Mijin Malama Hausa Novel
Duk wata mace yana da kyau ta nutsu ta bi labarin nan.
MIJIN MALAMA
Paid book ne.
Book 1 and 2 1kne
0811923761616
Maganganun Imran su ka yi wa Majeederh dirar mikiya a kunne. Duk yadda take so tayi shiru ta kuma daure amma har zuciyarta ta kasa yin hakan gani take da zarar Imran ya fasa aurenta babu wanda ya yi saura zatai ta tabbata a gida. Majeederh ta runtse Idanunta a hankali cikin muryar dake nuna zallar abin da zuciyarta ke buƙata ta ce "Imran ba tsofa na yi ba, am just 20, na fi kowa kyau a gidanmu" ta ƙare maganar tana sanya duka hannunta tare da dafe kanta dake juya mata tana ganin komai bibbiyu. Imran ya miƙe ƙafafuwan a saman office ɗin shi idanunsa buɗe cikin isgili ya cewa Majeederh. "Tsari na ne haka, ina son auren macen da bata haura sha bakwai zuwa takwas ba, lokacin da na zo neman aurenki wanne irin rashin mutumci ne ba a nuna mini ba? Ko an faɗa miki ke kaɗai ce mace Majeederh, ki je kici karatu daman ni wayewar ki tsoro take bani karatunki ya yi yawa" ya juya kaɗan sbd ya ƙara sanyawa zuciyarta dafi, dafi irin wanda ta sanya masa, domin har ranshi yana ƙaunar Majeederh a shekaru biyun da suke shige "Ki roƙi Allah kada ki tsofa a gida, domin darajar mace gidan mijinta gadai ƙannenki....,"
“....Stop it, ya isa..”
Ta kashe wayar da sauri tana zubewa a gefen gado, ta kasa tantance wanne kalar yanayi zuciyarta ke ciki, da gaske ta tsofa ko kawai faɗar Imran ce? mene abun iliminta na addinin? Ta kifa kanta a tsakanin cinyoyinta tana ambaton sunan Allah. Aure take so da gaske yanzu ta fahimta kuma shi ne dalilin da yake sawa tayi azumi domin riƙe kanta.
Tana jin wayarta na ƙara ta shareta domin babu wanda zai kirata idan ba Latifa ba, mai kiran nata al'amuran bikin Widad ya sha kanta. Sai da ta kwashe adadin mintina kusan goma kafin ta ji sauƙin zuciyarta, ta miƙe a hankali tana cire kayan jikinta kai tsaye bathroom ta nufa ta yi wanka tana fitowa ta goge jikinta tare da zura night wear masu ɗan kauri sbd sanyin hadarin dake fusawa, ciwon Limoniyarta yana ƙoƙarin tashi, bata jin daɗin komai rayuwar tayi mata juyin wainar tan da wannan shi ake kira da gwara na yi bara a bulayi yin bara a kofai.
Jikinta sai fitar da ƙamshin Nivea men active clean shower Gel yake. Ta juya kaɗan tana jan pillow ƙarar ƙofar da ta ji ya sa ta yi saurin rufe Idanunta tana jiran ta ji wannan karan kuma mene? Waye kuma?.
Mami ta dubi Majeederh tana sakin murmushi ta ce "Hawwa'u shiru ke ɗaya? Sau zan faɗa miki ki daina zama haka, bakya gudun abin da zai taɓa lafiyarki 24hrs kowa na shira banda ke rayuwa za tayi haka?"
Majeederh ta lumshasshun Idanunta kamar tana jin bacci so romantic domin gabaɗaya idan bata yanayi na jin daɗin zuciya shagwaɓewa take kamar ba ita ce babba ba, bata taɓa riƙe da nuna shagwaɓarta ga abin da take so. "Ina magana ki na ji? Oh! Ni Asabe Allah ya ye miki wannan miskilanci maza tashi ki kwashe kayan dinner ɗin can" da tsananin mamaki wanda Majeederh ta kasa shanyewa ganin ita ko hannu bata saka cikin abinci ba. A hankali cikin jan idanunta tana lumshewa ta ce "Kaya? Dinner?" Ta furta cikin sanyin murya wacce take always cool and so romantically.
"Eh, abincin da su Rumana da Raihana suka ci, naga gabaɗaya suna wajan fira sun yi baƙi ke kuma babu abinda ki ke sai zaman banza, to tunda suna wajan mazajen da za su aura ai ke sai ki yi aikin gidan"
Tunda Mami take magana Majeederh ta zuba Idanunta wanda suke farare tas kamar madara. Rayuwa kenan! Zamani riga duk shekaru data bawa su Ruma amma yau ita ake cewa ta kwashe kayan abincin da suka ci sbd suna wajan samari duk sanda su kai aure bata san mene zai iya faruwa da ita ba. Bata ce komai ba ta miƙe tare da ɗaukan hijabi ta saka Mami ta ce
"Allah dai ya yanke kazar wahalar nan, ya kawo ƙarshen zamaninki bana iya bacci sbd tausayinki yanzu ke babu wani daya taɓa cewa yana son ki da aure?" Ba tare data kalli Mami ba tayi gaba tana cewa "Babu"
Washegari da wuri Majeederh ta tashi sbd daman tun Subhi idanunta biyu dalilin azumin data ɗauka ta gyara gidan bakiɗaya, tana cikin haɗa breakfast Aaliyyah ta fito tana murza Idanunta ta ce
"Good morning Anti Jeederh" bata kalleta ba sai data gama haɗa kunun gyaɗar ta juya tana harɗe hannu a ƙirji tana juya idanunta da suke ɗauke da ruwa kamar mai shirin kuka. Sai kawai ta girgiza kai tare da juyawa tana faɗin
"Ki haɗa a parlour" she said. "Ok Maah"
A parlour Majeederh ta samu Ruma na waya tana ganin Majeederh ta ce "My Imran ga Anti Jeederh ku gaisa"
"Antynmu, ok give her the phone" Imran said.
Ruma ta miƙe tana bawa Anti Jeederh wayar ta ce "My Imran zai magana da babbar yaya, yama ce mini wai zai haɗaku aure da ƙanninsa idan Muzayyid ya amince"
Majeederh tayi jim she was so speechless.
Sai kawai tabar parlourn Idanunta rufe zuciya babu daɗi. Kaya ta sauya cikin Nidha abaya dark blue tayi rolling da babban vail kafin ta ɗauki kyakkyawan liƙab ɗinta ta sanya, gabaɗaya yau ta kasa jurewa dole ta isa gare shi, shi ke ɗauke mata kewa. Ta samu Abbu a parlourn shi ta tsuguna har ƙasa ya amsa yana cewa.
"Ya maganarmu dake?" Ta yi shiru ta kasa cewa komai. "Zan iya ɗaukar shirunki matsayin amsa"
"Abbu ka zaɓa mini ko waye, na amince zan aure shi" “…. Karatu na zaɓa miki, ki je nan da shekaru uku zuwa huɗu sai ki aure kafin nan kin kammala karatu"
Ta runtse Idanunta bata san amsar data bawa Abbu ba sai tsintar kunnenta tayi ta jin yana cewa "Allah ya yi miki Albarka, su dai bar su suyi auren tunda shi suka zaɓa"
Fitowa tayi bayan tayi sallama da mutanen gidan kanta a ƙasa tana rungume da ƙirjinta tafiya take a hankali mai cike da nutsuwa da kamala, ilhamarta ta gama bayyana gidan karamcin data fito, tare da tarbiyyar da take da shi. Napep ta tsayar ta shaida masa inda zata, tunda suka shiga kanta ke sunkuye lokaci zuwa lokaci mai napep ɗin ke kallonta ta cikin madubi har ya isa bakin gate ɗin data shaida masa. "Mun iso" ya ce yana karkaɗe kujerar da yake kai da dosta. Shirun da ya ji yasa ya juya mamakin yadsuta zuba tagumi Idanunta rufe yake yatsun hannunta kawai ya kalla yasan za a zuba kyau kuma Ubangiji ya gama tsara halittar shi a jikinta. Ya ce "Malama mun iso" Majeederh ta yi saurin buɗe Idanu, domin sunan da ɗalibanta na makarantar Ahlul Madar suke faɗa mata kenan Malama Majeederh Abdul'aziz Khan!
Ya saki murmushi ta cikin liƙab tare da fitowa tana ɗaukar jakarta ta bawa mai napep ɗin guda ɗari biyu. Ya ɗauki hamsin ya bata ta kalli hamsin ɗin ta ce
"100 ne" "Tab,Yoo maganar da kike wazai kawo ki nan a ɗari inda aka ƙarawa litar mai kuɗi" bata iya musu ba ta juya tare da nufar gate ɗin da aka rubuta.
*"An orphanage for young children"*
Ta faɗaɗa murmushinta tare da ɗan ƙarawa tafiyarta sauri zuciyarta sai janta take Idanunta ya kwaɗaitu ta son ganin abin da su kayi kewa. Kewarta ya yi mata jagora har zuwa office ɗin Akeeth. Yana ganinta ya miƙe tsaye with so much respect na tarin iliminta bawai don ta girme shi ba ya ce
"Your wlcm Majeederh-khan" ta jinjina kai tare da zama kan kujera tana rarraba Idanunta dake cikin liƙab, Akeeth ya ce. "Bar gaigaye za kici tumu ne"
"Uhm" ta furta ta ɗauki Wayarsa ringing ɗin farko aka ɗauka Akeeth ya ce "Come with him"
Ya kashe kiran yana kallon Majeederh yadda take kallonsa yasa ya fahimci me take nufi ya ce "She's goode, but she's trouble Maker very stubborn boy" "....Am very sorry for that"
Majeederh said. Tana haɗe hannu waje guda alamar ban haƙuri.
Akeeth ya watsa hannu baya ya ce "Is there nothing serious, kawai har yanzu bai sauya ba"
Ya gyara zama sosai cikin fahimta ya ce "Baya jin magana, ya yi ƙanƙanta da irin trouble ɗin da yake haɗa mana, he just Five years amma fitar shi ne sai shi, baya ɗaukan karatu da muhimmaci" Majeederh tayi shiru kawai domin bata san me zata ce ba, bawai don ta rasa ba, sai don bakinta ya yi mata nauyi harshenta ya harɗe bakiɗaya. Tun kafin ya shigo jikinta ya bata yana tsaye a ƙofa ta juya da ɗan sauri ganinsa tayi tsaye daga shi sai gajeren wando na Adidas sai wata ƴar shirt mai photon lion a gaba wacce ka yaga masa ita ta baya, jikinsa futu-futu.
Kan nan na shi gabaɗaya a cure fatar shi haƙa ƙarin, ta dube shi suka haɗa idanu da gudu ya ƙarasa wajanta cikin farin ciki da murn ya faɗa jikinta yana cewa
"Mamina, ƴar madara"
Faɗa zata yi masa amma jin yadda yake sauke ajjiyar zuciya a jikinta ya yi lamo tare da ƙanƙameta ya sa rauni ya bayyana a tare da ita, rauni irin na uwa da ɗanta ta lumshe idanu tana shafa sumar kan shi "Little" "Ƴar Madara"
Ya ce yana rufe Idanu tasan tunda ya ce Ƴar madara bai ce Mamina ba to fushi yake da ita.
Akeeth ya ce "Majeederh ni banga cancantar riƙe shi a wajanki ba, duba da cewa ke ba aure gareki ba, kuma idan kika duba yanayin society ɗinmu akwai wasu abubuwan da idan mutum mara aure ya yi shi musamman ɗiya mace za a fara yi mata wani irin kallo nada ban, tunda mutane basa buƙatar bincike kafin making decisions zuwa zatar da shi, kawai the only thing da suka iya yaɗa jita-jita da ƙanzon kurege, You have to be very careful"
"I'll, but" ta yi shiru daga maganar. "But what? Open your heart Mrs Khan" Majeederh ta ce
"About his family?" Akeeth ya ce "Oh Yes! Babu wata amsa gamshasshiya wacce bincikenmu ya nuna, na faɗa miki a bakin masallaci aka tsince shi a shekaru uku da suka gabata,zan ci-gaba da bincike komai ake ciki I'll let you know" ta jinjina kai Akeeth yana ta son ko sau ɗaya ne yaga fuskar Majeederh amma ina. Ta miƙe tsaye tana riƙe da hannun Little.
"Thank you!"
"Always Wlcm" fita su ka yi har bakin gate tana kallon yadda Little yaƙi ce mata komai, alamun ya yi fushi sosai ta duba hamsin ɗin da tayi saura a hannunta sai kawai ta bawa mai ice-cream na kan hanya ya bata na hamsin ɗin ta kalli kyakkyawar fuskar shi wacce ta kasa bayyanar da asalin yare ko ƙabilar daya fito ta ce "Take Little, Mami ce am sorry muje gida na baka chocolate" ya buɗe idanunsa ya ce "Ƴar madara" ta dungure masa kai, ganin daga gidan marayun zuwa gidansu akwai tafiya ya sa ta durƙosa tare da cewa "Hau baya, sweetheart" da sauri ya haye bayanta ya maƙale hannunsa a ƙasan ƙirjinta....
MIJIN MALAMA
Paid book ne
Book 1 and 2 1kne
Pay....0811923761617
Tafiya suke a nutse duk da ya yi mata nauyi a baya shekarun shi biyar a duniya amma yana da girma jiki ga shegen wayo. Ya ƙara shigewa bayanta ya ce "Mamina"
"Little babe" ya leƙo ta gefen fuskarta ya ce
"Mamina ke baki da mota? Me ya sa baki zo wajena ba, me ya sa kike mini faɗa ai nayi ƙarfi duka nakewa yara, I will fight, and I will win"
Murmushi kawai ta yi masa a zuciyarta tana mamakin yadda da yawan lokaci turanci ke zama a bakin shi, bai ci ace daga fara karatun shi ya fara turanci har haka ba. Jin ta yi shiru ya ce
"Get me down, Mami"
"No, little ba zaka iya tafiya ba" ya fara buga ƙafa a bayanta tare da ƙoƙarin sakin kuka. A hankali ta tsaya tana mai da numfashi kana ta sauke shi a ƙasa ya yi mata murmushi yana rufe Idanu tare da suɗe baki na daɗin ice-cream. Gani tayi ya durƙosa a gabanta ya ce "Ni ma zan rama muki, haka muke a school"
"What! wa zaka goya?'
Ya tura baki gaba ya ce
"Ke Ƴar madara, ai duk wanda ya goyaka kai ma kai masa haka ko Mami?" Ta tsora masa idanu surutun shi na bata mamaki ƙwarai ta sunkuya daidai tsayin shi ta shiga kaɗe masa gasar jikinsa tana shata samar kan shi daya hana a aske ta ce "To ai uwa duk abin da ta yi wa ɗanta daidai ne"
"Kyautatawa nada daɗi kin ce Mami?" Ta jinjina masa kai cike da jin daɗi tana faɗin "Shikenan ka bari idan ka sake girma ka goyani" ya dinga tsalle da murna zai goya Maminsa ƴar madara.
"Promise?" Ta miƙa masa hannu ta ce "Promise" ta kama hannunsa suka cigaba da tafiya tana jin zuciyarta daɗi ga wani farin ciki yau zata kwana da Little daman sabgar shagalin musabaƙa ya sanya ta kai shi can tunda ba kowa yake kula da shi a gidan nasu ba. Tun daga can har gida suka ƙarasu a ƙafa suna tafe yana mata surutu wasu ta gane wasu kuma kamar wani yare nada ban haka yake. A daidai ƙofa Majeederh taci karo da Latifa taja baya tana ƙara riƙe hannun Little dake ƙoƙarin tafiya wajan daya hango yara age mate ɗin shi suna faɗa. "Yanzu na shiga ake ce mini bakya nan" cewar Latifa. Ta lumshe Idanu cike da gajiya ga azumi don ma rana ta fara sanyi a gajarce ta ce "haka ne" Latifa ta ce "Ki ce ɗan rigima kika ɗakko daman tun da mu ka yi waya nake son tambayarki shi sai kuma naga you're not on the mood na share" Majeederh ta ce "Ayya, muje" suka shiga cikin gidan a tare tana shiga ta jiyo muryar Uncle Isma'il ta faɗaɗa murmushinta tana sakin hannun Little ta shiga parlourn Abbu. Uncle Isma'il ne da Uncle Bello suna zaune suna tattaunawa akan maganar Widad da kuma kuɗin Ruma da za a kawo. Ya Uncle Bello ya dubi Majeederh ya ce
"Hawwa'u an dawo? Yanzu ake ce mana bakya nan" ta sunkuyar da kanta ƙasa cike da ladabi ta ce "Eh Uncle, an yini lafiya" "Allahamdu lillahi" ya bata amsa yana mai jin tausayinta har ranshi sbd zurfin ciki da take da shi ga yadda duk al'amarin rayuwa yake jirkice mata. "Uncle..," Uncle Isma'il ya yi saurin ɗaga mata hannu cike da ɓacin rai da damuwa ya ce "Kin kyauta tunda tsarin da ki kaiwa kanki kenan, ba bu abin da zamu iya ikon ki ne ke kike da kanki Hawwa'u" zuciyarta ta buga tsoro da fargaba suka risketa a wannan lokacin idan aka tsaga jikinta ba lallai a samu jini ba sbd tsabar fargaba. Amma sam fuskarka ko yanayinta bai nuna hakan ba. Cikin sanyin murya ta ce "Me nayi Uncle?" A hassale kamar zai daketa ya ce
"Ni kike tambaya me kika yi ko Hawwa'u? Yanzu yaron nan Imran kwanaki yazo yana son ki har iyayensa ya fara yunƙurin turawa, ban san mene ya faru ba naji maganar shiru, yanzu kuma na samu labarin zai kawo kuɗin Rumana na tambayi Abdul'aziz ya ce da kanki kika cewa Imran bakya son shi kada ki sake ganin ƙafar shi?"
Duk da sanyin shigewar hadari bai hana Majeederh jin wata zufa ta yanko mata ba, daga ina wannan al'amarin ya bayyana waye ya shirya mata maganar da bata san da ita ba, waye yake shirin wargatsa burinta?. Ta kasa cewa komai yawun bakinta ya maƙale ga ƙishin azumi ganta ya shiga juyawa. Uncle Isma'il ya gyara zama domin ya fi kowa zafi akaf familyn Khan.
"Duk abin da ya faru ki kuka da kanki, ruwa cikin cokali ya ishi mai hankali wanka, itikafi rayuwa kaɗai zai sanya ki kai kanki tubalin tundun mun tsira, idan ba sukike rayuwar duniya ta baki naki kason ba, ina cewa akan idanunki aka haifi Widad? Sa'ar Aaliyyah ce amma aurenta za ayi, akan idanunki aka haifi Du'a Yaronta ɗaya ciki ne da ita yanzu, shi ne kin samu mijin aure zaki wasa da damarki akan wani karatu? Anya lissafi da burin zuciyarki da kwaɗayin ganin kin samu wadatacce ilimi ya miki adalci? Hawwa'u aure da haihuwa da arziƙi na Allah ne, kuma lokaci ke wanzar da samuwar su kada ki rufe idanunki akan wani abu wanda bashi da wani muhimmaci, ke ba a bin kunya bane ace saurayin da yake son ki ya koma wajan ƙanwarki, baban abin takaici ma wai ke ce da kanki kika lamumce masa auren Rumana, Goodness what noises? Meke damunki ne?" Majeederh ta fara shiga ruɗani da fara kokwanto anya ana sonta a gidan? Me ya sa ake shirya mata abin da bata sani ba? Ta ɗago kai a hankali tare da zare liƙab ɗin kanta, fuskarta ta yi jajur cikin muryarta mai sanyi kamar wacce take shirin yi musu shagwaɓa ta ce "Uncle ka yi haƙuri, ka zaɓa mini mijin ko a gobe ne" Rashin sani ya fi dare duhu, rashin sani baƙo ya sha ruwa wanka, sun kasa fahimtar ita kanta a ɓukace take da yin aure, babu abin da take sha'awa irin ta ganta gidan mijin babu abinda ke birgeta irin ta juya taga nata mijin a gefenta. Uncle Bello ya numfasa a lokacin ya ce
"A'a ba ayi haka ba, ai darajarki da kimarki ta shige a nema miki mijin aure, kaf yaranmu ba wanda muka sadakar ko zaɓawa miji ba zamu fara a akanki ba, kin yi kuskure tun farko sai ki gyara ki je Allah ya zaɓa mafi alheri" Uncle Isma'il ya ce "Wallahi kin ɓata rawarki da tsalle Majeederh iliminki bai amfana miki da komai ba....." "Uncle Mami na kakewa faɗa?"
Siririyar Muryar yaron ta tsayar da Uncle Isma'il daga yin magana. Sai a lokacin Abbu ya ɗaga kai ya ce "To rasai yanzu za a san ka dawo, ko zaka rama mata?" Little ya dinga kallon Uncle Isma'il yana huci idanunsa suka kaɗa tare da yin jaa wata kalar zuciya ce da yaron kamar kuturu ya shiga surutu a ranshi bakinsa kawai ke motsawa.
Cikin sauri Majeederh ta kama hannun shi ta ce "Say sorry to him" ya yi shiru idanunsa ƙuri akan Uncle Isma'il ganin yadda ya sanya Maminsa a gaba yana mata faɗa gashi har fuskarta tayi jaa daman ta haka yake gane kukan zuci take. Majeederh ta finciko Little ta ce "Ka bawa Uncle haƙuri" ba tare daya kalleta ba ya ce "He is shouting at you"
"He's my Father, am i your mother, na ce ka bashi haƙuri, say sorry to him" ya kafe yaƙi cewa hannu Majeederh ta ɗaga hannu ta zabga masa mari nan take yatsun hannunta ya bayyana a fuskar shi duk da kasancewar fatar shi baƙa. Cikin ɓacin rai ta jawo shi har gaban Uncle domin gani take idan bata hukunta shi ba a haka zai tashi da rashin kunya da shiga sabgar da babu ruwan shi.
“....Say sorry to him..”
"Uhm, Allah ya shirya ya kyauta, tun baki haifi naki ba kin fara dakon wahala Majeederh?" Cewar Uncle Bello Abbu ya ce
"Hankaka mai da ɗan wani naka kenan, kin kyauta kina riƙe wanda yake zagine yayyina"
Idanunta ya kaɗa sosai ta ce "Don Allah Uncle ka yi haƙuri ba zai sake ba"
Ta miƙe tana kama hannunsa lokacin Latifa ta gaji da jiranta har ta tafi gida. Ta samu Aaliyyah ta dawo daga makaranta tana shirya abincin rana lunch. Raihana na zaune ana waya da saurayi. Babu wanda ta kula sai Aaliyyah dake cewa "Sannu da dawowa Anti Jeederh" ta shige ɗaki tana jinjina kanta alamar "Yawwa" suna shiga ta saki hannun Little tare da ɗakko bulala ta waya ta kama hannunsa ta zirara masa guda ɗaya
"As form today na ƙara jin kayi magana da babba sai jikinka ya faɗa maka" ta ƙara zirara masa hannun ya taro jini amma bai motsa ba sai cewa ya yi "Faɗa ya miki ƴar madara" Majeederh ta ware Idanu tama rasa me za tayi sai kawai ta miƙe tare da shigewa Bathroom tayi wanka da Alwala ta wanke fuskarta sosai har jan fuskar ya daidaita domin ta fahimci sauyin fuskarta yake sawa Little ya fahimci halin da take ciki, bata taɓa ganin yaro mai fikira da shegen wayo kamar shi ba ga ɗan banzan wasa da shiga faɗan da bana shi ba. Duguwar riga ta sanya ash ta saka hijabi a kan idanunsa tayi sallah har sallar Asr tayi Asstagafirullah na lattin da tayi kana ta fara azkar na yamma ta dube shi fuska a haɗe ta ce "Sallah" da sauri kamar zai kifa ya shige bathroom. Babban abin da yake bata mamaki kafin ya yi sallah sai ya duba ko'ina yaga ita kaɗai ce a ɗakin yake yi jikinsa har rawa yake sbd tsoro ta rasa dalilin haka. Yana idarwa ta dawo kusa da ita a hankali ya ce "Sorry Mami"
Tayi shiru fuska haɗe sosai ya marairaice ya ƙara cewa "Sorry"
Sai a lokacin ta ce "Uncle zaka bawa" ya maƙale ka faɗa ya ce "I hate him, faɗa yake miki" wata kalar tsawa ta daka masa tare da nuna masa waje ta ce "Out"
Dai-dai lokacin Aaliyyah na shigowa ta ce "Mun shiga wannan tsaiwar ai ta sa na kusa sakin fitsari a wando, wai little kikewa tsawa haka?" Idan Majeederh ta gini ya motsa Majeederh ta motsa. Aaliyyah ta ja hannunsa suka fita yana tirjewa shi a wajan Majeederh zai zauna duk da tsawar da tayi masa. Har akai sallar Magriba Majeederh ta sha ruwa tai sallah Idanunta bai ƙara ganin Little ba, a wajan Mami take ji wai ko abinci yaƙi ci ya fito waje sun yi faɗa an fasa masa kai. Sosai tai mamaki babu yadda za a yi aci galaba akan Little a kullum ita take bada haƙuri ta tabbatar hakan baya rasa nasaba da faɗan da tayi masa. Tana son ta tambayi yana isa amma girman kai da nauyin baki irin na Majeederh sai kawai tayi shiru. Cikin dare wajan ƙarfe ɗaya taji saukar numfashi a jikinta, Numfashin mai ɗauke da zafi da buɗe Idanunta da suke ciki da bacci ganinta ya sauka akan Little dake rawar sanyi kayan safe ne a jikinsa har yanzu ta buɗe ido da kyau tare da taɓa wuyansa jikinsa zafi zau bakinta har ɓari yake ta ce "Little, little" ya buɗe ido yana ganinta ya ce "Sorry Jee Mami" bata kula shi ba ta ɗauki paracetamol na ruwa tare da ɗora shi a cinyarta zata bashi maganin ya girgiza kai ya ce "Ba zan sake ba ƴar madara, na daina Jee" jin ana ce mata Anti Jeederh shi kuma ba zai iya faɗa bakiɗaya ba ya sa yake cewa Jee, sai watarana data bashi alawar madara ya ce da Maminsa da alawar madarar suna kama tun daga nan yake cewa ƴar madara. Ta ɗauke kai ya ƙara sakin jiki yana kwaɓe fuska ya ce "Zan sake ba Mami, zan sake ba" ta saki fuska tana murmushi ta ce "Ok good boy I forgive you" da sauri ya shige jikinta ya rungumeta jikin nan nasa zafi sosai ta shafa kansa taji ya saki ajjiyar zuciya da sauri ta taɓa cikin shafal ba komai da alamar yadda yunwa ke damunsa ta ɗago shi za tayi magana taga har bacci ya ɗauke shi a hankali ta ɗauke ajjiyar zuciya tare da jansa jikinta ta rungume shi wani irin son shi na ƙara ratsa zuciyarta...
MIJIN MALAMA
Paid book
Book 1 and 2 1k
08119237616
Nimcyluv18
Baccin Little ya yi nisa sosai kafin ta miƙe tare da rufe shi da bargo ganin iska sosai na ɗaga labulen bedroom ɗinta. Wajan window ta ƙarasa tare da tsayawa ta sanya hannunta duka guda biyun ta ɗaga labulen Idanunta rufe a hankali iskar dake kaɗawa ta tasuwar hadarin dake kwance tun safe ta shiga ratsa ta. A duniya Majeederh tana so da ƙaunar taga ana ruwan sama, ko bata cikin yanayi na jin daɗi sai ta samu kanta cikin farin ciki nutsuwa ta saukar mata a lokacin duk wata damuwar data samu gurbi a zuciyarta take yayewa. Ƙara tura kanta tayi wajan window ɗin tana rufe ido fresh air ɗin na ratsa ta tana jinta har ƙasan zuciyarta damuwa da tunanin maganganun Uncle Isma'il ya goge a zuciyarta. Ta ɗauki wasu mintuna a wajan kafin ta ji motsi a bayanta ta juya da ɗan sauri tsaye ta gabashi daidai kafaɗarta ya jawo locker tare da hawa kai idanunsa na waje ita kuma tana kallonsa. Shi ma yadda ruwan zai sauka yake kallo yasan Maminsa indai ta tsaya a nan to ruwan sama za ayi, ganin ba ruwa sai gari take ta ihu da rugugi ga iska mai daɗi yatsuna fuska ya yi looking damn cute. Majeederh tayi masa murmushi taja baya ta ce "Ai kowa bani da abinci, waye yace ka kwanta kai kana fushi da Mami harda fita ai maka duka, thank God" kamar mai shirin rarrafe ya sauka daga kan locker tare da zubawa Majeederh Idanu yana kwaɓe fuska domin da gaske yunwa yake ji, ita kaɗai ke sawa ya nutsu duk rashin jinsa, daga yunwa sai faɗan da zatai masa idan ya yi abu. Ta ƙarasa kan gado tare da kwanciya tayi rigingine tana kallonsa tare da ganin zai haƙura ya kwanta ko sai ya yi rigimar yunwar. Bata kammala tunanin da take ba taji gabaɗaya ya haye cikinta tare da sanya mata kuka yana yarfe hannu. Ta zare Idanu da sauri ta miƙe da shi tare da ɗaukar shi a kafaɗa ta ce "Ai yau fa babu kai babu cin abincin dare salon kayi girman da zan kasa goyaka" Little ya ƙarawa kukansa ƙarfi ya ce "Mami Indomie"
"Sannu baban Indomie" ta ƙarasa da shi main parlour tare da shigewa kitchen yana goye a bayanta ya saƙalo hannayensa ta wuyanta. Ya dinga leƙawa. "Ok get down, zaka fasa mini ƙirji" ya saki dariya while hawaye na gangaro masa. A saman sink ta ajjiye shi ta kunna gas-cooker indomie ta dafa masa ba tare data saka attarihu ba domin baya son ya ji.
"Mami egg fa?"
"Babu" ya ce "baki da kuɗi?" Ta dube shi tare da girgiza kai ya ƙara cewa "baki da kuɗi?". Ba zai taɓa barinta ba idan ba amsa ta bashi ba. Tana juye masa Indomie a plate ta ce "Kayi addu'a zan samu ƙarshen wata ya kusa" ya yi ta kallonta ya ce "Me ake a ƙarshen watan?" Ta sauke shi daga kan sink ɗin tare da tsugunawa ya hau bayanta plate ɗin abinci a hannunta ɗaya kuma bottle water ne guda ɗaya ta ce "Idan end of month ya yi zan samu salari kuɗin aiki kenan"
"To idan baki samu ba, ba zan ƙara cin egg ba, kuma ba zaki sai mota kina kai ni school ba?"
Daidai lokacin ta buɗe Ƙofar bedroom ta shiga ta mayar ta rufe tare da sauke shi. Ta zauna a ƙasan carpet yana zaune a cinyarta ta tallafo fuskarsa cikin kyakkyawan lafazi da magana wacce ƙaramin yaro zai fahimta ta ce
"Little ya sunanka?"
"Little" ya bata amsa
"Ba pronoun ba, asalin sunanka me ake ce maka" yadda yake kallon cikin Idanunta kaɗai zai tabbatar mata bai ma san akan me take magana ba, balle ya bata amsa. Majeederh bata son sunan Little ya bisa, lokacin data tsince shi bakin masallaci he just 3yrs bai san komai ba, ba zai iya tuna komai ba. Shekarunsa biyu a wajanta ciff da wasu watanni. Tana tsintar shi kuma kai tsaye ƴan sanda taiwa reporting amma sam yaƙi zama a wajansu tun a lokacin ya dinga ƙanƙameta yana cewa “Mamina”. Ganin yadda ya kasa sukuni ya sa ta buƙaci subar mata shi a duk sanda iyayensa suka bayyana zata bada shi, sosai aka sha faɗa domin Mami da Abbu idanunsu suka shafawa toka, sai dai Uncle Isma'il da Uncle Bello da Yaya Bilkisu suka shiga cikin maganar. Aka je orphanage tare da cike komai da komai aka an mallaka mata shi abadan. Tun a lokacin tasu a sanya masa suna amma fur yaƙi cewa komai he just watching her face a duk sanda ta tambayi sunan shi. Har kawo yanzu da yake zaune akan cinyarta yana kallonta. "You don't even know your name?"
"Little, ƴar madara"
Ta haɗe fuska tare da ɗaukan spoon ta shiga bashi Indomie yana ci yana gyaɗa kai tare da wasa da stone na gaban rigarta. Little na masifar son abinci, cikin abinci bashi da favorite sbd yadda yake mutuwar son food. Duk wasan shi da zarar ya fara jin yunwa yake nutsuwa ya sanyata a gaba da tambayar
"Mami food, I want to eat food" sau tari biyu take raba albashinta duk wata ta sai gatan ɗin Indomie da egg da kuma chocolate domin bata bashi ko sisi na makaranta zata haɗa masa breakfast box hadda chocolate ciki. Da kuɗin ta take biyan school fees bata son duk wani abu daya danganci maraya little ya yi kuka da shi. Da fari ta ɗauka rashin sanin sunan is nothing amma yanzu school sun matsa basa buƙatar wani little cikakken sunansa suke so, wannan dalilin ta shiga taraddadin sanin wanne irin suna zata bawa Little ɗin nata?
"Ƴar madara"
Ya dawo da ita daga tunanin ya watsa hannu ya ce "Na cinye"
"Zaka ƙara?" Ya girgiza kai ta ɓalle bottle water tare da tsiyaya masa a cup ta bashi bayan ya sha ta ce "Say Allahamdu lillahi" ya faɗi exactly abin da ta ce. "Mami zan siya miki mota babba irin ta Uncle Akeeth, zan baki kuɗi ki dinga siya mini Indomie da abin yin ƙarfi"
"Ƙarfi kuma?"
"Eh Mami, ina son yin ƙarfi na dinga dukan Uncle idan yana saki kuka" Nan da nan Majeederh ta haɗe fuska cikin tsoro da fargaba ya ce "Sorry Mami" ya faɗa yana kame kunnenshi.
Ta kama hannunsa ta ce
"Little zaka iya dukana idan ka girma?" Ya zare idanu ya ce "A'a"
"Why?" "You're my mother" ta ce "Good, Uncle Isma'il mahaifina ne, duk abin da ya yi mini daidai ne yana so na, ba zai bari na wulaƙanta ba, ka zama good boy mai haƙuri da rayuwa ka rage zafin zuciya,na shiga uku ni Majeederh idan ka girma a haka da zafin zuciya wacce Mace ka ke tunanin zata iya zama dakai" da sauri ya ce
"You! Mami ke zaki iya zama" ta watsa masa harara ta ce "Yaro ba Mutum ba sai ya girma, daman duk lalacewarks ni ya zamewa dole zama da kai ok" ganin tana son sanya masa tunanin daba nasa ba yasa ta sauya topic ɗin da cewa.
"Muje bacci"
Gabaɗaya suka kwanta akan gado kanta akan pillow nashi kan a hannunta suka kalli juna lokaci ɗaya kamar yadda suka saba yin waƙar su a koda Yaushe suka haɗa baki wajan faɗin.
_“Darling promise you wait for me, i go think of you everyday my love”_
Little fararren haƙoran shi waje ya ce "I love you Mami" ta rungume shi tana faɗin
"I love you too sweetheart"
Tana kallon shi har bacci ya ɗauke shi yana riƙe da ita kamar mai tsoran ta gudu ta basshi, duk sanda zai bacci koda rana ne dole sai ta zauna ya dinga cewa "Mami ba zaki tafi ko'ina ba? Mami zaki iya tsaya ido ya buɗe?" Da yawan lokaci haka yake cewa ta fahimci har yanzu a ransa ji yake zata gudu ta barshi. Ta shafa sumar kansa tare da yi masa addu'a ta shafa masa a haka bacci ya ɗauke ta rungume da ɗanta Little. Kana ganinsu kasan soyayya ce da Ubangiji. Love for blood, love from God. Babu mai rabawa sai Allah.
Washegari ta su makara, an kusa idar da sallah ta farka tayi alwala tare da sallah tayi azkar. Tana kammalawa ta matsa ta shiga tashin Little amma kamar bai san me take ba, wani irin nauyin bacci ne da shi musamman idan ya samu yadda yake so, an kawo wuta ga iskar Subhi gata fanka. Sai a ɗauke shi a zura shi a buhu bai sani ba. Ɗaukar shi sai banɗaki acan ta dire shi ta sakar masa shower. Ya buɗe ido da sauri jin ruwa akan shi. Ta ɗauki ƙaramin towel ta ɗaura masa a ƙugu kana ta zare masa wando tana ji yana ta dariya yana jan gashin kanta tayi masa shiru. A haka tayi masa wanka da towel a jikinsa tana gamawa ta ɗauke shi ta shafa masa lotion ɗin shi ta taje masa sumar kan da mataji riga da wandon Adidas ta saka masa red and black suka amshi jikinsa kana ta sanya shi gaba ya yi sallah. Kasancewar cikin dare ya ci abinci bai nemi abinci sassafe ba. Fargaba ta risketa domin bata da raguwar wata Indomie, sai kawai taga ya kwanta ya juya mata baya bacci ya sake ɗaukan shi. Hamdala tayi a ranta tana fita daga cikin bedroom ɗin ta zuwa main parlour.
Ba kowa aciki ta nufi ɗakin Abbu yana zaune saman ladduma yana jan carbi ta tsuguna ta ce
"Ina kwana Abbu?"
"Lafiya lou Hawwa'u, ya ɗan naki?" Sosai tai mmkin yadda ba damuwa a fuska ya tambayi Little "Bacci yake" ya ce "to Allah ya yi albarka, Yaya Bilkisu na nemanki wai tunda aka fara sabgar biki bata ganki ba ko laifi akai miki?" Tayi shiru kawai
"Akwai damuwa ne?"
"Zani Anjima" hannu ya sa ya fito da ɗari biyu da hamsin ya bata ya ce
"Ki hau napep, ko Yaya Bilkisu zata baki na dawowa na ji ance fetur ya ƙara farashi"
"Na gode, Allah ya ƙara arziƙi" ya dubeta ya ce
"Daga nan ki je kiyi photo zan tura da wasu takardunki tafiyarki ta matso" yanzu bata data cewa burinta Ubangiji ya bata haƙuri da juriyar yadda take ji Allah ya tsare imaninta da mutuncinta na ɗiya mace
"Ki na ji na?"
"Eh, Abbu" ta ɗaga kai cikin sanyin nan nata ta ce "Me zan karanta acan? Shekara nawa zan?" Abbu ya ce
"Islamic studies, zai ɗauke ki shekara uku zuwa huɗu" kenan a lokacin tana da shekaru Ashirin da huɗu kafin kammala tunaninta ta ji ya ce "Sai ki juya zuwa Islamic language, zai ɗaukeki zuwa shekaru huɗu haka" lokacin shekarunta Ashirin da takwas babu lissafi aurenta gabaɗaya a maganar Abbu. Bata son musu da duk abin da Abbu ya shimfiɗa mata tana ganin hakan shi ne daidai tunda abin da ya hango ba lallai ta hango shi ba. Tana zaune ta ji Mami ta rangaɗa uwar buɗe wacce ta sanya Majeederh saurin rufe Idanu faɗuwar gaba ya sameta haka kurum. Mami ta shigo tana gyara ɗaurin zani ta ce
"Allahamdu lillahi, ma sha Allah ashe Rumana ƙashin arziƙi ce, shi ya sa ake cewa ko kana gudu haifi ka yar" Abbu kallonta yake yana jiran jin me zata ce ta zaune dab da shi ta ce "Yanzu Matar Isma'il Luba take shaida mini an kawo kuɗin na gani ina so na Rumana Dubu ɗari biyu har sanya rana, kai Allhamdu lillahi kafin nan da wata guda an kawo kuɗin Raihana kaga sai mu haɗe bikin waje guda" Majeederh ta miƙe tsaye tana jin jiri na ɗaukanta shikenan za su aure gori zai ƙara tabbata. Tana ƙoƙarin fita Mami ta ce "Babbar yaya magajiyar uwa, Majeederh Imran ne fa wanda kika ce bakya so? Shi ne ya kawo kuɗin ƙanwarki Rumana saurayin yaya zai zama mijin ƙanwa" Majeederh ta haɗiye yawu da ƙyar kafin ta tattaro abin da ya yi masa saura a baki ta ce "Allah ya sa albarka" "Amin Amin ke kuma Allah ya sawa karatu albarka"
A parlour ta samu Rumana na tiƙar rawa tana cewa "Ko anƙo ko an su aure ya ɗauro murna muke daga fuska har zuwa ranmu, zan zama matar Imran"
Tana rawa Raihana na yi mata rawa Aaliyyah na kitchen tana haɗa breakfast. Ƙosai take soyawa a lokacin da kunun gyaɗa. Hukuncin Ubangiji ne kawai ya kai Majeederh ɗakinta ta zube a bakin gado tana riƙe kanta da zuciyarta take bugawa. Little daya tashi tun ɗazo ya ce
"Mami kai ne? Ciwo?"
Ta sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya tana ƙaƙaro Murmushi ta ce "My little son" ya yi murmushi ya durƙosa a gabanta ya ce
"Good morning ƴar madara Mamina" ta ja hancinsa tana shafa sumar kansa ta ce "Ok jeka ka yi brush kafin na dawo" ya ce "Zani Mami"
Ta haɗe fuska ta ce
"Yanzu zan dawo ok" ya ɗaga mata kai ɗari biyu da hamsin ɗin da Abbu ya bata ta ɗauka tare da sanya hijabi har ƙasa ta ɗauki liƙab ta saka tare da ficewa ya bita da kallo. Katin dake kusa da gidansu Majeederh ta ƙarasa cikin muryarta mai daɗi da sanyi ta ce "Indomie zaka bani ƴar 170 sai egg guda biyu 60" ya ce "Malama Majeederh kuɗin ya kama 290 ne, kuma 250 kika bayar ta yi jim kafin ta ce "Ok bani ƴar 150" ya bata indomie ɗaya da ƙwai guda biyu. A ranta tana cewa sai dai na je gidan Yaya Bilkisu a ƙafa idan ya so sai na goya Little a baya.....
MIJIN MALAMA
Paid book ne
Book 1 and 2 (1k)
08119237616
Nimcyluv19
Lokacin data koma gida ta same su duk suna breakfast Mami ta ce "Majeederh danƙi baya cin ƙosai shi ya sa ban kira shi ba" Majeederh ta san babu abin da Little baya ci kawai dai bata taɓa gwada bashi ƙosai bane balle ta ce. A hankali ta jinjina kanta kawai alamar "Eh" kana ta nufi cikin bedroom ɗinta. Ta samu Little a tsakiyar gado ya yi ɗai-ɗai tare da langwaɓe kai kamar mara lafiya ta yi murmushi tana ɗauke kai ya ce "Mami yunwa ina ji" a taushashe cikin sanyin murya ta ce "Na sani, bani 10 minutes"
Ya ɗaga mata ta fita wajan 15 minutes ta dawo hannunta ɗauke da plate ɗin Indomie gefe kuma ta soya masa ƙwai sai ƙamshi suke. Yana ganinta ya miƙe tsaye yana kyakkyawan murmushi tare da tsalle ya ce "Idan na yi kuɗi zan baki kuɗi da yawa"
"Aikin me za ka yi" ya ɗaga kai sama alamar tunani kafin ya watsa hannu baya ya ce "Zan samu kuɗi, naiwa duk wanda ya saki kuka duka" "Allah ya shirya ka ya yi maka albarka"
Ya yi murmushi da kyawawan haƙoran shi ta shiga bashi Indomie a baki yana zaune akan cinyarta. Bashi abincin kawai take amma a zahiri tunanin yana wani wajan daban ita kanta ba zata iya lissafa inda tunanin nata ya je ba,idan ta tafi wazai kula mata da Little? Wazai jure rigamar shi da ɗakko mata magana da yake? Tana wannan tunanin ta ji yatsun shi biyar a cikin bakinta ya tura mata wainar ƙwan data soya masa, ta zare idanu cike da maɗaukakin mamaki ta kasa magana sbd ya yi mata yawa a baki Little ya dinga tun tsire dry. Ta ɗaga hannu kamar zata dake shi ya yi saurin rungumeta yana cewa "Sorry Mami" hugging nasa back ta yi tana shafa kansa tana gama bashi ta miƙar da shi tsaye akan gadon ta kama hannunsa ta marairaice fuska ta ce "Little" "Mamina"
"Za mu gidan Uncle Isma'il yanzu" nan da nan ya haɗe fuska kamar bai taɓa dry ba zuciyarsa ta motsa ya yi ƙasa da kansa. Ta yi murmushi domin ta san za a rina an saci zanin mahaukaciya.
Ta leƙa fuskarshi ya yi saurin rufe Idanu ta ce "Ba zaka ba?" Ya ɗaga kai da sauri ta ce "To ni zani, ka zauna a gida"
Ya maƙale ka faɗa ya ce "Mami mu zauna a gida" "Dole za mu, ai Uncle Isma'il ɗin baya nan ka ji kuma a bayana zaka goyaka zan" ya yi saurin cewa "Baki da Kuɗi?"
"A'a kawai tafiyar ƙafa akwai daɗi" Ta tallafo fuskarsa ta ce "Don Allah banda faɗa ka zama nice har mu taho yau ɗin zan zan maka siyayya harda motar da ka ce"
"Har bindiga?" Ta kame fuska tana ɗauka shi zuwa toilet ta ce "A'a, ko soja zaka zama?" Ya yi mata shiru. Ruwan wanka ta haɗa kana ta ɗaura masa towel ta cire masa kayan tayi masa wankan tana mamakin baƙar fatarshi kamar ƙara mata baki ake amma baƙin irin mai kyau ɗin nan da ɗaukan Idanu. A wajan saka kaya ma faɗa sosai shi baya son manyan kaya dole ta saka masa wata brown ɗin t.shirt mai photon tiger a jiki sai wando 3gauter kayan su kayi masa wani irin sahihin kyau tare da amsar fatar shi. Tana gyara masa sumar kai ta ce "Ka tsaya na shirya ko ka fita parlour" ya ce "to"
Tana shiga wanka ta ya fita parlour ya leƙa yaga Aaliyyah ta ce "Big boy yau sai ina?" Ya lumshe idanu ya buɗe ya ce "Da Jee zamu" Aaliyyah ta ce "To daman ka isa ka fita kai ɗaya? Zo na yi maka photo" ta tsayar da shi a gabanta ta shiga yi masa photo suna tsaye Raihana ta fito ta ce "A'a ɗan baƙi na Anti Jeederh, kaga yaro mai uwar rana" bai kalleta ba daman jininsa bai zo ɗaya da ita ba. Little yana da wanne irin hali ga shegen wayon masifa kamar wassafa masa wasu abubuwan ake. Duk wanda suke takura rayuwar Majeederh ya haddace su tar kuma baya kula su. Raihana har ranƙwashin kansa tayi ta ce "Miskilin banza, daga gani uwarka fama tayi dakai kafin ya ɓata" "Mamin?" Ta ce "Uwarka na ce, ko an faɗa maka MAJEEDERH ita ce Uwarka?" Ya yi shiru kawai domin baya fahimta gabaɗaya. Suna nan yana yiwa Aaliyyah surutu yana itama zai siya mota bayan ya siyawa Maminsa ƙatuwa "Wato dole sai ka nunawa kafi son Maminka, to ai Mamin taka tafi so na" ya maƙale murya ya ce "A'a" Aaliyah ta yi masa gwalo ta ce "Ohho, wooo Mami ta fi so na akan ka" nan da nan ya haɗe fuska duk da yaro ne amma ya tsani ace Mami bata son shi. Aaliyyah za ta yi magana ya ji an sakar mata ranƙwashi akanta. Ta kwaɓe fuska ta ce
"Kai Anti Jeederh akan Little zaki dakeni" Little ya yi tsalle sosai ya ce "Mamina" Majeederh dake tsaye sanye cikin shigarta as usual abaya ce mai kyau da ɗaukan hankali ta yi rolling kana ta ɗora liƙab. Cikin wani sabon yanayi data samu kanta ta ce "Ki kiyayeni Aaliyyerh" Aaliyyah ta tura baki ta ce "To Anti Jeederh ai da gaske kin fi so na" Little ya kalli Majeederh yana jiran ya ji me zata ce. Sai bata ce komai ba ta kama hannunsa zuwa bedroom ɗin Mami ta sameta zaune ana ta buga waya ana faɗawa ƴan-uwa an kawo kuɗin Rumana Dubu ɗari biyu cif. A sanyaye ta ce "Mami na ta fi" Mami ta ce "Zuwa ina?" "Gidan Uncle Isma'il, Yaya Bilkisu na kirana" Mami ta ce
"To to na ji, yanzu Ruhuma zata wajan Widad maganar ankon biki Imrana ne zai kaita na ji ma ta ce yana hanya ki bari ku ta fi tare, kici arziƙin ƴar-uwarki ko?"
Bata son musu sai kawai ta ce "To" tana fitowa ta ja hannun Little su ka yi waje. A bakin ƙofa taci karo da Latifa cikin shigarta riga da skirt na atamfa ta yafa mayafi ta kalleta sosai sai bata ce komai ba. Latifa ta yi dry ta ce "A'a fa yadda kike takura kanki da zafi cikin duguwar riga da liƙab ni ba zan iya ba, shi imani a zuciya yake" Majeederh ta ce "Wane ya yi maganar imani?" Latifa ta ɗaga kafaɗa ta ce "yanzu zaki fara faɗar na bayyana tsaraici ki shiga kawo fatawa kala-kala, ke dai ka san ko a malamai tsaurin ra'ayi zaki" Ita dai Majeederh bata ce komai ba Latifa ta sake cewa "Sai ina?"
"Gidan Uncle Isma'il" "mu je na rakaki" tafiya suka fara a hankali Latifa ke surutu ita ɗaya domin Majeederh idan ka ji maganarta Little ne ya ce wani abu ko da Aaliyyah da suke Uwa ɗaya Uba ɗaya bata fiya hira da ita ba, sai dai faɗa idan ta yi kuskure akan abu. Tun da ya karyo kan motar shi idanunsa ya sauka akanta, wani irin maganaɗisun abu ya shiga fisgarsa zuwa gare ta. Ya tsorawa yatsun hannunta idanu wanda suke ɗauke da Little dake kafaɗarta a hankali yake lura da juyawar Idanunta tana bubbuga bayan yaron tafiyar a hankali mai cike da ɗaukan hankali wani abu ya ratsa zuciyarsa irin abun nan da ake kira da soyayyar fari, har suka zo daidai motarshi bai kula ba sai da suka gilma kaɗan ya sauke numfashi tare da buɗe motar shi ne ya fito. Kyakkyawan matashin saurayi mai fama da rufin asiri daka gani yanzu yake ji da samartakar shi. Fari ne kyakkyawa mai matsakaicin jiki nutsuwa da ilhama a tare da shi, yana sanye cikin kyakkyawar shigar dake nuna kamalar shi. Amy green ɗin shadda ce a jikinsa ya murza hula saman kansa zai ƙamshin turaren (Thierry mugler). Ƙamshin dake narkar da dukkan wata zuciyar ƴa mace. Ya ƙarawa tafiyarsa sauri harya tarar da su tunda ba wani sauri suke musamman tafiyar Majeederh wacce take kamar an zare mata laka. "Assalamu alaikum" Cak suka tsaya tunda sun san darajar sallama babu cancantar suna tafiya kuma wani na binsu. Ƙamshin Thierry mugler bai firgita Majeederh ba, deep down na zuciyarta addu'a take Rabbil izzati ya sanya wa'adin zamanta a gidan Abbu ne ya zo ƙarshe, addu'ata take Allah ya sa mai rusa zuwanta karatu ne ya bayyana, Al-hakkamu sarki kowa da kowa ya ƙaddarta masa ikonsa a yanzu nan, Allah ya da mai yaye mata damuwar dake sanyata azumi ne ya zo. Ta rufe Idanunta tana jiran ƴar manuniyyarsa ta tsaya akanta. "Wassalam" cewar Latifa tana duban matashin wanda ya amsa komai na kamalar mutum. Ya dinga kallon Majeederh ba zai ce ga kalar kyan fuskarta ba, amma yatsunta sun bayyana wace ita abubuwa da yake ji game da ita sai ya ji sun ninku ainun kamar zubar ruwan sama ya yi da hadari ya ƙara kankame. Cikin wani irin al'amara da gilamar wasu sabbin ƙaddarori masu wahalar fasaltasu ba tare da sanin abin da yake faɗa ba ya juya gabaɗaya kan Latifa ya ce "Amincin Allah ya tabbata ga ma'abociyar kyau da kwarjini, fatan san samu number wayarki ganin akan hanya kuke" a baɗini kalamar direct domin Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Ya zayyana su amma a zahiri tubalin ginin maganarsa da yadda ya zayyana su ya nuna mai fahimta da ganin komai cewa da Latifa Omar yake. Latifa ta yi jim ta ce "Ni, ko ita?" Ya ɗan tafe baki kaɗan ba tare sanin ainahin abin da yake ba ya ce "No, dake nake kyakkyaw" Dam! An koma. Zuciyar Majeederh ta bada sauti ta ƙara rufe Idanunta Allah ya sa zalamarta bata fiyi ba balle ta kunyatar da ita. Majeederh ta ƙara lamuncewa zuwa karatun nan nata na daga cikin ƙaddarorinta masu girma. Latifa ta ce "Amma sauri muke" "Kuyi mini alfarma ba don na isa a yi mini ba, sai dai ta yaku kare mutumci ku shiga na ƙarasar daku" ya faɗa yana haɗe hannu bibbiyu. Latifa ta juya ta kalli Majeederh ta ce
"Malama Majeederh ke ce me matsala Kinga Little har ya yi bacci ki zo mu je" Bawai fuskarta suke gani ba,amma ta ƙara kame kanta bata da wani kuzarin yin magana. Ya juya a hankali da ɗan sauri kuma ya buɗewa Majeederh ƙofa ta shiga a nutse da addu'a bakinta. Ya buɗewa Latifa Omar gaban motar ta shiga. Tafiya suke a nutse ya gyara zama ya ce "Sunana Barrister Aliyu Sufyan Alhassan" "Nice" Aliyu ya shafa gemu ya ce "A gida more especially Hajia suna ce mini Zaki, am the second born of my parents, ina da babba yaya Almustapha, mahaifina sunan shi Sufyan Alhassan yana nan tare damu, ya su nayi aikin jarida na ƙi, to ya na iya abincina yana ga Shari'a, sai mahaifiyata we call her Hajiya, I love my mother more than anything dake duniyar nan tamu, na yi karatu mai yawa akan Shari'a now an working with Shari'a court of appeal ban jima da fara aiki ba" Tunda ya fara magana Latifa ta rufe Idanu sosai har cikin zuciyarta Aliyu ya kwanta mata irin mijin da take so daka gani zai yi haƙuri sosai. Har suka isa gidan Uncle Isma'il Majeederh ko tari ba tayi ba ta rungume Little kamar zata mayar da shi ciki, lokaci zuwa lokaci Aliyu ya dinga kallon Majeederh ta madubi, duk sanda ya kalleta sai ya sauke numfashi a ɓoye. Suna tsayawa ta buɗe ƙofa ta fita ta shige ciki, da sauri kamar wacce wani abu ya biyota. Innati dake maƙale a bayan labule ta buga tsalle tana faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, wahala haula wala ƙuuwata, uban waye a wannan wajan?" Majeederh ta shiga tana sauke numfashi Innati ta ce "Amma dai Allah ya isa Kululu, Allah ya isa saura kaɗan na saki gudawa ɗaukan hakƙin nan har ina? Ashe ƙatuwar jahila muke zaune da ita kinsan alhakin da kika ɗauka? To wallahi ba wani yafewa nayi ƴar banza da fuska kamar karas" Majeederh ta tura baki tare da kwaɓe fuska ta ce "Ki barni" Innati ta riƙe haɓa ta ce "Na barki ba? Idan na barki a duniyar nan Kululu na kama ubanwa? Wa kike da shi daga duniya har lahira wanda ya shige ni?" Majeederh dai ba tayi magana ba ta ɗaga liƙab ɗin fuskarta Innati ta zabga sallati ganin yadda fuskar Majeed ta yi jajur kamar jini ya kwanta. Innati ta kwasa a guje zani na faɗuwa ta shiga faɗin "Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama, Isma'ila masifa ta faɗo mana uban kowa ya yi ta kansa Aljana mai kama da Kululu a ɗakina....
*A yi karatu a nutse, a fahimta a ilmance, a nishaɗantu. Muna nutsawa a labari zaku kasa bacci da sukuni. Soyayya ce mai wahalar gogewa, ƙaddara ce mai wahalar fahimta. Babu batun sadaukarwa faɗa ne akan Soyayya!*
Allah ya nuna mana Monday Lafiya, a yi weekend cikin farin ciki.... 08119237616
Nimcyluv20
"Masifa da bala'i, Kamarni har wata Aljana ta isa ta firgita? Ina Isma'ila ya zo ya yi mini iyaka da wannan Aljanar tun kafin raina ya ɓaci" Innati ta faɗi hakan jikinta gabaɗaya rawa yake na fargaba da tsoro, tuni ta yi wurgi da zanin jikinta sai ɗan tofin daya rage mata banda haka tsirara za ta yi.
Uncle Isma'il daya fito a hargitse sbd jin kiran shi da Innati ke yi ya sa yana zuwa ya ce "Innati lafiya dai? Mene ya faru?"
Ta girgiza kai ta ce "Lafiyar kenan, maza maza a haɗa mini kayana yau sai gidan Bello, ba zan zauna matarka da kasheni ba, ina sane ita take tura mini Aljanu" Uncle Isma'il ya kusan tuntsirewa da dariya amma babu hali duk abin da ya kuro ɓera da ga wuta, ya fi wutar zafi. "Majeederh ta ƙarasu?" Ta zare idanu ta ce "Wata abace haka? Ka je dai kaga turan da akai mini da wata Bafullatanar Aljana" Uncle Isma'il ya bar Innati a tsaye, tare da nufar ɗakinta. Yana shiga ya samu Majeederh durƙoshe a saman gwiwoyinta ta dafe kanta da hannu bibbiyu wanda yake bazaranar rabe mata gida biyu sbd tsananin ciwon da yake mata, ta rufe idanu sosai sbd komai bibbiyu take ganinsa a cikin idanun nata. Uncle Isma'il ya zuba mata ido cike da tausayinta yasan duk abin da zai sanya Majeederh cikin wannan yanayin ba abu ne mai sauƙi ba. Ya dubi Little dake tsaye ya ɗora kansa a bayanta ya saƙalo wuyanta tare da yin lamo, yanayin Mamin tasa ya taɓa kuzarin yaron. Ya nemi waje ya zauna saman kujerar dake ɗakin na Innati, cikin kulawa ya ce
"Hawwa'u!" Ta yi sauri ta ɗago kanta tare da ƙaƙaro murmushi ta ɗorawa fuskarta matsayin dole. Cikin sanyin murya kamar kullum ta ce "Ina yini Uncle?" Ya ce
"Lafiya" ya yi jim kafin ya ɗora da "Ke kika firgita mini uwata ko?" Ta ƙara yin murmushi kamar ba za ta yi magana ba ta ce
"Da Aljana take haɗani fa" Ya yi murmushi ya ce "Dole ta haɗaki da Aljanu, ni kai na mamakin kyan da Ubangiji ya yi wa ƴata nake, sai yanzu nake ƙara ganin cancantar suturta fuskar da kike"
"To ALLAH ya isa, Allah ya isa shi kaɗai zai isar mini idan ka yafe Allah ya tsine" Innati dake bakin ƙofa tana leƙowa ta furta hakan lokacin data tabbatar Jikarta ce Majeederh Abdul'aziz Khan! "Ki yi haƙuri Innati"
Innati ta fashe da kuka sosai tana face hanci ta ce "Wallahi ba dani kike ba, ba kuma ni ki kaiwa ba, Ubanki mai faɗin ran nan da manyan Idanu Audil azizu shi kika tsoratar" Majeederh dai bata kulata ba, domin tunaninta baya wajan gabaɗaya zuciyarta tana wani birgire wanda kullum take ganin kanta acan, a cikin mafarkanta na kullum.
"Majeederh wa kika bari a waje? Na ga mota" Uncle Isma'il ya faɗi hakan cike da zumuɗin jin Majeederh ta ce wani ne ya kawota, addu'a yake Allah ya sa nata rabon auren ne ya zo.
"Latifa Omar ce"
"Ayya to, Allah ya amfana" Ya gyara zama sosai ya ce "Hawwa'u ki faɗa mini gaskiya, mene hujjarki na barwa Rumana saurayin dake son ki yake son aurenki a lokacin baya, sai yanzu kwatsam! Reshe zai juye da mujiya wai kin fasa auren shi ya auri ƙanwarki Rumana anya akwai ƙamshin gaskiya? Domin na lura da rashin nutsuwarki, A can gidan" Ta yi shiru domin bata da amsar tambayar Uncle ɗin nata, ita yanzu a yadda take ji ko sa'an mahaifinta Abbu aka bata matsayin miji da gudu zata amsa, koda ha za ta yi farin ciki ba da zama da shi muddin zai ɗauke buƙatar ta, wacce ke damunta take sanyata rama da ibadar dole.
"Ina jinki, kin fi ganewa ki zauna duka ƴan-wanki su yi aure ke kina gida? Kin fi ganewa ki gansu da mazajansu gwanin sha'awa suna yin soyayya da rayuwar aure mai tsafta? Su haifi ƴaƴa wanda ko wanne mai rai yake muradi, inma namiji inma mace? Zuciyarki ta yi rayuwarki adalci? Anya Hawwa'u-Jidderh?"
"Ka yi haƙuri Uncle, Idan da rabo zan yi auren"
Maganarta ta narkar da zuciyar Uncle Isma'il, kalamanta sun nuna karaya zahirin fuskarta kuma ta amshi ƙaddarar tare da godewa Allah bisa tarin Ni'imar da ya yi mata, tasan yana sane da ita bawai barinta ya yi ba. "Shikenan, ALLAH ya yi miki Albarka ki je wajan Luba" caraf Innati ta ce "Wacce masifar ce Luba? Ka fita daka idanuna Isma'ila matar taka da ban gama sanin zuciyarta ba ita zaka turawa Kululu? Ƴar Gombe? Wato ta tsaface ta bayan kasan yadda Fulanin Gombe suke?"
"Allah ya baki haƙuri Innati, zan shige taron da ake yau babu mamaki na samu dacewa da aiki mai kyau" "A to! Ya dai fi maka, kamar tsiya akan ƴaƴana ta kare kowa fama yake da kansa da azababben talauci, In sha Allah tsalelen miji Kululu zata aura na tarkata na koma gidanta" Murmushi kawai Uncle Isma'il ya yi tare da shafa kan Little ya ce "Yau ba magana?"
"Mami kakewa faɗa"
"To ɗan Maminta Allah ya baku haƙuri kai da Mamin" Yana fita Innati ta yi ƙasa da murya ta ce
"Munafuki, ai duk tsinewa matarsa da nake to ta shi nake, daga shi har Ubanki Audil azizu sai na kai su hisba uban kowa ya huta, turmin atamfar ankon wannan yarinyar Wifat fa na ce ya siya mini wai bashi da shi?" Ta ƙara girgiza kai ta ce "Hoo! Ƙasa Ubangiji ya baki miji mai kuɗi wanda zai so ki"
Majeederh ta marairaice fuska sosai ta ce "Innati bar maganar auren nan"
Innati ta riƙe haɓa ta ce
"To ba zan bari ba, Annamimiyya ina nan watarana idan ban mutu ba sai mijinki ya sunkuya ya miki doki-doki dake da yaran da zaki haifa, wallahi ko bana raye sai kin tuna wannan maganar tawa, zaki haifi zuri'a mai yawa zuri'ar da babu Uban wanda ya taɓa haifarta a cikin ƴan-uwanki da iyayen naki" Majeederh ta lumshe idanunta a zuciyarta tana tona tsayin shekarun da zata ɗauka kafin tabbatuwar hakan! Innati ta fashe da kuka ta ce "Allah ba zai barki haka ba, wallahi halin Uwarki Fulani kika ɗauka, har tsinannen kyan da kike da shi duk nata ne, ki rubuta ki ajjiye watarana sai labari ni dai ki sani ina son ki ba zan baki gurguwar shawara ba, amma dai Allah ya yi ɗaiɗai da zuciyar Rumana" Surutun Innati ya hau wa Little ka, daman ba daɗi yake ji ba ta shagwaɓe fuska tare da fashewa da kuka ya faɗa jikin Majeederh ya ƙanƙameta "Mami gida"
Majeederh ta yi saurin rungume shi tana shafa kansa yau ɗin gabaɗaya ta rasa meke damunsa ga kanshi zafi kamar mai zazzaɓi. "Innati kin firgita mini yaro" Innati ta riƙe baki ta kasa cewa komai sai can ta ce "Ba zan ce komai akan yaron nan ba, amma dai a guji gobensa akwai abubuwan Al'ajabi cikinta" Majeederh ta ɗauke ɗan ta tare da rungume shi sosai a ƙirjinta tana ji yana sauke numfashi ya ƙanƙameta.
Latifa Omar ta yi murmushi mai kyau tare da kallon Aliyu ta ce
"Kana da abin dariya"
Aliyu Sufyan Alhassan ya ce "Uhm Latifa Ina son ki, bana son a ɗauki lokaci ki bani dama"
"Daka ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi?" Ya yi murmushi kawai kana ya ce "Bani labari"
"Na me? Akan wa?" Latifa Omar ta tambaya. Ya ce "Your friend"
Ya nuna ƙofar gidan da Majeederh ta shiga. Latifa ta juya idanunta ta ce "Oh, Sunanta Majeederh Abdul'aziz Khan! Iyayenta suna yawan ce mata Hawwa'u, ƙannenta musamman Aaliyyah tana ce mata Jeederh. Mun yi makarantar primary lokacin ɗaya, amma ta fini ƙoƙari ne sa ba kusa ba, da yawan lokaci ina hana kai na bacci ganin na zama ita, sai na fahimci iliminta baiwa ce, daga Allah. Biye ɗaya takewa ayar Alkur'ani ta hadda ce ta, tun muna primary ta rasa mahaifiyarta, she left her, at the same time ta yi saukar Alkur'ani, ni kuma na maimaita aji, a lokacin da ta zama hafiza a lokacin na yi sauka ta farko" Ta yi jim,tana rayuwa da step mother ɗin ta, kishiyar babbar ta, ilimin Majeederh ya sa Manyan mutane na primary school ɗin mu suka shige mata gaba wajan samun scholarship a matakin secondary school, ta samu makaranta mai kyau tun a lokacin Karatun ta a ɓangaren Islamic yake, yanzu maganar da nake maka ranar Candy ranar ta zama Gwarzuwa a ɓangaren musabaƙar Alkur'ani, wannan shi ne kashi na wajan uku na dai manta Makarantarmu Ahlul Madar tana bada sunanta matsayin wacce zata jagoracemu, yanzu haka sunanta yaje ko'ina duk wata gasar karatun Alkur'ani indai Kano zamu shiga to ita za ta yi" Ta ja aya tana sauke numfashi. Tunda ta farar maganar idanun Aliyu a rufe yake ruf ta ce
"Lafiya?" A taushashe ya ce "Ina jinki"
"Majeederh ta zama malama a Ahlul Madar duk wata suna bata albashi, da albashin take kula da yaron daka gani a wajanta" Ya ware idanu da mmki ya ce
"Yaro? I heard you kin ce single take, not house wife" ta ce "Eh, Tsintar yaron ta yi, kuma tana son sosai banda kada na yi maka ƙarya bayan iyayenta babu wanda take so kamar Little, tana iya haƙura da cikinta ta bashi ya ci, kuɗin Makaranta, kayan sawa duk da albashinta take masa, kuma a ciki take taimakon Abbu da abincin gida, by the way yanzu tana shirin tafiya ƙasar waje Africa, ta samu scholarship za ta ɗora University ɗin ta a can ɓangaren Islamic and Arabic studies"
Ta yi shiru ganin kamar Attention ɗin Aliyu baya kanta ta ce "Ya dai?"
