Sakayyah Book 2 Page 7

 

                        
By




      *GARKUWAR
MARUBUTA**SAKAYYAH book 2 page 7*



          Na



*Aysha Aliyu Garkuwa*



 



Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin
gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin.
Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya,
melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. BuÉ—ewar gaba,
domin har budurwa infection na iya buÉ—ata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi
al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin
wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma
saduwa, da dai sauran abubudann ban 
lissafa. Sune manyan alamomin infection.



Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman
kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari
kiji illolin infection wato cutar sanyi.



Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin
kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi
bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiÉ—a ta
lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya
Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk
tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki
nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.



KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA
BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya
dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da
zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki
magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji
sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta
gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai
kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic
infection ne yar uwa.



INFECTION set É—inmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara,
Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar
komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin
infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar
infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin
set É—in na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki É—aya na
shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in
akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita
tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki,
idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu
musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na
muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin
yasa ina raba rabin set É—in in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set É—in 10k ne.
Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA
ALIYU GARKUWA, ki turo kuÉ—inki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na
09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau
kika tura kuÉ—inki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan É—aÉ—É—aya.
Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso
in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada
kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.



 



 



 



Khausar kuwa cikin sanyi da rauni tunowa da M Jameel da ya
dawo mata sabo ahankali ta kife kanta abakin gado tafashe da kuka mai cike da
fargaba da kuma tsoron Allah.



Kallonta Mommy tayi cike da tausayawa tace.



“Kiyi haÆ™uri ki daina kuka Khausar addu'a zaki yiwa  Jameelu sannan Insha Allah za acika masa
burinsa da wasiyyar daya bari in Allah ya ya nufa”.



Ta ƙare mgnar tare da sauƙe numfashi.



 Idanta ta tsaida kan
Khausar da har zuwa lokacin kanta ke kife jikin gado cikin tausasawa tace.



“Amma kisa Aranki cewa haÆ™uri zakiyi da duk rayuwar da
zakije ki tarar, sannan wasiyya zaki cikawa Jameel, sannan ki sani shi zaman
Aure kansa Ibada ne, koda ana son juna wata ran akanji babu daÉ—i, bare ke da
dama kin san matsayinki a wurin wanda kike ganin kina da ƙarfin guiwar zama
dashi,



  dan haka kisa Aranki
cewa ba lallai ne kiji daÉ—in zama da Moddibo ba, amma tunda kince kinji kin
gani zakiyi abinda Jameel ya buƙata kafin barinsa duniya zan biki da addu'a
Ubangij ya tabbatar da al'khairi tunda har iyayensa duk ya gayawa kuma tuni
suma sun sa baki a mgnar, kinga ni bani data cewa tunda kun mamayeni”.



Cikin rauni Khausar ta sake fashewa da sabon kuka tabbas
gaskiya Mommy ta faÉ—a ba Lallai tayi zaman daÉ—i da Moddibo ba tunda baya sonta
hasalima koda kallonta ne baya sonyi tuno da hakan yasa wasu hawaye masu
masifar zafi suka zubo mata tama sani tabbas cikin uƙuba zata rayu dashi, to
amman ya zatayi rayuwa Yah Jameel al'ƙawarin amincewa da batun auren Amininsa.



 



Cikin sanyin murya Mommy ta cigaba da cewa.



“Sanin bake kaÉ—ai Jameelu ya barwa wasiyya ba yasanarwa da
Kakar Moddibo sannan ya sanarwa Umminsa da kuma Abbansa nima da farko hankalina
ya tashi.



Amma yanzu barina É—akin Abbanku yake cemin shekaran jiya da
daddare Abban Jameel da Malam Ahmad da malam ArÉ—o sunzo da batun, abinda yasa
baiyi mgnar ba Hajja Nana bata bashi dama bane daya mata bayani”.



Wani irin rauni, Kunya,damuwa da rasuwar Jameel ne suka
dawowa Khausar alokaci É—aya.



Cikin sanyi jiki ta miƙe ta nufi ɗakinta tana shiga ta faɗa
kan gadonta kana ta cigaba da kuka cikin rauni tasan dai iyaye keyiwa Æ´aÆ´ansu
auren dole a tarihin duniya, sai gashi ita dai itace zatayiwa kanta da kanta
auren dole bisa wasiyar Yan Jameel malami na musamman mai matsayin babban Yaya
wanda ita dai da fari har ranta shi takeyiwa kallon mai iya jiɓantan lamuranta.



 



Washe gari da safe Misalin ƙarfe 8:00 Anutse Moddibo ya fito
daga falonsa cikin wani É—anyen Boyel Sky blue Fuskarsa tayi fayau manyan
Idanunsa dake lumshe sun sake girma sabida ramar da yayi, sajensa ya sake
yawaita yayi fadi da cika, yana kuma É—an hargitse alamun an kwana biyu ba'a
gyarashi.



Kafadarsa na dama rataye da jakar laptop É—insa daga zip É—in
gefen wayoyinsa ya zira, sai hannunsa dake riƙe da jakar kayansa, a hankali
yake tafiya, yayinda jikinsa ke fitar da sanyayyan ƙamshin tularen sa.



Kai tsaye sashen Innayi ya nufa ahankali Innayi dake
breakfast ta ɗago Kai ta kallesa Anutse ya ƙarasa tare da zama gefenta.



Da mamaki take Kallonsa ganin kamar alamar cikin shirin
tafiya yake.



Cikin sauri tace.



“Aliyu”.



Kallonta yayi da sauri domin bata fiye kiransa da Aliyu ba
sai da babban dalili.



Cikin sanyin murya yace.



“Na'am Innayi”.



Hannunta riƙe da kofin tea tace.



“Ya haka? ya na ganka kamar mai yin tafiya?”.



Kai ya gyaɗa mata tare da tanƙwashe ƙafafunsa kana ya
fuskanceta cikin ƙoƙarin danne damuwarsa kana yana mai jin farin cikin zai bar
garin Gembila haka nan ya tsinci kansa da jin farin cikin yau dai zai bar Jahar
Taraba domin baki É—aya garin ya fice masa arai cikin sanyin murya yace.



