Sakayyah Book 2 Page 15

 

*GARKUWAR MARUBUTA**SAKAYYAH book 2... Page 15*



 




          Na



*Aysha Aliyu Garkuwa*



 



Assalamu alaikum mutanan arziki masoya kamshi ma abota
kamshi Amaren kamshi masu jargon kamshi Yammata wadanda sukasan darajar kamshi
ni Aysha Aliyu Garkuwa na kawo muku tallan wasu Amintattun turarukana masu
matukar kamshi da Kama jiki



Masu saukin farashi sannan ga biyan bukata



Yarhjya_incense_and_more



Ta shirya tsaf domin ta gwangwajeku da Turaruka na alfarma



Farar khumrah



Bakar khumrah



Turaren Wanka



Oil 6ml 1



Oil 12ml 1



Turaren fesawa 24 hours guda 1



Duka Akan 10k kacal



   Sannan kayanta suna
tafiyane da guarantee duk wacce tasiya taji babu kamshin nan na alfarma ko kuma
basuda lasting to tayi alkawarin mayar muku da kudinku



    Wannan garabasar
zata kare on 5th September insha Allah



    Ku hanzarta ku
mallaki naku domin kayan yarhjya babu Danasani a cikinsa saidai kuyi alfahri da
siyan kayanta



Account number 1419787445 Amina Umar usman access bank



Kitura evidence of payment to



08092664954



Kuyi saving number TA domin ci gaba da ganin Turaruka Kala
Kala



 



 



Yayin da gaba dakin sune bin Khausar kallon, sabida yadda
annurinta ya cika fuskarta, tare da haska É—akin, lokaci daya ta zama tamkar
tauraruwar da tafi ko wacce haske acikin duniya.



 



Acan cikin sauran É—akunan kuwa, tuni su Ummi da kuma su
Aunty Hajara, Aunty rukayya, Hajiya Bunayya, sun sha kwalliya cikin shigar
Alfarma, had’i da kece raini, sun kuwa yi matukar kyau, domin hatta su Innayi
da Hajja Nana ba abarsu a baya ba, musamman Hajja Nana duk tsufanta, bai hanata
yin kyau cikin doguwar rigar data sanya ba kasancewarta Æ´ar duma-duman tsohuwa
kai hakama bata shekarun da take da suba, dukansu sunyi kyau sai É—aukar idanu
suke, kowanne daga cikinsu kuwa kaga ni kasan yana cikin farin ciki, musamman
Innayi da ayau farincikin dake kan fuskarta ya kasa É“uya.



 



Hakama ɓanƙaren su Abban Jameel da Lamiɗo da Malam Arɗo
Bappa Jimeta da Haiydar harma da Dr Jameel sosai sukayi shiga ta al'farmar.



Su tuni sun iso wurin taron bisa jagorancin Sheykh Jabeer.



 



Hakama su Innayi suma tuni sun sauƙo bisa jagorancin innayi,
sun zauna a gefen inda su Abban Jameel suke, don dama an ware musu wurin
zamansu na musamman.



 



AÉ“angaren Moddibo kuwa tsaye yake acikin cikin É—akin da ya
lura nanne É—akin Ibraahim,  yayinda yake
cikin wata irin Amintacceyar shiga ta al'farmar da kamala.



Dandatstsiyar jalabiya ace a jikinshi Sky blue mai masifar
kyau da shaƙi sai ɗauke ido take tamkar madubi, sai kuma wata tattausar
Al'kebba fara Æ™al mai ratsin Sky blue da golding  kala na zaren da aka yayyarfawa alkebbar wani
irin Mashahurin aiki mai cike da tambarin masarautar Mouley É—in. Sai kuma farin
hirami mai gidan dara-dara Sky Blue, wow Masha Allah. Wani irin sheƙi da ƙyalli
yakeyi kai kace taurarone sajenshi kuwa sai walwali yakeyi fuskarshi ta fito
ras.



