana shinshina. Ƙanƙamesa tayi dan salonsa a kullum mai wahalane a gareta.....

______________★★

         *_ABUJA NIGERIA_*

      Isowar Solomon Nigeria shi kaɗai yayi matuƙar tadama papa hankali. Duk da baice dasu komai ba saboda darene anan 9ja sanda ya iso ɗin. Amma sai papa ya kasa haƙuri ya shiga antayama Yoohan kira a waya. A lokacin shi kuma bai kulaba dan wayar na'a silent ne. Itama Madam Chioma tashin hakalinta ganin Solomon ɗin shi kaɗai babu Nu'aymah babu Yoohan ɗinne ya sakata kiransa taji su kuma suna inane? Amma sai yaƙi ya ɗaga. Daga ƙarshe ma sai suka daina samun layin nasa gaba ɗaya. Da wannan tashin hankalin suka kwana. Duk da ma barcin nasu rabi da rabi sukayisa. 

        Aiko gari na wayewa suka nemi Solomon da shima dai kiran nasu dama yake jira. Dan shima ɓacin rai bai barsa yayi isashen barcinba. Kwana yayi yana mafarkin Nu'aymah da tsanarta ke ƙara hauhawa masa a rai a kowane daƙiƙa na rayuwarsa. 
       A falon papa ya samu Momy da papan. Bayan ya gaishesu suka buƙacin bayanin dawowarsa babu su Yoohan. Tsaf ya kwashe komai ya faɗa musu harda ƙarawa da ƙarya. A take ransu ya ƙara ƙololuwar tashi. Papa ya miƙe a fusace yana faɗin, “Lallai yarinyarnan ubanta dama ya turota gidan nan ne bisa wani dalili. Darling bani keys ɗin sashen John. Dole na bincikima ɗakin yarinyarnan yau..........✍

(Munga idi hotonmu😱🏃).


Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 66

.............Da sauri madam Chioma ta shiga ɗakinsa ta kwaso spare keys ɗin gidan ta kawo masa. Amsa yay ya nufi sashen Yoohan ita da Solomon biye da shi. Kai tsaye ɗakin Nu'aymah suka shiga. Ɗakin yayi ƴar ƙura, dan ma Yoohan duk ya tattare abinda yasan ƙurar zatai masa illa. Buɗe-buɗe suka shigayi a lungu da saƙo na ɗakin. Har cikin Wadrobe ɗin kayanta dan tsabar rashin mutunci. Duk abinda idonsu ya gani bai musu ba sai sun masa filla-filla. A haka Madam Chioma ta dinga tiɗo kayan Nu'aymah a ƙasa har hoton nan data ɗaukko ɗakin papa ya faɗo. 
      Duƙawa tai ta ɗakko farar envelope ɗin, ta ɗaga bakin zata buɗe kira ya shigo wayarta. Gajeren tsaki tayi da ɗora hotan a kan fallen Wadrobe ɗin ta zaro wayar a aljihunta, ganin Madam Rebecca ne ya sakata ɗan juyawa ta dubi papa. Sai tai saurin barin gaban Wadrobe ɗin tama fice falo danta amsa kiran.
      Faɗowa hoton yay ƙasa kasancewa bata ɗaurashi da ƙyau ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Solomon wajen. Take hoton yayi ya matsa jikin Wadrobe ɗin ya cigaba da tiɗo kayan ƙasa shima yana bincike dalla-dalla kamar yanda madam Chioma yaga tanayi. 
         Tsaf suka gama harmutsa ɗakin basu sami komaiba. Kayan sakawarata ne kawai sai turarurruka da buks ɗinta na addini dana boko. Shiru sukai kowa ransa cike da jin zafin rashin samun komai. Papa ya fara jan tsaki ya fice. Solomon ma ya bi ɗakin da harar ya takema papa baya. Madam Chioma suka bari ƙarshe tanata dube-duben inda zataga envelope ɗin nan amma ta rasa. Ta ɗan juyo zatama Solomon tambayar koya gansa ta shuresa da ƙafa batare data saniba. Kasancewar santsin tiles dana envelope ɗin ya sakashi tafiya suuuu sai ƙarƙashin gado. Taji ƙaran wucewar abu, hakan yasa tahau waige-waige. Sai dai kuma bataga komaiba. Tana niyyar fita ta hango farin takarda a ƙasa mai kama da envelope ɗin. Ɗauka tai ta buɗe sai taga zane ne Aymah tayi a ciki na teddy bear. Cike da takaici tai wurgi da takardan tare da shurar kayan Aymah da suka watso ƙasa tai ficewarta itama.

         Cike da jin zafi suka yini a wannan yini. ga Yoohan yaƙi ɗaga kiran kowa a gidan hatta da su Uncle Mike da papa ya saka su kira masa Yoohan a bisa wayonsa.
      Sai dai baisan Yoohan duk a lure yake da komaiba. Ya kumayi shirin tsaf akan ƙin amsa wayar kowa tunda yasan dai bai wuce zancen Solomon. Shi kuma ya riga da ya gama yanke hukunci dan yana buƙatar farin cikin matarsa da mallakar zuciyarta yanda ya kamata. Hakan kuma bazai tabbata ba har sai ya faranta mata kamar yanda iyayenta suma suka faranta masa a rayuwa. Sannan shi kansa a yanzu yaga kasancewar Solomon tare da shi a ko'ina babu wani tsari ai. Kodan kiyaye martaba da mutuncin iyalinsa. yana da kishi kuma gaskiya.
       Kiran da yaso kawai ya dinga ɗagawa a wannan yinin. Gefe ɗaya kuma yana manne da matsarsa sarkin taɓara suna shan sharafin soyayyarsu. Dan duk hanyar da yasan zata saki jiki da shi ita ya kebi da kulawa a gareta.
               Da gaske kuwa aikinsa na yin ƙyau ga jikar ɗan jibiya. Dan sosai karatun nasa ke tasiri akan Nu'aymah yanda ya kamata. Tasan taso Yah Ab kamar zata mutu. Amma lallai da gaske soyayyar ƙuruciyace tai ɗawainiya da zuciyarta a wancan karan da kuma darajar jininsu daya kasance guda. A yanzune take banbance minene ma soyayyar ga mahaɗin rayuwarta.
       A hankali ta fara sabawa da yanayin ƙasar U.S ɗin. Ƙasar ƴan gatan duniya masuyin yanda suka gadama a cikinta babu ƙasar data isa nuna musu yatsa. Hatta da U.K ɗin ma data rainesu a yanzu shakkarta suke saboda hatsabibanci da tsaurin ido irin na ƙasar ta Amuruka. 
         Kwannsu biyu da zuwa Yoohan ya fara aikin daya kawosa. Hakan yaɗansa ta koma yini ita kaɗai a gidan. A rana ta huɗu ma sai kusan gabannin asuba ya dawo gidan. Nu'aymah bata da tsoro sam tun fil'azal. Sai na Duhu da allura kawai. Hakan yasa Yoohan bai taɓa ganin damuwa a fuskarta na barinta gida da yake ita kaɗaiba. Duk da shi duk inda ya shiga tana nan manne da ransa da zuciyarsa. 
     Kaɗaicin da yake tunanin tana a cikine ya sakashi kaita tai register ɗin sabon layinta ya ɗora mata akan waya. Tare da saita mata duk wani folder na yanar gizo ta koma harkokinta da ƴan uwa da abokan arziƙi. Takoji daɗin hakan dan har ya fahimta akan fuskarta bayan runguma da sumbata daya sha da godiya.
        Samar da Sim card a wayar Aymah ya ƙara nutsar da ita. Dan kullum Umm da Hajjo cikin mata nasiha suke da ɗorata akan abinda ya dace. Harma baba malam da Ananah da Addah ba'a barsu a bayaba. Hakama Aunty Hajarah wata shaƙuwace take ƙara shiga tsakaninsu tana koyama Aymah dabarunsu na ƴan zamani akan gidajen aure. Dan tasan wautar ƙanwar tasu.
      Alhmdllh aikinsu na ƙyau kuwa. Dan huɗubar tasu nama Nu'aymah tasiri sosai. Har shi kansa Yoohan na fahimtar hakan. Dan randa suke cika sati guda da zuwa U.S da kanta ta samesa da zancen ya kaita tayo shopping dan ta ringa musu abinci. Ita ta gaji da jagwalgwalon turawan nan gaskiya.
            Kallonta yayi da kulawa yana ajiye wayarsa da yake dannawa. “Uhm yaushe kika iya girki?”. 
     Yay mata tambayar da iya gaskiyarsa. Dan shi dai harga ALLAH ba taɓa sanin ta iya yayiba. Ya dai fahimci a fanin gyaran gida yarinyar gwarzuwa ce. Dan yanda gidan nan yake shan gyara a wajenta yana sakashi farinciki matuƙa. saboda a rayuwa yanason tsafta.
          Cike da ƙwaɓe fuska take dubansa daga kwancen da take a shakkiyar falon akan carpet. “Amma wlhy ka ragemin daraja. Girkinne kake tambayar yaushe na iya? Kira Umm ko Abbana kaji to. To ALLAH har Abba inama girki, dan nafi Umm ma data koyamin iyawa. Dan ni idan naso a yanzun sai in haɗa maka idea ɗin kalar girkin da zaisa ka manta kunnenka a cikin plate”.
         Da ƙyar ya iya danne dariyarsa ya murmusa kawai. Sakkowa yay daga kujerar da yake zaune ya zauna a gefenta ya jingina jikinsa da kujerar tare da ɗan karkatawa. Hakan yasa ta dawo kamar a jikinsan take dan ya miƙe hannunsa ta bayanta a jikin kujerar. Anan kuma ya tanƙwashe ƙafarsa ɗaya, ɗayar ku a ajiye ya ɗaura ɗayan hannunsa bisa gwiwar ƙafar.
      “Sweet girl! Dan ALLAH da gaske kin iya girki?”.
     Wayarta ta ɗauka batare data bashi amsaba ta shiga ma'ajiyar hotunanta. A take ta ƙwaƙulo masa pictures ɗin abincin da tayi lokacin da yay tafiyar nan. babu musu kuwa ya amsa yana kallo ɗaya bayan ɗaya a tsanake. Harga ALLAH yaji abincin ya birgesa harma yaji ƙwaɗayin abincin 9ja. Amma dai kuma bai gaskata ita ɗin tayiba. Dan haka ya mannata da jikinsa tare da saƙalo hannunta saman cikinta yana shaƙar ƙamshinta ta jikin dokin wuyanta. 
      “To muje muyi shopping kenan, dan nidai sai anyi a gabana zan yarda. kuma nine zan zaɓi abinda za'a dafa idan kin yarda. Idan kinyi dai-dai kinada ƙyauta ta musamman. Idan kika kuskure akwai hukunci na musamman”.
        Cike da gatsen sanin ta iya ɗin ta juyo kanta da ɗora hannunta saman fuskarsa ta shafi sajensa. Da wani salo tace, “Na yarda da wannan game ɗin Mr Man”.
         Hannu yasa shima ya tallafo fuskarta tare da ɗora laɓɓansa akan nata yaɗan tsotsa. Jin zai zirma ya saka Aymah galla masa mintsini mai zafi a cinya. Sakin mata kai yayi yana sosa wajen da ɓata fuska kamar zaiyi kuka. Ta miƙe da sauri tana dariyar shakiyanci da faɗin, “Maganin mai kwaɗayin bakin mutane kenan”. Ta ƙare maganar da shigewa bedroom ɗinsu tana dariyarta.
     Murya ya ɗan ɗaga yanda zata jiyosa da ƙyau. “Silly girl! ALLAH kinci bashi, nasan ta inda zan fanshe muguntarnan da kikafi ƙwarewa a kai ai”.
       Dariya Aymah dake jiyosa daga ɗaki tayi tana zira skirt pink a jikinta irin mai bajewa gaba ɗaya ɗin nan. (Buje inji hausa😂lol). T-shirt yellow sosai da tambarin heart a gaba ta saka a saman skirt ɗin. Sannan ta gyara fakin din gashinta ta ɗaure a tsakkiya tare da naɗa gyale baƙi maiɗan girma sannan ta ɗaura pink jacket mai ƙyau a sama. Sosai tayi ƙyau, musamman yanzu datake ƙara yin wani uban haske jikinta na bajewa da ƙyau ƙibarta na dawowa. Ga ƙirji ya sake cika masha ALLAH. Taɗan saka hoda da lipstick pink kaɗan. Tana saka turare dai-dai misali ya shigo ɗakin. tsayawa yay kawai yana kallonta dan ta masa masifar ƙyau. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe a kanta da sakin ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana ayyana sirrin dake cikin auren ƙaramar yarinya mai yawan gaske. A fili kam baice komaiba sai ida shigowa da yayi ya ɗauka riga shima ya saka a saman singlet ɗin jikinsa. Sannan ya ɗora jacket baƙa shima data sake fidda masa sirrin ƙyau na angwanci dake ɗawainiya da shi.
      Gaban mirro ɗin da Aymah ke ƙoƙarin saƙala sidebag ta wuyanta tana daidaitata a gefen cikinta ya ƙaraso. Hannu yaɗan buɗe mata batare da yayi magana ba. Sanin abinda yake nufi ya sakata ɗauka gwangwanin turare batare da tace komaiba itama ta shiga fesa masa. Sannan ta ɗauki comb ta taje masa sumarsa data sake cika kan sosai saboda ƙaunarta da yakeyi, sai dai kuma yanzu askin arzikine a kan ba irin na daba. Sajenma gyara masa shi tayi tana magana cike da tsogumi. 
       “Nifa karya zam inama kaina ramin muguntane ma. Inje na gama gyaraka wasu tambaɗaɗɗu can suyita kallemin miji. Wlhy duk wadda ta kalla ALLAH ya isana ban yafe ba”.
        Cike da neman magana yaɗan waro idanu waje da faɗin, “Uhm uhm fa Sweet girl. Matan U.S ɗin nan shegen ƙarfine da su ba irin na 9ja bane da kika gama rainawa kina karya musu ƙafafu da fasa musu baki. Su laƙaɗa miki shegen duka zasuyi babu ruwana”.
      Sosai ta turɓune fuska tana zuba masa harara. Tace, “To na rantse kuwa zakaja kafin mu dawo gidannan a fara wucewa damu police station ɗin garin nan, saboda ɓalla ƴaƴan jama'a zanyi na zubar a banza. Dama gasu ba ƙwariba girman ƙanƙara da Ice-creem da biscuits”.
        Ransa fes da fahimtar soyayyarsa dake tattare da matarsa ya rungumota ta baya dan tana gama maganar ta juya tana ajiye turaren data fesa masa. A cikin kunnenta yace, “I love you irin trillions ɗin nan My Cutie”. 
     Hannu tasa zata ture masa fuska danfa taji haushin zancen ƴammata da yayi mata. Harda Miracle da tuni ta manceta a babin rayuwarta. tunda ita dai tasan itace ta taɓa ɓallama ƙashi da fasama baki.
     Da sauri ya riƙo hannunta yana dariya. “Na tuba wasa nake. Ai wannan Zenabu ɗin har abadan a bada, insha ALLAHU ita kaɗaice da Dr Yahya goshpower har ƙarshen numfashi. My angel kece kaɗai uwar ƴaƴana da yardar UBANGIJI. Ke kaɗaice sirrin Yoohan in ALLAH ya yarda. Daga ke babu wata mace data isa sanin koda sirrin murmushin Yoohan ne balle ma ta raɓu miki miji My Noorunnisa”.
      Cike da jin daɗin jin kalamansa da suka sanyaya mata jiki ta juyo a hankali ta jingina da mirror ɗin, shi kuma tana fuskantarsa. Ƙwallar da suka taru mata a ido suka ƙarama idanun ƙyau ta zuba masa. A hankali ta motsa laɓɓanta wajen faɗin, “Idan nace kai na dabbane, ina nufin na dabban har ƙasan zuciya da bugun numfashina My boo. Tabbas bani kaɗai bace haske a gareka. Kaima haske ne a rayuwata. Dan ka cetoni daga wahalhalun jarabawar rayuwa da ƙaddara ta tilasta zamansu a tafin hannuna. I love you so very much Yah Yoohan”. Ta ƙare maganar da faɗawa jikinsa ta rungumesa.
        Idanu ya lumshe a hankali yana mai ƙarɓarta da hannu biyu. harga ALLAH yanama yarinyarnan soyayya da ƙauna mai tsanani. Wanda ɓata lokacine wajen zama yayta faɗa da fatar baki. Tana riƙe da wasu darajoji da martabobi da mace tagari ce kawai ke iya samunsu a wajen ɗa namiji. 
       “I love you more.... More.... More and more Zeeynab ”.  Ya faɗa shima cike da shauƙi da sarƙewar harshe a cikin kunnenta. A tare suka sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗaggo daga jikinsa. Sumbatar laɓɓanta yayi yana lumshe idanu da sake buɗewa a kanta. Kafin ya juyata suka kalli mirror ɗin yay musu hoto. Sosai sukayi ƙyau kuwa. Tamkar ka sacesu ka gudu dan tsabar dacewa da sukai da juna. Daga haka yaja hannunta suka fice a gidan gaba ɗaya. Cab suka samu zuwa wani haɗaɗɗen shopping mail da Amerikawan ke ji da shi. Dan yasan zasu samo duk abinda zasu iya buƙata a can.
        Aiko sosai wajen ya birge Nu'aymah. Babu kunya balle damuwa tattare da ita ta shiga kashe kwarkwatan idanunta tana jinjina jin daɗin duniya da turawan nan keyi. tare da ɗunbin jin tausayin Africans da wahalar Yunwa da kashe-kashe ta gama jigatawa da fiddamu a hayyacinmu gaba ɗaya.
        Yana riƙe da hannunta suke duba duk abinda zasu iya buƙata. Kasancewar kowa harkar gabansa ya keyi babu ruwan wani da wani sai suke komai kansu tsaye. Bayan sun kammala shopping ɗin suka fito ta ɗan wajen mail ɗin kafin a gama musu packaging ɗin kayan zasusha coffee. 
          Sosai Nu'aymah yanzu take bala'in son coffee. Ta rasa dalilin hakan. Dan dacan har haushi takeji yanda Yoohan ya ɗauki amanar kansa ya bama coffee ɗin. Amma tunda suka dira U.S ta koma tamkar mayya akan coffee. 
         Shi dai Yoohan yakanyi dariyane idan yaga yanda take bankarma cikinta. Cike da shakiyanci yake faɗin, *_Bugun daga kai sai mai tsaron gida kenan_* duk yanda Aymah taso fassara kalmar nan tasa ta kasa. Da taga ma wahala kawai take bama kanta sai ta daina damuwa da sanin. Daya faɗa sai ta zuba masa harara kawai ta cigaba da hidimarta.
        Sunsha coffee suna ƴar hirarsu cike da farin ciki. Dan kayansu tuni an tura musu gidansu. Kusan zaman awa guda sukayi a wajen sannan suka miƙe. Gaba sukai wani shagon sai da tsuntsaye dake tsallaken mail ɗin. Aymah ta zabi wasu kyawawan tsuntsaye mata da miji dake cikin keji. Yoohan ya biya yana tausayama ƴan kuɗaɗensa da yau Nu'aymah kema ɗibar karan mahaukaciya😂🤣. Zata ƙara nuna wasu yay saurin riƙo mata hannu yana magana da ƴar hausar daya fara iyawa a wajenta.
       “Hy madam ki taimaka mani karki ƙaremin kuɗi anan. Bakiga munyi shopping ba, kalli wallet ɗinafa”. Yay maganar yana nuna mata cikin wallet ɗinsa kamar zaiyi kuka.
        Ƴar dariya tayi ƙasa-ƙasa da cewa, “Humm sarkin raki na haƙura. ALLAH zai baka wasu masu albarka tunda ka farantama iyalinka rai ne. Kaima ALLAH ya faranta maka da ƙyaƙyƙyawan sakamako My boo”.
       Murmushi yay cike da jin daɗi. Dan duk wautarta ya shaideta da iya lafazi mai daɗi a garesa. Ko tsiwa take masa zaka samu babu kalaman raini a ciki sam. Sumbatar laɓɓanta yayi da kashe mata ido ɗaya, yace, “ALLAH yay miki albarka my Sweet girl”.
       “Amin my Boo”. Ta amsa masa cike dajin daɗin addu'arsa. Daga haka suka fito yana riƙe da cage ɗin ƙyawawan tsuntsayen masu daddaɗan kuka. A ƙafa suka ɗan ringa tafiya suna hira kamar yanda Aymah ta bukata. Ya fahimci tanason ganin kanta a inda bata saniba. Shiyyasa yake biye mata wajen ɗan fita da ita dan tai farin ciki, ya kuma rage mata kewar ahalinta daya rabota a cikinsu ya kawo nan ya ajiye.
      Saida suka gaji da tafiyar sannan ya tare musu abin hawa suka ƙarasa gida. A barandar gidan suka iske shopping ɗinsu. dan haka ya buɗe gidan suka dinga kwasa suna shiga da kayan ciki har suka kammala.

        Sallar la'asar data riskesu a hanya sukai ƙoƙarin gabatarwa. Bayan sun idar Aymah ta fara wucewa kitchen ɗin. Kayan da duk suka siyo ta fara buɗewa tana ajiye komai inda ya dace da zamansa. Tana kammalawa kenan ta ɗakko tukunya zata ɗauraye Yoohan ya shigo waya manne a kunnensa yana magana. Idonsa a kanta ya dafe kitchen cabinet ɗin dayin ɗan tsalle ya haye samansa ya zauna. Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke idanunta ita dai, dan ta fahimci wayar tasa mai muhimmanci ce.
         Sai da ta gama wanke duk abinda zatai aikin da shi sannan ta jawo rigan girki ta ɗaura. Dai-dai kuwa da kammala wayar Yoohan. Sauka yay ya nufeta da ɗan alamun gajiya tattare da shi. “Wlhy duk kin gajiyar da ni Sweet girl. Inata murna yau zan huta a gida bazanje asibiti ba. Amma sai da kika sakani yawo”.
        Hararsa ta ɗanyi tana riƙe ƙugu da duk hannayenta. Cike da rigima tace, “Uhm uhum uhmyy. Wani aiki sai rago dai wlhy”.
      “Oh nine ma ragon?”. Ya faɗa yana wani hangame baki.
      Gira ta ɗage masa tana wani juya idanunta manya masha ALLAH. Tace, “Na gaske ma”.
         Wata dariyar mugunta yayi yana matsota, da sauri ta manne jikinta da cabinet ɗin tana marairaice fuska. Kafin ta samu damar magana yazo dab da ita. Matseta yay a wajen ya hanata ko guntun space yana wani ɗage gira sama da ciskule fuska. Hannayensa na a gefe da gefenta ya kai fuskarsa gab da tata suna shaƙa da busama juna numfashi. Ga idanunsu cikin na juna kowa kwarjini da sirrin na ɗan uwansa na ratsa masa jiki da zuciya. Da wani irin karya harshe na ma'abota shauƙin soyayya yace, “Yarinya kema kinsan ni ɗin ba rago bane. Amma zan sake tabbatar miki kuwa a yau ɗin nan da iznin ALLAH. Sai wannan bakin rakin naki ya kai titi saboda neman agaji”. Ya ƙare maganar da ɗallar laɓanta da yatsunsa biyu.
           Da sauri ta dafe bakin hawaye na cika mata idanu. Ta kai hannu bisa damtsen hannunsa yay saurin kaucewa yana wata shaƙiyyar dariya ƙasa-ƙasa dan yasan muguntar da zatai masa. 
     Kumbura tayi tai fam. Cike da haushi ta kama rigar zata kunce ya riƙe hannunta. “Ai yarinya baki isa ba. Kin riga da kin yarda da game ɗin nan dan haka girki dole ne”.
       Baki ta tura masa tana kwaɓe fuska da faɗin, “Na fasa game ɗin. Girkinma sai dai kay.....”
        “Hhh daga baya kenan hajjaju Zenaba ƴar farar bakanuwa ƙyaƙyƙyawa”.
    Yay maganar da riƙota hannunta ya maida ɗaurin rigar yana mata wani dariyan iya shege a gefen wuya. 
        Gaba ɗaya neman susuta mata jiki yake da salonsa. Saurin zame jikinta tai ta koma gefe tana faɗin, “Ai inba yau a kwai gobe indan ALLAH ya kaimu. Ka ɗauka yau ɗin kaine a sama ni a kwana. Sai dai kuma zaka dawo kwanar ne ni na koma ciki...”
   Ta ƙare maganar da wani salo tana kashe masa ido ɗaya.
       Da gasken gaske saƙonta ya iso inda ta turosa. Dan gaba ɗaya jijiyoyin Yoohan suka saki dama kwana biyun nan rakinta ya sakashi ɗan bata ƙafa. Lip ɗinsa ya cije da ƙarfi yana wani jan ajiyar zuciya ya ɗauke kansa. Batare da yace komaiba ya jawo wayarsa ya miƙa mata. Yana mata wani kallo ƙasa-ƙasa. Amsar wayar tayi da tura baki gaba tana ƙunƙuni. Ta kalli hoton abincin da ƙyau sannan ta ɗan dubesa ta ɗauke kanta tana murmushi.
        Kujerar dake gaban tebir ɗin tsakkiyar kitchen ɗin yaja ya zauna. Ya wani miƙe ƙafafu da bajewa da ƙyau, irin fa shine boss ɗin nan.
         Nu'aymah bata sake bi ta kansa ba ta fara ƙoƙarin ɗaura girkin tana addu'a a ranta da fatan yin komai yanda ya kamata. 

         Ko ɗauraye cokali bai tayataba, tunda ta fara. Yama ɗauke kansa gaba ɗaya daga gareta sai danne-dannen waya yake yi hankalinsa kwance. Duk da kuwa a baɗini duk wani motsinta nakan idonsa ne. 
       Kasancewar ta kwana biyu batai girkin ba yasa takeyin komai cike da ɗoki. Kafin cikar awa ɗaya kuwa sai ga ƙamshi ya gama gauraye kitchen ɗin gaba ɗaya har falo. Shi kansa Yoohan shaƙa yake cike da jin daɗi da kwaɗayin son cin abincin. Tsaf ta kammala komai ta gyara kitchen ɗin da ɗauraye duk abinda ta ɓata duk yana zaune dai yana kallonta. Abincin ta zuba a plate tare da ɗan ɗora kwalliyar data ƙara ƙawatashi ta ɗauki cokali tazo ta dire gabansa tana wani shan ƙamshi.
      Idanu ya tsirama abincin dake ta tashin ƙamshi mai saka yunwa. Kafin ya ɗago ya kalleta. Ɗauke fuskarta tai gefe murmushi nason kufce mata. Sai kuma taje ta tsiyayo apple and orange juice ɗin data haɗa a glass cup tazo ta ajiye shima a gabansa. dai-dai yana gyara zamansa. Bai fahimci minene ba, amma yaga sanda take markaɗa abu dai. Cokalin ya ɗauka ya ɗiba abincin kaɗan ya kai bakinsa tare da yin bismilla. Duk da daɗin daya ratsa masa baki da kunne da ƙwaƙwalwa sai ya wani yamutse fuska harya haɗiye. sake ɗiba yay yaci nanma fuska a yatsine. Aymah dai na kallonsa baki a ɗage dan tasan wlhy ƙarya yake yace abincinta babu ɗanɗano.
       Cike da son danne dariyarsa na ganin yanda tai da fuska ya kai lauma ta uku. A hankali ya lumshe idanunsa da sauke wata sassanyar ajiyar zuciya. Sai kuma yay mata alamar jinjina da kashe ido ɗaya ya haɗe yatsunsa biyu👌🏼 alamar komai zam.
       Itama ajiyar zuciyar ta sauke a hankali da juya bayanta idanunta na cika da ƙwallar farin ciki dajin ƙaunar Umm ɗinta mai tsanani. Dan itace ta maidata tauraruwa wajen tsayawa akanta tun tana ƴar mitsitsiyarta. Ƙanƙantarta baisa Umm ta taɓa rangwanta mata ba akan aikin gida duk da sunada mai aiki. Kamo hannunta da Yoohan yayi ya ɗora bisa cinyarsa ne ya sakata sauke ajiyar zuciya a karo na biyu.
      “K ta dabance Cutie”. Ya faɗa a cikin kunnenta yana tura hannunsa cikin rigarta.
      Idanunta ta lumshe itama da kai hannunta ta shafo kwantaccen sajensa mai laushi dake cin kuɗaɗe wajen gyaransa. Kiss ya bata a wuya tare da ɗagowa ya kamo fuskarta ya manne bakinsu waje ɗaya. Bata hanashi ba. Dan ya riga da ya koyar da ita wannan sirrin.
      Sai da taga wasan na neman canja salone ta ƙwace kanta da ƙyar tana masa dariya. Sai ko ya ƙwaɓe fuska tamkar zaiyi kuka dan da gaske ya zurma da yawa.
         Plate ɗin abincin ta ɗauka ta ƙaro musu tare da ɗakko juice ɗin gaba ɗaya shima. Sai lokacin Yoohan ma ya ɗauki wanda ta fara kawo masa yasha yana sauke ajiyar zuciya. Cike da ɗage gira yace, “Kin haɗu a abubuwa da dama Hausa girl”. 
     Murmushin jin daɗi tayi, dan har ranta tanajin nishaɗi idan ya kirata Hausa girl. Tana son yarenta tana alfahari da shi fiye da zaton mai karatu. Tanaji a ranta komi ta zama dolene duniya tasan itaɗin ƴar ƙabilar HAUSA ce gaba da baya.
       Sunci abinci cike da farin ciki, yana bata tana bashi har suka kammala. Da taimakonsa yanzu kam suka tattare wajen suka fice a kitchen yana faɗin ta zaɓi ƙyautarta.
    Ita dai dariya take masa kawai. Sai da suka fito falo ya zauna da ita a jikinsa sannan ta dubesa tana murmushi. “Soyayyarka da kulawarka a gareni kaɗai ta isheni tukuyci my sweet boo”. Tai maganar cike da salon da take ƙara ƙwarewa wajen koya a hannun Aunty Hajarahn mai sonta da ƙaunarta.
      Rungumeta yay a jikinsa ƙaunarta na sake ratsasa. A ƙasan ransa kuwa godiya yakema ALLAH da samunta tare da jin girma da darajar iyayenta a cikin ransa. Fatansa ALLAH ya basu ƴaƴa masu albarka suma su basu irin wannan tarbiyyar tata abin son kowanne ɗa nagari.

__________★★

      Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa ga Nu'aymah da Yoohan cike da farin ciki da tattalin juna kasancewar har yanzu a amarci da ɗokin juna suke. (Kunsan shi farkon aure dama haka yake. Za'aita nunama juna soyayya cike da zalama. Ku kanku jin kanku kuke tamkar babu ya ku a duniya. Sai rayuwa ta fara nisane abubuwa ke fara tsauri. Sai dai da yake UBANGIJI mai rahama ne da jinƙai sai kaga hakan baya hana a nunama juna soyayya da kulawa koda saɓani na shiga. Duk da jarabawa kan ratsa a zamantakewar ma'aurata kaga matsalolin nata yawaita fiye da hasashe. ALLAH ya cigaba da zaunar damu a gidajenmu lafiya tare da mazajenmu da ƴaƴanmu da abokan zamanmu baki ɗaya mata sarakunan gaskiya a fadar gaskiya😘😍🤗).
         
      Kwansu goma sha uku a U.S Yoohan yay shirin zuwa Oman yin wani aiki na kwana biyu. Daga can kuma zai wuce Nigeria insha ALLAH.
         Yasha taɓara kuwa a wajen Aymahn sa. Dan kuka sosai ta dinga yimasa akan saita bisa. Da ƙyar ya lallaɓata da tabbatar mata Juliet matar Omar (Rich) tana zuwa daga 9ja a daren yau. Idan ma batason zaman anan gidan ita kaɗai sai ya kaita gidan Juliet ɗin ta zauna a can harya dawo.
     Da ƙyar ta amince kuwa. Shima sai da aka haɗa da hajjo wajen lallashi. A ranar kuwa Juliet ɗin ta iso. Sun tarbi juna da mutuntawa. Kuma har cikin zuciya Nu'aymah taji zata iya zama tare da Juliet ɗin. Musamman yanda taga itama Juliet ɗin na nuna mata ƙauna da yaba komai nata tana sake taya Yoohan murna. Shi dai murmushi kawai yakeyi yana bin mutuniyar tasa da kallo ƙasa-ƙasa.
      Washe garin da zai wuce sai da ya rakata gidan Juliet sannan ya wuce ya barta da kewarsa kamar yanda shima ya tafi cike da tata kewar.

★★★★

          Tamkar jira jikin Aymah keyi Yoohan ya wuce ta fara ƙananun ciwuka. Kullum da zazzaɓi take wayar gari, zuwa ƙarfe ɗaya na rana kuma sai ya gudu. Tun Juliet bata fahimtaba harta fahimta saboda shaƙuwar dake ƙara shiga tsakaninsu da Nu'aymah. Dan Juliet tanada sauƙin kai sosai. Bata taɓa kuma nuna ƙyamar addinin Nu'aymah ba koda kuwa akan fuskartane. Wani lokacinma idan Aymah na salla ko karatun Al-qur'ani har zama take taita kallonta. Dan itama zuwa yanzun tasan mijinta Omar (Richard) ya musulinta............✍


*_Gaba ɗaya na manta yau monday fa😥🤦🏻🏃😂_*


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/1, 2:39 PM] +234 806 331 2486: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 67

............Juliet taso kiran Yoohan ta sanar masa amma Aymah ta hana. A cewarta ta barsa wai dama ta saba irin wannan zazzaɓin duk shekara. Asibiti ma taƙi yarda suje sai magani data amsa tasha. Daga haka ta fara ɗan ƙarfafa kanta duk dan ta kwantarma Juliet ɗin da hankali ganin ta damu. Gashi itama fama take da kanta dan cikine da ita ɗan wata kusan takwas.
      Dole Juliet ta barta, sai dai duk motsinta na akan idonta. Ita har mamakin yanda Nu'aymah ke bankar coffee takeyi babuji babu gani. Gason yawan kwanciya bisa tiles wai sanyin take so. 
        A hankali tama daina cin abinci, dan kotaci sai tayi amansa take samun sauƙi. Hakan na damunta, sai dai ta kasa faɗama ko Juliet ɗin balle Umm da Hajjo da Addah da kusan kulumm sai sunyi waya. Ko sun kirata ko ita ta kirasu sai taita ƙarfafa kanta yanda babu mai ganewa. Sai dai Uwa dabance. Dan Umm kan tambayeta anya tana lafiya kuwa? Dan a muryarta da yanayin sanyin da tayi na rage surutu da rawar kai Umm takan ji kamar Aymah na cikin wani haline. Amma sai take cemata babu komai, kawai yanayin wajene.
     Juliet nada coffee powder a gida, sai dai kota haɗama Aymah bata sha sai dai suje shagwan shan coffee ta sha tayo guzirinsa kuma. A duk sanda sukai waya da Yoohan ko video call kam sai taita ƙarfafa kanta harda masa ƙarfin halin tsiwa wai karda ya fahimci halin da take ciki.
       Batasan kallonta kawai yakeba, dan tun kafin akai haka ya gama fahimtar shigar ɗan tayin cikinsa a mahaifarta. Sai dai ya barma ransa har ALLAH ya bayyana ikonsa da kansa tunda shima hasashene kawai da shegen ganin ƙwaf irin na likitanci bisa baiwar da UBANGIJIN al'arshi ya azurtasu da shi.

_________________

      Kwanan Yoohan huɗu a ƙasar Oman ya wuce Nigeria. A abuja ya sauka, sai dai maimakon ya tafi gida direct sai ya sauka a hotel ya kama ɗaki. Dan dama babu wanda yasan da zuwansa ƙasar a cikin su papa. Yama toshe duk wata hanyar da zasu iya samunsa a waya tun barinsu Austria. Ya fi son yazo su fuskanci juna akan maganar Solomon ɗin fiye da suyi magana ta waya.
        A daren ranar ya samu aka samo masa Number ɗan sandan nan da ƙyar ta hanyar wani abokinsa da shima ɗan sandan sirrine babba.
     Gajiyar daya kwaso ce ta sakashi yin barci da wuri ranar ko waya da Aymah baiyiba. To itama dai da yake ranar zazzaɓi ya mata rigif ko nemansa batayiba ma. 
      
      Washe gari ƙarfe goma na safe Omar (Rich) ya iso hotel ɗin daga birnin Lagos. Ya iske Yoohan ɗin cikin shirin suit royal blue da sukai masa masifar ƙyau. Musamman yanzu da yay wani ɗan ɓul-ɓul dashi saboda madarar angwanci data hudashi. Rungume juna sukai cike da so da ƙyauna da begen juna. Kai kace basa waya kullum. Bayan sun gama ƴar chapter ɗinsu da suka iya suka fito gwanin sha'awa zuwa motar Omar ɗin. Omar ne ya jasu zuwa headquarter ƴan sanda na jami'an tsaron sirri suna ƴar hirarsu.
      Sai da suka gama shan tambayoyi da uban bincike kafin su sami damar shiga da taimakon abokin Yoohan ɗin da aka sanarma zuwansu daga baya.
     Da ƴar dariya Dawood yake kallon Yoohan daya ciskule fuska saboda haushi binciken da akaita musu yana faɗin. “Yi haƙuri bokan turai, wlhy banyi tunanin zakuzo a yau bane da nazo na tsaya a gate ɗin na jira isowarku ai. Tunda aka ɗora mana adalin shigaba a hukumarnan tamu tsaro ya ƙara tsauri dan sam bashi da wasa”.
       Dariya shima Omar yayi yana taɓe baki. Yace, “Kai Dawood manta da lamarinsa kewar matarsa ke ɗawainiya da shi badan wannan binciken yake fushi ba”.
    Hararsu Yoohan yayi su duka amma baice komaiba. Da haka suka ƙarasa can sama inda office ɗin oga kwata-kwata na hukumar DSS yake. Duk da Dawood yay masa bayani akan zuwan su Yoohan ɗin sai da suka jira shi ya fara shiga office ɗin sannan ya fito yay musu iso.
      Ƙyaƙyƙyawan dattijo ne da a shekaru a ƙalla zai iya kaiwa 64 Zaune a kan kujerar office ɗin hankalinsa gaba ɗaya akan Computer ɗin dake saman desk ɗinsa. Batare da ya ɗago ba ya amsa musu sallamarsu cike da nutsatstsiyar muryarsa mai tarin kamala da dattako. 
       Sosai kwarjininsa ya cika zukatan su Yoohan duk da bai ɗago sunga fuskar tasa ba da ƙyau. Da hannu yaɗan nuna musu kujerun yana faɗin, “Bismillanku”.
     Kusan a tare Omar da Yoohan suka sauke ajiyar zuciya da duban Dawood dake ƙame a tsaye. Kai shima ya jinjina musu alamar su zauna ɗin. Zaman sukayi tare da haɗa baki wajen faɗin, “Good morning sir”.
        Cikin ɗan fesar da iska Boss *_Jawaad Abdul-aziz Yusif tafida_* ya ɗago gaba ɗayansa fuska babu walwala kamar ko yaushe yace, “Good Morning”. yay maganar da miƙa musu hannunsa alamun suyi musabuha.
      Omar ne ya fara miƙo masa hannun suka gaisa, kafin ya miƙama Yoohan da shima zuciyarsa ke wani bugawa da harbawa da sauri-sauri. sai dai cike da dauriya ya faɗaɗa fuskarsa da murmushin ƙarfin hali. 
      Da ga shi har Boss Jay zukatansu suka buga da ƙarfi. Hannun Yoohan ya dinga rawa dan yama kasa ƙarasawa da shi inda na Jay dake ƙoƙarin zare glass ɗin idonsa yake.
       Hakan yayi dai-dai da shigowar wata kamilalliyar mace da shekarunta zai kai kimanin 53 cikin office da sallama, hannun ta riƙe da takardu. Sanye take cikin doguwar rigar jallabiya baƙa. Shigar tata ta ƙara fidda kamalarta da mutuncinta ga mai kallonta.
       Akan mijin nata ta fara sauke idanunta da mamakin yanayin data gansa. Sai kuma ta maida dubanta ga abinda yakema kallon ruɗani da tsoro. Baya tayi da sauri har takardun hannunta na watsewa a ƙasa. Saurin sunkuyawa Dawood da ke binsu da kallon mamaki yayi yana tattare takardun da faɗin, “Am sorry maa”.
        Bilkisu bata iya cewa komaiba sai takawa da tai da sauri inda Jay yake. Zatai magana yay saurin damƙe hannunta alamar shi ya dawo cikin hankalinsa. Girgiza mata kai yayi alamar kartace komai. Sai ma wayancewa yayi da faɗin, “Wai nikam da gaske likitan da naso gani ruwa a jallo shekara ɗaya data shuɗe ne amma hakan ya gagareni a gabana?”.
       Duk da Yoohan yaji sam a ransa ba wannan batun bane jefa adalin ma'aikacin cikin ruɗanin ganisa sai shima ya sauke ajiyar zuciyar da sam bata samun nutsuwa bace. Cike da ladabi ya jinjina kansa yana murmushin ƙarfin hali. Dan wani masifar kwarjini da Jay ya masa. Yace, “I'm very sorry sir. Nasan ni mai laifine sosai a gareka”.
      “No no no son. Inama mutane irinka uziri sosai ni a rayuwa. Dan haka manta kawai da wancan batun, tuni an kauda matsalarma”. Jay ya faɗa yana maida glasess ɗinsa akan ido.
      Cike da jin daɗi Yoohan yace, “Thanks you Uncle”. Sai kuma ya ɗan kalli Bilkisu da alamu suka nuna har yanzu tana a cikin ruɗani ita dai yace,  “Good morning maa”.
         Da wani irin sanyi tace, “Good morning dear”. Shima Omar (Rich) da al'ajabi ya cika gaisheta yayi. Ta amsa masa da kulawa shima tana duban Jay da har yanzu idanunsa akan Yoohan suke. Kauda kansa yayi ya ɗan dubeta saboda taɓa masa kafaɗa da tayi. Murmushin ƙarfin hali yay mata da nunama su Yoohan ita faɗin, “My wife. Itace naso na kawo maka a wancan lokacin muka gagara samun dama. Itama ma'aikaciyace a wannan hukumar. Amma Alhmdllh, daga baya mun fahimci babu waccan matsalar da mukai zargi”.
       Cike da girmamawa Yoohan da Omar sukace masha ALLAH. ALLAH ya ƙara kiyaye gaba.
         Amin suka amsa musu. Bilkisu data fahimci zamanta a wajen zai iya kawo matsala sai tai ɗanyi murmushi da ranƙwafawa saitin kunnensa tai magana. “Bara naje, su Zuhrah na jirana zamu wuce. Ga takardun nan duka na haɗo maka na case ɗin matar nan mai safarar ƙwayoyi”.
      Kansa ya jinjina mata kawai yana murmushi. Yana son ɗan sumbatar matarsa babu dama. Dan haka ya kashe mata ido ɗaya cike da salon ƙwarewar manyan masoya😉😂.
      Itama murtani ta maida masa da nata salon taima su Yoohan sallama ta fice. Numfashi Jay ya furzar a ɓoye. sannan ya maida duka hankalinsa gasu Yoohan da kansu ke a ƙasa. Dan gaba ɗaya zuciyar Yoohan ta gaza samun nutsuwar zama a waje ɗaya. Yadai dage yanata ambaton sunayen ALLAH kozai samu sassauci daga abinda yakeji cikin jininsa.
         “Tom Doctors ina saurarenku. Dawood ya sanarmin kuna son ganina cike da magiya a garesa. Ina fatan dai lafiya ko?”.
       Omar yace, “A lafiya lau sir. Wani taimako mukazo nema ne a wajenka da alfarma akan wani case”.
       “Okay. Babu damuwa. Dawood zoka ɗauka dukkan bayanansu dan kar a samu kuskure ko”.
        Da tsantsar girmamawa Dawood yace. “Okay sir”. Yay maganar da ƙame jikinsa waje guda yana buga kafarsa ƙasa. Hannu Jay yaɗan miƙar alamar amsawa. Daga haka ya ciro takarda da pen ya zauna ya fara sauraren bayanin da Omar ya farayi kasancewar Yoohan ya sanar masa komai dangane da gidan su Aymah akan abinda yaji daga gareta da wanda ya sani.
        Sai da ya kai aya Jay ya sauke numfashi yana janye pen ɗin da yake gogawa saman laɓɓansa. Ya ɗan murmusa da faɗin, “Babbar magana. Ɗan jibiya family kam ba ɓoyayyan gida bane. dan ahaline na masu daraja saboda ilimin addini da harkokin kasuwancinsu. So dama akan samu irin waɗanan rikice-rikicen da ZAGON ƘASA a irin mafi yawan waɗan nan gidajen. Shi kuma zagon ƙasa Kamar wani SARAN ƁOYE ne mai cin rai da ruɗa tunanin wanda akemawa. So na tayaku murna tare da shigowarku cikin hasken musulinci. Na kumayi alƙawarin taimaka muku wajen ban kaɗo abinda kuke buƙata bisa son ƙyautatawarku ga Sheikh Soorajidden Hashim. Saboda nima malamina ne ai. Kuna ambata masa sunana zai baku labari. Har ɗaurin aurenku naje ma. tabbas kwanaki dana buƙaci zuwa wajensa muyi magana ya sanarmin zaiyi tafiya za'aima yarinyarsa aikin ƙwaƙwalwa a ƙasar ƙetare”.
     Da jindaɗi a fuskokinsu suke dubansa.
    Shima murmushi yayi yana zare glasess ɗinsa. ya cigaba da cewa, ”Ina ƙaunarsa sosai dan yayima rayuwata hidima mai yawa. Insha ALLAH nima bazan gajiya ba wajen bankaɗo azzalumai masu cin dunduniyarsa. Sai dai wannan aikin dolene ya kasance na sirri”. Yakai ƙarshen maganar da duban Dawood.
      “Dawood! Ina buƙatar ganin Bilkisu Jawaad”.
      Da sauri Dawood ya miƙe yana faɗin, “Okay sir”.
    
      Cikin mintuna ƙalilan sai ga Dawood ya dawo tare da matashiyar mace da bazata gaza shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba. Daka ganta babu tambaya kasan jinin Boss Jawaad Abdul-aziz ce. Sanye take cikin wando da riga na Uniform ɗin hukumar. Da alama itama jami'ace a hukuma (dan ƙari. Bilkisu ƴar bilkisu jikar bilkisu kenan😉. Ita ƴar sanda, mamanrta ƴar sanda. Babanta ɗan sanda😝. Wani aiki sai Jay😂lol).
       Fuskarta cike da miskilancin data gada wajen iyayenta ta ƙame tare da salute ɗin mahaifinta kuma oganta a wajen aiki. tace, “Sir gani”.
      Daga Yoohan har Omar kallon mamaki suke mata. Dan basa buƙatar ƙarin bayanin komai game da Biljay.
       Takardar da Dawood ya rubuta ya miƙa mata cike da bada umarni a gareta matsayin oga ba mahaifiba. “Duba min wannan takardar”.
      “Okay sir” ta faɗa tana ɗaukar takardar. Cike da hazaƙar ƙwarewar aiki ta duba rubutun takardar tsaf, kafi. ta ɗago ta kallesa tana sunkuyar da kanta da ƙamewa. “Na duba Sir”.
       “Me kika fahimta?”.
“Report ne na case ɗin ɓoyayyun mutane masu laifi”.
       “Masha ALLAH. Little bee kece zakiyi wannan aikin. Waɗanan sune masu kawo Report ɗin. Zakiyi joining ɗinsu kuyi aikin tare. Sai dai kece zakiyi kutse a cikin gidan ko mubi ta wata hanyar insha ALLAH. Kinsan banson wasa, bana son kuskuren ganganci akan aiki, so be careful”.
      “Insha ALLAH sir”.
Kai ya jinjina mata da maida dubansa kan Dawood. “Dawood tare zakuyi wannan aiki da ita, so zata kasance ƙarƙashin control ɗinka, dukanku kuma zaku kasance akan umarni”.
     Shima ya amsa da “Okay sir”.
Daga haka Jay ya maida dubansa gasu Yoohan. “Doctors waɗanan nan sune zasu taimaka muku akan wannan case. Insha ALLAH daga nan zuwa kwana uku zamu san wadda zata shiga cikin gidan matsayin maiyin hutu a wajen Sheikh. Sauran aiki duk zasu yisa baku da damuwa. Sai dai dole kuma sai da hannunku a ciki dan kun fisu sanin sirrin gidan a yanzun. Zaka haɗata ƙawance da matarka ta waya. Dan wasu abubuwan ta hanyartane zasu sami haske sosai. Duk abinda ya dace zaku cigaba da ji ta hanyar Dawood, dan shine oganta”.
      Godiya sosai su Yoohan suka shiga yimasa. Dan sam basuyi tunanin samun mafita cikin sauƙiba haka daga garesa oga kwatakwata da ganinsama ke da matuƙar wahala. Yanda bai musu bayani akan matsayin Bilkisu a garesaba suma basu tambayaba duk da sunada buƙatar ji. 
      A tare da shi suka fito office zuwa massalaci saboda kiran sallar zuhur. Bayan an idar da salla kuma sukai masa sallama da ƙarin godiya suka wuce cike da farin cikin wannan karamci da samun sauƙi. Sai dai ƙasan ran Yoohan shi kaɗai yasan mi yakeji game da Jay ɗin.
    Koda suka ɗauki hanya kasa haƙuri Omar yayi sai da yayima Yoohan maganar kallon da yaga Jay ɗin na masa da matarsa. Harma hanata maganar da yayi. Tare da cewa nifa, “Wlhy fisgen kamannima kukaimin”.
        Da mamaki Yoohan yace, “Kamanni kuma?”.
      “Yes X-man. Wlhy a fisge kunyi kamanni like na jini haka”.
      Nannauyan numfashi kawai Yoohan yaja da ƙarfi ya fesar batare da ya iya cewa komaiba har suka ƙarasa wani gidan cin abinci. Anan sukai lunch da cigaba da tattaunawa akan abinda ya shafesu. Daga haka sukawuce General hospital wajen Dr Shikurah. Sai dai sunyi rashin sa'ar samunta wai batama ƙasar.
     Yoohan yayi gaisuwa da abokan arziƙi suka koma hotel ɗin daya sauka. Omar ya jima a wajensa dan har dare suna a tare sannan ya koma gidan papa dan acan ya sauka shi. Amma sai bai faɗama kowa Yoohan na ƙasarba.
      Washe gari Yoohan yaje kaduna yin wani aiki. Sai washe garin daya cika kwana uku a 9ja ya dawo. Dai-dai da ranar da Little bee zata shiga gidan baba malam kenan. Dan haka kai tsaye gidansu ya nufa. Sai dai kawai su Madam Chioma suka gansa tsilum tamkar daren Christmas inji su.

___________★★

          Tun wucewar su Yoohan Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye a office ɗinsa. Gaba ɗaya man kan sa ya gama tsiyayewa tas akan wannan kamanni. Goshinsa ya murza da cewa, ‘Kai anya kuwa. Dolene nasan wanene wannan yaron’. Ya ƙare maganar da ɗaukar telephone yay kiran Dawood. 
        Dandanan Dawood ya amsa kiran boss. Nuna masa kujera yayi alamar ya zauna. Bayan kusan mintuna uku ya ture files ɗin gabansa yana kallon Dawood ɗin.
      “Dawood nikam a ina kasan yaron nan ne?”.
      Cike da girmamawa ya bashi amsa da faɗin, “Sir, tare mukai secondary school da su”.
      “Masha ALLAH, lallai kayi masa sani na sosai. Anan cikin abuja suke?”.
        “Yes sir. Ai yaron sanannen Pastor ɗin nanne Goshpower mai ƙaton catholic church ɗin nan dake a wuse2”.
     Ɗan jimm Jay yay yana kallon
Dawood. Sai kuma ya sauke numfashi kaɗan yana wani guntun murmushi mai kama da an masa dole. “Okay thanks you, zaka iya tafiya”.
     Miƙewa Dawood yayi tare da salute ɗinsa ya fice yana mamakin tambayoyin ogan nasu.

      Dawood na fita Jay ya shiga Google. Bayanai ya nema akan dukkan handles ɗin papa dake a social network. Cikin mintuna ƙalilan kuwa suka watso masa komai. Facebook, Twitter, Istagram, Telegram, dama wasu daban-daban. Harda youtobe chennal da suke ɗaura dakan abubuwansu na church ɗinsu. Numfashi yaja ya furzar tare da shiga kowanne shafi ya duba followers nashi da duk wani posts da yayi a kai. Yawanci duk akan church ne dai.
       Komawa yay bincike akan pictures nashi. A take kuwa suka bashi su da yawa. ‘Oh my GOD!!’. Jay ya faɗa da matuƙar razana. Gaba ɗaya kansa ya sake kullewa. yama rasa kalar tunanin da zaiyi dan da gaske shi dai ya shiga ruɗani. Ta yaya hakan zata kasance bayan shi shaidane akan abinda ya tabbatar a zahirin gani da ido. To amma inhar ta tabbata a tunanin da zuciayarsa ke bijiro masa lallai sai dai idan akwai yaudara a lamarin kenan, ko kuma...... Yay saurin girgiza kansa alamar ba haka baneba sam. dan da sun sani ai.
      A wannan yanayin Bilkisu ta sake shigowa ta samesa. Rungumesa tayi ta baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke sannan ya zagayo da ita gabansa. Kaɗan ya ranƙwafo ya sumbaci laɓɓanta da goshinta.
       “My Boss ina baƙin naka suke?”.
“Sun wuce Miemaa. sai dai ina cikin ruɗani wlhy”. Yay maganar yana jan hannunta wajen kujerarsa.
     Zama tai a kujerar tana bashi amsa itama. “Bakai kaɗai bane a ruɗani. Ni kaina rikicewar ta hanani zama na gudo nabar su Ummie acan”.
      Ta bayanta ya ranƙwafo yana nuna mata abinda ya samo game da papa. Ƙwarai da gaske ta cika da mamaki itama saboda ganin hoton papan. Dan haka sukayi zaman tattaunawa yay mata bayanin dukkan hukuncin daya yanke. Tare da alƙawarin zuwa wajen baba malam kozai ƙara samun wasu bayanai ta wajensa game da papan tunda sun zama surukai.
     Ta gamsu ɗari bisa ɗari da hakan. Harma da zuwan wani cikin gidan, dan Little bee bazai yuwu taje gidan baba malam ɗin ta zaunaba saboda mijinta da wahala ya amince duk da yasan dokar aikin. Amma zai tura ƙaramar ƴarsu autar su Little ɗin mai suna Afrah akan case ɗin da su Yoohan ɗin suka kawo report.

_____________★★★

         Lokacin da Yoohan ya shigo gidan ya iske duk suna church. Sai guards ɗinsa kawai da maigadi aka bari alamar papa yaji shawararsa ta kwanaki kenan. A cikin gidanma daya shiga ya samu Blessing. Cike dajin daɗin ganinsa da tunanin tare yake da Aymah ta shiga masa welcome. Ya amsa mata kadaran kadahan. Ya kama ƙafar benen zai haura Blessing da haƙurinta ya ƙare tace, “Sir Aunty fa?”.
      Juyowa yay ya ɗan kalleta yana lumshe idanu da buɗewa. Sai kuma ya ɗan mata murmushi a bazata dan bata taɓa ganiba. Shi kuma jin daɗin nuna kulawarta ga matarsane ya sakashi yin murmushin. Sai da ya juya ya cigaba da hawa steps ɗin sannan ya bata amsa da, “Tana can na barota. Kina missing nata ne?”.
        Cike da haɗiye ɗokinta tace, “Sosai ma Sir. I miss her so much”.
     “Thanks you”. Ya faɗa a taƙaice yana idasa hayewa.
      Da sanyin jiki Blessing ta koma kitchen dan ta haɗa masa wani ɗan abun duk da baice yana buƙata ba.

      Shikam Yoohan ƙofar sashensa ya buɗe ya shiga. Mayen ƙamshin turaren da Nu'aymah ta fara amfani da su yana nan nane da sashen. Cike dajin sabuwar kewarta ya shiga yana kalle-kallen falon. Tsahon mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya ya nufi bedroom ɗinsa. Harya tura ƙofar ya shiga sai kuma ya fasa ya dawo da baya. Bedroom ɗin Aymah ya nufa, yana ƙoƙarin saka key ya buɗe ya ga ƙofar a buɗe. cike da mamaki ya tura da sauri ya shiga. Turus yaja ya tsaya yana kallon yanda aka hargitsa ɗakin. Kayanta na sawa duk a watse a ƙasa. Littatafanta hardasu Al-qurani duk an yasar. Saurin ƙarasawa yay inda Al-qur'anin izu sittin ke a kife a ƙasa alamar jefarma da shi akayi. Ya ɗaukesa ƙwalla na cika masa idanu. Wani masifaffen fushi na yunƙuro masa da tarar masa a ƙirji.
       Babu wanda yazo masa a rai da yin wannan aikin sai Gebrail. Kodan dama yana nan a maƙale a ransane oho. Ajiye Al-qur'anin yay saman mirror ya fito a matuƙar harzuƙe yana ƙwalama Blessing kira....
     Hakan yayi dai-dai da shigowar su madam Chioma cikin falon suna dariyar shirmen Abraham. A kusan tare suka tsaya cak suna kallon yanda yake sakkowa daga upstairs ɗin da gudu-gudu. Ga wani razanannen kira da yake ƙwalama Blessing. Yana gama sakko idonsa ya sauka akan Gebrail da yake shigowa kusan a ƙarshe.
      Ture Blessing dake isowa gabansa jiki na rawa tana amsa kiransa yayi gefe. Cikin rufewar idanu na rashin ganin su mama debora ya nufi kan Gebrail da duk ya daburce saboda tsorata na rashin gaskiya. A bazata Yoohan ya saukema Gebrail wasu gigitattun maruka a jajjere bisa kumatu. Kafin wani ya samu damar jin ba'asin wannan tashin hankali ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukansa da shi kai kace ALLAH ne ya aikosa. Gaba ɗaya idon Yoohan ya rufe, Al-qur'anin nan kawai yake ganowa yashe a ƙasa da Nu'aymah a sume a randa Gebrail ya shigar mata.
       Tunda su madam Chioma suke a rayuwarsu basu taɓa ganin irin wannan tashin hankalin da matsanancin fushin Yoohan ba. A take falon ya rikice da kuka da kururuwar ihu. Ina Yoohan sam bama yajinsu. Laftar Gebrail dake ihu yashe a ƙasa iya ƙarfinsa kawai yake ta ko ina. 
      Duk yanda madam Chioma da su mama debora ke kuka da masa magiya basa gabansa. hakama guards ɗin gidan kowa ya gagara matsawa inda Yoohan yake. Solomon da suka dawo tare da su Madam Chioma da yay ƙoƙarin matsawa wai ko Yoohan ɗin zai sauraresa sai da ya samu rabonsa. Dan zuba masa belt ɗaya Yoohan yayi jiki. Da wani irin mahaukacin tsalle da ihu yay gefe saboda azaba.
          Dukan Gebrail Yoohan yayi sosai har sai da yaga ya daina motsi, dan har papa daya shigo gidan tare da su Uncle Godwin bai sauraresuba. Sai da yay tiɓis shi kansa sannan ya jefar da belt ɗin gefe. Daga Momy harsu Joy kan Gebrail sukai suna kuka. Yayinda Momy Destiny ta riƙo Yoohan da shima ƙwalla ke silalo masa tsabar zafin zuciyar da yake a ciki. Zaunar da shi tayi a cikin kujera.
        A can gefe kuma Omar (Rich) daya shigo yanzun ne gidan, saboda ya fita tun safe. Tun a compound sauran guards ɗin gidan ke sanar masa abinda ke faruwa. Da sassarfa ya ƙaraso falon. A yanayin da yaga Gebrail da ihun Madam Chioma daya hargitsa falon da kururuwar cewar Gebrail ɗin ya mutu ya saka bama su Solomon daya gama shan tasa azabar umarnin cicciɓar Gebrail shi da sauran guards ɗin sufice da shi zuwa asibiti.
          Sannan ya ƙarasa inda Yoohan ke zaune yanata huci har yanzu da sassarfa. Cike da tashin hankali ya kamashi ya miƙar batare daya saurari ihun da Maman madam Chioma kema Yoohan ɗin a kai ba. Dan ya tabbata shirun da yay mata zuciyarsa sake kumbura take. Idan kuma har ya miƙe wlhy zai iya bugeta itama dan Yoohan ALLAH yay masa zafin zuciya na bala'i.
         Duk abin nan dake faruwa papa da su Uncle mike na tsaye suna kalonsu tamkar wasu gumakan farkon karni. Hakama baƙi da suka ɗan fara shigowa ziyara sunyi cirko-cirko da tsoro.
       Harabar gidan Omar ya fita da Yoohan da binsa kawai yake cike da rufewar ido. Turasa yayi a mota ya maida ya rufe tare da zagayawa mazaunin driver yaja ya fice da shi daga gidan. Kai tsaye hotel ya nufa da shi. A motar ya barsa yaje ya kama ɗaki sannan ya dawo ya sake kamashi ya shiga da shi ciki.
       Koda suka shiga cikin ɗakin zubewa Yoohan yayi a kujera kawai yana sauke wasu azababbun huci masu ban tsoro. Ruwa mai sanyi Omar ya ciro a fridge yazo ya miƙa masa. Fisgar robar ruwan kuwa yayi ya kafa kai. A mamakina sai gashi ya shanyeta tas yayi wurgi da robar yana juya idanunsa dake jajur abin tsoro.