“Innayi ba kama bace tafiyar ce”.



Cike da mamaki ta É—ago kanta kana tace.



“Aliyu tafiya zaka yi amma ban sani ba sai dai in ganka kana
fita da jaka haka?”.



Ahankali ya riƙo tafin hannunta acikin nasa cike da mmkia
yace.



“Kiyi haÆ™uri Innayi tafiyar ce nima tazo min a bazata
kuma  ba jiya Abban Jameel ya gaya
mikiba”.



 



Kai ta girgirza tare da cewa.



“A'a bai gaya minba zakayi tafiya ba, ya dai cemin yana
neman al'farma ni kuwa nace umurni kawai zai baka kamar yadda yake bawa Jameel
ni na amince duniya da ƙiyama, ban bari yamin bayaniba sabida kar yaga kamar
zan hanaÆ™a yaji ba daÉ—i. To waima Tafiya zuwa ina zakaje?”.



Cikin kwantar da murya yace.



“Tafiya zuwa Marocco!”.



Cikin tsananin kaÉ—uwa ta zaro idanunta baki É—aya lokacin É—aya
ta Æ™ware tare da fara tari sakamakon Æ™warewa da tayi da dankalin dake bakinta”



Moddibo kuwa ganin yanda ta ƙware yasa yayi saurin daukan
kofin ruwa ya miƙa mata tare da cewa.



“Sannu”.



Amsa tayi tasha amma still tarin bai tsaya ba lokaci É—aya
Idanunta yayi ja zufa ya shiga tsats-tsafo mata agaba É—aya ilahirin jikinta shi
kuwa Modibbo ido ya zuba mata tare da jera mata sannu da kuma É—an bubbuga
bayanta kaÉ—an-kaÉ—an yana mmkin wasu al'amuran a ranta domin ya sani tsawon
zamansu da J ta hanashi zuwa Marocco wanda bai san me dalilntaba, kasancewar sa
ba mutum ne mai yawan bincikeba yasa bai taɓa mata musuba ko bincike.



Ahankali ya ke mata sannu cike da tausayawa takai kimanin
minti biyar kafin tarin ya lafa sannu Ahankali ta fara maida numfashi.



 



Tana sauƙe ajiyar zuciya ta juya ta kallesa kana tace.



“Marocco!!!! kuma Aliyu?”.



Jinjina kai yayi cikin sanyin murya yace.



“Eh Innayi Marocco zanje amma idan har kin amince, idan
bakya so, bazanje ba sai in bawa Abba haÆ™uri”.



Ahankali ta gyara zama tare da fuskantar sa da kyau kana
tace.



“Toh amma mai zakaje kayi a can?”.



Tayi tambayar zuciyarta na mai cigaba da bugawa da ƙarfi.



Lumshe Idanunsa yayi tare da sauƙe Ajiyar zuciya kana yace.



“Abba ne ya nemi al'farma da Inje in kula da Company'nsa
sannan kuma jiya daya zo nayi tunanin kunyi cikekkiyar maganar ne dashi kafin
ku shiga wurina, shiyasa ni ban faÉ—a miki ba, ya nemi taimako da Inje in
taimaka masa akan batun Company sa buga Abaya, jallabiya, Carpet, Sallayu
blanket's da dai sauransu”.



Kallonsa kawai Innayi keyi yayin da take ji tamkar zuciyarta
zai fito saboda yanda yake bugawa.



Cikin sanyi Moddibo ya riƙe Hannunta dake cikin nasa yace.



“Akwai sabbin injinan aiki da za'a sauÆ™e na Company,  sannan kuma za'a fara aikin dasa Injina  za'a kakkafa toh akwai É“uÆ™atar sa ido da kuma
kula da abubuwan,  amma Insha Allah bazan
wuce wata biyu zuwa uku ba zan zo Innayi”.



 



Girgiza kai tayi tare da jingina bayanta da jikin bango ta
lumshe Idanunta kana ta shiga maida numfashi.



 



Moddibo kuwa ido ya zuba mata kana Asanyaye yace.



“Amma Innayi idan har bakyason Inje zan kira Abba in FaÉ—a
masa yayi haÆ™uri”.



Uffan bata ceba kana bata buÉ—e Idanunta ba daga ita sai
Ubangiji kaÉ—ai suka san mai take tunawa aranta takai kimanin minti biyar ahaka
kafin ta É—ago Idanunta ta kallesa kana taja dogon numfashi ta sauÆ™e tare  da sakin Murmushin mai tarin ma'anoni  sannan tace.



“Bazan hanaka tafiya ba Aliyu, domin ko baka tafi yanzu ba,
dama lokacin tafiyar ya ƙarato. na amince kayi masa duk kan abinda Jameelu zai
masa daya kasance araye, domin hakan zai rage masa raÉ—aÉ—in ciwon rashin
Jameelu”.



Kai Modibbo ya gyaÉ—a yana kallon yanayin fuskartar ahankali
yace.



“Toh shikenan Insha Allah zanyi hakan”.



 



Innayi kuwa kallonsa tayi kana cikin sanyin murya tace.



“Amma yanzu-yanzu tafiyar kenan Aliyu?”.



Kai ya gyaÉ—a kana yace.



“Eh Innayi zanbi jirgi zuwa Abuja ne, in naga komai biza na
ya fito zan wuce”.



Jinjina kai tayi tare da cewa.



“Shikenan Ubangiji Allah ya sanya alkhairi Allah ya tabbatar
da alkhairi sai nazo”.



Saurin Kallonta yayi cike da Mamaki yace.



“Sai kinzo kuma?”.



Sunkuyar da kanta ƙasa tayi tare da Girgiza masa kai kana
tace.



“Mantawa nayi sai ka dawo nake son cewa".



A hankali ya zaro ATM É—inshi na Zenith Bank daga
al'jihunsa,  cikin tafin Hannun ta yasa
matashi kana a hankali yace.



“Ga ATM É—ina na Zenith Bank, kin san pin number É—in, akwai
kuÉ—i a ciki kusan 5 Million”.



Da sauri tace.



