Sakayyah Book 2 Page 17

 

*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 17*



 




         Na



*Aysha Aliyu Garkuwa*



 



 



Assalamu alaikum mutanan arziki masoya kamshi ma abota
kamshi Amaren kamshi masu jargon kamshi Yammata wadanda sukasan darajar kamshi
ni Aysha Aliyu Garkuwa na kawo muku tallan wasu Amintattun turarukana masu
matukar kamshi da Kama jiki



Masu saukin farashi sannan ga biyan bukata



Yarhjya_incense_and_more



Ta shirya tsaf domin ta gwangwajeku da Turaruka na alfarma



Farar khumrah



Bakar khumrah



Turaren Wanka



Oil 6ml 1



Oil 12ml 1



Turaren fesawa 100ml 24 hours guda 1



Duka Akan 8k kacal 



   Sannan kayanta suna
tafiyane da guarantee duk wacce tasiya taji babu kamshin nan na alfarma ko kuma
basuda lasting to tayi alkawarin mayar muku da kudinku



    Wannan garabasar
zata kare on 5th September insha Allah



    Ku hanzarta ku
mallaki naku domin kayan yarhjya babu Danasani a cikinsa saidai kuyi alfahri da
siyan kayanta



Account number 1419787445 Amina Umar usman access bank



Kitura evidence of payment to



08092664954



Kuyi saving number TA domin ci gaba da ganin Turaruka Kala
Kala



Normal price



Bakar khumrah 1500



Farar khumrah 2k



Turaren Wanka 1500



Oils 6ml 800



Oils 12ml 1500



Turaren fesawa 100ml 3500



Turaren fesawa 50ml 2k



  Kayanmu available ne
a koda Yaushe



Akwai turarukan wuta na jiki na Kaya Dana daki duka sai
Wanda kika zaba



 



 



“Kazo mu koma ciki Maghriba tayi muje muyi alwala mu tafi
masallaci”.



Cikin gamsuwa ya gyaÉ—a kai,



Ibraahim kuwa hannun Moddibo ya riƙe tare da faɗin.



“Yah Aleey daga yanzu zaka riÆ™a zuwa jam'i yanda kake buri
da fata da marari”.



Sanyayyan numfashi Moddibo ya fesar kana yace.



“Alhamdulillah, dan babu abinda nafi bege kamar zuwa sallah
jam'i da kuma Innayi na”.



Ya ida maganar tare da bin bayan Ibraahim suka fara tafiya.



Tuni Æ´an Uwa sun fiffita falon ya rage babu mutane sai É—aÉ—-É—aya.



Innayi dake riƙe da hannu Khausar ta nufi wajensu Ummi tare
da faÉ—in.



“Kuzo mu koma masauÆ™inmu sai kuma gobe idan Allah ya kaimu,
za'a cigaba da hidima”.



 



Sheikh Jabeer kuwa da kansa ya nufi inda su Abban Jameel ke
zaune yace.



“Kuzo mu tafi Maghriba ta Æ™ara to”.



Kai suka gyaɗa kana suka miƙe suka bi ta ɗaya ƙofar suka
tafi.



Moddibo da su Ibraahim kuwa a hankali suke tafiya cikin
nitsuwa auka shiga Corridor da zai sada su da falon Side da suke.



 



Su Khausar kuwa sun fara haurawa kan steps din.



 Asma'u ta juya da
sauri ta kalli Ummi tare da faÉ—in.



“Ayyah Ummi bari inje na gaida Yah Moddibo in faÉ—a masa
saÆ™on Bashir”.



Ƴar dariya Ummi tayi kana tace.



“Bismillah keda É—an Uwanki”.



 



Kai ta gyaÉ—a cikin sauri ta juya ta nufi wajensu Moddibo
tana faÉ—in.



“Yah Moddibo! Yah Modibbo”.



Moddibo kuwa Already sun riga sun shiga falon da Dr Jameel
ke ciki.



 



Shi kuwa Dr Jameel jiyo motsinsu ne yasa ya sassauta murya
cikin wani irin yanayi da yake ciki bisa ga duk kan alamu hirar batsa suke
awayar cikin lumshe idanu yace.



“Please Baby kiyi haÆ™uri muna cikin wani Uzuri ne fa na
Fada”.



Murmushi tayi tare da cewa.



