SAKAYYAH Book 3 PAGE 1

 *SAKAYYAH Book 3 PAGE 1*


                    Na

*Aysha Aliyu Garkuwa*





*Sanarwa!  Sanarwa!! Sanarwa!!!*

*PART OF OUR DESTINY*

*Shin ko kunsan shahararriyar marubuciyar nan me suna *FATYMASARDAUNA* marubuciyar *SHU’UMIN NAMIJI* *SOORAJ* *LAYLERH MALEEK* *MAJNOON*  ta sake kawo muku sabo kuma dadd’an littafinta dake cike da tarin zazzafar soyayya me gigita hankali, sadaukarwa, k’addara, da kuma hamshakiyar Kaunar dake gudana acikin jinin jikin mazaje guda biyu da suka kasance y’an uwan juna, duk acikin littafin nata me suna *PART OF OUR DESTINY* kada ku sake abaku labari domin samun karantawa da kuma shiga cikin group din marubuciyar zaku biya 500 ne kacal ta wannan account number din 2268498748 Fatima Abubakar UBA bank, ko ku tuntub’eta ta WhatsApp number dinta kamar haka 07069917168.

Kada ku Bari abaku labarin wannan littafi me suna *PART OF OUR DESTINY* littafine dake cike da tarin zazzafar soyayya....




Ahankali ya kwantar da ita kan cikinsa, tare da yi mata pillow da ?irjinsa, sai kuma ya jawo blanket ya ?an rufe su. ahankali ya ha?a tafin hannunsa waje ?aya tare da karanta addu'oin bacci _Fala?i, 3 Nasi 3, ?ulhuwa 3, Ayatulkursiyyu, 1 kana ya ha?a da Amanarrasulu1 La?adja'akum_ yanayi yana hura hucin numfashi nai cikin tafukan hannunsa.

Cikin kulawa ya shafa mata kana.

Yayi kansa shima ya shafa ajikinsa yana mai lumshe Idanunsa, hakanan yake jin wani irin farin ciki wanda tunda yake a iya tsawon rayuwarsa bai ta?a riskan labarin da yasa shi farin ciki da jin da?i ba kamar wannan labarin ba, ko labarin kasancewar su Didi iyayensa baisa shi farin ciki kamar wannan labarin cikin nasa ba, ya rasa ya aka yi labarin ya kasance masa ba?on lamari abin yazo masa abazata, sabodaai kawo hakan a ransa da sauriba, shi ganima yake ai Khausar ?in ?aramace.


Haka ya kwana cikin tsananin jin da?i da farin ciki kusan a zaune ya kwana da zaran ta motsa zai gyara mata kwanciya.


A gefen Hajiya Bunayya ma ita ma haka ta kwana da azabebben ?ai?ayin dake addabar rayuwarta Rayuwa tayi mata ?unci haka ta kwana ?ai?ayi ya hanata kata?us.


  Ana kiran Sallar Asbah ta fara sau?e numfashi saboda jin ya fara lafawa, kamar abin Jaraba ?ai?ayin ya daina wunin ranan haka tayi tana rama bacci da bata samu ta yi shi a daran ba.


 Ana kiran Sallar Maghriba ?ai?ayin na Assalamu alaikum yana sake dawowa haka wannan ranan ma haja ta kwana ?ai?ayi, gaba ?aya ta rasa inda zata sa kanta jin ?ai?ayin ya gallaza mata yasa ta ha?a ruwan zafi da gishiri ta cika Baho  da ruwan ?umi da gishiri ta shiga cikin.

Numfashi wahala ta fara sau?ewa jin abin ya fara lafawa,

Sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta jin yadda wasu abubuwa caccakarya a wurin.

Ido ya kuma fiddawa sosai saboda ganin wasu ?ananan tsutsotsi masu ba?in baki suna fita ta gabanta asaman ruwa bisa alamu sune suke sa mata ?ai?ayin kuma suke hanata bacci.

Shiyasa idan ta shiga ruwan zafi sai take jin sau?i idan ta fita kuwa ko awa ?aya bazai kai ba zai da meta..


Haka dai take fama da wannan rayuwar da zaran dare yayi tayi sallama da kwanciyar hankali da bacci sai kuma safiya.

Haka ta rayu tsawon Makonni biyar tana fama da wannan azabebben ?ai?ayin da bai nuna alamun akwai sau?i ko sassauci ba.


A gefen Samira Sani ma ita baki ?aya rayuwa ta sake yi mata ?unci da duhu abin ba a cewa komai.


Morocco Acan gefen su Khausar kuwa rayuwa tayi da?i Khausar na samun kulawa na musamman daga gefen uwar mijinta da kuma Kakar Mijinta Niyna kana da Innayi.

 Hadimanta nayi mata komai daya kama na rayuwa har zuwa yanzu bata iya wani cin abinci amma ko yaushe cikin Hidima suke mata haka Didi nayi mata komai na sungullan rayuwa takowa mata wannan ta kawo mata wancan, amma bata iya cin komai yau tsawon kwana goma shabiyar da jin labarin Khausar nada ciki, wanda haka yayi dai-da cika wata biyu kenan da cikin yayi.


Kwance take akan 3sitter yayinda tayi pillow da cinyarsa.

Cikin sanyi ya shafa kumatunta tare da juyiwa ya kalli plate ?in abincinta kwata-kwata ko cakali shida mai kyau bata yiba.

Cikin takaicin rashin cin abinci ya shafa cikinta dake lafe kamar bata da komai cike da damuwa yace.

“Minha”.

A hankali ta ?an ?ago kanta ta kalleshi jin yadda ya kirata da alamun damu cikin kula yace.

“Rashun cin abinci kinnan yana damuna,

 ina ga zan kira Momy in fa?a mata matsalar rashin cin abinci nan koda shawarar da zata bamu”.

Ware manyan Idanunta dake lumshe kamar na mejin bacci tayi tare da cewa.

“Momy kuma?”.

Kai ya jinjina mata, cikin sauri tace.

“Bana ce maka mubar maganar fa?a wa Momy nan ba”.

Yana shafa gashinta yace.

