Sakayyah Book 2 Page 8

                       
By



     *GARKUWAR
MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... page 8*




 



               Na



*Aysha Aliyu Garkuwa*



 



*Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa.*
Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko
ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko
Æ´an manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. BuÉ—ewar
gaba, domin har budurwa infection na iya buÉ—ata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani
yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko
kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da
kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban 
lissafa. Sune manyan alamomin infection.



Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman
kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari
kiji illolin infection wato cutar sanyi.



Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin
kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi
bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiÉ—a ta
lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya
Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk
tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki
nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.



KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA
BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya
dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da
zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki
magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji
sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta
gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai
kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic
infection ne yar uwa.



INFECTION set É—inmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara,
Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar
komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin
infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar
infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin
set É—in na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha kala uku na tsarki É—aya na
shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in
akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita
tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki,
idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu
musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na
muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin
yasa ina raba rabin set É—in in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set É—in 10k ne.
Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA
ALIYU GARKUWA, ki turo kuÉ—inki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na
09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau
kika tura kuÉ—inki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan É—aÉ—É—aya.
Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso
in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada
kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.



 



 



Da sauri ya juya baki ɗayansa kana ya nufi hanyar ƙofar
masallacin ta waje yana ida fita yaga anja motar dake gefe ta wajen masallacin
antafi dashi cikin sauri ya sanya hannunsa duka biyu ya dafe kansa yana
maimaita duk wata addu'a da tazo bakinsa.



 



Batare da yace Uffan ba ya juya kansa ya nufi cikin hotel
cikin raunin murya yace.



“Meyesa idanuna ke yimin gizo yau kuma J É—ina nake gani”.



Haka yaci gaba da mgnar zuci har ya shiga É—akinsa.



Baki É—aya abin ya fara bashi tsoro anya kuwa bai far zaucewa
ba. Ya ƙare mgnar zuci tare zamewa ya zauna bakin gadon.



 Wayoyinshi guda biyu
dake gefen jakarshi ya ɗan juya ya kalla sabida jin ƙaramar tana ruri.



 Hannunsa yasa ya
zarosu, duk da kiran ya katse. Numfashi mai sanyi ya fesar ganin tarin miss
call É—in Abba, Innayi, Ummi da Malam ArÉ—o ahankali ya fesar da numfashi tun da
yabar masauƙinsa na Abuja gaba ɗaya mancewa yayi da wayoyin suna cikin jaka bai
buÉ—e ba sai yanzu da yaji kiran. Da sauri yayi picking call É—in Abba da ya sake
shigowa.



Cikin sanyin yayi sallama tare da cewa.



“Barka da dare Abba”.



 



“Barka dai Aliyu ya gajiyar hanya tun É—azu nake ta kiranka,
shiru”.



Cikin lumshe ido yace.



“Alhamdullah Abba phones É—in ne suna cikin jaka”.



Ajiyar zuciya Abba ya sauke cike da kulawa yace.



“Amma to ya hanya”.



Murmushi Moddibo yayi kana yace.



“Lafiya lau hanya Alhamdulillah Abba gashi har na isa nayi
sallar maghariba, yanzu wanka zanyi kafin sallar Isha'i ta gabato”.



Jinjina kai Abba yayi kana yace.



“Alhamdulillah ahuta gajiya amma kafin nan ka kira Innayi da
Malam ArÉ—o da kuma Ummin ka dan hankalinsu ya kwanta”.



Kai ya gyaÉ—a cikin alamun gajiya yace.



“Toh Abba Insha Allah zan kira”.



 



“Wanne hotel ka sauÆ™a”.



Abba ya tambaya.



 



ÆŠan guntun numfashi ya fesar tare da cewa.



Sofitel Mouley Youssef na sauÆ™a Abba dan naga  Hotel yanada Kekkyawan tsari kuma a binciken
da nayi naga yafi kusa da Companyn' namu”.



Cikin gamsuwa Abba ce.



“Sosai ma kuwa, anan kusa da shine ma gidana yake inda nake
sauÆ™a in nazo. Kaima dan ba'a gyarashi bane shiyasa”.



MiÆ™e tsaye yayi da wayar saÆ™ale  a kafaÉ—arsa yace.



“Amman yanada tsada kam”.



Shi kuwa Abba gyara zama yayi tare da cewa.



“Ka zauna anan zuwa lokacin da za'a gyara gidana dake nan
bayan hotel ɗin ƙadan, sai ka koma can, zan turo maka mai gadin gidan zai zo ya
kawo maka key ɗin motar da zaka rinƙa zirya dashi, zai kuma nunnuma maka duk
abubuwan da suka dace”.



cikin gamsuwa yace.



“Toh Abba sai yazo”.



Daga nan sukayi sallama.



Yana katse kiran yayi dearling number Innayi lokacin da
kiran ya shiga Innayi na kan Sallaya bayan ta idar da sallan maghariba tana
ganin kiran tace Alhamdulillah kana ta É—aga tare da kaiwa kunnenta tace.



“Moddibo”.



Lumshe Idanunsa yayi tare da komawa yayi bakin gadon ya
kishingiÉ—a kana yace.



“Na'am Innayi”.



Ajiyar zuciya ta sauƙe cikin sanyin murya tace.



“Fatan ka isa lafiya?".



Kai ya gyaÉ—a kana yace.



“Lafiya lau Alhamdulillah”.



Numfashi ta fesar kana tace.



“Masha Allah cikin Rabat kake ko kuma  cikin gefenta kake?”.