____________★★★

         A ɓangaren Jay kuwa tun randa su Yoohan sukaje wa jensa a ranar kasa haƙuri yayi, da yamma liƙis ya shirya shi da Afrah suka nufi kano ta dabo gidan baba malam. Abinda bai taɓa yiba. Dan bai taɓa kai iyalansa gidanba tunda suke mu'amulat nasu.
     Sosai baba malam yaji daɗin ganinsa. Dan yamasa ziyarane ta bazata. Ya kumaji daɗin zuwa da Afrah da akai. Wadda bai taɓa saniba a ido, sai dai a baki. Shima bawai ya taɓa tantance ƴaƴan Jay ɗin maza ne ko mata ba. Duk da kuwa Jay ɗalibinsa ne sosai. Dan ya sanshi ne a dalilin mijin Ummu. Dan shiɗin ɗalibin mijin Ummu ɗinne acan saudia. To acan suka taɓa haɗuwa da Jay shi baba malam yaje miƙa gaisuwa ga malaminsa, shi ko Jay yaje  gaida Ummu ɗinsa ne da kuma yin Umrah shi da iyalansa.
       Tun a can suka ƙulla alaƙa. Bayan sun dawo Nigeria kuma Jay ya ringa zuwa ɗaukar karatu wajen baba malam ɗin a duk ranakun weekend lokacin suna a gari ɗaya.
      Har cikin gida baba malam ya kai Afrah. Inda ta samu ƙyaƙyƙyawar tarba a wajen Umm da Muhammad mai saurin sakin jiki da mutane. Cike da ƙwarewar aiki irin na Afrah data sha tun a cikin uwa da uba ta dinga jan Umm da hira akan hotunan Aymah data gani a falon. Umm kam tanada son yara. Gashi Afrah ta shigar mata rai lokaci ɗaya dan ta tuna mata da tata ɗiyar dake nesa da ita. Duk da kuwa Afrah zata girma Nu'aymah da kusan shekaru huɗu ma da wasu watanni, Afrah zatai shekaru ashin da biyu.
      A take Muhammad ya shiga bama Afrah labarin sister ɗinsa. Umm na tayasu da dariya dan sosai drama ɗin Aymah yake bama Afrah ɗin. Har ranta kuma taji kaɗayi dason ganinta.
       Lokacin da Baba malam ya shigo dan kiran Afrah da Jay ke jiran su wuce dan jirginsu ya kusa tashi sai Muhammad duk yay kalar tausayi. Umm ta haɗa mata kayan kwalliya da su kayan fulawa tanata saka mata albarka da godiya. Tare da roƙon ta dinga zuwa musu ziyara dan ita dai sosai yarinyar ta shigar mata zuciya................✍
       

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
[7/2, 2:08 PM] +234 808 711 8630: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No 68


_______________

INA MASOYA MA’ABOTA SON ‘KAAWATA KITCHENS DINSU DAMA DECORATION NA GIDAJEN SU? TOH KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA..._

_KAYA NE INGATTATU DA AKE KAWO MUKU SU TUN DAGA KASAR 🇩🇪 GERMANY..! KOWA YASAN GERMANY AKWAI KAYA MASU INGANCI, SEKA SHEKARA DA SHEKARU KANA AMFANI DA KAYAYYAKIN SU BASA LALACEWA. ANYI SU CIKIN TSANTSAR INGANCI DA KUMA RAHUSA... WADANNAN KAYA *MAAB LUXURY HOME* DAKE GERMANY TA KAWO MANA SU NIGERIA. RIGIJI GABJI FA KENAN.. BABU RUWAN KU DA WANI PRE-ORDER KO SHIPPING FEE, KAYAN *MAAB LUXURY HOME* SUNA NAN A KASAR MU NIGERIA, SAI DAI KAWAI KU HANZARTA KU GARZAYA KU BIYA KUDI KU KARBA..._

_MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME..._

_SUNE A KAN SAHUN GABA INDE WAJEN SIYAN KAYAN KITCHEN NE DA NA KAWATA GIDA, WATO A TURANCE KITCHEN UTENSIL’s& HOME DECOR..._

_INA UWARGIDA? AMARYA? YAMMATA DAKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI? ZAWARA MASU SHIGA DAGA CIKI? IYAYE MASU NEMAN INDA ZASU SAYAWA ‘YAYAN SU KAYAN GIDA? YAYYE MAZA, MIJIN MATAR SA😉? SAURAYI DAKE SON BURGE BUDURWAR SA WAJEN GWANGWAJE KYAUTA? TOH *MAAB LUXURY HOME* TA TANADAR MUKU DUKKANIN ABUBUWAN AMFANI NA KITCHEN, DANA KAWATA GIDA, YAITA WALWALI YANA HASKAKAWA.._

_AKWAI KAYAN KITCHEN MAI KAWATA KITCHEN, WANDA ZAI SA KISHIYA KWAFA, YASA DANGIN MIJI SU FARA HABA HABA DAKE, DUK INDA AKA SHIGO CIKIN GIDAN KI ASAN EH TABBAS KEMA KINA AMFANI DA KAYAN *MAAB LUXURY HOME*, KAYAN KAWAATA GIDAJE MASU HASKA KO’INA NA GIDAN KI, KAGA GIDA A NIGERIA AMMA TAMKAR A NAHIYAR ‘KETARE.._

_MAAB LUXURY HOME, TANA SAIDA KAYAYYAKI MASU INGANCI DA KYAWUN GASKE, AKWAI RAHUSA WANDA KOMAI KANKANTAR KUDI KANA IYA SIYAN WANI ABUN AWAJENTA, KAYANTA BA SAI MASU KUDI BA, KOWA YANA IYA GARZAYAWA YA SIYO NASA, ABUBUWAN DA YAWA, KAYAN DAGA CIKI AKWAI IRIN SU:_

_DINNER SETS, SERVING TRAYS, CUTLERY SETS, JUGS, FOOD FLAKS, THERMO FLASKS. DA SAURAN SU ABUBUWAN HOME DECOR._

_DOMIN NEMAN/TUNTUBAR KAYAYYAKIN *MAAB LUXURY HOME*, GA DETAILS DIN KAMAR HAKA: _

_INSTAGRAM: MaabLuxury home._
_WhatsApp number: +491521 4642007_
_Facebook: Maab Luxury Home_
_Adireshin su na yanar gizo: maabluxury.com_
_suna garin KANO. Amman suna tura kayayyakin su ko ina a fad’in nigeria. _

_KYAU, INGANCI, RAHUSA... SAI MAAB LUXURY HOME_

_______________

   No. 68

............Sun fito har ƙofar gida Muhammad biye da su zai mata rakkiya. Shima Jay ya jashi a jiki da kulawa. Anan ne yake tambayarsa miyyasa yaga yana fushi. Hawaye cike da idonsa yace, “Uncle Please ka bar mana Aunty anan ta zauna. Kaga Aunty N Uncle Yoohan ya gudu min da ita. sai ni kaɗaine a sashenmu. Ni kuma inason na dinga ganina da abokiya kamar Aunty N”.
      Cike da ƙaunar yaron Jay ya sumbaci kumatunsa yana ƴar dariya. Yace, “Oh woow sarkin wayo. inko hakane na maka alƙawarin Aunty Afrah zatazo maka hutu dan tana hutu dama yanzu haka”.
     Cike da ɗoki Muhammad yace, “Uncle yaushe?”.
     Yanda yayi ɗin har saida yasa baba malam da Afrah da Jay dariya. Jay yace, “Karka damu zaka iya ganinta a koda yaushe”.
      Duk da Muhammad yaso jin ranar da zatazo dai sai yayta ɗoki. ya koma cikin gida da gudu ya sanarma Umm.

     Bayan wucewar su Jay da kwana biyu Muhammad ya addabi su baba malam da zancen yaushe Aunty Afrah zata zo? Shifa idan bazatazoba to shi a kaisa gidansu yay hutu. Ganin ba hutu suka samuba shi sai baba malam ɗin ya kira jay da bukatar yaushe Afrah zata zo ɗin. dan sufa an saka musu zuma a baki kuma duk sun ƙagu. Hakan yama Jay daɗi, dan shirinsu na tafiya yanda ya kamata cikin rahamar ALLAH.
      Bai wani ja zancenba yace zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kawota da kansa insha ALLAHU. Wannan shine dalilin samun ƙofar shiga gidan su Nu'aymah da Afrah ta samu domin cika aikin ysyarta. Dan haka a safiyar yau kuma lahadi ta tashi da shirin tafiya can zatai zaman wata ɗaya rak insha ALLAHU.
     
      Sai karfe biyar na yamma Anuwar ya gama shirin kai Afrah kano gidansu Aymah. Dan haka bayan ya kammala shirinsa tsaf ya saka Al-hassan Ya kira masa ita a can sashen Uncle Anuwar. Dan ita acan take zaune kamar yanda little bee ma acan tai rayuwarta har tayi aure. Tsakaninta da sashen iyayenta sai dai tazo gaisuwa kawai ko hira. Amma ita Uncle Anuwar da aunty Nabeelah ne iyayenta. Sauran yaran kuma Miemaa da Abie.
      Tana zaune a falo hankalinta akan lap-top tana hidimarta Al-hassan ya shigo  da sallama. Kasancewar yayima Aunty Nabeelah laifi yau da safe. ta kuma tabbatar masa idan ta kamashi sai ta zanesa sai ya dogare a bakin ƙofar yana kalle-kalle. Daga can yace, “Aunty Afrah kizo Abie na kiranki”. Bai jira ko amsarta ba ya shilla waje da gudu saboda leƙowar aunty Nabeelah dake kitchen dan jin muryarsa da tayi.
     Aiko mi Afrah zatai inba dariya ba. Tace, “Mamma wlhy kin hana auta Sukunin shigowa sashen nan yau gaba ɗaya. Ɗazun ina kallonsa daya hangoki kin fita har faɗuwa yake wajen tiƙar gudu zai shige sashensu”.
     Dariya Nabeelah tayi itama da faɗin, “Ai ya gama gudunsa babu fashi saina ruɗa masa jiki da bulala tunda shi bayajin magana. Iskancin yaron nan baya tashi sai ya ga su Miemaa na gida. To in ALLAH ya yarda shi abin nema da tsokana ya samu a wajensa tunda yasan basa bari a taɓasa”.
      Miƙewa Afrah tai tana dariya da zura Slippers a ƙafarta. “A daiyi haƙuri Mamma na. Bara naje Abie na kirana inaga ya gama kimtsawa”.
      A take mood ɗin Nabeelah ya canja. Cike da damuwa tace, “Kai ni dai wannan aiki nasu Abie yana moremin, da ƙarfi da yaji ya maida kowa jami'insu a gidan nan, ALLAH banason kina nesa dani ko kaɗan. Amma yaya zanyi, nanda lokaci kaɗanma zaki gudu gidan aurenki ki barni da kewa ta haƙiƙa kamar yanda little taimin. 
      Ƙasa Afrah tayi da kanta kawai cike dajin kunaya. Sai dai bata iya cewa komaiba dai.
        Sallamarta Nabeelah tayi ta tafi dan tasan Jay jiranta yake. Ilai kuwa ta iskesu a falonsa shi da Miemaa suna jiranta. sai da tayi sallama suka bata izinin shiga sannan ta shiga. Bayan ta durƙusa ta gaishesu ne Jay ya nuna mata gabansa alamar ta zauna. Babu musu tazo jikin ƙafafunsa ta zauna cike da ladabi da ƙaunar iyayen nasu.
      Gyaran murya Jay yayi yana kallonta fuska babu wasa. Yace, “Afrah!”.
       “Na'am Abie”. 
Ta amsa masa kanta a ƙasa.
      Zamansa ya sake gyarawa sannan ya cigaba da faɗin, “Inason ki nutsu ki saurareni. Duk da bani da fargaba a kanki game da aikin nan tunda nasha sakaki inason sake jaddada miki muhimmancin na wannan lokaci. Kisa hankalinki da ƙyau dan banason kuskure a ciki. Baba malam yanada muhimmanci mai girma a gareni dake kanki. Inason kiyi komai da ƙwazo da hikima ok?”.
       “Insha ALLAHU Abie zanyi duk yanda kace. Kuma zan kula nayi komai yanda ake buƙata. Kudai tayani da addu'a”.
        “To Alhmdllh, addu'a kuwa dama akoda yaushe cikin yi muku ita muke. ALLAH ya baki nasara yay riƙo da hannunki kiyi komai cikin sauƙi. Wannan camaras ne”. Yay maganar yana miƙa mata wasu ƴan ƙananan dutsuna tamkar diamonds kusan goma. “Dasu zaki tafi, inason kibi duk sashen gidan ki maƙalasu a kowanne parlors. Idan sun wadata har Backyard na gidan dan suma wajene da masu baƙin hali zasu maƙale suyi magana. Ki ajiyesu da tsantsar kulawa yanda babu wanda zai gane minene. Duk da nasan koda a zahiri suke bawai ganewar zasuyiba inba dai ganinsu da yawa yasa suyi tunanin wani abun kuma daban ba. Inhar kika samu nasarar saka cctvs ɗin nan a ko ina na gidan to aikin zaizo da sauƙi insha ALLAHU. Dan zasu bamu damar kula da motsin kowa hankali kwance. Banason Little da Dawood susan komai kan camaras ɗin nan, wannan aikinane ni kaɗai zakimin.  Abu na biyu shine saka ido akan duk wani baƙo da zai shigo gidan. Ma'aikatan gidan da yaran gidan suma. Banda wauta da surutu mara amfani, duk da namasan waɗanan ba halayenki bane. Biyayya ga nagaba. Aiki basai ance tashi kiyiba tunda nasan iyayenki sun tsaya akanki babu abinda baki iyaba. Dan ALLAH ki kula da mutuncin kanki dan gidane family house akwai samari a ciki. Duk da har raina bana zargin rashin tarbiyya daga wannan zuri'ar koda a mafarkina. Amma dai dolene na jadada miki kame kanki da kuma kula da ibada dan na fahimci aikin zai kaiki har cikin azumi dake gabatomu”.
        “Inasha ALLAHU Abie zaka sameni mai kiyayewa”.
    “To ALLAH yay miki albarka da sauran ƴan uwanki baki ɗaya”.
      Amin ta amsa ita da Miemaa dake saurarensu. itama daga baya ta ɗora da nata nasihan da wasu dabarun aikin. Duk da kuwa tunda aka tsura maganar cikin koya mata take salo-salo harma Jay din kansa. To Alhmdllhi kuwa tana haddace komai. Dan dama itama bata wasan yara bace wajen tsayawa tsayin daka akan aikin nan da ba yau iyayenta suka fara tsundumata a ciki ba. 

        Anuwar da kansa ya kai Afrah ɗin Kano. Dan akwai harkar business ɗinsa da zaiyo acan. Koda jirgi ya diresu kuwa ana sallar magriba. Amma duk da haka sai ya fara kaita suka gaisa da baba malam yay sallar har isha'i acan sannan ya wuce nasa harkokin. Duk da baba malam ɗin yaso ya kwana anan amma fir ya ƙi saboda uzirinsa.
         Da ga Muhammad har Umm sunyi matuƙar jin daɗin zuwan Afrah. Dan gaba ɗaya saita ɗauke musu kewar Nu'aymah. Tun a daren Umm ta kaita sashen hajjo ta gaisheta. Nanma ta samu tarba sosai a wajen ƴar tsohuwar. Dan nutsuwar Afrah ɗin ya saka hajjo jinta a ranta. Taita tsokanarta kuwa tamkar yanda takema jikokinta idan taso. Afrah komai bata iya cewa sai murmushi. Dan miskilace ta gaske itama kamar little. Tama dama Jay da bily ɗin a miskilanci dan ta gada a uwa da uba da yaya. Idan kaji tana hira da dariya to Mammata ne (Nabeelah) ko Daddynta (Anuwar). Sai ko Miemaa da Abienta shima.
       Basu baro sashen hajjo ba sai lokacin kwanciya. Umm ta kaita ɗakin Aymah da aka gyara mata tsaf, kayantama tuni suna can. Sosai ɗakin yayma Afrah ƙyau. Taita kallon hotunan Nu'aymah da aka mammaƙala a bango. A hankali tace, ‘Masha ALLAH ƙyaƙyƙyawa da ita kuwa’.

_______________★★★

           *_U.S_*

   Sosai Nu'aymah batajin daɗi. Dan ma Juliet tsaye take sosai wajen kula da ita. Dan ta fahimci laulayin ciki takeyi. Sosai taji tausayin yarinyar ya kamata. Yaushema aka gama rainonta da za'ace itama ta samu ciki. Gaskiya tana mamakin ganganci irin na baƙar fata. Kasa haƙuri tayi sai da taima Omar wannan complain ɗin. Shiko yay dariya tare da mata faɗaɗɗen bayanin data gamsu, harta koma bin Nu'aymah da addu'ar fatan sauka lafiya.
              Duk da Aymah tanata ɓoyema kowa halin da take ciki na ciwon da ita ɗauka take Thypoid ɗinta ne ya motsa yau dai ta tonama kanta asiri batare data farga ba. Dan suna waya dasu Umm da Muhammad ya takura a kira a kirata ya sanar mata yayi sabuwar Aunty. Bayan sun gaisa da Afrah da Muhammad ɗin Umm ta amsa wayar suka gaisa itama. Cike da shagwaɓa Nu'aymah tace, “Umm Yah Yoohan yazo?”.
      “Oh dama ya shigo ƙasar?”.
“Eh Umm. Yaufa kwanansa uku”.
      “To Abbanki ya manta, ni koma maganar bamuyi da shi ba. Amma kinsan shi da uziri, nasan zaizo insha ALLAH”.
       “Umm idan yazo kiyi min yajin daddawa da farin yaji, da ɗan wake, da alawan madara, da iloka. Da fara. Da manja. Da aya suyan gishiri. Da.......”
       “Oh ni Firdausi wannan lissafin kumafa Nu'aymah?”.
       Baki ta tura gaba kamar tana gabanta. “Umm duk so nakeyi fa dan ALLAH”.
       Ɗan jimmm Umm tai na hasashe. Sai kuma tace, “Niko Nu'aymah ai period ɗinki ya dawo ko?”. Tai mata tambayar cike da salon bugar ciki irin na manya. 
      Zimbir Nu'aymah ta miƙe zaune. Dan ita kuwa man kanta ma ya tsiyaye tas ta shafa'a da zancen rashin ganin period. Ai idanma bata manta ba rabonta da jini tun na abinda ya faru. A randa ta fara jin alamun zuwansa kuma Accident ɗin nan ya faru suka wuce Austria. Daga nan bata saniba tayi ko batayi ba? Tunda bata cikin hayyacinta........
      “Kinajina kuwa Nu'aymah?”. Umm ta katse mata tunani. 
    Da ɗan rawan muryan shiga ruɗani tace, “Umm wlhy ni tun na lokacin nan ban sakeyiba. Na shiga uku Umm na kamu da wani ciwo ko?”.
      Dariya ce taso kufcema Umm, amma sai ta gimtse da sauri tana saurin faɗin, “A'a lafiyarki ƙalau. Inaga saboda kinyi wancan rashin lafiyarne shiyyasa. Zanma mijinki magana ya baki magani”.
     Cike da sanyin murya tace, “To Umm. Amma dan ALLAH ki haɗamin duk abinda nace idan Yah Yoohan zai taho yazomin da su. Harda garin dawa na tuwo fa Umm. Da daddawa da kuka da bushashshen kuɓewa dan ALLAH”.
         “To zan haɗa miki duka insha ALLAH. Amma kayan kamar zasu masa yawan ai Nu'aymah”. 
     “Ni dai Umm dan ALLAH ki taimakeni. Wlhy duk banason abincin garin nan yanzu. Coffee kawai nake iya sha sai gasashen kofi. Amma sauran abincin da naci sai nayi amai. Abincin Austria yafi na nan min daɗi”.
       Umm dai na murmushi ta amsa mata. Daga haka sukayi sallama dan Juliet jiranta suke zasu fita shagon shan coffee ɗin na ƙa'ida. Itama taɗan motsa jiki daga can.

____________★★★

         Tunda ya kawosa hotel ɗn ko sau ɗaya bai tambayesa miya fruba. Shi kuma baice dashi komaiba dan ransa a ƙololuwar ɓace yake. Yadda Al-qur'anin nan yafi komai zafafa masa zuciya. Dan har yanzu fushinsa yaƙi sauka. Daya rufe ido dan yai barci sai ya hango Qur'an a ƙasa a yashe. Daga ƙarshe dai har dasu yin hawaye.
      Sanin halinsa idan yay fushine ya saka Omar yanke shawaran kiran Nu'aymah. Juliet ya turama text message dan taja ra'ayinta.
       A lokacin basuyi ko mintuna biyar da shigowa gidan ba. Aymah na kwance a falon saman tiles idonta a rufe. Sai dai ba barci takeba. Hasalima tunanin Yoohan takeyi dan rabon da suyi waya tun jiya da yace mata zai koma Abuja daga kd....
      Gyaran muryar da Juliet tayine ya saka Aymah buɗe ido tana kallonta. Juliet ta ɗaga mata gira ɗaya tana murmushi, yayinda duk hannayenta ke akan cikinta tana shafawa. “Da zaman tunani ai gara kiyi kiransa” tai maganar cike da tsokana. Murmushi Nu'aymah tayi da gyara kwanciyarta tana fuskantar Juliet ɗin. “Ke dai faɗa mana gaskiya. Ko kina kewar Yah Umar ne ni zaki nanamin?”. Kusan a tare suka kwashe da dariya. Juliet ta miƙe tana faɗin, “1-1 kenan. Ni bara naɗan watsa ruwa na kwanta”.
        Juliet na shigewa Aymah ta sauke numfashi. Cike da son jin muryarsa kuwa ta lalubo hotonsa a wayarta tana kallo. Kamar kuma an tsikareta sai kawai tai kiransa. Shigowar kiran Aymah yayi dai-dai da sake sakkowar hawayen Yoohan. Dan ji yake kamar zuciyarsa zata ƙone. Sam dukan da yayma Gebrail ɗin bai wadacesaba....
     Kamar bazai kula wayar ba sai kuma ya buɗe idanu a hankali. *_My Sweet girl_* daya ganine ya sakashi ɗauka a kasalance. A kunne kawai yasa batare da yayi magana ba. Daga can Aymah ta sauke sassanyan numfashi. Sai dai itama batayi maganarba. Sun share kusa sakan goma sannan ta ƙara sauke numfashi da faɗin, “My boo yau miskilawan ne a kusa?”. Shiru baiyi maganaba. Hakan yasata fahimtar akwai damuwa. Dan a ɗan zamansu ta fara fahimtar wasu da yawa halayensa. Musamman fushinsa da farin cikinsa. Kwanciya ta gyara tana lumshe idanu. Cike da nutsuwar data ɗan farayi na wahalar ciwo tace, “Waya taɓa ɗan lelen Abba ne? To lallai ya nema wajen ɓuya tun kafin na kira Abba na sanar masa ɗan lelensa na fushi da kowa har Silly girl ɗinsa”.
       A bazata murmushi ya ɗan kufce masa. Sai dai idanba lura kayi ba bazaka taɓa fahimtar yayinba. A hankali yace, “Parrot, ke dai bakison barin bakin mutane ya zauna shiru”.
     Baki ta kumbura cike da sakalci tace, “Ai yanzu parrots ɗin biyu ne. Dan kaima ALLAH ka shigo tawaga Yah Yoohan”.
     “Silly girl”.
Ya faɗa yana gyara kwanciyarsa.
      Murmushi tayi mai faɗi tana lumshe idanu. Sai kuma ta dai-daita muryarta, cikin nutsuwar da inta gadama zaka sameta da ita tace, “I'm so sorry My Handsome. Nifa kaga idan aka bani haushi a gidanmu mi nakeyi da?”.
       Yace, “Uhm-uhm”.
Sake gyara kwanciyarta tayi tace, “Sai in ɗauki Al-qur'ani naita karatu. Zakaga inata kuka a farko, kafin wani lokacin kuma sai na samu nutsuwa na cigaba da karatun da nishaɗi. Cikin amincin ALLAH bana ajiye Qur'anin nan sai zuciyata tamin sanyi”.
      Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Murya da matuƙar sanyi yace, “Zeeynab I love you. Ke ta dabance a rayuwata”.
      Murmushi tayi kawai. Kafin a hankali tace, “Thanks you Uncle Boo”.
     Kansa ya jinjina mata a hankali. Sai kuma ya yanke wayar batare da yace mata komaiba. Omar dake gefe yana jinsa sai dariya yake dannewa. Batare da Yoohan ya kallesa ba yace, “Umar Al-qur'ani”.
      “Okay bara na kawo maka a mota”.

  Cikin mintuna ƙalilan Omar ya dawo masa da Qur'ani. Tashi yayi yayo alwala ya dawo ya zauna. Cike da bin shawarar Aymah ya fara karatu. UBANGIJI mai Rahma mai jin ƙai sai ga Yoohan ya sami nutsuwa cikin lokaci ƙanƙani. jiyay tsoron ALLAH ya ƙara ratsashi. Ya shiga jeramasa kirari da godiya bisa koyarwar Nu'aymah.
      Umar ma yaji daɗin ganinsa ya dai-daita a lokaci ƙan-ƙani, dan haka yaje ya samo masa abinci har suka ɗan zauna suka tattauna akan abinda ya farun. Omar yaji a ransa ba Gebrail bane ya shiga ɗakin Aymah. Ya taka sawun ɓarawone kawai da kuma zafinsa da Yoohan ɗin yakeji dama. amma sai yay shiru baice komaiba. Dan yafi buƙatar Yoohan ya fahimci wanene mahaifinsa da kansa.

______________★★

          A gidan su Yoohan kuwa uffan papa baiceba game da dukan Gebrail da aka kai asibiti a sume da Yoohan ɗin yayi. Su Uncle Mike ne ma keta faɗa da son jin miya kawo rikicin? Sai dai amsa ɗaya suke samu. Shine kowa bai saniba. Dan iya abinda idanunsu ya gani kawai suke faɗa jama'ar gidan.
     Har zuwa lokacin da labarin farfaɗowar Gebrail ɗin yazo kunnensu papa dai yaƙi yace uffan. Sai da daddare bayan sunje sun duba shi a asibiti bisa tursasawar mama debora da maman madam Chioma da yau sukaci masifa har bakunansu sukai tsaho. Bayan barowar tasu asibiti ne papa ya kira Baba malam da shi har yanzu ma baisan Yoohan na ƙasar ba. Dan sunata shirye-shiryen bikin sauka da auren yaransu na gidan marayu nanda bayan salla babba. Yayi Busy da yawa. Rabonsa dayin waya da Yoohan tun yana Oman.
      Yasha mamakin ganin kiran papan. Amma sai ya ɗaga yana ambaton sunan ALLAH. Baiyi sallama ba, sai cewa da yay, “Barka da dare Pastor Goshpower. Yau kaine ka tuna da Soorajidden bin Hashim?”.
      Wani wawan tsaki papa ya sauke a jere. Batare da jiran cewar baba malam ba ya fara zazzaga masifa. “Kai ɗin banza da zan ɗauki waya na kiraka. Gargaɗi na kira na maka a karo na farko kuma na ƙarshe. Ka rikitamin yaro gaba ɗaya ya fita hayyacinsa. Sai yanzu na gama fahimtar manufarka akan ɗana. So kake ka maida minshi ɗan ta'adda shiyyasa ka aura masa wannan shegiyar ƴar taka mai zuciyar dutse? To wlhy Sheikh Sooraj kafin kaga bayana nine zanga bayanka. Sanna kayi gaggawar sakarmin kurwar yaro. Ka kuma saka ya maido maka ƴarka gida tun kafin lokaci ya ƙure maka. Idan ba hakaba na rantse saina halakata da hannuna kafin kaima na halakaka...”
     Kafin baba malam yace wani abu papa ya yanke wayar. Nannauyar ajiyar zuya baba malam ya sauke kawai yana girgiza kansa. a gaba ɗaya kalaman papa babu wanda ya bashi tsoro. Abinda ya fahimta kawai shine cikin fushi yake. Duk da kuwa yasan papan zai iya aikata duk abinda ya lissafa masa. Abinda kawai ya sakashi a ruɗani shine, ‘Miya faru?’. 
      Ganin bashi da mai bashi amsa sai kawai ya ajiye tunanin ya cigaba da harkar gabansa.

__________★

       Yoohan ko takan gidansu bai sake biba. ya dai saka Omar zuwa da mai saka keys ya sabunta duk keys ɗin dake a sashensa. Da yake lokacin duk ƴan gidan sun fita, su mama debora kuma na wajen Gebrail sai babu wanda yasan mi akayi. Solomon dai yaso shiga ya duba sai dai fitowar Omar yay masa katanga da hakan. Dan yana kai mai saka keys ɗin shi fitowa yay dan ya hana su Solomon ɗin kowacce damar sanin abinda ya farun. Sosai ya jima da fahimtar wanene Solomon dama. Labarin korosa da Aymah tasa akayi kuma da Yoohan ya bashi ne ya sake tabbatar masa akwai wata a ƙasa. Sai dai komai sake ɗaure kansa yakeyi shikam. Dan baiga miye dalilin aikata abu a sarƙaƙe da su papan keyiba game da Yoohan ba.

           Shiri yay tsaf domin shiga Kano. yanason daga Kano Lagos zai nufa. Yay kwana uku su juya U.S shi da Omar.
     Misalin huɗu kuwa Yoohan da Omar suka iso anguwar su Nu'aymah. Kasancewar anata hada-hadar shiga salla sai kawai suma sukai alwala suka shiga. Bayan an idar sun fito Yoohan yaketa faman jan ƙananun tsaki saboda kallon damutane suketa musu. Duk da yasan wasu a cikinsu sunriga da sun sanshi zuwa yanzun. Amma duk sanda zaizo basa iya daina binsa da kallo kamar wani baƙo. Ya rasa mi suke kallone wai? Gashi shi kuma ya mugu-mugun tsanar a sakamasa ido.
      Umar daya san dokar dai yanata murmushi. Dan ya tabbatar kallon ne ya bama Yoohan ɗin haushi. Bai dai ce komaiba har suka sami iso daga baba malam ta hanyar malam ƙarami daya fito ya gansu. Sakawa yay malam ƙarami shiga dasu cikin gida, shi kuma ya nema alfarmar ɗalibansa shima yabi bayansu. Sashen hajjo aka kaisu. Dan mutuniyar Yoohan ce yanzu sosai. Danma bajin zancen juna sukeba sai da tafinta. Amma a wannan karon hajjo ta fahimci Yoohan ya fara jin hausa kaɗan-kaɗan. Takoji daɗi, duk da harshen nasa a karye yake. Wani abunma koya faɗa bata ganewa.
      Sosai aka cika musu gaba da kayan ciye-ciye. Shi dai Omar nasa kallo ne da tayasu dariya. Dan yau ne karan farko daya shigo gidan. Anan baba malam ya samesu kuwa. Suka gaishesa da tsantsar girmamawa. yayinda shima da kulawa yake amsa musu da tambayar iyali. Da ga haka suka ɗan zauna hira. Anan hajjo kejin Omar ma abokin Yoohan ɗinne, kuma ya muslinta. Daɗi sosai ya sake kama Hajjo. Lallai tarkonsu ya kama kurciya. Dan ga nasasorin auren Yoohan da ɗiyarsu nan sun fara bayyana.
      Daga Sashen Hajjo baba malam ya shiga da su dan su gaida Umm. Yasan dai ganin Yoohan ɗin zaisa taji sanyi a ranta da raguwar kewar Nu'aymah. Aiko hasashen baba malam ɗin yayi dai-dai. Dan sosai Umm taji ɗunbin daɗi, duk da kuwa akwai ƴar kunya a tsakaninsu. Dan daga ita har shi babu wanda ya iya saka idon juna. Da yake sun iske Addah a sashen itama suka gaisheta. Ta amsa musu da kulawa tanata tambayar ɗiyarta Nu'aymah.
      Suna ɗan hira da Addah ne, wadda ta kasance duk akan Nu'aymah Afrah da Muhammad da suka dawo daga islamiyya suka shig falon da sallama. Kallonta duk su Yoohan sukayi. Itama fuska ɗauke da nuna rashin sani a garesu, dan miskilace ta gaske, ga salon aiki. ta shiga gaidasu tana ƙoƙarin wucewa ɗakin Aymah daya zama nata yanzu batare ta nuna alama tama taɓa ganin mai kama dasu ba a rayuwa. Su dai da kallo kawai suka bita. Yayinda Yoohan ya miƙama Muhammad hannu alamar yazo garesa.
       Muhammad akwai wayo, dan haka tsaf ya gane Yoohan. Hannu ya bashi sukai musabaha. Yoohan ya shafa kansa yana murmushi, yace, “Oh my dear Friend ka ƙara girma fa”. Cike da jin daɗi Muhammad ya zauna kusa da shi yace, “Thanks Uncle. Ina Aunty N ɗina?” Yay maganar yana waige-waigen neman Nu'aymah.
           Murmushi Yoohan yayi yana ɗan rungumo Muhammad ɗin jikinsa. Yayinda Omar ke bashi amsa yana dariya. “Ta maka wayo tana U.S abinta”. Da ƴar damuwa Muhammad yace, “To Uncle yaushe zatazo itama?”. 
       Yoohan yace, “Soon insha ALLAH Darling. Amma karka damu idan kunyi hutu zan kaika ka ganta”.
     Daɗi sosai ya kama Muhammad, nafa ya shiga tsallen murna su Addah na masa dariya.
       
      Sai bayan isha'i su Yoohan suka bar gidan da kayan Nu'aymah ghana must go guda. Baba malam baicema Yoohan komaiba game da wayar da sukayi da papa. ya da masa nasiha cikin hikima shi da Omar ɗin akan muhimmanci iyaye. Ta hakane Yoohan ya ɗan tsargi akwai abinda ya faru kenan. Amma sai shima baice komaiba. 
        Ƙarfe goma na dare suka wuce Lagos. Inda zasu kwana uku yay aikin daya kawosa 9ja ɗin.

★★★

       Tunda suka shigo lagos Yoohan bai samu kansa ba. Aiki yake tuƙuru tamkar yanda ya saba hidima ga al'umma. Ya ɗanyi wasu ziyarce-ziyarce dake ransa. Batare daya sake bi takan su papa ba suka wuce U.S shi da Umar.

  *_U.S_*

        Kasancewar su Nu'aymah sunsan da dawowar mazajen nasu a ranar da safe Juliet ta maida Nu'aymah gidanta. Yaɗanyi ƙura kaɗan kuwa saboda rashin mutane. Dan haka Juliet ta taimaka mata suka gyara duk da Aymah na hanata. To itama dai ƙarfin haline dan a jigace take komai. Bayan sun kammala Juliet tai mata sallama ta koma nata gidan. 
      Cike da ƙarfin hali Aymah taima Yoohan girki. Da ƙyar kuwa ta kammala tai wanka. Batare da tabi takan wani kwalliya ba tai shiri cikin Bomshort jeans bleu da pink top kawai tazo falo ta kwanta a ƙasan tiles kamar yanda takeyi a yanzun. Duk da kuwa da farko taci alwashin masa kwalliyar tarba amma hakan ya gagareta. Cike da rashin jin daɗin jiki kuwa barci yay awon gaba da ita a wajen. Ga zazzaɓi mai zafi daya fara saukar mata na yamma.
        A ƙagare Yoohan yake da son ganinta. Hakan yasa yaƙi yarda su hau cab ɗaya shi da Omar. Duk da kuwa kusan anguwa ɗaya suke. Sai ma an fara sauke Omar ɗin a gida kafin a ƙaraso nasu.
        Tsabar zumuɗi a barandar gidan yabar kayan da yazo dasu ya shige ciki. Sassanyan ƙamshin daya doki masa hancine ya sakashi lumshe idanu. Kafin ya buɗesu a hankali kan Aymah dake kwance a ƙasan tiles barcin wahala yay gaba da ita. Kallonta yake da matsanancin shauƙi da kewa. Ya taka a hankali zuwa inda take. Tsugunnawa yay a gabanta ya ɗaura tattausan hannunsa saman fuskarta dake shining na masu ciki ya shafa yana sauke ajiyar zuciya. Ko motsi batayiba kuwa. Sai ma numfashi da take saukewa a hankali. Zamewa yay ya zauna. ganin baya ganinta da ƙyau sai kawai ya kwanta shima ya ɗora kansa saman filon datake kwance yana kallonta da ƙyau. Sai dai kwanciyar tasu ta kasance tamkar kai da ƙafa bawai a jere ba. Hakan yasa goshinsa na saitin haɓarta ne. Itama nata goshin na saitin tasa haɓar. Yanda take busa masa numfashinne shima yana busa mata nasa ya sakashi sauke ajiyar zuciya idonsa ƙyam akan ɗan bakin tsiwarta. Matsar da kansa yayi a hankali ya daidaita bakinsu. Tare da ɗora hannunsa ya ringumo kanta jikinsa ya fara kissing nata cike da zalama da kewa.
       Cikin barci Nu'aymah taji salon da duk duniya na mutum ɗaya ne a gareta. Batare data buɗe idanuntaba cikin kasala itama takai hannu bisa kansa ta ringumosa tana mai bashi haɗin kai yanda tasan yana buƙata. Sunfi minti shida a haka sannan ya barta yana sauke numfashi da sauri-sauri. Dan harga ALLAH harya hau network.
      Shanyayun idanunta ta buɗe a hankali tana kallonsa. Dan har yanzu yana akan filon bai tashi ba. Murmushi yay mata mai sanyi, ya maida hannunsa akan fuskarta suna kallon juna cikin ido. 
    “Welcome my boo”.
Tai maganar a hankali kamar mai tsoron ajisu. 
     Lumshe idanunsa yayi ya sake buɗewa a kanta. Cikin ɗan sake matsar da kansa jikin fuskarta yace, “Sweet girl mike damunki?”. 
     Maimakon ta bashi amsa sai hawaye shar. Saurin tashi yayi zaune har jikinsa na rawa..........✍
       

ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.*_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 69


______________

INA MASOYA MA’ABOTA SON ‘KAAWATA KITCHENS DINSU DAMA DECORATION NA GIDAJEN SU? TOH KU MATSO, DOMIN NESA TAZO KUSA..._

_KAYA NE INGATTATU DA AKE KAWO MUKU SU TUN DAGA KASAR 🇩🇪 GERMANY..! KOWA YASAN GERMANY AKWAI KAYA MASU INGANCI, SEKA SHEKARA DA SHEKARU KANA AMFANI DA KAYAYYAKIN SU BASA LALACEWA. ANYI SU CIKIN TSANTSAR INGANCI DA KUMA RAHUSA... WADANNAN KAYA *MAAB LUXURY HOME* DAKE GERMANY TA KAWO MANA SU NIGERIA. RIGIJI GABJI FA KENAN.. BABU RUWAN KU DA WANI PRE-ORDER KO SHIPPING FEE, KAYAN *MAAB LUXURY HOME* SUNA NAN A KASAR MU NIGERIA, SAI DAI KAWAI KU HANZARTA KU GARZAYA KU BIYA KUDI KU KARBA..._

_MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME, MAAB LUXURY HOME..._

_SUNE A KAN SAHUN GABA INDE WAJEN SIYAN KAYAN KITCHEN NE DA NA KAWATA GIDA, WATO A TURANCE KITCHEN UTENSIL’s& HOME DECOR..._

_INA UWARGIDA? AMARYA? YAMMATA DAKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI? ZAWARA MASU SHIGA DAGA CIKI? IYAYE MASU NEMAN INDA ZASU SAYAWA ‘YAYAN SU KAYAN GIDA? YAYYE MAZA, MIJIN MATAR SA😉? SAURAYI DAKE SON BURGE BUDURWAR SA WAJEN GWANGWAJE KYAUTA? TOH *MAAB LUXURY HOME* TA TANADAR MUKU DUKKANIN ABUBUWAN AMFANI NA KITCHEN, DANA KAWATA GIDA, YAITA WALWALI YANA HASKAKAWA.._

_AKWAI KAYAN KITCHEN MAI KAWATA KITCHEN, WANDA ZAI SA KISHIYA KWAFA, YASA DANGIN MIJI SU FARA HABA HABA DAKE, DUK INDA AKA SHIGO CIKIN GIDAN KI ASAN EH TABBAS KEMA KINA AMFANI DA KAYAN *MAAB LUXURY HOME*, KAYAN KAWAATA GIDAJE MASU HASKA KO’INA NA GIDAN KI, KAGA GIDA A NIGERIA AMMA TAMKAR A NAHIYAR ‘KETARE.._

_MAAB LUXURY HOME, TANA SAIDA KAYAYYAKI MASU INGANCI DA KYAWUN GASKE, AKWAI RAHUSA WANDA KOMAI KANKANTAR KUDI KANA IYA SIYAN WANI ABUN AWAJENTA, KAYANTA BA SAI MASU KUDI BA, KOWA YANA IYA GARZAYAWA YA SIYO NASA, ABUBUWAN DA YAWA, KAYAN DAGA CIKI AKWAI IRIN SU:_

_DINNER SETS, SERVING TRAYS, CUTLERY SETS, JUGS, FOOD FLAKS, THERMO FLASKS. DA SAURAN SU ABUBUWAN HOME DECOR._

_DOMIN NEMAN/TUNTUBAR KAYAYYAKIN *MAAB LUXURY HOME*, GA DETAILS DIN KAMAR HAKA: _

_INSTAGRAM: MaabLuxury home._
_WhatsApp number: +491521 4642007_
_Facebook: Maab Luxury Home_
_Adireshin su na yanar gizo: maabluxury.com_
_suna garin KANO. Amman suna tura kayayyakin su ko ina a fad’in nigeria. _

_KYAU, INGANCI, RAHUSA... SAI MAAB LUXURY HOME_

______________

     No. 69

............“Oh God baby”. Ya faɗa da kamota ya tayar zaune. Sakata yayi cikin jikinsa ya rungumeta. A tare suka sauke ajiyar zuciya kowa kewar ɗan uwansa na ratsashi. 
         Sake lafewa tai a jikin nasa tana mai shaƙar ƙamshinsa da ke mata daɗi sosai. Yayinda shi kuma ɗumin jikinta ke ratsashi, tare da tausayinta har ƙasan zuciyarsa. Harga ALLAH yana matuƙar son yara. Musamman a yanzu da yayi aure. Badan hakaba daya cire mata cikin nan dan tayi ƙanƙanta yake gani. Duk da kuwa shi likitane daya zaga cikin duniya. Yayi gamo da mutane iri-iri harma waɗanda basu kaita a shekaruba ya gansu da cikin kuma sun haihu lafiya.
      Jin tana neman fara barci ya shafa mata fuska. Idanun ta buɗe a hankali da ɗagowa ta kallesa. Sai kuma ta bi jikinsa da kallon mamaki. Sanye yake cikin wata ɗanyar shadda ash color mai duhu. Tasha ɗinkin da yay dai-dai da samarin wannan zamanin. Hardasu hula ƙube. A bazata murmushi ya suɓuce mata. Ta sake kwantawa a jikinsa da zagayesa da hannayenta tana murmushi.
      “Hausa man”. Ta faɗa cike da shauƙi. 
      Murmushi yayi mai faɗi ganin taji daɗin ganinsa da shigar yarenta. Ya miƙe ɗauke da ita yana ƴar dariya da faɗin, “Hausa man mijin hausa girl”. Dariya suka ƙyalƙyale da shi a tare, dan yanda yay maganar dole ya baka dariya. Ta kai hannu kan tattausan sajensa dai-dai yana zama da ita a kujerar. Tace, “Mun haɗu fa da yawa. Dan irinmu a tarihi kaɗanne”.
       Murmushi ya sakeyi mai faɗi yana lumshe ido da buɗewa a kanta. Zai bata amsa kira ya shigo wayarsa. Karkatawa yay kaɗan ya ciro wayar a aljihun gefensa. Hakanne ya bama Aymah damar sauka dan ta tuna ko ruwa bata bashi ba. Da kallo ya bita yana sauke wani nannauyan numfashi da har ya kai Osin jinsa da ga can.
           Cikin son ƙarfafa kanta ta haɗa masa ruwa da kofi a ƙaramin tire. Duk da ta fahimci bai cika damuwa da kayan lemo-lemon nan ba ta ɗauka masa shima. Falon ta dawo inda ta barsa har yanzu yana waya. Ta ajiye tiren a table taɗan kallesa. Shima idanunsa ƙyam akanta. Lemo ta fara nuna masa, ya girgiza mata kai alamar a'a. Hakan yasa ta buɗe ruwa. Koda ta miƙo masa sai ya haɗa da hannunta ya maidata saman cinyarsa. Jin numfashin daya furzar ya saka Osin faɗin, “Mr X anya kuwa kana cikin nutsuwarka?. Nikam sai anjima. Ina magana kanata min uhm, ah, a'a”.
     Murmushi Yoohan yayi mai sanyi yana kai hancinsa bisa dokin wuyan Nu'aymah. Osin bai jira amsarsa ba ya yanke wayar cike da jin haushi dan magana dama yake masa akan su papa. Shi kuma harga ALLAH Yoohan hankalinsa gaba ɗaya Aymah ta tattareshi kojin Osin ɗinma bayayi da ƙyau. 
       “Yah Yoohan zakasa na jiƙamu fa”. Ta faɗa cike da shagwaɓa”. Tai maganar tana ɗan ture masa kai Jin yana neman ruɗar mata da jiki. Bai iya cemata komaiba. Dan a kallo ɗaya zaka fahimci ta gama narkar da shi. Ya kamo hannunta da ruwan ke ciki ya kai bakinsa kozai samu sassauci. Dama gashi ƙishin yakeji. Tas kuwa ya shanye shi. 
      “A ƙaro?”.
   Kai ya girgiza mata da lumshe idanu yana jingina kansa da kujera. 
       Gaba ɗaya ƙoƙarin Nu'aymah neman gazawa yakeyi, cike da son danne halin da take ciki tace, “Muje kayi wanka ga abinci ma”.
         Idanun ya buɗe ya zuba mata su. Dan ya fahimci tanayin komai da ƙarfin haline. Yanzu haka har cikin jikinsa jin zafin nata jikin ya keyi. Baice komaiba ya kamata ya miƙar yana faɗin, “Fara bani abincin naci yu nwa nakeji”.
       
       Koda suka zauna a dining ɗin duk sai taji batason ganin abincin kuma duk da itace ta girkashi. Fahimtar hakan da Yoohan yayi ya sashi cemata taje ta kwanta zai zuba. Da sauri kuwa tabar wajen. Binta yay da kallon tausayi, tana ƙoƙarin kwanciya a ƙasa yay saurin faɗin, “No ba ƙasaba. Koma saman kujera ko kije ɗaki”.
     Sosai ta ɓata fuska zatai kuka. “Please Yah Yoohan, wlhy banason ko ina sai nan. Yafi min daɗi”.
      “Bazai yuwuba Sweet girl, wannan sanyin illane a gareku ai. Indai kika kwanta a wajen nan tofa na fasa baki maganin zazzaɓi kawai zan haɗa da allura....”
      Kafinma ya rufe baki ta haye saman kujera tana hawaye. Murmushi ya ɗanyi ganin yanda ta kwanta da juya masa baya. Bai sake yin maganaba ya hau cin abincinsa yana yabama ƙoƙarin ta, dan shikam yanzu ya sallama mata akan iya girki kuma. 
        Juye-juye Aymah ta dingayi a kujerar tana ƙunƙunin, sam kwanciyar batai mata daɗi ba, ita tafi son ƙasan saboda sanyin tiles. Yoohan dai na kallonta amma baice komaiba. Sai da ya kammala cin abincinsa hankali kwance sannan ya miƙe. Dan yama tuna kaya na waje. Zuwa yay ya shigo da su duka. Duk da Nu'aymah na jinsa bata juyo ta kallesaba. Cike take da haushin an hanata kwanciya a ƙasa. Babban akwatin kayanta da yazo da shi ya kai ciki, ghana must go ɗin kuwa ya barta anan falon dan baisan mine a ciki ba. Amma yanda yakeji ƙamshi-ƙamshin abubuwa yasan dai ba kaya bane. sannan akwai nauyi ma.
     Cak ya ɗauki Aymah daga kujerar ya nufi bedroom da ita. Ƙin motsawa tai, sai ma fuska data kumbure na fushi. Shi dai baice komaiba ya kwantar da ita a gado yana sumbatar goshinta. Daga haka ya cire kayansa ya wuce toilet yin wanka.
      Koda ya fito ya sameta a gadon bata sauka ba yaji daɗi. Dan baiyi zaton zata haƙura ba. Boxer kawai ya saka ya haye gadon, yanason yaɗan huta daga uwar gajiyar daya kwaso a sati biyun nan.. Sai yanzu ne ya fahinci ashe barci ƴar rigimar tasa tayi, yay murmushi mai ƙayatarwa da sumbatar laɓɓanta da idanu. ‘My Trouble maker an kusa zama mah-mah’ yay maganar yana ɗaga rigarta da ƙara faɗaɗa murmushinsa. Sunkuyawa yay ya sumbaci cikin da babu alamar akwai wata hallita a ciki. Sannan ya fara magana tamkar jinsa ya keyi, “Little boss how are you?. ALLAH ya kareki. ya fiddoki duniya lafiya, yasa kizam mahaddaciyar Al-qur'ani kaman Mie-mien ki. Ki kumayo kamanninta”. ya ƙarasa faɗa da ɗaga kai yana kallon fuskar Aymah dake barci batasan yanayi ba. Kwanciyarsa ya gyara da rungumeta. Kamar kuwa jira take sai ta sake lafewa dan sanyin jikinsa.

        Barci sukasha sosai. Sai dai Alhmdllh lokacin da suka tashi zazzaɓin Aymah ya sauka. Tare sukayi wanka bayan Yoohan ya mata gwajin fitsarin da batasan na minene ba. Tsabar wauta kuma bata tsaya tambayarsaba. Ta zata dai ko complain ɗin maganar rashin ganin jinin da sukayi da Umm ne ta sanar masa tunda shi Doctor ne. (Umm ba irinki bace madam😬). 
     Ta rigashi fitowa. Dan sai da ya jira result sannan ya fito. Duk da ya jima da zargin ɗan tayinsa hakan bai hanashi farin cikiba. Ya ɗagata yanata juyi da ita. Tun tana tambayarsa lafiya harta koma tuntsura dariya kamar yanda yakeyi. Da ƙyar ta samu ya sauketa a godo suna faman hakki.
     Yasha murnarsa batare da Aymah tasan dalilinta ba. Dan ya ƙi sanar mata. Acewarsa ba yanzunba. Duk da taso tajin saita share kawai. Musamman da ganin ɗinkinan daya yo mata cike da akwati. Lesss, shadda, atamfa. Dan a cewarsa yana son ganinta a kayan hausawa sosai. Tayi mamakin ganin ɗinkin dai-dai jikinta kuma. Koda ta tambayesa yaya akai yasan seize ɗinta haka? Sai cewa yayi abun sirri ne. Ta fahimci yau jan rai yake mata akan magana. Nanma sai ta share ta shiga jera masa godiya da addu'oi.
      Ya ce shifa tabar masa godiya dan akwaima lefenta a kansa wanda baiyiba. Aymah dake dariya tace, “Ai gashi anan kayi my boo”.
     Hancinta ya lakace da faɗin, “No. Wancan special ne hausa girl. taso muje kiga saƙon Umm”.    

       Tunda Aymah taga duk abinda tacema Umm an haɗo mata shi saita haukace da murna har Yoohan na mata dariya. Ta tasa fara gaba ta hau ci harta bashi tausayi. Dan yayi-yayi taci abinci taƙi, tace sai dai suje shagon shan coffee. Haka dole bayan ta gama cin farar da shan su alawar madara ya ɗauketa sukaje shan coffee ɗin. Tako shawosa bana wasaba harda guzirin na anjima. Shi dai gaba ɗaya sai take bashi tausayi, dan yasan da bata shan coffee.
        
       Haka su Nu'aymah suka cigaba da kasancewa suna rainon ɗan tayin cikinsu ita da mijinta abin sonta. Duk da yaƙi faɗa mata gaskiyar zancen cikin, a yanzu bata da abinci sai kayan da Umm ta aiko mata da su. Randa tayi tuwon dawa miyar kuka ta tsare Yoohan wai sai yaci. Dan itama ai taci abincin yarensa lokacin da aka kaita gidansu. Shiru kawai yayi yana kallonta idanu na farfar dan shikam dai harga ALLAH miyar kukar har saka masa tsigar jiki tashi take. Garama tuwon yana masa kallon amalan yoroba. Dan yana ɗanci a dalilin joseph data zama abincin yarensane. Ganin yanda yakeyine ya saka Aymah yin fushi. Marairaice mata yayi akan tayi haƙuri shi wlhy bai iya ci ba. Batama nuna taji miya faɗa ba.
     Ganin da gaske fa fushin ta ɗauka ya tilasta masa daurewa ya rintse ido ya matsa kusa da ita. Muryarsa har sarƙewa take wajen faɗin, “To kawo zanci Sweet girl. Shiru ta kuma masa tana cin abinta cike dajin daɗi harda lumshe ido, gashi ya sha yajin daddawa da man shanu kuwa sai ƙamshi yake. Sake marairaice mata yayi cike da lallashi.
      “Nace zanci ai ko. Tunda Unborn ɗina yanaci nima a bani zanci, yi haƙuri”.
       “Sai dai na baka da hannuna, dan karma kaita zubashi a riga ban saniba daga baya kaje ka zubar”. 
    Ta bashi dariya, amma sai ya gimtse dan ya kula itafa da iya gaskiyarta take maganarta. Yace, “To na yarda”. 
      Laumar farko dai Yoohan sai da ya riƙe numfashin sa sannan ya korata da ruwa batare da ya tauna ba. Lauma ta biyuma haka. Ana uku ƴar rigimarsa ta tubure bata yarda ba. Yoohan dai kam yaga takansa. dan rigimar Nu'aymah dabance a rayuwa. Dole-dole kuwa sai da ya tauna lauma ta ukun nan. Daga haka yace. Dan ALLAH tayi haƙuri ta barsa haka tunda koya yakeyi. Dariyar mugunta taita masa kuwa.
       Tun daga ranar daya fahimci zatayi tuwo sai ya gudu. Idan kuma ya fita asibiti sai ya bigi cikinta yaji mitaci ko zataci. da yaji batun tuwo sai yaki dawowa da wuri. Tun Aymah bata fahimtaba harta ganosa. Aiko saita daina sanar masa idan zatayi. Haka ta dinga ritsashi akan cin tuwon nan dole. Tun yana gudu bayaso har ya fara masa daɗi. Sai gashi cikin ƙanƙanin lokaci ya iya ci kuwa. Shima kuma komawar da yay Nigeria sau kusan uku duk xuwan da zai dawo sai yazo da wani abinda yasan na yaransune. Sai dai cikin ikon ALLAH kuma ita Aymah ciki ya sakata ci take hankali kwance. Dan yanzu kuma komai ci take anbar coffee. kayan wajen Umm ma duk zuwa sai yazo mata dasu. 
      Watan su Aymah ɗaya da sati biyu a U.S Juliet ɗin Omar ta haihu mace mai kama da ita. Su Aymah ansha murna. Sai taji itama tanason ta haihu. Tako dage harda addu'a a cikin salla (😂bar wahal da kanki baby Aymah).
       Shi Yoohan baisan tana addu'ar ba shiyyasa bai sanar mataba. Dan a lokacinma baya ƙasar shi. Sai da ya dawone yaga baby. Omar ɗinma yana 9ja bayan haihuwar da kwana ɗaya yazo. Dan dama yaso Juliet ɗin taje Nigeria ta haihu taƙi. Yarinya dai taci suna biyu. Aysha & Lisa, Dan shi dai Omar duk abinda ya dace uba musulmi yayi akan ƴaƴansa shi yayi akan baby Aysha. Itako Juliet da yake dama bawani bidi'oin suna sukeba suna kawai ta sakama yarinyarta bayan wanda Omar ɗin ya saka mata. Saima yazam itama yanda Nu'aymah ke kiran sunan Aysha ɗin yana mata daɗi. Sai gashi tafi kiran yarinyar da Ayisha ɗin. Saboda daɗin da Omar yaji har ƙyauta yayma Nu'aymah da godiya. Tare da roƙonta dan ALLAH taita jan Juliet ɗin a jiki ko itama za'a dace ta gane gsky. Aymah ta amsa masa. duk da tasan hakan abune mai wahala ga baturen ba'amuruke irin Juliet. To amma komai ai na ALLAH ne.