“Ina ka samosu?”.



Gyara zamanshi yayi kana yayi mata bayanin yadda sukayi da
Abba sannan ya É—aura da cewa.



“Akwai wasu a wurina, wannan ki riÆ™e kiyi dukkan abinda kike
buƙata kafin in dawo, in haɗasu muyi ƙoƙarin barin garin nan, domin ya fita
raina”.



Yayi mgnar yana tuno kalaman Hajja Nana ita kuwa Innayi cike
da sanyi tace.



“Uhmmm Aliyu in Sha Allah kamar ma mun barima ai kama barin
kai kam”.



Cikin sanyi ya jinjina



Kai tare da miƙewa yace.



“Toh shikenan Innayi amma dai bakiyi fushi dani bako?”.



Da sauri tace.



“La la la Aliyu banyi fushi da kaiba”.



hannunta ya riƙo tare da ɗaurawa a kanshi kana yace.



“Toh kuma baki samin Albarka ba”.



Cikin sanyin Murya tace.



“Allah yasan ya Albarka Ubangiji ya tsare gabanka da bayanka
Allah maidakai lafiya ya kuma tsareka da lafiyarka, Ubangiji ya rabaka da
sharrin duk kan abin Æ™i walau mutum ko aljan ko 
wani irin abune ya *Tsareka da Tsoffin magauta ya hanasu ganeka bare
cutar da kai kafin isarka tushenka”.*



Lumshe Idanunsa yayi kana yace.



“Ameen ya Allah Innayi ni zan tafi”.



Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.



“Toh ka tsaya bari na zo".



Kai ya gyaÉ—a sannan ya tsaya É—aki tashiga ba daÉ—ewa ta fito
sanye da hijabi, suka nufi  wurin
motarsa,



“Yau innayi zafa ki koma gidan Abba ko Ummi dan zamani ke É—aya
a nan bai minba”.



Cikin sauri tace.



“Eh toh gsky k nima ina tsoro Ni kaÉ—ai a nan to amman, gsky
gwara min gidan Ummin Jameel kaga ita kamar É—iya take a gareni gidan Abba kuwa
ba wani sabawa nayi da matansa ba, amman can zamu zauna É—akin Asma'u nasam
Malam Ahmad kuma baida matsala”.



Cikin gamsuwa da haka yace.



“Gsky kam hakan yafi, zan gaya Abban in kin gama haÉ—a
kayanki Asma'u zata zo ku tafi”.



Kai ta jinjina cikin gamsuwa tace.



“Ba laifi”.



Jingina yayi da jikin motar bayan yasa jakarsa gefen mai
zaman banza.



Ita kuwa Innayi a hankali ta matso kusa da marfin motar zira
hannunta tayi ta ciki, zip É—in jakarsa tabuÉ—e tasa jim kaÉ—an kuma ta maida ta
rufe kana sukayi sallama ya mota ya tafi.



 



Kai tsaye gidan Ummi Moddibo ya nufa cikin nutsuwa yake
Driving yayin da yake sauraran ƙira'ar Ahmad Sulaiman cikin suratul An'am yana
isa gidan Ummi yayi Parking aƙofar kana ya fita ya shiga coumpund ɗin yana
tafiya ahankali yana ɗaura ƙafarsa akan farandar sautin muryar Khausar ya ratsa
Dodon Kukensa cikin sauri ya tsaya tare da rumtse idanunsa.



Sabida jin yadda tsikar jikinsa ya fara tashi tun daga tafin
ƙafarsa har tsakiyar ƙwaƙwalwan kansa, ahankali ya jingina bayan sa da jikin
bango yayin da zuciyarsa ta shiga bugawa da kaso Cassa'in da tara cikin É—ari.



 Aransa yakeji kamar
ya koma domin gaba É—aya ya rasa meke sashi shiga wani yanayi da zaran yaji
sautin Muryanta zaiji tamkar ana tsikara masa allura yama rasa ta wani irin
yanayi zai misalta yanda yake ji akan yarinyar shin kunyarta yake ko kuma
tsoronta yakeji, ko shakkarta shi kansa ya kasa tantancewa, taune Lip É—insa na
ƙasa yayi da ƙarfi tare da buɗe idanunsa da suka sauya launi kana ya tura ƙofar
falon tare da sallama yana mai tsare fuska.



 



Ummi dake zaune ta tsira masa ido tare da cewa.



“Babana har ka shirya kenan?



Kai ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.



“Eh Ummi”.



Kana ya zauna agefenta ya zamana yana facing É—in kichen.



Kallonsa Ummi tayi cike da kulawa tace.



“Amma dai ba kayi breakfast”.



Kai ya girgiza kana yace.



“Uhm-Uhm”.



Da Mamaki tace.



“Toh ya za'a ayi ka tafi da 
yunwa ba zaiyu ba Babana ba zaka tafi da yunwa ba”.



Langwaɓar da kai yayi tare da Marerece murya yace.



“Ummi bana jin yunwa fa”.



Fuska ta É“ata kana tace.



“Bafa zaiyu ba Babana baza ka tafi da yunwa ba”.



 



Khausar na fitowa daga kichen ta girgiza kai tare da kallon
Asma'u tace.



“Toh ni zan tafi sai anjima”.



Da mamaki Asma'u ta kalleta kana tace.



“Bangane ba kamar ya sauri kike?



Dama ba nan kika zoba ne?”.



Khausar kuwa kai ta girgiza tare da kallonta kana tace.



“A'a ba nan nazo ba dama gidan Aunty RuÆ™ayya naje to da naje
sai na sameta tare da baƙi shine na kira Mommy nace zan ƙaraso nan mu gaisa.



 Mommy kam  cewa tayi wai da safiyar nan zanzo”.



Moddibo kuwa tunda yaji sautin Muryanta akusa dashi ya kasa É—auke
idanunsa akanta duk da cewa kallon Kasan ido yake mata.



Cikin sanyi Khausar ta cigaba da cewa.



“Toh shine nace tayi hakuri ba daÉ—ewa zanyi ba shine fa tace
inzo amma kada in daÉ—e saboda mune da aikin rana zan koma in ta yata nazo muyi
wata mgna ce, kuma nafasa”.