“Ok bye bye Amma please kazo Ina jiranka, kasan cewa kwana
biyu bamu haÉ—u ba ina kewarka”.



Ta ida maganar tare da katse kiran.



Dr Jameel na miƙewa su Moddibo na shiga....



 



Cikin yanayin takaicin halayyarsa Zakariyya ya maka masa
harara tare da cewa.



“Wallahi kai dai kam Jameel kayi asara,  komai aka shirya da kai da zaran mace tashiga
ciki saita ware ka cikin mu, musamman wannan shegiyar Baby na rasa yanda zanyi
in raba ka da ita”.



Moddibo dake jinsu ne ya girgiza kai kana yace.



“Alhamdulillahi kaima kenan abin na damunka Zakariyya?”.



Kai Zakariyya ya gyaÉ—a yana mai cigaba da hararan Dr Jameel
dake murmushi yace.



“Sosai ma kaga an tsara fitan nan dashi amma dayake shi
Mamajone mayen mata, ni wlh ban na lura da lokacin daya zame ya dawo ciki ba,
sai da muka shiga na gane baya tare damu”.



 



Sai kuma Moddibo yayi saurin juyawa jin muryan Asma'u na
cewa.



“Yah Moddibo”.



Da murmushi afuskarsa yace.



“A'a Asma'u”.



Asma'u kuwa idanunta ta zare tare da É—aura hannunta É—aya
akai kana ta buga ɗaya hannunta a ƙirjinta tare da faɗin.



“Yah Jameel”.



Tayi maganar idanunta na kan Dr Jameel dashi ma ita yake
kallo.



Cikin sauri Moddibo ya juya ya kalli Asma'u sai kuma ya juya
ya kalli Dr Jameel.



 



 Cikin yanayin kaÉ—uwa,
mamaki, Al'ajabi ta fara takowa har ta isa gaban Dr Jameel ta tsaya cikin
sarkewar murya ta furta.



“Yah Jameel”.



Kallonta Moddibo yayi tare da girgiza kai yace.



“A'a Asma'u”.



Cikin ficewar hayyaci ta É—aura hannunta akai tare da faÉ—in.



“Ummiiii kizo ga Yah Jameel”.



Sai kuma tayi baya luuu idanunta sukayi sama.



Cikin wani irin sauri Dr Jameel da tun time data kira
sunansa ya zuba mata idanu yana kallon ƙiranta da kuma yanda Ubangji ya ƙawata
surarta, lokaci ɗaya yaji wani irin yanayi da bai taɓa jin makamancin sa ba
akan ko wacce irin mace da yake mu'amala da ita karon farko yaji wani irin
tsarkakekken soyayyar ta ya mamaye masa zuciya.



Azabure ya nufe ta ganin saura kaɗan takai ƙasa ya tallafota
jikinsa ta faɗa kan ƙirjinsa asume.



 FaÉ—awa jikinsa da
tayi yasa ya koma baya ya faÉ—a kan kushin ya zauna, hannunsa yasa ya tallafo
fuskarta sai kuma ya É—aga kansa ya kalli Moddibo kana yace.



“Suma fa tayi”.



 



Cikin Sauri Moddibo ya riƙe tsintsiyar hannunta cikin
yanayin damuwa yake faÉ—in.



“Asma'u”.



Ina tuni ta samu kallon Ibraahim yayi kana yace.



“Ibraahim ka miÆ™o min ruwa”.



Dr Jameel kuwa kallon Moddibo yayi cikin wata kasalalliyar
murya gami da shauƙi yace.



“Ya dai kake shiga hurumin daba naka ba, ya ina matsayin Dr
sannan ta suma ajikina kake cewa amiÆ™o maka ruwa”.



Wani kallo Moddibo ya mata tare da watsa masa harara kana ya
buga masa tsawa da faÉ—in.



“Kai Mahaukacin ina ne ya yarinya zata suma sannan ka tsaya
kana maganar sai huruminka wani irin hurumi kake dashi a kanta, idan zakayi
abinda zata farfaɗo kayi ka wani maƙale yarinya atsakanin cinya haukane akan
ka”.



Kallon Moddibo yayi tare da juya idanunsa kana yace.



“Kamar ya kake cewa haukane akaina Ni naga matar Aure”.



Cikin tsawa da hararansa Moddibo yace.