_________________★

        *_KANO NIGERIA_*

Anan kano ta dabo kam Umm najin daɗin zama da Afrah data ta fara aiwatar da aikinta cike da ƙwarewa da nutsuwa. Gaba ɗaya ta ɗauke musu kewar Aymah. Koda yaushe Muhammad inhar ba makaranta ya wuce ba yana nane da ita. Itama tana matuƙar son yaron, dan yana ɗauke mata kewar ƴan ƙannenta.
      Haka ma tana matuƙar jin daɗin zama da baba malam da Umm. Dan mutanene masu dattako matuƙa. Ita da hajjo kam ai ba'a magana. Daka gansu tamkar jika da kaka. Kai gaba ɗayama al'ummar gidan Afrah nada ƙyaƙyƙyawar alaƙa da kowa. Dan malam ƙarami harya ƙyasa. Ita kuma taƙi sanar masa tanada mijin aurenta a hannu. Dan gab ma ake da saka musu ranar aure tunda iyaye duk sun shaida tuni. 
       A cikin dabarun da ALLAH yay mata a sashe su Nu'aymah ta manna cctv ɗin nan mai kama da stones. Hakama sashen hajjo da duk wasu gurare na cikin gidan batare da kowa ya farga da itaba. Bata da wata ƙawa mai shekarunta a gidan, dan haka taita jan yaran gidan jikinta sosai. Dan su Adawiya ma har yanzu suna Abuja. Admission ma za'a nemar musu su fara karatu tunda na Adawiya yasha kashi. Su baba malam sunso ta koma saudia ɗin ta cigaba hajjo ta hana hakan. Acewarta su jira dai suga iya gudun ruwan Abdallah ɗin.
         A cikin kwanaki goma da Afrah tayi a gidan ta kammala aikinta na manna camaras a duk inda ya dace. Sosai Jay yaji daɗin ƙwazon ƴar tasa. Hakama Bily. 
        Sai kuma ta koma bama Dawood da little, Yoohan, Omar bayanai akan duk motsin ƴan gidan. Da wanna suka fara aywatar da aikinsu batareda jama'ar gidan sunsan sirrin ba. Hatta da Nu'aymah batasan hidimar da akeyiba. Dan koda Yoohan ya koma U.S bai sanar mataba. Takan dai gansa yayi serious a lap-top duk dare. kuma baya zama latse-latsen sai tayi barci. Inko har yazam ta farka to yabar aikin kenan. Dan duk dabarar da zaiyi ya ajiye abinda yake ya sani. 
        A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa har aka shiga watan azumin Ramadan. Wanda ya kasance na farko ga Yoohan da Omar. Sosai Aymah ta yabama ƙoƙarin Yoohan randa aka kai azumin farko. Dan ko irin nuna yau ya fara ɗin nan bai nunaba. Itacema sai da ta karya nata saboda jiri data dinga gani, daga ƙarshe kuma taita amai.
       Omar U.S ya koma domin yin azumi. Hakan yasa kullum anan wajen Nu'aymah yake zuwa shan ruwa. Wani lokacin ma harda Juliet suke zuwa da Baby Ayisha. 
       Azumi nada kwanaki goma sha biyu hutun Afrah ya ƙare. Ta tattara ta koma Abuja cike da kewar su Umm. Dan ita dai taji masifar daɗin zama da waɗanan bayin ALLAH musamman cikin azumin nan. Su kansu duk sai da sukaji babu daɗi akan komawar tata. Sai dai babu yanda suka iya tunda zata koma kan aikintane.

        An kammala azumin watan Ramadhan lafiya. Ansha kuma bikin salla a ƙasashen musulmai. Yayinda su dai su Aymah sai ɗan yawo sukai anan U.S, da ɗanyin nasu bikin sallar anan cikin gida.
     Tsakanin Yoohan dasu papa har yanzu basu taɓa masa magana akan dukan Gebrail da yayiba. Dan komawar da yayi 9ja can gidan ma ya sauka abinsa. Sun kuma tarbesa kamar yanda suka saba. Ya iske su momy Destiny sun koma. Hakama maman Madam Chioma. Mama debora kawai ya iske da sauran ƙannensa sai guards ɗin gidan su Solomon daya koma gadin nadam Chioma yanzun. Gebrail kam tunda yaji Yoohan ɗin yazo gidan ya gudu. Har yabar ƙasar kuwa basu haɗuba. Daya sake komawama yay wajen  kwana goma shima wasan ɓuya suka dingayi da Gebrail ɗin.
        Wannan shiru da sukai ya bama Yoohan mamaki matuƙa. Badan dukan da yayama Gebrail ba. Sai dai maganar Solomon da baiji sun sake tayar masaba. Sai dai kuma shima baiyi magana ba ya bar Solomon ɗin cigaba da kasancewa da shi da sauran guards ɗinsa duk sanda ya shigo Nigeria. Duk inda ya shiga suna tare anan kam.

_____________________

           A kwana a tashi babu wahala sai ga cikin Nu'aymah ya shiga watanni shidda. Tun cikin azumi kuwa ta fahimci ciki gareta. Murna taitayi zasu samu baby suma. saɓanin yanda Yoohan yay tunanin zata tayar da hankalinta. Aiki shima yaji daɗin yanda ta nuna murnarta akan Unborn ɗin nasu. Wata ƙaunarta mai girma na sake faɗaɗa masa a rai.
        Ganin laulayin ya rage mata a lokacin sai kawai ya shiga ƙoƙarin nema mata admission. Wannan abu ya saka Aymah murna harda kuka. Dan tanason karatu sosai a rayuwarta.  Addu'a ta dage ta dingayi babu dare babu rana akkan samun gurbin karatun nan. Su Umm ma sunsha addaba akan su tayata da addu'ar. Har Muhammad tasa ya faɗa a islamiyya wajen ƴan ajinta su mata addu'a. 
      To Addu'a dama takobin muminine ai. Balle gashi result ɗin Ayman da Yoohan ya amso a gida wani zuwa da yayi dama yayi ƙyau masha ALLAH. Sai gashi kuwa an dace. Ranar kowa yasan Aymah ta samu cikar burinta. Yoohan kam ai yafi kowa shan kallo dacin dariya a wannan rana, sannan kuma yasha tukuyci mai tsoka da ba'a bama yaro mai ƙiwa.
      Da taimakon Juliet yay mata komai daya dace, dan itama tanayin wani course ma a cikin makarantar yanzu haka. Sai dai a online take ɗaukar lecture. Da wannan damar Yoohan ma yay amfani akan Aymah. Zata dinga ɗaukar lectures ta online. Idan kuma taso shiga school bai hanata ba bayan ta haihu. Yayi hakane saboda yanayin jikinta. 
      To da yake itama yanzu lallaɓa cikin take sai ta amince (wa yaga ba sabanba su Aymah za'ayi ƴaƴa😂).
        Umm, baba malam, hajjo ne kaɗai sukasan da zaman cikin Nu'aymah a kaf jama'ar gidansu. Dan ko Addah Umm bata faɗamawa ba sam. Tabar abinta a zuciya wai randa Nu'aymah tazo kowa ya gani. To kuma anyi sa'a duk wautar Aymah da surutu ita bamai irin sakin zance ɗin nan bace ako ina. Dan ko su Umm ɗin ai ba fitowa fili tai tace musu tanada ciki ba. Sune suka fahimta ita da hajjo. Baba malam ma a wajensu ya sani.
        Cikin ya mata ƙyau sosai a jiki, sai dai yasata ta ƙara ƙiba, kumatun sun fito masha ALLAH. Idan Yoohan najin neman magana yakan tasata gaba yayta dariya. Ita kuma taita hawaye dan yanzun dai kam bakin tsiwarnan duk ya mutu. ta kanta takeyi duk tazama wata shiru-shiru.
           
  ★★★★★

      Akwai aikin da Yoohan zaizo yi Ƙasar ghana, daga nan kuma zai shigo Nigeria akan case ɗin gidan su Aymah. Dan zuwa yanzu sun tattara abubuwa da yawa ta dalilin Afrah. Sai bayanan sirrin da jay ya tattara ta hanyar camaras ɗin nan wanda shi da bily kawai suka san dasu. Amma suma ɗin basu duba komai ba a yanzu, dan sunbar komai ne ya tattaru, So suna son fara buɗe abubuwa a bayyane insha ALLAH a hankali. Sun san kuwa a wata uku kenan da zaman camaras ɗin a gidan sun naɗi abubuwa iri-iri, musamman daya kasance ansha shagalin bikin ƙaramar salla da babba, duk kuma ahalin gidan sunzo, idan ka cire Abdallah da yay hijira.
      Shirinsu na farko dai yanzu shine fara kama Rabi. Daga haka sauran abubuwa zasu cigaba da tafiya a buɗe. Nu'aymah taso biyo Yoohan a wannan karon. Sai dai kuma ya lallaɓata akan ta bari sai hutun ƙarshen shekara idan ALLAH ya kaimu. Tunda baifi saura wata ɗaya da sati biyu ba. Batai masa musu ba, dan yanzu duk ta ƙara yin laushi, danma wahalar cikin ta mata sauƙi sosai zuwa yanzu Alhmdllh. Gashi kuma dama cikin fari. Ga kuma karatunta da ke mata matuƙar daɗi. Dan harya kaita da mantawa da wasu su madam Chioma. Lamarin papa ne dai kam sun tattauna da Omar sosai a wani zuwa da yayi U.S ɗin. Annan take faɗa masa gaskiyar lamari game da hoton data ɗakko a ɗakin papa ɗin, harma da waɗanda ta gani. Abin shima ya bashi mamaki sosai. Nan shima yake sanar mata abinda ya taɓa faruwa tsakaninsu da Jay kwanaki. Itama sai abin ya tsaya mata a rai. Har taji sha'awar son samun kusanci da zuri'ar Jay ɗin. A take Omar ya bata Number Afrah. Dama Afra ɗin ita tanada ta Aymah, kirantane dai bata taɓa yi ba. Dan sanda tana a gidansu sai dai su gaisa a wayar  Umm ne. Tun daga sannan suke ɗan kiran juna a hankali, suna kumayin chart lokaci-lokaci kasancewar duk sunyi busy.
     To yanzu dai sun ajiye magana akan duk sanda taje 9ja zata bashi hoton ya gani, daga nan sai su san tudun dafawa akan wannan al'amari. Daga haka suka ajiye batun.

       Sai dai kuma abinda su Aymah basu saniba ita da Omar shine tun randa Jay yaga Yoohan bai hutar da kansa ba a bincike dabin diddigin papa. A hankali duk wani motsin papa ya kasance akan idon Jay batare da shi yasan hakan na faruwaba. Dan ya rigada yayi imani da cewar ya toshe duk wata hanya ta leƙen asirinsa daga wasu mutane koda jami'an tsarone. Sai gashi shi Jay yama kansa hanyar da yake kallon papan tsirara.
       Dirar safe Yoohan yayma 9ja wannan karon. ya kuma sauka a Lagos ne. Sai da ya kwana uku sannan ya ƙaraso Abuja. Kamar ko yaushe ahalin nasa sunyi murna da zuwan nasa. Musamman ma madam Chioma da duk zuwa saita banka masa kayan tsibbunta a abinci yaci. Sai dai duk da bataga wani canjiba daga garesa tana ɗauka aikinta na tafiya dai-dai. Musamman da bata taɓa jin ya zauna yimata zancen Nu'aymah ba.
       Tun isowarsa gidan Gebrail ya gudu kamar yanda yakeyi yanzun. Tun dukan da Yoohan yay masa bai sake yarda sun haɗu a inuwa ɗaya ba. da zarar yaji labarin zuwansa yake barin gidan, bakuma zai sake shigowaba sai Yoohan ya koma kokuma yaje wani jahan aiki. Duk da Yoohan na lure da Gebrail ɗin bai taɓa nuna yasan yanayi ba. Gaba ɗaya yi yake tamkar ya manta da wani halitta Gebrail a cikin ƙannensa.
      Blessing da su Favour yasa suka gyara masa sashen nasa wannan karonma. Bayan ya watsa ruwa yaɗan miƙe a gado yanason ya huta. Sai da ya fara kiran Aymah suka ɗan taɓa hira sannan ya kwanta. A ƙanƙanin lokaci kuwa barci yay awan gaba da shi. 
              
          Madam Chioma da tun shigowar Yoohan gidan yau ta kasa zaune ta kasa tsaye ta fito wankan maganin da boka Bangaruta ya bata a gurguje. Zama tai gaban mirror ta shiga tsara kwalliya kai kace fita zatayi. Sai da ta tsuke cikin wando da riga da sukai mata matuƙar ƙyau sannan ta feshe jikinta da kalolin turarruka masu tsada da ƙamshi. Gashin Attachment ɗin nan sai uban walƙiya yake da ɗaukar ido kasancewar sa mai uban tsada. Cike da takun gayu da ƙasaita ta fito daga sashenta dan papa baya nan yayi tafiya yau kwana biyu. Mama debora dasu Victoria kuwa tasa sunbar gidan a cikin shirinta. Ta aika Blessing kuma kasuwa. Amma abinda bata saniba Blessing ɗin batakai da fitaba saboda toilet daya kamata.  Kanta tsaye sashen Yoohan ta nufa, hakan yayi dai-dai da hawowar Miracle sama hannunta ɗauke da five alive da kofi. Waya takeyi da wata ƙawarta tana bata labarin zuwan Yoohan. Saurin ɓoyewa Mira tayi dan kar madam Chioma ta ganta, tare da jan wani shegen wawan tsaki dayin kamar zatai jifa da kwalin lemon. Sai kuma ta fasa saboda uban kuɗin data kashe wajen yima lemon haɗin magunguna saboda Yoohan. Itama kanta cikin gayun take na kece raini. da alama kuma sashen Yoohan ɗin ta nufa. Sai dai gashi Maman Yoohan ta ruguza lamarin. Ranta cike da ƙuna taje ta zauna a kan wasu kujeru biyu dake a upstairs ɗin tana huci da bama ƙawar tata labarin abinda Momyn Yoohan ɗin tai mata. Zugata ƙawar tata take famanyi daga can akan ya kamata Miracle tazo suyi duk yanda zasuyi wajan raba Yoohan da uwar tasa. 

         A ɓangaren madam Chioma kam ta shiga da dukanin gadaranta sashen ne. Key ta sakama ƙofar falon sannan ta nufi ɗakin Yoohan kai tsaye. Baisa a ransa kowa zai shigoba, musamman da yasan yanzu Momy ta bar masa ɗabi'ar banza na shigo masa sashema gaba ɗaya. Dan duk zuwannan da yakeyi bata shigowa, sai dai idan shine yaje sashenta gaisheta kosu haɗu a falon papa. Shiyyasa yake kwance abinsa daga shi sai boxer yana barci hankalinsa kwance. Ga iskar ac na shiga da ratsa masa ɓargo.
       Nanma maida ƙofar tai ta rufe harda saka key. Kafin ta ƙarasa gaban gadon jikinta har tsuma yake saboda ganin a yanda Yoohan ke kwance. Duk da ma yayi rubda ciki ne. A hankali ta zauna a bakin gadon saitin kansa. Ta kai hannu kan sajensa da ke bala'in burgeta. Cike da ƙwarewa a bariki ta kwanto jikinsa tana sauke nannauyan numfashi, sai kuma ta shiga yin sama da hannun nata ta tura cikin sumarsa. Dan tasan tun yana yaro yanason a dinga masa wasa cikin kai. Yanda take da hannun nata a cikin sumarsa ya sakashi sauke ajiyar zuciya a cikin barci. GGashidama mafarkin matarsa yake. Sai abinda madam Chioma ke masa yay tasiri a garesa. 
        A hankali yay juyi gaba ɗayansa ya koma ringin gine. Kansa kuma ya ɗora akan cinyarta ɗaya dake a gadon. Wani irin daɗine ya kama Madam Chioma dan duk zatonta aikintane yay tasiri. Ranƙwafowa tayi da fuskarta daf da tashi tana wani lasar baki tamkar mayya. Yayinda hannunta ɗaya ke yawo a jikinsa. Tana gab da kai laɓɓanta kan nasa ALLAH ya bashi ikon farkawa a dalilin jin ƙamshi saɓanin na Aymahr sa. A wani irin matsanancin tashin hankali ya angizata daga ranƙwafomasa da tayi, danshi da farkoma yayi zaton Miracle ce............✍

 *_Wayyo tazo kwartanci😱🏃🏃🏃_*


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/3, 3:48 PM] Queen Meenali👑: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 70

............Sai dai kuma ɗagowar da zaiyi cikin matsanancin fushi sai idonsa akan Momynsa daya yasar a ƙasa. A matuƙar razane yace, “What!!. Momy! Innalillahi wa'innalillahirraji'un”. Cikin karkarwa jiki ya shiga bin ɗakin da kallo, tabbas daga shi sai ita ne, hakan na nufin ba Mira ba. Ƙirjinsa ya sake bugawa da ƙarfi. Yay azamar jawo rigarsa dake gefe danya saka Madam Chioma da ALLAH yaba damar tashi tai saurin riƙe masa hannu. Dan ita haukanta gaba ɗaya bai nuna mata maganinta baya aikiba. Faɗa masa tayi ajiki tana faɗin, “Haba my boy ya kake abu kamar wani.......”
      Ai kafinma ta ƙarasa ya sake hankaɗata da rawar jiki. “Momy kina lafiya kuwa? Ninefa Yoohan?! Kodai kinsha barasa ne?!”.
       Duk da mamakin yanda yakeyi ya fara sata dawowa hayyacinta, ga zafin maguzar daya sake mata hakan bai hanata sake nufosa ba. Hankalin Yoohan ya sake kololuwar tashi, dan shi yafi tunanin Maman tasa bata a hayyacinta ne. Ta sake riƙe rigar daya ke ƙoƙarin sake kai hannu ya ɗauka tana wani narkewa hawaye na zirara mata. “My boy kaine mafarkina. Kai ne farin cikina. Tunda ka kai shekarun girma ka ɗauke hankalina ga kowanne namiji a duniya. Hatta da papanku baya birgeni gaba ɗaya duk da auren soyayya mukayi. Please masoyina kazo na baka zumar da wata a duniya bata taɓa baka itaba, na maka alƙawari........”
      Duk yanda Yoohan yaso jurewa yama mahaifiyar tasa uziri ya kasa, dan haka ya fisge hanunsa data riƙe wani matsanancin tsoro na sake kamashi. Da sauri ya nufi hanyar ƙofa danya kuɓuta. Sai dai kuma ya sameta gam alamar ta kulle. Sunayen ALLAH ya shiga kira babu ƙaƙƙautawa, yay azamar kaucewa ganin ta sake nufoshi ido rufe. Dan har ta cire rigar jikinta tana ƙoƙarin cire wandon ma.
     Wata azababbiyar ƙara da hatta Miracle da Blessing dake ƙasa a laɓe sai da suka jiyosa ya daka mata. 
        “Momy!!!! Are you mad?!!” Ya faɗa yana hankaɗata da iya ƙarfinsa da matsanancin fushi dan gaba ɗaya hankalinsa ya kai ƙololuwa a tashi. Sai ko gata a ƙasa wanwar. Wata wahalalliyar ƙara ta saki saboda faɗawa datai akan hannun damarta. 
      Ya cigaba da magana cikin fushi na ficewar hayyaci. “Wane irin ruɗaɗɗen al'amarine haka momy? Momy na tabbatar wlhy baƙya cikin hankalinki. Ninefa ɗanki Yoohan. Mikike shirin aikatawa haka?!!.......”
       “Cikar burina John. Idan har bakai tarayya dani ba zan iya halaka Yoohan. Dan ALLAH ka daina ɗaga murya kazo gareni. na maka alƙawarin a yau duk ƙishirwarka ta shekara da shekaru sai na gusar maka da ita, nima ka gusarmin da taw......”
       Da sauri ya tura yatsunsa cikin kunneta alamar baya buƙatar jin kalamanta. Sai da ya fahimci tayi shiru sannan ya nufeta. Da wani irin zafin nama ya kai hannu ya fisge key ɗin ɗakin daya hanga a yatsan hannunta. Ƙara ta saki dan taji zafi. Shiko ko saurarenta baiyina ya nufi ƙofa ya buɗe ya fice. Rasa inda zai dosa yayi a sashen nasa. dan ko ina a kulle yake. Cikin azama ya nufi ƙofar falon ya buɗe dan tabar key ɗin a jiki. Yana buɗewa tana fitowa daga ɗakinsa da jan jiki tana kuka da roƙonsa karya tafi.
         Da wani irin mugun sassarfa ya fice yana karasa saka t-shirt ɗin daya fito da ita a hannu. Wani irin mahaukacin jiri yakeji, kansa tamkar zai tarwatse saboda firgici. Da steps bibbiyu ya sauka a benen. Hakan yasa Miracle dake ɓoye fitowa ta biyosa da sauri tana ƙwala masa kira. Yana gab da ficewa ƙofar falon gaba ɗaya ta riƙo masa hannu. A wani irin juyowa tamkar wani walƙiya yayi sai jin saukar tagwayen maruka tayi a duk kumatunta. Kafin ta dawo hayyacinta ya hankaɗata ya fice abinsa duhu na mamaye masa cikin idanu. Hakan yasa sam ya daina ganin hanyar da yake ajiye ƙafa da ɗaukewa........

★★★
   
           A hankali yake buɗe idanunsa ya saukesu akan Omar dake a kujera zaune. Nauyin da sukai masa ne ya sakashi sake maidasu ya lumshe a hankali. 
       “Sannu Son”.
Muryar Dr Shikurah ta shiga kunnensa. Sake buɗe idon yayi a hankali yana mai juya kansa kaɗan ya kalleta itama. Babu zato sai kawai sukaga hawaye na gangaro masa ta gefen ido. Da ga ita har Omar dake jera masa sannu shima a tsorace suke kallonsa. Dr Shikurah ta shiga jera masa tambayar ko wani waje na masa ciwo ne?.
       Karan farko yay guntun murmushi mai ciwo da ƙunan zuciya. Dan ya tabbatar da ciwon da yakeji a zuciyarsa gara ace duk jikinsane ke masa wannan ciwon da raɗaɗi zaifi masa sauƙin ɗauka. Yunƙurawa yay a hankali zai tashi zauna. Sara masan da kansa yayine ya sakashi saurin dafewa yana faɗin, “Ya ALLAH!”. 
        Da sauri Umar ya riƙosa. Yana faɗin, “Dude be careful mana”. Yayinda Dr Shikurah kuma ta gyara masa filo Omar ya jinginasa a jiki itama tana jera masa sannu tamkar zata fasa kuka. Dan har ikin ranta takejin zafin halin da yake ciki. Gyara masa drip ɗin da ake ƙara masa tayi, kafin ta dubi Omar da shima dai yana cikin tsantsar damuwa. “Omar kodai allurar za'a sake masa ne? Barcin kamar bai ishesa ba”.
     Kafin Omar yay magana Yoohan yay saurin girgiza kansa. “A'a Momy babu buƙatar haka. Bazan iya sake kwana a ƙasar nan ba, dan zuciyata zata iya bugawa.....”
       Cikin katsesa Umar yace, “Taya zakai maganar barin ƙasa kana a cikin wannan halin? kana son yin wasa da lafiyarka ne komi Yoohan?”.
      Kallon Umar ɗin yayi da idanunsa dake jajur yana wani murmushi mai ciwo, gazafafan hawaye na ziraro masa a saman kumatu. “Bazaka ganeba Omar, duk bayanin dazan maka bazaka fahimceni ba. Tafiyata ba itace wasa da lafiyata ba, zamana a ƙasarnan shine wasa da lafiya ta. A yanzu haka inajin tamkar na rufe ido naga bana numfashi saboda ruɗanin da ƙwaƙwalwata take a ciki. Umar ni Momy zata n......”
     Sai kuma ya fashe da kuka mai cin rai batare daya iya ƙarasawa ba. Jikinsa sai wani irin rawa na ɓacin rai yakeyi dan Yoohan akwai zuciya dama. Hankalin Dr Shikurah da Omar ya sake ƙololuwar tashi. Umar ya riƙo hannunsa yana lallashinsa. Amma sam hankalin Yoohan baya a jikinsa gaba ɗaya. Babu abinda ƙwalwarsa ke tariyo masa sai abinda ya faru shi da Momynsa tamkar a film. Gaba ɗaya ƙwalwar kansa da tunaninsa neman jirkicewa suke.
      Wani irin bahagon numfashi ya fara ja da ƙyar alamar motsawar Asthma ɗinsa. Hankalin Omar yakai matuƙa a tashi, dan yasan Yoohan nashan wahala akan Asthma ɗinsa. Takan daɗe bata tashi masa ba. Amma duk lokacin data motsa yana shan wahala sosai. Gashi shi koma yawo da inhaler bayi yakeba saboda yana jimawa bai yiba.
        Ganin abin babbane yasa Dr Shikurah tambayar Umar a ruɗe. 
     Shina Umar ɗin a rikice yace, “Mom yanada Asthma, sai dai tana jimawa bata motsa masaba. Da alama yanzu kuwa itace”.
       “Hasbinallahu wani'imar wakil”. Dr Shikurah ta faɗa tana fita da hanzari.
       Babu jimawa sai gata ta dawo suka shiga bashi taimakon gaggawa ita da Omar. Basu ƙara samun nutsuwa ba sai da Yoohan ya koma barci mai nauyi.
     Cikin sauke tagwayen ajiyar zuciya Dr Shikurah tace, “Omar anya kuwa ba wani abune mai girma ya firgita ɗan uwanka ba?”. Duk da Umar yasan ainahin abinda ya faru. saboda Blessing ta sanar masa ta waya sai ya ɓoyema Dr Shikurahn. “A'a Mom, faɗowar Momynsa daga benen ne kawai ya firgitashi”.
        “ALLAH sarki, ai jikin nata itama da dauƙi, duk da bata farfaɗo ba har yanzun, amma Alhmdllh bataji wani mummunan ciwobama kamar yanda mukai hasashe”.
     “ALLAH ya basu lafiya”. Umar ya faɗa a taƙaice. Daga haka Dr Shikurah ta fita daga ɗakin. 
          Fitar Dr Shikurah ɗakin tayi dai-dai da shigowar Papa da Uncle Joshua cikin asibitin. Dan isowarsa kenan ƙasar ya iske gidansa a harmutse. bayan ya tambayi dalili aka sanar masa Yoohan ne ya yanke jiki ya faɗi batare da ansan dalili ba. Wajen biyosa kuma madam Chioma ta faɗo daga bene. (Dan su iya abinda suka gani kenan. Miracle da Blessing ne kawai sukasan ainahin abinda ya faru. Su kuma babu wanda yace komai. ita dai Blessing tsoron rasa aikinta takeyi. Itako Miracle bamusan dalilinta na ɓoyewarba).
     Sun sanar masa Richard yazo gidan a daidai faruwar al'amarin, shine ya tafi da su asibiti su duka. Wannan shine dalilin zuwan papa a sibitin da hanzari.
        Kasancewar Yoohan sannan likita duk ma'aikatan sun sanshi. papa na ambatar sunansa da kuma tabbatar musu shi din mahaifinsane ko sai gashi an rakosa har office ɗin Dr Shikurah. Itace ta fara kaisu ɗakin da Madam Chioma ke kwance a sume har yanzun, sunata dai tsammanin farfaɗowarta. Duk an mata dressing ciwukan da taji, tare da gyara mata tsagewar ƙashi data samu a hannunta. 
        Papa harda su hawaye yayi na tausayin matar tasa. Dan yasan yanda take tsananin son ɗan nasu. Suko su Dr Shikurah sai faman masa sorry sukeyi. Daga haka suka fito zuwa ɗakin da Yoohan ke kwance shima. Anan ma hankalin papa ya tashi da ganin halin da yaronsa yake a ciki, dan tashin Asthma ɗinsa sunsan bata musu daɗi.    

*_WASHE GARI_*

         Washe gari suka tashi da farkawar madam Chioma. Sai dai tanata faman raki akan hannunta. Dan kuka ta dingayi kashirɓan kamar ƴar yaye. Papa kuwa dake nane da ita yana tayata da tattali. 
      Yoohan kam Alhmdllh tun a daren ya farka. Ya kuma takurama Omar sai ya nema masa ticket ɗin wucewa U.S. duk lallashin da Omar ya dinga masa sam yaƙi saurarensa. Ya dage akan shifa sai ya bari ƙasar. Kuma bayason papa ya sani. dan duk da ya farka duk shigowar da papa yazoyi dubashi sai ya nuna bai farka ɗinba. Badan Umar yaso ba dole yaje ya nema masa ticket, sai dai bana zuwa U.S bane direct. Amma duk da hakan Yoohan yace ya yarda. Sannan yaje gidan ya haɗoma Yoohan ɗin kayansa na buƙatar yau da kullum kamar su waya da sauransu.
     To kuwa a safiyar yau ƙarfe goma batai masa a asibitinba. Dole Omar ya fita da shi a ɓoye batare da ko Dr Shikurah ta sani ba. Shine ya kaisa airport ɗin ma. Yanaji yana gani Yoohan ya wuce ya barsa da damuwa.
      Asibitin ya dawo, inda ya tarar anata neman Yoohan. Shima kawai sai yayi pretending ɗin shiga cikin ƴan nema. Dan baisan wace amsa zaiba papa akan tafiyar Yoohan ɗinba. Bayan kuma shi kansa Yoohan ɗin ya masa magiya da roƙon bayason su papa susan ya wuce da saninsa.  
             Jin Yoohan ya wucene yasake birkita madam Chioma, yanda ta tashi hankalin nata har mamaki ya bama Uncle Joshua shi dai, amma sai baiyi maganaba dan hakan ba huruminsa baneba. Daga ƙarshe ma allurar barci sukai mata saboda yanda take faman rubzar kukan ita dai a nemo mata yaronta. Shi kansa papan itace ta sake birkitasa. Dan yasan dai Yoohan bazai ɓataba. Abinda kawai ya tsaya masa a rai shine minene ya saka Yoohan ɗin tafiya bayan kuma baida lafiya?. Dama tun jiya yaketa tunanin akan faɗuwar da akace yayi babu gaira babu dalili tunda har waya shidai yayi da shi a ranar da safe, kuma baiji wata damuwa tattare da yaronsa ba a lokacin da shuke wayar. Dan shine ma yace karya faɗama Momyn nasu zai dawo a jiya yana son ya mata surprise ne. Har Yoohan ɗin na masa dariya akan hakanma. Sai kuma gashi ya dawo ya iske waɗanan rikitattun tashin hankali da gaba ɗaya ya rasa makamar riƙewa akan faruwarsu.
  

___________________

       Nu'aymah na gidan Juliet Omar ya kira akan taje gida ga Yoohan nan a hanya. Abin ya bata mamaki dan sunyi da shi sai nan da sati biyu ma zai koma. Haka dai tai shiri ta koma gidan nata ttareda Juliet da tai mata rakkiya danta tayata gyara waje. Duk da ma tasan baza'a samu datti sosai ba tunda duka yau kwananta biyar da barinsa.
     Babu dattin dai kam sosai. Amma sai da suka gyara komai tsaf. Juliet ta tayata sukai har girki saboda tausaya mata da takeyi na halin da take a ciki. Sai da suka gama komai tsaf sannan ta wuce tabar Aymah na wanka.  
       Bata wani jimaba ta fito tai shiri cikin doguwar rigar atanfa mai faɗi data ɓoye cikinta. Wayarta ta ɗauka ta nufo falo dan yunwa takeji ta bala'i. Turus ta tsaya tana kallon Yoohan dake kwance a kujerar falon idanu a lumshe. koda wasa bataji motsin shigowarsa gidanba sam. Cigaba tai da takawa a hankali inda yake. Batare da tayi magana ba ta zauna a gefensa da kai hannunta ta janye nasa hannun daya dafe kai da shi.
      A hankali ya buɗe idanunsa dake jajur ya zuba mata su. Itama kallonsa take cikin ido sosai. Sai kawai yaji zuciyarsa ta ƙara raunana. A take hawaye suka cika idanunsa. Ɗayan hannunsa ya kai saman cikinta yana murmushin ƙarfin hali.
     Ita dai Aymah kallonsa take tamkar wata sokuwa, dan yanzu kam sai dai ta bama wani labarin mijinta badai ita a bataba. Cikin sanyin murya tace, “Baka da lafiya?”.
        Haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙoshi yayi da ƙyar, sannan ya yunƙura ya tashi zaune yana cije baki daboda kansa dake masa ciwo har yanzun. Zama yay da ƙyau ya rungumota jikinsa, hannunsa nakan cikinta yana shafawa a hankali. Cike da raunin murya yace, “I miss you Sweet girl”. 
       Maimakon ta amsa masa sai ta ƙara jefa masa kalar tambayar ɗazun. Murmushi ya sakeyi da sumbatar kanta. “Lafiya ta ƙalau baby, sai dai kewarki ce”. Duk da Aymah bata yardaba saita ƙyalesa kawai a hakan. Itama ta rungumesa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Duk da ciwo da ƙunar da yakeji zuciyarsa na masa bai hanashi bata haɗin kai ba. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ta janye bakinta a cikin nashi suna maida numfashi. Batare data bari wani cikinsu ya sake magana ba ta kama hanunsa suka wuce bedroom. Sai da ta rakasa har bayi, duk da tana fama da kanta ta taimaka masa yay wanka. Da suka fito ɗinma da taimakonta ya shirya sannan sukai salla.
       Bata samu matsala da shi ba sai a wajen cin abinci, dan cayay mata shi ya ƙoshi. Hankalin Nu'aymah ya sake tashi matuƙa saboda ta kasa gane kansa gaba ɗaya. da ƙyar dai ta samu yaci kaɗan ya sata ta ɗakko masa magani ya duba wanda ya dace ya sha. Bedroom ya koma ya kwanta daga haka sai barci.
      Gadon tazo ta sauna tai tagumi kawai ta zuba masa idanu tana kallonsa cike da tausayi da damuwa akan da tasa damuwar data fahimci yana son ɓoye mata ne kawai.

*_KANO NIGERIA_*

           A lokacin da madam Chioma ke can neman sa'a akan Yoohan anan kano su Little bee ne suka samu damar ƙwamushe Rabi mai aikin su Aymah da ta zo yima Umm aika a kasuwa. 
     Tunda ta fito gida suke biye da ita batare data sani ba. Sai da tazo bakin titi domin tsallakawa taga mota a gabanta kawai. Kafin ta wani yunƙuri aka fisgota ciki tare da daɗe mata baki yanda ta kasa ihu. Daga ƙarshe ma suka danna mata allurar data bugar da ita. Harko suka iso garin abuja bata sake sanin ina hankalinta yake ba, sai wayar gari tayi taga kanta a wani ɗakin da bata saniba. Da matuƙar tashin hankali ta tashi tana ƴan waige-waige, sai kuma ta fashe da kuka ganin da gaske dai fa baƙon waje aka kawota......
        Tsawar da aka daka matane ta sakata sake gigicewa harda sakin guntun fitsari. Murɗeɗen ƙatone da iya gani kasan ya damƙi namiji ma sai ya shinshino ƙamshin lahira bare ita mace da girma ya kama. Abincin hannunsa ya dangwarar a tebirin ɗakin dake tare da kujera ɗaya. Sai yololuwar guntuwar katifar da Rabi ta kwana agefe. Da tsananin kaushin murya yace, “An gaya miki nan gidan kuka ne. Karna dawo na samu wannan abincin da hawayen fuskanki”. Ya ƙare maganar da juyawa ya fita abinsa.
     Tashin hankali iya tashin hankali Rabi ta shiga. Hakan yasa ta share hawayen nata ta zauna ta fara cin abincin data san bazata ƙoshiba. Ga uban yaji a ciki na tashin hankali. Amma tasan inhar batacinba yunwa halakata zatayi. Mutumin nan kuma kashetama zai iyayi ƙila. Sai da ta kammala da kusan minti talatin, zuwa lokacin yajin ya gama wajiga rayuwarta sannan aka kawo mata ruwa rabin gora. Jikinta har rawa yake wajen ɗauka ta sha, dan ita kaɗai tasan a tashin hakalin da take ciki game da cin yajin nan...

      Haka aka ringa wajiga rayuwar Rabi har tsahon kwana goma. Tayi kuka harta rasa hawayen zubarwa. Sai da suka tabbaar tayi laushi iya laushi sannan suka nema su sanarma su Yoohan. Sai dai an samu akasi Yoohan ya wuce U.S sai Omar kawai ne ya amsa zaizo, dan jikin madam Chioma yayi sauƙi sosai anma sallameta tun kusan kwanaki uku kenan, satinta ɗaya a asibitin. Ranta dai na nan danƙare da damuwar rashin sanin inda Yoohan ya nufa da kuma rashin samun cikar burinta. Duk da tun a asibiti sun yake magana da Rebecca zasu koma gidan Bangaruta, sannan Marcy ma tace zata rakata wajen wani bokan a Lagos.

____________★

          Bayan isowar Umar kai tsaye office ɗin Dawood sukaje. Sai da sukai zaman jiran Bilkisu Adam Makaho, mata ga Oga Jay sannan, dan itace oga kwata-kwata akan case ɗin. Tana isowa kuwa suka amsa kira ta hanyar telephone.
       Sun sameta a office ɗinta. Bayan sun gaisheta ta basu iznin zama. Sam babu wasa tattare da ita, dan yanzu bayan miskilancinta girma ya ƙaru ga daraja. Babbar Officer ce da aikinta ke girgiza sansanin duk wani mai kunnen ƙashi. 
    Batare data kallesu ba tace, “Dawood azomin da matar nan”.
     “Okay maa”. Dawood ya faɗa da sauri yana miƙewa. Kusan mintuna goma sai gashi ya dawo tare da Rabi dake wujiga-wujiga, dukta fita hayyacinta a kwanaki goma kacal. Kuma babu zagi babu duka. Zai gurfanar da ita a ƙasa Bily ta hanashi. Wata kujera dake can gefe ta bashi umarnin ya bama Rabi ta zauna. Shi dai Omar nata kallonsu ne da mamakin ganin yanda Rabi ta koma. Gashi kuma ko ƙwarzanen duka shi dai bai gani a jikinta ba. Itako bama ta gane Umar ba saboda a jigacen da take.
          Little bee ce ta shigo bayan tayi knocking an bata izini. Tai salute ɗin mahaifiyar tata kuma ogarta a wajen aiki kafin ta ajiye takardun hannunta a tebir ɗin. Takardun Bily taja gabanta ta duba kafin ta ajiyesu gefe ta kalli Rabi.
        “Nasan dai zuwa yanzu kinsan a inda yake ba wajen wasan nanaye bane. Dan haka ya rage ruwanki nutsuwa ki bamu duk amsar tambayar da zamu miki, ko kimana ƙarya”.
      Muryar Rabi na rawa tace, “In ALLAH ya yarda bazanyi ba ranki ya daɗe”.
      “Wannan ya rage naki”.
Bily ta faɗa cikin halin ko in kula tana sake ɗaukar takardun da Little bee ta shigo da su. A gaban Rabi ta diresu dai -dai lokacin da fuskar Yoohan dake zaune a office alamar yana a asibiti ta bayyana a cikin lap-top ɗin da Omar ya ajiye inda Yoohan zaiga kowa dake office ɗin.
        “Wannan takardun bayanai na duk abinda ke cikin wayarki. Randa kika sayi layi, randa kika fara ɗorashi a waya. Sau nawa kina canja shi a wasu wayoyi. Mutanen da kika taɓa kira ko suka kiraki duk akwai bayanansu anan. Dan haka ki nutsu sosai”.
        “In ALLAH ya yarda ranki ya daɗe”.
       Kallon sashen da Dawood da Little bee suke Bily tayi, kafin ta kalli lap-top ɗin. Kai Yoohan ya risinar cike da girmamawa ya gaisheta. Itama ta amsa masa da kulawa kafin ta nuna masa Rabi.
     “Ina fatan kana ganinta da ƙyau?”.
“Yes maaa!”.
        Duk da Rabi ta kalli fuskar lap-top ɗin itama bata kawo komaiba, tadai ga kamar hoton mijin Nu'aymah, kafin tunaninta ya faɗaɗa Little bee ta katseta da faɗin, “Minene sunanki?”.
         Murya na rawa tace, “Rabi?”.
“Shekararki nawa kina aiki a gidan Sheikh Soorajidden Hashim Jibiya?”.
       “Goma sha takwas. Dan an kainine lokacin matarsa nada tsohon cikin dake wahal da ita dan na taimaketa”.
    “Kin taɓa aure?”.
             “Eh na taɓayi harda yarana biyu”.
  “Keda ke aure miya kaiki gidan aiki har tsahon wannan shekarun?”.
      “Ranki ya daɗe ai auren ya mutu ne a wancan lokacin. To domin neman na kaina saina samu aikatau ɗin dan nayi saboda iyayena duk sun rasu ni marainiyace”.
       “Ƙwaɗayin zama gidan masu kuɗi yasa baki sake tunanin sake ƙara aure ba kenan?”.
       Shiru tayi kanta a ƙasa ta kasa bada amsa. Shima Dawood da yay maganar sai ya shareta da ga haka ya sake jeho mata wata tambayar.
     “Waye ya kaiki gidan?”.
A take ta ruɗe jikin na rawa, sai in ina take ta kasa bada amsa. Hakan yasa Dawood daka matsa gigitacciyar tsawa. Fashewa Rabi tayi da kuka. “Dan ALLAH ku gafarce ni zan faɗa”.
     Babu wanda ya tanka mata. Sai bindiga da little bee ta ciro a gefen ƙugunta ta dire a gaban Rabi. Hakan yasa ta kuma diriricewa. Cikin hadiye kukanta tace,
       “Ranku ya daɗe ni bansan ainahin wadda tasa aka kaini gidan ba. amma naje ta hannun wata matace amma yanzu ALLAH yay mata rasuwa”.
       “Oho, idan na fahimci amsar nan taki kenan dama an kaiki gidan ne da wata manufa? Ba wadda kike a wajenta bace tasa aka kawoki gidan!!”.
     Yoohan yay magana a matuƙar zafafe. Maimaita mata Dawood yayi da hausa. Dan duk da Yoohan ya haɗa da kalmomin hausa a maganar Rabi bata fahimta da ƙyau ba. Amma shi Alhmdllh yana fahimtarta sosai tunda jin nasa yafi faɗi da baki.
       A take Rabi ta ƙara rikicewa, dan har ga ALLAH tazatafa hoton Yoohan ɗinne kawai a wajen. Suma dai su Bily yanda yay maganar duk sai da ya sakasu kallonsa. Tebir ɗin Little bee ta daka da hannu, da tsawa tace, “Ki basa amsar tambayarsa malama kin ɓata mana lokaci”.
       Jikin rabi na cigaba da rawa tace, “Ranka ya daɗe ba haka nake nufi ba. Ni dai kawai an kawonine na kula da mai ciki, daga haka babu wani dalili dana sani na rantse muku da girman wanda ya halicceni”.
      A karan farko taji saukar mari mai gigitarwa a fuskarta. Kafin ta dawo hayyacinta Dawood ya ƙara mata wani. Sannan kuma Bily dake zaune duk tana kallonsu ta hanata kuka. Dole Rabi ta haɗiye hawayenta sai ajiyar zuciya.
     Dawood yace, “Inhar zakiyi mana ƙarya to zakiyita amsar irin waɗanan marukan babu ƙaƙƙautawa. Wa kikema aiki a gidan?”.
     “Wlhy yallaɓai iya gaskiyata nake faɗa muku. Bani yima kowa aiki sai Hajiya Firdausi matar Sheikh Sooraj ɗin”.
           Sai a yanzu Umar yay magana. “Eh ansan dama ita kikema aiki a zahiri. a baɗini kuma akwai ogarki mai sakaki shiryamata sharri ita da tilon ƴarta. Bayan ƙyautatawar data dinga miki a rayuwarki na tsahon shekaru goma sha takwas”.
       Dawood ne ya sake fassara mata. Dan haka cikin rawar harshe da kuka mai cin rai tace, “Na rantse da ALLAH. wlhy tallahi ban taɓa cutar da Hajiya Firdausi da zuriyar ta ba. Ko Nu'aymah da muke yawan faɗa wani lokacin ina takalartane kawai wlhy saboda nasan bata barin saita kwana. Amma bada wata manufaba. Ko a mafarki bana fatan na cutar da waɗan nan bayin ALLAH ai balle a zahiri”.
       Cike da ɗaurewar kai suka shiga kallon juna. Amma duk da haka bayan Dawood ya gama sanarma Omar abinda ta faɗa sai Umar ɗin ya bada vr ɗin nan na kwanaki da sukaji tare da Nu'aymah. Aka kuma tabbatar mata a wayar wanda aka samu.
       “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Rabi. Wlhy wlhy kinji na rantse ni ban taɓa waya da mai aikin Nu'aymah ba. Hasalima sam ban santaba tunda randa akazo za'a wuce da ita abuja a sashen hajjo Umm taje ta sameta itama. Yanzu haka ko zaku kasheni bazan iya nuna fuskartaba balle harna samu Number ta nayi waya da ita akan Nu'aymah. To niko idan ta faɗamin halin da Aymah ke ciki gidan aurenta ribar mi zanci bayin ALLAH?”.
        Tsawa little bee ta daka mata. “K bama son rainin hankali. Idan kince bake bace waɗan nan lambobin dake akan wayarki harda ta Uwaliya ɗin na uwar waye? Wa kuma ya sakasu da har zaiyi zaman magana da su a wayarki batare da kin saniba?”.
       “Wlhy iya gaskiyata nake faɗa muku. Ni yanzu haka ko waya zanyi ma sai naba Muhammad ya dubamin lamba. Dan shine kemin sebi idan ko zansa lambar wani ɗan uwana. Idan kuma zanyi kira shima ke dubamin abinda ya samun dan banyi boko ba. Da Nu'aymah ko Adawiya kemin, to sai suyita jamin rai, shine na koma bama Muhammad ganin ya iya. Amma ni lambar ma ƴan gidan bata kowa gareniba wlhy”.
     Hannu Dawood ya ɗaga zai ƙwaɗa mata mari Bily ta dakatar da shi. Dan ita duk shirun datai musu nazarin komi takeyi. sannan kuma Jay ma duk yana saurarensu daga office ɗinsa ta hanyar na'ura. Shinema yay saurin cema Bily ɗin kar Dawood ya mareta yanzun ta hanyar abibda ke a kunnenta da su basu fahimta ba.
     Dakatawa kuwa Dawood yayi yana huci. Bily dake kallon Rabi cike da nazari tace, “To amma ranar da Nu'aymah tai bleeding ko zamu iya sanin miya faru? Dan bincikenmu ya nuna mana kece kika bata abu na ƙarshe tasha a gidan. Daga haka ta fara ciwon ciki sai jini kuma ya ɓalle”.
      Shiru Rabi tayi tana tunani dan tama manta. Sai zuwa can kuma tace, “Lallai kuwa ranki ya daɗe kamar anyi hakan. Ta sakani na dafa mata ruwan shayi baƙi”.
       “Kenan a ciki kika saka mata maganin zubda jini da aka ɗauka cikine ta zubar??”..............✍
       

*_Tofa masu karatu man kai na fa zai fara malalewa a dalilin amsoshin Rabi, nama rasa mizan tunano kuma. amma bari mu bita muji wace amsa zata bada a gaba??😱🤧._*


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[7/3, 3:48 PM] Queen Meenali👑: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 71

..............Saurin zaro ido waje Rabi tayi tana mai girgiza kanta. “Wlhy ba haka bane ranki ya daɗe. Mizaisa na aikata hakan ga Nu'Aymah. Bayan sikari da Lipton sai ruwan dana dafashi da shi ne kawai a ciki”.
       Wani irin tafasa zuciyar Yoohan takeyi daga can, ji yake kamar ya ziro hannu ya shaƙo wuyan Rabi ta cikin system ɗin, sai dai babu dama.
        
     Little bee zatai magana Bily ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Inaga ku maidata inda aka ɗakkota tukkunna”.
       Babu wanda ya iya cewa komai a cikinsu. Sai tasa ƙeyar Rabi da aka saka wani jami'i yay tana kuka aka maidata inda aka ɗakkota.
      Bayan fitarsu ajiyar zuciya bily ta sauke tana rubuce-rubuce. Kusan mintuna biyu kafin ta ɗago ta kalli Yoohan da zuciya ta kume daga can.  “I'm sorry Dear wannan case ɗin duk yanda kuke tunaninsa ya wuce haka. Akwai wani abu dana fahimta dangane da wnanan matar wanda sam na kula ku duk baku gansaba. Kodai ya kasance amfani akeyi da ita a gidan batare da ita kanta ta sani ba. Kokuma tana kan sani ta fi yarda ta shanye duk wata azabar data fuskanta anan danta rufama wancan asiri. Kokuma an mata gargaɗi mai girma da tsoratarwa akan sanarwa tun ba yanzuba.
         Dole wannan wayar tata na buƙatar sabon bincike. Sannan waɗannan voice recording ɗin suma zamu sake bincike sosai a kansu, idanma har ba'ita ɗin bace zamu gano ainahin mai muryar insha ALLAHU”.
     Dukansu sun fahimceta. Hakan yasa Yoohan tabbatar musu da shima zai shigo Nigeria zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, kuma harda Nu'aymah. Dan ya fahimci lallai wasan na gaske ne.

_____________★★

           Tunda ya shigo gidan yau taketa faman binsa da kallon mamaki. Dan tun randa ya dawo daga 9ja ta kasa gane kansa gaba ɗaya. Kullum yana cikin ƙunci da tunani, baya son yawan magana, sai su yini su tashi har dare magana sau biyar bata shiga tsakaninsa da shi ba. Tayi tambayar harta gaji tayi fushi ta ƙyalesa. Daga ƙarshe ma sai ya koma fita asibiti. Idan ya tafi tunda safe sai tayi barci zai dawo. Ta fahimci yana hakane duk dan karta cigaba da masa tambaya akan abinda ke damunsa. Dan idan ya fita yata yawan kiranta kenan wai yaji yaya take ita da Unborn ɗinsa.
     Hakan data ƙara fahimtane ya sata sake tattare maganar damuwar tasa ta watsar gefe. to shinefa aɗan kwanaki ukun nan ya fara sakin jikinsa yana kuma dawowa gidan kafin tayi barci. Yau kuma abin mamaki sai gashi kusan ƙarfe uku ya shigo mata.
       Yanda batai maganaba shima baiyiba. Sai dai kallonta yake cike da tausayawa a gareta. Tana zaune ne a kujera ta miƙe ƙafafunta bisa centre table ɗin falon. Sai filo ƙarami a cinyarta ta ɗora lap-top a kai tana sauraren lecture da akeyi daga can school ɗinsu.
    A ɗan kwanki goma sha huɗu ɗin nan duk ta rame saboda damuwarsa da itama ke damunta. Hakan yasa cikin nata ɗan watanni bakwai sake fitowa sosai gamai kallo. Musamman yanzuma da take sanye da skirt na atanfa da t-shirt mai ƙarancin girma. Sai dai ta ɗara waɗanda take sawa a da kafin samuwar cikin da girmansa. plate ne a cinyar tata shima gab da cikinta ɗauke da green apples a kai, sai ɗaya dake a hannunta da ƙaramar wuƙa tana yanka tana ci a hankali.
     Sassanyan numfashi ya sauke da lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta. sai kuma ya shiga takowa har inda take dan ganin taƙi daina kallonsa. Gefenta ya zauna daf da ɗora hannunsa akan fuskarta ya juyar mata da kanta ta koma kallon lap-top ɗin.
         Cike da sanyin murya yace, “K da kike ɗaukar Lecture miye na zubamin ido kuma?”.
       Uffan batace masa ba, sai iska data furzar daga bakinta. Itama da sanyin muryar tace, “Lafiya naga ka dawo da wuri haka?”.
      Ajiyar zuciya ya sauke a karo na biyu, ya dora kansa a kafaɗarta tare da kamo hannunta dake riƙe da yankan apple ɗin ya kai bakinsa. Bata musaba ta saka masa itama. Sai da ya tauna ya haɗiye yana kallon lecturer ɗin shima sannan yace, “thanks you Sweet girl” ya ƙare maganar da kaima kuncinta sumbata, ya kuma tura hannunsa a rigarta yana shafa cikinta cike da ƙwarewar likitanci.
       Kamar koda yaushe kuwa sai ga cikin na motsi. Dan duk sanda zai masa irin wannan shafar sai kaji ya motsa. Har mita Aymah ke masa akan ita miyasa cikin baya mata haka sai idan yaso motsinsa da kansa yakeyi. Kokuma idan tanajin matsanancin yunwa nanma yana motsawa.
       A hankali yace, “Sheikh ɗin Daddy ga daddy ya dawo gida. Ina fatan bakai fushi da canjawarsa ba?. kana kuma cikin ƙoshin lafiya zinarin zuciyata”.
     Fuska Aymah taɗan taɓe tana ɗauke kanta ta maida ga lecture ɗin da sam yanzu ma ba fahinta takeba ita. 
     “Jealous ɗin ya motsane madam?”. Yoohan ya faɗa a cikin kunnenta cike da neman tsokana.
          Hannu tasa ta ture nasa da zuba masa harara. “Tunda Jealous ɗin nakeyi mizai hana a ciremin na huta”. Gimtse murmushin dake neman kufce masa yayi yana taɓe baki da ɗage gira ɗaya sama. “Silly girl, ai idan kinga mun barki sai mun cika watanni tara da kwanaki tara ciff insha ALLAH. magajin Uncle na zuwa kuma wata ƙwallon zata kuma faɗawa rag.....”
     Lap-top ɗin da take shirin saukewa a jikinta yay azamar riƙewa dan yasan sotake ta gudu. “Oh am sorry sweetheart wasa nake fa ni. Mu mun isa miki gadara bayan yanzu kece boss ɗin gidanma, kammu bisa wuya Mie-mie. Nifa namazo miki da wani albishirne mai daɗi”.
      Batare data tanka masa ba ta sake yunƙurawa zata tashi. “ALLAH seriously Sweet girl”.
      Ajiyar zuciya taɗan sauke kaɗan. Sai kuma ta kallesa, “To ka bari naje na kawo maka ruwa”.
      “Okay harda abinci. dan yunwa nakeji”.
    “Ai baka da kaso anan gidan malam”.
  Tai maganar tana shigewa kitchen. Murmushi yayi mai faɗi daya jima ba'a gani a fuskarsaba. Ya jingina da kujera yana furzar da zazzfar iska. Shi kaɗai yasan mi yakeji a ransa. Yana daurewa ne kawai saboda fahimtar halin da yake ciki na ƙuntata ta itama. Shikuma bayason haka kodan yanayin da take ciki........
      “Uhyimmm! An tafi tunanin ko?”.
Saurin dubanta yayi yana ƙoƙarin canja yanayin fuskarsa, Aymah da idanunta suka cika da ƙwalla ta ajiye tiren data ɗoro masa plate ɗin abinci  da ruwa sai kofin lemo ɗaya. Saurin riƙota yayi ganin zata gudu. Ya ɗorata a cinyarsa duk da tanata ƙoƙarin ƙwace kanta ga hawayen sun fara sauka a kumatu da gudu. Matseta yay da ƙyau ya lumshe idanunsa, tun tanason ƙwatar jikinta harta haƙura tayi luf a jikinsa tana shashshekar kuka da sauke ajiyar zuciya.
      “Am sorry Zeeynab. I'm very sorry. Nasan tabbas ina ƙuntata rayuwarki da laifin da banakiba. Nima bada son raina bane, ina cikin tashin hankaline mai tsananin ruɗani Nu'aymah.......”
     “Shine ka zaɓi ka ɓoye min saboda ni banda matsayin sanin sirrinka? Amma ni har sirrin daya kasance na family ɗina mun baka dama ka shiga tsundum saboda baka darajarka, sai ni da.......”
       “Shiii!!!. Wlhy bani da wani sirri a duniyar nan sai ke Nu'aymah. Da ana buɗe zuciya ma'abocin kallo yaga sirrin dake cikinta dana buɗe miki tawa kin gani Zeeynab. Da kinsan wacece ke a gareni da dukkanin tasirin da kikayi a rayuwata da bazaki taɓa yin tunani irin wannan ba. Amma kiyi haƙuri nasan da laifina. Laifina shine ɓoye miki damuwata. Bana ɓoye miki dan baki isa bane, na ɓoye miki ne saboda al'amarine mai girma a gareni. Ki tayani da addu'a ke dai kinji. Ki kuma cire komai a ranki, ki yarda ke ta dabbance ga mijinki. Bakiga duk yanda kika rameba, hakan na tayarmin da hankali.....”
      “Yah Yoohan amma ai......”
“Oh my Cutie karkice komai Please. Yanzu dai mu ajiye wancan batun bashi da wani muhimmancin cigaba da hargitsa mana rayuwa da tunani ok?. Ina miki albishirin zuwa Nigeria gobe insha ALLAHU ”.
       Duk da kewar ahalinta da ɗokin son zuwa garesu da takeyi sai taji kamar tafiyar bata lafiya bace, musamman da tasan yace itada 9ja ɗin sai ta shiga watan haihuwa lokacin sun sami hutun ƙarshen shekara da Christmas.......
     “Tunani again baby?”.
Numfashi ta kawo tana kallonsa. Kallo irin na tambayoyin da baki ya gaza furtawa.
      “To ko a fasa nayi tafiyata kawai ni kaɗai”.
      Da sauri ta girgiza masa kanta alamar a'a. Ya ɗan murmusa da sumbatar laɓɓanta. “Karfa kisa komai a ranki surprise ne kawai”.
       Duk da bata yarda da shiba haka ta shanye abinta a rai. Sai dai ta masa maganar karatunta yace babu damuwa ko suna a can zata cigaba da ɗaukar lectures ta online ɗin. Daga haka suka fara shiri a ranar, duk da daima bawani sun haɗa kaya bane dan bama zasu tafi da kayanba tunda akwaisu acan babu buƙatar hakan.
     A dai ranar duk wani abu da zai iya lalacewa sun fitar da shi. Suka ɗan fita shopping na abinda zata iya buƙata saboda lalurarta. Ranta cike yake da ɗokin Isa ga ahalinta bayan rabuwa da su tsawon watanni tara. A gefe kuma cike take da fargabar sakamakon abinda zataje ta tarar.

*_WASHE GARI_*

        Washe gari safiyar juma'a jirgin su Nu'aymah ya sauka a ƙasar haihuwarsu batare da kowa yasan da zuwan nasuba. Sai da taimakon Yoohan ta sakko a jirgin saboda ƙafafunta da sukai mata tsami da kumburi. Sai faman taɓe fuska take kamar zatai kuka. Shi kam dai ga tausayinta ga dariya na cinsa a rai. a zuciya ya ayyana, ‘Abufa yazo ga ma'iya’.
        Bayan shigarsu texi taji yace a kaisu hotel. Ai babu shiri ta kallesa, “Hotel kuma Yah Yoohan? Gidan papa ɗin fa?”.
      Cikin jin zafin dake taso masa a rai ya girgiza mata kansa. “Zamuje, amma yanzu muje ki huta ko?”.
       Hankalinta tashe akan tunawa da hoton nan da sauri tace, “A'a ni dai gaskiya inba gidan papa ba sai dai ka sani a motar kano na wuce. Yaya gamu da gidan iyaye mu kama raɓe-raɓen hotel kamar wasu marasa galihu. Kayi haƙuri gaskiya ni dai bazanje hotel ba”.
      Duk yanda yaso lallashinta akan suje hotel ɗin dan shi bayason zuwa gidansu. Ko sha'awar kallon fuskar Momy bayayi sam. Amma Nu'aymah ta tubure duk da bawai dan tanason zama gidan bane itama. Tana son sujene saboda hoton nan. Gara suje tun a yau ta ɗauka kafin papa ya farga suna ƙasar tunda ya bada kwangilar kasheta. Daga lokacin da matsaloli suka fara kuma ai maganar hoto sai tasha ruwa.
     Badan Yoohan yaso ba dole yasa mai taxi ɗaukar hanyar anguwarsu dan kuka Aymah ta sanya masa rirus babuko kunya. Sam baya buƙatar damuwarta a irin wannan lokacin. Dan yama fahimci jininta yayi sama saboda wannan tafiyar mai nisa da sukayo. Daga haka kuwa bai ƙara maganaba, sai dai ya sakata a jikinsa kawai yana shafa bayanta alamar lallashi. Saiko faman cijar lip ɗinsa na ƙasa yake da ƙoƙarin danne abinda ke taso masa a rai.
         Har ciki mai taxi ɗin ya shiga dasu, koda maigadi ya leƙi yaga Yoohan sai ya koma da sauri ya buɗe gate ɗin ransa fal murnar ganinsu. Da taimakonsa Aymah ta fito yanzunma. yayinda gaba ɗaya Guards ɗin gidan suka rufu musu a ka suna kwasar gaisuwa bakin kowa a washe na murnar ganinsu. Zuciya kam fal gulma ganin Nu'aymah da ciki. Musamman ma Solomon daketa faman zare ido.
      Solomon ɗinne ya amshi ƴan kayansu dake a trolly ɗaya sai lap-top bag ɗin Yoohan. handbag ɗin Aymah kuwa tana a hannun Yoohan ɗin ɗayan hannunsa kuma riƙe da nata.
      Da Gebrail suka fara cin karo zaune a dining yana lunch ɗin daya makara baiyiba. Idonsa na sauka a kansu kuwa ya sarƙe da abinci har sai da Blessing ta fito daga kitchen a guje dan jin mahaukacin tarin da yakeyi. Ko kallon inda yake kuwa Yoohan da Aymah basuyiba.
     Wani bala'in waro idanu Blessing tayi tare da daka tsalle gefe hannayenta duka a saman kai tace, “Heeyyy!!! Ahhhhhh!! Emiiii!!!”.
     Dariya ta bama Aymah sosai. Hakan ya sakata darawar kuwa. Yoohan kuwa daya zaunar da ita a kujera ko kallon Blessing ɗin baiyiba. Sai durƙusawa yay a gabanta ya kama ƙafafunta ya zare takalman da take sanye da su masu taushi, amma saboda tsabar hawa da ƙafar tayi sun manne mata har sunyi mata sayi. Matsa mata ƙafar ya farayi a sannu-sannu ransa fal tausayinta duk da yasan bawai wata matsala bane. Yanayine kawai da wasu masu cikin kan shiga.
       Ihun Blessing ne ya fito da Joy da Miracle daga ɗaki suma a guje. Sai ga Victoria dasu Favour da har yanzu su suna abuja basu koma ƙauye ba. Makaranta ma Yoohan yace zai duba musu anan, sai kuma aka samu akasi wancan matsalar ta faru Yoohan yabar ƙasar babu shiri.
         Da gudun bala'i su Destiny sukayo kan Nu'aymah da itama take kallonsu fuskanta washe da dariyar Blessing data gama kwasa... 
     A wani zabure Yoohan ya miƙe yana dakatar dasu, amma ina sukam idonsu ya rufe yau saboda farin cikin ganin auntynsu da kullum suke nacin son dawowarta. Gata kuma da ciki zata haifa musu baby a gida.
      Goshi kawai Yoohan ya dafe yana faɗin, “Oh GOD!”.
          Itako Aymah da dama ba hankalinne ya gama isartaba oho. Tuni ta tarbi ƴan yaranta da suka nuna mata ƙauna zalla a gidan babu algus. Sai da Yoohan yaga lamarin nasu bana ƙare bane yasa hannu ya fara ɗagasu ɗai-ɗai daga kan Nu'aymahr. 