Da sauri Asma'u tace.



“Dan Allah muyita”.



Kai ta jujjuya tare da cewa.



“Ba damuwa in kin samu dama kizo zamuyita, yanzun sauri
nake”.



Ta ida maganar tare É—ago kanta.



Idanunta ne suka sauƙa cikin idanun Moddibo.



 Atsorace ta zira
Idonta cikin nasa tare da juya su acikin nasa wanda hakan ya zama kamar
hararansa tayi ita kuma cikin mamakin yadda ya rame ya wani zama shiru, ne yayi
matuƙar bata mamaki da tausayi domin da dane da tuni ya danna mata harara.



Cike da tsoro ta janye kwayar idanunta daga garesa, tana mai
mamakin sauyinsa rayuwa, cikin wani irin sauri ta nufi ƙofar falon yayin da
jikinta ke tsuma Muryanta na rawa tace.



“Ummi ni na tafi”.



Kallon yanda ta nufi ƙofar Ummi tayi kana ta kallo Moddibo
da har zuwa lokacin idanunsa ke ƙasa da mamaki tace.



“Ya da sauri kamar kinga Dodo?”.



Kai ta girgiza batare data juya ba tace.



“A'a Ummi nikam na tafi”.



Cike da kulawa Ummi tace.



“Toh ki tsaya Kiyi breakfast mana”.



 



Kai ta girgiza still jikinta na tsuma tace.



“A'a Ummi Allah Mommy na za tayi faÉ—a idan na daÉ—e”.



Jinjina kai Ummi tayi kana tace.



“Toh shikenan nagode 
ki gaida Mommy ki gashi kin ki kitsaya kiyi breakfast”.



Da sauri tace.



“Allah Ummi sai da nayi breakfast agida kafin na fito”.



Kai Ummi ta gyaÉ—a kana tace.



“Ki gaida Mommy naki da Raudat dasu Haiydar”.



Cikin sauri ta fice daga falon bayan tace zasuji.



 



Moddibo kuwa ahankali ya jinginar da kansa da jikin kujeran
tare da lumshe Idanunsa kana ya cije Lip ɗinsa na ƙasa, sai kuma yayi saurin buɗesu
sabida ganin surar jikinta da yayi ziraran miraran.



Gashi  da zaran yaji
muryan yarinyar zai riƙa jin wani irin abu mai wuyar fassarawa kana lokacin da
ƙwayar idanunsu suka haɗu babu abinda suka hango masa face.



Ƙirjinta tamkar zasu tsole mishi idanu.



Asma'u Mommy tasa ta kawo masa É—an waken da sukayi sai ruwan
Tea ba laifi yaci danwaken da É—an dama kana yasha ruwan Tea.



Malam Ahmad ne yashigo tare da yi masa addu'ar Allah ya
tsare miƙewa yayi ya fita kana yaja tsohuwar motarsa zuwan gidan Abba yana isa
yayi Hong mai gadi ya buÉ—e masa Parking Yayi aharabar gidan kana yashiga sashen
Abba bakinsa É—auke da sallama ya shiga falon Cike da kulawa Abba da Hajiya
Turai dake zaune gefensa suka amsa masa.



 



Anutse ya ƙarasa tare da zama gefen Abba cike da kulawa Abba
yace.



“Aliyu ka Æ™ara so?”.



Jinjina kai Moddibo yayi cikin sanyin murya yace.



“Eh Abba ina kwana ya Æ™arfin jikin”.



 



“Jiki da sauÆ™i Aliyu”.



 



Bayan sun gama gaisawa Abba yayiwa Moddibo duk kan wasu
bayanai kana ya bashi wasu takardu da duk wani abu daya kamata sai da Abba ya
masa bayani.



Ajiyar zuciya Moddibo ya sauƙe kana yace.



“Toh Abba ni zan tafi”.



Ahankali Abba ya sanya hannu a aljihu tare da ciro key mota
sabo dal Æ™iran PRADO  ya miÆ™a Masa tare
da cewa.



“Ga wannan Aliyu za'a kaika Airport dashi, in Manu driver ya
dawo kuma gidan ku zaije ya ajiye maka ita”.



Cikin sauri Moddibo ya É—ago kansa tare da Kallonsa.



“Abba mota kuma?”.



Kai Abba ya gyaÉ—a masa alamar eh.



Cikin sanyi Moddibo ya sake kallon key motar kana yace.



“Abba to ai ina da mota”.



 



Ajiyar zuciya Abba ya sauƙe kana yace.



“Uhm-Uhm Aliyu kenan. ÆŠan Allah kada kayi min gardama ka karÉ“a
kawai ka sanya albarka aciki”.



Sunkuyar da kai Moddibo yayi batare da  da yace Uffan ba.



Kallonsa Hajiya Turai tayi kana tace.



“Ka karÉ“a mana Aliyu ai yanzu kam an zama É—aya”.



Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.



“Toh shikenan Abba Nagode Allah yasaka da Akhairi Ubangiji
Allah ya mayar maka da dubunsa”.



Murmushi Abba yayi kana yace.



“Ameen”.



Nan take ya ɗauko takardun motar ya miƙa masa tare da cewa.



“Jiya mukayi magana da Alhj Abubakar nasa ya kawo min da
yamma gatanan lafiyarta Æ™alau anyi mata dukkan abinda ya dace”.



Jinjina kai Moddibo yayi kana yace.



“Nagode Abba Allah yasaka da alkhairi ni zan tafi”.



Ahankali Abba yace.



“Allah ya tsare Aliyu Allah ya bada abinda akaje nema”.



Ameen ya amsa kana ya miƙe Abba ya rakasa da kansa ya buɗe
masa bayan motar ya shiga, sabuwar motarsa sosai motar ta burgesa duda bai wani
damu da bakin abuba, amman collor bakin yayi masifar kyau dan sai sheƙin
sabunta takeyi,



Manu ne ya shiga yaja motar suka fita.



 Kai tsaye gidan Malam
ArÉ—o ya wuce dashi bisa umarninsa.