Cikin alamun gajiya yace.



“A'a cikin Rabat nake a tsakiyar garinma kuwa”.



Kai ta gyaÉ—a cikin sauke numfashi tace.



“Wace Unguwar?”.



Hannu yasa tare da shafa sumar kansa kana yace.



“Tsetse amman a hotel ne”.



Kai ta jinjina tare da sauke numfashi tace.



“Ayyah Tsetse kuma kai bansan Unguwar ba”.



Ware ido yayi tare da miƙewa daga kishingiɗar da yayi da
mamaki yace.



“Dama to kinsan Rabat ne bare kisan Unguwannin su?”.



Cikin sauri ta girgiza kai kana tace.



“Um-um bansani ba amma ban taÉ“a jin sunan bane”.



Ahankali yace.



“Ayyah yanzu ina so inyi wanka ne”.



Kai ta gyaÉ—a cike da kulawa tace.



“Toh shikenan ahuta gajiya”.



Daga nan ya kira Ummi da Malam ArÉ—o bayan sun gama gaisawa
ya shiga toilet, da ido yabi  turaren
wanka Maclean brush towel pich colour yana kallo komai na ciki sabone Anutse ya
fara wankan lokaci ɗaya yaji tsikar jikinsa na miƙewa sabida wanirin sanyin na
ratsa baki É—aya ilahirin jikinsa, cikin sauri yaja dogon tsaki Aransa kana
yace.



Anya wannan aljanar yarinyar zata bar rayuwata ta nitsu
kuwa, yarinya sai mata da nacin tsiya.



Towel ya janyo ya É—aura kana ya É—aura alwala ya fito dai-dai
lokacin aka kira sallar Isha'i jikin Dressing mirrow ya nufa ya shafe jikinsa
da mai kana ya fesa turare sa masu daɗin ƙamshi kana ya buɗe jakarsa ya ciro
Jallabiya Sky blue me taushi kana ya ɗaura hirami kamar ɗankwali ya riƙe farin
carbin sa sosai yayi kyau tun da aka sace M Jameel aka kashe sa bai sake yin
wankan daya nutsu irin na yau ba yana fita ya nufi Masallaci akayi sallar
Isha'i ana idarwa yayi adduo'i kana sai da aka wawwatse kafin ya fito ya nufi
cikin  Æ™oÆ™arin shiga ya haÉ—u da mai gadin
na fitowa.



 



Kallonsa mai gadin yayi cike da girmamawa yace.



“Aliyu Youssef Mouley?”.



Ya faÉ—in sunan da sigar tambaya tare da duba hoton Modibbo
da Abba ya tura mishi ta whatsapp.



Kai Modibbo ya haÉ—a mishi tare da bashi hannu.



Cikin fara'a mutum miƙo hannunsa tare da cewa.



“Assalamu alaikum Yah Mouley”.



Rumtse ido Modibbo yaui domin tunowa da Jalaladdeen ne kaÉ—ai
ke kiransa da wannan suna. Sai kuma ya ƙara rumtse idanun da ƙarfi, sabida
tunowa da tsawon lokacin da baiji motsin Jalaladdeen ba, tun kafin a sace. Jameel,
ya tabbatar babban abune kaÉ—ai zai iya ritsa Jalaladdeen da har zai iya hanashi
nemansu na tsawon wannan lokacin.



Cikin sauri ya buÉ—e idanunsa tare da gyaÉ—a tsayuwarsa yana
jan Carbin hannunsa jin Mutumin na cewa.



“Sunana Habibullah nine mai gadin gidan Alh Bashir kuma nike
kanshi in yazo duk inda zaije nike kaishi kuma nida matata ke zaune a BQ É—in
gidan”.



Kai Modibbo ya gyaÉ—a masa tare da cewa.



“Eh Abba ya gaya min”.



Jinjina kai mai gadin yayi tare da cewa.



“Ganan abinci  na kawo
maka”.



Kallonsa Moddibo yayi da mamaki yace.



“Abinci kuma?”.



Kai mai ya gyaÉ—a alamar Eh.



Jinjina kai Moddibo yayi tare da kallon womers É—in hannunsa
yace.



“Toh daga ina aka samu abincin?”.



Murmushi mai gadin yayi kana yace.



“Ai akwai abokin Alh anan lokacin da Marigayi Jameel yazo
har ya koma daga can ake kawo masa abinci”.



Lumshe idanu Moddibo yayi cikin sanyi yace.



“Ayyah yayi kyau angode”.



Sannan yayi gaba, mai gadin kuma na biye dashi.



 



Bisa kujerar ya zauna shi kuwa Habib kai tsaye dining area
ya nufa kana ya ajiye mishi É—an kondon da kulolin ke ciki, kana ya dawo
gabanshi tare da miƙa mishi key ɗin mota tare da cewa.



“Ga wannan da ita zamana fita, in kuma baka son draving ga
number'n ta sai ka Kur'ani, zanzo in kaika duk inda kakeso”.



Ya ƙare mgnar tare da miƙa masa hannunsa alamun ya bashi
wayarsa ya saka mishi number's.



Wayar ya miƙa mishi ba tare da yace komai ba.



Shi kuwa Habib number's sa ya sawa wayar Modibbo kana ya
miƙa mishi.



Amsa yayi tare da ajiye wayar.



Shi kuwa Habib sallama yasa kana ya miƙe ya ficee.



 



Shi kuwa Modibbo a hankali ya miƙe jin yadda cikinsa ke ƙugi
alamun yunwa.



