SAKAYYAH Book 3 PAGE 4

 


                     By

*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH Book 3 PAGE 4*



                    NA

*Aysha Aliyu Garkuwa*




Tallah !! Tallah !!


Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce  ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka ,  *Rai daya janzaki*.

Yau na sake dawowa domin Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a*  littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba  Hausawa sukace Gani yakori ji.


Karku Manta  *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa.

Ya zarce duk littafai na , na baya.

RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi bu?ata zaki biya kudin sa Naira ?ari biyar kacal.


Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal  

Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci.

Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank

Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku.



Ahankali ya sha?i ?amashin jikinta tare da kallon plate da cup dake gabanta wanda da alama akwai abinda taci kafin ta bin ba ba kwanta.

A dai-dai lokacin kuma Momy ta fito daga Kitchen idanunta suka sau?a akan Moddibo dake zaune a hannun kujeran Khausar na zaune gefensa ta manna kanta da kafa?arsa yayin da hannunsa ?aya ke bayanta yana shafawa ganin haka yasa Momy saurin komawa kitchen.


Ahankali Moddibo ya ?ago kansa tare da kallon ?ofar Falon jin sautin muryan da ko agigin bacci ya farka zai gane ta muryan Hajja Nana.

Khausar kuwa cikin yanayin baccin da take ji ta bu?e idanunta ta kalli Hajja Nana sai kuma ta maida idanunta kan Moddibo ahankali ta sake maida idanunta kan Hajja Nana tare da cewa.

“Da sassafen nan?Wannan wani irin sammako kika yi?”.

Cikin sauri Hajja Nana ta kallesu tare da fa?in.

“Toh ?ar nema wato karota ma kike yi?,Ni ina nan tunda kuka zo na gaza bacci ina ta begenki ina son ganin ki shiyasa ana fitowa masallaci nace wa Baffa Liman da Abba su kawoni amma shine kike cewa nayi sammako toh ai ba gidanki naje ba sai ki bari idan gidanki naje kiyi min iyaka da zuwa”.

Murmushi Moddibo yayi kana yace.

“Toh ki zauna mana kina tsaye”.

Kai ta gya?a tare da ?arasawa tsakiyar falon madadin ta zauna kan kushin sai ta zame ?asa ta zauna tare da kamo ?afafuwan Khausar ta fara jan yatsun sai kuma ta maida idanunta kan cikinta cikin mamaki ta ri?e ha?a tare da fa?in.

“Ohhh Allah mai iko, Allah mai kyauta da da?i”.

Sai kuma ta maida kallonta kan Moddibo.

Moddibo kuwa kansa ya ?an jujjuya kana ya juya ?wayar idanunsa sai kuma ya sanya hannunsa na dama ya shafa sajensa ya fahimci kallon cikin Khausar yasa take yi masa kallon irin sannu. Jarabebbe mayatacce har ka ?irka mata ciki? fahimtar hakan yasa ya kauda kansa.

Hajja Nana kam ganin yanda ya jujjuya idanunsa yasa ta jinjina kai tare da fa?in.

“Hmmm Allah Ubangiji ya shirye ka ke kuma Allah ya sau?eki lafiya”.

Cike da kunya Khausar ta sake manna kanta da kafa?an Moddibo kana ta motsa la??anta ta furta.

“Ameen”.

Cikin ?an ?aga sautin murya Moddibo yace.

“Amin Amin Ameen ya Allah, Allah ya amsa addu'ar ki mun gode da addu'a”.

Kallonsa tayi tana mamakin yanda zamani ya sauya sukam a zamaninsu ko kusa da makamancin wannan ba'a yi ga yadda ya wani ?wa?umeta a farkon surka.


Momy dake kitchen kuwa jiyo kaman muryan Hajja Nana yasa ta le?o.

Ganin tabbas Hajja Nana ce yasa cikin sauri ta fito tare da cewa.

“A'a Hajja Nana, dama naji kamar Muryar ki na dan kasa kunne ashe dai ke ?in ce”.

Murmushi Hajja Nana tayi kana tace.

“Wallahi fa tun randa mukayi waya kika cemin tazo nake ta son zuwa washe garin ranan kuma Mashin ?in Abba ya samu matsala shine malam Liman yace na bari sai yasa mai a mota kafin muzo, tunda zai zo ya marabci su Abualeey yanzu ma tare muke suna falo da Lami?o”.

Kai Momy ta gyada tare da fa?in.

“Kai Masha Allah sannun ku da zuwa.

Ahankali Moddibo ya juya da naiyyar gaisheta

Sai ya ga har ta shige kitchen Momy kuwa already ta gama ha?a breakfast Sultan Cheaps ta soya wanda yaji Vegetables da naman rago mai laushi sai kuma ?osai data soya wanda keta tururi wanda Khausar ce tace tana so sai kuma Koko wanda duk za?in Khausar ne sai kuma tea dake ?amshin Kanunfari, Citta Na'a'na'a ta fito dasu.

Anutse. Moddibo ya sunkuyar da kansa kana yace.

“Momy Barka da safiya".

Cike da kulawa tace.

“Barka dai Moddibo ka iso?”.

Kai ya gya?a tare da fa?in.

“Eh Momy ina kwana”.

“Lafiya lau Alhamdulillah ya gida”.

Kallonta ta mayar kan Khausar tace.

“Ki tashi ki samu ku abinci kuci”.

Juyawa Khausar tayi tare da kallon Momy kana tace.

“Momy kinyi min ?osan?”.

Kai Momy ta gya?a cike da tarin ?aunarta tace.

“Nayi miki mana ai dole na inyi miki”.

Hajja Nana dake cigaba da matsawa Khausar Kafa tayi dariya tare da fa?in.

“Aikam dole kiyi mata naga abin na musamman ne”.

Baki Khausar ta ?an tura tare da hararan Hajja Nana kana ta ?an janye jikinta daga na Moddibo wanda shi har ga Allah yama manta Momy na wajen jin ta ?an matsa ne yasa ya kalleta.

Ganin yana kallonta yasa ta juya mishi ido alamar yaga Momy na nan.

Fahimtar hakan yasa ya gyara zama sai kuma ya zame ya zauna akan tattausan Carpet ?in ya zamana suna fuskantar juna yayin da Hajja Nana ke gefensu.

Kulan farkon ta jawo ta bu?e idanunta suka sau?a akan ?osan dake zuba wani irin tururi da ?amshi ajiyar zuciya mai sanyi ta sau?e irin yanda duk wata mai ciki keji asanda ta samu abinda take so.

Flaks din dake gefe ta jawo ta bu?e sai taga tea.

Fuska ta kwa?e kamar za tayi kuka tace.

“Momy kunun fa?”.

Momy na ?o?arin janyo Flaks din gabanta tace.

“Gashi nan ki bu?e mana ki gani ke kina da ci da zuci”.

?an Murmushi tayi kana ta bu?e tare da cewa.

“Kai Momy Ubangiji Allah yabar min ke Allah ya miki Albarka Ubangiji ya miki sakayya da gidan Aljanna”.

Murmushi momy tayi tare da fa?in.

“Ameen ya Allah Mamana”.

Murmushi Hajja Nana dake gefe tayi kana ta kalli Khausar sai kuma ta kalli Momy ahankali tace.

“Ubangiji Allah ya rabaku lafiya”.

Cikin sanyi Khausar tace.

“Ameen”.

Moddibo kuwa fuskarsa ?auke da murmushi ya gyara zama tare da cewa.