       Ihun su Destiny ne ya farkar da mama debora a barcin da takeyi. Ta fito jikinta na rawa dan ta ɗauka wani abunne ya faru da yaran. Kaɗan ya rage bata bangaje su Joy da Miracle tai suman gigitaba ta tarota. Kota kansu batabiba ta fara sauka a benen da gudu zane a hannu.
     Wani bala'in waro ido tayi akan Nu'aymah tana faɗin, “Jesus John matarka ne da ciki? Cikin jikana ɗanka. Kaima zaka haifi yaronka John ?”. Sai kuma ta nufeta cike da Sassarfa. A take annurin fuskar Aymah ya ɓace ɓat, hakama Yoohan kallon kakar tasa yake yaga mizatayi. A mamakin kowa sai mama debora ta fashe da kuka tana rungume Nu'aymah. Sai kuma ta durƙusa ƙasa ta ɗaura hannunta akan cikin Aymah tana sambatun zance da yare wanda sam Aymah ba ji takeba. Sai dai yanda taga Yoohan ya langaɓe kai yana kallon kakar tasu fuskarsa da murmushi ya sata fahimtar ba mummunan abu mama debora ke faɗi akan gudan jinin nasu ba. Tabbas duk wanda ya kalli mama debora a wannan lokacin yasan farin cikine na gaske tattare da ita. Ba komai yay silarsaba kuma sai cikin jikin Nu'aymah ɗin. Dan kanta batasan yaya akai ƙaunar cikin ta saukar mata ba lokaci ɗaya tare da Nu'aymahn kanta. (Nace Ƙarfin addu'a ce mama debora). 
     Tana faman sharar ƙwalla ta kamo hannun Yoohan ta zaunar a kusa da Nu'aymah. Ta haɗa hannayensu cikin na juna sannan tai Kneeling a gabansu tare da rufe idanunta duka ta ɗaga hannaye sama ta fara raira waƙar addu'a da yare tana hawaye, ganin hakan yasa su Victoria ma durƙusawa tare da Blessing suka fara tayata suma duk idanu a rufe.
      Cike da zaro idanu Nu'aymah ta kalli Yoohan kamar zatai kuka. Dariya taso kufce masa. Amma sai ya gimtse yay murmushi kawai. A cikin kunnenta yace, “Karki damu addu'ar kariya sukema baby dakema ALLAH ya saukeki lafiya cikin ƙoshin lafiya”.
     Duk da tasan su ba musulmai bane ta ɗanji sanyi a ranta tunda ba wani tsafi baneba dai. sai kawai ta ɗora kanta a gefen hannunsa tana mai addu'a a ranta itama ALLAH yasa sunada rabon musulinci. Dan tabbas yau taji gaba ɗaya haushin mama debora da takeji ya kwaranye. Dama ance mai ɗa wawa.
     Bayan sun gama addu'arsu sun zauna, mama debora nata wani ji da Nu'aymah. Ita dai abin har dariya yake bata. Hakam Yoohan dariya kakar tasa ke basa da gaske. Ta dungure masa kai tana faɗin, “Mara mutunci. kasan matarka nada ciki baka taɓa faɗama kowaba. Yarinyata watansa nawa?”. Ta maida maganar kan Nu'aymah bayan ta zubama Yoohan dake kumbura mata fuska saboda mangarar masa ƙeya da tayi harara.
      Haka kawai sai Aymah taji nauyin faɗa. Sai Yoohan ɗinne ya bata amsa. Sai kawai ta tashi ta kama rawa tana waƙar yarensu irinta tsoffi.
      A wannan yanayin papa da Madam Chioma da basa gidan suka shigo suka samesu. Gaban Nu'aymah yay mummunan faɗuwa. Da sauri ta shiga karanto addu'a a cikin ranta. Sannan ta yunƙura ta miƙe kamar yanda taga Yoohan ya miƙe fuskarsa a tsuke saboda ganin Momy.
      Da wani irin kallo papa kebin Nu'aymah da cikinta. madam Chioma kam Yoohan take kallo kamar wata tsohuwar mayya. Dan sam hankalinta bai kai kan Aymah ba tukkunna.
    Cike da farin ciki Mama debora ta nufi papa tana rera waƙarta da ke nuna tana a tsantsar farin ciki na haƙiƙa, hannunsa ta kamo ta nufi inda Nu'aymah take. Da sauri Madam Chioma takai dubanta inda mama debora ta nufa da Papa. Aiki idanunta sukai mata mummunan gani. Da tsanin gigita ta furta, “What??! Impossible!. Na rantse da ALLAH impossible!!!”. 
      A kusan tare kowa dake a falon ya kalleta, sai kawai ganinta sukai a ƙasa ta sulale sumammiya.
      A guje su Destiny sukayi kanta da papa. Yoohan kam fuska ya kauda gefe cike da ƙunar zuciya. Nu'aymah da tasan ba sonta madam Chioma keyiba dama can sai bata ɗauki hakan komaiba face ƙiyayyar da take nuna mata dama can.
     Mama debora kam wani irin taɓe baki tayi da faɗin, “Aiko Chioma zaki mutune a haifamin jikana duniya. Kujimin yarinya da baƙin halin baƙin ciki. Ke sanda kika haifi John nayi miki hassada ne? Bandama inada zuciya me ƙyau ai saina saka ayar tambaya a kanki dan Yoohana baya kama dake, nayi shirune kawai dan yana kama da yarona, amma kekam ai kamarma ba ɗanki ba. Sai shi yanzu zaki baƙin ciki matarsa zata haifa masa ɗa. Kema sai kinji abinda naji na rabani da ɗana da kikayi......”
      A guje Blessing ta kawo ruwa aka yayyafama Madam Chioma. Tako fasa wata razananniyar ƙara da miƙewa zaune tana nuna Nu'aymah. “Wannan ba cikin yarona bane, kufitarmin da ashawo ɗinnan a gida, na rantse da ALLAH john wannan ba cikinka baneba. Dan hakan bazata taɓa kaswncewaba. Idan baku fitarmin da ita a gidaba zan kasheta. Ku kaita can ta nemo uban cikinta dan bana John bane. Darling narsantse damfararmu yarinyar nan zatayi cikin nan bana John bane. Sun tsafemin yaro sun rabani da shi. Yanzu zasu manna masa cikin kuma da ba nasab.......”
        Yanda take surutan zaka ɗauka bata da hankalima sam. Yoohan da takaici ya kume yaja hannun Nu'aymah suka haye sama abinsu batare da yayi ko tariba. Mama debora ma wani dariya da ihu ta sanya tana tafa hannaye. “Chioma kishi da matar ɗanki yasa kin haukace gaskiya. Tunda ni kakar John na yarda cikinsa ne koke da goshpower kukaƙi yarda nasan kishi ne. Yanda nasha baƙin cikin rabani da ɗana da kikayi kema sai kinsha fiye da wannan baƙin cikin na rabuwa da John. Wuuuuuuu!!! She she Shem!!! Wuuuuuu!!!! Hhhhhhhh!!!! Anji kunya uwa mai kishi da matar yaronta!!!!”.

        Hankalin papa ya sake tashi da abinda mahaifiyarsa keyi. Dan har cikin zuciya shima a kiɗimen yake game dayin tozali da wannan cikin da ko a labari bai taɓa sanin akwaishi ba.  Lallai wannan shine lokacin daya kamata a fara yaƙin na gaske. Dan tura takai bango anzo dai-dai wajen.
     Madam Chioma kam ihu takeyi da kururuwa har su Yoohan dake sama na jiyota.
       Idanun Aymah da a yanzu sam batason yawan hayaniya cike da ƙwalla ta kalli Yoohan daketa kai da kawowa a cikin falon. “Yah Yoohan Please ka barni na wuce kano kawai zaifi. Wannan wane irin tashin hankaline? Maimakon ciki ya zama abin farin ciki sai kuma a maidashi tashin hankali? Kayi haƙuri mahaifiyarka ce, amma ina tsoron ta cutar dani nikam gaskiyar magana”.
        Kallonta kawai Yoohan yake ransa na ƙara zafafa. Sai dai sam baiji zafin kalamanta ba, dan yasan gaskiyarta take faɗa. Shi kansa a yau ɗin nan ya sake shiga ruɗani dangane da halin mahaifiyar tasa. Wace irin uwace ita? Miyasa halayenta suka banbanta dana sauran iyaye? Tunba yanzuba wasu abubuwan nata suke dama masa lissafinsa da zurmasa a yawan tunani. Sai dai bai taɓa zaman musu fashin baƙiba saboda karta munana a cikin idanunsa. A wannan karon kam yaji bazai iyaba, dolene ko yanaso ko bayaso yasan dilin da yasa mahaifiyar tasa zafafa abubuwa akansa bayan kuma bashi kaɗai bane gudan jininta........
       “Yah Yoohan maganafa nake”.
Nu'aymah ta dawo dashi hankalinsa saboda riƙe masa hannu da tayi. Nannauyan numfashi ya sauke tare da rungumota jikinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya. Sunkai tsahon mintuna uku a haka sannan ya ɗagota, fuskarta cikin tafin hannayensa yana mai kallon ƙwayar idanunta data cika da hawaye. “Nima nafi aminta da tafiyarki Kano baby love, amma ina roƙonki kiyi haƙuri da safe idan ALLAH ya kaimu sai mu wuce kinji. Karkuma ki damu da zantukan Momy babu abinda zatai miki ɓacin rai ne kawai yasata faɗinsu itama kinji Heartbeat ɗina”.
      Duk da bata gamsu baneba sai ta ɗaga masa kanta dan babu abinda take hange a cikin idanusa sai tsantsar tashin hankali da damuwa, itakuwa indai akan iyayensane bazata bari ya shiga tashin hankaliba insha ALLAH.
     Yaji daɗin yanda ta nuna ta amince. Dan haka ya zaunar da ita duk da akwai ƴar ƙura a falon. Fita yay da kansa. Bai iske Momy ba da papa a falon, da alama sun shige daga ciki. Sai mama debora dake waya tana masifa da alama da ɗaya a cikin su momy Destiny take wayar, dan tana faɗa mata abinda ya farune. 
      Baibi takantaba itama yay kiran Blessing dasu Destiny suzo su musu gyara. Tare ya koma dasu, ya zauna yana mammatsama Aymah ƙafa daya tarar tana matsawa, su kuma suka fara aikin gyaran.

        Koda suka kammala ɗakinsa ya janyeta sukai wanka a tare. Suna fitowa babu jimawa Blessing tai knocking. Jallabiya ya zura ya fita danya duba wanene?. Samunta yay tsaye da ƙaton tire ɗauke da abinci. Hanya ya bata ta shiga. Ta ajiye tiren a dining sannan ta fita kanta a ƙasa. Ƙofar ya maida ya rufe, yaje ya ɗauki tiren ya nufi ɗakinsa da shi. 
        Nu'aymah na kwance a gado ko towel ɗin jikinsa ta kasa cirewa saboda gajiya da barcin dake ci mata idanu. “Kefa yanzu kin zama raguwa Sweet girl. Tashi to ga abinci”.
      Tashi tai zaune fuskarta da murmushi itama. Tace, “Duk ba ɗanka bane ya maidani hakan? Nida naci burin duk randa nazo 9ja yawo sai inda ƙarfina ya ƙare. Amma gashi tun ba'aje ko inaba lalaci ya fara mamayeni”.
     Ƴar dariya yayi yana miƙa mata t-shirt ɗinsa mai girma sosai. Ta amsa ta saka sannan tazo inda yake zuba abincin. Tasan Blessing ce tai girkin shiyyasa zataci. Da taimakon Yoohan kuwa taci ta ƙoshi tai nak, shima ta bashi yaci sai dai kaɗan yaci dan sam zuciyarsa bata cikin jin daɗi. Yana dannewane kawai danya ƙarfafa Nu'aymah. 
     Suna gamawa gadonsa ta haye ta kwanta saboda uban barcin dake cimata idanu. Bai hanataba, saboda shima yafi buƙatar tayi barcin a yanzu. Babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay gaba da ita.

_________★

      Tunda Blessing mai kawoma Omar rahoton gidansu Yoohan ta kirashi ta sanar masa da abinda ya faru game da isowar su Yoohan ɗin hankalin Umar yay ƙololuwar tashi. dan shi kansa da yasan Yoohan gidansu zai wuce da Nu'aymah ba hotel ba ko kano da bazai bariba. Dolene shima yau ya kwana abuja kuwa dan harga ALLAH lamarin papan Yoohan yanzu tsoro yake bashi harma Momyn, bai ƙara tsinkewa da al'amarinsu ba sai akan abinda ya faru tsakanin Yoohan ɗin da Momy. duk da su hasashe sukeyi tunda su su Blessing bawai sunga komai baneba akan idonsu.
       A take ya bincika ko akwai jirgi mai tashi zuwa abuja. Yakoyi sa'ar samun mai tashi nanda sa'oi biyu, dama shekaran jiya ya baro Abujan ai. Bai kira Yoohan ba, dan yafi son ya gansa tsulum kawai a bazata.

___________★

        Shiko Yoohan yana samu Aymah tayi barci saiya fito zuwa sashen papa.  Zaune ya samesa a falo yana waya. Yana ganin sa kuma ya yanke wayar. Ko a jikin Yoohan, dan ba wannan ne ya kawosa ba.
     Zama yay a kujera, batare da ya dubesa ba yace, “Good afternoon”.
      Papa ya danne abinda ke a maƙoshinsa da ƙyar ya amsa masa. Ya ɗora da faɗin, “Saukar yaushe haka babu labari. Aini nazata yanzu ni narigada na haifama Sheikh Sooraj ne kai?”.
       Shiru Yoohan yayi baiyi magana ba. Hakan sai ya ƙara harzuƙa papa matuƙa. Cikin tsagwaron masifa yace, “Ina magana da kai kamin banza. Wato na fahimci dama nika maida ɗan iska game da cewar wani aiki kakeyi akansa. John dolene yau insan minene tsakaninka da Sooraj?”.
        A matuƙar ɓacin ran da Yoohan shima baisan dalilinsaba, cike da suɓutar baki yace, “Papa nima inason sanin shin da gaske Momy itace ta haifeni? Dan ban taɓa jin mai halin uwa irintaba. Inhar ka amsamin wannan tambayar ni kuma na maka alƙawarin sanar maka alaƙata da Uncle Soorajidden Hashim jibiya. Sannan kama matarka gargaɗi, wlhy inhar wani abu ya samu cikina ko matata a gidan nan komaima zan iya aikatawa..”
     Yana kaiwa nan ya miƙe fuuuu ya fito yana huci. Da sauri madam Chioma dake bakin ƙofar tsaye tai baya ta bashi hanya cikin matuƙar rawar jiki da tsagwaron tashin hankali. Dan taji komai daya gudana tsakanin papa da ɗan nata.
         
       Wani irin zufar tashin hankalice ta shiga karyoma papa. Jikinsa na rawa ya zamo ƙasa daɓas kan carpet ya zauna. Gaba ɗayama duniyar sai take juya masa. Yau John ɗinsane ke kallan cikin idanunsa yana faɗa masa magana irin haka babu kunya babu tsoro. To tayaya hakan ta faru? Minene kuskurensa? Karfa ace lokacin da yake jira domin nasara ne ke shirin masa juyen ruwan hadarin da ba'a tsammaci zuwansa ba. cikin rawar jiki ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa batare da ya kula da madam Chioma dake a tashin hankalinba itama. A gurguje yay shiri ya fito daga ɗakin. Idonsa a rufe ya sake bangaje madam Chioma ya wuce dan harga ALLAH bai gantaba yanzuma, idanunsa har wani yana-yana suke masa saboda jirkicewar ƙwaƙwalwa dana tunani...........✍
      
    
     
ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[7/6, 9:38 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 72

...........Washe gari bayan sallar asuba Nu'aymah ta ɗorama Yoohan karatu kamar yanda suka saba. Daga haka ya shiga ɗakin motsa jikinsa. Ita kuma sai tayi amfani da wannan damar ta shiga ɗakinta domin ɗakko hoton nan. Duk da ta jima bata shigesaba ta fahimci an canja mata zaman wasu abubuwa da dama. Wasuma babusu. Bata bar hakan ya dametaba ta nufi Wadrobe direct inda ta ajiye hoto. Sosai gabanta ya faɗi ganin yanda kayanta suka koma a harmutse ba yanda tasan sukeba. Cikin gigita ta shiga tiɗosu ƙasa tana faman zazzagewa. Sai dai kamar da wasa babu hoto babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, har takaita da duba indama tasan bata ajiye ɗinba amma ko mai alamarsa babu.
        Jagwab ta zauna a bakin gado tanabin ɗakin da kallo daki-daki, dan sai a yanzune ma harmutsewarsa ba yanda ta barsaba yake dawo mata a zuciya daki-daki. Yoohan ta fara kawowa a zuciyarta. Sai kuma ta girgiza kanta dan bata tunanin zai mata bincike. Can ƙasan zuciyarta yace, ‘Omar ne. Bashi kika sanarma maganar hotonba’. Nanma da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. Gebrail. ‘Kai bazai zama shiba. Dan shi manufarsa daban data masu hankali. Wannan bashi da man kai akan hakan’. Madam Chioma. Nanma a fili tace, ‘Kai ina bana sata a wannan layin dan kanta baya ja tacika kidahumanci kamar kifi’. ‘To wa zan zarga?. Ko dai papa ne?’. Mikewa tai da sauri tana kaɗa kanta hannayenta duka biyu a saman cikinta. ‘Lallai tabbas shine abin zargina, musamman daya kasance ya riga yabi diddigina akan shigar masa ɗaki da nayi, zai iya kasancewa tunaninsa ya basa zuwa nan yamin bincike. Shin minene wannan mutumin ke ɓoyewane akan mijina? Lallai ya kamata na sani kafin na sake barin ƙasar nan’. Sai kuma ta dafe goshi cike da damuwa. ‘Hoto shine kawai hope ɗina. Gashi yanzu ɗan barahazar ya sace min, bayan na gama baza bayani wajen Abbana da wannan Umar ɗin. Kenan dolene na sake satowa. (Idan bai ƙonaba ko?) zuciyarta ta ayyana mata. Karan farko da matsanancin tsoro ya risketa. Da sauri ta fita a ɗakin zuwa can cikin gidan. Gidan shiru alamar masu gidan babu wanda ya tashi kasancewar weekend ne. Kitchen ta nufa. Tako iske Blessing kawai tana haɗa breakfast kamar yanda tayi hasashe.
       Ko gaisuwar Blessing ɗin bata amsaba taja hannunta suka shige cikin store. Sai da ta leƙa ta tabbatar da babu kowa sannan ta tura ƙofar store ɗin ta rufe ta juyo ga Blessing da jikinta harya fara rawa. “Please ki nutsu, ba wani abu bane tambaya zan miki, ina fatan kuma zaki bani amsa kamar yanda kike bama Omar... Oh sorry Richard”.
      Cike da tsoro Blessing zata fara rantse-rantse Aymah ta tsaidata......
      “Karki wahal da kanki wajen mani rantsuwa nasan komai daga wajensa. Inason nasan zuwan Richard nawa gidan nan?”.
     Da tsoro sosai a fuskar Blessing tace, kusan bakwai”.
          “Dama can anan yake sauka kenan tunkan aurena da Yoohan kokuwa a yanzune yake sauka anan?”. 
      “Eh dama yana sauka gaskiya, amma sai Oga yana ƙasar”.
     Jimm Nu'aymah tayi alamar tunani, sai kuma tace, “Mikike tunanin yana zuwa yi nan gidan?”.
    Cike da tsoro sosai Blessing ta buɗe ƙofar kaɗan ta leƙa, hakan yasa Yoohan daya biyo Aymah yake a laɓe saurin komawa ya lafe a bango. sai da ta sake tabbatar da babu kowa sannan ta dubi Aymah murya can ƙasa sosai. “Na yarda dake sosai Aunty na, dan tun a zuwanki gidan nan na fahimci ke mutuniyar kirkice wlhy. dan haka zan sanar miki komai duk da nima ba komai ɗin na saniba”.
     “Okay ina saurarenki”.
“Tun bayan wucewarku Austria nakeji wasu maganganu masu gidan nayi a kanki. Dan akwai randama na taɓajin an bada kwangilar kasheki ta hanyar likitan da zasu miki aiki. To sai dai kwanan mutuwarki bai rigada yazoba dan ke ƴar baiwane. Sai akazo baki mutuba. Su boss sunje dubaki, bandai san miya faruba bayan dawowarsu Uncle Richard naga ya nacema zuwa gidannan. Sanan yakan sani na masa wasu abubuwa akan boss ko madam ɗin gidan nan. Sannan ko baya gida zai kirani yaji mi akayi ko mi ya faru. Badai komai nake fahimtaba gaskiya, tunda banida hurumin yin komai. Sai dai matsalar dana fuskanta shine randa su papa suka shiga sashenku ita da Solomon da Madam. Sun miki bincike a ɗaki sai dai basu sami komaiba suka fita. Bayan hakan Uncle John yazo ƙasarnan yaga yanda akai miki da ɗaki shine ya zane Gebrail a tunaninsa shine ya shigar miki. A zahiri papa baicema Uncle John komaiba akan dukan Gebrail. Amma bayan barinsa gidannan ba ƙaramin rikici akayiba tsakaninsa da maman madam dama madam ɗin. Shima kuma papan naji yana wasu maganganu tsakaninsa da Brothers ɗin nan nasa wanda ban ganema kansuba sam. Wanann rikicin ne ya saka su Maman Destiny barin gidan nan. Dan sun nuna goyon bayan Uncle Yoohan fiye da Gebrail. Shine yasa akai rikici duk suka wuce. Bayan nan kuma sai Uncle john ɗin da yazo last time madam ɗin gidan nan ta shigar masa ɗ.........”
      Da sauri Yoohan dake a laɓe ya rin tse idanunsa tare da shiga kiran sunan Nu'aymah tamkar ya shigo nemantane. Rikicewa sosai Blessing tayi, amma Aymah ko'a jikinta saima ɓata fuska tayi ta buɗe ƙofar bayan ta ɗebo noodles guda biyu. 
       “Oh Sweet boo ganinanfa a store. Nazo amsar noodles ne a wajen Blessing shine take nunamin inda take”.
            Cike da mamaki yake jinjina wayonta. Amma shima sai ya waske yana mai dafe kansa da faɗin, “Kinsa duk na ruɗe na fito ban gankiba a gaba ɗaya sashen”.
      “I am sorry Hubby”.
“Silly girl yana iya dake. Yanzu yaya za'ai da Noodles ɗin?”.
     “Zan dafa ne anan”. Ta faɗa saboda son ya barta ta ƙarasa jin zance a wajen Blessing.
     Fahimtar hakan da yayine ya sakashi hayewa saman kitchen cabinet ɗin yana cewa, “Okay dafa to mu wuce. Dan kinsan akwaima fa inda zamuji ga lokaci nata ƙurewa, Omar ma jiranmu yakeyi tuni. Koma kibama Blessing ɗin ta dafa miki muje ki shirya data gama sai kici kawai”.
     Duk da Aymah bataso hakan ba sai ta amince kawai. Dan ita bama cin noodles ɗin zatayiba sam. Blessing ta ƙwalama kira. Sai gata ta fito da sauri hannunta ɗauke da abinda zata dafa da rana irin dai shi ta tsaya ɗebowa. Sai dai kallo ɗaya Yoohan ya mata ya fahimci tsoron dake tattare da ita.
    Bata dahuwar noodles ɗin tayi suka fice. Gaba ɗaya hankali Nu'aymah akan Blessing yake. Amma Yoohan yay mata tsayuwar sojan badakkare aka komai tare sukayi. Koda suka fito Blessing ta kawo noodles ɗin catai ta ƙoshi. Sai Yoohan ɗinne yaci tare da Omar. Dama yasan baci zataiba ai. Dan tunda ta samu cikin nan tabar cin indomie sam.
      Koda suka gama ficewa sukai a gidan batare da sunbi takan kowa ba. garama mama debora sun haɗu da ita a falo tana shan shayi. Tako hanasu fita saida akaima Aymah addu'oi ita da cikinta. Dan tace ita yanzu ta daina yarda da madam Chioma a gidan sam😂🤣.

     Ita dai Aymah yanzu tsohuwar birgeta takeyi. Dan har suka bar gidan batabar murmushi ba akan abinda ya faru.
    Tafiyarsu ta ɗanyi nisa Omar ya fahimci ana binsu a baya. Shima Yoohan ya gani amma baice komaiba. Dan babu abinda zuciyarsa ke masa sai tariyar zancen Aymah da Blessing. Tunaninsa wane abu ne Aymah ke zargin an shigar mata ɗaki akansa ana nema? Sannan kuma ashe papa ne da madam Chioma suka shigar masa ɗakin mata hardama Solomon?. wane bincike Umar keyi akan iyayen nasa?  Mi Aymah ta shiga yi ɗakin papa a wancan karon daya dage kareta a wajensu amma hardayin ƙaryar taga wanda ya shiga ɗakin ashe itace?  Miyasa mahaifinsa yasa a kashe masa mata? Dolene yasan waɗanan tambayoyi a lokacin ƙanƙani insha ALLAHU.
    Da wnanan tunani da yakene yasa har Omar ya gudama masu binsu shi baisan yaya akaiba. Sai ganinsu kawai yayi a station ɗin su Jay.
         Aymah dai har suka shiga tana maibin wajen da kallo tare da jami'an tsaro. Ko ɗar batajiba duk da ta fahimci wajene bana wasan yaraba. Yau saɓanin ranar Office ɗin Jay aka kaisu direct, acan suka sami Dawood da Little bee da bily. Sai Afrah da adalilin zuwan Aymah Jay yasa akazo da ita. Dan ita karatun lauyanci takeyi batabi ayarin su little bee ba.
      Duk da a hoto sukasan juna ita da Aymah hakan bai hanasu gane junaba. Suka rungume juna kuwa cike da ɗoki dan sunyi sabo sosai ta chart da waya. Daga haka Aymah ta gaida little bee dake zaune tanata danne danne a Computer alamar miskilawan na kusa. Dan duk ihun dasu Aymah sukeyi ko kallo basu ishetaba, aikinta takeyi hankali kwance. Gaisuwarma a haka ta amsata. Sai daga baya ta ɗago ta kalli Nu'aymah sannan suka gaisa dasu Yoohan.
    Nu'aymah dai bata sake bi takantaba itama ta juya ta gaida Dawood da Miemaa data amsa mata da fara'a da kulawa, dan itama ta taimaka mata ta zauna a kujera. Daga haka ta gaida Jay da a kallonsa sai da gabanta ya faɗi. Duk da ba tsananin kamanni suke da Yoohan ba dolene kaga yanayin gittawar jini tattare a tsakaninsu. Duk da ba mutum bane shi mai yawan wasa saida ya tsokaneta kaɗan. Har hakan ya bama su Yoohan mamaki. Dan su dai ba taɓa ganin dariyarsa sukaiba tunda suke mu'amula da shi.
     Sai da aka lafa da gaishe-gaiahe Jay ya fara magana.
       “So ba shirita ne ya taramu ananba. Inason ku bani hankulanku nan gaba ɗaya. Da farko dai kece bakisan dalilin zamanmu ananba duk da mijinki ya tabbatar mana ta hanyarki yasan wasu abubuwan. Sai ko Afrah da sanin nata baida muhimmanci daga tushe duk da itama da taimakonta ne muka samu bayanan sirri game da gidanku. So yanzu little zata miki sabon bayani, ke kuma Afrah jeki waje ki jiramu”.
     Sosai Afrah ta ɓata fuska kamar zatayi kuka. Cikin magiya tace, “Abie Please ka barni dan ALLAH, wlhy nima zan taimaka muku da wani abun kaimafa ka sani. Duk da ba aikin nan nakeba so nawa ina muku aiki ta ƙarƙashin ƙasa”.
    Fuska ya haɗe zai mata magana Aymah da duk kwarjininsa ya cika mata idanu tace, “Abie dan ALLAH, indai hakan ba laifi bane ka barmin Aunty zanfi samun ƙwarin gwiwa nima”.
      Kasa cewa komai Jay yayi, ya kai dubansa ga little. Da wani style na ƙwarewar aiki taima mahaifin nasu alamar roƙon yabar Afrah ɗin. Dan itama tana hasashen tasirin zamanta a wajen.
     Ɗauke kansa kawai yayi ya maida ga Yoohan dake ta kallonsa kamar ya samu television. Sai kuma ya ɗauke ya sake maidawa ga little bee alamar ya bata damar yima Aymah bayani.
    Tsaf ta gama yima Nu'aymah bayanin komai. Dan haka taketa duban Yoohan da Umar cike da mamaki. Da damuwa a harshenta tace, “Amma Yah Yoohan baka gudun Abbana kar yaga ba'a ƙyauta masaba. Sam baya son laifin jama'ar gidan nan namu, shiyyasa yake ƙoƙarin maida laifukansu kuskure dan gudun lalacewar zuminci”.
      “Zeeynab inhar muka cigaba da bama Uncle goyan baya akan hakan tabbas sai an salwantar da ran ɗaya daga cikinsu ko ke ko Muhammad a wannan gidan naku. Dan ni nasan mina ganarma idona a Austria da wasu maban-banta wajaje dangane da ke”.
     Bata iya tace komaiba dan tasan gaskiya Yoohan ya faɗa. Bandama ALLAH yasa tanada sauran kwana a duniya ai da tun tana jinjira an aikata barzahu ɗin. Sannan shima Muhammad ɗin ai ansha gwada rayuwarsa a mabanbanta lokuta Abba na ɓoyewane kawai........
     Cikin katse mata tunani Jay yace, “Karki damu akan Sheikh, ni zan masa bayanin dazai gamsu akan hakan. Yanzu zamu tafine kai tsaye akan abinda ya taramu anan tunda kin gama jin bayanan farko. Dan dama munsa mijinki ya dawo dake ƙasarnan ne dan zamu ɗanaki a gidanku ne matsayin tarko. Dawood minene bayani akan binciken wayar matar nan da aka sakeyi?”. Ya ƙare maganar da maida hankalinsa ga Dawood.
       Takardun gabansa ya ɗauka ya fara bayani. “Sir bayanan sununa tabbas ana amfani da wayarta batare data saniba. Kamar maganar yin waya da mai aiki da aka turoma matar Yoohan anan Abuja, sam ba Rabi bace ke waya da Uwaliya. Mun tabbatar da hakane ta hanyar binciken ainahin muryar da aka samu a voice recording ɗin nan. Haɗine ta hanyar makirci babba na masu ilimin sani akan na'ura mai ƙwaƙwalwa. Suna amfani da wani app... Ne da aka saka cikin wayar matar, dama kowacce waya idan ta sake sai suke sarrafa wayar tata daga wajensu batare da ita ta saniba, suna barin mata bayanan abinda sukai da tasu wayar, dan ko an tashi bincke ita za'a zarga kai tsaye. Hakan yana nufin kenan tun fil azal da aka kawota gidan dama akwai manufa a ciki, kokuma daga baya aka fara amfni da ita. Waɗanan sune tatattun bayanai akan ainahin contact dake a wayar Rabi wanda suke aiki da saninta. Waɗanan kuma sune ainahin waɗanda ake amfani da ita ta wayar batare data saniba. Kuma insha ALLAHU zasu taimaka mana mu zaƙulo kosu wanene masu aikata hakan kamar yanda Abdurrahman Sameer Saifudden ya bamu tabbaci, dan shine yay wannan bincike gaba ɗaya tun daga ƙasar india. Ya kuma tabbatar mana idan ana buƙatarsa zai iya zuwa koshi ko abokan aikinsa yan uwan tagwaicinsa kenan”.
       Cikin jinjina kai Jay ya amshi takardun yana duban little bee. “Bilkisu! Minene bayanan wajenki akan zaman Afrah gidan?”.
      Juyowa Little bee tayi da kujerar da take a kai tana fuskantarsu. Yoohan ta sake kallo kamar yanda dama tuni shi take kallon a sace bisa ƙyaƙyƙyawan nazari datakeyi akansa tun farkon fara ganinta da shi.
     “Sir! Bayanan dake anan sun nuna wasu sunaye da Afrah ta rubuta akan zarginta, saboda wasu al'amura da suke aiwatarwa a gidan na marasa gaskiya. Akwai Rabi. Mai aikinsu, a yanzu tana a hannunmu. Sai Mai aikin sashen Addah, sai ita kanta Addah da tafi kowa kusanci da Umm a gidan. Sai Nasir wanda asali shi bama ɗan gidan bane yana zuwane lokaci-lokaci. da wasu sunaye a jerin ɗaliban Uncle Soorajidden ɗin. Ta tattara waɗan nan sunayen ne bisa dalilai mabanbanta da suka faru akan idonta da kuma yanda labarin yazo garemu. Zamu iya jin bayani daga bakinta gata nan idan da buƙatar hakan”.
        A yanzu kam bily ce tai wani gutun murmushi tana kallon Jay. Cike da nuna ƙwarewar aiki tace, “Boss niko kaga a duk jerin sunayen nan mutum uku kawai naba ayar tambaya. Sauran kuma inaji a jikina basa zaune a cikin gidan. Abinda yasa nai wannan maganar shine duk lokacin da za'a cutar da ita Nu'aymah akan yine lokacin wani taro a gidan. Hakan na nufin akwai mazauna gidan dake zaune a waje cikin tafiyar. Amma ƙasurgumin azzalumin yana nan cikin gidan tare da su ko akasin haka. 
     Murmushi Jay yayi a karo na farko. Ya sauke numfashi da ɗan buga pen ɗinsa akan takardar gabansa. “Tabbas komai zai iya kasancewa. Dan suma sauran ai hasahe mukeyi, tunda ga Rabi a hashe muka samota kuma sai gashi babu laifinta”.
     “Hakane kuma boss. suspect ɗinmu na gaba sune, Nasir, Ameer, Hamisu, Kubrah, Abdallah. Da iyayen su Abdallah n”.
     Da sauri Aymah tace, “momy!” cikin zaro idanu. sai kuma ta shiga girgiza kanta da sauri-sauri tana cigaba da faɗin, “Bazai kasance hakaba Momy. Uncles ɗina suna matuƙar son Abbana. Hakama Yah Abdallah na matuƙar sona. Bazasu cutar damu ba sai dai idan Nasir ne”.
     “Relax Nu'aymah. Muma bamun tabbatar bane hashene kawai. Dan dolene mu alaƙanta laifin nan da mafiya kusanci da iyayenki dake kanki, shiyyasa zamuyi amfani da wannan lokacin da mukasan duk ahalinki zasu taru a gida saboda bikin aure da saukar yaran gidan marayunku mu ɗana musu ke a matsayin tarko wajen damƙesu batare da sun fargaba.....”
        Yoohan ya katse Bily da cewar, “Humm tabbas Momy bana tantama akan hakan. Musamman akan Abdallah. Dan ta dalilinsa na sakama sauran ayar tambaya. Abdallah yayi fushi yabar Nigeria saboda ba'a aura masa itaba. Amma kuma a bayan fage yana a cikin ƙasar, dan yana yawan shigowa akai-akai. Sannan kuma yana bibiyar al'amarinta dani kaina. Dalilina na biyu a kansa shine wani business da yakeyi a ɓoye batare da sanin iyayen nasaba. Dalili na uku akwai harƙalla akan aurensa da yara biyu na gidan da aka aura masa dalilin sace Zeeynab da akai ranar wancan auren nasu. Ya saki yaran batare da ɗaya ta tare ba. Wadda ta tare ɗin bincikena ya tabbatar min da tasha wahalar zama da shi. Zargi na uku. Akan hotona da aka kai gidansu ni da ita. A yanda labarin yazo kakarsu bata bari su Abdallah sunga hotunanba a waccan ranar, amma daga baya sai hotunan suka zo hannun Abdallah harya kaisu office ɗina. Hakan na nufin bayan na hannunsu akwai wasu kenan dama a wajensu komi? Zargi na biyar, Abdallah yafi kowa ɗaukar zafi akan hotunan a gidan, duk da kuwa nasan Uncle da Umm sai sunfi kowa jin raɗaɗi da zafin hakan game da tilon ƴarsu. Amma sai ya nuna zaƙewa akan hakan harda kawomin abokinsa wai yay Arresting ɗina. Zargi na ƙarshe, miyasa a duk lokacin da akai tunanin ƙulla aurensu sai wani dalili ya ruguza shi?......”
       “Please Yah Yoohan ya isa haka mana. Miyasa dukanin zarge-zargenka zai ƙare akan Yah Abdallah? Kana kishi da shi ba shike nufin komai ka yaya ka aza a kansaba”.
      Sosai zantukan Aymah suka zafi zuciyar Yoohan, dan gani yake matar tasa tana goyen bayan tsohon saurayin natane kawai. Sai dai kuma uffan baice akan hakanba, yama ɗauke kansa daga gareta kawai.
     Karan farko little bee ta saki murmushi tana kallonsu. Sai kuma ta taɓe baki da faɗin, “Wannan faɗane da ya shafeku a gidanku Mrs and Mr”.
    Hararta Yoohan yayi, dan dama tunba yauba yana jin haushin yanda take zaman yimasa kallon ƙurilla a fakaice. Yana nuna bai gani bane kawai saboda kunyar iyayenta.
     “A'a bar hararata malami, ni yanzu saina sassafa ka a gaban sahibar taka babu ruwana”.
       “Ashe kuwa mijinki ma zai sassafu a hannuna tare da wannan miskilar fuskar taki mai ƙinyima mutane dariya”.
      Harara itama little ta zuba masa tana tsuke fuska. “Oh kace dama kullum cikin takaicina kake bana maka murmushi, to ƙwalelen kare da hantar kura”.
     Baki Yoohan ɗin ya taɓe da ɗauke kansa gefe yana cije lip. Dan saiya saita yarinyarnan akan layi kafin a gama case ɗin nan. shi babu ruwansa da wani ƴar-sandancin ta ehe. (Kuji ƙarfin hali irin na Yoohan. Da alama mafa little bee ɗin zata bashi shekara ɗaya a duniya, amma wai yarinya😂lol)
      Babu wanda drama ɗintasu baisa dariyaba. Sai Jay da Bily basu dara ɗinba a fili sai a zuciya. Sundaita kallonsu cike da nazarin suɓutar harsunan nasu. 
        Kai jay ya girgiza kawai yana katse little dake son ƙara magana. “Kunga ku aje wannan shirmen naku sai kun fita can sai kuyi, idan kunso ku sassafa kawunan naku munada likita a kusa da zai duba ku. Yanzu dai Yoohan dole a yau ɗin nan Nu'aymah ta wuce kano. Dan aikin nan banason ya shige satin nan bamu kammalashi ba. Maganar Abdallah kuwa na tabbatar jin Nu'aymah na Nigeria zaizo shima koda a ɓoyen daya saba ne. Yanzu zan baza jami'ai da zasu fara bibiyar lamarin motsin kowa na gidan idan ya fito. Shima Nasir ina buƙatar a jawomin hankalinsa yazo kano. Babu sanya a aikinmu, duk wanda mukaci karo da rashin gaskiyarsa zamu kamasane mu tuhumesa kamar Rabi. Za kuma mu maida Rabi itama dan wayarta zata taimaka mana sosai wajen zaƙulo abubuwa”.
     Cike da gamsuwa kowa ya amsa masa. Duk da kuwa Yoohan dai da alama baiso yin nisa da matarsaba. Amma ya fahimci hakan zai taimakesa gameda ƙudirin papa kuma a kanta. duk da kuwa a kanon ma wasu kurayen zata tarar. amma gara can akwai jami'ai masu sanya ido a lamarinta.

________★

     Koda su Aymah suka dawo gida bata ga Blessing ba. Hakama Madam Chioma da papa da alama basa gidan ma. Yara kawai suka tarar da Mama debora. Joy ta wuce makaranta, Miracle kuwa mama debora ke basu labarin wai ta haɗa kayanta ta koma gida.
     Ko a jikin Yoohan. Aymah kuwa yar dariyar shaƙiyanci tayi abinta ta wuce sama cike da tunanin ina Blessing ta shiga. Ɗakinta ta nufa direct, ta fara zame kayanta zuciyarta taf damuwa akan maganar hoton nan. Agogonta data cire ne ya faɗi ƙasa. ta ɗan matsa baya tana dubawa ta tillesa da ƙafa yay ƙarƙashin gado. Abin ya bata haushi, dan harta barsa akan yayta zama sai kuma taji tanason ɗakko kayanta dan Yoohan ya batashi matsayin ƙyauta a ranar da suka cika shekara ɗaya da aure. Fita tai ta ɗakko mopping stick dan Yoohan bai shigoba har yanzu yanacan tare da mama debora. Durƙusawa tai gaban gadon batare da damuwa da cikin dake gabantaba saboda wauta. Ta kunna fitilar wayarta ta haska. Da ƙyar ta iya hango agogon ta saka mopping stick ɗinnan ta turosa a hankali. Sai da yazo dab da ita ta fahimci harda wani abu take jawowa. Hannu ta miƙa danta jawosu duka ta kasa. Dole ta sake zungurowa da iccen mofa ɗin sannan suka fito. Jikinta har rawa yake wajen fara ɗaukar envelope ɗin ta buɗe. Tai wani irin waro ido na al'ajabi da mamaki. Batama san sanda ta ƙwaƙume hoton a ƙirjiba saboda murna. Jin an taɓa ƙofar za'a buɗe tai saurin sakin hoton ƙasa, kafin Yoohan daya shigo ya ƙaraso ta tura hoton ciki yanda bazai ganiba.
       Duk da ta masa alamun rashin gaskiya sai bai nuna yama fahimcetaba. Yay baya da fiɗin, “Oh ashe kina nan, bara na watsa ruwa saiki shirya kema zuwa biyar na yamma zamu wuce kano. Amma mi kikeyi ma a durƙushe anan? Bayan kinsan bake kaɗai bace?”.
     Miƙewa tai tana nuna masa agogon data ɗakko. “Kaga abinda na yadda nan na ɗakko”.
     “Ki kulafa, dan na fahimci har yanzu wautanki na nan”.
    Baki ta kumbura da iska batare datace masa komaiba. Shima sai ya juya abinsa ya fice kawai ya barta batare daya sake maganaba. Sai dai bai rufe ƙofaba. Da wannan damar ya samu zarafin laɓewa kozaiga mitakeyi. Aiko tana ganin ya fita ta sake duƙawa ta ɗakko hoton tana ambaton ‘Alhmdllh ya ALLAH. Da banga hoton nanba da bazan taɓa yafema duk wanda ya ɗaukesaba. Dolene nasan wacece wannan mai kama da mijina ɗin insha ALLAHU’.
     Dukkan maganganun Aymah a cikin kunnen Yoohan ne. Hakan yasa zancen tsaya masa a rai tare da son jin ganin hoton nan shima. Yayi kamar zai dawo sai kuma ya fasa. Akan idonsa ta maida hoton a Wadrobe. Tafiya yay ɗakinsa tunda yaga inda ta ajiye. Sai dai kamar tasan yana kallonta. Yana barin wajen ta ɗauke hoton ta sakashi a ƴar jikkar data haɗa kayan tafiya kano wai dan kar wani ya sake shigo ya sace mata. Tana shiga wanka Yoohan ya dawo duba hoton. Sai dai kuma komai kama da shi bai ganima. sai ma kamashi da Aymah taso yi ALLAH dai ya taimakesa ya gudu. 
      Haka suka kammala shirin wucewa kano mamakin atsabibancin Aymah na damun Yoohan, shi ganima yake ta gansa shiyyasa ta canjama hoton waje.
     Itako Aymah ranta fal baƙin cikin rashin ganin Blessing da Yoohan yasa tabar gidan har sai sun wuce dan bayason ta sanamar Nu'aymah abinda ya faru tsakaninsa da Momynsa.

*_KANO TA DABO_*

          Ƙarfe bakwai dai-dai jirgin su Aymah ya sauka a kano. Batare da sanin kowa daga ahalintaba har su baba malam. Sai da Yoohan yasa suka fara biyawa sukai shopping na tsarabar da zata kaimusu sannan suka wuce gidan.
        Ganin Aymah da Yoohan ya saka mai gadi buɗe musu gate mai taxi ya shiga har ciki. Nu'aymah zata fita da kwakwazo Yoohan ya riƙota yana girgiza mata kai. “Please kibi a hankali, a ganinama ba gara ki shige babu wanda ya san da zuwanki ba da safe sai kiyi musu surprise”.
    Baki ta ɗan tura gaba. Sai kuma tai saurin sakin dariya da cewa, “Yes Yah Yoohan kayi gaskiya kuma”.
     Murmushi yay mata da bata sumba a gefen kumatu. Daga haka suka fito a motar. Gidan shiru kowa yana a sashensa, hakan yasa Yoohan taya maigadi kaima Aymah kayanta bakin ƙofa. Sannan ya turata ciki ya sulale ya koma taxi ɗin suka fice. Dan hotel yake son guduwa kafin baba malam su fito massallaci su ritsashi.
     Umm na zaune a bedroom tana karatu da jiran lokacin sallar isha'i sai ji kawai tai an rungumeta. A firgice ta juyo dan harga ALLAH ta tsorata. Ta waro idanu sabida mamakin ganin wadda batayi zatoba. 
     “Nu'aymah wai kece da gaske?”.
Kukan murnar ganin Umm ɗinta ta saki tana faɗin, “Nice Ummna, I miss you so much”.
       Rungumeta Umm tayi da ƙyau a jikinta itama ƙwalla na cika mata idanu. Kai ɗa dabanne gaskiya. Sanin ba ita kaɗai bace yasa Umm tadata daga durƙuson da tayi a ƙasa ta zaunar da ita a bakin gado. Gaba ɗaya Aymah sai kuma taji kunyar Umm ta mamayeta, sai ta duƙar da kai ƙasa tana ƙara lulluɓe cikinta da gyale. Dariya abin ya bama Umm sosai. Sai dai bataiba. Saima tambayarta tai ina mijin nata?. 
   Kan Aymah a ƙasa tace waje ta barsa ita dai suna kwaso kaya shi da maigadi. Jin haka yasa Umm fita ta leƙa. Sai dai babu Yoohan babu dalilinsa sai maigadi kawai dake shigo da kayan ɗan barandar falonsu. Shine ke sanar mata Yoohan ɗin ya juya tare da mai taxi akan da safe zai dawo insha ALLAH.
      Kai kawai Umm ta girgiza ta koma ciki, inda ta iske Aymah ta fito daga toilet da alama fitsari tayo. Cike da kulawa tace, “Kinji mijin naki ya tafi wai zai dawo da safe. Dama kunyi dashi hakan?”.
     “A'a wlhy Umm, ni kawai yace na shigo zaije massallaci ne”. Tai maganar cikin ɓata fuska. Murmushi kawai Umm tayi ita dai, tace, “To kiyi wanka kawai sai na samo miki abinda zakici ke tunda shi ya gudu. Cike da kunyar Umm ɗin data aro ta yafama kanta ta amsa da to. Daga haka ta koma toilet ɗin danyin wanka.

         Babu wanda Umm ta sanarma da zuwan Nu'aymah a gidan sai hajjo. Sai ko Muhammad daya dawo massalaci ya ganta a bazata. Baba malam ma sai da ya sallami ɗalibansa ya shigo yaci karo da ita a falo zaune ita da Hajjo da Umm da Muhammad dake liƙe da ita.
     Tuni Nu'aymah ta manta da kunya, ta miƙe da sassarfa ta nufi Abbanta dake kallonta cike da kewa da so da ƙaunarta. Gabanta tai niyyar durƙusawa ya riƙota yana faɗin, “A'a mamana keda ke fama da kanki. Irin wannan zuwa haka na bazata”.
    Hannunta yaja ya maida a kujera sannan shima ya zauna. Kanta a ƙasa ta shiga gaisheshi cike da kewa. Shiko yana amsawa da kulawa. Abakin Umm yaji cewar Yoohan ya gudu. Dariya kawai yayi dan ya fahimci kunya Yoohan ɗin keji da alama.
        Haka sukayi murnarsu su huɗu kawai. Ganin dare ya farayi Hajjo taje sashenta danta kwanta. Aymah kuwa a ɗakin Umm zata kwana tare da Umm ɗinta data bar baba malam shi kaɗai.
     Aiko maimakon barci sai suka buɗe sabon babin hira ita da Umm ɗin, sai da suka kusan kai asuba sannan barcin ya kwashi Aymah, daga nan itama Umm tayi.

__________★

        Washe gari kam a bazata kowa yaga Nu'aymah a gidan. Kafin kace mi sun rikice da murna da hayaniya. Tun Aymah na ƙunshe-ƙunshen ciki harta saki jikinta ta shige cikin ƴan uwanta anashan shafta. Zuwa tashin hantsi kuwa sai ga Hajarah tazo gidan, dan ita dama tasan da zuwan nata. Rungume juna sukai cike da farin ciki. Yanda suka nuna ɗin har mamaki ya bama kowa. Dan gaba ɗaya salon shaƙuwar Adawiya da Nu'aymah ne ya koma kan Hajarah a yanzu.

      A ranar da yamma suma ƴan Abuja suka iso. Ganin Nu'aymah kuma ya matuƙar basu mamaki dansu da suke Abujan ko a labari basusan da zuwan nataba. Har Momy ma sai da ta kasa haƙuri tai complain ɗin cewar Yoohan bai ƙyautaba. Suna matsayin iyayen Nu'aymah amma yazo da ita har Abuja bai fara kaita canba sai dai suzo su ganta anan tsulum.
     Daga karshe dai Yoohan ɗinne da yazo gidan ya kare kansa akan wannan tuhuma. Dan Aymah bata iya cewa komaiba tunda itama tunanin zuwa can ɗin baizo mataba. Zumuɗinta kawai azo kano.
     Ya bama su baba malam haƙuri akan rashin tsayawarsa jiya. Acewarsa aikin gaggawa ne ya samesa shiyyasa bai tsayaba. Duk sun masa uziri akan haka. Sannan suka ɗora da godiya akan hidimarsa ga gidan marayunsu daketa ƙara nunkuwa a koda yaushe. Akan bikin nanma kawai da za'ai ba ƙaramin hidima yayiba.

      Washe gari baƙi suka fara cika gidan, ƴan katsina, ƴan lagos da sauransu, kowa kuwa yana sake yaba yanda Aymah ta ƙara girma da canjawa a cikin shekara ɗaya kacal. Gashi daga gani ansan ta samu lafiya yanzu. Sai dai fatan ALLAH ya sa ta sauka lafiya kuma.
    Da yamma sukaje can orphanage akai walima, anan ta haɗu da sauran yayunta su Kubrah. Tayi mamakin ganin yanda Aunty Kubrah ɗin dukta lalace. Harta kasa haƙuri ta tambayi aunty Hajarah. 
    Cike da damuwa Hajarah tace, “Humm Aymah ke dai ALLAH ya ƙyauta, zaman natane babu daɗi daga ita har mijin da kishiyar. Kwanaki ai kusan watanta biyu a Lagos wajen Abbah Musbahu. Sunyi faɗa ya daketa shine taje can”.
     Kasa magana aymah tayi saboda damuwa. Kodai babu komai Kubrah ƴar uwartace duk da a yauma ta nuna har yanzu ba sonta takeba.
    Duk wannan hidima da akeyi kuwa su Aymah zagaye suke da yaran Jay ta ko ina. Motsin kowa akan idonsu yake faruwa. Tun daga orphanage har cikin gidansu.

    Washe gari juma'a aka ɗaura auren amare ashirin da takwas maza da mata. Kowa ya kalli su baba malam yasan suna cikin farin ciki. Sai dai ai fatan ALLAH ya basu ladan hidimarsu ga marayun ALLAH babu gajiyawa.
    An miƙa amare ɗakunansu, daga haka baƙi suka fara raguwa sai na jiki kawai aka bari. Kamar yanda Jay ya samu tattaunawa da baba malam a ranar ɗaurin aure a yau suka yanke hukunci bisa shirinsu. Duk da kuwa da ƙyar baba malam ɗin ya yarda da buƙatar Yoohan, Jay, Omar ɗin. Dan basu ɓoye masa komaiba game da shirin nasu gudun kar a samu matsala.  
      Tun a yammacin ranar baba malam ya fara takalar Umm da batun mallakama Nu'aymah wasu kaddarorinsa dan yasan lallai mai musu laɓe na tare da su saboda tuna Nu'aymah tazo garin ya fahimci mai laɓen ya ƙara ƙaimi wajen yimusu. Ta riga tasan shirinsu, itama sai ta biye masa. Sai dai zancen bai tsahoba suka barshi akan zasu ƙarasa da safe dan lokaci baba malam nada uziri..........✍


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[7/6, 9:38 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 73

.............A yau kam su Nu'aymah da duk wanda yasan da wannan shirin sun tashi a shirye tsaf bisa yaƙinin tarkon da suka ɗana ya ɗanu. Kasancewar sanyi da akeyi duk sauran jama'ar gidan da ƴan biki suna can a sassan gidan a maƙale, duk da madai ƴan bikin da suka rage duk na jikine babu bare. Babu kowa a tsakar gidan sai yaran Jay dake ɓoɓɓoye. 
         Yau kam Jay ya shiga har falon baba malam tare da lauyan malam mahaifin su baba malam a zuwan zasu tattauna akan kaddaririn baba malam ɗin. Acan kuma ta waje little bee ce da wasu jami'a a harabar gidan a mabanbanta wajaje duk da Jay yasan akwai camaras ɗin da Afrah ta saka masa a wancan zaman. Yafi buƙatar gani ga ido ga kowa kafin ya bankaɗa sirrikan dake a cctv ɗin. An kira Aymah da Yoohan falon, sai su Abban Abdallah da hajjo data san komai itama. Sai Omar da yazo matsayin lauyan Nu'aymah shima.
       Bayan buɗe taro da addu'a baba malam ya fara da nasiha a garesu duk dai a cikin salon tarkonsu, dan a zahiri fa babu wani maganar mallakama Nu'aymah kaddarorinsa da yakeyi. Shirine kawai irin nasu Jay. 
      A gefe kuwa idanun su Yoohan gaba ɗaya na'a Windows ɗin falon a kaikaice. Baba malam kuwa na cikin nasiha sai ga abinda suke jira ya bayyana. Kallon juna sukai shi da Jay dasu Yoohan sukayi murmushi. Daga haka ya cigaba da bayaninsa hankali kwance.