Dinning table ya nufa, kujerar yaja ya zauna tare da zuba
abinci kana ya fara ci bayan ya gama ne ya dawo falon.



 



Lumshe yayi  dearling
number Abba.



Bayan Abba ya ɗaga sun sake gaisawa ya sauƙe Ajiyar zuciya
tare da cewa.



“Toh Abba yanzu me ake ciki idan Allah yakai mu gobe dame
dame za'a fara?”.



Kai Abba ya Girgiza cikin yanayin sanyin muryarsa yace.



“A'a Moddibo gobe kam ka huta tun da kaga yau  Alhamis gobe kuma jumma'a ne ba aiki a Æ™asar
tasu dan jumma'a da asabar ne ranakun hutun ƙarshen makonsu, shiyasa dama naso
yau ka tafi ka kwana ka huta gobe ma huta sai jibi lahadi in Allah ya yarda
zaka fara zuwa Company”.



Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.



“Toh shikenan Abba Allah ya kaimu”.



Ameen Abba ya amsa kana sukayi sallama.



 



MiÆ™ewa yayi akan kushin É—in ya lumshe Idanunsa  a hankali yayi miÆ™a da alamun gajiya
kasancewar yayi doguwar tafiya sannan dan kusan wuni yayi a zaune, da fari  akan Æ™arfe tare jirginsu zai tashi. Ashe tun
dare sun mishi text sun caza lokacin tashin sun meda sai biyu zasu tashi bai
ganiba, saida yazo Airport É—in, shiko yanaga komawa ciki wani jidaline shiyasa
ya zauna anan kawai.



To hakan ne yasa ya wuni a zaune, shiyasa gaba ɗaya gaɓoɓinsa
ciwo suke masa ahankali ya gyara kwanciyar sa still Idanunsa na lumshe cikin
sauri ya miƙe kana ya tashi ya zauna numfashi mai zafi ya fesar, tsaki yaja
kana ya miƙe tare da nufar ƙofan Falon ya fita yana mgnar zuci Mayya
jarabebbiya nan É—inma sai kin adaddabeni.



 



Ahankali ya tsirawa coumpund É—in  ido zuwa wajen ganin yanda fitilu suka haska
wajen kamar rana komai na hotel É—in abin burgewane da ban sha'awa ne ahankali
ya fara taka step ɗin farandar yana sauƙa kallon dattijon mai gadin dake zaune
daga can wurinsa ya nufa,



Duk da tarin motocin dake wurin Hausa wurin ya cunkushe ba,
yayinda kuma kowa harkar gabansa yake.



Hannu ya mikawa tsohon tare da yi mishi sallama.



Cikin tsananin girmamawa tsohon ma ya bashi hannu tare da
zuba mishi ido cikin ƙare masa kallo.



Shi kuwa Modibbo a ya buÉ—e bakinsa tare da É—an É—aga sautin
muryansa yanda zaiji yace.



“Baba”.



Miƙewa Dattijon yayi tare da da ɗan rusunawa kana ya ɗan ɗaura
hannunsa na dama kan kirjinsa tare da É—an sunkuyawa cike da tsananin girmamawar
da ta fara bawa Modibbo haushi ya za'ayi dottijo kamar wannan yake kishi haka,
in Habib ya mishi haka zai iya amsa sabida ya girmeshi.



Numfashi ya fesar tare da É—an sakin fuska jin dottijon na
cewa.



“Na'am Alh ya aka yi?”.



Gyara tsayuwar sa yayi kana yace.



“Baba kana zaune kai kaÉ—ai ne?”.



Kai Dattijon mai gadin ya gyaÉ—a kana yace.



“Eh Alh gacan abokan aikina yanzu sune a bakin gate, ni sai
da safe zan koma can kuma, yanzu anan nake”.



Ya ƙare mgnar yana buɗe wani mutun da yazo shiga, saida
mutumin ya shiga kana ya kuma rufewa.



Girgiza kai Moddibo yayi yana kallon kalimin Dattijon
numfashin ya fesar tare da cewa.



“Sunana Aliyu Youssef Muhammad Mouley, daga Nigeria amma
kakata tana kirana da Moddibo zaka iya kirana Modibbo”.



Jinjina kai Dattijon mai gadin yayi yace.



“Ayyah Alh yayi kyau”.



 



Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe cikin sanyin murya yace.



“A'a ba sai kace min Alh nan ba ka kirani da sunana kawai”.



Kai ya gyaÉ—a yana jinjina karamcinsa Aransa yace yana nan
kamar ƙaninsa Ibrahim Youssef Muhammad Mouley. Ibrahim bashi da girman kai sai
dai shi Ibrahim yafi wannan dariya afili kuma sai yace.



“Toh Moddibo”.



Murmushi Moddibo yayi kana yace.



“Yawwa ai yafi sannan kuma akwai abinci da aka kawo min so
naci yamin yawa, kaje ka É—auka mana sai kaci sabida kada ya lalace!”.



Cikin tsananin mamaki da ganin tsananin karancin Dottijon ya
haɗa kai, tare da amsar key ɗin ɗakin da Moddibo ke miƙa masa, cike da yarda
aminci yace.



“Ngd Ngd matuÆ™a Modibbo, Allah ya kara girma ya kare zuriyar
Mouley baki É—aya”.



Gyara tsayuwa yayi tare da girgiza kai yace.



“Amin Ya Allah”.



Gefensa mai gadin yabi kana yace.



“Bari na É—auka to”.