“Gsky ni dai inaga gwara mu gaya mata wata ?il kiga mun samu mafita?”.

Kai ta girgiza tare da cunno bakinta gaba tace.

 “Kenan me zaka ce mata?”.

Kallonta yayi tare da tallafo kanta ya juyo da ita suna fuskantar juna cikin sassauta murya yace.

“Ce mata sanyu Minha bata cin abinci ni kuma rashin cin na damuna”.

Lumshe Idanunta tayi tare da bu?e su akansa cikin yanayin irin mata masu fama da laulayi tace.

“ Idan tace maka me ya hanani cin abinci ke zaka ce mata?”.

Matsota yayi sosai kana yace.

“Ce mata zanyi kina da cikine  kuma yana hana ki cin abinci?”.

Zare idanu tayi kamar wacce tayi wani laifi sai kuma ta kife kanta akan ?irjinsa.

Lallausan murmushi ya saki kasancewar tun washe garin ranan da akace tana da ciki yace zai fa?a wa Momy amma fir ta?i yarda wai tana kunya, sosai ta sake mannuwa ajikinsa kana ta manna kanta da faffa?an ?irjinsa cike da kasala tace.

“Nikam Yah Mu'allim Ina kunya taya zaka fa?awa Momy wannan magana Taya zaka fa?a wa Momy cewa ina da ciki Fisabilillahi yanzu sai ka iya fa?a?”.

Murmushi yayi tare da cewa.

”Toh mene cikin nan fa halartacce ne, cikine mai gata mai daraja gashi da mahaifinsa na rasa kunyar me kikeji?”.

Kallonsa tayi da mamaki sai kuma ta langwa?ar da kai tace.

“Yanzu Yah Mu'allim baza kaji kunyar cewa Momy ina da ciki ba?”.

Idanunsa ya bu?e tare da karkata mata kai kana yace.

“Toh me aciki?,me abin kunya aciki don kina da ciki?”.

Wani kallo ta masa mai tattare da shau?i da yanayi na musamman ahankali ta motsa la??anta kamar mai ra?a tace.

“Yanda aka samu cikin shine abin kunya kowa fa yasan me muka yi”.

Ta ida maganar tana rufe fuskarta janyota jikinsa yayi tare da rungume ta kana yayi murmushi tare da fa?in.

“Toh shikenan tunda baki so, Sarkin kunya zanga yanda zakiyi kuma idan munje Auren su Dr Jameel ai zata ga cikin kafin nan”.

Cikin sauri ta girgiza masa kai tare da narke fuska  sai kuma ta janyo hannunsa ta ?aura akan cikinta tace.

“Toh ai cikin baya wani girma".

Yana ?unshe dariyarsa yace.

“Ai kafin nan zai ?aru tunda zuwa lokacin ya cika wata uku tunda kinga an ?ara wata biyu a asalin date ?in kinga har zai shiga wata na hu?u ma kafin nan”.

Kanta ta ?an jujjuya sai kuma ta tsirawa sajensa dake ?yalli Ido tace.

“Ha'a sai dai-dai lokacin Auren yayi zamu tafi ne?”.

Kai ya girgiza tare da cewa.

“A'a sai bikin ya rage saura sati zamu tafi kinga kafin nan cikin ya cika wata uku har ya shiga na hu?u ma”.

Ganin yanda ta narkar da fuskarta ne yasa ya janyonta jikinsa ya sake rungumeta cikin tura baki tace.

“Nikam gaskiya ina jin kunya wallahi”.

Sosai ta bashi dariya amma baiyi ba yace.

“Uyumm idan kina jin kunya ki ri?a cin abinci”.

Narai-narai tayi da idanu tare da fa?in.

“Yah Mu'allim toh bana jin yunwa kaga kuma yanzu nasha fruit Alhamdulillah na ?oshi”.

Janyota yayi ya rungumeta daga haka bacci ya ?auke su.


Acan ?angaren Amina kuwa yanzu baki ?aya rayuwa tayi mata ?unci gani take kamar rayuwarta yazo gangara.

Cikin sau?e numfashi ta kalli Uncle Naseer Dake gefenta kana tace.

“Uncle Naseer bani da lafiya”.

Wani kallo ya mata sai kuma tayi murmushi tare da fa?in.

“Ba wani nan lafiyarki ?alau”.

Cikin sanyi da kasala daya gama baibaye rayuwarta ta fesar da numfashi kana tace.

“Allah da gaske bani da lafiya Ni nasan yanda nake ji ajikina”.

Yana ?an latsa wayarsa yace.

“Kada ki damu”.

Araunane tace.

“Ji nake kamar zan mutu”.

A wannan karon ma murmushi yayi yana gyara zamansa yace.

“Baza ki mutu ba yarinya ki kwantar da hankalinki”.

Kanta ta jinginar da jikin kushin tare da cewa.

“Uncle Naseer to yaushe zamu tafi gida naga Auren Addah Asiya ya matso du-du-du saura wata ?aya da sati ?aya”.

Juyawa yayi ya kalleta sai kuma ya ?aga kansa sama alamar tunani yana sauke kansa ?asa yace.

“Auren saura sati ?aya zamu tafi kinga yanzu kenan saura 1month zamu tafi”.

Cikin sanyi ta gya?a kai tare da fa?in.

“Shikenan Toh Allah ya kaimu”.

Kafin yace wani abu wayarsa ta hau ruri ahankali ya mi?e ya fita tare da picking call ?in.


 Daga ?aya bangaren akace.

 “Ranka yada?e nan Veazer ka na komawa India zai fita”.

Cike da farin Yace.

“Alhamdulillah Nagode bari zuwa anjima zan kiraka”.

Kana ya katse wayar tare da komawa Falon ya zauna gefen Amina ahankali ta ?ago Idanunta ta kallesa tare da cewa.

“Uncle Naseer ya batun tafiyarmu Indi'a ne?”.

Still da murmushi afuskarsa yace.

“Sai mun dawo bikin Asiya”.

Cikin sanyi tace.

“Toh Allah ya kaimu”.