“Koma yayane yanzu kayi abunda yarinya zata farfaÉ—o”.



Ahankali Zakariyya ya tsugunna kansa tare da bubbuga
kumatunta yana kiran sunan da yaji Moddibo na kiranta da.



“Asma'u³”.



Hannunsa Dr Jameel ya janye kana ya ture gefe tare da cewa.



“Dakata Zakariyya nasan kai Likita ne amma wannan ba hurumin
ka bane Saboda wannan hiruminane”.



 



Alalace Zakariyya ya banka masa harara tare da faÉ—in.



“Mayen banza mayen wofi, wato daga ganin Yarinya itama ka É—aura
Æ™olafacinka da kwadayin ka akanta”.



Araunane ya É—ago kansa ya kallesu baki É—aya cikin yanayin
gaskiya da gaskiya yace.



“Wallahi ban kalleta da idanun da nake kallon sauran Æ´an
matan da nake mu'amala dasu ba, na kalleta ne da wasu irin idanu masu matuƙar
daraja domin ita mai darace da mutunci”.



 



Tsaki Moddibo yayi cikin hasala da abinda Dr Jameel keyi ya
karɓi goran ruwan da Ibraahim ke miƙa masa ya watsa mata afuska amma bata farfaɗo
ba.



   LangwaÉ“ar da kai Dr
Jameel yayi tare da faÉ—in.



“Dan Allah kar ka jiÆ™amu Ni nasan yanda zanyi in farfaÉ—o da
abuna”.



Moddibo kuwa cikin mamaki ya zubawa Dr Jameel idanu yana
kallon ikon Allah da karfin hali.



 



 Cikin lumshe idanu Dr
Jameel da har zuwa lokacin yake rungume da Asma'u ya sunkuyo da kanta.



Da wani irin azabebben sauri Moddibo ya riƙe ka sa fuskarsa
babu walwala yace.



“Wallahi kada ka kuskura, Idan ka yarda ka kuskura Ni nasan
abinda zanyi maka hauka ne akan ka? Ko kuma kayi tunanin itama irin Æ´an matan
da kake rayuwa dasu ne da zakayi Æ™oÆ™arin kai bakinka kan nata?”



 



Hannunsa biyu ya haÉ—a kana yace.



“Dan Allah kayi haÆ™uri Moddibo na rantse da Ubangijin daya
busa min numfashi bana kallon wannan Baiwar Allah Asma'u amatsayin matar da
zanyi lalata da ita”.



Sai kuma ya furzar da iska mai zafi daga bakinsa kana ya
cigaba da cewa.



“Idanuna suna kallonta ne amatsayin matar Aurena, kuma uwar
Æ´aÆ´ana wallahi bawai kissing É—in ta zanyi ba ya kuke maidani kamar Bunsurune
zanyi Æ™oÆ™arin dawo mata da numfashinta nefa”.



Still babu walwala atare da Moddibo ya gyaÉ—a kai kana yace.



“Ok”.



Dr Jameel kuwa cikin lumshe idanu ya sunkuyar da kansa kanta
kana ya É—aura bakinsa kan hancinta yana hura mata numfashi.



Asma'u kuwa ahankali taja wani dogon numfashi tare da faÉ—in.



“Ummi wallahi Yah Jameel É—in mu bai rasuba ga Yah Jameel É—in
mu na ganshi da rabshi”.



Sai kuma ta buÉ—e Idanunta 
ganinta kwance acinyar Dr Jameel cikin sauri ta yunƙura ta zauna tare da
faÉ—a wa kansa ta rungumesa yayin da take kuka mai tsuma zuciya kana tace.



“Yanzu dama Yah Jameel baka mutu ba, aka kawo mana gawar
wani akace ka mutu?”.



Kasa ƙara sa Maganar tayi saboda yanda kuka yaci ƙarfinta
kana kallo zaka san daga ainihin zuciyarta maganar ke fitowa.



 



Lokaci É—aya tausayin ta ya mamaye baki É—aya ilahirin zuciyar
Dr Jameel hannu ya É—ago da niyyar rungumeta.



Da sauri Moddibo ya buge hannunsa.



Shi kuwa Dr Jameel zafin bugun da Moddibo ya masane yasa shi
saurin mayar da hannunsa yana yarfawa sai kuma ya kalli fuskar Asma'u dake
cigaba da kuka yace.



