Sakayyah 39
SAKAYYAH
Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole sunason wurin da kwatanta Zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata. Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION WANDA BAYA BAYYANA KANSA. Wanda kawai sai dai kijiki, kamar kwalta kin bushe ƙyamas ya dauke miki dukkan sinadaran ni'imomin ki, da sha'awarki, duk kayan matan da zakisha a wofi zadai kiji ƴan uwa da abokan arziƙi da ƙawayenki na yaba miki magunguna GARKUWAR MA'AURATA, amman ke in kinsha jiya I yau, duk nacin oga da yi miki wasannin bazaki ji sha'awa ba, toh wlh muguwar infection ce, wacce bata bayyana kanta har sai ta gama yi miki rugu-rugu. Ta lalata miki zaman aure. Lokacin da zata bayyana sai kiji Doctor's suna kira miki, ovarian cyst, ko kuma fibrod duk a cikin chronic infection ne yar uwa.
INFECTION set ɗinmu na kowa da kowane Mata, Maza, Bazawara, Budurwa, Maijego, Yara, Ke yar uwa Wlh har maiciki zatasha, bashi da matsalar komai na Gargajiya ne mai rakake INFECTION ya fito miki dashi, wlh duk nacin infection koda na cikin mahaifane bi'izinillahi ta'ala zaki rabu dashi, cutar infection cutace mai masifar naci, so yar uwa kana dole ki nace masa da maganin set ɗin na 10k ne kuma maganin kala biyarne nasha da kala uku na tsarki ɗaya na shafawa ɗaya. Yar uwa idan har kin saya to kiyi ƙoƙarin kisha da mijinki, in akwai abokiyar zama, kisa miji ya saya mata, domin ko kin rabu da shin dai ita tana dashi tofa kin kashe macijine baki cire kaiba, ma'ana zai sake dawo miki, idan kuna da yara suma a saya musu, domin tsoron kada ya riƙa a jikinsu musamman ya'ya mata ya buɗa miki ƴa tun tana ƙaramarta, ki aurar da ita miji na muku kallon lalatattun iyaye da baku iya bada tarbiyaba. Saboda yamayin garin yasa ina raba rabin set ɗin in sa miki komai rabi-rabi 5k amman set ɗin 10k ne. Idan kin san a shirye kike ga account number na nan 0005388578 Jaiz bank AISHA ALIYU GARKUWA, ki turo kuɗinki kafin kiyi min mgn ta WHATSAPP NUMBER'N na 09097853276 sai ki turo min shaidar biyanki, domin akwaishi Available ko yau kika tura kuɗinki, gobe kayanki zai taho, ina bada sari ko sayan ɗaɗɗaya. Farashin Sari da sauƙi daga kan mutum 3 ko 6 ko 12. Kai ko na mutum 24 kikeso in Sha Allah zaki samu. Please dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn ki bari sai kin shirya. Taku ce dai GARKUWAR MA'AURATA.
60
*Book 2*
*6*
Shiru Hajja Nana tayi kafin ahankali ta É—ago ta kallesu É—aya bayan É—aya tace.
“Shikenan ni babu abinda zance acikin wannan al'amari zira ido da kunne nawa duk abinda yaje ya dawo Khausar ita tajawa kanta”.
Ƙwaffa tayi kana ta cigaba da cewa.
“Tunda kuma iyayenta kuce kun amince, to ni dai babu abinda zance bare inyi baÆ™in jini”.
Kallon Baffa Jimeta daya sunkuyar da kai ƙasa tayi taɓe baki tayi kana tace.
“Yo ni me zai da meni tunda uban daya haifi Aliyu bai damuba yanuna ayi mata yanda take so ai shikenan, tunda bata illar tsintacciyar mage bata mage ba, É—an da ba'asan Asalinsa ba ba'a san tushensa ba duk abinda ya faru ita tajawa kanta”.
Anutse LamiÉ—o ya É—ago kansa ya kalli Hajja Nana cikin sauri yace.
“Insha Allahu ma babu abinda zai faru sai Al'khairi”.
Abba kuwa karɓan maganar yayi ta hanyar cewa.
“Insha Allah Moddibo zai riÆ™e ta da amana da gaskiya da Izinin Ubangiji Khausar ba zata tozarta ba yanda Khausar ta amince tayi niyyar cikawa Jameelu na wasiyyar sa”.
Ahankali Khausar dake can cikin ɗaki ta lumshe Idanunta zuciyarta na bugawa da Masifaffen ƙarfi.
Cikin sanyin murya Abba ya cigaba da cewa.
“Insha Allahu Ubangiji bazai tozarta taba Allah zai cika mata burikanta na rayuwa insha Allah zata kasance cikin kwanciyar hankali da nutsuwa”.
Kallonsa Hajja Nana tayi kana ta jinjina kai tace.
“Haka kake gani kk? Hmm ta yaro kyau take bata Æ™arko, kai yanzu Alh Bashir tunda kuke kasan asalin yaron ne?”.
Ahankali Abba ya sunkuyar da kansa ƙasa batare da yace Uffan ba.
Ƙwaffa tayi kana tace.
“Hmm ka buÉ—e baki kai tsaye kace baka sani ba shine magana”.
Kallonta ta mayar kan Malam ArÉ—o tace.
“Malam kai da suke aiki a Æ™arÆ™ashin ka kasan Asalinsa?, kasan waye Ubansa? Kasan inane Ƙasar da suka fito kasan inane Jaharsu? kasan menene tushensa? Waye ubansa waye Uwarsa?”.
Ajiyar zuciya Malam Arɗo ya sauƙe kana ya kalleta Anutse yace.
“Ai a al'amarin Aure wannan duka ba magana bane”.
Kai ta girgiza cikin tsira masa ido tace.
“Yanzu ina magana da Malam Liman zai miÆ™e yace min Allah yace Annabi yace amma ai Aure abin bincike ne ko”.
Cikin sanyin murya LamiÉ—o yace.
“Dan Allah Addah Nana kiyi haÆ™uri wannan tone-tonen basu da Amfani”.
Baki ta taɓe tare da Kallonsa kana tace.
“Eh basu da amfani Ni tunda dai aka samu antsira ba É—an Mayun bane zata aura, aishikenan sai inzira mata ido ni naÉ—an ji sauÆ™i ma akan abin”.
Kallon ƙannenta tayi kana tace.
“Yo ai gaskiya ne na fada da kuka wani tsareni da ido, kuma dole idan gaskiya ta taso a faÉ—eta da ace ta auri É—an mayu jikan Mayu ai gwara É—an shegen tunda taji ta gani tana so ta bone dai tayiwa Æ´aÆ´anta da ahalinta”.
Kai Baffa Liman ya girgiza tare da sunkuyar da kansa ƙasa cike da takaici Hajja Nana ta cigaba da cewa.
“Tunda ta yiwa kanta tabo ita tasani amma Ni dai babu ba kina babu hannu na babu Æ™afana na suje can su Æ™arata sanda Æ´aÆ´anta zasu ce ina dangin Ubansu ta nemi abin faÉ—a musu”.
Ahankali Mommy da Lamiɗo suka sunkuyar da kansu ƙasa Khausar kuwa hannunta riƙe da kofin madaran da bata shaba bata ajiye ba ɗumin na ratsa tafin hannunta ta tsirawa waje ɗaya ido ba ƙeftawa.
Ajiyar zuciya Malam Liman ya sauƙe tare da girgiza kai kana cike da ladabi da nutsuwa yace.
“Dan Allah Addah Nana ya za'ayi ana kitse gaba kina warware baya dan Allah wasu furucin ki riÆ™a sanin abinda zaki riÆ™a faÉ—a saboda Manzon Allah (SAW)
_FalyaÆ™un Khairan Auliyastumu”_.
Baki ta taɓe kana tace.
“Naji naji Liman aini zuwa yanzu ko Æ™waÆ™walwar kifi ne dani yaci ace in haddace Hadisai sama da dubu tunda duk motsin da nayi sai kace min ga abinda Allah da Manzonsa suka faÉ—a”.