"Wacce ƙasa?" Ya faɗa yana murmushinsa mai kyau da aji. "Misira"
"Ok Egypt, Allah ya taimaka" Latifa Omar ta ce "Amin".
A can cikin gida Hajiya Luba ta kalli Majeederh ta ce "Yanzu karatun zaki?" Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya a fili tare da jinjina kanta alamar "Eh, Mama"
"To Ubangiji ya sa rabokin ke kiranki, Allah ya baki ikon cinye ƙaddarorinki mutane ne kawai da basu son zama lafiya gabaɗaya nawa kike balle ƴan-uwanki shekaru Ashirin bai ci har a fara gorantawa mutum bai aure ba"...
“...... Allah ya kyauta”
Ta ci-gaba da bata haƙuri da ban mamaki. Har Latifa Omar ta shigo suka ta fi gidan Yaya Bilkisu domin acan ake Sabgogin bikin Widad ɗin. Ko! Da ta je bata iya zama ba ƴan matan familyn Khan, suka shiga sauke magana. Kusan duk akan Idanunta aka haife su sbd rashin aure ya sa girmanta ya zube. Tana zaune kiran gaggawa ta sameta zuwa Orphanage for young children, kira ne daga kai tsaye daga Akeeth. Yaya Bilkisu ta bata kuɗin napep daman tuni ta ce Latifa Omar ta tafi kawai. Tana gab da zuwa ta sake kiranta.
"Assalamu alaika"
Majeederh ta furta cikin muryarta mai sanyi daɗi a kullum. Akeeth ya amsa ya ce "Am sorry Majeederh,na samu meeting na gaggawa idan na gama ko kiranki ne zan yi" Jikinta san yi ƙalou ta kashe wayar ba tare data ko amsa masa ba.
Unguwar Darmanawa
Idanunsa rufe yake kallon selling ɗin dake cikin bedroom ɗinsa, lokaci na farko a rayuwa da ya yi nauyin baki wajan furta abin da yake so. Ya juya kaɗan yana sake mirginawa hoton idanunta kawai suke gilmawa cikin nasa idon, ganin abin bazai goge ba sai ma ƙaruwa da yake ya sa a hankali ya miƙe ya shiga bathroom tare da sakarwa kansa shower yana riƙe ƙugunsa bugun zuciyarsa na ƙaruwa gabaɗaya Latifa Omar ba tsarin aurensa ba ce, me ya kai shi? “Density” Shi kansa bai adadin lokacin daya ɗauka a bathroom ɗin ba, sai da ya ji ana knocking ƙofar part ɗin shi ya fito ɗaure da towel a jikinsa.
"Meke damun ɗan autan Hajia yau da bai yi dinner damu ba?" Aliyu ya shagwaɓe fuska sosai autar ta motsa daman rauninsa da wuri yake fallasa asirin zuciyarsa. Ya ja baya yana zama kan kujerar dake kusa da gadon shi, ɗan ƙasar Turkiya. "Hajia"
"Na'am Autan Hajia" Hajia ta amsa tana jiran ta ji dame yau kuma ya zo, domin shi Aliyu baya rabo da issues sbd tsabar taɓara gashi kyakkyawan ajin farko sai ka ɗauka Half-caste ne. Looking so classic. "Aure zan yi, na samu mata" Ya faɗi hakan domin a tunaninsa shi ne mafita ga abin da yake ji, wacce zai aura daban, wacce ta yi zuciyarsa kamo daban. Ko mene hakan hakan? Only God knows.
Sosai Abbu ya yi wa Majeederh faɗa don me bata ƙarasa ta karɓo form ɗin ba? Ita dai bata ce komai ba ita kaɗai ta san abin da take ji. Yau ɗin ma sai da ta yiwa Little wanka ta sanya masa kaya masu ɗan sauƙi bata son ya kwana da zazzaɓi. Ta tsora masa idanu a hankali ta ce "Little zaka manta dani?" "Me?" Ta tambaya domin bai fahimta ba.
Ta ce "Idan na ta fi karatu, karka manta dani ka ji? Kada ka bawa wata matsayin uwa a zuciyarka idan ba Maminka ta gasky ba, ka da ka ci amana" Ita kaɗai take magana ita kaɗai kuma take fahimtar me take cewa. Ya shafa laɓɓanta da suke jajir ya ce "Mami ni ma irin naki"
Ta yi murmushi tana ɗaukar shi tare ta ɗora a cinyarta ta ce "Until you grow up" Ya shiga buga ƙafa da yarfe hannu shi a dole sai laɓɓansa sun yi irin na Maminsa Jee ta tura masa baki ta ce
"Ok Shafi kaɗan, da safe sai koma red" Ya yi murmushi yana tsalle ya ɗora bakinsa a nata ya shiga goga sai ta gaji ta ɗauke shi tana dungure masa kai, ƙara wayarta ta yi tana duba taga albashi akai mata sosai ta ti farin ciki gobe za ta yi masa siyayya. Tunanin yadda zata rabo da Little tsayin shekaru takwas shi ne ya bijiro mata, rabon da ta yi kuka ta manta sbd kansa cewar ta mace jaruma da zurfin ciki. Ta samu kanta da rungume Little ta fashe da kuka sosai, kukan da rabon da ta yi shi tun rasuwar Fulani. Wani irin kuka take da dukkan ƙarfinta wanda yake tasowa tun daga ƙasan zuciyarta. Ganin tana kuka ya sa Little fashewa da kuka sosai. Da ƙyar ta rarrashe shi suka kwanta bacci. Kiran sallarsa farko ya farkar da Majeederh daga bacci a hankali ta shafa tana son taɓa jikinsa ta ji ko da zafi. Wayam! Ta buɗe idanu taga babu Little a kan gadon ta miƙe da sauri idanunta ya sauka akan ƙofar ɗakinta dake buɗe bayan har rufewa ta yi. Da sauri ta ce "My Son, Little?....
Paid book
MIJIN MALAMA
0811923761621
Sosai Majeederh ke kuka kamar ranta zai fita har da shassheƙa Mami dake tsaye ta riƙe haɓa ta dubi Majeederh ta ce "Yanzu ke kina Ina yaron ya zare sakata ya yi nasa waje" Ta kasa cewa komai sai kuka gabaɗaya hankalinta ya ta shi ta zama kamar ƙaramar yarinya. Mami ta ƙara tafa hannu ta ce "Yaro ne mai shegen karambanin tsiya, ko gidan uwar wa ya sani wanne hannu zai faɗa ohho, ga yadda ƴan mafiya da ƴan kidnaping su ka yi yawa a gari" Majeederh ta ƙara rushewa da kuka ta ce "Little ba zai taɓa buɗe ƙofa ya fita ba, ina yaga tsayin?" Aaliyyah ta ce
"Kuma ko ya iya buɗe Ƙofar ɗakin ki Anti Jeederh ai ba zai iya buɗe ƙofar waje ba" Abbu wanda ya fito da shirin fita Masallaci ya gyara muryar kowa ya shiga hankalinsa kamar sun ga mala'ika ya dube su ɗaya bayan ɗaya kafin ya ce "Lafiya?" Ruma ce ta ce "Abbu wai Little ne ba a gani ba" Ya yi jim alamar tunani kana ya kalli Majeederh dake fuskarta ta yi jajur a cikin wutar lantarkin dake gidan. "Hawwa'u garin ya ya?" Jikinta na rawa ta ce "Abbu wallahi ban sani ba, tare muka kwanta sai da ya yi bacci na yi, yanzu na farka nayi raka'atul fjr na ga babu shi" Ta goge hawayen fuskarta wasu na sake zubuwa ta ce "Na rufe ƙofa, amma na ganta a buɗe" Ya dubeta sosai yana nufar waje ya ce "Allah ya bayyana shi, akwai ban mmki? Wani ya shigo? Wani ya buɗe masa ƙofar? Ko fita ya yi da kansa?" Ruma ta ɗaga kafaɗa tare da shigewa ɗakin da suke kwana su uku, ita, Raihana, Aaliyyah. "Abbu zan je duba shi?" Da sauri ya ce
"Ina?" Kanta a ƙasa tana shassheƙa ta ce "Waje, maybe yana waje ko police please Abbu"
“.... Bada yawona ba”
Cewar Abbu. Ta marairaice fuska ta ce "Ka tausaya mini, bashi da kowa" Cikin tsawa ya ce "Ki fita daga idanuna Hawwa'u, ke bakya tausayin kan ki sai yaron da baki san waye ba? Kin san wanne kallo ake miki a unguwa? Wasu tunaninsu ɗanki ne kawai kike ɓoyewa, to wahainiyarki ta kiyaye ramata, nan da waje kika fita dalilin neman yaron nan ban yafe ba, ina akan shi kika ƙi zuwa karɓo form wato kin girma kin manta wahalar dana sha akan ki, har ki ka yi growing zuwa yanzu? Idan kika je Misira yanzu kin san irin matsayin da zaki taka? Ni za Hawwa'u ni mahaifinki?" Ya ƙare maganar yana nuna kansa da yardarshi. Majeederh ta zube gaban Abbu akan gwiwoyinta hawayenta ya tsaya zuciyarta ta yi mata nauyi sosai ta kasa tantance wanne kalar yanayi take ciki. Ta riƙe ƙafafuwan Abbu ta ce"Na tuba Abbu, na tuba na bi Allah na bika Mahaifina ka yafe mini zan zama yadda ka ke so, zan yi karatu zan je matakin da kake buƙata ka yafe mini Abbu don Allah?" Aaliyyah kukan tausayin yayarta Majeederh ya kamata ta durƙoshe a wajan tana kuka sosai. Abbu ya ɗan sassauta murya ya ce "Ki je anjima zan kira ki, amma ki cire maganar yaron nan a ranki" A karon farko a iyakacin rayuwarta da za ta yi wa Abbu magiya ta ce "Abbu please... Little.,"
"This is noises!"
"Ka yi haƙuri" Jikinta duk rawa yake kamar ba babbar ƴar daya haifa ba ta yi cikin ɗakinta. Sosai Raihana ta ji tausayin Anti Jeederh amma babu yadda ta iya, ta ja bakinta ta yi shiru. Mami ma ɗakinta ta yi tana ɗaukan hijabi domin daman da alwala a tare da ita. Aaliyah ta miƙe bayan ta ci kuka ta ƙoshi sosai ta nifi ɗakin Majeederh. A zaune ta sameta bakin gado ta sanya hannunta a tsakanin cinyoyinta tana kaɗawa a hankali kanta sunkuye. Jiki ba ƙwari cikin muryar kuka sosai Aaliyyah ta ce "Anti Jeederh mene haka? Me yake shirin faruwa? Me ya sa sai ke kawai?Anya Abbu shi ne Ubanmu? Wannan abun it's too much, this is not fair zuciyata ta fara raya mini bashi ne Ubanmu ba ko Uncle.....," Kau! Majeederh ta ɗauke Aaliyyah da wani kyakkyawan mari har sai da ta yi baya daga tsugunen take. Ta fashe da kuka sosai ta ce "Anti Jeederh ki dakeni son ranki, beat me amma ba zai iya sauya tunanin da zuciyata ta fara wanzar mini da shi ba, na buɗe idanu da soyayyar da kike mini Anti Jeederh, na fahimci kece madadin uwa a gareni ko da baki shaida mini Mami ba ita ta haifemu ba, Innati ta faɗa mini komai, amma kullum kina nuna mini hanzar tsira hanzar da zan kare kai na a matsayina na ɗiya mace, na tashi naga yadda Abbu ke son ki ya fifita ki da kowa, komai Hawwa'u musamman ɓangaren karatu, Anti Jeederh baki da lokacin kan ki kullum karatu kullum karatu, mene nufin Abbu? Imran ya zo neman aurenki ya ce ba aure zai miki yanzu ba, ya yi masa korar kare, yanzu kuma ya amshi kuɗin auren Ruma bayan kece babba kece ya kamata ki fara yin aure kafin ita..." Kuka ya ci ƙarfin Aaliyyah ta ce "Soyayyar kenan? Za a ci karatu ne? Idan bai barki kin yi aure ba yanzu sai yaushe, Anti Jeederh tun kina jss 3 na ji kina faɗawa Yaya Latifa aure kike so, idan ya tilasta miki yin karatu ya hanaki aure shin ya miki adalci? Mufa ƴa ƴa ajjiye ce, amana ce a wajan iyayenmu za a tambaye su yadda suka kula damu, Malaminmu ya faɗa mini duk ɗiya macen da ta ce ayi mata aure bata son karatu mafi alheri shi ne a aurar da ita, domin ita tasan me take ji,mene ya sanya ta ce tana son auren, idan ba a aurar da ita ba komai yana iya faruwa da ita kuma...." Majeederh ta yi saurin toshe bakin Aaliyyah tare da rungume yarinyar a jikinta ta ce "Enough, enough is a enough, ok"
Kukan zuci take wanda ya fi komai cin rai da sanya damuwa da ciwo a zuciya, bata son hawayenta ya zuba gudun ƙarawa Aaliyyah nata kukan da damuwa. Sun jima a haka tana jin Aaliyyah na kuka tana bubbuga bayanta a hankali har ta fara sauke ajjiyar zuciya kafin ta ɗagota tana riƙe fuskarta murmushin dole bayyane a fuskarta ta ce "Stop crying my dear, hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar, Abbu yana so na, soyayya ce ta sanya ya yi haka, kuma yana da iko kaina, yana ganin kuma karatu ya dace dani ba aure ba, shi ne mahaifinmu our own father, biological father ok ba a taɓa sauya tuwo suna, kuma idan na yi karatu zan samu aiki Abbu zai ji daɗi i most be proud, zai alfahari da ni, zan gyara mana gida, na siya masa mota, na kaisa Makka na buɗe masa wajan aiki ya fita daga halin talaucin da yake ciki" Da sauri Aaliyyah ta ce "Aure fa?"
"Zan yi, idan da rabo" Ganin zata sake magana Majeederh ta haɗe fuska sosai ta ce "Je sallah, kiyiwa Fulani addu'ar samun rahama a kabarinta, kiyiwa Abbu addu'a da su Ruma da Mami" Ta ce "Anti Jeederh ke ma zan miki addu'ar Allah ya kawo miki mijin aure ko gobe ne" Majeederh bata ce komai ba, a ranta tana jin cewa karatu zata aura shine zai zame mata miji da zuri'a. Bayan fitar Aaliyyah kuka taci ta ƙoshi son ranta, kukan ya dace da ita ƙilan hakan zai sanyaya mata zuciyarta daga yadda take ji, idan ta tuna babu Little bata san kuma inda zata same shi ba, bata san wanne hannu zai faɗa ba zai samu kula ko ba zai samu ba sai zuciyarta ta karaya damuwarta ta ƙaro fiye da ko yaushe. Ga Abbu ya yi mata katangar ƙarfe tsakaninta da nemo Little ɗinta. Tunaninta ya tsaya ta rasa me za ta yi, rashin Little tamkar rasa wani gefe ne na rayuwarta. Ganin lokaci na tafiya ya sa ta miƙe tare da shiga banɗaki yau ko wankan da take da asuba domin kiyaye jikinta daga mafarkan da take yi bata samu zarafin yi ba, ta ɗaura alwala tare da shimfiɗa ladduma ta yi sallah raka'a biyu. Ta jima tana addu'a akan Allah ya dawo mata da Little ɗinta abin sonta, abin wasanta, abin hirarta, me ɗauke mata kewa. Ta yi shiru na rashin abin yi har ƙarfe 7 tana zaune kanta ƙasa sai wajan 7:48 bacci ɓaraho ya ɗauketa.
Misalin 11 na safe Hajia dake zaune cikin haɗaɗɗen parlourn gidanta ta yi ado cikin atamfa mai kyau da ɗaukan Idanu (Valisco) fara ce kamar buzayen Niger. Ta dubi agogo dake parlourn ganin lokacin na tafiya ya sanya ta ɗauki wayarta tana ƙoƙarin kiran Aliyu taga Almustapha ya fito, ta ajjiye wayar idanunta akansa tare da duban bayansa har ya iso ya zauna dab da ita ya ce "Good mrng Hajia" Ta dube shi kafin ta ce "Mrng, Zaki fa?" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Tun sallar Subhi rabona da shi" Ta yi shiru "Bai fito bane?" Almustapha ya faɗa yana miƙewa, Hajia ta ce
"Jeka kawo mini Yarona"
"Ya zama dole ai" Tsakanin part ɗin Musty dana zaki ba nisa suna opposite da juna ko wanne ha haɗu kasancewar su masu rufin asiri sosai. Komai na part ɗin zaki light blue ne, looking so Masha Allah. Furniture's ɗin ƴan Turkiyya sbd yadda suke ɗaukan Idanu. Ganin ƙofar shiga cikin bedroom ɗin a buɗe bayan ta parlournsa dake buɗe ya tura kai ciki, ƙamshin room air-freshener, a hankali Musty ya shiga hannunsa ɗaya yana gyara hular kansa yana faɗin "Autan Hajia bacci har yanzu? U have to wake up" Jin shiru ya sa Musty ƙarasawa har bakin bed ɗin da Zaki ke kwance ya lulluɓe jikinsa bakiɗaya idanunsa rufe numfashinsa na sauka a hankali. Da mamaki Musty ya ce "Zufa?"
Ya duba yaga A.cn ɗakin na working domin har yawa taso yi, ya ɗan bubbuga pillown da kansa yake kai. Slowly a hankali Aliyu-haydar ya shiga buɗe idanunsa wanda su ka yi masa nauyi, ganin sauyin idanun Zakin Hajia musamman da yake cikakken Baushi Nigerian, ya bawa Musty tsoro. Suka kalli juna ya ce "Lafiya kake?"
"In capital letters, FINE"
Aliyu-haydar ya faɗa yana janye jikinsa daga bed ɗin kansa ya yi masa nauyi sbd rashin bacci na kwana biyu, hakan ma jiya ta kasance masa sai daya dawo daga masallaci bacci ya ɗauke shi. Musty ya bisa da kallo musamman yadda yake tafiya kamar bai so sai kawai ya girgiza kansa ya shiga danna waya. Yana zaune har Aliyu ya fito ɗaure da towel cikin sauri ya shirya cikin wani carton ɗin Yadi mai kyau da taushi wando da half ɗin riga sai hannun rigar half dark blue ya haska farar fatarshi. Bai saka hula ba sai sunglasses daya saka ko gyara sumar shi bai ba. Ya nufi waje kai tsaye, Musty ya miƙe yana mita "Ji wulaƙanci na gama gadinka har ka shirya shi ne zaka fita?"
"Waya kake dannawa fa Yaya?" Suna fitowa a jere Hajia ta miƙe tsaye a daidai lokacin Papa ya fito cikin shirin fita office. Ya dubi samarin yaran nashi a tare suka ce
"Mrng Papa"
"Babana, Almustapha, kun makara yau" Almustapha ya ce "Yanzu zan fita" Papa ya juya ga Aliyu-haydar ya ce "Kai fa?" Ya ɓata fuska ya ce "Ina gida" Da mamaki Papa ya ce "Gida? Daga fara aikin?" Nan da nan Aliyu ya nuna Autansa a fili ya marairaice fuska tare da langwaɓewa, Papa murmushi kawai ya yi ya ce "Hajia bari na fita" Hajia ganin yadda idanun yaran nata ya sauka akanta suna jiran su ji me zata ce, ta girgiza ƙafa kawai ta ce "Allah ya tsare ya kiyaye" Papa ya yi jim kamar na jiran wani abu sai kuma ya ce "Amin" A tare suka fice shi da Almustapha kowa ya shiga mota, Almustapha na driving kansa, Papa kuma yana baya Busy reading news paper driver na jansa a haka suka fice. Hajia ta dubi Aliyu ta ce "Auta sai yanzu?" Ya rufe idanu ya ce "Just woke up Hajia"
"Ka yi breakfast?" Ya girgiza kai kawai tare da miƙewa tsaye ya ce "Ki mini addu'a zan fita yanzu zan dawo" Tana lura da yadda yake yawan lumshe idanunsa yana riƙe kai ta ce "Allah ya tsare" Hannunsa ɗaya zube cikin Aljihu ɗaya riƙe da key ya nufi harabar gidan, motarshi ya shiga yana yi mata key while yana kiran number Latifa Omar. Majeederh na zaune idanunta ya yi zururu sun faɗa fuskar nan jajur karan hancinta ya yi jaa sosai sbd damuwa. Da ƙyar ta cira kai ta kalli Latifa Omar ta ce "To ya zan yi? Mahaifina ne, na haƙura da Little" Latifa Omar ta ce "haka zaki zauna Takaicin Uba na cin zuciyar ki?" Kallon da Majeederh ta yiwa Latifa Omar ya sa ta fahimci bata ji daɗin maganar ba ta ce "Ki yi haƙuri, yanzu kina nufin bakya nan zan yi aure?" Kamar ba za ta yi magana ba ta ce "Aure zaki?" Latifa ta yi dry tana gyara zama ta ce "Aure zan yi In sha Allah, ina wannan wanda ya kaimu gidan Uncle Isma'il da Yaya Bilkisu? To shi ne ya ce yana so na, na ji tsoro ganin shi ne wani ne masu arziƙi kuma ni gani ƴar gidan Malam Shehu, amma ya ce babu komai iyayensa basu da matsala yana da kyawawan hali" Ba zata iya gane yanayin reaction na Majeederh ba kanta a ƙasa yake. "Majeederh kina ji na?" Ta ce "Allah ya sanya albarka" Kafin Latifa Omar ta yi magana wayarta ta fara ƙara ganin wanda yake kira yasa tafiya murmushi hannunta na rawa ta ɗauka ta ce "Hello"
"Is not allowing, Assalamu alaiki" Majeederh ta miƙe zuwa ɗakin Abbu cikin ƙaton hijabi har ƙasa kana kallonta kasan a hargitse take. Ta yi sallama yana zaune hannunsa riƙe da wani file na takardun Majeederh ya ce "Hawwa'u kin fito? Yanzu zan office ɗin zaki?" Ta ɗaga masa kai ya ce "To ya za ayi? Bani da kuɗin mota" A sanyaye ta ce "Ina da shi" Ya miƙa mata file ɗin yana murmushi na nuna jin daɗi ya ce "Allah ya yi miki Albarka, Kinga kina zuwa Misira Shekaru takwas kin gama karatunki, idan da hali kawai ki yi zamanki a can ki fara aiki ance albashinsu akwai auki sosai" Ba zata iya tantance halin da maganar Abbu ya sanya zuciyarta a yanzu ba, kuma ta yi alƙawarin ba zata sake masa ƙorafi ba. Ta miƙe taiwa masa sai ta dawo taiwa Mami ma, Aaliyyah da su Ruma na makaranta. A hankali ta nufi waje kanta a ƙasa ga yunwa domin kafin ta farka har an cinye abinci abincin safen, jiri na ɗaukarta a haka ta yi waje ganin mota a ƙofar gidansu ya sanya ta ɗaga kanta cikin rashin sa a Idanunta ya faɗa cikin nasa suka kafe juna da wani irin kallo....
MIJIN MALAMA
PAID BOOK
0811923761622
Mutumin dake zaune cikin motarshi ya zame idanunsa daga cikin nata a hankali ya rufe Ido yana jin abin da Latifa Omar ke faɗa. "You surprised me, Aliyu" Yana jinta dai bai ce komai ba, Latifa Omar ta ƙara cewa "Zuwan bazata har haka? Bayan am not in a dreams, kuma ba dare ba balle na ce?" Aliyu ya buɗe idanunsa cikin gajiyawa a gajarce ya ce "To ya na iya? My heart beating so faster" murya bata fita sosai ya ƙare maganar. Ganin Majeederh na ƙoƙarin shige su bayan daman tare za su fita ɗin ya sa ta ce "2 minutes please" Fita tayi da sauri harta isa ga Majeederh tana riƙe hannunta ta ce "Me kike ƙoƙarin yi? Bayan kinsan ke nake jira kada ki bari ƙwaƙwalwarki ta daina aiki ko ta samu matsala sbd tuna-ne-tuna-ne" Kallonta kawai Majeederh ta yi ba tare da ta ce komai ba. "Kizo muje, ya ce hanyar B.u.k ɗin zai yi shi ma" Yadda Majeederh ke kallon Latifa Omar yasa ta fahimci kusan dalilin kallo. Murmushi ta yi ta ce "Uhm I knw ur problem Majeederh, kina tsoran what those few people are going to say, right? Ai na faɗawa Baba ko waye kuma Abbu ma ya sani you can ask idan baki yarda ba, kawai if you trust me you have to believe" Majeederh da fararen Idanunta wanda suka kuɗe kawai ake gani,ta juya su a taushashe ta ce "Ke macace, ita mace sirri ce, sirrinki tsaraicinki ne, ki riƙe shi kamar tazugenki" Latifa Omar ta saka dariya mgn ɗaya kawai Majeederh za ta yi mai cike da ma'ana da azanci ta ce "Ok zan riƙe da hannu bibbiyu, Majeederh sbd ke na ce zai kaimu, nasan Abbu bai baki kuɗin mota ba, kuma is like compulsory to you na zuwa karɓo form ɗin, ki yarda dani in sha Allah nothing will happen as you think" Kafin Majeed ta yi magana ta yi gaba abinta hakanne kawai zai saka ta taho. Ta cikin madubin motar yake ƙare mata kallo har ta buɗe ta shiga sai a lokacin nauyin da zuciyarsa ke masa tun daren jiya ya saki, ciwon kan ya yi nasa waje. A ransa yake mamakin yadda ko kwalli bata sakawa cikin Idanunta. Key ya yi tare da yin reverse kana ya ɗauki hanyar da zata kaisa B.u.k new side.... Sun yi nisa sosai babu abin da ke tashi sai maganar Latifa Omar, Aliyu ya ɗan ya tsuna fuska yana tunanin yadda abu kamar wasa yake neman zamar mishi gaske, ya ce yana son Latifa Omar amma baya jin aurenta a ran shi duk da furta a baki, ya rufe idanu ya buɗe saman kwalta his heart disappointed him. Ya kasa daurewa ya ce "Na zama drivern kurma" Latifa ta ce "Kurma? Yana driver idanunsa rabi da rabi akan madubi ya ce "Ur friend, Jiddatul-khairy" Latifa ta buɗe ido kana ta juya ta ce "Malamarmu, Malama Majeederh mijin da zan aura ba sai anja masa aji? Ba gaisuwa" Aliyu-haydar ya ce "Hakan kuma ba halin Malaman ƙwarai bane" Duk tana jin su sai da suka gama surutu da wajan minti biyu suka ji ta ce "I don't want interfere" Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke lokacin muryarta ta sauka cikin kunnenshi, ba zai iya cewa ko ranar daya fara ganinta ya ji muryarta ba, sbd baya cikin nutsuwarsa ji yake kamar new Aliyu akai a lokacin ba shi Aliyun ba, sai ya ji kamar bai taɓa jin murya irin haka ba in his whole life, sanyi, nutsuwa, haƙuri da kamalarta duk ta bayyana cikin maganar da tayi ta kalmomin da baza su gaza biyar ba. Suna zuwa cikin B.u.k ɗin Majeederh ta fita babu jimawa ta dawo lokaci Aliyu na zaune hannunsa riƙe da Swn water yana sha ganin yadda ta yi tsaye ta kasa knocking Glasses ɗin motar yasa gently ya saka hannu ya fito daga cikin motar yana zuba hannu a aljihu tare da juyawa ya dinga ganin Students different department suna ta zirga-zirga. Ya kalli Majeederh ya ce "Jiddatul-khairy, you are too..." Da sauri ta ɗaga kanta a tunaninta ko yau Allah zai sanya wani namijin ya ce tana da kyau, saɓanin Uncle Isma'il da yake cewa tana da kyau da kuma ƴan-uwanta mata sai ta ji ya yi shiru ya ce "Kin gama ne?" Ta girgiza kai tana addu'a a zuciyarta Aliyu yana son ya ƙara jin muryarta ya ce "Mene ya faru? Me bada form ɗin ne baya nan ko?" Har ranta ta gaji da magana ga yunwa sosai take ji ga kewar Little da rashin sanin inda yake ta marairaice kamar za ta yi kuka sosai ta ce "Uhm ba nan bane" Aliyu ya ware ido hadda riƙe ƙugu ya ce "Oh ni Haydar sai aka ce ina?" Batai magana ba har Latifa ta fito daga cikin motar ta ce "Meke faruwa nan?" Aliyu ya yi mata shiru Majeederh ta ɗauke kai can ta ce "Murtala way" Murmushi kawai Aliyu ya yi ya ce "Oh Kano state ministry of education, i think Government office?" Ya faɗa yana duban Majeederh "To yanzu can zamu kenan? Domin idan muka koma gida ba wannan form ɗin mun shiga uku wajan Abbu kwana zai yi yana faɗa" Aliyu ya ce "Waye?" Kai tsaye Latifa Omar ta ce "Her father" Sosai ran Majeederh ya ɓaci Latifa na son nunawa Aliyu Mahaifinta masifaffe ne ko yana takura musu ta ɓata fuska duk da ba'a ganin yanayin nata. Cikin Aljihu ya saka hannunsa ya ji ba kuɗi ya juya yaga babu wani pos a kusa da su, babu cash da sauri ya juya mota tuna cewa kamar ya bar kuɗi ciki jiya daya siyi Popcorn 2k ne ya miƙawa Latifa ya ce "For transport, ku yi amfani da shi wajan napep ina da shari'a 1:00" Latifa ta ce "Ok bye" Ya girgiza kai kawai jin ko godiya babu bawai kuma damuwa da hakan ya yi ba, Majeederh ya san ba za ta yi magana ba.....
Sun jima cikin haɗaɗɗen office ɗin na commissioner for education ɗin, kafin a hankali su ji an shigo duk suka miƙe tsaye ya nemi waje ya zauna, magidancin mutumi ya zauna saman kujera, babba ne mai shekaru amma kuɗi sun zauna rayuwar daula ga hutu da kwanciyar hankali plus jin daɗin rayuwa. Ya amsa gaisuwa ya ce "How can I help you?" Majeederh ta yi ƙasa da kanta a hankali ta ce "Sunana Majeederh Abdul'aziz Khan, ance na zo na amshi Form na scholarship ɗin da akai mana al'ƙawari ranar Candy da Musabaƙa" Ya jinjina kai ya ce "Ok" Kana ya shiga jawo file gefe ɗaya kuma yana danna waya ya ce "I, Alhji Aliyu S, Commission for education" Bayan sun amshi form ɗin ya haɗa su da wani ya yi musu bayani, Sai dare Majeederh ta ci abinci towon masara biyar kuɓewa bushasshiyya bacci ɓarawo shi ne ya ɗauketa. Washegari babu inda ta fita sbd ciwon kai da zazzaɓi tana ta kiran number Akeeth shiru a kashe. 5days left da yamma ranar laraba tana zaune a ɗaki tana tunanin hanyar da za ta yi cigiyar Little sai kawai ta yi ta sauke application ɗin facebook ta buɗe Acct da full name ɗinta Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, ta saka photon Little cikin uniform da rubutu mai tsayi da ma'ana, tausayi da neman taimako. Comment ɗin data gani ya ɗaga hankalinta zuciyarta tayi nauyi, ta ji kanta na juyawa komai ya yi mata zafi, ta ƙara buɗe Idanunta akan comment ɗin da aka ce mata “Ke aure ya kamata dake, shekaru sun ja” Ta cillar da wayar tana miƙewa tsaye kena kowa ya san bata da aure? Me ya sa ake son goranta mata yin aure ne? Ita zata aurar da kanta ne ko ita za taga namiji ta ce tana son auren shi? Ta ƙarasa gaban madubi ta shiga kallon kanta Majeederh ba zata iya tantance da gaske tana da kyau ko bata da shi ba, tasan dai ita fara ce ba ruwanta da Powder, kwalli, lipstick kullum fuska a rufe cikin liƙab sai duguwar riga da take sawa ko ƙaton hijabi. Ko dai gwada fita za ta yi babu wannan abubuwan? Idan ta fita hakan zata samu wanda zai ce yana sonta? Ta yi shiru... Washegari Alhamis bikin Widad ya kama yau za a fara za su yi Arabian night. Gabaɗaya suna zaune a parlourn gidan Uncle Isma'il, ga Uncle Bello ga Abbu sai Yaya Bilkisu da Innati. Uncle Isma'il ya ce "Na fahimci matsalarka Abdul'aziz, sbd baka da ɗa namiji shi ya sa ka ɗauki Majeederh kamar namiji? Tunda ita ce babba, duk abinda yake faruwa na sani, kawai zan maka cewa ba ka yi kanka da ƴarka mai hankali adalci ba, Majeederh does not deserve this Abdul'aziz, idan karatu ne kaima kana iya faɗaɗa naka kaje ka ƙaro ilimi, idan ma hakan kake so ta yi why not ka fara yi mata aure first sai karatu ya biyo baya, kaga da mijinta da komai babu wata fargaba, amma Fisabilillahi ka ɗauki Majeederh wacce take kan shekarunta na balaga tun daga Nigeriya zuwa Misira? Kasan halin da zata kasance a tsayin shekaru takwas ɗin da za ta yi? Yanzu ko namiji ne ka sadaukarwa ilimi shi ba tare da tunanin lafiyarsa ba?" Abbu ya kalli yayan nasa Uncle Isma'il ya ce "Lafiya kuma? Ina tunanin ai akwai kulawa ta makaranta?" Uncle Isma'il ya ce "Ok bari na na fito maka a mutum, idan Majeederh ta buƙaci namiji makaranta zata bata? Ko maza zata fara bi? Ka haifi yarinya a cikinka amma You don't even know abinda ke damunta, da abinda take so ba, Majeederh Allah ne kawai yake kula da ita kuma shi ne ya bata yawon da take da shi, gata ƴar fari ga babu kulawar uwa data uba a wajanta" Sai a lokacin Yaya Bilkisu ta ce "Allah na tuba gata dai kyakkyawa amma ai babu mai ganin kyanta bata da kaya sai duguwar riga kamar haihuwar Larabawa, ai Allah ne ya san manufar Fulani da tace ka aurar da ita tun tana 15 amma kaƙi, ka ci mana wasiyya Allah ya sanya ta fito da kabari tai maka fatalwa sai ka fahimci tashin hankalin da take ciki" Innati ta zare idanu ta ce "A'a ba amin ba wannan kuma ai fatan tsiya ne meye kuma fatalwa ana zama lafiya abi dai komai a nutse tunda shi ya ce karatun take so ku zuba masa idanu idan yana laifi sai ya yi, duniyar gabaɗaya nawa take? Allah na tuna ya rubuta ya ajjiye komai ya faru ya shirya amsa" Uncle Bello ya ce "In sha Allah babu abin da zai faru, da dai ya barta tayi auren shi ne kawai" Abbu ya ce "Aure fa baya bari ayi karatu by the way waye ya ce yana son aurenta na hana?" Duk su ka yi masa shiru haka dai taron ya tashi ba fahimtar juna tsakanin Abbu da Uncle Isma'il da ƙaninsa Uncle Bello, familyn Khan maza ba su fiya yawa ba mata duk sun fi yawa. Majeederh na parlour ta yi shiru tana kallon yadda ƴan matan suke shiryawa cikin abayas baƙa Ruma jiya Imran ya bata, Raihana ma saurayinta ne ya siya mata, Aaliyyah kuma Majeederh ta siya mata da kuɗin albashi. "Anti Jeederh ba zaki ba?" Majeederh ta kalli Ruma ta ce "Eh" Aaliyyah ta ce "Amma me ya sa Anti Jeederh?" Ta yi musu shiru kawai Mami ta ce "Hawwa'u me ya sa baki son shiga cikin ƴan uwanki ne?" Ta ce "Ba komai" cewar Majeederh tana rufe ido Mami ta ce "To Allah yana kallo na yi nawa yin, Majeederh idan kana da kyau ka ƙara da wanka amma dai kuma ta wani ɓangaren kina da gsky tunda duk kin girme su sai dai ko Sahar" Aaliyyah ta ce "Kai Sahar ɗin ce sa'ar Anti Jeederh? Naga na girmeta da shekara ɗaya ma" Mami ta ce "Ji ƙuruciya to ai duk wanda ya yi aure ya zama sa'anta yanzu hirar da za ayi da Sahar waye zai yi da Majeederh?" Majeederh ta miƙe tare da shigewa bedroom ɗinta zuciyarta a cunkushe ji take gwarama kawai ta tafi karatun ta huta zuciyarta ta samu salama. Gidan Uncle Isma'il akaiwa decorations ya yi kyau sosai bride mate da friends ɗinta sun yi kyau aci make up, ga abokan ango sun kyau yawancin su classic ne masu aji ilimi ga wadata ta iyaye. A hankali Majeederh ta sako ƙafarta cikin harabar gidan kiɗa na tashi zuciyarta sai rawa take for the first time data zo event har haka, wanda kuma bayin kanta bane tabi ragamar zuciyarta akan abinda take jin kamar shi ne daidai, abaya ce mai ƙaton hannu a jikinta ga faɗi da take da shi ta yi mata yawa sbd ramewar da tayi, tayi rolling kanta a hankali ta saka hannu ta zame liƙab ɗin fuskarta a karo na farko in her whole life data cire liƙab a gaban maza tafiya ta fara yi zuwa wajan, gabaɗaya idanun jama'ar wajan suka dawo kanta duk wanda ya ganta sai ya taɓo na kusa da shi ya nuna masa Majeederh daga mazan har matan, ta ci-gaba ta shiga cikin wajan tana zuwa dab da wani matashin mutum tun kafin ta ƙarasu ya juya da sauri kamar yaga Aljana yabar wajan jiki na rawa......
MIJIN MALAMA
Via this number..... 0811923761623
Duk inda ta sanya ƙafarta sai taga ana matsawa tare da jan jiki baya, Majeederh was Shocked ta yi saurin saka hannunta ta shiga shafa fuskarta ko wani abu ne ya sameta, amma bata ji komai ba, bata iya shiga razani ba sai numfashinta ya fara sauka da ƙarfi ciwonta ya fara neman tashi, wani saurayi ya dinga kallonta daga nesa ganin attention ɗinsa yana kanta ya sa ta nufesa duguwar rigar jikinta na neman yarda ita sbd tayi mata yawa sosai. Tana zuwa wajan saurayin taga ya yi saurin rufe idanunsa a fili ya shiga faɗin "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Ya subuhanallahi!" Kalamansa da salatin da yake na neman taimako daga Ubangiji ya ƙara firgita Majeederh da jirkita duniyarta idanunta da sukai jajur ta buɗe akan saurayin ta ce "Don Allah mene ya samu fuskata? Me ya sa kowa ke kallo na?? Me ya sa maza suke guduna?" Sosai muryarta ta razana shi amma ya dake deep down na zuciyarsa addu'a yake na neman tsari ya dai daure ya ce
"But are you a Baha'i?" Majeederh ta dinga kallonsa ya ce "Ina nufin ke Bahaushiya ce?"
Ta jinjina masa alamar eh ya ce "Ki dai bincika amma duk wanda ya ganki zai ci Aljana ce, kyanki ya yi yawa ni ma dauriya kawai na yi" Yana faɗin haka ya bar wajan da sauri jikinsa na rawa. "Aljana??" Majeederh ta tambayi kanta tana nuna kanta da yatsa a fili ta ce "Is this really happens to her?" Ta zube saman kujera tare da dafe kanta "Wai meke faruwa? Ni ce Majeederh ko wata new Majeederh? Ko dai gaske Aljana ce, Innalillahi" da ƙyar ta iya jan jiki tare da ɗaukan liƙab ta mayar a fuskarta tana fita Aliyu ya shigo wajan shi kansa bai san mene ya kawo shi ba..... Gabaɗaya suna zaune a parlour Hajia ta gyara zama speaking calmly ba faɗa ta ce "Sannu fa, ai zata aikata duk me aka ce ta yi bana doubting" Hajiya Rahmerh ta ce "I don't think so, amma dai ta ce komai zai daidai In sha Allah" Hajia ta girgiza ƙafa kawai hankalinta yana ga Aliyu-haydar da har yanzu ba taga shigowar shi ba. Anti Biba mai bin Hajiya Rahmerh ta ce "Ni wai ina Autanki ne Hajia? Babu shi ba Almustapha?" Kafin ta yi magana Aliyu ya shigo muryarsa mai ɗauke da damuwa ta ɗan baiyana a parlour. Daga Mahaifiyarsa Hajia har ƙannenta Hajiya Rahmerh da Anti Biba suka dubi Aliyu. "Kai lafiya kake? Wannan idanun kamar mai azumin Kaffara?" Ya nemi waje kusa da Hajiya ya ce "Am Good, ya hanya Aunties?" Anti Biba ta ce "Lafiya, lawyer sarkin ƙarya" Bai ce komai ba ya shafa kansa feeling better ganinsa kusa da Hajiarsa "Aliyu" Aliyu ya kalli Hajiya Rahmerh har sai da gabansa ya faɗi ta ce "Aliyu, Aliyu, Aliyu how many times do I call your names?" Ya yi ƙasa da kansa ta ce "Ok na kira na ji daɗin bakina ne ko mene? Eh?" A hankali ya ce "Afuwa" Ta gyara zama ta ce "Kana da gata, kana da kuɗi, kana da ilimi ka fara aiki zaka gina kanka to me ka ke jira? What are you waiting for??" Shi dai bai magana ba ta ce "To ka fita daga cikin idanuna, ku biyu kawai Allah ya bawa Hajiya Laylerh ai yana da kyau yanzu zuri'a su fi haka yawa, bari na buɗe maka zancan a faifai maganar aure nake maka" Ya yi shiru daman ya san abin da zata ce kenan ya ce "To" ta ce "Ba wannan nake son ji ba, cewa zakai to Hajiya Rahmerh zan yi nan da wata kaza ka gane, ni a kawo maganar ba ga can ƴar uwarka ta ƙare karatunta a London Buhayyerh talk to her ina da tabbacin zata amince maka" Ya cira idanunsa ya kalleta ya ce "She is not strong enough to be my wife, I need someone stronger" Ta ce "Are you kidding me, right?" Ya yi shiru, Hajiya Rahmerh ta shiga faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba har tayi masa tas bai ce komai ba. Ya miƙe tare da shigewa part ɗinsa, yana shiga Anti Biba ta bi bayansa ta ce "baka kyauta ba Aliyu" ya riƙe kansa ya ce "Goodness, me na yi?" Ta ce "Ba haka ya dace ka bata amsa ba, ana iya yin ƙarya domin kare kai wannan ya halatta a mazahabar malam Bahaushe, ana iya lashe rai ɗaya domin kare rai dubu" ya yi shiru for some seconds ya ce "Kawai sai a haɗa aure? Kamar an daina wannan abun an shige ƙarnin tun tuni" Ta yi Murmushi kawai ya ce "Ina Antin Turkey?" Anti Biba ta ce "Sun sauya sheƙa an yi mijinta transfer na wajan aiki" Yana kwanciya tare da rufe idanu ya ce "Zuwa ina?" Ta ce "Ban san ƙasar da take ba, tana ta complain dai bata so sbd karatun yaranta baya yake dawowa" Ya mirgina ya ce "Tana da gaskiya" Hira su ka yi sama tana lura da yadda ƙirjinsa ke ɗagawa sosai da ramar da ya yi sai ba tayi masa magana ba.... Washegari da safe Innati ta dira gidan Abbu lokacin duk suna karyawa ta dubi Abbu ta ce "Audil azizu saɓon Ubangiji kake amma ba zaka gane ba" Da damuwa sosai ya ce "Saɓo Innati?"
"A'a, Allah na tuba ai duniyar gajere ce kaje ka yi bance komai ba, amma zaka sha mamaki da izinin Allah ka kuma shirya" Kalaman Innati suka daka Abbu cikin shakku na rashin sanin abinda ya aikata har haka da zai gani? Innati ta kalli Majeederh data raƙube gefe ɗaya kamar ba gidan Ubanta ba ta ce
"Babu komai, jarrabawa ce amma ni kaɗai na san abinda idanuna ke gani akan ki Kululu ki yi ta addu'a takanas na zo wajanki tunda na ji ance jirgi zaki hau ki bar duniyar"
"Ƙasar dai ba duniyar ba" Aaliyah ta faɗa tana kallon Majeederh wanda ko kunun ta kasa sha. Kamar daga sama kuma su ka ji ta ce "Inna da Aljanu nake kama?" Innati ta zare idanu tana dafe ƙirji ta ce "Yanzu to mene haka? Ina ruwanki da zancen Aljanu da sanyin safiyar nan don Allah? Allah ya yafe miki" A raunace kamar bata son yin magana ta ce "Na taɓa ji kince na tsorataki" Innati ta ce "To bance komai ba, ke kuma kwaɗayayyiya wacce ta sha nonon maita ki ke idan wancan yaron ne zaki gani, abin da naga komai ina kan gani" Ta faɗa tana nuna Ruma da hannu ita kuma ta tura baki gaba, ta juya kan Mami ta ce "Ban yi mamaki ba, haihuwar Legas ce ke sai abinda Ubangiji ya ƙaddara za mu gani, duk ƴan iska ne Legas ɗin ai" Abbu dai bai ce komai ba sbd yasan halin mahaifiyarsa kamar wacce take da matsala idan tana abu sai dai kawai su dinga jinta. Majeederh ta yi shiru a ɗakinta inda take kwance akan gado sai juyi take, bata san meke damun zuciyarta ba, wacce kullum ke ƙaryata ta akan zata iya samun wanda zai aureta ya rusa zuwanta Egypt.
Ta juya a hankali tana ƙanƙame pillow jin tsigar jikinta na tashi wani abu yana mata yawo a jiki, wanda ta kasa sabawa da jinsa a kullum, yanzu ko ta ɗauki azumi ma sai ya karye bata san meke kawo wannan abun ba, ta ƙara juyawa tana kiran sunan Allah ko zata daina jin abin amma ina, ruwan saman da akayi ya ƙara haddasa bayyanar abu a jikinta kamar cin wutar kara. Miƙewa tayi ta nufi toilet tana zuwa ta dinga sheƙawa kanta ruwan sanyi a hankali ta durƙoshe akan ƙafafuwanta duk yadda ta kai da haƙuri, juriya, da miƙa lamura ga Ubangiji sai da ta fashe da wani raunataccen kuka har da shassheƙa. Da ƙyar bacci ya ɗauke ta, ta farka da wani irin zazzaɓi ta juya tare da kallon Mami dake zaune bakin gado ta zabga uban tagumi ta ce "Kin farka?" Majeederh ta miƙe zaune tana mistake idanunta da suka kumbura "Mami"
"Kuka ki ka yi Majeederh?" Ta yi shiru domin bata ƙarya Mami ta sauke numfashi ta ce "Hawwa'u, kina ji cewa a ranki bana kyautawa ko?" Majeederh couldn't speak Mami ta ce "Majeederh bani da iko dake, haka kullum mahaifinki yake ce mini, shi ya sa na tattara komai na ja bakina nai shiru, to na ce me? Ina tofa tawa zai ƙullace ni, mun sha samun saɓani da shi akan ki amma ya ce ba ruwana ƴarsa ce ke ba wani ya haifa masa ke ba, hatta tafiyarki ba a son raina ba dana faɗa masa gasky cewa ya yi zan yi ta igiyar aurena, ni kam mene ya yi mini zafi? Ƙatuwa dani ina shirin kai ƴa ɗaki na samu jika da yawon zawarci?" Ta ja numfashi ta sauke ta ce "Allah yana gani na fara gajiya yana neman shafa mini baƙin fenti" Murmushi kawai Majeederh ta yi ta ce "Ba komai"
"Da gaske babu?" Ta jinjina kai ta ce "To Allah ya iya mana, ko can ɗin kika je kiyi ta addu'a, ki riƙe mutumcinki har zuwa shekaru takwas ɗin" Kanta a ƙasa ta ce "Na gode" Mami ta miƙe tsaye tana cewa "Maza ki tashi ki shirya wani sa'ilin ke kike mai da kanki baya ayi mace ba kwalliyya? Ba kwalli ba powder, fuska kullum a rufe da wata ƴar malafar uban duguwar riga, kamar matar mamaci ko wacce aka koro daga Saudiya? Fuska a maiƙaci sai farin bala'i kamar an kwara miki man ɗanyar gyaɗa haba Majeederh? To ai shikenan" ta saka kai ta fice abinta.
Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya, wai ta yi kwalliyya? Ai bata da wata sauran dama ta riga ta sallama, ta yarda ta amince domin ta yi ilimi da bautar Ubangiji take raye, ta yarda ita ta rako mata duniya ko me za ta yi a rayuwa ba zai taɓa sauya abin da zuciyarta ya yarda da shi ba, ko fata za a sauya mata ba zata taɓa samun mijin aure ta yarda za ta yi karatu zata zama cikakkiyar Malamar addinin Musulunci zata fafata da duk wanda zai ja da wata ɗiyya mace zata zama jaruma mai yarda da suke abin da Ubangiji ya zo mata da shi, yarda da ƙaddara ta zama feminist. Ta buɗe wayarta tare da kunna network ta shiga facebook, abin ya bata mamaki ganin ta samu mabiya da yawa sosai kamar jira ake ta buɗe. Ta shiga wajan timeline ta yi rubutu ta ce “ITA MACE, BA BAIWA BA CE, KO A GIDAN MIJI" tana gama rubutawa hannunta na rawa ta yi posting ɗinsa, Just now amma over 100 comment ta duba sunan wani Bilal-Habib ya ce
“Uhm ke ba aure ba, kuma zai kashewa wasu? Shi aure ne ba bauta ba? To uwarki ne?" Tana gama karanta idanunta ya sauka akan wani da ya rubuta.
"Malama Majeederh ki bari ki fara auren ko? Ai wannan maganar bata yara ba ce" Da sauri ta yi wurgi da wayar bayan ta kashe datar zuciyata na harbawa. Ta daɗe kafin ta samu nutsuwa. Mami da maƙociyyarta na zaune suna hira Latifa Omar ta yi sallama ta shigo cikin wani lace mai kyau ta sha kwalliyya ta ce "Ina yini Mami?"
"Lafiya lou Latifa ya Maman taki?" Ta ce "Ta ce a gaisheki, Majeederh fa?" Da hannu ta nuna mata hanyar ɗakin Majeederh ta shiga da sallama ta sameta zaune ta ce "Ya naganki zaune ba kyan gani? Kamon ba?" Ta yi shiru idanunta akan waya tana da Research more than 2hrs tana abu ɗaya "Amma dai baki isa ki ce ba zaki ba ko? Bikin Widad ƴar uwarki ni ma zani balle ke?" Ta ce "Mene amfanin zuwa? Ana zuwa domin farin ciki ni raina ke ɓaci Latifa Omar ki bari kawai karatu zan yi" Latifa ta zauna ta ce "Mene ya faru?" In brief ta faɗa mata komai, Latifa ta yi jigum ta ce "Kamar wata mujiya, Majeederh anya lafiya?" Majeederh ta yi murmushi ta ce "Lafiya lou, i believed Ubangiji ke komai i trust ni mutum ce ba Aljana ba....
MIJIN MALAMA
0811923761624
Latifa ta kalli Majeederh ta ce "Amma ba zaki gudu ba kowa? Ki bar gidan kawai idan a kaga babu ke dole a haƙura" Majeederh ta shanye mamakin da Latifa Omar ta bata, she just staring at her kafin ta girgiza ta ce "Kina nufin na gudu na bar gidanmu? Sbd buƙatar mahaifina?" Latifa ta ce "Yes, that's what i mean, idan kika ta fi after a month or a year sai ki dawo nasan babu abin da zai ce, sai murnar ganinki Majeederh" Tunda ta fara Maganar Majeederh ke jin zafin zuciyarta na ƙaruwa ta ce "Anya ke ƙawar arziƙi ce?" Latifa ta ce "Haba Majeederh? Is just a suggestion bawai dole sai kin aikata hakan ba, kawai gani na yi kina cikin takura na mahaifinki by the way ga rashin saurayi da baki da shi balle mijin aure"
"Kuma ɗan ƙaramin tunaninki ya baki na gudu? Kina gidan iyayenki,ni ki bani shawarar na yafi yawon duniya? Na taɓa ce miki Abbu ya takura ni?" Latifa ta yi shiru, Majeederh ta haɗe fuska babu alamar her heart stopped beating, ta ce "Ban so, a gaban saurayinki kin zauna kina zayyana masa Abbu faɗa zai mini idan ban amshi form, mene nashi? Ko halin ubana kike faɗawa wani? Ba ruwana da wanda kuke tare ki daina faɗa masa wace ni ko ya nake" Latifa da mmkin maganar Majeederh ta ce "Ba dai wata manufa kika juya zancan ba?" "Ban ji daɗi ba" Majeederh said quietly. Kana a raunace ta ce "Na yarda ni macace mai tarin buƙatu, ina sane da abin da ke yawo akaina, amma Latifa ban taɓa cewa ki bani ko biyar ba, na yarda Allah ke yi, na riƙe aikina da albashina nake komai, na taimaki mahaifina, kun fimu wadata amma Allhamdu lillahi, ina da wadatar zuci kuma yanzu na fahimci maganar Abbuna, to ki daina tunani komai mahaifina ya yi zan iya barin gidan nan, ya zama first and last time da zaki bani wannan shawarar" Ta faɗa cikin daɗin zuciya tare da miƙewa zata bar wajan, Latifa Omar ta riƙeta ta ce "Ki yi haƙuri Majeederh, i don't mean to hurt you, ba zan sake ba" Ta jinjina mata kai alamar babu komai ta ce "And yana da kyau ki kwanta ki huta, naga bacci da ciwon kai a idanunki sosai" Majeederh ta harɗe hannu a ƙirji tana kallon Latifa Omar kamar me nazartar wani abu kafin ta ɗauke kai tana duba littafin hannunta ta ce “Ok Dr Latifa Omar.”
“You need as much beauty sleep as you can get.” Latifa ta faɗa tana dry ganin yadda Majeederh har yanzu ranta ke a haɗe alamar dai sam bata ji daɗin shawarar data bata ba, kuma ita ma ɗin ta fahimta Majeederh doesn't deserve that, Ta gyara zama ta ce "Amma bakya tunanin farinki ya yi yawa? Shi yasa ake zaton wani abu daga gareki, ni a tunanina ki zauna yau na miki make up a shafa miki baƙi a fuska kiyi duhu wa'allah sai kiga an dace idan muka je wajan kamon Widad" Majeederh ta ajjiye littafin hannunta ta yi shiru alamar tunani speaking calmly ta ce "bleaching?” Latifa ta ce "Wanne irin bleaching ni ƴar nan, kin taɓa ganin farin mutum na bleaching?? Kawai baƙi zan shafa miki a fuska" Majeederh bata sake magana ba, ta shiga ta yi wanka ta fito ɗaure da towel wani irin kallo Latifa ke binta da shi, zata iya cewa tunda suke bata taɓa ganin Majeederh haka, tafi ganin ta gama shiryawa tana saka kaya ko tana zaune, ko aiki, ko kuma dai tana karatu domin ko bacci bata fiye samu taga tana yi ba. Ita da kanta zata iya cewa Majeederh ba Mutum ba ce, in her whole life bata taɓa ganin mace mai kyau da tsarin halitta kamar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan ba. "kallon fa?"
"No, na fara missing ne" Bata ce komai ba harta gama zaro abaya zata saka, Latifa ta ce "Yau ɗaya sai kin kafa mana tarihi a ƙasarmu Nigeria da jiharmu Kano" wata atamfa ta ɗakko tun wacce matar Uncle Isma'il ta bata, ɗinkin riga da skirt, atamfar Golden ce mai blue sai ɗaukan idanu take, daman tun tuni Latifa ta kwaso kayan make up. Majeederh bata san meke damunta ba, amma zuciyarta ta amince da buƙatar Latifa Omar, ta zauna akan stool Latifa ta shiga yi mata kwalliyya ita dai idanunta rufe ta tafi wani tunani nada ban, wanda sam bai dace da ma'aunin iliminta ba. harta ɗaura mata head bata buɗe Idanunta ba, Latifa ta ce "Wow, wallahi kin yi kyau kalli kanki fa" slowly kamar mai tsoran ganin kanta ta buɗe Idanunta, tare da kafe kanta da kallo ta cikin madubin, gabaɗaya ta tashi daka baƙa, fuskarta sai azababben maiƙo take na baƙin kwallin da Latifa ta shafe fuskar da shi tas, sai fararen Idanunta wanda aka shafa musu kwalli ga wanin jambaki tun na iyaye da kakanni da aka lafta mata a lips ɗinta, ko ita ɗin ɓaka ce da wahala a nan a samu mai irin baƙin ta, amma har zuciyarta ta ji hankalinta ya kwanta da ganinta a haka fiye da ganinta a fara, sai taga baƙin ya mata kyau ta juya ta kalli Latifa ta ce "To ba zan iya baka Black gabaɗaya ba?" Latifa ta ce "how? Baƙin mutum zai iya bleaching ya dawo fari, fari kuma no way sai haƙuri" Ta yi jim ta ce "What about my hands? Legs, da wuya"
Latifa ta ce "Ki saka Safa, ƙafa da hannu, wuyanki kuma ki rufe da mayafi" haka ta yi ta ɗauki babban mayafi ta rufe jikinta ruf sai baƙar fuska kamar bayan tukunya a waje tana da ƙyalli. Ba kowa a gidan suka rufe jawo gidan tare da ficewa, yammaci ne kusan duk samarin unguwar na nan, suka dinga bin Majeederh da kwallo suna mmkin inda Latifa ta samu mahaukaciya domin duk mutum mai hankali ba zai taɓa irin kwalliyyar da Jiddatul-khairy ta yi ba, ganin kallon na yawa kuma Latifa bata son su fasa zuwa gidan bikin a haka sai ta tsare napep ta masa kwatancen gidan Uncle Isma'il..... Compound na gidan ya zama kamar hall event yadda aka tsara akai komai, ga manyan mutane ƙawayen amarya da sauran family. Bugawar kiɗan ya yi daidai da bugawar zuciyarta, ta sako ƙafa a hankali kanta ƙasa musamman da taga mutane kamar furanni sbd tsabar kyau da iya matching colour na dress, Hajiya Luba ce ta shige Majeederh tana sauri ganin Latifa ya sa ta tsaya ta ce "A'a zuwan yaushe Latifa? Ina babar taki?" Latifa ta ce "Yanzu na zo, wallahi bata jin daɗi ta ce ayi muku Allah ya sanya alheri" Hajiya Luba ta ce "Allah sari, Allah ya bada lafiya Majeederh bata zo ba ko?" Latifa ta ce "A'a, gata nan tare muke" Baki sake Hajiya Luba take bin wacce aka ce Majeederh ce da kallo with shocked ta ce "Malama Majeederh tamu nake magana, wannan ai na ɗauka wata mata ce mai taɓin hankali dake kusa damu" Latifa ta zare idanunta ta ce "Wallahi Malama Majeederh ce Anty, kalli cikin Idanunta zaki yarda" Hajiya Luba ta riƙe haɓa ta ce "Jama'a mun shiga uku, Majeederh lafiyarki ɗaya kuuwa? Kinga kalli kanki" Ta ƙare haɗe rai ta ce "Shawarar wace a cikin ku? Yin kwalliyyar?" Da sauri Latifa ta nuna Majeederh ta ce "Ita ce"
Sosai ran Anti ya ɓaci ta ce "Tsaya a nan ina zuwa" Tana barin wajan sai ga amarya Widad da friends ɗinta suka gaisa da Latifa tana ta mata complain bata zo da wuri ba, gashi Anti Jeederh ita ko zuwa ba ta yi ba. Ta juya ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, wacece wannan waye ya ƙara barin wannan mahaukaciyar ta shigo?" Majeederh ta runtse Idanunta ganin yadda ake haɗata da mahaukaciya bata ji ba bata gani ba, kafin Latifa Omar ta yi magana ta sulale da sauri tabar wajan. Tun daga nesa wasu tawagar maza suke dariya ɗaya hadda ɗakko waya yana danna vedio yana cewa "Lallai bikin Widad da Mansur ya yi albarka, hadda su mahaukaciya a wajan?" Ta ƙarawa tafiyarta sauri harta shigewa bayan ƙofa ta shiga gidan Uncle Isma'il tana dafe ƙirjinta. Her heart broke, she hugged her knees even righter. She felt warm tears running down her cheeks, nothing hurts like they words, ta wulaƙanta kanta akan neman mijin aure sai gashi buƙata bata biya ba mazan ma kallon mahaukaciya ce suke bata, a wancan karan ance Aljana yanzu kuma suna kiranta da mahaukaciya. Ba abinda ke bata tsoro ganin hatta Aaliyyah da suke ciki guda bata ganeta ba. Ta ƙara ƙanƙame jikinta waje guda.
Hannunsa duk biyun ya sa ya rufe kunnenshi wanda sautin kiɗan ke neman fasa masa dodon kunnen, a hankali ya juya yana buɗe idanunsa cikin sauri kuma ya sakko daga kan gadon yana jan tsaki, gabaɗaya ƙaddara ce ta kawo shi gidan Uncle Isma'il ya ɗauka a gidan Uncle Bello za su yi Shirman abun nan, gashi daga dawowarsa garin ba a bar kunnenshi ya wuta ba, idanunsa sun ƙanƙance sbd bacci ya buɗe ƙofar ya fito daga shi sai wani 3gauter, tunda ya fito ta tsora masa idanunta da suke ɗauke da jiƙaƙƙun hawaye tana mamakin yaushe ya dawo shi kuma? Harya gama watannin kenan, yana zuwa ya fice ta gefen ƙofar kai tsaye kuma wajan M.c ɗin ya nufa "Hi" M.c ya ce "Hi" Ya kame fuska sosai ya ce "Kwashe kayanka kabar wajan nan yanzu, duk wanda ya yi magana ka ce Alpha Bello khan ya saka ka ok" Yana faɗin hakan ya juya, Ruma ce ta fara magana ta ce "Kai Dj ya haka? Yanzu fa abokan ango za su zo, kawai sai ka shiga kwashe kaya" M.c bai magana ba sai Dj ne ya ce "Wa nine ya ce mu kashe yanzu" Ruma ta ce "Kan uba waye?" Ya ce "To gashi nan dai, amma kamar Soja yanayin jikinsa" M.c ya ce "Sunansa Alpha Bello khan" Da sauri Ruma ta rufe baki tana zare idanu daidai nan Widad ta zo tana complain me ya sa ta ji shiru, Ruma ta faɗa mata Alpha is back, wani irin rushewa da kuka ta yi shikenan ta shiga uku, yanzu dinner ɗin gobe hanata zai yi ta dinga kuka, Anty ta zuwa ta ce "What did i miss?" Sahar ta ce "Captain ya dawo, Alpha" Anty ta ce "Na gode Allah, ya dawo a daidai".... Majeederh na zaune ta ji an saka hannu tare da miƙar da ita tsaye da sauri ta buɗe ido ganinsa tsaye a gabanta ya harɗe hannu a ƙirji yasa ta haɗiye sauran hawayen, ya dinga kallonta frm head to toe ya girgiza kai ya ce "Follow me" Ya juya zuwa bedroom ɗin daya fito, a hankali ta tura ƙofar ta shiga yana zaune hannunsa riƙe da waya yana magana a hankali ya nuna mata toilet "Clean your face, now" Za ta yi magana ya haɗe dole ta shige, ya daɗe zaune kafin ta buɗe ƙofa ta fito a hankali take takawa zata bar bedroom ɗin ta ji ya ce "Come, Jiddatul-khairy" Ta juya tare da zubewa a ƙasa ya ce "Meke faruwa?" Ta girgiza kai, ya ajjiye wayar tare da juyawa gareta bakiɗaya ya saka hannu ya tallafo haɓarta ta yi saurin ja baya zai ƙara ta ɓata ta marairaice fuska cikin shagwaɓa wanda daman ita halittace a jikinta ta ce "Don Allah Yaa Alpha kar ka sake ta ɓani" ta faɗa har zuciyarta domin daya ta ɓata ji tayi kamar an watsa mata wani abu, tsigar jikinta ya miƙe, ya nuna mata ƙofa ya ce "Out" ta fice da sauri.... Bayan gama bikin Widad aka zauna family meeting amma rawar bata sauya zani ba, har su Uncle Isma'il suka zare hannunsu daga kan al'amarin Abbu, har lokacin Alpha bai san meke faruwa ba, shi ne babban ɗan Uncle Bello, daman jininsa bai haɗu da Mami ba shi ya sa bai damu da zuwa gidan Abbu ba, Ranar monday aka gama komai na batun tafiyar Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, daman tana yin dashi kuma ita ce ɗaukan ƙarshe aka bata kuɗi ta siyi kayan sawa sabbi da taimakon Latifa, sosai ta yi mamakin yawan Abayas ɗin data tambaya sukai mata shiru kawai, ta siyawa Abbu buhun shinkafa, katan na tafiya dana makaroni, ta siya musu masara ta Tuwo, ta bawa Aaliyah kuɗi ta ce ta riƙe a hannunta kana ta bawa Abbu ya dinga murna yana cewa "To gashi ɗan ƙaramin albashi ya yi rana, ina ga idan ta fara aiki a Misira ai shi Allhamdu lillahi, Majeederh ta wanke masa zuciya" Kanta a ƙasa, a daren ta shiga sallama da ƴan-uwa Innati kuka sosai, Majeederh na zaune a gaban Anty tana mata faɗa suka ji an shigo ɗakin ganin yadda yake huci kamar an maciji yasa Anty jin tsoro ta ɗauka ko wani abun ya faru domin tasa duk wani soja kullum cikin shiri yake ta ce "Alpha lafiya??" Idanunsa jajur bai kalleta ba, ya saka hannu ya damƙi hannun Majeederh tare da janta zuwa ɗaya bedroom ɗin yana shiga ya juya ya sakawa ɗakin sakata tare da harɗe hannu a ƙirji ya shiga takawa zuwa inda take tsaye.....
