Sakayyah Book 2 Page 1




 *SAKAYYAH book 2... Page 1*



 



 



Spndeɗɗ. Baya Moddibo ya koma. Suuuuuu ya faɗi a sume, cikin
sauri Lamiɗo ya tarosa, ya faɗa jikinsa cike da tashin hankali Lamiɗo yace.



“Innalillahi ya suma fa Subhanallah!”.



Cikin sauri Malam Arɗo ya ƙara sa kusa da Lamiɗo idanunsa
akan Moddibo ya shiga kiran sunan sa yana faɗin.



“Moddibo!, Moddibo!!, Moddibo!!!”.



Ina tuni Moddibo ya sume babu alamar numfashi atare dashi.



Abba kuwa kansa ya ɗaga tare da kallon fuskar skeleton M
Jameel kana ya maida Idanunsa ƙasa kan takalmin dake sanye aƙafarsa ahankali ya
leƙa bayan idanunsa suka sauƙa akan guntun rigarsa da bai gama sauƙa daga jikin
skeleton ba jinjina kansa yayi cikin wata dakakkiyar murya ya juya ya kalli
Moddibo dake sume kai ya girgiza tare da sakin murmushin da yafi kuka ciwo
murmushi da yafi ihu zafi, murmushin da yafi ciwo, Ciwo murmushin da yafi raɗaɗi
zafi, ya saki kana ya juya ya kalli sauran mutanen dake tsaye sai ya kuma kalli
fuskar skeleton tare da maida kallonsa kan yatsun hannunsa.



Cikin wata dakakkiyar murya me ɗauke da tarin raɗaɗi da ƙuna
yace.



“Uhmmm Jameelu na ne”.



Kallonsa ya mayar kan Moddibo da har zuwa lokacin yake.
Rungume a jikin Lamiɗo taune lips ɗinsa yayi tare da cewa.



“Kai kam Aliyu kahuta, inama ace nima zan sume ko kuma in
mace ma gaba ɗaya da hakan yafi min sauƙi”.



Cikin sauri ɗaya police ɗin 
ya juya tare da isa gefen Abba ya riƙe sa cike da alhini da tarin
tausayawa yace.



“Alhj Bashir kayi addu'a kaji”.



Kai Abba ya gyaɗa cikin wata dakakkiyar murya yace.



_“Innalillahi wa'inna Ilahi rajiu'n lahaula wala ƙuwwata
Illah billahil aliyul Azhim Hasbunallahu wani'imal wakil Allahumma Ajirni fii
musibati wa'ahlifli khairan minha La'ilaha Illah anta subhanaka Inni kuntu
Minal Zhalimin”_ sune Adduo'in da yake iya maimaitawa afili da kuma ransa.



 



Ori dake tsaye ciki ruɗu da tausayawa yayi saurin ƙarasawa
gaban skeleton gawar M Jameel ya ɗauko goran ruwan kana ya dawo tare da miƙawa
Lamiɗo yana mai cewa.



“Lamiɗo gashi ayayyafa masa”.



Karɓa Lamiɗo yayi kana ya buɗe tare da yayyafawa Moddibo
dake kwance jikinsa amma ko kaɗan Moddibo bai motsa ba.



Kallon Buba Lamiɗo yayi kana yace.



“Ori taimaka min mu saka shi cikin Mota”.



Kai Buba ya gyaɗa.



Ɗaya daga cikin Folisawan ne yace.



“Ranka shi daɗe bari mu saka shi”.



Ya faɗa tare da kallon ɗan gidansa da Ido ya masa alamar
yazo su kama Moddibo ƙarasawa yayi sannan suka ɗauki Moddibo suka sauƙa kasan
dutsen, tare da sanya shi abayan Motar Malam Arɗo.



 



Folisawan kuwa ƙara sawa sukayi suka shiga ɗaukar hoton
gawar skeleton M Jameel.



Bayan sun gama ɗauka tare yan dube-dubensu, da Babbansu da
sauran suka saka handglove suka ƙarasa gaban gawar da niyyar sunjanye gawar
Babbansun  najan Igiyar da aka ɗauɗaureshi  ƙasusuwan suka kakkarye tare da zubewa a ƙasa
babu ta yanda zasu iya daukarsa Babban su ya umarci Coustable yaje ya ɗauko
musu kwali abayan mota kana suka tattara gawar suka zuba acikin kwalin kana
suka kwashe takalmansa da wayoyinsa suka saka awata leda.



Abba kuwa cikin wani irin yanayi ya nufi cikin jejin  yana tafiya ba tare da shi kansa yasan inda
ya nufaba.



Cikin sauri Lamiɗo ya nufesa tare da riƙe hannunsa cike da
tausayawa yace.



“Alhj banan zamu bi ba can baya ne, hanyar kazo innu na maka
hanyar da zamu bi”.



Kai Abba ya gyaɗa tare da bin bayan Lamiɗo baki ɗaya baya
cikin nutsuwarsa ya kasa gane shin mafarki yake ko kuma azahirance komai ke
faruwa.



Bayan sun isa Lamiɗo da kansa ya buɗe masa mota yashiga
sannan shima yashiga.



 Folisawan kuwa kwalin
da gawar M Jameel ke ciki suka ɗauka tare da sawa abayan motarsu suka tafi
gida.



Abba kuwa kallon hanya kawai yake baki ɗaya baya cikin
hayyacinsa ganin yanayin da yake ciki ne yasa Malam Arɗo ya fara yi masa
Adduo'i yana tofa masa kana yana faɗa afili.



Ahankali Abba ya fara sakin Ajiyar zuciya kana yashiga
maimaita Adduo'in sannu Ahankali ya fara jin hankalinsa ya fara dawowa jikinsa.



Motar da Moddibo ke ciki Ori da police ɗaya ne aciki direct
Asibiti suka nufa dashi.