Sunkuyar da kai Malam Liman yayi cikin taɓe baki ta cigaba da cewa.
“Ni dai na faÉ—a ba bakina ba hannu na babu Æ™afana kuje duk abinda kuka ga ya dace kuyi. Kai kuma”.
Ta nuna Baffa Jimeta da kansa ke ƙasa kana tace.
“Tunda kaine madadin Uba agareta kace kaji ka gani ko? Sannan kaima”. Ta nuna LamiÉ—o daya É—ago kansa cikin haÉ—e girar sama da na kasa tace.
“Kai kuma kaine wakili kuma Uba data tashi agabansa kai kace kaji ka gani ai shikenan na cire bakina aciki amma dan Usmanu na baya raye bazan bari jinjinsa ya cuta ba”.
Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauke kana yace.
“Insha Allahu ma ba zata cutuba da izinin Ubangiji zai riÆ™e ta da Amana”.
Baki ta taɓe cike da takaici ta juya cikin ɗaki.
Takalli Khausar da har zuwa lokacin hannunta ke riƙe da kofin madaran Harara ta watsa mata kana tace.
“Ke kam kinyi asara gaki mace har Mace Bafulatana tsayayyar mace Kyakkyawa zubin zamani Æ™irar masu tsada amma ace wai ke zaki buÉ—e baki kice kina son Namiji”.
Cikin sauri Khausar ta É—ago kai ta kalleta.
Harara Hajja Nana ta watsa mata kana tace.
“Ki É—auke wannan tsayayyun idanun naki akaina Ke zakice kina sonsa wanda baisan dake bama sannan baice yana sonki ba bai damu dake ba wai kice kina sonsa shi zaki Aura”.
Fuska Khausar ta É“ata kana ta kawar da kanta gefe tare da murguÉ—a mata baki da Ido Mommy tayi mata alamar kar tayi magana.
Tsuke bakinta tayi tare da kawar da kanta gefe, jin lokacin sallar La'asar yayi yasa duk mazan suka miƙe suka tafi masallaci.
Bayan sun daeone suna isa afarfajiyar gida suka zauna Anutse Abba ya gyara zamansa tare da fuskantar su da kyau kana yace.
“Toh Alhamdulillah yanzu dai Kamar mun samawa tufkar hanci amma kuma dai Babban abu da yake tafe damu acikin al'amarin”.
Ya sauke ajiyar zuciya kana ya cigaba da cewa.
“Ayi Æ™oÆ™ari ayi abin cikin Æ™anÆ™anin lokaci in Allah ya yarda ya lamunce mana komai abune mai sauÆ™i agaremu inhar kuma kun shirya”.
Jinjina kai Baffa Jimeta yayi kana yace.
“Bakomai in dai wannan ne mu ba matsala awajenmu tunda abin yazo na wasiyya kuma dama a wasiyyar sa ya roÆ™a ayi cikin gaggawa sannan ya faÉ—a ya kara cewa yaron nan yana É“uÆ™atar aure”.
Jinjina kai Abba da Malam ArÉ—o sukayi alokaci É—aya.
Cike da kamala Baffa Jimeta ya cigaba da cewa.
“Tunda har ya fadi haka to yakamata ayi Æ™oÆ™ari ayi abinda ya kamata ni awajena Insha Allah ba matsala tunda dama zan kwana biyu saboda zan samu inji da tsohuwar kasan fatanmu da Adduarmu Allah yasa mu rabu dasu lafiya”.
Kai Malam ArÉ—o ya gyaÉ—a kana yace.
“Hakane Æ™warai fatanmu da addu'ar mu rabasu da lafiya domin shi yafi al'khairi”.
Murmushi Baffa Jimeta yayi kana yace.
“Toh shine nake so in Zauna da ita Ni nan awajena duk abinda ake buÆ™ata wanda uba zaiyiwa É—iyarsa Insha Allah bazai gagara ba komai Ashirye muke Insha Allah”.
Cikin sauri LamiÉ—o ya Girgiza kai kana yace.
“A'a Alh Muhammadu ai wannan hurumi nane don Allah dan Annabi kada kuyi min haka Khausar É—iyace awajena tun tana wata uku nake tare da ita bata da bambanci da É—iyan cikina inaji tamkar Ni na haifeta”.
Kallonsa Baffa Jimeta yayi cike da kamala yace.
“Anya LamiÉ—o za ayi haka kuwa abar maka É—awainiya?”.
Kai LamiÉ—o ya Girgiza cike da dattako yace.
“Haba dai wace irin É—awainiya kuma?,Meye aciki ai babu wani É—awainiya acikin al'amarin nan”.
Numfashi Abba ya fesar kana ya fuskance su da kyau yace.
“Ni duka wannan aikin ma na É“angaren Khausar da Moddibo zanso abarmin domin burin Jameeluna ne ni kungama yimin komai da kuka lamince zaku wanzar da wasiyyar sa bayan rayuwarsa”.
Jinjina kai sukayi kana ya cigaba da cewa.
“kungama yimin komai babu abinda zan iya yi muku tukuici dashi sai dai kubarni inyi dukkan abinda ya dace na fannin Auren nan”.
Murmushi Malam ArÉ—o yayi kana yace.
“Masha Allah wannan Auren yazo da al'barka Ubangiji Allah yasanya al'khairi”.
Zama Malam Liman ya gyara tare da faÉ—in.
“Muma kanmu duk al'amarin Khausar hakkinmu ne mu sauÆ™e”.
Cikin sanyin murya Abba ya kallesu kana yace.
“Ni dai dan Allah na nemi alfarma abarmin wannan aikin nayi”.
Ajiyar zuciya Baffa Jimeta ya sauƙe kana yace.
“To ai ba laifi duk zamuyi buÆ™atun Æ´a mace suna da yawa”.
Jinjina kai LamiÉ—o yayi kana yace.
“Ni dai nafi so abarmin komai na fannin Khausar”.
Dariya Malam ArÉ—o yayi idanunsa akan su yace.
“Lallai dai kam wannan ai sai dai É—akuna uku za aware mata irin wannan lissafin.
Kai Abba ya gyaÉ—a kana yace.
“Insha Allah wannan duk bazai gagara ba da É—akuna da kuma duk abinda za'a buÆ™ata zanyi”.
Numfashi Baffa Jimeta ya fesar kana yace.
“Allah ya temaka nima insha Allah nan da mako É—aya zan koma”.
Jinjina kai Abba yayi kana ya gyara zamansa cike da farin ciki yace.
“Ai shi kansa Aliyu ma yanzu haka yana can Æ™asar Marocco yana kulamin da ayyukan Company na to Auren ma bazata muke son yi masa”.
Murmushi sukayi jin sigar da Abba yayi magana Cike da farin ciki Abba ya cigaba da cewa.
“Idan yaso bayan an É—aura auren da kaina zan Kai masa matarsa da izinin Ubangiji sai dai yaga mata dan yanzu ya tafi yana rayuwa shi kaÉ—ai wasu sabbin damuwa zai sake sawa ranshi”.
Cikin sauƙe numfashi Malam Arɗo yace.
“Toh Alhamdulillah gamu da gishiri da goro na tambayar mu na forko muka zo,".
Sai kuma duk suka juyo suka kalli Malam Liman sayi gyaran murya tare fuskantarsu da kyau cikin kamala da dottaku yace.
“Tunda ga yanayin yadda abin ya kasance, mu shammaci Adda Nana, domin bata da alÆ™ibila yanzu tace ta yarda zuwa anjima zata iya cewa ta fasa, don haka mu É—aura auren nan yanzu-yanzu ana da goron da kuka kawo in dai akwai sadaki a hannunsu tunda ga waliyan yaro ga kuma nata waliyan”.
Ya ƙare mgnar tare da yin ƙasa da murya gudun kada Hajja Nana taji mgnar.