        Acan waje kuwa su Little bee na mammaƙale a maɓoyarsu sai ga mutum sanye cikin dogon hijjab har ƙasa da niƙab ya fito daga tacan bayan gidan yanda babu mai iya fahimtar daga ainahin sashen da aka fito. Basu da tabbacin mace ce ko namiji, dan komai an rufe ba'a gani. 
      A yanda mai laɓe ke tafiya da dabaru zaka san cewar lallai an ƙware, sannan aikine da akeyi tunba yanzuba. Cikin salon iya aiki Little bee taima abokan aikinta wani salo da yatsun hannunsa suka bada ɗass!! Sau ɗaya. A take duk suka ƙara shiryawa dan suma dai suna biye da mai laɓe akan idanunsu.
       Sai da suka tabbatar mai laɓe ya isa dai-dai sashen Malam marigayi alamar dai ɗan gidanne, tunda har ansan a ina su baba malam zasuyu taron nasu aiko sai wanda yasan gidan. Kamar yanda mai laɓe ya saba a koda yaushe ya isa jikin Window. Wani siririn abu ya saƙa a tsakanin glasess ɗin Window ɗin da alama na ɗaukar magana ne. Dan yana gama turashi ya kai hannu ya taɓa kunnensa alamar tabbatar da daidaitar komai. Ƙaramin tsaki akaja jin Nasihar da baba malam ya fara dan ba ita ake buƙataba a yanzu. Jin baba malam zai fara jawabinsa mai laɓe ya ƙara nutsuwa da maida hankalinsa ga window ɗin domin saurare.. 
         Da wannan damar su Little bee sukasamu isowa wajen cike da ƙwarewar aiki suka toshe gaba da baya na ɗan siririn lungun bayan ɗakin malam marigayi. Ƙarar saƙon daya shigo wayar Little bee daga Jay ne ya fargar da mai laɓe ya juyo da sauri. Sai kawai ganinsa yayi zagaye da mutanen da baisan ta ina suka ɓullo ba.
      Tashin hankali ba'a saka maka rana. Wannan shine ɓoyayyar kalma a zuciya da bakin mai laɓe duk da bai fito ya furta manaba a zahiri. Dan kuwa dai gabas da yamma kudu da arewa babu wajen guduwa. Katanga a bangon gabas. Ginin sashen malam a bangon yamma. Little bee da jami'ai uku a bangon kudu duk sun nunasa/ta da bindiga. Dawood da jami'ai uku shima a bangon arewa duk sun nunata/sa da bindiga nanma.
     Wannan itace kwana casa'in da tara ta barawo ɗaya tak ta mai kaya. Little bee ta ciwo wayarta da hannu ɗaya a aljihu ɗayan kuma riƙe da bindigar data nuna mai laɓe. Kiran Jay tayi a waya. Yana ɗagawa tace, “Sir! Aikinmu ya kammala zaku iya fitowa”.
       “Woow!” Jay ya faɗa yana miƙewa idonsa akan su baba Malam. Takawa yay jikin windown da yake hango inuwoyinsu ya zuge gilas ɗin tare da net. Abinda mai laɓe ya saƙala ya faɗo. duƙawa yay ya ɗauka yana jujjuya shi a hannunsa kafin ya kalli su baba malam da suma duk shi suke kallo. 
           “Malam zama ya ƙare ai, suspect ɗinmu yazo hannu zamu iya zagayawa”.
    Harga ALLAH sai da gaban baba malam da Umm ya faɗi. Hakama Aymah duk sai taji tsoro kuma. Su Abba Musbahu da basusan mi akeyiba suka shiga kallonsu da tuhuma. Ko a jikin Yoohan da Umar. Dan sunema farkon ficewa a falon.
    Baba malam dake kallon su Abban Abdallah yace, “Kuyi haƙuri wannan itace kawai mafita a garemu gudun kar wataran a kai ga rasa rai bisa makircin da bamusan wake ƙullasa ba”. Daga haka yay gaba ya barsu da kallon kallo ma juna sai dai ganin kowa ya fice suma sukabi bayansu jiki a sabule.
      Ganin duk sun iso Little bee ta dakama mai laɓe tsawa da faɗin, “Cire Niƙaf”. Ko motsi ba'ayiba. Sai dai yanayin tsayuwar ya tabbatar da koma wanene a tsorace yake kuma cikin ƙololuwar tashin hankali da firgici. 
       “Inada cikaken dama nayin harbi, hakan na nufin bullet ɗin zasu iya fita a cikin bindigarnan zuwa jikinki/jikinka a koda yaushe. Zan irga iku kawai bisa lasisin dama a gareki ko a gareka. *_Ɗaya! Biyu! Uku!!”_* ta fita daga bakin Little bee tare da bullet ɗinta zuwa ƙafar mai laɓe da ko motsi baiyiba balle ya nuna kota nuna zata cire nikab din da aka bada umarni.
     A take ƙarar muryar mace ta karaɗe gidan saboda azaba shigar bullet. Ƙasa ta durƙushe jiki na rawa. Da wannan damar Little bee ta ƙarasa gareta tasa hannu ta fisge niƙab ɗin ta jefar gefe. Baba malam da Umm da sauri suka kauda kawunansu gefe da tsananin fargabar tsoron ganin koma wanene. Sai da Nu'aymah ta furta,
       “Illalillahi wa'inna ilaihirraji'un Addah!! Kece dama?!!!”.
     Sannan su Umm suka juyo a firgice. A take wajen gaba ɗaya ya ɗauki salati. Dan duk jama'ar gidan kururuwar ihun Addah da Little bee ta harba dama duk ya fito dasu a hautsine.
     Cikin girgiza kai hawaye na sakkoma Umm a guje tace, “Inaa bazai yuwuba. Addah ki sanar musu ba abinda suke zargi bane ya kawoki nan. Dan ALLAH ki tabbatar musu domin bamu kariya kema kika zo nan. Ki tabbatar musu bake bace kike laɓen nan dama can dan ALLAH, kicemin yau kika farayi......”
      “Bata da bakin baki waɗan nan amsoshin domin wanke kanta Umm-Muhammad. Domin kuwa duk saɓaninsu da baki eson ji daga bakinta sune gaskiyar amsoshin naki da ma kowa dake anan wajen”.   
     Bily dake kusa da Jay tsaye ta bama Umm amsa kanta tsaye.
        “Karkice dani haka Maman Awwab. Dan ALLAH karkice haka. Wannanfa Fauza ce, wadda muka tashi tare tun ƙuruciya tamkar uwa ɗaya uba ɗaya ta haifomu. Ban taɓa ɓoye mata sirrinaba, itama bata taɓa ɓoyemin nata ba. Tare muke raba farin ciki, sannan mu raba kuka tare idan ya samemu.....”
         Murmushi Bily tayi da takawa a hankali zuwa gaban Addah daketa faman magowar azabar ƙafarta dake zubda jini. Ta nunata tana mai kallon Umm ɗin, “Tabbas a zahiri haka take a gareki Umm-Muhammad. Amma a baɗini itace babbar maƙiyyarku. Idan kuna buƙatar tabbatarwa mu a shirye muke wajen nuna shaidar gani da ido a gareku dan duk mun tanajesu dama”. Ta ƙare maganar tana duban su baba malam da alamu ya nuna tamkar duk sunyi sumar tsaye ne har yaran Addah da duk suma suna a wajen.
      Daga haka Jay ya bama Yoohan da Omar damar cire bullet ɗin jikin Addah. Cike da ɗacin murya Yoohan ya dubi Jay ɗin idanunsa jazur. “Uncle ka gafarceni, hannuna bazai taɓa iya aikata jinƙai ga maci amana ba”. Daga haka ya kama hannun Nu'aymah da jikinta ke karkarwa suka bar wajen.
      Murmushi kawai Jay yayi. Baba malam zaiyi magana Jay yace, “Karka takura masa Malam. Umar Please ka cire mata sai mu wuce da ita. Malam sai ku samemu a statlon ɗinmu nan kano mu ƙarasa maganar”.
       Da sauri baba malam yace, “A'a Jawaad ina neman alfarma komi zai faru muyisa anan cikin gidan domin rufin asirinmu, wannan itace alfarmar da zan nema a gareku”.
     Ɗan jimm Jay yayi, sai kuma ya kaɗa kansa alamar karɓawar alfarmar baba malam ɗin.
     Badan Umar yaso ba ya amince zai cire. Dan haka aka ɗakko Adda daga lungun zuwa sashen Malam. Gaba ɗaya yaran sa'an su Muhammad zuwa kansu Adawiya ba'a barsu sun shigaba. Duk da kuka da Adawiya keyi iyakar ƙarfinta wanda babu wanda yasan dalilinsa. Su Hajarah da sauran yayunta na ma'auri duk suna gidajensu basusan abinda akeyiba. Sai malam ƙarami kawai da sauran ƙannensu. Shiko gaba ɗaya da alama ma jinsa da ganinsa sun gushe dan bai iya motsawa a lungunba har kowa ya fice. Hakama Abba Mustapha saida Hajjo ta kama hannunsa da kanta saboda tsabar firgici.

★★★

        Bayan azabar cire bullet da Addah ta gama sha Omar yay mata allurar rage raɗaɗi. Umm dake kuka har yanzu ta sake duban Addah. “Fauza dan ALLAH ina roƙonki a karo na ƙarshe ki ƙaryata tuhumar da ake miki. Ki tabbatar musu da kawai yau ƙaddara ta kawoki amma ba ke bace. Har abada bana fatan kunnuwana da zuciyata suji saɓanin tunaninsu a kanki Fauza.......”
        Shiru Addah batai ko motsiba, kanta a ƙasa kuma taƙi kallon kowa. Gyaran murya Jawaad yayi da gyara zama. “Hajiya karki wahal damu anan, dan alfarma ki ke ci, badan darajar malam ba da zamu wuce dake station ne ki mana bayani ta duk hanyar da mukaso bi da ke. Kar kiyi tunanin ɓoye mana komai dan a tafin hanunmu kike, duk wanda ke cikin labarinki sai da na gurfanar da shi a gabana kafin ki ganni anan, na zaɓi bin komai mataki-mataki ne saboda sauƙaƙa firgici a zuciyar waɗanda kikema cin dunduniya. Nasan kinsan Hamisu ai gashi a gabanki tsaye”.
    Da sauri Addah ta ɗago ta kalli inda Jay ke nuna mata. Kallon ido cikin ido sukaima juna kuwa ita da Hamisu. ya ko zuba mata mummunan kallo. Da sauri maida kallonta ga Jay. Kai shima ya jinjina mata fuska a ɗaure. “Bayan Hamisu akwai ƴarki Kubrah ko, sannan akwai......”
      Da sauri ta ɗaga masa hannu, sai kuma ta fara tari, gefen ɗan kwalinta tasa ta tare bakinta sai ga jini na zuba. Babu wanda bai mata kallon tsoro da firgici ba a falon. Ta goge mabinta saboda tsagaitawar tarin sannan ta kalli kowa dake falon tana Murmushi mai ciwo a karon farko. Ta kalli ƙafarta dake naɗe da bandage hawaye na ziraro mata. Dan har yanzu tanajin raɗaɗin azabar shigar bullet a karon farko na rayuwarta. Kallon baba malam tayi ta sake sakin murmushi sannan ta maida akan Umm dake a gabanta zaune.
      “Ko babu ƙarfin iko hukuma dama lokaci yayi da Firdausi! Zata san wacece Fauza a gareta. Dan tun bayan auren Nu'aymah wannan ranar dama nakewa zaman jiran tazo a gareni, dan nasan tana cikin ranakun da ko naso koban soba sai sun riskeni a duniya ko a lahira, musamman daya kasance gajerun kwanaki suka ragemin a duniya. Wannan Fauzar dake gabanku ba Fauza bace ta shekarun baya mai lafiya, hatsabibiya, mai aiki da zuciya kawai bada tunaniba, mai son kanta, mai aiki da huɗubar shaiɗan. Wannan Fauzar maƙasƙanciyace a gabanku yanzu, mai rauni, mai ɗauke da ciwon zuciya da ciwon kansar jini (blood cancer), wadda likita ya tabbatarma watanni kaɗanne suka rage mata a duniya. Wannan Fauzar mai dana sani ce da nadama da yin kaico akan ayyukan data tafka batare daku kun saniba saboda iya SARAN ƁOYE”.
     Tarine ya kuma sarƙeta da kuka. Nanma tanayi jini na fita, saida ta tsagaita sannan ta sake dubansu. “Da wahala shara'ar alƙalin duniya ta iya dacewa da laifukan Fauza, shara'ar UBANGIJI datafi cancanta dani ta fara bayyana a gareni tun daga randa likitanci suka sanarmin sakamakon abinda nakeji a jikina. Amma lallai halina dolene yaje kunnunwan mai saurare ko zai zama izina ga masu irin halin suji tsoron ALLAH su canja kafin lokaci ya ƙure musu”. 
         “Firdausi! Da gaske ni Addah na soki so na gaskiya a zamanin ƙuruciyarmu. Duk da ko a wancan lokacin duk randa kika samu abinda ni nafi cancanta da samunsa inajin zafinki a raina. Musamman idan nai la'akari dana fiki komai a rayuwa. Ni ƴar gatace ko a gidanmu, duk wani jin daɗi da yaro kan tashi ya samu daga iyaye na samesa. Mahaifina yafi naki komai a rayuwa. Hakama mahaifiyata tafi taki. Hasalima da yawan lokuta ƴan gidanku kunaci ne daga alfarmar iyayena. Sai dai kash duk da wannan gatan namu da tarin alfarma kin fini basirar karatu, bama ke kaɗaiba duk ƴan gidanku ALLAH ya basu wannan baiwar, gashi duk kun fimu ƙyau, sannan da wahala ku zauna da mutane basu soku ba. Dan yayyenki ma sunsha ciwo nasarorin dake sa yayuna jin zafinsu, sai dai mahaifiyarmu kan ƙwaɓemu akan hakan. Nasararki a kaina bata taɓa kaini ga ƙololuwar jin zafinkiba sai a randa Sheikh Soorajidden yazo har gidanmu akan neman aurenki”. 
       Ta share hawaye masu zafi dake gangaro mata har yanzu sannan ta cigaba da faɗin,
       “Hakan ta faru dalilin soyayyarsa da taimin shigar sauri cikin zuciya tun a ranar kammala karatunmu. Idan baki mantaba tun a wajen bakina bai hutaba da zance a kansa har kika nuna ƙosawarki akan hakan. Mun dawo gida zuciyata na ɗunbin begensa, sai dai a randa na buɗi ido na gansa a gidanmu sai labari ya canja salo. Ke! ke! ke!! Firdausi! kin sake yanke igiyar nasarata kamar yanda kika saba a koda yaushe”.
       Tai maganar da matsanancin kukan da har ya hanata kasa cigaba da magana sai da tai tari mai tsaho. Falon kansa yayi tsit ko motsi kowa ya kasa saboda shock. Da ƙyar ta tsagaita kukanta da tarin sannan ta cigaba.
         “Naji zafinki a wannan ranar zafin da idan aka bani makami zan iya halakaki. Nayi kuka harna rasa hawayen zubarwa. Amma daga ƙarshe sai nayi haƙuri bisa ga shawara da nasihar da babbar yayarmu ta min, a lokacin sai naji na haƙura na barmiki, duk da dai son nasa na nan maƙale a raina. A haka aka kammala komai na maganar aurenku ni bani da wani tsayayyen saryima. Har lokacin biki yayi mukasha bikinku. ALLAH ya sani ban taɓa cin karo da rana mai ciwo da raɗaɗi ba irin ranar aurenku. Dan aranar na gama yanke hukuncin dolene na shigo gidanki matsayin kishiyarki. Amma sai kash. Ƙaddara ta riga fata, dan kuwa haɗuwata da Mustapha sai ta kasance almakashin daya datse wannan zaren a karo na biyu. Ya nuna yana sona, amma ban amsa masaba a ranar, shi kuma ya zata kunyace ta sani ƙin amsawar, dan haka yay amfani da wannan damar yayma rayuwata kutse ta bayan gidan adalilin neman aurena da Sooraj yaje yayima ƙaninsa a gidanmu tamkar yanda yayima kainsa. Babana kuma babu wani tsayawa ja'in-ja ya bashi. Na sake shiga ruɗani a karo na biyu, amma sai yayata dai ta sake ɗorani akan mizanin hankali da nasiha kamar wancan karon. Ta kuma tabbatarmin Mustapha shine mijina dama ba Sooraj ba, tanada yaƙinin kuma shine zai zama mafi alkairi a gareni insha ALLAHU. A wannan karonma taci nasara. Dan duk da babu son Mustapha a raina na aminta zan auresa kodan darajar jini da suka haɗa da Sooraj, sannan a fuska ma suna kammani da juna”.
     Ta share hawayenta tana murmushi da kallon Umm.
        “Firdausi! Shigowata gidan nan shine ya sake canzama zuciyata salo a kanki. Dan tun a yanayin taron aurena da Mustapha na fahimci a wannan gaɓarma kin sake min tsere. Ban sake tabbatarwa ba sai da na tabbata ɗaya daga cin wannan ahalin. Zamantakewar ki da Sooraj tana ɗaya daga abinda ya dagula min tunani. A zahiri mutane ɗauka suke tsoron Sooraj kikeyi, amma wanda zai ganku a sashenku kaɗaine zai goge wannan tunanin a ransa saboda soyayya da tattalin da kike samu daga garesa. Sannan kasancewarsa babban ɗa a gidannan duk wata daraja ta matar gida kin kwashe a sama da tamu. Wannan yasa ita kanta Momyn Abdallah kejin zafinki ganin anan kikazo kika sameta. Abinda ya ɗan sakamin sassauci a kanki lokacin haihuwa dana rigaki yi kuma namiji, har takai sai da na jera huɗu sannan kika samu ciki. Maganar gaskiya bazan ɓoye mikiba naji matuƙar jin kishi akan samun cikinki duk da kuwa inada ƴaƴa har huɗu a lokacin. Dan idan ina ƙaunar mutuwata to ina ƙaunar buɗar ido naganki da wani cigaba daya ɗara nawa a rayuwa, dan na tsani cikin nan naki tun yana ɗan tayinsa. Duk da ban taɓa tunanin cutar dake ba adalilin cikin nan zuciyata ta fara rayamin hakan, dan kullum huɗuba takemin na ɓarar da cikin kawai kowa ya huta. Sai dai ina shirin aikata hakan a gareki Sooraj ya ɗaukeki kuka wuce saudia, nayi baƙin ciki nayi takaici irin wanda bazai misaltuba. Gashi baku dawoba sai gab da zaki haihu. Koda kuka dawo ban fasa aiwatar da ƙudirina akan cikinki ba, sai dai babu wata makamar yin hakan dana samu har ALLAH ya saukeki lafiya a wani dare. Hankalina ya tashi ganin kema da namiji kika fara, zuciyata ta sake bushewa da kangarewa akan na kashesa kawai tun yana jaririn.........”
      Cikin ɗacin murya Baba malam ya katse Addah da cewar, “Fauza kenan kece kika kashe mana yaro?”.
         Kuka Addah ta sake fashewa da shi kanta a ƙasa ta kasa kallonsu. Ga tari ya kuma sarƙeta har jini na fita guda-guda yanzun. 
   Ko batace komaiba sun fahimci shirunta na nufin haka ɗinne. A take gaba ɗaya falon suka ɗauki salati. Umm kam ido kawai ta tsurama Addah hawayenma sun tsaya cak. Hakama baba malam kallon ƙasa kawai yake ya gaza koda motsi. Abba Mustapha zai miƙe Hajjo ta hanashi, dan har yanzu ai ba'azo inda take buƙatar ba.
       Jay ne ya katse shirun nata da faɗin, “Ke muke saurare”. Yay maganar yana kallon agogon hannunsa.
        Da ƙyar Addah ta tsagaita kukanta ta cigaba da faɗin, “Na shaƙa masa maganine, irin wanda naso shaƙama Nu'aymah aka samu akasi Rabi mai aikinki ta kusa rutsani, dan a lokacin kin tafi wanka Nu'aymah kin barta ta dinga leƙata a ɗaki, ni kuma saina aiketa domin aiwatar da ƙudirina, sai akai rashin sa'a kafin na shaƙama yarinyar maganin Rabi ta shigo, motsin nufowarta bedroom. Wannan shine dalilin tsoratata na saketa a ƙasa kanta ya bugu. A take ta suma, ni kuma nai saurin ɓoyewa dan kar rabi ta ganni gakuma kema naji yanda kika rikice a toilet kina ƙoƙarin fitowa. Sai da ta fita da gudu tana ihun kiranki saboda rikicewar da tayi ni kuma na samu na fita a sashen, daga baya na shigo cikin matan gidan muka shiga jajen yaya akai a tare. Kowa yama zata Nu'aymah ta rasu, sai dai hajjo ta matsa a kira likita. Zuwansane ya tabbatar mana da suma tayi, ba haka nasoba, amma lokacin da aka dawo da ita daga asibiti da tabbacin sanadin faɗuwar tata ta samu ciwo a ƙwaƙwalwa sai naji daɗi a raina saboda bushewar zuciya da huɗubar sheɗan”. 
        “Likita ya fara ɓusa zargin yaddota akai daga gado, kema kuma Firdausi kin tabbatarma kowa kina toilet kinji motsin shigowar mutum bedroom ɗinki, sai dai kin zata Rabi ce, sannan kuma kinji sanda yarinyar ta faɗi ƙasa ta bugu. hakan yasa aka tuhumi Rabi, amma kuma saita rantse da iya gaskiyarta ba ita bace dan nama aiketane ta dawo,, tana shigowa taji ƙarar Nu'aymah datai sau ɗaya kafin ta suma. Maigadi ne ya sake wanke Rabi a wajen kowa. Haka kawai na tsargi kaina akan karfa asirina ya tonu, dalilin da yasani saurin ɗaukar mataki kenan na saka malamin da ya bani abinda zan shaƙama yarinyar rufemin bakin kowa a gidan nan akama bar wani hasashe-hasashen son sanin yaya akai Nu'aymah ta faɗo a gadon?. Ban sake yunƙurin cutar da yarinyarba, dan a ganina ciwon data kamu da shi ya isa kai rayuwarta ƙarshe. Sai dai na saka an daɗe bakin mahaifarki yanda bazaki sake haihuwa ba. ALLAH kuwa ya amincemin baki sake samun ciki ba sai bayan haihuwar Nu'aymah da kusan shekaru biyar, hankalina ya sake tashi na nufi malamina. Saina iske ALLAH ya masa rasuwa. Lallai nayi gamo da tashin hankali na haƙiƙa a wannan lokacin, dan zan iya cemuku daga wannan lokacin ban sake samun malamin da yaymin aikin da yaci a kanku ba.......”
       “Mtsoww!! Malami ko boka dai”. Abban Abdallah ya faɗa a fusasce.
       Wani irin kallo Addah tai masa, sai kuma ta kwashe da dariya ta ɗauke kanta kawai. Hakan da tayi kuwa yaba kowa mamaki. Amma sai babu wanda yayi magana. Har shima Abban Abdallah ɗin bai sake cewa komaiba.
      Addah ta cigaba da faɗin, “Tunda na fahimci aikin malami ya daina tasiri sai na koma laɓe da son zubar da cikinki, to ALLAH ya tabbatar Muhammad sai ya shaƙi iskar duniya sai gashi kin haihu lafiya duk da ba haka nasoba. ta wannan hanyar laɓe ne nakejin duk wani abinda ya shafeku, dan duk da amintarmu firdausi ke mutumce mai zurfin ciki. Nakan faɗa miki sirrikana kai tsaye ko kema zaki warwaremin naki babu shamaki. Amma sai da na fara muku laɓe na fahimci kina bala'i-bala'in rainan hankali. Dan babu wani sirrinki mai muhimmanci da kike sanarmin sai ƙananu kawai. Hakan yasa nima na ɗauki ɗammarar bi dake ta yanda kikazo min”.
      Ta kai dubanta ga Abban Abdallah. Wanda a take mood ɗinsa ya canja ya wani zazzaro mata idanu kamar zai haɗiyeta da su. Murmushi tayi da ɗauke kanta ta cigaba da faɗin, “A dalilin son halaka Muhammad na haɗu da babban makirin daya ƙara faɗaɗa ƙwaƙwalwata akan ƙiyayyarki da zuri'arki. Dan ta sanadinsa ne wasan ya canja salo daga soyayyar Sooraj zuwa wani abun daban. Ba kowa nake nufiba sai Lurwan ga shinan”. Tai maganar tana nuna Abban Abdallah da tun fara maganar tata ya zabura zai miƙe a fusace amma Hajjo ta riƙoshi cikin fushi.
       Babu wanda bai zaro ido ba a jama'ar falon. Abban Abdallah ya sake zabura yana ƙoƙarin ƙwace hanunsa daga hajjo. “K baƙar annamimiya, makira, azzaluma. dan ubanki sharrin naki da makirci yazo kainane kenan komai?”.
     Dariya sosai Addah tayi tana kallonsa, tace, “Lurwanu ai ka fini iya makirci, dan kaine malamina a wannan fanin kuwa. Da farko ta hanyar malami kawai nake samun nasara akan Firdausi, amma haɗuwata da kai ya sani hutawa daga zuwa wajen kowanne irin malami, dan kai kafi malamin hatsabibanci ma. Yau ranace mai kama da ranar hissabi, yanda nasan cewar ayyukanmu bazasu ɓoyu ba a wannan rana dake jiranmu to ina tabbatar maka yau ɗin nanma tun a duniya zan fara fallasasu dan kowa ya yaji. Dan wlhy yanda duniya tasan waceceni a yau, ƴaƴana sukaji shukar danayi, mijina yaji, dolene kaima uwarka da yayanka da matarka da ƴaƴanka da sauran ƴan uwanka susan kai wanene a cikinsu”.
       Sake zabura yay kanta kuwa da ƙarfin tuwo ya fisge hannunsa a cikin na hajjo, amma sai Dawood yay azamar shan gabansa da bindiga. “Ka kama girmanka, inba hakaba zan maka irin tabon dake a ƙafarta kaima. Ka nutsu ka riƙe sauran mutuncinka”.
      Jikin Abban Abdallah rawa yakeyi sosai, dan bai taɓa kawowa a ransa tone-tonen Addah zai iso kansaba musamman da yasan irin gargaɗin da yay mata kafin ya yarda su fara aiki tare, da kuma kalaman datai amfani dasu a yau wajen shimfiɗa labarinta. Yayi zaton zata rufa asirinsa ne.
            A hankali baba malam ya yunƙura ya miƙe hawaye na sakko masa akan fuska. Yasa babbar rigarsa ya share sannan ya dubi jama'ar falon. “Inaga dan ALLAH mubar maganarnan gaba ɗaya, wannan tone-tonen a ganina sam bashi da amfani. Sun aikata abinsu a ɓoye sai mu barsu kawai da nauyinsu suje can su ƙarta. Bana buƙatar jin abinda Rudwan ya aikata ku barni haka, n.......”
      “Dolene kuwa kaji ɗan malam, dan haka koma ka zauna”. Hajjo tai maganar cike da bada umarni. Baya iya ƙetare maganar mahaifiyarsa. dan haka ya koma jagwab ya zauna yana mai dafe kansa da hannaye biyu saboda jirin dake kwasarsa.
       Addah tai murmushi mai ciwo da cigaba da faɗin, “Lurwanu shiya canja tunanina daga fushin rasa masoyi zuwa na mallakar dukiya, dan huɗubarsace ta fahimtar dani cewa ina dukan taiki ne kawai ina barin jaki, haukana kawai nake akan nafi Firdausi ƴaƴa nafita nasara yanzun. sai dai ashe dukiyar da mijinta ya mallaka a cikin ƴan uwansa ta ninka wadda nawa mijin ke da shi sau fiye da bakwai. Kaso biyu na dukiyar gidan nan mallakarsace, kaso ɗaya ne na mazajenmu da Hajjo. Gaba ɗaya komai ya susuce min a lokacin nama nema rasa makamar tunani da hankalina. Amma sai ya dinga kwantarmin da hankali ta hanyar nunamin inhar zan taimakesa muyi aiki tare to lallai dukiyar baba malam zata koma ƙarƙashin ikonmu ne. Nace masa ta yaya kenan?. Ya bani tabbacin ta hanyar Abdallah. Tunda akwai shaƙuwa sosai tsakanin Nu'aymah da Abdallah hakan na nufin nangaba kaɗan soyayya zata iya bayyana a tsakani duk da ƙuruciyarsu.  Dan bazaiyi wasaba wajen ɗora Abdallah akan matakin daya kamata game da Nu'aymah. Ɗari bisa ɗari na yarda da hakan a wancan lokacin. Saboda a yanda ya faɗaɗa min bayanansa na fahimci inba ta wannan hanyarba babu ta inda zamu mallaki wannan dukiyar. Wannan shine sanadin dunƙulewarmu waje guda ni da Lurwan muka fara aiki tare. Amma wlhy kullum hankalinmu cikin ƙara tashi yake gameda haɓaka da dukiyar Sooraj keyi abun tamkar roƙo. Shima kuma sake ɗaukaka yakeyi fiye da sauran ƴan uwansa akan ilimi da soyayyar mutane. Wanda ɗaukakar tasa itama tana ɗaya daga cikin abinda ke ƙara ɗora Lurwan ga son cutar da shi. Haka muka cigaba da tafiya munama Sooraj *SARAN ƁOYE* da iyalinsa harma da duk wanda tsautsayi ya sakko a tarkonmu. Dan kuwa dai Rabi na ɗaya daga cikinsu. Mun sakata tana mana wasu ayyukan akan dole wasu ko bama tasan muna amfani da ita munayiba musamman ta wayarta. Akwana a tashi mun cigaba da tafiya wataran muyi nasara akan aikinmu wataran su tsallake tarkonmu. A haka maganar soyayyar Abdallah da Nu'aymah ta fito, har takai Nasir yayi zuciya yabar gidan nan dan shima yana sonta. Da gaske Abdallah tsananin son Nu'aymah yakeyi, kamar yanda itama sonsa takeyi saboda tsananin shaƙuwar dake a tsakaninsu, amma a hankali muka fara canja tunanin Abdallah muna kwaɗaita masa dukiyar Sooraj. Tun yaron nan baya fahimtar mi muke nufi yana bijire mana harya hau kan hanya saboda ɗaukesa da iyayensa sukayi zuwa wajensu. Dan mun fahimci zamansa da Firdausi ne ke mana illa komin masa huɗuba itake wargaza mana komai ta hanyar ƙaunar da take nuna masa ta gaskiya. Gaba ɗaya mun tattara shirinmu ne akan auren Nu'aymah da Abdallah, shiyyasa duk likitan da aka samo da tabbacin zai mata aiki akan matsalarta sai munbi duk hanyar da zamubi wajan daƙile hakan saboda wani likita ya tabbatar mana da wahala ai mata aikin nan ta tashi, mukuma burinmu muyi amfani da wannan damar sai bayan aurenta da Abdallah aimata aikin ta sheƙa mu samu abinda muke buƙata, dan inhar muka gama da yarinyar kauda ƙaninta abune mai sauƙi a garemu. Har ALLAH yasa burinmu ya cika aka tsaida ranar auren Abdallah da Nu'aymah. Sai dai Abdallah baisan da shirinmu akan bayan aurensa da Nu'aymah so muke ta mutu ba. Wannan daga ni sai mahaifinsa ne muke shirinmu. Amma kash tarihi sai ya nema maimaita kansa tsakanin Adawiya da Nu'aymah tamkar ni da Firdausi. Dan kuwa dai Adawiya soyayyar Abdallah ce tai mata shigar sauri, tanata ɓoyewa har takai ta gagara hakan lokacin data tabbatar zai kubuce mata. Na jima da fahimtar tana sonsa amma sai na ɗauka kawai ƙuruciyace, sai da aka tsaida rana na fahimci yarinyata da gaske takeyi. Shine fa na samu Abban Abdallah da zancen kozamu samu mafita. Kai tsaye ya nunamin hakan bamai yuwuwa bane. Na harzuƙa matuƙa, dan ina buƙatar farin cikin ƴaƴana, dan haka nace to kuwa sai dai kowa ya rasa. Da dai ya fahimci zan lalata komai bayan nasara dake tunkaromu sai ya lallasheni akan to na fahimcesa mana, mu bari ayi auren Nu'aymah da Abdallah. bayan komai ya faru Aymah ta mutu wajen aiki duk yanda zaiyi zaiyi a aurama Abdallah Adawiya. Na zauna nayi nazari sosai kafin na yarda da tsarinsa, dan nima a nawa hangen dukiyar da zamu mallaka ɗin idan Abdallah ya auri Adawiya zata sake dawowa wajenane tunda jikokina sune zasu zama magadan Abdallah, daga haka muka cigaba da shirye-shiryen biki, sai dai kash ana gobe matakin cikar burinmu zai tabbata aka sace Nu'aymah. Ina mai tabbatar muku munfi iyayenta shiga tashin hankali a wannan lokacin, duk da ni ɗaura auren Adawiya da Abdallah ya ɗan min daɗin da har tashin hankalina ya sassautu. Amma bayyana muku kalar ruɗanin da Lurwan ya shiga a wannan ranar ba'a magana. Dan har sai da muka samu matsala kanmu ya rabu, ni haushina ƙiyayyar da Abdaallah ya nuna akan yarinyata, shi kuma Lurwan takaicinsa suɓucewar damarmu. Daga baya dai muka dai-daita muka tafi shirya filan b. Iya bincike kuma munyi mun rasa gano yaya akai? ta wace hanya hakan ta faru? Sannan wanene ya aikata mana hakan? Da gaske mun fara zargin asirinmu ne ya tonu, sai dai har ƙura ta lafa bamuga wani alamar hakanba sai hankalinmu yaɗan kwanta”.
        Karan farko Hajjo tai murmushi mai ciwo. Amma batace komaiba.
       Addah ta cigaba da faɗin. “Mun sake son ƙulla auren Abdallah da Nu'aymah a karo na biyu. Sai kuma ga Naser ya dawo wai shima da soyayyar ta. Da alama kuma tayi shirin amsarsa. Sannan hajjo da Ananah sun goya masa baya a wannan karon. Shi kansa Sooraj mun fahimci so yake ya bama Naser ɗin. Dan yanda suke takun saƙa da Abdallah baisa wani ya taɓa nuna goyon bayan Abdallah ba. Muna tsaka da neman mafita Abdallah ya saki Adawiya da Yusrah. Wannan saki shine ya kawo saɓani mai girma a tsakaninmu. Dan nikam dai na tabbatar musu sai Abdallah ya maida Adawiya zan cigaba da basu goyon bayan cigaba da aiki tare. Amma sai Abdallah ya tubure, ƙarshema ya gudu ya bar gidan saboda takurawar da mukai masa ni da Abbansa. Sai dai ya tabbatar mana shifa da gaske yanason Nu'aymah ya kuma gaji da biye mana. Hankalinmu duk ya tashi, dan tabbas da gaske munga soyayyar yarinyar a cikin idanunsa. Mun kuma tabbatar da ya daina mana biyayya kenan”.
       “Ana tsaka da wannan rikicine ciwon da nake yawan ji ya takura mani, batare da sanin kowaba Mustapha ya kaini asibiti, a gwaje-gwajensu aka tabbatar mana da ina ɗauke da ciwon kansar jini, ga kuma ciwon zuciya daya ci jikina sosai shima, wanda na tabbatar yanada alaƙa da hana kaina zaman lafiya danai akan ƙadarar da ban isa canjataba tunda rubutacciyace daga littafin Firdausi da Sooraj. Lallai jikina yayi sanyi, duk wani kaushina ya sulale, adadin watanni da likitanci sukai ƙiyasin bazan zartaba ya ruguza dukkan burikana da zalamata. A karan farko zuciyata ta kwaɗaitu da son yin ƙyautatawa ga Firdausi koda sau ɗaya ne a rayuwata”. Kuka yaci ƙarfinta da tari. Yanzu kam gaba ɗaya ta cire ɗan-kwalin ta tare jinin dake fita da tarin, sai da ta tsagaita da ƙyar sannan ta cigaba da faɗin, 
         “Na roƙi Mustapha ya rufe zancen ciwona harga ƴaƴana saboda banason ɗagama kowa hankali, da farko bai aminceba, amma da naita lallaɓasa da hujjoji sai ya fahimta. Son kuɓutar Nu'aymah daga tarkon Lurwan ya sakani sakebin hanyar wani malami aka sakar mata jini. Ni da kaina na zuba garin magani a zoɓo na kai sashensu saboda a gabana Firdausi tasa Rabi ta dafama Sooraj zoɓi shima. sai nayi amfani da wannan damar kawai, ni na kwaɗaitama Rabi kaima Nu'aymah zoɓon ɗaki lokacin dana shigo sashen da nufin neman cucumber. Sai na aiketa ta faɗoma Firdausi zan ɗauki cucumber ɗin. Tana fita na zuba maganin. Ina laɓe ta bayan kitchen lokacin da Rabi ta tafi kaima Nu'aymah zoɓo sai ma suka gamu a falo. Inajin Nu'aymah tace bazatasha zoɓon ba na shiga damuwa. Inata ƙulla yaya zanyi kuma sai ga Rabi ta dawo kitchen ɗin ta ɗaura shayi. Dabarar bugar glass ɗin Windown nayi, Rabi ta kalla wajen ta ɗauke kai. Na sakeyi har sau biyu, shine ta leƙo, bataga komaiba da alama, shine na sake bugarsa. Shine fa tai tsaki ta fito domin dubawa. Nikuma nai amfani da wannan damar na shigo na zuba maganin na fita ta falo. Inda na wuce Aymah na kallo, sai  hankalinta bai kau kainaba harna fice da sauri. Na bada awa guda sannan na sake dawowa na laɓe jikin window ɗinta, banbar wajenba harta fara ciwon ciki wanda na tabbatar magani ya fara aiki. Nabar wajen cike da farin ciki. Kafinma na isa sashena ihunta ya karaɗe gidan. Malam ya tabbatar min dama kowanne irin bincike likitoci zasuyi ciki kawai zasuyita gani ya zube a jikinta, hakanne kuma ya faru. Da wannan damar zancen ciki na sakeyin amfani na tursasa Hamisu bisa tsoratarwar zan kashe mahaifiyarsa ya kawo hotunan da ni na ɗauki Yoohan da Nu'aymah su ba shiba, ba kuma Kubrah ba kamar yanda nasan Nu'aymah zatai zargi. Nayi amfani da Hamisu ne saboda kusancinsa dana sani da Sooraj sosai, na kuma san Sooraj ya yarda dashi. Duk da Sooraj da Firdausi sun bani tausayi sosai a wannan halin na danne zuciyata na cigaba da aikata shirina dan nasan shine kawai zai kuɓutar da Nu'aymah daga sharrin Lurwan akan kwaɗayin dukiyar mahaifinta...............✍


Turƙashi😭🚶🏻


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 74

............“Dabarata ta jingina ciki ga Nu'aymah, da kawo hotonta ita da Yoohan shine burina Sooraj yay fushi yace sai Yoohan ya auri Nu'aymah. Ta hakanne kawai aurenta da Abdallah ko Naseer zai gagara. Duk da bana zargin Nasir da komai, amma inhar shi Nu'aymah zata aura tsugunne bata ƙareba kenan. Amma indai ta auri Yoohan inada yaƙinin zai bata kariya. Saboda alwashinsa na ranar da aka kirashi akan wannan batun ya birgeni. Ko bayan babu raina ina fatan ya zama garkuwa ga ahalin Firdausi. Sannan Nu'aymah ma zata samu lafiya ta dalilinsa tunda shine likitan da dama aka basu Number sa muka sace ni da Lurwan. Alhmdllh naci nasara, dan kuwa da bakinsa ya furta son auren Nu'aymah, duk da Sooraj bai bashi goyon bayaba a lokacin saboda jin nauyin ƴan uwansa akan su Abdallah na tabbatar yanason bashi. Lurwan ya shiga ruɗanin ganin zai rasa dama ta biyu, hakan ne ya sakashi sake dawowa gareni mu haɗa kai a wannan karonma. Ya kuma bani haƙuri da tabbacin zaisa Abdallah ya maida aurensa da Adawiya da zarar anyi aurensa da Nu'aymah. Na nuna masa na amince dan na samu a gama maganar auren Nu'aymah da Yahya cikin kwanciyar hankali. Daga haka na cigaba da gayama ALLAH dan agareshi kawai nake hangen samuwar nasarar kubutar da Nu'aymah daga tarkon Lurwan. Hidimar aurar da ƴaƴa kawai nake a zahiri, a baɗini kuwa ba wannan bane a gabana sam, shiyyasa na samu Firdausi da shawarar duk yanda zatayi tayi kar Sooraj ya bama Abdallah ko Nasir Nu'aymah, gara a auramata Yahya bisa wasu dalilan dana lissafa mata a lokacin waɗanda Alhmdllh sunyi tasiri a gareta. Sai da ina shirin fitowane naga Sooraj tsaye bayanmu alamar yaji komai da muka tattauna kenan. Hakan yamun dadi, dan insha ALLAHU koba komai inada yaƙinin samun nasara”.
      Ta share hakawayenta ga murmushi a fuskarta. Cigaba tai da faɗin,
       Jin tabbatuwar ɗaura auren Nu'aymah da Yahya shine nasarata ta farko da kobayan nabar duniya inason ƴaƴana su tuna suyi farin cikin aikin alkairi dana taɓa ƙullawa a rayuwata ta zaman gidan nan. Ko murnanr aurar da ƴaƴana guda biyu a ranar banyi murnarsa da tsananin farin ciki ba kamar yanda nayi na Nu'aymah. Amma a baɗini nabar wannan nasarar tawa. A zahiri kuwa na shiga jerin masu shiga ƙololuwar tashin hankali kamar su Abdallah da Lurwan da rayuwarsu ke a gigice. Dan wlhy aranar da aka ɗaura wannan auren kaɗan ya hana zuciyar Lurwan bugawa a gidan nan. Ya kuma sake ɗaukar alwashi kala-kala akan koma ta halin ƙaƙa saiya samu cikar burinsa. Wannan furici nasane ya sakani saka ƙanwata bin ƴan tawagar kai amarya. Sai da na tabbatar Nu'aymah ta shiga ɗakin mijinta lafiya ta hanyar ji daga gareta sannan hankalina ya kwanta. Duk da na tausayama yarinyar inda ƙaddara ta jefata. Amma sai nai mata fatan samun kariyar UBANGIJI da nasarar canjasu dalilin shigowar tata cikinsu. Daga haka na cigaba da ɓoyayyar jiyyar da mijinane kawai yasan inayi da duƙufa neman gafarar UBANGIJINA ko zan samu sassaucin raguwar zunubaina. Abinda yasa nabiku Austria ganin Nu'aymah saboda kozan samu na nema gafarartane. Ban saniba ko kafin ta dawo ƙasar ni na rasa raina. Ta ɗayan gefen kuma inason sakama Lurwan idone. dan a yanzu na daina sanin komai daga shirinsa saboda ya fahimci bana tare dasu a yanzu. Ko amincewa da zaman Adawiya da nai gidansa tanamin aikin sakamasa idone. Dan duk wani motsinsa itace ke kirana tana sanarmin batare da ita kanta tasan aiki takeminba dan ban fito fili na sanar mata manufataba”.
      Wannan shine labarina, shine ƙaddarata, shine kuma son zuciyar SARAN ƁOYE dana aikata muku Firdausi, nasan bazaki taɓa yafeminba ke da zuri'arki, shiyyasama bazan matsaba wajen neman yafiyarku. Kai koma ke kin yafemin ALLAH bazai yafemin ba, dan nasan na cutar daku iya matuƙar gaya ta hanyar SARAN ƁOYE. na aminta ku kaini kowace irin kotu a yankemin hukuncin daya dace dani kafin naje na fuskanci babbar shari'ata ga babban alƙali”.
     Ta ƙare maganar da fara tari mai tdanani. Sosai yanda take tarin guda gudan jini na faɗowa ya tada hankalin kowa a falon. Umm ta matsa gareta ta riƙeta sosai jikinta tana kuka. Da ƙyar aka samu tarin ya lafa. Duk da Yoohan najin zafinta har yanzu, dan shi baiji wani tausayin taba, duk da ƙoƙarin ƙulla aurensa da tai da Nu'aymah a ƙarshen ɓarnakun data tafka, amma sai ya bada shawarar a kwantar da ita zata samu sassauci daga yawan tarin. Da shawararsa akai amfani wajen kawo ƙaramar katifa aka kwantar da ita ɗin. Aiko sai tarin ya lafa sosai.
     Murmushi tayi tana kallonsa, murya na rawa tace, “Nagode Yahya, ALLAH ya azurtaku da ƴaƴa nagari da zasuji ƙanku, ALLAH ya sauki Nu'aymah lafiya naga gudan jininku kafin nabar duniya”.
     Uffan baiceba, baima nuna yaji mita faɗaba, amma jama'ar falon sun amsa mata da amin, duk da wasuma irin zuciyar Yoohan garesu basuji tausayin nataba.

          Abban Abdallah da keji kamar ya tashi ya ƙarasa rayuwarta saboda zuciya data kumesa ya yunƙura zaiyi magana Hajjo ta dakatar da shi ta shanyar ɗaga masa hannu. Dole kuwa ya koma ya zauna yana zare idanu.
        Tai gyaran murya sannan ta gyara ƙafarta mai ciwo da dubansu ɗaya bayan ɗaya ta fara faɗin, “Karma ka wahal da kanka wajen ƙaryata abinda duk Fauza ta faɗa Lurwanu. Idan bakai tunanin ana kallonku ba yau zan sanar maka cewar na jima da fahimtar kai da ita su wanene a cikinmu. Na barkune saboda na muku talalar zuwan wannan ranar. Na jima ina zargin akwai wani abu a zuciyar Lurwanu game da ɗan uwansa, dan yasha kawomin sukarsa akan miyasa kaza da kaza dole sai da umarnin ɗan malam akeyi a gidan nan?, sai dai ina nuna masa ɓacin rai. Amma ban sake tabbatarwa ba sai bayan tsaida ranar auren Abdullahi da Zainabu. Da kunnena naji dukkan abinda kuka tattauna akan soyayyar da Adawiya kema Abdullahi, tare da shirinku na bayan mutuwar Zainabu zai aureta. Hankalina ya tashi, dan zan iya cewa wannan shi e sanadin girmama samuwar hawan jini na ma. Na riƙe komai a raina na kasa faɗa har ƴar uwata tazo diba ni (Ananah) banso faɗa mataba. amma na fahimci dolene na samu shawara daga wani kafin lokaci ya ƙure. Dan wannan abune mai matuƙar sarƙaƙiya. haka na samu lokaci a wani dare mukai maganar. Itama hankalinta yayi ƙololuwar tashi dajin wnanan zance. Itace ta kawo shawarar ai tunda SARAN ƁOYE kukeyi muma yakamata mubi ta ZAGON ƘASA mu kamaku a hannu dumu-dumu. Itace ta kawo shawarar sace Zainabu ranar daren aurenta, dan hakanne kawai zai wargaza auren cikin sauƙi. A cikin shirinmu Ameer ya shigo rayuwar Zainabu matsayin abokin Abdullahi. Ameer kuwa abokin Naser ne, dan Naser shine mukaba aikin a hannunsa. Nice da kaina na shiga na haɗo kayan Zainabu a ɗakinta, na kuma jajjefa wasu ta taga. Ina cikin yi Yusrah ta shigo ɗakin da alama banɗaki zata shiga. Na tabbatar taga mutum, sai dai ban saniba kota gane waye ko bata ganeba. Abdullahi yaso lalata mana shiri a ranar saboda jan ra'ayin Zainabu da yay tayi akan suyi hira. Sai dai kuma ta dalilin Adawiya hirar batai tsaho ba. Naser ya samu damar ɗauke Zainabu ya kaita wani gida. Bamu dawo da itaba sai bayan sati biyu. Daga haka muka cigaba da bibiyar duk wani taku naku. Hatta da sace Number likitan da zaima Zainabu aiki naji a raina wani a cikinkune ya saceta, sai dai banida hujja shiyyasa nai shiru. Ina kan sani na amince da aurama Abdallah Adawiya saboda ɗana tarkon farko a gareku, inason kuma tabbatar da hannun Abdallah akan shirinku, kokuwa kuna amfani da shi ne kawai batare dashi kansa ya sani ba?. Na kuma hana Yusrah tarewa dan dama bazan yarda ta tare ɗinba. Tafiya da Zainabu Umrah yanada nasaba da son sake tabbatar da komai. Na kuma tabbatar ɗin. Waya da aka ɗagama Khadijah na hana Abdullahi zuwa Nigeria duk a cikin shirinmu ne. Munsa Nasiru ya dawo rayuwar Zainabu ne daman dan ya sake wargaza magar auren da Abdallah keta naci da son sake ganin ya ƙullu tsakaninsa da ita. Da kuma sanin da nai duk cikin shirinkune”.. 
        “Maman Aaida data zama ƙawar Adawiya a saudia duk a cikin shirinmune itama. Mune muka sakata samun kusanci da Adawiya da ɗorata mataki-matakin kasancewa da Abdallah, a tunaninmu ko zaku dawo hayyacinku ku yarda da ƙaddara. Amma sai kuka sake tura kanku a cikin ramuka. A tarayyar maman Aaida da Adawiya ne ya bamu damar sake fahimtar bada sanin Abdallah kuke wani abunba. Dan ba komai kuke sanar masa akan shirinku ba, sannan lallai da gaske yana son Zainabu duk da ya raba hankalinsa biyu akan soyayyarta da dukiyar mahaifinta da kuka ƙwaɗaita masa a rai. Ta kuma hakane muka fahimci banzar sana'a da Abdallah yake ƙoƙarin jefa kansa a ciki. Amma Alhmdllh munyi ƙoƙarin maidosa hanya ta dalilin mijin maman Aaida ɗin, wanda ta hannunsa mukejin duk wani motsin Abdallah a yanzu haka. Maganar cikin Zainabu shine ya hautsina min tunani, saboda batare kukai aikinba yasa ban fahimci komaiba a ciki ba, duk da ina zargin kuɗinne duk da haka. Koda na tabbatar Zainabu takai mutuncinta gidan aure wannan ruɗanin na maganar ciki bai barniba sai yanzu da Fauza ta warware komai akan samuwar ciki da fitarsa. Na kai Uwaliya aiki Abuja ne dama dan Lurwanu yay yunƙurin yin amfani da ita kamar yanda Nasiru ya gano mana hanyar da sukebi wajen aamfani da Rabi itama. Na tabbatar alwashin da yahya ya ɗauka akan gano ko wanene bazai tashi a banzaba. Bakuma zai samu sauƙin ganowarba sai da wani a tsakani. Shiyyasa na tura Uwaliya ta fara sauka gidan Lurwanu ta kwana biyu sannan aka kaita wajen Zainabu. Ita kanta batasan amfani zamuyi da itaba, na ɓoyene saboda fahimtar idanunta a buɗe suke dasan kuɗu itama. Ko nawa Lurwanu ya bata lallai zata amince tai masa aikin daya buƙata akan Zainabu. Ankoyi sa'a shirinmu ya tafi dai-dai saboda Nasiru ma mutumne mai ƙwaƙwalwa da hikima. Hatta da yawan shigowa Najeriya da Abdallah ke yawan yi suna ganawa da Lurwanu duk mun sani dan duk inda yasa ƙafa Nasiru na biye da shi batare da yasani ba. Kai hatta binmu da Abdallah yayi ƙasar da akaima Zainabu aiki nasani. Dan ko a randa Yahya ya gansu suna magana shi da Lurwanu nima na gansu, sanin da nayi babu ta hanyar da zasu iya cutar da Zainabu saboda tsaron da take samu a wajen yasa na watsar da al'amarinsu. A yanzu haka mijin maman Aaida shine ya taso mana ƙeyar Abdallah zuwa Najeriya harya halarci wannan bikin duk da yazone a makare”.
       Ta ƙare maganar da nuna inda Abdallah ke zaune kansa a duƙe tamkar munafuki. Harga ALLAH da yawan mutanen dake falonma sai yanzu sukasan da zamansa a falon. Hajjo ta sake gyara zamanta tana duban kowa.
       “Nasan wasu zasuce miyasa duk nasan wannan amma na ɓoye matsayina na mahaifiya ga waɗan nan yara su duka?. Amsarku itace duk da ni mahaifiyace a garesu fitowa da lamarin kai tsaye dasa sabuwar fitinace da zatafi wadda muke ciki girmama. Dan inhar da tun a wancan lokacin na fiddo komai zasu kare kansu akan ba haka bane, su jefa zuciyarmu a ruɗani mu duka kokuma su canja salo, ko komai ya ɓaci duniya tasan halin da muke a ciki maƙiyanmu dake a waje su sami ƙofar yin kutse cikin wannan zuri'a su ƙarasa ɓarar da sauran abinda ya rage daga garemu. Ƙyaƙyƙyawar rayuwar da aka gina tsahon shekaru zata wargatse ta lalace kowa ya fita a hayyacinsa. Idan hakan ta kasance banci riba ba. Sannan wahalar da malam ya sha akan son gina zuri'arsa baici riba ba kenan shima. Dukansu ni na haifesu, tun a ƙuruciya nasan halin kowannensu. Dama can Lurwanu hatsabibine tun yana ƙanƙaninsa, a cikin ƴan uwan nan nasa babu wanda baisha wahalarsaba. Kaifin addu'a ne kawai ya ladabtar da shi, sai kuma kawaici da iya zama da su da ɗan uwansu yayi. Na yarda inhar ka samu ƙyaƙyƙyawar tushiya a cikin yabanyarka da izinin ALLAH zaka azurta da ƙyaƙyƙyawar albarka. Kasancewar ɗan malam ɗa nagari, mai haƙuri da kawaici, mai juriya da riƙe girmansa matsayin babba ga ƴan uwansa shine ya taimaki wannan zuri'a da kaiwa haka batare da mutanen waje sunyi tunanin samun ɓarakar shigowa cikinmu su wargazamuba. ALLAH yayima ɗan malam baiwa da ƙyautar abubuwa da yawa. Ilimi, hankali, dattako, dukiya, sanin ya kamata, nasaba. Sai dai hakan ba yana nufin zai more rayuwarsa ɗari bisa ɗari ba tunda ya haɗa komai. Shiyyasa ALLAH ya jarabcesa da atsabibancin Lurwanu dana matar ɗan uwansa Mustapha. Suka dinga wajiga rayuwarsa saboda UBANGIJI ya gwada ƙarfin imaninsa. Koni da nake mahaifiya a garesa inajin sha'awar koyi da halayensa na haƙuri da juriya duk da zuciyarsa na ƙonuwa shi da matarsa da ƴaƴansu. Wannan kawaicin da uziri shine ya kaimu ga matakin nasarar da a yau gashi su da sukecin dunduniyar sane a gabanmu suna faɗin tsiyatakun da suka aikata da bakinsu, miyafi wannan nasarar daɗi ga bawa kuwa?”.
       Abban Adawiya ya share hawaye da fadin, “Babu inna, wlhy babu makamancin wannan nasara kuwa, dan hakan yana nuna mana duk mai haƙuri da tsayawa akan gaskiya, da adalci gana ƙasa da shi, ma'abocin bautar UBANGIJI, ALLAH bazai taɓa taɓar da shi ba, ALLAH bazai taɓa ƙasƙantar da shi ba. ALLAH bazai taɓa wulaƙanta rayuwarsa a hannun azzalumai ba. Ni shaidane akan hakan, dan Lurwan yaso jan ra'ayina sosai akan lamarin Yaya, kullum zancensa shine Yaya cutarmu yake a ɓoye. wai tayayama za'ai ace a raba mana gado tare, amma yazo ya fimu komai. Yafi kowa kaso mai tsoka a duka kamfanonin mu. Ga wasu harkoki da yakeyi kuma a gefe masu bala'in bashi kuɗi. Sannan kuma wai ai muduka munada ilimin addini amma tayaya za'ace kowa yafi sonsa da ƙaunarsa dajin maganarsa. Hatta mahaifiyarmu sai abinda Yaya yace takeyi a gidannan. Acewarsa wai Yaya ya asirce kowane kawai amma yake fakewa da malanta. Da farko na fara bin ra'ayinsa. Sai dai ba'ai nisaba ALLAH ya soni da rahamarsa ya fargar dani, danni dai ban taɓa ganin wani abu saɓanin ƙyautatawa ga yaya ba. Da kuɗinsa na gado ya tsaya mana mukai karatu duk da kuwa muma muna dasu. Da kuɗinsa na gado ya dinga mana hidimar rayuwa tamkar mahaifi. Idan mukai kuka shima sai kaga ƙwalla a idanunsa. Idan mukai ciwo shima sai kaga raɗaɗin a fuskarsa. Idan mukai dariya sai kuga tashi fuskar faɗaɗe da murmushi mai tsada. Shine ya nuna mana hanyar tashi mu nema na kanmu, dan shine ya fara shan wahalar kafa dukkan kasuwancin da ayanzu sune suke riƙe da duk wani motsinmu. Shine ya tsaya akanmu mukai karatu tuƙuri bayan ya tattare martabar mahaifinmu ya riƙe mana bai bada ƙofar da zamuyi sakacin da zata kufce mana ba. To miyasa son zuciya zaisa zamuyi sakaci ya sargafe tunaninmu?.  Hakan yasani janye jikina daga wannan mummunar a ƙidar naita istigifari akan zargin da aka sakani nai masa babu gaira babu dalili. Ashe ya koma sun ƙulle da matata suna cutama yaya da zuri'arsa da basujiba basu ganiba. Minene laifin waɗan nan ƙananun yaran da basuma gama sanin rayuwarba balle daɗinta. Basai nace komaiba, dan Fauza azabarma da kike ciki ta isheki. kai ko Lurwanu ka jira naka sakamakon kaima, dan duk wanda yaci zalin gwani rabbi zai saka masa da alkairi a duniya ko a lahira”.
        Abba Musbahu yace, “Tabbas haka zancenka yake Yaya Mustapha. Dan koni ma yaso jan ra'ayina. Sai dai fa ka sanni ni, a zuwan farko na shata masa layi duk da kasancewar sa yayana. Shine dalilin da yasa zama waje ɗaya a Lagos ya nema gagararmu sai da yabi ya lallaɓa yaya malam ta ƙarƙashin ƙasa aka maidasa Abuja aka buɗe masa company wanda ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnar da yake a cikinsa shi da abokan aikin nasa. Domin a duk lissafin ƙarshen shekara idan mukayi sai mun tsamo yawan cuwa-cuwa da akai da kuɗaɗen company. Shi Yaya cayake daga ma'aikatanne. Niko nasan Yaya Rudwan ne dama wlhy. Nayi shiarune kawai dan ina fatan Yaya Malam ya kamashi da hannunsa dumu-dumu. To ashe aikin nasama ba anan ya tsayaba duk bala'in da ake kunnama Yaya malam da ƴan ƴaƴansa biyu da suka rage yanada hannu aciki. Wlhy ko alhakin ƙananun yaran nan bazai barku ku zauna lafiya ba balle kuma haƙƙin yaya malam da Umm-Muhammad da a kullum burinsu su ƙyautata rayuwar ƴaƴanmu a gidan nan. Kaɗanma kuka fara gani yanzu kuma”.
          Momyn Abdallah daketa kuka tun ɗazun tace, “Lallaikam yanzu suka fara gani Musbahu. Wannan wace irin cin amanace haka? Wane kalar son zuciya ce?. Ba yaya kaɗai kuka cutarba ai, muma kammu iyalanku kun cutar damu, kun shiga haƙƙinmu. Wace irin ni'ima ce ALLAH bai baku ba a rayuwa amma ku gaza gode masa har sai kun ɗaura ɗammarar shiga haƙƙin wani. Alhalin dukiyar da kukema zarin ma kunfi mai ita amfana da ita ku da iyalanku. Wai miyasa ɗan adam ɗin da ALLAH yayma ni'ima shike fin tsaurin idon rashin gode masa? ALLAH ya baku ilimi alhalin ga wasu can jahilai ko yanda zasu bauta masa basu saniba. Ya baku lafiya, ga wasu can a gadon asibiti kwance basu da kuɗin neman lafiyar. Ya baku muhallin zama. Ga wasu can suna raɓe-raɓe basu da ko kangon da zasu raɓa. Ya muku sutura. Ga wasu can tufafin da zasusa su rufe tsiraicinsu bai wadacesu ba. Ya baku mutunci da daraja a idon duniya, bayan akwai dubunku da suka fiku shekaru a ƙasƙance. Ya baku dukiyar da bama kuda iyalanku ba, waɗanda suka raɓu da ku zaku iya ciyar da mutum sama da ɗari a kowanne yini. Ga wasu can iyalansuma basa iya wadatawa. Ya azurtaku da ƴaƴa maza da mata,  ga wasu can suna nema da miliyoyin kuɗaɗe basu samu ba. Ya azurtaku da iyaye na gari, bayan ga wasu can iyayen nasu a gidajen baɗala. Duk waɗan nan ni'imon kuka gagara godema ALLAH a kansu, to mikuke jira UBANGIJI ya muku kafin ku gode masan? Mi kuke nema kukuwa a duniya bayan duk waɗan nan tarin ni'imomin da yay muku. Bafa kunfi waɗanda basu da shi bane, ba kuma tsoronku yasa aka baku ba. Ba kuma ƙoƙarin ibadar kuce tasa aka baku ba. Kai jama'a kaicon hannu mai butilcin amsa ga mai bashi. Kaicon zuciya mai baƙin cikin cigaban mai ƙyautata mata, Kaiconku Rudwan, tabbas bazan yafe muku ɗoramin yaro akan mummunar aƙida da kukayiba........”
      Kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana. Shi dai Abban Abdallah ya kasa koda ƙwaƙwaran motsi, kansa duƙe a ƙasa ya gagara kallon kowa. hakan yasa babu wanda zai iya cewa ga a yanayin da yake.
       Baba malam ma dai kansa a ƙasa yake duƙe. Babu mai shaida yanayinsa. Umm kam ganin al'amarin take tamkar a mafarki zuwa anjima zata farka. Zuciyarta ta kasa gaskata komai akan Abban Abdallah da Fauza. Mutanen da sukafi kowa kusanci da su a gidan. Kai jama'a duniya ina zaki kaimu?.....
      Jin kowa bai ƙara cewa komai ba yasa Jay yin gyaran murya. Kusan duk kallonsa sukayi. Ya furzar da numfashi na takaici da faɗin, “To inaga idan kun gama da su zamu kaisu station mu haɗa bayanansu sai mu miƙasu kotu su amshi hukunci kamar yanda shari'a ta tanadar”.
       Tari Addah ta fara kaɗan-kaɗan, hakanne ya saka baba malam ɗagowa ya kalleta ya maida dubansa ga Jay. “Muhammad Jawaad mubar zancen zuwa kotu kaji. Ita wannan kuma miya rage mata a duniyarma gaba ɗaya. Ai wannan izayar da take ciki kawai ta isheta izina. Sai dai mu taimaketa mu miƙata asibiti kawai....”
     Murmushi Jay yayi yana jinjina kai. “Duk da haka malam ai ya kamata su fuskanci shari'a kodan hakan ya zama ilimi ga ƴan baya masu sha'awar sake aikatawa. Duk da tana cikin halin ciwo bashi ke nuna zata mutu ba, mutuwa ta ALLAH ce, takanzo a sanda taso ga wanda taso. Dan haka zamuje asibitin taga likita amma bisa ƙarƙashin kulawar hukuma. Shi ko zamu wuce da shi station”. Ya ƙare maganar yana nuna inda Abban Abdallah yake zaune.
      Baba malam zai sake magana Hajjo ta katsesa da cewar, “Ɗan malam hakan shine dai-dai kuma ya kamata. Kaga idanma da mai sha'awar aikatawa a nan gaba sai ya bada himma”.
      Tarin Addah daya ƙara ƙarfine ya sakasu duk maida hankalinsu gareta. Da wannan damar Abban Abdallah ya samu ya sulale a hankali yabar sashen. Sauran jami'an dake a waje basusan yaya aka ƙareba shiyyasa basu hana Abban Abdallah bi ta gabansuba ya wuce sashensa yaje ya haɗa duk wasu abubuwa nasa masu muhimmanci ya zuba a ƙaramar jikka ya fito. A gaban jami'an ya shiga motarsa maigadi ya buɗe masa gate ya fita batare da shima yasan mike faruwa ba. 
       Daga ciki ma babu wanda ya farga da rashinsa sai bayan an fito da Addah daketa faman zuba aman jini aka saka a mota domin kaita asibiti. Suna wucewa su Jay suka koma kan Abban Abdallah sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye. A take suka hau cigiyarsa a lungu da saƙo na gidan, sai daga baya sukeji daga bakin maigadi cewar ya fita a mota tun kusan mintuna talatin da suka shuɗe.
      A razane Jay yace, “What?!!, shine kuka barsa saboda baku da hankali?!”. Yay maganar wa yaransa. Duk rawa jikinsu ya kamayi suka hau rantse-rantse su basusan mai laifi bane. Ai kota kansu Jay baibiba ya shiga motarsa shi da Bily da Little. Suma duk suka shiga a wacce sukazo. sai da suka tambayi maigadi motar daya fita a ciki da lambarta sannan suka fice a guje.
      Wayar Jabeer Jay ya kira, yana ɗagawa ya ce, “Jabeer inason a baza zami'ai a kowacce hanyar fita garin kano domin tsaidamin mota mai Number..... Ruwan toka”.
     Jabeer na amsa masa ya yanke kiran, C.P ya kira shima dan ya taimakesu.