Acan gefen Hajiya Bunayya kuwa rayuwa tayi mata tsanani abubuwan ta kullum gaba-gaba yake da safe zuwa rana zata yini cikin kwanciyar hankali sai dai da dare yana yi bata da kwanciyar hankali zuwa yanzu ?yan?yamin kanta da kanta ta keyi.


 Cikin sau?e numfashi ta kalli Hajiya Lami Idanunta cike da ruwan hawaye tace.

“Na lura ko ?ana Sulaiman ?yamar zama kusa dani yake yi sannan Lami?o koda abinci na kai masa sai yace in tattara in fita dashi shi ya ?oshi.

 Hankalina ya tashi Hajiya Lami kaddai mugun abinda naje yiwa Khausar ya dawo kaina ya addabi rayuwata?

Ji nake kamar ?ai?ayin yasa gabana ya ha?e da bayana”.

Zare idanu Hajiya Lami tayi cikin yanayin tashin hankali tace.

“Mun shiga ukun mu Hajiya Bunayya wannan wani irin abu muke fuskanta a rayuwar ki kalli haka Samira fa yanzu yanda ta bushe ta rame duk ta lalace sannan nima bana bacci dana kwanta da daddare sai muggan mafarkai na rasa yanda zanyi da rayuwarta” 

Cike da damuwa Hajiya Bunayya ta girgiza kai tare da cewa.

“Ke koni?,Auren Asiya sai matsowa yake gashi Lami?o ko zama kusa dani muyi maganar Auren nan baya yarda sai kyara da hantara ina ga ba?in jinin da Boka yace Khausar za tayi ya tabbata nice nayi shi”.

Cikin mamaki Hajiya Lami ta tallafe kuncin ta tana sauraron masifar daya riskesu lokacin ?aya duniya tayi musu atishawar kaji.

Hajiya Bunayya kuwa da damuwa ta cigaba da cewa.

“?a?ana ma duk sun fita har?ana dama Asiya ita tun can ba shiga har?ana take ba.

Kuma abin mamaki itace take ?an daurewa tana zama kusa dani shekaran juya da taga ina ta fama da ?ai?ayin nan ina zirya da sintiri shine ta fa?a wa Lami?o aje asibiti koda ta fa?a masa ma cewa yayi shi bazai samu damar kaina ba inje in Kai kaina idan na ku?ine in fa?a masa ko nawa ne magana ta ?are”.

Tallafe kunci Hajiya Lami tayi kana tace.

“Ohhh Mukam munga ta kanmu wannan al'amari wacce irin Musifa da fitinace ta Kunno mana kai”.

Kafin Hajiya Bunayya tace wani abu Asiya ta fito daga cikin Bedroom ?in ta kana ta zauna gefen su tare da girgiza kanta sai kuma ta kallesu ahankali ta sunkuyar da kanta Idanunta na cika da ruwan hawaye murya cike da rauni tace.

“Umma ku koma ga Allah ku nemi gafarar wa?anda kuka cutar sai kuga Allah ya kawo muku sau?i wannan ishara ne Ubangiji yai muku Allah ya soku da Rahma ne daya kama ku tunda ranku baku mutu ba dan haka kunemi yafiyar wa'anda kuka cutar tun kafin lokaci ya ?ure muku”.

Kallonta suke tunda ta fara magana har ta dasa aya basu katse taba kamar yadda suka sqba.

Karo na farko a rayuwar su da suka ji jikinsu ya mutu akan abinda suke aikatawa kana kalaman ta ya ratsa su.

Ganin yanda jikinsu yayi sanyi alamar nadama tare dasu yasa cike da girmamawa matsayinsu na iyaye taci gaba dayi musu nasiyya mai ratsa jiki kana ta nuna musu kuskuren su da basu shawarar su nemi gafarar wa?anda suka cutar kana su nemi yafiyar Allah da yardarsa...



Morocco bangaren Khausar sosai al'amura ke tafiya yau ya kama Auren Asma'u da Dr Jameel saura mako biyu haka Auren Asiya da Zakariyya da kuma Yah Aliyu da Dija saura mako biyu Cif-cif sukuma a shirye-shiryen su saura Mako ?aya su tafi Nigeria.


Ahankali ta ?aga kanta tare da zubawa ?ofar falonta Ido jin sanyayyan kamshin turaren Moddibo wanda da alama ya dade da dawowa harma ya shiga side ?in sa yayi wanka kai tsaye gefenta ya nufa ya ya kwanta kana ya ?aura kansa kan cinyarta kasancewar tana kan 3sitter sai kuma yasa hannunsa ya shafa cikinta kafin ahankali ya maida hannunsa kan cikinta yace.

“Baby ya kake kana lafiya?”.

Murmushi Khausar tayi amma bata ce komai ba.

Sake manna kansa da cikin yayi tare da cewa.

“Meimei ta baka abinci Kaci?”.

Still shiru tayi sai kuma ya ?ago ya kalleta tare da cewa.

“Kinci abinci ko?”.

Kai ta gya?a masa tare da fa?in.

“Eh wallahi da gaske naci”.

Cikin tsira mata idanu yace.

“Da gaske?,Me kika ci?”.

Kai ta gya?a kana tace.

“Nayi wainar Fulawa kuma naci guda uku”.

Kai ya jinjina tare da fa?in.

“Masha Allah Alhamdulillah haka yayi kyau ai naga cikin ya ?an tashi”.

A hankali ta ?an ?aura hannunta bisa sajenshi tana shafawa a hankali tace.

“Yau ina ka tafi tunda safe baka dawo ba”.

Saman hannunta ya shafa tare da cewa.

“Mun fita ne da Dr Jameel da Zakariyya kinsa ya dawo tun shekaran jiya sunje sun nuna min gidansu an tsara musu komai masha Allah.

Dan su bikin saura kwana goma ma zasuyi gaba”.

Cikin sauri ta kallesa sai kuma ta langwa?ar da kai tace.

”Toh muma mu tafi dasu mana Yah Mu'allim”.

Kai ya girgiza tare da fa?in.

”Tafiyarsu da ban tamu da ban”.

Sake marairaice murya tayi tace.

“Allah mu tafi dasu na ?agu naga Raudat nayi kewar Momyna sosai”.