 



Yayin da Motar dasu Abba da kuma gawar M Jameel ke ciki kai
tsaye gida suka wuce, suna isa kai tsaye falonsa suka wuce police ɗin ne ya ɗauko
kwalin Gawar M Jameel ya shigo dashi kana ya ajiye agabansu.



Hajiya Turai dake sashenta tana jin tsayuwar motoci ta fito
zuwa falon Abba.



Ganin Abba zaune tare dasu Lamiɗo yasa ta nufi gefen Abba
cikin yanayin damuwa tace.



“Alhj lafiya ya ake ciki Gawar waye kuka samu?”.



Ahankali ya ɗago Idanunsa da suka kaɗa sukayi jawur ya
kalleta kana yayi ƙasa da kansa cikin raunin murya yace.



“Gawar Jameelu na ne!”.



Arazane Hajiya Turai ta kallesa zuciyarta na bugawa da
masifar ƙarfi Idanunta akansa tace.



“Gawar Jameelu kuma!?”.



Kai ya gyaɗa mata Cikin tsananin tashin hankali da ruɗu ta
fashe da kuka me tsuma zuciya tana furta.



“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n ina gawar yake?”.



Da hannu ya nuna mata kwalin dake gabansa.



Da kallo tabi kwalin cikin sauri ta sake Kallonsa Idanunta
cike da ruwan hawaye tace.



“Gawar Jameelu ne acikin kwali haka?”.



Kai ya gyaɗa batare daya ɗago kaiba yace.



“Shine”.



Wani sabon kuka ta fashe dashi tana Girgiza kai Kukanta ne
ya fito da Hajiya Karima itama ganin abinda ke faruwa yasa ta fashe da kuka.



 



Acan Asibiti kuwa ana kai Moddibo likitoci suka shiga bashi
temakon Gaggawa saidai koda wasa bai farfaɗo ba ganin haka yasa suka dauƙo wani
na'ura mai kama da Iron akafara danna masa aƙirji.



Amman ina babu alamun zai motsa, sosai likitocin suka dugufa
wurin ganin sun cetoshi, a karo na biyu suka kuma danna mishi a ƙirjunshi,
amman ina, Dr Lukman ne ya karɓi aikin tare da goggoga jikin na'urar ya manna
masa a kirjinsa da ƙarfi.



Cikin ikon Allah yaja wani dogon numfashin sake dannawa yayi
da karfi wani irin maraitaccen numfashi ya sake ja amma still bai farfaɗo ba
sake dannawa sukayi akaro na biyar ne yaja wani dogon numfashi tare da buɗe
idanunsa kana yace.



“Jyyyyyyy”.



Malam Arɗo da bai daɗe da dawowa daga gidan Abba bane,  yayi saurin riƙe hannunsa tare da cewa.



“Moddibo kayi addu'a”.



Duk da cewa baya Cikin nutsuwarsa hakan bai hanashi maimaita
duk wata addu'a da tazo bakinsa ba ahankali ya ɗago kansa tare da kallon Malam
Arɗo yace.



“Malam J ɗina nefa!”.



Jinjina kai Malam Arɗo yayi cike da tausayawa yace.



“Eh shine Moddibo Allah ya karɓi Jameelu muyi masa addu'a
Allah ya karɓi shahadarsa”.



Girgiza kai Moddibo yayi tare da cije lips ɗin sa duka biyu,
kana ya runtse Idanunsa cikin wani irin yanayi mai wuya yace.



“Malam Arɗo mutuwar azaba suka masafa, ɗaure sa sukayi suka
ajiye masa goran ruwan agabansa ta yanda yana ji yana gani bashi da damar sha
sun barshi da azabar ƙishi”.



Kallonsa Malam Arɗo keyi cike da tausayawa yana ganin yanda
zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.



Cikin wata raunan'niyar murya Moddibo ya cigaba da cewa.



“Malam ɗaure sa sukayi suka ajiye masa wayoyinsa agabansa ta
yanda yana kallon muna kiransa bashi da damar ɗauka bare yace mukawo masa ɗauki”.



Sai kuma ya rintse idanunsa da masifan ƙarfi zuciyarsa na
cigaba da buguwa da masifaffen ƙarfi kana yace.



“Ɗaure sa sukayi ta yanda yana ganin ga hanyar tsira sai dai
bashi da damar kiran wani ya kawo masa ɗauki ɗaure sa fa sukayi ta yanda yana
ganin kiran mu amma bashi da damar ɗauka”.



 Jujjuya kansa ya
farayi kamar zautacce hawaye na bin gefe da gefen idanunsa har suna shiga
kunnensa cikin Muryan kuka yace.



“Ɗauresa fa sukayi ta yanda yana ganin kiran Abbansa bashi
da damar ɗauka,Mutuwar azaba da raɗaɗi suka masa da ƙishi fa suka kasheshi”.



Kasa ƙarasa maganar yayi kawai ya fashe da matsanancin kuka
mai tafiya da numfashi Atake numfashinsa ya ɗauke ya sake sumewa!.



 



Cikin sauri Malam Arɗo ya miƙe tare da kiran likitoci kana
ya sanar dasu ya sake suma taruwa likitocin sukayi akansa kana suka shiga bashi
temakon Gaggawa da kyar da temakon Allah suka samu ya farfaɗo ganin ya farfaɗo
yasa Dr ya masa Alluran bacci Atake baccin wahala ya ɗauke sa.



Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe tare da miƙewa ya fita
kana yayi dearling number Lamiɗo yana ɗauka yace.



“Ranka shi daɗe yaron nan fa gashi agigice yake baki ɗaya da
zaran ya farfaɗo sunan Marigayi Jameelu yake kira, yana kiran sunan kuma zai
sake suma!”.



 



Acan gidan Abba kuwa zaune yake afalonsa hannunsa riƙe da
waya tunda suka dawo yake zaune awajen ya kasa koda motsawa se kwalin Gawar
Jameelu daya zubawa Ido yana jujjuya wayar hannunsa ajiyar zuciya ya sauƙe tare
da kiran number Ummi Yana Jin tayi picking ya fesar da numfashi kana yace.