Cikin É—an fesar da numfashi yace.



“Anya zan iya wannan tsaraÉ“e-tsaraÉ“en kuwa”.



Yayi mgnar cikin ƙosawa da yadda ake wani shiryashi kamar
yaro.



Murmushi Ibraahim yayi, had’i da cewa.



“A’a zaka iya, mana, kayi haÆ™uri kasan al’adarmu ce anan,
duk ranar da za’ayi wani abu na musamman, shirya mutum ake, musamman irinka
masu girman daraja.”



Kai Modibbo ya girgiza cikin yanayin k’osawa yace



“Afwan ni a barni haka”.



 



“A’a Yah Aleey dan Allah, kasan nan masarauta ne, kuma kana
da matsayi na musamman, kadai bari ashirya kan.”



 



Kokarin magana yake, sai kuma ya fasa saboda Sheykh Jabir
daya shigo, cikin shiga ta alfarmar da takasance shigarsa akoda, wanda a
wurinshi Modibbo ya gaji don irin wannan shigar,  ganin 
Modibbo’n azaune yasa shi, bud’e baki da mamaki yace.



 



“Har yanzu Aleeyu basu gama shiryaka ba, lokaci yana
k’urewa, tashi maza a Æ™arisa shirya ka da hanzari.”



 



Ya k’are maganar yana me jawo hannunsa, suka nufi gaban
dressing mirror wanda yake cike tab da ababen gyaran jiki, komai na wurin
tsabtsab yake, komai neat da alama Ibraahim din gwanin tsabta ne.



 



Suna isa wurin É—aya daga cikin hadiman ya ja mishi kujera,
ya zauna, bisa umarnin Sheykh Jabeer way’annan hadiman suka ci gaba da shirya,
shirin da ya bayyana cikakken kwarjininsa me burgewa.



“Masha Allah.”



Ibraahim ya fad’a lokacin da kwararrun hadiman nan suka
nad’a masa kyakkyawan farin hirami me ratsin adon sky blue akansa, da yayi
matuk’ar k’ara bayyana kwarjininsa, still suka gyara mushi zaman tattausan
farar, alkyabbar da taji ado, me d’auke ido da jan hankali, wacce tana da faÉ—i
kuma a buÉ—e take, tabbas zan iya cewa Modibbo bai tab’ayin kyau irin na yau ba,
domin shi kansa ya shaida hakan, saboda tsananin kyaun da yayi, Sheykh Jabeer
da Kuma Ibraahim murmushi kawai suke idan sun kalleshi.



Kyakkwawan takalmin sarauta light blue aka sanya masa
aƙafarsa, wanda shiya ƙara cika adon nasa, domin harda adon bit din gold
ajikinsa, ahannunsa kuwa wani tsadadden agogon gold suka d’aura masa, wanda
cikinsa ke d’auke da tambarin masarautar tasu ta Mouley.



 



Murmushi Ibraahim ya sakeyi, wanda hakan yasa Modibbon
Æ™anÆ™an da idanunsa, cikin sanyi da taushin muryar da taza me masa d’abi’a yace.



 



“Wai Ibrahim duk wanna murmushin na menene?”



 



Murmushi Ibraahim din yayi, yana me gyara masa zaman
takalman ƙafarsa yace.



 



“Duk wannan murmushin da shigar taka ta musammance, yau din
rana ce ta farinciki Yah Aleey, yau da za’a gabatar dakai awajen dangin
mahaifinka, yau kowa zai san da zamanka, ni gani nake kamar masu shiryakan ma
basa sauri.”



 



Ya ƙare maganar yana sake kallon tattausar alkyabbar dake jikin
Ya Aleey’n nasa, wacce Sheykh Jabeer ke k’ara gyara masa zamanta.



Aransa yake yaba baiwar kyau kwarjini had’i da haiba da
Allah Yayiwa Aleey’n.