Cikin kwantar mata da hankali yace.

“In sha Allah zakije ki ganta”.

Kallonsa tayi sai kuma ta make kafa?a tace.

“Ni dai wallahi da zamu tafi tare nafi so".

Yana gyara kwanciyarsa yace.

“Su?in ma ina ga zance su ha?ura kawai mu tafi tare, tunda saura sati ?aya zamu je gwara su ha?ura mu tafi”.

Cikin sau?e ajiyar zuciya tace.

“Toh Allah yasa su ha?ura mu tafi".

“Ameen”.

Sai kuma yayi saurin mi?ewa daga jikinta jin wayarsa na ruri ?agawa yayi ta kalli screen ?in, sunan Sheikh Jabeer ya bayyana da murmushi afuskarsa ya dauka tare da cewa.

“Kaka”.

Daga ?aya bangaren Sheikh Jabeer dake zaune cikin falonsa A'ish ?in sa na zaune gefe ya saki murmushi tare da cewa.

“Na'am Jikalle Barka da yamma”.

Moddibo na gyarawa Khausar zama ajikinsa yace.

“Barka dai ya gida?".


Ahankali Sheykh yace.

“Lafiya lau”.

Ya ?are mgnar yana gyara zama yace.

“Kwanaki munyi magana da kai akan ?atan Jameel da plate number motar ?in da muke magana akai?”.

Kai Moddibo ya gya?a tare da fa?in.

“Hakane”.

Anutse Sheikh Jabeer yace.

“Masha Allah idan ban manta ba cikin  mutanenku akwai wacce tasan number motocin da ake zargin suna yawan binbiyarku gab da ?acewan Jameel ”.

Kai Moddibo ya jinjina yana mai tuno J dinsa yace.

“Eh Khausar ce ma ”.

Cikin sau?e ajiyar zuciya Sheikh Jabeer ya gyara zamansa tare da fa?in.

“Toh ba matsala idan har yanzu tana ri?e da number ka turo min saboda akwai ?ungiyar da Tabital Fulani suka kama a Taraba.

Wanda an kamasu da motoci tawaga guda kusan guda goma wanda gaskiya muke zaton motoci ne da suke harkan Kidnapping dasu saboda a dokar adaji aka kama su da kuma makamai kana da tarin ku?a?e".

Numfashi Moddibo ya fesar kana yace.

“Toh shikenan In sha Allah bari muyi maganar da ita”.

Bayan ya katse wayar ya maida kallonsa gare ta ahankali ya ri?e hannayenta cikin nasa cikin natsuwa ta zuba masa ido.

Cikin fesar da numfashi yace.

“Minha batun number motar nan da Asma'u tace kin ri?e,har yanzu kina ri?e dashi akan ki?”.

Kai ta gya?a cikin tabbatar tace.

“Tabbas kuwa har abada bazan manta number motar nan ba saboda na ganta alokuta uku maban-banta na ganshi a Jauro Yaya.

Na ganshi a bakin Makarantar mu.

Sannan ranan da muka yi rabuwa ta ?arshe da Yah Jameel na ganshi yana bibiyarmu”.

Numfashi ya fesar tare da fa?in.

“Yanzu zaki iya fa?a min?”.

Kai ta gya?a mishi.

Ganin hakane yasa ya

 ?auki wayarsa ya danna kan number Sheikh Jabeer ya shiga wajen text yace.

“Gashi sa”.

Kar?a tayi ta rubuta number motar da komai da komai harda collor ta mi?a masa number ya tsirawa idanu sai kuma ya kalleta yace.

“Kin tabbatar shine dai-dai?”.

Kai ta gya?a tare da cewa.

“Na tabbata shine babu shakka ko Haufi ko yanzu na rufe Idanuna ina kallon number motar”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Ok ba laifi”.

Ba ?ata lokacin ya yiwa Sheikh Jabeer sending.

Ahankali ya maida hannunsa kan cikin nata wanda zuwa yanzu ya fara bayyana kallonta yayi tare da langwa?ar da kai yace.

“Minha yunwa nake ji mai zan samu?”.

Tana lunshe Idanunta cikin nasa tace.

“Mekake so?".

Muryansa cike da kasala ya sake narkewa jikinta tare da cewa.

“Me kika yi min?”.

Manyan Idanunta ta juya sai kuma ta sakar masa da murmushi tare da cewa.

“Nayi maka abinda kake so?”.

?an ware idanunsa yayi yana cigaba da shafa cikinta yace.

“Mene?”.

Langwa?ar da kai tayi tace.

“Nayi dambu a tunanina zan iya ci sai kuma naji bazan iya ciba”.

Wani kallo ya mata me cike da tarin tausayi da jin ?ai yace.

“Ke kuma me yake miki da?i In banda Fakala ba”.

Da sauri ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta tare da cewa.

“Kai Yah Mu'allim”.

Kai ya jinjina kana yace.

“Ehem sai an jima da daddare zaki ce min kina son pakala”.

Marairaice fuska tayi kana tace.

“Ni dai wallahi kabar fa?a min haka kar kayi min sharri”.

Idanunsa ya bu?e kanta tare da fa?in.

“Sharrine ma?,Toh bari zan kama kine?”.

Murmushi tayi tare da fa?awa jikinsa amma bata ce komai ba.


AnanTaraba shirye-shiryen biki ya kankama tuni aka fara gyara amare an killace su.


Momy da kanta je gyara Asma'u Asiya ita ke mata Dilke sai wani ?yalli suke sunyi kyau gwanin ban sha'awa soyayyar ta da Dr Jameel ?in ta kuwa na tafiya hakama su Asiya.

Yau ya kama Auren saura kwana goma wanda ya rage saura kwana uku Moddibo su taho da Angwaye da ?an ?aurin Aure.


Yau tun safe Ummi da kanta da Asma'u suka tafi gidansu Innayi kasancewar key na hannunta Ummi da kanta ta shiga Side ?in Moddibo da kanta ta gyara masa ta killace Asma'u kuwa gefen Innayi ta gyara ta killace ko ina yayi gonin ban sha'awa.