Cikin tsanananin mamaki da farin ciki mara misaltawa Abba Jameel yasa hannunshi cikin aljihunsa jiki na rawa ya zaro sabbin kuÉ—in yar dubu dubu wanda ya dauko dan yin hisani. Bandir É—aya ya ajiye a tsakiyarsu wanda har jikinsa na rawa dan farin ciki yace.
“Gashi ina nemawa Aliyu Youseep Muhammad Mouley auren Khausar bisa sadaki dubu É—ari”.
Da sauri Bappa Jimeta ya gyara zamanshi tare da cewa.
“Na bawa Aliyu Youseep Muhammad Mouley auren Æ´ata Fatima Usman Abubakar Leewal bisa sadaki dubu É—ari.”
Cikin tsananin jin daɗin wannan al'amari da yazo musu da sauƙin aka ɗauka Auren Khausar da Modibbo a yau Litinin a cikin rugar Jauro yaya bisa shaidu Lamiɗo, Malam Arɗo, Malam Liman, da sauran ƙananan Hajja Nana baki ɗaya.
Bayan sun gama gudanar da É—aurin auren kamar yadda shari'ar Muslunci ta tsara.
Cike da gamsuwa haÉ—in da tsananin jin daÉ—in É—aurin auren Baffa Jimeta yace.
“Toh ba matsala Insha Allah duk abinda ake ciki zan gayawa Hajja Nana kuma zan taushi zuciyarta”.
Sai kuma duk suka juyo suka kalli Hajja Nana dake fitowa daga cikin rumfarta tana mai cewa.
“Uhmmm ta yara kyau take bata Æ™arko, ai duk abinda kuke cewa dayi ina jinku badai kun É—aya aurenba, toh ai hikenan maji magani”.
Cikin Sauri suka kuma kalli juna, ayi mace kunne kamar na maciji duk ƙantar sauti sai taji.
Sai kuma suka maida kallonsu kam Malam Liman dake cewa.
“Toh kisanya albarka kawai”.
Kai ta gyaÉ—a cike da takaici tace.
“Hmmm Allah ya sanya al'khairi Allah yasa yadda muka É—auki mgnar marigayi da mahimmanci shima Modibbo a É—auki mgnar da gsky”.
Bata jira cewarsu ba kuma ta juya cikin É—akin,
Ida ta zubawa Khausar da tun lokacin da taji Hajja Nana nacewa badai kun É—aura aurenba ta daskare a zaune, yayinda Mommy mgnar ta daki zuciyarta, dan batayi zaton abin da gaggawa haka ba. Sai kuma duk suka kalli Hajja Nana dake cewa.
“Wlh kinyi asarar Æ™uruciyarki da kyanki ji yadda aka É—aura aurenki kamar na bazawara mara gata”.
Zuwa yanzu Khausar kam bazata iya fahimtar kalaman Hajja Nana ba bare ta bata amsa. Ita kanta Mommy abin ya sata tafiya dogon nazari.
A can waje kuma
Anutse LamiÉ—o ya gyara zama kana yace.
“Toh Alhamdulillah dama kwanan ake batun auren Amina nanda kwana goma, tunda an auren Khausar za'a haÉ—a bikin ayishi lokaci É—aya, kana akai ko wacce gidan mijinta”.
Kusan a tare duk sukace.
“Allah ya kaimu lokacin”.
Amin Ya amsa tare daci gaba da cewa.
“Insha Allah zuwa gobe ko jibi Insha Allah zan dawo in muyi magana mahaifiyar yarinya”.
Nan dai suka gaba da tsastsara duk yadda abin zai kasance.
Sai Misalin ƙarfe biyar suka bar Jauro yaya ahanya sukayi sallar maghariba sai gab Isha'i suka isa gida.
Kasancewar ranan girkin Hajiya Bunayya ne yasa kai tsaye Mommy ta wuce Sashen ta tare da Khausar wacce take tafiya tamkar kazar da ƙwai ya fashewa, domin jin kanta take tamkar wacce aka rufe da ɗanyen fatan rago, wasu abubuwa na musamman ne ke yawo a jiki da zuciyarta ita kanta ta rasa yanayin da take ciki, kawai dai ta tsinci kanta da rayuwa da Modibbo a cikin zuciyata tun lokacin da taji wai an ɗaura aurensu.
Suna shiga kai tsaye É—alibta ta wuce, duk da tsalle da Raudat keyi na ganinta ta gaza yi mata mgn.
Sai Mommy ce data ruggume Raudat É—in.
Ita kuwa Khausar a hankali ta faÉ—a bisa gafonta, tare da rumtse idanunta da karfi.
Sai kuma ta buɗesu ganin fuskar Modibbo a ranar da sukayi robuwar ƙarshe jujjuya idonta tayi kamar yadda tayi mishi a lokacin, sai kuma ta lumshesu jin wasu tafasassun hawaye dake kwaranyo mata ba ƙaƙƙautawa.
Kamar a Film haka yanayin da suke rayuwa dashi a makaranta ya fara dawo mata, one by one, har zuwa ranar da suka kasance a mota, haka nan taji wani murmushin da batasan manufarsaba ya kumce mata, wanda kuma ya korowa hawayen da bata san ya kubce mata da kukaba.
Sai kuma ta saki sassayyan kuka jin Mommy ta zauna kusa da ita tana mai cewa.
“Toh kuma kukan me kikeyi Fatima”.
Ta ƙare mgnar da kiran asalin sunanta wanda bata cika kiranta da shiba.
Ita kuwa Khausar cikin ci gaba da sassayan kukan tace.
“Mommy kinaji fa wai sun É—aura auren”.
Jawota jikinta Mommy da hawaye zubomata tayi tare da É—aura kanta bisa cinyarta tana mai danne kukanta tace.
“Ba komai Mamana kiyi shiru, ai ba yau za'a tafi da keba ki share hawayenki, addu'arta bazata bari ki muzantaba a gidan aurenki”.
Ta ƙare mgnar tana share mata hawaye, daga nan taci gaba tausarta da kwantar mata da hankali dan ta lura gaba ɗaya ta ɗimauce abin ya daki zuciyarta ya kauda nitsuwarta.
Washegari Da safe Kai tsaye Bedroom din Mommy LamiÉ—o ya shiga tare da yi mata bayanin duk yanda sukayi a Jauro yaya bayan sun dawo Sallar La'asar da batun auren da suka dauran.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe cikin sanyi ta ɗago kai tare da kallon Lamiɗo kana tace.
“Toh yanzu har an É—aura Auren kuma ba jan lokacin asan yaron yana sonta, sannan kuma ace za ayi bikin cikin Æ™ankanin lokaci haka?”.
Ta ƙare mgnar cije da rauni.
Jinjina kai Abba yayi yana kallon yanayinta yace.
“Toh me za ajira Aysha ai abune na wasiyya kuma akwai damar yi sannan Already Khausar ta gama Secondary kawai tayi Aurenta tunda Alh Bashir yace a Marocco zasu zauna kinga shida kanshi yace zai kaita wurin mijinta”.
Kallonsa kawai Mommy keyi sabida tama rasa abincewa.
Ahankali Abba ya cigaba da cewa.
“Saboda ya lura yaron bayan son zaman nan sannan yana so yabar masa ragamar Company ahannunsa kinga idan sunje can sai ta cigaba da karatunta acan tunda dama yanayin makarantar su akwai cikekkiyar larabci kinga zata iya karatu a can, ta kuma yi zaman aurenta cikin aminci”.
Sunkuyar da kai Mommy tayi tana wasa da yatsun hannunta yayinda tausayin yarta yasa hawaye cika mata idanu A hankali tace.
“Kuma ba wanda ta sani a canfa, ya zatayi”.
Abba ya cigaba da cewa.
“Kada ki damu, É—an naji Abban Jameel yace in Malam Ahmad ya yarda da rakiyar Ummin Jameel da Asma'u zasuje, ga kuma Hajia Bunayyah itama zan biya mata su kaita tare”.