Sallama yayi masa kana daga nan suka É—auki hanyar da zata
sadasu da cikin Taraba Jaligo ja gari na Baba Abasu babban birnin Gembila kenan
wanda kuma tsakanin local government ɗin nasu zuwa cikin ƙwaryar birnin Taraban
tafiyace ta musamman.



Koda suka isa cikin Taraba, basu tsayaba suka nausa hanyar
Adamawa Yola.



 



Jauro yaya



Baffan Liman ne zaune agaban Hajja Nana cikin sanyi murya da
ladabi yayi ƙasa da kansa tare da cewa.



“Hajja kiyi haÆ™uri bai kamata ace kina fushi akan abinda bai
kai ya kawoba, wannan al'amari ba wani al'amari mai girma bane bai kamata ace
ki É—auki zafi akansa har haka ba”.



Kallonsa kawai Hajja Nana keyi tana girgiza ƙafa tare da
girgiza kai.



Ajiyar zuciya Baffa Liman ya sauke kana ya cigaba da cewa.



“Idan kin lura Khausar fa jika ce agareki ba Æ´a bace, kinga
kuwa duk ikon ka akan jika yana zama mai rauni, bare wannan zamanin da muke ya
bambanta dana baya dan Allah Addah Hajja kiyi wa wannan al'amarin Kyakkyawan
fahimta”.



Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.



“Na lura sannan na fahimci Liman da kai dasu Garga, Sadu,
Jauro baki É—aya bakin ku É—aya akan al'amarin Khausar tun da haka kuka ce ni
bani da abinda zance kuje kuyi duk yanda kuka ga dama”.



Ahankali Baffa Liman ya É—ago ya kalleta kana ya sake
sunkuyar da kansa.



Cikin alamun É“acin rai ta cigaba da cewa.



“Amma fa kusa ni ba zata Auri wannan yaron ba, tunda har ta
iya buÉ—e baki ta kalli tsabar idona tace bata son. Aliyu jikina kuma É—an Uwanta
toni babu hannu na akanta kuyi mata yanda take so amma banda Auren mara tushe
da asali”.



 



Gyaran murya Baffa Garga yayi kana yace.



“Dan Allah Addah Hajja kiyi haÆ™uri shikansa. Muhammadu
Jimeta yace zai zo amma yafi so yazo ya sameki cikin farin ciki kada akan batun
Khausar ranki ya dinga É“aci abanza a wofi”.



 



Fuska ta É“ata tare da Kallonsu É—aya bayan É—aya kana tace.



“Idan yayi niyyar zuwa yazo idan kuma baiyi niyyar zuwa ba
yayi ta zama tunda shi kansa bayanta yake bi, tun da wai har cewa yake bazai yi
mata dole ba”.



 



Baffa Liman ya sake sassauta muryarsa yace.



“Dan Allah Addah Hajja kiyi haÆ™uri ki bi lamarin asannu da
izinin Ubangiji komai zai dai-dai-ta amma bama son ganinki cikin damuwa”.



Haka suka riƙa Rarrashinta tare da kalamai masu kwantar da
zuciya.



 



Acan É“angaren Moddibo kuwa tafiya tsakanin  Taraba da Yola tafiya ce mai zaman kanta sai
dai bata wuce awa biyu zuwa uku,  tuÆ™i
Manu keyi cike da ƙwarewa ga samun sabuwar mota.



 



Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da sassayan numfashi.



Sabida ji yake wani irin yanayi yana lullubeshi gaba É—aya
tunanin J É—in sa ya dawo masa ji yake tamkar idan ya juya gefen damansa zai ga
J É—in sa, ahankali ya zira  hannunsa ya
kara volume din ƙira'ar da yake ji acikin Suratul Nisa'i, sai kuma ya koma baya
ya jingina bayanshi da jikin Seat É—in.



Domin idan har ba karatu yake jiba ko kuma yake yi sam baya
taÉ“a samun nutsuwa, saidai kuma ta wani É“angaren haka nan  yake jin wani irin farin ciki da yabar garin
Gembila, ji yake tamkar yabar wani yanki da yake da tarin ƙunci, ji yake tamkar
yabar wani waje mai duhu da zafi ji yake tamkar ana zare ransa da ruhinsa daga
waje mai ƙunci da azaba, kana kamar ana nufar dashi awaje mai tarin nutsuwa da
salama yakeji.



 Domin tun bayan
rasuwar Amininsa garin Gembila tayi masa zafi da ƙunci kana tayi masa duhu baya
kallon haskenta gaba É—aya ya tsani garin, to dama Meya rage masa da garin
Innayinsa ce kaÉ—ai sai kuma Ummi dasu Asma'u.



 



Sai Misalin ƙarfe biyu da rabi ya shiga cikin Adamawa suna
isa cikin  Adamawa.



Manu yayi Parking A dai-dai Masallacin jum'ae dake cikin
Atiku Abubakar shopping mall É—insu nan 
sukayi Al'wala sukayi sallar Azahar Kasancewar hanya zai kama, É—an
tafiya yasa a gaba shiyasa yayi niyar Æ™asaru 
ya haÉ—a da sallar La'asar domin karfe uku dai-dai jirginsu zai tashi.



Baya jin zai iya cin wani abu haka yasa ya kalli Manu cikin
mutuntaka yace.



“Manu sannu da yunwa”.



Cikin girmamawa Manu yace.



“Laa ba komai ai kafin mu fito ma naci abinci”.



Kai ya jinjina kana yace.



“Muje ka kaini cikin Airport É—in, sai kayi sauri ka juya,
kada kayi dare a komawa”.



Cike da gamsuwa Manu yace.



“Toh”.



Daga nan ya kaishi Airport sannan shi kuma ya fito, ya É—an
samu abin da ya taɓa kana ya kama hanyar komawa Taraba, Gembila.



 



 



Ƙarfe uku Dai-dai jirginsu Modibbo ya tashi daga Adamawa
zuwa birnin tarayyar Nigeria Abuja.



 



 



Alhamdulillah cikin kwanaki huÉ—u bizi'nsa  ya fito da yake business bisa ne ba wuya.