Abayyane kuwa cewa yayi.



 



“Masha Allah,



 



Sheikh Jabeer kuwa cikin kulawa yace.



 “Fatabarakallahu fiy
ahasanil khali kiyn.



Allah Ubangiji ya albarkaci rayuwarka, ya kareka daga
sharrin mugun mutum da aljan, ya kuma tsareka daga sharrin idanun al’ummar da
zasu kalleka, ka shiga da addu’a, Ubangiji na tare dakai akoda yaushe.”



Amin Ya Allah, Jabeer bin Jabeer dake shigowa ya amsa.



Shi kuwa Modibbo Cikin dai É—aurewar kai da har yanzu ya ke
ciki ya gyaÉ—a mishi kai.



 



Yayinda Ibraahim kuwa, tsananin kyaun da Yah Aleey’n yayi
duk ya gigitashi, hakan yasa shi zaro wayarsa kirar iphone 14pro max ya shiga
daukarsa hoto, yana me sake yaba kyawun da yayi, koda ya kammala yi musu hoton
falo ya fito, nan ya iske Dr. Jameel da kuma Zakareeya suna zaune cikin shiga
ta al'farmar da alama suma sun gama shiryawa, ganinsa yasa suka miƙe tsaye, sai
kuma suka juyo jin motsin su Modibbo kusan a tare sukace.



“Wow masha Allah, lallai jini baya É“uya”.



Suka ƙare mgnar suna matsowa kusa da Modibbo.



 



Shi kuwa Ibraahim da sauro ya nufi inda za’a gudanar da
taron, yana zuwa cikin babban falon taron masarautar tasu kuwa ya tararda wajen
acike maƙil, ƴan uwa duka sun hallara kowa da kowa nasu na nan, iyaye, kakanni
dama jikoki harda ƴaƴan jikoki, babban falon ya cika maƙil, yayinda acan gefe
kuwa wurin da aka warene waje na musamman na zaman amarya da ango zasu zauna a
tsakiya.



 



Sai kuma gefen su Didi dake zaune tare dasu Lalla Hafsa da
Lalla Khadija sai sauran matan Abualeey da yaransa.



Ibraahim na shigowa Rahma ta miƙa da sauri tazo nufoshi tana
fad’in.



“Yah Ibraahim, har yanzu baku gama ba, duk an fitofa ku ake
jira, dangi duk sun zak’u dason ganin Yah Aleey.”



 



“Yanzu zamu shigo, nazo duba yanayin wajen ne.”



Ibraahim ya amsa yana me shakan daddad’an kamshin turaren
wutan dake hannunta, wanda hayakinsa ke tashi acikin kasko.



Cikin sassarfa kuma ya juya, domin yiwa Modibbo da kuma
Kakansu Sheykh Jabeer jagora.



A falon ya samesu cikin jin daÉ—in yace.



“Bismillah mufa ake jira”. Ya faÉ—a tare da tsayawa gaban
Modibbo, yayinda Sheykh Jabeer kuwa yake gefen damanshi, Zakariyya kuma da Dr
Jameel a gefen hagunshi



Kana suka fito cikin Corridor da zai sadasu da falon.



 Dr Jameel a hankali
ya É—an ja baya ya koma cikin falon da suka fito É—in sabida ganin kiran
Babynshi.



Amsa kiran yayi tare da maida ƙofar ya rufe.



 



Su Zakariyya kuwa basuma kula É—aya komaba.



Sabida Hadiman da suke zagaye dasu.



Tafiya suke a hankali cikin ƙasaita da Kuma nutsuwa, haɗi da
tsananin jinin sarautar dake gudana acikin jinin kowannensu, musamman Modibbo,
wanda yake jin kansa acikin wani irin yanayi na daban.



Tsantsar girma yake ji, haɗi da zumma da ƙasaitar da bai
tab’a jin kwatan kwacinsa ba, haka suka nufo babban falon dake cike da dangi da
y’an uwa.