Ajiyar zuciya Mommy ta sauƙe kana tace.
“Hmmm abin ne naga kamar anyi sa da gaggawa Khausar fa yarinya ce, wlh tsoron yaronan ne fal zuciyarta jiya kwana tayi batayi bacciba”.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da riƙe tafin hannunta acikin nasa yace.
“A ba wani yarinta aciki ai Insha Allah komai zai tafi dai-dai zakiyi alfari da Aurenta da Moddibo ke lokacin da aka aurar dake ai bakima kaita shekaruba, mijinta kuma bar tunanin tana tsoronshi a a bata sonshi ke dai ku zuba ido zakusha mamakin yadda al'amarin zai kance in dai Khausar ta É—auke ki ai kiyi shiru kawai yaro zayi mubaya'a”.
Ya ƙare mgnar da cikin sigar wasa da son kwantar mata da hankali.
Kai ta gyaÉ—a kana cikin sanyi tace.
“Allah yasa”.
Amin yace tare da miƙewa ya fita.
Acan É“angaren Ummi kuwa bayan Sallar Azahar bayan Malam Ahmad ya dawo daga gidan Abba ya zayyanewa Ummi duk yanda Abba ya faÉ—a masa.
Ajiyar zuciya mai nauyi Ummi ta sauƙe tare da fesar da numfashi cikin tsananin jin daɗin kana tace.
“Alhamdulillah yau dai burin Jameeluna ya cika sannan wasiyyar daya bari ta kasance kai baki daÉ—in wannan al'amarin”.
Jinjina kai Malam Ahmad yayi cike da farin ciki yace.
“insha Allah”.
Numfashi Ummi ta fesar kana tace.
“Toh Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kaimu lokacin tafiyar, shiru zanyi bazan gayawa Asma'u ba tukun sai naga yadda Khausar É—in ta nufeta da mgnar”.
Ameen ya amsa kana ya fice.
Ahankali Asma'u ta fito daga Bedroom tare da kallon Ummi kana tace.
“Ummi wai maganar me naji kuna yi kamar batun Aure?”.
Kai Ummi ta jinjina da alamun farin ciki afuskarta tace.
“Hmmm”. Sai kuma tayi shiru, ita kuwa Asma'u cikin son tabbatar da abinda kunnuwanta suka jiyemata cike da kaÉ—uwa tace.
“Dan Allah Ummi ki gaya min na tuba”.
Cikin tsanananin jin dadin É—aya kasa biya a saman fuskarta tace.
“Eh maganar Auren Moddibo mukeyi”.
Zare ido Asma'u tayi kana tace.
“Ummi Yaya Moddibo zaiyi Aurene?”.
Jinjina kai Ummi tayi tana kallonta tace.
“Eh yanayi Aure dai”.
Murmushi Asma'u tayi cike da farin ciki tace.
“Ummi Wacece matar?”.
Ummi na murmushi tace.
“Aminiyar kice matar”.
Asma'u kuwa cike da matsanancin mamaki da al'ajabi ta zare Idanunta waje kana tace.
“Khausar!?”.
Kai Ummi ta jinjina tare da faÉ—in.
“Tabbas kuwa da izinin Ubangiji Itace”.
Tafa hannu tayi tare da buga still da Mamaki da kuma al'ajabi tace.
_“Lahailah ha Illallahu Muhammad Rasulullahi (S.A.W)”_ Yah Moddibo da Khausar.
Kallon yanda ta zare ido da sallami Ummi tayi kana tace.
“Haƙƙun kuwa dan tuni an É—aurama”.
Dafe kunci Asma'u tayi da matsanancin mamaki gani da kaÉ—uwa É—oki da bai sake taba tace.
“Dan Allah Ummi yaushe aka fara wannan maganar?”.
Hannunta Ummi ta riƙe tare da zaunar da ita agefenta yace.
“Ki nutsu mana Asma'u me wannan kamar wanda akace an haÉ—a Auren mutum da Dodo!?”.
Sake baki Asma'u tayi cikin Mamaki tace.
“Tabb Ummi ai kusan Auren Dodo da mutum za ayi dan wallahi Khausar matsayin Dodo take kallon Yah Moddibo”.
Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kana tace.
“Aikuwa da saninta”.
Zare ido Asma'u tayi tamkar zasu zubo tace.
“Ummi Khausar É—in ta sani?”.
Kai Ummi ta gyaÉ—a kana tace.
“Eh”.
Dafe ƙirji Asma'u tayi Idanunta akan Ummi tace.
“Shine kuma bata faÉ—a min ba iyeee Kam bala'i bari Inje in sameta”.
Ta Ida maganar tare da miƙewa.
Cikin sauri Ummi ta riko tsintsiyar hannunta tace.
“Zauna ai zuwa ta Æ™arshe naji tana cewa tazo kuyi wata magana kuma ta samu kuna aiki sannan fitowar ku kenan taga Moddibo yazo kinga ai jikinta na rawa ta fita”.
Jinjina kai Asma'u tayi still Hannunta na cikin na Ummi tace.
“Eh dan na kirata awaya ma nace ta faÉ—a min shine tace idan inaso Inje gidansu inji labari ashe dama wannan ne maganar amma Ummi tasan maganar kuma ta yarda?”.
Cikin sanyi Ummi tace.
“Eh ta sani ta yarda kuma ta amince”.
Dafe kunci Asma'u tayi kana tace.
“To amma Ummi garin ya akayi haka?”.
Kallonta Ummi tayi tare da gyara zamanta kana ta sauƙe numfashi cikin sanyi tace.
“Wasiyyar Yayanki zata cika?”.
Cikin sauri Asma'u ta kalleta fuskarta É—auke da mamaki tace.
“Wasiyya kuma Ummi ya bar mata?”.
Jinjina kai Ummi tayi tare da fesar da numfashi kana ta jingina bayanta da jikin kushin É—in tace.
“Idan baki manta ba Ranan da yazo gidan nan na Æ™arshe itama Khausar tazo sannan tare suka tafi”.
Cikin sauri Asma'u ta jinjina kanta kana tace.
“Ƙwarai kuwa Mommy na tuna aishine tace suna tafiya taga wata mota na binsu”.
Kai Mommy ta Jinjina kana tace.
“To awannan ranan ne ya bar mata wasiyar. Mommy ta ke sanar min yanda suka yi”.
Jinjina kai Asma'u tayi cike da tausayawa Aminiyar tasan yanda Khausar ke masifar tsoron Moddibo tabbas ta ɗauki al'ƙawari mai girma cikin sanyin murya tace.
“Allah sarki Khausar!, Allah sarki Aminiya!!, Ubangiji Allah yabar Æ™auna Allah yabar Æ™auna tsakaninta da Yah Moddibo”.
Sai kuma ta kalli Ummi da fuskarta ke É—auke da murmushi tace.
“Ummi inshirya inje”.
Kai Ummi ta gyaÉ—a kana tace.
“Kije mana Asma'u wa zai hana ki zuwa wajen Aminiyarki”.
Cikin sauri Asma'u ta miƙe tashiga Bedroom ta sanya hijabinta kana ta fito tayiwa Ummi Sallama.
Aɓangaren Hajiya Lami kuwa miƙewa tayi daga Bedroom ɗinta ta nufi ɗakin Samira zaune ta sameta Idanunta sun kaɗa sunyi jawur tamkar garwashi alamar tasha kuka sosai cikin sauri ta ƙarasa kana ta zauna gefenta cike da kulawa tace.
“Samira wai lafiya yau baki fito ba meya faru?”.
Ahankali ta É—ago kanta Idanunta da suka sauya launi ta kalleta Muryanta na rawa tace.
“Mommy ni baÆ™i É—aya wari nake ji idan na tambaye ki kinajin wani sai kice min bakya ji Mommy kullum warin nan Æ™aruwa yake ya zanyi da raina”.