“Ameen ya Allah aini ina ga yau tukuici na musamman zan banki tunda kika zo kike mana addu'a da fatan Alkhairi ”.

Baki Hajja Nana ta ta?e tare da cewa.

“Allah yasa dagaske kake”.

Cikin tabbatar wa yace.

“Dagaske nake mana ai ina ga ke tare zamu tafi dake kiyi ta mana addu'ar nan sannan kiyi ta kula mana da ita”.

?an zare idanu Hajja Nana tayi kana ta hararesa tace.

“Kunyi ?arya nikam bazan zama mai aikin kuba kuda gacan innare kuna tare da ita ai magana ta ?are duk kular da kuke bu?ata zaku samu”.

Kai ta jinjina kana tayi Murmushi tare da fa?in.

“Aikam itama munzo dasu jiya ma take cewa tana son zuwa wajen ki sai Khausar ke cewa ai kema zaki zo shiyasa bata jeba”.

?an gyara zama Hajja Nana tayi tare da fa?in.

“Aikam toh shikenan”.

Khausar kuwa ?osai ta zuba kusan guda goma kana ta zuba Kokan sai kuma ta zuba wa Moddibo Sultan Cheaps da Perpe Chicken mug ta ?auka ta ha?a masa tea mai kauri.


Hajja Nana ma ?osan Khausar ta zuba mata tana kallon ?osan da yayi kyau a ido ta kalli Momy tace.

“?osan ya isa haka, asamin shayi sai aha?a min da biredi”.

Kai Momy ta gya?a kana ta mi?e ta ?auko Bread Mai yanka-yanka Kar?a Hajja Nana tayi ta shiga ha?a breading, ?osai da tea tana sha.

Khausar kuwa ?osai da Kokon ta shiga sha cikin tsananin mararin abin.


Ahankali ta gutsiri ?osan da cikin tsakiyarsa ke ?auke da diddigin nama kana ta kuma kur?an kokon daya sha kayan ?amshi yawun bakinta sai tsinkewa yake saboda yanda ya mata masifar da?i.


Moddibo kam cike da mamaki yake kallon yanda Khausar ke cin ?osai da Koko tsakaninta da Allah.

Hajja Nana dake kai biredi da ?osai baki ta kalli Moddibo daya zubawa Khausar idanu yana cew.

“Ni mamaki nake bata cin abinci fa agida”.

Murmushi Hajja Nana tayi tana kallon yanda Khausar ke shan Koko tsakaninta da Allah tace.

“Ai dama haka wani yake in dai yana da ciki baici agidansa amma da zaran yaje unguwa zai ci abinci”.

Kansa ya girgiza tare da cewa.

“To ai can ko munje gidan Lalla Khadijah bata cin abinci amma kinga tunda muka zo nan cin abinci fa takeyi”.

Momy dake fita zata kaiwa Abba da Man Liman nasu tayi Murmushi tare da fa?in.

“Sosai ma kam tunda  aka zo nan abinci take ci babu kama hannun yaro taci ta ?ara ?ayan daren ma munyi  hira mun gama tace min yunwa take ji sai da naje na dama mata Quaker oats tasha kafin tayi bacci”.

Cike da farin Moddibo ke sakin murmushi yana kallon Khausar dake ?an Cunno baki gaba Momy kuwa idanunta akan Hajja Nana ta cigaba da cewa.

“Sannan da safe kafin ta kwanta plate da kuka zo kuka samu shima indomei taci tasha tea kafin ta kwanta tayi bacci anan gashi yanzu ma tana ta ?urawa”.

Langwa?ar da kai Khausar tayi tare da fa?in.

“Toh Momy yunwa nake ji na da?e bana cin abinci fa”.

Dariya Momy tayi kana tace.

“Keee dama haka kike da cin abinci nayi mamaki ma da akace wai ciki ya hanaki cin abinci.

 Don banyi tunanin akwai abinda zai hana ki cin abinci ba, tunda ke ciwo ma baya hana ki cin abinci”.

Kanta ta sunkuyar ?asa ta cigaba da cin ?osanta kallonta Moddibo yayi ganin ta gama cinye duk ?osan hannu tasa ta sake janyo kular ?an ware idanunsa yayi tare da fa?in.

“Minha bazai Miki yawa ba?”.

Kallonsa tayi sai kuma ta girgiza kai tace.

“Um-um ka?an zan ?ara naji cikina ya ?oshi amma bakina bai gaji dashi ba”.

Yana rufe kulan yace.

“Toh ki bari sai anjima”.

Marairaice fuska tayi ganin haka yasa Momy cewa.

“Ki bari na rage Miki ?ullu a fridge idan kina so anjima zan sake soya miki ”.

Gyatsa tayi kana ta gya?a kai tare da fa?in.

“Toh shikenan”.

Ta ida maganar tana jingina bayanta da jikin kujera.

Ahankali Moddibo ya matsa kusa da kujeran da take ya ?an jawota jikinsa tare da cewa.

 “Zo, Zo zonan kada ki kwanta, ki ?an zauna tukun mu samu abincin yabi jikinki”.

Ya fa?a yana manna kanta da kafa?arsa yayin da hannunsa ?aya ke kan cikinta yana shafawa shi kuma yana cigaba da cin abinci da hannunsa na dama.

Ahaka suka gama cin abinci suna ta?a hira jefi-jefi.


Suna gama cin abinci Momy ta shigo idanunta akan Khausar tace.

“Toh tashi ki tattare wurin”.

Kai ta gya?a tare da fa?in.

“Toh”.

Kana ta yun?ura zata mi?e.


Ahankali Moddibo ya kalli Momy kana yace.

“Momy bari na tattare”.

?an ware idanu Momy tayi kana tace.

“Ta isa tana zaune ka tattare mata kwanika”.

Cikin sanyi yace.

“Momy toh ta gaji ne kuma ta cika cikinta da yawa bata son motsi”.

Kai Momy ta girgiza tare da fa?in.

“Aikuwa dole tayi motsi maza tashi ki tattare su”.

Ta ?are maganar tana kallon Khausar.

Hajja Nana dake kallonsu ta ?an ta?e baki tace.

“Kai dai kai dai kam wannan akwai ka da tsirfa iri-iri yo in Mai ciki bata motsa jiki ba mai za tayi!? Ko kaine zakayi mata na?udar”.

?an hararan Hajja Nana Khausar tayi sai kuma ta kalli Momy tare da cewa.

“Nima fa bance yayi ba shi yace zaiyi”.

Ta ?arashe maganar tana kwashe kwanukan ta kai kitchen kana ta dawo ta zauna bayan ta dawo sun zauna Momy suka gaisa da Hajja Nana bayan sun gaisa suna cigaba da hira.

Asiya ta shigo cikin sassarfa kamar an jefota cikin yanayin tashin hankali tace.

“Momy dan Allah kizo kiga Ummana baki ?aya yau tunda gari ya waye atsaye take bata zauna ba kona minti ?aya fa gaba ?aya yau jikinta ya tashi!”.

Da damuwa Momy ta mi?e cikin sauri tabi bayan Asiya suka nufi Side ?in Hajiya Bunayya.

Khausar kam ahankali ta juya ta kalli Hajja Nana itama Hajja Nana kallonta tayi sai kuma ta juya ta kalli Moddibo cikin sanyi tace.

“Yah Mu'allim nace maka batun jikin Umma da Amina ayi musu addu'a sannan ka turo Dr Jameel yazo ya duba su amma Yah Mu'allim har yanzu baka ce komai akai ba”.

Ahankali Moddibo ya dafe kansa da hannunsa na hagu yace.