Ya faÉ—i tare da nufar cikin, cikin nitsuwa Modibbo yabi
bayanshi.



Yana shiga falon ya dauko Warmers din sannan ya fita.



Cike da girmamawa Moddibo yace.



“Toh saida safe Baba”.



Mai gadin na fita yace.



“Allah ya tashe mu lafiya ahuta gajiya”.



Sannan ya fice.



 



Ahankali Moddibo ya rufe ƙofar falon tare da kashe wutan
falon da Ac kana ya nufi Bedroom É—insa Kallon AC bedroom din yayi jin kamar
yayi mishi yawa ne yasa hannun ya É—auki rimot É—in kana ya rage gudunshi.



 



Kwanciya yayi akan gadon tare da lumshe Idanunsa cikin sauri
ya buÉ—e Idanunsa tare da dafe Æ™asan 
lokaci É—aya zuciyarsa da jikinsa sunka harba a tare, baki É—aya ya
fahimci wannan muguwar yarinya haka zatayi ta addabar rayuwarsa kenan.



awannan rana dai haka ya kwana cikin wani irin yanayi bacci
rabi da rabi yayi.



Washe gari Jumma'a haka ya wani cikin hotel din sai sallan
jumma'a da ya fita ana isarwa ya dawo, daga nan ko  bakin titin hotel É—in bai leÆ™aba.



 masallaci ne kaÉ—ai ke
fitar dashi.



 



Hakan yayi kwana biyu yana hutawansa.



Yau Lahadi a bisa tsarin ƙasar Marocco yau ɗin ne forkon
sati.



 Æ˜arfe takwas ya samu
Moddibo acikin Company Abba bisa jagorancin Habib.



 Yana isa suka fara
aiki gadan-gadan aiki ake tako ina babu kama ƙafar yaro domin dama sa hannunsa
kawai ake kira da sahalewarsa a matsayinsa na mataimakin MD duk sabbin Injina
da aka kawo aka shiga daddasasu da duk wasu gyare-gyare daya kama suka shiga yi
domin samun asabunta Company da habaƙashi don har buga atamfofi, Laces,
Mayafain laffaya da duk sauran abubuwan buÆ™ata suke so  farawa.



Domin shine Company na farko da aka buÉ—e sa acikin Rabat
wanda aka haɓakasa sannan ake inganta kayyakinsu.



Bai bar cikin Company ba sai shida saura kwata kai tsaye
masauƙin ya wuce yana isa yayi Hong mai gadi ya buɗe masa gate yana Parking
suka gaisa.



 



Kana ya wuce yayi ciki. kai tsaye Bedroom ya wuce ya watsa
ruwa kana ya É—aura alwala ya fito Masallaci kasancewar ankira Maghariba bai
fito ba saida akayi Isha'i kafin ya dawo yaci abinci da Habib ya kawo masa. bayan
ya kammala ya É—auko system É—in sa ya tura Abba duk yanda sukayi tsare-tsaren
abubuwan da kuma hotunan yanda abubuwan suka tafi sosai yayiwa Abba bayanin
sannan Abba ya kara masa haske akan sauran abubuwan sai misalin shaÉ—aya ya
tashi yana jin wani irin kasala bini-bini zaiyi miƙa tare da hamma kai tsaye
toilet ya nufa ya watsa ruwa.



 Anutse ya fito tare
da kumtsaawa, kana ya kwanta akan gado tare da lumshe idanunsa tsikar jikinsa
na tashi sanyin AC da ƙamshin Roomfreshner da kuma ƙamshin tularensa shi yasake
haddasa masa jin wani masifaffen kasala cikin wani irin yanayi ya ƙudundune
tamkar yaro lokaci É—aya bacci yayi awon gaba dashi.



A hankali yake juye-juye yana mai jin da ganin abin kamar a
mafarki kamar kuma a zahiri.



Kanshi longwaɓar cikin narkekkiyar murya yace.



“Zakeeh kasheni fa”.



Cikin tsoro tace.



“Ana asped Yah Mu'allim”.



Kai a jujjuya mata tare da cewa.



“Kije keda Allah, kiyi ta dakon zunubi, kina sane dai in har
ban yafe mikiba cikin fushin Allah zaki kwana”.



Da sauri ta ƙara kwaɓe fuska, tare da cewa.



“Dan Allah Yah Mu'allim kayi haÆ™uri ka yafe min, nayi maka
al'ƙwari ina nan tafe zanzo gare cikin aminci da rakiyar amintattu a ranar nayi
al'ƙawarin gujewa fushin Ubangiji a ranar kada ka ɗaga min ƙafa ka mallaki
dukkan Æ™udurinka”.



Wani irin mataccen murmushi yayi tare da cewa.



“Yaushe ne ranar?”.



Da sauri tace.



“Nan kusa take”.



Wani irin kallo yayi mata tare da cewa.



“Ranar yaushe ce”.



A hankali tace.



“Raanar larabace ce”.



Cikin wani irin kallo yace.



“Na'amin ce, tunda al'Æ™awari kikayi”.



Cikin sauri ta miƙe ta nufi toilet cikin mawuyacin hali ya ɗago
idanunsa dake cike da feeling kana muryarsa na rawa yace.



“Pleaassss Hayatieee kada ki saÉ“a min al'Æ™awarin dan idan
kika saÉ“a min a wannan ranar”.



Girgiza kai Khausar tayi cikin kuka da raunin murya tace.



“Bazaka mutuba”.



Amatuƙar galabaici ya yunƙura da niyyar binta tayi saurin
rufe kofar toilet.