MIJIN MALAMA
Paid book
08119237616
Na'ima Sulaiman Sarauta
Nimcyluv sarauta
Ba posting weekend, mai buƙata mu haɗu a arewabooks da special grp🤓🙏🏻25
Huce ta ya yi tare da neman waje ya zauna, a hankali kuma ya sake miƙewa cikin ƙasa da murya Alpha ya ce "Why Majeederh?" Majeederh ta yi shiru ya sake juyawa a fusace kamar zai daketa ya ce "Don't let me to repeat myself Jiddatul-khairy" Ya faɗa yana hargitsa sumarsa. Majeederh ta ɗago kanta suka haɗa idanu ta yi saurin yin ƙasa da nata idon, ya san halinta da kafiya da rashin son magana ga shegen zurfin ciki, ya saisaita murya ya ce "Yanzu kina jin tafiya wata uwa duniya ya dace dake a matsayinki na mace? Duk ilimin da kika samu baki gode Allah ba? Idan karatun kike so me makarantunmu suka rasa? Bakya tunanin aure Ke??" Baki ta buɗe za ta yi magana ya daka mata tsawa yana ɗaga mata hannu ya ce "You have nothing to say, Ai na je wajan Abbu ya faɗa mini komai everything, bai san lokacin da kika nemi scholarship ba, sai form kawai ya gani kina kuka kika bashi uzurin tafiya karatu wannan dalilin ya sa kika kuri wancan that stupid Imran, akan karatu? Me kika rasa?" Tunda Alpha ya fara magana Majeederh ta yi ƙasa da kanta amma jin abinda ya furta Abbu ya shaida masa ya sa ta ɗago kanta da sauri ta shiga kallon bakinsa dake motsawa yana mata faɗa da ihunsa na sojoji. Baya ta yi tana riƙe ƙirjinta tare da nufar hanya zata fice daga cikin bedroom ɗin duk da ya sa key amma ita ta riga data mance, kafin ta ƙarasa wajan ƙofa Alpha ya ƙara yi mata wata mahaukaciyar tsawa wacce bai bata taɓa jin irinta ba, hakan ya sa ta rikice ga ƙirjinta da ya yi mata nauyi a hankali ta fara gani dishi dishi, sama-sama kuma take jin muryar Alpha daya riƙe kafaɗunta yana girgizata tasan ta faɗa jikin mutum kuma ya rungumeta daga nan bata sake sanin komai ba.... A hankali yake tafiya a cikin wrld ɗin hannunsa zube cikin Aljihu, yana sanye da wani floral jacquard one button suit, black colour sai necktie ɗin daya kasance red, ƙafarsa cikin Loafers mai kyau, sai fidda ƙamshi yake a nutse yake sauraran Latifa Omar dake gefensa tana cewa "Wallahi ban san meya sameta ba, ni ina gida ita kuma taje sallama yanzu nake samun labari wajan Aaliyyah ina ƙoƙarin tafiya kuma kace na jiraka, ashe hadda su kwanciya asibiti??" Aliyu ya fesar da iska ya ce "Allah sarki" Daga haka bai sake cewa komai ba, Aaliyyah Latifa ta kira ta fito zata nuna musu inda aka kwantar da Majeederh, su kaci karo a hanya ta durƙosa har ƙasa ta gaida Aliyu-haydar, ya bita da kallo yana yabawa da nutsuwarta, ga sahihin kyan da take da shi, ya fara tunanin ko ya Majeederh take? Idan babu wannan abun na fuskarta? Ya yi saurin cire tunanin a ransa har suka ƙarasa ƙofar room ɗin suka samu Anti,da Mami, sai mahaifiyar Alpha da kuma Uncle Isma'il da Ruma, Aliyu ya durƙosa har ƙasa ya ce "Ina yini Uncle ya mai jiki?" Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Jiki Allhamdulillah, sallamarta ma za ayi" Ya jinjina kai ya ce "Allah ya ƙara afuwa" Ya juya ya gaida sauran jama'ar wajan, Anti sai kallonsa take sbd abinda ta gani kwance akan fuskar shi ta ce "Aliyu ka shiga kaga jikin nata mana, Latifa raka shi" Latifa Omar ta yi jim ta ce "Ba kowa a ciki?" Uncle Isma'il ya ce "Da kowa ba kowa, Soja ne yayanta Alpha shi kawai a ciki" Latifa Omar tayi kamar karta shiga haka kurum jininta bai zo ɗaya dana Alpha Bello khan ba, baya kulata ko gaishesa ta yi, sai kuma ta miƙe tsaye daman tuni Aliyu ya miƙe tayi gaba ya bi bayanta a hankali ta murɗa handle ɗin Ƙofar tare da shiga bakinta ɗauke da sallama, ta matsa gefe Aliyu ya shigo idanunsa ya sauka akan Majeederh da kanta ke cinyar Alpha sai kuka take rusa masa mara sauti wanda ya fi ko wanne cin rai, yadda idanun Alpha ya yi jajir zai baka tabbacin kukan na Majeederh yana taɓa masa zuciya. Aliyu ya dinga kallon yadda Majeederh kewa Alpha kuka kana gani kasan kukan data jima tana tarawa a zuciyarta ne, ya rasa kukan na mene? Hannunsa ya sauka akan hannun Alpha da yake ɗan shafa kan Majeederh da sauri Aliyu ya juya har yana birgewa da ƙofa jiri na ɗaukarsa ya fice daga room ɗin, Latifa ta biyo bayansa, Uncle Isma'il dake tsaye shi da Dr ya dubi Barrister Aliyu ya ce "Badai har kun gaisa ba?" Ya daure murya can ƙasa ya ce "No, zan dawo" Yana faɗin hakan ya nufi harabar asibitin tare da shiga mota ko Latifa dake kiransa bai saurara ba yaja motar da gudu yabar asibitin...
Alpha ya ɗago Majeederh ya kasa cewa komai can ya sauke numfashi ya ce "It's okay, stop crying" Ta kasa daina kukan harda shassheƙa daman kuma Alpha ne kawai ke iya jin zurfin cikin na Majeederh tun tana yarinya, ya sa hannu ya riƙo fuskarta ya kalleta ya ce "What again? Kina so ni ma na shiga damuwa ne?" Ta girgiza kai ya ce "Gashi kina ta kuka, 20 yrs kamar yarinyar goye" Ya sa hannu ya share hawayen fuskarta a hankali ya cire hannunsa ya yi shiru, Majeederh ta ce "Kada ka faɗawa kowa abinda nace please" Ya kalleta kawai ta ƙara marairaice fuska ta ce "please" A hankali ya ce "Ok" kasa ci-gaba da ganinta haka ya yi a hankali ya fice daga room ɗin yana jinta tana wani kukan. Anti ta tsare Alpha da idanu ta ce "Har yanzu bata ce maka komai ba? Na yi mmki" Maman Alpha dai kallonsu kawai take da idanu dake magana bai dameta ba, Uncle Isma'il ya ce "Lallai al'amarin babba ne tunda har ta kasa cewa Alpha komai" Alpha bai tsaya ba ya nufi wajan Dr ya biya bills na komai kana ya dawo ya ce "Uncle zamu iya tafiya" Anti ce da kanta ta shiga wajan Majeederh ta bata hijabi ta zura kanta a ƙasa suka shiga motar Alpha kai tsaye kuma Gidan Abbu ya nufa, lokacin Abbu yana zaune saman kujera yana duba littafi Anti ta yi sallama hannunta riƙe dana Majeederh sai Maman Alpha, Uncle Isma'il da Aaliyyah da sauran napep suka shiga shiyasa tafiyar bata yi daidai ba. Bayan sun gaisa da Abbu suka nufi ciki har kan gado Anti ta kwantar da Majeederh ta ce "Ki kwanta ki huta sosai, Kinga ace 7 jirgin naku zai ta ce" Ta juya ta kalli ɗakin ta ce "Kin dai gama haɗa komai?" Majeederh ta ce "Na ji sauƙi fa, na gama" Ta ce "To Allah ya ƙara afuwa, bari ni ma duk na gaji kwana biyun nan" Mami ta yi musu godiya suka samu Alpha zaune da Abbu Maman Alpha ta ce "Kai fa?" Ya ɗan yatsuna fuska ya ce "Momi kuje kawai, ga kuɗin napep" Ya zaro dubu biyu ya bawa kowa duba ɗaya suka tafi, Abbu da Alpha suka ci-gaba da magana har aka kira Magriba suka nufi masallaci a tare. Mami na haɗa abincin dare Alpha ya yi sallama ya shigo parlourn Mami ta ce "Soja mazan fama, sai da ranka akan na wasu" Ya shafa kai kawai bai ce komai ba ta ce "Ga abincin dare zauna ka ci" ya ware idanu ya ce "No thank you, am full" Mami ta haɗe fuska ta ce "You're always full dama" Ta ƙara cewa "Tana ciki ai" Ya nufi ɗakin Majeederh ya sameta zaune saman ladduma tayi wanka ta sauya kaya kanta a ƙasa, shi kuma ya tsareta da idanu kamar zai magana sai kuma ya ajjiye takeaway ɗin hannunsa tare da fita.
Har aka kira sallar Issha Majeederh na zaune tana azkar, turo ƙofar ɗakin aka yi Mami ce ta shigo ta kalli Majeederh ta ce "Kizo inji Abbu" Tana faɗin hakan ta juya tabar ɗakin, sosai gaban Majeederh ya faɗi ko sunan Abbu aka kira sai ta ji faɗuwar gaba, gudun kada ta yi laifi ya sa ta ajjiye azkar ɗin ta nufi waje ta samu su Raihana a parlour suka dinga yi mata sannu, ta samesa a zaune yana wanke hannu zai ci tuwo ta yi sallama ya amsata ta nemi waje ta zauna. Cikin ɓacin rai ya ce "Ni mahaifinki Majeederh zaki tuzarta? Sbd ki nunawa duniya forcing naki nayi zuwa Misira kika kwanta ciwo? Na haifi yarinyar da zata haɗa da ƴan-uwana Majeederh ni zaki saka ciwon zuciya? Sbd na nemi alfarma a wajanki? Ko riƙonki nake ban cancanci ki wulaƙanta ni ba irin wulaƙantawar da ki kai mini yanzu ba, babu komai ki je na soke tafiya Masar ɗin" Majeederh ta zube akan ƙafafuwanta ta shiga girgiza kai idanunta cike da hawaye ta ce "Ka yafe mini Abbu, na tuba na bi Allah na bika, wallahi ban san na faɗi ba gani na kawai nayi a gadon asibiti, kuma bance bani da lafiya ba, bance kai kace naje karatu ba, ni nake son karatu nina zaɓi tafiya Egypt ba kai ba, na shiga uku idan kalamanka su ka yi tasiri a gareni, ka yafe mini na tuba na bi Allah na bika Mahaifina, ka yi mini komai yanzu ya kamata na baka farin ciki gwargwadon yadda zan iya" Abbu ya haɗe rai ya ce "You surprised me, as your father you will humiliate me, ni Majeederh? Har kin yi girma hakan? Ba zaki iya sacrifice akaina ba?" Jikinta duk rawa yake ta gigice da kalamansa wani irin kuka take kamar zata haɗiye zuciya ta ce "Ka yafe mini don Allah, ni mai laifi ce na yi alkawarin zan yi karatu zan yi aiki duk acan ƙasar, har sai mutuwa ta riskeni ko ka bani umarnin dawowa?" Abbu ya sauke numfashi ya ce "Kin yi mini alƙawarin zaki aiki a can?" Ya jinjina masa kai sbd kuka ya ci ƙarfinta ya ce "Allahamdu lillahi, idan ki kai hakan kin gama mini komai Allah ya yi miki Albarka maza jeki kwanta kada ki makara" Ajjiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa tabar ɗakin ta nufi nata tana jin kamar zuciyarta ce zata faɗo......
A can Darmanawa a rikice Aliyu ya shiga cikin haɗɗen gidansu lokacin Hajia da Almustapha da Papa suna zaune a parlour Almustapha ya ce "Papa amma Gwamnati mai ci a yanzu tana ƙoƙari, na ji ɗalibai wajan ɗari biyar aka ɗauka scholarship shi, hadda allowances every month" Papa ya ajjiye remote ɗin hannunsa ya ce "sosai ga hukumar jakadanci ta jiha ta saka hannu, haka na tsaro, hukumomin fikira, da tawaga ta musamman duk an zuba idanu akan ɗaliban gudun samun matsalar rikicin ƙabilanci, ko wani abu" Almustapha na ƙoƙarin yin magana Aliyu ya shigo babu ko sallama hannunsa riƙe da kansa, Hajia ta miƙe da sauri ta ce "Zakina Lafiya? Baka da Lafiya ne? Meke damunka?" Aliyu ya kasa cewa komai sbd parlourn dake juya masa a hankali ya ce "Hajia lulluɓeni san yi nake ji" Hajia da bata jure rashin lafiyar yaran nata gabaɗaya ta rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Aliyuna mene ya sameka yanzu ka fita lafiya lafiya fa?" Papa ya kalli Almustapha ya ce "Kira Dr" Almustapha ya juya da sauri zuwa ɗakko waya, Papa ya kama Aliyu ya kwantar saman duguwar kujera sai rawar sanyi yake idanunsa rufe jijiyoyin kansa duk sun fito, Hajia ta fashe da kuka ta ce "Na shiga uku mayu sun kama mini yaro, yarana kwaya biyu kacal a duniya shi ne za a ga bayan ɗayan?" Papa ya dinga kallon Aliyu shi kansa ciwon ya bashi mamaki, Aliyu dake cikin ciwo ya kama hannun Hajia ya riƙe ya ce "Ki danna mini ƙirjina Hajia, zuciyata zata fito waje" Hajia ta ƙara saka kuka, daidai nan Almustapha ya dawo babu jimawa Dr ya zo allura ya yi masa tambayar duniya ya faɗi meke damunsa amma yaƙi. Suna zaune har bacci ya ɗauke shi a cinyarsa Hajia yana sauke numfashi a wahale..
Har gari ya waye bacci baiga idanun Majeederh ba, ana kiran sallah ta tashi tayi wanka tare da yin Sallah ta jima tana addu'a sosai kafin ta shirya cikin wata duguwar riga Maroon tayi rolling kanta. Tana tsaye Latifa Omar ta shigo idanunta ya yi jaa taci kuka son ranta ta ce "Wai ki fito ba lokaci" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Haka aka damu dani? Irin wannan kuka" Latifa ta sake fashewa da kuka, bata hanata ba don dai itama taiwa kanta al'ƙawarin daina kuka ne, da babu shakka sai tayi nata kafin ta tafi, safiya ce amma ƴan-uwa sun cika gidan Abbu kowa yana son ganin tafiyar Majeederh, tafiya ce wacce ba lallai a sake ganin juna ba, inma ita ta mutu inma su, kanta a ƙasa ta fito daga nan suka rankaya airport, anan sukai ta ganin ɗalibai masa da mata, kasancewar a makare suka ƙarasu wajan yasa ta shiga sallama da mutane ta ƙarasa wajan Abbu ta ce "Abbu na tafi ka yafe mini don Allah" Ya ce "Babu komai, Allah ya bada sa a" haka ta dinga bin mutanen wajan tana zuwa wajan Aaliyah ta rungumeta, a can gefe ta hango Alpha yana tsaye rungume da hannunsa, uniform ɗin sojoji ne a cikinsa amy colour ta nufi inda yake ya kalleta bai ce komai a hankali ta ce "Na tafi" Ya gyara tsaiwa ya ce "All The best, ki kula" Za ta yi magana ya yi saurin shigewa mota, sai a lokacin hawaye ya taro a Idanunta ta nufi cikin wajan har tayi nesa da su kai tsaye jirgin ta shiga sai da ta zo matattakalar ƙarshe ta ɗago kanta ta kalli ƴan-uwanta kamar ance ta kalli gefe idanunta ya sauka akan Aliyu hannunsa maƙale da carnoner...
MIJIN MALAMA
08119237616
Uhm get ready...... Yanzu zamu fara🥹26
Majeederh ta sake kallon Aliyu, she saw that he had changed from the way she knew him, duk da ba wani mugun sani ta yi masa ba, ta ɗauke kai ganin yadda ya kafeta da idanunsa da suka janye, a hankali ta juya idanunta cike da hawaye ganin Khan's family maza da mata yara da manya suna ɗaga mata hannu. Jikinta na ƙyarma da ɓari na rashin sabon tafiya ita ɗaya ta ƙarasa kujera ta zauna tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta, wani rauni ya mamaye dukkan zuciyarta fargaba da tsoran abin da zata tarar a ƙasar daba tata ba ya wanzu a zuciyar Majeederh Abdul'aziz Khan. Ya za ta yi a garin da babu uwa ba uba? Garin da ba wa ba ƙani? Garin da babu idon sanin? Garin da babu mai kwaɓarta? Ya za ta yi idan abu ya faru da ita wa kuma zata tunkara? Rashin sanin wanda zai bata amsar tambayoyinta ya sanya ta ƙara tura kanta wani mahaukacin kuka na kwace mata ta yi saurin rufe bakinta. "Assalamu alaiki" Wata murya ta sauka cikin kunnenta a hankali ta goge hawayen idanunta tas ta ɗago kanta bayan ta gyara zaman liƙab ɗin fuskarta. A hankali ya daidaita tsaiwar shi ya ƙara cewa "Assalamu alaiki" Su take ta amsa amma harshenta ya yi mata nauyi ta ɗaga kanta suka haɗa idanu, yana tsaye ya rungume hannu ɗaya a ƙirjin fuskarsa maƙale da face mars, ya ƙara zuba mata idanu ganin yadda take ta sauke ajjiyar zuciya ya ce "Ki duba number seat ɗin ki" Sai a lokacin ta duba taga a number 35 take zaune number ta kuma 34 ne, ta langwaɓar da kai alamar ban haƙuri kana ta tashi a hankali ta zaune a number dake window. Ya nemi waje ya zauna yana danna airplane mode a wayarsa tare da ware jarida ya shiga dubawa, yadda Majeederh ke sauke numfashi a wahale ya sanya ya juya ya kalleta tare da cewa "Are you okay?" Ta jinjina kanta.
"Are you sure?" Ta ƙara jinjina kanta ya bita da kallo kafin ya ce "Okey"
Sanarwar aka fara kowa ya shirya jirgi zai ta shi, a hankali ta jawo ballet ta ɗaura a jikinta.
Jirgi ya fara juyawa a ƙasa tsayin wasu daƙiƙo zuwa mintuna, Majeederh ta rufe Idanunta tare da ƙanƙame jikinta waje guda, lokacin da jirgin ya yi katantanwa zai tashi ji tayi kanta yana sarawa amai na shirin zubo mata. A taushashe ya ce
"Sorry" tana cikin wannan yanayin jirgin Emirates Airplane ya ɗaga da ɗarorun ɗalibai. Ta sauke ajjiyar zuciya ya ɗauki ruwa ya miƙa mata ta girgiza kai, har lokacin bai ji maganarta ba.
"Please bear with the interruptions, is this your first time on a plane?"
"Uhm" ta furta a yanayin da ba zai iya haddace muryarta ba.
"I see, sorry" Ya mai da hankali zuwa ga jaridar dake hannunsa deep down na zuciyarsa he was thinking ko dai bata jin magana, kurma ko bebiyya? Only God knows... Majeederh ta rufe Idanu yayinda da dukkan wani farin cikinta ta barshi a jihar Kano, ƙasar Nijeriya.
Aliyu ya zame idanunsa daga kan jirgin su Majeed wanda ya gama shigewa cikin gajimare, ji ya yi kamar da zuciyarsa ta tafi tare da nutsuwarsa ya sauke numfashi yana ƙoƙarin buɗe murfin motar shi ya ji an ce. "Hi"
Ya tsaya ta buɗe motar ya juya idanunsa ya sauka akan Alpha wanda baya jin zai iya mance yanayin daya gansu shi da Majeederh. Bai ce masa komai, Alpha ya gyara zama ce ya ce
"Alpha Bello khan my name, Captain, It is the highest rang in Tactical troops organization"
"Good" Aliyu haydar ya ce murya kuma can ƙasa, Alpha ya gyara tsaiwa ya ce "Sunanka Aliyu Sufyan Alhassan, ɗan Jarida a matakin farko na fara aiki, Kayi karatu a Al'ƙalam University, daga nan ka shige Cairo ka ɗora da karatu, a gida anso ka karanci ɓangaren politics Democracy, kai kuma ka ce Law ka ke so, mahaifinka Alhaji Sufyan Alhassan shi ne Commissioner for education, ku biyu iyayenku suka haifa, yayanka Almustapha shi ne Manager a Bua campaign, mahaifiyarku tana ji daku sosai shi ya sa bata jure dukkan ɓacin ranku, wannan dalilin ya sa bata takura ku akan maganar aure duk da akwai ƴan mata a familynku amma kuna jin kun girmi ajin su" Alpha ya yi murmushin gefen baki ya zuba hannu a aljihu ya ce.
"Idan har a kwana ɗaya zan iya sanin waye kai, to karantar zuciyarka ba zaiwa Alpha wahala ba, bayan kasanceweta soja ina aiki a hukamar fikira ta jiha ka kiyaye, kada ka fara abin da ba zaka iya ba, kada ka sanya zuciyarki cikin ramin da zata kasa fitowa, kada ka yi ƙullin da zaka saka cikin kejin kaza, kasan kaza uwar tune-tune ce, stay away from her, Ina nufin Majeederh Abdul'aziz Khan she's my sister"
Bar Aliyu Sufyan Alhassan dake jingine da jikin lafiyayyiyar motarshi ya ɗan miƙe hannunsa mai ɗauke carnoner ya ɗaga ya shafa kansa ya ce "Anzo wajan"
Ya dubi idanun Alpha dake kwance cikin nasa idanun kai tsaye ya gane me launin idanun yake nufi domin a yawan karatun English Novels da yake da literature daya karanta yasa fahimtar hakan bai masa wahala ba "Uhm"
Sai kuma ya ce "Me ya sa zaka nuna maitarka a fili? Kada ka manta nan fa ba filin yaƙi bane ko dajin sambisa Captain Alpha Bello khan, a tsare rayukan jama'a kafi ƙarfi, amma ba zaka nunawa Babba lauya fahimtar waye mutum ba, by the way, who are you talking about? Stay away name? Please open your heart ƙilan na fahimta sosai"
"Ka janye jiki daga gare ta, baku dace ba?" Cewar Alpha. Cike da rainin hankali irin na Lauyoyi Aliyu ya ce "Wai wa kake magana? stop bitting around the bush, just go to the point" Ya faɗa da muryar marasa lafiya.
"Na hango soyayyar Majeederh a cikin ƙwayar idanunka, shi ne nake maka gargaɗi kada ka sanya son abin da ba naka ba, ku dan muhimmancin rayuwarka ga wanda suka damu da kai" Alpha Said, ya na buɗe ido.
Aliyu ya ware idanunsa ya ce "Soyayya? Ni ɗin? Kuma wai da sister naka? Goodness, to an faɗa maka halin Lauyoyi da Sojoji ɗaya ne? A cikin gari muke fa ba wai barrack ba, balle ka ce zakai kishi akan kilaki, and ka yi kuskuren fahimta zatonka ya saɓa lissafinka"
Aliyu ya taka a hankali har gaban Captain Alpha ya ce "Yes Am in love, amma da ƙawar Hawwy ba ita kanta ba, bani da tabbaci da zuciyata, ban yi kuma al'ƙawari ba, domin shi kayana ne, zuciyata ba sansanin sojoji bane wanda a koda yaushe za a cillaku duk garin da aka so, zuciyata ba rigar sawa ba ce, balle a cire sanda aka so a kuma saka sanda aka so, Shi kuma so a makaho ne, baya ji baya gani baya kuma fahimta balle a gargaɗe shi, shi ne kamar dukiya ne wanda maganar mai shi kawai take ji, Ni bana soyayya domin So tsuntsune yana iya tashi daga kan wata ya koma kan wata, abun da zuciyar Barrister Aliyu Sufyan Alhassan ta sani shi ne _“KAUNA”_ irin ta har abada, ƙauna wacce zan iya mutuwa akan ta, ban san sacrifice a cikin Ƙauna ba, Cikakken namiji shi ne mai faɗa domin cimma nasara, nasara bata tabbata sai da tarin ƙalubale, ƙalubale a rayuwa shi ke nuna yarda da ƙaddara, yadda da ƙaddara ke nuna yarda da Allah Ubangiji maɗaukakin sarki" Ya yi shiru yana sauke numfashi kafin ya daki kafaɗar Captain Alpha ya ce "My friend, fight for your love"
"And you too Barrister Aliyu Sufyan Alhassan, kada ka manta ko a kasancewata Cousin zan iya yi maka illa"
Alpha ya sake faɗa a siga ta ya zama dole ka bar abinda zuciyarka ke so. Murmushi kawai Aliyu ya yi domin ƙoƙarin magana kawai yake yana faɗin hakan ya shiga mota, daidai nan Latifa ta ƙarasu ta ce
"Meke faruwa, kai da.....,"
Sauran maganar ta maƙale ganin Captain Alpha tsaye jikinsa sai ɓari yake shi kaɗai ta yi saurin nufar Aliyu ta ce "Yaushe ka zo?" “.... Not too long”
"Tafiya za ka yi?" Latifa ta sake tambaya ba tare daya kalleta ba ya ce
"In sha Allah" Ta ce "Ok then, Bye zan ki raka na ji jikin" Ya ware idanu akan Lafita ya ce "Ok love"
Ya yiwa motar key tare da yin reverse ya bar wajan da gudu.
Da sauri Alpha ya shiga ta sa motar har lokacin jikinsa ɓari yake yana jin Anti na kira amma ya yi banza. Gabaɗaya Khan's family suna can kan Aaliyyah dake ta faman kukan tafiyar Majeederh da ƙyar suka lallaɓata tare da shiga napep su kai gida.
New life
Airplane ɗin Emirates ya sauka a filin sauka da tashin jirgi na Cairo International Airport, kasancewar tsakanin Nigeria da Egypt tafiyar 5 hours 25 minutes ce. Ya sanya su ka yi saukar dare, weather garin ta bambanta data ƙasa Nigeria, Ruwan sama: 1 Laimar iska: 30 Iska 18km/h tun a step ɗin farko na jirgin ƙofofin fatar jikinta suka buɗe suka shiga amsar saƙon sauyin yanayin da suka samu. A hankali Majeederh ta ɗaga kanta sama tana ganin sararin samaniya sama ɗaya ce kaf duniya, amma ta bambanta da saman data gani a taushashe ta ce “Majeederh a Misira”
Misira/ Egypt
Kasar Misra,ko Masar tana kudu maso gabashin Afrika, kuma tana kudu maso yammacin Asiya, ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewarta a kan mararraba ta kusa da nahiyar Turai. Sannan kuma tana matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar maliya. Harshen ƙasar Larabci ne, Shugaban ƙasar Abdul-Fatah El-sisi ya wadata ƙasar shi da komai, kuɗin ƙasar kuma Fam ne, ita ce ƙasar da tafi ko wacce yawan Al'umma a cikin ƙasashen Larabawa, ga babban birninta Al'ƙahira har ila yau gata a ƙarshen kogin Nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya.
Majeederh ta buɗe ido jin ana tambayarta da larabci "Shin ko lafiya kike?" Majeederh ta kalli kyakkyawar farar budurar dake tsaye kusa da ita kafin ta ce.
"Lafiya lou" Budurwar ta ce "Ma sha Allah, Sunana Ƙhulud Arzaan daga Saudiyya na zo nan karatu tare da mijina Ajlaal" Ta yi mata bayanin cikin larabci. Majeederh ta sake murmushi ta cikin liƙab ɗin kafin ta ce "Ma sha Allah, Allahumma Barik"
"May i knw You?"
Cewar Ƙhulud Arzaan Majeederh ta ce "Me zai hana?" Ta gabatar mata da kanta ganin yarinyar nada nutsuwa, Ƙhulud Arzaan ta juya idanu ta ce "Ina mijinki?"
"Bani da aure" Majeederh ta faɗa a taƙaice, Ƙhulud Arzaan da bakinta baya shiru ta ce "Oh sorry, kuma Abbanki ya barki barin ƙasarku zuwa wata babu muhrrami? Ba kyau hakan, shi namiji Garkuwa ne"
"Nawa Uban da kansa ya tursasani zuwa, ko da zan mutu a nan" Majeederh ta faɗa a zuciyarta tana ƙara karaya da lamarin mahaifinta. Daga nan gabaɗaya babbar mota ce ta sake kwasar su zuwa inda aka tana ta domin su, zuwa wayewar gari kuma za su fara shiga Al-Azhar University.
Tana kwance idanunta a sama tunanin rayuwarta da makomarta kawai take na yadda zata iya gabatar da rayuwa a ƙasar Misira babu kowa nata, har dare ya tsala bacci ya kasa ɗaukan idanunta a lokacin kuma ta mance da batun wanda suka haɗu a jirgi. Ta mirgina kaɗan tana riƙe mararta dake mata wani irin murɗawa tsigar jikinta sai tashi take tana zubewa kofofin gashin jikinta duk suka buɗe alamar a shirye suke da karɓar abin da suke buƙata. Ta ƙanƙame jikinta tare da jurewa waje guda tana jin gabaɗaya duniyar na yi mata zafi, al'amarin da take ji ya tsananta ta miƙe tare da tsugunawa tana girgiza kanta a raunace ta ce
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangiji ka kawo mini ɗauki, Allah ka dubeni ka kare mini martaba da kimata har zuwa ɗakin mijina idan ina da rabon yin aure idan bani da rabo Ubangiji ka tsare mini imanina ka kare mini budurcina har zuwa sanda raina da ruhina zai dawo gareka" Jikinta duk ƙyarma da ɓari yake ji take kamar ana kwara mata wuta a fatarta mararta ta kumbura, ƙirjinta ya ƙara girma fiye da ƙima tabbacin tana kan buƙatar namiji. Tana nan har ta ji kiran farko na sallar Subhi da sauri ta miƙe tsaye tare da shiga toilet ta sakarwa kanta shower tana sauke wani wahalallan numfashi, ta fito ɗaure da towel duk a tsorace take na rashin sabo. Duguwar riga ta saka ta buɗe fridge ta ɗauki fruits da ruwa da dabino kaɗan ta ci ta sha ruwa sosai kana ta ɗauki niyyar azumi kamar yadda ta saba. Raka'atul fjr ta yi tana zaune Ƙhulud Arzaan ta shigo cikin kyakkyawar shiga ta ce "Zo mu je masallaci"
"A masallaci ake sallah?"
Ƙhulud Arzaan ta ce "Eh"
Ta faɗa ne kawai amma hankalinta duk yana kan fuskar Majeederh bata taɓa ganin zubi da tsarin halitta kamar na Majeederh Abdul'aziz Khan ba, har ta shirya cikin wata abaya ruwan huda idanun Ƙhulud Arzaan akanta ta sanya hijabi mai kyau kana ta saka Liƙab sabo. A hanya Ƙhulud ta ce
"Kuma are you sure a Nigeria kike?" "In sha Allah" cewar Majeederh "You look familiar"
"Me??" Majeederh ta tambaya domin bata ji ba, Ƙhulud ta watsa hannun ta ce "Mafi mushkila"..... Suna shiga Al-Azhar University Majeederh ta cike komai da komai akai sa a department ɗaya suke da Ƙhulud Arzaan, course ɗin farko Majeederh ta ɗauke komai da komai a kanta domin da gaske karatun ta zo ba wasa ba, burin mahaifinta zata cika har ƙarfe biyar suna cikin makaranta.
Abbu ne tsaye a gaban wani mutum ya ce "Maganar gaskiya nake maka, gidana da nake ciki nake so a rushe komai a sauya sabo kafin bikin ƴata Ruma" Alhaji Bashir ya ce "Taya zaka biya?" Abbu ya ce "Ni nake da hanyar biya, mai ƴa kamar Majeederh har a faɗa masa wani abu?" Alhaji Bashir ya yi dariya ya ce "Ƴarka jarinka, to yanzu dai gasky ko zan maka wannan kwangilar sai na ƙara maka kuɗi a ƙalla dubu ɗari biyar akai shi ne ribata, idan kuma ni zaka bani auren yarinyar ma shikenan zai na yi maka haɗaɗɗen gida 200by 200 matsayin sadakinta kaga data dawo sai ayi maganar biki, ko kuma a ɗaura auren idan ya so sai na bita can" Abbu ya yi shiru Alhaji Bashir ya ce "Think about that Malam Abdul'aziz, bayan gida har kyauta zan maka muddin zaka aura mini Majeederh" Abbu ya ce "To a nawa zaka iya bani?" Alhaji Bashir ya zaro takarda ya ce "Faɗi adadin miliyan nawa ka ke so, ni kuma take zan baka zaka tashi daga matsayin Malam ka koma Alhaji" Jikin Abbu na rawa ya ce "Na amince, na amince wallahi zan baka auren Majeederh.....27
Alhaji Bashir ya gyara tsaiwa yana shu'umin murmushi ya ce "Bana ɗaukan asara ba kuma zan fara akan ka ba, ka yarda zaka bani auren yarinyarka Majeederh? Ni kuma na baka dukkan abin da ka ke so?" Abbu bai dugun tunanina ba ya ce "Na baka aurenta ƴata Majeederh halak makal, ko bayan bana raye" Alhji Bashir ya ce "Baka raye to waye zai tashi matsayin shaida?" Ya yi jim kafin ya ce "Allah da Manzonsa su ne shaidar hakan?" Alhaji Bashir ya haɗe fuska ya ce "Na san da haka, amma mutane huɗu shaidu nake so" Abbu ya shiga nazari idan ya ce a'a ya san tabbas zai dauma cikin wannan gidan nasa da baya samun ci-gaba, mafarkinsa na zama wani a duniya ba zai tabbata ba, hanya ɗaya ce wacce ta kasance madafar shi shi ne “Majeederh” Abbu ya ce "Zuwa dare sai ka dawo ni kuma zan haɗa maka shaidun" Alhji Bashir ya ce "Never mind, Allah ya kaimu" Su kai sallama Alhji Bashir ya shiga mota ya tafi, Abbu kuma ya koma gida. Yana shiga ya samu Mami zaune ya nemi waje ya zauna tare da yin shiru yana mamakin abin da ya hana Majeederh kiransa gashi har anyi kwana biyu.
"Lafiya?" Ya sauke numfashi ya ce "Ina yaran? Aaliyyah, Raihana, Ruma?" Mami ta ce "Ruma ta tafi raka Imran, Aaliyyah da Raihana sun je gidan Widad" Abbu ya numfasa ya ce "Rumana ta dinga janye jikinta daga yaron nan"
"Wanne yaron?" Abbu ya tsareta da idanu babu alamar wasa ta yi saurin cewa "Naga aurenta zai yi shiyasa bana damuwa" Abbu ya ce "Kina da tabbacin haka? Baki san meke ɓoye ba" Mami ta yi saurin cewa "Me ka ke nufi? Bayan shi ya ce yana son ta zai aureta?" Bai ce mata komai ya miƙe ya shiga duba gidansa lungu da saƙo deep down na zuciyarsa yana tunanin wa zai kira matsayin shaidu?...
Da daddare misalin ƙarfe tara Latifa Omar na kwance idanunta a sama kewar rashin Aminiyyarta na damunta, ga rashin kiran Aliyu wayarsa ma gabaɗaya a kashe take, she so much loves you ya yi tasiri a zuciyarta sosai. Ta ƙara juyawa idanunta rufe a hankali ta sake jawo wayarta tare da danna kira a number da tayi saving da “Heart choice” Cikin sa a kiran farko ta ji an ɗaga a marairaice cikin damuwa ta ce "Sweetheart" Almustapha ya yi shiru yana gyara zaman wayar a kunnenshi tare da juyawa ya kalli Aliyu dake kwance saman gadon asibiti ya yi mahaukacin ramewa "Hello"
Muryar Latifa ta sake dawo da shi hayyacinsa ya ce "Majeederh Abdul'aziz Khan, right?" Latifa ta zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa, mene haɗin Aliyu da Majeederh? Ta yi shiru tuna muryar da ta ji kamar bata Aliyu ba, a hankali ta ce "No, Latifa Omar ke magana, Aliyu fa?" Ta yi saurin tambayar hakan cike da bin umarnin zuciya. Almustapha ya ce "Ok, mai wayar yana kwance asibiti" A ruɗe cikin tashin hankali idanunta har ya ciko da hawaye ta ce "Subuhanallahi! Wanne asibiti" Musty ya ce "Aminu Kano"
"Am on my way" kafin ta ajjiye wayar ya ce "Amma kamar dare ya yi, da kin bari zuwa safiya" Ta girgiza kai kamar yana ganinta ta ce "I can't, ba zan iya bacci bangan shi please" Musty ya ce "Ok, daman daya farka ke ya kira, so na kira ki wayar a kashe shi ne ya ce a nemi Malama Majeederh kuna tare" Ya faɗi hakan yana gyara ɓarnar da ya yi a baya. Daga haka ya yi hanging off.
Papa dake jin duka maganganun Musty da Latifa ya ce "Me ya sa kayi mata ƙarya Almustapha Sufyan Alhassan?" Almustapha ya shafa kansa ya ce "Shi ne mafita Papa, zan so a ɗaura auren shi da Latifa in prioud time. "He doesn't like her" cewar Papa. Almustapha ya ce "Yanzu mene amfanin haka Papa? Duk jiya yake kira mana suna ɗaya Majeederh, Hawwy, Hawwa'u, na tambaye shi me ya sa yake son Latifa bayan Majeederh ce a bakinsa?"
"Me ya ce?" In ji Papa.
"He refused to answers my question" Hajia ta juya kan Aliyu dake jin duk abin da suke faɗa amma idan ka ganshi zaka ɗauka bacci yake, hannunsu dake danne da ƙirjinsa kawai ke motsawa dalili bugawar da zuciyarsa ke yi.
"Me ya sa Zaki?" Ya buɗe gajiyayyun idanunsa da sukai jajur kamar ba zai magana ba har Hajia ta ƙara cewa "Meke faruwa ne?" Ya yi saurin riƙe hannun Hajia ya ce "Ban sani ba, Amma ina sonta a gefena" "Aurenta za ka yi?" Hajia ta tambaya tana riƙe nasa hannun.
"A duk sanda na ji ina son aurenta sai na ji na tsaneta, amma idan na cire batun auren sai na ji babu wacce nake son gani sai Majeederh, i want to see by my side, ko sunanta na ji zuciyata bugawa take don Allah ki taimaka mini Hajia please" Papa ya yi zuru yana ganin ikon Allah, wani abu mai kama da almara. Bai taɓa ganin hakan ba, ko a film na hausa, Indian movie ko series balle novels, ace wacce mutum ke son aura daban wacce kuma take zuciyarsa daban "Ikon Allah" Cewar Papa Hajia ta ce "Ikon gaske, Yanzu me ka keso" Cikin sauri Aliyu ya ce "Majeederh na keson gani Hajia please" Hajia ta zabga tagumi Idanunta jajur alama ta jima tana kuka domin tun jiya Aliyu bai san inda kansa yake ba sai yanzu, Papa ya sauke numfashi cike da jimamin al'amarin da kuma tausayin ɗan nasa ya ce "Zan nema maka auren ita Majeederh a wajan Mahaifinta idan ka amince, kada ka sanwaltar da rayuwarka akan ta" Aliyu ya girgiza kai ya ce "Ba aurenta zan ba" Almustapha dake tsaye harɗe da hannu ya ce "Ok ita Teddy ce da za a ajjiye maka ita kai ta Kallonta? Me ya sa ka ke son kan ka har haka? Kana ganinta, But you don't want to marry her? what kind of nonsense and stupidity is that??" Aliyu ya marairaice ya ce "Ka tausaya mini Yaya, ni kaɗai na san halin da nake ciki idan kai baka rarrashi su Hajia ba waye zai taimaka mini?" Jikin Almustapha ya yi sanyi ya ce "Papa Hajiya help him don Allah kada wani abu ya same shi" Papa da ran shi ya fara ɓaci ya ce "Ok kai ma da kake da hankali kenan ko? To ba zan ɗauki wannan haukan ba, zan je na nema masa auren Latifa Omar ƙilan hakan zai sanya ya manta da batun Majeederh" Wani irin rikitaccen kuka Aliyu ya saka jikinsa sai rawa yake ya riƙe Hajia da ƙarfi numfashinsa na sarƙewa yana riƙe ƙirjinsa, Almustapha ya shiga faɗin "Dr... Dr... Dr.." Likitoci suka haɗu akan Aliyu da ƙyar suka dawo da numfashinsa tare da yi masa allurar bacci dake jininsa mai ƙarfi ne sai bacci ya gagari idanunsa ya dinga surutai. Dr ya kalli su Papa ya ce "Alhaji zaku tafka babban kuskure idan zaku dinga yin abin da zai ɓata masa ran shi" Papa ya kasa magana sai kan shi da yake jinjinawa. Suna haka wayar hannun Almustapha ta fara ringing ganin sunan “Latifa Omar” ya sanya ya ɗaga kiran "Ok" ya furta yana barin cikin ɗakin, not too long suka dawo tare da Latifa da kanta ke ƙasa sanye da hijabi ta yi sallama tare da durƙosawa ta ce "Ina yini ya mai jiki?" Hajia ta dinga kallon Latifa Omar frm head to toe a taƙaice ta ce "Alhmd" kana ta miƙe ta bar ɗakin, Papa ma ya fita Almustapha ya ajjiye wayar Aliyu ya fice wajan ya rage daga Latifa Omar sai Aliyu dake kwance. A hankali ta miƙe ta zauna a gefen gadon ta ce "Nasan ba bacci ka ke ba, ya jikin?" Aliyu sai ya ji tamkar muryar Majeederh lokacin da take cewa _“ I don't want to interfere”_ Da sauri ya buɗe idanunsa tare da sauke su akan Latifa Omar wacce a yanzu ta zame masa Majeederh Abdul'aziz Khan sak! Duk da bai san fuskarta ba amma zubin yadda idanunsa suka kalle masa Latifa sai yaga kawai Majeederh ce gabansa, ya mance drip a hannunsa ya tashi zaune yana kafeta da idanunsa wanda suka sauya Latifa na ƙoƙarin magana ta ji gabaɗaya ya jawota ya riƙeta tsam a jikinsa ya ƙanƙameta yana sauke wata mahaukaciyar ajjiyar zuciya cikin magagin allura ya ce "Don't leave me alone please, ban so kada ki barni please Hawwy" Ya riƙe ta yana cusa kansa a wuyanta, Latifa Omar tsoro ya kamata sbd babu wani namiji daya taɓa yi mata hakan a tsayin rayuwarta, gefe na zuciyarta kuma bata jin zata iya hana shi yin haka sbd Allah kaɗai ya san irin son da takewa Aliyu. "Ba zan barka ba, ni ɗin taka ce Allah da Manzonsa ma sun shaida hakan" Ta faɗa a sanyaye ta kuma rasa faɗuwar gaban na mene?..
_*5 Month later...*_
Majeederh ce ke ta fe a hankali kanta a ƙasa hannunta riƙe da littafai yadda take tafiya zai tabbatarwa da mai Kallonta a mugun gajiye take, kusan haka ɗin ne domin karatu ya yi mata yawa bata da lokacin komai da kowa sai karatu tsayin watanni biyar da zuwanta Egypt bata taɓa kiran number kowa a Nijeriya ba, haka kuma bata da ƙawa idan ba Ƙhulud Arzaan ba, hakan ya sa da yawan student suke mata kallon mai masifar girman kai suka yi tunanin ƴar gidan wani ce a duniyar ma bawai a Nijeriya ba, Ilimin da Majeederh take da shi ya ƙara mata kwarjini a idanun malaman jami'ar da sauran ɗalibai, ita kuma suka zaɓa matsayin shugaban ɗalibai duk da ta ce bata so amma aka tilasta mata amsa, da yawan Student na zuwa ta ƙara musu haske, wasu kawai don su ji maganarta wasu kuma ko Allah zai sanya suga fuskarta suga mene dalilin rufe fuskar. A cikin watanni biyar harshenta ya juye sak cikakken Balarabiya ba zaka taɓa cewa ta san hausa ko English ba idan tana larabci, to ta je garin larabawa uwa uba ɓangaren Arabic take karanta. Duk rashin son maganarta sai da ta saba da Ƙhulud Arzaan ba tare da sanin dalili ba, haka kawai take son yarinyar kamar Aaliyyah, Ƙhulud Arzaan ta taka rawa sosai wajan wayar da Majeederh ta jata har shopping ta kwasu mata abayas masu mahaukacin kyau tsada very expensive classic one and unique. Liƙab ɗin ma ta sauya mata irin na Larabawa da suke sawa, a cikin 5 Month ɗin nan Majeederh a rame take bata gaba bata baya jia iyau kamar kazar matsiyata ramar kuma ta samu asali akan abinda ke hanata bacci kullum yake sanyata azumi wanda babu fashi ya zame mata jiki kullum. "Majeederh... Majeederh" Kiran ya dakatar da ita daga tafiyar da take Ƙhulud Arzaan ta ƙarasu tana dariya ta ce "Shi ne kika taho ko?" Majeederh ta ɗan saki numfashi ta ce "Kin tsaya gulma" Ƙhulud Arzaan ta ce "Gulmar ta yi mini amfani kam" Ita dai Majeederh bata ce komai ba sbd an kusa kiran sallar Magriba bata so ta yi mata a hanya Ƙhulud Arzaan ta ce "Musabaƙar Alkur'ani za a yi, Ta duka ƙasashen duniya na Muslunci" Majeederh ta waro idanu ta ce "Ma sha Allah, za mu ga manyan malamai mu tada haddarmu mu ma" Ƙhulud Arzaan ta ce "Au haba? Kin san me gabaɗaya ko wacce ƙasa ta bada sunan wanda zai wakilce su, ƙasar ku Nigeria kawai ta rage" Majeederh ta yi shiru tana tunani wa Nigeriya zata zaɓa? Allah ya sa ko waye ya dawo musu da martabar ƙasar su. Kafin ta yi magana Ƙhulud Arzaan ta ce "Kuma Saudiya ta sallamawa Misira kamar yadda suka buƙata ayi Musabaƙar a nan ƙasar, kuma hadda Granny ta a mutanen da zasu zama masu tantance ƙasar da tayi nasara" Majeederh ta ce "Kullum ana bani labarin Granny Finally zan ga Granny" Ƙhulud tayi dariya sosai ta ce "Like serious, ba ruwanta idan kin ganta sam ba zaki ce ta haifi Sarki Sultan ba" Majeederh ta ware idanunta ta cikin liƙab ta ce "Kai, ke jinin sarauta ce?" Ƙhulud Arzaan ta yi shiru domin bata son cewa Majeederh ita surukar gidan ce babanta kuma ƙanin Sarki Sultan ne. Suna hira har suka ƙarasa gidansu Majeederh ta yi part ɗinta Ƙhulud Arzaan ta shige nata. Wanka Majeederh ta yi kana ta yi sallah sannan ta sha ruwa, tana mai yin watsi da maganar Ƙhulud Arzaan. A nutse ta jawo wayarta ta kunna cikin nutsuwa ta danna number Abbu, ringing ɗin farko ya ɗaga ta cikin wayar ta ji ya ce "Ko baki faɗa ba nasan Majeederh ce" Ta sauke numfashi ta ce "Asslaymu Alaika Ya Abbu" Ta faɗa a nutse.
"Ke ce Majeederh?" Ta faɗa a fili wanda ya jawo hankalin su Aaliyyah, sosai muryarta ta sauya ta zama ta Larabawa. "Ni ce Abbu" Abbu ya ce "Allahamdu lillahi shiru shiru har wata biyar?"
A nutse cikin tarin kamala ta ce.
"ليلة سعيدة ، أتمنى أن تكون بخير"
Ma'ana "Barka da dare, fatan kana lafiya" Abbu ya ce "Wallahi lafiya, kina lafiya ya karatu?" Cikin Larabci ta ce "Allhamdulillah" Ta tambayi kowa na gidan duk ya basu suka gaisa Aaliyyah hadda kuka wurjajjen. "Hawwa'u shiru ba kira ba saƙo?" Majeederh ta ce "Ka yi haƙuri Abbu" Ya ce "To na yi" Ta ce "Ma sha Allah" Jin shiru bata ce komai ba ya ce "Har yau dai gamo jiya iyau, ba wani abu" Sosai Majeederh ta ji babu daɗi ta ce "Zan tura maka kuɗi Abbu ta nita sai aje a cire" Abbu ya ce "Yawwa to nawa ne kuɗin? Daman an kusa bikin Ruma don ma anyi jinkiri ne" Majeederh ta ƙara yin shiru domin rashin son maganarta ya ƙaru fiye da baya ta ce "Ƙilan su yi 200k fam ne ban san nawa za su tashi a Nigeria ba" Abbu ya ce "Dubu ɗari biyu ya yi kaɗan Majeederh ina laifin Miliyan ɗaya" Majeederh ta zaro idanunta da suke farare tas ta ce "Miliyan? Abbu ina zan gan su wannan ma Albashin da gwamnatin Nijeriya ke bamu ne bana taɓa wa" Abbu ya ce "To babu damuwa amma duk wata idan aka baki kada ki taɓa ko ficika ko kwabo karki ɓatar" Mamakin mahaifin nata ya cika mata zuciya ya kira sunanta ya ce "Majeederh babu ke ba namiji, ko aurenki mutum zai yi ki ce ke ba zaki aure ba ki ce kina da miji kawai, Majeederh wallahi wallahi duk sanda na ji labari ko na ganki da wani namiji to Allah ya isa ban yafe ba, karatu kawai zaki a tsayin shekaru takwas ɗin nan........
Mijin Malama
0811923761628
Majeederh was listening to her father with great surprise, her heart was pounding, A ranta tana jin cewa ko mahaifin nata bai ce kada ta kula kowa ba, babu wani ɗa namijin da zai ce yana son ta balle ya yi ji sha'awar aurenta, This is her destiny, and she answered with both hands as a complete Muslim. "Majeederh" Abbu ya kira sunanta cikin kakkausar murya ta kasa amsawa sbd taraddadin rashin sanin abin da zai biyu baya ya ce "Ni ne ubanki, mahaifinki jinina ke yawo a duka jijiyoyin jikinki, ƙwayar haihuwata ita ce ta samar da ke, idan kina zaton a zuciyarki kiyi gaggawar cire zaton, wallahi tallahi nine mahaifinki Allah ya shaidawa, Manzonsa ya shaida, Mala'iku sun shaida haka.....,"
Majeederh ta katse Abbu jikinta na rawa ta ce "Na sani, na sani bani da wanda ya fika duka duniya Abbu don Allah ka yi haƙuri kada ka aibata ni" Abbu ya ce "Kin yarda da hakan?" Ta yi saurin ɗaga kai sbd ba zata iya magana ba, ƙirjinta ya yi mata nauyi. "Hawwa'u a matsayina na wanda ya haifenki wallahi wallahi idan kika kula wani namiji sau ɗaya tak da sunan soyayya Allah ya isa ban yafe miki ba, karatu kawai na yarje miki kiyi tsayin shekaru takwas ɗin nan" Maganar Abbunta ta sanya mata wata iriyar faɗuwar gaba mai tsanani da ƙyar ta ce "Na yi maka al'ƙawari Abbu, ka tayani da addu'a kuma ka yi mini alfarma ɗaya don Allah Abbu"
“.... Alfarmar me?” Abbu asked. Ta yi saurin cewa "Abbu ka duba halin da nake ciki idan da hanyar da zaka iya mayar dani jinsin namiji don girman Allah Abbu ka taimka ka mayar dani namiji,ni ma zan fi nutsuwa zan fi yin karatun yadda ya dace"
Abbu ya ce "A'a ba shakka, ni kikewa hannunka mai sanda? Ni kike son nunawa ban isa ba, duk abinda ɗa namiji zai kema zaki iya, daga yau yanzu ki daina kallon kanki matsayin mace ki fara ganin kanki tamkar ɗa namiji, wanda zuwa nan gaba yake fatan zama babba a ƙasar, ta hanyar zama Gwamna, shugaban ƙasa, ko shugaban wani katafaren kamfanin, amma idan kina jin ban isa ba go ahead Hawwa'u kina da full right na yi duk mai kikeso haihuwa ce a haife dai mun haifa" Cikin hanzari Majeederh ta girgiza kai ta ce "Wallahi ka isa, ni ikonka ce ba zan sake cewa komai ba ka yafe mini na bi Allah na bika Abbuna" Ya yi shiru jin haka ya sa Majeederh runtse Idanunta zuciyarta na wani irin zafi da raɗaɗi. A takaice Abbu ya ce "Duk wata kina tura mini kuɗin Albashin nan, kada ki ciri ko kwabo idan kuɗi kike buƙata ki nemi taimako wajan wani" A sanyaye ta ce "In sha Allah"
Kashe wayar ta yi tare tsorawa kanta idanu ta cikin madubi, ta jima tana kallon kanta kafin a fili ta ce "What should I do?" She don't know What to expect and kept thinking about how her father would react to seeing her after so long, yanzu ma ya aka ƙare balle ta ja lokaci, ta dafe kanta dake juyawa azumi ta kai babu komai a cikinta sai ruwa. _“Majeederh, pray ki faɗawa Allah komai”_ Wata zuciyar ta bata amsa. She breathed out, trying to calm herself nerves.
Tana zaune har aka kira sallar Issha amma bata motsa ta yi nisa cikin tunani domin ko kiran ma Allah bai nufeta da ji ba, ta zama kamar zararriyya. Kafaɗarta da aka jijjiga da ƙarfin gaske ya sa ta sauke wani wahalallan numfashi tana mai buɗe idanu a firgice ganin Ƙhulud Arzaan ya sa ta haɗe fuska sosai tana ɗauke kai, Ƙhulud Arzaan ta ce "Ƙarfe 10 na dare ke kam kina zaune?" Majeederh ta kalli Ƙhulud Arzaan ba tare da ta ce komai ba "Ki zo ku gaisa da Kalb" Majeederh ta ce "Maimaita" Ƙhulud ta ce "Kalb ya ce na kira ki ku gaisa" Majeederh ta girgiza kai ta ce "Kafin wannan, kin ce wani abu?" Ƙhulud Arzaan ta dinga kallon Majeederh kana ta ce "Ƙarfe 10 kina zaune?" Zumbur Majeederh ta miƙe ta ce "Asstagafirullah Ya Allah" .... "Lafiya?"
"Ban yi sallar Issha ba" Ta faɗa a gigice kamar ta yi kisan kai. Ƙhulud ta nemi waje ta zauna tana mai cewa "Eh to da sauƙi, ai sallar Issha bata ɓaci Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce; da ba don kada na matsantawa al'ummata ba, dana umarce su da yin sallar Issha bayan sun farka daga bacci, Talatainin dare" Ita dai Majeederh bata ce komai ba, Ƙhulud Arzaan sai bin Majeederh da kallo take zuciyarta fal tunani har ta iddar da sallah kana ta fara azkar. Ganin Majeederh bata da niyyar ta shi yasa Ƙhulud Arzaan miƙewa ta koma part ɗinta, ta samu mijinta Ajlaal zaune yana danna waya hannunsa riƙe da Apple sbd yana ƙaunar dangin kayan lambu, ta zube a saman cinyarsa idanunsa akan wayar ya ce.
"Meke damun rayuwar Yarima Ajlaal Sultan?" Ƙhulud ta kwaɓe fuska ta ce "Allah daga kai har Majeederh baku son ku gaisa" Ya yi kyakkyawan murmushi kawai yana girgiza ƙafarsa alamar rarrashi can ya ce "Ga ni fa... Call her" Ta tura baki ta ce "Gashi nan sai sallah take Allah don kar tazo ne" Ya saka hannu ya zame hular kanta yana cusa hannunsa cikin sumarta bai ce komai ba. "Ka zo muke part ɗin nata, ka ji Kalb my prince"
Ya waro dara daren idanunsa cikin murya irin ta masu mulki ya ce "Prince ɗin Saudiyya da zo wajan wata? Ni Ajlaal? " Ta yi shiru tana kallonsa ya ce "Uhm, shi ya sa kike ta zubar mini da ƙwayaye a hanya ƙasa ƙasa, kin kasa riƙe ko ƙwai ɗaya balle Sultaan ya saka ran samun grandson?" Ta daki ƙirjinsa dake buɗe cike da yalwataccen gashi kafin ta ce "Ajlaal wayo zaka mini, idan ka fara haka" Ya tsorawa lip's ɗinta idanu kana ya saki wayarsa a gadon ya ce
"Damn it...!"
"Me?" Ya miƙewa gabaɗaya tana wutsil wutsil haka ya cillata gadon yana kashe hasken ɗakin gabaɗaya muryarsa can ciki ya ce "Yarinya ina zama lafiya wajan aikina kika saka rigima ashe Allah ke sona da rahama"....... Cikin dare Majeederh ta kasa bacci sai juyi take saman gado tana riƙe cikinta a hankali take kiran sunan Allah, jin azabar ta yi yawa ya sa ta miƙe a haukace tana girgiza kanta tare da zubewa saman gwiwoyinta ta ce "Ya Allah ka ɗauke mini abin da na ke ji har gaban abada wlh ban so, Ubangiji ka karkatar da halitta jikina zuwa ta jinsin maza" Ta yi shiru duk da sanyin ac amma zufa take jikinta na ƙyarma da ɓari, ta zari hijabi tare da sakawa ta nufi wajan part ɗin. Lokacin data fito yana zaune saman kujera a daidai corridor wanda zai mayar da kai part ɗin Ƙhulud, daga shi sai wata Jersey fara tas faffaɗan ƙirjinsa a bayyane, ya ɗora ƙafarsa saman table hannunsa riƙe da system yana dannawa, lokaci zuwa lokaci yake yatsuna fuska yana ɗaukan green tea tare da sha a hankali, sumar kan nan nashi har wuya, Prince Ajlaal Sultaan gabaɗaya mahaifinsa ya ɗakko sak. Yana zaune ya ji motsi ya juya kansa ya hango mace durƙoshe ta cure waje guda tana yarfe hannu, taɓe baki ya yi tare da kwasar system nasa ya na jan tsaki..... Washegari dai wajan 11 ta shiga Al-Azhar University tun kafin ta nufi department ɗin su taci karo da babban malaminsu. Cike da tsantsar ladabi ta gaisheka ya ce "Majeederh Abdul'aziz Khan?" Ta jinjina kai ya ce "Follow me" Yana tafe tana binsa kamar bata son takawa har ya isa office ɗinsa, manyan mutanen data gani a office ɗin ya bata tsoro ta zauna gefe guda. Malamin ya yi gyaran murya ya ce "Majeederh ga jakadan ƙasarku Nijeriya dake zaune a nan Misira, bayan zaman tattaunawa da manyan ƙasar ku kama daga shugaban ƙasar, gwamnan sauren jihohi da naku, shugaban malamai na ƙasa dana jiharku daga ƙarshe sun bada sunanki matsayin wacce zata wakilci ƙasarku Nijeriya a gasar musabaƙar Alkur'ani ta duk duniya" Majeederh ya zaro idanu waje ta shiga girgiza kai a raunace ta ce "Ba zan iya ba, ba zan iya ba ni Ɗaliba ce"
Jakadan Nigeria ya ce "Zaki iya Majeederh, Malamin daya baki ilimi ya shaida hakan, mahaifinki ya shaida" Muryata na rawa ta ce "Duk duniya fa? Ba zan iya ba please a sauya wata" Ta faɗa a shagwaɓe Ajlaal Sultaan ya ɗago kansa dake naɗe da hirami ya ɗan kalleta kana ya taɓe baki yaci gaba da abin da yake. "Ki nutsu wannan dama ce da ba kowa Allah ke bashi ba, abin alfahari ne ko da baki nasara ba ace kina cikin jerin Ɗaliban da suka shiga, Nijeriya yanzu ke ya zubawa idanu, jikarki, unguwarku, Malaminki, mahaifinki ke ce hope ɗin su, sun yarda dake don haka ki basu mamaki" Majeederh ta yi shiru ta ce "Ina tsoran rashin nasara" Wani dake zaune ya ce "Good, than sai ki miƙe ki tashi tsaye ki saka yaƙini sai Ubangiji ya tabbatar, kuma sai nan da wata biyar za ayi kafin nan kin samu hurarwa" Ta ƙara yin shiru tabbas dama ce a gare ta ta bawa Abbu abin da yake buƙata.
"Zan yi" Suka sauke ajjiyar zuciya kana suka sanya mata albarka ta miƙe a hankali ta fice Ajlaal ya ɗan saci kallonta yana ɗauke ido.
Tun daga ranar Majeederh bata da lokacin kanta, manyan malamai suka sanyata a gaba, karatu safe, rana, dare. Daman tuni haddar Alkur'ani sittin ɗin suna zaune a kanta daram, Tajwid da mukarijin hurum ake tisa mata, da saita ƙira'a daman Ubangiji ya bata murya kamar haihuwar Larabawa. Ya zamana a tsaye bacci take sbd karatu, Ƙhulud Arzaan ganin Majeederh ya yi mata wahala idan tana bita da rigima Ajlaal baya ce mata kanzil. Majeederh ta goge harsu malaman mamaki kawai suke idan tana karatu, hakan ya ƙara sa musu hope mai girma akanta...
*5 Month later..... The day*
Ranar Musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa ya tashi ranar watan tafiyar alhazzai, watan zul-hajj. Tun ana sati ɗaya gabaɗaya Ɗaliban ko wacce ƙasa ta Muslunci suka sauka a ƙasar Misira, daga nan kuma manyan mutane, shugaban ƙasar ko wacce ƙasa, da gwamnoni, hatta Sarkin Saudiyya Sarki Sultaan ya halaccin Misira ana kwana ɗaya da shi da Mahaifiyarsa Zaytoon, hadda. Babban hall ɗin ya cika da jama'a fal, ƙabila da yare daban daban farar fata da ɓaka, jami'an tsaro kamar me. Saura minti ashirin a fara Ɗaliban duk suka shigo ko wanne da tambarin ƙasar shi a jikinsa, kowa aka nuna masa wajan zama kana zama computer zata nuna sunanka da kuma ƙasar da kake, gabaɗaya kuma ya kasance mata ke namiji ɗaya ne daga Qatar. Majeederh kanta a ƙasa sbd jiri da faɗuwar gaban dake riskarta na rashin sanin su waye a wajan. Zagaye biyar ne masu zafi, da kayi kuskure Computer zata tsayar da kai. Aka fara da ƙasar Saudiyya ta tayi karatu yadda ya kamata, a zagaye na huɗu dana biyar ta samu matsala. Abun kamar abin mamaki Majeederh ce ta zamo ta ƙarshe ma'ana Nigeria, Computer ta nuna mata farkon shafin suratul Yusuf, kana malamin ya ja.
Kanta a ƙasa ba tayi kuskuren ɗago kan ba, lokacin da tayi Basmala shiru wajan ya ɗauka ya zamana kamar ba a ji ƙira'ar kowa ba sai nata, sbd zaƙi da sautin muryarta daya zaga ko'ina na hall ɗin, a tare Sarki Sultaan da Zaytoon suka ɗago kan su, tare da kallon inda Majeederh take zaune fuska rufe, Zaytoon ya dubi computer gaban Majeed taga ansa. _“Majeederh Abdul'aziz Khan, from Nigeria”_ Karatu take mai ɗauke da zallar ƙa'idoji na Kur'ani. Tunda ta fara karatun idanunsa akanta ya kafeta da wani irin rikitaccen kallo yana mamakin yadda a ƙasar su Nigeria aka samu mai daɗin murya da ilimi kamar Majeederh. Tunda ta fara karatun babu gyara ko tuni, waƙafi, aya ko wasali har zuwa zagayen ƙarshe. Computer ta nuna mata Suratul Maryam tsakiyar surah. Cikin rashin sa a ta ɗago kanta da nufin sauke numfashi nan take komai nata ya kunce dalilin ganin dubban jama'ar da suke gabanta tare da kallonta suna kuma saurarenta. Ai gabaɗaya neman duk haddar Alkur'anin dake kanta tayi ta rasa kaf, a tare kuma Aliyu-haydar, Captain Alpha, Prince Ajlaal Sultaan da wani matashi dake kusa da Gwamnan jihar Kano suka ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!....
MIJIN MALAMA
Paid book
08119237616
ALLAH ya nuna mana ranar Monday Monday Lafiya.... Have a nice weekend👑🍷29
Da sauri Aliyu ya juya tare da fita daga hall ɗin, Alpha ya harɗe hannu a ƙirji zuciyarsa na harbawa, Ajlaal Sultaan kowa numfashi ya sauke yana mai lafewa a bayan matarsa tunani fal a zuciyarsa, kyakkyawan matashin dake zaune kusa da Gwamna ya runtse idanunsa. Tsoro da fargaba ya cika zuciyar ko wanne haifaffen ɗan Nijeriya dake zaune a hall ɗin. Idanun dubban jama'ar wajan ya sauka akan Majeederh da jikinta ya fara rawa ƙwaƙwalwarta ta tsaya cak kamar wacce akaiwa formatting. Malaman da suke lura da musabaƙar suka dinga kallon Majeederh cike da mamaki da tu'ajujji tunda ta fara babu gyaran da akai mata, babu shakka mu'ujizarsa Alkur'ani ce ta sauka akanta, hakan ya sa ta mancewa komai. A hankali ta kifa kanta cikin rauni ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ubangiji ka taimakeni kada na kunyata a idanun ƴan ƙasata" Da sauri wani malami ya yi mata alama data ɗauki ruwa ta sha, kasa yin musu ta yi ta ɗauki ruwan ta sha ta cikin liƙab ɗin fuskarta, a daidai lokacin kuma computer ta Kaɗa wanda yake alamanta mata cewa ta fita daga cikin lokacinta. Jikinta jama'ar wajan duk ya yi sanyi domin kowa ya ƙaddara Majeederh matsayin wacce za ta yi nasara ganin har zuwa zagaye na biyar ɗin ba a cita gyara ba, makinta ya fi na kowa saɓanin sauran da duk zagaye aci su gyara wajan biyu ko uku. Akai sanarwar tafiya break bayan an dawo za ayi Finally round wanda shi ne zagaye mafi wahala aka umarci gabaɗaya ɗaliban da suje su sha ruwa su huta.