“Wallahi na manta, koyie ha?uri mantawa na keyi Minha”.

Kamar za tayi kuka tace.

“Yanzu fa kaji abinda Asiya tace”.


Hajja Nana da batasan meke faruwa ba ta kalli Khausar tare da cewa.

“Meke damunta?”.

Cikin rauni Khausar tayi ?asa da kanta kana ta kwashe labarin duk yanda ta fa?awa Moddibo ta fa?awa Hajja Nana.


Ajiyar zuciya Hajja Nana ta sau?e tare da jinjina kanta tace.

“Ai dama haka duniya take idan kace tukunyar wani bazai tafasa ba naka ko ?umi bazai yiba arayuwa ka taka ahankali kada ka shiga hurumin da bana kaba duk lokacin daka shiga hurumin da bana kaba sai ka samu abinda zai shiga huruminka”.

Araunane Khausar ta risinar da kanta Hajja Nana kuwa cikin jimami ta cigaba da fa?in.

“Ya hanaka zaune ya hana ka tsaye yanzu wa gari ya waya ita wancan ta haukace ?arta ta zama mai wari ita gata nan ?arta ta zama wata halitta daban gashi ita kuma yanzu ?arta tazo tana cewa tunda gari ya waye bata zauna ba ta isa ta zauna tsutsotsi na cinta”.

Ahankali Khausar ta rausayar da kanta hawaye na kwaranyowa daga idanunta tace.

“Hajja Nana Ni tausayi suke bani musamman Amina tana bani tausayi gaba ?aya sai kinga yanda ta dawo ita ma Umman na ban tausayi bata isa ta zauna bafa Hajja Nana wlh ko jiya data shigo nan mu gaisa tsutsotsin har bin ?afarta suke yi sai in taji kiga tana ta buge-bugen ?afart kamar itama so suke su haukatata gaba ?aya ”.

Cikin sau?e numfashi Hajja Nana ta gyara zama tare da cewa.

“Dama haka duniya take”.

Still idanunta na zubda hawaye ta kalli Moddibo tare da fa?in.

“Ni dai ina so a samar mata magani ayi mata addu'a ane ma mata sau?i awajen Allah”.


Acan Side ?in Hajiya Bunayya kuwa Momy na shiga ta sameta atsaye sai bubbuga ?afa take saboda yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke gefenta tana zazzaro harshenta waje.

Da sauri Momy ta ?arasa wajenta ta ri?e hannunta kana tace.

“Yaya ki zauna mana”.

Kai ta girgiza cikin tarin damuwa tace.

“Ina Momyn Khausar bazan iya zamaba idan na zauna ji nake har cikin hanjina tsutsotsin suke ci suna gigitani na rasa yanda zanyi na cutar dake arayuwa gashi nima yanzu na samu abinda yake cutar dani na rasa yanda zanyi a rayuwata”.

Cike da tarin tausayinta Momy ta girgiza kai tare da fa?in.

“Bakomai in sha Allah zaki samu lafiya”.

Kai ta girgiza tana cigaba da buga ?afarta kana tace.

“A'a nikam nasan na nemowa kaina abinda yafi ?arfina Momyn Khausar ki yafe min ki cewa Khausar ta yafe min”.

Cikin sauri momy ta juya tare da fa?in.

“Ki kwantar da hankalinki Yaya bari naje na kira Lami?o yazo ya kai ki asibiti ”.

Ta ida maganar tare da nufar Side ?in Lami?o.


Cikin ki?ima tace.

“Wallahi Lami?o Yaya ce babu lafiya gaba ?aya ta kasa zaune ta kasa tsaye ta ki?ime ta gigice ga Amina ma ita ma baki ?aya yau jikinta nata abin ya sake motsa wa”.

Anutse Lami?o ya juya ya kalleta kana yace.

“Hmmm shine baki ?aya kika gigice haka?, Mutanen dake suka cutar Sakayyah ce ta sau?a akan su shine zaki gigice haka?”.

Kai ta girgiza kana tace.

“Nikam basu cutar dani ba kuma koda sun cutar dani na yafe musu Duniya da lahira”.

Gyaran murya Man Liman yayi tare da cewa.

“Wayene ba lafiya?”.

Zama Momy tayi muryanta ?auke da damuwa tace.

“Uwar gidata ce babu lafiya Baffa Liman jinyan kuma ya ki?ima mu”.

Kai ya jinjina yace.

“Toh kunje asibiti ne?”.

Kai ta gya?a tare da cewa.

“Munje asibiti. Likitocin da kansu sunce bana asibitinba ne na gidane sai kaga yarinyar mijin da aka Aura mata ne bisa duk kan alamu tsafi yayi da ita ita kuma Yayan dai baza ka tantance ba”.

Zama Lami?o ya gyara kana yace.

“Ki daina cewa ba za'a tantance ba ki fito kice sihiri tayi Miki keda Khausar ya dawo kanta haka zaki fa?a masa ki fito fili ki fa?a masa abinda ta miki Saboda ko baki fa?a ba Allah ya sani kuma taga Sakayyar abinda ta aikata”.

Kai Momy ke girgiza masa shikam cikin tsanar Muguwar ?abi'ar Hajiya Bunayya ya cigaba da cewa.

“Ita kuma Amina dama ai ?ulle ?ulle sukayi Ni kaina tsoron Al'amarin Naseer nake yi suka nuna dole-dole sai Naseer ya auri Amina yaje yayi tsafi da ita ya dawo da ita me zance musu su suka jawa kansu jiki magayi.

Ai dama sai dana ce duk abinda ya faru babu Ni aciki ba hannuna bare ?afata aciki”. 

Cike da nutsuwa Man Liman ya kalli lami?o tare da fa?in.

“A'a Lami?o baza ayi haka ba ai ita rayuwa rai da lafiya ita ake bibiya ake duban Lamarinsu kuma komai lalacewan Amina jinin kace tsatsonka ce kana Hajiya Bunayya komai lalacewan ta Matarka ce Uwar ?a?an kace”.

Da sauri ya girgiza kai yace.

“Uwar ?a?ana ne babu yanda na iya amma Ni na saketa na saki Hajiya Bunayya tun wata ?aya daya wuce Ni yanzu babu ala?a tsakanina da ita na barta dai ta sauna a gida nane albarkacin Asiya da Sulaiman, taje can rayuwarta da ban rayuwata da ban”.

Mommy kam kallonsa take cike da matsanancin mamaki jin cewa ya saki Hajiya Bunayya ko ka?an batayi farin cikin jin haka ba sai ma damuwarta ?aya karu.


Man Liman kuwa cike da nutsuwa yace.

“Ai baza ayi haka ba yanzu idan babu matsala kayi min jagora muje in gansu Babu abinda yafi ?arfin Ubangiji zanyi musu abinda Allah Ubangiji ya sanar dani”.

Kai Lami?o ya girgiza kana yace.

“Baffa Liman ka barsu baka san su bane”

Cikin rauni Momy ta kallesa kana tace.

“Dan Allah Lami?o kayi ha?uri ka taushi zuciyarka”.

Ahankali Lami?o ya ?ago ya kalleta kana ta girgiza kai ganin yanda ta tashi hankalinta yace.

“Kina jifa da bakinta tace ita tayi sihiri ta kashe Ramadan ”.

Cikin sauri Momy tace.

“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un yanzu kai Lami?o sai ka yarda ita tayi sihiri ta kashe Ramadan?”.

Kai ya gya?a tare da fa?in.

“Ehem ita ta fa?a da bakinta ai ”.