 



Acan side din da Khausar take kuwa, jakadiya ce da kanta
tare da Lalla Salma wato mahaifiyar Zakariyya, suka rik’o Khausar din wacce ta
zama tamkar wata flower saboda tsabar kyau, kamshi kawai take bazawa me tsuma
zuciya.



Lalla Salma da takejin Kaunar Khausar har cikin zuciyarta ne
ta É—an sunkuyo da kanta daidai saitin kunnen Khausar din tace.



 



“Ki yawaita ambaton sunan Allah a bakin ki har muje mu dawo,
Ubangiji Allah Ya kareki daga sharrin masu sharri, Allah ya tsareki ya kuma
kauda idon mak’iya daga gareki, Allah Yasa ki shiga cikin zuri’ar mu da k’afar
dama, alfarmar annabi da al’qur’ani, kiyita adduan Allah ya tsareki da
fuskantar k’alubalen da surkuwarki ta fuskanta lokacin da ta shigo ahalinmu,
Allah ya miki al'barka ya dauwa mar dake cikin farinciki.”



 



Da “Aameen” ta amsa cikin ranta, yayinda a fili kuwa jinjina
kanta kawai tayi, tanajin matar ta kwanta mata arai, saidai tambayar azuciyarta
take wai shin menene ke naÉ—e cikin tarihin Modibbo waye shi, meyasa innayi ta
koma dashi can? Me hakan yake nufi haka tai ta jerawa kanta tambayoyi?



Tambayar da bazata samu amsarta ayanzu ba.



Ahaka suka ci gaba da tafiya Jakadiya da kuma Lalla Salma na
rike da ita, sai kuma Hadimai dake biye dasu abaya, hadi dasu Asmau Asiya da
kuma Dije.



 



Sassanyan busar sarewa me tsananin dadin jine ya cika
kuwannuwan way’anda ke zaune a falon, kasancewar isowar su Modibbo, wanda hakan
yasa duk idanun mutanen dake wajen ya koma kansu.



“Masha Allah, fatabarakallahu fiy ahasanil kali kiyn.”



Shine abunda ke fitowa daga bakin tarin mutanen dake wajen,
saboda yanda Modibbo yayi matukar kyau had’i da k’awatuwa, tsananin kwarjini da
haiba sun bayyana akan kyakkywar fuskarsa, da tayi kama dana mahaifinsa sak,
sarautar zalla yau ita ta bayyana kanta ajikinsa.



Yayinda wasu daga cikin mutanen wajen kuwa, suke raba
idanunsu wajen kallonsa shida Ibraahim, saboda tsananin kamar da sukeyi da
juna.



Ayau fuskokin da yawa daga cikin  masarautar ya cika da farincikin da har ya kasa
É“uya.



 



Cikin tsananin jin dadi suke wasu dayawa ke fitowa suna
rungumar Modibbo, wanda tsananin kwarjininsa ya haifar musu da soyayyarsa me
tsanani.



 



Cikin sauri Innayi ta nufi inda suke tare da fara ware
wannan sandar nan da take ajiye dashi da Æ´an silalla, ware sandar ta farayi
daga cikin furen da aka naÉ—eta.



Tana isa wurin ta tsaya gaba Modibbo tare da miƙa mishi
sandar, shi kuwa Modibbo cikin tsananin mamaki da kaÉ—uwa ya ware idanunshi a
kan fuskarta murya cike da mmki yace.



“Yah Salam wa nake gani a gabana ni Aliyu”.



Murmushi mai cike da farin ciki innayi tare da kamo
hannunshi ta danƙa mishi sandar kana tace.



“Innayinka ce a gabanka ba kama bace, nice nan Modibbo nazo
maka da tsaraba mafi daraja a gareka tare da rakiyar masoyanka”.