Cike da tausayawa Hajiya Lami ta janyota jikinta cikin sanyin murya tace.
“Haba Samira ki kwantar da hankalin ki mana idan ya dawo sai mu sake komawa wajensa”.
Cikin raunin murya tace.
“Mommy wani irin in ya dawo zaku koma wajensa ni dai ina ganin mutumin nan ya lalata min rayuwa ne yanzu ayanda nake warin nan ko maigadin gidansu Modibbo ma zai yarda ya aurenki ne bare Modibbo da É—an karen tsabta”.
Sai kuma sharce hawaye masu masifar zafi kana tace.
“Yanzu Mommy wani namiji ne zai kalleni bare yace yana sona! ga ruwa mai wari da Æ™arni yana ta bina ko yaushe ina tare da Æ™unzugu kamar mai jego”
Cikin sanyi Hajiya Lami tace.
“Bakomai Samira kasa ki damu Insha Allah yana dawowa zamu koma wajensa”.
Cikin muryan kuka da tashin hankali tace.
“Mommy Ni dai ina ji ajikina wannan al'amari ya zama min bala'i arayuwata na saÉ“i Ubangiji gashi ya kamani tun ba aje ko ina ba Wayyo Allah! Kaico na! Ni Samira”.
Asanyaye Hajiya Lami tace.
“Haba Samira kar ki karyar min da zuciyata mana Insha Allah burinki zai ciki”.
Kai ta girgiza kana tace.
“Mommy ni kam hankalina bai kwanta ba burina inga na samu lafiya wannan ruwan ya daina zuba shine kwanciyar hankalina”.
Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafa shoulder ta tace.
“Kada ki damu Insha Allah Samira Zaki samu sauÆ™i”.
Jinjina kai tayi kana tace.
“Allah yasa Mommy Ina fatan hakan Allah na tuba Allah kayafemin Allah kaji Æ™aina ka gafarta min”.
Acan ɓangaren Lamiɗo kuwa bayan ya fita ɗakin Mommy Kai tsaye sashen Gimbiya Dadu yashiga bakinsa ɗauke da sallama zaune ya ganta da ƙanwarta Hajiya Kubra.
Anutse ya ƙarasa tare da zama kana da murmushi afuskarsa yace.
“A Yafendo Kubra kin zo ne?”.
Kai ta gyaÉ—a tace.
“Eh LamiÉ—o kana gida kenan?”.
Kai jinjina kana suka gaisa bayan sun gaisa Hajiya Kubra ta gyara zamanta tare da kallon sa tace.
“Toh yau dai kam nazo da aiken Ƙaninka duk da yace min iyayenshi maza sunzo”.
“Wanne Æ™arin nawa”. Yayi tambayar a bauÉ—o domin babu wanda ya taÉ“a mishi mgnar.
Shi kanshi mahaifin Naseru cewa yayi yaji suna mgnar ne bakwai sun gaya mishi bane, to kuma shima sai abin ya kwanta mishi musamman da yasan Nasiru na biye-biyen mata shiyasa ya nemi alfarma a bashi Amina kuma ayi auren cikin gaggawa.
Murmushi tayi tare da Kallonsa tace.
“Naseeru mana”.
Kai ya jinjina kana yace.
“Ikon Allah Naseeru kuma ko É—azun ma muna tare kuma bai faÉ—a min ba shine sai ya aiko ki? ai da kin kirani ma zanzo har gida in sameki”.
Kai ta girgiza kana ta kalli Gimbiya Dadu sai kuma ta kalli LamiÉ—o tace.
“A'a ai aiken ne dole muzo da kan mu tunda iri muke nema”.
Jim yayi kana yace.
“Ikon Allah wani kalar iri kenan?”.
Ƴar dariya tayi ta gyara zamanta kana tace.
“Iyeee al'amarin ne ya sauya sheÆ™a”.
Gyara zama Gimbiya Dadu tayi kana tace.
“Eh aihakama shi yafi alkhairi Hausawa sunce naka sai naka daÉ—in zama sai bare gwara dai kome za ayi ace na kane” .
Ido kawai Lamiɗo ya zuba musu cikin rashin fahimta ko kaɗan bai taɓa fuskantar alaƙar dake tsakanin Amina da Naseer.
Ganin yanda yake kallon Hajiya Kubra tayi murmushi tayi kana tace.
“Akan al'amarin Naseeru ne da Amina”.
Cikin sauri ya kalleta ya girgiza kai kana yace.
“Ba dai Amina da Naseeru ba saidai Nasseru da Khausar dai ko?”.
Dariya tayi tare da gyara dankwalinta tace.
“A'a da Aminar dai”.
Ido ya zuba mata cike da son nazartansu yace.
“Da Amina dai?”.
Jinjina kai tayi ta kalli Gimbiya Dadu kana tace.
“Tabbas da Amina”.
Jingina LamiÉ—o yayi da jikin kujeran kana yace.
“A'a baki fahimci maganarsa da kyau ba da Khausar ce kuma al'amarin ma dai gashi nan yanda yazo abirkice”.
Fuska Gimbiya Dadu ta É“ata kana tace.
“Babu abinda ya birkice sai dai sune ya birkice musu acan tunda Khausar ta nuna bata sonsa ai Alhamdulillah ga Æ´ar Uwarsa ta soshi”.
Cike da Mamaki LamiÉ—o ya É—ago kansa ya kalleta yace.
“Da ita Aminar kenan?”.
Jinjina kai Hajiya Kubura tayi kana tace.
“Eh ai Amina da Nasseru sun daÉ—e da haÉ—a kansu soyayya suke sosai basu dai fito sun faÉ—a maka bane suna so sai angama shirya abubuwa komai ya kankama”.
Jinjina kai LamiÉ—o yayi still da mamaki atare dashi yace.
“Allah mai iko shi kuma Naseeru Æ´arsa zai Aura?”.
Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.
“Ya haramta ne?”.
Murmushi yayi tare da girgiza kai yace.
“A'a a'a bai haramta ba na isa in haramta abinda Allah ya halatta ba wai ya haramta bane amma da yake tana sunan Æ´arshi ce”.
Baki Gimbiya Dadu ta taɓe kana tace.
“To wannan dai ba wani abu bane aciki ka dai kayi fatan alkhairi Allah yasanya albarka acikin al'amarin”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Kuma haka abin ya zama kenan?”.
Kallonsa Gimbiya Dadu tayi kana ta kalli Hajiya Kubura dake murmushi tace.
“Sosai ma tunda naji Kakar Khausar tana cewa ba zata bawa Zuri'ar Mayu ba tana Æ™ananun surutai shiyasa nace ya janye da nemanta ya nemi Amina Æ´ar Uwarsa shiyafi mana kwanciyar hankali”.
Ahankali Lamiɗo ya sunkuyar da kansa ƙasa batare da yace Uffan ba.
Dariya Hajiya Kubrua tayi kana tace.
“Ai shiyasa nace bari nazo da kaina muyi magana”.
Anutse ya ɗago kansa ya kalleta ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh Yafendo Kubura ai wannan al'amarin Aure magana ce ta maza bata mata ba ai da Babban Naseeru ne zaizo muyi magana zai fiko sai insamu gamsuwa da sahalewar sa za ayi dukkan maganar?”.
Cikin sauri Gimbiya Dadu ta katsesa da cewa.
“Ai zaizo amma dai ta fara zuwane ta sanar maka saboda bakasan da Maganar ba”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Toh shikenan Ubangiji Allah ya mana zaÉ“in alkhairi”.
Gimbiya Dadu kuwa cikin sauri ta tari numfashi ta hanyar cewa.
“Shine ma alkhairi Nasseru ya auri Æ´ar uwarsa ita kuma taje can ta Æ™arara ta auri duk wanda taga dama da masifaffiyar Kakarta”.
Murmushi yayi kana yace.
“To Allah ya kyauta”.