Cikin sau?e numfashi ta kalli Man Liman ta kalli Lami?o tace.

“Amma ka manta tun lokacin da Ramadan yayi accident an gaya mana cewa yana da brein Cancer tun lokacin daya karye ka manta cewa Likita ya fa?a mana kuma ko kai kanka kasan cewa ciwon kan da Ramadan yayi dare ?ayane sannan kuma an tabbatar mana da cewa ciwon ne ya kashe sa”.

Kai Abba dake gefe ya jinjina Momy kuwa cikin rauni ta cigaba da fa?in.

“Ko Sihiri da tace tayi Ni banyi Imani Sihirinta da tayi shi ya kashe min ?ana ba imma shine ya kashesa tsakaninta da Ubangijinta kuma ko cikina da take cewa ita tayi sihiri ya zube wallahi bata isa tayi Sihiri cikina ya zube ba face dama Allah ya ?adarta wa?anan cikin bazan haifesu su taka doron ?asa ba,  shine ka?ai amma Ni bata isa ta kashe min ?a ba bata isa zubar min da ciki ba wa'adin sa ne yayi”.

Cikin sanyi ta ?are maganar tana mai zubda hawaye ta cigaba da cewa.

“Kuma ai ita in tayi zalunci mu bai kamata mu saka mata da zaluncin ba sai mu barta da Allah shi yasa Sakayyar da zaiyi mana”.

Jikin Lami?o ne yayi sanyi jin abinda ta fa?a sai kuma ya kalli Man Liman dake cewa.

“Kayi ha?uri muje mu dubata”.

Ahankali Yah Abba ya gyara zamansa tare dasa baki acikin tattaunawar su yace.

“Ayyah Lami?o ayi ha?uri adubasu ai rai da lafiya ake dubawa”.

Kai ya gyada tare da cewa.

“Shikenan”.

Momy ce ta fara mi?ewa ta fita Lami?o na biye da ita sai kuma Man Liman da Yah Abba Abaya.


Suna shiga falon Hajiya Bunayya suka sameta atsaye sai bubbuga ?afanta take tana tsalle ga ?an mili-milin tsutsotsin nan na bin ?afafunta yayin da Amina ke kwance kan 3sitter  tana karkata kanta tare da zaro harshenta Man Liman na ganinta yace.

“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”.

Juyawa yayi ya kalli Hajiya Bunayya kana ya kalli Amina sai kuma ya sake juyawa ya kalli Momy tare da fa?in.

“Momyn Khausar akwai Zam-zam?”.

Kai ta gya?a tace.

“Eh akwai”.

Ajiyar zuciya ya sau?e tare da fa?in.

“Toh ki temako min dashi”.

Da sauri tace.

“Toh”.

Kana cikin hanzari taje ta dauko Zam-zam Babban gora ta kawo kar?a yayi kana yace.

“Allah yasa kuna da ganyen Magarya ko ?anye ko bushesh-she amma idan akwai ?anye anfi bu?atar shi”.

Ajiyar zuciya Momy ta sauke kana tace.

“Alhamdulillah akwai ?anye abayan window na adan kwai bishiyarsa”.

Cikin sauke numfashi yace.

“Toh Alhamdulillah aje atsinko akawo min”.

Cikin sauri ta juya taje ta tsinko ganyen Magarya ta kawo masa tana kawowa ya kar?a kallon Asiya dake kuka yayi kana yace.

“Asiya idan akwai sabon roba mai haske ki kawo min”.

Cikin sauri tace.

“Toh”.

Kana ta shiga kitchen ta ?auko roba mai ?an girma kar?a yayi yasa rabin Zam-zam ?in aciki zama yayi ya Tofa Ayatul Shifaa gaba ?aya aciki idan ya gama tofawa yasa ganyen Magarya guda bakwai aciki kallon Asiya yayi yace ta kawo masa karamin kofi cikin minti ?aya ta kawo kofin ruwan addu'ar ya ?ebo ya bawa Amina yace.

“Kar?i kishi”.

Akarkace Amina ta mi?e tare da kauda kai gefe.

Cikin tausasa murya ya sake cewa.

“Kar?i kisha”.

Still juyawa tayi alamar bazata shaba.


Kallon Lami?o Man Liman yayi tare da cewa.

”A danneta Abata tasha”.

Cikin takaici Lami?o ya girgiza kai kana yace.

“Ta kar?a tasha sai adanneta ai jiki magayi lafiyarta ne ko lafiyanmu”.

Man Liman na gyara alkyabbarsa yace.

“Ayi ha?uri Abata ai sihirin da aka yi mata ne an ha?a mai tafiya da siffar maciji bayin kanta bane bazata sha ?inba”.

Cikin rauni Asiya ta kalli Lami?o tace.

“Ayyah Abba don Allah Abata ”.

Ta ?are maganar tare da karban kofin ta matsa kusa da Amina.

Amina na ?o?arin ture kofin Lami?o yayi saurin kama hannayenta kana ya rike kanta Asiya ta ?ura mata ruwan Tofi da ganyen Magaryan tasha mai ?an yawa amma sauran ya zube.

Ahankali ta fara yin gyatsa lokaci ?aya jikinta ya saki ta koma ta kwanta kan kujeran atake bacci ya ?auke ta.


Tana yin Bacci Man Liman ya sau?e ajiyar zuciya yace.

“Alhamdulillah tunda har tayi bacci in Allah yaso ya yarda zata rabu da abinda ke tare da ita amma wannan yaron da kuka Aura mata ya cika ta?adirin Jahili makirin mutum mushirki”.

Kai Lami?o ya girgiza tare kana yace.

“Su suka siyawa kansu”.

Cikin kuka da nadama Hajiya Bunayya ta dur?usa gaban Man Liman tace.

“Dan Allah nima ataimaka min mana abani abinda zansha inji sau?i atemaka min”.

Kai Man Liman ya gyada yace.

“Ba matsala in Sha Allahu”.

Sai Kuma ya tsiyayi ruwan Zam-zam daban akofi yasa ganyen Magarya aciki yayi mata Tofi kana ya bata yace ta taune ganyen Magarya Zam-zam ?in shi kai ta gya?a kana tayi kamar yanda yace tana gama yi taji kamar fitsari take ji cikin sauri ta nufi bedroom ?in ta ta wuce Bathroom.


Man Liman kuwa kallon Asiya yayi tare da cewa.

“Idan ta farka wannan ruwan daya rage ta samu tayi wanka dashi awajen da babu najasa”.

Kai Asiya ta gya?a tare da fa?in.

“Toh In Sha Allahu”.

Yana kallon Aminan dake bacci yace.

“Kuma in sha Allah akwai tofin da zan mata amma da Zam-zam ?in ne sai dai zai ?auke Ni tsawon kwana biyu in sha Allah idan anyi shi in zamu zo daurin Auren su Jameelu zamu zo dashi da izinin Ubangiji zata samu sauki”.

Kai Asiya ta gya?a kafin cikin sanyi tace 

“Umman mufa?”.

?an gyara tsayuwar sa yayi kana yace.

“Toh bamu san mai Ubangiji zaiyi ba amma itama in sha Allah muna kyautata zaton Allah zai bata lafiya”.

Cikin sanyi da ?an jin nutsuwa tace.

“Allah yasa mun gode”.

Nan Lami?o da Man Liman da Yah Abba suka fita.

Momy kuwa cikin jin sassauci tace.

“Alhamdulillah Amina ta samu sauki”.

Kai Asiya ta gya?a.