“Fatima”.



Cike da mamaki Ummi tace.



“Abban Jameel”. Jin muryansa.



Cikin raunin murya ya sake cewa.



“Fatima”.



Anutse Ummi ta amsa da.



“Na'am”.



Runtse Idanunsa yayi kana yasake cewa.



“Fatima”.



Cikin dakiya Ummi da taji zuciyarta ya tsinke da Masifar
ƙarfi tace.



“Na'am Abban Jameel ka faɗa min me yasamu Jameelu na sun
kira ne ko kuma yaya!?”.



Cikin rauni yace.



“Hmmm”.



ya faɗa tare da katse kiran kana ya fito da Number Malam
Ahmad.



 



Malam Ahmad na ɗagawa Abba yace.



“Malam kazo da Fatima da yaranta!?”.



Cikin tsinkewar zuciya Malam Ahmad dake Bedroom ɗinsa ya
miƙe tare da cewa.



“Meya faru Alhj Bashir ka faɗa min”.



Girgiza kai Abba yayi tare da taune lips ɗinsa kana yace.



“Ga gawar Jameelu na agabana”.



Cikin tsanananin tashin hankali Malam Ahmad ya dafe bango
tare da faɗin.



“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Allahumma Ajirni fii
musibati wa'ahlifli khairan minha”.



Katse kiran Abba yayi cikin sauri ya fito falon tsaye ya
samu Ummi riƙe da waya a hannunta cikin ƙoƙarin ɓoye tashin hankalin sa yace.



“Fatima Lafiya!?”.



Ahankali Ummi ta juya ta kallesa tare da cewa.



“Yan zun nan Abban Jameel ya kirani, to kuma ya yanke gashi
kuma ina ta sake kira naji line Busy”.



Da ƙyar ya haɗiye wani abu mai masifar ɗaci  kana cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarsa yace.



“Toh kada ki damu kizo muje muji meke faruwa”.



Kai ta gyaɗa tare da cewa.



“Toh”.



Sannan ta nufi hanyar fita.



Kallon Bashir da Asma'u dake tsaye yayi kana yace.



“Kuma kuzo mu tafi”.



Kai suka gyaɗa kana suka bi bayansa suka fita.



 



Suna isa falon suka samu Hajiya Turai da Hajiya Karima da
ƴaƴan Hajiya Karima na kuka cikin sauri Ummi ta ƙara sa shiga falon tare da
tsayawa agaban Abba kana tace.



“Abban Jameel meye faru?”.



Ahankali ya ɗago ido ya kalleta, sai alokacin yaji kuka ya
kufce masa ganin Ummi agabansa baki ɗaya ta gigice jikinta na rawa.



Cikin rawan murya tace.



“Abban Jameel meyafaru!?”.



Kasa cewa komai Abba yayi sai kuka da yake tamkar ƙaramin
yaro.



Da sauri Ummi ta juya tare da kallon yanda su Hajiya Turai
ke kuka cikin rawan murya da yanayin tashin hankali tace.



“Ku faɗa min mana meke faruwa!?”.



Tayi tambayar baki ɗaya ilahirin jikinta na rawa.



Asma'u da Bashir dake tsaye Atare suka fashe da matsanancin
kuka ganin yanda ƙannen M Jameel ke kuka.



Ahankali Malam Ahmad ya matso kusa da Ummi tare da cewa.



“Fatima ki zauna”.



Girgiza kai tayi kana tace.



“Ni bazan zauna ba kafaɗa min abinda ke faruwa”.



Cikin sanyin murya Lamiɗo yace.



“Maman Jameel kiyi haƙuri ki zauna”.



Kallon sa tayi tare da cewa.



“In zauna?”.



Kai ya gyaɗa mata kana yace.



“Eh”.



Cike da tausayawa Malam Ahmad ya janyo hannunta tare da
zaunar da ita.



 



Abba kuwa kallonta yayi cikin tsanananin fargaba da tashin
hankali yace.



“Fatima”.



Cikin rawan murya da raunin zuciya tace.



“Na'am Alhj Bashir”.



Cikin sauri Abba ya kalleta wannan shine karo na farko
arayuwar sa da yaji ta kira sunan shi kai tsaye.



Jinjina kai tayi Idanunta tsaye akansa tace.



“Eh Alhj Bashir ka faɗa min menene? kafaɗa meke faruwa”.



Rintse idanunsa yayi yana jin kansa na sarawa Araunane yace.



“Fatima Jameelun mu”.



Kai ta gyaɗa kana tace.



“Eh nasani akan Jameelu ne to Menene ya faru?”.



 



Kasa cewa komai Abba yayi kawai sai ya fashe da matsanancin
kuka yayin da hawaye ke bin kuncinsa Shar-shar-shar.



Cikin raunin murya yace.



“Fatima ga Gawar Jameelun mu”.



Atake maganar ya daki dodon kunnenta kana ya ratsa
ƙwaƙwalwar ta zuwa zuciyarta saurin kallon Abba tayi tare da sakin Murmushi
kana ta juya tare da kallon su Hajiya Karima dake kuka cikin wata dakakkiyar
murya mai cike da ƙuna tace.



“Toh kukan me kukeyi!?,



Juyawa tayi tare da kallon Abban M Jameel kana tace.



“Har kaima kuka kakeyi!?Haba Alhj Bashir Addu'a ya kamata ka
masa amma ba kuka ba!, Su mata suyi kuka kaina kayi Yanzu ina yake?”.



Cikin sheshsheƙan Kuka Abba ya nuna mata kwalin da ya tsarsa
kana yace.



“Gashi can”.



Saurin Kallon wajen tayi Zuciyarta na bugawa da masifar
ƙarfi still Muryanta adake da wani irin bushewa da hurawar zuciya tace.



“Gawar ne kuma acikin kwali”.



Cikin wata raunan'niyar murya ya Girgiza kai kana yace.