A sanyaye Majeederh ta tashi juwa na ɗaukanta Ƙhulud na ganin haka ta miƙe cikin sauri ta ƙarasa ta ce "Mu je ki huta" Majeederh ta tsorawa Ƙhulud Arzaan idanu kasa magana tayi sai jikin Ƙhulud data faɗa ta ƙanƙame tana sauke numfashi, da ace taga idanun wani ahhali nata da babu shakka ta ji sauƙin abinda take ji a zuciya, amma ƙaddara ce haka babu kowa nata a wajan da zata iya raɓar shi ta ji sanyi. "Ba zan iya fa, I alrdy told them"
Ƙhulud ta ce "Zaki iya, kina da cikakken lokaci"
Ta faɗa tana rungume Majeederh. Daga gefe suka ji an ce "Daman dai Nijeriya ai ta saba samun failing, bata taɓa winning ba ko sau ɗaya, babbar matsalar sun ɗauki daƙiƙiya matsayin wacce zata wakilce su" Ya taɓe baki ya ce "Goodness, please Maa step down for Juwaira ki barwa Qatar domin baki da ilimin cin gasar Alkur'ani ta duniya, actually baki da shi, baki cancanta ba"
Ba Majeederh ba, hatta Ƙhulud ta girgiza da jin maganar kai tsaye ta fahimci mamallakin muryar ta juya suka haɗa idanu da Ajlaal ta ce
"Kalb, Majeederh ce fa? Ita ce Daƙiƙiya?? Duk ciki ita kaɗai ce ba aiwa gyara ba, me ya sa?" Ajlaal idanunsa akan Majeederh da kanta ke ƙasa ya fahimci yadda maganarsa ta yi tasiri a zuciyarsa musamman da yaga jikinta na rawa
"Ita fa, ni muryarta ce ma ta firgitar dani wallahi, karatu sakaka kamar zubar ruwan sama, Asstagafirullah gaskiya Nijeriya akwai saura gashi sun saka hope kuma za su yi failing" Ajlaal Sultaan ya sake faɗa yana lumshe idanu. Ƙhulud ta kafe shi da idanu ta kasa fahimta yanayinsa, bata taɓa jin ya yi magana mai tsayin haka ba, a rarrabe yake yinta. "Me ta yi maka da zaka jefe ta da wannan maganar Ajlaal Sultaan? Da zaka wulaƙanta ta?" Ya watsa hannu irin ko a jikinsa ya ce "I don't know what comes over me, amma na ji kamar bata yi mini ba, ina bala'in son mace mai tsayawa akan nasara wacce bata yarda da faɗuwa ba, Sorry Nigeria" Ya yi gaba
"Meke damun Ajlaal?" Ƙhulud ta furta tana binsa da kallo ganin yadda yake tafiya kamar bai so. Majeederh kasa motsi ta yi maganganun Ajlaal suka zauna daram a zuciyarta tare da yi mata amsa kuwwa! Ta ji jarumta ya zo mata, komai na kanta ya dawo fresh, Ƙhulud za ta yi magana Majeederh ta girgiza kai tana ɗan yi murmushi "Babu komai"
Majeederh ta faɗa a taushashe tana nufar wani corridor, duk abinda yake faruwa akan idanun Captain Alpha daya jingina yana kuma jin komai deep down na zuciyarsa godiya yakewa Ajlaal yasan Majeederh ta tsani ace bata da ilimi ko a jefata da kalmar _“Kasawa”_ Ya yi murmushi kawai yana ɗauke kansa gefe guda. Majeederh ta buɗe bottle water mai sanyi ta shanye tas, a hankali ta shiga safa da marwa idanunta rufe, idan ta ja numfashi sai ta sauke. Tana tsaye Wani malami ya ce "Ki nutsu, tunda kin fahimci weakness na ki sai ki kiyaye kallon mutane, mu je lokaci ya yi" Ta jinjina kai har yanzu idanunta rufe yana gaba tana binsa a baya. Cikar da hall ɗin ya yi har yafi na baya, kanta a ƙasa ta nemi wajan zamanta a hankali girgiza cinyarta idanunta rufe. Rabin jama'ar wajan idanunsa yana kanta mamakin yadda sauran ɗaliban aka rufesu malamai da jagororin ƙasar su, ita kuma ba kowa. Ɗaya bayan ɗaya aka fara gabatar da final round babu ƙasar data tsallake sai da suka sha gyara, gyara kuma na ban mamaki har aka zagayo kan Majeederh. Ta runtse idanu jin computer na gabanta ya yi ƙara kafin ta ji computer ta ce. "الله"
"Ma hukumu?" Ma'ana hukuncin kalmar Allahu.
Ta sauke ajjiyar zuciya a taushashe cikin sanyin murya mai daɗi ta ce
"Tafkimun laámun ismul jalala" Computer ta nuna blue alamar “Mumtaz" ta yi daidai aka ci-gaba da yi mata tambayoyi na Alkur'ani kafin daga bisani aja mata aya
“Allah taziru waá zirataán uƙƙurrah" Ba sunan sura ba number aya kawai ita ce zatai tunanin wacce surah ce. Ta yi shiru ta rufe Idanunta tare da dunƙule hannu exlty yadda take yi idan tana haddar Alkur'ani.
Ajlaal dake hakimce saman kyakkyawar kujera ya zubawa Majeederh Idanu, haka Aliyu da shigowar shi kenan sai Alpha daya kasa Kallonta, matashin saurayi kuma ƙanƙame jikinsa ya yi waje guda.... Daga can ƙasa Nijeriya gabaɗaya Khan family ne zaune a babban parlourn gidan Uncle Isma'il, sun tisa plasma a gaba tsoro ya cika zuciyar kowa musamman Abbu. Ba iya Khan family ba duk wani gida idan ka shiga kallon musaɓar suke live, wanda basu da t.v a rediyo suke saurara. Abbu ya saka hannu ya share zufar data gangaro masa, ya kasa zama waje guda ya gama tsara plan ɗin yadda zai yi da duk wata kyauta da kuɗin da Majeederh ta samu, amma da alama yarinyar baƙin ciki take masa yana da tabbacin ta iya mugunta ce kawai. Ba zai iya zama ya ji wannan abun ba ya nufi hanyar fita daga parlourn daidai nan ya ji sautin saukar muryarta a cikin kunnenshi wacce ta wadatu da zallar ƙira'a Tajwid mukarijil hurum, ta fitar da komai da karatun Alkur'ani yake buƙata ta saka komai cikin muhallinta. Cak Abbu ya tsaya yana washe baki farin ciki fal zuciyarsa. Uncle Isma'il, Uncle Isma'il Bello, Maman Alpha, Anti, Mami, Aaliyyah, Ruma, Raihana, Widad, Innati... E.t.c suka sanya kabbara.
Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Ajlaal Sultaan ya sauke yana tasbihi a ransa, Aliyu ya yi ƙasa da kansa hall ɗin tsit sautin ƙira'arta ne kawai yake tashi har computer ta tsayar da ita alamun lokaci ya yi. Lokacin daya shiga cikin kundin dairy ɗin Majeederh Abdul'aziz Khan, ta kasa tashi a hankali ta durƙoshe a wajan jikinta na ɓari rawa da ƙyarma wani irin raunataccen kuka ya ƙwace mata lokacin da alƙalai suka tabbatar da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Matsayin wacce ta zama Gwarzuwa a jerin ɗalibai sama da 100 wanda yake nufin Nigeria ta ƙwace kambon tarihi daga hannun Ƙasar Misira wanda sune su kai na ɗaya a shekarar data gabata. Shugaban ƙasar Nijeriya riƙe kai ya yi ashe kafin ya sauka da rabon a teniwarsa uwa Nigeria zata amsa wannan kambon? Sauran gwamnoni suka miƙe lokaci guda hadda gwamnan Kano suka shiga ɗaga hannu da kabbara, da sarkin Misira dana Saudiyya Sarki Sultaan suka nufi inda Majeederh Abdul'aziz Khan take durƙoshe, Zaytoon ta saka hannu ta ɗagota tare da jawota ta rungume tana cewa
"Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar ma sha Allah" Majeederh daman waje take nema domin ta kasa believing na nasarar data samu, ta ƙanƙame Zaytoon tana sakin wani mahaukacin kuka, She just wished that her parents were here to see her suga nasarar data samu, musamman Abbu burinsa ya fara cika. Ƴan jaridu gidan t.v da rediyo sukai kan Majeederh ɗaukarta suke ta ko'ina, lokacin da aka ɗauki wata farar hula ta silver aka saka mata tare da ɗaukan wani abu mai kama da Award na zallar tagulla aka bata wanda ya biyo ta hannun Sarki Sultaan, yin duniya ta cire liƙab ɗin taƙi haka aka dinga yi mata photo wanda kai tsaye ake watsa su a duniya, wasu mahaukatan kuɗi aka bata wanda ita kanta ba zata ce ga adadin su domin hankalinta baya kai tunaninta yana ga mahaifinta. Aka rataya mata sarƙa gold daga nan aka dinga mata kyauta wannan gwamna ya ce ya bata kaza wannan ya ce ya bata kaza, Shugaban ƙasar Nijeriya har yanzu kasa tantance me zai bata matsayin kyauta, duk abinda ya yi tunani sai yaga ya yi kaɗan. Kyautar kujerar Umara data hajji aka bata sarkin Makka ya ƙara bata kyautar kujerar hajji. Kana aka dinga photo lokacin da aka sanya mata albarka bata san mene ya faru ba, Majeederh ta samu kanta da wani irin jin girma wani abu mai girma ya hau kanta daga nan taro ya watse sai walimar da za ayi da daddare. Ƙhulud ta rungume Majeederh tana kuka murmushi kawai Majeederh ta yi tare da bubbuga bayanta a hankali ta ce "Ina mijinki?"
"Yana wajan takawa" cewar Ƙhulud, Majeederh ta ce "Rakani" Da sauri Ƙhulud ta kama hannun Majeederh suka isa wajan Ajlaal na tsaya rungume da Zaytoon da yake tsokanarta Majeederh ta tsaya kanta a ƙasa Zaytoon ta ce
"Ba dai ita ce wacce kike bani labari ba?"
“.... Ita ce Grandma”
"Ma sha Allah, na yi farin ciki ina alfahari dake da ƙasarku" Murmushi Majeederh ta yi ta ce "Na gode Mama" Zaytoon ta ce "Laa, wacce irin Mama bayan zan iya jika dake?" Ta yi murmushi kawai Ajlaal dai yana lafe da bayan Zaytoon ya kasa Kallon Majeederh ya ji ta ce "Thank you"
"For?" Ajlaal ya tambaya yana gyara tsaiwa ta ce "Kai ne ka ƙarfafa mini qiwwa na kasa mance kalmar Daƙiƙiya" Ajlaal ya ɗan shafa gemunsa ya ce "Congratulations"
Yana faɗin hakan ya bar wajan. Bayan sun fito tana ƙoƙarin shiga mota domin komawa gidansu ta ji ance "Hawwa'u"
Cak ta tsaya ta kasa tuna inda ta ji muryar ta juya, yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu sanye da wani tissue ɗin farin yadi ƙal da shi ta yi murmushi ta ce "Aliyu"
Ya yi jim domin bai ɗauka ta san sunan shi ba ya ce "Congratulations Hawwa'u ko wani zai nuna mini farin ciki ina tunanin bayan Abbu ne" Kafin Majeederh ta yi magana aka ce "A sbd kai ne wa?" Majeederh ta ware idanu ganin Captain Alpha bakinta na rawa ta ce "Yaya?" Ya ware mata idanu ya ce "Me kike? Yana da kyau ki huta" Ta ce "Ayya yau ai bana iya bacci, Aliyu baka da lafiya?" Aliyu dai bai ce komai ba sai kafeta da idanu da yake ya ce "Congratulations once again, take this matsayin nawa gift ɗin" Ya dubi hannunsa ta box ne ɗan ƙarami ta ce "No thank you, hakan ma ma gode sosai" Calmly ya taka har inda take ya ce "Please, ki amsa kamar yadda kika amshi ta kowa" Tana ƙoƙarin amsa Alpha ya karɓa ya ce "Mun gode, let's go" Majeederh bata ji daɗi ba amma haka ta daure ta ce "Jazakallah-bil khair, ina Latifa Omar? Kun yi aure hala?" Ta faɗa cikin muryarta wacce ta juye bai amsata ba ya juya kawai tare da barin wajan. Majeederh ta shiga mota Alpha ya shiga baya kusa da ita, driver ya ja suna tafe ya buɗe box ɗin wani ɗan ƙaramin ring ne mai kyau sosai, sai wani farin tissue da akai rubuta cikin good handwritten a hankali ya fara karantawa da sauri kuma ya tura tissue ɗin cikin aljihu ya maida ring ɗin yana tafe baki. Har Magriba Majeederh na tare da yayanta Alpha sosai tayi farin ciki, har akai walima. Ƙarfe 12 na dare ta buɗe wayarta message kamar hauka musamman daga wajan Aaliyah da Anti cikin sauri ta dinga dubawa ko za taga na Abbu domin tasan he's the first person da zai cnrgt nata amma har ta gama dubawa babu nasa jikinta ya yi sanyi a hankali ta danna number Abbu ringing ɗin farko ya ɗaga ta ce "Assalamu alaiyka Ya Abbu" Abbu ya ce "Majeederh na ji labarin irin kuɗaɗen da kika samu, da na yi lissafi sun haura miliyan 20 banda kujerar makkan " Sosai abin ya bata mamaki ta ɗauka zai farin ciki ya sanya mata albarka kan nasarar data samu amma sai ta ji babu batun hakan a bakinsa maganar kuɗi kawai yake? Ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Ban san nawa bane Abbu, amma dai da yawa" Abbu ya ce "To da kyau ai tuni na lissafa, a hakanma banda kuɗin albashinki" Ta jinjina kai idanunta cike da hawaye wanda ya fara sakkowa saman fuskarta ta ce "Abbu ka shirya tafiya aikin hajji, ni ma zani Uncle Isma'il da Mami su je Umara" Abbu ya yi zumbur ya miƙe daga zaune ta cikin wayar ya ce "Ashe Majeederh baki da hankali baki da wayo?" Muryarta na rawa sosai ta ce "Me na yi Abbu? Ka yi haƙuri don Allah" Ya ce "Daga ni harke har su Uncle Isma'il ɗin da ita Asaben babu mai zuwa ko nan da airport balle aikin hajji, siyar da su za ayi a haɗe kan kuɗin tas" Majeederh ta ware Idanu while hawaye na zuba a fuskarta ta rufe bakinta ta kasa cewa komai "Hawwa'u?" Muryarta na rawa ta ce "Na'am Abbu?" Ya ce "Kuka zaki akan na ce haka? Shikenan riƙe kuɗaɗenki" Da sauri ta girgiza kai tana zubewa saman gwiwoyinta jikinta na rawa ta ce "Ka yafe mini Abbu wlh ba kuka nake ba, idan kukanne ma na farin ciki nake, na bar maka kuɗin halak makal ko biyar ba zan ɗauka ba, amma don girman Allah Abbu ko kai ɗaya ne ka je aikin hajjin idan ya so sai a siyar da sauran"
Abbu ya girgiza kai ya ce
"A'a ai tas za a siyar da su, nan gaba sai ki sama mini kuɗin da zan je aikin hajjin hakan ya fi ko?" Ta jinjina kanta ita gabaɗaya ba ruwanta da kuɗin ba shi take buƙata ba burinta kawai ta ji ya ce "Majeederh Allah ya yi miki Albarka" Wannan kalmar ita kawai take buƙatar ji, babu uwar da zata sanya mata albarka uban kuma bai damu ba. Abbu ya ce "To sai anjima aci gaba da ƙoƙarin adana kuɗi banda ɓarnatarwa" Kafin ta yi magana ya kashe wayar, sakin wayar ta yi tare da durƙoshewa ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita tana buƙatar sanya albarka ko sau ɗaya ne idanunta ya kumbura sosai da ƙyar ta iya kiran Uncle Isma'il ya yi mata addu'a haka Uncle Bello ta kira Anti da Mama kana ta kira Mami sai Aaliyyah ji tayi duniyar ta yi mata zafi komai ya jirkice mata bacci ya ƙauracewa idanunta...... Majeederh ta tattara komai ta ajjiye waje guda karatu take sosai, shaƙuwa sukai sosai da Ƙhulud Arzaan Ajlaal kuma basu taɓa magana ba tun ranar, duk wata sai ta turawa Abbu kuɗi bata san me yake da su ba, Majeederh kullum cikin azumi take ta rame sai ɗan jiki fatarta ya goge sosai, zamanta da Ƙhulud ya ƙara sawa ta zama wayayyiya sosai rashin magana ya ninka nata, tun a lokacin da Abbu ya ja mata kunne ta cire batun aure a ranta, tun tana sha'awar yi har ta fice mata a rai, ta sanyawa ranta ba zata taɓa yin aure ba, duba da cewa tun a lokacin babu wanda ya ƙara cewa yana sonta, a shekarar ƙarshe ta zanna jarrabawa mai kyau ta samu first class tayi farin ciki sosai ta zama cikakkiyar Malamar addinin Muslunci ga tarin magoya baya da take da shi a facebook ta fara faɗakarwa akan maza da mata kamar yadda taga Fauziyya d sulaiman tana yi....
*After 8 year's.... Nigeria*
Aminu Kano airport...30
*After 8 year's.... Nigeria*
Misalin ƙarfe 6 na yamma jirgin sama na Emirates ya sauka a fili tashi da saukar jirgi na Aminu Kano airport, mai ɗauke ɗaliban ƙasar wanda suka kammala karatun su na scholarship da gwamnatin baya ta samar musu. Ɗalibai ne suka ta sakkowa maza da mata ko wanne fuskarsa ɗauke da wani irin farin ciki bayan shekaru takwas yau sun dawo ga iyayensu. "I couldn't believe Aunt Jeederh would come back from Egypt today" cewar Aaliyyah daga gefe aka ce "Me ya sa?" Ta kalleta "Haka nan" Aaliyah ta bawa Widad amsa. Ko wanne banza idanu yake yaga ta ina Malama Majeederh zata fito... Jawaad ɗan gidan Anti da Uncle Isma'il ya ce "Finally" Jin hakan yasa gabaɗaya suka kalli direction ɗin jirgin inda ake sakkowa. A hankali take sakkowa kanta a ƙasa tana sanye da wata Abaya ruwan sararin samaniya wacce akaiwa feshin dutsuna na masu ruwan huda, tayi rolling kanta da vail sai liƙab ɗin data sanya a fuska da wani sirrin farin photochromic ɗin Glasses a Idanunta. Hannunta ɗaya yana jan ƙatuwar trolley ɗinta ɗaya kuma riƙe da hand bag a nutse take sakkowa, lokacin data sakko ta tsaya cak ta lumshe idanu sbd wani daɗi daya ratsa, farin ciki ya wanzu a zuciyarta. Da ace tana da iko kuma zata iya da buɗe fuska za ta yi ta shaƙi ƙamshin iskar ƙasarta wacce rabonta da ita shekara takwas kenan, tun tana shekara ashirin a duniya yanzu kuma tana dab da cika shekaru talatin domin kaɗan ne ya rage mata 28 take yanzu going to 29 tunda end of the year suka kammala Final exm.
"Ma sha Allah" Majeederh ta furta cikin lallausar murya. A hankali ta shiga rarraba idanu taga ko akwai wanda ya zo tafiya da ita, domin komai ya sauya mata. Ihu ta ji an kurma tare da ƙanƙameta ana faɗin "Wlcm back Anti Jeederh" Majeederh ta ware idanunta akan Aaliyah cike da mamakin ganin yadda ta girma sosai ta yi murmushi tana hugging nata back.
"Sannu da dawowa ƙasa Nigeria" Widad ta furta murmushi kawai Jeederh take sbd tsantsar farin ciki. A hankali ta ɗaga kanta sai a lokacin taga tarin jama'ar da suka zo tafiya da ita, Anti, Ruma da Raihana sai Jawaad da Uncle Isma'il da Innati. Ta dinga ware idanu ko za taga Abbu amma babu shi sai jikinta ya yi sanyi. Tana zuwa Ta faɗa jikin Anti ta ce "Na yi kewa Anti"
"Mu ma mun yi rashin yarinyar arziƙi barka da dawowa" A hankali ta dinga bin kowa tana bashi hug Uncle Isma'il ya shafa kan Majeederh ya ce "Kin zama abin alfahari, Ubangiji ya baki zuri'a masu hali irin naki" Majeederh ta kalli Uncle Isma'il a ranta tana maimaita kalamar "Zuri'a" Ganin motoci har guda huɗu duk na familynsu ya bawa Majeederh mmki musamman da taga Ruma ta shiga wata kuma matsayin driver, motar Uncle Isma'il ta shiga ita da Anti a baya sauranma duk suka shiga mota, On their way back home, Majeederh kept looking at the road, everything has changed for her since she went to Egypt until now, eight years after returning. Ta ɗan ware idanu ta ce "Yaushe akai wannan a Government house?" Anti ta ce "Mefa?" Ta nuna musu roundabout Uncle Isma'il ya ce "Bayan tafiyarki da shekaru biyu, gwamanti data sauka" Ta jinjina kai Calmly ta ce
"Amma kamar ba hanyar gida ba, ko ni ce na manta?" Anti ta yi murmushi ta ce "Daman kam za a sha tambaya, nan ai hanyar Lodge Road ne bari mu ƙarasa za kiga komai" Murmushi kawai Majeederh ta yi tana jin sauƙi a ranta ganinta kusa da ƴan uwa shi ya sa bakin nata ya buɗe a taushashe ta ce
"Uncle yanzu ya yanayin garin yake, waye Governor da mataimaki?" Uncle Isma'il ya ce "Engineer Dr. Muhseen Bagayya" Ta yi saurin cewa "A'a ai daman shi ne Governor har lokacin dana bar ƙasar" Uncle Isma'il ya ce "Yes, ai shekara takwas ya yi yanzu ake ƙoƙarin yin zaɓe duk sun tashi hankali"
"Kenan wanne jam'iyyu ne?" Uncle Isma'il ya ce
"Yaushe Hawwa'u ta zama Talkative ne? zamanta a Egypt?" Murmushi kawai ta yi Anti ta ce "A'a ka barta ta tambaya ai ta zama maƙowa, kuma tana da ikon sani ai" Majeederh bata ƙara cewa komai ba har suka isa Lodge Road suka isa street ɗin da zai kai su har gida, Majeederh ta waro idanu waje ganin sun nufi wani tamfatsetsen gida mai mugun kyau, ta kasa ɗauke Idanunta daga gidan domin kaf unguwar babu na biyun gidan, gida ne iya gida 200by 200. Uncle Isma'il ya danna horn gatekeeper ya miƙe da sauri yana buɗe musu, shi kansa jikinsa rawa yake yau zai ga Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Mamaki bai gama sakin Majeederh ba idanunta ya sauka akan wasu lafiyayyiyun motoci na alfarma har guda huɗu a rumfar ajjiye motoci. Parking Uncle Isma'il ya yi yana fitowa Anti ta buɗe ta fito, a hankali Majeederh ta fito tana lumshe idanunta tare da bin cikin compound ɗin da kallo, a hankali kuma sauran motocin suka shigo. Aaliyyah ta kalli yadda Majeederh ke kallon komai ta ce
"Mamaki ko?" Ta jinjina kai Aaliyah ta ce "Ai zaki sha labari" Gabaɗaya suka shiga gidan a Main parlour suka zauna ita dai Majeederh kallon komai take cike da mamaki. "Ya kamata a cire mana liƙab ɗin" In ji Ruma murmushi ta yi ta cire liƙab ɗin, Gabaɗaya suka tsora mata idanu ta waro nata ta ce "Lafiya?"
"Wallahi baki da maraba da Balarabiya Anti Jeederh kin ga mahaukacin kyan da ki kai, sa maza hatsari a titi" Majeederh ta ce "Kyau ya zama Annoba idan har za ai accident" Suka saki dariya Mami ta ce "A bar mini ƴa ta huta haka nan, ta ci abinci" Innati ta ce "Azaba ji munari nabi abinci da gudu ba wando" Aaliyah ta fasa ihu ta ce "Rufa mana asiri ki saka wando" Innati ta ƙanƙance idanu ta ce "Da ubanki kike mara zuciyar nan, mai yawa ƙasa ƙasa yawan kasuwanci, ƴar banza da idanu fiƙi-fiƙi kamar malafar kwaɗo" Aaliyah ta murguɗa baki ta ce "Bani da lokacinki, Allah ya sa kiga fatalwa yau" Tsit Innati ta yi bata sakewa cewa komai ba. Anti ta sassauta murya ta ce "Majeederh jeki wanka ki sallah kici abinci" Ta marairaice fuska ta ce "To ban san ina zan shiga ba" Ruma ta ce "Zaman house ya dawo kenan" Ba wanda ya kalleta Aaliyah taiwa Majeederh jagora zuwa wani part mai kyau sosai da tsari With so much surprise ya dinga kallon komai kana ta cire kaya ta shiga bathroom a hankali ta saukewa kanta shower tana sauke numfashi, ta ɗaura alwala wata duguwar riga mai sauƙin nauyi ta saka, ta saka hijabi bayan tayi sallah ta ɗauki vail tare da rolling kanta kana ta nufi main parlour duk suna zaune saman dining area ta ƙarasa tare da jan kujera ta zauna. Spoon ɗin kawai take juyawa ta kasa cin abincin can dai ta runtse idanu ta ɗan ci kaɗan. Innati ta ce "Shi ya sa kike kamar kazar matsiyata firit a fige ba tsiya ba arziƙi, tirrr" Hira aka dinga yi har su Anti suka yi sallama tare da komawa gida.
Misalin 12:30 na dare Majeederh da Aaliyyah na zaune saman gado Aaliyah ta ce "Bayan tafiyarki babu jimawa Abbu ya ce za a rushe wancan gidan namu a yi sabo, ya ce kuɗi ya samu sama da miliyan biyar, ni dai ban ce komai ba ban kuma nemi sani ba, sbd i don't have any business with that, kuma ubanwa ya bani ikon tambayar inda ya samu kuɗin ma? Muka tattara gabaɗaya muka koma Gidan Uncle Isma'il Mami Kuma da Ruma suka tafi can dangin Mami, ba a ɗauki lokaci ba aka gina gida haɗaɗɗe aka dinga surutu a unguwa ina Abbu ya samu kuɗi shi ba sana'a ba?? Ya yi burus dai a lokacin akai bikin Ruma da Imran sai Raihana......,"
"Amma na gansu gida?" Majeederh ta katse Aaliyah da faɗin hakan ta ce "I have no idea, amma idan suka zo gida sai su yi wata gudu wai mazajan nasu basa gari" Majeederh bata ce komai ba, Aaliyah ta ɗora da cewa "Daga nan kuma Abbu ya buɗe shago a kantin kwari ya zuba kaya da yara masu kula da komai, ya ɗinka sutturu kamar yaƙi, lokacin da kika samu nasara a Misira da bayan wata huɗu ya ce gabaɗaya tashi za mu yi daga gidan nan zamu koma Lodge Road, haka muka koma bamu da wani option, shekarunki uku da tafiya akai bikin Anti Latifa" Majeederh ta waro idanu waje cike da mamaki sosai kafin ta yi magana Aaliyah ta ce "Wallahi anyi bikin bayan jinyar da Yaya Aliyu ya yi a ƙasar waje tsayin shekaru biyu, to bayan ya dawo akai bikin" Majeederh ta sauke numfashi ta ce "Ikon Allah, ina aka kaita?"...... "Gata nan kusa damu, ita ce neighbor namu fa" Majeederh kamar ƙaramar yarinya tai zuru ta ce "How?" Aaliyah ta ce "Good, bamu san mene ya faru ba daman akwai gida kusa damu dake duk kusan gidan haya ne na masu kuɗi kawai sai mu kaga ana fara gyara, daga nan ne Latifa take cewa Aliyu ne ya ce nan zai zauna yafi kusa da wajan aikinsa, ana yin bikin ya ta tare, amma a ranar auren ana ɗaura auren Aliyu ya tafi Cairo ƙaro karatu maganar da nake jiya ya dawo cikin dare" A gajarce Majeederh ta ce "Allah ya sa albarka, ke fa?" Aaliyah ta zaro idanu ta ce "Tab ai nayi al'ƙawari sai kin yi aure zan yi" Majeederh bata ce komai ba ta yi shiru da sauri ta ce "Abbu bai dawo ba?" Ta ce "Kai ai tun 7 ya shigo gida, baku gaisa ba?" Majeederh ta yi shiru kawai.
"Na manta ban faɗa miki ba" Aaliyah ta gyara zama ta ce "Bro Alpha an ƙara masa matsayi daga Captain zuwa General" Majeederh ta ce "Ma sha Allah, Allah ya riƙa" Daga nan Aaliyah ta nufi ɗakinta ba don ta so ba.
A hankali Majeederh ta miƙe tsaye tare da ɗaukan hijabi hankalinta yana kan Abbu shi kawai take son gani, taga ya mahaifin nata yake? Kai tsaye part ɗin da aka nuna mata aka ce shi ne nashi ta nufa, sosai part ɗin ya haɗu iya haɗuwa gashi parlourn farko ta gansa buɗe da dinga kallon komai cike da sha'awa da mmki, ganin baya parlourn ta shiga wata ƙofa da zai kai ta ɗaya parlourn wanda daga shi sai bedroom, ta tsaya cak tare da yin knocking ta ɗauki good 10 minutes tana knocking kafin cikin faɗa aka ce "Who is there?"
"Majeederh ce, Abbu"
Abbu ya maimaita "Majeederh?" Ta ce "Eh" muryarta duk rawa take gefe guda kuma farin ciki take zata saka mahaifinta a Idanunta can ta ji ya ce "To ya akai?" Sosai tambayar ta bata mamaki da tsoro ta ce "A'a daman tunda na dawo ban ganka ba, ina ta duba ka ina so mu gaisa" Daga cikin parlourn Abbu yana zaune saman lallausan kujera watching TV hannunsa riƙe da cup yana shan black tea ya ce "Ok bani da lokaci zuwa safiya" Majeederh kamar zata zunduma ihu sbd abin da ya tsaya mata cikin rauni ta ce "Please naga kowa banda kai, shekara 8 ban ganka ba" A ɗan hassale ya ce "Ok na bar abinda nake na fito ki ganni kenan ko Hawwa'u? Bani na ce ki bari sai safiya ba, ni ma ina da buƙatar ganin naki" A sanyaye ta ce "Kayi haƙuri" Tana faɗin hakan ta nufi part ɗinta. Waje ta nema ta zauna a saman bed tana cusa hannunta a tsakanin cinyoyinta tare da yin shiru tana girgiza ƙafa, ita kanta ba zata iya cewa ga abinda take tunani ba.....
Washegari misalin 7 na safe Majeederh ta fito tana mustsike idanu sbd baccin daya ɗauketa bayan sallar asuba, ta ci karo da Mami ta ce "Ina kwana?" Mami ta kalleta sosai ta ce "lafiya, me ya samu idanun naki?" Majeederh ta ɗan yatsuna fuska ta ce "Sometimes ya yi ta mini zafi, wani lokaci kuma ban fiya gani ba musamman duhu" Mami ta ce "Kuma Kinga Dr?"
"Eh" Ta bawa Mami amsa a gajarce, Mami ta ce "Result?" Majeederh ta kalli Mami da idanunta ya fara yin ja ta ce "Wai yawan karatu da nake hasken littafi dana computer wajan Research, amma an bani medical Glasses bayan an yanka daidai idanuna sai drugs" Cikin damuwa da alhini Mami ta ce "Subuhanallahi, Allah ya sauwaƙe yanzu dai sai ki haƙura da wasu abubuwan ki huta sosai ki rage duba wayar ko?" Ta jinjina kai a sanyaye kamar jin tsoro ta ce "Abbu fa?" Mami ta ce "Ai tun 6 ya fita wai yana da appointment da wani" Sai duk jikinta ya yi sanyi ta juya zuwa bedroom. Wajan 12 tana zaune wayarta data saka line ɗin Nigeria ya fara ƙara, ganin sunan Latifa Omar ya sa ta ɗan yi cute smile tana answering "Amarya" Latifa Omar ta ce "Ke dilla wacce amarya, ai mun zama tsofaffin hannu" Majeederh bata ce komai ba "Ya hanya? Da Misira da kuma baƙunta?" A taushashe ta ce "Allahamdulillah" Latifa Omar ta ce "Please ki zo mana, ni ban tambayi Sweetheart ba, kuma he alrdy left" Majeederh kamar bata gane ba ta ce "Nazo ina?"
"Wallahi kin gane" Ta yi shiru, Aliyu dake zaune a kujerar dake facing Latifa ya yi mata nuni da hannu ta cewa Majeederh bata jin daɗi ne da tuni ta shigo don Allah ita ta zo, Latifa ta kanne masa idanu ta ce "An gama Sweetheart" Majeederh ta ce "Me?"Latifa ta yi saurin rufe baki ta ce "Wallahi bani da Lafiya ne da tuni na shigo kema ai kinsan ba zan iya jira har haka ba, shekaru takwas ba kwana takwas ba" Majeederh ta ce "Ok" Tana ta zaune sai da ta yi sallar zhur kana ta yi wanka ta shirya cikin abaya ruwan toka tayi rolling kana ta saka Liƙab ta nufi fita daga cikin gidan, mai gadi jikinsa na rawa ya dinga gaida Majeederh murmushi kawai take masa, tana fita ta nufi gate ɗin gidan da akace na Latifa ne. Latifa Omar duk a hargitse take ta shiga gyara parlourn cikin sauri tana fesa air-condition Aliyu dai na zaune cike da mmki yana binta da kallo, yana ƙoƙarin magana ya ji knocking Aliyu ya saka hannu ya danne saitin zuciyarsa yadda take bugawa da ƙarfi ya san cewa ita ce, tabbas Majeederh ce "In"
Ya ce, ta murɗa handle ta shigo cikin sassanyar muryarta mai tasiri a zuciyarsa tana ƙarasa shigowa yana miƙewa tsaye ya zuba duka hannu a aljihu idanunsa kafe a kanta da ɗan sassarfa cikin sauri ya nufi inda take tsaye hakan yasa ta gwalo ido tare da haɗe fuska...
Ƙilan sai bayan sallah🤓 Idan Allah ya saka mini shauƙi kuma ku gani gobe, a samu masu kawo mini naman sallah da barka da sallah domin za ni ƙasa mai tsarki na roƙawa Abbu ya fiyar Ubangiji Allah ya shirya ya ɗangwalawa zuciyarsa tausayin Jeena🙁.... Masu karantawa As free common baby an daina yayin haka ki waye ki biya a saka ki grp albarkacin wannan ranar🙏🏿
Allah ya amshi tubanmu, ya gafartama ya kyauta makwancin wanda suka gabace mu😪 0811923761631
Aliyu na zuwa ya bi ta gefenta ya shige da sauri, a hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana ɗan juya idanunta, fita ya yi waje can wajan mai gadi ya nemi waje ya zauna yana riƙe kansa. Ayuba ya ce "Yallaɓai lafiya? Yau kai ne zaune a nan?" Aliyu ya kasa cewa komai sai numfashi da yake saukewa, lokacin da idanunsa ya sauka akanta tunaninsa ne ya tsaya, amma yana ƙarasawa inda take sai yaga ta rikiɗe masa. "Yallaɓai" Maganar Ayuba ta dawo da Aliyu ya yi saurin ware idanu a hankali ya ce "Ka ce me?"
"Na ganka a firgice, kamar baka cikin nutsuwarka?" Aliyu ya shafa kansa yana mai miƙewa tsaye hannunsa zube cikin Aljihu ya ce "No...."
"Ka tabbata?" Cewar Mai gadin Aliyu ya girgiza kai ya ce "Goodness, lafiya nake" Ayuba ya washe baki ya ce "To... To ma sha Allah, ai yanzu naga magidanciya ta shige wallahi nutsastsiyya da ita kana ganin idanunta kaga Balarabiya amma ta bani tsoro kamar mai idanun maciji ko mage" A ɗan hargitse Aliyu ya dubi mai gadin nasa ya ce "Okay daman sa idanu kake zama yi ba gadi ba? Har kake description ɗin how beauty she's?" Mai gadin ya zaro idanu ya ce "Kwarankwatsa ba saka idanu nake ba"
"Ok munafurci ne?" Aliyu ya faɗa yana saita kansa domin nan da nan ya ji ransa ya ɓaci, shi dai Ayuba bai ce komai ba.
"This is the first and last time da zaka ke sakawa mace idanu more especially ita" Ayuba ya gwalo idanu ya ce "Yallaɓai da dai kayi mini da Hausa, wallahi ban ji komai ba banda ok, Daƙiƙe ne ni na ajin ƙarshe" Aliyu bashi da mood ɗin yin dariya. Rai ɓace ya ce "Ai kowa naga alama, ka tabbatar ka iya turanci domin I will not live with an uneducated and poor person in my house" Ayuba ya ce
"Turanci fa kace?" Ayuba ya ƙara dafe ƙirji ya ce "Turanci? Dai irin wanda na ji kana yi to wallahi ko A..B..C sai na yi da gaske zan iya, ni dai ka rufa mini asiri" Aliyu dai bai sake furta komai ba ya juya zuwa garden na gidan.... Majeederh ta ɗan buɗe idanu akan Latifa ta ce "Ba dai a haka kike zaune ba?" Da alamar rashin fahimta Latifa ta ce "Kamar yaya kenan?" Majeederh ta kalli jikin Latifa tas, kaya ne haɗin bauta riga daban zani daban haka ɗan kwalin daban ta ce "Ina nufin haka" Ta faɗa tana nuna mata shigar jikinta, Latifa ta yi saroro sai kuma ta ce "Oh don mind me, zuwa anjima zan shirya kin san na ce miki bana jin daɗi" A taƙaice Majeederh ta ce
"Allah ya bada lafiya" Ta miƙe tsaye tana mayar da liƙab Latifa ta ce "Meye haka to kamar kurarriyya? Ba dai tafiya ba?" Majeederh dai ba tayi magana ba tana ƙoƙarin fita Aliyu yana shigowa bakinsa ɗauke da sallama. Ya kalli Latifa ya ce "Baƙuwa ki kai ne?" Ta ce "Baka nan ta shigo ne?" Ya ɗan ɗaga kafaɗa ya ce "Am in the garden" Ya nemi waje ya zauna idanunsa akan Majeederh kaɗan, Latifa tayi dry ta ce
"Nikam how long ka ɗauka ba kaga bestie ba?" A takaice ya ce "I can't remember."
Latifa ta zauna kusa da shi "8yrs going to 9 fa, tunda yanzu muna end of the year ne, gasky yau ya kamata ayi hirar yaushe gamo" Sosai Majeederh ta fahimci daga matar har mijin neman magana suke. Aliyu ya ce
"Bestienmu ina yini?"
A cikin nutsuwa a takaice ta ce "Allhamd, ya jiki?"
"Sai godiyar Ubangiji jiki"
Bata sake cewa komai ba ya juya kan Latifa ya ce "Wife yunwa ina ji sosai, wallahi kamar zan ci babu" Yadda ya langwaɓe kai da yanayin daya nuna yunwar yake ji da gaske kuma bashi da haƙuri akanta ya sanya Majeederh lumshe idanunta tunanin Little ya faɗo mata, ko yana raye ko ya mutu ko yana wacce duniya? Sai ta ji zuciyarta ta karaya ƙafarta tayi sanyi. Latifa Omar ta ce "Bestie taimakawa sweetheart da Superghetti"
"What?" Majeederh ta faɗa lokacin da maganar Latifa ya dawo da ita daga tunanin Ɗanta Little. "Kinga bana jin daɗi, warin gas hawar mini ka yake ki taimaka please ki dafawa Sweetheart wani abu" Majeederh ta zare idanu har sai dai Aliyu ya ɗan sauke numfashi kamar ba zatai magana ba sai kuma ta ce "Amma kin san am not your maid?"
"Mun sani" Aliyu ya ce
"Don Allah, please Bestie me" Latifa ta faɗa a marairaice. Tasan weakness na Majeederh da zarar ka haɗata da Allah magana ta ƙare, Majeederh ta ja gajeren tsaki kamar wacce akai forcing nata wajan magana ta ce "Kitchen"
A tare suka nufi Kitchen ɗin, Latifa na nuna mata ta dawo tare da zama kusa da Aliyu ya ɗan ja gefe da sauri ta ce "Me kuma?" Ya dubeta yana girgiza kai ya ce "Baki jin kunya?" Ta juya masa idanu alamar "Kunya? Akan me kuma"
Ya taɓe baki yana faɗin "Rayuwarki abar tausayi ce, ban yi zatonki haka ba gaskiya" Latifa ta ware Idanu akan Aliyu ta ce "Kayi mini bayani, bana fahimtar wannan zancen" Ya ce
“ina nufin ƙazantarki"
Latifa ta ce "Sbd ka ganta?" Cikin rashin fahimta ya ce "Wa kenan?" Ta yi masa shiru ya ce "Yanzu ke baki ji kunyar Hawwa'u ba? Riga daban, zani daban, abin kanki daban? Ƙamshin parlourn daban da warin da yake fitarwa daban? What exlty wrong with you Latifa? Haka zaki haifi yara kina wannan ƙazantar su tashi da abinda suke ganin kina yi?" Bakinta cike da yawo ta buɗe zatai magana ya yi saurin ɗauke kansa zuciyarsa na tashi.
"Oh! Daman fa haka ku maza kuke bazan kasan dalili banda cikin dake jikina har zaka ce haka?" Aliyu ya ɓata fuska ya ce "Sbd Allah duk matan da mazan su ke musu ciki haka suke wannan azababbiyar ƙazantar? Parlour warin yawo, part ɗinki haka nikam na shiga uku" Zata buɗe baki sai ga wayo zarara Aliyu ya yi saurin tashi ta juya kanta bayan kujera ta zubar da yawo ta ce
"Nikam ina yin iya bakin ƙoƙarina, baka da godiyar Ubangiji" Aliyu ya kasa cewa komai dan takaici can ya ce "Tun satin aurenmu ai haka kike, matsalolinki nada yawa idan zasu zan yi a zuciyata tsaf zata buga tunda na kawo abokaina suka ci abinci suka dinga amai na sare miki, ciki kuma wannan shi ne na biyu wancan ya zube wannan kuma sai ki kula zan kawo ƴar aiki kawai" Ta yi saurin miƙewa ta ce "Kan uban nan a wanne gidan zaka kawo ƴar aiki? Ai wallahi baka isa ba, tsohuwo ko yarinya bana mara ba da su, haka kurum a aure mini miji, matan yanzu da basu da mutumci kamar mayu haka suke akan mazajen wasu musamman yanzu da za a saka ƴan candy marriage, ina son ka ina Mahaukacin kishinka kai ka sani kuma......," Shiru tayi ganin Majeederh na shigowa cikin parlourn hannunta riƙe da wani kyakkyawan warmer wanda Latifa bata taɓa amfani da shi ba, Kullum a warmer ɗaya take zuba masa abinci idan tayi ma kenan. Latifa ta yi murmushi ta ce "Thank you Bestie sannu da aiki" Majeederh ta ɗora warmer ɗin akan table tana nuna tamkar bata jin Conversation ɗin su ba, Aliyu ya dinga satar Kallonta Majeederh na ƙoƙarin miƙewa Latifa ta ce "Ina zuwa"
Ganin ta nufi part ɗinta yasa Aliyu shafa cikinsa ya ce "Zuba mini please" Ta cikin liƙab ta harare shi sarai ya gani sai kawai ya shafa kansa yana jan plate tare da zubawa a ciki, sosai Superghgett take tashin ƙamshi gashi ta sha sadin, kasancewar kaɗan ta dafa kuma gas ne ga komai a zube ya sa cikin ƙaramin lokaci ta gama dafawa. Idanunsa ya rufe lokacin da daɗin abincin ya ratsa cikin kunnuwansa Gabaɗaya jijiyoyin da suke amsar saƙo zuwa ƙwaƙwalwar sun ɗauka tuni sun kaiwa tasa ziraya, cin abincin kawai yake hannu baka hannu kwarya har ya mance Majeederh ce gabansa, ya daɗe bai ci abincin mai daɗinsa ba. Ya goge bakinsa da tissue a hankali yana kallonta ya ce.
"Kin ceci rai" Ba tayi magana ba, ya saita murya ya ce "You're the best cooker Hawwa'u thank you" Miƙewa tayi bata jira zuwan Latifa ba tayi gaba abinta tare da ficewa daga parlour bakiɗaya... Shigowarta compound ɗin ya yi daidai da fitowar Abbu daga cikin mota, har zai tafi sai kuma ya tsaya yana Kallonta har ta ƙarasu, Majeederh na zuwa ta zube a ƙasa ta ce "Barka da dawowa Abbu, ina yini?" Ya dinga Kallonta kafin ya ce "Lafiya, daga ina?"
"Gidan Latifa..." Ta bashi amsa kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ya numfasa ya ce "Ki sameni a part ɗina" Yana faɗin hakan ya juya cikin gidansa nasa wanda ya zama sai mai hannu da shuni ne kawai iya gina gida kamarsa, iya compound na gidan abin kallo ne balle kuma ciki wanda duk sanadin ƴar cikinsa Majeederh ya same su ta tara masa kuɗi na ban mamaki. Lokacin data shiga main parlour tuni Abbu ya shige ɓangarensa Mami ce kawai zaune tana kallon shirin Mata a yau, ta shiga da sallama tana cire liƙab ɗin fuskarta tare da zama, Mami ta kalleta ta ce.
"Sai yanzu?" Ta ce "Eh" Ta ƙara cewa "Zaman me ki kai a gidan ma'aurata?" Kamar zatai shiru sai ta ce "Latifa bata jin daɗi shi ne naiwa mijinta girki" Da mamaki sosai Mami ke kallon Majeederh ta rasa ma me zata ce kafin ta ce
"Ba kiji nauyin cewa Aliyu ki kai abinci ba? Ba kiji nauyin furta kalmar nan ba? Mijin Aminiyyarki ki kai girki? Ban taɓa jin haka ba ko da wasa na Asabe" Mami ta ƙara tafa hannu ta ce "Sai kika shige madafa kika bar miji da mata a parlour suna jiran abinci" Majeederh kanta a ƙasa ita sam ba taga aibun hakan ba, tunda taimako ta yi Mami ta ce "To liƙab kika cire?" Ta girgiza kai ta ce "A'a" Sai a lokacin Mami ta sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya kafin ta ce "Na gode Allah" Miƙewa ta yi ta nufi part ɗinta, bayan ta shiga ta nufi toilet tare da yin wanka ta ɗaura alwala wata jallabiya ruwan toka ta saka mai yafin farin duwarwatsu bayan ta idar da sallar Asr tayi azkar idanunta rufe ta shiga tilawar Alkur'ani ta yi hakan ne sbd rashin abin yi kuma bata son yin baccin Asr, tana nan zaune Mami ta murɗa handle ɗin bedroom ɗin Majeederh ta shigo daga tsaye ta ce
"Zaki mana dinner" A sanyaye Majeederh ta ce "Mami kai na ciwo yake, tunda na dawo ban yi bacci ba, can ma ba bacci nake ba" Mami ta saki ƙofar ta shigo tare da zama saman gado ta kalli Majeederh ta ce
"Kenan Raihana ko Ruma zan kira daga gidan mazajen su suyi mana ko?"
"Sun tafi ne?" Cewar Majeederh, Mami ta ce "Da ke zasu tsaya su taya zaman gida bayan su Allah yaye musu wannan ƙaddarar? Majeederh shekarunki nawa yanzu ne?" Kanta a ƙasa zuciyarta na bugawa ta ce "28"
Mami ta ce "To da kyau tunda har kina lissafe, Sahar a gabanki aka haifeta yanzu yaranta huɗu cif, Widad a gabanki aka haifeta haihuwa ta uku ta biyu za tayi a hakan ma don Allah bai bata da wuri bane, Raihana, Ruma duk akan idanunki aka haife su ita Ruma cikin ne baya zama, ita Raihana Allah ne bai bata ba, duk wannan ba zai sanya kiwa kanki karatun tanatsu ba Hawwa'u? Me kike nema a duniya, kina da kyau, kina da iliminki, kina da kuɗi mene ya yi saura?"
Majeederh ta kalli Mami jin ta ce tana da kuɗi, bayan ko ƙwandala bata da shi da sunan mallakinta, komai data mallaka a Misira ta sallamawa Abbu. Mami ta gyara zama ta ce
"To na fara gajiya nikam, gashi nan jama'ar gari sun fara zagina da ƙana nan gulmace-gulmace akan wai an tura ki neman kuɗi ba wani karatu da kike, wasu ma cewa suke neman maza kike gashi nan baki aure ba, kuma bama ta kuraki akan aure kina neman tsofe mana a gida" Tunda ta fara magana Majeederh ta kafe Mami da manyan idanunta wanda gefe ɗaya ya yi ja sbd ciwo Kallon nata kawai take amma tunaninta yana wani waje guda, kalmar neman maza ta girgiza Majeederh ta kasa fahimtar wake neman mazan? "Kina jina?"
"Wake neman maza?" Majeederh ta faɗa muryarta na rawa Mami ta bata amsa da "Ke mana, kuma dai bani da shaida akan ki ɗana ne ka haifa baka haifi halinsa ba, tunda gashi sam baki damu da rashin auren naki ba" Kalma “Zina” babbar kalma ce wacce a duniya ta tsaneta balle mai aikata yinta amma ita ake ƙoƙarin laƙabawa wannan muguwar kalmar? Bayan data aikata zini gwara ta kashe kanta kawai ta huta, da zina zatai ko yawan bin maza ai tun kafin tabar ƙasar zata fara sbd abinda ke damunta, sai yanzu ne da Allah ya ye mata dukkan wani abu da take ji zata fara zina? Bayan shi isn't interested at all! Ɗigon sha'awa yanzu babu a tare da ita, ta wannan ɓangaren har mancewa take ita ɗiya macace?... Kai ta ɗago ta ce "Allah ne shaidata"
"To Allah ya rufa asiri, kin tabbatar kafin shekarar nan ta ƙare kin kawo mijin aure, idan ba haka ba wallahi sai ranki ya ɓaci kinfiso muna jerawa a gida muna haɗa kafaɗa? Kuma daga yau duk wani aiki na gidan nan ke zaki nama sallami ƴar aiki, Aaliyah makaranta take zuwa" Tana faɗin hakan ta miƙe tare da ficewa daga ɗakin tana zuba kumfar baki... Majeederh ta bi bayanta da kallo, to ita yanzu za ta yi da ranta? Tallan kanta za tayi kenan? Ko kuma dai photo nanta zata raba masallatai? Wata zuriyar ta ce mata.
"Kin manta kenan ko Majeederh? Bayan mazan gudunki suke babu wani wanda zai ce yana son ki balle aure" Zuciyarta tayi mata nauyi da ƙyar ta samu ta ja numfashi kafin ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi part ɗin Abbu. Yana zaune saman ladduma gabansa cike da kayan marmari hannunsa riƙe da jarida ya dubawa ta yi sallama, bai amsa ba sai gyaran murya da ya yi mata alamar ta shiga. Ta zauna a gefe cike da tsoransa ta ce "Ina yini Abbu? Na sameka lafiya?" Ya ce "Lafiya lou" Ya yi shiru ta ɗan ɗago kanta ta saci kallon Mahaifin nata, ba zaka ce shi ne ya haifeta ba, sbd ya samu duniya da abinda yake so wato kuɗi jikinsa ya murje alamun kwanciyar hankali sun bayyana a tare da shi. Ta sauke ajjiyar zuciya a hankali ta furta "Allhamdulillah na cika burin Abbu" Ta ɗauka zai tambayeta kalar rayuwar da tayi a Egypt ba tare da iyaye ko wani nata ba, ta ɗaukan zai sanya mata albarka bisa namijin ƙoƙarin da tayi na zama Gwarzuwa a musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa, ta ɗauka zai albarkaci rayuwarta bisa burinsa data cika sai ta ji ya ce "Na haifi ƴar da bata san girma da ƙimata ba, na haifi ƴar da take son tuna mini asiri a cikin al'umma, na haifi ƴar da take son saka mini ciwon zuciya...,"
A gigice Majeederh ta dakatar da Abbu da faɗin "Me na yi Abbu, me aka ce nayi idan zuwa gidan Latifa ya ɓata ranka don Allah ka yafe mini" Jikinta duka rawa da ɓari yake sbd tsoran ɓacin ran mahaifin nata. Abbu ya dubeta sosai kana ya jawo laptop ɗinsa ya shiga Gmail ya nuna mata wani saƙo ya ce "Hukumar makarantarku ta ƙasar Egypt take ƙorafin sun nemi alfarmar ki zauna musu domin zama malama amma ki kaƙi bayan sun yaba miki ba za su samu wata ɗaliba data kai ki ba" Majeederh ta ce
"Ka yi haƙuri Abbu" Ya ɗaga mata hannu cikin tsawa ya ce "Haƙuri? Kin manta al'ƙawarinmu dake?" Ta ce
"Ban manta ba" Cikin zafin rai ya ce "Ok isa ce ban ba? Anya zaki albarka kowa Majeederh? Kina son wanyewa lafiya?" A ruɗe ta ce
"Ka yi haƙuri Abbu, rayuwata a wata ƙasar da bani da kowa akwai hatsari ba zan iya zama ba, na yi ƙoƙarin cika al'ƙawarin amma na kasa ka yafe mini, bana da kowa a Misira bana da mai mini faɗa, bana da wanda zai kalla a matsayin wani nawa, bana da wanda zan zauna nayi fira da shi" Abbu ya dinga kallon Majeederh cikin tarin tsana da ƙonar rai ya ce
"Shi ɗan uwanki Alpha ba mutum bane? Da yake tafiya cikin jeji sai ya yi shekara bamu sa shi a idanun ba, ba kuma mu san halin da yake ciki ba, gwara ke mun san inda kike...,"
Ta ce "Abbu taya zaka haɗa ɗiyarka mace da namiji? Namijin daya kusa tun karar shekaru arba'in? Kuma zai iya kula da kansa?" Ta ƙare maganar tana sakin kuka sosai. Abbu ya ce "Ok ke yarinyar goye ce kenan ba zaki iya kula da kanki ba? Kinga tashi maza ki bar mini parlour idan na ci-gaba da ganinki zuciyata bugawa zatai mu zauna mu cinye ƴan kuɗaɗen da suka rage kinga ma dawo gidan jiya talakawa" Zatai magana ya ƙara daka mata tsawa kamar ba Mahaifinta da take mutuwar so kamar rai ba ta miƙe jiki na ƙyarma da ɓari ko kallon gabanta ba tayi ta nufi waje ga idanunta da suke mata wani masifaffan ƙaiƙayi nan da nan sukai jajir ta shiga susawa tana yin main parlour kuka na cin ƙarfinta, karo tayi da mutum tsaye wanda shigowarsa kenan cikin garin Kano tana ƙoƙarin yin compound a tunaninta main parlour ne sbd idanunta rufe yake caraf ya sa hannu ya riƙo nata hannun....
*BOOK 1 PAGE 31*
MIJIN MALAMA
LITTAFIN KUƊI NE WANDA YAKE SO YA YI MAGANA 08119237616
Ina godiya bisa ta'aziyyar da akai mini ta babban rashin da na yi na wan mahaifina Alhaji Musa Zakari sheka ( Dagacin sheka) Na gode sosai Allah yabar zumunci marubuta da yawa wasu ma ban san su ba, sun nuna mini kara ƙwarai makaranta ina alfahari daku kune silar kai ni inda nake kune kuke goya mini baya ta hanyar siyan littafaina, ina fatan ba zaku gajiya ba🙏🏿🙏🏿32
Janta ya yi har tsakiyar main parlour yana zuwa ya saki hannunta yana binta da wani irin kallo kafin ya ce "Baki da hankali?" Ta buɗe idanu wanda sukai jajir ta ce "Me na yi?" Da idanu ya dubi shigar dake jikinta da kuma kallon fuskarta dake buɗe, itama tayi saurin kallon kanta tana ɗan marairaice fuska zuciyarta duk babu daɗi ta kasa cewa komai sbd yadda ƙirjinta ke ɗagawa ga zafin da idanunta suke mata duk ta sushe su. Ya gyara tsaiwa yana harɗe hannu a ƙirji shi ma nasa idanun sun yi ja sbd abubuwan da suke masa yawo a zuciya can ƙasa ya ce "Kuma da gaske fita zaki haka? Tsirara?"
“.... Tsirara!?” Ta faɗa da sauri cike da tsoro, Alpha ya haɗe fuska ya ce "Mene marabar dambe da faɗa?" Majeederh ta yi shiru domin ita sam tunaninta baya nan wajan, zuciyarta ta Kaɗaita da maganganun Abbu, lura da yanayinta ya sa Alpha bai ƙara magana ba ya bi ta gefenta ya shige ya zauna saman kujera yana harɗe ƙafafuwan. Majeederh ta shige part ɗinta not too long ta dawo sanye da rolling na vail a kanta, ta nemi waje saman kujera ta zauna, shiru ya biyo baya can ta ce "Ina yini?"
"Lafiya" Ya bata amsa a taƙaice. Majeederh ta yi ƙasa da kanta cikin sanyin murya ta ce "Ance an maka ƙarin girma congratulations" Alpha ya ce "Uhm" Yana ɗan kaɗa ƙafa kafin babu wasa idanunsa ya kira sunanta ya ce "Majeederh!" Ta yi shiru.
"Zabiya?" Ta kwaɓe fuska tunda bata son sunan ya ɗan shafa kai daman He just wants to tease her. Ta miƙe zata bar parlourn ya ce
"No, please" Ta zauna kamar zatai kuka ta ce "Tun ina ƙarama kake ce mini Zabiya Yaya, ni ban so idan kai ma da Aljanar nake maka kama to"
"Stop it Majeederh!" Ya furta a tsawa ce, domin ji ya yi kamar ta caka masa nashi a ƙahon zuciya, ya girgiza kai ya ce "Sorry"
Ta yi shiru speaking calmly ya ce "Sannu da dawowa ƙasa Nigeria, yanzu sai me?" Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ce "Sai abin da Abbu ya ce" Alpha ya watsa hannu ya ce "Kina sane da problem ɗinki, komai zaki ki fara tuna aure first" Kunya ta kama Majeederh sai yanzu take dana sanin sanar masa da matsalarta, kuma yanzu da baya ai ba ɗaya bane tuni Ubangiji ya ye mata "Kina ji?" Ta ce "Aiki zan nema" Da wani irin sauri ya ce "Aiki?" Ta ɗaga kai ya ce "Shi ma Abbu ne?" Tayi shiru cike da tausayawa ya ce "Am sorry, zan masa magana ya fara bari kiyi aure" Wani irin abu ne mai ɗaci ya tsayawa Majeederh a maƙoshi ta runtse Idanunta tuni ta ji rauninta na son bayyana muryarta na rawa amma ta dake domin tayi al'ƙawarin ko hawan jini zai sameta, ko zuciyarta ce zata buga ta mutu nan take ta daina yin kuka ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Idan ya amince nayi auren wa zai aureni?" Alpha ya zura mata manyan idanunsa ya ce "Kamarya? kina nufin tsayin shekarun da ki kai a Egypt baki saurayi ba?" A hankali Majeederh ta girgiza kai ta ce "Even friend ban ba, shekaruna ashirin da takwas 28 ban taɓa yin saurayi ba idan ka ɗauke Imran shi ma ya guje ni ba tare da sanin dalili ba, baƙin jini ne dani Yaya na zama mujiya a idanun mazan duniya, hatta soyayyar ƙuruciya ban san ya take ba, ban san daɗin soyayya da wahalar cikinta ba, ko saurayin da zai zo ya yaudareni ban taɓa yi ba, balle wanda zai ji muradin aurena a zuciyarsa....,"
Ta yi shiru sbd numfashinta dake fisga kaɗan kaɗan kafin ta ce "Duk son da maza suke wa farar mace, duguwa mai kyan fuska nawa ya tashi a banza, mummunar mace wada ta fini farin jini, to idan ban yi aiki ba me zan Yaya? Shi ma Abbu fahimtar hakan ce ta sanya ya zaɓa mini wannan rayuwar kuma ina farin ciki da ita" Duk rashin imanin Alpha kasancewar shi Soja, wanda yaga masifu da yawa ya kashe rayuka da yawa amma a yanzu a gaban Majeederh sai dai zuciyarsa ta karye ya miƙe tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana bugawa hannayensa waje guda kafin cikin sauri ya tsaya a gaban Majeederh ya ce "Majee ki minin wani al'ƙawari, do me a favor please" Ta kasa kallonsa ya kai hannu zai riƙe nata tayi saurin janye nata tana ɗan yi murmushi ta ce "Na maka"
Ya ja baya ganin bata son ya taɓa jikinta, numfashinsa na sauka ya ce "Kiyi accepting duk wani abu dana yanke miki muddin ba cutarwa bane, ki yarda ba zan cuceki ba Majee" Ta ce "Me zakai?" Ya bata amsa ya ce "Zaki ji, ki amince first" Ta jinjina kanta bai ƙara cewa komai ba, ya fice daga part ɗin ya shige part ɗin Abbu ita kuma ta nufi Kitchen ta fara haɗa dinner harta gama ta shige part ɗinta ba taga fitowar Alpha ba....
Washegari ya kama weekend ne, Aaliyah na zaune a parlour watching Ds t.v lokacin 10:10 na safiyar Saturday jin ana sallama ya sanya Aaliyah ɗago kanta tana amsawa da faɗin "Wasalamu Alaiki, Anti Latifa" Latifa ta zauna tana cewa "Ashe fa yau weekend da tuni kina school" Aaliyah ta yi murmushi ta ce "Ina kwana?" Ta amsa da "Lafiya lou" Sukai shiru can Latifa ta ce "A level nawa kike ne yanzu?"
“... 200" Aaliyah Said, tana ɗan buɗe Idanunta akan series ɗin _My heart knows_ da take kallo a zee wrld. "All The best little sister, ina Malama?" Aaliyah ta nuna mata hanyar kitchen da hannu ta ce "She's in the kitchen" Lura da hankalin Aaliyah nakan series ya sanya Latifa miƙewa ta nufi hanyar kitchen ɗin tana zuwa ta samu Majeederh tsaye gaban sink tana wanke hannunta tayi dariya ta ce "Sannu da aiki Madam koko" Majeederh ta ɗan yi murmushi ta ce
"Uhm" Latifa ta ce "Gasky am lucky na samu abinda nake so"
“... Kike so? Ko ya ke so?"
Latifa ta ce "Shi wa?"
Majeederh ta watsa mata harara tana ɗauke plate ɗin data wanke ta ce "Nasan ciki ne dake"
Latifa ta ce "A'a ba ciki ba, baya ne dani" Ta faɗa tana tofar da yawo a bakin kitchen ɗin har sai dai Majeederh ta runtse idanu a ɓoye.
"Ni dai zuba mini breakfast yunwa na ke ji" Da mamaki Majeederh ta ce "Idan na baki mijinki fa?" Latifa ta jima tana kallon Majeederh can ta ce "Na yi fa, idan ni nayi bana iya ci sai na kwaɗayi" Bata ce mata komai ba, ta haɗa mata breakfast fal cikin warmer hadda kunun gyaɗa mai kyau, tana bata tayi godiya ta fita a hanya taci karo da Raihan tana shigowa cikin compound ɗin a haɗaɗɗiyar motar ta, bata kulata ba ta fita tare da shigewa nata gate gidan... Lokacin da Raihana ta shiga gidan duk suna parlour suna breakfast ta cire mayafinta tare da ajjiye hand bag ɗinta tana zama saman dining ta ce "Ki ce nazo a daidai" Aaliyah bata ce komai ba haka ma Majeederh, sai da Raihana ta kai abinci bakinta ta ce "Majeederh ba gaisuwa?" Da sauri Aaliyah ta ce "Wakike so ta gaisheki Anti Raihana?" Kai tsaye ta ce "Majeederh?" Baki buɗe Aaliyah ta juya ta kalli Majeederh kana ta kalli Raihana ta ce "Anti Jeederh ce zata gaisheki? Bama ke ki gaidata ba?" Raihana ta ce "Ai ni ya dace ta gaisar" Aaliyah da ranta ya fara ɓaci ta ce "A sbd kin haifeta? Shekaru nawa Anti Jeederh ta baki?" Raihana ta saki dariya hadda buga dining ɗin dake gabanta ta ce "Ji banza wake ta ƙama da shekaru? Ai tunda nayi aure to yanzu ni ce gaba da ita, bayan nayi aure haihuwa zan yi Kinga durƙosawa wada ba gajiyawa bane ko? Ai aure shi ne martabar ko wacce mace, kiyi ƙoƙari ki aure sai mu iya haɗa kafaɗa dake"
Aaliyah ta miƙe tsaye itama tana sakin dariya ta ce "hehehe, matar na tuba bata rasa miji aure, ai dake da Anti Jeederh da ke kwaryar sama ce take dokan ta ƙasa, mene marabarki da ita? Sunan kinyi aure amma kullum kina hanyar barbaɗa na zuwa gida ana ƙarar da albarkar aure akan titi, Anti Jeederh da izinin Ubangiji ba zatai auren barbaɗa irin naki ba, zata auri miji wanda yake kishinta yake sonta wanda zai jure duk wani ƙalubale nata wanda zai sota fiye da yadda take son shi zatai aure inda aka san darajarta, ba zata taɓa auren wanda zai sallamawa duniya matarsa ba" Aaliyah ta riƙe ƙugu ta ce "Mema kika ce haihuwa? Ai sai dai kici ki haifi kashi ba dai ɗan mutum ba, domin juma'ar da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta....,"
Hannu Raihana takai zata kifawa Aaliyah mari tayi saurin ja baya, Raihana na huci ta ce "Zan yi maganinki dan uwarki idan ni sa'arki ce" Aaliyah ta zare idanu ta ce "Ni na isa na haɗa kaina da uwar mata mai aure? Wlh wani ya kalleki sai ya ɗauka kin yi shekaru 20 da aure duk kin rakwaɓe kamar tsohuwar mota" Wani baƙin ciki ya turnike Raihana ta ce "Ni kike faɗawa haka?" Sai a lokacin Majeederh ta tashi ta zabgawa Aaliyah mari ta ce "Ya zama ƙarshe" Aaliyah saka kuka sosai ta ce "Na gaji Anti Jeederh na gaji da abinda suke miki, su basu da aiki sai gorin aure? Kamar ke zaki aurar da kanki sun manta komai lokaci ne? Ita Anti Raihana da take yin ɓari ta taɓa zama ta tambayi kanta me yasa cikin baya zama? Da aure da haihuwa da arziƙi duka na Allah ne, wani jinkirin alheri ne kuma da aure irin nasu wallahi gwara mutum bai aure ba, mata nawa suke aure amma baya zuwa ko'ina auren ke mutuwa" Majeederh na ƙoƙarin yin magana suka ji gyaran murya a tare suka juya Alpha ne tsaye hannunsa harɗe a ƙirji fuskar nan kamar an aika masa da saƙon mutuwa, yana sanye cikin wani jeans da Racing jersey ya saka p.cap a kansa sai ƙamshi yake. Gabaɗaya sukai shiru jikin Aaliyah da Raihana ya ɗauki rawa musamman Aaliyah domin tasan Alpha baya son raini da rashin kunya ga babba bakinta na rawa ta ce "Ya...yaya A.b don Allah....,"
Hannu ya ɗaga mata, idanunsa akan Raihana ya ce "Ke dan kan uwarki Majeederh sa'arki ce?" Raihana ta yi shiru ya ƙara sakar mata tsawa ya ce "Shegiya munafuk za kici ubanki daga ke har mijin da kike tunanin kin aura wanda yasa kikewa wata gori akan haka, duk sanda na ƙara ganin ƙafarki a gidan nan without any reason wlh sai na kusa karya ki" Ya nuna mata ƙofa ya ce "Bar nan wajan kafin na karyaki na karya banza, shi ma mijin naki bashi da tunani bai san ciwonki bane" Ganin ta juya zata shige part ɗin Mami yasa ya nufeta ta kwasa a guje tana kurma ihu ta faɗa part ɗin Mami, tsayawa ya yi yana shirin komawa kan Aaliyah yaga wayam babu ita sai Majeederh dake tsaye. Bai ce mata komai ba ya juya zuwa part ɗin Abbu. Mami ta kalli Raihana dake haki duk tayi wujiga-wujiga ta ce "To shi haka ake bai ji ta bakin kowa ba sai ya hau faɗa?" Raihana ta ce "Shi daman baya son mu ai, ya fi son Anti Jeederh da Aaliyah he's so selfish" Mami ta ce "To ai shi ba Allah bane, kuma ke matar aure ce yana dokanki Shari'a ba zata barsa ba, yabar ganin shi soja ne wlh garƙame shi za ai a bayan canter" Raihana tayi shiru Mami ta kalleta ta ce "Kema bana son rashin ta ido, ina ke ina zabgawa Majeederh wannan maganganun? Kar na kuma ji balle ki ja mini zagi" Raihana ta tura baki Mami ta ƙara cewa "Yau kuma me ya kawo ki?" Ta ce "Jiya da daddare ya dawo, ya kuma da asubar fari a haɗa kayansa wai wani aiki ke ya taso masa" Mami ta zabga tagumi ta ce "Shi kuma ƙaddararsa kenan tafiye-tafiye? Wai aikin me yake ne?" Raihana ta ce "Ni ban sani ba" Ta ce "To Allah ya kyauta"...... Kwana biyar kullum sai Alpha ya zo wajan Abbu ba tare da sanin meke kawosa ba, da yamma liƙis Anti ta shigo gidan ƴarta Sona bayan sun gaisa da Mami ta ce "Ina Majeederh?" Mami ta ce "Ta leƙa gidan Latifa daga nan ance sun fita" Kafin Anti tayi magana Majeederh ta shigo bakinta ɗauke da sallama Anti ta amsa "Daga ina kike?" Majeederh ta ce "Mami gidan Latifa" Cikin faɗa Mami ta ce "Ji munafukar ƙarya ba ance kun fita ba?" Majeederh ta ce "Oh na rakata asibiti na sameta tana ta amai ne ashe ɓari za tai" Mami ta ce "Au ciki ne da ita?" A hankali ta ce "Eh" Mami ta ƙara cewa "Yanzu ya ɓare cikin?" Nan ma Majeederh ta ce "Eh" Mami ta jinjina kai ta ce "Ikon Allah, wannan ɓarinta na uku kenan, mahaifarta ce bata da ƙauri ina zato" Babu wanda ya yi magana tsakanin Anti da Majeederh, Mami ta gyara zama ta ce "To me Likitoci suka ce kuma" sai a lokacin Anti ta ce "Haba Asabe wannan tambayoyi kashi da kashi ita yanzu Majeederh me zata ce?" Mami ta ɗan yi murmushi, Anti ta ce "Daman abin alheri ya same mu" Mami ta ce "Ma sha Allah" Anti ta kalli Majeederh kana ta ce "Alpha ne yake son Majeederh yana son ya aureta" Da wani irin Shock mai kama da mamaki Mami ta ce "Shi Alpha ɗin? Kuma Abbu ya amince?" Anti ta ce "Shi ne ma ya saka ranar auren ai" Da wani irin Scorned expression Mami ta ce "Ikon Allah bani da labari Allah ya sanya albarka" Majeederh ta yi shiru She couldn't say a word sai bin Anti da idanu take. "Majeederh kin amincewa da yayanki kuma ɗan-uwanki Alpha? Kin aminci ya zama mijinki?" Buri Majeederh ta auri wanda ya san kima darajar ta, wannan yasa take yawan kallon Alpha matsayin crush ɗinta take jin inama ya aureta? Ganin bashi da interested akanta yasa bata taɓa sanyawa ranta ba, Majeederh ta tsinci kanta cikin tashin hankali sbd babban burinta ta zama matar A.b Alpha Bello, It's her dream tun sanda ta buɗe idanu ta gansa yana kula da ita, She can't afford to lose him, her life will be incomplete without him, She's felling scared and restless me yasa take jin tsoro?... "Majeederh"
Anti ta kira sunanta. Ta ɗan kalleta kana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Kina son auren Alpha?" Majeederh ta ce "Anti ai zaɓi ba nawa bane kamar taimakona ya yi" Anti tayi shiru sai kuma ta ce "Shikenan jeki Allah yasa haka ne alheri a rayuwarki" Miƙewa tayi ta shige bedroom amma deep down na zuwarta mamaki take anya shi yace zai aureta? Mai yasa bai fara neman Soyayyarta ba? "Ke da za a taimakawa ina ruwanki da neman soyayya?" zuciyarta ta bata amsa.