 



Akuma dai-dai lokacin ya farka da wani irin azabebben kasala
dafe kansa yayi da hannu bibbiyu yayin da Idanunsa suka cika da ruwan hawaye
haka ya kwana cikin mawuyacin hali Allah ya sani ya fara ganin yarinyar  aljana.



 



Washegari da sassafe ya tashi yayi wanka kana ya shirya
cikin gezner fari ƙal da ya fito da ainihin kyawunsa Anutse ya fito falon
hannunsa riƙe da Breafcase a dining area ya tsaya tare da buɗe Warmers din da
Habib ya jere Wainar shinkafa ce da miyar taushe sai kuma soyayyan Arish da tea
Wainar yaci kana yasha tea bayan ya gama ya mike tare da É—aukar Breafcase É—insa
da wayoyinsa da kuma mukullin motarsa kai tsaye Company ya nufa.



 



 



Gembila



 



AÉ“angaren Abban sosai hankalinsa ya dan kwanta fahimtar
lallai Moddibo yana aiki gadan-gadan bisa tsari da hikima komai na tafiya
dai-dai.



Numfashi ya fesar tare da ciro wayarsa yayi dearling number
Malam ArÉ—o bayan ya dauka sun gaisa.



Abba ya sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.



“Yau kusan kwana shida kenan da zuwan mu gidan LamiÉ—o akan
maganar Aliyu da Khausar amma har yau bamuji ya sake neman muba amma tunda mu
muke da buÆ™ata yakama muji ta bakinsa”.



Ya gyara zamansa wayar akunnensa kana ya cigaba da cewa.



“Musamman ma da yanzu na tura Aliyu Marocco yana rayuwa shi
kaɗai ya kamata ace anyi ƙoƙari anyi batun auren nan saboda kaɗai ci da damuwa
zaiyi masa yawa”.



Jinjina kai Malam ArÉ—o yayi cike da gamsuwa yace.



“Nima abinda nake tunani kenan amma Insha Allahu gobe zamuje
da daddare idan Allah ya kaimu rai da Lafiya”.



Ahankali Abba ya jingina bayansa da jikin kujeran kana yace.



“Toh Allah ya kaimu bisa rai da Lafiya”.



Ameen malam ArÉ—o ya amsa kana suka katse kiran.



 



 *Jauro Yaya*



 



Hajja Nana ce zaune ta tanƙwashe ƙafafunta Baffa Garga dake
gefenta yayi Murmushi yana kallonta yace.



“Addah Nana É—azu nayi magana da Hammadu”.



Kallonsa tayi tare da kawar da kai gefe tace.



“Ya masa kyau”.



Murmushin Baffa Garga ya faÉ—aÉ—a yana kallon yanda tayi
kicin-kicin da fuska sassauta murya yayi kana yace In gaishe ki”.



Taɓe baki tayi ba yabo ba fallasa tace.



“Idan ya damu da gaisuwar ai sai yazo inda  nake”.



Gyara zama Baffa Garga yayi kana yace.



“Addah Nana ai yace ma zai zo In sha Allahu gobe da safe
zaiyi sammako yazo”.



Sassauta fuskarta tayi kana tace.



“Toh Allah ya kawo shi lafiya”.



Ameen Baffa Garga ya amsa tare da É—auko mata wani hiran.



 



Washe gari:Asuban fari Baffa Jimeta yayi sammako ya É—auko
hanyar Taraba duk da sammako da yayi sai ƙarfe biyar da rabi ya isa Jauro yaya
Aka shiga gaishe-gaishe da tambayar juna koda wasa bai kawowa Hajja Nana
maganar Khausar ba sai bayan sallar Isha'i bayan sun ci abinci sun zauna da
mahaifiyarsa da kuma Kawunnansa ana hira.



 



Ahankali ya gyara zamansa kana ya tanƙwashe ƙafafunsa
agabanta ya karyar da wuyarsa cikin sanyin murya yace.



“Hajja Nana alfarma nake nema awajenki”.



Kallon second ukun tayi masa kana tace.



“Ni kuma wace alfarma zanyi maka ai da har ina da abinda
zaka nemi alfarma awajena Umarni na zaka bi”.



Ahankali ya sassauta muryarsa yace.



“Ai yanzu ma Umarnin ki nake bi Hajja Nana Ni dai temako
nema”.



Kallonsa tayi kana tace.



“Taimako akan me?”.



Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin ƙasa da kansa yace.



“Taimako akan Marainiyar Allah”.



Baki ta buɗe tare da kallon ƙannenta sai kuma ta kallesa tace.



“Ai kowa ma Maraya ne sannan kowa ma zai iya kasancewa
Maraya”.



Kai ya gyaɗa yana kallon yanda take jijjiga ƙafa yace.



“Eh nasani amma akan Khausar nake magana Hajja Nana nazo ne
in sake Baki haƙuri akan laifin data aikata sannan muyi mata uzuri matsayinta
na yarinya Æ™arama”.



Kai ta gyaÉ—a ba yabo ba fallasa tace.



“Shikenan komai ya wuce tunda Ni ban kaiba Ni kaka ce kun
nuna min bani da matsayi sannan banida ikon faÉ—a aji”.



Da sauri Baffa Jimeta ya kalleta amma baice komai ba ta
cigaba da cewa.



“Acikin maganar rayuwar Khausar to ba matsala na cire
hannuna ta Auri duk wanda taga dama take so Ni bani da damuwa aciki na janye
hannu na tunda haka kuke buÆ™ata”.