Ta ƙare mgnar tare dayi mishi nuni da inda su Abban Jameel
Malam ArÉ—o Bappa Jimeta LamiÉ—o Haiydar, suke zaune.



 Cikin sauri ya dawo
da ganinsa kan Innayi tare da cewa.



“Yah ilahi Abba harda LamiÉ—o da kuma Malam ArÉ—o”.



Sai kuma ya kalli inda ta nuna mishi tana faÉ—in.



“Harda Umminka ma ba”.



Wani irin amintaccen numfashi ya fesar lokacin da kwayar
idanunsa suka sauƙa kan fuskar Ummi, yalwataccen murmushi ya sakar mata, sai
kuma ya kalli Innayi da tuni ta juya ta nufi wurinsu Ummin sai kuma ya kalli
Hajia Bunayyah, tabbas ya ganeta a fili yace.



“Toh ita kuma me haÉ—ina da ita?”.



Sai kuma ya maida kallon sa kan Haiydar dake mishi murmushi
a hankali yace.



“Harda Haiydar”. Shi kuwa Haiydar cikin jin daÉ—i ya kalli
LamiÉ—o tare da cewa.



“Kai Masha Allah Abba kalli yadda Modibbo yayi kyau, kai
shigar sarauta akwai kyau”.



Murmushi kawai LamiÉ—o yayi dan ya fahimci cewa shima Haiydar
jinin sarautar ne ya motso.



 



Shi kuwa Modibbo bisa jagorancin Sheykh Jabeer da kuma
Ibraahim Zakariyya da Jabeer bin Jabeer ne yasa yake biye dasu zuciyarsa fal
tarin tambayoyi kana da mamakin ganin su Innayi musamman kuma LamiÉ—o barma ace
ta Bappa Jimeta da baisan shiba.



Ahaka har suka isa wajen da zasu zauna, Sheykh Jabeer na
riƙe da hannunsa.



Saidai kasancewar a tasu al’adar ango baya bazai zauna
har  harsai amarya ta Æ™araso hakan yasa
koda suka iso wajen zaman tsayawa sukayi, yayinda tuni Fadawa suka zagayesu
tare da ware tabka-tabkan rigunansu sukayi musu ƙawanya.



Suna tsayuwa kuwa suka soma jiyo, wani daddaÉ—an busa sarewa,
me ɗauke da sassanyan kirarin da akayita da harshen larabci da marabta baƙi.



Wanda hakan yasa gaba É—aya idanun ya koma saman steps din
dasu Khausar ke takowa, domin tuni anfara shelan zuwan amarya.



 



Jin hakane yasa fadawan nan kuma janye rigunansu, tare da
zagayawa suka koma bayan kujerar da aka ƙawata dan zaman ango da amarya,
yayinda wasu kuma duk suka rusuna ƙasa.



 



Shi kuwa Modibbo kasancewar yana fuskarta ta inda suke
tahowanne yasashi saurin ware idanunshi a saman lips enshi yace.



“Asma'u?”. Yayi mgnar da ko Ibraahim dake gab dashi baijiba,
cikin son fahimtar me ke faruwa ya kuma kalli Asiya sai kuma ya maida idonsa
kan Asma'u dake sakin murmushin, shi kuwa idon shi ya maida ƙasa tare da fara
kallo su daga ƙasa.



Ahankali suke taka kan stairs din da yasha red carpet me
masifar kyau da ƙawa yayinda kan ko wanne step akwai Hadimai gefe da gefe suna
riƙe da kaskon turaren wuta.



Asmau ce ke gefen damanta yayinda Asiya kuwa ke gefen
hagunta, sai Dije dake  gefen Asma'u.



Sai kuma wata Æ´ar matashiyar HaÉ—ina dake bayanta wacce ita
ke riƙe da mayafin da aka sanya mata akanta, wanda saboda tsabar tsawonsa har
jan ƙasa yake yi.