“Asma'u Wayyo Allana Yayanki zai kashe Ni kafin komai ya
kankama”.



Moddibo kuwa ahankali ya kira sunanta cikin girma da
kamalada da zame mata matsayin babban wanta kana jagoro kuma uba yace.



“Asma'u”.



Ahankali ta juya ta kalli Moddibo sai kuma ta maida kallonta
kan Dr Jameel ta sake rungumesa.



 



    Ganin haka yasa Moddibo saurin fin cikota
daga jikin Dr Jameel ya tsaidata  sai
kuma yace.



“Zo ki zauna anan”.



Ya faÉ—a tare da zaunar da ita akan Kujeran cikin yanayin
nutsuwarsa da tuno yadda J É—insa ke killacesu da basu kariya akan kamilallun
mazama bare irin Dr Jameel a hankali yace.



“Asma'u ki buÉ—e ido ki kalleni da kyau”.



Idanunta ta buÉ—e da tuni hawaye suka kwaranya ta kalli
Moddibo.



Cikin fesar da numfashi ya gyara zamansa tare da cewa.



“Wanene Ni awajenki?”.



Cikin raunin murya tace.



“Yah Moddibo Yah Jameel”.



Kai ya gyaÉ—a tare da faÉ—in.



“Menene matsayina awajenki?”.



Still idanunta na zubar da hawaye tace.



“Tamkar uba kuma tamkar Yaya Jameel”.



Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da faɗin.



“Toh kiyi haÆ™uri da abinda zan faÉ—a miki, Dr Jameel ba J É—ina
bane mai kama dashi ne kawai, nima nashiga irin yanayin da kika shiga lokacin
dana fara ganinsa”.



   Kai Asma'u ke
girgiza wa tare da cewa.



“Wallahi Yah Moddibo  
ban yarda ba Yah Jameel ne”.



Cikin rauni ya kira sunanta da faÉ—in.



“Asma'u”.



Ahankali ta É—aga ido ta kallesa cikin sanyi Murya yace.



“Na taÉ“a yi miki Æ™arya ne?”.



Cikin wata raunatacciyar murya ta girgiza masa kai tare da
cewa.



“Yah Moddibo baka taÉ“a yimin Æ™arya ba, amma wallahi bazan
yarda da abinda kake faÉ—a ba”.



Ta ida maganar tare da miƙewa ta nufi Corridor data shigo
tana gudu tana cewa.



“Ummi Ummi”.



 



Ahankali Moddibo ya koma ya zauna tare da É—aura hannunsa
duka biyu ya dafe kansa.



Ya tabbar kafin Asma'u ta yarda cewa wannan ba É—an uwanta
bane za'a É—auki lokaci.



Sai kuma ya ɗaga kansa tare da kallon Dr Jameel dake ƙoƙarin
binta yana kiran Asma'u asanyaye yace.



“Ka dawo ka zauna saboda bazata saurareka ba.



Wallahi Ni kaina zuciyata bata gama yarda min cewa ba J É—ina
bane kai.



Kawai jikina da zuciyata tana gamsuwa da cewa Kai ba J É—ina
bane”.



Sai kuma ya lumshe idanunsa da yake jin ruwan hawaye na
tsats-tsafowa kana ya cigaba da cewa.



“Saboda yanayin lalacacciyar É—abi'ar da kake yi na tabbatar
kuma babu abinda zaisa Ummi, Asma'u,da Bashir su yarda cewa ba kai bane J sai
In har sun fuskanci mummunan É—abi'unka da halayyar ka da yanayin ka na neman
mata shine kaÉ—ai zaisa su yadda”.



Sai kuma ya sanya bayan hannunsa tare da goge hawayen da
suka saƙƙo asaman kuncinsa kana ya cigaba da faɗin.



“Saboda J É—ina Amintaccene mai Aminci mai kamala ne mai
mutunci ne, kuma tsarkakekkene bai kasance yanayin makamancin É—abi'unka ba”.



 



Tunda Moddibo ya fara magana jikin Dr Jameel yayi bala'in
sanyi, ganin maganar da Moddibo keyi daga ainihin zuciyarsa ke fitowa kana yana
jin magan-ganunsa nada muhimmanci da kuma ƙarfi kana yana ganin yana da yaƙini
da gamsuwa.