“Kiyi haƙuri kiyi ta maimaita Addu'a”.



 



Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da rintse Idanunta kana tace.



“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Hasbunallahu wani'imal
wakin La'ilaha Illah anta subhanaka inni kuntu Minal Zhalimin Allahumma Ajirni
fii musibati wa'ahlifli khairan minha³”.



Ahankali ta gyara zamanta tare da naɗe ƙafafunta  tare da sakin murmushi kana ta fuskanci gabas
yayin da Idanunta suka kaɗa sukayi jawur jikinta na wani irin tsuma na tsananin
tashin hankali cikin raunin murya tace.



“Ya Allah kaine ka bani Jameelu, kai kasa ya zamemini
Garkuwa, ya Allah kajiƙan sa da rahma, ya Allah kasa ya huta Alfarman Annabi da
Alkur'ani, Allah kayi mana SAKAYYAH akan dukkan waɗanda suka cutar damu ya
Allah kayi mana SAKAYYAH”.



Kusan a haɗe baki daya mutanen falon suka amsa da Ameen.



Wani irin kuka mai tsuma zuciya ne ya kufcewa Asma'u da
Bashir musamman Asma'u numfashinta har fisga yake baki ɗaya Falon kaurewa yayi
da koke cikin rawan murya Ummi tace.



“Ina gawar yanzu Jameelu na ne haka acikin kwali?”.



Jinjina mata kai Abba yayi tare da cewa.



“Eh shine”.



Still Muryanta adake tace.



“Wani irin mutuwa yayi da har gawarsa zata ƙankace ya zauma
acikin kwali”.



 



Asp dake tsaye ya kalli Ummi cike da tausayawa yace.



“Hajiya kiyi haƙuri ya riga daya bushe, shiyasa ana taɓa shi
ya kakkarye!”.



Ahankali ta juya ta kalli Asp kana tace.



“Toh ya akayi kuka tabbatar Jameelu na ne?”.



Cike da tausayawa Asp ya ƙara sa gaban Kwalin kana ya buɗe
mata ahankali Ummi ta tsirawa jerarrun gabɓan gawar dake cikin kwalin ido
ahankali ta sauƙe Idanunta akan zara-zaran yatsun, hannunsa da suka bushe kana
ta tsirawa zoben hannunsa ido.



Cikin wani irin yanayi na ƙunan zuciya da sadaukarwa tace.



“Hmmm!”.



 



Ahankali Asp ya sake nuna mata takalmin M Jameel dake cikin
leda da kuma wayoyinsa cikin sanyin murya yace.



“Ga takalmansa da kuma wayoyinsa duk agabansa muka samu sun
ajiye masa da goran ruwa.



 



Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da fesar da numfashi kana tace.



“Tabbas Jameelu na ne”.



Ahankali ta matsa jikin kwalin sosai tare da sanya tafin
hannunta ta rufe kana ta sunkuyar da kanta akan kwalin cikin Muryan ta daya
fara karaya tace.



“Babana bazan yi maka kuka ba, sannan baza zubar maka da
hawaye ba, kana bazan yi maka Ihu da kururuwa ba, amma zan ƙarashe baki ɗaya
sauran rayuwata ina maka addu'a, zan ƙare rayuwata da ƙunan rashinka zan ƙare
rayuwata babban giɓin rashinka”.



 



Wani irin tausayinta ya ratsa baki ɗaya jama'ar dake falon
ahankali Malam Ahmad da Lamiɗo suka sanya hannu tare da share hawayen da suka
saƙƙo musu.



Cike da rauni Ummi ta cigaba da cewa.



“Babana zan ƙare baki ɗaya sauran rayuwata ina maka addu'ar
Ubangiji ya karbi shahadarka Allah ya maka SAKAYYAH tun daga nan duniya akan wa
anda suka zalince ka har zuwa ranar tashin Alkiyama. Allah Ubangiji yajiƙan ka
da rahma Allah ya gafarta maka yasa kahuta”.



Cikin sauri Hajiya Turai ta ƙarasa kusa da ita tare da
Rungumeta ajikinta kana cikin Muryan kuka tace.



“Kiyi haƙuri Hajiya Fatima kiyi shiru”.



Kallonta Ummi tayi still Muryanta adake tace.



“Idan banyi haƙuri ba Hajiya Turai ya zanyi. Ubangijin daya ɗauke
Jameelu shi yabani shi kuma shi ya ɗauke sa kana ya fini sanin wanene Jameelu
agareni, sannan ya fini sanin Jameelu Allah ya masa rahma”.



Ta ida maganar tare da janye Jikinta daga na Hajiya Turai
tare da juyawa ta kalli Abba kana tace.



“Ina Moddibo!?”.



Tana gama fadar haka tayi baya tare da sumewa.



 



Cikin sauri Hajiya Karima ta mike tare da ɗauko ruwa ta
yayyafa mata dogon numfashi Ummi taja tare da buɗe Idanunta kana tace.



“Ina Moddibo yake?”.



Cike da tausayawa Abba yace.



“Moddibo yana asibiti asume tunda abin ya faru daya farfaɗo
idan ya kira sunan Jameel zai sake sumewa, yanzu ne da aka samu ya farfaɗo aka
masa Alluran bacci”.



Araunane tace.



“Ku kaini inga Moddibo sannan kada aje abinne Jameelu abari
sai Moddibo ya farfaɗo yaga J ɗinsa na ƙarshe ya tabbatar cewa J dinsa tafi ya
barsa bari na har abada, idan yaga haka zai dangana ya sawa ransa haƙuri amma
yanzu dan Allah ku kaini wajen Moddibo”.



Abba ne yace.



“Yanzu zaki tafi can?”.



Kai ta gyaɗa tare da cewa.



“Eh ku kaini wajensa”.



Ahankali Malam Ahmad ya miƙe tare da riƙe hannunta suka
tafi.



 



Asma'u da Bashir kuwa kuka suka sake fashewa dashi har
muryarsu baya fita saboda tsananin tashin hankali.