Numfashi Baffa Jimeta ya fesar cikin kwantar da murya yace.



“Toh shikenan kiyi haÆ™uri ki sanya Albarka aciki”.



Taɓe baki tayi kana tace.



“Zansa al'barka ai tunda bazan sa tsinuwa ba Ni dai babu
bakina aciki sannan babu batub aurenta da wancan É—an gaba da fatihan kam”.



Kai ya girgiza cikin sassauta murya yace.



“Mu dai kiyi haÆ™uri dan Allah kiyi haÆ™uri kiyi mana fatan
alkhairi aciki”.



Ahankali ta kallesa kana tace.



“Toh Allah ya kyauta ya kiyaye gaba dama maganar data kawo
ka kenan??”.



Cikin sauri ya girgiza mata kai kana yace.



“A'a bashi bane ya kawoni kewar ki nayi shine nace bari nazo
in gaisheki”.



Hararansa tayi tare da kallon sauran ƙannenta tace.



“Oho dai”.



 



Akuma dai-dai lokacin Malam ArÉ—o,Malam Ahmad da Abba ne
zaune afalon LamiÉ—o bayan sun gaisa sannan suka yimasa jawabi kan cewa sunji
shiru shiru bai sake neman suba yasa suka dawo.



Anutse LamiÉ—o ya gyara zama cike da dattako yace.



“Badamuwa Insha Allahu dama nima ina shirin zan ne meku É—in
saboda bani da ikon bada ita akaran kaina amma munyi magana da Baffan yarinya
yau É—in nan ma yazo daga can Adamawa zai nemi sahalewar kakar yarinya”.



Ajiyar zuciya suka sauƙe atare Kallonsu Lamiɗo yayi kana ya
cigaba da cewa.



“Dake Itace taso kawo tangarÉ—a acikin al'amarin amma yace
zaiji da lamarin duk abinda ake ciki yace min Insha Allahu gobe muyi ƙoƙari
muje gamu gashi gata ya zama na munje neman Auren ne”.



Numfashi Malam Ahmad yafesar kana yace.



“To ai wannan duk mai sauÆ™i ne badamuwa za'ayi hakan”.



Kai Abba ya gyaÉ—a kana tare da faÉ—in.



“Bakomai Insha Allah goben zamuje”.



Murmushi LamiÉ—o yayi cike da kamala yace.



“Eh zamu bari gobe idan munyi sallar Azahar sai muje kafin
nan ya tattauna da mahaifiyarsa idan anyi sa'a abin zai zo da sauƙi dake shi
yana da kyakkyawar fahimta sannan bashi da son zuciya”.



Jinjina kai Malam ArÉ—o yayi idanunsa akan LamiÉ—o yace.



“Ba matsala Insha Allah nima ina da Æ™afa agarinsu dan Malamin
dana ke zuwa ɗaukan karatu awajensa ai ƙanin Kakarta ce kuma sunzo wajena tare
shima nasan yana da kawaici, kara da dattako”.



Jinjina kai sukayi tare da tsaida magana akan washe gari
Bayan Sallar Azahar zasu tafi.



 



Washe gari baki É—ayansu suka shirya har Mommy da Khausar
LamiÉ—o yace su shirya atafi dasu Khausar da Mommy suna motar LamiÉ—o Malam ArÉ—o
da Malam Ahmad suna motar Abba kai tsaye suka dauki hanyar Jauro yaya suna isa
Jauro yaua kai tsaye gidan Hajja Nana suka nufa dai-dai lokacin dasu Baffa
Jimeta suka fito daga sallar La'asar Malam Liman na ganin Malam ArÉ—o ya faÉ—aÉ—a
fara'ar fuskarsa kana yace.



“A'a Malam marhaban lale sannunku da zuwa”.



Baffa Jimeta kuwa cikin sauri ya nufi Lamiɗo tare da miƙa
masa hannu yace.



“A'a Sannunku da zuwa har kuzo kenan?”.



Murmushi LamiÉ—o yayi cikin yanayin dattako da kamalarsa
yace.



“Eyyy sosai ma ai ba'a bori da sanyin jiki”.



Abba dake tsaye jikin mota yace.



“Aikam dai ba'a Bori da sanyin jiki”.



Baffa Garga da fitowarsa daga masallaci kenan yace.



“A masha Allah harda 
Alh Usman mai Dala ne a Lallai sannun ku da zuwa maraba maraba ku
karaso?”.



Ya faɗa tare da shigewa gaba kasancewar yanzu shine ƙarami
tun bayan rasuwar Baffa Umaru yana shiga ciki yace.



“Addah Hajja abamu taburmai munyi baÆ™i”.



Miƙewa tayi daga zaune da take da murmushi afuskarta ta ɗauko
taburmai ta miƙa masa karɓa yayi kana ya shimfiɗa musu Abaranda.



 



Daga ciki tace.



“Aaa baÆ™i mukayi sannunku da zuwa sannunku”.



Tana ƙoƙarin fita Khausar da Mommy Kuma na kokarin shiga
Atake fara'ar dake fuskarta ya gushe Harara ta watsawa Khausar sai kuma ta
maida kallonta kan Mommy tace.



“A Aysha kune atafe?”.



Kai Mommy ta gyaÉ—a kana tace.



“Eh”.



Sannan suka shiga cikin dakin mazan kuma Baffa Garga ya
shimfida musu taburmai daga waje.



Koma ciki Hajja Nana tayi tare da ɗaukan ƙwaryar nono da
ƙorron soyayyan Zabbi da aka yiwa Baffa Jimeta na zuwansa ta kalli Khausar dake
gefen Mommy zaune haÉ—e fuska tayi babu walwala atare da ita tace.