Da daddare bayan Majeederh ta gama dinner tayi sallar Magriba tana zaune tana azkar wayarta ya yi ringing ganin sunan Alpha yasa gabanta faɗuwa har kiran ya katse bata ɗauka ba, wani kiran ya sake shigowa ta yi bismillah ta ɗauka a hankali ta ji ya sauke ajjiyar zuciya ya ce "Me kike?" A hankali ta ce "Azkar" Ya yi jim ya ce "Shi ne baki picking kiran farko?" Ta ɗan marairaice ta ce "Kayi haƙuri" Ya share maganar ya ce "Majeederh" Ya kira sunanta ta kasa amsawa ya ce "Wannan shi ne hukuncin dana yanke mana, ina fatan banwa rayuwarki Shisshigi ba, idan kuma baki so na baki son aure let me know first" Ta yi shiru Ya ce "Kina son Aurena? Majee?" Da sauri ta kashe wayar tana rufe Idanunta kamar yana gabanta, daga can ɓangaren murmushi Alpha ya yi kana ya kashe wayar ya shiga Parlourn Mahaifiyarsa zaune ya sameta ya ce "Sannu da dare Mama" ta ɗaga masa hannu ta ce "Ya isa" Tana faɗin hakan ta miƙe tare da ficewa daga parlourn...... Ciki sati gudu wata muguwar shaƙuwa ta wanzu tsakanin General Alpha Bello da Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Tana jinsa har cikin zuciyarta gashi da masifaffen kishi, Anti ta kira mai gyara aka shiga yiwa Amarya Majeederh wani mahaukacin gyara, sosai Alpha yake kashe kuɗi har kawo lokacin ko hannu Majeederh ta hana ya riƙe mata..... Ana saura kwana ɗaya ɗaurin aure tun safe aka haɗa Family meeting gidan Uncle Isma'il an cika sosai yara da manya maza da mata, Alpha ne kawai babu a wajan can Uncle Bello ya ɗakko wayarsa ya kira shi yana ɗagawa ya ce "Wanne irin iskanci ne haka? Mu zamu zauna zaman jiranka?" Muryarsa can ƙasa Ya ce "Am sorry" Uncle Bello ya kashe kiran babu jimawa ya shigo kansa a ƙasa ya zauna can kujera, aka buɗe taro da addu'a Uncle Isma'il ya ce "Ma sha Allah, a gobe In sha Allah muna da ɗaurin auren da zai kafa tarihi a Khan family" Cikin sauri Alpha ya ce "Auren wa za'a ɗaura Uncle?" Gabaɗaya aka kallesa cike da mamaki Uncle Isma'il ya kasa bashi amsa, Alpha ya ce "Me ya sa kowa ke kallona? Why are you staring at the?" Anti ta ce "Gidanku General Aurenka mana" Ya ware idanu ya ce "Aurena kuma Anti? Dawa?" Ta ce "Da Majeederh" Ya ƙara waro idanu ya ce "Wacce Majeederh? Ni zan yi aure kuma Majeederh zan aura?" Innati ta ce "Ji wawa dilla kuyi abinda ya kawo ku" Uncle Isma'il ya kwaso katin ɗaurin auren ya ce "Gashi nan It's too late ka bawa friends ɗinka" Alpha ya kwashi katin da Shock ya dinga bin sunansa da idanu da kuma na Majeederh ya ɗago kansa ya ce "Ke ni na ce zan aureki? Wai meke faruwa ne?" Uncle Bello ya miƙe ya zabgawa Alpha ya ƙara zabga masa ya ce "Bana son hauka, lokacin da kazo da maganar aurenta kwana bakwai daga shige uban waye ya yi maganar ba kai ba?" Alpha ya girgiza kai ya ce "Wallahi Abba ni ban taɓa cewa ina sonta ba, ni me zai saka na aureta ƙanwata ce fa?" Innati ta ce "To da sauƙi tunda ba nono ɗaya kuka sha ba" Alpha ya ce "Uncle,Abba this is misunderstanding wlh ni bance zan auri Majeederh ba infact ina da wacce nake so kuma gobe zan kawota ku ganta don Allah kada ku aura mini Majeederh.......
*BOOK 1 PAGE 32*
*MIJIN MALAMA*
_littafina na kuɗi idan kina so ki biya ki karanta.... 08119237616 ko yayane kada ki karanta free without my permission please siyan littafinmu shi ne nuna soyayya a garemu🫂_
*Ƙaddarar mace abace mai wahala musamman ƙaddarar za dinga maka gori da ita, ana ganin kamar ganganci ne ko kuma kai ka ɗorawa kanka ba yin Allah bane🥹 Yadda da ƙaddara shi ne cikar imanin mutum, Ubangiji bai baka abu ba hakan na nufin abin nan ba alheri bane a gareka da rayuwarka, ƙaddara na tafiya da lokaci shi kuma lokaci ne abu ne da baya jira, hakan na nufi ita kanta ƙaddarar ba tabbatacciyya bace, akwai lokacin da zai zo ta zama tarihi... Wani jinkirin alheri, rasa abu baya nufin rasa rayuwarmu hakan wata dama ce da Ubangiji ya baka wajan gane laifinka da kuskurenka, wasu suna sakaci da addu'a, wasu kuma rashin biyayya ga iyaye, wasu kuma ruɗin ƙawaye, wasu kuma ƙaddarar ce dai.... Idan aka haɗa zamu fahimci gabaɗaya lokacin kowa ne bai ba, da zarar lokaci ya yi komai zai zama shuɗaɗɗen, cimma manufa bashi iyawa ma, cimma nasara da tsayawa akan ra'ayinki shi ne cikakken mutum. 🌚 NO MAN IS THE MAN WITHOUT A WOMAN🫰🏽🤘🏼*33
Murya na rawa ya ce "Don Allah ku tausaya mini wallahi ban taɓa son ta ba, balle na ce zan aureta, why should I? Allah kuka aura mini ita mutuwa zan yi mana son ta, bana ƙaunarta, kada ayi mini auren dole" Ya faɗa His voice was shaking. Yanayin yadda kowa ke binsa da kallon mamaki ya sanya shi ƙarasawa gaban Uncle Isma'il ya ce "Kun sai dai ni ba mahaukaci bane? Balle ayi mini uzurin taɓin hankali, I don't know what is going to happen to me, I don't know when this happened.....," Tass! Mama ta ɗauke Alpha da mari, without letten him to recover ta ƙara sauke masa wani wanda ya sanya shi yin baya sai kuma ya dawo ya tsaya da ƙafafuwan shi dafe da kuncinsa tayi pointing ɗinsa da yatsa ta ce. "Idan ƙwayar ku ta sojoji ta faɗa maka ba daidai ba, ko allurar da ake muku to gabaɗaya haukanka ya zama na banza a nan, kayi kaɗan kayi tsararo bamu haifi ɗan da zai juyamu ko ya raina mana hankali ba, We are your parents, you are the child we gave birth to, we have the power to pass the sentence on you...." Mama ta ja ƙwafa ta ce "Let make it clearly for you, idan harni na ɗauki cikinka wata tara, na haifeka na baka nono na, naci kashi da fitsarinka wallahi wallahi ko zaka mutu ka farko sai ka auri Majeederh aurenka da ita a gobe babu fashi" Ta faɗa Sounding very angry. “.... Mam....”
Alpha's Expression softened slightly as he looked at her ya juya ya kalli Majeederh wanda take zaune kamar anda sata, bata ko motsi sbd tsananin tashin hankali ruɗu da fargaba, da kuma tu'ajujjin abinda yake shirin faruwa da ita, An fasa aurenta? Kuma ranar ɗaya kasance saura kwana ɗaya a ɗaura? Ko dai ba ita jin ake nufi ba? Fizgota da Alpha ya yi ya sanya ta dawo daga hayyacinta ta dinga kallonsa kamar zautacciyya a hargitse ya ce "Kiji tsoran Allah Majeederh ki faɗa musu gaskiya, tunda nake na taɓa cewa ina son ki? Yaushe na sameki nace zan aureki kada ki bari a cutar dani ina da wacce nake so" Majeederh ta girgiza kanta tana jan jikinta baya ƙirjinta na ɗagawa sama tana dafe saitin zuciyarta ta ce "Me ya sa zaka zaɓi tuzartani a lokacin dana saka rai da samun ƴanci kamar ko wacce mace? Me ya sa zaka samun son abin dana fidda rai da samun shi? Me ya sa ka dawo da kwaɗayin kasancewa ɗaya daga cikin matan da zamu martabar aure bayan kasan ba haka bane? Me na yi maka a rayuwa daka nemi ɗaukan fansa ta hanyar da zuciya ba zata iya ɗauka ba? Me ya sa ƙaddara zata juya ta zo mini ta hanyar da ba zan iya jure mata ba?..." Ta girgiza kanta duk wannan abun jikinta ƙyarma da ɓari yake kamar mai shirin yin jijjiga ta zube a ƙasa saman ƙafafuwanta tare da rarrafawa ta riƙe ƙafar Alpha ta ce "Ko a lissafin ƙaddara ban taɓa lissafa zuwan wannan ƙaddarar ba, ka tausaya mini ka aureni kuma aure zaɓin zuciyarka, zan zauna da kai a haka koda baka so na, koda zan zama ƴar aiki a cikin gidanka dakai da matarka, wallahi ba zan iya jure wannan ƙaddarar ba fasa aurena da zakai daidai yake da tsayawar numfashina" Majeederh ta ƙara ƙanƙame ƙafafuwan Alpha ta ce "Tunda na buɗe idanu naga kana damuwa da duk wata damuwata naji babu wanda ya dace dani sama dakai, zuciyata ta ƙauna ce ka Yaya, ƙauna mara algus ina sonka zan zauna da kai komai wahala, ƙunci, damuwa,takura ka rufa mini asiri kamar yadda Allah ya rufa maka kada ka muzanta ni kada ka sanya na sama abar kwatance a dangi da kuma unguwa ka dubi girman Allah ka amince da aurena wallahi da bakinka kazo mini da maganar da......,"
"Stop it, stop!" Alpha ya faɗa yana janye ƙafarsa daga gareta ya ce "Wallahi ba zan iya aurenki ba, baki mini komai but i can't be your husband, i don't love you anymore ki barni na aure wacce nake so ni ko zan takura miki ba zan iya aurenki ba ni ma kiyi mini wannan rufin asirin" Ya faɗa yana riƙe kansa da hannu bibbiyu.
Majeederh ta kallesa irin kallon ka rusa mini rayuwata kafin ta ce
"What have i done to deserve this from you?? Wallahi ina sonka ni" Aaliyah ce ta tashi tare da ƙarasawa wajan Majeederh ta ce "Anti Jeederh ki barsa Allah zai kawo miki naki rabon, ya yi haka ne domin ya kunyata ya sanya ƙaddararki ta ƙara tsamari" Majeederh ta girgizawa ƙanwata kai ta ce "No Aaliyah ba zan iya jure gorin aure a wannan lokacin ba" Kuka sosai Aaliyah take kamar ranta zai fita, tana tausayawa halin da yayarta take ciki. Anti girgiza ƙafa kawai take lokaci zuwa lokaci take jan ƙwafa, Abbu tunda aka fara maganar ya sunkuyar da kansa ƙasa baka iya gane yanayin da yake ciki, wai ƴar cikinsa take durƙoshe tana roƙan wani ya aureta? Me ya yi mata da zata nemi tuzarta shi har haka? Mami ta yi jigum idan ranta ya yi dubu to ya yi tsatsa ya lalace, kana ganin yadda idanunta ya yi jajur zaka san zuciyarta a kusa take. Uncle Isma'il kallon Alpha kawai yake, Uncle Bello ya dubi ɗan nashi ya rasa me zai ce masa he really disappointed him. Innati zare idanu tayi kana ta ce
"Komai yana da lokacin, lokacin bayyanar hakan ne ya yi kada ku damu, gaggawa aikin shaiɗan nasan za rina ansaci zanin mahaukaciya na jima da ganin wannan rana" Ganin babu wanda ya ƙara cewa komai ya sa Uncle Bello ɗaukan wayarsa ringing ɗin farko aka ɗauka cikin sauri ya ce "Liman kayi haƙuri an samu matsala a invitation card ɗin nan, ɗaurin auren ƙarfe 9:00 na safe sai a sanar a masallaci" A gigice Alpha ya kalli mahaifinsa ya ce "Abba me na yi maka da baka son farin cikina? Wallahi kuka aura mini Majeederh zan kashe kaina" Wani Mahaukacin mari Uncle Bello ya sauke Alpha kafin ya dawo hayyacinsa Mama ta ƙara sauke masa wani, ganin haka yasa Widad fashewa da kuka sosai ganin yadda ake marin yayan nata Uncle Bello ya nuna Alpha da hannu ya ce “General Ajzan-Alpha Bello Khan wallahi yau ko da gawarka ne sai an ɗaura aurenka da Hawwa'u" Alpha ya juya ya kalli Majeederh ya dawo ya dawo ya kalli Uncle Bello muryarsa bata fita ya ce "Sai a ɗaura da gawar tawa"
Yana faɗin haka ya fice daga cikin parlourn, Majeederh ta miƙe zata bi bayansa sai a lokacin Anti ta ce "Kada ki kuskura ki bi bayan wanda bashi da imani" Uncle Isma'il ya miƙe da hanzari ya ce "Kada Alpha ya cutar da kansa fa?" A takaice Uncle Bello ya ce "Rabo dashi daidai nake da zamaninsa, he really disappointed me ya nuna bashi da biyya ban isa da shi ba" Kafin kowa ya yi magana aka ji faɗuwar abu gabaɗaya suka juya Majeederh ta faɗi babu numfashi a ƙirjinta.....
Duk da kiran asubar da ake bai sanya ɗaya daga cikinsu ya motsa ba, ko wanne ka kalli fuskarsa za kaga tashin hankali musamman Dattijan mazan. Uncle Isma'il ya saka hannu ya sharce zufar data gangaro masa yana cire hular kansa ya ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya juya ya dubi Uncle Bello daya kasa cewa komai idanunsa ya yi jajur ya kalli Mama dake rusa kuka sosai ya ce "Wai mene ya faru mai zafi har haka da yaron nan zai mana wannan cin mutunci?" Mama ta share hawayenta ta ce "Idan ni na haifi Alpha da cikina to wallahi.....," "A'a please" Anti ta tare ta da sauri wanda ya hana Mama ƙarasa faɗin abinda tayi niyya. Uncle Bello ya ɗago kansa ya ce "Ɗan cikina? Ɗan dana haifa Isma'ila?" Uncle Isma'il ya sauke numfashi ya ce "Dole akwai wani abu, yadda Alpha ya birkice kamar Mahaukaci sabon kamo zaka san something is fishy?" Jinjina kai kawai Mama take kafin suyi magana motar Abbu ta shigo cikin compound ɗin gidan Uncle Bello wanda aka baza rumfuna na ɗaurin aure, Abbu ya jima cikin motarsa kafin ya buɗe ya fito da sauri Mami ta fito tana mara masa baya, tun a balcony kafin su ƙarasa ƙofar parlour suka fara jiyo kukan Mama, Mami kamar zata kifa haka ta bangaje Abbu ta shige "Ba dai an fasa auren ba?" Abinda Mami ta faɗa kenan tana binsu da idanu, Abbu ya shigo tare da jingina da jikin bango can ya ce "Isma'ila, Bello na ji kira cikin gaggawa gashi ina ƙoƙarin rasa sallar asuba?" Uncle Isma'il ya miƙawa Abbu white paper ya ce "Read, karanta" Har Abbu yaƙi amsa sai kuma ya saka hannu ya karɓa tare da buɗewa hannunsa na rawa idanunsa ya sauka akan handwritten ɗin Alpha da yake cewa....
DEAR PARENTS.
_Bani da baki ko kalmar da zan muku bayani wajan fahimtar daku abinda nake nufi, amma na zaɓa mana hanya mai sauƙi da warware ƙullin da yake ƙoƙarin raba zumunci, ban kashe kaina ba, ban kuma zauna a cikinku na ɓata muku sunan family ba, more especially mahaifina, kayi mini komai a rayuwata ta duniya har kawo lokacin da nayi wayo na girma na mallaki hankalin kai na, Ina son Majeederh a matsayinta na ƴar uwata wacce jinina da nata suke yawo a jijiyoyin ko wannenmu, amma bana sonta ta aure bana ƙaunar zama da ita, akwai yarinyar da nake so a duk sanda kuka amince mini zan gabatar muku da ita a matsayin matar da zan aura kuma sirikar ku._
_Naso karɓarta matsayin mata kuma nayi muku biyayya, amma wallahi zuciyata ta kasa yarda da wannan ƙudirin idan na auri Majeederh ba zan iya sauke hakƙin aurenta akai na, zanta cutar da ita, zata zama bora a cikin gidana, zan wulaƙanta ta, wulaƙanci da human rights za su iya hukantani, zan muzantata, muzancin da babu macen da aka taɓa yiwa irinsa, zata zama baiwa a cikin gida, irin bayin da ba a samun su a yanzu sai ƙarnin baya irin bayin gidan sarauta ɗin nan, zata zama almajira a cikin gidan mijinta, To idan zan iya aikata mata duk wannan gwara ban aureta ba, nima ina mata fatan samun rayuwa mai ƴan-ci, ina gudun na tashi da ɓari ɗaya a shanye rana gobe ƙiyama_
_Babban Dalilia na rashin aurenta shi ne, Ni mashayi ne, ni mazinaci ne Majeederh bata dace da mutum mara tsafta kamar ni ba, ku yafe mini don girman Allah, kuji tausayina kada ku aibata ni, zan dawo duk sanda kuka yarje mini idan kuma mutuwata ta riskeni ina roƙan kuyi mini addu'a da samun dacewar Ubangiji!_
~G.A.B Alpha~
Abbu ya ɗauke numfashi lokacin da idanunsa ya sauka akan kalma ta karshe, date da time. A sanyaye ya ce "Yaushe ya tafi?" Mama ta ce
"Ya tafi ko ya gudu? Wallahi ƙarya Alpha yake baya Shaye-shaye, duk mutum bai hali irin wannan baya zama inda yake, ya tsani zin kamar yadda ya tsani fitar hawayena" Anti ta ce
"Me ya sa zaiwa kansa irin wannan tabon to?" Uncle Isma'il ya ce "That's what i was thinking too" Wayar Abbu ce tayi ƙara ya ce "Ina zuwa" fita ya yi yana ɗaga kiran ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce "Thank you, na gode sosai" Ya kashe wayar kana ya dawo. "Yanzu mene abin yi?" Uncle Bello ya miƙe ya ce "Ku san hanyar daza ku bi ku kwantar da hankalin Majeederh, ita nake tausayawa wallahi da ina da wani yaron bayan shi da a yanzu ba sai anjima ba zan ɗaura masa aure da ita, Allah ne shaidata, Alpha kuma sam ba zan masa baki ba, amma zan ga illar bijrewa iyaye nasa kalar godiyar kyautatawar da mukai masa kenan" Yana faɗin haka ya fita gabaɗaya mazan fita sukai domin gabatar da sallar Asuba zuciyoyinsu babu daɗi. Mami ta kasa cewa komai domin ta girgiza da al'amarin, wani irin baƙon al'amari ne wannan? Only God knows! Bayan Anti tayi sallar Asuba bata jira mijinta ba ta nemi napep zuwa gida...
Wajejen huɗu na rana ta fara buɗe Idanunta da ƙyar, wanda sukai mata nauyi har lokacin drip ne manne a hannunta, ta juya kaɗan sbd ciwon da ɓarin kanta yake mata ga wani dishi dishi da take gani kamar mai hawan jini, da sauri kuma ta buɗe idanun tare da yin shiru tana ƙoƙarin tina mene ya kwantar da ita ciwo haka? Duk ƙoƙarinta na son ganin bata kwanta ba? "Sannu Anti Jeederh" Aka faɗa daga can gefe, ta juya suka haɗa idanu da Aaliyah da kuma Sona ɗiyar Anti ta ce "Ƙarfe nawa?" A sanyaye Aaliyyah ta ce "Huɗu da kusan minti goma" Majeederh tai shiru sai kuma ta ce "Huɗu?"
“....Ai an kwana har yamma tayi, don baki da lafiya ne" Majeederh ta ce "Kina nufin kwana na ɗaya kwance?" Ta bata amsa da "Eh" Daidai nan Anti ta buɗe ƙofa ta shigo tana kallonsu ta ce "Yaushe ta tashi?" Sona ta ce "Yanzu Anti" Anti ta ce "Sannu Hawwa'u" Ta ɗan yi murmushi tare da yin shiru a hankali kuma ta ce "Shikenan na zama matar Yaya? Ni ma nayi aure an ɗaura mini aure da Yayana General Alpha ko Anti? Allah na gode maka za a daina yi mini gorin aure ni ma nayi aure ƙaddarata ta zo ƙarshe....
*Mijin Malama it's a paid book..... Subscribe before you Read🤓*
6850917335
Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank..... Kindly send your evidence via 08119237616 Book 1 and 2 1k.
Naso yin typing ɗin ya fi haka yau Sadakar Bakwan rasuwar da akai mini🙏🏿 Mu haɗu weekend a arewabooks.*_Huhuu! To bance komai ba, amma ya kuke yaƙin neman MIJIN MALAMA Don't you know cewa na kuɗi ne? Mata masu fama da Jinkirin aure wannan littafin sadaukarwa ne a gareku🤓😥..... A daina shelar neman Mijin Malama tunda akwai Mazan da yawa Allah kaɗai yasan waye mijin Madam come and Subscribe before you read, meye wata ƴar 1k da zata muku wahala?........ Chat me via WhatsApp 08119237616_*
Kasa bata amsa tayi saboda tashin hankali, ganin kowa ya yi shiru ya sa ta ce "Finally, ni ma na zama matar aure Allah na gode maka bisa wannan tarin Ni'imar da kayi mini, na ƙara yadda wani jinkirin alheri ni Anti, gashi yanzu Ubangiji ya bani nagartaccen miji" Majeederh ta yi murmushi tana goge hawayen farin ciki, duk wani zafi da ƙunci ya kau a ranta, tabon dake cinta a zuciya ya hanata sukuni gabaɗaya ta neme shi ta rasa. Aurenta da Yayanta Alpha ya zama abu na farko wanda ba zata taɓa iya mantawa fashi ba.
Anti ta juya ta kalli Aaliyyah da Sona ta ce "We need privacy, ku je waje yanzu zan fito" Aaliyyah ta yi waje, Sona ma ta bi bayanta. Anti ta kalli Majeederh tana murmushi wanda bai kai zuciya ba ta ce "To Amarya" Kunyar Anti ta kamata, ta ɗan yi ƙasa da kanta a hankali Anti kamar kazar da ƙwai ya fashewa ta ce "Ki je ki yi sallah, wanka,cin abinci we need to talk ok" Majeederh ta miƙe tsaye da sauri ta dafe gefen kanta "Sorry kan ne dai?" Anti ta tambaya tana riƙe kan nata, jijiyoyin kan duk sun fito sai har bawa suke idanunta jajir, ta ƙara yin murmushin ƙarfin hali ta ce
"Abbu ma zai farin ciki ko Anti? Zai yi farin ciki yaga aurena, ni kuma zan aurar da Aaliyyerh" Gabaɗaya Anti tunanin dake sarrafa ƙwaƙwalwarta ne ya tsaya da aiki ta tsaya ta dinga kallon Majeederh da ƙyar ta iya cewa "Ki je ina jiranki Majeederh" Ta nufi bathroom da ƙyar ta yi wanka tare da sallolin dake kanta, Anti ta kawo mata wata atamfa Valisco milk da yafin blue a jiki, ɗinkin duguwar riga Ashap. Majeederh ta dinga kallon kayan domin bata saba saka irin su ba, tina cewa ko wacce amarya irin kayan da take sakawa kenan sai bata ce komai ba, ta shirya tsaf tayi wani irin masifaffen kyau, kamar irin Fulanin Usul ɗin nan ko na Daji ko kuma irin Half-caste ɗin nan jinsan larabawa da yankin Niger na Agadas ko Sudawa. Idanunta zuru-zuru tayi muguwar rama kamar kuɗin guzuri, fuskarta kamar tafin hannu. "Anti na kira number Yaya a kashe fa? Zan yi masa godiya da aurena da ya yi" Anti ta kasa bata amsa ta juya da sauri tare da ficewa daga bathroom ɗin ta nufi part ɗin Uncle Isma'il lokacin yana zaune saman kujera yana waya, tana zuwa ta rushewa Uncle Isma'il da kuka tsabar firgici ya saki wayar hannun sa tare da miƙewa jikinsa na rawa ya ce "Subuhanallah! Ƴar Aljanna ke dawa?" Anti ta dinga kuka jikinta har rawa yake kai kace Uncle Isma'il ne ya rasu, ko kuma an aiko mata da mutuwar mahaifinta daga Gombe.
Cikin kuka ta ce "Mun shiga Uku Yallaɓai, mun shiga uku Abban Jawaad" Uncle Isma'il ya ce "Ba mu shiga uku ba da izinin Allah, Ubangiji na tare damu" Ya saka hannu ya ɗagota yana riƙe fuskarta ya ce "Majeederh ko?" Ta kasa magana sai kuka Uncle Isma'il ya rasa yadda zai rarrashi matar tasa ya kamo ya rungume ya ce "Haba bansan fulani da raguwar zuciya ba, haba jinin Gwambawa haba ƴar Bafullatanar matata uwar ƴaƴana kukanki azaba ne a zuciyata" Ya yi murmushi cikin dauriya ya ce "Akanki bulala nawa na shanye? Gwambawa sun gana mini azaba a haka na shanye shaɗin na aureki, mene ya kawo haka? Kinga juriya ce da yadda da Allah da ƙarfin addu'a, ki zama jaruma kamar yadda na zama jarumi a soyayyarki ki yi haƙuri don Allah uwar Jawaad da Sona, garkuwar Du'a haba matar Isma'il amarya kuma uwar gida, idan baki jure ba ina zaki samu ƙarfin qiwwar rarrashin Majeederh" Ya goge hawayen da suke bin idanunta tana shassheƙa ta ce "Na rasa yadda zan yi babu kalaman ban haƙuri ga Majeederh, wannan yaron ya cucemu he disappointed us" Uncle Isma'il ya ce "Da wannan salon yaudarar taki da kika sace zuciyar Isma'ila da shi zaki rarrasheta, komai na rayuwa yin Allah ne ba namu ba, bama da ikon hana komai ko faruwar shi take heart please" Miƙewa tayi tana gyara ɗaurin zaninta ta nufi part ɗin da Majeederh take ciki. A zaune ta sameta idanunta rufe ƙirjinta na ɗagawa kamar wacce asthma ɗin ta take shirin tashi, kafin ta ƙarasa ta nufi wajan freezer ruwa ta ɗauka mai sanyi ta tsiyaya a kofi ta ce "Drink"
"Azumi nake" Majeederh ta bata amsa, Anti ta ce "Ai kowa zaki karya azumin me?" Ta yi ƙasa da kai ta ce "Nuna godiya ga Ubangiji" cewarta.
Anti ta nemi waje ta zauna tana bin bedroom ɗin da kallo a hankali ta ce "Hawwa'u!"
"Na'am Anti" Ta amsa gabanta na faɗuwa haka kurum. Anti ta ce "Mece ƙaddara?" Da mamaki Majeederh ta kalli Anti sai kuma ta ce "Jarrabawa ce da Ubangiji yake jarabtar bawansa domin gwada imaninsa, shi ya sa aka ce yarda da ƙaddara shi ne cikin imanin ko wanne musulmi" Anti ta sauke ajjiyar zuciya ta ce
"Allahamdulillah" Wajan ya yi shiru can dai Anti ta ƙara kiran sunan Majeederh a wannan karam kasa amsawa tayi ta ce "Hawwa'u mace da ciki da ciki ta mutu, miji ya rasu ya bar matarsa da yaransa, uwa ta rasu tabar miji da yaranta, iyaye sun rasu sun bar yara, Gabaɗaya hakan tsarin waye? TSARIN ALLAH, Ubangiji ke da ikon ƙaddara kuma shi ne wanda masarrafar rayuwarmu ke hannunsa, ya haliccemu domin bauta masa dayin biyya da iyaye duk mutumin da ya cika haka bazai taɓa tuzarta ba, ƙaddara shuɗaɗɗiyya ce, ba za'a taɓa hana zuciya ƙuntata ba, domin baka da ikon yin haka amma akwai mataki na kare kai, Majeederh ki yarda Allah ke tsara duk abinda zai faru, Mu so wanda ya ke son mu shi ne soyayya, mu so Mutum ya so me shi ne dacewa a soyayya, mun so abu babu damuwa maybe abin ya dace aso shi saboda nagartar da yake da ita, rasa abinda zuciyar mu ke so, bashi yake nufin rasa rayuwarmu ba, watakila rabonmu na ta wani wajan yana jiranmu, idan soyayya na gudunm ƙauna ta har abada tana can wata duniya idanu rufe tana nemanmu, faɗuwa a soyayya nuni na cewa hakan ba alheri bane a ranmu, ba laifi bane don munyi kuka idan an yaudaremu, babbar asara ce ka komawa wanda ya guje ka ko ya yaudareka, hakan na alƙinta mana mun rasa wani abu a baya inma mu rayuwa inma mutum mu rayu da sanin Ubangiji ke zana komai cikin tsaftaccen allon lauhil mahfuz, yi kuka Majeederh akan farin ciki kada ki yi kuka akan baƙin ciki...." Anti ta yi shiru kana a hankali cikin rauni tausayi da fargaba ta ce "Ba a ɗaura aurenki da Alpha ba, domin ya gudu bisa ra'ayinsa na ƙin auren wanda Ubangiji ne kaɗai ya san dalili" Da wani irin Expression Majeederh take kallon Anti, kallon da sai da hantar cikinta ta motsa, gabanta ta faɗi domin bata taɓa ganin rikiɗewar idanu lokaci ɗaya irin na Majeederh ba, ƙarar tsayawar abu a wuyan Majeederh yasa Anti taɓata ta ce "Majeederh ki yi haƙuri ki yi haƙuri, ban san yaushe ne hakan ta faru ba, ban san mene ya sauyawa Alpha ra'ayi ba, amma nasan yana son ki ina ganin hakan acikin idanunsa, rabonki yana wani tsagin rabo mai girma rabon da zai bawa kowa mamaki,ki yi haƙuri da rayuwa Majeederh" Maimakon kuka sai taga Majeederh ta saki Murmushi, murmushi mai kyau wanda bata taɓa ganin irinsa a fuskarta ba, irin wanda dashi gwara kayi kuka irin sa yafi kuka ciwo a zuciya hakan na nufin Mutum yana cikin halin da kuka ya yi masa kaɗan. Ta miƙe tsaye ta ce "Zani gida"
"Majeederh are you okay?" Ta ce "In sha Allah" A hankali ta ce "Kiyi haƙuri ki miƙa lamuranki ga Ubangiji please" Ta ƙara yin murmushi ta ce "Ba komai, bani hijabi da liƙab ɗin Sona" Ba zata iya tsayar da ita ba, akan Idanunta ta saka hijabin da liƙab ɗin tare da amsar kuɗin napep wajan Anti ganin haka yasa Anti ƙwalawa Aaliyyah kira ta ce "Maza jeki ku tafi akwai matsala" Jefa ƙafafuwanta kawai take without knowing ina take takawa, da gudu kuma Aaliyyah ta cimmata ta tsare mai napep ta ce masa Lodge Road..... Misalin 8 na dare wani irin ciwon kai ya kama Majeederh har bata iya gani sosai ga jiri da ƙyar ta miƙe ta nufi part ɗin Abbu da yake kiranta tana zuwa ta zube a ƙasa wajan ƙafafuwansa ta kasa cewa komai. Ya dubeta ya ce "Kin kyauta"
Da sauri ta kalle shi tana son tambayar mai tayi sai kuma tayi sbd nauyin da harshenta ya yi mata wanda ya tilasta mata kame bakin. Ya gyara zama da kyau ya ce "Kin tuzartani cikin dangi Majeederh,kin kunyatani kin cin mutuncin shekaruna, akan namiji? Yanzu me gari ya waya? Kin barwa kanki abin gori kin bar mini nima koma babu komai tarihi zai kafo akan Alpha ya gudu saboda baya ƙaunar aurenki" Ya girgiza kai ya ce "Majeederh kin yarda ni mahaifin ne?" Da sauri ta ce "Wallahi Abbu ban taɓa kokwanto hakan ba" Ya miƙe tsaye tare da ɗakko Alkur'ani mai girma daman yana da alwala ya ɗora hannunsa akan Alqur'ani izzu sittin ya ce "Wallahi wallahi Allah Majeederh ni ne ubanki mahaifinki, wanda jinina ke yawo a jijiyoyinki, na rantse da Allah ni ne mahaifinki ni Alhaji Abdul'aziz Khan" Ta dinga girgiza kai babu hawaye ko ɗaya a Idanunta ta ce "Don Allah Abbu ka bari" Ya kalleta ya ce "Amma ni ina tunanin kamar an sauya mini ɗiyata, kamar ke ɗin ba Majeederh ta bace"A rikice ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, Ya Allah wallahi bana gane komai ko fahimta" Ya zauna ya ce "Kin kasa bani abinda nake so nake buri Majeederh, na rasa yadda zan yi dake kin kasa rufa mini asiri, Hawwa'u aure fa ba dole bane tunda zaki iya riƙe kanki, kuma ni na san jinkiri ne kawai kika mijinki nan zuwa ki taimaka mini, ni mahaifinki ne" Majeederh ta ce "Ka yafe mini, ba sake cewa ina son kowa ba shi na don Yayana ne ai kaga ma bai aurenin ba shikenan sai na fara neman aiki" Abbu ya saki kuka wiwi yana cewa "Faɗa kawai kike Majeederh ki je kawai nama haƙura kiyi aurenki kawai kuma na yafe" A rikice, rikicewar da ko sanda aka faɗa mata Alpha ya gudu ya fasa aurenta ba ta yi ba ta riƙe ƙafar Abbu ta ce
"Nayi asara Abbu, rayuwata ta halaka na shiga uku akaina kake zubar da hawaye mai yasa zaka ja mini azabar Ubangiji Abbu Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Abbu kuka kake a kaina??" Ganin yadda halinta ya tashi ƙarara yasa ya ƙara rushewa da kuka tashin hankali ya bayyana akan Majeederh amma ko ɗison hawaye babu a fuskarta zuciyarta ta ƙafe ta ce "Na tuba, wallahi na tuba gobe zan nemi aiki zan fara nayi maka al'ƙawarin wadataka da abinda kake so iya kacin iyawata, za ka yi alfahari dani Addu'arka da albarka ka nake nema kawai" Ya share waye ya ce "Da gaske zaki aikin?" Ta ce "Na yi alƙawari" Ya sauke ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ya ce "Kin cika ƴa, na gode ƙwarai Allah ya yi miki Albarka" Ta miƙe da ƙyar zata fita ya ce "Ga mata nan da yawa na garari duka babu aure, shi fa auren nan lokaci ne kiyi ta azumi" A wannan lokacin bata fahimtar komai, dishi dishi take gani ga jiri ga kuma haki da ƙyar ta lalubi hanya ta nufi part ɗin tana ta faɗi wanwarsa a tsakiyar ɗakin babu numfashi..... Bayan kwana bakwai da faruwar komai Latifa na driving fitowar su kenan daga B.u.k sun shiga duba wani ita da Majeederh, ganin ta ɗauke hanya ya sanya Majeederh ɗago kai a hankali tare da zubawa titin idanun sai dai bata ce komai ba, ta maida idanunta ta rufe mamakinta kuma bai shige ganin yadda Latifa take wani Mahaukacin driving ba. A hankali ta ce "Kee" Murmushi kawai Latifa ta yi cikin sauri ta ce "Ina da hankali ba kashe mu zan ba, nasan adadin giyar dana saka ban shige limit ba" Ta juya ta kalli Majeederh suka haɗa idanu ta ɗaga mata gira ta ce
"Afuwa Malamarmu zan shiga Tahir Quest Palace ne" A gajarce Majeederh ta ce "Hotel?" Latifa ta ce "Eh, Abu zan amsa ai" Majeederh ta yi shiru tana tunani me zai sanya ita kowa ta shiga hotel? Ai hakan babban zunubi ne, kayi ta ganin kartin maza ba zata iya wannan mummunan saɓon ba. Bata ce komai suna zuwa gate ɗin shiga Majeederh ta ce "Wait"
"Like how? Kamarya na tsaya?" Ta ya motsa fuska ta cikin liƙab ta ce "Amai nake ji" Jin hakan yasa Latifa tsayawa Majeederh ta fito da ƙafafuwanta daga cikin motar tana fitowa ta ce "Shiga,ki saman nan" Girgiza kai kawai Latifa ta yi taja motar a 150 ta shige cikin Hotel.... Tana tsaye bakin Hotel ɗin ta ji an ce "Malama Majeederh me kike a nan?" Da sauri ta ɗago kanta ganin ɗan unguwarsu yasa tayi saurin jan jikinta baya daidai nan mai napep ya tsaya ta shiga, saurayin ya dinga mamakin ganinta a bakin hotel. Har sama da awa guda Latifa bata fito ba, can sai ga motar ta ganin babu Majeederh ya sanya ta kirata a waya ta ce "Kina ina ne?" A taƙaice ta ce "Gida"
"Gida kuma? Au tafiya ki kai" Ta ce "Kamar uzurinki babba ne, ni kuma ina jina Uncomfortable a wajan" Kafin ta yi magana Majeederh ta kashe wayar. Lokacin da Latifa ta isa gida ta samu Aliyu tsaye a balcony sanye da wata farar singlet sai gajeren wando hannunsa riƙe da coke yana sha, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kai, ta ƙarasa inda yake tana murmushi ta ce "Sweetheart harka dawo?" Bai ce komai ba. Ta saka hannu ta karɓe coke ɗin hannunsa tana sha ta ce "Am sorry"
"For...?" Aliyu ya tambaya yana zuba mata narkakkun idanunsa. A hankali ta ce "Da daɗewa, na raka Majeederh meeting ne a Tahir Quest Palace" Ya dinga kallonta sai kuma ya ce "Ohk" ta zauna a cinyarsa ta ce "Me kake yi kai ɗaya?" Ya haɗe fuska sosai ya ce "Ɗaga ni" Ta ɗaga shi ya dinga kallonta up to toe kana ya ce "Exlty, tun jiya kayan nan ke jinki kenan baki wanka ba?" Ta yi shiru ya miƙe tsaye tare bi ta gefenta ya shige ciki, yana zuwa ya haura sama not too long ya fito cikin tattausan voyel fari tas sumarsa kwance luf hannunsa zube cikin Aljihu ganinsa haka ta ce "Ina zaka?" Ya dinga kallon parlourn kamar na mahaukata sai warin yawu yake, Aliyu ya rasa me ma zai ce can ya ce "Ki tabbatar kin gyara gidan nan, Hajia na hanya" Yana faɗin hakan ya fice, ya ɗauki good 20 minutes kafin ya shigo yana fitowa daga mota ya nufi cikin gida, yadda yabar parlourn tun jiya haka yake ya ajiye takeaway ɗin hannunsa cikin ɓacin rai ya nufi bedroom ɗinta yana toshe hanci, ganinta ya yi durƙoshe jini na zuba ta ƙasanta a rikice ya nufeta yana faɗin "Wife lafiya badai cikin ne ya sake zubewa ba?" Cikin mawuyacin hali ta ce "Aliyu shikenan yanzu ma mun rasa shi, na rasa babyna Aliyu cikin ya zube" Gabaɗaya Aliyu ya rikice tashi ƙaddarar kenan ya ce "Taya kika san ya zube? Wife kada ki tarwatsa mini zuciya" Da ƙyar ta ce "Wallahi ya zube" Bai magana ba ya sunkuceta zuwa mota, suna zuwa likita ya tabbatar ya zube Aliyu har kuka ya yi domin wannan shi ne karo na uku.... Majeederh na zaune tana shigar da bayananta domin ta samu offer a B.u.k za tana koyarwa, da kuma gidan t.v akan yiwa mata wa'azi musamman da Ramadan ke gabatuwa. Mami ce ta fito fuskarta ɗauke da murmushi ta ce "Yawwa Majeederh shirya yanzu ki je gidan Amani ƴar wajan Hajiya Nusaiberh haihu tayi kuma babu wanda zai zauna mata" Majeederh ta kalli Mami ta ce "Mami kuma ni zan zauna mata? Ina cewa ko Aaliyyah ta girmi yarinuaty? Ina Hajja? Kakar Amani ɗin?" Mami ta ce "Hajja tana Gombe, yayyun Amani kuma duka aure ne da su Kinga ai ba a ce suzo ba suna gidan mazajen su, Su Raihana ma haka, za a Turo Hajja na ce kawai ta zauna ke kyaci tunda kina zaune gida ke ba aure ba, ki je kiyi mata arba'in ɗan wanki da abincinta dana mijinta" Majeederh ta kasa cewa komai ga biyya da take da ita bisa dole ta shirya ta nufi Badalawa.... Daddare Majeederh ta gama abinci tsaf tana zaune a parlour Amani ta ce "Allah sarki ashe Alpha guduwa ya yi wai za a ƙaƙaba masa ke kuma baya so? Haka Raihana ta ce mini, ni dai don Allah ba ruwanki da mijina daya dawo ki shige bedroom kawai haka kurum yadda mata suke kwantai ki aure mini miji na shiga uku" Majeederh dai ta yi shiru Amani ta ce "Kema dai ƙuruciya ke damunki ina ke ina Alpha? Yaran zamani kenan" Majeederh ta miƙe zuciyarta a ƙun ta ce wai ƙanwar ƙanwarta take faɗa mata haka? Maybe ƴar cikinta da auren wuri ta yi.....Majeederh ta fara koyarwa a B.u.k kuɗi take samu sosai ta zama feminist ɗin dole, a cikin shekarar Abbu ya je makka arziƙi ya ci uban nada, tsakanin Majeederh da kuɗi siyan suttura itama ba da yawa ba gudun kada Abbu ya ce ta kashe kuɗin....
*After 3yrs*
Lokacin Majeederh nada shekaru 31 cif a duniya a lokacin ta ƙara cin ta ƙara cin gasar Alkur'ani ta duniya, Nigeria ta ƙara ɗaukan award, kuɗin data samu ba zai faɗo ba, wannan karan a Saudiyya akai murmushi kwance a fuskarta ta tarawa Abbu dukiya tana tsaye riƙe da Award idanunta ya sauka akan wani Matashin ko magidanci da yake ta kallonta Without blinking his eyes sai ta ji ta tsargu ta shafa fuskarta ta jita a rufe ta sauke numfashi, tana ƙoƙarin barin hall ɗin musabaƙar ta ji an ce "Tagawa lafiya Meke faruwa?" Ta sauri ta juya idanunta ya sauka akan kyakkyawar fuskarsa sai ya motsata yake kamar yaro ga wata ilhama dake kwance a kanta, ta ƙara ware idanu a ranta ta ce "Ƙhulud's husband, Ajlaal?" Gabaɗaya fadawa suka rufe shi ruf ganin sai zufa ce ke yanko masa jikinsa na wani irin ɓari "Sannu Tagawa, Allah ya ƙarawa sarki lafiya" A ranta take Mamakin yaushe Ajlaal ya zama sarki? Kuma ta san sarkin Makka ai bai mutu ba, tana tsaye a wajan aka shigar dashi wata ƙaramar mota mai azabar kyau aka nufi Palace da shi. Ta ɗan taɓe baki ta nufi mota zuwa masauki domin a gobe zata koma ƙasarta Nigeria tabar Saudiyya ɗin, Majeederh ta zama kamar namiji sbd jajir cewa ƙoƙari da neman na kai, sai dai ba ruwanta da kowa magana sai ya zame dole ga bala'in ji da take a lokacin kuma gabaɗaya dangi kowa ya shiga yar bata da habaici babu aure sai gantali Anti ce kawai ke bata baki Uncle Isma'il ma ganin laifinta yake aka juya mata baya ko taro ta daina shiga......
Titin Government house cike yake da abun hawa an tara uban go-slow manyan mototci da ƙanana, masu napep da barura hankalin kowa a tashe yake sbd ranar data ƙwalle, an kuma rasa abinda ya haddasa go-slow ɗin... Abbu ya gyara zamansa a bayan mota yana jan tsaki ya ce "Nigeria ba zata sauya ba" Driver ya ce "Wallahi Alhaji kamar faɗa ake a tsakiyar titin ma" Abbu ya ƙara jan tsaki ya ce "Fita if there's any way sai ka bi" Driver ya fita, cikin sauri yake kutsawa har ya ƙarasu tsakiyar titin. Wata baƙar mota ce lafiyayyiya daka gani ba a jima da siyanta ba, ita ta tare kan titin, sai wasu ƴan matasa wajan su goma tsaye a wajan sun saka wani a tsakiya wanda bakinsa ya fashe jini na zuba, sai a lokacin ya ƙara lura da sauran motocin da sukai blocked hanyar.... "Fouk You" Wani ya furta daga cikin samarin daga shi sai gajeren wando ko riga babu jikinsa kansa babu ko gashi sbd tabbatacce ne shi Ya nuna guy ɗin da suke doka ya ce "Kai dan ubanka sa'an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that? He?" Taj ya saki dariya ya ce.
"You're just wasting your time, ka ci uban ɗan Shegiya muga waye ya tsaya masa a Nigeria, Legas ma babu wanda ya isa damu balle Kano"
"Exlty, We are Nigerians, we will decide, we will say whether it is heard or not, there is no one behind us..... Tell them" John Ya faɗa yana murza gun ɗin hannunsa. Taj ya ƙara sakin dariya ya ce ya ce "Speak louder John, ba wani shege" Joshua ya ce "Mahaukata ne ku, wallahi kun saɓa ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa ƙafar daba da hannun hango a zubar titi" Driver ya zare idanu. A na kana wani police ya zo ya ce "who are you? Waye uban a garin nan? Dalla ku matsa akan titi.....,"
"What if we refuse?heeee?" Gabaɗaya Gang team ɗin suka juya idanunsa ya sauka akan shi, fitowarsa kenan daga cikin mota, Matashin saurayi mai ji da ƙuruciya. Police ɗin ya ce "I'll report, za ku yi prison for life" Guy ɗin daya fito daga motar yana wata iriyar tafiya majestic har ya ƙarasa gaban police ɗin a taƙaice ya ce. "Ohhh" Ya faɗa yana hura masa yahaƙin Cigarettes... Police ransa ya ɓaci ya ɗaga hannu zai nuna shi da yatsa cikin zafin nama guy ɗin ya kama hannu tare da murɗewa nan take hannun ya kare.......Kuka Abbu yake wiwi hannunsa dafe da Alkur'ani ya ce "Wallahi wallahi Majeederh ni ne ubanki, mahaifinki ni na haifeka jinina ke yawo a jijiyoyin jikinki, Majeederh ina tunanin ke aka sauya mini kin tuzartani kin ɓata mini suna a dangin kina roƙan Soyayyar namiji? Ni na cancanci haka?" Majeederh ta ce "Ka yafe mini, zan yi aikin ba zan ƙara ba kuma ba ai bai aurenin ba he left me"...... Shekarunta 31 cif tun ranar ba wanda ya ƙara cewa yana sonta balle aure, a haka ta ƙara zama Gwarzuwar Alkur'ani wacce aka gabatar a Saudiyya.....
Sun cike titi babu wajan da mota zata shige, sun haddasa go-slow na ban mamaki wasu ne da basu da maraba da ƴan fashi wajan su goma a tsakiyar titin sun saka wani a tsakiya suna duka.
" Kai dan ubanka sa'an ubanka ne ni? How dare you talk to me like that? He?" " Wanda suke doka ya ce "Me nayi muku?" Taj ya ce "You're just wasting your time, ka ci uban ɗan Shegiya muga waye ya tsaya masa a Nigeria Bama kano ba, Lagos ma babu wanda ya isa damu balle Kano"
Joshua ya ce "Mahaukata ne ku, wallahi kun saɓa ba haka bad boy ya ce ba, a karya masa ƙafar daba da hannun hango a zubar titi" Wani police ne ya ce "Ku titin iyayenke ne? Zaku jawa kanku dilla ko kwashe motocin ku, ku bawa jama'a waje.
Daga bayansa aka ce "What if we refuse?heeee?" Gabaɗaya Gang team suka kalli Bad boy wanda ya fito daga mota, police ɗin ya ɗaga hannu zai nuna Bad boy kafin ya yi pointing ɗinsa ya kama hannu tare da karya shi nan take....
https://arewabooks.com/chapter?id=64ac50ef324ef73a495e70b9"This is the first and last da za ki yi pointing nawa da finger, Dog!" Guy ɗin ya furta hakan a tsawa ce, mai da police ɗin ma ce ta hanyar faɗin “Za Ki yi” Saboda rashin cikakkiyar hausa maganar ta shi ma a gurɓace take. Sosai Police yake jin azaba nan take hannun ya kumbura zufa na yanko masa ya ce "This is not fair, su waye ku? You came and blocked the road and prevented the vehicles from entering"....“Your Father” Guy ɗin ya faɗa. Yana ware kuma dara-daren idanunsa akan Ɗan sandan, Kyakkyawan saurayi ne mai ƙarancin shekaru domin baifi 16yrs ba, kulawa da kwanciyar da jin daɗin rayuwa haɗi da samun duk wani abun da yake so ya sanya jikinsa wani irin mahaukacin buɗewa, domin gabaɗaya cikin Gang team ɗin yafi kowa girman jiki, tsayi da kauri jikinsa a murɗe yake ga wasu six-pack da suka bayyana musamman saman ƙirjinsa, baƙi ne shi sosai irin baƙin ƴan America ɗin kana ganinsa kaga Ba'amurke baƙar fatarshi mai kyau da sheƙi irin baƙin da yafi farar fata kyau da ɗan kan idanu. Gabaɗaya jikinsa zanen tattoo ne daga wuya har zuwa ƙirjinsa da hannaye ga wata ƙatuwar sarƙa mai tabon Cross a jiki. Sumar kansa a murmurɗe kamar indomie wacce ta ƙara fito da kayan fuskarsa da jajeyen laɓɓansa.... he is outstandingly handsome and robust, very masculine. Cikakken namiji mai iko da tsayawa akan ra'ayinsa. Police ɗin ya nuna kansa ya ce "Ni ka ke zagi?"
"An zage ka titin na ubanka ne?" Taj ya faɗa yana nufar kan Police ɗin ganin haka yasa ya yi saurin yin baya tare da barin wajan. Taj ya ja tsaki ya juya ya kalli Guy ɗin daya karyawa police ɗin Hannu ya ce
"Abraham let's go" Da wani irin kallo wanda aka kira da Abraham ɗin yake bin Taj da shi cikin warning ya ce "Sai na ci Babarka, duk sanda ka sake ce mini Abraham" Ya faɗa cikin harshen turanci. Da sauri drivern Abbu ya juya zuwa wajan mota yana isa jiki na rawa ya ce "Yallaɓai wallahi ƴan fashi ne, mun shiga uku" Abbu ya ɗago kai ya dubi driver a hankali ya ce "No! Ba ƴan fashi ne, ƴan fashi da rana??" Driver ya ce "Kwarankwatsa su ne, hadda bindiga irin ta film na gani fa? Innalillahi mun shiga uku" Abbu ya ajjiye Jaridar hannunsa domin meeting ne da shi na gaggawa akan wata contract da zai yi signing akan papers ɗin. Ganin haka ya sa Driver buɗewa Abbu ƙofa ya fito yana tattare babbar riga cikin sauri kana ganinsa kaga manyan Alhazawan nan masu tashe da kuɗi, ya dinga ratsa mototci yana shigewa har ya isa tsakiyar Gang team ɗin. Abraham na tsaye hannunsa riƙe da Cigarette yana busawa tare fitar da yaƙinta zuwa sama. Taj ya ce
"Guy's let's go, go go" Abraham na ƙoƙarin shiga mota ya ji an damƙi wuyansa ta baya, abinda tunda uwarsa da haife shi ba a taɓa yi masa ba, kasa juyawa ya yi saboda tsananin mamaki kafin a ankare ya ji an fizgoshi tare da sauke masa wasu tagwayen maruka. Gabaɗaya Gang team ɗin, Taj, Joshua, John... Da sauran sukai kan Abbu kowa yana fito da bindiga Jikin Abraham har wani tsuma yake naman wajan na wata kakkarwa idanunsa sukai jajur Yatsun Abbu suka fito raɗau a saman kyakkyawar fatarsa. Da wata murya ya daka musu tsawa ya ce "Noo!!!!! Don't shoot him" John ya ce "But why? Marinka ya yi, He slapped you, waye shi a Kano? Ubansa ma ubansa zamu ci dan kaza kazanshi" Abraham dai kallon Abbu yake without blinking his eyes. "Ni ne zan hukunta shi, Ba a taɓa mini haka ba in my whole life" Abraham ya basu amsa. Cikin sauri kuma ya ƙwaci bindiga a hannun Taj zai bugawa Abbu kan bindigar ya ji Abbu ya ce "Wato kune irin gagararrun da muke da su a kano ko? Haihuwar kan titi wanda baku san girma da darajar kowa ba? Shegu gayyar tsiya, gayyar na ayya" Cak Abraham ya tsayar da hannunsa dab da fuskar Abbu ya runtse rinannun idanunsa. Ganin ya tsaya Gang team ɗin suka haɗa baki wajan faɗin "Bad boy Shoot, Shoottt him" Ko motsawa bai yi ba balle ya yi ƙoƙarin harbin Abbu, murmushi Abbu ya yi ya ce "Idan kai ɗan halak ne harbeni, ɗan daba masu kwacan wayoyi sisi babu a aljihu maimakonsa ku nemi aikin yi kun bige da sata da bashi da makami, me ake da talauci shi yake saku irin wannan Allah wadaran naka ya lalace" Wani acikin jama'ar wajan ya ce "A'a Alhaji ɗa ai na kowa ne, ka yi musu fatan shirya idan da rabo watarana sai kaga sun zama wasu a Nigeria bana jihar nan ba" Abbu ya girgiza kai ya ce "Goodness! Ai basu da rabon shiriya irinsu da haihuwar su gwara ɓarin su, basu da wani muhimmaci talakawan banza, maybe na shan wiwi da sigari basu da shi" Yadda jikin Abraham ke ɓari kaɗai zai bawa mutum tabbacin maganganun sun shige su, duk da ba komai yake fahimta ba cikin yaren Hausar.
"Useless" Abbu ya ƙara furtawa yana tofar da yawu. Kafin su Taj su lura Abraham ya shigo dukan kansa da ƙasan bindigar nan nan da nan jini ya fara zubar masa. Ganin hakan ya sa John nufar Abbu Gadan-gadan zai harbe shi kafin ya ƙarasa Abraham ya cimmasa yana zuwa ya dunƙule ya naushi John a ciki yana huci kamar zaki ko kumurcin maciji cikin ƙara ji ya ce "I said no!"
"Bad boy akan wannan tsohon ka ke cutar da kan ka?" A fusace ya sake juyawa kan Taj ya ce "Abu ɗaya ka ƙara cewa zan kashe ka, I'll kill you Taj" Yana faɗin haka ya ƙwaci key ɗin motar shi hannun Joshua motar da tafi ko wacce mugun kyau ya nufa yana zuwa ya buɗe tare da shiga ya jata da wani irin sauri kamar zai tashi sama haka yabar wajan, ganin irin gudun da yake saka Gang team ɗin suka shiga mota tare da marawa Bad boy baya, Abbu ya ja tsaki tare komawa a hankali masu tsaron kan hanyar suka dinga bawa mutane hannu suna shigewa "Ƴan iskan yara gantalallu" Abbu ya faɗa bayan driver ya shige da shi zuwa hanyar su da Murtala Muhd way.... Gudu kawai Abraham yake idanunsa yana zuwa kan corner da zai You-turn danja ta tsayar da shi, a hankali ya ɗora kansa akan string motar zuciyarsa kamar tayi tsalle ta fito sbd wani irin baƙin ciki da takaici da yake ji, This is the second time he finds himself in this situation, bai damu da jinin da yake zuba daga kansa ba burinsa kawai ya tuna inda ya taɓa jin muryar, tabbas ya san muryar Abbu but where? Ba a taɓa riƙe wuyan rigarsa ba balle wani ya yi attempting marinsa, bai kuma san dalilin daya sanya ya kasa yin komai akan Dattijon ba, da alama he's special da wani da wallahi sai ya kuntile hannu idanunsa har wani ruwa ne ke kwanciya sbd tsabar zuciya da taurin rai.... Knocking Glasses ɗin motarshi ya ji ana yi a fusace ya ɗago zai zabga ashar idanunsa ya sauka akan wata yarinyar wacce take duƙun-duƙun ya ja siririn tsaki ganin yadda fuskar yarinyar take duk majina, idanunsa ya ɗauke tare da rufe shi yana jin komai ya duniyar ya fice masa a rai, ya yi dana sanin dawowa ƙasar bakiɗaya. Ci-gaba da knocking kawai tayi ya zuge Glasses ɗin zuwa ƙasa da sauri ta ce "Ka taimaka mini dana abinci saboda Allah Yallaɓai" Bai san meta ce ba, amma ya ji sunan Allah sarai sai ya ci gaba da kallonta, nan da nan zuciyar tausayin sa ta motsa musamman akan ɗiya mace yana da tausayin mata ƙwarai tashin hankalinsa yaga mace na kuka, ya ɗauke yana kwaso kuɗi ya watsa mata ta ƙofa da sauri kuma ya ja motar ya yi gaba... Tun daga ƙofar gate ɗin gidan yake danna horn kafin gatekeeper ya fito ya yi saurin fitowa kansa a ƙasa domin baya jira bai yarda kuma a jira shi ba, ya nufi ƙaramar ƙofar shiga tare barin motar a buɗe a waje, cikin sassarfa cike da kuzari duk da jiri na ɗaukarsa haka ya nufi cikin gidan ya tsaya a ƙofar farko yana danna password ƙofar ya buɗe, a Main parlour ya tsaya cikin zafin nama kamar Mahaukaci ya shiga ɗaukan duk abinda hannunsa ya je kai yana doka shi da ƙasa... Daga saman upstairs aka ce "Grandson!" Abraham bai tsaya daga abinda yake ba, ganin zai jiwa kansa ciwo ya sa David ya shiga sakkowa daga steps ɗin benen da sauri yana zuwa ya kama hannun Abraham ya ce "Waye? Kai da wa?" Yaƙi cewa komai sai huci da yake jikinsa na rawa David ya san Abraham ba zai taɓa magana ba, hakan yasa ya ja hannunsa zuwa saman kujera ya damƙa masa wani cup ya ce "Drink"
Bai tsaya tantance mene ba ya amsa tare da kafawa a baki ya shanye tas, David ya ƙara zuba masa wata ya shanye daga nan ya miƙe ya nufi wani part not too ya dawo hannunsa riƙe da first-aid box ya gyara masa wajan.
"Who is he?" David ya tambaya, cikin mayen daya fara ɗaukar shi ya ce "I don't know, but i knw him na san muryar" David ya ce "Where?" Ya yi shiru... Ganin yana cikin maye kuma zai fi ɗaukar magana ya sa ya ce "Look Grandson, na ce ko da wasa bana son ganin jini a jikinka gwara ka fitarwa da wani jini da a fitar maka, ka ci mutuncin wanda ya ci naka, ka taka wanda ka ke so, kai ɗaya nake da shi a gefena You're my grandson exit? Babanka yabarka, baka da Mother baka da kowa a duniya sai ni, ni ne Grandfather naka, idan kuɗi na maganin komai a duniya to duk irin bala'in daka ɗauko zan ji da shi, ni ne shugaban church ni ne Pasto bayan haka kafi kowa sanin matsayina a ƙasar nan bana country ba, ina da kuɗi mai kuɗi shi ke da magana, a top 5 na masu kuɗin Nigeria zan shiga ciki, Mahaifinka Daniel zai shiga.....," "Stop calling his name, i hate him he's not my father" Abraham ya faɗi hakan idanunsa na lumshewa ya shiga surutan maye yana faɗin
"She left me, Mamina Grandpa, Mamina Mamina" Sai kuma jikinsa ya shiga jijjiga. Grandpa ya yi shiru kafin ya ce "Mamin nan taka maybe she's no more bata ra....," Tasss! Ya ji saukar Glasses ya miƙe da sauri yana riƙe Abraham ya ce "Am so sorry Dear, Maminka na nan I'll find out where she's hiding to" Da ƙyar bacci ya ɗauke Abraham bakinsa ɗauke da sunan “Mamin, JEENA" Ganin ya yi bacci yasa Grandpa kiran Taj a waya ta prvt line nasa yana ɗagawa ya ce "What's happened?" In brief Taj ya faɗa masa komai Ya ce "Ka nemi mai Zane ya yi drawing na mutumin ka kawo mini nan gida" Taj ya ce "Bad boy fa? Ai zai fi yin zanen yadda ake so" Grandpa ya ce "It's secret"....
Saudiya. Majeederh na zaune saman kujera gabanta ɗauke da laptop tana duba abubuwan da zatai a B.u.k idan ta koma Nigeria, komai nata maturel ne nutsuwa ga wani irin jan aji da kamon kai bata sakewa kowa fuska, har office ya buɗe wanda za a dinga samunta kai tsaye a ranakun weekend, ba ruwanta da batun tama sakawa ranta ba zatai ba tunda babu wanda ya ƙara tunkararta tana jin surutai na yawo a unguwa harda Social media ba ga family taƙi yin aure sai yawo... Door bell ta ji ta yi ƙara a hankali ta ɗan zame hannunta daga keyboard ɗin laptop ɗin, tare da ɗan yi shiru tana tunanin who is there by this time? Bata da appointment da kowa amma waye kuma? A hankali ta miƙe tana saka sunglasses ɗin ta na medical kana ta ƙarasa jikin ƙofar ta ce "Who's there?" Aka amsa da "Messenger" "Ok came in" Ta faɗa a gajarce, tana kowa tayi saurin saka hijabi da liƙab kana ta buɗe ƙofar, da mamaki ta dinga kallon mutumin ganin uniform ɗin masarauta a jikinsa da alamar Bafade ne shi yana ganinta ya zube a ƙasa yana kwarara mata gaisuwa, ita dai bata ce komai ba ya miƙe mata wata envelope ya ce "Saƙo ne daga Palace ranki ya daɗe Gwarzuwar Nigeria" Da hannu ta nuna masa ya ajjiye nan ƙasa ya ajjiye bayan ya tafi ta durƙosa ta ɗauka envelope ɗin tana komawa cikin bedroom ɗin, a hankali ta ware iya haɗuwa Envelope ta haɗu wani irin zaibar rubutu ne manne a jiki an rubuta.