Ga kuma sabbin part guda biyu da ake ?en?esa sabon gini, na alfarma wanda tuni an gama komai nasu, wanda bisa shawarar inanayi aka tsara da umarnin Abualeey tare jagorancin Abban Jameel abune na ku?i shiyasa tuni an gamsu wanda nanne masau?insu in sun iso.


Morocco Khausar ce kwance akan kujerar bisa alamu da Momy take waya cike da farin ciki ta gyara kwanciyarta tare da cewa.

“Momy In sha Allah mun kusa zuwa".

Murmushi Momy tayi kana tace.

“Toh Khausar me kike so in shirya miki idan kin zo.

Ga Raudhat baki ?aya lissafinta da tunani Adda Khausy ta kusa daeowa.

da an ta?a ta sai tace sai Addah Khausy tazo, wanka ma ?inyi tayi yau wai sai Addah Khausy tazo tayi mata”.

Dariya Khausar ta sanya tare da fa?in.

“Yau mun bonu kafin inzo ai datti zai kashe ki Raudat ”.

Ta ?are fa?in haka jin muryan Raudat ta amshi wayar Raudat kuwa itama cikin dariya tace.

“Addah Khausy datti bazai kashe niba fa zan ri?a fesa turare sannan insa humran Momy saboda nayi kamshi sai kinzo ki min wanka”.

Dariya suka sanya Dukansu daga nan suka cigaba da hira.

Suna gama waya dasu Momy ga Mamaki ta sai  ga kiran Hajja Nana ya shigo tana ?agawa tace.

“My Kakus”.

Baki Hajja Nana ta ta?e tare da fa?in.

“?ar tselen Uwa tunda muka dawo sau ?aya mukayi waya dake baki sake kirana ba”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Kai Hajja Nana kuma abin harda Sherri ne?

kin manta cewa garin ku babu network in baku kuka kira ba baya shiga,  kullum fa kina raina”.

Dariya Hajja Nana tayi tare da fa?in.

“A yayi kyau yaushe zaku zo?”.

Cikin sauri tace.

“Next week”.

Cikin so da ?auna Hajjaj Nana tace.

“Yau da kaina na ?ibo ?afana har bidhiyar ?are zancenka saboda inji Labarin ?ar jikata dan nayi kewarki ina so in San yaushe zakuzo”.

Khausar na murmushi me ?auke da ?aunar Kakar tata tace.

“In sha Allah nan da kwana uku dai muna cikin Nigeria”.

Kai Hajja Nana ta gya?a tare da fa?in.

“Toh Allah Ubangiji ya kawo ku kafiya”.

Bayan ta gama wayar ne ta mi?e ahankali kasancewar tun safe bata le?a Didi ba kallon jikinta tayi ganin dogon riga ce budadde da mayafinsa babba yasa ta sau?a falonta ta wuce Side ?in Didi.


 Tana shiga Falon ta samu Didi zaune da ahlinta, Modibbo Sai Zakariyya da Dr Jameel, Sai kuma Lalla Khadijah da Lalla Salma da Hafsat wanda ga duk kan alama sunzo tafiya bikin ne Didi na ganinta ta mi?a mata hannu idanunta akan cikinta,.

Sai lokacin itama ta kalli cikin ta ga Mamaki ta sai taga cikin nata har ya tura rigar ta ka?an cikin jin kunya ta zauna gefen Didi cike da kulawa Didi tace.

“Barka da yamma?”.

Kai ta gya?a tare da cewa.

“Yawwa Barka dai Didi”.

Didi na gyara zama tace.

“Yau tun safe nake ta zuba ido zan ganki ban ganki ba ki shigo ba, nace Rahama taje ta du baki data dawo sai tace kina bacci”.

Tana kallon Moddibo tace.

„Eh Didi ina bacci ban da?e da tashi ba shine nayi wanka sai kuma na ?anyi waya da Momy na Momy tace in gaishe ki ma”.

Fuska a sake Didi tace.

“Ina amsa wa Masha Allah fatan suna lafiya?".

Kai ta gya?a tare da fa?in.

“Lafiya ?alau”.

Ita kuwa Khausar kallonta ta mayar kan Lalla Khadijah da Lalla Salma da Hafsat cike da girmamawa ta gaishesu cikin sakin fuska suka amsa mata suna tambayar jiki.

Kallonta ta mayar kan Didi jin tana cewa.

“Khausar ya shirye-shiryen tafiya?”.

Dariya Khausar ta sanya tare da fa?in.

“Aini har na gama shirya wa ma”.

Ahankali Moddibo ya ?ago Idanunsa ya  kalleta kana yace.

“Toh da kika gama shirin ma ai ke ba zuwa zakiyi ba”.

Zare idanunta tayi sai kuma ta kwa?e fuska ahankali ta maida kallonta kan Didi dake murmushi tace.

“Didi kiji fa abinda yake cewa".

?an dariya Didi tayi ganin yanda ta kwa?e fuska yasa tace.

“Rabu dashi waya isa ya hana ki zuwa Mamana ai kece agaba idan baki zoba amaren ma baza su zoba”.

Ware idanu Dr Jameel yayi tare da sanya dariya yace.

“Anya kuwa Didi wannan zai sa?u dan bata jeba ace Amare baza su zoba ai ita ta zauna gidan mijinta mu muje mu ?auko Matan mu". Cikin murmushi Zakariyya cewa.

“Gaskiya dai kam”.

Dariya Didi ta sanya kana tace.

“A'a Zakariyya har kaima wato zama da Jameelu ya dawo da kai mai surutu da baki”.

Dariya Lalla Khadijah ta sanya tare da fa?in.

“Aikam Didi Hausawa sunce zama da ma?aukin kanwa shi ke kawo farin kai".

Dariya suka sanya Lalla Hafsat ta kar?e da cewa.

“Aikam dai ko kurma ne ya zauna da Dr Jameel Sai ya koyi magana".

Zakariyya kuwa ?eya ya sosa tare da sunkuyar da kai...


?ago kansu sukayi atare tare da kallon Ibraahim dake shigowa cikin mamaki suka ha?a bakin cewa.