“Toh fitsararriya uwar fitsararru zoki kai musu abin taÉ“awa
kin zauna kina zare ido sai kace wata ta Allah rasa kunya É“erar tanka”.



Uffan khausar bata ce mata ba ta miƙe ta ɗauki Ƙorran ta
fita ta kai musu sannan ta dawo wani ƙorron Hajja Nana ta miƙa wa Mommy kana
tace.



“Aysha Bismillah”.



 



Kallon yanda tayi kicin-kicin da fuska Khausar tayi taɓe
baki tayi cikin tsira mata ido tace.



“Hajja Nana Ni kar inci ne?”.



Harara ta watsa mata kana tace.



“Duk yanda kika ga dama kiyi”.



Ware ido Khausar tayi ta kalli Hajja Nana data kawar da kai
gefe murmushi tayi cikin sanyin Murya tace.



“A'a Idan kada inci sai inbar miki kayanki”.



Baki Hajja Nana ta taɓe kana tace.



“Oho cikin ko nawa 
fitsararriya Mara kunya mai ido atsakar ka”.



 



Fuska Khausar ta É“ata ta buÉ—e baki da niyyar magana Mommy
tayi saurin É—aga mata hannu alamar kada tace komai hakan yasa ta tsuke bakinta
Mommy kuwa kindirmon ta É—aga ta burga kana tasa sugar.



 



Daga waje LamiÉ—o yace.



“Khausar fito mana ki burga mana Nonon”.



Kai Baffa Garga ya Girgiza kana yace.



“Ba matsala bari na burga muku”.



Murmushi LamiÉ—o yayi kana yace.



“A'a bari dai ita É—in tazo ta burga mana”.



Miƙewa Khausar tayi tare da ɗaukan goran zuwa ta fita ta
burga musu Nonon kana ta zuba musu zumar sannan ta miƙe ta koma ɗaki bayan sun
gama taɓe taɓe an sake gaisawa Lamiɗo ya kalli Baffa Jimeta cikin sassauta
murya yace.



“Toh Alh Muhammadu Hausawa sunce maso É—an tsun-tsu shike
binsa da jifa, mun zo wajenku neman yafiya, afuwa da kuma alfarma sannan da
neman iri domin nima ina cikin Æ´an neman Auren ne”.



 



Cikin sauri Baffa Jimeta yayi dariya kana ya girgiza kai
tare da kallon LamiÉ—o yace.



“Haba LamiÉ—o ba zamuyi haka da kaiba ai kai mai bada Auren
Khausar ne baka cikin masu neman aure kana cikin masu bada Auren Khausar ne”.



Murmushi LamiÉ—o yayi cike da jin daÉ—in karancinsu yace.



“Nagode da karamci”.



Gyara zama Baffa Jimeta yayi da murmushi afuskarsa yace.



“Ka cancanci fiye da hakan LamiÉ—o”.



Jinjina kai Baffa Liman yayi cike da kamala yace.



“Ai mu saidai muyi addu'a da fatan alkhairi amma kaine mai
bada Khausar”.



Cikin jin dadi yace.



“Nagode da kawaici Allah yasaka da alkhairi”.



 



Gyara zama Malam ArÉ—o yayi da murmushi afuskarsa yace.



“Toh mu mun yarda mun amince mune masu neman Aure”.



Abba dake Kallonsu ya faÉ—aÉ—a Murmushin fuskarsa kana yace.



“Mune masu neman aure da kuma neman iri agareku bisa cika
wasiyyar da É—ana ya bari ina fatan zan samu sauki da haÉ—in kanku wajen cikawa É—ana
burinsa koda bayan ransa kamar yanda ya faÉ—a min”.



Ya ida maganar cikin rauni idanunsa na tara ƙwalla.



 



Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauke cike da tausayawa yace.



“Bakomai Alh Bashir Insha Allah babu abinda zai gagara aida
mu daku duk mun zama É—aya LamiÉ—o yamin bayanin duk abinda ke tafiya kan cewa
wasiyya ce daga wajen danÆ™a marigayi Jameelu”.



Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa hawaye na cigaba da
taruwa akwarmin Idanunsa.



Cikin sanyi Baffa Jimeta ya cigaba da cewa.



“Insha Allah bazai gagara ba zamuyi Æ™oÆ™ari amma yanzu kuyi
haÆ™uri da al'amarin tsohuwa in Allah ya yarda babu abinda zai gagara”.



 



Ajiyar zuciya LamiÉ—o ya sauke tare da gyara zamansa yace.



“Allah Ubangiji yasa haka mukam ma da gwaÉ“in mu muka zo duk
da cewa akwai tsoro atare damu amma muna da kyakkyawan yaƙini akanku hakan yasa
kafin muzo muka taho da gishiri da goro na neman izini”.



Murmushi Malam Liman yayi yana kallon LamiÉ—o yace.



“Lallai kuwa zamu barku da Hajja Nana ku fafata”.



Zare da ido LamiÉ—o yayi tare da sanya dariya kana cikin
sauri yace.



“Na tuba ayimin afuwa ai Hajja Nana saiku zakuji da ita”.



 



Gyara zama Malam Liman yayi cike da nutsuwa yace.



“Insha Allah itama munyi Æ™oÆ™ari mun samu ta É—an sauko amma
duk da haka akwai karin É—an lokaci da za'a bayar”.