_Your Highness Ajlaal Sultaan_
Invite
_Malama Majeederh Abdul'aziz Khan_
Ta duba date yau kenan sai kuma time 4 na yamma, ta dinga juya Envelope ɗin Ajlaal mijin Ƙhulud Arzaan kenan? za taga Ƙhulud farin ciki ya wanzu a zuciyarta duk da fargabar kiran ya ɗarso a zuciyarta.... 3:45 Daidai ta fito cikin wata Abaya dark blue tayi rolling kanta da vail sai liƙab da wani sirrin Glasses a Idanunta hannunta riƙe da hand bag da wayarta, tafiya take cikin tarin nutsuwarta kamala da sanin ya kamata, harta isa motar da ake jiranta tana zuwa driver ya buɗe zata shiga gaba ya ce "Ranki ya daɗe baya, ni driver ne" Ta ɗan girgiza masa kai kamar ba za tayi magana ba sai ta ce "Ina so gaban" Ta shiga ta zauna cikin sauri taja motar sai Palace.... Ƙhulud Arzaan na tsaye cikin shigar larabawa ga tsohon ciki a jikinta wanda shi ne karo na farko da zata haihu, fuskarta ɗauke da murmushi Majeederh na yin sallamawa Ƙhulud ta fasa ihu tare da nufar Majeederh, cak ta tsaya idanunta na gizo mata wani abu sai kuma ta nufeta suka rungume juna sosai sukai farin ciki bayan shekaru nawa sun sake haɗuwa, Ƙhulud ta ce "Ina mijinki fa?" Majeederh ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce "Ban yi aure ba" Cikin wasa Ƙhulud ta ce "Kina jiran haɗaɗɗan namiji ko?" Murmushi kawai ta yi sai kuma ta ce "Kamar labari littafi? Kawai Allah bai kawo ba" Ƙhulud ta ce "Ubangiji ya kawo na gaban kwatance amma na yi mamaki na ɗauka ma kin haihu wlh" Majeederh ta yi shiru Ƙhulud ta ce "Mu je wajan Granny Zaytoon" Suka miƙe wani plat suka nufa mai kyau da tsari. Zaytoon na zaune saman ladduma gabanta cike da kayan itatuwa ana mata firfita suna shiga Zaytoon ta sauke wani irin kyakkyawan murmushi tana tafa hannu ta ce "Lale lale da babbar Malama" Gabaɗaya Hadiman suka fita Majeederh ta zube gaban Granny tana gaisheta ta amsa da "Ma sha Allah, Allahamdulillah Sannu kin ji ina sake tayaki murna" Ita dai kanta a ƙasa, Granny ta dinga kallonta ko zata cire liƙab ɗin fuskarta amma taƙi itama kuma bata ce ta cire ba sbd she don't want interfere a rayuwar Majeederh. Majeederh ta ɗago kai idanunta ya sauka akan wata matashiyar mata mai wani kyau kamar ba mutum ba, ta dinga kallon matar sai kuma ta ce "Ina yini?" Granny ta juya ta kalli matar da Majeederh ke gaisarwa wacce take zaune saman wheelchair Granny ta ce "Wai Gimbiya kike gaidawa? Allah sarki Hawwa'u ai bata da lafiya bata magana bata tafiya hannunta kawai ke motsawa" Cikin tausayawa Majeederh ta ce "Allah sarki, Allah ya bata lafiya" Granny ta ce "Ƙarasa wajanta mana, takwararki ce sunanta Hawwa'u yadda take kallon naki kamar ta sanki bayan ko Nigeria bata taɓa zuwa ba" Majeederh ta ƙarasa gaban matar ta durƙosa ta ce "Sannu Allah ya baki lafiya" Ga mamakinsu sai su kaga tayi murmushi harda hawaye ta riƙe hannun Majeederh ƙam! Sun jima kafin ta ce "Naga saƙon kira" Ƙhulud ta ce "Ohh Takawa ke kiranki" Gabanta ya faɗi ta ce "Mai martaba Sultaan?" Ƙhulud ta ce "Tsohon zance tuni muka ture shi mijina ke kan karaga ai, Mai martaba Ajlaal Sultaan ke kiranki" Ta yi shiru bata ce komai ba Granny ta ce "Fulani rakata mana, yana part ɗinsa ai ya bar fada tuni sai miskilanci yake ji jiya da yau" Ƙhulud ta ce "A'a jinin sarauta ke yawo a jikinsa fa, ba wani miskilanci" Tana faɗin hakan ta miƙe tsaye Majeederh ta miƙe ƙirjinta sai bugawa yake a haka suka ƙarasa wani irin ƙyakƙyawan plat mai ɗaukar kyau ga matso tsaran ƙofa nan birjik suna ganin Fulani suka zube Ƙhulud ta yi murmushi tare shigewa Majeederh ta bi bayanta, suna shiga Ƙhulud ta yi sallamawa yana zaune hakimce idanunsa rufe yana cikin wata Jallabiya mai kama da Alkyabba, ya ɗora hirami a saman kansa ga gefensa fuskarsa suma ta sakko kamar ka taɓa shi jini ya fito, bai amsa gaisuwar Ƙhulud ba, bai kuma buɗe idanunsa ba, Ƙhulud ta miƙe ta ce "Ina zuwa Majeederh" Majeederh kamar ta saka kuka ta cikin liƙab ɗin, amma ta kasa ko motsi. Wajan ya yi shiru ita ba tayi magana ba shi ma bai ce komai ba, bashi da niyyar cewa komai ɗin, shafewar seconds kafin Majeederh ta ce "Barka da hutawa Takawa" muryarta na rawa domin ba ƙaramin kwarjini ya yi mata ba, tana jin kanta Uncomfortable a gabansa musamman da taga kamar bai taɓa sanin wani Abu Annuri ba a saman fuskarsa. Ta ɗauka bai ji ba ta ƙara maimaita gaisuwar nan ma shiru tana ɗago idanunta da niyyar ganin ko baya wajan cikin rashin sa a idanunsu ya sarke cikin na juna, Ajlaal Sultaan ya kafeta da narkakkun idanunsa can kuma ya taɓe baki kana ya janye idanunsa a hankali ta ce "Gani" Ya jima kafin ya ce "Ke wa?" Tama ɗauka ba zai magana ba sai ta ji ya ce hakan. "Ance kana kirana" Bai ce komai ba ganin tana ƙoƙarin wulaƙanta kanta gabansa duk da tarin nata kimar ya sa ta miƙe tare nufar hanyar fita, sai da ta je bakin ƙofa ta ji an ce "Wait" Bata ɗauka da ita yake ba duka jikinta rawa yake Allah ya gani bata taɓa ganin mutum nai haibar Ajlaal ba zata fita ta ji an ɗora hannu akan hannunta dake jikin Handle da sauri ta juya ta ganshi tsaye kamar ya haɗiyeta gabaɗaya ya yi mata rumfa da ƙaton jikinsa rawar jikinta ya tsananta haka ma bakinta ƙirjinta na ɗagawa tunda uwarta ta haifeta bata taɓa yin kusanci da namiji kamar yadda sukai da Ajlaal ba, hannunsa ya murza akan nata kana jata zuwa cikin bedroom ɗinsa ba parlour ba......
No Edited
Zamu fara page biyu kullum, biyu a arewabooks ɗaya a WhatsApp group🤓....... MIJIN MALAMA it's a paid book Subscribe before you read..... Via WhatsApp for more information 08119237616Zame hannunsa ya yi yana ɗan kame fuskarsa a hankali kamar bai son magana ya ce "Remove the vail" Ta yi saurin ɗago kanta zata kallesa amma ta kasa ya yi mata wani irin bala'in kwarjini, ta kasa cewa komai ta kasa aikata abin da ta yi niyya. Ajlaal ya tsuke tamau yau sai ya ga abinda ya turewa buzu naɗi. Bakinta na rawa ta ce "Baa...ba...baaaa!" Ta kasa furta abinda tayi niyya kaifin idanunsa sosai ya tasirin a kanta a hannun ta ce "Am sorry i can't do that" Ta faɗa tana ƙoƙarin barin bakin bedroom ɗin nasa, wanda ta turje taƙi yarda ta shiga domin ta san sirrinsa ne. "Fita" Ya nuna mata hanyar fita tun kafin ta nufi hanyar ai kamar zata kifa duk da girman jan ajinta haka tayi waje, zata gilma ta gabansa ya sanya hannunsa mai taushi ya fizgota ta dawo gabansa, kai tsaye kuma fuskarta ya nufa da hannunsa He tried to lift the mask off her face. Duk jikin Majeederh rawa yake nan da nan ta ruɗe ta marairaice ita bata taɓa ganin rashin kunya haka ba, daman larabawa ba wani ta ido gare su, gashi ba zata iya yi masa rashin kunya ba, ta rirriƙe shi ta ce "Please don't"
"Ohh!" Ya furta yana riƙe hannunta gam, sai ka rantse ba Mai martaba bane, ganin da gaske yake ya sa ta ce "Please Mai martaba" Nan ma ya yi mata banza aikowa ta daddage ta sakar masa cizo a hannu da sauri ya saketa yana faɗin "Auchhhii" Ta re da ɗan lumshe idanu sai kuma ya buɗe, suna haɗa idanu ya zaro mata manyan idanunsa ta kwasa da gudu ta nufi ƙofa ya yi saurin shafa kansa tare da nufar bedroom ɗinsa. Tun kafin ya ƙarasa ya ji muryar Ƙhulud na faɗin "Ya na ganki tsaye?" Ita dai Majeederh ba ta yi magana ba, Ƙhulud ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce "To wannan hakin kamar kin yi tsere na zaki fa?" Sai a lokacin Majeederh ta ɗan sauke numfashi tana kame kanta ta ce "Zan ta fi"
"Baki isa ba, sai mun yi lunch tare, Mai martaba bai faɗa miki ba?" Ganin Majeederh ta ƙi cewa komai ya sa Ƙhulud kallonta frm head to toe,She wants to understand Majeederh's situation but she can't understand anything. Ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Ba dai miskilancin naki kika gwadawa mijina ba?" Majeederh ta harareta ta ce "The train at six o'clock in the evening will drop me off, I don't want to miss the train" Ƙhulud ta ce "Ki rasa mana, sai a ƙara neman wani" Kafin Majeederh ta ce komai Ƙhulud's ta shige haɗaɗɗan Bedroom ɗin Mai martaba Ajlaal Sultaan, komai na bedroom ɗin white colour ne, the furniture, bedsheet, Curtain, everything da ake zubawa a bedroom ba ɗakin Ajlaal fari ne, ga wani irin ƙamshi mai sanyi dake tashi. Ƙhulud tayi tsaye tana kallonsa ya fito daga toilet yana tsane ruwa akansa ta ce "Ba dai wanka kayi ba?" Shi dai bai ce komai ba, har ya nemi saman kujerar dake kusa da tafkekekn royal bed ɗinsa ya lumshe idanunsa tare da riƙe kansa da hannu bibbiyu, Fulani Ƙhulud ta ƙarasa kusa da shi tare da zama a hankali ta leƙa fuskarshi suka haɗa idanunsa taga idanunsa jajur "Takawa lafiya kake?" Ya yi shiru sai kallonta da yake tasan kuma ba magana zai yi ba ta ƙara da cewa "Kun gaisa da Malama Majeederh?" Sai a lokacin ya ɗauke yana miƙewa tsaye tare da nufar wajan mirror ta ce "Ran Takawa ya daɗe ina ta magana?" A hankali cikin kasala ya ce "Wa fa?" Ta ce "Malama Majeederh Abdul'aziz Khan, baka ganta ba?" Yana nufa wajan clothes ɗinsa ya ce "Gaskiya, bamu ga kowa ba nan ta zo?" Ta ce "Wai da gaske naga har tsakiyar parlour fa ta shigo, daman Majeederh ɓoyewa ta yi haka last time kuka mini fa ku baku san zumunci?" Shi dai bai ce komai ba ta ce "Ina nan saka kaya kawai ka fito" jin haka yasa ya fasa ɗaukar Jallabiyar da zai saka ya dawo kusa da ita ya zauna yana ɗan turɓune fuska ya ce "Haka zamu zauna" Ta gwalo ido ta ce "Ba kaya?" Ya jinjina mata kai kafin tayi magana ya sunkuceta sai zuwa other bedroom ɗin nasa dana zare idanu ta ce "Ajlaal cikina ya tsofa please ka rufa mini asiri" Ya direta yana binta da wani irin kallo kallo ɗaya tayi masa tasan ba zai ji roƙan ba ya ce "Me?"
"Nothing" Nan da nan Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sanya Ƙhulud yin baccin dole ya shirya cikin wata golden ɗin Alkyabba mai masifar kyau da ɗaukan idanu yana fidda ƙamshin LONG BOARD. Wayarsa daya daɗe bai ɗauka ba ya ɗauka tare da kiran wani Digits, a nutse cikin izza da gadara ya ce "Follow her" Yana faɗin hakan ya kashe kiran ya juya ya tsorawa fuskar matarsa Ƙhulud da kallo sai kuma ya ɗan shafa kai ya ce “Harnarn”........ Majeederh ce tsaye tana kallon kanta a madubi ganin irin sauyin da tayi, tana mamakin yadda take zama tamkar wahainiya, yau ƙirjinta ya cika sosai gobe kuma taga ya koma yadda yake, duk da irin ciwon idanun dake damunta wanda ta same shi sanadin nacin karatu a Egypt, bai hana nuna asalin zubi da tsarin halittar ƙwayar Idanunta, duk inda ake neman cikakkiyar mace wayayyiya, mai hankali nutsuwa sanin ya kamata, educated one za a sanyata a ciki, duk inda ake neman mai ma tsarin diri na ɗaukan hankalin ɗa namiji nan take dole ka sanya Majeederh, takai ta cika bata buƙatar a rayuwar yanzu wanda ya shige ta ganta a ɗakin mijinta, when? Sai kawai ta ɗan yi murmushin takaici a fili ta ce "Bani da rabo ba" Ta sauke liƙab ɗin tare da jan trolley ɗinta zuwa waje, ta shiga mota suka nufi airport, tana zuwa ta samu an fara shiga saura few minutes ya rage jirgin ya tashi, ta shiga ta zauna a mazauninta tana mai sauke numfashi bata jin daɗin komai, dauriya kawai take da nuna jarumtarta a fili. Tunda ta shigo Jirgin idanunsa yake kanta, bai ɗauka zai sake ganinta sbd tun a hall ɗin musabaƙar ya nemeta ya rasa, muryarta kawai tabar masa wacce take masa amsa kuwwa a cikin kunne! Duk wani juyi da harabar daƙiƙo zuwa sakanni, da juyewarsu zuwa mintuna har kawo su zama awa guda basa taɓa tafiya ba tare da amon muryarta ba da bugun zuciyarsa, jin muryar a cikin lokaci ɗaya ta wargatsa masa lissafin shekarun da ya yi na bayyana ta mantar da shi ainahin abinda ya kawo shi Saudiyya. Ganin kamar zata buɗe idanu ya sanya ya ɗauke kai yana mai da dubansa ga Hammad dake masa magana ƙasa ƙasa amma baya ji, tunaninsa ya yi ƙaura daga masarrafar dake sarrafa nutsuwarsa ta ƙwaƙwalwa... Hammad ya ce "Meke damunka wai?" Ya haɗe fuska ya ce "Da aka yi me?" Hammad ya yi shiru sai kuma ya ce "Tun jiya da muka bar hall ɗin nan naga sauyi a tare da kai, babu shiru kasa muka shirya dawowa Naija wai meke faruwa?"
Abuturab ya ɗago kansa baki ɗaya ya zubawa Hammad ya ce "Stop Interrupt!" Hammad ya ce "Oh tambayar ya kake shi ne ƙatsalandan?" Abuturab ya haɗe fuska ya ce "Ban so"
"To Ubana, wallahi sai na tambaya ai kasan ba ishasshiyar lafiya gareka ba, yanzu idan ka mace mini a nan ai na shiga uku wajan Maysoon" Annurin fuskar Abuturab ya ɗauke nan da nan, ya kasa cewa komai a hankali kuma ya juya ya ƙara kallon direction ɗin da take zaune, yana mmkin yadda tunda ta zauna ba tayi motsin kirki ba. Ana haka jirgin ya fara juyawa a ƙasan kwalta kafin a hankali ya shila sama cikin sararin samaniya.... Mai martaba Ajlaal Sultaan ya sauke numfashi yana jin zufa na karyo masa all over himself, ya ƙara fitar da wani irin ɓoyayyan nunfashi a nutse ya ɗaga kai ya dubi yadda jirgin ke nutsuwa cikin gajimare can ƙasan maƙoshi ya ce "Nigeria” faɗin kalamar Nigeria sai ya ji nan da nan ransa ya ɓaci kansa a shiga sarawa da sauri ya ce "Palace please"
Misalin 10:7 jirkinsu ya sauka a airport ɗin Malam Aminu Kano, a hankali suka dinga fitowa, can ta ta fara tako steps ɗin jirgin hannunta ɗauke da trolley, idanunta rufe tana shaƙar iskar dake kaɗawa, idanunta kuma ta buɗe sosai a harabar wajan bayan ta fito daga can wajan da akai iyaka da jirgi mmki ya ishe ta babu wanda ya zo da sunan tafiya da ita, Ya Allah wacce irin rayuwa take ciki me ya sa kowa ya juya mata baya a dangi sbd kawai ba tayi aure ba? Ta duba haɗaɗɗan agogon hannunta taga dare ya yi ta nufi tafiya daga bayanta ta ji an ce "Hawwa'u" Ta yi cak ba tare data juya ya ƙara so cikin nutsuwarsa ya tsaya gabanta yana zuba mata Idanu ya ce "Ba sai saukarki kenan ba?" Ta ɗan kallesa tana kame kanta fuska haɗe duk da ba ganinta yake ba ta ce "In sha Allah" Aliyu ya shafa kai ya ce "Oh wlcm, na yi dropping Papa ne zai je Brazil" Ta jinjina kanta ya ce
"Can i help you? By dropping off?" Ta ɗan yi shiru sai kuma taja trolley nata zuwa gaba ya yi saurin shan gabanta ya ce "Please Malama Majeederh, it's my responsibility to do that" A ɗan taƙaice ta ce "No thank you" Ya marairaice ya ce "Don Allah, ki yi mini alfarmar nan" Bata da wani option daya shige shiga motar ta shi.... Tunda ya fara driving ta rufe Idanunta ta samu kanta da faɗuwar gaba sun jima suna tafiya ta ji ya tsaya bai daɗe ba ya dawo hannunsa riƙe da leader alamar takeaway.
"Sorry, Yunwa nake ji sosai kamar n ci babu tun safe da na ci abinci a wani restaurant" Sai a lokacin ta masa ƴar duguwar magana ta hanyar faɗin "Restaurant? Da aurenka? Akwai adalci ga Latifa anya?" Aliyu ya dai kalleta sai kawai ya girgiza ya ce "Bata jin daɗi, shi ne nayi takeaway" Ta ce "Allah ya sauwaƙa" Parking Aliyu ya yi a ƙofar gidansa bayan ya kashe motar ya fito yana zube hannu a aljihu wani irin baiwar kyau Ubangiji ya zubawa Aliyu, domin ko Ajlaal sai dai ya nuna mana hasken fata da suma mai yawa da kuma launin idanu, gashi da wani irin haƙuri da kawaici amma idan ransa ya ɓaci kamar Mahaukaci haka yake yana da ƙulafuci da saka abu a rai. Ya ce "Kamar an rufe gidan ko?" Ta yi masa shiru yana mmkin yadda Majeederh ke feeling kanta da yawa, tsayin shekaru bai taɓa ganin munafukar fuskar da ake rufewa ba. Jin shiru ta ɗago kai suka haɗa idanu ta kame fuska tana jan jakarta zuwa hanyar gate domin tuni gatekeeper ya buɗe tana jinsa yana magana amma ta yi shiru a gareta haramci ne babba da ɗaukar ƙaton zunubi ga yin magana da namiji baligi sai ya zama dole. Tana shiga cikin gidan taga Abbu tsaye a Balcony ta zube har ƙasa ta gaishesa ya amsa a wannan karan ta yi mamaki da ya ce mata "Congratulations" Ta nufi cikin gidan tana shiga Aaliyah ta rungumeta tana ihun murnar ganinta, Majeederh ta cire liƙab ɗinta bayan ta tsuguna ta ce "Barka da dare Mami" "Yawwa" Ta ce tana binta da ido, Raihana ta ce "Allah mai iko! Ana ta shiga rigar Muslunci ana ci da addini" Aaliyah ta kalleta ta ce "Idan fitsari banza ne kaza ma ta yi mana" Raihana ta watsa mata harara tana cewa.
"Ji saƙarya, ana maganar kan giwa wake jiyo ƙamshin zomo? Mai da wuƙar ni ba tsararki ba ce" Aaliyyah ta riƙe haɓa ta ce "Hooo ƙaasa, to aini walkice daidai da ƙugun ko wanne lalatacce, kuma Majeederh kuturwa uwa ce zama da ita dole murucin kan dutse bai fito ba sai daya shirya" Raihana taja tsaki ta ce "To ai ga sararin subuhana ɗin nan, sai a zuba muga idan za a kwashe daidai, ba girin girin ba ta yi mai" Majeederh dai ikon Allah kawai take kallo domin ita bata ma iya karin magana da habaici ba shi yasa ta rasa fahimtar me suke cewa, Mami na zaune watching all of them. Aaliyyah ta saki dariya ta ce "Ai gurbin idon ba idanun bane, ni masallacin kurawa ce bawa kare limanci daidai yake da datse iskar dake shaƙa, kiyi a hankali domin na kawo kai nasan fari na san baƙi kada ki ja nayi miki wankin babban bargo, domin naga fahimtar ki daidai yake da fahimtar yaron goye, bana son kuma ya kasance duk kun far bakinki kiyi haihuwar guzuma" Raihana ta ce "Me kike nufi da haihuwar Guzuma? An faɗa an ƙara faɗa idan Majeederh tayi zuciya gobe muji loud speaker Liman na sanar da ɗaurin aurenta, waye bai san cewa Majeederh ba auren ne a gabanta ba? Office ɗin data buɗe na mene? Gari gari da take zuwa da sunan kaiwa marayu taimako bayan ƙarya ne na mene? Ke yarinya wahainiyarki ta kiyayi ramata, ta dauwama ba tayi aure ba har Mahadi ya bayyana" Aaliyyah idanunta a cicciko da hawaye ta ce "Bar gaigaye za kici tumu ne, ƙaddara zane gwara ita tata ƙaddarar ya fito sarari mun gani, kuma komai ya yi farko zai yi ƙarshe" Ruma ce ta fito daga ɗaki ta ce "Kaza uwar tune tune mene ya faru kuma?" Kafin Aaliyah tayi magana Abbu ya shigo gabaɗaya suka nutsu ya dinga binsu da kallo kafin ya ce "Kun kyauta, ko wacce ta fice mini daga cikin gida" Raihana ta ce "Abbu ka yi haƙuri baya nan fa, gidan shiru tsoro nake ji" A fusace ya ce "Ya kashe ki, kuzo ku fi ce mini" Jiki na rawa suka ɗauki mayafi da handbags ɗin su ya ce "Shashai, ku dinga faɗa kamar ba jini ɗaya ba zan yi maganin ko wannenku kada ɗan banzan yada dake dawo mini gida" Ya juya kan Aaliyyah ya ce "Dage, basu girmeki ba?" Ta ce "Kayi haƙuri Abbu Anti Jeederh sukewa gorin aure hadda sharri" Ya kalleta ya ce "To kashin awakai, ita Majeederh Ubangiji bai bata baki bane? Sai ke rasai? Ba ita ta sake musu ba da tana cin ubansu tun farko za ayi haka?" Mami ta dinga kallon Abbu sai bata ce komai ba, ya dawo kanta ya ce "Asabe kin kyauta,na kuma gode" Ya kalli Majeederh ya ce "Da safe ki same ni"..... Washegari da safe bayan Majeederh ta shirya cikin wata tsadaddiyyar Abaya Marron irin turkies Abaya ɗin nan ta samu Abbu a parlourn shi yana zaune ya yi shiru bayan sun gaisa ta ce "Abbu gani" Ya ce "Hawwa'u, Hawwa'u, Hawwa'u" Ya yi pointing nata ya ce "Sau nawa na kira sunanki?" Ta ce "Uku Abbu" Ya jinjina kai ya ce "To wallahi Allah na gaji da ganinki a gidan nan" Da wani irin Shock take kallon Mahaifinta tashin hankali ya bayyana akan fuskarta tsoro da wasa fargabar Abinda zai biyo baya ya wanzu a zuciyarta Abbu ya ce "Shekararki 31 a duniya kina gantali,duk sha'aninki suna gidan mijinsu harda yara uku wasu huɗu amma ke kina yawon neman abin duniya? Yaran da aka tsuguna aka haifa akan idanunki duk suna ɗakin mazajan su banda ke, kina jerawa da Majaufiarki kamar sa'arki? Ka kaf Family ke ɗaya ya rage idan kika ɗauke Aaliyyah da Sona? Wallahi wallahi idan ina ganinki a gidan nan zuciyata zafi take daurewa kawai nake idan kuma na ci-gaba da ganinki tabbas zuciyata bugawa za ta yi sbd baƙin cikin ki......
Littafina na kuɗi ne, biya ki karanta cikin kwanciyar hankali da salama da fitar da hakƙina.......
MIJIN MALAMA it's a paid book, pay before you read...... For me information via WhatsApp number 08119237616Ya gara zama ya ce "Allah ya na gani na ga ji da ganinki a cikin gidan nan ba aure, gorin dangi ya Isheni ba zan jure ba, ba kuma zan lamunta ba, shekaru 31 kina haɗa kafaɗu da mahaifiyarki? Gabaɗaya ke ɗaya ya rage a dangi ƙannen bayanki suna gidan mijinki" Da tashin hankali kawai take bin Abbu da idanu ta kasa koda jan numfashi domin a ƙirji komai ya tsaya mata, zufa na yanko mata all over herself, kullum tana jin ciwo a zuciyarta, bata da burin daya shige tayi aure amma kuma bata da ikon aurar da kanta ai? Ciwon dake damunta kullum ƙara yawa yake This pain was different, it was draining and excruciating painful, and soon it stopped abruptly. Abbu ya ce "Kina ji na?" Ta ɗaga masa kai a hankali ya ce "Good, Tun kafin na nuna mini The other side of me ki shiga hankalinki, ko mazan auren ki ka rasa? Kawai kin tsaya zaɓe da ruwan Idanu" Majeederh dai bata ce komai ba, domin sama sama take jin maganganun mahaifin nata rai ɓace ya ce "Get out, ki fari na sake miki maganar fito da mijin aure" A sanyaye ta ce "Kayi haƙuri Abbu" Zata miƙe ya ce "Sit down"
Ya kalleta sosai sosai cikin magana ta fahimta tsakanin uba da ƴar shi ya ce "Mene matsalarki?"
Ta yi ƙasa da kanta, tsayin shekaru 31 bai taɓa zaunar da ita ya ce meke damunta ba, sai yanzu da komai ya ƙare mata “When all is gone” to yanzu ta ce me? Bayan faɗar bata da wani amfani, it's too late to cry. Cikin tsawa Abbu ya ce "Ina magana kina ji na?" Ta girgiza kai ta ce "Lokaci ne bai ba Abbu, ka yi haƙuri" Abbu ya ce "Eclty, ni ne kike cewa lokaci ne bai yi ba? To buɗe kunnenki da kyau ki ji" Ya gyara zama ya ce "Wallahi wallahi ki fita daga idanuna, dana matsa miki a shekarun baya ki yi karatu ai saboda rufin asiri mu ne nothing more, yanzu i have what i want, kin rufa mini asiri yanzu kema ki rufawa kanki kiyi aure hankalina zai fi kwanciya, Hawwa'u am telling you as your father lokacin da zan ƙara miki maganar aure zaki sha mamakina wallahi Allah" Yana faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsa ya barta zaune kamar gunki. "Majeederh!"
Zuciyarta ta kirata, ta yi saurin ware idanunta tana dafe ƙirjinta. Zuciyar tata ta ƙare cewa "Nutsu Majeederh, think about that, wai kina da saurayin ne ma?" Waya taɓa cewa yana son ki? Balle ya yi tunanin sanyaki a gidansa matsayin matar aure ta sunna?" A razane Majeederh ta girgiza kanta, cike da tashin hankali tana sauraren abinda zuciyarta ke faɗa mata, ta yi shiru jin ta ce "To kenan yanzu ya zaki? Shelar kan ki za ki yi ko yaya? Kinga dai bakya son ɓacin ran Abbu ya zame miki dole neman mijin aure.....," Da sauri ɗaya zuciyar ta buge ɗayar ta ce "Ji banza, ke dai ƙwaƙwalwarki bata aiki kamar mai shan miyar kuka, banda awon igiya ce ke kamar Malama Majeederh ce zata yi shelar kanta? Kuma shi Abbun bai san ƙaddara bane? Waye ya jefata wannan halin tun farko? Ba son zuciyarta bane da neman abin duniya? Do what is right not what's easy, yadda ya dama zaka zai shanye abinsa, tsuntsun daya ja ruwa, shi ruwa akan doka! Dole abu ya yi haƙuri domin shi ne silar faruwar komai shi ne ya haddasa mata jinkirin auren, by the way Ubangiji hakan jarabta mu, kuma shi aure lokaci ko ita Majeederh ce zata aurar da kanta? A wannan zamanin bafa ita kaɗai ce take da wannan matsalar ta rashin aure ba, jarrabawa ce! Kuma zurfin cikin ki ya yi yawa Majeederh You have to do something, do something Majeederh! Biyyar da kikewa Abbu is too much....,"
Kamar zautacciyya haka Majeederh ke sauraren shirar zuciyoyin nata guda biyu, da mai faɗin gaskiya da mai kushewa tana ɗora ta a tubalin da zai kai ta halaka. Kyakkyawar zuciyar ta ce "Oh! Kina nufin ta wulaƙanta mahaifinta kenan? Daman haka ya dace ɗan halak ya yi wa iyayensa? Ba Abbu da yake mahaifinta ba, ko Mami idan ta yi magana dole Majeederh ta yi mata biyayya, mai haƙuri shi ke da riba a wannan rayuwar, na tabbar Ubangiji ba zai taɓa barin Malama Majeederh ta haka ba, dole akwai wani rabo da tanada mata albarkacin biyayyar da takewa Mahaifinta, rabonta yana ta wani ɓangaren" Majeederh ta yi zuru domin tafi gasgata maganar kyakkyawar zuciyar, muguwar zuciyarta ta ce "Hoo ƙaaasa! Yau ga bikin zuwa babu zanin ɗaurawa, waya hanata auren tun fil azal, lokacin yana wagairawun bai ajjiya ko sisi ba, a matsayinsa na uba wanda zai fita ya nema ya ciyar da iyalansa amma ya jingina ƴar cikinsa mai tsafta da kamala matsayin jarinsa, ya sadaukarwa duniya ita idanunsa ya rufe, kuɗi kawai yake so arziƙi yake nema ta ko'ina sbd yanzu ta tara masa ya shiga jerin masu kuɗin Kano shi ne zai ce ta fito da mijin auren? Ya ja mata ƙaddara sai su amsheta da hannu bibbiyu, rayuwar Majeederh ta shiga cikin lack of parents careless, Takaicin Uba zai iya kai ruhinta zuwa kushewa, yanzu daya tilasta mata kawo mijin aure idan zuciyarta ta buga fa? Kawai ki share mahaifinki ki ci-gaba da sabgar gabanki ya je ya ci kansa, Allah kaɗai ya san yadda zai da shi" Da hannu bibbiyu Majeederh ta toshe kunnuwanta, sosai maganganun da zuciyoyinta suke, suke mata amsa kuwwa a kunne! Jikinta har ɓari yake yana wata jijjiga. Kyakkyawar zuciyar ta ce "Amma ke baki da lissafi, da kina da shi ba kya ce haka ba, komai yana da sanadi Ubangiji ya ƙaddarawa Majeederh Jinkirin aure, amma Abbu shi ne sila, idan mutum ya kauce hanya addu'a ake masa idan da rabo ya dawo, abu ɗaya Majeederh za ta yi ta ci-gaba da addu'a, sadaƙa da yawaita azkar, kuma shi Imran ƙilan ƙaddararta da tashi daban shi ya sa a lissafin ƙaddararta babu auren shi, abu guda ɗaya ne ke ɓata mini rai da Majeederh yadda take yin shiru shirun nan, yaran cikinta na rainata ta ci uban kowa ta tattaka kowa, ta kuma cigaba da kare mutumcin kanta..." Ceceku ce aka shiga yi tsakanin zuciyoyi biyun! Kowa yana son Majeederh ta ɗauki shawararsa, ta saka hannu ta rufe kunnenta tare da sakin wani irin gigitacciyar ƙara ta zume wajan a sume.... Misalin 12 na rana, ta shiga buɗe Idanunta wanda sukai mata nauyi, a hankali ta saka hannu ta dafe gefen kanta dage barazanar tarwatsewa.
"Sannu Hawwa'u" Muryar Anty ta sauka a kunnuwanta. Ta ya motsa fuska a hankali ta miƙe zaune tana jingina da jikin frame ɗin gadon bedroom ɗinta, cikin son nuna ta ji sauƙi ta ce "Ina yini? Yanzu kika zo"
"I haven't been here long" Anti ta bata amsa cikin ƙasa da murya sai kuma ta ce "Meke faruwa dake har haka?". Majeederh couldn't speak sai da Anti ta ce "Kina da ilimi, kuɗi, hankali, kyau, amma duk da haka da sauranki baki gama cika mace ba". Anti ta yi shiru can ta kuma cewa "I'm starting to get tired of seeing you in this situation,It is good that now you are married and you are in your husband's house, Majeederh duk wani ɗaukaka da da iliminki a banza yake, macen da bata san komai ba wacce take gidan mijinta sai anfi ganinta da girma da daraja, sai anfi martabata fiye da komai, Abbank Uncle Isma'il shi ne ya turo ni ya ce na faɗa miki ya gaji idan ya haɗu dake ba zaki ji da daɗi ba, You're a darling ke abar so, kina da kyau" Murmushi kawai Majeederh ta yi wanda ya fi kuka ciwo ta kalli Anti ta ce "Mene amfanin kyau? Wallahi ban taɓa fariya sbd ina da kyau ba, ina tausayawa duk wata mace mai kyau"
"Kyau abin so ne Majeederh" Majeederh ta runtse Idanunta ta ce "Bai ƙare ni da komai ba, wallahi da na san inda ake sauya fata daga fara zuwa baƙa da tuni na yi, na gaji da duniyar nan Anti" Ta faɗa tana riƙe ƙirjinta hawaye ma ya gagara fito mata. Anti ta ce "Kin gaji da duniya ga shi duniya na son ki, Majeederh mazan aure kika rasa ne?" Kanta a ƙasa ta kasa cewa komai Mami dake zaune looking so worries ta ce "Ta yani tambayarta Maryama, ni dai ba ruwana dole na ja baya idan ina matsa Majeederh za ta yi zaton dan bani na haifeta bane wallahi,to me ma zan ce? Nan nan wata Neighbor ɗinmu ta zo ta mini ta tas kamar uwata, zagi kala-kala tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin tashin hankali irin na ranar ba" Ta yi jim! Sai kuma ta ce "To akan me"
"Uhm, ta tsuniyar gizo ai bata shige na ƙogi, cewa ta yi wai bata yarda da Majeederh ba, gani take gantali kawai take a duniya shi ya sa bata damu da aure ba" Anti ta ce "To fa, ita wa kenan? Ina cewa akwai zabga zabgan ƴan mata a gidan wata ma ta yi Arba'in kamar uwata wallahi, amma ita ba taga na gabanta ba sai munafurci a ɗaure a ƙugu? Mutane basa kashe wutar dake ci a gabansu sai na wani? Baka da gadon mutum yana da gadon maganarka, to da izinin Ubangiji ba zamu ga wannan mummunan ranar ba, wani hanin ga Allah baiwa ne" Mami ta ce "A to, munafurci ne kawai irin na mutane wallahi Maryama, nan ta zo ta wata yaƙunanniyyar atamfarta duk gansa kuka, ai kana ganin wannan matar kaga zubin munafukai Inyami take kowa?" Anti dai bata ce komai ba. Ta juya kan Majeederh ta ce
"Ki tausayawa kan ki, ki tausayawa mana dan Allah Majeederh, zaɓen miji yanzu ba naki bane, duk wanda ya fito da niyyar aurenki kawai ki amince masa As long as you trust his morals, his behavior, his mind and his religion"
Kallon Anti kawai Majeederh take domin bai ɗaki shiyasa inda yake masa yayyu, wai ba a yarda da ita ba? Babu wanda ya taɓa riƙe hannunta sai Ajlaal shi ma kuma ta yi Asstagafirullah! Ta ja masa Allah ya isa kuma har azumi za ta yi bisa hakan wani ƙato ya riƙe mata hannu. Ta rufe Idanu "Ban ya fe ba Ajlaal" Anti ta ce "Waye haka?" Ƙasa magana ta yi sai a lokacin ta kifa kanta in between her legs ta shiga rera kuka kamar ƙaramar yarinya takaici da baƙin cikin Ajlaal ya cika mata zuciya.
Ta riga ta manta da wani Alpha domin shi ne mutum na farko daya tuzarta ta a duniya, She laid back down to rest but couldn't. Tears of fear, betrayal and sadness streamed down her cheeks, and she knew that her life had been altered completely......
ZAZU Restaurant, Sultan Road Giginyu Nasarawa.
Suna zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru wajan wani gefen ruwa dake gudana, su wajan biyar ne kana ganinsu kaga tantiran marasa jin magana, wanda suka gagari kowa, abu mafi jan hankali a gare su ko wanne yana da class ɗinsa, ka taɓa ɗaya goma su hau kan ka, basa ɗaukan raini basa gudun abin magana, sun mai da jami'an tsaro kamar abin wasan su, Police station kamar shiga restaurant suka mayar da shi ko beach ko club... They're all education natured enough, gabaɗaya kuma a Gang team ɗin Bad boy Abraham shi ne ƙarami, amma yafi ko wanne girman jiki da tsare idanu, baya ɗaukan raini baya son munafurci, idan ya faɗi magana haka ne domin baya ƙaunar ƙarya yafi son gaskiya ko zata kashe sa ko ta ja masa wata masifar, wani irin masifaffen jan aji ne da Abraham Bad boy, basu taɓa ganin dariyarsa ba, gashi da wani irin fikira ya ƙware wajan yin zane..... Abinci ne birjik a gabansu da difference types of drinks a gabansu, ga Shisha ga wine. Taj ne ya ce "John yarinyar ta ci banza kenan?" Ya faɗi hakan cikin turanci. Nan da nan fuskar John ta sauya ya ce "How do you think I will forgive her?" Taj ya yi dariya ya ce "To You didn't take any action akanta" Wani lalataccen murmushi John ya yi ya ce "Tomorrow is Luna's birthday, I will call her the club where the birthday will be held" Sai a lokacin Joshua da hannunsa yake riƙe da Luc Belaire Rose Ya ce
"Sai ka yi mata me?" John ya ce "I will rape her, and I will beat her to death" Ambaton Fyaɗe da akai ya sanya tsigar jikin Abraham ta shi tana zubewa, baya ƙaunar jin kalamar bare har ya ji ana faɗin za a aikata, gashi dai ƙaton arne amma bai son ƙazanta ko kaɗan. Ya ɗago kansa da wani irin sexy eyes ɗinsa wanda sukai wani irin kalar launi kamar na mage haka zubin halittar idanunsa suke, ga girar shi kamar zata haɗe lips ɗinsa da suke jajir ya taune, jikinsa sanye da Tommy Hilfiger T.shirt Maroon, da Levi's crazy jeans iya qiwwa, ga wasu gargasa kwance lub daman dark skin ɗinsa wacce take ɗaukan idanu sun yi gwanin sha'awa, six-pack ɗinsa sun kama rigar hakan yasa ya yi wani ƙato irin mazan nan ne wanda ko kallon mace sukai sai ta kusa yin fitsari a wando don tsoro. Ya saka bandana a kansa hakan yasa sumar ta Kwanto har goshinsa idan kaga Abraham ba zak taɓa ɗaukan farin namiji ba, irin colour ɗin su ake wahalar samu.... A hankali yake jujjuya drink ɗin Gold berg wanda shi ne favorite drink ɗinsa. Bai ce musu komai ba sbd he's not interesting da conversation ɗin na su. Ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious sai tashi yake a jikinsa. Taj ya yi wata mahaukaciyar dariya ya ce "Wallahi kaci uwar Shegiya ka yi mata fata-fata" Joshua Shi ma ya yi murmushi ya ce "I support you, the girl has no shame, kama yi ƙoƙari da zaka iya goga fata da ita, datti gal" Taj ya ce
"Abinda nake tunani kenan, kaga idan kana son jin daɗi da more wa ka samu babies ɗin Brazil, idan asalin kyau ne most beautiful ladies in the world jeka duba Ethiopia.... Matan Nigeria are not romantic at all, shiyasa soon zan bar wahalalliyyar ƙasar nan" John ya taɓe fuska ya kalli Abraham ya ce
"Are you okay, Bad boy?" Ya yi masa banza kamar ba da shi ake ba. Wani a cikin su ya ce "Wai fa ko sau ɗaya Bad boy bai taɓa sanin mace ba" Taj ya ce "He's not romantic, kamar baya da lafiya" Sai a lokacin ya ɗago fitanannun idanunsa ya zuba akan Taj cikin wata husky voice ya ce
"Ko!" John ya ce "Haka ne ma, baka da lafiya" Ya miƙe tsaye yana feeling kansa, ya ce "Maybe"
Taj ya ce "Soon zan sanyaka yin haka, na baka wata mahaukaciyar Alcohol" Cak Abraham ya tsaya tare da zubawa Taj idanu calmly ya ce
"Da na ci uwarka, kashe ka zan Dog!" Ya juya kan John ya ce "Let me make it clearly for you, ka sake kayi rapping wata ma rantse da Jesus sai na yanke maka abar, try it" Yana faɗin haka ya yi gaba walking full of peace and tranquility. Gang team ɗin suka bisa da idanu, ganin yadda ake musu gadara kamar ubansu, and he just 16 yrs.. Motarshi ya nufa Hyundai Ioniq 6 black colour, har zai shiga ya ji ana hayaniya cak ya tsaya jikinsa ya fara tsuma da idan da akwai abinda aka jarabci Abraham da shi bai shige abu biyu ba, yana mugun son yin faɗa musamman wanda bai shafe shi ba. Da wani sarrafa ya nufi direction ɗin yana zuwa yaga wasu maza guda biyu cikin kakkausar murya ya ce "Heee what's going on?" Wani ya ce "Faɗa suke" Guy ɗin ya nuna Wani ƙyakƙyawan mutum ya ce "Wannan bawan Allan ne ya ɗan bugi motar wannan wai ko Joseph sunan shi? Shi ne ya fara zaga-zage" Abraham bai jira jin wani abu ba gabaɗaya jikinsa ɓari yake ya damƙi hannun wanda aka ce Joseph ɗin kafin ka ce me ya ɓalla masa hannu, ya ƙara damƙar ɗayan ya ɓalla wani irin ihu Joseph ɗin ya yi yana jin kamar zai mutu. Wani ya ce "Kai Mahaukaci ne? Haka ake raba faɗa" Ko inda yake bai kalla ba ya juya abinsa zuwa mota ya ja da wani irin 150 yabar cikin Zazu ɗin. Bar Aliyu ya sauke numfashi yana mamakin zafin zuciya irin ta wannan gwalilin yaron yafi tunanin ma mahaukaci ne..... Tun a Main parlour Abraham ya fara fatali da komai jikinsa duka rawa yake da wani irin karkarwa. Grandpa ya sakko yana mai ɓoye photon Zanen fuskar Abbu da aka kawo masa ɗazo, so yake ya saka aiwa Abbu Mahaukacin duka tunda ya taɓa masa lafiyar Grandson ɗinsa, yasan kuma Abraham ba zai taɓa bari ba shi yasa zai yi asirrin ce. Ya dinga bin Abraham da idanu kafin ya ce "Mami ko?"
"Yes Grandpa" Ya faɗa yana kallon Grandpa, David ya ce "Na saka private Investigators amma shiru, ina tunanin wannan Mamin taka bata duniya ta mut....." Kafin Grandpa ya ƙarasa Ya ji Abraham ya buga kansa da jikin wani Glasses yana faɗin "No!!!!!!, Mamiii..."
A hankali Majeederh ta duba agogon hannunta taga 12 saura minti goma, gabaɗaya ta manta akwai wani taro a B.u.k na gabaɗaya students ɗin makarantar musamman na Department ɗin Politics Democracy. Ta sauke ajjiyar zuciya a ɓoye a hankali ta kalli mutanen da suke gabanta ta ce "I can't do that, abu ne na cakuɗeɗeniyya da mata, am sorry" Mutumin ya ce "Please Malama Majeederh Ngo ɗin nan tana buƙatar ki, zamu baki ko nawa kike so, kawai muna so kiyi aiki damu" Bata kallesa ba ta dubi wata ta ce "Kika ce me?" Matar ta fashe da kuka sosai ta ce "Ki taimaka mini, yarinyata aka aurawa wani yaƙunan tsoho saboda yana da kuɗi, gashi yanzu yarinyar ya ja mata masifa yayyun fitsari take sbd takura rayuwarta da yane kamar ɗan taure, gashi yanzu ya gudu wai ba zai iya zama da ita ba, wannan masifar duk Ubanta ya ja mata saboda son kuɗi ne da shi kamar ƙudan cizo" Majeederh was speckless hango kanta take matsayin yarinyar a hankali ta ɗan rufe ido ta buɗe ta ce "Zan kira ki weekend, ina da aiki yanzu thank you Inna" Ta amshi number Dattijiwar "Na gode na gode, Ubangiji ya jiƙan gobenki ya baki zuri'a ta gari ya raya miki su ya barki tare da mijinki" Majeederh dai ta yi shiru, Mai Ngo ɗin yin duniya amma taƙi tanka shi ya yi ƙwafa ya fice,daga nan ya fito tabar masu kula da Foundation ɗin nata ya shiga motar ta tare da yin Bismillah ta harba motar kan titi ta nufi B.u.k new side...... Hall ɗin a cike yake da manyan baƙi, masu kuɗin garin da jami'an tsaro da ƴan jarida haɗi da Lauyoyi na jihar. Yana can tsaye domin bai wani jima da shigowa ba, ya runtse idanunsa jin zuciyarsa na bugawa, ya wani kwaɓe fuska har zai juya ya ji wani ya ce "Malama Majeederh Abdul'aziz Khan is here" Attention ɗin Students ɗin sama da 300 ya dawo kan Majeederh dake tafiya cike da kamala kana ganinta kaga cikakkiyar mace mai nagarta, abayar jininta kaɗai ya nuna arziƙin da Ubangiji ya yi mata daga baiwarta. Mutumin ya ce "Allahamdulillah ita ce zata gabatar mana da addu'a daga ɓangaren musulmai, kafin mu je ga addu'ar zamu gabatar muku da sunanta da kuma matsayinta a makarantar" Da ƙarfi John ya ce "Allow her to speak" Gabaɗaya Students ɗin suka ce "Yes! Yes!" Ya ce "Ok zata yi bayani da kanta Malama Majeederh Bismillah" Tafi ƙarfin Minti biyu kafin ta ɗan yi gyara Muryar ta ce "Bismillahir Rahmanir Rahim, In the name of Allah....," Cak ta yi shiru jin kamar ita ɗaya ake kallo, Da wani irin firgici Abraham ya ɗago kansa dake ƙasa zuciyarsa kamar zata faɗo bakinsa na rawa ya ce "Mami...?" Sai kuma ya miƙe yama manta su waye a wajan kuma daman shi mutane basa gaban shi, gaba ya bawa kunya ba baya ba, Gadan-gadan ya nufi wajan Majeederh takun tafiyarsa kuma ya ja hankalin mutanen hall ɗin, Majeederh na ƙoƙarin yin magana taga kamar an cillo mata mutum a gaba ta ɗago idanu slowly idanunsu ya sarƙe dana juna ta dinga kallon ƙwayar idanunsa bakin Abraham na rawa yana kwaɓe mata fuska ya ce "Ma...ma... Mami Jee...!" Sai kuma ya yi kanta gabaɗaya zai rungumeta....
*MIJIN MALAMA* It's a paid book pay before you read don Allah........ For more information via WhatsApp number 08119237616Baya tayi da ɗan sauri ganin yadda idanunsa rufe a gaban ɗarurun jama'a yake ƙoƙarin rungumeta. Abraham ya tsaya cak, zuciyarta ba harbawa na fargabar kar da Mamainsa ta manta da shi a duniya, bayan duk tsayin shekarun daya ɗauka basa tare ya rayuwa ne da tunaninta, duk yake tunanin zai ganta ya duba bata nan. Malama Majeederh a kallon ƙwayar idanun Abraham na farko ta fahimci Little ɗinta ne, Yaronta he came back. Kallonsa ta dinga yi without blinking, shi ma itan yake kallon yana kwaɓe mata fuska, saboda ya fahimci kallon na mene tuhumarsa take, da kuma son gasgata shi ne ɗin ne ko yaya? Wani irin rawa jikinta ya fara duk yadda take so ta riƙe kanta, ta hana shocked shigarta tana mamakin ganin Little ɗinta Yaronta wanda take masa wani irin mugun so.... Rufe idanu ta yi a hankali ta buɗe lokacin da shagwaɓiyyar muryarsa wacce ya saba yi mata magana da ita idan yana son abu ta ji ya ce "It's me Mamina" Ita dai bata ce komai ba domin tana cikin wani irin farin cikin da zata iya losing control ɗinta a wajan. Fahimtar kamar akwai sanayya tsakanin Abraham da Malama Majeederh ya sanya securities ɗin tsaya daga nufar inda Abraham yake, mai gabatar da Shadol na taron ya kalli Majeederh yana ɗan rusinawa domin bata girma ya ce "Malama Majeederh ke muke sauraro babu lokaci" A kame cikin riƙe kanta ta jinjina masa kanta, tana haɗe fuska tamau kamar wacce ake ganinta ta ƙarasa gaban loud speaker ɗin cikin nutsuwa da wani irin golden voice ta ce "Please bear with us for wasting your time, and we will go directly to what has brought us together here...!" Da ɗan yi shiru tana mai da numfashi, Abraham ji ya yi hankalinsu ya kasa kwanciya saboda daddaɗar muryar Mamainsa daya cika wajan haka kurum ransa ya ɓaci, ya turɓuɗe fuska idanunsa sukai jajur naman jikinsa har rawa yake, ya kasa motsawa sai kafe da gajiyayyun idanunsa da ya yi abubuwa ne fal a ransa. Malama Majeederh a jikinta ta ji yana kallonta maybe yana kare mata kallo saboda tsayin shekarun daya ɗauka bai ganta bane. Ta kalli hall ɗin ta ɗora da faɗin
” رَبِّ اشْرَحْ لِي صَدْرِي* وَيَسِّرْ لِي أَمْرِي وَاحْلُلْ عُقْدَةً مِّن لِّسَانِي يَفْقَهُوا قَوْلِي.....“
Caraf ta ji an riƙe mata ƙaramin bakinta dake motsawa ta cikin liƙab ɗin fuskarta, wani Irin zaro idanu ta yi waje hankali tashe ta ware idanunta akan wanda ya yi mata wannan ɗan yan aikin da son kunyatata a gaban jama'a. Abraham ta gani tsaye dab da ita ya riƙe mata bakinta sosai sai zare idanu yake yana haɗe girar sama data ƙasa kamar wani ɗan shekaru 30 nan kowa ko 20 bai ba. Kunya kamar Majeederh ta nutse a wajan, idanunta ta ware ta kallesa sai taga yama ɗauke kansa can saboda kar idanunta ya yi masa kaifi ta kuma san taurin kansa sarai! Wani ya ce "Kai wanne hauka ne wannan sbd rashin kunya da rashin addini dake damunka kamar Malama Majeederh zaka riƙewa baki, C'mon saketa ta ƙarasa mana addu'ar" Abraham ya yi shiru mutumin ya ce "Baka ji na ne, ko sai an kira securities?" Gently Abraham ya ɗago kansa ya kalli mutumin ya ce "Ohk" Yana faɗin hakan ya kalli Majeederh dake tsaye kunya ta gama daskarar da ita, gashi bata son taɓa hannun Abraham sbd idanun jama'a, he's her little son nothing else amma wasu na iya juya hakan. Ya narke mata fuska ya ce "Mami let's go!" "Ji wani ɗan rainin hankali, ku tafi ku je ina" A haukace Abraham ya saki bakin Majeederh ya juya kan mutumin kamar zai dakesa, cikin turanci ya ce "Stop interfere ko na ci uwarka" Mutumin ya ce "Ni kake zagi? Kai waye, waye ubanka a garin nan" Ya faɗa yana ƙoƙarin kaiwa Abraham duka, Nan da nan Gang team suka shiga tattare hannun riƙe suna zuwa wajan da sauri umarnin Bad boy kawai suke jira, yatsu biyu ya kaɗa musu suka ɗan tsaya ya kalli mutumin sai kuma ya yi wani killer smile ya ce "Ni ba kowa ba ne, bani da uba amma ina da uwa Maluma is my mother, ka taɓa ta kasan waye ni" Yana faɗin hakan ya nufi tsakiyar hall ɗin tare da ɗaukar speaker cikin gadara yana feeling kansa ya ce "Babu uban wanda zai ji muryarta, ku nemi wani ya yi muku" Ya faɗi cikin turanci domin few words ya sani in Hausa language kuma a gurɓace yake magana, kuma yana bala'in son magana da Hausa kawai bai iya bane. Gabaɗaya mutanen wajan suka shiga mamakin wannan al'amarin, yaushe Majeederh ta samu ɗa? Kuma mene haɗin ta da wanda ba Musulmi ba, ma biyin addinin Yesu, ganin faɗa na ƙoƙarin sarƙewa tsakanin Gang team da securities ya sanya Majeederh daurewa ta nufi wajan wani mai muƙami a makarantar magana kaɗan ta yi masa ya ce "Oh! Na fahimta that's not a problem" Ta jinjina kai alamar godiya ya ce "Sure think" Juyawa tayi ta nufi hanyar fita daga hall idanun jama'a a kanta, a hankali shi ma ya juya tare da bin bayanta yadda yake tafiya fuska ɗaure zaka ɗauka wani babban mutum ne kowa sai ya yi shakkar fuskarsa, lokacin daya fita harabar makaranta tuni ta yi nisa saboda rawar da ƙafarta ke mata, a haka ta isa office ɗinta tare da neman kujerar ta zauna tana kifa kanta saman table ɗin gabanta. Nutsuwa ta ji tana saukar mata a hankali babu shakka Addu'arta ce ta karɓo wacce take yi dare da rana akan Ubangiji ya bayyana mata shi cikin ko wanne hali ne, addu'a ta amsu amma bata taɓa tunani zai dawo mata a halin da yake ciki ba, hankalin ta ya yi masifar tashi ganinsa a wani addini wanda ba nata ba, waye ya sauya mata Yaronta! Waye ya ruguza mata tarbiyyar shekara biyun da tayi cike da kulawa da soyayya? Wane ya dawo mata da hannun agogo baya? Tana tsaka da wannan tunanin ne ta ji an buɗe Ƙofar office ɗin nata tare da shigowa, ta ɗan matse kana ta ɗago kanta a hankali zuba masa idanu tayi kamar yadda yake kallonta a hankali ta harɗe hannunta a ƙirjinta kana kallonta kaga uwa mai nagarta ga yaranta, ganin kallon da take masa ya sanya shi yin ƙasa da kansa ya rasa sukinsa bakiɗaya a hankali ya ce "Am sorry Mami" Bata ce masa komai ta miƙe a hankali tare da nufar fridge ɗin office ta ɗauki gorar ruwa mara sanyi sosai da Glasses cup ta tsiyaya ruwan a ciki sabis gabaɗaya ta rasa tunaninta saboda ganin Little ɗinta cikin wannan halin, jin ta yi masa banza ya sanya ya ƙarasa gabanta tare da zubewa akan ƙafafuwansa ko Grandpa bai taba yiwa haka ba cikin wata damulalliyyar Hausa ya ce "Na ce ka yi haƙuri" Na ce ɗin ya kusa bawa Majeederh dariya ta dake ya marairaice ya ce "Am sorry Jee"
A hankali ta ajjiye cup ɗin bayan ta gama shan ruwan ta ɗan yi ƙyakƙyawan murmushi tana ɗaga liƙab ɗinta sama, domin ita bata taɓa haɗa Little da wasu maza ba, kawai kallon ɗan cikinta take masa dole ta buɗe fuskarta ta ƙyakƙyawan Yaronta ta kuma gyara masa rayuwa! "Stand up"
"Jee, Mami" Ya faɗa lokacin daya miƙe ya zubawa fuskarta sexy eyes ɗinsa masu launin cikin sauri kuma ya ƙarasa wajanta yana zuwa ya rungumeta sosai yana sauke wata mahaukaciyar ajjiyar zuciya ya ce "I miss Mom, bana da kowa" Tausayinsa ya kamata tayi hugging nasa bag tana shafa ƙyakƙyawar sumar kansa murmushi kwance a fuskarta, sun jima a haka sai sauke ajjiyar zuciya yake yana ƙara ƙanƙameta idanunsa, tasan ɗumin jikin uwa ɗaya daɗe bai ji bane yake ɗawainiyya da shi. A hankali ta cire shi a jininta tare da kama hannunsa zuwa duguwar kujerar office ɗin ta nemi waje ta zauna, ta nuna masa kusa da ita amma yaƙi ya zame a hankali wajan ƙafafuwanta ya zauna tare da ɗora kansa a cinyarta. Shiru shiru can ta ce "Your name?"
"Bad boy" Ya bata amsa. Ta haɗe fuska a takaice ta ce "Kai ne Bad boy ɗin?" Bai kalleta ba, bata san kuma dalilin daya sanya baya son kallon nata ba Ya ce "Yes, Jee"
"Call me Mami" Ya jinjina kai ta ce "Real name"
Kamar ba zai magana ba sai kuma ya ɗago kansa gabaɗaya ya zuba mata idanu yana kwaɓe mata fuska ta harare shi tana janye idanunta ya ce "Wai Abraham, Maa i don't like it ka sauya mi" Ta ce "Ki not ka, ki sauya mini" Ya jinjina kai ta zame hannunta daga sumar shi jin y daina sauke numfashi ta ce "But it's beautiful name, Ibrahim or Khalil in Musulmi name" Ya ce "Uhm"
Irin sunan bai wani gamshe shi ba, In a serious talking Majeederh ta ce "Khalil"
"Maa!!" Irin baya son sunan ganin wani irin kallon da take masa yasa ya ce "Am sorry, Bad boy is my name" "Who gave you that name?" Ya ce "Gang team, ni ne leader na team ɗin, Ni nakewa mutane duka na karya kowa Jee" Ta dinga kallonsa kawai tana girgiza ƙafa nan da nan fuskarta ta yi jajur daman ta san ba zai taɓa yin ƙarya ba. Ya ce "Ni nake tare hanya sbd kawai naga ko zan ganki, ni nake shigarwa mutane faɗa, police su kama ni su kaini station amma Grandpa na karɓo ni, Ance ni criminal ne, ina da record wajan ko wanne station na kano har state C.i.d na je, saboda faɗa maka n gudu daga Rushia zuwa Naija" Jin shiru yasa Abraham ɗago kansa ya kalli Majeederh ganinta ya yi ta tura kanta tsakanin cinyoyinta ya dinga kallonta ya ce "Jee" Ta jima kana ta ɗago kanta a rikice ya durƙoshe gabanta ganin fuskarta ta rine ta yi jajur ya ce "Am sorry Maa, Na tuba" Sosai take Mamakin yadda Little bai manta komai nata ba, wato ya fahimci ranta a ɓace a hankali ta ce "Wajan wa ka ke nan?" "My Grandpa, shi ne Pasto na church" Gabanta ya faɗi ƙirjinta dinga ɗagawa da gaske Little ɗinta Christa ne? Wani ya sauya masa addini ko daman can shi ne ba musulmi bane? Ta ce "Full name?"
"Abraham Denial David" Ta runtse Idanunta tare da yin jikin kujera ta ce "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ta dinga maimaitawa hankali tashe. "I hate my father"
Bata kula da maganar Father ɗin ba ta ce "Your mother where's?" Ya kwaɓe fuska yana ɗan ɗage mata gira bai ce komai ba. "Ka yarda kai Bad boy ne?" Ya jinjina kai ya ce "Yhhhh" "Kai Mahaukaci ne?" Nan ma ya ce "Eh" Ta dinga kallonsa cike da tausayawa kana ta miƙe tsaye shi ma ya miƙe Ta ce "Jeka gida" Ya marairaice mata ya ce "Jee zan bika, I will sleep with you today, Mami, I miss you so much" Ta kalle shi bata ce komai ba har ta nufi wajan motar ta, yana ta mamaki Maminsa tayi kuɗi ko me? Ganin zata shiga mota ya ce "Kawo key ɗin, I'll drop you" Frm head to toe ta kalle shi tana harɗe hannu a ƙirji ta ce "Wani ɗan kwanini da kai ina ka iya driving?" Kasancewar da Hausa tayi maganar sai bai fahimta ya kalleta da kasalallun idanunsa yana riƙe da murfin motar ya ce "Me?" Da Turanci ta ce "Idan zaka iya Hausa ka iya Little ban iya surutu da turanci dama dai larabci ne" ba tare daya fahimta ya ce "Ohk" A hankali ya zuba hannunsa a aljihu yana kame fuska ya ce "Let me drive you and drop you off at home" Ta ce "Wai kai yaushe kaga ɗan ƙaramin yaro yana driving? Kawai ka zubar dani lallai yaron nan" Ta faɗa cikin turanci sbd bata son wani surutun kuma. Wani irin Expression Abraham ke kallon Mamin tasa, a ransa yana ƙara maimaita kalmar yaro Ta ce "Kabari ka ƙara girma da wayo ka san halin kanka zuwa matakin aure" Calmly ya ce "Ohk" Yana tsaye harta fice daga cikin makamatar yamma lis, ya dinga kallon ƙofar kana ya cire hannunsa ɗaya daga aljihu ya dinga hargitse sumar shi. Gang team ɗin suka dinga dariya Taj yadda riƙe ciki ya ce "Gaskiya Mamin nan taka ta rainka da yawa, wai kai ne yaro?" John ya ce "Da kana kula babies wata rana ta ganka da wata a kwance manne kamar chewing gum ai ba zata ce maka yaro ba" Joshua ya ce "Wai kabari ka ƙara wayo sai ka yi driving nata, Goodness!" Abraham kallon su kawai yake. Taj ya ce "Amma seriously i like ur mother classes one Educated women, amma mene wannan a fuskarta? Naso ganinta" John ya ce "Amma dai ƴar rainin hankali ce wai kai ne yaro?" Gadan-gadan Abraham ya yi kan John tare da shaƙe masa wuya kamar wanda ke ƙoƙarin kashe shi "Am sorry Bad boy, sorry" Sai dai Numfashin John ya fara sama kana ya sake shi yana pointing nasa da hannu ya ce "Ko Grandpa ba zan ƙyalle ba akan Malumana Mamina, Jeena balle kai" Yana faɗin hakan ya shige motarsa ya mance kalmar yaro ya nufi gida wajan Grandpa cike da farin ciki yaga Mamainsa..... Wani irin kwara amai Aliyu yake kamar kayan cikinsa zai fita lokaci ɗaya ya fita hayyacinsa, Latifa ta dinga masa sannu ko kulata bai ba, da ƙyar ya wanke bakinsa a sink yana mai da numfashi ya fita parlourn daya zage ya gyara shi, zubewa ya yi saman kujera yana ƙaro gudun A.c Latifa ta ce "Wai lafiya? Mene ya saka amai?" Ya yi mata banza daga ƙarshe ya miƙe zai bar parlourn ta ce "Please Aliyu what's going on? Muje hospital" Ya kalleta kawai ta ce "Please Sweetheart" Ya girgiza kai ya ce "Kyankyaso cikin abincina Latifa? Kyankyaso dai na cikin toilet ki haɗe kika dafa abinci da shi, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!" Ya dafe kansa yama rasa me zai ce Ta ce "Kayi haƙuri ban san yaushe ya shiga ba" Da ƙarfi ya ce "Haƙuri haƙuri, I'm tired of your behavior, I feel sorry for you" Yana faɗin hakan ya fice daga gidan bakiɗaya he need to see a doctor ji yake kamar komai na cikinsa zai zube. Cikin dare Latifa na bacci ta ji an jawota ta yi saurin buɗe idanu tare da kunna switch haske ya bayyana, Suka haɗa idanu da Aliyu ta ce "Lafiya?" Da mamaki ya ce "Are you exlty questioning me?" Ta yi shiru ya ce "Ke ba matata ba ce?" Ta haɗe fuska ta ce "Yanzu mene?" Ya miƙe tare da jingina da frame ɗin gadon ya ce "Why are you answering my questions with a question?" Ta ce "Naga ai dare lokacin da ko wanne mai rai yake hutawa yana bacci gajiya, 1/24 idanun Mutum biyu" Ya jinjina kai ya ce "Ko?" Ta ce "Wallahi fa, mu kwanta mu yi bacci" A hankali ya ce "To" Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye yana jin mararsa kamar zata cire saboda azabar ciwo haka ya raya dare ido biyu tar sai asuba ya yi wanka tare da nufar masallaci a hankali suka haɗu da Abbu suka gaisa... Misalin 9:00 na safe Majeederh na bacci sbd jiya ba tayi baccin kirki ba tunanin yadda zata sauya Little kawai take ya dawo musulmi kamar ita da sauran jama'a, gefe guda kuma maganganun Uncle Bello da ya zo har gida ya yi mata ta tas akan taƙi tana yawo ta gaggauta fito da miji suka taro sukai mata tsaye a zuciya wanda ya hanata bacci sai asuba. tashin da Aaliyah ke mata a gigice ne ya sanya ta buɗe idanu Aaliyah ta ce "Anti Jeederh ki tashi" Ta kalli Aaliyah alamar "Lafiya?" A ruɗe hankali tashe ta ce "Wallahi Wani ne ya zo yana ta kwalla kira wai Mami, Malumana, hadda Jee" Majeederh tar ta buɗe idanu ta ce "Tun yaushe?" Ta ce "Tun Ɗazo fa, am sure Abbu bai ji ba da tuni ya fito" Jikin Majeederh duk rawa yake gashi kayan bacci ne jikinta ta ɗako hijabi ta saka ta ce "Shi da waye?" Ta ce "Shi kaɗai" Ta yi gaba bata saka Liƙab ba, gabaɗaya shap ɗin jikinta juyawa yake sbd ɗan saurin da take, Aaliyah ta rufa mata baya, tana zuwa compound idanunta ya sauka akan shi daga shi sai armless white colour sa gajeren wando gargasa duk kwance a fatar jikinsa gashin kansa a hargitse sai surar jikinsa da ƙarfafan maza ta bayyana, daga nan idanunta ya sauka akan wasu dalla dallan mahaukan matoci a ƙofar gate ɗin su daga waje, kafin ta yi magana taga ya kama katanga ya diro cikin gidan nasu tana ƙoƙarin juyawa tana girgiza masa kai amma ina tuni yayo kanta idanunsa cikin nata yanzu zuwa ya rungumeta sai gabaɗaya ta shige jikinsa duk girmanta hadda empty space daidai nan Abbu da Mami suka fito compound ɗin...