Momy kuwa ganin Hajiya Bunayya ta tafi daki yasa tayi zaton sauki ta samu tana kallon Asiya tace.

“Barin tafi ina da ba?i kinsan Hajja Nana nacan” 

Cikin ?aunarta da sake jinjina kyawun halinta Asiya tace.

“Toh Mun gode”.

Lami?o Man Liman da Yah Abba kuwa Side ?in Lami?o suka koma...


Momy na shiga falon Moddibo ya mike kana yace.

“Toh Momy Ni zan wuce”.

Kai ta gya?a tare da cewa.

“Toh mun gode”.

Khausar kuwa cikin sanyi ta kallesa kana tace.

“Dan Allah Yah Mu'allim kada ka manta Dr Jameel yazo ya duba Umma”.

Kai ya gya?a kana yace.

“In sha Allahu bazan manta ba Minha baza ki rakani bane”.

Kanta ta langwa?ar tare da ?yafta ?wayar idanunta ciki nasa sai kuma ta daura hannunta na dama kan ?afarta tace.

“Ayyah kayi ha?uri baki ?aya ?afafuna rawa suke”.

Lallausan murmushi ya sakar mata tare da motsa la??ansa cikin ?asa da murya yanda ita ka?ai zata ji yace.

“Toh sai nazo da daddare”.

Kallonsa tayi da sauri tace.

“Me kuma za kazo yi da daddare?”.

Yana ?an lumshe Idanunsa cikin nata yace.

“Bakyaso in kawo Dr Jameel ?in ne?”.

Ahankali tace.

“Ina so mana”.

Kai ya gya?a yana gyara tsayuwar sa yace.

“Toh idan nazo kuma ki shirya zamu tafi tare”.

Langwa?ar da kai tayi tare da fa?in.

“Ayyah Yah Mu'allim ka barni in kwana mana”.

Kai ya girgiza tare da fa?in.

“Bazan iya ba dole fa yau zamu tafi muje mu kwana tare”.

Sake langwa?ar da kai tayi tare da marairaice fuska tace.

“Dan Allah Yah Mu'allim ”.

Cikin sauri ya ?an tsuke fuska yace.

“Kada ma ki ha?ani da Allah ki cuceni”.

Shiru tayi ganin kallon da Momy ke mata me nuni da alamun garga?i.

Shi kuwa Modibbo Hajja Nana ya kalla jin tana cewa.

“Idan Allah ya kaimu gobe ko jibi in ba matsala zamu tafi jahar Gombe muje kaga asalin masarautar su Khausar kuna mahaifarta”.

Cikin murmushi Khausar tace.

“Gobe dai zaifi dan Allah Yan Mu'allim kace gobe”.

Kai ya jinjina cike da jin yana son yaje yaga Masarautar su yace.

“Allah ya kaimu goben in ya samu in kuma bai samuba sai jibi, za dai muje kafin ayi bikin”.

Amin suka amsa kana shi kuma ya juya fita.


Yana isa gida kai tsaye Side ?in su Dr Jameel ya shiga nan yasa masu suna ta maganar abinda za'a yi kasancewar yau  saura kwana hu?u ne ?aurin Auren kasancewar yau ya kasance Litinin.

Talata Laraba Alhamis juma'a za'a ?aura Auren.

Nan dai suka cigaba da hiransu.


Acan gidansu Asma'u ma shirye shiryen biki ya kankama.


Alhamdulillah washe gare suka tafi Gombe.

Harda Dr Jameel da Lallai Khadijah da Rahma harda Didi da Innayi da Galadima suka je dan ya gabatar da masarautar su.

Kwana su biyu suka dawo Gembilan.


Alhamdulillah zuwa yanzu Amina ta fara samun sauyi dan yanzu ta daina zare harshenta.


Hajia Bunayya kuwa abu kam sai gaba gaba.

Samira Sani kuwa jin Amina ta samu sau?ine da yadda akayi yasa itama ta zo ta kokawa Momyn kuma Alhamdulillah yau dasuka dawo daga Gombe.

Man Liman yayi mata tofi, ya bata ya bawa Amina.


Alhamdulillah cikin ku?irar Ubangiji kafin zuwa la'asar Samira ta fahimci zuban ruwan nan ya ragu sosai.

Amina kuwa sosai itama mummur?ewa da jikinta keyi ya fara raguwa.


Nan ya sake yi musu tofi cikin zam-zam ?in na wasu ke?antattun ayoyi da sauri kamar haka.

*Al-araf ayata 117, 118, 119, 120, 121 da kuma  122.  Sai Suratul Yunus daga ayata 79, 80, 81, 82, Sai kuma suratul Ta-ha aya ta 65 66, 67, 68, 69, 70, Sai kuma suratul al-Kafurune gaba ?ayanta, da kuma suratul al-ikhlas dukanta sai suratul al-falaq itama dua da kuma suratul An-nas itama dukanta  da forko zaki samu zam-zam ki zuba mai yawa a tsabtacecen mazubi ko roba ko kwarya, ki tabbatar zam-zam ?in zai ishe ki sha da kuma yin wanka, sai zuba a robar kana kisa kanyen magariyar guda bakwai an fison ?anye Amman busheshenma ba matsala zaki daka guda bakwai in ?anyen nema ki daka bakwai, sai ki zuba a Zam-zam ?in kana ki karanta ayoyin Alkur'ani mai tsarkin dana lissafa Miki da surorin ki ?an motsashi zakiga ya ?an buga kumfa sai ki ?iba a cup wanda zakisha ki ?oshi kuyi gyatsa, sai ki zauna bisa ya?ini da niyar Allah ya yaye Miki matsalarki ko wacce iri yace Sihiri, ko tsafi, Sammu, ko kambun baka, ko cutar da ba'a gane kantaba ko sharrin iska. Kisha koyi hamdala kana ki ?auki sauran na cikin robar ki samu sarkakekken wurin da babu najasa kiyi niya da duk matsalarki kiyi wanka. Wlh da izinin Ubangiji zakiji sau?i ki samu sauyi anaso na farko dai kiyishi da Zam-zam inda hali duk bayan wata shida ko shekara ?aya kiyi kiyiwa yaranki da mijinki dan makarine mai girma in ba hali saboda tsadar da Zam-zam keyi in kinyi na forkon da Zam-zam to na biyu kiyi da ruwan sama na uku da duk ruwan da ya sauwa?a gareki, inda hali ko yaushe da Zam-zam in ba hali ayi na forkon da Zam-zam in bai samuba ayi da ruwan sama na ro?on da na biyun da na ukun, kiyishi ma?o ma?o ko wata wata ana dai son duk bayan wata shida ko shekara ?aya kiyi, yar uwa ko ?anki, ?arki mijinki ?anwarki ?a?an yar uwa ki ko ?an uwa duk inda kukaga yaro ko yarinya sun cika rashin ji gagara rawan kai gardama da alamun kwaucewa hanya kuyi masu yanada matu?ar fa'ida da falala, sadakace fisabilillahi idan kinji da?inshi kiyi niya kiyiwa Mahaifiyata Fatima Dedde na ?u'huwa ?afa uku da fatan Allah ya ji?anta ya kai haske da ni'ima Qabarinta. Ni kuma inada wata bu?ata mai girma da falala da daraja a wurin Allah kuyi min addu'a kisa yaranki suyi min addu'a kice su ro?awa Aysha Aliyu Muhammad Garkuwa Allah ya biya mata bu?atarta akan alkhairi, ya raya mata ?a?anta Muhammad Jabeer da Maimuna Ikhram da Ibraahim ya shirye su ya basu ilimi mai amfani da albarka yasa su zama abin alfahari ga Musulunci da Musulmai mazan ya basu mata na gari da zuraya ?aiyi ba, macen ya bata miji na gari da zuri'a ?aiyiba, kana Allah ya bani wasu ?a?an masu albarka da nisan kwana tagwaye inyiwa Deddena takwara da Babana in samu Aliyu Haiydar da Fatima Khausar in samu auta A'isha takwarar kakata mafi soyuwa*


Man Lima  da Hajja Nana ma bayan sunyi sallar la'asar da Baffa Liman da Yah Abba suka kama hanyar komawa Jauro Yaya.