 



Anutse Mommy ta gyara zamanta tare da kallon Hajja Nana
cikin sanyin murya tace.



“Dan Allah Hajja Nana kiyi haÆ™uri abinda ya kawo mu nazo ne
in baki haƙuri naga kin tafi ranki aɓace abinda Khausar ta aikata ba laifi na
bane ba kuma da yawuna bane”.



Ta ida maganar Muryanta na rawa tamkar zata fashe da kuka.



Hajja Nana kuwa jin yanda Muryan Mommy ke rawa yasa tayi
saurin Kallonta har ranta take Jin Mommy domin alokacin zamansu tasan bata da
matsala cike da kulawa tace.



“Kar kiyi kuka Aysha aina zauna dake nasan halinki fitsaran
Khausar ba daga gareki bane kuma ba daga Allah bane halitta ce da tayiwa
kanta”.



Cikin sauri Khausar ta É—ago kanta ta watsa mata Harara cikin
ƙasa da murya tace.



“Inma tsiwarce ai awajenki na gada”.



Harara Mommy ta watsa mata hakan yasa ta tsuke bakinta.



Ahankali Mommy ta sauƙe Ajiyar zuciya kana ta fuskanci Hajja
Nana cikin sassauta murya tace.



“Itama kanta Khausar al'amarin yazo mata adolene”.



Baki Hajja Nana ta taɓe kana tace.



“Bangane yazo mata adole ba inace soyayya take da wani can
yasa ta kalli tsabar idona tace bata son É—an Uwanta”.



Kai Mommy ta Girgiza kana ta kwashe duk yanda Khausar ta faÉ—a
mata sunyi da M Jameel aranan da aka sace sa kana ta daura da faÉ—in.



“Sannan kuma yaron shine Æ´an Kidnapping suka sace sa suka É—auresa
har ya rasu”.



Ahankali Khausar tayi ƙasa da kanta hawaye na taruwa
akwarmin Idanunta.



Cikin sanyi Mommy ta cigaba da cewa.



“Sai maganar tasa ta zama kamar wasiyya kuma ya roÆ™i alfarma
ya faÉ—awa kakar Amininsa Moddibo kana Ya faÉ—awa mahaifiyarsa da mahaifinsa
yanzu ma haka da mahaifinsa muka zo kuma yace alfarma yake nema ko bayan ransa
acika masa wannan burin nasa, jin haka yasa nima baki É—aya jikina yayi sanyi”.



Numfashi Hajja Nana ta fesar kana tayi ƙasa da kanta cikin
sanyin murya tace.



“Allah sarki shine akace ansace sa a daure sa ya rasu ko?”.



Asanyaye Mommy ta gyaÉ—a mata kai tare da faÉ—in.



“Eh shine aka sace aka É—aure har ya rasu”.



Jinjina kai Hajja Nana tayi tare da watsawa Khausar Harara
ta kalli Mommy cikin raunin murya tace.



“Ayyah Allah sarki Allah yajiÆ™an sa da rahma ina ma ace yana
raye dashi zan bawa Khausar ya aura wallahi koda Khausar bata auri Aliyu ba
bazan damu ba”.



Cikin raunin murya Mommy tace.



“Gashi kuma shi É—in Ubangiji bai nufa za ayi dashi ba, babu
gatan da zamuyi masa sai dai addu'a”.



Jinjina kai Hajja Nana tayi cikin sanyi tace.



“Sosai ma”.



Mommy kuwa sassauta murya tayi kana tayi ƙasa da kanta tace.



“Kuma inda hali mu samu mu cika masa wasiyyar daya bari”.



Gyara zama Hajja Nana tayi tare da kallon Khausar da kanta
ke ƙasa kana ta kalli Mommy nunfashi ta fesar cikin sanyin murya tace.



“To aini bani da tacewa acikin wannan maganar sai abinda
iyayenta suka faÉ—a tunda annuna min bani da iko da ita”.



 



Dai-dai lokacin Baffa Jimeta ya shigo Anutse ya zauna
gefenta ya tanƙwashe ƙafafunsa kana ya fuskanceta da kyau yace.



“Kina da iko da ita mana muma kam mu aike kike da iko damu
amma ana neman alfarma awajenki gacan Baban yaron ma awaje sai hawaye yake
zubarwa yana neman alfarma acikawa dansa wasiyyar sa”.



Daga waje ta jiyo sheshsheƙan Kukan Abba cikin sauri ta miƙe
ta nufi ƙofa ta fita kusa dashi ta zauna cike da tausayawa tace.



“Kuka kuma kake Alh Bashir?”.



Cikin sheshsheƙa Abba yace.



“Ya za ayi ba zanyi kuka ba burin da Jameeluna da kuma fatan
da yake so yana tangarɗa koda aranan da muka rabu na ƙarshe yace min shine
babban burinsa daya rage aduniya”.



Cikin zubda hawaye ya cigaba da cewa.



“Yace babban burinsa yaga Moddibo yayi Aure kafin nasa
Saboda Aliyu yana buƙatar mace yana buƙatar ayi masa Aure sai dai Allah bai
nufa Jameelu na zai gani ba ina tsoro saboda bani da damar da zan cika masa
wasiyarsa”.



Gyara zama Hajja Nana tayi kana ta gyara É—aurin dankwalinta
ta sunkuyar da kanta ƙasa kana ahankali ta ɗago Muryanta na rawa tace.



“Na amince ina dai dan nice. To acikawa yaron nan burinsa
Allah yajiƙan sa da rahama na amince Ayi aure...



 


No comments