Miƙewa yayi ya fita kai tsaye sashen sa ya nufa zaune ya samu Hajiya Bunayya da waya maƙale akunnenta tana magana da Hajiya Lami ganinsa yasa tayi saurin cire wayar kana ta katse ta juya ta kallesa zama yayi tare da tsira mata ido tamkar shine rana ta farko da yafa ganinta acikin rayuwarsa.
Ganin kallon da yake bin ta dashi ne tace.
“Ya dai Mai martaba naga kana ta kallona lafiya kuwa?”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe kana cikin tsira mata Ido yace.
“Wai me yake faru tsakanin Naseeru da Amina ne?”.
Cike da farin ciki tace.
“Meye kuma yake faruwa LamiÉ—o banda lamarin Aure da muke fatan zai tabbata tunda sun daidaita kansu”.
Wani irin kallo ya watsa mata kana yace.
“Sun dai-dai-ta kansu Meyesa ban sani ba”.
Zare ido tayi tare da É—age hannunta sama tace.
“Lalala nima Wallahi ban saniba sai kwanan nan bai kai sati ba Amina take cemin wai zai aiko ya gama haÉ—a kayan Aure su goro da kayan gishiri da kuma sadaki”.
Ido kawai Lamiɗo ya tsira mata bako ƙyaftawa ta cigaba da cewa.
“Hatta kayan rufi ya gama haÉ—a komansa yana so ayi auren nan da mako biyu nanne nasan da maganar toh tsoron yi maka magana nake ta yanda zan tunkare ka da maganar”.
Cikin wani irin yanayi LamiÉ—o ya tsira mata ido tamkar mai son fahimtar wani abu.
Marerece fuska tayi kana tace.
“Ya dai ka zuba min ido LamiÉ—o ka yarda dani ai danasan da maganar dana faÉ—a maka nima abin ya daure min kai shiyasa ban faÉ—a maka ba”.
Sai kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa kana ta cigaba da cewa.
“Domin nasan da farko Khausar Naseeru yake so to amma shi Naseeru da kansa ya sameni yace Khausar tace bata sonsa to shi ya hakura sannan Gimbiya Dadu ma tace ya nemi Amina Æ´ar Uwarfashi LamiÉ—o ya fesar kana yace.
“Allah ya kyauta amma batun kice baki sani ba zancene Bunayya magana kike”.
Cikin sauri ta kallesa kana tace.
“Wallahi tallahi LamiÉ—o ban saniba”.
Cikin yanayin É“acin rai da takaici yace.
“Dakata Bunayya kada ki rantse dan na lura kamar baki san girma da darajar rantsuwa ba idan kika ce baki sani ba magana ya Æ™are”.
Cikin tsinkewar zuciya take kallonsa.Cike da É“acin rai ya cigaba da cewa.
“Idan kika faÉ—a kona yarda ko kar nayarda wannan tsakanina ne dake akan abinda kinsan Æ™aryane kinsani sannan nasani kuma inada tabbaci da yaÆ™inin ke kika Æ™ulla wannan alamarin”.
Cikin yanayin tashin hankali da damuwa tace.
“Fisabilillah taya zan Æ™ullah”.
Ƙwaffa yayi kana yace.
“Bunayya gani kike kamar bansan komai akanki ba ko?”.
Atake zuciyarta ya tsinke zufa ya fara wanke mata fuska duk da sanyin irin na garin Gembila cikin sauri tace.
“Toh yanzu dan Allah ni menayi?”.
Kai ya girgiza still Idanunsa na kanta yace.
“Hmmm jiki magayi tunda haka kika zaÉ“awa kanki, duk abinda ya kasance ku kuka da kanku acikin al'amarin nan ya kamata ace komai zakiyi kiyi shawara dani”.
Kasa cewa komai Hajiya Bunayya tayi sai zufa dake wanketa cike da takaici ya cigaba da cewa.
“Amatsayina na mijinki kuma Uba ga Amina amma bakuyi shawara dani ba sai kuka tura Iyayena ta yanda zasu tsareni acikin maganar tunda haka kuka zaÉ“a magana ta Æ™are, kowa ya É—eÉ“o da zafi bakinsa!!!”.
Cikin É“oye tsoronta tace.
“Naseeru fa shiyace ya daina son Khausar”.
Cikin sauri ya katseta ta hanyar cewa.
“Khausar ko baice ya dena sontaba Ni kaina inada nufin bazan bashi Auren Khausar ba, tunda kuma yazo ya zagaya kukayi haka ke kika sani Æ´a Æ´arki ce shi kuma É—an uwana ne babu abinda zance”.
Marerece murya tayi kana tace.
“Ni dai wallahi babu abinda na sani aciki kuma itama Amina tace in faÉ—a maka Babansa yace zai zo gobe”.
Wani kallo ya watsa mata Afusace yace.
“Idan kinga dama kice masa yanzu yazo aÉ—aure ba haka kike so ba?”.
Asanyaye ta kallesa kana tace.
“Toh fisabilillah dan Amina za tayi Aure shine zai zama laifi ko kuma so kake itama tayi ta zama kamar yanda Asiya take zaune?”.
Cikin tsawa ya É—aga mata hannu kana yace.
“Ki kiyayi kanki kada ki yarda kijefi Asiya da mugun furuci, Insha Allah Asiya Ubangiji zai jiÉ“anci lamuranta Asiya zatayi Aure aure mai daraja da izinin Ubangiji baza ta taÉ“e ba”.
Kallon yanda yayi kicin-kicin da fuska Hajiya Bunayya tayi cikin fushi ya cigaba da cewa.
“Da yardan Allah tunda tayi haÆ™uri da jarabawar da Ubangiji ya mata za taci nasara baya ga haka duka-duka nawa Asiya take bare Amina dududu ba shekaran daya gabata bane ta gana Secondary ba?”.
Uffan batace ta lura aharzuƙe yake cikin rashin walwala ya miƙe yashiga Bedroom ɗinsa.
*MOROCOW*
AÉ“angaren Moddibo Baki daya kansa ya É—auki zafi aiki suke gadan-gadan Anutse ya fito daga masallacin dake cikin Company ya nufi ainihin inda ake buga Abaya, kama daga Dubai Abaya, Morocco Abaya, Saudia Abaya, da kuma Turkiya Sai kuma Veils,Bags,shoes da sauransu.
Babba wajene sosai ankafa manyan ijinina sabbi ana ta haɗa su ga manyan-manyan AC dake aiki kana ga sanyin garin dake sauƙa wajen ya ɗauki sanyi baki ɗaya aiki suke gadan-gadan babu kama ƙafar yaro da alama nan da Kwanaki biyar za'a haɗa komai gashi an dakatar da aikin komai sai sabbi dake aiki Saboda sabunta Injina da akayi Ma'aikatan na ganinsa suka nufo sa suna Cikin harshen larabci suke masa Barka cike da mutuntawa da kuma girmamawa shima sannu yake musu yana yaba aikin da suke.
ÆŠaya daga cikin ma'aikatan wanda yake shine Babba yace.
“Alh aiki na kyau yanda ake buÆ™ata insha Allah nan da kwana biyar za'a gama daddasa Injinan da za'a gama aikin”.
Kallon yanayin wajen Moddibo yayi kana yace.
“Masha Allah abu yayi kyau sosai”.
Kai Engineer ya Jinjina kana yace.
“Sosai ma ai saboda ansamu zaÆ™aÆ™uran ma aikata kuma baki É—aya cikin kwanaki Ukun nan da aka dakatar da buga Abaya's,Veils,Jakankuna da Takalma *BASJAM”.*
Ahankali Moddibo ya lumshe Idanunsa Aransa yace Allah sarki Abba gashi ya haÉ—a sunan sa dana J É—ina a Company sai dai bashi da ikon aiki a Company Engineer ya cigaba da cewa.
“Baki É—aya har abin ya fara Æ™aranta zuwa Æ™asashen da ake kaiwa danma ansamu antanadi masu yawa suna zaune amma Alhamdulillah aikin zaiyi gaggawa tunda ansamu zaÆ™aÆ™uran ma'aikata”.