“A'a Ibraahim kuma”.

Kai ya gya?a tare da bu?awa Rahama hannu wacce ta nufo kansa da gudu da murmushi afuskarsa yace.

“Surprise dama bazata na shirya muku Yah Jameel ba jiya muna waya kana zaton bazan zoba, har kana fushi”.

Ya ?are maganar tare da ?arasawa gefen Lalla Khadijah ya zauna kana ya ?aura kansa kan kafadarta Dr Jameel cikin murmushi yace.

“Aikam da har nayi fushi da kai”.

Jujjuya idanu yayi yace.

“Amma dai yanzu ka huce ko?”.

Kai Dr Jameel ya gya?a tare da cewa.

“A na huce tunda kazo”.

Lalla Salma ce tace.

“Toh dama taya za'a yi Auren Yayun ka har biyu baka nan ai dole saida babban ?anin ango za'a ?aura Aure”.

Dariya yayi tare da fa?in.

“Aikuwa dai Lalla Salma kin gane”...

Haka dai suka cigaba da hiransu.


Ana gobe zasu tafi da misalin karfe goma na dare Moddibo ne kwance a gefen Khausar yana romance ?in ta tare da shafa cikinta ahankali ya ?ago Idanunsa ya kalleta tare da cewa.

“Gobe idan munje Nigeria gidan Innayi zamu sau?a” .

Idanunta dake shanye kamar na mai jin bacci ta bu?e tare da tura baki tace.

“Yah Mu'allim gidan ku kuma? Nikam dai inje gidan Momyna ”.

Da sauri ya ware idanunsa tare da dafe ?irjinsa kana yace.

“Na isa ki tafi kibarni da waye idan kin tafi gidan Momy?”.

Cikin tura baki tace.

“In barka da Innayin ka mana”.

Kissing ?in goshinta yayi tare da cewa.

“Innayi zata bani abinda kike bani ne Minha?

Innayi bazata bani abinda kike bani ba Minha sabida duk duniya babu wanda yake bani abinda kike bani fa Minha ya za'a yi kice dan ina tare da wasu za kiyi nesa dani ai bazan iya jura ba”.

Ahankali ta fesar da numfashi tare da cewa.

“Kai Yah Mu'allim Kuma fa kasan nayi missing na Momy”.

Tafin hannunta ya ri?e cikin nasa yana matsawa yace.

“Nayi miki al?wari idan munje kullum zan na kaiki ki wuni amma kwana bazan barki ba.

Babyna ma bazai iya ba saboda yana son ?umin jikin Abbansa”.

Ta bu?e baki da niyar magana ta fasa jin wayarsa na ruri ahankali ya mi?e tare da janyota jikinsa yana shafa bayanta ganin number Sheikh Jabeer yasa ya dauka muryansa can ?asa yace.

“Kai baka san dare yayi bane?".

Ware idanu Sheikh Jabeer yayi tare da cewa.

“?aniyarka ne ni kake fa?awa dare yayi?”

Cikin kwa?e fuska Modibbo yace.

“Toh Amman dai kasan inada iyali ko?”.

Wani irin murmushin mai cike da tuna baya Sheykh Jabeer yayi tare da cewa.

“Hmmm yaro man kaza da kake cemin bansan dare yayi bane shin baka san cewa duk abinda ?anyen ganye ya sani ya kuma ganiba bushesh-she ya riga saba".

Murmushi Moddibo yayi tare da cewa.

“Can maka dai da karin maganar ka Ni ban fahimci me keke nufi ba".

Dariya Sheikh Jabeer yayi kana yace.

“Ai baza ka fahimta ba,

amma dai kasani duk abinda kake tunanin kasan shi na fika sanin shi kai abayana kake”.

Moddibo kuwa hannu ya cusa cikin sumar kan Khausar yace.

“Toh naji Ni dai yanzu ka fa?a min me yake tafe da kai ina da abinyi”.

Cikin so na kaka da jika Sheykh Jabeer yace

“Eh Ya maka kyau.

Dama akan batun number motar da kuka turo min ne tun jiya nayita kiranka baka ?auka ba bansan me kake ba”.

Cikin sauri Moddibo ya dai-daita nutsuwarsa tare da cewa.

“Kuma banga Miss call ?in ba”.

Cikin fesar da numfashi Sheik Jabeer yace.

“An samu motar cikin motocin da aka kamo  sannan acikin mutanen ana so gane su waye ke amfani da motar dan mutanen kusan su ashirin da biyar aka kama.

 Toh muna so mu gane su waye ke amfani da wannan motar sannan su waye suka sace Jameel suka kashe sa”.

Cikin fesar da numfashi da kuma rauni Moddibo yace.

“Alhamdulillah in Sha Allahu Jinin J bazai tafi abanza ba”.

Kai Sheikh Jabeer ya jinjina tare da fa?in.

“Yanzu shine abinda muke so tunda har ita mai ?akin ka ta gansu tasan Fuskarsu tunda jibi kuna hanya idan kun iso kafin ku wuce sai munje kun gan su”.

Cikin sauri Moddibo ya runtse idanunsa yace.

“Yah Sheikh bana son ganinsu”.

Ahankali Sheikh Jabeer yace.

”Meyesa?”.

Araunane ya girgizar kai tare da cewa.

“Bana son ganin wa?anda suka kashe min J idan na gansu bansan me zanyi musu ba, kar nazo nima nayi abinda bashi bane, bansan mai zan musu ba, na tabbatar dai in na zan ga wanda ya kashe J.

Bazan iya barinshi arayeba zan iya yi musu komai”.

Cike da nutsuwa da dattako Sheikh Jabeer yace.

“In sha Allah babu abinda zaka musu dole zaku zo ku gansu ”.

Idanunsa na tara hawaye yace.

“Bazan gansu ba bazan iya ba har abada bana ?aunar ganinsu.

 Babu wa'anda na tsani gani a duniya sama dasu”.

Ahankali Khausar ta mi?e ta zauna Sheikh Jabeer kuwa ahankali yace.

“Toh ba laifi ku dai ku shirya idan kun zo sai kun biya nan”.