Cikin mutuwar jiki ya koma ya zauna karo na farko arayuwarsa
daya fara jin tsananin ƙyamar kansa da kansa akan ɗabi'unsa na neman mata.



Lokaci É—aya ya riski kansa da wani mummunan tsinkewar zuciya
saboda har ƙasan ransa Allah ya jarabcesa da son wannan yarinya daya gani wacce
ake kira da Asma'u.



Wacce ita kuma take masa kallon É—an uwanta wanda zuwa yanzu
ya fahimci komai nasa yana mata kama da É—an Uwanta ne daya rasu.



Hakanan ne yasa zuciyarsa ya cika da tsoro da taraddadi anya
Moddibo zai lamunce abashi Auren Asma'u ayanda yake nuna tsananin ƙyamarsa akan
halayyarsa na zina...



 



Kansa ya riƙe da hannunsa duka biyu kana ya furta.



_“Astagfirullah wa'atubu ilaik”_.



 



Moddibo kuwa cikin sanyi jiki ya juya ya kalli Zakariyya
dake cewa.



“Moddibo muyi alwala muyi sallah ana kiran Sallah”.



Kai suka gyaÉ—a kana suka miÆ™e sukayi al'wala kana  nufi masallaci alayi É—aya sukayi jam'i koda
suka idar da Maghriba basu dawo gida ba saida akayi Isha'i kana suka dawo.



Suna dawowa suka samu an shirya musu komai na a binci
dining....



 



 



Acan falon da aka sauƙe su Khausar kuwa cikin gigita Asma'u
ta shiga falon tare da faÉ—awa kan Ummi dake zaune cikin ficewar hayyaci take faÉ—in.



“Wallahi Ummi naga Yah Jameel”.



Da sauri Ummi ta zaro ido kana tace.



“Me kike faÉ—a Asma'u”.



Cikin zubda hawaye da rauni Asma'u ta gyaÉ—a kai tare da
cewa.



“Wallahi Ummi naga Yah Jameel tare da Yah Moddibo”.



Yanayin da take magana cikin alamun kiÉ—ima da gigita yasa
Ummi saurin janyota ta riƙe ta.



Innayi ma matsowa kanta tayi kana ta riƙe hannunta tare da
cewa.



“Asma'u wanda ya rasu yana dawowa ne?”.



Kallon Innayi tayi da jiƙaƙkun idanunta kana tace.



“Innayi wallahi Yah Jameelu na gani naga Yah Jameel Wallahi
na ganshi”.



Cikin fesar da numfashi Ummi tace.



“Asma'u ki nutsu mana, In dai Jameelu ne da gaske ai zai iso
mu”.



Ummi kam kallonta kawai take aranta tasani cewa tabbas
Jameelunta ya rasu ya barta tasan cewa babu wani Jameelu sai dai in gezo yake
wa Asma'u ta.



Aunty Ruƙayya dake zaune can gefe ta miƙe ta matso gefen Asma'u
ta zauna tare da riƙe hannunta tace.



“Asma'u ya za'a yi wanda ya mutu ya  dawo? Shi wanda ya mutu baya dawowa ai shi
mutuwa É—ayace idan mutum yayi ta yayi ta har abada”.



Cikin matsanancin kuka Asma'u ke girgiza kai kana tace.



“Wallahi Allah Aunty RuÆ™ayya na gansa”.



Ƙiran Sallar Maghriba da akayi ne yasa Ummi kallon Asma'u
cikin tsawa ta haÉ—e fuska kana tace.



“Maza tashi Kije kiyi a''wala kizo kiyi Sallah”.



Da sauri tace.



“Wallahi! Wallahi!! Ummi Yah Jameel na gani, ki yarda dani”.



Cikin haÉ—e fuska Ummi tace.



“Zakije kiyi salla ko zaki tsaya hauka”.



Jiki asanyaye ta miƙe taje tayi al'wala kana tazo ta shimfiɗa
Sallah kana tayi Sallah koda suka idar da sallar Maghriba Azkhar sukayi har aka
kira Isha'i kana sukayi ...



 



Bayan sun idar da Isha'i Asma'u ta koma gaban Ummi ta zauna
cikin muryan kuka tace.