Acan ?angaren Hajiya Bunayya ma tunda tasha wannan ruwan tofin sai tsutsotsin suka yawaita fita yayin da suke cinta da gasken gaske sai dai tana shiga ruwan ?umi zai lafa amma bazai wuce awa biyu zuwa uku ba zai sake dawowa haka tayi wannan yinin ranan zunibi da sakayyan aikinta na bibiyarta.


Daddare bayan sallar Isha'i Moddibo ne da Dr Jameel zaune afalon Hajiya Bunayya tana zaune Sai murtsukuku take yi akan kujeran jin yanda tsutsotsin ke cinta yayin da Amina ke zaune gefenta bisa duk kan alamu Alhamdulillah ta fara samun sau?i har nishinma duk ta daina .

Anutse Dr Jameel ya kalli Hajiya Bunayya kana yace.

“Akwai tests ?in da za'a Miki.

Sai kiyi ?o?ari kije asibitu aduba ki acan”.

Cikin sanyi tace .

“Nagode Nagode Dr Jameel Allah ya saka da Alkhairi ”.

Kai ya gya?a tare da cewa.

“Bakomai”.

Kana suka mi?e suka fita dai-dai  lokacin kuma Dr Zakariyya da Asiya ne zaune amota suna hira fitowa su Dr Jameel ne yasa Asiya yiwa Dr Zakariyya sallama ta fita kana Dr Jameel ya shiga Motar.


Moddibo kuwa bayan Khausar dake shiga Side ?in Momy ya nufa yana shiga falon yaga ba kowa sai Raudat dake kallon Catoon yace.

“Raudy ina Addah Khausy?”.

Hankalinta na kan kallon tace.

“Tana ?akinta”.

Kai ya gya?a tare da cewa.

“Momy fa?”.

Still idanunta na kan tv tace.

“Tana gidan Ummin Jameel Yah Haiydar ya kaita”.

Kai ya gya?a kana ya shiga ?akin Khausar zaune ya sameta agaban Weldrop ?in ta gabanta littafaine tana ta duddubawa.

Da mamaki ta kallesa kana tace.

“Yah Mu'allim har nan kuma?”.

Kai ya gya?a kana yace.

“Eh ai gidan mune”.

Kai ta gya?a hannunta na kan littafin tace.

“Eh nasani ai yanzu in Momy tazo ta same mufa?”.

Murmushi yayi tare da shafa sajensa kana yace.

“Eh dai-dai kenan idan Momy tazo ta ganni zata san ina bu?atar matata zata kora min ke mu tafi tun da ke yanzu kin iya gardama da taurin kai ”.


Kanta ta langwa?ar tare da cewa.

“Ayyah Yah Mu'allim ba gardama da taurin kai bane kaga idan mun koma kafin na sake ganin Momy fa zai da?e ”.

Yana gyara zamansa gefenta yace.

“Amma Ni bakya jin tausayina tunda muka zo fa kike bari na ina rayuwa Ni kadai kamar Maraya Babu kowa  kusa dani”.

Kallonsa tayi tace.

“Yah Mu'allim aima mun kusa komawa dai kayi ha?uri kwana nawa ya rage”.

Ta ?are maganar tana cigaba da dudduba littattafan sai kuma ta ajiyesu ta gefensa kallon yanda ta hargitsa Littattafan yayi kana yace.

“Me kike nema?”.

Tana cigaba da abinda take tace.

“Wani littafi na nake nema?”.

Da mamaki yace.

“Littafi kuma?”.

Kai ta gya?a tare da cewa.

“Eh”.

Kamar mai ra?a ya sake matsawa kusa da ita yace.

“Toh me zakiyi dashi?”.

Kanta na kan tulin littattafan tace.

“Wani abu ne aciki?".

Da mamaki yace.

“Wani abu ne kuma aciki?,ki bari gobe sai ki duba”.

Kai ta girgiza tare da fa?in.

“Ina so ne in tabbatar yana nan ko baya nan saboda da nazo na samu Raudat tana wasa takarduna da jakar makarantana ta bubbu?e min ban sani ba ko ta jefar min da littafin ”.

Cikin mamakin yanda take neman littafin yace 

“Toh littafin na wani Subjects ne?”.

Tana ?an tura baki tace.

“Um-um fa littafin bana karatu bane?”.

Yana ?an ?ara matsota yace.

“Ikon Allah toh littafin na menene?”.

Ya ?are maganar yana dudduba littattafan data tutturo gefensa yayin da take sake zaro na cikin jakar ganin basu cikine yasa ta jawo durowan ?asan Weldrop ?in tare da cewa.

”Toh ban sani ba bari in duba ko suna cikin nan ne”.

Dai-dai lokacin yaga wani note Book An rubuta *SPECIAL MAN* da manyan ba?i Aransa ya maimaita Special Man ahankali ya jawo littafin yana ?an jujjuyawa Khausar kuwa baki ?aya hankalin ta na cikin durowan Weldrop ?in.

Ahankali ya bu?e shafin farko na littafin.

ga mamakinsa sai yaga Drawing ?in hoton fuskarsa ne rau?au ba abinda aka bari har sajensa.

Cikin tarin wani irin mamaki al,ajabi da kuma ka?uwa ya kalli gefen shafin.

A gefen kuwa Drawing ?in fuskarsa ne acikin aji hannunsa na kan Black board kamar yana rubutu cikin sauri ya kalli rubutun da akayi da kalo wanda akayi musu design yanda ya kasance na musamman haka sunansa ya kasance na Musamman _Aliyu Youseef Mohammed Mouley (Moddibo)_

 da mamaki ya kalli inda aka rubuta sunansa anyi zanen ?? sai kuma ya maida idanunsa inda akayi Drawing ?in fuskarsa yaga date and time ?in da akayi rubutun Drawings ?in.

Idanunsa ya jujjuya ya kalleta amma baki ?aya hankalinta na kan tarin himilin sauran littafan.

Kallonsa ya mayar kan date ?in idan har baiyi kuskure ba toh shekaru hu?u kenan ranan dasu Khausar suka fara zuwa SS3 cikin mamaki da wani irin yanayi ya bu?e page ?in gaba sai yaga Drawing ?in Fuskarsa ne amma ba'a fitar da fuskan sosai ba sai sajensa a?asan ta rubuta.

_One's if I remember your face, my actionable will be change to cool,  is your Breed brightly my heart always yo be sunshine , i really love you with deep voice. Uncle Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_

Ahankali ya motsa la??ansa ya furta.

“Ya salam”.

Wani irin amintaccen numfashi ya fesar saboda jin kalaman suna Barka duk kan lakar jikinsa.

Fahimtar da yayi baki ?aya littafin kamar akansa yake magana haka nan yaji wani abu yana sau?a tun daga ?wa?walwar kansa har zuwa babban yatsarsa a iya shafi biyu daya bu?e ya fuskanci gaba ?aya Khausar ta rayune da soyayyar shi acikin zuciyarta shi kansa baisan meyesa ba ya dai tsinci kansa da na?e takardan yasa cikin aljihunsa.

 tare juyawa yayi mata wani amintaccen rugguma yana mai kallonta yace.