Allah ya nuna mana Monday Lafiya..... Wanda ba zai jira ba mu haɗu Arewabooks
MIJIN MALAMA na kuɗi ne dan Allah ki biya kafin ki karata ki kuma sauke nauyi.... 08119237616A tsorace take bin shadow ɗinsa da kallo, kasancewarta mai mugun ji da kanta girman kai da kame kanta cike da tarin nutsuwa da kamala ya sanya kai tsaye ba zaka fahimci girman tashin hankalin da take ciki ba. So take ta samu zarafin buɗe baki, ta tambaye why he's here? But she couldn't. Ta ruɗe sosai ta can cikin zuciyarta dalilin rashin kayan arziƙin dake jikinta, ɗan ta ne, amma tasan bashi da ikon ganin wani sashe na jikinta. "Little, why are you here? and why did you turn off the light?" Ta ji shiru ba amsa, sai shadow kawai idanunta suke gane mata. Ƙoƙarin Miƙewa take ta kasa sbd wani irin masifaffen ciwon kan dake nema juya gurɓata mata tunaninta,ji take kamar kan zai rabe biyu, ga zazzaɓin daya gama cinye mata kuzarin jikinta, a hankali ta koma ta kwanta tare da ɗora kanta a frame ɗin gadon ta curkuɗe jikinta da white duvet ɗin dake shimfiɗe saman royal bed ɗinta na turkey. "Ok fita a ɗakina idan ba za ka yi magana ba" Majeederh ta faɗa so calmly ba hayaniya a muryar sai raunin dake son bayyana, still bai magana ba, sai hasken da taga ya mamaye bedroom ɗin lokaci ɗaya, ta sauke ajjiyar kana ta juya side ɗin da take tunanin yana wajan, haɗa idanu sukai da shi yana zaune saman ƙatuwar kujerar dake ɗan nesa da bed ɗin kaɗan, ya saka hannunsa guda ɗaya cikin tsakiyar kansa ya birkitata, sumar ta cukurkuɗe har gaban goshinsa idanunsa sun yi wasu mahaukatan jaa, fuska ɗaure tamau. "How are you feeling now?" Ya jima yana kallonta kafin a takaice ya ce "Lafiya ina" Majeederh ta tsaya kallon ikon Allah jikinsa duk bandeji amma wai lafiya yake? Sbd taurin kai da zafin zuciya ta ce "Come, muga jikin" Ya yi mata shiru yama ɗauke kansa daga direction ɗinta. Ta ɗan saki fuska ta ce "Common baby, zo nan yaro ne" Ya juya a ɗan hargitse yana kallonta sai kuma ya ɓata fuska sosai cikin gadara ya ce "Stop calling me boy, am not"
"Oh sure? Shekararka nawa?" Kamar ba zai bata amsa ba ya ɗan lumshe jiƙaƙƙun idanuna ya buɗe a takaice ya ce "16" Majeederh ta gwalo fararen Idanunta waje, kamar ruwa ya kwanta a ciki dan haske. A hankali ta shiga ƙarewa Abraham kallo, idan aka ce namiji daya amsa sunansa to ana nufin Abraham Daniel David. Wata iriyar suffa Ubangiji ya wadata masa a jiki, zagayayyar fuska ce da shi wacce aka cewa Round face, yana da kwantaccen saje mai yalwa baƙi siɗik da shi, wanda ya taho har gemunsa ya haɗe waje guda. Ɓata lokaci ne tsayawa description na how handsome he's, The first look she gave him. Ganin yadda ya kafeta da idanu ya sa ta hararesa cikin ƙarfin hali ta ce "Yafi na goyaka a bayan nan nawa kamar yadda na saba, meye wani 16yrd na ɗauka ma zaka ce 50" Shi dai bai ce mata komai ba, kallonta kawai yake ta ƙara ɓata fuska ta ce "To mu da a garin nan kake ma, wallahi ina faɗa maka yanzu za a maka kaciya, idan ba a maka ba kuma ka faɗa na kai ka, I want my child to grow up very well" Dake da turanci duka take maganar yasa ba wani big wahala na fahimtar Abinda take cewa ga Abraham. Ya saka ya shafa sumar kansa yana son yin murmushi ko yaya ne amma he couldn't speaking calmly ya ce "Na zo ki duba?" Ta ce "What?" Nan ma dai ya jima kafin ya bata amsa da "Anyi kacin ka ba ai ba" Majeederh ta yi shiru tana mai da numfashi domin ita har bata bata jin ba daidai ta faɗa ba. "Yaushe ka zo why are you here?" Ya miƙe tsaye yana nufar window ɗin bedroom ɗin nata ya ce "Since 12 at night, Maa check your hand" Baki sake take kallon, kenan tsayin awa nawa yakai zaune yana kallonta tana bacci? Ta juya sai a lokacin ta lura hannunta dake manne da audiga ta ƙara ganin robber na drip daya ƙare da shocked ta ce "Are you a doctor?"
"Yhh, I am" Da mamaki ta ce "But me kake zuwa yi B.u.k a Department na politics Democracy? Yaushe ka zama doctor a ƙarancin shekarunka you're too young da zama likita, likitan me?" Ta girgiza kai ta ce "Kayi yaro da yawa Baby, ban ma yarda da karatunka ba" Ta juya ta kalle shi taga yana tsaye harɗe da hannu ya zuba mata Idanu, idanunsa har yafi baya rinewa. "Zo nan ɗan yaro na" Majeederh ta sake faɗa, domin idan tana ganinsa komai na zuciyarta yayewa yake, sosai take son ɗanta kamar ko wacce uwa. Da sassarfa ya ƙarasa inda take tare da zube ƙafafuwansa a ƙasa ya ɗora kansa a cinyarta da wata kalar murya ya ce "Ki daina ce mini yaro Mami, am not a child" Dariya ta so kamata tayi shiru ta ce "To idan ba yaro bane kai mene? You're just 16 fa haba Khalil" Abraham ya ƙare haɗa fuska tare da zuba idanunsa cikin nata sun ɗauki daƙiƙo suna kallon tsakiyar idanun juna ya ce "Ni ba yaro bane" Majeederh ta ce "Ni dai a wajena kai yaro ne,kaje can inda kake firgitarwa da ƙaton jikinka, amma ni bai fi na goyeka ba" Gani tayi da gaske yake baya so gabaɗaya Annurin fuskar Abraham ya ɗauke kamar an watsa wuta Ya ce "Ohk" Ta share ta ce "Ɓangaren me ka karanta? Ba dai kayi mini allura ba" Ya ce "No! Yanzu zan miki"
Nan da nan ta haɗe fuska itama ta ce "To wallahi na ji sauƙi ma, lafiya ta lou dan ka ji" Ya miƙe cikin wata tafiya ta masu izza da ji da mahaukan kuɗi ya nufi wajan bed side table ya ɗauki wata injection yana zuƙar ruwan ciki, a hankali yake kuma lumshe idanu yana jin kamar kansa zai rabe biyu, Majeederh ta ruɗe domin babu abinda ta tsana sama da injection ta ce "Zo ka fice mini daga ɗaki, Allahamdulillah na ji sauƙi sosai" Bai kulata baz domin a maganarta ba kana jin masharsharar zazzaɓi, gabanta ya faɗi ganin ya nufu inda take tama mance daga ita sai under wear ta miƙe jiri na kwasarta ta nufi har bathroom, tako ɗaya ya yi ya saka hannu ya riƙo ta. "Wayoo Son Allah ban so, kayi mini mutuwa zan yi" Ji ta yi ya saketa, ta sauke numfashi.
"Am sorry Mami" Ta fahimci haƙurin na mene ta ce "Go and ask my father's forgiveness,not me Khalil, shi ka yiwa laifi ba ni ba, da al'adarmu ta ko akwai bambancin, ka je ka bashi haƙuri" Ya matsa kusa da ita tare da sunkuyar da kansa ya ce "I am sorry, Jee" Sai ta ji tausayinsa shi akaiwa laifi shi za a bawa haƙuri,amma yana da kyau yasan muhimmacin bada haƙuri akan kuskure. Kafin ta sake magana ta ji ya ɗan shige jikinta ya marairaice ya ce "Ka yi haƙuri Jee" Majeederh ta ce "Ok, i for give you, but in one condition" Bai ce mata komai ya shiru akan kafaɗarta ta ce "Bana son sunan nan bad boy, bana son zafin zuciyar nan naka Khalil tun kana ɗan 3yrs kake da zafin zuciya har yanzu nothing changes about that, bana son ƙatuwar sarƙar nan wannan team ɗin ban so idan har ka yarda am your mother, kuma.....," Cak! Ta tsaya tare da yin ƙara tana ƙanƙame Abraham jikinta na rawa da ɓari sbd shigar tsinin allura da ta ji a jikinta, tsabar tashin hankali da zafin da ta ji numfashinta kusan ɗaukewa ya yi, kamar yarinyar goye haka Majeederh ta saki wani irin raunataccen kuka bakinta na rawa tana kallon Abraham ta ce "Amma ba na ce na ji sauƙi ba, ni Maminka ka yi wa Allura..." Ta kasa magana sai kuka kamar ta kwanta a ƙasa ta yi ta kuka haka take ji ganin idanunsa kawai ya hanata, tunda aka haifeta ba a taɓa yi mata allura ba sai ta saka drip itama da ƙyar, Abraham ya saka hannu ya kama kunnensa ya ce "Am sorry, ban sakewa" Tana shassheƙa ta ce "Da ƙyar wajan bai kumbura ba, ina ji ma ƙafar cirewa za ta yi" Ya ɗan shafa kansa Calmly ya ce "To bari a lailaya" Kafin ya kafaɗu ta miƙe da sauri zata shige bathroom sai kuma ta saka sbd dishi dishi data fara gani kanta ya shiga juyawa, allurar ta fara aiki a jikinta a hankali tayi baya zata faɗi ya yi sauri ƙarasawa ta faɗa saman chest ɗinsa. Sukutar ta ya yi har zuwa saman bed ya kwantar da ita ya ja mata duvet tare da rufeta ya ƙaro gudun A.c Jin ta riƙe hannunsa sosai bakinta na motsawa ya sanya Abraham zama gefen gadon ya ɗora kunnensa a bakinta a hankali ya ji ta na cewa "Stay with me son, Abbu bai so na ya tsane ni ba wanda ya tsana a duniya sama dani, tayaya zan fito da miji a kwana biyu? Good 31yrs bani da farin ciki sai yanzu dana ganka, my son are still alive kada ka barni, Abbu ya tsane ni" Zame kansa ya yi yana jin maybe ya kashe Abbu kawai, Aure? Miji? Sati biyu?" Sune abubuwan da bai gane ba ya jima zaune yana jinta tana surutu a hankali bacci ya ɗauketa kuma ya taɓa wuyanta ya ji ba fever ya sauka.... Washegari wajejen 8 na safe kiran Uncle Isma'il ya farkar da ita daga bacci ta miƙa hannu da ƙyar ta ɗauki wayar tana kaiwa kunne ta ce "Assalamu alaika, barka da safiya Uncle" Cikin sakin fuska ta wayar ya amsa mata da "Allhamdulillah Hawwa'u" Ta yi jim can ta ji ya ce "Hawwa'u da gaske yaron nan ɗan rainonki ne?" ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke tana jin nutsuwa jin maganar Little ta ce "Shi ne Uncle" Uncle ya kalli Anti ya ce "Ikon Allah, mene sunan shi?" Ta ce "Khalil" Uncle ya ƙara cewa "Oh, Ibrahim-Khalil kenan? Amma kin san ba Muslim bane?" Ta jinjina kai ta ce "Eh" Ya ce "Good, ki bashi address na gidana anjima ya zo ya saman" Ta yi shiru ita yanzu ina zata sake ganinsa ma? Uncle Isma'il ya ce "Kin ji ko?" A hankali ta ce "Bani da Digits nasa, kuma Abbu ya hanani fita" Uncle Isma'il ya ce "Akan me kuma? Aikin naki fa?" Ta ce "Wai na fito da miji immediately cikin 2days" Cikin ɓacin rai Uncle Isma'il ya ce "To ya garƙame ki a gida tayaya zaki samu mijin? Ko akwai wanda kuke dating da shi ne?" Cike da takaici da ɗacin rai ta girgiza kai ta ce "A'a" Uncle ya ce "Kina kina gida a garƙamen zaki samu mijin aure? Ko shi ne zai nemo miki mijin ne eh?" Uncle Isma'il ya saki tsaki ya ce "Abdul'aziz baya kyautawa kansa kuma kema baki kyautawa kanki ba, ai ba mijin aure kika rasa ba" Yana faɗin hakan ya kashe wayar rai ɓace. Majeederh ta kifa kanta akan pillow tana jin zuciyarta kamar tayi bindiga damuwa ta mata yawa, ita yanzu ina zata samu mijin aure? Waye zai aureta? Wama take da shi ita wallahi bata taɓa soyayya bama bata san ya take ba, daɗinta da wahalar cikinta duka bata sani ba, amma zo da nufin yaudararta babu wanda ya taɓa, ita ko gurgu ko tsoho ne ya zo da nufin aurenta wallahi da gudu zata amince masa ta gaji over gajiya rayuwarta a jirkice take gabaɗaya, ƙaddarar rayuwa ta sanya ta ciki tsaka mai wuya, rana zafi inuwa ƙona, a dangi a goranta mata rashin aure, a gidan da aka haifeta wanda take jin tana da ƴanci nan ma haka, few people suke supporting nata always. Miƙewa ta yi da nufin shiga bathroom idanunta ya sauka akan Card ɗinsa wanda da gayya ya ajjiye ta dauki card ɗin dake ta sheƙi taga an rubuta Dr. Abraham Denial David, so da gaske dai likita ne shi? How? Ita kam ta raina shekarunsa da zama likita, number ta gani uku ta ƙasashe daban-daban ta dubi ta Nigeria taga ganta special one domin kusan duk digit ɗin 1 ne. Ta saka number ta yi saving da _Son My world_
Kira ta yi lokacin Abraham na zaune cikin garden na gidan su idanunsa kwance a saman tsuntsayen da suke yawo wajan, a hankali yake kaɗa ƙafarsa wacce take cikin ruwa hannunsu riƙe da coke yana sha da kuma shisha gabansa. Wani cool ring tone ya shiga tashi kai tsaye ya fahimci me kira, tun ɗazo Gang team ke kiransa amma yaƙi ɗagawa, ya ɗaga kiran yana mannawa a kunne yana jin sanda ta sauke ajjiyar zuciya ta ce "Uncle Isma'il na kiranka, check your inbox za kaga address ɗin gidan nasa" Tana faɗin hakan ta kashe kiran yasan haushin Allura ne dai bata shige ba. Ya cije lip's yana shafa sumar ƙirjinsa yana gani ta yi mata Dm na address ɗin gidan a hankali cikin ƙasa da murya kamar shi ma da kansa bai son jin maganar shi ya ce
"Mamina mai tsoran allura"..... Innati ta ƙanƙance idanunta tana kallon Mami zuwanta gidan kenan ita da Maman Alpha sbd acan Innati take da zama ta dubeta ta ce "Ke baki isa ba, bana buƙatar lalatacciyar munafukar gaisuwarki, mijinki nake nema maza kira shi" Mami ta ce "Kiyi haƙuri Innati" Innati ta yi shiru ta juya wajan Maman Alpha ta ce "Ai ka ji tsiyar da Maryama ce uban me zai sanya tayi shiru? Kin zo kin jaɓe kamar kayan wanki" Maman Alpha dai ta yi shiru babu jimawa Abbu ya fito cikin wata dakakkiyar shadda shampo sai ɗaukan idanu take ya tsuguna ya ce "Sannu da zuwa Innati, anzo lafiya?" Innati ta yi mitsi mitsi da idanu ta ce "Kai bayan son zuciya ta hakƙin lafiyayyiyar ƴarka mai zuciya mai kyau, hadda bakin uwa ke binka Audil azizu" Abbu ya ce "Subuhanallahi me na yi?" Kamar zata dage shi ta ce "Me kowa na ce kayi? Cewa na yi bari na zo na ji wanne marar tsoran Allan ne yake rusawa yarinya farin cikinta? A wanne dalilin ka hanata fita aiki? Kuma da zaka karkace ɗuwawu bayan ta tara maka arziƙi ka ce cikin kwana biyu ta nemo mijin aure, ita ƴar bori ce ko aiki da ruhainai da zasu bata mijin aure?" Abbu ya ce "Ni Majeederh ta tarawa arziƙi? Duk faɗi tashin da nake har Ubangiji ya dafa mini? Kuma sbd kare mutuncin kanta na ce ta fito da mijin aure, shekaru 31 banda ita wa kike gani a family bashi da Aure? Sai fa Sona da Aaliyyah, ka kaf area ɗin nan namu babu mai shekarunta sai dai kullum ta yi wanka ta saka kaya ta shiga mota ta tafi aiki? Ba batun aure a ranta ta mayar da kanta tamkar namiji sbd gogagawa da take da su ta zama kamar wata feminist sai dai ta bawa wasu shawarar zama gidan miji da yadda za su yi haƙuri da rayuwar aure amma ita tana zaune gabanmu tana haɗa kafaɗa da uwarta?" Innati ta ce "Ka gama?" Ya yi shiru ta gyara zama tana saka hannu a ƙirji ta fito da yagulallen nono duk a bushe ta ce "Me ya wannan Audil azizu?" Ya saurin cewa "Don Allah Innati ki yi haƙuri Please" Ta girgiza kai ta ce "Ni fa ƴar banza ce, shiru dai kawai nake bance komai ba, idan kana jin kai ka haifi Kululu to ni kuma ni na haifeka ina umartarka daka gaggauta janye sharaɗin ka akan ta, ko kawai na saki nonon ya faɗi ƙasa kasan me hakan ke nufi" Abbu ya ce "In sha Allah" Ta ce "Maza kirata, ai ba wani yaƙunanne bane ya tara arziƙin gidan" Abbu ya ce "Asabe kirata" Mami ta miƙe tare da nufar part ɗin Majeederh not too long suka dawo tare, ta yi wanka ta shirya cikin wata designer ɗin Abaya mai kyau da tsada tayi rolling kanta kyanta ya bayyana idanunta ya faɗa kamar Balarabiya. Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Ta tsuguna ta gaida Maman Alpha da Innati da kuma Abbu bai amsa ba ya ce "Ki koma aiki" Innati ta ce "A'a daman waye ya sanya ta fara aikin ba kai ba, cewa za ka yi ka janye maganar miji ta nemo a nutse ba tashin hankali" Ya faɗi yadda ta ce Majeederh ta ce "Na gode Abbu" Fita ya yi Innati ta bisa da idanu ta ce "Yanzu ma jin kansa yake wani ɗan iskan me kuɗi ne, rabon daya taka ya je ya gaidani anfi shekara Ashirin wallahi tallahi" Maman Alpha ta ce "Shi ne ina ta kiranki shiru ko Majeederh?" Ta sunkuyar da kai ta ce "Zan zo In sha Allah" Sun jima kana sukai sallama... Yau tunda ta tashi da ciwon mara a hankali take duba lokacin tana jiran zuwan Latifa kafin ta shige B.u.k Allah yasa yau ba mutane a office ɗin nata tana zaune saman duguwar kujera zufa na yanko mata, ta saka hannu ta riƙe wajan dake mata ciwo daidai mara duk iya yadda takai ga dauriya ta kasa jure zafin ciwon jikinta ɓari yake, hannu ta kai da nufin ɗakko wayarta ta faɗo daga kujerar ta kwanta saman carpet rolling ɗin kanta ya cire yalwatacciyyar sumarta tayi ɗaiɗai a saman carpet ɗin sbd zamewar ribbon kanta, kiran sunan Allah kawai take domin ta gama fidda ran mutuwa ma za ta yi idanunta har ya fara ɗaukewa sai fari, shigowarsa cikin office ɗin ya yi daidai da sarƙewar numfashinta a rikice ya ƙarasa shiga ciki yana cillar da wayarsa yana zuwa ya zube a ƙasan carpet ɗin duk da kyan kayan jikinsa da ƙamshin dake ta shi yana zuwa ya saka hannu ya ɗagota zuwa jikinsa gashin kanta na rufe masa fuska ya shiga girgizata ya kasa cewa komai, can ta ja numfashi jinta a jikin mutum yasa ta fashe da kuka Majeederh bata ƙaunar ciwo ko kaɗan balle wannan ciwon cikin da take jin kamar ta mutu bata taɓa jin irinsa ba, ta ƙanƙame wanda take jikinsa sosai a hankali muryarsa na fita da ƙyar ya ce "Sorry, meke miki ciwo?" Ta kasa bashi ba tare data san waye ba sbd bata hayyacinta ta kama hannunsa da manna a mararta ta ce "Zan mutu, ciwo wayyo" Ya yi shiru yana jin kansa na sarawa tsigar jikinsa na tashi ta ƙara danna hannunsa a marar ta ce "Ka danna mini....
MIJIN MALAMA na kuɗi ne, don Allah ki biya ki karanta da ƙyar nayi typing sbd masifaffen zazzaɓi ga wani nataccen ciwon kai........ More especially chat me via WhatsApp 08119237616Zame hannunsa ya yi da ɗan sauri yana jin kamar ya yi abinda take buƙata ɗin, but he can't do that. Ya dubeta yaga gabaɗaya a hargitse take gashi ya rufe mata fuska, a nutse cike da kalama ya miƙa hannunsa da yake fidda wani ƙamshi ya fara ƙoƙarin tattare gashin fuskarta, baya da abinda yake burin gani sama da fuskar a yanzu. Kafin ya ƙarasa daga bayansa an ce"Oh hello!" Cak! Ya tsayar da hannunsa yana mai dungule su, gently ya miƙe tsaye tare da goya hannunsa a baya as asual kamar yadda ya saba. Ya juya sukai idanu biyu da Abraham, kamar yadda shi ma Abraham ɗin ke kallon Mutumin, Bad boy ya janye fararen Idanunsa cikin sigar tuhuma ya ce "Who are you? And why are you here?" Ya tambaya a ɗan gajarce cikin nutsuwar murya ganin wanda ke gabansa kamar yana da bala'in nutsuwa. Mai martaba Ajlaal Sultaan ya basar yana mai da idanunsa ga haɗaɗɗan agogon wrist ɗin sa. "Am talking to you?" Ajlaal ya ɗan rufe ido ya buɗe kamar ya zame face mars ɗinsa sai kuma ya nuna masa inda Majeederh ke kwance kamar numfashinta ya ɗauke ya ce"Ur Mom" Abraham bai jira jin waye wannan mutumin ba ya nufi kan Majeederh yana durƙosawa, da wannan opportunity ɗin Mai martaba Ajlaal Sultaan ya samu dama ya fice daga office ɗin, yana jin duniyar kanta na juya masa. Abraham kansa ya kulle ya rasa wanne kalar taimako zaiwa Majeederh, a hankali ya ɗora kanta a cinyarsa yana shafa sumar kanta slowly kamar bai tsoran taɓawa tashin hankalin Abraham ɗaya kada Majeederh ta mutu ta barsa, ya shiga bubbuga kumatunta a hankali ta buɗe idanu tana jan numfashi da ƙyar, idanunta ya sauka akan fuskarsa, ta marairaice fuska sosai kamar yarinyar goye ta ce "Little my son, mutuwa zan yi cikina" Kallonta shi dai kawai yake ta kama hannunsa da kyau za ta yi magana ya girgiza mata kai alamar ta yi shiru, sunkuyawa ya yi gabaɗaya tare da sunkutar ta bakiɗaya ya nufi duguwar kujera ya kwantar da ita, Majeederh azaba ta sanya ko idanu ta kasa buɗewa, ƙirjinta na yin sama da ƙasa ta jima ba ta yi ciwon ciki kamar haka ba. "Ina ke maki ciwo?" Abraham ya faɗa a takaice kuma a ɗan rarrabe, ba zata iya cewa komai ba sai hannunsa data kama ta riƙe ita ba abin ta ce masa ya yi mata addu'a ba, gashi bata ma gama yarda shi likita bane, ga tsoron kada ya sake yi mata wata allurar sai kawai ta nuna masa ya danna mata cikinta. Ɗaga kanta ya yi ya mayar kan cinyarsa a hankali ya ɗora hannunsa ta saman rigarta ajjiyar zuciya ta sauke lokacin da ta ji saukar hannunsa daidai inda yake mata ciwo, slowly ya shiga danna mata yana shafa kanta cike da kulawa kana ganinsa kasan bai wani iya ba, idanunsa sun yi jajur yana mamakin yadda tsigar jikinsa ke tashi kamar waya na jan shi sometimes, a haka har ya ji saukar numfashinta damtsen hannunsa data ƙanƙame, abubuwa biyu suke yawo a kan Abraham, idanunsa kuma kafe a kan fuskar Majeederh dake bacci lokaci zuwa lokaci take yatsuna fuska.Ta ɗauki almost 45 minutes tana baccin wahala sbd lafawar ciwon, idanunta ta shiga buɗewa da ƙyar bakinta ɗauke da addu'a, ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious dake tashi a hankali yana ratsa cikin hancinta ya sanya ta juya ga mmkinta sai ta jita kwance male male a cinyarta mutum ta runtse Idanunta da ƙarfi, ƙirjinta na bugawa ta shiga furta "Asstagafirullah" Yau ita Majeederh ke kwance jikin wani? Ta shiga uku "Sorry" Ta ji husky voice ɗinsa mai tasiri a zuciyar duk wanda ya ji, wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke jin muryar wanda take kan cinyarsa sai a lokacin ta lura gabaɗaya ta ƙanƙamesa ta yi bacci sosai duk da na wahala ne, ta miƙe zaune cikin sauri ta tashi tsaye tana riƙe kanta da kyau ta ɗauki vail ɗinta ta yi rolling ƙoƙarin kawai take bayan ta yi baya ta zauna to others sofa ta kallesa taga gabaɗaya ba ita yake kallo ba, kansa a kife yake hannu ɗaya a tsakiyar kansa ya hargitsa sumarsa. "Are you okay?" Gently ya ɗaga kansa ya kalleta da idanunsa da sukai jajur kamar gauta ta ƙara cewa "Are you okay?"
"How can i be okay kina jikina Maa?" Ya bata amsa, ta ce "Me?"
"You scared me" A hankali ta ce "Sorry" Ya shafa kai yana danne laps ɗinsa kamar mai mata raɗa ya ce "How do you feel now?"
"Allahamdulillah!" Ta ce masa tana nuna masa hand bag ɗinta da phone da car key ɗinta ta ce "Miƙo mini" Ya dubi kayan ya ce "Home? Ok I'll drop you" Ta haɗe fuska nan da nan duk da yanayin da take jin kanta bai hanata cewa "Khalil"
Yaƙi amsawa don baya son sunan ta ce "How many times do I have to tell you sai ka ƙara girma, before you start driving me? Ko so ka ke na shiga ka watsar dani a titi kafin naga aurenka?" Ya yi shiru sai kallonta yake ta ɗauke tana kallon wayarsa dake kawo haske tun ɗazo ta ce "Zuwa nan da shekaru 10 idan na gama rainonka sai na sallama maka Matsayin driver, Under age like you kamata ya yi a hanaku driving, ka kawo mini all bunch of keys ɗinka na mota" Speaking calmly ya ce "Ohk" Ta ce "Pick your call" Ya taɓe fuska kawai kalmar yaro na yi masa yawo a brain ɗinsa. Majeederh ta ce "Oh Allah, ba Grandpa bane?" A hankali ya miƙe yana cewa "Why do you want me to pick up the call?" Tana miƙe tsaye itama ganin ya tattaro mata kayanta ta ce "Masu kiranka sun damu, fatana kawai ba wannan yaran bane ku haɗu ku dinga nuna ƙuruciya" Ta faɗi haka tana nufar waje sai a lokacin ya ɗan yi murmushi ya ce "Haka zaki fita?" Ta tsaya tana duba jikinta ta ce "Akwai matsala ne?" Ya girgiza mata kai kawai kafin ta nufi ƙofa ya ƙarasa wajan ƙofar da sauri yana tsaya a bayanta ya cire rigar jininsa ta sama ya ce "Ki rufe jinin" Majeederh ta yi sai, sai kuma ta kai hannunta ta shafa ta jita duk a jiƙe ji tayi kamar ta nutse a wajan da kunya me ya sa wannan abin zai zo mata yanzu? Daman shi ne kenan shi yasa take ta ciwon ciki amma yaushe rabon da tayi ciwon ciki dan za ta yi al'ada, ta gefenta ya shige yana ɗan cije baki. Majeederh ji ta yi kamar ta dauwama a wajan, Abraham bayan ya kunna motar ya ɗan ɗaga murya cikin gurɓatacciyar Hausar shi ya ce "Na zo na ɗauke ka Jee?" Ta yi masa shiru gani ta yi ya buɗe mota hakan yasa tayi saurin sakin liƙab ɗinta ta nufi motar tata, front seat ta buɗe ta shiga, ya kunna motar tare da yin reverse cikin nutsuwa ya shiga murza kan motar lokaci zuwa lokaci yake ɗan kallonta ta mirror yana girgiza kai, Majeederh addu'a take Allah dai ya kai su gida lafiya har sukai nisa bata yarda ta kallesa ba haka kawai yau take jin nauyin ɗan nata yana tsaka da driving ya ji ta ce "Ina motar taka?" Sosai ya jita sai ya yi ƙasa da waƙar da yake ji ta crisdanial ya ce "What?" Ta ce "Banga motarka ba tana ina?" Ya ce "Ohk" Ta ce "Me?" Ya saki kan motar gabaɗaya ya zuba mata gajiyayyun idanunsa ya ce "I can't drive, kina mgn" Yana faɗin hakan ya riƙe kan motar ya ci gaba da driving da mugun gudu tun a lokacin bata kuma cewa komai ba, wani irin mahaukacin gudu yake kamar zai tashi sama baya taɓa tsayawa danja, sun zo daidai roundabout suka samu ana faɗa tsakanin wani ɗan karota da wani me napep, Abraham ji ya yi jikinsa ya ɗauki rawa da ɓari ganin abinda yake shirin yi ya sa Majeederh cewa "Kada ka fita" Bai kalleta ba, domin yana kallonta dole ya bi umarninta a hankali ya ce "Zan amshi ruwa" Yana faɗin hakan ya buɗe motar tare da saka mata key kai tsaye ya nufi tsakiyar inda ake faɗan. Majeederh ta shiga bugun ƙofar hankali tashe domin tasan idan Abraham ya isa wajan ba sa a haifar da ɗa mai ido ba, cikin sa a ƙofar ta buɗe garin saurin yaje wajan faɗan ƙofar bai rufe ba, ta riga data mance rigarsa a jikinta saman abaya ɗinta ta shiga takawa zuwa wajan da ƙyar kanta na juyawa. Abraham ya kalli ɗan karota ɗin da yake cewa "Daman idan ana duba yanayin society to Gwamnati babu uban da zata iya ta ɓukawa, duk ƙoƙarinta wajan ganin komai ya yi daidai amma al'umma bata taɓa bata goyan baya, kuma sune kan gaba wajan tsinewa gwamnatin dake ci, kuna tsine musu suna ƙara lalacewa dole kuga abubuwa suna ta faruwa, yadda suka dama haka za a sha" Mai napep ɗin ya ce "Ok daga maganar hakƙina sai ya zama laifi? Akan miliyan ɗaya da rabi ake bamu napep ɗin nan, kafin mu biya kuɗin mu yi batun riba ta kwararraɓe tuni, amma baku gani abu kaɗan ƴan adaidaita za su yi aci su tara kenan mu ba mutane bane, bamu da ƴancin yin magana ko?" Ɗan karota na ƙoƙarin yin magana ya ji an kifa masa mari an kuma kifa masa, ya buɗe baki zai magana ya ji an sakar masa naushi a bakin.
Ihu ya kurma na azaba, yana kallon Abraham dake huci kamar zaki ya ce "Me na yi maka, wanne irin zalunci ne wannan?" Abraham ya shiga dukan ɗan karotan kamar an aiko shi.
"Fouk You!,
How dare you insulate him, like that, Eh?"
Har ya juya ya tafi yaga dukan bai masa ba, ya dawo da sauri tare da kama hannun ɗan karotan zai karya. A gigice ta ce
"Ibrahim-Khalil!" Bai kula ba sbd bai yi tunanin da shi yake ba, cak kuma ya tsaya dalilin muryarta da ya ji. Ya ɗago jiki a sanyaye sbd shi bai ba san yaushe ne ya shiga dukan mutumin ba, kallonta ya yi ya ce
"Sorry Mami" A fusace ta ce "Sorry for yourself Khalil" Ta kalli mutumin ta ce "Don Allah ka yi haƙuri, yaro ne ina mai baka haƙuri" Ta juya ta kalli Abraham da ransa ya yi masifar ɓaci jin ta ce wai shi yaro ne? Ta ce
"Say sorry to him, ka bashi haƙuri" Ya ɗauke kai tare da yin shiru.
Tun da aka fara faɗan yana zaune cikin mota, sanye da wata dakakkiyar shadda gezner sai ɗaukan idanu take, komai na jikinsa da mugun kuɗi aka siye shi. Uncle Isma'il dake ɗaya side ɗin ya ce "Majeederh's disappointed me, na kasa yarda ita ce cikin tsakiyar mutanen nan" Abbu ya runtse idanunsa,wai ƴar cikinsa ce a nan wajan? Idanunsa ya sauka akan rigar Abraham dake jikinta, a hankali ya dinga binta da kallo, frm head to toe ganin jini kwance a bayanta ya sanya Abbu fara tari yana girgiza kai, Uncle Isma'il ya ce.
"Take heart Abdul'aziz,
Ka bi komai a sannu dan Allah, Please!" Shi kansa Uncle Isma'il idan ransa ya yi dubu to ya ɓaci, he can't believe cewa Majeederh yake gani, akan idanunsu ta saka hannu ta jawo hannun Abraham har zuwa cikin mota. Shi kowa Abbu tari ne ya sarƙe shi idanunsa ya yi jajur sosai, da ƙyar yana jan numfashi ya amshi bottle water ɗin da Uncle Isma'il ke bashi ya shiga ja yana komai ya fice masa a rai.
Misalin 5 na yamma wata ƙatuwar mota, Mercedes-Benz EQS Black colour ta yi parking a compound na gidan Uncle Isma'il, Driver ya ce "We're here, Sir"
Abraham dake bayan mota, ya shiga buɗe idanunsa da suke always sleeping sbd ƙwayoyin da yake sha, tar ya buɗe ganinsa akan harabar gidan, har ranshi ya ɗauka gidan zai ninka tunaninsa sai ya ga ko kwatan na Grandpa bai kama ba, balle kuma nasa gidan da bai fiya zana cikinsa ba. Sanye yake da Brown ɗin Armani suit, wacce ta kama jikinsa sosai dark black skin ɗin ta fito sai sheƙi take, hannunsa maƙale da agogon wrist na Patek Philippe, ga wani takalmi Half Cover Leather Shoe, komai na jikinsa designer ne. Fitowa ya yi daga cikin motar yana rufe idanu tare da zuba hannu a aljihu, a hankali yake bin komai na harabar gidan Uncle Isma'il, yana tsaye Uncle Isma'il ɗin ya fito cikin nagartacciyyar shigarsa tun daga nesa yake kallon Abraham har ya ƙarasu ya ce "Oh har ka iso?" Abraham ya nufi wajan Uncle I zai rungumesa alamar gaisuwa Uncle Isma'il ya miƙa masa hannu alamar musabaha bai musa ba ya amsa a hankali ya furta "Good day Sir" Uncle Isma'il ya ce "Come in, bismillah" Suka shiga har Parlourn baƙi. Uncle I ya gyara zama cikin turanci ya ce "Sunana Isma'il mahaifi ne ga Majeederh uwar riƙon ka, Ban yi wahalar gane ka ba, a wancan lokaci Little ake ce maka, sbd yadda kake baƙi ƙyakƙyawan mai ɗaukan hankali, ga saurin fushi da zafin zuciya,na lura har yanzu akwai ta kuma" Abraham dai kallon Uncle Isma'il yake bai ce komai ba.
"Kana da shekaru 3 a duniya Majeederh ta tsince ka, ta raineka da hannunta, ta ciyar da kai da albashinta tana hana cikinta ta baka, bata faɗa amma akan ka tana yi kamar wacce akaiwa asiri da jininka, a haka har kayi shekaru biyar bi ma'ana kayi 2 years a wajanta, Tayi kuka sosai lokacin daka sake ɓata a hannunta sai gashi yanzu ka bayyana a bayyanar da ban ji daɗi ba, ka bayyana a wani addinin da ba namu ba" Uncle Isma'il ya gyara zama ya ce "Tambayoyi nake son yi maka, ina fatan zaka bani amsa?"
Abraham ya jinjina kansa alamar yana jinsa.
"What's your real name?
And who are you?
Meme aikinka? Matakin karatu? Ina familynka suke, Father, mother, e.t.c" Abraham ya sauke numfashi a ɓoye ya daɗe yana kallon Uncle Isma'il kafin a hankali ya ce "Abraham Daniel David, that's my name, Who is me?" Ya yi shiru for a second kana ya ce "Bani da uba, but i have a mother" Uncle Isma'il ya ce "Mene sunan mahaifiyar taka?" Abraham ya ɗauke shi fa duk ya gaji da tambayoyin nan, kawai don Uncle ɗinsa ne ya ce "Ohk, Jee Malumana, i can't I can't pronounce the name" Ya faɗa yana ɗan yatsuna fuska.
Uncle Isma'il ya ce "Ok, Ina son faɗa maka abinda baka sani ba, Majeederh uwar riƙo ce ba uwar asali ba, ina nufin akwai aure tsakaninka da ita ba kamar yadda ba zaka taɓa auren wacce ta tsuguna ta haifeka ba, yadda kake zuwa kana rungumeta itama tana biye maka is prohibited in Islam. Ka saka a ranka duk sanda ka fara feelings na Majeederh to zaka iya aurenta, kasan Developing feelings towards opposite sex shike kawo So ka ji kana son mutum ko kasancewa da shi ko aurensa zama na dindin wani kuma sha'awa ce kawai take jan mutum ga abinda yake gani, kasan mata komai nasu mai kyau ne Zasu iya attacking opposite sex ɗin su, su ja ra'ayin namiji ya kwaɗaitu da su, Abraham I am telling you this as your Uncle, not as my guest" Tunda Uncle Isma'il ya fara maganar Abraham ke sauraren shi cike da fahimta, nan take ya ji komai na zuciyarsa na sauyawa. Uncle I ya ce "Think, U can marry Majeederh, but u can't marry your real mother, maybe a duk sanda kke rungumeta kana jin wani abu a ranka baka saki jikinka ka fahimci mene ba sbd tunanin Majeederh is ur mother amma yaudarar kanka kawai kake, itama Majeederh takai matakin da zata iya haifar ɗa kamar ka shi ya sa ta manta cewa abin da take kuskure ne, ina fatan ka fahimta za ku ka yi nesa da jikinta" Abraham was speckless da ƙyar ya jinjina kai tare da miƙewa suka fito waje anan ya ci karo da Sona kamar ta san shi ta ce "Uncle" Ya ɗan yi murmushi domin yana ana bashi girma ya ce "Sorry gashi bana yawo da kuɗi?" Sona ta ce "Ba komai, kai ne mijin Anti Jeederh?" Bai gane ba sbd da Hausa ta faɗa ya yi al'ƙawarin zai dawo mata da gift...
Majeederh ta share hawayenta kwana biyu duk ta zama raguwa mai saurin kuka ta kalli Latifa ta ce "I'm tried Latifa na ga ji da rayuwar nan, tun ina son aure har ya fita akai na, yanzu wa nake da shi wa zai aureni da za a ce mini na kawo miji nan da 2weeks wlh bana da kowa" Katifa ta yi murmushi ta ce "Kina da wanda zai aureki mana Majeederh" Majeederh ta ce "Wallahi babu, ko zance ban taɓa yi ba" Latifa ta ce "C'mon ni na amince Mijina Aliyu ya aureki ko gobe ne...
Not edited
MIJIN MALAMA na kuɗi ne pay before you read..... More information via WhatsApp number 08119237616"Na auri mijinki? Do you want me to marry your husband?" Da wani Expression na tashin hankali take faɗar maganar tana kallon idanun Latifa Omar. Latifa ta watsa hannunta cikin rashin damuwa ta ce "To mene na tashin hankali a nan? Bayan iyayena dake, babu abinda nake a cikin duniyar nan irin mijina, amma wallahi na amince miki hundred patient da ki auri Aliyu, ki auri mijina mu zauna tare, ba zan taɓa yi miki kallon kishiyata ba, don Allah ki rufa mini asiri ki auri Aliyu" Latifa ta faɗa muryarta na rawa. Miƙewa Majeederh ta yi tana ɗaukan handbag ɗinta da wayarta ta nufi hanyar fita daga cikin parlourn. Da sauri Latifa Omar ta miƙe tana shan gaban Majeederh ta ce "Ina zaki? Ki tsaya mu yi magana don Allah, this is the right time da zamu kawo karshen matsalarki Majeederh" Murmushin takaici Majeederh ta yi hawaye na sakko mata a a kumatu ta ce "Well-done Latifa Omar, sbd na tako ƙafa da ƙafa har cikin gidan ki na faɗa miki matsalata shi ne zaki dubi idanuna kika ce i should come and marry ur husband? Are you mad?" Magana take amma hawaye ne ke zuba daga cikin idanunta. Latifa ta girgiza kai itama hawaye ya shiga sauka daga cikin idanunta ta riƙe hannun Majeederh sosai cikin nata ta ce "Wallahi that's not what i mean, tun kafin yanzu ayi miki maganar fitar da miji nake son faɗa miki ki auri mijina ina tsoran abinda zaki faɗa, Majeederh na san halinki nasan how hard you're, You have a deep heart, even if the worry will kill you, you will never tell anyone, na kasa jure yanayin na kasa fahimtar cewa jarrabawa ce, maganganun mutane akan ki ya fara yawa, me ya sa ina da maganin damuwar ki a hannu zan zuba idanu kina cutuwa? Aliyu na da kyau, ilimi both boko da Arabic, yana da kuɗi ko kuɗin mahaifinsa bai damu da shi ba, Hajia Mahaifiyarsa na da kuɗi, Ubangiji ya hore masa arziƙin da zai zauna da mata har huɗu ba biyu ba, Zan iya mallaka miki komai na rayuwa daga ciki har mijina If that makes you happy,if that will make you look like any other woman in her husband's house,Please marry my husband, Aliyu!" A hankali Majeederh ta zare hannunta daga cikin na Latifa Omar ta durƙoshe a wajan tana sakin wani irin raunataccen kuka, mai cin rai da ciwo a zuciya. Wani irin kuka take Wanda ta jima ba ta yi irinsa ba, ga ƙoshi ga kwanan yunwa,ga maganin matsalarta amma ko duniya da abinda suke cikinta zasu haɗu ba zata taɓa auren mijin Latifa ba, bata taɓa kawo hakan ba ko da, da wasa. Zubewa Latifa ta yi itama ta rushe da wani irin kuka kamar an musu mutuwa ta ce
"Ashe ba zan iya rufa miki asiri ba? Ashe zumuncin banza muke? Ashe ban zama ƙawar da zata ɗauki damuwar ƙawarta matsayin tata ba? I have been friends since we were children, we trust each other, we know each other's behavior,Even if you marry my husband, there will be no worries between us, wlh ko Aliyu kika aura babu ɓarakar da zata gilma tsakaninmu, babu wani yaƙunanne ko shegen kan lafiya da zai sako lalataccen bakinsa, zamu zama abu ɗaya, zuri'a ɗaya one single family mu zama Matan Aliyu, ki haifa masa yara tunda har yanzu Allah bai bani haihuwa ba" Majeederh kuka take sosai kamar ance Abbu ko Little ko Aaliyyah wani ya mutu, ta kasa cewa komai sai jikinta dake mahaukacin ɓari da ƙyarma kamar an jona mata shocking.
Bar Aliyu Sufyan Alhassan da tunda ya yi parting da motarshi ya shigo gidan ya tsaya cak a ƙofar da zata sada shi da main parlour na gidan nasa, tun daga farkon conversation ɗin su har kawo yanzu ya ji komai, zufa ce kawai take yanko masa all over himself, jira yake ya ji me Majeederh zata ce akan requesting ɗin Latifa?.
"Majeederh say something, ki daina kukan hakan" Majeederh ta kalli Latifa Omar da rinannun idanunta wanda ba lafiya ya cika ba, ta ce
"Dole na yi kuka Latifa, ban taɓa tunanin watarana da zata zo ace zan auri mijinki ba, me ya sa kike tunanin zan iya auren mijinki, why should I do that? Me mutanen unguwa za su ce? Me ƴan-uwan ki za su ce? Su ce na zama munafuka, maci amana mayaudariya, wacce ta aure mijin aminiyyarta? That's what you want? Sbd ina kawo miki matsalata ashe ke tunaninki mijinki zan aura? Sbd ƙaddara ta faɗa mini shi ne zaki manna mini hauka ki zautar dani da gurɓataccen tunaninki mara amfani a gareni, zaki forcing mijinki ya aureni? Bayan kin san mazan guduna suke, basa ƙaunata, balle muradin aurena, banda Imran daya taɓa furta kalmar so a duniyata babu wani ɗa namiji da ya ce yana so na, ko da sunan iskanci ne....," Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya sanya ya kasa ci-gaba da maganar ta haɗe kanta da qiwwa kamar ƙaramar yarinya. Latifa kukan take sosai ta ce "Ba zan taɓa forcing Aliyu ba, nasan ba zai gujewa maganata ba, ku zauna da juna na 1week am sure zaku ƙaunaci juna, mutanen gari kuma ki barni da su" Majeederh ta miƙe tare da goge hawayenta tas ta saki liƙab ɗinta. "Kin Amince?" Aliyu dake tsaye cikin zuciyarsa ya ce "Say Yes, Hawwa'u"
Har bakin ƙofa Lafita ta biyota amma Majeederh bata kulata ba, lokaci ɗaya suka saka hannu akan handle jin an murɗa ya sanya Majeederh saki tare da komawa baya, a hankali ya buɗe Ƙofar ganinsu a har gitse ya sanya Aliyu dake cikin nevy suit hannunsa ɗaya riƙe da rigarsa ta lauyoyi sai zabga ƙamshi yake, a hankali ya ce "What did i miss?" Latifa ta ce
"Ka tsayar da ita" Muryarta bata fita sosai ta ce "Bani hanya" Gefe ya koma ta raɓa ta shige abinta, muryar Latifa na rawa ta ce "Me ya sa zaka bata hanya, ba zata taɓa dawowa ba fa, kuma na ce ka tsayar da ita" Bai ce mata komai ba ya mayar da ƙofar ya rufe, hannu tasa zata buɗe Ƙofar Aliyu ya yi sauri riƙo hannunta ya ce "Let her go, Wife" Kuka ta fashe masa da shi ya jawota jikinsa "Sorry" kawai ya samu zarafin faɗa sbd zuciyarsa da tayi masa nauyi, ganin taƙi yin shiru ya sa ya jata har zuwa bedroom ɗinsa dake tashin wani cool ƙamshi na air-freshener, cikin dabara ya shiga bata saƙo albarkacin Majeederh Aliyu ya samu abinda ya daɗe bai samu ba a wajan matarsa Latifa tsayin wata wajan goma. Yana zaune saman wata ƙatuwar kujera ya harɗe ƙafafuwanshi saman sofar idanunsa lumshe breathing ɗinsa na sauka a hankali alamar bashi da lafiya, ya ƙara yin wani farin idanunsa sun faɗa, cikar haiba da da zati da kamalar shi na nan zaune daram a jikinsa. Wata Embroidery Islamic jallabiya ce a jikinsa fara tas, sai jiramin daya ɗora akansa looking so good. Rohaan dake tsaye cikin damuwa ya ce "Allah ya ƙarawa Mai martaba Ajlaal Sultaan lafiya, wannan tunanin da kake isn't good for ur health" Mai martaba Ajlaal bai magana ba sai idanunsa ya buɗe yana kallon ɗan uwan nasa Rohaan, ganin kallon da Mai martaba Ajlaal Sultaan yake masa ya sa ya ce "Ba tare da sanin abinda ke faruwa ba, a karo na farko wani jininmu ya sako ƙafa zuwa Nigeria, ka matsa yanzu kuma gashi ka ce mu tafi ba tare da yin abinda ya kawo mu ba" Nan ma Ajlaal bai ce komai ba, Rohaan ya numfasa ya ce "Idan akwai abinda ke damunka yana da kyau ka faɗa, tunda kasan idan har a duniya yake dole zaka same shi, ka tsallake Zaytoon, da Mimi wacce kai kaɗai kake controlling ciwonta idan ya tashi, ka bar Fulani Ƙhulud da tagwayen yaranta, Palace ba kowa sai Hadiman, Meke faruwa dakai Mai martaba? Yana da kyau ace....," “Rohaan” Ajlaal ya kira sunan Rohaan da ɗan ƙarfi a kuma taushashe, Rohaan ya ce "Tuba nake Mai martaba" A nutse Ajlal ya duba agogon Rolex dake hannunsa yana mai kikewa tsaye cikin izza har ya je bakin ƙofa sai ya tsaya ya juya kaɗan ya kalli Rohaan, da sauri Rohaan ya durƙosa ya ce "Prvt jet ɗin na hanya, ban san ya akai aka samu labarin zuwanka Nigeria ba, gabaɗaya zuwan naka shi ne latest new in the world" Da wani irin Expression Mai martaba Ajlaal Sultaan yake kallon Rohaan jin abinda ya ce, zufar dake tsastsafo masa a tsakiyar goshinsa ita ke nuna tashin hankalin jin mummunan labarin, ya dunƙule hannu tare da kallon Rohaan alamar ƙarin bayani.
Rohaan ya ce "A karo na farko Sarki makka Mai martaba Ajlaal Sultaan magajin Ex Sarkin Makka Sultaan ya sauka a Nigeria, har yanzu ba a san dalilin zuwansa ba, ana kyautata zaton zuwan sirri ne ya zo ganawa da wani ɗaya daga cikin sarakunan Nigeria, zuwan nasa ya ja hankalin dubban mutane ganin tun ƙarnin baya na kafuwar masarautar Saudiyya jininsu bai taɓa zuwa ƙasa Nigeria ba, ko mene dalilin zuwan nasa?" Daga nan Rohaan ya kashe T.v da remote ɗin hannunsa ya ce "Ire-iren wannan sune news ɗin da suke trending a duniya da Social media tare da photonka, alamarin ya fi tsamari a Al Jazeera, BBC World News,CNN International da kuma Arise News" Duk maganar da Rohaan yake a tsorace yake yinta, Ajlaal ya zame idanunsa yana riƙe kansa da kyau, duk da tashin hankalin da yake ciki, a taushashe cikin tarin ilhamarsa nutsuwa da kamalar dake zaune a jikinsa cikin kamilalliyar muryarsa yana lumshe idanu ya ce
"A san yadda aka yi, aka dakatar da news ɗin" Ya shiru yana juyawa can ya ƙara fesar da iska ya ce
"Kowa na Palace, ya zama lafiya, a san yadda akai aka ƙaryata zuwan namu Rohaan" Da girmamawa Rohaan ya ce "An gama Mai martaba, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana" Tuni ya kai cikin bedroom ɗinsa yana hana kansa jin abubuwan da suke masa yawo a jiki... Majeederh na zaune a ƙasa an haɗa family meeting kowa da kowa yana nan cikin babban parlourn na gidan Abbu, Uncle Isma'il da Uncle Bello, Innati,Yaya Bilkisu, Maman Alpha, Anti Hajiya Maryama, Sona, Du'a, Widad, Raihana, Ruma, Aaliyyah, Mami, Jawaad,Sahar. Kaf Familyn Khan General Alpha ne kawai babu a ciki, Idanun Maman Alpha ya nuna tsananin kewar ɗanta da take shekaru sun ja, babu ko labarinsa gashi abin mamaki fur Uncle Bello ya rufe ido akan bai yarda ayi cigiyarsa ba, ko headquarters na sojoji ba a maganar shi har sun yi replacing nasa da wani, kamar wanda aka rufe musu baki aka saka makulin a ruwan maliya. Bayan Addu'a da Anti tayi kasancewarta malama ita ma Yaya Bilkisu ta gyara zama ta ce "Ina Hawwa'u?" A sanyaye Majeederh ta ɗaga kanta ta kasa amsawa, a hankali kuma ta juya zuwa direction ɗin Abbu taga sam ba ita yake kallo ba, ko fahimtar yanayinsa ma ba zakai ba, ya sha shadda Light blue ɗinkin Jamper da babbar riga ba zaka ce haifi ƴar shekaru 31 ba, kullum ƙara fresh yake kuɗi sun zauna jiki ya murje. Yaya Bilkisu ta ce
"Wannan zaman naki ne, dominki akai, Majeederh ɗago kan ki sosai ki dubeni" Majeederh ta kalli Yaya Bilkisu "Dubi a gabanki aka haifi Widad yaranta nawa? Du'a, Sahar, Raihana, Ruma gabaɗaya akan idanunki suka zo duniya yanzu ko wacce tana ɗakin mijinta ta rufawa kanta asiri, ke kuma kina nan zaune kina tsofa a gida, Hawwa'u mene damuwarki ne? Kina da kyau, ilimi, boko da arabic, kina da kuɗi kina da asali kowa yasan waye mahaifinki, yau a gabanmu a gaban iyayenki ki faɗa mana mene ya hanaki aure?" A wannan karan ma Majeederh ta kasa cewa komai sai kanta data ɗaga zuwa direction ɗin Abbu cikin sa a Idanunta ya shige nasa daya jima yana kallonta, ya zame idanuna ya miƙe tsaye zai bar wajan Uncle Isma'il ya ce "Daka zauna ai" Ya zubawa Uncle Isma'il ido a hankali ya ce "You can handle it" Ya faɗa tare da gyara zaman babbar rigarsa ya shige cikin part ɗinsa, gorar y ɗauka ya ɓalle wani chaset ɗin magani ya watsa a baki a hankali ya kwanta kan bed yana rufe idanunsa feeling relieved. Majeederh zata tarwatsa masa zuciya da issues ɗinta, Allah ya ware masa ita matsayin ƙaddararsa yaran dake neman ɓata masa suna a duniya, she really disappointed him, actually. Sosai Yaya Bilkisu ke faɗa kamar zata ari baki ta ce "Mun gaji da sanya miki idanu, tunda ke baki amfani da iliminki ba, wallahi wallahi idan baki fito da miji in few days ba zaki sha mamaki, wannan ƙannen naki duk sun fiki martaba a idanun jama'a, kuma tunda haka kika zaɓa aiki da neman kuɗi da kurɗa kurɗa ya fiye miki aure ga Sahar zata haihu sai ki ma zaman daɓaru mutuniyar banza" Anti ta ce "Ki yi haƙuri Yaya Bilkisu komai fa lokaci ne" Yaya Bilkisu ta ce "Saurara Maryama wannan yarinyar dole mu nuna mata ikonmu na iyaye" Maman Alpha ta ce "Haka ne, amma dole a fara binciken daga ina matsalar take?" Mami ta ce "Wacce matsala? Kawai ba auren a ranta tafi gane yawon Ngo ɗin nan da Foundation" Uncle Bello ne ya ce duk yaran su fice, su kaiwa Majeederh faɗa sosai kana ya ce "Ki shiga ki bawa Mahaifinki haƙuri bashi da lafiya" A sanyaye ta miƙe ta nufi ta nufi part ɗinsa tsaye ta gabashi hannunsa riƙe da waya kamar yana kallon wani abu ko dannawa. "Abbu" Cikin sauri ya kifa wayar ba tare da ya ce komai ba, Majeederh ta zube a ƙasa ta ce "Abbu ni mai laifi ce a gare ka, don Allah ka yafe mini In sha Allah zan yi abinda kuke buƙata" Ya juya da sauri ya kalleta a hankali ya ce "Zaki me?" Ta ce "Zan kawo mijin aure" Wani dugun numfashi ya sauke ya ce "Are u sure?" Ta jinjina kai ta ce "Kayi haƙuri Abbu, na sanya maka damuwa a zuciya ban zama yarinyar arziƙi ba, ina ladama da kasancewata mara amfani a gareka, ka yafe mini ka dinga amsa gaisuwata" zuciyarsa ta kare tausayin ƴar tashi ya kamasa ganin ko hawaye ta kasa sai ƙirjinta dake harbawa, ya miƙa mata hannunsa ya ce "Stand up" Kama hannu ta yi ta miƙe, yaro a gaban iyayensa baya tsofa ya taka har gabanta ya saka hannu ya riƙo fuskarta a hannayensa cikin kasa da murya ya ce "Hanyar aljanna nake nema maki, ke ɗin tamkar amana ce dake da Aaliyyah" Ta saki kuka ta ce "Am sorry Abbu" Kasa magana ya yi sai buɗe hannunsa da ya yi ya ce "Come" Cikin sauri ta shige jikinsa tana wani irin kukan farin ciki yau Abbunta ya rungumeta rabonta da jin ɗumin jikinsa tun tana ƙarama. Can ya saketa ya juya zuwa bedroom da sauri.... Bayan sallar Issha tana zaune a bedroom ɗinta dake ba sallah take ba, ta jawo wayarta jin ƙara kafin ta ɗauka ya katse miss calls wajan 10 na gani 7 na Son my world, 2 na Latifa 1 kuma babu suna wata mahaukaciyar special number ce da bata taɓa ganinta ba, number Abraham ta kira tana fara ya ɗaga "Assalamu alaika Baby little me" Tana jin sanda ya sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya jin bai amsa ba ta ce "Khalil" Nan ma shiru ta ƙara cewa "Baby are you okay?" Harta fara tunanin ko kiran ya katse ta ji can ƙasan maƙoshi ya ce "Are you crying?" Ta haɗe fuska kamar yana gabanta ta ce "Uhm Baka damu da Maminka ba, no calls no text, anyway how are you?" Ya yi shiru ta ce "Zan ajjiye wayata" Can ta ji ya ce "You're still crying as always, wahh happen?" Ta yi Ignoring nasa ta ce "Khalil ina mahaifinka wai? And ur mother ina ne garinku ina son sani Please kuma dai ba kana cikin wannan yaran bane ko? Baka faɗa da kowa....," A tsawa ce Abraham ya ce "Stop asking too much, why are crying? What's happening eh?" Ya faɗa tana jin yadda yake fidda huci kamar ma baya cikin hayyacinsa, haka kawai tsoransa ya kamata ta fashe da kuka sosai tana marairaicewa ta ce "Shi ne zaka mini tsawa Mamin taka?" Ya yi mata shiru cikin faɗa da kuma alamun damuwa ya ce "Don't let me to repeat myself Mami" Ta ƙara fashe masa da kuka ta ce "To ba cewa akai na fito da mijin aure ba?" Wannan karan a hankali ta ji muryarsa tana sauka ya ce "In english" Duk a tsorace take da tsawarsa cikin turanci ta ce "Abbu da Uncle's ɗina sun yi faɗa sosai wai na fito da mijin aure kwana nan, na rasa yadda zan yi kuma bani da kowa ba wanda ya taɓa cewa yana so na ko da wasa yanzu Little ya zan yi?" Ya yi shiru ta wayar yana jin tashin kukanta ƙit kuma ta ji ya kashe wayar, da sauri ta sake kira ta ji a kashe, sai yanzu take mamakin yadda akai harta faɗawa Abraham a matsayinsa na ɗanta bai dace ya ji wannan matsalar ba, raba dare ta yi tana tunani daga ƙarshe ta yi addu'a ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta, bata kashe wutar ɗakin ba sbd bata son duhu ko kaɗan... Can cikin dare fitsari ya kamata ta buɗe idanu da ƙyar ganin duhu gabaɗaya a bedroom ya sa gabanta ya faɗi, ko nepa aka ɗauke? Ko ai basa amfani da nepa inji ne 24/7 ta miƙe a hankali ta shiga laluba hanya, can ta ji hannunta ya sauka akan chest ɗin mutum ga suma nan fal kwance luff a tsorace take ƙoƙarin cire hannun ta ji an saka hannu an fizgota ta faɗa ƙirjinta baki ta buɗe za ta yi ihu ta ji ya rufe bakin da na....
MIJIN MALAMA pay before you read please..... If you want to Subscribe my book via WhatsApp number... 08119237616.
Have a nice weekend👑Rawa jikin Jee ya fara da wani irin ɓari naman jikinta na wani irin ƙyarma, tsoro da fargaba ya wanzu a zuciyarta, tana jin ƙirjinta na wani kalar ɗagawa da ƙarfi, sosai hankalinta ya tashi jin an sanya hannu tare da rufe mata baki, duk da kasancewar duhu bai hanata fahimtar waye ba, domin ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious ya riga daya fallasa waye. Majeederh na ƙoƙarin zame hannunsa ta ji ya cire nasa da sauri yana ɗan ja baya, cikin sauri ta miƙe jikinta na rawa ta nufi wajan socket ta kunna hasken bedroom ɗin, riƙe kanta tayi da kyau tana kai dubanta zuwa direction ɗin inda yake ta ganshi durƙoshe a kusa da kujera ya kifa kansa a armchair hannunsa duk biyun tsakanin cinyoyinsa, rawar da jikinsa yake da karkarwa ya sanya gabanta ya faɗi tare da tunanin ko bashi da lafiya ne? Me yasa mesa? Me ya kawo shi gidansu, har cikin bedroom ɗinta? Ko yau ɗin ma ta katanga ya shigo? Sake ware idanunta ta yi a kansa taga har lokacin jikinsa rawa yake ga jijiyoyin kansa da suka fito sosai. Da sauri ta ƙarasa kusa da shi ta ce "Khalil" Shiru bai bata amsa ba, duk da yana jin muryarta a tsakiyar kansa, Majeederh ta rikice domin daman tun yana ƙarami bata jure ciwonsa balle yanzu da take ganin ya yi ɗan wayo idan ya yi ciwo zai iya mutuwa, a yanzu kuma Abraham ya mutu zata iya zaucewa Ubangiji ne shaidar irin son da take masa, tuna hakan yasa ta ƙara yin ƙasa da murya ta ce "Khalil are you okay?" Ya yi mata shiru, ganin rawar jikinsa ka ƙaruwa fiye da kima har wata miƙa yake faffaɗan ƙirjinsa na buɗewa yana matse ƙafa ya sanya a ruɗe cikin tashin hankali Majeederh ta kai hannu zata taɓa kafaɗarta cikin sauri muryarsa bata fita sosai ya ce "Don't torch me" Ya faɗa a rarrabe murya can ƙasa abubuwan da suke masa yawo a jiki ya sanya baya fahimtar taƙa maimai abinda gangara jikinsa ke buƙata. Majeederh ta cire hannunta a hankali kuma ta juya idanunta ya sauka akan wayarsa dake yashe har ta fashe ma, cikin sauri ta ɗauki wayar da mamakinta tana shafa saman screen ɗin iphone din idanunta ya sauka akan photonta wanda take zaune a office ɗin ta na B.u.k idanunta lumshe a photon kamar mai bacci sai ɗan murmushi da ta yi wanda ya sanya dimples ɗinta lomawa ta yi wani irin kyau sosai. A hankali ta lumshe idanunta tana wani irin son Abraham na ƙara yawa a zuciyarta, hasken da wayar ya kawo da sunan Taj a saman screen ya sanya Majeederh kallon wayar tana mamakin me ya sa ake kiran shi by this time? Kiran ya katse wani ya ƙara shigowa a sanyaye ta saka hannu ta ɗaga kiran tana mannawa a kunnenta tare da yin shiru tana son ji Who's on the line? Daga cikin wayar Taj ya yi dariya ya ce "Bad boy gani a hanya ina following naka, amma banga motarka ba, ka nutsu wallahi ba zaka iya driving a halin da kake ciki ba, kuma duk masifar taurin kan ka yau ƙaryar alawa ƙasa dole sai ka nemi mace ka kwanta da ita kamar yadda na yi maka al'ƙawari, idan kowa ba haka ba You won't sleep a wannan daren, shi ya nace Joshua ya zuba maka ƙwayar kaɗan a cikin Cork ɗin amma ya juye" Taj ya ƙara fashewa da dariya sosai ya ce "Zan yi dropping Debeka a gidanka sai ku kwanta tare kasan yadda take mahaukacin sonka, yarinyar classic beb ce yanzu zata gigitaka ka faɗa mini inda kake idan na yi dropping ɗinta a gidanka sai na zo na ɗauke ka, ni zan koma club ne Now the party has started, the classic babies are coming into the club, wallah ka yi missing Bad boy.....," Cikin tsawa Majeederh ta katse Taj idanunta har wani rufewa yake a karo na farko na rayuwarta ta ce "Uwar Debeka da uban Debeka, wato kune kuke bashi kayan Shaye-shaye ko? Ko ke son haɗa shi da wata figaggiyar yarinya mara tsafta wacce take fama da Datti a jiki" Takaici ya sanya Majeederh yin shiru. Taj ya ce "Au wai wajanki ya zo?" Ya faɗa yana zare idanu, yana kuma danne dariyar dake ransa. Majeederh ta ce "Meye Sunanka?" Ya ce
"Taj" Ta jinjina kai ta ce "Baka da hankali ko? Kana forcing na shi ya aikata abinda Muslunci ya hana?" Taj ya ce
"A'a Mami, Debeka fa budurwar shi ce, kuma a gidansa take zaune, bayan itama akwai wasu ƴan matan da suke zuwa wajansa,kuma duk mu'amala yake da su kenan dai a lalace yake, kuma mene haramcin daga kwanciya da mace Mami?" Wani irin rikitaccen tashin hankali ne ya rufarwa Majeederh ta runtse Idanunta da kyau, tana son hana kansa gasgata abinda Taj yake ƙoƙarin faɗa mata. Ta cikin wayar Taj ya ce "Good night Mami, ki lura dashi please cikin dare yana yawon firgita" Yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da kifawa a jikin kujera ya dinga wata mahaukaciyar dariya kamar zautacce. John ya ce "Taj why?" Taj ya ɗaga kafaɗa hannunsa riƙe da pen Shisha ya ce "What?"