Alhamdulillah ranar Al'hamis da misalin ƙarfe biyu dai-dai
jirginsu ya É—aga daga Abujam Nigeria.



 Zuwa Rabat babban
birnin ƙasar Marocco kenan



 



A hankali ya fesar da wani irin zazzafan numfashi dai-dai
lokacin da tayun jirginsu ke raɓuwa da ƙasar Nigeria, rumtse idanunsa yayi da
karfi sabida wasu irin zafafan hawaye da yaji 
suna tsastsafo mishi ta cikin dukkan jijiyoyin idanunsa.



Wani irin yanayin da bai taɓajiba duk tafiye-tafiyen da
yakeyi yaji yana dabaibaye rayuwarsa haka kawai yakeji kamar ya bar kasar kenan
bari na har abada.



Lokaci É—aya tunanin Jameel ya dawo masa, wanda hakan yasa
yayi saurin jingina bayansa da kujerar jirgin.



Yana mai jin wani irin sassayan kuka na taso mishi daga can
cikin ƙahon zuciyarsa, hakanne yasa ya fara karatun Alqur'ani mai girma a
hankali.



 



Yayinda mutanen cikin jirgin kuwa kowa keta hidimar gabansa.



 



Shi kuwa Modibbo tunda ya zauna bai É—ago kansa ya kalli
kowaba.



Sabida yanayin da yakeji.



 



A hankali dai tafiya ta fara nisa, tuni sun kutsa cikin
sararin samaniya jirgi ya kama hanyarsa.



 



Koda akazo tambayarsu me yake buƙata.



Cewa yayi baya buƙatar komai.



 



A ƙalla sunyi tafiyar awa uku a sararin samaniya.



Zuwa yanzu kam mafi akasarin matafiyan kowa ya nitsu
hada-hadar ta ragu matuƙa, wanda zuwa lokacin kuma sauran musu 57 minutes su
dira cikin birnin Rabat sabida daga Abuja zuwa can tafiyar awa uku da minti
hamsin da bakwai ne cib-cib.



 



A hankali ya gyara zamansa tare da kallon farin matashi da
ya zo ya zauna gefensa wanda bazai wuce sa'anan ba.



Murmushi matashin yayi tare da miƙa masa hannun yana mai
mishi wani irin kallo mai cike da tambayo al'ajabi da kaÉ—uwa.



Shima É—an murmushin yayi tare da bashi hannu sukayi
musabaha.



“Jabeer bin Jabeer JoÉ—a. Wanda ya kira kansa da Jabeer É—an
Jabeer JoÉ—a É—in ya kare mgnar cike da masifar mamaki da zurawa fuskar Modibbo
idanu yana matuƙar mamakin kamanninsa.



Shi kuwa Modibbo cikin yanayin sanyi yace.



“Aliyu Youssef Muhammad Mouley”.



Cikin tsananin bayyanar mamaki ya zazzaro idanu waje tare da
juyowa garesa da kyau cikin alamu rawan jiki ya juya harshe zuwa larabci yace.



“Yah Salam toh kuma yaushe kazo”.



Cikin É—an sanyi Modibbo shima juya harshe ih zuwa asalin
amintaccen larabci yace.



“Nazo kuma? Nida Æ™asata, me zanje yi a Marocco dai zaka ce”.



Kai Jabeer bin Jabeer JoÉ—a ya jujjuya tare da juyawa yayi
mishi mgn da hausa yace.



“Kamar yaya Æ™asar kuma?”.



Ga mamakin Jabeer sai yaji Moddibon na bashi amsa da harshen
hausa.



“Sabida ni É—an Nigeria ne girman Nigeria”.



Da sauri Jabeer yace.



“A'a wannan ai ko makaho ya shafa yasan kai ba É—an Nigeria
bane kuma ma sunan da ka fadi ai ya isa shaidar inda ka nufa komawa zaka yi ba
zuwaba”. Ya Æ™are mgnar da iya haÆ™iÆ™anin gskyrsa da  rawan jiki.



Cikin ɗan ƙosawa da surutun sa Modibbo yace.



“To sabida me?”.



Da sauri Jabeer yace.



“Sabida kafi kama da Larabawa”.



 



“Toh gashi kuma kaima da larabawan kake kama”.



 



Gyara zama Jabeer yayi tare da cewa.



“Kuma ni dai ba fullatanine”.



A hankali shima Middibo yace.



“Minfu mi pullo”.



To zuwa yanzu kam mamakin Jabeer ya tsananta.



Ya buÉ—i baki da niyar zaiyi wata mgnar kenan aka kirashi a
baya bisa dukkan alamu Kakanshi  ne da
sauri ya tashi ya nufi can bayan.



 



Shi kuwa Modibbo a hankali ya fesar da numfashin gajiya da
surutun da Jabeer ya sashin.



Tare da fara karatun Alqur'ani mai girma.



 



Jim kaÉ—an da tafiya Jabeer sai gashi ya dawo zama yayi
bakinsa cike da tarin mgn to amman samun yana karatun Alqur'ani mai girma yasa
dole ya haÉ—iye dukkan rogowar mgnarsa da tarin tambayoyinsa.



 



A hankali Moddibon ya É—ago manyan idanunsa tare da kallon
taswirar kasar Rarat da suka iso tsakiyarta.



Wanda tuni an sanar musu.



Haka nan yake jin wani irin salama da kwanciyar hankali kana
da nutsuwa tunda suka shiga yankin ƙasar Marocco yake jin wani irin sanyi da
more happy Wanda har ya iya jure surutun Jabeer.



Numfashin mai sanyi ya fesar tare da ƙara ware manyan
idanunsa yana kallon garin ta window'n jirgin.



Haka nan yakeji tamkar yabar damuwarsa baki É—aya acikin
Nigeria ya kuma saki dukkan ƙuncinsa a cikin Taraba.



Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yake bin tsarin dogayen
benayen gidajen garin da kallo kana sassayan muryarsa na ratsa kunnuwansa yana
jin sautin karatunsa da yakeyi jikin suratul Kahf.



 



Misalin ƙarfe shida saura minti uku rak.