Rintse Idanu Abba yayi cike da tausayawa ya kallesu kana
yace.



“Ku daina kukan nan kuyi masa addu'a babu abinda Jameelu ke
buƙata awajenmu yanzu kamar addu'a.



 



Acan asibiti kuwa Ummi da Malam Ahmad na isa  a reception suka samu Malam Arɗo tsaye
ganinsu yasa ya ƙara sa kusa dasu kana yace.



“Maman Jameelu kiyi haƙuri. Ubangiji Allah ya jikansa da
rahma Allah ya gafarta masa Ubangiji ya amshi shahadarsa”.



Cikin sanyin murya tace.



“Ameen Malam Arɗo ina Moddibo?”.



Ahankali ya gyara tsayuwar sa kana yace.



“Gashi can yana ciki”.Ya faɗa tare da shiga gaba Ummi da
Malam Ahmad na biye dashi.



Suna shiga ɗakin Ummi ta zubawa Moddibo idanu dake kwance
plat Fuskarsa tayi fayau duk da bacci yake amma tashin hankali da fargaba ne
kwance asaman fuskarsa.



Ahankali ta riƙe hannunsa acikin nata kana tace.



“Moddibo munyi rashi, rashin da baza mu maimaita gurbinsa
ba, munyi rashi rashin da har abada ba zamu mance shiba, munyi rashi rashin da
saidai namu mutuwar ne zai mantar mana dashi”.



Moddibo kuwa duk da Alluran baccin dake jikinsa hakan bai
hana shi jiyo sautin muryan Ummi ba. So yake ya farka domin kunnuwansa na
sauraronta haka zalika yana iya motsa gaɓɓansa sai dai koda ya buɗe idanunsa
baya ganin komai cikin wani irin yanayi ya damƙe hannun Ummi acikin nasa,
yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da masifar ƙarfi.



Kallon Malam Ahmad Malam Arɗo yayi kana yace.



“Toh tunda kunzo bari na wuce na faɗawa Kakarsa halin da ake
ciki”.



Jinjina kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.



“Ya kamata kam aje afaɗa mata sannan itama ataho da ita”.



 



Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana ya juya ya fita kai tsaye gidan
su Moddibo ya nufa yana isa yayi Parking ɗin motarsa kana ya shiga gate din
farko ya daga sautin muryarsa tare da yin sallama.



Cikin sauri Innayi ta fito ganinsa yasa ta saki Ajiyar
zuciya tare da cewa.



“Alhamdulillah dama yanzu nake tunanin in kira ka dan.
Moddibo tun safe daya fita bai dawo ba, duk da cewa dama yanzu bai cika dawowa
da wuri ba”.



Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe kana yace.



“Ki zo mutafi”.



Saurin Kallonsa tayi kana tace.



“Ina zamuje”.



Cikin sanyin Murya Malam Arɗo yace.



“Wajen Moddibo zamuje yana asibiti”.



Da sauri ta dafe ƙirjinta sai kuma ta juya ta nufi cikin
gida hijabinta ta ɗauko ta sanya kana ta rurrufe kofofin gidan kafin ta fita.



Bayan sun fara tafiya acikin motar Malam Arɗo ya kalli
Innayi kana yace.



“An samo gawar Jameelu fa!”.



Cikin tsanananin ruɗu da tashin hankali ta dafe ƙirjinta
tare da faɗin.



“Gawar Jameelu kuma?”.



Kai Malam Arɗo ya gyaɗa kana yace.



“Eh gawar Jameelu aka samu sun kashe sa”.



Atake hawaye suka shiga zubowa Innayi cikin tashin hankali
da jimami ta saki sassayan kuka tare da addu'o'i.



 



A dai daren wannan ranar haka kowa ya kwana cikin ƙunci da
raɗaɗi azuciya.



 Asp da tawagarsa sun
koma gida bayan sun gama dukkan abinda ya dace na bincikensu, haka zalika  Lamiɗo ma ya koma gida Abba kuwa kwana yayi
da gawar Jameelun sa agabansa batare daya rintsa ba.



 



 Asma'u kuwa Hajiya
Turai ta jata zuwa ɗakinta Anan ta kwana duk da cewa ba tayi bacci ba.



 Bashir kuwa aɗakin
ƙannen M Jameel ya kwana tare dasu Aɓangaren Moddibo kuwa haka ya kwana cikin
wani irin yanayi shi ba bacci ba kuma kuma shiba Ido biyu ba ba kuma a sumeba.



Ana kiran Assalatun Farko acikin kunnen Moddibo sannu
Ahankali ya fara bude idanunsa da yaji sunyi masifar nauyi har ya sauƙesu akan
Ummi dake riƙe da hannunsa Idanunta abushe alamar ko rintsawa ba tayi ba bare
kuma bacci.



Cikin wata murya mai cike da karaya da kuma rauni yace.



“Ummi”.



Kallonsa Ummi tayi tare da faɗin.



“Na'am Aliyu”.



Girgiza kai yayi yayinda zuciyarsa ke cigaba da bugawa da
masifar ƙarfi yace.



“Ummi J ɗina”.



Cike da tausayawa ta rintse Idanunta kana tace.



“Aliyu kayi haƙuri”.



Cije Lips ɗinsa yayi tare da damƙe hannunta acikin nasa kana
yace.



“Ummi J ɗina”.



Jinjina kai tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya tace.



“Kayi haƙuri kaje kayi sallah duk abinda kake ji Aranka kana
so ka faɗa min ka faɗawa Ubangiji”.



 



Cikin sauri Malam Ahmad dake tsaye ya ƙara so bakin gadon
tare da riƙe hannun Moddibo cikin sanyin murya yace.



“Kayi haƙuri kaje kayi alwala”.



Kallon Malam Ahmad Ummi tayi kana tace.



“Toh ni yanzu zan tafi gida”.



Girgiza kai Malam Ahmad yayi tare da cewa.