Jinjina kai Moddibo yayi tare da lumshe idanunsa saboda sanyin da wajen ke dashi kana yana jin yanda Kasan mararsa ke murɗawa ahankali ya ɗaura tafin hannunsa na dama akan maransa ya danna sai kuma ya cije Lips ɗinsa na ƙasa cikin dauriya ya kalli Engineer tun jiya ya kwana da ciwon cikin kana har yau bai lafaba na awa ɗaya mai kyauba da zaran yayi minti talatin zai sake murɗa masa ahankali ya cije Lips ɗinsa kana yace.
“Abu yayi kyau Allah yatemaka insha Allah nan kusa zamu kammala akoma bakin aiki a cigaba da aiki gadan-gadan”.
Ya ida maganar tare da juyawa ya nufi gefen dama wanda office, Office ne awajen wani Corridor ya shiga tare da buɗe makeken Office da yafi sauran kyau da tsaruwa sosai Office din ya haɗu table ne kansa ɗauke da system da takardu sai flowers kana daga jikin bango kujera ce mai juyawa daga gaban table ɗin kuma kuma jeru biyu ne sai Cottons sky blue da fari daga gefen dama Ac ne daga ɗaya gefen kuma tamkar falo ne manyan kujeru ne guda bakwai suma Sky blue sai Tv Plasmer ajikin bango da frigde sai kuma showglass dake ɗauke da kofuna ahankali ya ɗauki remote din AC yaƙara gudu duk da kuwa sanyin da ake stugawa yayin da zufa ya shiga tsats-tsafo masa agaba ɗaya ilahirin jikinsa kana maransa na cigaba da murɗawa jikinsa sai zufa yake karyo masa rintse idanunsa yayi da ƙarfi jin yanda mararsa ke murɗawa tamkar zai fita ahankali ya zauna kana ya ɗaura kansa akan Center table dake tsakiyar falon ya lumshe idanunsa sai kuma yayi saurin buɗewa kana ya lashi busassun laɓɓansa baki ɗaya jikinsa ya fara rawa jin yanda maransa ke dunƙulewa yana tsikarinsa cike da damuwa da rauni ya soma faɗin.
“Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n”.
Kana yaja wani numfashi me nauyi ya yunkura da niyyar miƙewa ji yayi bashi da kuzarin da zai iya tsayawa ji yayi tamkar an haɗa maransa da bayansa ana dinkewa ga wani irin harbawa da zuciyarsa keyi da Masifar ƙarfi kwanciya yayi akan 3sitter yayi rub da ciki baki daya ilahirin jikinsa rawa yake ga zufa dake tsats-tsafo masa tamkar babu Ac saboda yanda azabebben ciwon cikin ke gallazarsa yakai kimanin minti talatin yana murƙususu akan kujera kafin ya fara lafawa sannu Ahankali ya fara maida numfashi yana fesaewa.
*Gembila*
Asma'u kuwa ta daɗe tsaye aƙofar gida bata samu Adaidaita ba jin kiran sallar La'asar yasa ta juya da niyyar koma gida tayi Sallah kuma sai tasamu adaidaita shiga tayi tana isa gidan Kai tsaye falon Mommy ta shiga bakinta ɗauke da sallama zaune ta samu Khausar da Haiydar tana riƙe da hannunsa tana yanke masa Farce.
Haiydar kuwa kallon Khausar yayi kana yace.
“Nifa ki kula kar ki yanke min hannu”.
Hararansa tayi sai kuma ta cigaba da yankewa kana tace.
“Tunda dai baka iya ba kona yankekama kai ka jawa kanka”.
Ta ƙarasa maganar tare da sauke Idanunta akan Asma'u data gama shiga falon da sauri ta sake masa hannunsa tare da miƙewa da sauri ta Rungume Asma'u cike da farin ciki tace.
“Oyoyo Asmeey ta”.
Zare ido Haiydar yayi tare da yarfe hannunsa yace.
“Wayyo ta yankeni Wayyo ya tsana”.
Da sauri Mommy ta fito daga Bedroom É—inta Idanunta akan Haiydar tace.
“Lafiya kuwa”.
Yarfe hannu Haiydar yayi kana ya Marerece fuska yace.
“Mommy ki kallafa Addah Khausi ta yanke min yatsana daga kallon Asma'u”.
Langwaɓar da kai Asma'u tayi kana tace.
“Ayyah Haiydar Sorry sannu bata sani bane”.
Hararansa Khausar tayi tace.
“Rabu dashi Æ™ato dashi tunda dai har yanzu bai iya yanke Farce ba sai dai in yanke masa aikuwa nata yanke masa hannu”.
Kallonta Mommy tayi kana tace.
“Wato ma da saninki kika yanke sa?”.
Cikin sauri ta girgiza kai tare da langwaɓar da kai tace.
“Wallahi Mommy ban sani ba ganin Asma'u ne yasa na tashi da sauri ashe na yanke sa”.
Kai Mommy ta gyaÉ—a tare da kallon Haiydar tace.
“Sannu Babana mu gani”.
“Mommy Ummina tace in gaisheki”
Jinjnna kai Mommy tayi kana tace.
“Ina amsawa”.
Hannun Asma'u Khausar taja suka shiga Bedroom É—inta suna shiga Khausar tace.
“Fisabillah baki zoba sai yanzu ko dai kwana zamuyi?”.
Zare ido Asma'u tayi kana tace.
“Mu kwana kuma wa zai taya Ummina aiki da safe?”.
Langwaɓar da kai Khausar tayi sai kuma tace.
“Don Allah Asmeey mu kwana zan kira Ummi mu roÆ™eta”.
Kai Asma'u ta girgiza kana tace.
“A'a keto muje mu kwana mana”.
Ware ido Khausar tayi tare da sanya dariya tace.
“CaÉ“É“ lallai kam”.
Murmushi kawai Asma'u tayi kana ta zauna abakin gadon.
Khausar kuwa fridge ta buÉ—e ta É—auki Plate ta sanya Faro water da Ayaba ta mikawa Asma'u.
Karba Asma'u tayi tana É“are Ayaban tace.
“Ke dai bakya rabuwa da Ayaba aÉ—aki kina nan kamar biri”.
Murmushi Khausar tayi kana tace.
“Wallahi kuwa Ina son Banana yana min daÉ—i”.
Jinjina kai Asma'u tayi tare da faÉ—in.
“Ai lallai dai kam”.
*Morocco*
Aɓangaren Moddibo kuwa haka yaita fama bayan minti talatin cikin yake sake Murɗansa yana kallon gari yayi duhu maghariba ta kawo kai har wasu massallatai sun fara kiran sallah amma ya kasa miƙewa saboda yanda ciwon cikin ke kartansa jin ciwon ya lafa yasa ya miƙe tare ya fita yaga wajen shiru alamar duk ma aikata sun tattafi sai securities da mai bawflowes ruwa kasancewar karfe biyar da wasu Mintuna ake tashi ma tsaye wajen motarsa yashiga yaja ya fita a gate one.
Ya miƙe titin ya fito gate ɗin La riva restaurant dake Opposite da Company yazo Dai-dai wajen Traffick sun tsaida shi saboda sauran motoci da suke wucewa ahankali yasa hannunsa ya dafe fuskarsa ta gefe yatsunsa na dafe da kuncinsa ya tsansa ɗaya kuma na cikin bakinsa kana ya fito da fuskarsa ta wajen motar yana ɗan shan Iska jikin katangar Company sa yana shaƙan iskar bishiyar dabino dake zagaye da Company wanda ta ko ina sune da gudu yaga wata mota ta gilma ta gabansa wacce ta fito daga gefen yamma zata yi gabas kana shi kuma yana gefen kudu ne idan ya samu dama zaibi arewa ganin wulgawar motar yaga fuskar J ɗinsa ne aciki cikin sauri ya zare Idanunsa sakamakon kallon fuskar J ɗinsa aciki Motar cikin wani irin sauri ba tare da anbasa hanya ba ya figi motar ya karya kwana yabisa har ya kusa bige wata mota.