Kai ya gya?a tare da katse kiran sai kuma ya maida kallonsa kan Khausar cike da rauni lokaci ?aya mutuwar Jameel ya dawo masa sabo idanunsa muryansa cike da sanyi da kuma rauni yace.

“Kinji fa waifa cewa yayi inje in Kalli wa?anda suka kashe min J.

 Ina zan iya kallonsu?”.

Hannunta tasa ta tallafo kansa tare sa ?aura a?irjinta kana tace.

“Yah Mu'allim zamuje ko domin mu tabbatar da cewa su?in ne suka kashe sa sannan mu tabbatar da cewa su?inne an kamasu, sannan ayi musu hukunci dai-dai da laifinsu.

 Ni na tabbatar muddin na gansu wallahi zan gane su da Izinin Ubangiji”.

Araunane ya girgiza kai tare da cewa.

“Muje kuma Minha?, Minha bazan iya ganin suba fa”.

Kansa ta tallafe tana ?an shafa bayansa alamar kontar da hankali tace.

“Yah Mu'allim zamu iya zamu iya ganinsu kodan ahukuntasu abinsa cutar damu da sukayi”.

Zuciyarsa na ?una yace.

“Minha zan iya musu abinda basuyi tunani bafa”.

Sake tallafo kansa tayi tare da cewa.

“Yah Mu'allim babu abinda zaka musu hukumane za tayi aiki akansu kamar yanda Shari'a ta tsara”.

Ta ida maganar tana shafa kansa ganin yanda mutuwar Jameel ya dawo masa sabo ahankali ta ha?e lips ?in su waje ?aya wani gauron numfashi ya saki tare da janyo jikinsa ya fara shafa sassan jikinta ahankali ya ?ago kai ya kalleta tare da yin murmushi kana yayi ?asa da rigar baccin jikinta muryansa asha?e yace.

“Minha kina ganin gaba ?aya abin nan sai sake girma suke”.

Shanyayyun idanunta ta ?ago ta kallesa tare da sakin murmushi hannunta na shafa kansa tace.

“Yah Mu'allim ba dole su sake girma ba gaba ?aya ka buwaye su ka gigita su sannan ka hanasu nutsuwa da kwanciyar hankali ”.

Hancinta ya lakace yace.

“Ba dole ba wa?an'nan kayan marmarin ai ba'a barinsu Minha suna da matsayi babba dama rashin samun hannu ne shiyasa basa girma sosai yanzu kuma kinga sun samu”.

Dariya tayi haka tayi ta yi masa abubuwan da suka mantar dashi damuwa da kuncin daya shiga haka suka kwana cikin farin ciki...


Ranan dasu tafi Misalin 12:00pm jirginsu ya tashi daga kasar Morocco zuwa Nigeria.

 Kasancewar Private Jet ne shida Khausar suna First class daga can ?arshe Zakariyya,Dr Jameel, Abualeey, Galadima, Waziri, suma na cikin First class daga gaba sai Innayi kana Didi, Lalla Khadijah da Lalla Hafsat duk suna baya.

Misalin ?arfe biyar dai-dai jirginsu ya sauka a Adamawa kai tsaye motoci suka zo suka ?auke su daga Airport zuwa fadan Mai martaba sarki Jabeer Nuruddeen Bubayaro.

 Kyakkyawan masauki na musamman aka basu anan suka kwana bayan anyi musu tarbar na mutuntaka Didi takasance ga Mahaifiyarta da Mahaifinta sannan ga Ummi Kakarta Ummei Jakadiyarsu.

Washe gari da safe Misalin ?arfe bakwai na safe Sheikh Jabeer da kansa ya wuce Masau?in da aka bawa Moddibo da Khausar yana shiga ya samu Moddibo na ha?a mata tea.


Juyawa Moddibo yayi ya kallesa tare da fa?in.

“Wai ya kake shigo mana haka ba neman izini”.

Kallonsa Sheikh Jabeer yayi tare da cewa.

“Ka manta nan Fada tace ba Fadar kuba da zaka ce  sai na nemi izini”.

Murmushi Moddibo yayi yana mikawa Khausar tea ?in yace.

“Toh me kake nema da sanyi safiyar nan da kazo mana?”.

Sheikh Jabeer na gyara tsayuwar sa yace.

“Tashi zakuyi mu tafi inda zamuje”.

Langwa?ar da kai Moddibo yayi tare da fa?in.

“Ni bazan jeba”.

Cikin sauri Khausar tace.

“Kayi ha?uri Yah Mu'allim muje”.

“Gwara kam ki fa?a mishi muje mu tabbatar dan kada a?aurawa wasu laifin da bana su ba”.

Haka dai suka ta lalla?a Moddibo har ya amince  suna fita sai ga Amintaccen Hadimin Sheikh Jabeer ya ?auke su a mota suka tafi kurkukun dake cikin Yola suna isa bisa sirri akayi musu jagora da iso, aka wuce da ciki.


Duna shiga Khausar tayi saurin komawa bayan Modibbo tare da ri?e hannunsa gama, cikin rawan jiki ta ?ago hannunta tana nuna wasu ?attun mutum biyu da babu alamun imani tare dasu, shiyasa aka ?an waresu gefe suna zaune sai kuzurai suke.

Cikin tashin hankali gami da tsanarsu ta fashe da kuka murya narawa tace.

“Ga sunan wallahi Yah Mu'allim sune, sukayi ta bin motarmu da Yah Jameel randa aka sace shi, kuma sune suka je Jauro Yaya sannan kuma sune suka je bakin Makarantar.

Wallahi tallahi sune suka bibiye mu aranan da muka rabu da Yah Jameel na ?arshe har da muka tsaya a suma suka tsaya”.

Cikin Tsananin tsana takaici da ?unar rai Modibbo ke binsu da wani irin kallo mai nuna jin zafin illar da sukayi mishi.

Shi kuwa Sheikh Jabeer nan take yasa aka killace su waje na musamman da kansa ya tsananta bincike Matsayin sa na SS mai zaman kansa wanda yasan kansa da aikinsa da ?irewa.