Jirginsu yayi sauƙar angulu a cikin babban Airport dinsu.



 Rabat Sale
international airport.



Wanda dai-dai lokacin kuma ya dire ayar ƙarshe ta Suratul
Kahf É—in tuni kuma jirginsu ya dai-dai-ta da'irar tsayuwarsa.



Da sauri Jabeer ya kalleshi sai kuma yayi sauri ya
mayar  kallonshi gefen damanshi ganin har
an buɗe ƙofar jirgin.



Juyowar da zaiyi kuwa sai ganin Middibo yayi a tsaye yana
jawo jakarsa daga drower dake samansu.



Da sauri ya miƙe shima, sai kuma yaji ana kiransa a baya, da
sauri ya nufi bayan.



Shi kuwa Modibbo agogon dake hannunsa ya kalla, da É—an
hanzarin sa ya nufi wajen sabida ƙaratowar lokacin sallan magrib.



 



A hankali ya fesar da sassayan numfashi, dai-dai lokacin da
ya taka step na forko wanda ya fito da kanshi sararin garin Rarat, duk da dai
duk Arfica ne amman ƙasar Marocco sunyi mana rata zarrama mai girma, sunada ci
gaba na musamman.



A hankali ya furta.



“Yah Salam”.



Sabida wani irin ni'imtaccen iskane mai cike da salama ke
ratsashi yana shiga duk ta inda hudar gashin jikinsa yake.



Wani rin amintaccen numfashin mai cike da yanayin sauƙe
ajiyar zuciya ya shaka, like É—an da ya daÉ—e baiga mahaifiyarsa ba, kuma yayi
kuka.



A hankali yaci gaba da taka steps din yana sauƙo ƙasa.



 



Wani saurin runtse idanunsa yayi lokacin da ya dire tafin
ƙafarsa kan ƙasar Marocco cikin yankin Rarat.



Wani irin tsuma yaji naman jikinsa nayi tun daga can cikin
jikinsa da zuciyarsa yakejiyo wani irin tsuma.



Wanda ya ta'allaƙa hakan da tsananin yanayin sanyin garin
ne.



“Alhamdulillah!!!”.



Ya furta a saman lips inshi sabida, tunda Allah ya halicce
shi bai taɓajiba irin yanayin da yakeji a yanzu, ko Saudia yaje bayajin yanayin
nan.



 



Yana mai shaƙar sassayan iskan garin ya fara bin ayarin
sauran matafiya.



Yayinda can gefen kuma manyan motocine na al'farma wanda
bisa dukkan alamun wani babba akazo É—auka.



 



Su kuwa a cikin yanayin gajiya suka ƙaraso inda masu tarɓarsu
suke.



 



ÆŠan dube-dube ya yayi.



Da sauri ya nufi wani Balarabe dake jingina da Taxi yana
riƙe da ɗan allon tarba wanda aka rubuta Aliyu Youssef Muhammad Mouley.



Yana isa yayi masa sallama.



Cike da tsananin girmamawa Balaraben yayi saurin buÉ—e masa
marfin motar tare da cewa.



“Marhababuka”.



Kai ya jinjina masa cike da gajiya da ƙosawa.



Yasan Taxi Abba ne ya turosa.



 



Da sauri shima ya shiga Taxi É—in kana yaja suka fita daga
cikin Airport É—in.



A hankali yayi miƙa tare da jingina bayansa da seat ɗin
dai-dai lokacin da suka ratso ta cikin unguwar Ben slimane.



Anƙuwace ta masu alfarma, haka yasa tsarinta na musamman ne.



haka nan yaji yanayin Weather yayi masa masifar daÉ—i da
kyau.



 



Gashi yanayin damuna ne Iska mai sanyi da ratsa jiki na kaÉ—awa
gashi duk ta inda ka wulga ido bishi yoyin dabinone masu kyan tsari ke
rausayawa sunyi kore shar dasu iska na kaɗawa suna rangaji ga kasar garin ajiƙe
yake alamun anyi ruwa.



 



Ƙarfe shida da minti sha biyar dai-dai mai Taxi ɗin ya juya
hancin motarsa kan wani gini mai kyau da É—aukan indo wanda a samansa aka
rubuta.



Belere Hotel Rabat.



Kai da ganin masifar kyau da tsaruwan hotel É—in kasan zaiyi
masifar tsada.



Cikin taushin murya ya kalli Balaraben dake riƙon.



Tare dayin mgn da larabcin.



“Muje wani wanda bai kaishi ba”.



Cikin sanin darajar aiki mai Taxi É—in ya É—an kalleshi ta
madubi tare da cewa.



“Toh".



Daga nan ya juya akalar motar ya É—auki hanyar da zata
sadashi da unguwar Sidi bettache.



Tafiya kaÉ—an sukayi suka fito kan babban titinsu.



Da sauri Modibbo yace.



“Masha Allah”.



Dai-dai lokacin da



 Idanunsa suka sauÆ™a
akan tamfatsetsen masha'hurin hotel mai masifar kyau da tsari daga can sama
tsololuwan ginin an rubuta.



Welcome to Sofitel Youssef Mouley hotel.



Da sauri yace.



“Tsaya mu shiga nan”.



Yayi mgnar still idanunsa na kan sunan hotel É—in da yayi
kama da sunanshi hakan don sunan hotel ɗin yaji yana son sauƙa a nan.



Murmushin mai Taxi É—in yayi tare da cewa.



“Toh ai wannan yafi wancan tsadama”.



Da sauri ya gyaÉ—a mishi kai tare da cewa.



“Eh shi yayi”.



 Ya Æ™are mgnar da
lumshe idanunsa jin sautin kiransan salla a masallacin dake cikin hotel É—in.



Haka yasa shima mai Taxi É—in saurin shiga.



 



 Numfashi mai sanyi ya
fesar tare da buÉ—e Idanunsa daya lumshe kana ahankali.