“Wallahi Ummi Yah Jameel na gani Ummi ki yarda dani ku nemi
Yah Moddibo wallahi Yah Jameel na gani fa Ummi”.



Ganin yanda ta rikice yasa Ummi sauke zazzafan ajiyar zuciya
tare da kallon Innayi da tazo gabansu kana tace.



“Innayi ane momin Moddibo al'amarin Asma'u yayi yawa fa,
gaba É—aya agigice take kinga Sallar nan har aka idar da Maghriba kuka take har
aka zauna Azkhar still kuka take har muka jira Isha'i kuka Asma'u keyi”.



Kai Innayi ta jinjina tare da faÉ—in.



“Toh shikenan”.



Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi side ɗin Didi.



Tana shiga Side É—in Didi suka sake gaisawa kana ta yiwa Didi
bayanin abinda ke faruwa.



Cikin sauƙe numfashi Didi tace.



“Tabbas ai shima kanshi Aleeyu sanadin shigowar sa
Masarautar nan haÉ—uwar sa da Dr Jameel ne”.



Cikin yanayin mamaki Innayi ta tallafe kuncinta tare da faÉ—in.



“Toh waye Dr Jameel É—in?”.



Ahankali Didi ta shiga bata Labarin da Dr Jameel ya bata.



Ajiyar zuciya Innayi ta sauƙe kana tace.



“Toh dan Allah ayi min iso zuwa Side É—in dasu Moddibo suke
dan bansan inda suke ba”.



Ƴar dariya Didi tayi tare da cewa.



“Ai suna kusa daku suna Æ™asa,  kuna sama bari nayiwa Jakadiya magana ta
rakaki”.



Nan Didi ta umarci Jakadiya kana ta yiwa Innayi jagora zuwa
sashen dasu Moddibo suke...



 



     Innayi na shiga
ta samu Zakariyya Dr Jameel Ibraahim suna Kan dining yayin da ta haÉ—u da
Moddibo gab bakin ƙofa da alamun zai tafi wajensu ne, dan ya duba halin da
Asma'u ta tafi.



Yana ganin Innayi sai yayi saurin komawa baya.



Innayi kuwa tana ganinsa tayi murmushi.



Shi kam hannunta ya riƙe suka ƙarasa cikin falon kana suka
zauna kan kujera suna zama kan kujera yace.



“Innayi nayi kewarki”



Cikin jin daÉ—in ganinsa ta gyara zama tare da faÉ—in.



“Nima nayi kewarka, amman dama ai nasan cikin danginka za
taho nasan ka dawo cikin Æ´an uwanka muhallinka”.



Kai ya jinjina kana yace.



“Innayi wani irin tarin abubuwa kikayi ta É“oye min a iya
tsawon rayuwata?”.



Numfashi ta fesar da cewa.



“Sai ahankali yanzu dai farko waye Asma'u ta gani ta koma
tana ihu tana ce mana Jameel ne”.



Kai ya jinjina tare da lumshe idanunsa kana yace.



“Gashi can Innayi juya ki kallesa baiyi miki kama da Jameel
ba?”.



Da ƙarfi Innayi ta tashi kana ta buga hannunta akan ƙirjinta
cikin tsananin ruÉ—u tace.



“Kamar yaya kama?,Aliyu kace min Jameel dai Ashe gaskiyan
Asma'u Jameelu ta gani”.



Ta ida Maganar tare da juyawa ta nufi dining area cikin
sassarfa.



 



Tana zuwa ta kamo hannun Dr Jameel tare da riƙewa tace.



“Jameelu”



Kallonta yayi tare da yin murmushi shima kansa yanda suke
zuzuta tsananin kamansa da Jameelu ya fara bashi tsoro da mamaki.



Innayi kuwa batare data jira komai ba ta kama hannunsa tana
ja.



Shi kuwa Dr Jameel tsintar kansa da bin bayanta yayi.



  Shima Moddibo cikin
sauri yabi bayansu yana cewa.



“Innayi ba Jameelu bane 
wallahi tsananin kama ne”.



Ina tuni Innayi ta fice batare data sauraresa ba ta fara
haurawa step É—in tana cewa.



“Ummin Jameel”.



Zakariyya da Ibraahim ma na biye dasu suna shiga Falon da
Ummu ke zaune Innayi na cigaba da cewa.



“Ummin Jameel Wallahi gaskiyar Asma'u ne Jameelun kine”.