__________★★

       A gidan su Nu'aymah kam musalta muku halin da suke ciki ɓata lokacine. Dan motocin su Jay na fita a gidan Umm ta yanke jiki ta faɗi. Hakama Malam ƙarami shiɗe musu yayi. Ga kukan da su Adawiya keyi ya taru ya ƙara ɗaga musu hankali. Baba malam kansa dauriya kawai yakeyi dan gaba ɗaya jinsa yake kamar kansa zai tarwatse dan ciwo. Gashi su Yoohan sun wuce da Addah asibiti. Hakan yasa dole aka kwashi su Umm ma zuwa asibitin.

   Ɓangaren Abban Abdallah kam tunda ya fito anguwarsu kai tsaye hanyar Katsina ya ɗauka, shi kansa baisan mi yake shirin aikatawaba. Ceton kansa ko gudun kunya? Ko tsoro?. Gudu ya ke na hauka babu wasa a cikinsa. Musamman daya kasance ta gefe-gefen gari yake tafiyar, dan bai yarda yabi ta cikin gariba sam. Yana fara ɗaukar hanyar Ktn bayan ya gota Dawanau kaɗan ko mintuna goma baiyiba ya ga motar ƴan sanda na binsa a baya. A take ya ƙara ƙarfin gudun motar tamkar ya manta da kasancewarsa Dattijo. Abu kamar a film suka fara rere tsakaninsa da jami'ai.
       ALLAH sarki rayuwa, duk iyawarka baka isa zarce ƙaddarar UBANGIJI ba. Dan kuwa dai wannan ƴar tsere na Abban Abdallah da ƴan sanda sunansa gudu akan igiyar ƙaddara. Dan kuwa bisa tsautsayi sukau taho mu gama da wata mota dake nufo cikin kano. A take waccan tayi gefen titi, shiko ta Abban Abdallah sai ta kife ta fara wuntsil-wuntsil daga titi ya gangara cikin gona. Tun suna jin yanda yake neman ɗaukin UBANGIJI har sukaji tsit, motar kuma ta bugi bishiyar dalbejiya ta tsaya cak.
      Cikin sauri ƴan sandan da dama tuni sun fito a mota suka nufi motar domin bashi taimako. Da ƙyar kuwa akayi kama-kamar ɗaga motar aka zarosa a ciki. Gaba ɗaya jikinsa yayi face-face da jini har ba'a iya gane inane ya bugu koma yanada rai ko ya mutu. Kasancewar sun kira sun sanar sai ogansu ya basu umarnin maza su ɗakkosa su dawo cikin kano asibiti. Bisa wannan umarnin ya sakasu ɗakkosa suka juyo a guje.
    Kai tsaye babban asibiti suka nufa, cikin amincin ALLAH kuma akai sa'a can aka kai Addah da su Umm suma. Su baba Malam na tsaka da tashin hankalin abinda ya faru sabon labari akan haɗarin Abban Abdallah yazo musu. A take na gida dana asibitin suka sake harmutsewa. 
     A yanda Yoohan yaga al'amarin ya kasance sai da yaji nadamar shigewa gaba wajen wannan bankaɗe-bankaɗe. Sai gashi da idanunsa ya ga baba malam na rusar kuka. Nu'aymah kam ai sai allurar barci ya danna mata saboda yanda ta birkice kamar dai ƙwaƙwalwar ta bata gama dawowa dai-dai ba.
      Lallai wannan ranace da waɗaɗan nan ahali bazasu taɓa mantawa da itaba a jerin tarihinsu. Sauƙinsu ma har yanzu ainahin labarin bai fita kunnuwan jama'ar gariba. Sai dai kawai ana maganar Sheikh Rudwan Hashim jibiya yayi Accident a hanyarsa ta zuwa Ktn yanzu babu jimawa. A take mutane suka shiga jera masa addu'ar ALLAH ya tashi kafaɗa, musamman ma mabiyansa.
      Zan iya ce muku yanda wannan ahali sukaga yinin wannan rana haka sukaga dare. Duk da kuwa Alhmdllh zuwa dare an tabbatar da Abban Abdallah bai rasuba. Ya dai samu karaya a kafaɗunsa duka biyu da kafafu. Sai manyan raunika da sukai masa kaca-kaca da jiki. Itako Addah barci suka sakata yi. Umm ma Alhmdllh ta farfaɗo ita da malam ƙarami. Hakama Nu'aymah ta farka.
         Sai kusan tara na dare suka bar asibitin, ba kuma a barsu sunga Abban Abdallah ba dai. Yoohan da kansa ya fiddo Nu'aymah da ga ɗakin office ɗinsa daya sakata barci. Ananah ta taimaka mata suka ƙarasa shiga mota. Baba malam yaso su Yoohan su bisu can gidan su kwana amma suka bashi haƙuri akan zasu zauna anan asibitin ne. Badan yaso ba ya barsu.

       Yoohan na ganin motocinsu sun gama wucewa ya sauke ajiyar zuciya mai kauri, A ɗaya daga kujerun dake a waje ya zauna hannayensa duka dafe da kansa. Sai yanzu komai ke dawo masa a ƙwaƙwalwa tamkar almara. Dan ɗazun su Addah na bayani ne little na fassara musu shi da Umar, duk da shi yana ɗan jin hausarma kaɗan-kaɗan yanzun. 
      Kusa da shi Umar yazo ya zauna shima yana sauke nasa ajiyar zuciyar. Yoohan bai motsaba balle ya kallesa. Shima sai bai damuba ya fara magana a hankali. “Haka mafi yawancin mutanen da suka samu ɗaukaka suke. Sai kaga na nesa da su na matuƙar sonsu da begen kasancewa da su. Amma waɗanda ke tare da su mafi yawancinsu ba son gaskiya suke musu ba. Ƙaso ɗaya bisa uku a ciki zaka samu suna musu ƙauna ta tsakani da ALLAH. Kaso biyun kuwa sai kaga suna raɓe da sune bisa wannan ɗaukakar da ALLAH yay musu. A zahiri kuwa su zugasu da nunama duniya babu kamarsu, a baɗini sune masu musu SARAN ƁOYE. lallai waɗanan mutanen masu zagon ƙasa suna ɗaya daga cikin jarabawar masu mafi yawan ɗaukaka”.
      Ajiyar zuciya Yoohan ya sake saukewa. Ya ɗago ya dubi Umar a karon farko, idanunsa sunyi jajur. Ga barci ga yunwa ga gajiya. Shi kansa Umar ɗin a galabaice ya ke. “Zancenka haka yake Umar, bazan ɓoye makaba al'amarin mutanen nan ya sake saka tsoro a zuciyata gaba ɗaya, nasake jin tsoron halin mutum da ayyukansa. Wannan wane irin bushewar zuciya ne haka? Su da ya kamata su zauna suyita godema ALLAH bisa ni'imar da yay musu ta rayuwa, su dinga ibada sai suka zama masu butulcewa ta hanyar cutar da wanda shi ya kusan ƙare tasa rayuwarne a ƙyautata tasu da ta ƴaƴansu. Umar wai miyasa ɗan adam keda manta alkairi da yawan butulci ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda da biyayya wa huɗubar shaiɗan akan dokar ALLAH ne?. Miyasa ɗan adam yafi yarda ya zama mai samu bamai sadaukarwa ba?  Miyasa mafi yawan mutane sunfi sha'awar cutar da wanda suka ƙyautata musu amma sunajin tsoron mai munanasu?. Ko addu'a mutum zaiyi, sai kaji yace ALLAH ka tsareni daga sharrin masu sharri. To miyasa bama addu'ar ALLAH ya karemu da aikata sharri ga masu ƙyautata mana ne?”.
       “Wannan shine halin ɗan adam ɗin da ake faɗa Dude, munada son kanmu, duk kuma mutum mai son kasa zakaga shine kullum a cikin wahalar nema da faɗuwa. Dan bazai taɓa doguwar nasara ba. Daya samu take kufece masa. Amma saboda bushewar zuciya gobe ma sai ya koma sake neman sa'a. Kowane addini akwai na banza akwai na gari. Irin waɗan nan mutanen suke ja ana zagin addinin islama bayan shi kuma addinine mai koyar da ƙyawawan ɗabi'u. Ko shekara banyi da shiga musilinci ba, amma wlhy Yoohan na fahimci babu wani addini dake gogayya da shi akan koyar da ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Komai musilinci ya haɗa. Amma ka duba su da keda ilimin sani a tsahon shekaru sunfi zaɓar su saɓama ALLAH bisa son zukatansu”.
     Sosai zukatansu Yoohan suka ƙara rauni da wannan al'amari. Imani da tsoron ALLAH ya sake shigarsu a zuciya da ɓargo. Suma kansu dai a wannan dare sunyi barci ne kawai badan jin daɗi ba.

*_WASHE GARI_*

        Washe gari aka bama su baba malam damar shiga su duba Abban Abdallah. A lallai duniya abin tsoro. Bawa daina cikama rayuwa baki kai ba komai bane. Duk damar da kaga ka samu a rayuwa da ga rahamar ALLAH ne. Amma wlhy idan yaso ko ƙyaftawar ido baka isa gittawa ba. A jiya iyanzu shine zaune tare da ƴan uwa da iyalansa. Amma yau gashi babu ko ƙyan gani a fuska saboda tsabar jigata da rayuwarsa tayi. Ita kanta Addah jikin nata babu daɗi.
    Duk wanda ya shiga duba Abban Abdallah sai kaga ya fito da kuka. Hakan yasa dama Yoohan bai bar Nu'aymah a wajenba. Suna zuwa ma ya jata wai tazo suje wajen awo. Bata fahimci wayo yake mataba ta bishi. Sai ya kaita office yasa aka kawo mata abinci. Duk da tace masa ta ƙoshi, dan basu fitoba sai da Umm ta bata abinci ya dage sai taci. Dole taci kaɗan dan ya barta. Sauran kuma ta bashi dan ta fahimci shima yana buƙatar a tsaresa yaci abincin.
         
     Zuwa ranar dai dukan ahalin gidan sunsan halin da ake ciki, ƴaƴan Addah dake aure da ƙannen Abdallah ma duk sunzo. Ansha sabon kuka dai kam yau ma. Daga ƙarshe baba malam dake ta ƙoƙarin danne tasa damuwar yay musu nasiha da nuna musu muhimmancin ƙaddara. Ya tabbatar musu da cewar hakan jarabawane. Dan bazai yuwu dama a rayuwa a rayuwa babu jarabawa ba. Ya hana kowa kakkausan lafazi akan su Addah, dan kuwa shi a take ranar ya tabbatarma da kowa cewar ya yafe musu. Sai su cigaba da musu addu'ar ALLAH ya basu lafiya kawai.
     Baba malam ya ƙara kima a idanun iyalan Addah da Abban Abdallah. Musamman ma Abdallah da har ran yakejin tsanar mahaifinsa da Addah. Sunso su gurɓata masa tunani ALLAH ya hana hakan. Dan bayan Addah ta ɓale a cikinsu Abbansa sake zaunar da shi yay ya ɗora masa sabon karatu akan maido da Nu'aymah rayuwarsa koda ta ƙarfin tuwo ne. Wannan shine dalilin da yasa dinga bibiyar rayuwarta. Ko a randa ya bisu shopping mail ɗin nan da nufin kidnapping Nu'aymah ya je. Sai akai rashin sa'a Yoohan ya gansa tun lokacin da suke faɗansu da Aymah harta faɗa a jikinsa. Dai-dai lokacin da yake cemata ta tara musu mutane idonsa ya sauka akan Abdallah ɗin. Har suka shiga mail ɗin kuma yana sane da shi. Sannan yana akan sani yabar Aymah a wajen ita kaɗai dan yaga mi Abdallah zaiyi?.
     Lokacin da Nu'aymah taji ƙamshinsa da gittawar mutum Abdallah ne, yana gab da isa gareta Yoohan ya jasa baya da ƙarfi ya toshe masa baki suka koma ta bayansu. Cikin fushi Abdallah ya hakaɗe Yoohan ɗin yana faɗin. “Kai shasha minene haka?”.
     Murmushi Yoohan yayi sannan ya haɗe fuska. Cikin ƙanƙance ido ya nuna Abdallah da faɗin, “Idan ka bari gangancinka ya ɗora zuciyarka bisa dokin shiga gona ta. Na rantse da ALLAH Abdallah sai na dawwamar da rayuwarka a dana sani. Na fika hatsabibanci fiye da yanda kake tsammani. Dan haka ka kama kanka kafin na ajiye mutuncin ahalinka da nake gani gefe na ɓata rayuwarka. Karka zata bansan wanene kai ba da ubanka. Ka kiyayeni kona fallasaku duniya ta sanku da aiyyukanku akan ahalinku”.
     Yana gama faɗa yabar wajen, shine yaje yaja Aymah suka wuce wajan biyan kuɗi.
      Tabbas kalaman Yoohan sun girgiza Abdallah. Hakan yasa ya janye daga bibiyar Nu'aymah. Dan dama can shi mutum ne da a rayuwa bai son yawan matsawa kansa, sannan baison fitina sam. Wannan halayyar tasa tasa lokacin yana yaro ake ganinsa matsoraci a cikin yara ƴan uwansa. Dan da gaske tabbas yanada tsoron faɗa a rayuwarsa. Dai-dai da film ɗin faɗa Abdallah baya zaman kallonsa sam saboda baya ra'ayin fitina, daya zama saurayune ma dai ya fara canjawa. har zuciyar tasa tai tauri saboda zuciyar gidansu ta gado.
      Ƙin faɗama Abbansa zancen yayi. Amma yayi ƙudirin janye jikinsa daga bibiyar Nu'aymah. Daga bakin Abbansa yaji samuwar Uwaliya, dan a randa aka kawota a ranar Abbansa ya tattauna da ita tun a office kafinma a kaita gidansa. Uwaliya akwai son kuɗi. jin maƙudan ƙuɗin da Abban Abdallah ya tabbatar mata zata samu akan kaso masa auren Nu'aymah da kawo musu dukkan bayanai a kanta yasa ta amince zatayi. A ranar ya bata rabin kuɗin, sauran kuwa sai aiki ya kammala.
      Tasha murna a ranar, ta kuma tabbatar da lallai ta shigo Abuja da ƙafar dama. Yo ko Yoohan ɗin sukace ta bibiya akan waɗanan kudin ai ta halakashi kuwa.
       Wannan shine dalilin da yasa ta fara musu aiki. Sai dai abinda bata saniba suna amfani da wayar Rabi da muryartane idan suka kirata.
     Lokacin da aka wuce da Nu'aymah Austria da gaske Abdallah yaje dubatane saboda son da yake mata. Sai dai baiso Yoohan da su baba malam su gansa. Shine yaso su fara haɗuwa da Abbansa. koda suka haɗun Abban ya dinga masa faɗan da har zancen Nu'aymah ya shigo ciki saboda Addah da tazo taga Abdallah ta zata cutar da Aymah zasuyi. Anna ne Yoohan yaji da Hajjo sukaji, abinda kuma basu saniba shine baba malam ma ya gansu, ya kuma jisu. amma sai bai taɓa nunawa ko da Umm ba balle su..........✍  
[7/6, 9:39 AM] +234 913 412 2711: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 75

.............Su Jay dai sun wuce abuja, amma  duk da su Addah na a asibiti suna a ƙarƙashin kulawar hukuma ne. Bayan wucewar su Jay shi ma Omar da Yoohan suka wuce da yamma. Ya bar Nu'aymah anan kano saboda Umm bata da lafiya. Har yanzu ta kasa fida daga ruɗanin data shiga. Ga jininta yaƙi sauka yanda ya kamata. Ita kanta hajjo jininta ya hau sosai. Sai dai ita Alhmdllh bai kai na Umm da komai yazo mata a yanda bata zata ba. Bama Umm kaɗai ba hatta da ƴan uwan Umm dana Addar wannan al'amari yay masifar rikita tunaninsu da basu tsoro. Anatama Addah ALLAH wadarai da wannan hali nata. Su Hajarah kam sunyi kuka har sun rasa hawayen zubarwa. Musamman Kubrah da dama ba daɗin zaman gidan mijin take jiba. Fitinar yau daban ta gobe daban.
      Yanda gidan dai yay wani iri daga shigowa zaga fahimci akwai matsala. Baba malam salla kawai ke fiddashi. Da an idar yake dawowa gida. Komansa ya tsaya cak. Dan duk da daurewar da yakeyi a bala'in gigice ya ke da al'amarin. Bai taɓa ƙawowa a ransa cikin ƴan uwansa za'a samu mai wannan tunaninba akan dukiya dauɗar duniya. Yayi kuka bana wasaba a ɓoye, har ji yake gaba ɗaya ƙasar ta fita masa a arai.

___________★★

        Su Yoohan na isa Abuja suka iske sabon tashin hankali. Dan sun iske gidansu zagaye da jami'an tsaro. Da ƙyar ma aka barsu suka shiga saboda sanin Yoohan ɗansa ne. Cikin tashin hankali Yoohan ya ƙarasa falon inda ya tarar da ƙannensa duka da mama debora a hagitse. Suna ganinsa kuwa duk suka taso kansa a guje suna rusar kuka. Su duka rungumeshi sukayi har mama debora da Gebrail dake gudunsa a da.
     Kallonsu kawai Yoohan keyi cike da tsoro, maganama ya kasa yi. Sai da Umar yay dauriyar cewa, “Granny wai mike faruwa hakane? Ku sanar mana Please. Gida zagaye da ƴan sanda. Gaku kuma cikin tashin hankali. Ina su papa suke ne?”.
        Cikin matsanancin kuka joy tace, “Sun gudu Brother Richard”.
       “Sun gudu kamarya? Ban ganeba nikam Joy?”.
      Sakin Yoohan duk sukayi, mama debora ta kama hannunsa ta zaunar a kusa da ita. Shima Umar ɗin ya zauna. Sauran yaranma duk zama sukayi bisa umarnin mama debora. Tana sharar hawaye ta fara musu bayani.
         “John munata kiran wayarka tun jiya ai amma mun kasa samunka. daren shekaran jiya kusan ƙarfe goma na dare wani mutum ya shigo gidan nan a kiɗime jikinsa jina-jina saboda harbi da akai masa. Lokacin duk munyi barci, kururuwarsa ta sakamu tashi batare da mun shirya ba duk muka fita compound. Tun a yanda mahaifinku ya ambaci sunansa a kiɗime na fahimci ya sanshi. Dan gaba ɗaya ya ruɗe shi da Chioma da guards ɗinsu. Shine ya sakamu komawa ciki akan dole batare da munji mike tafe da wannan mutumi dake a cikin jini ba. Muna falo tsaitsaye mun kasa komawa ciki mu kwanta sai ga shi sun shigo. Duk ɗakunansu suka shiga batare da sunce mana komaiba. Sai kuma suka sake fitowa a rikice. Mahaifinku ya rungumeni yana faɗin, karna damu na masu addu'a kawai, ga ATM card ɗinsa nan duk abinda muke buƙata Gebrail zai dinga ciro mana kuɗi. Daga haka suka fice zuwa garden. Ban taɓa sanin akwai wata hanyar fita gidannan ta garden ba sai a ranar. Dan sai bayan wucewarsu da kusan mintuna talatin ƴan sanda suka shigo anguwarnan sunata harbe-harbe. wasu suka shigo nan gidan suna nemansu harda guards ɗinkun nan. Sai lokacin mukasan guduwa sukayi harsu Solomon. Amma an kama guards uku a cikinsu. Su kuma ba'asan inda sukeba har yanzun”.
       Wata irin masifaffiyar zufa ce ke ketoma Yoohan ta ko ina, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yaketa faman maimaitawa. Shi kansa Umar zancen yay masifar rikita tunaninsa. Batare da Yoohan yace komaiba ya kama hannun Umar suka haye sama. Duk binsu sukai da kallon mamakin mizaiyi?. Bai saki hannun Umar ba sai da suka shiga sashensa can cikin ɗakin motsa jikinsa. Inda tanan yana iya hango duka ƴan sandan dake a compound ɗin gidan da anguwar ma.
          Cikin matsanancin fushi ya yarfar da hannun Umar sannan ya tsatstsare sa da jajayen idanunsa. Muryarsa da tsananin kaushi da fushi yace, “Umar mi kuke ɓoye min kai da Matata akan iyayena?. kar kaimin ƙarya, dan ba ita nake buƙataba a yanzu na roƙe ka”.
      Yanda ya ƙare maganar muryarsa na rawa kamar zaiyi kuka da haɗe hannayensa waje guda kuma sai zuciyar Umar ta ƙara raunana. Hannayen ya riƙe duka a cikin nasa ya sauke. “Yoohan anzo gaɓar da basai ka roƙeniba zan sanar maka. Sai dai inason ka fahimceni Please. Nima bani da wani zaɓin daya wuce hakan”.
     Komai Yoohan bai ceba, saima cire rigarsa da yayi ya hau wani machine ɗin motsa jiki ya fara da sauri-sauri. Huci Omar ya sauke tare da fara bama Yoohan labari. Tun daga abinda ya fara ji akan kashe Nu'aymah da papa ya bama Dr Mateo kwangila har zuwa ɓoyayyun harƙalloli daya fahimci papa nayi a ɓoye. Kamar safarar miyagun ƙwayoyi da cocaine. Safarar makamai, satar yara yana tarasu a wani gida acan ƙauyensu........
       Ihunsu Mama debora daya cika gidanne ya saka Yoohan dan Umar fita da gudu zuwa ƙasa.
     Cike da firgici da tsoro Yoohan da Umar ke kallon Little bee da tawagar jami'an hukumarsu. Ta haɗe fuska matuƙa, babuma alamar tasansu. A fusace Yoohan yace, “Lafiya kuwa?”.
      Uffan Little bee batace masa ba. Sai ma i'd card ɗinta kawai ta nuna masa. Sannan ta ɗora da faɗin, “Muna buƙatar shiga ɗakin Mr Goshpower domin yin bincike”.
     Magana Yoohan zai sakeyi Umar ya girgiza masa kai alamar karya ce komai. Hannayensa duka biyu ya tura cikin aljihun wandansa ya koma jikin bango ya jingina saboda jiwa dake neman yaddashi a ƙasa.
      Da Gebrail sukai amfani ta hanyar ɗora masa bindiga akai. Tuni fitsari ya jiƙe gaban wandonsa kuwa. Babuko kwana-kwana wajen kaisu har sashen papa. Tun a falo suka fara bincikensu. Yoohan baiyi niyar binsu ba, amma sai Omar ya kama hannunsa suka shiga. Basu sami komai a falon ba sai cctv dake a ɓoye. dan haka suka wuce cikin bedroom. Akan idon su Yoohan akaima ɗakin dalla-dalla. Ta hanyar tsabar ƙwarewar aiki su little suka gano ɓoyayyar drawer ɗin nan ta sirri dake a jikin bango. Sai dai kuma garƙame take da security, gashi kuma basu sani ba. An gwada password kala-kala baiyiba. Daga ƙarshe suka yanke shawarar yin amfani da na'urar fasa ƙarfe ko wane irine. Ta wannan hanyar aka fasa wajen. Sosai Yoohan ya firgita da ganin kalolin bindigu, da harsasai kala-kala. Sai tarin hodar ibilis da ƙwayoyin shaye-shaye masu matuƙar haɗari. 
      Kasa daurewa Yoohan yayi, sai da ya furzar da wani zazzafan hucin da sai da kowa ya juyo ya kallesa. An ƙara bibbincika ɗakin sosai kafin su kwashe duka kayan da suka samu ɗin sannan suka sakko ƙasa inda su mama debora keta faman kuka. Ganin makaman kuma ya sake rikitasu fiye da farko.
         Koda suka fito sai suka shiga bincike gaba ɗaya lungu da saƙo na gidan, su dai su Yoohan suna binsu ne kawai da idanu. Sai da suka tabbatar da basu sake samun komaiba sannan suka tattara waɗanda suka samu ɗin zuwa mota. Sun buƙaci tafiya da wasu a cikinsu zuwa asalin ƙauyen su Yoohan ɗin, zakuma su cigaba da riƙesu har sai papa da madam Chioma sun bayayana kansu. 
      A take falon ya sake ruɗewa da kukan su mama debora. Ganin yanda suke neman fita hayyacinsu Yoohan ya ce zai bisu kawai shi da Gebrail. Kuka harda kururuwa Gebrail ya fashe da shi. Abun zat-tausayi zad-dariya. Haka su Mama debora naji na gani aka wuce da Gebrail daketa kwasar kuka da Yoohan.
       Yoohan bai sake fahimtar al'amarin mahaifin nasu babba bane sai da suka iso airport, anan ma wasu jami'an suka tarar da alama jiran isowarsu sukeyi. Babu wani tsayawa ya akai ya za'ai aka shiga da su jirgi. Gebrail na nane da Yoohan cikin tashin hankali. Koda suka isa canma sun iske wasu jami'an tare da helicopters biyu. Nanma babu ɓata lokaci suka shiga zuwa can ƙauyensu. A canma sun iske garin a ruɗe sosai, dan uban batakashi akeyi tsakanin jami'an tsaro da yaran su papa. Gaba ɗaya ƙauyen a harmutse yake, dole aka bar su Yoohan a helicopter ɗin su little kawai suka firfita suma da nasu bindugun. Sai a yanzu ne fuskar Yoohan ta nuna tsantsar ruɗani. Gaba ɗaya komansa ya sare akan wannan al'amari. Lallai da alama mahaifin nasu ya jima cikin wannan mummunar harkar batare da su sun sani ba. Haba no wander yake ganin mahaukatan kuɗi basa gajiya da shiga accaunt ɗin papa. Sannan sam bayajin fargaba ko ciwon fitar da kuɗi wajen musu hidima ta bajinta.
    Kallo dai iya kallo su Yoohan sun yisa. Daga ƙarshe su Little bee suka sami nasarar cafke gaba ɗaya yaran papa da su Uncle Godwin da aka ritsa a garin tun jiya. wasu sun sami raunika, wasu ko ma an kashesu. A cikin su little ma wasu sun sami raunuka.
      Daga haka aka fasa ƙaton gidan da su papa ke ajiye yaran da suka sato ciki. ‘Hazbunallah’. Yarane mata da kananu, sai wasu baƙaƙen ƙartan bayi da kallonsu kawai ya ishi mutum amai, wasu da tsohon ciki, wasu cikin ƙananu ne, wasu kuma suna a tsaka tsaki. Sai jariran da aka haifa da har an gama cinikinsu ga masu buƙatarsu.
        Tsabar tashin hankali little sai da tayi kuka ita da sauran ƴan uwanta jami'ai mata. A take Dawood yay kiran Jay ya tabbatar masa al'amarinfa babbane gaskiya. Ga ƴan jarida sunyi caa suna neman bayanai. Kamar yanda I.G na ƴan sanda ya kasance a wajen dole Jay ma ya taho ƙauyen da tawagarsa su Hafeez. Hakama gwamnan jihar dole ya shigo ƙauyen, dan kuwa kowa yasan da taimakon su papa ya hau mulki. Dan papa nada matuƙar ƙarfi cikin jahar tasu musamman daya kasance yana riƙe da muƙamin shugaba (Pastor).
      Dole aka kawo manya-manyan motocin guda uku aka kwashe kaf mutanen dake gidan zuwa can babban birnin jihar. Su Dawood kuma suka shiga yima gidan filla-filla da bincike ta ko ina. daga haka suka sake kwasar jiki zuwa ainahin family house ɗin su Yoohan ɗin da suke zama idan sunzo garin. Ananma an samu abubuwa da dama, harda ɗakin sirri dake danƙare da Computers da suke gudanar da ayyukansu na yima mutane kutse, da zuba uwar sata a asusun bankuna dana mutane. A takaice dai papa shugabane mai zaman kansa na ƴan Yahoo.
      Tuni zuciyar Yoohan ta gama bushewa tayi tauri akan wannan al'amarin. Binsu kawai yake da kallo tamkar mai kallon film a television. Shi ba zuwa ƙauyen yakeba sosai saboda karatun daya tafi ƙasashen ƙetare yayi. Bayan ya kammala kuma aikinsa baya bari sa samun nutsuwar irin waɗan nan ziyarce-ziyarcen. Idan ka gansa a ƙauyen sai lokacin Christmas da hutun ƙarshen shekara. Wannan kam a ko ina yake a duniya dolene sai yazo bisa sharaɗin papa. koda baizo Christmas ba zaizo a kwanakin ƙarshen shekara yayi new year. To mafi yawancin lokaci ma sai dai ya samesu anan. Bai taɓa damuwa da sanin sarrin duka gidanba. Iyakacinsa ɗakinsa da garden. Sai ko compound. Yawo ma a ƙauyen sai idan su Osin na tare da shine yake fitarsa. Amma shi kaɗai baya zuwa ko ina. Yafi buƙatar yay zamansa a gida.

      Tone-tone dai kam an yisu a ranar game da sirrikan papa masu ban mamaki da tsoro. Hakan yasa su Jay fahimtar riƙe su Yoohan bazai taɓa saka Papa kawo kansa hannun hukumaba. Dan haka suka sallamesu su koma gida kawai. Dan aikine babba wannan ya wuce wasan yara. Shi dai Gebrail yaji daɗin barinsu da akayi. Yoohan kam gaba ɗaya kansama ba aiki yakeba a wannan lokacin. Dan brain ɗinsa ta toshe.
         Tun a wannan daren ƴan jarida da masu alhakin faɗin albarkacin baki suka fara kayayatu. Inda ƙungiyar catholic tai azamar fara fitowa ta banbanta tafiyarta data goshpower. Sun tabbatarma duniya bada yawunsu ko saninsu yake aikata duk wannan al'amarin ba. Hakama gwamnan jiharsu da manyan ƴan siyasa sun fito sun nisanta kansu da papan kai tsaye.
     Tofa abin magana ya samu lallai da gaske. Dan ƙasar tuni ta ɗauka tare da kafafen yaɗa labarai na televisions da redios. Yanar gizo dama duk wata kafar maida yanda akayi. Videos ɗin da wasu a cikin ƴan ƙauyen sukai ƙarfin halin ɗauka tuni ya fara yawo a yanar gizo. Yayinda ƴan jaridu suka fara tabbatar da cewar mafi yawan yaran da aka samu a gidan nasu papa yarane da aka sata daga arewacin ƙasar. Ƙalilanne a cikinsu suka fito daga kudanci. Tofa magana ta girma.

__________★★

        Baba malam ne ya fara cin karo da wannan babban al'amari a labaran ƙarfe goma na dare da yake kallo. Sai ga Nu'aymah data shigo kawo masa shayin da rabi ta dafa masa dan baya iya cin abinci sosai itama ta ganema idanunta.
     Da ga ita har baba malam ɗin kasa magana sukai, sai tv da suka zubama idanu da tsananin mamaki da al'ajabi. Ganin tayi tsaye ta kasa zama baba malam yace ta zauna saboda ba ita kaɗai bace. Zama tai a kujera jikinta har rawa yake saboda ganin yanda aketa bata kashin ruwan harsasai a ƙauyen su papa da aka nuna. Idonta bai ganar mata Yoohan ba sai lokacin da akaje family house ɗinsu. Anan kuma Umm ma ta fito ta samesu. Duk da batajin ƙarfin jikinta itama saita zauna zaman kallo.
       Can sai ga Hajjo a rikice itama ta shigo tana ƙwalama baba malam kira. Sai da Rabi ta sanar mata yana falonsa sannan ta nufo nan. Tunkan ta shigo ta fara faɗin, “Ɗan malam kaga kuwa tsiyatakun da aka tono yau na surikinka?”. Tana ida shigowa taga suma abinda suke kallo kenan ta shiga tafa hannu da jera salati. A kusa da Nu'aymah ta zauna suka cigaba da kallon tare.
       Kafin kace mi sai ga kiraye-kirayen waya sun fara shigoma Baba malam a wayoyi. Yasan kwanan zancen, dan haka yaƙi ɗaga wayar kowa. Kansama gaba ɗaya sai ya ƙara ɗaukar zafi. duk da yasan papa riƙaƙen ɗan harƙalla ne baiyi xaton al'amarin ya kai haka girma ba. Dan yasan papa ne shekaru ashirin da takwas da suka shuɗe a jami'ar ƙasar France, lokacin yana haɗa degree ɗinsa na biyu a can. Shima papan yazo ne wani course na wata tara. Tunda yazo makarantar a tantirinsa yazo dama. Dan karatunma asha ruwan tsuntsaye yake masa. Duk wasu abokan banza zaka samu papa da su, dan adalilin takurama wata yarinya mai suna Sadiya ƴar ƙasar Niger da papan yayi akan dole sai tayi soyayya da shine ya zama sanadiyyar sanin juna da sukai da baba malam ɗin. Kasancewar baba malam shine shugaban mss na makarantar a lokacin duk da ba wani ƙarfi ne dasu ba sai yay tsaye a kan lamarin papa da Sadiya. yayma papa gargaɗi sosai akan ya fita harkar yarinya ya barta tai karatunta. Idan ba hakaba kuma zai ɗauki mataki a kansa. A lokacin papa baice komaiba sai dariya da suka shiga sheƙawa shi da yaransa suna busama baba malam hayaƙin taba da suke sha. Baba malam dai ya ja musu gargaɗi ya kama gabansa. Ba'a rufa wata ɗaya da wannan al'amari ba tsakanin papa da baba malam sai baba malam yaga wai papa  ya zama Pastor. Harma yana kula da church ɗin cikin jami'ar. Abin ya ɗaure kan baba malam sosai, dan ya fahimci lallai da biyu goshpower ya samo wannan muƙamin.
      Baba malam dai baice komaiba, dan sunama haɗa kwanaki sama da takwas basu haɗuba kasancewar kowa da sabgar gabansa. Sai dai tunda Goshpower ya zama Pastor a cikin jami'ar ƴar tsama mai ƙarfi ta shiga tsakaninsa da baba malam. a kuma lokacin akaima Sadiya fyaɗe tare da kasheta. Wannan al'amari yayi masifar girgiza baba malam dama sauran musulmai da suke a jami'ar. Dan kowa yasan goshpower ne zai iya aikata hakan ga sadiya. Su baba malam sun kai ƙararsa ga hukumar makaranta, an kuma amshi ƙorafinsu a zahiri, amma babu alamar za'a ɗauki wani mataki. Hakanne ya harzuƙa zuciyar baba malam yaje ya samu Pastor goshpower da kausasan maganganu. Amma abin mamaki ko ɗar papa baiyiba. Hasalima da bakinsa ya sake jaddadama baba malam cewar shine yayma Sadiya fyaɗe ya kuma kasheta. Tunda taƙi yarda ta bashi kanta da arziƙi shiyyasa ya ƙwata da ƙarfi dan yana ƙwaɗayinta sosai. Kasheta kuma da yayi yayine dan yaga mi baba malam ɗin ya isa yayi?.
       Baba malam akwai zuciya, hakan yasa a take ya fara dukan goshpower da iya ƙarfinsa. Kafin kace mi makaranta ta ruɗe da ihun ɗaliban dake ta wajen da abin ke faruwa. Kowa yayi mamakin yanda baba malam ke dukan goshpower. Dan babu wanda yay tsammanin zaiyi wannan ƙarfin. Musamman da ake ganinsa shiru-shiru baida kwaramniya sam a cikin ɗalibai. Hasalima ko ƙwaƙwaran aboki baida shi. Jina jina baba malam yayma papa a wannan lokacin, dan da ƙyar security ɗin makaranta suka amshi goshpower a hannun baba malam. Harma wasu na tsammani da zaton papa ya mutu.
     Kwana biyu da yin wannan rikici abin mamaki sai ga takardar sallama baba malam ya samu daga hukumar makaranta. Babu wanda yay kiransu ya zauna dasu domin neman ba'asin yanda akayi? Musulman ɗalibai dake makarantar hankalinsu ya tashi akan wannan rashin adalci da akaima baba malam. Amma sai shi baba malam ɗin ko a jikinsa. Dan dama koda basu koresaba yayi alƙawarin bazai ƙarasa karatunsa a wnann makarantarba, tunda har za'a iya kashe rai suƙi nutsuwa suyi ƙwaƙwƙwara bincike akai su gano mai laifi su yanke masa hukunci. Tunda baba malam ya baro jami'ar France bai sake haɗuwa da goshpower ba sai a sanadin Yoohan. Wannan shine dalilin da yasa yay matuƙar mamaki akan papa bai isa haihuwar Yoohan ɗin ba sam. Sai dai kamar da Yoohan ke ɗanyi dashi ya sakashi yin shiru da tunanin ko acan wajen yima ƴaƴan jama'a fyaɗen ya samosa. Sai dai zuciyarsa sam bata yarda da wannan tunaninba. Musamman da yaga yanda Yoohan ke da ƙyawawan halayya abin koyi. Sai gashi a hankali ya fara fahintar akwai wani ɓoyayyen al'amari dake a tsakkiyar papa da Yoohan, daga hakane ya fara burin saka ido aka lamarin papa ta hanyar Nu'aymah da wasu ɓoyayyun hanyoyi nasa. To binciken nasa bai gama kaiwa inda yaso ɗinba Jay yazo masa da tambayoyi akan Yoohan ɗin shima. sai dai shirin nasu akan binciken papa ɗin bai ƙarasa kaiwa can ɗinba gashi ɓoyayyun halayen papan sun fito a idon duniya. 

        Tun a dare Nu'aymah ta shiga neman Yoohan amma ta gagara samunsa sam. Sai washe gari tana idar da sallar asuba ta kuma gwadawa anan ta samesa. Hankalinta ya tashi dajin muryarsa. Ta tabbatar masa ita dai zatazo abujan tunda taji kamar baida lafiya. Amma sai ya lallasheta akan tai haƙuri ta cigaba da zama a kano dan gidansu bazai zaunu a garetaba yanzu kodan halin da take ciki. Bazai yuwu taita ganin tashin hankaliba. Jin yanda yaketa lallashin natane yasa taɗanjin sassauci. Daga haka ta kira Umar dan ta ɗan ƙarajin bayanai. Shine ya tabbatar mata da karta damu Yoohan ɗin yana cikin ƙoshin lafiya damuwar abinda ya faruce kawai. Hakan kuma dolene a garesa tunda al'amarin yazo masa a bazata. 

     Baba malam ma ya kira Yoohan yay masa nasiha da kwantar masa da hankali, tare da faɗa masa yayta addu'a a ransa ALLAH zai sauƙaƙa musu waɗanan jarabawoyi da suka samesu a kusan lokaci guda.

★★★★

       Jami'an tsaro sun cigaba da neman papa, tare da zaƙulo dukkanin abokan harƙallarsa ta ƙarƙashin ƙasa. Harma waɗanda suke a ƙasashen ƙetare. Yayinda zancen yara da ake zargin mafi yawansu ƴan arewacin ƙadar ne ya tabbata. Wasu tun suna yara aka satosu, wasu ko suna a manyansu. An saida wasu ga masu buƙata. Wasu kuwa ana kaisu wasu ƙasashen ƙetare batare da sauran sunsan mi suke yi acan ba.
    Yarinyar da aka tattauna da ita tace, shekararta tara kenan a hannunsu. An satota ne a jihar Jigawa bisa hanyarta ta dawowa daga makarantar islamiyya a wani yammaci ranar litinin. Tana kuka tace, “Wani abu suka shaƙamin, wanda yasa ban sake sanin ina kaina ya keba sai a wannan gidan da kuka ganni a ciki. A randa na dawo hayyacina abinci kawai aka bani naci wani ƙato ya haikemin yaymini fyaɗe. Naga tashin hankalin rayuwa kala-kala a wannan tsakani, dan saida ta kasance kullum sai mutumin nan yayi amfani dani. Bai barniba sai da aka tabbatar da na samu ciki sannan. Sai a lokacin na fahimci ashe duk macen dake gidan hakane ke faruwa da ita. Waɗanan gardawa zasuyita amfani da ke ne har sai ka samu ciki. Ka gama wahalar rainon cikin a randa ka haihu a ranar za'a ɗauke yaron, watama ko ganin fuskar ɗan nata batayi. Kina haihuwa da sati biyu waɗan nan maza zasu koma yi miki fyaɗe har sai kin sake samun wani ciki”.
    Kuka ya sarƙeta ta kasa ci gaba. Sai da tayi sosai wasuma a jami'an tsaron na tayata, harma da ƴan jaridar dake ɗaukar rahoton. Da ƙyar ta cigaba da faɗin, “A shekara tara dana samu ni yanzu haka haihuwata takwas, dan duk shekara ƙa'idane sai ka haihu, a yanzu hakama satina baifi shida dayin wata haihuwarba. Bana tantama kuma ƙila na ƙara samun wanu cikin ma”.
       Ai Yoohan baima san sanda ya fashe da kuka ba, dan tunda yake a rayuwarsa bai taɓa cin karo da makamancin tashin hankali irin wannan ba. Sai gashi wai mahaifinsa shine tushen aikatawa. Abin takaicima harda sanin Momynsa. No wander ta mitsike idonta ta nema yin tarayya da shi duk da shiɗin ɗanta ne. A yanda yakejin zuciyarsa game da waɗannan yaran koshi ya ga Papa da Momy sai ya ɗaukesu ya damƙama hukuma ya rantse da ALLAH kuwa.

_________

      A kano ma dai su Abban Abdallah na cigaba da kasancewa a hannun kulawar likita. Duk da dai jikin nasa kam dai babu ƙyan gani dan gaskiya yanajin jiki, dan har yanzu baya iya gane kowa dake a kansa. Addah ma dai jikin nata wataran yayi sauƙi wataran yayi tsamari. Duk da tsiyatakun da suka tafkama baba malam kuma bai gaza wajen fidda kuɗaɗen da ake kula da lafiyarsuba. Sannan shiketa tausar ƴaƴansu da zantuka masu taushi, tare da ƙoƙarin ganin wannan al'amari ya zama sirri a tsakaninsu batare da sauran jama'ar gari sunsan tushensu ba.
     Abban Mustapha dai ya riga ya saki Addah, sai baba malam ya hanashi faɗa mata ita da ƴaƴanta, sunbar maganar a tsakaninsu su manyan har sai ta samu lafiya kamar yanda baba malam ya roƙa mata alfarma. Dan yanzu bai kamata a haɗa mata zafi goma da ashirinba musamman daya kasance tayi nadamar kurakuranta. Halin datake ciki kaɗai ya isheta tashin hankali mai tsanani ai.
       Aikoda gaske tashin hankalin da Abban Abdallah da Addah ke ciki ko shi kaɗai kam ya ishesu. Dan suna cikin tsananin azabar ciwo da magauta. Duk taurin zuciyarka ka gansu dole ka tausaya musu kuwa.

     Haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa. Su Adda ba faman jiyya a asibiti, jami'an tsaro na neman su papa ruwa a jallo. Masu maida yanda akayi na cigaba da tattaunawa da ƙara gishiri da magi akan al'amarin. Yayinda ƙungiyar kiristoci ma ta fito ta nuna cewar bata goyon bayan papa sam, sannan bata tare da shi. Hakama Pastors nata sharhi akan papan da tabbatarma duniya wamnan ba halin kirsata na ƙwarai bane aka samu papa da shi, dama suma ba ƙaramin matsi suke fuskanta daga garesaba ta ƙarƙashin ƙasa.

     Duk wannan cece kuce da ake famanyi suna shiga kunne papa a maɓoyarsa shi da mike, Anthony, Joshua da Solomon, sai madam Chioma. Abinda yasa aka gaza samunsu shine ajiye duk wani layin wayarsu da sukayi, dama duk abinda zaisa a iya bibiyarsu. Godwin da sauran ne ke a hannun hukuma. Duk wahalar da sukesha kuma sunƙi faɗar ina za'a samu su papa saboda basu saniba suma.

    Haka dai kwanaki suka cigaba da shuɗawa har Yoohan ya bar ƙasar saboda aikinsa, Nu'aymah ta cigaba da zama anan Nigeria bisa shawarar da baba malam ya bama Yoohan ɗin. Dan rashin kama su papa ba ƙaramin haɗari baneba. Musamman daya kasance Nu'aymah tana ɗaya daga cikin mutanen da a yanzu haka suke a cikin mummunan ƙudirinsa ita da baba malam ɗin. Yoohan kuwa yaji wannan shawarar duk da baiso yin nisa da iyalinsaba. Itama kuma Nu'aymah taji daɗin haka duk da kewar mujinta na tare da ita. A haka kwanaki suka cigaba da shuɗawa cikin rahamar UBANGIJI da jin ƙansa.
       Cikin Nu'aymah ya shiga watan haihuwa, aiko su Umm nashan raki sosai da taɓara, Hajjo taita mata dariya da kiranta ragguwa. Yoohan kansa yanashan nasa shagwaɓan ta waya. Inko yazo ƙasar kuka rurus take tasasa a gaba tanayi wai itadai ta gaji wlhy a cire mata cikin nan. Takan bashi tausayi da dariya, sai dai bayayin dariyar sai yayta lallashinta da nuna nata tayi haƙuri saura ƙiris ai.
       Ai ko zuwan ƙarshe da yayi yay kusan sati ɗaya sannan ya koma, kamar jira Aymah keyi ya wuce washe gari ta tashi da naƙuda. Wayyo zo kaga raki wajen masu haihuwa. Yoohan har ALLAH ya isa sai da yasha a wannan ranar😂, takuma rantse bazata sake yarda da wani cikiba dan wannan haihuwa daga ita bazata sake ba. Tun hajjo dake tare da ita a asibiti itada Mama amaryar Abba Musbahu na danne dariyarsu har suka kasa saida sukayi. Baiwar ALLAH tako sha wahala sosai, har dai ALLAH ya sauketa lafiya ta sunkuto jaririnta dake ta faman canyara uban kuka.
        Su Dr Aysha sun gyarata tsaf da bata dukkan kulawa kodan darajar mijin aurenta da iyayenta. Shima yaro aka gyara shi tsaf sannan aka fiddoma su Hajjo shi. Kowa sai ambaton masha ALLAHU yakeyi a baki da zuciya. Yayinda Hajjo ta saka Ahmad ya kira mata Yoohan wai itace zatai masa albishir. Aiko ita dince tai masa dan ya dai gane hausar tata saboda Alhmdllh zuwa yanzun harshensa na ƙara faɗawa. Rikicewa yay gaba ɗaya, dan yasan dai hajjo bazata faɗa masa Nu'aymah ta haihu ba danta zolayesa. Sai kawai ya durƙusa yay sujidar godiya ga ALLAH. Duk da a ransa yaji babu daɗi da sai da ya taho ta haihu. Sauƙinsa ma zai tafi hutun ƙarshen shekarane daman dan al'umar Christians nata shirin bikin Christmas.

         Zuwa dare aka sallami su Nu'aymah da ɗan jinjirinta bayan an tabbatar da ingancin lafiyarsu, kai tsaye sashen hajjo aka nufa da Nu'aymah, duk da ita dai a ranta taso zama ne wajen Umm ɗinta. Kafin su kwanta Yoohan ya kirata a waya a karo na kusan huɗu kenan. Dama tuni hotunan ɗansa sun gama cika masa wayarsa. Ganin jaririn nan Abdallah har hawaye sai da yayi, dan da yanzu ɗansane fa Nu'aymahrsa ta haifa masa. Sai dai ƙaddara ta riga fata labarin ya canja daga yanda ya fara.  
         Video call sukayi mai tsaho ita da Yoohan, tana rungume da ɗansu da sai a yanzune ta samu damar zaman masa kallon sosai. Yayinda ran Yoohan ke cike taf da tarin farin cikin ganinta da yaron a jiki, tayi ƙyau sosai ta kuma dace da uwa. Musamman da ƙibar ciki ta sata komawa wata babbat mace. Bai barta ba har sai da ya ga tana hamma. Yasan babu abinda tafi buƙata a yanzu kamar barcin, dan lokacin da cikin ya shiga watan haihuwa bata iya barci sosai. Wani lokacinma kwana take a zaune, sai da rana takan ɗanyi ta rage nauyin ido.
       Washe gari ƴan uwa da abokan arziƙi suka fara isowa gidan ganin ɗan jinjiri. Yayinda tun a farar safiya ta amsa kiran ƴan Abuja su Mama debora, dan har yanzu suna nan a gidan su Yoohan ɗin tare da jami'an tsaro. Tun jiya kuma Yoohan ya sanar musu da haihuwar Nu'aymah harma ya tura musu hoton jariri. Sunso kira tun da daren yace suyi haƙuri sai da safe. Aiko gari na wayewa saiga shigowar kiransu ta hanyar video call.
    Nu'aymah tasha mamaki matuƙa ganin wai harda Joy da Gebrail cikin ƴan murnan haihuwarta. Sun mafi kowa zaƙewar cewar zasuzo kano. Taji daɗin hakan har cikin ranta, dan koba komai dai ba'a canjama tuwo suna. Dole su wannan ɗan nata zai kalla matsayin dangin mahaifinsa. Sune kuma adonsa a cikin al'umma.
       Baba malam shine ya tauna dabino ya bama jin jiri bayan yayi kiran Yoohan ya tambayesa akan yayi masa huɗuba kokuwa zaizo da wuri yayma yaronsa da kansa. Maganar ta bashi kunya sosai sosai. shi ko bama ɗansaba koshi kansa ai Baba malan ya isa da shi. Cikin jin nauyi yace, “Uncle dan ALLAH ka daina neman izinina aka. dukkan abinda ya dace da shi. Kai masa dan kaima ubane a garesa ai. Suna kuma asa masa sunanka, dan ina fatan ya zama mai gadon ɗabi'u da ƙyawawan halayenka da tarin ilimi”.
      Baba malam yaji daɗi sosai da wannan girmamawa. dan haka yayma yaro huɗuba da suna Muhammad Soorajidden. Sai dai ya bar hakan a ransa sai ranar suna idan ALLAH ya kaimu. Ya dai sanarma Umm da hajjo kawai.
         A washe garin data haihu da kwana biyu aka maido su Abban Abdallah gida daga asibiti. Dan baba malam dai da kansa ya roƙa Jay akan a bar maganar zuwa kotun ɗin nan a barsu suji da ciwukan dake tare da su. Badan Jay yaso ba ya yarda da buƙatar ta baba malam aka rufe case ɗin ma gaba ɗaya daga can ofishinsu.  jikin Abban Abdallah yayi sauƙi, sai dai kuma fa akwai matsaloli sosai, dan sakamakon karayar da yayi a kafaɗu wuyansa baya iya zama sam, gashi kansa ya bugu ƙwaƙwalwar sa ta samu matsala daga ciki, matsala irin waddama tafi ta Nu'aymah muni. Baya gane wasu abubuwan yanzu tamkar ƙaramin yaro, ko dubashi kaje yi sai dai ya dinga kallonka kamar wani soko.
      Addah ma dai al'amari ya tsananta a gareta, duk ta rame ta lalace tayi baƙi. Har yanzu da tayi tari kuma sai kaga jini duk da dai ya ragu ba kamar da canba.
     Alƙawarin ALLAH ya cika ta ɗauki gudan jinin Yoohan da Nu'aymah a hannunta. Tai dariya tai kuka abin tausayi. Abban Abdallah kuwa koda aka kai masa jaririn kallonsa kawai ya dingayi amma babu bakin magana, hasalima ba wani fahinta yayi da ƙyau ba sai da Monyn Abdallah tai masa bayani, dan suna nan kano sunma dawo gaba ɗaya. Cikin karkacewar baki ya nuna Nu'aymah ya nuna jaririn yana magana yawu na dilalowa. Yace, “Mamana. Ɗanta?”. 
    Kai Momy ta jinjina masa. Hakan ya sakashi yin murmushi mai ciwo sai ga hawaye na zirara masa da gudu. Sosai hakanma da yayi ya bama kowa mamaki, dan baya magana balle nuna fahimtar mutane.
      Ranar dai ansha sabon kuka a gidan, dan komai sabo ya dawo a zukatansu. Sai da baba malam ya sake musu nasiha sannan suka samu nutsuwar zukata. 

       Ƴan Abuja basu sami isowa kano ba sai kwana huɗu da haihuwar Nu'aymah. Ba ƙaramin shan mamakin ganin da gidan da Aymah ta fito sukayi ba, sun sake tabbatar da lallai itaɗin jinin babban gidace. Dan duk da kasancewarsu ba ƙabila ɗayaba, ga abinda mahaifinsu ya aikata daya jawo musu baƙin jini a waje. mutanensu acan anan sai ake nuna musu mutuntawa da girmamawa. Hakan ba ƙaramin sakasu jin kunyar Nu'aymah yayi ba. Mama debora harda kukanta kuwa. Dan batai zaton dangin Aymah zasu amsheau da hannu biyu kamar haka ba kodan cin kashin da taima ƴarsu..
         Washe gari ana gobe suna shima Yoohan ya iso tare da Juliet ɗin Umar da baby Ayisha. Kai tsaye nan kano suka nufo dama. Inda Yoohan yay masauki a hotel da Omar ke jiransu. Juliet dai zuwa dare aka kaita gidansu Nu'aymah. Sunyi farin cikin ganin juna sosai, Juliet nata mamakin Nu'aymah da ɗa. itako dariya ta dingayi tana rungume da Ayisha ɗinta. 
     Su kansu Omar da Yoohan kallonta kawai suke. Daga baya Umar da Juliet suka basu guri. Tasowa Yoohan yayi yazo ya rungumeta yana sake godema ALLAH ɗan jaririnsa na jikinsa.
      Tai dariya da faɗin, “Silly boy duk ka wani rikice kai ka zama Baba ko?”.
     Dariya sukayi a tare cike da jin daɗi da farin ciki. Yoohan ya sumbaci goshin yaron da faɗin. “ALLAH ya raya Sheikh to be insha ALLAH”.
     Murmushi kawai Aymah tayi da faɗin amin.

*_RANAR SUNA_*

         Washe gari aka raɗama yaro sunansa Muhammad Soorajidden a masalaci. Tare da doguwar addu'a a garesa. Kowa yaji daɗin wannan suna musamman Nu'aymah da taji kamar ta haɗiye Yoohan dan farin ciki. Dan babu yanda batai da shi ya faɗa mata sunan jiya ba yaƙi. Kusan ƙarfe goma na safe kuma sai ga tarin alkairi daga Yoohan. Duk wani al'ada na hausawa a bikin suna sai da yayisa bisa shawarar Ahmad da Hamza manager.
      Kowa kam ya yaba ƙoƙarin sa, baba malam ma ya dinga faɗa hidimar tayi yawa.
       Amaryar jego tasha ƙyau harta gaji. hakama ɗan jinjiri Deen. Da yamma akasha walima a ƙofar gidan. wadda tai sanadin karyar da zukatan su Gebrail da su mama debora da suka fahimci Yoohan ɗinsu ya zama musulmi, basu nuna ƙyamar hakanba ko a ransu, saima yanda tsarin yake gudana da ɗabi'un musulman yasa Momy Destiny kasa yin shiru har sai da ta yaba. Dan har ranta abubuwan sun birgeta gaskiya.
     Bayan tashi da ga walima ƙarfe takwas na dare kuma wani tashin hankali ya biyo baya. Dan sama da ƙasa an nema ɗan jariri Deen an rasa. Kafin kace mi gidan ya hargitse. A take Nu'aymah ta sume musu sai da aka zuba mata ruwa. Yoohan na cikin ɗimuwa shima aka ƙwamushesa. Faruwar hakan a gaban mutane ya sa Omar da Ahmad da Omar ɗin su Nu'aymah, da Abdallah da Naseer binsu a mota. Yayinda Nu'aymah ta faɗa miotar batare da kowa ya fargaba sai da sukai nisa.
    A yau tai niyyar nunama Yoohan hoton papa da wadda suke zargin itace mahaifiyarsa. Sai gashi kuma abinda basuyi zatoba ya auku...........✍

‘Hummm mikuke tunani masu karati😱🏃?’.  


ZAFAFA BIYAR 2021

Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.




[7/8, 10:16 PM] Sweet Sis: *_LITTAFIN nan na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki daure ki biya kafin ki karanta, idan kuma bazaki iya biya ba ki haƙura domin ALLAH karki karanta. Idan kuma kin saya dan girman ALLAH karki yaɗa mana🙏🏻_*.


No. 76

.............Gaba ɗaya gidan ya hargitse. Su Naser dai sunbi motar data ɗauki Yoohan a mota, sai dai babu tabbacin zasu iya cimmasu, musamman daya kasance dare ne.
     Afrah da yake tazo wajen sunan ce tai azamar kiran Jay ta sanar masa, shima kansa hankalin nasa ya tashi matuƙa, amma sai ya shiga kwantar mata da hankali akan karta damu, indai da waya a jikin Yoohan gano inda ya ke abune mai sauƙi, ya kuma tabbatar a duk inda za'a kai Yoohan Deen na wajen insha ALLAH.
     Suna yanke wayar yay kiran su Aliyu ya sanar musu. Tare da tura musu Number Yoohan dan yana son a bibiyesu da sauri kafin suyi tunanin yadda wayar a wani waje ko wani abu daban. Haka kawai a ransa ya kejin wannan aikin papa ne.
       Lallai hikimar Afrah na saurin kiran Jay ya taimaka ainun. Dan cikin amicin ALLAH kuwa ta hanyar bibiyar wayar Yoohan ɗin da ke a jikinsa suka samu nasarar sanin inda aka kaisa.