Bisa jagorancin Jalal yasa aka musu ?an banzan bugun da ya karya ?arfin zuciyarsu.

Kana yacewa su Modibbo su shiga.

Cikin tsaresu da ido ya nuna musu Khausar tare da cewa.

“Kunsanta?”.

Agalabaice suka ce.

“Eh mun santa itama an bamu kwangilar kashe ta”.

Aru?e ta zare ido kana ta ?aura hannunta a?irji tace.

“Kasheni kuma nima? me nayi muku”.

Kai Sheikh Jabeer ya jinjina kana ya nuna Moddibo dake binsu da wani irin kallon tsana gaba ?aya jikinsa rawa yake shi kuwa Sheikh Jabeer cikin sanin makamar aikinsa yace.

“Wannan fa kun san shi”.

Kai na farkon ya gya?a tare da fa?in.

“Eh ai dama shi tare aka bamu kwangilar karshe sa da Malam Jameel”.

Zama sheikh Jabeer ya gyara tare da fa?in.

“Waya baku kwangilar kashe su?

Sannan akan me zaku kashe su?”.

?ayan da yafi galabaitane ya ?ago fuskarsa da duk halittarsa ta canza saboda azabebben bugu da ya sha yace.

“Mu mutanen garin  dake gefen Jauro Yaya ne, kuma manyanmu ne  suka bamu kwangilar karshe su".

Akai Khausar ta ?aura hannu tare da fa?in.

“Ai kune ma na gani a Jauro Yaya ”.

Cikin tsawa Sheikh Jabeer yace.

“Me ya kaiku Jauro Yaya kuma?”.

Na farkon ne ya kar?i zancen da cewa.

“Mu muka kashe Garkuwan Rugar Jauro Yaya Umaru”.

Wani irin raunataccen kuka ne ya kubcewa Khausar yayinda gaba ?aya jikinta ya ?auki rawa.

Jalal kuwa a hankali ya gyara ri?on da yayiwa wayarsa saboda video'nda yake yi musu.


Zama Sheikh Jabeer ya gyara tare da ci gaba dayi musu tambayoyi.

Shi kuwa  Moddibo gaba ?aya ilahirin jikinsa rawa yake ji yake duniyar tayi masa ?unci ji yake tamkar ya fisge bindigar dake hannun Sheikh Jabeer ya kashe su kowama ya huta”.

Amma ya kasa motsa wa saboda Khausar dake rungume dashi ita ta hana shi motsi.

Dayan ne ya kar?i maganar da cewa.

Kamar haka uuna ?aya daga cikin mutanen dake Ma?oftaka da Rugar Jauro Yaya wanda sun kasance arna ne sannan manyan sune suka bamu umarnin su kashe Garkuwan Rugar Jauro Yaya saboda shine yake shiga cikin Sabgoginmu yana hana mu Kidnapping yanda suke a yankin, dan da in sun sato mutane a nan cikin tsaunukan dake zagaye dasune suke zuwa su ?oye mutane, sai an biya su ku?i wanda in za'a samu mutane a wurin kai tsaye cewa za'ayi Fulani wurin ne suke satosu.

saboda haka ne in sunje sunyi kidnapped shi yake hana su sakewa, kuma basu isa su ?auki dabbobi yanda suke so saboda kasancewar mutum mai sa ido da kuma Jarumta”.

Cikin tafarfasan zuciya Sheikh Jabeer ya dasa masa bindiga akansa kana yace.

“Shi kuma Malam Jameel meya muku?,”.

Cikin haki da fusgar numfashi yace.

“Shima Malam Jameel manyan mune suka bamu kwangilar kashe sa Saboda shine mutum na farko daya buwayi al'ummar mu da wa'azi wanda yake zama sanadin da matasanmu da yawa suke Musulunta shiyasa manyan mu suka bamu umarni shi da Moddibo mu ha?a su mu kashe su shine abinda zai fi mana sau?i da kwanciyar hankali idan ba haka ba zasu janye mana ra'ayi da tunanin matasan mu”.

Dafe kai Sheikh Jabeer yayi tare da cewa.

“Innalillahi wa'inna alaihi raji'un”.

Cikin tashin hankali Moddibo ya dafe kansa tare da fa?in.

“Hasbunallahu wani'imal wakin".

Sai kuma ya koma ya zauna yana dafe kansa da hannun ?aya yayinda ?aya hannun kuma ke tallabe da Khausar cikin ka?uwa yace.

“Ana zaton wuta ama?era sai gata a masa?a ina zaton kashe J akayi tunda aka kamasa na tabbatar cewa magautane acikin kashe sa amma duk atunanina  akwai sa hannun ?aya daga cikin Yadikkonsa ashe babu su Astagfirullah Allah na tuba ka yafe min da zargin da Nai ta yiwa Hajia Turai da Karima Allah na tuba”.

Cike da rauni da tausayinsa Khausar ke zubda hawaye, shi kuwa Modibbo cikin rauni ya cigaba da cewa.

“Manzon Allah (S.A.W)da kansa yace _Azzhana zhambu Walau kana ha??un_ sai naje na nemi yafiya da gafarar Hajiya Karima saboda duk tunanina ko ita ko Hajiya Turai akwai sa hannun ?aya daga cikinsu a?acewan J ashe suma ba abinda suka sani wa?an nan kafiran ma?iya Allah da Manzonsa suka sa aka kashe min J ?ina”.

Sosai Sheikh Jabeer yasa aka azabtar dasu suka fa?i duk laifinsu daga nan aka tura su waje na daban aka killace su domin jiran yanke musu hukunci.

Jalal kuwa nan take ya tura Modibbo video da yayi musu na cikekken bayanansu da sukayi.


Sheykh Jabeer kuwa da kansa ya tara su Abualeey yayi musu cikekken bayanin, ya ?ara da cewa, sai yazo ?aurin auren su Dr Jameel shi da kansa zai yiwa Ummi da Abban Jameel dukkan bayani.


Aranan ?arfe goma dai-dai na safe suka kama hanyar tafiya Membila da rakiyar motoci na musamman.


?arfe hu?u dai dai ya musu acikin garin Gembilan...



No comments