“A'a ki bari mu tafi gidan Alhj Bashir yanzu”.



Girgiza kai tayi kana tace.



“A'a mu tafi gidanmu dai”.



Girgiza mata kai yayi kana yace.



“A'a gidan Alhj Bashir zamu je acan fa za ayi jana'izar mu
tafi can ɗin!”.



 



Shiru kawai Ummi tayi ahankali.



 Moddibo da har yanzu
hannunsa ke cikin nata yace.



“A'a Ummi dan Allah muje gidan Abba”.



Kai ta gyaɗa masa cikin sanyi tace.



“Toh shikenan”.



Batare da an sallamesu ba suka fita Moddibo da Malam Ahmad
suka shiga gaba Ummi tashiga baya Anutse Malam Ahmad yayiwa motar key kana yaja
suka bar Asibitin kai tsaye gidan Abba suka nufa suna isa Malam Ahmad ya danna
hong ta cikin ƙaramin ɓulin. Mai gadi ya leƙa jin ana ta danna hong ganin motar
da tazo jiya da safe ne yasa ya koma cikin gida tare da sanarwar Abba yaga
motar da jiya tazo yauma ta dawo.



Kai Abba ya gyaɗa kana yace.



“Eh kaje ka buɗe musu Maman Jameel ne yanzu aka sallame su
daga asibiti kaje ka buɗe musu”.



Kai ya gyaɗa sannan ya buɗe musu gate din suka shiga bayan
Malam Ahmad yayi Parking suka fito kai tsaye falon Abba suka shiga.



Zaune suka samesa shi kaɗai a falon hannunsa riƙe da Carbi
ya tsirawa kwalin Gawar Jameel Ido.



Ahankali Ummi ta ƙarasa tare da zama agefen kwalin shima
Moddibo zama yayi agefen kwalin Malam Ahmad ma ya zauna agefen kwalin sai ya
zamana sun saka kwalin Atsakiyar su.



Moddibo kuwa kallon kwalin yayi kana ya kalli Ummi cikin
raunin murya yace.



“Ummi yanzu J ɗinane aciki?.



 Ummi da gaske J ɗina
ne ya rasu!?”.



Kai Ummi ta jinjina kana tace.



“Da gaskene Moddibo, tabbas Jameelu ne yarasu Jameelu ya
tafi yabar mu bari na har abada, ba zamu sake ganinsa ko jin sautin muryarsa ba
sai dai ahoto”.



Girgiza kai Moddibo yayi tare da ɗaura kansa akan kwalin ya
fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya cikin sheshsheƙan Kuka yace.



“Yanzu shikenan J ɗina mun rabu har abada bayan yana burin
yin Aure ya zauna gida ɗaya da Ummi da ƙannensa yanzu shikenan wannan burin ya
tafi”.



Ya sake Rungume Kwalin tare da cewa.



“Yanzu shikenan J ya tafi ya barni shin dawa zan rayu duk
wani farin ciki ne da walwala na J ɗina ne shin waye zai fahimcini a duniya? J ɗina
ne kaɗai yake iya fuskarta halin da nake ciki shikenan sun rabani da aminina
kuma farin cikina!”.



Wani irin tausayinsa ne ke ratsasu Abba kam kasa daure wa
yayi ya sunkuyar da kansa ƙasa hawaye na zuba.



 



Cikin sheshsheƙa Moddibo ya ɗago kansa tare da kallon Ummi
idanunsa cike da ruwan hawaye yace.



“Shikenan Ummu sunyi mai kisan gillah, sun hanashi shan
ruwa, ya mutu da kishi da begenmu, yana ganin muna kiransa amma bashida damar ɗauka,
Ummi ashe duk kiran da mukewa J yana kallon kiran mu!”.



Sai kuma ya kife kansa akan kwalin hawayen sa na sauka akai
yace.



“Ummi J yana ganin kiran mu amma bazai iya ɗagawa ba Ummi
sun azabtar da J ya mutu da tsananin begenmu da muradin son kasancewa damu Ummi
sun cutar da J mutumin da koda ƙwaro baya iya cutarwa bare bil adam shin wani
irin zunubi suka aikata!”.



 



Jin ankira assalatu yasa Malam Ahmad sauƙe ajiyar zuciya
tare da cewa.



“Moddibo kayi haƙuri ku tashi muyi alwala mu tafi
masallaci”.



Ahankali Moddibo ya ɗago kansa akan kwalin daya jiƙe da hawayensa
cikin ransa yace shikenan J ya tafi yabarni bari na har abada shikenan ni kaɗai
zan rayu.



Hajiya Turai ce ta shigo falon tare da jan Ummi suka tafi ɗakinta
Anan sukayi sallah.



 



Dole Gawar M Jameel yanda ya kasance a kakkarye ahaka aka
yayyafa masa ruwa madadin wonkan kana aka kaisa makwancinsa na gaskiya.



 Jana'izar data samu
halarta ɗumbin jama'ar domin kafin gari ya waye mutuwar ta zagaye cikin
Gembulan da kewayenta har Taraba Yola da dai sauransu.



 



Rayuwa tayiwa duk wani makusancin M Jameel ƙunci da zafi
musamman Ummi, Abba, Moddibo, Asma'u, Bashir daga Jiya zuwa yau sunyi wani
masifaffen ramewa kallo ɗaya zaka musu kasan cewa suna cikin tsananin ƙuncin
rayuwa musamman Moddibo baki daya ya fita cikin hayyacinsa duk ya gigice ya
sake zama wani shiru.



 



Misalin ƙarfe biyu na rana bayan andawo daga sallar
jana'izar M Jameel Lamiɗo ya koma gidansa kai tsaye falon Mommy ya shiga
bakinsa ɗauke da Sallama.



Anutse Mommy da Khausar dake zaune suka amsa masa Sallamar.



Cike da kulawa Mommy tace.



“Sannu da zuwa yinin yau duk baka nan sau biyu ina zuwa
sashenka”.