Sunyi matukar kyau da burgewa, hakan yasa duk aka maida
kallo kansu.



Tafiyarta me tsananin jan hankali da ma’ana, haÉ—i da
tsananin ƙawatuwar da shigar nata shiya sanya Modibbo dake tsaye zuba mata ido,
duk da cewar baya iya ganin fuskarta, amma tsananin annurin da take fitarwa ya
cika masa ido, yayinda takun da takeyi me kama da tafiyar É—awisu ya tsaya masa
arai, domin yanajin tamkar ya taɓa sanin me wannan tafiyar, tabbas ya taɓa
ganin irin tafiyar.



 



Jin ana shelar amarya ta iso tare da fara zuba kirari.



Amarya Fatima Zahra mata a gidan Aliyu Youseep  Mouleey.



Da sauri ya rumtse idanunsa da ƙarfi dan so yake ya nazarci
kalaman.



 



“Amaryar kuma? Toh amaryar waye? meyasa naji ana kiranta da
matarta, wace matarta kuwa? me suke nufi? Yaushe aka aura min ita? Toh ma
wacece ita? Shin wai su waÉ—annan me suke nufi dani? da zasuyi ta juya min
rayuwa suna sarrafa min abinda basu nemi izininaba". waÉ—annan tambayoyin
su suka cika zuciyarsa da ta samu kanta cikin tsananin ruÉ—ani.



Shin me ake nufi dashi ne? me sukeson maidashi? wani irin
aurene wanda akayishi babu saninsa? Bare sahalewarsa, toma uban waye yace musu
shi ya shiryawa aure a wannan taƙin.



Ya kuma yiwa kansa tambayar yana me tsareta da idanunsa, duk
da cewar baya iya ganin fuskarta saboda mayafin da aka sanya mata.



Ji yayi kansa na wani irin juyawa zuciyarsa kuma na bugawa
da ƙarfi, so yake ya buɗi bakinsa ya cewa Sheykh Jabeer shifa kada a liƙa mishi
wata jarabar amman ina ya gaza sabida ruÉ—anin da yake ciki.



 



Sun Khausar kuwa ahankali suka ƙaraso cikin parlorn, wasu
daga cikin Hadiman dake ta hidima ne suka nunawa Asma'u Asiya da Dija, wajan
zaman da aka tanada musamman domin su, haka yasa cikin nitsuwa su Asma'u suka
nufi wurin zamansu, yayinda Hadiman kuma duk suka zube a ƙasa.



Yayinda su Lalla Salma 
kuwa suka nufo da ita wajen dasu Modibbon ke tsaye.



Da sassarfa Rahama ta taso ta biyo bayansu.



 Lalla Salma ce ke
rike da Khausar yayinda kowani taku É—aya da sukeyi na kusanto inda Modibbo
yake.



Hakan ke kara duk’unzuma tunanin Modibbo, wanda yakejin
abubuwan suna zuwa masa awasu yanayi na daban.



 



Dab dashi Lalla Salma ta kawo Khausar din, tare da sakin
hannunta, da sauri Rahma ta Æ™araso hannunta rik’e da wani babban glass bowl wanda
cikinsa ke d’auke da kyakkyawan furanni masu fitar da sassanyan k’amshi.



Cikin tsananin farinciki ta soma watsa musu furen, Lalla
Salma kuwa matsowa kusa dashi tayi, tare da ɗan ranƙwafowa ahankali tace.



 



“Abisa al’ada Aleey kai zaka buÉ—e fuskar amaryar taka ka
juyata ta fuskanci family inka su ganta da kyau, kayi Bismillah ka bud’e
fuskarta, idan ka juyata an ganta sai ka riƙe hannunta ku zauna bisa kujerar
nan ka tabbatar kun zauna da bisimilla.”



 



Cikin sauri ya kalleta hadi da kallon Ibraahim dake gefensa
na dama, sunkuyar dakai Ibrahim yayi kana cikin yin kasa da murya yace.