 Akuma dai-dai lokacin
Ummi ta juya da sauri idanunta suka sauƙa akan Fuskar dake tsananin kama da
Jameelunta komai na Jameelunta a fili.



cikin wata raunatacciyar murya tace.



“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”.



Sai kuma ta koma ta faÉ—a kan kujera idanunta na zubda hawaye
shar-shar-shar.



Itama Asma'u cikin sauri ta riƙe hannun Ummi tare da faɗin.



“Ummi ba kin gani ba na faÉ—a miki Yah Jameel ne”.



Sai kuma ta saki hannun Ummi ta koma ta riƙe hannun Dr
Jameel na dama Innayi kuma na riƙe da hannunsa na hagu suka zo gaban Ummi suka
durƙusa sai shima ya tsinci kansa da durƙusawa agabanta, haka nan yaji kima da
martaban matar sun cika masa idanu.



Da sauri Moddibo ya ƙarasa shiga wa falon tare da zama gefen
Ummi wacce ke kan 3sitter kana cikin raunin murya yace.



“Ummi”.



Cikin zubda hawaye ta juya ta kallesa cikin rauni ya cigaba
da cewa.



“Ummi ki kalli duk komai na Jameel ne muryansa, Tafiyarsa,
Gangar jikinsa, Har fa asakin da Jameel keyi shi yake yi amma wallahi Ummi ba
Jameelunki bane kamannin ne yayi yawa Wallahi!³ Ummi ba Jameelunki bane”.



Juyawa Ummi tayi ta kallesa cikin jinjina masa  take cigaba da gyaÉ—a kanta jikinta yana bata
ba Jameelu bane domin jikinta ba amsheshi a matsayin Jameel ba wannan bawai É—an
ta bane agabanta amma zuciyarta taƙi yarda.



Kai ta girgiza still hawaye na bin fuskarta ta juya ta kalli
Dr Jameel da yake durƙushe agabanta.



Ganin yanda take zubar da hawaye yasa shima yake zubar da
hawaye.



Murmushi tayi tare da cewa.



“Toh meyesa ka kuma?”.



Ahankali ya É—ago kai ya kalleta cikin tarin tausayinta da
kuma rauni yace.



“Saboda kukan da naga kunayi shiyasani kuka, nasan ko waye
Jameel awajenku mutum ne mai daraja, mai kima wanda shine jigo acikin
rayuwarku”.



Kallonsa kawai Ummi keyi hawaye na cigaba da zuba daga
idanunta sabida yadda muryasa ma sai ta Jameel É—inta.



 



Shi kuwa  Dr Jameel
kuwa cikin rauni da zubda hawaye ya cigaba da faÉ—in.



“Na fahimci kuna jin Æ™una na rashinsa amma Ummi nayi miki
al'ƙawari in dai kin amince kun bani dama in sha Allah zan maye muku
gurbinsa”....



 



 



 



*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn,
masu cewa wai sun goda suga number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya
zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuÉ—in bai cikaba tukun sai sun cika, ko
kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai duk nisan state da
kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen wajema.
Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina
min mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki É“ata min lokaci a banza, wlh ni
na tsani harkar karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuÉ—in kaya
ga account no ga numberta ai sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga
alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in kina dashi faƙat in babu kada ki
wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki kenan*



Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin
gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin.
Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya,
melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. BuÉ—ewar gaba,
domin har budurwa infection na iya buÉ—ata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi
al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin
wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma
saduwa, da dai sauran abubudann ban 
lissafa. Sune manyan alamomin infection.



Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman
kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari
kiji illolin infection wato cutar sanyi.



Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin
kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi
bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiÉ—a ta
lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwaranya,
zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk
tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki
nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.



KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA
BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya
dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da
zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki
magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau,  duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji
sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta
gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai
kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic
infection ne yar uwa.



INFECTION set É—inmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara,
Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar
komai Maganin na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk
nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi,
cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da
maganin set É—in na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki
ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da
mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da
shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai
sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a
jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita
miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin
garin yasa ina raba rabin set É—in in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set É—in
10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz
bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuÉ—inki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP
NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi
Available ko yau kika tura kuÉ—inki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko
sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na
mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki
shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR
MA'AURATA.

No comments