“Wai wani littafi kike nema ne?”

Batare data kallesa ba tace.

“Wani Littafina ne na musamman, nasan da wuya in Raudat bata ?atar min da shiba dan haka ta?atar min da ?an uwanshi da Nai ta rubutawa tun daga JSS one to 3”.

Kai ya gya?a kana yace.

“Ko dai Diary kine?”.

Kai ta gya?a kana tace.

“Kusan haka amma shi babban littafine ai yama fi Diary daraja awajena”.

Gira daya ya dage tare da fa?in.

“Toh tashi mu tafi da safe sai muzo na tayaki dubawa”.

Kai ta langwa?ar kana tace.

“Allah ina so ba mamaki yanzu Raudat ta ?atar min dashi. In dai ta baddashi wlh sai na daketa dan yana tunamin abubuwa da yawa a rayuwata”.

Kai ya girgiza tare da fa?in.

“In sha Allah ma bai ?ata ba kada ki damu kizo mu tafi da safe za'a zo mu duba”.

Ya ?are maganar da ?aguwar so yake ya ga su ?e?e daga shi sai ita.

Kai ta girgiza tana cigaba da hautsina littattafan tace.

“Um-um.ni dai ina son gani ”.

Fuska ya tsuke tare da cewa.

“Mu tafi nace ko?”.

Ganin yanda ya tsuke fuska yasa ta gya?a kai tare da fa?in.

“Toh”.

Kana tattare littafan ta mayar cikin drawer.

Hannunta ya jawo ya ri?e kana ya kalli gyalen jikinta ganin babu laifi yasa yace.

“Mu tafi toh”.

Suna fita motarsu Dr Jameel na fita agidan motarsu suka shiga kana suka tafi gida.


Suna shiga Falonsu ya rufe ?ofan kana ya ?alle botir ?in wuyan rigarsa ya zare ya ajiye kana ya jawota jikinsa ya rungumeta ajikinsa cikin sanyi ya kai bakinsa saitin kunnenta kana ya shiga ra?a mata abinda ta rubuta yana cewa.

“ _One's if I remember your face, my actionable will be change to cool,  is your Breed brightly my heart always you be sunshine , i really love you with deep voice Aliyu Youssef Mouldy (Modibbo)_”

Cikin sauri ta ?aga ido ta kallesa tare da wani irin fiddo idanun duka tamkar zasu fa?o ?asa, ido ?aya ya kashe mata kana yace.

“Tukuocin soyayyar da kike min nake son baki a daren yau”.

Baki ta tura tare da kwa?e fuska kana tace.

“Waye ?in?”.

Ido ya kashe mata tare da cewa.

“Ke?in mana”.

?an ware idanunta tayi akansa kana tace.

“Kamarya tukuicin soyayyar da nake maka kuma?”.

Ta ?are maganar cikin kunya da son waskewa.

Cikin wani irin yanayi yace.

“Shekara nawa kika yi kina dakon soyayyata azuciyarki?”.

Kallonsa tayi da mamaki sai kuma ta lumshe Idanunta tace.

“Kamarya kuma nayi dakon soyayyar ka azuciyata?”.

Murmushi yayi tare da cewa.

“Littafin da kike nema yana hannuna fa?”

Still kallonsa tayi tace.

“Wani littafi kuma?”.

?an murmushi yayi kana ya hura mata sanyayyar iskan bakinsa yace.

“Littafinki da kike nema”.

Littafin ya zaro acikin rigarsa ya nuna mata cikin mamaki ta kallesa kafin tace.

“Yaushe ka ganshi?”.

Dariya yayi tare da cewa.

“Tun ?azu har na karanta shi ma”.

Da sauri ta kife kanta akan ?irjinsa cike da kunya murmushi yayi kana ya shiga tura yatsunsa ?asan ?afarta jin haka yasa ta ?aura ?afanta kan rumfar ?afansa.

 A hankali ya fara tafiya da ita har suka isa bedroom.

Cikin sanyi ya kwantar da ita akan gado.

Kana yayi kissing ?in goshinta da lips ?in ta ahankali ya fara cire mata rigarta cikin wata kasalalliyar murya yace.

“Khausar da shin da gaske kina min soyayyar da baza ki iya furta min ita abaki ba Khausar?Meyesa baza ki fa?a min ba inji sanyi raina sai kiyita dakon soyayyata tsawon shekaru meyesa baki fa?a min ba meyesa baki nuna min ba? Da gaske kece kika rubuta littafin nan”.

Ahankali taja numfashi mai tsawo hannunta na cikin sumar kansa tana shafawa kana manyan yatsunta guda biyu na kan sajensa tace.

“Ni ba ni na rubuta ba.

Haka kawai ka'ida basona kake ba kalen ince ina sonka ka kashe ni?”.

Cikin sau?e numfashi ya gyara ta ajikinsa tare da cewa.

“Wayace miki bana sonki? Minha”.

Idanunta ta lumshe zuciyarta na bugawa tace.

“Nasan baka soma kuma nima ba nice na rubutaba”.

Yana shafa sumar kanta yace.

“To amma tunda ke kina sona ai da kin fa?a min munyi ta cutar da juna tsawon lokaci?,bamu sani ba”.

Muryan cike da sanyi ta ?an cije  gefen bakinta tace.

”Ni dai bance ina son wanda baisona”.

Saurin girgiza mata kai yayi tare da fa?in.

“Ki daina cewa bana sonki Minha”.

Sai kuma ya shiga romance ?in ta yana shafa saman Breast ?in ya cigaba da cewa.

“Kinsan dalilin zamana a?asan nan kuwa?

Na?i na koma Jami'atul Madina nayi aikin dana samune saboda ke tun lokacin dana fara sauke idanuna akan ki Allah ya jarabceni da sonki na soki alokacin da bakisan kanki ba Minha”.

Da wani irin sauri mai nuni da zallan farin ciki Khausar ta tallofo kansa tana kissing ?in dogon hancinsa cikin kasala da shau?i kana da yanayin da yake ji yaci gaba da cewa. 

“Sanadinki na zauna anan nasoki soyayyar da bazan iya yiwa kaina ba duk Drawing da kike yi na ki wasa ne ni duk wani motsin da kikayi a duniya idan na dawo sai nayi Drawing ?in sa na ajiye babu abinda yake sani farin cikin gani a duniya kamar fure da kuma ke saboda furanni kansu kin fisu kyau sai dai suna ?ebi min kyewar rashin ganinki ne, kana suna cike min gurbin kallonki”.

Cikin mamaki Khausar ta ?ago ta kallesa ido cikin ido tace.

“Yah Mu'allim kenan kana sona da gaske?”.

Kai ya jinjina tare da fa?in.

“Minha ina sonki son da bansan adadinsa ba nayi Miki son da ba yiwa kowacce ?a mace irinsa a duniya ba”.

Sai kuma ya mi?e da sauri, ya bu?e durowar dake jikin gadonshi, wasu manyan takardu masu kana da kalandu ya ja, a kan kadon ya zubasu.

Da sauri ta zubawa na forkon idanu.

Sai kuma ta kalleshi domin ta tuno yanayin da suka kasance a cikin mota a ranar daya rage mata hanya.

Da sauri yaja mata na ?asashi.