“Dan Allah Yah Aleey kayi abunda Lalla Salma tace, kada kayi
abunda za muji kunya, kar kayi abunda zaisa mutane su fara tunanin babu abunda
ka sani adangane al'adun masarautar da ake tunani za’a damÆ™a maka ragamarta a
hannunka, kayi hakuri dan Allah Yah Aleey!!”



 



Ya k’are maganar cikin magiyan, da yasa Modibbon juyawa ya
kalli Didi  da ta tsura masa ido.



Sai kuma ya É—an juya idonshi ya kalli Innayi wacce itama
kallon nasa take, tare dayi masa alama akan yin biyayya.



 



Idanunsa ya dan lumshe tare da shakan numfashin dake kokarin
kwace masa sabida tsanantan bugun da zuciyarsa keyi.



Cikin bada umarni Sheykh Jabeer ya É—an matse hannunsa dake
cikin nasa, kana ya É—an rongofo tare da faÉ—in.



“Kayi abinda ya dace, umarnin kakarkace macen da tasha wuyan
rainonka tsawon shekaru, kana kuma fata ne da burin mahaifiyarka data raini
cikinka tsawon wata tara da kwana tara, sannan burin mahaifinka kanan”.



A hankali ya buÉ—e lumsassun idanunsa lokaci da yaji
zuciysrsa na bashi umarni.



“BuÉ—e kaga wacece?”. 
ji yake wani abu na fusgarsa, batare da sani ko shiryawa hakan ba, sai
ji yayi hannayensa na motsi, duk da karkarwar da suke.



 



Ganin haka yasa Rahma dake bayan Khausar É—an turo Khausar
din tare da cewa.



“Yes my Aunty jeki kusa da mijinki ya buÉ—e mana fuskarki mu
ganki”.



Sai kuma ta ɗan ƙara ɗan tureta kaɗan da kafaɗarta, wanda
haka yasa Khausar da zuciyarsa ke buga lugude tara-tara ta É—an yi motsi kaÉ—an
da yaɗan ƙara kusancinsu da Modibbo.



 



A hankali ya É—an É—ago hannunsa, yatsunsa biyu yasa gefe da
gefen mayafin nata ya kamo tare da d’an d’ageshi sama, yanajin zuciyarsa nayi
masa wani irin duka uku uku.



Yana janye mayafin kuwa kyakkyawar fuskarta na bayyana.



 



Cikin wani irin baƙin al'amari ya zazzaro idanunsa cike da
kad’uwa had’i da mamakin ganin fuskar Khausar, wani irin masifeffen kasalane ya
rufe mishi jiki da zuciya, a take kuma yaji wani irin abu mai masifar sanyi ya
tsoki ƙahon zuciyarsa, kana a take ya kuma jin wani irin abu daya harba daga tsakiyar
maÉ—igan kansa, ya game dukkan sasanjikinsa, har zuwa kan babbar yatsarsa, wani
abu me kama da mamaki, hadi da mutuwar jiki ne suka lullubeshi lokaci d’aya.



Bak’on yanayi me kama da zazzafar bege da bai tab’a jiba ya
lullube dukkan jikinsa, dake wani irin tsuma.



Hadi da sanya masa wani yanayi na kaucewar tunanin.



Wanda ya sashi bud’e hannayeshi tare da ware  tattausar al'kyabbar dake jikinsa.



Wanda ganin hakan yasa Rahma ɗan ƙara tura Khausar,
kasancewar takalmin da ta sanya me tsinine hakan yasa ta tafiya garesa batare
da ta shiryawa hakan ba.



 



Shi kuwa Modibbo wani irin mataccen numfashi yaja tare da
fesar da sassayan numfashi mai dogon sauti.