 



Wani irin hotel ne mai masifar kyau da tsari da girma duk da
cewa a farfajiyar akwai masallaci sai dai ba wani Babba bane, amma farfajiyar
babbe ne me kyau da tsari daga gefen dama wajen Parking din Motoci ne wanda
aƙalla zai ɗauki motoci settu zuwa saba'in da biyar kana daga jikin doguwar
kantamgar kuwa bishiyoyin kwakwane zagaye da ginin daga can gefe kuma wasu irin
flowers ne dake wadace  da damshin ruwa
haka yasa jikinsu sai sheÆ™i  kayi, tafiya
kaÉ—an zaka samu side É—in shiga Reception É—in.



  Atsakiya daga gefe
da gefe kuma hanya ce kana daga baya wani ƙaton gardin ne wanda yana iya hango
bishiyoyin dake ciki kana yana jiyo sautin kukan tsuntsaye kala da ban daban.



Ahankali É—ago daga jingina da seat din da yayi.



 Yana Jin zuciyarsa na
harbawa kaÉ—an kaÉ—an cikin sauri mai taxi É—in 
ya rufe marfin gefensa   cikin
sassarfa ya zagoyo gefen da Modibbo yake tare da buÉ—e masa murfin motar kana
fuskarsa É—auke da murmushi yace.



“Lalle marhaba fatan an ka isa Marocco lfy”.



Cikin sanyin murya da tarin gajiya yace.



“Yawwa”.



Kana ahankali ya ziro ƙafafunsa waje ya sauke aƙasa.



 Da sauri ya rumtse
idanunsa tare da kuma buÉ—esu a lokaci É—aya yaji wani irin abu mai masifar sanyi
ya zira masa tun daga tafin ƙafansa har zuwa ƙwaƙwalwar kansa irin dai abinda
yaji daya taka ƙafarsa a Airport. cikin sauri ya kuma lumshe idanunsa tare da
furta.



“Yah Salam”.



Kana ya fito dai-dai lokacin da mai kira sallah a masallacin
hutel É—in yazo dai-dai wurin kalmar shahada.



 



Cikin sanyi ya fara bin kalmar shahadar, wanda hakan ya
ankarar da mai  taxi dinma ya amsa, tare
da bin addu'a'o'in da yaji Moddibon yanayi.



 



Cikin sanyin murya Mutumin yace.



“Sannu da zuwa”. Lokacin da yaga ya É—an juyo ya kallesa.



Kai Modibbo ya gyaÉ—a masa tare da buÉ—e bayan motar ya É—auki
Breafcase É—insa tare da jakarsa, da sauri mai taxi É—in yasa hannunsa ya amshi
jakar kan nasa tare da kuma miƙa masa hannun zai amshi Breafcace ɗinma.



Kai Modibbo ya girgiza tare da faÉ—in.



“Barshi, zasu yi maka yawa ai”.



Cikin jin daÉ—i  yayi
gaba tare da



cewa.



“Bismillah  kashiga
ciki gashi ma Maghariba ta tayi”.



Cike da salama Moddibo yace.



“Bismillah”.



Yayi mgnar tare da nuna masa gabanshi alamun yayi gaba.



Cikin sauri  yashiga
gaba kana Moddibo yabi bayansa.



Cikin hanyar da flowers ke ajere gefe da gefe sai É—an
mawadacin hanya dake tsakani sukabi.



 Ahankali Moddibo ya
taka step É—aya biyu ana ukun ya hau kan barandar Kofar falon.



Ya sanya ƙafarsa na dama aciki tare da furta.



“Masha Allahu laÆ™uwwata Illah billahi”.



Sosai komai na hotel É—in keda tsari na Muslunci da burgewa.



 



Cikin yanayin gajiya ya ƙarasa gaban ma'aikatan dake binsa
da kallon ƙurilla.



Bayan sun gaisane ya kama É—aki, cike da mutuntaka da
martabawa suka gama komai, É—aya daga cikinsu, ya amshi jakarsa dake hannun mai
taxi É—in.



Kana yayi gaba tare dace masu bismillahi.



Cike da gajiya yabi bayanshi.



 



Lifter suka shiga cikin minti biyu suka isa hawa na biyu
inda na É—akin daya kaman yake.



Ma'aikacin hotel É—in ne da kansa ya buÉ—e É—akin ya shiga kana
ya shimfiÉ—a beshit tare blanket, kana ya wuce da sauran kayan kamarsu Towel da
Bathrobe da makilin da Brush sabulu ya ajiyesu bathroom tare da feffesasa Air
freshner kana ya fito tare da cewa mishi.



“Sir akwai abinda kake buÆ™atane?”.



Kai ya jujjuya mishi alamun a'a.



Ganin haka yasa ya fice.



 



Shi kuwa Modibbo cike da gajiya ya ajiye woyoyinsa yana mai
shaƙar ƙamshin Roomfreshner tare da kallon tsarin komai na ɗakin, komai na
cikin falon Ash & maroon colour ne mai masifar kyau kama daga Cottins
carpet dama kujerun.



 



Cike da gajiya a shiga bathroom al'wala yayi tare da fitowa
da sassarfa.



Lifter ya shiga ya sauƙa kana kai tsaye masallacin dake
cikin hotel ɗin ya shiga da sassarfa jin an tada iƙama.



Ya samu tuni sahu forko da na biyu duk sun   cika sai ana uku suka tsaya



Suna shiga suka tada kabbara dai-dai lokacin kuma aka tafi
ruku'un Farko.



Bayan anyi Sallah an idar Moddibo.



 Yayi Adduo'insa na
yau da kullum, ya kara da na neman aminci cikin wakilcin da zaiyiwa Abba tare
da samun nasara da roƙon Allah yayi riƙo da hannayensa ya bashi ikon riƙe
amana.



Yana so ya jira Isha'i amma saboda yanayin gajiya da yake ji
bazai iya jira ba yana so yayi wanka duk da cewa garin akwai sanyi,



Amma yana son yayi wanka dan yaji daɗin jin kinsa da sauƙin
gajiyar hanya.



 A hankali ya yunÆ™ura
da niyyan tashi, cikin sauri ya juya bayansa tare da fito da Idanunsa cike da
tsananin son tabbatar da ganinsa ya miƙa da sauri saboda gani fuskar da bashi
da hauki ko kokonta a kai cewa fuskar J...!



 

No comments