Zama yayi akan 3sitter tare da sauƙe ajiyar zuciya kana ya
jingina bayansa da jikin kushin ɗin tare da lumshe idanunsa kana yace.



“Eh yanzu na dawo daga jana'iza”.



Cikin sauri ta kallesa tare da cewa.



“Jana'iza kuma?”.



Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.



“Eh”.



Gyara zama tayi tare da faɗin.



“Janaizar waye!?”.



Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dafe kansa kana yace.



“Janaizar Jameelu”.



Cikin sauri Khausar ta dafe ƙirjinta tare da kallon Lamiɗo
kana tace.



“Abbah waye”.



Kallonta Lamiɗo yayi kana yace.



“Malam Jameelu”.



Cikin tashin hankali Mommy tace.



“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n Jameelu Yayan Asma'u”.



Kai Lamiɗo ya gyaɗa kana yace.



“Eh shi ɗin dai Allah ya masa rasuwa”.



Cike da kaɗuwa tace.



“Innalillahi Ayyah Ummin Asma'u Allahu Akbar duniya yanzu
yaron nan kashesa sukayi”.



 



Khausar kuwa tunda ta dafe hannunta aƙirji ta kasa koda
ƙokƙwaran motsi ne wani irin bugawa da masifaffen ƙarfi zuciyarta keyi.



Atake wani irin kuka mai tsuma zuciya ya kufce mata cikin
sheshsheƙan kuka mai cike da tausayi da tashin hankali tace.



“Abba Yaya Jameel ya rasu!? Abba kashe Yah Jameel sukayi?
Abba me yayi musu da zasu kashesa, suka rabasa da rayuwarsa”.



Kai ya gyaɗa mata kana yace.



“Eh Khausar sun kashesa kisa mafi ciwo".



Sau kuma ya zayyane musu yanda suka samu labarin har suka je
wajen da kuma yanda suka samu gawar.



Cike da tausayawa Khausar ke jujjuya kai tana cigaba da kuka
yayinda numfashinta ke sarƙewa.



 



Kallon Mommy da hawaye ke kwaranya daga idanunta Lamiɗo yayi
kana yace.



“Tun jiya ne, ai muka samu gasar, ban dai faɗa muku bane,
dan kada in hanaku bacci.



Yanzu ku shirya anjima idan anyi Sallar La'asar zan kaiku
gidan kuyi musu ta'aziyya”.



Cikin muryan kuka Mommy ta gyaɗa masa kai cike da rauni
tace.



“Ayyah Ummin Jameel ta ɗandani mutuwa me raɗaɗi da ƙunan
zuciya”.



Ta faɗa tana tuno Ramadan domin ko Rasuwar Ramadan bata samu
tayi kuka haka ba bayan Lamiɗo ya sake rarrashin sune ya miƙe ya nufi sashen
Hajiya Bunayya ya sanar mata.



Khausar kuwa Kuka takeyi tamkar zata mace.



 



Bayan anyi sallar La'asar Lamiɗo ya ɗebe su suka tafi gidan
Abba.



 



 Suna zuwa falon
Hajiya Turai suka nufa Cikin gidan da falon cike yake da mutane ƴan ta'aziyya
duk wanda yaji rasuwar M Jameel da kuma yanda aka samu gawarsa saiya zubda
hawaye tare da la'antar wa anda suka aikata masa haka.



 



Asma'u dake gefen Ummi zaune Idanunta cike da hawaye tana
ganin Khausar ta fashe da sabon kuka kana ta miƙa mata hannu cikin sauri
Khausar ta kamo hannunta tare da zama gefenta ta.



 Rungume juna sukay
tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.



Mommy da Hajiya Bunayya kuwa kusa da Ummi suka zauna.



Mommy na Kallon Ummi taji wasu sabbin hawaye sun zubo mata
cike da tausayawa Mommy tace.



“Ummi Sannu”.



Sunkuyar da kai Ummi tayi cike da dauriya tace.



“Toh ya zamuyi Aysha ya zamuyi da hukuncin Ubangiji.



 Jameelu ya riga mu
gidan gaskiya ya tafi ya barni da gurbin da bansan ya zai cikeminba”.



Kai Mommy ta gyaɗa tare da cewa.



“Kiyi haƙuri Ummi”.



Kasa ƙara sawa tayi sabida kuka yaci ƙarfin ta kawai saita
kife kanta gefen Ummi ta shiga rera kuka.



Ajiyar zuciyar Ummi ta sauƙe cikin sanyin murya me ɗauke da
ƙuna tace.



“Kiyi haƙuri Aysha haka Ubangiji ya tsara bamu isa muja da
lamarinsa ba addu'ar mu suke buƙata muyi musu addu'a Allah ya gafarta musu”.



Cikin sheshsheƙa Mommy tace.



“Ameen”.



Ahankali Mommy ta juya suka gaisa da Hajiya Turai da Hajiya
Karima sannan da ƙannen Abban Jameel Hajiya Maryam da Hajiya Fa'iza suka yi
musu ta'aziyya.



 



Khausar dake Rungume da Asma'u cikin Muryan kuka tace.



“Asma'u yanzu da gaske Yah Jameel ya rasu shikenan ya tafi
ya barmu!”.



Kai Asma'u ta gyaɗa tare da cewa.



“Da gaske Khausar Yah Jameel ya rasu shikenan gatanmu ya
rasu rufin asirin mu ya tafi garkuwan mu ya barmu Inuwarmu wajen fakewar mu ya
gushe, bangon da muke jingina muji daɗi ya fadi ƙasa”.



Kasa ƙara sawa tayi kawai ta fashe da kuka me tsuma zuciya.



Cikin sauri Ummi ta girgiza mata kai Araunane tace.



“Kul Asma'u!,Kada ki faɗi haka kada kiyi butulci ga Ubangiji
domin shi ya bamu Jameelu kuma shi ya ɗauke mana shi kuma zai jibanci laluranmu
muddin mukayi tawakkali”.