Wani irin murmushin ne ya subce mata ganin zanenta tana rawa a gaban motarsu ranar da suka ha?u gidan Ummi.

Baki ta turo ganin na ?asanshi ranar da take kakka?e ?an kwali ne sai kuma wani da bazata manceba na ranar data fara ganinshine da ta tsaya tana kallonshi harda karkata wuya ranar da ta fara zuwa JSS one kenan sai kuma wanda ta di?o kan bishiyar ranar da suka zo da Asma'u sai wanda suka ha?u a rugar Jauro yaya.

Ya Salam sai kuma wasu wanda bisa alamun nashine da Yah Jameel.

Kawai sai ta fa?a jikinsa.

Ture takardun yayi tare da ruggumeta da kyau.


Kanta ta kwanta ajikinsa tana jin yanda hannunsa ke yawo a sassan jikinta tace.

“Amma kuma Yah Mu'allim kullum dukana kake yi ya za'a yi na yarda dagaske cewa kana sona”.

Yana sakin ajiyar zuciya yace.

“Dole ne yasa nake Miki wannan yanayin saboda na fahimci kamar J yana sonki so kuma irin na aure”.

Saurin kallonsa tayi ya jinjina mata kai yana cigaba da cewa.

“A duniya ban ta?a son abu J ya?i shiba.

Kana J bai ta?a son abu na?i shiba sai nazo na fahimci akan mace ma zamuyi tarayya akan soyayya kuma hakan zai zame mana masufa a amintakarmun shiyasa nasawa raina hantarar ki da nisantarki da ?in kasancewa kusa dake saboda in yakice ki azuciyata J ya mallake ki dan nayi alkawarin mace bata isa ta shiga tsakanin amintakarmu ba”.

Idanunta ta lumshe tana jin wani irin ?aunarsa na huda duk wani magudanan jinin jikinta ahankali ya cigaba da cewa.

“Abinda J ya fa?a min kenan a voice ?in sa na ?arshe yace min ya fahimci ina sonki yamin voice da ace alokacin yana raye zance J ai kaima kana sonta amma tun a voice ?in yace min kana tunanin kamar ina son Khausar ko? Shiyasa kake hantararta dan ka yakiceta a zuciyarka.

Wai sabida zaka bar min ita ko?.

To ni ba sonta nake ina taya ka son abinda kake sone A.J ka Aureta dan naga zanenta da kayi a takardu, in su ka ?oyesu shin zaka ita ?oye na zuciyarta da ?wa?walwar kane, AJ. Ka aureta. abinda J ya fa?a min Kenan ”.

Duk da nasan ya fa?ane kawai Amman J ya soki Minha ya soki irin so na aure ashe ya gane ina sonki”.

Idanu ta tsira masa kana tace.

“Dagaske Yah Mu'allim?”.

Kai ya gya?a tare da cewa.

“Sosai ma”.

Daga nan ya cigaba da romance ?in ta ya dauki Kimanin minti arba'in da biyar akanta kafin ya jawota ya rungumeta yana sa mata albarka tare da cewa.

“Alhamdulillah ashe son da nake baso bane soyayya ce?”.

Tana sau?e Ajiyar zuciya tace.

“Kamar ya?”.

Murmushi yayi tare da fa?in.

“Eh so na gefe ?aya shi ake cewa so amma tunda kema kina sona kinga soyayya ce”.

Sake shiga jikinsa tayi kana tace.

“Dagaske Yah Mu'allim maganar daka ke fa?a?".

Cikin tabbarwa yace.

“Ki daina kokonto Minha Vidaa Ana uhubbuki kubban axeem”.

Wani irin farin cikine mara misaltawa ya mamaye gaba ?aya ilahirin zuciyarta.

Awannan daren haka suka kwana cikin farin ciki da kwanciyar hankali...


Alhamdulillah haka rayuwa ta cigaba da tafiya ranan Alhamis akayi walima ranan juma'a aka ?aura auren.


 Malam Liman da yazo ?aurin Aure ya kawowa Amina da Samira magani da yayi al?awar kamar yanda ya fa?a zuwa yanzu Alhamdulillah jikinu da sau?i amma dan Amina har abinci takeci.

Samira kuwa ruwan ya rage zuba sosai a wuni haifi sau uku zai zuboba.


 Hajiya Bunayya kam abin nata babu sau?i kullum gaba-gaba yake.


A ranan jumma'a akayi Dinner mai rai da lafi.


Alhamdulillah ranar Litinin sufa dawo Adamawa da amarensu Zakariya da Aseeya Asma'u  Da Dr Jameel Dija Yah Ali Su Didi sunje har falon bappa Jimeta.


Washe gari talata jirginsu ya ?aga zuwa Morocco.

Misalin ?arfe 2:00pm suka sau?a acikin Morocco anan suka samu motoci daga Masarautar Mouley na jiransu suka shish-shiga kana suka tafi motocin ajere ajere suke tafiya a sai da sukayi nisa Khausar taga motarsu ta fita cikin sauran tawagar motocin ahankali ta kalli Moddibo dake gefenta kana tace.

“Yah Mu'allim ya naga su sunyi can mu munyi nan?”.

Yana ?an shafa cikinta yace.

“Gida zamu tafi”.

Idanunta ta zare kana ta langwa?ar da kai tace.

“Yah Mu'allim gida kuma?

Baza muje inga gidansu ba? Ai kamata inyiwa Asma'u rakiya aminiyata fa”.

Kai ya gya?a tare da cewa.

“Za kije amma ba yau ba sai kin huta”.

Kai ta gya?a direct motarsu Masarautar Mouley ta nufa.

Yayin da Amare aka wuce dasu gidajen su batare da rakiyan kowa ba daga Nigeria kasancewar ga Didi da Innayi sun sai Goggo Asma'u ta wadatar dan a cewarsu ai Asiya ga Khausar dijama ga Khausar ga Yah Abbanta.


Khausar kuwa suna isa abinci suka ci kasancewar an shirya musu komai kana ko wanne yayi wanka ya kwanta dan huce gajiya.



Bayan kwana biyu Moddibo ne zaune akan sallaya gabansa ?auke da starm da Kur'ani ke kai, bayan ya dawo daga sallar Asbah yayin da Khausar ke gefensa ahankali ta ?ago kanta jin ringing ?in wayarta kallon Moddibo tayi kasancewar ya fita kusa da wayar da ido ta mishi alamar ya dai wake kira?.

Juyawa yayi kana ya kalli screen ?in wayar sai kuma ya kalleta yace.

“Asma'u ce”.

Da ?an sauri ta mi?e ta kar?i wayar tare da amsawa takai kunnenta tare da cewa.

“Hello Besty na kiyi ha?uri laifin yayanki ne. Yah Mu'allim ne ya hanani zuwa wai in barku ku gurji amarc...

Sai kuma tayi shiru ba tare da ta ?arasa mgnar ba, sabida jin muryan Asma'u a disashe kana yayi sanyi alamun taci kuka ta godewa Allah cikin raunin murya tace.

“Khausar”.

Da damuwa Khausar ta ?an jingina bayanta da kafa?ar Moddibo kana tace.

“Subhanallah Asma'u meke faruwa”.

Cikin rauni da zubda hawaye Asma'u tace.

“Khausar zan mutu dan Allah ki cewa Yah Mudibbo kuzo ki ?aukenu, wannan mutumin mungu ne ya kasheni ”.

Dariya mai sauti Khausar ta fashe dashi har tana ?an bubbuga kanta da jikin kafa?ar Moddibo kana tace.

“Ya kashe ki kuma kike magana?”.....






No comments