_______★

        A ɓangaren Yoohan kuwa an shammacesa ne. Dan yana tsaka da firgicin jin cewa ba'aga Deen ba, da cewar Nu'aymah ta suma juwa ta nema kwasarsa. Yana dafe kansa kawai yaji an jasa ta ƙarfi an tura a mota, al'amarin kamar wani wasan yara. Suna sakashi a motar suka ɗora masa bindigu. Binsu kawai yay da kallo ɗaya bayan ɗaya ya girgiza kansa. Kafin yace wani abu ɗaya a cikinsu yace, “Indai kana buƙatar ɗanka a raye ka bimu salin alin”.
       Guntun murmushi kawai yayi ya ɗauke kansa. Papa yana Nigeria kenan, dan a take ya gama fahimtar su ɗin yaran papa ne. A ransa yake tunanin shin da papa na buƙatar ganinsa sai ya bi ta hanyar sace masa yaro kenan? Minene amfanin yin hakan to?. (tsoron a kamashi mana) zuciyarsa ta raya masa. ‘To ashe kuwa shi da kansa zai damƙa papa a hannun huku yau ba sai gobe ba’.
      Ganin baice komaiba yasa yaran ɗauka yayi ladab ne. A haka suka iso wani hotel. Duk maida bindugunsu sukayi a jiki daga su har Yoohan suka fito a motar. Yaji a ransa zai bisu kamar yanda suke buƙata. Sun shiga cikin hotel ɗin babu wani alamun rashin gaskiya tattare da su. Hasalima sun shiga a rarrabe ne. Yoohan tare da ɗaya a cikinsu, suma sauran biyun suka shiga su kaɗai.
       Shi Yoohan sun wuce cikin hotel ɗin direct, sauran kuma suka tsaya reception kamar dai wani suke jira. Yoohan dai yanata bin hotel ɗin da kallon nazari har suka ƙarasa ɗaki mai lamba 23 vip section. Knocking ƙofar yayi sau ɗaya, sai ko gashi anzo an buɗe. da ido yayma Yoohan alamar ya shiga. Yoohan yay masa wani gajeren murmushi ya shige ɗakin, sai y  bisa a baya yanayin ƙwafa. Dan yaji haushin murmushin Yoohan ɗin har ransa.
           Ko kaɗan Yoohan baiyi mamakin cin karo da Momy a ɗakinba. Dan dama ai su zuciyarsa take raya masa gani ɗin. Ya kauda kansa daga kallonta saboda shegun kayan dake jikinta bata da maraba da tsirara. Takowa tai gabansa tana kwasar dariya da tafa hannaye ta shiga zagayesa. 
      Hannayensa kawai ya tura cikin aljihun wandon shaddarsa ya rumtse idanunsa. Sai da ta zagayasa sau kusan uku kafin tazo gabansa ta tsaya daf tamkar zata rungumesa. Ko motsi kuwa baiyiba, bai kuma buɗe idanunsa ba.
     Cikin raɗan maganar shaƙiyanci da  jin alfahari madam Chioma tace, “Abin mamaki ko my boy, haka muke ni da papanka kullum cikin bama mutane mamaki”. Sai kuma ta ƙyalƙyale da dariya mai cin rai tana ja baya. Komawa tai bakin gado ta zauna tana wani lashe baki da banƙaro ƙirji. Tare da jan rigarta sama sosai cinyarta ɗaya ta fito waje idonta akan Yoohan da har yanzu nasa idanun ke a rufe. Cike da salon iskanci ta sake narke idanu tana lasar laɓɓanta.
       “My boy karka takura kanka da tunani, dan baka buƙatar hakan musamman akan soyayyar jaririnka, oh sorry jikana nefa ashe”. Ta kwashe da dariya sanna ta cigaba da faɗin, “Yi haƙuri my boy na mantane. Ta hanya ɗayane kawai zaka iya cetar my grandson John. Dan nice kaɗai zan iya kaika inda zaka samesa. Hakan kuma bazata kasance ba sai ta hanyar biyamin buƙata ta. Hhhhhh My lovely john dolene fa na ɗanɗani zumar nan taka da kaketa min rowa, dan itace burina tun kana shekaru sha takwas a duniya. Hhhhhh kaga kuwa ai bai kamata nasha wahalar dakon lokaci ba, kaima nasan zaka tausaya min dear soooon”. Ta ƙare maganar da wani salon iskanci tamkar zatai kuka. Sai kuma ta taso zuwa gabansa ta tsaya tana matso hawayen da suka cika mata idanu.
     Hannayenta ta ɗora akan ƙirjinsa ta fara ɓalle maɓallin shaddarsa tare da cigaba da faɗin, “Karka damu duk ma na yafe maka wahalhalun dana sha a waɗancan shekarun kaji baby. Dan wannan daren kawai ya wadatar da cike gurbin duka sauran dararen da suka shuɗe”.
      Duk wannan iskanci da madam Chioma keyi Yoohan na tsaye tamkar gunki, har yanzu idanunsa a rufe. Sai da takai ƙarshen duka maɓallansa tana sambatun haukan zantukanta, ta tura hannunta cikin rigar ta fara shafa ƙirjinsa ta saman singlet ɗinsa. Wani irin cije baki yayi ya hankiɗata baya da iya ƙarfinsa.
        A take ta saki wani irin wahalalliyar ƙara saboda da gaske ta bugu. Da sauri yaran da suka kawosa wajen suka zagayesa da bindugu. Buɗe idanunsa dake a matuƙar jazur yayi akansu, ya wani ɗauke kai irin ba kune a gabana ba ya maida kan madam Chioma dake kwance ƙasa wanwar tana numfashi da ƙyar saboda azaba.
       A hankali ya fara takawa gareta fuskarnan kanta tayi jazur kai kace aman wuta zatayo. Suko yaran madam Chioma na biye da shi da bindiga abin nasuma abin dariya😂.
     Ƙafarsa ya taka a samna gadon ya ranƙwafo kanta. Wani murmushin tsantsar tsana ya jefeta da shi tare da nunata da ɗan yatsa. “Na tsaneki, har cikin raina na tsaneki, tsana irin wadda ban taɓama wani mahaluki ita a wannan duniyarba. Indai nine zaki mutu da takaicin rashin samuna har ƙarshen numfashinki. Nayi takaici mai yawa akan kasancewarki mahaifiya a gareni. Bakuma zan taɓa yafe miki ba har abadan tunda ke karya ce wadda sam bata da zuciya a ƙirjinta balle ƙwaƙwalwar tunani. Badan ke uwata bece da yau na tabbatarma duniya ke ɗin dabbace, a cikin dabbobinma kina jerin aladu dan sune basu banbance junansu wajen neman kansu. Wlhy kinji na rantse ko tabon ƙwarzane na samu a jikin yarona saina halakaki da wannan hannun nawa”. Ya kai ƙarshen maganar yana wara yatsun hannunsa da jujjuyasu akan fuskarta.
     Da gaske tsoro ya shigi Madam Chioma, dan tunda take a rayuwarta bata taɓa ganin irin wannan fusata da fushin na Yoohan ba. Tsaye ya miƙe yana zuba mata wani mummunan kallon tsana da ƙyama. 
      Da sauri ta zabura ta miƙe duk da azabar da bayanta ke mata. Tace, “Ku ɗauremin shi, wlhy koda ƙarfi saina lashi zumarka John. Kaje kaita tsanar tawa kai ya dama wannan kuma, ni ban tsaneka ba. Ba kuma zan tsneka ba”.
     Kafin Yoohan yay wani yunƙuri kuwa suka dabaibayesa da igiya, duk yanda yaso kuɓutar da kansa ya gagara hakan sam, dan tsam suka ɗauresa a tsaye sannan suka kamashi suka ajiye a kujera suka sake ɗaurewa suna dariyar yanda sukaga yana wani irin huci na zafin zuciya.
      Itama kanta Madam Chioma dariyar take tayasu da iya ƙarfinta. Ta tashi tsaye da ƙar tana riƙe ƙugu. Gabansa tazo ta tsaya tana cije baki. “John kana wasa dani ko? Na fika hatsabibanci yaro. dan tunkan asan za'a haifeka nake da taurin kai. Ai tunda nayi alƙawarin saina cikama rayuwata”.

      Lokacin da su Yoohan ke wancan dabi shi da madam Chioma su Nu'aymah suna shigowa cikin hotel ɗinne tare da jami'an tsaro. Dan tuburewa tai akan saita biyosu. Ganin yanda ta rikice ɗinne ya saka Omar bada shawarar aje da ita ɗin. Sai da jami'an tsaron sukai magana da manager ɗin hotel ɗin sannan suka nufi cikin hotel ɗin kamar yanda alama ke nuna musu dai-dai inda wayar Yoohan take. Wadda toshewar basirar madam Chioma baisa ta kawo a ranta sanadin wayar ballinsu zaiyi ruwa ba.
        Dai-dai madam Chioma ta ɗora kanta saman wuyan Yoohan tana shinshina kamar wata mayya ko tunkiya, hannayenta duka biyu na akan jikinsa. wani irin masifar tafasa zuciyar Yoohan keyi tamkar zata faso ƙirjinsa ta fito waje. Sai ko faman taunar lips nashi yake da masifar ƙarfi, a ɗaure yake, bashi da wata damar ɗaukar mataki akan uwar tasa.....
       Da sauri ta ɗago saboda jin an buɗe ƙofar. Hakama yaranta dake tsaye a gefe kawunansu a ƙasa duk zabura sukayi suna rarumar bindugunsu...
       “Ƙasa gaba ɗayanku, duk wanda ya taɓa wata bindiga anan kuwa a bakin ransa”.
    Ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa a tsawace yana nuna yaran madam Chioma. Da sauri ta fiddo tata ƴar ƙaramar bindigar jikinta ta ɗora bisa kan Yoohan daya buɗe idonsa a hankali ya sauke su akan Nu'aymah da ke shigowa tare da Jami'an.
       Cikin rawar jiki data murya Madam Chioma tace, “Ku fita a ɗakin nan kona tarwatsa masa kwanyar kai duk da kasancewarsa ɗana”.
        Da sauri Nu'aymah tace, “Ƙarya kike munafuka azzaluma. K! Ba mahaifiyarsa bace ba. Yah Yoohan wlhy ba itace mahaifiyarka ba ƙarya takeyi”. Tai maganar da fashewa da kuka tana zaro hoton nan daga envelope ta nuna masa balarabiyar nan. “Kaga mahaifiyarka nan Yah Yoohan, wlhy ba wannan shaiɗaniyar bace. Bana tantama akan har mijinta ba shine ya haifeka ba, akwai abinda suke ɓoye maka. Iyayenka na gaskiya bazasu sace maka ɗanka ba. Mahaifiya ta ƙwarai bazata so tarayya da ɗanta ba koda kuwa bata da addini, sai dai idan dabbace ita mai juyayyen tunani..........”
       “Hhhh da ƙyau tsagera”. Madam Chioma ta faɗa tana dariya har yanzu bindigarta na akan Yoohan da zantukan Nu'aymah sukema kai kawo a rai. Ta cigaba da dariya da faɗin, “Ashe tsaurin idon naki ya kai haka? Ko da yake ashefa kinsan zafin haihuwa ko? Hhhhhhh. Ashe kuwa za'a kwashi gawa da yawa a hotel ɗin nan yau”. Tai maganar da haɗe fuska ta nuno Nu'aymah da bindigar.
       Cikin kaushin murya Umar yace, “Kibar wannan haukar da kikeyi ki ajiye bindigar hannunki kawai madam”.
      Kallonta ta maida garesa. Cikin yatsina fuska tace, “Richard kake kowama? Kai kuma a suwa shiga family issue?. Maza kama kanka wannan ba shigarka baceba.....”
     Kafin ta rufe baki taji an hankaɗata, sai ga ta ita da bindigar ƙasa wanwar. Da sauri ɗaya a cikin ƴan sandamln ya ɗauke bindigar, wani kuma yazo ya danna mata ankwa ta baya. Yaran nata ma duk an kamesu. Nu'ayma kuwa da gudu ta ƙarasa jikin Yoohan dake a ɗaure ta rungumesa tana fashewa da kuka. Biyota Umar yayi ya fara warware igiyar da suka ɗaure Yoohan ɗin da ita, itama Aymah sai ta miƙe tana taimaka masa. Suna gama kwancesa ya rungume abarsa yana shafa bayanta. Sai dai bakinsa ya kasa furta komai saboda irin tafasar da zuciyarsa ke masa. Hoton hannun nata ya zare ya kafe balarabiyar jiki da kallo tare da papa dake gefenta. Jiyay wani abu na tsarga masa tun daga zuciya har zuwa tafin ƙafa. Ya kafe fuskar papa yana nazari sosai akansa batare da su Nu'aymah sun fahimci abinda yake nazartarba. A hankali ya janye Aymah a jikinsa yana miƙa mata hoton, gaban madam Chioma ya karasa. Babu wani kace nace yasa ƙafa ya taɗe ƙafafunta sai gata a ƙasa ta zube. Kasancewar hannayenta ɗaure suke ta baya da ankwa sai ta faɗi a rubda ciki. A take goshinta da hancinta da baki suka fashe, haƙoran gaba guda biyu sai gasu a ƙasa.
     Wata wahalalliyar ƙara ta saki. Yoohan yasa hannu ya birkitota ta dawo rigingine. Gaba ɗaya fuskarta ta gama damewa da jinin raunukan data samu, “Ina ɗana?”. Wannan itace kawai tambayar daya jefa mata batare da ya damu da yanda jini yayma fuskarta jage-jage ba.
       Kanta ta shiga girgiza masa, cikin rawar murya da laɓɓa tace, “Nima ban saniba John, Please ka yarda da ni”.
     Uffan Yoohan baice da itaba, sai bindigar hannun ɗan sanda ɗaya ya fisge ya ɗora mata a goshi. “Humm ke ƙaramar ƴar iskace ashe. Idan kika cigaba da min gardama ba shakka zan tarwatsa ƙaramar ƙwaƙwalwarki da harsashin cikin bindigar nan. Idan kinada taurin kai tun kan haihuwata, ni ki ɗauka bayan haihuwar tawa na damaki na shanye. Da kika ganina anan tsageran kainane nima wlhy. Faɗamin ina Yarona yake?”.
      Wutar bala'in da madam Chioma ke hangowa cikin idanun Yoohan ya sata saurin faɗin, “Zan gaya maka, amma ka taimakeni ka cikamin burina nima, kayi tarayya dani koda sau ɗaya ne naji sanyi a raina John. Ka tausayama wahalar danasha a kanka ta tsahon shekaru”.
         “Lallai k! a tumakin ma balama ce”. Yoohan ya faɗa yana cije baki da ɗana kunamar bindigar ya maida bisa tsakkiyar kanta. 
      Jikinta karkarwa ya farayi, tana kuka tace, “Kayi haƙuri karka kasheni zan faɗa maka Jonh. Na rantse zan faɗa maka. Yaronka na a hannun Papanku acan wani gida dake cikin G.r.a, nima ya sakanine na kai masa kai, shine nai amfani da wannan damar domin fara cikama kaina burina a kanka na tsahon shekaru. Na biyo da kai tanan kafin na miƙaka wajensa. Miracle ita aka saka ta sace maka yaro a wajen bikin da kukeyi, dan dama muna biye da duk wani motsinku.......”
      Duka ya kai mata a fuska ɗan sanda yay saurin riƙesa. “Cool down Mr Yoohan. Karka damu dolene ta kaimu har inda suke ai. Kwantar da hankalinka kaji”.
      Huci kawai Yoohan ya keyi, tsabar zuciyar dake cinsa sai ga hawaye sharrrr suna sakkowa. Matsowa Nu'aymah tayi ta riƙe masa hannu batare da tayi magana ba. Da sauri ya jawota jikinsa ya rungume ko zaiji sassaucin zuciyarsa.

            An tattara yaran madam Chioma zuwa police station da su. Su kuma su Yoohan da sauran jami'an suka shiga motar da aka sato Yoohan tare da madam Chioma bayan an sakata kiran papa ta sanar masa cewar gata ta samo Yoohan harda Nu'aymah ma. Wani ihun gigitacciyar dariya papa ya saki har su Yoohan na jiyosa. Umar da Jami'an sun rufe fuskokinsu tamkar su ɗinne yaran madam Chioma. Itace ta dinga nuna musu hanya har suka isa anguwar. A daidai ƙofar gate ɗin gidan suka tsaya. Maigadi na leƙowa yaga motar sai ya buɗe da tunanin su madam Chioma sun ciyo nasara suma.
        Yoohan da Nu'aymah aka sakama ankwa a hannu suka fara shiga, jami'an tsaron da fuskokinsu ke a rufe na biye da su a baya. Umar ne ƙarshe da madam Chioma a gabansa. Acan waje dama tuni ƴan sanda sun gama zagaye gidan dan dama babban burinsu shine kama papa da sauran mutanensa. Abinda suka share watanni biyu suna nema ga dama ta samu a lokacin ƙanƙani.
      Da sauri Papa dake zaune cikin kujera su Joshua zagaye da shi duk suka miƙe sabida ganin Yoohan da Nu'aymah. Deen na kwance akan centre table ɗin falon cikin showal ɗinsa. Yayi kukan wahala har ya gaji yayi barci. Gefensa an ajiye sharɓeɓiyar wuƙa.
       Cike da wata irin mahaukaciyar dariya papa ya shiga tafa hannayensa yana kallon su Yoohan.
   Ya tako gabansu a hankali batare da tunaninsa ya haska masa cewar waɗanda ke bayansu ba yaransu bane ba. Da dariyarsa ya shiga faɗin, “Oh my Son & Darling daughter in-low ɗina. Welcome to my new land. Nice meeting you my guys”.
       Da ga Ayma har Yoohan dai kallonsa kawai suke. Papa ya kalli jami'an da yake tunanin yaransa ne yana fa faɗin, “Ku cire musu ankwa amfaninta ya ƙare ai. Dan game zamu buga da su mai zafi”.
     Babu musu ƴan sandan nan suka cirema su Yoohan ankwa. Komawa papa yay ya zauna a kujerar daya taso. Ya ɗan taɓe bakinsa da dora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ɗauki kofin giyarsa ya kurɓa yana kallon su Yoohan. “John badan inada ƙarancin lokaci ba dana baka wani labari mai ban mamaki da al'ajabi. Amma share kawai muje ga game ɗinmu. Idan lokaci ya rage mana a cikinsa sai na baka labarin. Daughter in-low karki tada hankalinki kinji, ɗanki yana lafiya, kingama barci yake abinsa”. Yay maganar da tasowa daga kwanciyar da yayi jikin kujera ya yaye showal ɗin da deen yake ciki yana lakatar hancin yaron da ɗan yatsa. “Daughter kin iya haihuwar ɗa fa”. Ya faɗa yana kecewa da dariya su Mike na tayasa. Giyarsa ya kwankwaɗa ya ajiye kofin yana haɗe hannayensa waje guda. “Oh Sorry my son karka fusata na sanka da zuciya”. Takardun dake a gefen Deen ya jawo ya tura ƙarshen tebirin ta sashen da su Yoohan suke. “Wannan takardun sune game ɗinmu tare da ɗan jinjirinku ƙyaƙyƙyawa. John kanada zaɓi biyu. Kuɓutar da yaronka ta hanyar yimin signing a duk takar dunnan, ko kummaaaaa nai masa yannnnnkan rago da wannan wuƙar tawa a wannan lallausar fatar tashi”. Ya ƙyalƙyale da dariya yana ɗora wuƙar bisa cikin Deen dake barci a binsa yanata sakin ajiyar zuciyar kukan da yasha. 
       Ko motsi Yoohan baiyiba, haka ma Nu'aymah duk da hankalinta a tashe yake kallon papa kawai take zuciyarta na tunanin anya kuwa wannan mutumin ma mahaifin Yoohan ne?
        Hannunta taga Yoohan ya saki tare da takawa a hankali zuwa gaban papa yana wani ƙyaƙyƙyawan murmushi, dan cikin ƴan sandan nan ɗaya yay masa alamar yaje. Zuwa yanzu sunsan sauran ƴan uwansu sun gama tattare yaran papa gaba ɗaya dake cikin gidan. Sannan sun gama nazarin su papa kaf babu wani makami tare da su anan sai wuƙar dake akan Deen. Babu wani alamar damuwa a fuskar Yoohan balle tambayar papa ba'asin yin hakan. Yazo gaban tebirin ya zauna akan ƙaton tum-tum dake kusa da shi yana murmushi. Cikin kwanciyar hankali ya ɗauki pen ɗin dake saman takardun ya rike a hannu. Shafin farko na takardun ya karanta cike da nazari. Yaɗan ɗago ido ya kalli papa da shima ke kallonsa. Murmushi Yoohan ya sakar masa da taune lip ɗinsa na ƙasa ya ɗage gira ɗaya da lumshe idanunsa ya sake buɗewa akan takardun. Har cikin jini Murmushin Yoohan ya daki zuciyar papa da su Mike. Amma sai basuyi magana ba. Ɗaya bayan ɗaya Yoohan ya fara signing takardun. Yana gab da gamawa Mike da ya farga babu Madam Chioma. yace, “Brother wai nikam ina madam ma ne? Ta kawo mana su amma banga ta shigoba ita”.
     Da sauri Papa ya kalli Mike, sai kuma ya kalli Yoohan dake signing yana murmushi da taunar lip dinsa na ƙasa. “John mikake kullawa? Ina matata?”.
    Ko motsi Yoohan baiyiba balle ya kalli papa. Sai da ya gama signing ɗin duk takardun sannan ya kalli papa da tsoro ya fara bayyana masa a fuska. Wuƙar kan Deen ya dauka yana faɗin, “Ashe kuwa inhar wani abu ya samu matata saina halaka wannan yaron”.
      Murmushi Yoohan ya sakeyi har haƙoransa na bayyana. Ya miƙe tsaye hannunsa ɗauke da takardun da yay Signing. Yaɗan sosa pen din a gefen wuyansa yana duban papan. “Oh my sweet papa ya da karaya haka da wuri?”. Yay maganar da wani shegen murmushin yaƙe. Sai sukaga ya girgiza kansa yana ɗan buɗa hannayensa. “Karfa ka damu papa. taya zan cutar da mahaifiyata. Guys Please ku kawo masa matarsa”. Ya juya yana kallon ƴan sandan nan. Umar dake can ƙofar falon bai shigoba ya turo madam Chioma ta fara shigowa bakinta a ɗaure. Bindiga a bisa kanta.
    Wani irin zabura papa yayi jikinsa na rawa. Kafin yay magana Yoohan yay ƴar dariya yana faɗin, “Oh my sweet papa relaxxxxx!!. Idan ban mantaba kace zamuyi game ko? So karka damu bazan canja ba zamu buga ai. Nasan kana son matarka, ba kuma zakaso rasata ba, gata ƴar ƙyaƙyƙyawa kuwa”. Yay maganar da wata shegiyar dariya. Sai kuma ya gimtse fuska da haɗe hannayensa waje guda yace, “Oh sorry papa bazan sakeba. Ga takardu na maka signing kamar yanda ka buƙata. Sai dai kana da zaɓi. Matarka ko waɗanan takardun. Idan su kafi buƙata, zan baka, amma zan tarwatsa kwanyar matarka a gabanka. Idan kuma matarka kafi bukata, zaka bani ɗana, na kuma wuce da takardun nan a gabanka. Wannan shine game ɗin Yahyaaaaaa! Much💋! much💋!!, I love you my papa!!”. Suka kwashe da dariya a ƙarshen maganar shi da Nu'aymah tare da tafawa.
       Wani irin huci papa ya fara fitarwa kamar zai shiɗe. Ya kai hannu zai fisgi wuƙar nan Yoohan yay saurin faɗin, “No! no! no no no no!!!! Pastor goshpower. Karka fusata da yawa fa, kasan ɗan naka mai faɗa da cikawa ne. Ai yanzun game ya tashi daga tsakanin takardu da yarona, ya koma tsakanin takardu da matarka ok?”.
     Kafin papa yace wani abu Yoohan ya  fisge handkerchief ɗin da suka ɗaure bakin Chioma da shi. Wani wahallalen ƙara ta saki da fashewa da kuka. Cikin roƙo tace, “Please Darling ka basu yaronsu, ka taimakeni, na rantse john zai iya kasheni, kagafa yanda ya ciremin haƙwara, karkai jayayya dasu nan duk jami'an tsarone ba yaranmu ba”.
     “What!!!”.
  Papa da su Mike suka ambata a firgice. A take duk jami'an tsaron da Omar suka janye abinda suka rufe fuska. Sai ga wasu na shigowa suma akai ma su papa zobe. takawa Yoohan yayi gaban papa yana dariya ya ɗauki Deen ya rungume a jikinsa tare da sumbatar goshin yaron. Da sauri Nu'aymah ma ta matso garesa ta haɗashi shi da yaron ta rungume. Umar kuwa ya damkama ƴan sanda Madam Chioma ya matso ya ɗauki takardun da Yoohan yayma Signing yana dubawa.
      “Kai!! Dude!, anya kuwa mutumin nan ma shine mahaifinka kuwa?”..  
     Ɗagowa Yoohan yayi daga sumbatar kumatun Deeen, yasa hannu ya share hawayen da suka cika masa ido yana miƙama Nu'aymah yaron. Yace, “Goyashi akwai sanyi”. Babu musu Aymah ta juya ya ɗora mata Deen a baya ta goyashi, ya gyara mata hijjab ɗin jikinta sannan ya dubi Umar da yay tambayar da furzar da zazzafan huci.
       “Bana zaton haka Umar, dan abubuwa da yawa sun banbanta tsakaninsa da wanda ke a hoton nan. Sannan waɗanan takardun mallakin kaddarorine a cikinsu wanda alamu suke nuna ba nasa bane sam. Dan signing ɗin cikinsu ba irin nashi baneba. Akwai sirrin da yake ɓoyema duniya a kaina........”
         “Sirri mai girma kuwa”.
Muryar da basuyi zato ba ta karaɗe kunnuwansu a bazata. kusan gaba ɗayansu suka dubi bakin ƙofar inda maganar ta fito. *Jawaad Abdul-aziz Yusuf* ne tsaye cikin ƙananun kayan da suka rage masa shekaru, sai dai duk wanda yasan shekarun girma ya kallesa yasan shiɗin bana wasan yara bane, (Duk ya girmi masu karatu yanzu, duk da a gabansu aka haihesa😝😜🤣🏃).
         Bayansa jami'ai ne biye da shi. Cikin falon ya karasa shigowa ya zauna a kujerar da ke kallon papa dake a durƙushe bisa gwiwoyinsa yanzu shi da su Anthony saboda zagayesu da akai da bindugu.
       Ƙafa ya ɗora ɗaya kan ɗaya yana wani shegen murmushi, yace, “Hii Goshpower, sai kuma gaka. Hhhh ALLAH sarki. Haka rayuwa take ai, duk iya gudun mai tsere bai isa zarta ƙaddararsa ba. Dama naji a jikina dole ka dawo, dan yanzu da dukiyar da wannan takardun kawai kake tunanin ka tsira. Kafa birgeni, dan da gaske ka iya wasa. Kana da basira ƙwarai da gaske. Sai dai kuma kanada daƙiƙanci a wajen kuskuren lissafi. Da ace bakabar Yoohan a raye ba da lissafinka bazai taɓa ɓata ba. Sai dai kash a dalilin ƙwaɗayin abinda baka taraba ka saka kanka a tarko tsahon shekara talatin da biyu. Tsem! Tsemm tsemmm!!! Gaskiya ka bani tausayi. A farkon labarin dai cike yake da birgewa da ƙayatarwa ga marubucinsa. Sai dai a ƙarshe an samu dagulewar ƙwaƙwalwa ga marubucin. Mai makon yanda aka fara da nasara a ƙare da nasarori sai aka ɓige da faɗuwa ƙasa wanwar. Kash matsalar tunani ko Mr goshpower”.
     Jay yay maganar ƙarshe yana ɗage gira da sakin dariya. Ya cigaba da faɗin, “Oh sorry bara na taƙaita, dan ka sani tafiyar da ban shiryaba a daren nan daga Abuja zuwa kano ga uban sanyi. Maganar gaskiya ma ban yafe ba. Ƴan jarida ku shirya kayan aiki”. Ya faɗa yana shafar girarsa da nuna hanyar ƙofa.
       A take kuwa suka shigo kusan su shida. Duban Yoohan da Nu'aymah da Umar yay ya nuna musu kujerun alamar su zauna suma.
      Zama sukai a sanyaye kamar an doke gwiyawunsu da ƙarfuna.
     Jay ya kalli agogon hannunsa sannan ya dubi papa. “Mr Goshpower bamu da isashen lokaci, dan awoyi uku da mintuna ashirin da ɗaya suka rage alfijir ya keto. Bana son wasana da kai yay tsamari a wannan gaɓar dan daga ni har kai mun jigatu, inason sanin wanene Yahya? Su wanene kuma waɗanan na jikin hoton?”.
     Shiru papa yayi ya ƙi magana, hakan yasa Jay ɗinma bai sake magana ba, sai kawai ƙarar bibdiga su Aymah sukaji da ƙarar papa. Ruɗewa Aymah tayi ta ƙwaƙume Yoohan jikinta na rawa. Ga Deen dake bayanta ma ya farka da wani irin firgitaccen kuka. Taimaka mata Yoohan yayi ta sakko da shi, ya rungumesa a jikinsa yana jijjiga shi. Da kallon papa da Jay yayma harbi biyu a duka ƙafafunsa saboda tsabar ƙwarewa a iya harbi.
      Jay ya girgiza kansa da dafesa. Yace, “Oh kana neman fusatanine Mr Goshpower. Gashi ni kuma hannayena ƙaiƙayi sukeyi. Na faɗa maka a jigace nake matuƙa, karka jani da nisa ana idar da sallar asuba nake son komawa Abuja”.
       Cikin magautar raɗaɗi papa ya fara magana. Ga wata irin zufa ta jiƙesa a take duk da uban sanyin da ake zubawa a garin. Yace, “Shima sunansa Goshpower, shi ɗin twin brother ɗinane. Wannan kuma matarsa ce”.
       “Yayi ɗan gari, haka nake buƙatar jinka. Omar a cire masa bullets ɗin nan”.
       Da sauri Omar yace, “Okay Uncle ”.
       Tsabar son azabartarwa Umar sai ya ɗauki giyar da papa yasha ya rage ya zuba masa akan harbin. A take kuwa ya saki wata wahalliyar ƙara ya suma. Ko a jikin Omar. Ya amshi First aid box a hannun wani jami'i da sukazo da shi ya cire bullets ɗin cike da rashin tausayi. Sai da ya kammala komai sannan aka zubama papa ruwa ya farfaɗo.
       Sai da suka bashi damar hutun kusan mintuna biyar ya daidaita sannan ya fara bada labari.

       “Ni da shi twins ne. Muna tsananin kamanni har takai jama'a basa iya banbantamu inba mahaifiyarmu ta faɗa ba. Duk da itama wani lokacin rikicewa takeyi. Suna ɗaya iyayenmu suka saka mana wato Goshpower. Takai inhar ka kira ɗaya a cikinmu sai mu amsa maka mu duka. Mamanmu ta taɓa faɗa mana kaifin basira da muke da shi da farar fata tasa har ana dangatamu da wasu sunaye. Wasuko na tsoronmu da faɗin mama debora ta haifi waɗanda ba mayu. Wannan ba sabon a bu bane daga hallayar mutanen ƙabilarmu da yankinmu wajen danganta mutum mai fari da ƙyawun jiki da suna na tsoro. Mutane basu fara samun basirar banbantamu ba sai da muka fara girma halayenmu suka fara banbanta tsakanina da ɗan uwana. Mu duka munada kaifin basira da wayo, sai dai kowa da yanda yake gudanar da tashi. Duk inda gaskiya take zaka samu ɗan uwana a wajen, niko saɓanin haka shine zaɓi na. Kullum cikin takalo rikici nake wa iyayenmu, ɗan uwana kuma bai gajiya da bayyana gaskiya idan an tambayesa. A duk lokacin kuma da nai niyyar cutar da shi akan wannan abu da yakemin sai bana samun nasa. Dan ko faɗa zamuyi yafi ƙarfina. A haka dai muka kammala primary, akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninmu, amma bamu cika zaman lafiya ba da zama waje ɗaya na dogon lokaci. Bayan secondary skull muka wuce jami'a, inda anan mabanbantan halayenmu suka sake bayyana. Duk da mu duka muna karatu ni a koda yaushe hankalina nakan mata, sannan duk wani abokin banza zaka samu nawane. Hakan na ɓatama ɗan uwana rai, tun yanamin nasiha da faɗamin gaskiya har yayi zuciya ya daina, daga ƙarshema muka raba ɗakin kwana, dama ba department ɗinmu ɗaya ba. Haka dai muka cigaba da tafiya, kafin mu kammala jami'a na zama riƙaƙen mara jin magana dan har harkar ƙwaya na fara, sannan na shiga cikin ƴan Cult. Mun kammala degree ɗinmu na farko, ta hanyar ogan babanmu muka samu taimakon tafiya ƙasar Italy ƙaro karatu. Daga nan ne labarin canjawar komai ya fara. Dan watanninmu biyar kacal a makarantar na sake canjawa daga duk yanda aka sanni. Idanuna sun sake buɗewa sosai harna fara harkar cocaine. Ta hanyar wanda na fara harkar Cocaine ne idanuna suka sake bushewa. Ya kutsa dani cikin manyan mutane konace tantirai dake juya duk wani iya shege na duniya. Nasha wahala ba kaɗanba wajen karɓar horo daga garesu har takai makaranta ma na daina shiga duk da yawan damuwa da kirana da ɗan uwana keyi, tare da yawan ƙoƙarin son sanin abokan mu'amulata. Muna shekarar ƙarshe daya kamata mu kammala degree ɗinmu na biyu ɗan uwana ya haɗu da matashiyar Balarabiyar saudia mai suna Anum. Itama karatu tazoyi, wannan kuma shine zangonta na farko. Sun fara rayuwa kamar abokai a hankali suka rikiɗe zuwa masoya. Sam bansan da wannan soyayya tasu ba sai da tai nisa, muna ma gab da kammalawa. ko nace ɗan uwana na gab da kammalawa. Danni tuni na yaye kaina daga zuwa makaranta. Sai dai nakan shigo lokaci-lokaci saboda harƙallar dake tsakanina da ɗalibai ta kayan shaye-shaye. A wani shiga da nai cikin makarantar ne na haɗu da Anum, wadda ina cikin tafiyata tazo tasha gabana, a zatonta ɗan uwana ne. Da farko na harzuƙa matuƙa, sai dai ƙyawunta yayma idanuna barazana da danne fushina. Cike da tsokana take kallona tana dariyar wai yaushe nasai kayan jikina?, ita dai basu mata ba. Naji haushin kalamanta amma saina fuske na barta akan ɗan uwan nawa ne. Kiran wayata da ogana yayine yana min neman gaggawa yasa na sulale nabar Anum da nufin zan dawo gareta. Daga haka bansan yanda ta ƙareba bayan taga ɗan uwana. Shin ya warware mata mu ƴan biyu ne, kokuwa ya karɓa mata matsayin shine ni?. Kwana biyu da yin haka na dawo cikin skull neman Anum sai dai na samu labarin cewa sun wuce saudia ita da ɗan uwana. Samakon zuwa da yayunta biyu sukai suka ganta da ɗan uwana daba musulmi ba”.
        “Duk da bana shiri da shi hankalina ya tashi matuƙa, dan kodai babu komai shiɗin ɗan uwanane ai. Duk zatona ko zasu cutar da shi ne? Naso binsu duk da bansan ina suka nufaba sai kuma wani aiki ya sake taso mana zuwa ƙasar Germany. Haka na tafi al'amarin ɗan uwana na damuna a cikin rai. Kamar wasa sai ga wannan tafiya ta jani tsahon wata huɗu, lokacin da muka dawo ƙasar Italy saina samu munyi graduation, course mate ɗina duk sun kama gabansu har ɗan uwana. Na bincika Anum sai na samu wai itama tabar makarantar. Daga jin haka sai kawai na nufi Nigeria, a zatona ɗan uwana ya koma gida. Amma kash sai na iske saɓanin tunani. An dai tabbatar min yazo wata biyu da suka gabata wajen rasuwar mahaifinmu, nima anta nemana amma ba'a sameniba. Ko damuwa banyi da mutuwar babanmu ba, sai dai jin ogan babanmu ya bama ɗan uwana maƙudan kuɗin aikin da mahaifinmu yay aiki a ƙarƙashinsa dan yaje ya juya hankalina ya tashi na bukaci sanin ina ɗan uwana yake?. Mamanmu bata saniba, abinda kawai ta sanarmin shine ya sake barin ƙasar, bakuma susan ainahin ƙasar daya tafi ba. Yadai bar musu kuɗin da zasu ishesu, tare da musu alƙawarin nanda shekara guda zai dawo musu da daddaɗan labari. Nayi ƙwafa kawai bance komaiba. Daga haka na tattara kayana zan koma. Sai dai kafin na wuce na haɗa harƙalla da abokaina akan zanke turo musu kaya insha ALLAHU suna saidawa su tura min kuɗin. Sunko amince tare da min alƙawarin bazasu bani kunyaba. Daga haka na tattara na koma inda na fito, babu wani zancen nasarar da naci a karatuna dana zauna naima mahaifiyarmu. dan koma ban faɗaba nasan ɗan uwana ya gama tona mata dukkan zance a kaina”.
      “Ban sake sanin ina ɗan uwana yakeba, ba kuma mu sake haɗuwa ba sai bayan kusan shekara, ana gab da zai cika alƙawarin daya ɗaukama iyayenmu na komawa garesu da daddaɗan albishir. A lokacin naje kai kaya ƙasar Syria ne. Kwatsam zamu shiga wani shopping mail ni da abokin tafiyata sai ga twin Brother ɗina tare da balarabiyar yarinya dana taɓa haɗuwa da ita a Italy a bazata. Da gani har shi babu wanda baima ɗan uwansa kallon mamaki ba. Hakama mafi yawan jama'ar wajen kallon mamaki suke mana da al'ajabi. A zahiri dai gashi muna tsananin kamanni, amma a shigar sutura da yanayi bama muyi kama da ƴan yanki ɗaya ba. Ni na fara sakin murmushi ina kallon jaririn dake rungume a kafaɗarsa, sannan na kalli Anum na sake kallonsa. Goshpower kaine anan kuma?”.
      “Shima Murmushin ya saki a karo na farko yana girgiza min kai, yace my twin bro, wannan suna yanzu na bar maka. A yanzu sunana IBRAHEEM ne, wannan matatace Anum, ga yarona Abdul-Maleek. Woow!! Na faɗa ina dariya da tafa hannu, kafin na miƙa hannun ya ɗoramin jinjiri Abdul-maleek. Yaro ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kama da mahaifiyarsa, sai dai ya kwaso kamannina nima ni da ɗan uwana kaɗan. Ganin dai da gaske munsan juna abokin tafiyata ya barni tare da su yana faɗin mu gaisa shi zaije ya kai kayan zuwa anjima saimu haɗu. Na amsa masa da jin daɗi, dan koba komai ina buƙatar keɓancewa dama da ɗan uwana dan naji yaya batun kuɗin daya amso a Nigeria suke. Dan ko kaɗan banji wani damuwa da fahimtar ya koma musulmi ba. Kamar ya shiga raina kuwa. Sai ya buƙaci mizai hana muje gidansa kawai, ashe nan yake da zama yanzun. Mun shiga danƙareriyar motarsa dani da ke wahalar nema da shiga haɗarin rayuwa ko wadda bata kamitaba bani da ita. Wannan abu ya sosamin rai, amma sai ban nunaba muka shiga, suna gaba shida matarsa niko ina baya tare da jaririnsu a hannu. Al'amari bai kuma tadamin hankaliba sai da muka isa ƙaton gida da yaji kayan more rayuwa a matsayin wai nashine. Lallai nasha kallo, cikin mintuna kalilan kuma matarsa ta gama cika gabanmu da kayan ciye-ciye. Sai bayan munci mun ƙoshi mukai gaisuwa da tambayar bayan rabuwa. Bai ɓoye min komaiba daya shafesa bayan rabuwarmu”.
      Yace, (Ɗan uwana kamar yanda na sanar maka wannan itace matata, mun haɗu a jami'ar Italy dakaƙi nutsuwa ka ƙarasa. Da farko tsakanina da ita abota ce, sai daga baya muka fahimci muna son juna. Sai dai ta tabbatarmin babu yanda aure zai kasance a tsakaninmu saboda addinimu ba ɗaya baneba. Hankalina ya tashi domin ina tsananin ƙaunarta. Nai alƙawarin inhar zata yarda mu zama ma'aurata zan koma addininta. Ta sake tabbatarmin indai saboda aurenta ko soyayyar da nake matane zan zama musulmi wannan bazaisa ta yarda ta aureniba. Na musulinta kawai domin ALLAH badan tarayyarmu ba. A hakanma na yarda na amince, a randa muke shirin zan karbi shahada aranar ƴan uwanta biyu sukazo dubata. Sun nuna mata tsantsar ɓacin rai nayin tarayya dani, harma yanda ake musalta musu a cikin makarantar mun zama tamkar wasu miji da mata. Dagani har ita hankalinmu ya tashi muma. Dan tunda nake da ita ko maganar banza bata taɓa shiga tsakanina da itaba. Bata taɓa yarda ko zama gab da juna munyiba balle akai ga aikata wani abu mara ƙyau. Ni bamma taɓa kawo wani mummunan al'amari tsakanina da itaba kamar yanda nasan itama hakanne daga gareta. Kawai dai ALLAH ya haɗa jininmune kawai, kuma ina koya mata karatu. Duk yanda mukaso su sauraremu sunki, daga karshe ma suka tattarata wai zasu wuce da ita. Banyi ƙasa a gwiwa ba wajen tattara duk abinda nake da shi na bisu batare da sun saniba. Sai da muka dira ƙasar saudi-arebia suka fahimci jirgi ɗaya ma muka shiga da su. Sun nuna jin zafin binsu da nayi, amma sai basu hanani na bisu har gidansu ba. Koda muka isa gidansu sunma iyayensu bayani akan dukkan alaƙar dake tsakanina da Anum. Maimakon nai zaton za'a koreni sai naga saɓanin hakan, dan kuwa sun yarda da bukatata ta zama mai salla. Amma babu zancen aurena da Anum, dan suncemin yarinyarsu karatu takeyi. Duk da na shiga tashin hankali saina amince a hakan zan musilinta ɗin. A take kuma na amshi shahada. Komawata musulmi ya sake canja komai, dan kuwa sunmin gagarumar ƙyauta maiban mamaki ta maƙudan kuɗaɗe wai na riƙe kaina, tare da haɗani da wani malami dazan dinga ɗaukar ilimi a hannunsa a ƙasar Italy. Satina biyu a saudia na dawo saboda karatuna. Amma daka ganni kasan bana cikin hayyacina saboda rabani da akai da masoyiyata. Duk na rame na fita hayyacina, amma hakan baisa nayi sakaci da karatuna ba. Na cigaba da neman ilimin addini da zana jarabawar ƙarshe data rage mana na tsahon watanni biyar. Har muka kammala jarabawa banji labarin kaba. Na bincika ance bakaje Nigeria ba. Hankalina ya tashi matuƙa. Amma yaya zanyi. Bayan yin graduation ɗinmu na tattara zan koma gida ƙasata. Amma maimakon nayi 9ja direct saina kasa haƙuri na nufi Saudia wajen Anum. Nayi mamakin tarbar dana samu daga iyayen Anum da ita Anum ɗin kanta daya kasance tazo hutu, dan lokacin karatunta ya dawo nan ƙasar Syria. Albishir na farko da suka faramin shine bani auren Anum, ashe dama sun gwadanine dan suga da gaske nakeson komawa addinin islama kokuwa dan son ƴarsu?. Shiyyasa suka haɗani da malamin dake koyar dani batare da nasan bayanai yake basu ba a kaina. Nayi farin ciki nayi kuka dan daɗi. Sai dai da aka nema na gabatar da iyayena na fito fili na tabbatar musu  akwai matsala. Dan nasan kaf danginmu babu wanda zai amshi canjawata matsayin musulmi balle kuma auren musulma kai tsaye. Naji tsoron Anum zata sake kuɓucemin sai gashi ba hakaba. Dan duk da abinda na sanar musu sai gashi sun amince sun bani aurenta. Bayan ɗaurin aurena da Anum an bamu wajen zama kafin ta koma makaranta. Watanmu ɗaya da tarewa ta koma makaranta, ni kuma naje gida Nigeria, sai dai kowa ya tambayeni ina kake sainace kanacan baka ƙarasa naka karatunba sai next year. Na tarar jikin babanmu yayi tsamari, amma sunki kaisa asibiti. Inada kuɗaɗe masu nauyi a accaunt dana samu saboda musilintar da nayi, dan haka nai amfani dasu wajen kaisa babban asibiti aka fara bashi kulawa. Sai dai kash, kwanakinsa huɗu a asibiti ya rasu. Bayan rasuwarsa da kusan sati biyu nace musu zan koma domin yin kasuwanci. Ananne ogan daddy ya bani kuɗaɗen daddy, wai yace a bamu idan munzo, tunda mune manyan ƴaƴansa maza. Na amsa kuɗi na basu wanda zasu wadacesu na koma saudia. Mahaifin Anum shine ya ɗaurani akan harkar kasuwanci acan ƙasar Syria, ya bani shawarar na koma can kusa da matata ina kasuwancina tana karatunta. Naji daɗin wannan shawara kuwa. Tafiyata Syria ta zama tushen nasarata, dan ina zuwa na iske matata na laulayin ciki. Nayi farin ciki matuƙa, harma bansan yaya zan musalta makaba. Haka na zauna kulawa da ita tare da fara kasuwancina. Cikin amincin ALLAH sai gashi dan danan na haɓaka. Saboda na farane da kuɗaɗe masu nauyi. sannan kuma ta hannun babban mutum irin mahaifin Anum. A haka cikin Anum ya shiga watan haihuwa, tana gab da haihuwa na sayi wannan gidan da nake ciki, tare da motar hawa. Sannan na zauna na banbance dukiyar da take matsayin mallakina, na kuma fidda wadda ta kasance ta mahaifinmu. Kwanaki uku da yin haka Anum ta haihu namiji, wanda yaci suna Abdul-malik. bansan yaya zan bayyana maka ɗunbin farin cikinaba ɗan uwana. Amma babu abinda zancema ALLAH sai godiya. A yanzu haka watan Abdul-maleek uku a duniya, muna shirin zuwa Saudia ne domin nunasa ga dangin Anum dan babu wanda ya taɓa ganinsa sai mahaifinta da yazo mana nan sanadin harkar kasuwarsa. Daga Saudia kuma zamu wuce Nigeria na nunata ga dangina, na kuma sanar musu na zama musulmi duk da a tsorace zuciyata take. Dan yanzu haka maganar da nake makama nayi cinikin wani gida a Lagos, idan munje can zamu ɗan zauna kafin hutun Anum na ƙarshen shekara ya ƙare. Waɗanan takardun sune takardun shaidar company na dana mallaka da dukiyata. Insha ALLAHU kuma zan mallakashi ga Abdul-maleek ne. Dan haka kaima inason ka zama shaida, kaimin signing anan wajen, a duk lokacin da yakai shekaru talatin na girma zan mallaka masa shi. Wannan kuma sune takardun dukiyar mahaifinmu, idan nazo Nigeria mu dukanmu zamu haɗu mu saka hannu alamar tabbatarwa da banawa bane ni kaɗai).
     “Rungumesa nai a lokacin, na nuna masa tsantsar jin daɗina da wannan ƙoƙari nashi, tare da bashi goyen baya akan zamansa mai sallah. Yaji daɗin yanda na bashi goyon, hakama matarsa. Sai dai ni a cikin zuciyata ƙulla ta yanda zan kwashe waɗanan takardun nakeyi, tare da damfare duk wata dukiya da yake fankamar ya tara. Banbar gidanba sai dare, na tafi da ƙudiri kala-kala a cikin raina da zuciyata”.
     “Washe gari ma naje na samesu, shine ya ɗaukeni ya zagaya da ni duk inda companys ɗin suke guda biyu. Na ƙara girgiza da wannan al'amari, dan dukiyace bata wasaba ɗan uwana ya tara. Tofa sai tunanina ya ƙara faɗi da girmama. Dan koda nabar wajensu a ranar kasa barci nayi, har takai na fito na bayyanama abokin tafiyata. Yace na bashi dama zaiyi tunanin ta yanda dukkan wannan dukiya zata zama tawa, amma sai nan da kwana biyu mun gama abinda ya kawomu zai faɗamin hukuncin daya yanke. Naji daɗi, na kumayi murna. Sai dai wayewar garin ranar al'amari ya canja salo, dan bamusan yaya akaiba aka kama wanda muka kawoma kayan cocaine. Har bincike yazo ta kanmu. Da farar safiya mukaji jiniyar motocin ƴan sandan ƙasar. Hankalina ya tashi matuƙa ni da abokin tafiyata, cikin zafin nama muka samu nasarar tserewa ta bayan gidan kafin ƴan sanda su gama shigowa gidan. Muna barin gidan muka rabu nida abokina, domin wannan gudune na ceton rai, kuma hakan abune da kowa ya sani daga tsagera. Idan bala'i ya tunkaro kowa takansa yakeyi. Ba'a sauraren dukiyar da aka tara balle abokantaka. Cikin kiɗima na nufi gidan ɗan uwana, dan duk da wannan bala'i da nake a ciki ban manta da batun takardu ba. Ina isa na samesu a tsakar gida suna hutawarsu cikin kwalliya. Dakewa nai daga ruɗanin da nake ciki na amshi jaririnsu, tare da faɗama matarsa nifa inajin yunwa. Dariyar tsokana suka dinga min, ɗan uwana na faɗin to nazo nayi aure, yafimin wannan gararin, danshi sofa yake na dawonan tare da shi mu haɗa ƙarfi wajen kula da kasuwancinmu. Murmushi kawai nayi, na shiga daga ciki ɗauke da yaron. Matar ta shigo ta bani abinci. Tana kammala haɗamin komai ɗan uwana ya shigo, kallonta yay cike da so da kauna, yace tunda ga bro yazo kizo muje muyi shopping ɗin nan da bamuyiba jiya, sai mubar Maleek tare da shi dan harmu dawo da wahala ya farka. A take ta amince da shawararsa. Yayinda ni kuma kaina ya kawomin wuta a take. Jacket ɗin jikina na cire jin yana faɗin bara ya karo riga a saman kayansa. Nace bro indai rigace ga wanann ka saka nasan zata maka ƙyau, dan yanzun nan dazan fito na ganta a wani shago na siya. Nama tambayi biyu akace babu. Cike dajin daɗi ya amsa, dan shi mutumne mai saukin kai. Sannan bashi da saurin zargi. A gabana matarsa ta taimaka masa ya saka suna dariya da yaba ƙyan da rigar tai masa. Murmushi nayi ina dubansa na ajiye yaronsu na tashi ina gyara masa rigar, cikin dabara na saka masa wayata da wallet ɗina a aljihu, na zare tasa wayar da wallet ni kuma. Sunmin sallama sun wuce bayan sun tambayeni abinda nake buƙata a siyomin nima, dan yace idan ya dawo zamuyi magana akan zamana a gidan. Suna fita na kulle ƙofar falon, na bar yaron anan na shiga cikin ɗakinsu binciken takardu dama duk wani abu mai amfani. Duk kuwa da a raina ina addu'a da fatan tarkon dana ɗana musu ya zama sanadin tafiyarsu har abadan. Komai na gansa, dan haka na tattare tsaf na hada a jikka, na fito falo inda yaron ke barci na ajiye tare da zaman jiran sakamako”.
      “Mintuna talatin kuwa ban rufa da zamaba saiga babban labarin da nake jiran gani daga television. Ɗan jaridan  dake bada rahoto ne ke magana cikin tsantsar sarƙewar harshe, akan samun nasarar kama mutane biyu da suka shigo daga ƙasar Italy da hodar ibilis. An samu nasarar cafke ɗaya a airport, ɗaya kuma daidai traffic light tare da matarsa. Sai dai bisa kuskuren guduwa da sukayi na gardamar su basusan komaiba ƴan sanda suka harbesu, wanda bisa tsautsayi suka matu har lahira. Sai ga gawar ɗan uwana an nuno tare da matarsa kwance cikin jini. Hannayensu riƙe dana juna. Ga ƴan sanda na lalube wallet din dana saka masa tare da wayata anata faman bincike. Ko ɗar banji a raina na nadamar yin hakanba, dan koba komai asirina ya rufu, zan fara sabuwar rayuwa. A take na ƙarasa haɗa duk wani abu mai muhimmanci dake gidan, tare da kayan yaron na shiga mota na fice a gidan. Na tabbatar yanzu bazan fuskanci kowacce irin matsalaba, musamman daya kasance hankalin jami'an tsaron ya koma gaba daya akan nasarar cafke masu laifi. Aiko banci karo da kowace matsalaba wajen barin ƙasar ta mota. Duk da naci uwar wahala ga yaro nata zubamin kuka ban damuba. Haka nai nasarar fita a ƙasar zuwa ƙasar dake maƙwaftaka da su, acan kuma nabi jirgin ruwa, inda anan ne na haɗu da Chioma, itama tsagerace ta kanta, dan kuwa kusan duk irin harkokina shi takeyi, sai dai ita oganta a Nigeria take. A dai takaice na samu nasarar komawa Italy tare da jariri da ɗunbin dukiya da takardun kaddarori da taimakon Chioma. Ogana yayi farin cikin ganina dajin labarin ta hanyar dana kuɓuta, dan haka yaymin alƙawarin taimakona ta hanyar tabbatar duk waɗannan kaddarori na ɗan uwana a tafin hannuna. Yanda Chioma ke taimakona da rainon jariri dana canjama suna da John ne yay sanadin ƙulluwar soyayya mai ƙarfi a tsakaninmu har mukaima juna alƙawarin aure. Ta matsa matuƙa muyi aure sannan mu koma 9ja dan haka na amince mata saboda nima ina sonta. Bayan aurenmu muka nufi ƙasar haihuwarmu cikin danginmu. Wanda zuwa yanzu labari ya gama zuwa kunnen danginmu na rasu ta hanyar kamani ina safarar hodar ibilis ni da wata, dan a haka labarin keta yawo. Kowa kuma yana ɗauka ni aka kashe, saboda kowa yasan halina. ni kuma nine ɗan uwana. Munzo Nigeria ne dama da shirin hutu mai dogon zango, dan ogana ya tabbatarmin dolene inyi nesa da shiga kowacce ƙasa. Inba hakaba kuwa babu makawa sai an bankaɗo ainahin gaskiyar nine mai laifi ba ɗan uwanaba. Nayi amfani da wannan shawara kuwa, dan haka na yada zango a Lagos gidan da ya sanarmin ya saya ta hanyar abokinsa. A labarin nanfa da nake baku kowa ya ɗauka dama nine aka kashe, dan ansan nine tsagera, ɗan uwana kuma shine ni. Dan haka na canja sosai wajen ɗaukar ƙyawawan halayyar ɗan uwana na yafama kaina akan dole. halena kuma na ɓoyesu, dagani sai matata muka sansu. Ban wani cika burin ɗan uwana ba na mallakama mamana da ƙannenmu dukiya ba, sai dai naja ƴan uwan nawa a jiki wajen sakasu cikin harƙallolina. Bansan yaya akai Godwin ya fahimci banine twin bro ɗina ba, sai kawai rana tsaka ya fuskanceni da wannan zance shi da Mike. Na matuƙar tsorata da firgita, amma sai Chioma ta bani dabarun maidasu a hankalinsu ta hanyar ƙara jansu jikina da rufe bakunansu da dukiya mai tsoka da kuɗaɗenta. Danni a lokacin bawani kudine da niba. Sunko bi sun tsuke bakunansu kuma, tun daga nan suka zama sunsan kowacce irin harƙallata, sun kuma san John ba ɗana baneba”.
        “Abinda ya faru baisa na daina harƙallataba, sai harkokine suka sake buɗewa sabbi dan yanzun dukiyar Chioma muke juyawa, nazama jan wuya anan Nigeria, ta hanyar turomin da kaya da ogana yakeyi. Cikin shekara huɗu kacal na shahara, na kuma sakeyin kutse cikin addini har saida na zama Pastor a wata ƙaramar church duk da babu wani ilimi da nake da shi. Zuwa lokacin John ya fara wayo, yanada shekara huɗu, dan ko ina zuwa yake, ga surutu a bakinsa ba'a magana. Yanda yaron ya shiga ranmu muke tarairayarsa bazaka taɓa kawowa a ranka ba dɗanmu bane, dan soyayya ta gaske Chioma ke nuna masa. hakan yasa na ƙara sonta a raina, dukda kaf dangina basa sonta dan ta rainasu, su kuma gani suke ta ƙwaceni ta hanani taimaka musu bayan kuma dukiyarsuce tunda dai kallona suke a matsayin twin bro ɗina. Dukiyar ɗan uwana tazo hannuna, sai dai ba dukantaba, dan wata an tabbatar da dolene sai John ya girma sannan  nasoba kuwa dole na haƙura, na cigaba da juya abinda ke hannuna ta hanyar harƙalla daban-daban. A wannan lokacin ne naje ƙasar France yin wani couse na watanni tara, dan rashin yawan ilimi nason min tangarɗa akan zamana pastor. inda acanne muka haɗu da Sooraj Hashim Jibiya. Bayan korarsa da akai a makaranta sanadin dukan da yaymin nai jiyya kusan ta watanni uku, da ƙyarma na kammala abinda ya kaini na dawo gida cike da alwashi kala-kala akan Sooraj dama yankin daya fito gaba ɗaya. Dan nayi alƙawarin sanadin abinda ya aikata mani saina tarwatsa duk danginsa da jama'ar yankinsa. Wannan shine dalilin farkon fara sato yara daga yankinsu ana kawomin ina cinikinsu. Sai dai na gaza lalubo a ina Sooraj yake? Dan ko'a wancan karon dama bansan taka-maimai shi ɗan ina bane, nadai san musilmine ɗan arewa. a zahiri kuma na lulluɓe True color dina da rigar addini, babu mai cewa ni shege ne. Cikin kanƙanin lokaci na shahara, dukiya da girma suka zauna saina tattaro na dawo Abuja. Wani halaye da John ya fara nuna mana na ƙyamar addini da wasu abubuwan namu duk da ƙanƙantar shekarunsa yasa hankalina tashi. Dan da alama yaron yanada wata baiwa dake nuna ya fahimci kamar muɗin ba iyayensa bane. Mike ne ya bani shawarar zuwa gidan boka a kulle tunanin Yoohan gaba ɗaya, koda ya girma bazai taɓa kawo a ransa muɗin ba iyayensa bane koda yaga rashin kamansa da Chioma. Naji daɗin wannan shawara, nakumayi amfani da ita. Bayan munje wajen boka ya amsa zai mana aiki, sai dai aikin zai zama sanadin saka ciwon rashin barci ga John lokaci-lokaci. A take kuwa muka amince, akai asiri John ya koma tafin hannunmu sosai. Duk abinda muka sakashi babu tantama yake mana, sai dai ban taɓa yarda yasan ɓoyayyar harƙallataba Mamana ma da sauran ƴan uwana nasa akai musu asirin da bazasu taɓa tunanin ko kawowa a ransu niɗin ba ɗan uwana bane. Ana haka Chioma ta haihu twins itama, Gebrail da Joy. Nayi farin ciki sosai da samuwar nawa ƴaƴan, amma samun nawa baisa naji tsanar Yoohan ba. Bayan su Joy Chioma bata sake yarda ta haihuba sai da John ya shiga jami'a ta sake haihuwar Victoria. Ta sake Abraham wanda cikinsa yazo mata babu shirin hakan, dan tace daga yaƴa uku ta gama. To ashe da rabon zuwan Abraham. Abinda yasa nasaka Solomon kullum yake tare da John tun bayan gama karatunsa, saboda tsoron kar wajen yawon ƙasashensa da aiki ya tilasta masa yin  gamo da wani dangin mahaifiyarsa ƙwaɓata tayi ruwa. Shiyyasa dukkan motsinsa sai na sani ta hanyar Solomon”.
        “Abu mafi ɗagamin hankali daya faru shine tarayyarsa da Sheikh Sooraj. Lokacin dana san wannan alaƙa hankalina yayi ƙololuwar tashi,  na kumayi murna dan sanadin John maƙiyina dana ɗauki shekaru ina bulayin nema ya bayyana. har ƙauye naje mukai zaman meeting da sauran mutanena, dan saboda gudun irin haka yasa na cusa masa ƙiyayyarsu tun yana yaro, amma daga ƙarshe sai gashi abinda nake gudun ya auku. John ya xama musulmi kamar mahaifinsa. Ranar nayi tamkar mahaukaciya a gidan nan, harma na yanke hukuncin kashesa kawai na huta bayan na sakashi ya sakamin hannu a takardun da naketa a jiya tsahon shekaru, dan company ɗin yanata haɓaka zuwa yanzun, sai dai ina mamakin ta hanyar wa hakan ke faruwa?. Su Mike ne suka haɗu wajen bani shawarar mizaisa na damu da musilincinsa. Sun san dai babu ta yanda za'ai ya iya gano shiɗin wanene saboda asirin da ke a kansa. Sooraj kuwa amfani zamuyi da kusancinsa da John ɗin mu yashe masa asusunsa tsaf mubarsa da ɗimautar ƙwaƙwalwa da bugawar zuciya. Amma wai koda na tuntuɓi John akan mike alaƙarsu sai ya nunamin wani aiki yakeyi akan Sooraj ɗin. Nafa yarda da shi har cikin raina. Saboda nasan irin horon danai masa tun yana yaro akan wannan yanki. Har raina daɗi nakeji zai ɗaukamin fansa akan abinda Sooraj yaymin tsahon shekaru, dan duk da korar da akai masa a makaranta wancan karon baisa na huceba, na kuma daɗe ina addu'ar haɗuwarmu amma hakan bai yuwuba sai yanzun. Ban fahimci John folani yake a kwalayeba sai akan aurensa da ɗiyar Sooraj, idan nace zan bayyana muku halin dana shiga ni da matata dasu Mike a wannan tsakanin ɓata lokacine, da ƙyar Godwin ya kwantar min da hankali akan na amince da auren, bayan anyi mu kashe yarinyar yanda Sooraj zaiji ciwo sosai a ransa kafin kuma mu yashe masa asusunsa. Wannan shawarace ta kwantarmin da hankali na amince akai aure batare dana yarda na nunama Yoohan nasan ya musulintaba, sanann matata ma ban taɓa faɗa mata ya zama mai salla ba dan nasan tana son John sosai fiyema da ƴaƴanta, kodan shita fara samu matsayin ɗa ne kafin ta haifi nata oho. Shigowar ɗiyar Sooraj cikinmu ta sake ruguza komai na shirinmu, dan yarinyace hatsabibiya. takai ko ganinta nai sai naji matsanancin tsoro na shigata. Bala'in kwarjini takemin kamar ubanta, gata bata da tsoro. Ban sake tabbatar da yarinyarnan abar tsoro bace sai randa ta shigar min ɗaki, ta kuma nuna ba ita bace. Da gaske nima ɗin na yarda ba ita ɗin bace a lokacin, sai daga baya na gane itace ta hanyar cctv dake a falona wadda ko matata batasan da zamanta ba duk da kuwa harƙalla ɗaya mukeyi, kai hasalima na sakatane domin ita dan haka harkarmu take a kullum bama yarda da juna. Bawai ina tunanin itama zata cutar dani bane, dan ina tsananin ƙaunarta, na kuma yarda da ita. Ina tsoron kar dai cikin abokan harƙalla wani yay amfani da ita ya cutar dani ne dai. Sosai hankalina ya tashi da lamarin yarinyar, da kuma tunanin mahaifintane ya turota leƙen asirina. Sai kawai na shirya yanda Doctor ɗin da zasu mata aiki zasu kashe min ita ta cikin sauƙi kafin na dawo kan John ɗin shima. Naji daɗin abinda Gebrail yay mata, dan nasan nesa tazo kusa akan aiwatar da aikina a kanta, sai dai kash Dr Mateo ya lalatamin burina. Naji takaici, naji ciwo, na kuma yanke shawarar halaka John da yarinyar gaba ɗaya da zarar sun dawo ƙasar nan. Zan fara halakata ita da duka danginsu da ubanta kafin shi ma na juyo kansa. Amma taurin kai irin na John da bani da tantama wajen ubansa ya gada sai ya sake ruguzamin shirina. Ya koro Solomon, ya kuma ɗauketa daga Austria ya canja mata ƙasar da bani da damar shiga, dan tuni aka hanani lasisin shiga ƙasar U.S. Wamnan shine dalilin yimin katanga a garesu, na zauna dakon jiran dawowarsu ko zuwansu ƙasar a tare. A randa John ya dakarmin yaro wai ya shigar masa ɗaki naji kamar shima na halakashi da hannuna. Amma na taushi zuciyata dan nasan a tafin hannuna yake. Shina ƙanƙanin lokacine ya rage masa ai. Na tattara komai na ajiyeshine ban masa magana a kaiba dan banason ya zargi komai a kaina har sai randa ya sakamin hannu a waɗannan takardun, ya kuma kawomin shegiyar matarsa ƙasarnan. Dan nagama shiryawa tsaf akan yanda zan yashe asusun ubanta kaf na maidashi sifili. Wai kawai kwatsam rana tsaka saiga yarannan da ciki sunzomin gida. Lallai naga baƙar rana kuwa, dan da gaske ranar susucewa nasoyi gaba ɗaya. Randa na gama shirya ƙudirin aikata lahira suka baro Abuja batare da ko John ya sanar minba da yake shima tantirin ƙwallon shege ne. Nasa a biyota kanon, a daren da zasuzo bisa jagorancin Solomon kuma ƴan sanda suka ritsamin yaro a hanyarsa ta kawomin kaya daga ƙasar Cameroon. Da ƙyar yasha zuwa abuja, duk sun fasa masa jiki da bullets, amma sai yayi ƙoƙarin zuwa ya isarmin da saƙon na gudu, dan da gaske wanann tarkone babba aka ƙulla a kaina tsahon lokaci. wannan shine sanadin tserema ƴan sanda da nayi, sai da na bada ƙafa ta watanni biyu na dawo da baya saboda jin matar John ta haihu ta hanyar wani ɗan leƙen asirina. Na fahimci lokaci yayi da zai sakamin hannu a takardu, daga haka na kama gabana bayan na kasheaa shi da ɗan da matar tasa. Sooraj kuwa zan dawo masa da nasa shirin bayan ƙura ta kuma kwanciya.......”
       Kallonsa kawai kowa keyi a falon kamar sun sami television. Dan shi kansa Jay makircin na Goshpower ya matuƙar rikitashi. Ashe shine sanadin halakar ƙanwarsa da mijinta. Iya bincike sunyi bayan faruwan wancan al'amarin amma suka gagara sanin gaskiya, dan sudai basusan mijin Anum da wani twin Brother ba. Ba komai yaja hakaba sai sakacin rashin bincike danginsa koda a ɓoyene, duk da dai shi yaso yayi binciken a lokacin mahaifin Anum ɗin yace a barsa darajar gaskiyar yaron, a bashi dama har ya bayyana mana danginsa suma ya bayyana musu mu. Tunda dai shi sun gwadashi ta hanyoyi da dama basu samesa da wani mummunan hali ba. A lokacin haushi shi Jay yaji yace ya cire hannunsa akan batun, dan ya rasa wane irin so sukema mijin Anum ɗin. Ganin yanda ya dage da harkar nema da neman ilimin addini yasa shima Jay din ɗaga masa ƙafa ya bashi lokaci zuwa sanda Anum zata haihu, dan yayi alƙawarin da zarar ta haihu kosu Ummu sun yarda ko basu yardaba dolene yasan dangin mijin Anum ta hanyar tasa ƙeyarsu har Nigeria aje tare da shi. Sai gashi a dai-dai gaɓar da take shirin kawo musu ribar auren nata su gani su kuma je ga dangin mijin nata wannan al'amari ya bayyana. Wanda ta sanadin haka suka rasa ƴar uwarsu da mijinta da ɗanta. Suka kuma rasa ainahin gaskiyar zance akan zargin da akema mijin nata. Haka suka haƙura badan zukatansu sunsoba, suka ɗauka wannan itace ƙaddararta kuma. Tare da mahaifinta sukaje suka amshi gawarsu wajen ƴan sanda bayan ansha gwagwamaya suka sallacesu aka kaisu makwancinsu. Sai dai basuga gawar yaronba, sai suka ɗauka wani ya ɗauke gawar a cikin wannan rubibi. Sai dai a binda ya ɗaure musu kai rasa muhimman takardun mijin Anum a gidansa. Bayan wasu watanni kuma akazo musu da batun an ƙwace duka kaddarorin nasa dake a ƙasar ta Syria. Basu da ikon nuna rashin yarda tunda sunsan hakan shine dokar ƙasar ga duk wanda aka kama da irin wannan laifin. Badan zukatansu sunso ba daga haka suka rufe babin Anum da duk abinda ya shafeta. Sai kuma gashi kwatsam bayan tsahon shekaru sunci karo da mai tsananin kamanni da ita a Nigeria, tare kuma da mai tsananin kamanni da mijinta matsayin ubansa. Wannan abu ya rikita Jay matuƙa, harma yaji a aransa inama Ummu da mahaifin Anum na raye su tayasa wannan al'ajabi.....
     Ta ɓasan da Jabeer yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa daga tunanin daya tafi, Jabeer ya nuna masa agogo da faɗin, “Boss asuba fa na gab da shiga, muyi abinda ya dace kafin masu ƙarfin faɗa aji suce wani abu”..............✍
[7/9, 5:30 PM] Sweet Sis: No. 77