Kana ya yayi mata Kekkyawan masauƙi a ƙirjinsa tare bata
cikekkiyar kariya



da yalwatacciyar alƙyabarsa ta hanyar bata wani irin
kyakkyawan runguma, me É—auke da ma’anoni masu tarin yawa, da yafi kama da
tsananin shauki hadi da zallar kewa da bege.



Rungumeta yayi tsam a cikin jikinshi ya mannata da ƙirjinsa
da ƙarfi har yakai ga suna iya jiyo ɗumin jikin junansu wanda kuma tuni yayi
mata garkuwa da yalwatacciyar Al'kebbar jikinsa mai cike da ni'imtaccen ƙamshi.



Lib Khausar tayi a jikinshi tare da shaƙan numfashi daya
wadatu da ƙamshin turaren jikinsa wasu irin tagwayen numfarfashi take fesarwa
tare da lafewa a jikinshi da kyau tamkar mai tsoron kada a janye mata shi haka
nan takejin tamkar a barta ta rayu a kunshi a haka har gaban abadan haka yasa
ta liƙe lip a jiki nai.



 



Shi kuwa Modibbo a hankali ya lumshe idanunsa tare da laso
gefen lip inshi sama,



 



Yanayi ne na musamman a garesu, daya sanya su lumshe jujjuya
kwayar idanunsu a tare, musamman ita Khausar da taji ya lulluɓeta da
alkyabbarsa.



Wata duniya ce ta daban me shiÉ—arwa suka lula.



Cikin wani irin aminci da salama Modibbo ya É—an sunkuyo
kanta kaÉ—an tare da  kawo bakinsa dai-dai
saitin kunnenta.



Cikin sarƙafeffiyar muryarsa me kama da raɗa,cikin tsananin
sanyi, ta yanda ita kadai zata iya jiyoshi atausashe yace.



 



“I miss you my trouble maker. I really miss you my trouble
student.”



 



Wow gaba É—aya falon ya kacame da tafi da sowa.



Sai kuma sarewar da ta karaÉ—e falon.



 



Ummi kuwa wani irin amintaccen numfashi ta fesar.



Yayinda Didi kuwa tayin ƙasa da kanta tana sakin murmushin.



Su Lamiɗo da Malam Arɗo kuwa duk ƙasa sukayi da kansu cikin
konciyar hankali.



Haiydar kuwa wayarshi ya zaro tare da fara musu video,
hakama Rahama.



Yayinda tuni kuma masu É—aukar hoto suka fara kebta musu.



 



Zakariyya ne ya É—an zunguri kafaÉ—ar Modibbo da tashi kafaÉ—ar
tare da cewa.



“Kai Jinin Mouley a tsakiyar mutanefa kuke, ka ritsa yar
mutane kamar zaka maidata cikin Æ™irjinka”.



A can sama ya jiyo muryar Zakariyya wanda ya sashi buÉ—e
idanunsa a hankali.



Hango Lalla Khadijah da wasu mata a ƙalla su bakwai ne ya ɗan
sashi sassauta rungumar da yayi mata.



Tare da É—an jan baya kaÉ—an.



Fuskashi ya ɗan tsuke tare da kara ronƙofo da kanshi a
hankali yasa bakinshi dai-dai iunnenta 
murya can ƙasa yace.



“Toh yau dai burinki ya cika ai, na ruggume ki, hankalinki
ya kwanta tunda kinji É—umin jikina ko? Kin samu abinda kikeso ko”.



Mui-mui tayi da bakinta



Kara matseta ya É—anyi tare da cewa.



“Rashin kunya zakiyi minko”.



 Baki ta É—an tura tare
da cewa.



“Ni ka sakeni”.



ÆŠan haranta yayi tare da cewa.



“Kece ai kike riÆ™e dani mayya uwar son jiki, tashi min a
jiki Mage”.



Da sauri ta É—an janye jikinta kaÉ—an.



Dai-dai lokacin kuma Khadijah suka iso.



Kusan a tare suka fara yi musu wani irin....!

No comments