Innayi dake gefe ta matso kusa da Asma'u da Khausar ta
janyosu jikinta tare da ɗaura kansu akan cinyarta cikin Muryan rarrashi tace.



“Kuyi haƙuri kuyi masa addu'a”.



Ahankali Khausar ta ɗago tare da kallon Innayi kana tace.



“Innayi yanzu shikenan Yah Jameel ya tafi ya barmu har abada
baza ku sake ganinsa ba!? Bazai sakeyi mana nasihaba, bazai sake neman al'farma
a wajenaba ashe Yah Jameel Wasiyya yayi ta barmin a wancar ranar”.



Shafa kanta Innayi tayi kana tace.



“Khausar kada kiyi kuka muyi masa addu'a shine abinda yake
buƙata awajenmu kana mu cika masa dukkan wasiyar daya bar mana”.



Kai Khausar ta gyaɗa kana ta cigaba da kuka mai ciwo har
Idanunta suka kumbura.



Sai Bayan sun idar da Sallar Maghariba kafin Lamiɗo ya ɗebe
su suka tafi



A wannan daren ranar baki ɗaya haka suka kwana cikin ƙunci
zuciya da alhini Moddibo kuwa baya um bare Um-um ko awajen zaman makoki idan
akace masa sannu baya magana saidai kallo sai ance Allah ya jikansa kafin yace.



 “Ameen ya Allah
Nagode”. Iya abinda yake iya faɗi kenan.



 



Haka rayuwa tayi musu ƙunci da ɗaci haka aka ɗauki tsawon
kwanaki bakwai ana zaman makoki har awannan kwanaki kullum cikin gida da waje a
cike yake da masu zuwa ta'aziyya.



Washe garin rana ta takwas da safe Moddibo na fita bai nufi
ko ina ba sai gidan Ummi bakinsa ɗauke da Sallama yashiga falon zaune ya sameta
hannunta riƙe da carbi ta zubawa waje ɗaya ido.



 Jin Sallamar sane
yasa ta ɗago kanta tare da tsira masa Ido agefenta ya zauna.



Cikin sanyi tace.



“Babana”.



Ahankali yace.



“Na'am Ummi”.



Cike da tausayawa Ummi tace.



“Babana kalli yanda ka sake dawowa fa yaushe zaka sawa ranka
dangana ne? Kadafa muyi abinda Allah bayaso”.



Batare da yace Uffan ba yayi ƙasa da kansa yana jin wani
irin zafi azuciyarsa.



 Jin muryarsa yasa
Asma'u dake Bedroom ta fito tare da zama agefensa kana ta gaishesa.



 



Ahankali Moddibo ya juya ya kalli Ummi kana yace.



“Ummi yanzu a Duniya babu abinda nake buri daya wuce ingano
su waye suka sace J sannan suka yi masa kisan gillah ina so insani. Ummi inaso
inyi bincike akai ina so inga lallai a hukunta su kwatankwacin zalinci da suka
mana”.



Ajiyar zuciya Asma'u ta sauƙe tare da cewa.



“Aikuwa Yah Moddibo Khausar tana da dan abinda ta sani.



Domin ranan da muka rabu da Yah Jameel na karshe aranan ne
ya maida Khausar gida kuma tace mana.



 Taga wata mota na
binsu.



Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe kana tace.



“Amma Babana Meye amfanin bincike bayan sun kashesa!?”.



Cikin sauri yace.



“To ai Ummi nan nema yake da amfani tunda suka kashesa dama
mun biye musu ne saboda munji tsoron kada su kashesa shiyasa mukabi tsarinsu!”.



Girgiza kai Ummi tayi kana tace.



“Toh amma dai ni inaganin barin shi yafi A'ala kada kai ɗinma
da ka rage mana su cutar mana da kai”.



Sam Ummi ta rigada ta saki komai na duniya shiyasa duk yadda
yaso ayi mgnar a sake buɗe file din binciken taki.



Fahimtarsa bazata yardabane yasa ya nuna mata ya hakura.



Kallon Asma'u yayi tare da miƙewa kana yace.



“Asma'u zamuyi magana”.



Kai ta gyaɗa sannan ya fice.



 



Yau ya kama sati biyu da rasuwar Ramadan wanda yayi daidai
da kwanaki sha biyu da jana'izar M Jameel.



Acan gidan Lamiɗo kuwa da misalin karfe sha biyu na rana
Hajiya Ruƙayya da Mommy da kuma Khausar na zaune afalo suna hira kamar daga
sama suka jiyo Sallamar Hajja Nana da faɗin.



“Assalamu Alaikum”...!



 



*Kada kyiwa labarin bahagon fahimta. Wasu abubuwa na cikin
Labarin gaba ɗaya gaskiyane ya faru da gaske. Ina mai roƙonku da Allah kuyiwa
Jameel Addu'o'i Allah ya jiƙamsa da rahama ya kuma toni asirin waɗanda sunka
saceshi suka kasheshi kisa mai muni. Ku sashi a addu'o'i ku, domin Wallahi
tallahi rasuwar Jameel gsky ne kuma ya faru, da gaske wanda nasan mafi akasarin
mazauna Adamawa zasu san labarin rasuwar Jamilu matashi mai Kekkyawan ɗabi'un
sun kashewa sun bar mahaifiyarsa da ƙunshin a zuciya, sun sa mahaifinshi a
rauni mai ciwo. Yah Allah ka jiƙan Jamilu kayi masa rahama da gafara, ka
tausashi zuciyar iyayensa ka ƙara zamewa mahaifiyarsa Gatan*



 



 



🤝🏻KADA KUMA KU DAMU ZAKUSHA MAMAKIN YADDA
LABARIN ZAI SAKU FARINCI DA SHAUƘI ZAKUSHA MMKIN YADDA LAMARIN ZAI BADA CITTA,
KU DAI KU BIYONI KUSHA LABARI, WACCE BATA BIYA TA BIYA.



 

No comments