............Kai Jay ya jinjina masa zuciyarsa a matuƙar raunane ya dubi Yoohan da kansa ke a duƙe yana hawaye. Nu'aymah kanta kuka take hakama Umar. Cikin ɗacin murya da soyewar zuciya Jay yace, “Goshpower nama rasa abin faɗa a gareka. Dan kaine mutum na biyu da bazan taɓa yafemawa ba da mantawa da shi, bayan gagarumin zalincin da akaima rayuwata da barmin tabo a shekarun baya. Ka cika azzalumi na gasken gaske. Ni nan da kake ganina nine yayan wannan mata ta ɗan uwanka Anum. Mune mukaje har Italy muka taho da ita, tabbas inaji a raina UBANGIJI ya lulluɓe idanunmu daga garekane saboda wannan shine rubutacciyar ƙaddarar Yoohan, wannan wata hikimace daga hikimomin UBANGIJI, ya kuma fimu sanin dalilin yin hakan, kamar yanda ban isa goge abinda aka zana daga zuciya ba, haka ma ban isa canja abinda ya zama rubutacciyar ƙaddara ba domin ALLAH shine kaɗai masanin gaibu, sai yaso mu sani, sai yaso mu gani, sai yaso muji”.
       A kallo ɗaya zaka fahimci a tsananin firgice Papa yake, dan jikinsa har ɓari yake ya dubi Jay, bakinsa ma rawa yake amma ya kasa cewa komai. Hakama Yoohan da Nu'aymah wani irin kallo mai firgitarwa sukema Jay ɗin. Ya furzar da huci mai azabar zafi da ɗauke kansa. Dan ji yake kamar yay fata fata da goshpower kawai kozai samu sassauci a ransa. Lallai yanaji a ransa idan ya cigaba da zama a gidan nan babu abinda zai hanashi huhhuda jikin Goshpower da bullets, dan haka ya miƙe da sauri ya fice hawaye na ziraro masa a saman kumatu. Komai dawo masa yake sabo a rai da zuciya. Gawar Anum da mijinta ne ke dawo masa cikin ido tamkar yanzu komai ya faru. Zafi da raɗɗi da ruɗanin da suka shiga da mutincin mahaifin Anum da ya taɓu a idon danginsa da al'umarsa a wancan karon na dawo masa a zuciya. Aƙidar larabawa ce wannan gudun zubewar mutuncin dangi. Idan kuwa aka samu kuskure wani abu ya auku na zubewar mutunci ga ɗayanku sai ya shafi kusan duk zuri'arku. To hakance ta faru ga zuri'ar Anum, dan sanadin wannan al'amarin mahaifinta yabar duniya, ƴan uwanta kuwa sai da suka bar ƙasar saudia. Tsakanin rasuwar Abban Anum da Ummu kuwa baifi watanni bakwai ba. Kuma hakan nada alaƙa itama da kasa goguwar tabon da aka ringa jifan Anum da mijinta da shi na safarar ƙwayoyi. Duk da su sunsan ba haka baneba, amma tayaya zasu fahimtarma duniya ba haka ɗin bane?. wannan ciwon shine ya tarwatsasu zaman cikin saudiya ya gagaresu duk da kasancewarsu manyan mutane.
       A hankali Yoohan ya miƙe yabi bayan Jay kansa na juya masa, da ƙyar yake iya ganin wajen taka ƙafarsa. Jay na tsaye jikin mota ya kifa kansa kawai yana hawaye yaji an rungumesa ta baya. Kamar dama wannan damar Yoohan ya ke jira sai kawai ya fashe da kuka. Duk mai imani ya gansu a wannan yanayin sai yaji rauni ya ƙara riskarsa. Juyowa Jawaad yayi ya rungume Yoohan ɗin, hakanne ya sakashi sake fashewa da sabon kuka dan yama manta shi namijine a yau. 
     Jay dake murmushi yana bubbuga bayansa yasa hannu ya ɗauke nasa sabbin hawayen da suke sake zubowa yana kallon su Aliyu dake fitowa da Goshpower da yaransa daga cikin gidan. Basu Jabeer ba, hatta da papa kansa sai da zuciyarsa tai masa nauyi. Sai da aka gama tasa ƙeyarsu cikin motocin sannan Aliyu yazo inda Jay da Yoohan suke. Cikin lallashi yayma abokin nasu kuma ɗan uwan nasu magana akan ya kamata su wuce lokaci na tafiya.
       Kai kawai Jay ya jinjina masa. Sannan ya ɗago Yoohan daga jikinsa, hannu yasa yana share masa hawayen daketa zuba babu ƙaƙƙautawa. Ya ɗanyi murmushi da faɗin, “Yarona bazai kasance rago mai kuka a gaban matarsa da jikana ba ai na sani”. Murmushi ya suɓucema Yoohan da sabbin hawaye a lokaci ɗaya, sai yay saurin sake faɗawa jikin Jay ɗin kuma.
          Suma su Naser dake sharar hawaye duk ƴar dariya sukayi saboda yanda Yoohan ɗin yayi. Jay ya yafito Nu'aymah dake goye da Deen tana ta faman kuka itama. “Zo nan my daughter ki lallashi mijin nan naki naga da gaske ɗan shagwaɓa ne”. Ƙarasowa Nu'aymah tayi tana murmushi da hawaye. Jay ya sake ɗago Yoohan yana faɗin, “Kai dama ashe likitoci ragwagene ban saniba ni Muhammadu?”.
        Cikin dariyar ƙarfin hali Jabeer yace, “Boss da alama kam, dan gashi Son ya tabbatar mana”. Duk sukai ƴar dariyar ƙarfin hali data rage musu nauyin zukata. Daga haka suka shiga motoci, dan an bincike gidan babu komai a cikinsa. Sabone ma da alama suma su papan jiya suka shigesa. Su Yoohan mota ɗaya suka shiga da Jay. Umar yaja motar, Jay na gefensa, Nu'aymah da Yoohan a baya. Su Abdallah kuma suka koma a motar da sukazo suma. Waya Jay ya ɗauka ya turama Baba malam text message dan hankalinsu ya kwanta, kafin ya juyo ya kalli su Yoohan dake taimakama Nu'aymah ta sakko da Deen daya sake farkawa daga barci.
     “Abuja zan wuce da ku, zanyi magana da malam insha ALLAH”.
     Sun amsa masa da girmamawa, dan shi kansa Yoohan baya buƙatar yin nesa da Uncle ɗin nasa sam.
      Su Abdallah sun wuce gida kamar yanda Jay ya basu umarni, su kuma suka wuce airport domin komawa abuja, fatansu suyi sallar asubahi acan insha ALLAHU.

_____★

        Idan nace muku wani babba mai hankali a gidan su Nu'aymah ya rintsa  a wannan dare nayi ƙarya. Kamar yanda su Ahmad suka kwana zaune tare dasu Papa haka suma su baba malam suka kwana zaune cike da tashin hankali. Duk da ma Abdallah yayi ƙoƙarin kiran wani a gidan ya sanar masa anga su Yoohan ɗin amma network yayta basa wahala. Dole ya haƙura kawai musamman da labarin da papa ke basu ya ɗauke masa hankali da tunani.
          Motar su na shiga cikin gidan duk su baba malam suka firfito da yakema asuba tayi. Ganin babu su Aymah tare da su ya saka jikinsu ƙarayin sanyi kuma. Sai dai kuma Murmushin kwantar da hankali da Naseer yayi ya saka zuciyarsu samun sassaucin bugawar da takeyi. Su Abdallah suka ƙarasa garesu jikkunansu duk a sanyaye, dan gaskiya ba ƙaramin tausayin Yoohan zukatansu suke a ciki ba.
       Kafinma wani a cikin su baba malam yay magana malam ƙarami yace, “Abba ku kwantar da hankulanku duk an gansu, sai dai sun wuce abuja yanzu haka tare da Uncle Jay, harma da masu laifin”.
   Kusan a tare suka shiga sauke ajiyar zukata, dan baba malam baiga text message ɗin Jawaad ɗinba dama. Jin haka yasa baba malam cewa, “Alhamdulillahi ala'kullihalin, inaga sai muje kowa yay haramar salla dan lokaci yayi”.

      Ina idar da salla kuwa kowa dole ya nema gado ramuwar barcin daya gagaresu. Musamman ma Umm da jininta ya hau ita da Hajjo.

★★★

        Ƴan Abuja ma dai suna sauka wucewa akai da su Papa station, madam Chioma natama mutane kukan iskanci wai Yoohan ya taimaketa kar sonshi ya kasheta. Wannan kalma ta daki zuciyar papa. Ya bita da kallon tsoro da firgici sai dai babu bakin magana dan shi koma tafiya baya iyayi saboda duka ƙafafun sunsha harbi.
       
       Ganin yanda Deen ke numfashi da ƙyarne yasa Yoohan bayan sunje gida sun sauke Nu'aymah su kuma suka koma massallaci. Suna idar da salla yace zaije ya samowa Deen magani dan an ɗibar masa sanyi. Jikin yaronma zazzaɓine.

      Nu'aymah na shiga Miemaa ta fito ta shiga da ita ciki dan Jay ya kirata dama. Ganin yanda Deen keta kuka yasa ta amshesa ranta duk a jagule da ɗaukar alhakin yaron da akayi. Bata wani zauna jan zance ba tai ciki da shi, tare da cewa itama Nu'aymah ta biyota tazo tai wanka dan duk a galabaice take. Ruwa mai zafi ta haɗa mata, shima Deen tai masa wankan da ruwa mai ɗumi sosai. ta kuma gasa masa jikin da towel dan tasan mugayen can ba ɗaukar tausayi zasuma yaron ba. Aiko anayi yana uban kuka. ana kammalawa tunkan ta tsamesa a ruwan har yayi barci. Tausayin yaron ya kuma kamata. Goyashi tayi domin yin salla. bayan an idar ta nufi ɗakinta da Nu'aymah ke can. Har tayi wanka tama shirya cikin doguwar rigar data bata. kasancewar ba salla zatai ba tana zaune tana matsa ƙafarta da tun ciwon dataita mata da cikin Deen har yanzu data haihu bata gama saki da ƙyau ba. “Yauwa ɗiyata kin idar?”.
       Kan Aymah a ƙasa tace, “Eh Miemaa ina kwana?”.
    “Lafiya lau, ya gajiyar gwagwarmaya?”.
     Murmushi Nu'aymah tayi dan kuwa da gaske jiya sunsha gwagwarmaya mai wahalar mancewa a tarihin rayuwa. Miemaa ta bata Deen daketa ajiyar zuciya yana barci. “Kinga bashi abinci, kema bara na haɗo miki ko tea ne kisha ku kwanta ku huta”.
    Babu musu Aymah ta amshesa. Miemaa kuma ta fita haɗo mata tea. Yanda Deen ke amsar abincinsa har tausayi ya bata. Dan ita dai acan bawani samun nutsuwar ƙwarai tayi wajan basa ɗinba. Ta shafa kansa tare da kissing goshinsa, daga shi har mahaifin nasa ɗunbin tausayinsu da ƙaunarsu ya mamaye mata zuciya. Babu jimawa itama Miemaa ta kawo mata tea da bread da soyayyan ƙwai. Amsarsa tayi da cewa. “Zauna kema ki karya, bara naje da shi babansa zai dubasa, idan kin kammala ki kwanta kema ki huta”.
       Godiya Aymah tai mata. Miemaa kuma ta fita.

       A falo Yoohan ya amshi Deen ya dubashi da bashi maganin daya siyo sannan Miemaa ta sake amsarsa ta goya. Sashen Awwab da baya ƙasar yana Spain aka kaisu. Jay yace suyi wanka su sha tea ga shi nan da Miemaa ta haɗa musu suyi barcin gajiya. Sun masa godiya. Su dukansu barcine a idonsu, hakan yasa basu wani zauna zaman maida yanda akayi ba. Dan Yoohan ma sai da yasha magani saboda ciwon kai. da taimakon maganinne ya samu barci mai nauyi yay gaba da shi.

__________★

         Su Aymah sunsha barci sosai. Bayan tashinsu duk suka sakeyin wanka. Zuwa lokacin gida ya cika da su Little bee. Sunsha kuka labarin da Jay ya basu game da ainahin gaskiyar rasuwar Gwaggosu Anum da mijinta. Da kuma tabbatar Yoohan ɗan uwansu. Lamarin ya taɓa musu zukata sosai duk da bama sanin Anum ɗin sukai ba su. Sanda ta rasu Little kaɗai aka haifa, bakuma wanda ya taɓa faɗa musu gaskiyar magana akan rasuwar tata sai yau. Deen yana hannunsu kowa ji yake da shi, hakama da su Yoohan suka tashi sai murnar kowa ta ƙaru. Anuwar ya rungumesa yana kuka. Shima Yoohan ɗin sai da ya koka. Ransa kuwa cike yake da ɗumbin farin cikin tsintar kansa a cikin dangin mahaifiyarsa. Ya ɗauki komai matsayin ƙaddara kamar yanda Uncle Jay ya faɗa.
    Sunci sunsha tare, kafin su zauna kuma aka gabatar da juna. Sannan aka tsaida ranar da zasuje Oman wajen sauran dangin Anum da ke can a yanzu suna rayuwa. Anan kuma Nigeria za'a zagaya dasu cikin danginsu suma insha ALLAH.
       Kiran Jay da aketayine ya sakashi fita dole. Dan yau daga shi har Miemaa da little basu fita aiki ba. Duk da kuwa gari ya ɗauki ɗumi akan kama Papa da yaransa da akayi. Musamman daya kasance an saki video ɗin labarin da papa ya bayar akan saka twin Brother ɗinsa a tarko domin shi ya kuɓutar da kansa. Wannan al'amari ya girgiza zukatan jama'a sosai. Masana nata sharhi akan hukunci daya dace ace ya fuskanta. Wasuma gani suke a kashesan kawai shine babbar mafita ga ƙasar gaba ɗaya. Dan barinsa koda a prison ne wataran wani zai iya fiddosa a ɓoye tunda ƙasar tamu sai a hankali. Hakama jama'ar gari ba'a barsu a bayaba wajen maida yanda akayi dayin sharhi akan wannan al'amari.
      Lokacin da labarin ya isa gidan su Aymah har cikin kunnen Mama debora sai ta yanke jiki da faɗi. Dan su su Abdallah ne sukai zaman faɗa musu yanda komai ya faru ma. Kwasarta akai zuwa asibiti a rikice, su Victoria nata faman kuka dan suna ƙaunar kakar tasu. Musamman daya kasance yau sun wayi gari da wannan tashin hankali na halayen iyayensu da ya ƙara fitowa duniya taji. Basu da kamarta a yanzu, dan sun tabbatar ko ƙauyensu kam yanzu sai ya gagaresu zuwa, dan maimakon tarba da zasu samu daga jama'ar garin kamar da, yanzu idan sunje duka zasuci. 
    Ganin ta farfaɗo baba malam ya hana a faɗama Yoohan. Yace a barsa shima ya hutama ransa, idan ta warware zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai suma a maidasu Abuja ɗin.

      Su Nu'aymah basu san hidimar da akeba. suna nan cikin zuri'ar data kasance ta Yoohan hankalinsu kwance, kowa zallar ƙauna da kulawa yake ƙoƙarin nuna musu. Tare da bama Yoohan labarin dangi kala-kala dana mahaifiyarsa, tare da hotunanta. Ranar dai haka suka kasance cikin ɗumbin farin ciki, dan ma fitar Uncle Jay ta rage armashin hirar.

    A ɓangaren Jay kuwa ashe kirane na sirri ya samu daga manyan ƙasa. Inda sukai zaman tattaunawa dangane da shari'ar papa. Sun yanke shawarar a miƙasa hannun ƙuliya manta sabo da wuri. Wasuko sunce ai masa allurar poison tun kafin shiga kotun, dan suna tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo musamman da Goshpower ya kasace yaron manyan shegun duniya ne. Babu hanyar da bazasu iya biba domin ganin sun kuɓutar dashi. Barin irin su papa a duniya kam ai tashin hankaline. Dan babu makawa a yini guda suna iya tada jama'ar ƙasa da ƙasar baki ɗayanta. 
        Shi dai Jay bai yarda ya tofa wata maganaba, dan suma ɗin ai baisan yaya nasu zukatan sukeba, balle ayyukansu na ƙarƙashin ƙasa. Sannan baima saniba ko suma ɗin wani abu sukesan binnewa ta wannan hanyar tunda kowa yasan yanda papa ke mu'amula da manyan mutanen ƙasar ai. Sai da duk suka gama surutansu yace shidai a nashi shawaran kawai su bari a miƙasa kotun, yanke hukunci aikin alƙaline ba nashi shi jami'in tsaroba. Idan kaga mai laifi ya rasa ransa a hannun jami'in tsaro sai dai akan kuskure ko kare kansa ga mai laifi idan yanada makami. Amma haka ɓakatatan basu da damar yima goshpower allurar poison. Duk da wasu sun nuna jin haushinsa shidai bai damuba. Yay musu sallama ya wuce office. Gudun zuwan abinda zaije ya dawo ya sakashi tattara duk wasu bayanai dake a hannunsa a yammacin ranar ya tura ƙara kotu sannan ya koma gida.
      Miemaa kaɗai ya sanarma halin da ake ciki, amma su Yoohan baice musu komaiba, saima sakawa yay aka kawo masa Deen da bai gajiya da barci saboda kasancewarsa jariri har yanzu. Kwata-kwata yau kwanansa tara kenan ma a duniyar. Amma ya fara cin karo da gwagwarmayar cikinta.
     Kasancewar Aymah jego take yasa Miemaa tsayuwar daka a kanta ta ƙarasa jegon anan, dan summa gama magana dasu baba malam idan su mama debora zasu wuto Abuja gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho mata da kayanta dana Deen kawai. Koba komai hankalin Nu'aymah yaɗan nutsu waje ɗaya yanzu, hakan yasata ƙagara ma a kawo mata kayanta ta koma sauraren lectures kota online ɗinne kafin suga abinda ALLAH zaiyi akan maganar komawarsu. Danshi kansa Yoohan harma ya ɗauki hutun ƙarshen shekara mai nisan zango sosai.
     Washe gari su Jay suka tattare al'amarin papa suka miƙa kotu, yayinda dangi keta tururuwar zuwa gidan Jay ganin Yoohan. Dan su Afrah duk sun baza labari ta waya. Khairiyya kanta da ba'a garin take aure ba sai gata a wannan ranar ganin yayansu. Duk da dai bama wani girmanta yayi sosaiba, amma dai little ta girmesa. shiyyasa abu kaɗan ke sakasu fara faɗa. Shi son girma ita son girma. Daya motsa tace shiɗinfa ƙanintane. Shi kuma yace ALLAH ya kiyaye ya zama ƙaninta. Abun nasu na bama kowa dariya. Musamman ma Nu'aymah.

*_WASHE GARI_*

         Washe gari su Mama debora da taji sauƙi duk da bata koma garau ba suka iso abuja saboda suna son halartar zaman kotu da za'ayi. Ba kowa ya matsa hakanba kuwa sai mama debora. Dan tasha kuka, acewarta tanason taga idon papa ko zaiji kunyar yaudarar da yay mata na saka ɗanta mutumin kirki a tarkon da aka kashesa.
       Da yake tafiyar mota sukayo, kuma sun taho da wuri sai gasu kusan sha biyu sun shigo garin Abuja. Yoohan na tsakkiyar dangi da keta cigaba da zuwa kiran Gebrail ya shugo wayarsa. Ɗagawa yay ya koma gefe. Cikin girmamawa Gebrail ya gaidashi da faɗa masa gasu sun shigo Abuja. Zasu wuce can gidanne kokuwa suzo nan gidan Uncle Jay ɗin su samesa?. 
     Yoohan yay ɗan jimmm kafin ya furzar da numfashi, yace, “Okay, inaga ku wuce can, nima gani nan zuwa gidan”.
    Da girmamawa Gebrail ya amsa masa da to. Yana yanke wayar ya sami Uncle Anuwar da maganar, dan Uncle Jay baya nan ya fita saboda sunata kai kawo akan lamarin papa da yaransa su Solomon.
     Uncle Anuwar yace, “Yahya ai daka barsu sun wuto nanɗin kawai, dan an riga da an zama ɗaya yanzu. A gidan nan kuwa munada isassun masauki insha ALLAH. Sanann kusancin zama da zamu samu dasu yanzu zaisa suma idan sunada rabo sai kaga sun karɓa musulinci”.
      Cikin ɗan sosa wuya da jin daɗin wannan fata Yoohan yay murmushi idonsa nakan Nu'aymah da suke hira dasu Afrah acan gefensu. Yasan komi rayuwarsa ta zama a yanzu itace sila, dan haɗuwa da ita shine ya zama hasken da ya haska masa hanyar da yake taka ƙafa, iska yaɗan furzan da faɗin, “Okay Uncle bara naje zuwa anjima ai sai nazo dasu ɗin, kagama sannan Uncle Jay ya dawo”.
       
      Kamar yanda Yoohan ya faɗa bayan sallar azhur ya nufi gidansu. Duk an janye ƴan sandan da suke zagaye da gidan, ko maigadi yanzuma babu balle waɗannan guards da ke cike da gidansu a da. Rayuwa kenan, ka shuka alkairi sai ka girbe abinka. Horn yayi kusan sau uku sannan Gebrail yazo da ɗan gudunsa ya buɗe masa gate ɗin. Sai da ya gama ƙarema harabar gidan kallo da duk motocin dake cikinsa kafin ya furzar da nannauyan numfashi ya fito, dan Gebrail ya buɗe masa tuni.
      Cikin gidan suka nufa yanama Gebrail tambayoyi, shi kuma yana amsa masa cike da damuwa, dan har cikin ransa kunya da ƙaunar Yoohan ce cike da ruhinsa. Bama shi kaɗaiba, duk sauran ƴan uwansama hakane. Suna shiga kuwa da gudu su Victoria sukazo suka rungumesa. hakama mama debora rungumesa tai tana kuka da rera addu'ar neman sakayya a garesa da yarensu. Ba itaba ko mai saurarenta yaji yanda take addu'an zaisan akwai tausayi a ciki.
    Da ƙyar Yoohan ya lallashesu sannan suka zauna suka ɗan sake tattaunawa. Mama debora tace tunda har papa ya kashe ɗan uwansa da matarsa itama ta yarda a kashesa. Yoohan dai kunyar su Gebrail ya hanashi cewa komai akan iyayen nasu, daga ƙarshema yace su shirya zai wuce da su.

       Zan iya cemuku a ɗar-ɗar su mama debora suke da zuwa gidan Jay, kamar yanda sukaita ɗari-ɗarin zuwa kano gidansu Nu'aymah. Sai dai abinda ya basu mamaki anan ma sai akai musu tarba ta mutunci da kulawa. Hakan yasa suka sakeji a ransu lallai hausawa nada ƙyaƙyƙyawar zuciya a duk inda suke. Sannan musulmai ba mutanen banza bane kamar yanda a kullum papa ke musu huɗuba a gida da church. Sai gashi tundai suna ɗari-ɗari har suka saki jikinsu. Bayan Jay ya dawo suka zauna aka ƙara tattaunawa. Mama debora da su Momy Destiny sunsha kuka. Su kansu su Joy sunji ciwo da kunyar halayen iyayen nasu matuƙa. Sunata kuka da bama Yoohan haƙuri. Shi dai murmushi kawai yake musu. Nu'aymah ma haƙuri sukaita bata akan abinda sukai mata. Tace babu komai ita ta yafe musu. Gebrail kam ko yarda su haɗa ido Aymah baya yarda suyi sam saboda kunya. Ita har dariyama abin ke bata. 

____________

        Ranar data kasance za'a shiga kotu da su papa ƴan jarida a abuja har bama magana. Kowa burinsa ayi komai akan idonsa. Kuma burin kowa ya nuna komai live. wannan kuwa duk a cikin shirin su Jay ne. Sun gayyato ƴan jaridune ta kowanne ɓangare dansu katange dukma wata kitumurmura da za'a iya ƙullawa game da shari'ar.
        Kotu ta cika maƙil itama da al'umma, musamman waɗanda aka samu ƴaƴansu a gidan papa. Duk da ma wasu iyayen nasu sun gagara ganesu, sukuma basusan daga inda aka ɗakkosu ba dan tun suna ƙanana ne. Shari'a ce da bata buƙatar lauya sam, saboda komai na papa a bayyane yake. Zamane kawai da za'ai maganar ƙarajin abinda ya shuka a yanke hukunci kuma.
      Yoohan dai da farko baiso su Gebrail su bisu ba. Amma sai Uncle Jay yace ya barsu suje ɗin dan wannan itace kaɗai damar da zasu samu ganawa da iyayen nasu. Badan yasoba kuwa suka shirya suka tafi kotun, cikin amincin ALLAH kuwa sun sami gaba-gaba saboda sun tafi da wuri.
       
     Sai da kotu ta gama cika tab da al'umma, alƙali ya shigo sannan aka shigo da papa da su Mike. Papa saboda harbin da yasha a kafafu sai a wheelchair, sauran kuwa babu ko ƙwarzanen duka a jikinsu amma a ido zaka gansu a wani irin bala'in galabaice. Su Jay kaɗai sukasan irin horon da sukema rayuwarsu cikin hikima. Bayan buga gudumar alƙali kotu tayi tsitt na wasu mintuna, dan da anata ƴan kananun magana saboda shigo da su papa da akayi. 
    Alƙali ya sakeyin gyaran murya sannan ya fara magana, “Wannan shari'a ce da kowa zai iya fahimtar bata buƙatar wani kaiwa da komawa balle zaman lauyoyi a tsakani. Dan komai a bayyane yake wa duniya akan masu laifin. Amma duk da haka dolene mu karanto musu laifinsu su amsa kafin mu yanke hukunci”. Bai jira amsar kowaba dan ba ita yake jiraba daman. ya bama jami'an tsaro damarsu. Dawood ne ya miƙe ɗauke da file ɗin dukkan bayanan laifukan Papa ya kai ga alƙali. Batare da alƙali ya amsaba ya bashi damar karanto komai.
     Tsayuwa Dawood ya gyara yana fuskantar su papa. Ya fara bayani dalla-dalla. a duk gaɓar da yazo ƙarshe alƙali zai ma su papa tambaya akan shin hakane sun aikata?. sukan ɗan nuna tirjiya kafin papan ya tabbatar da sun aikata ɗin. A haka aka dinga bin duk laifukansu daki-daki tare da shedun da suka gani da ido wajen tabbatarwa. Hakanne yaja shari'ar tai tsaho sosai aka jima ba'a tashiba.
     Ƙara jin bayanan sai ya ƙara komawa mutane tamkar sabo a cikin kunne, wasu harda hawaye sukeyi, wasu ko kawai gani suke babu hukuncin da su papa suka dace dashi sai mutuwa. Da ƙyar Alƙali ya samu kotun nan ta lafa da ga hayaniyar data ɗauka akan cecekucen jama'a. Ya ɗauki ruwan dake a gabansa ya sha cike dajin gajiya da damewar tunani wajen yanke wannan hukunci.
    Bayan kotu ta sake lafawa alƙali ya fara magana kamar haka, “Ya kamata kuyi hakuri ku bamu haɗin kai, nasan duk wani hukunci da zamu yanke anan bai zama lallai ya gamsar da waɗanda wannan mutane suka cutarba. Amma zamuyi iya bakin ƙoƙarin mu dan ganin mun yima kowa adalci. Sun tafka kura kurai da kowanne idan zamu ɗauka yanada nashi hukuncin ne, to amma kisan kai da suka shigo sun shanye duk wani laifuka nasu. ALLAH kaɗai yasan iya rayukan da suka salwantar, dan kosu a yanzu ba iya lissafawa zasuyi ba. Dan haka wannan kotu mai adalci, ta yankema waɗanan mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya”. Yana gama faɗa ya doka gudumarsa.
    A take kotun ta ɗauki ihun kace nace ɗin mutane. Har bakajin zancen wani. Sai dai duk wannan surutai babu mai goyen bayan su papa. Wasuma duk da an ambaci kashesun za'ayi su hukuncin sai bai musu ba. a ganinsu ayi gunduwa-gunduwa da su kamar shine yafi dacewama kowa ya huta. Kamar yanda kotu ke a harmutse haka jama'ar gari ke a harmutse dan ƴan jaridu nata kai rahoto live. A take duniya gaba ɗaya ta ɗauka. Inda wasu ƙungiyoyi kamar Masu kare haƙƙin ɗan adam suka fito suka nuna bore da wannan hukunci. Har suna iƙirarin ɗaukaka ƙara. Sai dai to bamusan zuwa wane kotu suke da burin ƙarar ta kaiba, tunda mudai anan Nigeria a babbar kotun ƙasa gaba ɗaya aka yanke hukuncin.
       Duk yanda Yoohan yaso su mama debora su gana da Papa al'amarin ya gagara dan da ƙyarma aka fiddasu daga cikin kotun. 

______________★★

         Bayan kwanaki biyu da faruwar wannan al'amari da safe su Jay na tsaka da yin breakfast ya samu waya daga alƙali cewar sufa sun gama yanke hukuncin su papa. Dan sun fuskanci al'amarin neman canja salo yakeyi na ƙirƙirar rikici da hukumar kare haƙƙin ɗan adam ke neman haddasa musu. A yanzu haka maganar da ake ga gawarwakin su papa nan, a gaban ƴan jarida akai komi yanzu kuma zasu bada damar a saki labarin.
     Al-amarin ya girgiza zuciyar Jay matuƙa, to amma shima hakan yafi masa sauƙi tunda dai shine hukuncin da aka yanke musu a gaban kowa. Koda sukai sallama da shugaban alƙalai bai iya yima su Yoohan bayanin abinda ya faruba sai Miemaa kawai. Ita kanta duk da tasan su papa masu laifi ne sai da tausayin mama debora ya ƙara kamata da su Victoria. To amma wannan shine dai-dai kuma abinda ya dace..
      Kafin shabiyun rana labari ya gama zagaye ƙasar dama duniya akan zartar da hukuncin da aka yankema su papa. Wasu kam sun ɗauki ɗumi akan hakan, dan duk da mummunan halin su papa suna samun magoya baya musamman masu irin halayyarsu da ayyukansu. To andai yita ta ƙare. labarin su papa kuma ya zama tarihi, sai kuma na baya garesu, dan yanda mutane. kirki basa ƙarewa hakama mutanen banza kullum sake yawaita suke.
     Mama debora dai tasha kuka a ɓoye, dan ɗa da mahaifi sai ALLAH, musamman daya kasance mazan ƴaƴanta har uku. To amma tunda ta rasa mahaifin Yoohan da yafi sonta da ƙyautata mata tai haƙuri, dan ta rasa waɗanan azzaluman minene zaisa ta takura kanta kuma. Su Joy ma dai saida suka koka sosai. danma an hana Abraham da Victoria kallo sam. 
     Yoohan kansa sai da yay hawaye, koba komai yasan su ɗin jininsa ne. Nu'aymah ce kawai ta iya fahimtar shima kukan yayi, dan haka tana ganin ya fita itama ta bisa a sace ta ƙofar kitchen. Acan baya ta hangosa tsaye ya jingina da bango yay shiru idanu a lumshe. Ƙarasawa tai garesa ta kamo hannunsa cikin nata. Kusan a tare duk suka sauke ajiyar zuciya. Batare da yace da ita komaiba ya jawota jikinsa ya rungume. Luf kuwa tayi kusan mintuna uku sannan ya ɗagota yana murmushi. Kafin yay magana tace, “Silly boy! Kuka kakema waɗanda suka kashe mana su Abbabmu saboda son zuciya”.
     A karon farko ya saki murmushi da shafa fuskarta. Murya a raunane yace, “Silly girl! Kin samin ido da yawa fa”.
      Dariya tayi kaɗan ta kwantar da hankali, sannan ta ɗan marairaice fuska cike da kulawa tace, “Sai haƙuri Yah Maleek, haka rayuwa take, wani farkonsa yaji daɗi ƙarshen yasha wahala. Wani yasha wahala a ƙarshe yaji daɗi koba a duniyaba. Kaji labarin gwagwarmayar da Uncle Jay yasha shima shi da Miemaa. Amma bagasu komai ya wuce a garesuba tamkarma bai faru ba. Muma idan mukai haƙuri sai kaga komai ya zama tarihi insha ALLAH ”.
     Cike da jin daɗi ya sake rungumeta da sumbatar laɓɓanta. Ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. “Thanks you Zeeynab. Kin gama bama rayuwata dukkan abinda take buƙata, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci Deen, ALLAH yasa ya zama mai gadon baba malam. ALLAH ya gafartama iyayenmu ya ƙara mana haƙuri da abinda ƙaddara ta danƙa mana a tafin hannunmu”.
     “Amin ya rabbi yah maleek”.
Sake rungumota yay jikinsa yana dariya ƙasa-ƙasa da fadin, “Sunan nan fa yayi daɗi Sweet girl”.
      “Sosai ma, Mami da Abba sun iya zaɓen suna. Kaga yanzu ka zama mai suna biyu, danni kam daga yau Abdul-maleek zanke faɗa”.
      “Silly girl! ki rage jan faɗa yanzu akwai Deen a gabanki”. Ya faɗa yana jan hancinta.
    A tare suka sanya dariya, suna maijin farin ciki mai yawa a ransu.

        A daren ranar kuma sai ga saƙon rasuwar Addah ya samesu. Duk da abinda ta tafkama rayuwarsu Nu'aymah sai da taji duk ta rikice. Tasha kuka kuma a daren ranar. Washe gari kuwa tunda safe suka ɗauki hanyar kano a mota harda su Jay, cikin sa'a kuwa suka samu jana'izar Addah, dan sai goma aka kaita masaukinta na gaskiya. Sai kuma aje a girba abinda aka shuka.
     Duk da abinda Addah taima Umm rasuwarta tayi masifar girgizata, dan saida takai an saka mata ƙarin ruwan daya sakata dogon barci saboda ruɗanin data shiga. Jikin kowa ya ƙara sanyi kuma a agidan harma da sauran ƴan uwa. 
        Da yamma su Yoohan suka koma Abuja aka bar Nu'aymah anan kano, sai bayan anyi addu'a Yoohan yace zaizo ya ɗauketa dan zasuje Oman wajen dangin mahaifiyarsa da ƙaddara ta maida can.
          
        *_BAYAN SATI GUDA_*

Bayan sati ɗaya da rasuwar Addah da mutuwar su papa Yoohan yazo da kansa ya ɗauki Nu'aymah da Deen suka koma Abuja, zuwa yanzu kuma Alhmdllh Umm ta ɗan dake saboda kulawa da baba malam keta bata dan ganin ta samu kwanciyar hankali. Hakama Hajarah daketa fama da tsohon ciki sai Umm ta roƙu mijinta ya barta ta dawo nan gida harta haihu dan itama rasuwar mahaifiyar tata ta taɓata sosai. Bai musaba ya barta ta dawo, tana nan zaune wajen Umn yanzu haka. Zaman natanema ya ɗan ragema Umm raɗaɗi. Hajjo kuma koda yaushe takan yawaita shigowa ta sake kwantarma da Umm hankali itama, hakama Ananah da bata komaba.

*_OMAN_*

       SU Nu'aymah sun isa Oman lafiya, inda suka sami tarba ga dangin Mami (Anum) dan tunkan zuwansu labarin komai yazo musu. Abin mamaki sai su Yoohan suka sami Dr Shikurah acan Oman, ashe kanwarta datake faɗa ɗanta na kama da Yoohan itace ke auren yayan Anum da suke uba ɗaya. Sun haɗune acan Oman da taje karatu, a yanzu haka yaransu kusan shidda. Mahboob mai tsananin kamanni da Yoohan shine yaronsu na farko. Idan ka gansu shi da Yoohan saika ɗauka tagwayene saboda tsabar kamanni da sukeyi da juna, abin mamaki har tafi har maganarsu iri ɗayane. Sosai abin ya birge Yoohan. Har yaji a ransa inama ya amince tun sanda Dr Shikurah ke masa kamanni da Mahboob ɗin ya amince ta kawosa yagansa. To amma ya ɗauka hakan kawai matsayin abinda ALLAH bai hukunta ba.
          Da yake anzo dasu mama debora suma sai hakan yasaka dangin Anum ƙara jin daɗi, dan koba komai sun ƙara yarda IBRAHEEM mutumin kirkine shi. Ansha kuka da tunawa da rasuwarsu da yanda rasuwar tazo. tare da jifan su papa da kalmomin ALLAH wadarai danma ana ɗan tagawa darajar mahaifiyarsa dake a wajen. 
     Deen da Nu'aymah kam lallai sunga soyayya ƴar gaske, dan gatan da Yoohan bai samu ga dangin uwaba a yanzu kowa ƙoƙarin ganin ya nunama Deen yakeyi. Sunga gata kam sun kuma sha daɗi Alhmdllh. Satinsu uku cif suka dawo Nigeria badan ƴan Oman sunso hakaba.

      Suna dawowa kuma aka shiga hidimar bikin Naser & Yusrah, Abdallah aka maida masa Adawiya suje su cigaba da haƙuri da juna. Amal da malam ƙarami. Ahmad da Nanah yayar ƙanwar Umm. Ansha biki an raƙashe an ƙwalle Alhmdllh, yayinda Abban Abdallah ke kwance yana fama da kansa shima. Dan shikam bikinma bazaice yasan anyiba. To dama haka rayuwar take ai.

    Bayan an gama biki an miƙa amare ɗakunansu komai ya zama Alhmdllh Yoohan ya tattara matarsa da ɗan ɗansu da yay ɓul-ɓul gwanin sha'awa syuka koma ƙasar U.S saboda karatun Aymah, shi kuma zai koma aikinsa na hidima wa al'umma.
    Basubar ƙasarba sai da ya nemawa su mama debora gida anan kusa da su Uncle Jay aka saya musu, dan mama debora ta rantse bazata sake zama gidan can da papa ya gina ba. Hakan yasa aka saidashi suka dawo nan. Gebrail da Joy an nema musu makaranta a ghana. Mama debora zata cigaba da zama dasu Victoria dasu mama Destiny da suma suka dawo nan tare da mazajensu. Dan zaman can kauyen kam bazai yuwu yanzu a garesuba.

_____★

      Tunda su Nu'aymah suka dawo fa sai ta ɗaura ɗammarar dagewa akan karatunta, haka shima Yoohan ya sake dagewa akan neman iliminsa na addini. Ga renon ɗan ɗansu daketa ƙara girma masha ALLAH.
      Soyayyarsu da shaƙuwa kuwa sai abinda yay gaba. Yayinda Hajiya Nu'aymah aketa ƙara canjawa ana hankali da rage fitsara kamar ba itaba. Ga jikinta sai buɗewa yake tana ƙibarta masha ALLAH.
     Haka rayuwa ta ciga da gunguramawa waɗanan bayin ALLAH, yau asha zuma gobe asha maɗaci. Da sun sami hutu sukan shirya suje Nigeria, hakama ƴan Nigeria ɗin lokaci-lokaci Yoohan kan ɗakko wasu a cikinsu suzo su musu hutu.
    Daga Deen dai Nu'aymah shiru, da alama kuma dai sune asuka tsarama kansu hakan, dan a yanzu haka ga Deen da shekara ta huɗu, Nu'aymah kuwa na shirin kammala karatunta. Yaro ya girma yay wayau, ga miskilanci ga zuciya ko kuturu haka ya gansa ya bari. 
      burin Yoohan dama nu'aymah ta kammala karatunta ya tarkatasu ya maida Nigeria, cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ta kammala lafiya cike da nasarorin rayuwa. Wannan karon kuwa Umm da baba malam ma sunzo U.S, taso azo da hajjo baba malam yaki dan tsufa sosai ya ƙara kamata, ga ciwon ƙafa dake damunta. Kowa ya taya Aymah murna da nasarar data samu daga ita har mijinta, bayan kammala komai suka tattaro zuwa ƙasarsu ta haihuwa, inda Yoohan ya saya musu gida suma duk da su Jay sunso Yoohan ɗin yay zamansa anan gidansu, amma ya ƙi, dan gaskiya yanajin kunyarsu ainun.
             Ƴan uwa da abokan arziki sun tayasu murnar gida. Dan ƴan kano ma duk saida sukazo, harda su Aunty Kubrah da zuwa yanzu tayi haƙuri a gidan aurenta duk da ba daɗin zaman takejiba dai.
     A wannan dawowane kuma kowa ya fahimci Nu'aymah laulayin ciki takeyi. Anko tayasu murna da addu'ar ALLAH ya raba lafiya.

    Dawowarsu baifi da wata guda ba ALLAH yayma abban Abdallah rasuwa shima. Ansha alhini ansha kuka, daga baya kowa ya rakasa da addu'a. 

*_A KWANA A TASHI_*

      Lallai kam akwana atashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan yanzu shekarun Auren Nu'aymah da Yoohan goma kenan. Zuwa yanzu ALLAH ya azurtasu da ƴaƴa uku, Deen, Ibrahim, sai auta Anum. Jay ne ya hana a ɓoye sunan yaran, yace a bari ake kiransu da sunansu hakan zaisashi farin ciki. Dan haka aka barsu kuwa da sunayensu ana kiransu da shi.
         Abubuwa da dama kam sun faru a waɗannan shekaru, masu daɗi da akasin hakan sai dai kawai muce Alhmdllhi ala kulli halin.

*_“Sweet girl! Sweet girl!!”_* 

      Nu'aymah da ke a can backyard tana shanya kayan su Anum data wanke tana mita ta jiyo Yoohan na ƙwala mata kiran mafarauta. Kanta ta dafe dan ta tabbatar su Anum ne suka hanashi barci. Dawowarsa kenan babu jimawa daga asibiti a gajiye matuƙa. Sabodama kar yaran su gansa su hanashi hutawa a wajen gate yay fakin, ya shigo gidan a saɗaɗe saima yay sa'a su suna a can garden suna wasa Nu'aymah ta korasu itama ta huta. Shiyyasa itakam batama cika son weekend tai musu a gidanba. Tafi buƙatar su wuce gidan Uncle jay ko gidan Aunty Little ko wajen su maman Destiny.
      Jin ya cigaba da ƙwala mata kiran yasa ta ajiye abin matse kayan dake a hannunta ta nufi ciki da sauri. Ilai kuwa samun duk yaran tayi a bedroom ɗinsa ɗane-ɗane bisa gado kusa da shi kowa na ihun sai ya tashi an kaisa gidan Abie (Jay). Kai Nu'aymah ta dafe sannan ta ɗaure fuska ta daka musu tsawa. Tsitt kuwa sukayi kowa na kwaɓe fuska.
    Sai a lokacin Yoohan ya janye filon daya cusa kansa a ciki ya tashi zaune, kallon yanda yaran duk suka zuba tagumi yay, ya kuma dubi yanda Nu'aymah tai bala'in tsare gida. Sai shima kawai yay tagumi kamar yanda yaran sukayi ya zuba mata ido. Hararsu tayi su duka ta ida shigowa cikin ɗakin. Da sauri Ibrahim dake da shekaru shida ya matsa jikin Yoohan ya lafe, sai itama Anum dake da uku ta matsa ta lafe. Duk yanda Yoohan yaso daurewa sai ya kasa ya saki ƙaramar dariya yana kama kunnuwansu yaja kaɗan.
      “Wato kuɗinnan fa nagama ni kuka raina a gidan nan, ita Mie-mie kuna tsoronta, amma ni kunma maidani Uncle Jay kakanku ko?”.
   Yanda yay maganarne ya saka Nu'aymah yin dariya itama, ta yamutsa fuska da faɗin, “Dan ALLAH ka tattarasu ni kama kaisu gidan Miemaa, abar min Deen kawai anan”.
    Cikin ɗage gira Yoohan yace, “Oh, saboda kinga yarona mai hakuri kina samin shi aiki ko. To naƙi wayon, waɗanan tom and jerry ɗin zan bar miki anan, Abbana kuwa kano ma zan kaisa yayma Umm Hutu da Uncle Muhammad. Inama yake?”. 
        “Haba Yah Maleek dan ALLAH kar muyi haka da kai, waɗanan mi suka iya banda takurama mutane”.
      “Hhhh kunfi kusa ai. Kai mai jan kunne ina Abbana yake?”. Yoohan ya faɗa dajan kunnen Ibrahim.
     Ƙwaɓe fuska yaron yayi yana tashi daga jikinsa ya koma wajen Nu'aymah. “Mie-mie ALLAH nama fasa sayama Dada birthday gift ɗin da nace miki tunda bazai daina cemin maijan kunne ba. Gashi nan har Wannan Anum ɗin ta kama bayan itama jajayen kunnen ne da ita”.
      Sosai Yoohan da Nu'aymah suka kwashe da dariya. Cikin dariya Yoohan yace, “A to indai hakane bazan sakeba Abban Mie-mie. Zomu shirya kaji”.
    Ɗan jimm yaron yayi, sai kuma ya kalli Aymah. “Mie-mie kin yarda na shirya da shi?”.
      “Hhhh haba Abbana wake fushi da babansa dama inba shashasha ba”.
       “Ai dama nima bana fushi da shi ko Dada?”.
     Yay maganar da matsawa jikin Yoohan dake kallonsu da murmushi. Rungumesa yayi sannan ya dubi Aymah da wani narkakken kallo. “Wai ina Abbana?”.
    Miƙewa tai tana bashi amsa. “Yana ɗakinsufa yana gyarawa, dukansa nai shiyyasa yaƙi fitowa, yana can yana faman haɗiyar zuciya uwa budiddigin ƙwaɗo”.
     Sakkowa Yoohan yay daga gadon ɗauke da Anuma yana faɗin, Ayyah Mie-Mie mi mukayi haka ne harda taɓa mana lafiyarmu?”.
       “Miskilancin da kuka saba mana. Yaron nan a gabansa na gama gohon gyara musu ɗaki wai dan wulaƙanci yana zaune a ɗakin su Anum suka sake hargitsashi bai hanasuba shi shugaban miskilawan Najeriya. Shiyyasa na dakesa dan gobe idan sunyi ai ya hanasu ko”.
     “Aiko a kansu zansa ya rama. Abbana kana ina?”.
     Kafin Aymah ta bashi amsa Deen ya fito daga ɗakinsu baki cike da iska. Yana ganin Yoohan sai gashi da gudu yazo ya rungume Dadan sa.
    Cike da so da ƙauna Yoohan yace, “Oh my sweetheart so sorry yeah. Bar Mie-mie anayin hutu Kano zan kaika wajen Umm da Uncle. Aiko cike da jin daɗi yaron ya hau murna. Yayinda su Ibrahim suka koma jikin Aymah suka lafe wai sunan jealous ya motsa. Dariya Yoohan yayi suma ya miƙa musu ɗayan hannunsa. Da gudu kuwa suka ƙaraso ya haɗasu ya rungume yana maijin farin ciki a ransa da samuwarsu a garesa matsayin ƴaƴa. Waɗanda suka fito daga tsatson Nu'aymahrsa mai rigima da tsiwa. Shikam babu abinda zaicema ALLAH sai godiya kuma, dan ya gama masa dukkan rahama. Ko a musilinci n daya tsunta kansa a ciki bayan dulmiyar da shi da su papa sukayi ai ya gamacin ribar rayuwa. Balle kuma daɗin daɗawa ga ƙyautar mace ta gari da ƴaƴa nutsatstsu da ALLAH ya bashi. Wanda ya tabbatar tarbiyyar mahaifiyarsu ma tana taka rawar gani wajen samuwar tasu. Shiyyasa akace ka nemawa ƴaƴanka uwa ta gari, matama su nemawa ƴaƴansu uba na gari. Fatansa ALLAH ya raya masa su da baiwar ilimin addini tamkar mahaifiyarsu. Duk da shima zuwa yanzun Alhmdllh, ya sauke alkur'ani mai girma haryayi nisama a hadda. Yasan littatafai masu yawa na addini, bai kuma tsaya a hakaba yana cigaba da neman ilimi babu dare babu rana. Dolene ya kasance mai yawan ambaton Alhamdulillahi ala kulli halin a kowanne dakiƙa na rayuwarsa, suka kalli juna shida matarsa suna murmushi, hannu ya miƙa mata itama tazo ta haɗasu ta rungume cike da godiyar UBANGIJI mai rahama mai jinƙai.✍😭🤗👌🏼.

To nima bilyn ku dolene na kasance mai yawaita ambaton ALHAMDULILLAHI ALA LULLIHALIN a kowacce daƙiƙa ta rayuwata.

*_ALLAH na gode maka da dama daka bani da iko kammala wannan littafi, abinda na rubuta dai-dai ALLAH ya bamu ladar amfanuwa da shi da ikonsa. Wanda nayi kuskure ALLAH ya yafe mana ni da ku masu karantawa. Ina fatan zakuyi watsi da duk abinda bai kasance mai amfaniba sai dan ƙayatar da jin daɗin karatunku. Duk wanda na ɓatama rai a lokacin rubuta wannan littafi ya gafarceni. ALLAH ya haɗamu a gaba da alkairi😭🙏🏻🤗💋._*

*_ZAFAFA BIYAR na sake miƙa ɗumbin godiyarsu a gareku. Mun gode da ƙauna da kuka nuna mana, ALLAH ya bar zuminci ya cigaba da bamu ikon sauke haƙƙin junanmu. Muna fatan zaku sake kasancewa cikin shirin zuwan ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL insha ALLAH anan gaba kaɗan. Mun gode, mun gode, mun gode💋💋💋💋💋🤗🙏🏻😭_*

Harna fara kewarku silly guys😹😂🤣😫⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😭🙏🏻


*_Bilyn Abdull ce😉👌🏼_*




__________________
ZAFAFA BIYAR 2021
_______________________
   
                 
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
      (Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
   
          Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗

        Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗

        Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗

         Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋

    Duka akan farashi mai rahusar gaske.

Kamar haka👇🏻💃🏻

Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  09033181070

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM----ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.


No comments