Da mugun gudu yake bin motar kana ga cunkoson ababen hawa kasancewar maghariba ta kawo kai ƴan kasuwa sun taso ga kuma ma'aikata sun tattaso daga Office kowa na burin komawa gida wasu kuma na ƙoƙarin su samu masallacai dan kada su rasa jam'i hakan yasa cunkoso yayi yawa ga kuma duhun gari gudu yake yana bin bayan motar ga kuma cun kuson motoci da suka taresa ya cusa ta nan yaga antaresa baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake tun lokacin daya zare idonsa har yanzu bai maidasu daidaiba saboda idanunsa sun gane masa Allah ya nuna masa fuskar Jameel ɗin sa ne yasani Koda amagagin mutuwa yake ya tabbatar fuskar Jameel wulgawa daya zaiyi ya gane yasani wannan fuskar Jameel ɗinsa ne baki ɗaya ilahirin jikinsa rawa yake kana yana maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n yana cigaba da dannawa motocin gabansa hon baki daya mutane Kallonsa suke wasu kuma na cewa wannan kam lafiyarka ina zakaje haka kamar zaka tashi sama shidai haka ya cigaba da tafiya ya kutsa tanan ya kutsa tacan garin hakane ya bigewa wani motarsa mutumin na cewa Kai lafiya amma ina tuƙi kawai yake da gudu baki ɗaya hankalinsa baya jikinsa wani mai Napep ne ya tare gabansa madadin ya kalli gabansa amma baki ɗaya idanunsa na kan motar daya yaga J ɗinsa aciki yana samu ƙaramar ɗin ya kauce masa ya cigaba da bin bayan motar yanda yake gudu da masifaffen ƙarfi haka zalika motar da yake bi ɗin ma take gudu hakan yasa yasake tabbatarwa kansa J dinsa ne kenan gudunsa yake ko kuma yaya ahaka suka isa wani roud about nan yaga ya ɗauki hanyar da zata sa dashi da flyover gudu yake da ƙarfi haka shima wancen ke gudu duk da gudun da yake amma ya kasa kamo wancan motar saboda shima gudun yake ga kuma motoci dake tsakaninsu amma yana iya hangosa kasancewar be wuce motoci biyu zuwa uku bane agabansa sunzo daidai kan Flyover yasamu yabi sama Shima Moddibo cikin sauri yabi sama kasancewar ba cunkoso sosai numfashi mai karfi ya sake kana ya hau kan Flyover yabi sana kafin ya isa tsakiyar Flyover shi kuma wannan har ya sauƙa ya ɗauki hanyar Unguwar Mellila shima Moddibo cikin sauri yabi wannan hanyar tafiya kaɗan sukayi yaga motar ta wuce wani asibiti cikin gudu shima ya wuce tafiya kaɗan suka ƙara yaga motar taja kwana adai-dai wani tamfatsetsen gini mai masifar kyau da girma bisa duk kan alamu asabiti ne saboda sunan dake manne asaman ginin idanunsa ya ɗaga yaga sunan dake manne ajikin ginin *Youssef Mouley Hospital*.
Mai motar kuwa yana danna hong aka buɗe masa gate yashiga kafin ya juya akalar motarsa ya ƙarasa wajen kuma a maida gate din ana ƙoƙarin rufewa da wani irin sauri ya danna hancin motarsa cikin gate din.
Cikin sauri securities dake bakin gate din suka taso suka yo Kansa.
Shi kuwa mutumin cikin motar tuni yayi Parking ya buÉ—e motar ya fita da sauri Norses biyu suka biyu bayansa suna faÉ—in.
“Welcome Sir”.
Security din kuwa kan Moddibo suka nufa suna faÉ—in.
“Lafiya kuwa?”.
Shi kuwa Moddibo gadan-gadan ya nufi kan security din da sauri suka kauce masa yana shiga yayi Parking kana ya fito da sauri security suka yo kansa suna faÉ—in.
“Lafiya kuwa?”.
Bai tanka suba yabi bayan mutumin yana cewa.
“J!,J!!,J!!!,”.
Shikuwa Mutumin gaba yayi Norses na biye dashi jin hayaniya yasa ya juya ya kalli bayansa gani yayi Moddibo ya nufo kansa yana cewa.
“J”.
Security kuwa ƙoƙarin riƙesa suke suna faɗin.
“Malam lafiyar ka kuwa ina zaka je?”.
Cikin sauri Moddibo ya hankaÉ—esu kana cikin fushi yace.
“Ka matsa min anan ka bani hanya, J!J!!”.
Wata matace ta fito daga cikin Hospital din ta ƙaraso kusa da wannan mutum kana tace.
“Dan Allah Dr Jameel kayi sauri kaceci rayuwar Æ´ata tana cikin hatsari”.
Jin haka ne yasa Mutumin da takira da Dr Jameel ya juya ya nufi cikin asibitin.
Moddibo kuwa da gudu yabi bayan Dr Jameel da already ya shiga cikin reception tamkar wani zautacce haka ya dawo baki daya bashi da wani cikakkiyar nutsuwa Akuma dai-dai lokacin yaji cikinsa ya sake kartawa da masifaffen ƙarfi da gudu ya nufi kan Dr Jameel yana cewa.
“J!,J!!,J!!! Ina zaka je”.
Afusace Dr Jameel ya tsaya tare da juyawa yace.
“Wai lafiya Malam Security ku fita dashi mana me kuke jira ha'a ya zaizo yana mana ihu yana firgita mana marasa lafiya”.
Baki É—aya Norses da sauran mutanen ido suka zubawa Moddibo.
Cike da girmamawa security yace.
“YallaÉ“ai munyi Æ™oÆ™arin korinsa amma yaÆ™i tafiya sai turemu yake”.
Juyawa Moddibo yayi jin J ɗinshi na mgn da larabci wai a koreshi, da sauri ya buga hannunsa aƙirjin Dr Jameel Cikin juya harce zuwa larabcin yace.
“J ni kake cewa akaro?,J nine fa A.J É—inka ni kake cewa akaro?”.
Cikin fushi Dr Jameel ya fincike hannun Moddibo ajikin rigarsa yace.
“Ka sakeni wanene kai a ina na sanka kaji yanda kake ihu kana gigita mana mutane”.
Ya ƙare mgnar yana yiwa Modibbo wani irin kallo mai cike da tarin mmki da kuma son nazartan abubuwa da yawa musamman kamaninsa.
Shi kuwa Modibbo Cikin rauni da tsanananin tashin hankali da azabebben ciwon ciki Moddibo ya sanya tafin hannunsa ya dafe maransa muryarsa na rawa yace.
“J Nine fa J A.J É—inka kake cewa baka gane ba Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n J nine yau kake cewa baka sani ba?”.
Akuma dai-dai lokacin cikinsa ya sake murɗawa da masifaffen ƙarfi cike da ɓacin rai Dr Jameel ya Kalli security kana yace.
“Ku fitar min dashi”.
Norses É—in kuwa cikin alamun damuwa suka ce.
“Dan Allah Dr muje ka duba matarnan”.
Juyawa Dr Jameel Yayi Moddibo kuwa ganin haka yasa Cikin wani irin rauni ya kallesa muryarsa na rawa kana numfashinsa na fusga yace.
“Jameelu nine fa aduniya Koda baza ka gane kowaba amma Ni da Ummi da Abba bamu cancanci kamanta damu ba kuma ko me yafaru da kai aduniya Ni dai da Ummi da Abba bamu cancanci ka ce baka gane muba A.J dinka nefa”.
Yana gama faÉ—ar haka ya yanke jiki yayi baya...
*Zakusha Typing errors dan banyi editing ba, wani wurin zakuga kalaman a baude ko baibai*
By
*GARKUWAR FULANI*
No comments