Da turanci John ya ce
"Me ya sa zaka sakawa Bad boy ƙwaya a Cork? Muma da muka saba harka idan muka sha kusan haukacewa muke, balle shi da ko sakin fuska bayayi ko Debeka da yake ɗagawa ƙafa ta baro ƙasar su ta biyo su bai taɓa maganar 5 minutes da ita ba, even small hug bai taɓa yi mata ba, ka manta sanda tayi masa allurar bacci sbd buƙatarta kusan kasheta ya yi fa, amma all this ka ɗauki abu ka bashi yanzu kasan ba zai iya riƙe kansa ba idan ya aikatawa Mamin tasa wani abu fa? Jesus mummunar labari zai faru" Taj ya haɗe fuska irin ko a jininsa ɗin nan ya ce "Ni fa Am happy for him, ita Mamin tasa zata gane shi ba yaro bane"
Sai a lokacin wani da zuwansa country ɗin kenan kuma sun fi good time shi da Bad boy tsare girar su ɗaya ya ce
"This is not fair, how can you imagine yaje wajan Maminsa a haka? Kasan mugun son da yake mata? Ko fa president baya so kamar....." Sai kuma ya yi shiru da bakinsa. Taj ya ce "C'mon ka ƙarasa faɗar maganarka, wanne president? Meye haɗin President da Abraham?" Salamon bai ce komai ba ya ɗauki kwalbar giyarsa ya ratsa ta cikin mata ya shiga rawa hankali kwance. Taj, John, Joshua suka kalli juna John ya ce "Who's Abraham?" Taj ya ce "President's son" Joshua ya ce "Dream, idan shi ɗan gidan shugaban ƙasa ne meyasa yake zaune shi ɗaya tal sai Grandpa yana rayuwa kamar mara gata, sai kuɗi da yake da shi kamar hauka, wallahi idan shi ɗan President ne bamu isa ya shigo cikinmu ba, kawai Salamon yana raina mana hankali ne" Taj ya ce "Something is fishy, Farkon haɗuwata da Abraham a University of Oxford, a lokacin na duba card ɗinsa naga alrdy ya yi nisa a karatu, naga tambarin Germany da kuma National I.d card na germany bai bari na gama gani ba ya karɓe ya ce, asali Grandpa University of Munich dake Germany ya sashi shi kuma bai so yama tsani ƙasar bakiɗaya, muna level ɗin ƙarshe a University of Oxford wasu manyan mutane suka zo tafiya dashi ya kafe babu inda za shi nayi mamakin yadda suka kasa kama shi sbd at the end ma ɗaya ya harba shi ne muka tattara mukabar ƙasar, daga ƙarshe dai ban ina yaje ba domin ya barmu for good 1yr" John ya ce "Baka tunanin laifi ya yi wa mutanen?" Taj ya ce "Maybe, he's smart and stubborn boy to be honest ban taɓa ganin mutum bai iliminsa ba, baya taɓa zama lectures amma bugu ɗaya ya kewa exam, tun yana secondary haka record ɗin yake shi yasa aka dinga yi masa promotion da wur wuri ya gama secondary school sanda ya fara University zaka raina shi sosai, amma dake yana da jiki sosai ba a ganin shekarun nasa, kuma Grandpa ɗin nan nasa kuɗi ne dashi kamar su kashe shi wallahi, waye zai ce Bad boy ya karanci Likitanci? Kusan me ya sa?" Suka girgizawa Taj kai ya ce "Cos he's not his dream, Abraham's doesn't like it, Business kawai yake so bayan nan sai ɓangaren tsaro yana son sama sojan ƙasa, yanzu haka idan ya yi zanen gida miliyoyi yake samu, gabaɗaya shi ke siya mana suttura sometimes" Gang team ɗin sukai shiru kenan dole akwai abinda Abraham yake ɓoye musu na daga rayuwarsa. Taj ya ce
"Excuse me" Wayarsa ya ɗauka ya ƙara danna number Abraham yana ji tana ringing ba a ɗauka ba, ya miƙe ya ce "Bari nayi dropping Debeka"
Majeederh ta ɗauke kanta daga kan wayar Abraham da taga still Taj ke kira, maybe ya yi dropping Debeka ɗin can gidan kamar yadda ya ce, so he's waiting for Abraham to go back his home and... Ta yi saurin runtse Idanunta, fitar numfashinsa da ta ji ne ya sanya ta juya da sauri tana kallon at this time a kwance ta gansa yama kasa zama tsugunawa ta miƙe a hankali zuciyarta babu daɗi, ɗan ƙaramin yaronta wai har ya san mace? Mata ke bibiyar mata yaro? Yana Shaye-shaye shi ya sa ya zama criminal kenan bashi da tsoro? Banda haka ko zance Abraham bai isa ya tsaya yi ba, gabaɗaya nawa yake? He just 16 fa. “Innalillahi wa'inna ilahir raji'un!” Majeederh ta furta a ranta, ta durƙoshe gabansa zuciyarta na wani Irin harbawa bakinta na rawa ta ce "Khalil" Ya yi shiru Ta miƙa hannu zata taɓa shi cikin sauri ya ja baya yana mirginawa kamar zai shige ƙarƙashin gado muryarsa na shaking laɓɓansa na wani irin ɓari ya ce "Don't torch me" Kamar za ta yi kuka ta ce "But My son taya zan iya barinka haka? Faɗa mini me suka baka? Meke maka ciwo? Headache? Fever? Bari na ji ki da zazzaɓi sorry" Ya tsoro mata narkakkun idanunsa wanda sukai mahaukacin jaa sosai da ƙyar yake iya ɗan buɗe su, bai taɓa jin abu makamancin abinda yake ji ba in whole his life shi ko ciwo baya yi sosai, Ya ja idanunsa ya rufe yana curewa waje guda yana magana ƙasa ya ce "Don't torch me Maa.. Don't" Itama Majeederh ta marairaice fuska ta ce "Please Baby son, bari na taɓa wuyanka ko robe na shafa maka" A hankali cikin muryar marasa lafiya ya ce "Ohk"
Ta sauke ajjiyar zuciya ganin har lokacin idanunsa a rufe yasa ta ƙarasa dab da shi tare da miƙa hannu zuwa neck ɗinsa ya yi saurin buɗe idanu tare damƙar hannunta kafin ta yi magana ya fizgota zuwa jikinsa daga kwance da yake. Gabaɗaya ta faɗa kansa tana zare idanu, Abraham ya zaga hannunsa tare da ƙanƙameta sosai a ƙirjinta yana wani irin mimmiƙa tare da jijjiga, yana jin kamar wani abu na jansa mararsa na wani irin azababben ciwo. Majeederh ta ce "Sakeni Khalil na baka magani" Slowly ya girgiza mata kai a hankali kuma ya ƙara manneta da jikinsa ƙamshin CLINIQUE Deep Comfort Body Lotion shower gel ɗin da ta yi using da shi wajan wanka ya ƙara rusawa Abraham sabuwar zuciyar tashi na daga abinda ya ke ji. A hankali ya tura kansa tsakiyar wuyanta hannunsa ɗaya a waist ɗinta ya riƙe ta gam yana wani irin fitar da wahalallan numfashi, Majeederh ta ruɗe tare da zaucewa a rikice ta ce "Khalil let go of me, ka bari na baka paracetamol" Ta faɗa muryarta na rawa tana jin tsigar jikinta na tashi, bakinsa dake wani irin ɓari alamar yana buƙatar wani abu ya manna a kunnenta ta wani kalar zabura ta ji ya sake riƙe waist ɗinta gam ya manna da nashi yana wani irin saukar mata breathing a kunne lips ɗinsa na gogar fatar kunnenta a hankali cikin raunatacciyar muryar ya ce "Allow me to kiss u Jee.. ƴar madara...Saboda Shocked kasa motsi Majeederh tayi, take kuma jikinta ya fara rawa na rashin sanin abin yi da kuma gingimemen tashin hankalin dake neman zautar mata da nutsuwarta. Fahimtar Majeederh bata da bakin magana ya sanya Abraham janye gajiyayyun idanunsa wanda ya laushi ya ƙanƙance sbd Baƙon lamarin dake son tafiya da ruhinsa, yadda jikinsa ke rawa naman wajan na zillo da harabawa ya sanya ya fahimci akwai abinda yake buƙata urgently. Fuskarsa dake manne a wuyanta ya zame yana sake manna mata kwantaccen beard ɗinsa wanda ya sha Jack Black Beard Oil sai sheƙi yake. Shortly can ƙasa Abraham ya ce "Plxxxx" Sai kuma jikinsa ya fara jijjiga gab gab gab kamar wanda ake zarewa rai a kiɗime Majeederh wacce ta kasa koda motsi ta yunƙura zata miƙe daga jikinsa ya yi sauri kama fuskarta tare da jawota dab da nashi fuskar, Majeederh baki sake take kallon ikon yadda take zare idanu kaɗai zai sanya kasan shocked ne ya hanata ɗaukan action akan abinda ke faruwa, tsinin hancinsa ya ɗora akan nata ya ware idanu a hankali cikin saa itama shi take kallo da sauri ta janye nata jin tsigar jikinta na tashi tana zubewa kame kanta tayi da kyau tana faɗin “Asstagafirullah, Subuhanallahi, Allahu Akbar!” A zuciyarta Abraham ya buɗe baki da ƙyar ƙamshin Colgate Vedshakti Mouth protect spray na fita daga bakinsa, lips ɗinsa na gogar nata ya yi attention to kiss her lips. Sai kuma ya zame kansa tare da yin ƙasa da zuwa neck ɗinta. Lokacin da lips ɗinsa ya sauka a skin ɗin wajan wani irin zabura Majeederh tayi sbd harabar da zuciyarta tayi wani abu ya fara mata yawo saman fata. Gam! Abraham ya riƙeta da hannu ɗaya idanunsa rufe ruf jikinsa na karkarwa kamar mazari duk wasu ƙofofi na jikinsa wanda suke buƙatar abinda gangar jikinsa ke so sun gama buɗewa cikin fitar hayyaci da zaucewar tunani a hankali ya ce "I am sorry Mami" Yana faɗin haka ya sauke mata wani irin zazzafan light kisses a neck skin ɗinta tare da murza hannunsa dake bayanta a hankali kuma ya damƙe hannunta ya yi kamar zai saketa. Da sauri Majeederh ta miƙe zata tashi ta ji ya saki wata kalar sounds idanunsa na yin fari jikinsa na ƙyarma yana ƙanƙame hannunsa kamar zai suma, a haukace Majeederh ta tsuguna wajansa ta ɗora hannunta a ƙirjinsa tana jijjiga shi muryarta na rawa ta ce "Little, Baby my son what happening to you?" Yadda take jijjiga shi ya ƙara sanya shi cikin wani irin azababben yanayi numfashinsa ya fara fisga a rikice ta saka hannu ta ɗago shi tana yin kuka tana cewa "Plxxxx Khalil open ur eyes" Da ƙyar ya buɗe idanunsa yana jin kamar ba a duniya yake ba, zuciyarsa ta gama tsinkewa, ya kafe Majeederh da kallo data kamo hannunsa tana cewa "Khalil my son mene? Me kake so? Ina ke maka ciwo?" A hankali ya kai hannunta saman mararsa da yake jin kamar ya tsinke. "Here"
Ya furta shi kansa bashi da tabbacin ta ji, hannunta ta miƙa da niyyar danna masa ai da wani irin sauri ta sake shi tare da miƙewa tsaye idanunta na rufe yana yarfe hannu tana jin kamar ta riƙe ƙaton katako. Miƙewa ya yi kamar ɗan maye kana kallonsa zaka san ba'a hayyacinsa yake ba yayi muguwar faɗawa sbd azabar da yake ji a jikinsa wajanta ya nufa yana zuwa ya ɗauke shi da wani irin gigitaccen mari, Without letting him come back to his senses ta sake sauke masa wani irin zazzafan mari idanunta rufe murya ƙasa gudun kada a jisu ta ce "Out, out Khalil" Kallonta kawai yana yin baya kamar zai faɗi idanunsa sunyi jajur ga wani zafin zazzaɓi da jikinsa ya ɗauka ta ƙara nuna masa ƙofa ta ce "Zoka fita" Shi dai yasan ko kashe shi za ta yi ba zai taɓa iya fita ba, to inama yaga energy ɗin fita balle driving? Ganin bashi da niyyar fita ya sanya ta shige ciki ta ɗauki wayarsa ta damƙa masa kana ta saka hannu ta kama nashi ta shiga jansa har zuwa bakin part ɗinta ta ƙofar baya, ta tura shi kaɗan har lokacin da idanu kawai yake binta yana kallo ta garƙame ƙofar ta murɗe key. A hankali ya ja gajiyayyun idanunsa ya rufe tare da sulalewa ya zauna zaman dirsham a ƙasa ya rufe idanunsa hannunsa riƙe da mararsa sai numfashi yake saukewa a wahale tuni zazzafan zazzaɓi ya rufe shi wanda bai taɓa yin irinsa ba. Majeederh ta sulale ta zauna saman gado tare da haɗe ƙafafuwanta waje guda tana girgizawa, zuciyarta a cunkushe Asstagafirullah kawai take a ranta, Abraham ɗan ta yana buƙatar taimako tasan cikin maye yake da ba zai taɓa aikata abinda ya yi ba, dole kuma ta nuna masa nasa kuskuren na yin Shaye-shaye. Almost 10 minutes ta ɗauka kafin ta miƙe ta leƙa ta ƙofar window ɗinta ta hango shi durƙoshe ya riƙe kansa da hannu bibbiyu, ta yi matsawa tana hana kanta jin tausayin ɗan nata, har kiran sallar farko na Subhi bata runtsa ba, ta miƙe da ƙyar ta nufi bathroom tayi wanka da kyau, ta fito ta tsafta ce jikinta ta zauna zaman azkar tunda ba sallah take ba. Wajejen 10:10 ta gama haɗa breakfast da taimakon Aaliyyah suka jera komai a dining area a hankali kowa na gidan ya hallara, sai a lokacin Majeederh ta san Raihana da Ruma a nan suka kwana suna zaune Mami ta fito cikin wata dakakkiyar atamfa Valisco ruwan huda da feshin blue a jiki ta murza ɗauri ana tafiya a hankali taja kujera ta zauna, Aaliyyah ta ce "Ina kwana Mami?" Ta ce "Lafiya lou" Majeederh tana juya tea da spoon a hankali ta ce "Mrng Mami?" Ta ce "How are you?" Ta ce "Good" Raihana ta ce "Nikam Majeederh da zaki zo gidana ko sati biyu ki yi mini, kina ɗan tayani aiki tunda ba wani abun kike ba" Majeederh ta yi shiru, Ruma ta ce "Wlh idan ta gama miki ki sending ɗinta gidana, ma rage mata zaman kaɗaici" Daga Aaliyyah har Majeederh ba wanda ya kula su, Raihana ta ajjiye spoon ɗin hannunta ta kalli Mami ta ce "Yawwa gwara da ban manta ba, ni shawara ce dani idan tayi muku" Mami ta ce "All ears" Ƙamshin turaren Hugo boss da suka ji ya sanya sukai shiru, Majeederh jikinta ya ɗauki rawa amma ta dake Mami ta kalli Abbu da yake shigowa kamar sabon ango, wani tattausan voyel ne a jikinsa nevy blue ya murza jaddara akan shi ya nemi waje ya zauna. Mami ta ce "Barka da fitowa Alhji" Abbu ya jinjina kai, Raihana da Ruma suka haɗa baki wajan cewa "Sannu da shigowa Abbu" Aaliyyah ta ce "Abbu ina kwana?" A hankali ya ce "Lfy" Sanin ba a magana idan yana wajan duk sukai shiru. Gently Majeederh muryarta na rawa sosai ta ce "Mrng Abbu" Slowly ya ɗaga kansa tare da zuba mata idanu can kuma ya ɗauke ganinsa ba tare daya amsata ba, Duk motsin Majeederh yana gani juyawa spoon kawai take tana cakalkala dankali, few minutes ya sake ɗago kansa ya zuba mata Idanu "Hawwa'u" Ta ji saukar muryarsa ji tayi kamar tayi fitsari a wando ta ce "Na'am Abbu" Shortly ya ce "Leave" Miƙewa tayi tabar wajan da sauri tana jinta kamar ware a cikinsu. Mami ta ajjiya cup ɗin hannunta ta ce "Me ya sa kake yi wa yarinyar nan haka ne Alhji? Me ya sa kake son nuna fifiko a cikin yaranka, bana son haka a gaskiya ni" Bai ce mata komai ba, Aaliyyah ya tsame hannunta zata miƙe Abbu ya ce "Sit" Ta zauna tasan me yake nufi. "Raihana me kike cewa?" Raihana na rarraba idanu ta ce "Daman wani ne ke mini aike yana da hankali sosai daga ƙauyen Rurum yake naga da ƴar sana'arsa daidai gwargwado domin har ɗan dako yake, na ce ko shi za a haɗa da Majeederh tunda Kinga al'amarin nata shiru babu mashin shi ni, sunansa Tasi'u" Ruma ta ce "Lallai da kin yi aikin lada sosai Raihana" Mami ta ce "Shi ɗan dakon kenan?" Raihana na kallon Abbu ta ce "Wlh ai irinsu babu ruwansu, musamman ga Majeederh fara tas wlh haukacewa zai ya samu mata ta keta raini bama zai duba taimakon da ya yi ba, nan nan zai dinga yi da ita kamar ya lashe" Cak Abbu ya ajjiye cup ɗin hannunsa da yake ƙoƙarin kawai baki zai sha ruwa, ya mayar ya ajjiye tare da miƙewa ya fice daga parlourn. Compound ya nufa Driver na ganinsa ya miƙe tsaye, Abbu ya nufi wajan mai gadi ya ce "Waya shigo cikin gidan nan jiya?" Mai gadi ya kama kame kame Abbu ya ce "Ohk haɗa baki ake da kai ana shigo mini gida? Ka tattara kayanka na sallameka kuɗinka zan tura maka ta acct" Mai gadin ya rikice sosai ya zube yana bawa Abbu haƙuri amma ina tuni ya shiga mota... Zuwanta gidan Maman Alpha kenan ta nufi part Innati tabar Latifa tare da Maman Alpha, bayan sun gaisa Innati ta ce
"Ina Kululu?" Majeed ta ce "Gani kusa" Innati ta ce "A to bana ganki ba kuma, ƙara tabbatarwa zan yi" Ta ƙara zama ta ce "Shikenan ku dangin mahaifiyarku basa ƙaunarku ne?" A sanyaye Majeederh ta ce "Me kika gani?" Innati ta yi mitsi mitsi da idanu ta ce "Ji wata wulaƙantacciyar tambaya?? To ke yanzu dan Allah wa kika sani a dangin Fulani?" Majeederh ta ce "I don't know anyone, I've never seen anyone from my mother's family" Innati ta saki baki ta ce "To banda kin so wulaƙanta ni a idanun jama'a meye zaki sauya raye, ni zakiwa turanci?" Ita dai Majeederh bata ce komai ba, domin jikinta duk ya mutu tana son yi wa Abbu maganar Mother's family ɗin su tana jin tsoro. Innati ta ce "Kawai ki rutsa mahaifinki shi ne nunafukin ki ce ya fito miki da dangin mahaifiyarki, ki ɗaga masa hankali sosai idan ma kidnaping ɗin su ya yi sai mu ji labari, tunda ba wani yarda nayi da zuciyar Audil azizu ba, sama taka mu kaga yayi arziƙi fa? Shi yasa yake ta wani fankama yana ɗaga kai, to ai mu munga ƙaruna ma" Majeederh ta yi shiru Innati ta ce.
"Allahu Akbar, ai ba zaki san ƙaruna ba, munga ikon rabbi a wajan bawan Allan nan, gashi dai ƙarshen shi bai wani kyau ba, ai wallahi wannan kyan na fuskarki da farar fatar nan kamar sadaka yalla to haka uwarki take, har ta ɗaraki a kyau mace mai sanyin hali da haƙuri, ta sha fama da talaucin Audil azizu sana'a kala-kala tayi fa? Ko Attajirin uban naku bai baku labari ba? Babu mamaki gadonku ya tattara ya siyar kwasha kwasha, domin har gwala-gwalai ne da ita" Majeederh idanunta ya cicciko da hawaye ta kasa cewa komai. Innati ta zabga sallati ta ce "Yanzu kamata Kululu ni zakiwa turanci? Ni zaki sauya harshe, yanzu fa muke Shira dake rumi rumi kawai sai kika sauyan raye ni ki kaiwa turanci" Majeederh ta miƙe ta ce "Kyaci kanki ke kaɗai" Ta yi waje abinta, Innati tayi ƙasa da murya ta ce "Tab, kaɗan ya rage ban saki fitsari ba yarinya kamar Aljana, zaki Albarka,zaki Albarka mijinki daban yake sananne ne shi tauraro ne, wanda duniya ta gama saninsa" Haka take something kamar wacce ake buɗewa idanu. Maman Alpha da kalli Majeederh ta ce "Majeederh Kinga ɗan uwanki har yanzu shiru? Ko yana raye ko ya jima da mutuwa? Ko a hankalinsa yake ko ciwon hauka ya same shi Allah kaɗai ya sani" Gently Majeederh ta kalli Maman Alpha ta ce "Ki yi haƙuri, addu'a za a yi" Murmushi kawai ta yi kafin ta ce "Ya maganarki kowa? An samu tsayayyen?" Kafin Majeederh ta yi magana Latifa Omar ta ce "Aliyu ya ce zai aureta, amma taƙi" Maman Alpha ta ce "Mijin naki?" Latifa ta ce "Eh" Da mamaki Ta ce "Son ta yake?" Latifa ta ce "Sosai, sbd ya ce na yi conversing ɗinta to marry him take gaba dani" Maman Alpha ta yi shiru for a second kana ta ce "Eh to gaskiya conversing Majeederh to marry ur husband Aliyu, kamar ki yi forcing nata ta cakawa kanta wuƙa a ciki ne, How do you think she can marry her Aminyya's husband? It is a difficult thing that the mind cannot handle. Honestly, even I do not support this useless thought, Majeederh tana buƙatar taimakonki,She needs your help, but not this way, think of something else besides this" Latifa ta marairaice ta ce "Ni wlh tallahi na amincewa Aliyu, ba zan taɓa kishi da Majeederh ba, zamu ci-gaba da zama kamar yadda muka sabaSocially there is sacrifice, I sacrifice my husband's love for Majeederh" Maman Alpha ta ce "Sacrifice?"
"Eh" Cewar Latifa Omar
Maman Alpha ta ce "Let me tell you something you don't know, ko da ƙanwarki da kuke ciki ɗaya aka haɗaki waje gudu wlh sai kin yi kishinta, balle Majeederh? Sanda zaki shige ɗaki kina ihu idan suka keɓe Allah kaɗai ya sani,We are dedicated to Love, it does not mean that we have stopped loving, in love there is jealousy, Think about that Latifa Omar" Kafin kowa ya yi magana Innati ta shigo tana kuka wiwi hannunta riƙe da sanda. Maman Alpha ta ce "Subuhanallah lafiya Innati?" Innati ta ce "Fatima wai ni Kululu zata juyawa yare ta yi mini turanci?" Maman Alpha ta ce "Allah gasky bata kyauta ba, turanci ana zaune lafiya?" Lafita ta dinga dariya sosai sun jima a gidan kafin su ta fi. A hanya Lafita ta nufi Tahir Quest Palace Majeederh ta dai kalleta ganin hakan ya sa ta ce "Abu zan karɓo kin san mu ƴan jarida, muna amfani da Opportunity da zarar ya samu"
5 days left. Tun ranar Majeederh bata ƙara jin motsin Abraham ba even on the phone, har numbersa ta kira ta ji a kashe. A hankali ta rufe Idanunta da sauri ta buɗe kuma tama rasa wanne kalar tunani za ta yi, tana zaune wayarta ya fara ringing dubawa ta yi taga new number sharewa ta yi, kuma ba a fasa kiran ba, tunaninta ya bata masu neman taimako ne ko wani abu ne ya tashi a Ngo ɗinta. Ta ɗaga kiran tare da cewa "Assalamu alaika/ki" Taj ya yi wa Salamon alama da ya yi shiru a ladabce ya ce "Good day Mami" Sosai Majeederh ta ɗauki muryar ta yi shiru, Taj ya ce "Sorry na kira without ur permission, am very sorry about that" Bata ce komai ba, a ransa yana mamakin girman kanta ya ce "Abraham, baya da lafiya kwana biyar kenan, baya ci baya sha sunanki kawai yake kira gashi Grandpa baya gari" Majeederh ta yi shiru a hankali ta ce "Bashi wayar" Taj ya ce "Dr ya duba shi yanzu bacci ya ɗauke shi, amma yana da kyau idan ya buɗe idanu ya ganki" Shortly and silently ta ce "Address" Ya ce "Ohk check ur Dm" Kashe kiran ya yi ba jimawa ya tura mata da Address ɗin gidan. Sosai ta dinga duba location ɗin tana mamakin unguwar. Shiryawa ta yi cikin mik ɗin Abaya mai kyau ta ɗauki hijab ta saka tare da liƙab, waya da key kawai ta ɗauka ta nufi waje. Mami na zaune Main parlour watching TV ta ce "Mami zan ɗan je dubiya" Mami ta ce "Subuhanallah wani ne bashi da lafiya?" Majeederh ta ce "Eh" Ta jinjina kai ta ce "Kada ki jima" Fita tayi ta nufi wajan baƙar motarta tare da buɗewa ta shiga bismillah ta yi tare da yin key tai reverse gatekeeper ya buɗe mata, tana fita motar Abbu na shigowa, Aliyu dake tsaye a bakin gate ya ji he need to follow her, ya ga where she's going to?....
Babban gida ne wanda kafin kaga irinsa sai an tona, tsayawa faɗin yadda gidan yake ɓata baki ne, ga wasu mahaukatan securities birjik, gidan ta ciki part part ne. Gang team ne zaune a wani haɗaɗɗan parlourn gidan wanda ya kasance mallakin Abraham shi ya zana gidan da kansa. John ya ce "Taj me ya sa ka yi mata ƙarya?" Taj ya ce "Kawai ta zo ta gansa" Salamon ya girgiza kai ya ce "Baka da kirki wlh" Dry ya yi sosai duk sun cika parlourn da hayaƙin Shisha ya ce "Na kusa barin country ɗin nan" kafin su yi magana sun ji ƙarar doorbell. Taj ya miƙe ya ce "Ta ƙarasu, ku ɓoye kayan drugs ɗin nan" Da sauri suka kwashe komai, ya buɗe mata ƙofa ya ce "Wlcm Mami" Bata kula su ba sai parlourn data shiga ƙarewa kallo ya ninnka na gidansu a komai, ta yatsuna fuska. Gabaɗaya suka miƙe kamar marasa gsky sbd kwarjini ta yi musu duk da fuskarta a rufe yake. Salamon dake ya fi kowa bin diddigi ya shiga ƙarewa yatsun ƙafar Majeederh har wani yellow suke don fari. Waya Taj ya ɗauka kira Abraham dake can cikin wani narkakken part. Majeederh ta kasa zama har wajan minti biyar kafin ta ji John ya ce "Gashi nan ma" Bata ɗago kai ba haka nan Moment ɗin su ya faɗo mata, da tunanin wanda aka ce bashi da lafiya me ya fito da shi?
"Hold on. Who is that girl standing next to him....??" Jin an ambaci yarinya ya sanya Majeederh ɗago da kanta da sauri, idanunta ya sauka akan wata siririyar yarinya chocolate colour tana da kyau daidai da ita, daga ita sai half vest da wando iya laps ɗinta, ga wani gashin doki sai mannewa Abraham take, Wanda ya haɗe rai kamar ya ce ya shigo uku, tun faruwar abun babu wanda ya sake kulawa sbd ransa ya ɓaci da abinda Taj ya yi masa, Kallonsa Majeederh ta dinga yi ganin ya rame sosai idanunsa ya faɗa, a hankali ta juya ta kalli budurwar sunan Debeka ya faɗo mata wato ita ce Shegiyar dake lalata mata yaro? Salamon ya ce "Ur mother is here" Da wani irin sauri Abraham ya kalli Doorway idanunsa ya sauka cikin nasa, ya miƙe tsaye tare da ƙare mata kallo yaga tana kallon Debeka wacce ta yi tsaye tana kallon Majeederh, Shi kuma ya juya ya kalli Taj irin me ya sa? Ganin Abraham ya kasa cewa komai ta juya zata bar parlourn murya ƙasa ya ce "Ma....mi.. Mami" Cak ta tsaya ba tare data juyowa ba, Abraham ya nufi inda take yana zuwa ya rungumeta ta baya yana sauke ajjiyar zuciya a hankali dadai kunnenta ya ce "Am sorry Mami" Ta juya ta kallesa ta kasa ce masa komai ya riƙe hannunta har zuwa tsakiyar Parlour ya ce "Wlcm come to my house Mami" flowers ta ji suna zubu mata aka daga ita har Abraham ɗin, Kafin ta yi magana ta ji Gang team ɗin sun saki ihu tare da yin tafi sun ce "It's ur day bad boy, happy Engagement" Mami ta kalli Debaka bandai da ita ya yi Engagement ɗin ba? Debaka kowa suman tsaye ta yi numfashinta ya shiga ɗaukewa, Abraham ya ɗan yi cute smile da jajeyen laɓɓansa ya ɗauki wata ƴar ƙaramar box ya buɗe wani ɗan ƙaramin Gold ring ya bayyana sai sheƙi yake, a hankali ya durƙoshe akan ƙafafuwanta ya kama hannun Majeederh cikin low voice da wani irin sound ya ce "Ƴar Madara Mamina, Will you marry me?" Bugawar da zuciyarta tayi ya sanya ta yi baya kamar zata faɗi sai kuma ta tsaya da kanta jikinta ya shiga rawar da bai taɓa yi ba. Abraham na durƙoshe ya ce "Zaka auren Mami? Ɗan ki zai zama mijinki" Taj ya ce "Wip wip Wip hureee, baka faɗa mata how much u love her ba, tell her" Ya ɗan langwaɓar da kai shi fa bai wani iya ɓata lokaci da wani i love you ba, a aikace yake komai ya kwaɓe fuska ya ce "I don't need all this, ta san ina sonta ai ko Mami?" Majeederh kamar wacce ƙwaƙwalwarta ta tsaya ta kasa magana tana ji ya zura mata ring ɗin a yatsarta, ya sumbaci wajan ya ce "You're Mine" Wani kalar Ihu Gang team sukai tare da cewa "Happy Engagement Bad boy, the leader team the richer young boy" Ya miƙe tsaye yana lumshe idanunsa wanda suka azabtu da rashin ganinta sosai, John ya ce "Remain kiss, First kiss" Shi kansa Abraham mmkin yadda Majeederh batai masa komai ba yake, ta yi accepting nasa as her husband? Bai san cewa brain ɗinta ce ta tsaya cak ba. Slowly ya nufi inda take da niyyar kissing nata, Debeka dake tsaye tunaninta ya gama bata Majeederh ita ce wacce Taj ya faɗa mata Abraham ya je wajanta jiya ya kwana, Gadan-gadan ta nufi kanta da plate zata kwaɗa mata Abraham ya yi saurin tare Majeederh ta hanyar rungumeta ya ce "Mami..." Plate ɗin ya sauka a kansa nan take jini ya shiga fita ƙarar plate ɗin ya sanya Majeederh sakin ajjiyar zuciya ya haddasa dawowarta cikin tunaninta, Abraham ya juya da saurin still holding onto her ya ce "Debeka stop" Hawaye kwance akan fuskar Debaka ta ce "Stop? Na bar iyayena, karatuna ina level na ƙarshe na zama cikakkiyar low na bar ƙasata na biyoka sbd kawai ina sonka? Shi ne zaka kawo wata tsohuwa wacce ta haifeka ka ce zaka aura? To bari naga ta yadda za a yi auren" Ta ƙara nufar su Abraham ya ɗauka Majeederh zata daka babu zato balle tsammani yaji saukar hannunta a mararsa ta damƙa tare da murɗewa ya fisga, wani masifaffan zafi ya ratsa kwanyar kansa numfashinsa ya tsaya cak domin inda ransa yake ta taɓa, a hargitse Majeederh ta ce "No!!!!!! Zaki nasaka shi" Debaka ta ƙara murɗewa da ƙarfi ta ce "Sai ayi auren muga" Baya Abraham ya yi Majeederh ta tare shi suka zube a ƙasa ya faɗa kanta babu numfashi........
Har yanzu a labari muke,sai mun koma asalin labari za kuga muhimmancin baku wannan labarin..... The story is going to be different In sha Allah🫰🏽💔 muna zuwa page 50 zamu gama labari a nan book 1 ya ƙare.*_Sai Mace ta turo wata yaƙunanniyyar ƴar dubu ɗayanta tana son MIJIN MALAMA, kuma sai ta dinga sharing gari gari har Aljanu duk su karanta akan guntuwar 1k? To Sannunku ku ta nadi kuɗinku idan mun dawo labari a book2 zan muku Discount kowa ya karanta Allah ne ya taɓa zuciyata wlh........ MIJIN MALAMA 08119237616_*
Wani irin jijjiga shi ta shiga yi bayan ta mirgina ta zame jikinta sai kanshi dake saman cinyarta. "Khalil? Ibrahim buɗe idanunka" Duk ta rikice ganin yadda ya sanƙame baya ko numfashi. Debeka dake tsaye jikinta ya ɗauki rawa, Allah yana gani bata yi don ta kashe shi ba, he so much loves him,She loves him very much, his jealousy makes her feel that she will never let him be with another woman other than her. Tsananin kishi ya rufe mata idanu ya sa ta kasa controlling kanta. Gang team ɗin kallon Debeka suke sun san ko da wasa suka taɓa ta sun shiga uku. Majeederh gently ta zame kan Abraham dake cinyarta tana zuwa bata tsaya jiran komai ba ta ɗauke Debaka da wani mahaukacin mari, sai da ta jera mata maruka guda biyar cif wanda suka nemi zautar mata da tunani. Tana pointing ɗinta da hannu ta ce.
"Baki da tarbiyyar da zaki iya haɗa inuwa da Khalil, mara tsafta irinki sam bata dace da shi ba" Debeka da kumatunta ya kumbura ta ce "Who are you? Waye ubanki a duniya bakiɗaya, da har kika mareni kike tunanin kin mari banza?" Ta cikin liƙab Majeederh ta watsa mata harara cike da tsana wacce bata taɓa yiwa kowa ba ta ce "Me? Forget about my father, ki tambayi wacece ni kaina, I Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Idan kin sani better, idan baki sani ba You can search on Google zasu gaya miki" Debeka ta girgiza kai sosai ta ce "Ok shi ne sbd abin kunya wata tsohuwa dake sbd kin rasa mijin aure kika liƙewa masa ko? Kinga sabon jini, daman ke ce wacce kika shiga tsakani kike masa yawo da zuciya har ya kasa accepting nawa matsayin budurwa balle ya kwanta dani? Kin fa haifeshi haba Mama" Sosai Majeederh ta ji zafin maganar jin ta kirata da tsohuwo hala bata san matsayinta a wajan Abraham ba. Ta juya ta kalli Abraham dake kwance su Taj na shafa masa ruwa ya riƙe mararsa gam zufa na yanko masa, ta dawo da ganinta kan Debeka ta ce "Me kika ce? To ina nan ina addu'a da izinin Ubangiji babu wata ƴar iska data isa ta ja hankalin Khalil sai matarsa da sunna wacce addini ya bashi ita duk wuya duk tsanani, ba zai taɓa aikata zina ba, naga kamar baki da cikakken hankali idan baki sanni ba su abokan nasa sun sanni, na raineshi da hannu na yi masa wanka da hannuna, na goyasa a bayan nan nawa, ya yi bacci a jikina akan ƙirjina tun yana 3yrs a duniya, Abraham is my son, ni nake da ikon zaɓa masa matar data dace da rayuwarsa wacce zata taimake shi ya ɗora shi akan tubalin zuwa aljanna, wacce zata ribaci ra'ayinsa ga taimakon al'umma, wacce zata dawo da shi akan hanya, mace mai tsafta da hankali nutsuwa kamala, mai addinin ba wacce ke bin gidan maza ba" She slowly heard him say "The woman you are praying for me to marry is none other than you" Debeka ta saki dariya ta ce "Kenan kanki kikewa fatauci ko? Sannu uwar guzuma kune hajiyoyin dake lalata ƙana nan yara kenan no wonder"
Abraham na jin su, maganganun Debeka kamar saukar mashi haka yake ji, amma ya yi shiru yana son Majeederh bakinta ya buɗe ta fara kwatarwa kanta ƴanci ba sai an shigar mata faɗa ba. Hakan ya sanya ya yi shiru yana mayar da numfashi yana jin yadda lokaci guda jikinsa ya ɗaukeki zafi sosai, mararsa sai harba masa take tana wani irin yi masa masifaffen ciwo. Ganin Majeederh taƙi cewa komai ya sanya Debeka cewa "Na miki al'ƙawarin zan tafi, ban miki al'ƙawarin zan bar miki shi na har abada ba, domin don ni akai Abraham, mahaifinsa ma ya san da zamana, ke uwar riƙo ci ki zauna a matsayinki na hakan, don't interfere this is family issues, wlh wlh wlh ko wa kika aura masa, ko ke ya aura ku shirya zaman mace biyu a cikin gidan, ba lallai ki yarda ba, amma zaki tabbatar da hakan lokacin da na shigo cikin gidan Abraham Denial David matsayin mata, no one's can stopping me even him" Tana faɗin hakan ta juya ta ɗauki wayarta ko kayanta bata ɗauka ba ta fice daga cikin gidan.
Takaici ya sanya Majeederh juyawa itama zata bar gidan. A shagwaɓe ya ce "Kin kureta kuma zaki tafi?" Ta juya suka haɗa idanu ya narkar da nashi idanun cikin nata, da sauri ta janye nata sbd abubuwan da take gani cikin ƙwayar idanun nashi ya dafe mararsa ya ce "Mami come and see zafi sosai" Bata saurare shi ba, domin gabaɗaya a dame take jin kanta, ganin zata fita ya sa ya daddafa ya miƙe tsaye yana dafe da mararsa "Taj Close the door" Cikin sauri ya sakawa ƙofar password. A hankali ya juya ya kalle su, ɗaya bayan ɗaya suka miƙe tare da barin parlourn zuwa can garden suka fara hausan dambe a tsakaninsu.
Tun kafin ya ƙarasu inda take ta haɗe fuska sosai, bai damu ba walking slowly yana marairaice fuska cikin salo na jan hankalin wanda ya sanya Majeederh ɗauke Idanunta sbd tsigar jikinta dake tashi tana zubewa, Abraham ya ƙarasa yana sauke numfashi can ƙasa ya ce "Ta nakasa miki ni" Ta yi masa banza ya ƙara narke fuska ya matsa tayi saurin ja baya, yana binta tana yin baya har ta ƙarasa jikin ƙofa, ya saka hannu ɗaya ya dafe jikin ƙofar ya yi mata rumfa da ƙirjinsa da sauri ta runtse Idanunta ta ce "Leave" Ta faɗa muryarta na rawa, sbd gani tayi gabaɗaya ya sauya mata kamar wani babban mutum ya haɗe fuska kamar bashi ne mai yawan ce mata “Sorry Mami ba” Wani irin kallo yake mata magana yake son yi amma bai ma san me zai ce ba, sbd abin baya kansa kuma bai saba ba. Hana ya miƙa zai riƙe nata tayi saurin make hannunsa ta ce "As frm today kada ka sake riƙe mini hannu,ko gigin shigewa jikina" Slowly ya ja idanunsa ya lumshe yana jin wani abu na bin jikinsa musamman da tayi maganar kamar faɗa ta ƙareta a sanyaye. "Me kike tsoro? Idan na riƙe?" Ta yi masa banza tunda magana take son yi amma ta lura idanunsa yana saitin bakinta kaɗan yake jira. Ya ƙara matsawa tare da sakar mata ƙirjinsa wanda yake buɗadɗe sbd ɗaga ƙarfe, ji tayi numfashinta yana fisga da ƙyar ta ce "Ka danne mini ƙirji, ni Maminka?" Ya ware idanu sosai wanda da ƙyar yake buɗewa ya ce "Tafiya zaki?" Kamar ƙaramar yarinya ta ɗaga masa kai sbd ta gama tsorata, a karon farko cikin harshen Hausa ta ji ya ce "To ni fa?" Hausar ko daɗi a baki ba tayi masa ba, abin dry kuma idan ya yi magana. Ta haɗe fuska ta ce "Look! Wai meke damunka ne Son?" Silently ya ce
"Call my name, bana so son" Da wani Expression na tashin hankali ta ce "Ok open the door" Speaking calmly ya ce "In one condition" Kamar tayi kuka ta ce "Wai son mene haka? What exlty wrng wiz you? Ni mahaifiyarka kakewa haka? Kana neman albarka?" Wani lalataccen murmushi ya saki iya laɓɓa da sauri ya matsar da bakinsa daidai kunnenta ya ce "You're not my mother, u never be my mom, you're my life partner" Yana faɗin hakan ya zame bakinsa tare da kai hannu ya ɗage liƙab ɗin, yadda fuskarta tayi jajir ya san kuka take daga can cikin zuciya. Ya ɗaga gira yana zuba hannu a aljihu kamar wanda akaiwa dole ya ce "Uncle I told me that, ke uwar riƙo ce, ba kene kika ɗauki ciki kika haife ba, and i also agree with him, tunda muryarki idanunki attacking ɗina ina jin sha'awarki, Uncle I ya ce zan iya aurenki" Jikinta ne ya shiga rawa tana girgiza kanta ta ce "Yanzu kai auren nawa zakai?" Ya ɗan ɓata fuska yana lumshe idanunsa har ga Allah muryarta kaɗan azabtar da shi take, Abraham bai wani damu da kyau ba a rayuwarsa, babban dalilin daya hana shi kula mata sbd duk yara ne shi kuma yana mutuwar son babbar mace, maturel enough. "Har ciki zan baki ma" Sulalewa tayi zata zube a ƙasa don tashin hankali ya yi saurin taro ta, tare da kwantar da kanta a chest ɗinsa a hankali ya yake bubbuga bayanta, wani irin kuka ne ya kwancewa Majeederh tana jin kamar ranta zai fita, me ya sa Uncle Isma'il zai mata haka? Sbd kawai ba tayi aure ba zai lalata tsakaninta da Abraham ya sanya masa ra'ayin da bashi da shi a zuciya? Ya ja mata raini? Duk yadda take da dauriya da riƙe kanta tana mamakin yadda take da saurin kuka a gaban Abraham, he couldn't feel yadda tears ɗinta suke rige rigen sauka a ƙirjinsa, bai hanata kukan ba sai ma access ɗin daya bata ya kwantar da ita jikinsa ya riƙe gam ganin har wani jijjiga da take, kuka ne wanda yake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta wanda ta tara shi shekara da shekaru yake cinta a rai. Idan ta buɗe baki da nufin yin magana sai ta ji wani kukan ya sake taso mata, Abraham idanunsa sukai jajur daman yasan zai sha fama da Maminsa ya riga ya fahimci rauninta tuni, duk wanda ya fahimci rauninka kuma ya gama da kai. Ganin kukan ba mai ƙarewa bane ya sa ya ɗan kwantar da kansa a wuyanta a hankali maganarsa ke fitowa kamar raɗa ya ce "Crying Mama, Crying jee cry as so much as you can!" Kamar wacce ya ƙarawa volume haka ta ƙara narkewa jikinsa tana wani irin kuka mai cin rai. A hankali ya fara rarrashinta duk da bai iya ba cikin kunnenta yake hura mata iska silently with sexy voice yake cewa "Shiii, sorry" Jin tsigar jikinta na tashi ya sanya tayi saurin haɗiye kukan sai hawaye, a hankali ta kalli Abraham kamar yadda yake kallonta ta ce "Enough is enough ka bar maganar iya nan" A hankali ya ce "Ohk, until we get Marriage" Idanunta na wani wajan ta ce "Tsaurin idanunka ya yi yawa, sbd ƙaddara ta faɗa mini har na kawo yanzu ba aure shi ne kake tunanin zan aureka? Kalleka U just 16 yrs, gwanini da kai kake cewa zaka aureni? Kai tsakani da Allah baka ji kunya?" Ta gyara tsaiwa ta ce "I understood, baka son ganina babu aure ne? To i promise you zan fito da mijin aure ka ji Yarona, kabar maganar u still be my son my baby" Abraham she dry ba ta bashi magana take amma bakinta rawa yake inda take kalla kuma da ban. A hankali ya taka har inda take tsaye ya ɗan leƙa fuskarta tayi saurin rufe Idanu ya taɓe baki numfashinsu na haɗiye can ƙasa daga shi sai ita ya ce "I want you Jee, i want to you to be in my side, Ina son ka ƴar madara" Ta watsa masa harara ta ce "Har abada, ƙuruciya ke damunka" Hannu ya miƙa zai riƙeta ta yi saurin yin baya ta ce "Is prohibited in my religion" baya ya ja kaɗan yana ɗaga mata hannu a taushashe ya ce "Ohk, Your religion is difficult" Ya ɗan shafa kansa yana maida hannunsa baya a shagwaɓe ya ce "Marry me, I'll give u all the happiness in our life" Majeederh ta yi shiru, wannan kamar wani opportunity ne na gyara Abraham zuwa yadda take so, zata gyara masa rayuwarsa da tarbiyya da komai. Murmushi ta yi ta ce "Khalil" Calmly ya ce "Maa" Kujera ta nuna masa, ya miƙa hannu zai riƙe ta ta ƙara janye wa ta haɗe fuska. Zama ta yi saman kujera, shi kuma ya nufi wajan fridge ya buɗe ya ɗauki Favorite juice ɗinsa da apples guda biyu, gently ya juya ya ce "Maa i need food"
Ta yi masa shiru har ya gama kwasu komai, ya dawo ya zauna ya ɓalle murfin lemon idanunsa lumshe yake ɗan sha yana ya mutsa fuska he lost his appetite. "Who are you, Ibrahim?" Sosai ya jita ya basar ya ce "Yunwa ina ji" Ta ce "Ibrahim-Khalil" Ya zuba mata idanu sosai ta ce "Who are you? Where are you coming from? Me kke ɓoyewa?" Shortly ya ce "hiding?" Ya girgiza kai ya ce "Jesus" Ta numfasa cikin dabara ta ce "Ka taɓa ganin ayi aure ba a san mutum ba? Iyaye family e.t.c?" A hankali ya ce "Me kike son sani a kaina?" Ta ce "Ur Father, country da sunan mahaifiya" Murmushi kawai taga ya yi, tare da yin baya ya kwantar da kansa yana rufe idanun, bottle ɗin hannunsa ya matse nan take ta fashe juice ɗin ya zube hannunsa ya fara zubar da jini. "Khalil" ya yi mata shiru tana danne tsoranta ta ce "Abraham" Idanunsa ya buɗe tare da zuba mata su, wani irin ja taga yayi wanda bata taɓa ganinsa ba, a nan kuma ta ƙara tabbar da zuciyarsa rauninsa kuma iyayensa. Murmushi taga ya sake yi wanda ya fito da kyansa duk da baya yanayi na jin daɗi cikin sauyin murya ta ji ya ce "Mother? Uhm" A hankali ya sunkuyar da kansa ya ce "I don't know her, ban santa ba, she's alive or not I don't know" Kallonsa kawai take a hankali ya sake cewa "Idan an ce uwa ke nake kallo, kece mace ta farko data kula dani ta nuna mini soyayya ta uwa, wacce na rayuwa da wannan soyayyar har yanzu, Bayanke maza ne kawai suke tare dani Gang team ɗin nan su ne ahhalina, ina da 10yrs na gama secondary school na fara University a wata ƙasa" Ya yi shiru ta ce "Wacce ƙasa?" Calmly ya ce "Germany" Ta ce "Ohk ina jinka" Ya ƙara lumshe idanunsa wanda duk suka rine ya ce "Daga nan na sauya University, har dai na kammala" Ta jinjina kai ta ce "Ur Father?? Mahaifinka fa?" Ya ce "I hate him" Da mamaki ta ce "Why? Me ya sa me ya yi maka?" Murmushi kawai ya yi yaƙi ce mata komai. Ta ce "Ok Shi ne ya biya maka kuɗin makaranta?" A nan ya yi wata kalar dry sosai yana girgiza ya ce "Funny, ina yaga kuɗin kai ni Germany? Kuma Karatun Likitanci, Welder fa yake" shi kansa ya san ya yaudari kansa sai ya ji kansa ya masa girma na ƙaryar da ya yi. Majeederh ta ce "Kuma ina kai kke samun kuɗi? Me haɗinka da Gang team ɗin nan?" Ƙuri ya yi mata da idanu ta ji ya saki dry ya ce "you're asking too much, are you trying to change me? use your chance on me" Ya ƙara yin murmushi kawai idanunsa jajur jijiyoyin kansa duk sun fito kallo zakai masa kasan ba daɗin hirar yake ji ba, ya watsa hannunsa tare da cusa yatsunsa cikin suma ya birkitata ya zuba idanu ya ce "You can because I love you, kawai dai Gang team is my happiness in bani da lafiya sune, suke iya ɗaukan haukana" Idanunta ta ji ya ciko da hawaye sbd tausayinsa ya yi kamar bai gani ba ya ce "Me kike so?" Ta ce "Bana son Debeka" Da wani irin sauri ya ɗago ya kalleta bai ce komai ba, ta ce "Bana son Shaye-shaye, yawon banza, kula matan banza, bana son faɗa da kowa ka koyi controlling kanka, kana zuwa wajan mahaifinka bana son gajeren wando ka maida hankali akan sana'arka, idan ba wani doke ba bana son shiga cikin Gang team ɗin nan" Tunda ta fara magana yake kallon bakinta da idanunta ta ce "Kana jina?" Calmly ya ce "Ohk" A wannan karan da ƙyar muryarsa take fita ta miƙe tsaye zata ta fi ya bita da idanu ya saka remote ya cire password sai da ta je bakin ƙofa ta ji ya ce "Zan aureki dole, Abraham baya ƙarya" Da sauri ta fice daga cikin gidan tana sauke numfashi. Akan idanun Bar Aliyu ta fito da sauri ta shiga motarta tare da yin key, dake ya sauya mota bata sani ba, kuma bata hayyacinta hakan yasa sam bata gansa ba. Kifa kansa ya yi a kan hannun motar yana jin zuciyarsa kamar ta fito gabaɗaya ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, he want Majeederh in his whole life, amma tsoranta yake sauya masa take a ko wanne lokaci, duk sanda ya yi attempting faɗa mata he loves her sai yaga kamar ba ita ba, nan da nan ransa ya ɓaci. He couldn't sleep, eat, everything komai nasa ya tsaya ya yi asarar contract da yawan gaske. Failing a Shari'a ba a magana. A hankali ya kunna motarshi kai tsaye gidansu ya nufa, lokacin Hajia da Almustapha na zauna a parlour. Tunda ya shigo Hajia ke Kallonsa har ya nemi waje ya zauna yana mai da numfashi ta kasa daurewa ta ce "Aliyu lafiya?" Ba tare daya buɗe ido ba ya ce "Good, ina yini Hajia?" Ta yi shiru ta kasa amsawa. Wayarta ta ɗauka ta kira Dije ta ce "Ki haɗawa Babana abinci yanzu" Dije ta ce "Done Hajia" Ta ɗauke kallonta ga Aliyu ta ce "Almustapha ya matar taka?" Ya ce "Da tare zamu zo ma, bata jin daɗi ne" Ta ce "Ohk, Allah ya sauwaƙe" Ya ɗan juya ya ce "Papa fa?" A nutse ta ce "Ya je meeting, kasan an fara shirye-shiryen tsayar da ɗan takara" El ya ce "Kai, Shi Papa mene haɗin sa da wani takara ne, ban son ya tsaya wata siyasa wlh" Ta yi Murmushi kawai El ya ƙara cewa "Ohk i understand, jam'iyyar su ai ke kan mulki a yanzu, baya so mulki ya fita daga hannunsu" Almustapha ya yi dry ya ce "Kuma wallahi na ji jam'iyyar hamayya da ƙarfinta ta fito, suna da ƴan takarkaru har biyu dole sai sun yi primary election zaɓen cikin gida kafin fitar da gwani, amma da ina zaɓe Abuturab zan zaɓa, he's a kind of person that i have never seen before, a dai ƴan siyar nan tamu, ya taɓa neman takarar ko house of representatives or assembly na manta, yanzu na kamar ya yi aure wai, amma baya ƙasar jinya yake" Aliyu zancen ya ji yana hawa kansa haka kurum kuma Abuturab ɗin bai masa ba. Hajia ta ce "To Aku, duk ina kake jin wannan labaran?" Almustapha ya ce "Hajia media, a twitter a nan nake ganin latest news na ƴan takarkaru, musamman wanda suka ke viral suna trending in the world" Almustapha ya ce "Kuma ƙyakƙyawa da shi so Masha Allah" Sai a lokacin Aliyu ya buɗe ido tare da kallon Almustapha ya ce "To kai mace ne? Da zaka na description kyan ɗan uwanka namiji?" El ya ce "Kai ban taɓa cewa kana da kyau bane? Idan kaga abu mai kyau ka yaba shi ne kawai, day before yesterday na je gidanka ai" A tsorace Aliyu ya ce "But baka faɗa mini ba?" Almustapha ya dinga kallon Aliyu, shi kuma Aliyu tsoro da kunya ya kama shi "Na je, matarka ta iya girki sosai fa, na ganta tare da wata kamar munafuka mai liƙab" Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke, Majeederh ce ta yi girkin. Suna zaune Dija ta kawo Hajia ta saka Aliyu a gaba sai gashi ya tashi da abincin cikin babban plate Kallonsa kawai take tayi tambayar duniya ya ce "lafiya".... Abuturab na zaune feeling better gabaɗaya kwanan shi biyu da dawowa ƙasar daga Switzerland. Idanunsa ya buɗe da ƙyar jin Maysoon na cewa "Ka fita duba lafiyarka, ka dawo and you're still sick wai meke damunka ne Yallaɓai? Ina ta ƙoƙarin ganin na kyautata zamana da kai but i couldn't, ka hana ni duk wata dama da zan kafa soyayyata a zuciyarka" Hawaye na zubu mata hannunta dafe da cikinta wata tara ta ce "Nasan baka so na, amma ni ina son ka, bani da tabbacin zan haife cikin nan lafiya, inma mu mutu tare inma na mutu na barsa ko ya mutu ya barni, don Allah ka nuna mini soyayya a kwanakin nan kafin cikar EDD ɗina na roƙeƙa Haydar" Kuka Maysoon ta saki sosai tana dafe cikinta, Abuturab ya zuba mata Idanu a hankali ya miƙa mata hannu ya ce "Come" Ta ƙarasa ya zaunar da ita saman cinyarsa idanunsa akanta ya riƙo fuskarta ya ce "Maysoon" Tana kuka ta ce "Sir" Ya ce "Ina da ƙulafuci ina da naci, zuciyata nada kafiya akan abinda take so,ki yi mini uzuri ki amsheni a yadda nake, first love ɗina tana wani wajen ke kuma Allah ya ƙaddara zan zauna dake matsayin mata, ina baki ci sha, suttura ina saka miki kuɗi a bank duk wata, Maysoon ina jin zafi a zuciyata ina jin raɗaɗi ki taimaka mini na samu abinda nake so ta hanyar addu'a, yadda nake son ta ko mulkin nan dake tunkaro ni bana so haka, mene matsalarki?" Kuka take sosai ta ce "Are you going to insulate me? Kana faɗa mini ƙarara baka so na, dole akai maka, me ya sa ba zaka duba irin son da nake maka ba Yallaɓai? Ni bani da matsala kaso ko wacce kawai kulawarka nake nema lokacin ka nake buƙata, hatta wannan cikin na jikina Ubangiji ne kawai ya ƙaddara samuwar shi, yaushe rabon daka raɓeni?" A hankali ya ce "Sorry Maysoon" Kuka take ta ce "Please ko sau ɗaya ne" Ya ce "Am not in the mood, ki je" Za ta yi magana ya daka mata tsawa tare da hankaɗeta ta faɗi ƙasa saman ƙaton cikinta, wata ƙara ta saki tana runtse Idanunta Abuturab ko ta kanta bai bi ma ya nufi part ɗinsa, ƙarar data kuma yi ya ya jawo hankalin Mama da mai aikinta suka shigo parlourn a guje jinin dake malala a ƙasan Maysoon ya sanya Mama rikice Maysoon tuni ta fara kokawa da ranta, Mama ta fara kuka sbd tausayi cikin ikon Allah kuma suka fara jin kukan jariri da sauri Mama ta ɗaga Maysoon ta matsar da babyn Salati Maysoon take tana kiran sunan Abuturab tare da yin wata jijjiga idanunta na rufewa, Abuturab Mama ta shiga ƙwalawa kira yana ji ya yi shiru ganin numfashin Maysoon na tafiya baya dawowa yasa Mama fara kalmar shahada,idan ta kira sunan Maysoon sai ta faɗi kalmar shahada cak numfashinta ya tsaya jikinta ya saki idanunta ya yi sama rai ya yi halinsa Maysoon died.
Ban yi Edited ba.. bear with meDa hannun bibbiyu Abuturab ya riƙe kansa yana kallon ƙyakƙyawar jaririyar da matarsa ta mutu ta bari. Mama dake Kallonsa tayi jigum ta ce "Ka yi haƙuri, ko wanne mai rai mamaci ne, damuwata har yanzu ban san mene ya samu Maysoon har ya yi sanadin Ajalinta ba" Abuturab ya yi shiru yana jin wani iri a ransa. Kallonsa kawai Mama take kafin ta ce "Na yarda da kai na aura maka ƴar mutane ta zauna dakai a yadda ta sameka, Ali wallahi muddin ka saɓawa yardar da na yi maka Ubangiji ba zai barka ba, zaka samu jarrabawa ta yadda baka yi tsammani ba, gwara tun wuri idan akwai wani abu ka faɗa mini" A hankali Abuturab ya ce "Are you accusing me, Mom?" Ta girgiza kai ta ce "Ba zarginka nake ba, kawai dai tunatarwa na yi maka" Ya jinjina kai ta ce "A sakawa jaririyar sunan uwarta Maysoon" Da sauri ya ce "No Mama" Ta ce "Why? I don't think it's a crime to inherit her mother's name, no matter what, we'll always remember her" Cikin rauni da siga ta tausayi ya ce "Mama zan dinga jin kamar zata dawo gareni ne, ni kaɗai na san abinda ke damuna, ko a saka sunanta ko ba a saka ba, she's always be on my mind, she's a kind and nice person da ban taɓa ganin irinta ba, so Please Mama ki yi haƙuri kada a saka sunan Please" Mama ta tsora masa idanu kafin ta ce "To wanne sunan kake so?" A hankali ya ce "Hawwa'u, we can call her Jidderh" Mama ta ce "Hawwa'u?" Ta tambaya da mmki ganin ka kaf Familynta babu mai irin sunan ya yi shiru. Ta ce "Ubangiji ya rataya, ya bata haƙuri irin na mahaifiyarta" Miƙewa ya yi zuwa part ɗinsa sbd jin muryar ƴan gaisuwa duk da ya hana zaman makoki for no reason. Kwanciya ya yi yana lumshe idanunsa tun auren su da Maysoon bai samu nutsuwa ba, gani yake kamar ya ci amanar wacce zuciyarsa take so da ƙauna da muradin kasancewa da ita, yanzu kuma wani irin sauƙi yake ji da nutsuwa ko babu komai she's pass away frm his life,She was out of his life, He will live without constraints, he will live from him only what his heart wants. Ajjiye babyn ya yi yana jin son yarinyar har ransa musamman idan ya tuna sunan data mallaka. Wayarsa ce ta fara ringing a hankali ya duba ganin mai kiran ya sanya ɗauka. A nutse ya ce "Barka" Daga cikin wayar aka ce "Ka duba news kaga meke faruwa?" Ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce "Bana ce ba, kasan am not in the mood" Mutumin ya ce "Motar ƴan boarding school dake tafiya zuwa wani abu na makaranta aka cinnawa wuta, ɗalibai sama da 500 sun ƙune ƙurmus ga kabari mutane wajan goma da aka tune aka kwashe gawarwakin an rasa waye, Hon ina jin tsoro baka tunanin jam'iyyar hamayya ta aikata wannan abun sbd kawai taci mulki? Ko wani asiri suke ki tsubbu?" Miƙewa Abuturab ya yi zufa na yanko masa ya ce "Yanzu Sir al'amarin har ya kai sbd son mulki a sanwaltar da rayukan al'umma wanda basu ji ba basu gani ba? Me ake son zama ne?" Mutumin ya ce "Calm down Hon, ina tunanin we can do something about that" Ya ce "Kamar m" Ta cikin wayar aka ce "Mu je makarantar mu jajanta lamarin mu bawa iyayen ko wanne yaro haƙuri da kuma ɗan wani abu, tare da al'ƙawarin yin bincike idan jam'iyyarmu ta samu mulki" Tattaunawa sukai kana suka sauka akan layi.
After 1weeks
Majeederh na zaune tana duba wasu files da aka turo mata na Human rights akan wani cases da ake son ta taimaka kamar daga sama taga Abbu ya shigo cikin sauri ta ɗago kanta ta dube shi jikinta duk rawa yake ta kasa cewa komai Abbu ya ce "Hawwa'u me ya kai ki Bristol Palace Hotel?" Wani irin bugawa ƙirjinta ya yi ta ce "Hotel Abbu?" Hannu ya ɗaga ya zabga mata mari ya ce "Are answering my questions with a question? How dare you?" Yatsunsa ya fito sosai akan fuskarta sosai idanunta ya shiga fitar da hawaye ta ce "Abbu ban taɓa zuwa Hotel ba, don Allah..." Wani marin ya kuma sauke mata idanunsa sukai jajur kamar zasu fito waje yama kasa magana sai pointing ɗinta da hannu da yake "Ban haifi yarinyar da zata ɓata mini sunan family da nawa ba, kin yi kadan zaki san cewa ni na haifeki ba kece kika haifan ba wallahi lokaci kawai nake jira" Kuka take sosai kamar ranta zai fita ta ce "Why should i do that Abbu? Wallahi ban taɓa zuwa Hotel ba mene ribata bayan nasan illar hakan don Allah Abbu...," Hannu ya ɗaga ya ƙara sauke mata wani marin kafin ya ce "Idan ba ki ki Hotel ba to wace wannan? 1week ago wacce ta je gidan ƙartin maza? Past week's waye ya dinga hauro mini gida yana shiga ɗakin ki? Ko shi ma bake bace baki san anyi ba? Shekaran jiya kin ce mini zaki wani meeting a Abuja daga nan mene ya kai ki Lagos?" Wani irin kuka take sosai bakinta na rawa ta ce "Abbu zan maka bayani wlh ba abinda kake tunani bane" Jin hayaniya ya saka Mami fitowa Main parlour, Raihana ta fito itama da sauri Mami ta ce "Meke faruwa ne?" Da hannu Abbu ya ce
"Hawwa'u zata saka mini ciwon zuciya, tana sane ta ƙi yin aure take yawo tarbiyyar dana baki kenan? Na yarda dake na amince miki shi ne zaki aikata mini haka? Kin san bana iya bacci sbd damuwarki, burina kawai na ganki a ɗakin mijinki kamar sauran ƴan uwanki amma abin ya ci tura, ashe haka zurfin ilimi ke jawowa?" Mami ta ce "Take ur heart please Alhji baka da lafiya ka dinga bin komai a sannu Please, kada ka yanke hukunci ba tare da bincike ba" Abbu ya ce "Wanne irin bincike bayan wanda na yi? Komai nake idanuna yana kan Majeederh bani da cikakkiyar nutsuwa private Investigators nawa na saka akanta?" Da wani irin tashin hankali Majeederh ta ce "Zargina kake Abbu? Innalillahi wa'inna ilahir raji'un na shiga uku, wallahi Abbu ban taɓa aikata sabon Ubangiji ba, ba zan taɓa cutar da tarbiyyarka ba da nayi haka gwara mutuwata, taimakon al'umma musulmi kawai nake" Wata zabgegiyar bulala ya ɗakko ya nufi Majeederh zai daka da sauri Mami ta shiga tsakani idanunta na zubar da hawaye ta ce "Haba Alhaji idan rai ya ɓaci nutsuwa ake samu, hankali ke nemo shi, idan ka yarda da Majeederh tun farko bai kamata ka zargeta ba yanzu, zargi haramun ne a musulunce wlh" Yana huci sosai ya ce "Leave, Asabe ki matsa daga nan ko na haɗa dake" Mami na kuka sosai ta ce "Wlh sai dai ka dake mu tare, na fara gajiya wanne irin mutum ne wai kai? So kake a zageni ace sbd bani na haifeta ba? Ka sassautawa zuciyarka, kabi komai a sannu faɗa baya magani idan ba kangarar da yaro ba, ko ƙaddara ce fa ta faɗa mata dole ka zauna da ita ƴarka ce jininka ce hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar" A wannan karan hatta Raihana sai da ta ji tausayin Majeederh, babbar mace mai shekaru ilimin addini dana boko kuɗi hankali nutsuwa amma ita ake doka kamar Ƴar shekara biyar. Zubewa Abbu ya yi dafe da kansa dake juya masa yana jin kamar zuciyarsa zata fashe, shigowar Abraham cikin main parlour ya sanya Abbu miƙewa da sauri ya ce "Ban hanaka shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara tsafta me yawo da datti ya dinga shigo mini cikin gida ba? Ban hana mara gata da ƴanci wanda bashi da mara da almajirin kan titi shigo mini gida ba?" Abraham kallon Majeederh dake durƙoshe yake wacce gefen bakinta ya fashe, ta kasa ɗago kanta ta kalli Abraham sbd gujewa ganinsa da take rabon data ganshi ma ta mance ta rufe duk wata hanya da zata haɗata da shi ba da son ranta ba. Abbu ya ce "Da kai nake magana?" Abraham ya zame idanunsa ya kalli Abbu, sauyin idanun Abraham ya kaɗa hantar cikin Mami. "What brought you into my house?" Gently Abraham ya taka har gaban Abbu ido cikin ido ya ce "Ƴar ka nake so" Hatta Mami ta jijjiga da wannan maganar ta Abraham, Abbu kuma ji ya yi zuciyarsa ta tsaya na wani lokaci cikin rashin fahimta ya ce "Me ka ce?" A takaice Abraham ya ce "Zan auri Mamina" Abbu ya ce "A sbd kai Mahaukaci ne?" Shortly ya ce "Akan ta, ni Mahaukaci ne Grandpa ya turo ni wajanka just to ask ur permission na aurenta" Abbu ya juya ya kalli Majeederh wacce kanta ke sunkuye sai numfashi take da ƙyar ya dawo kan Abraham ya ce "Ka zo gidana, a gabana ka kalli cikin Idanuna ka ce kazo auren ƴata?" Abraham ya ɗan watsa kafaɗa tare da fito da Teller ya ce "Daga 1m zuwa ko nawa ka faɗi kuɗin da kke buƙata yanzu ka bani ita mu tafi" Mami ta ce "Son ta kake?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "I don't know, kawai ina son auren ta" Abbu ya ce "Mara addini kamar ka shine zan bawa auren ƴarta? Wanda bashi da gata, Ahhali mai yawo da ƴan iska suke fashi da bindigogi zan bawa auren ƴata? Mai Shaye-shaye da yawo da mata wanda yake gidan kansa maimakon na iyayensa shi zan bawa auren ƴata?" Abraham kallo Abbu kawai yake ba tare daya damu ba ya ce "Yanzu ma kuɗin auren nata ai fashin su na yi" Majeederh dai ta kasa motsi zaka iya ɗauka bata cikin hayyacinta ne Abbu ya ce "Ban yi mamakin hakan ba, bari na faɗa maka abinda baka sani ba, wallahi tallahi dana aura maka ƴata gwara naga gawarta, dana aura maka ƴata gwara ni na mutu, dana aura maka ƴata gwara duk me zai sameta ya sameta, dana aura maka ƴata gwara naga ta zube mini shego gwara ko wacce ƙaddara ta faɗa mata" Da wani irin tashin hankali Majeederh ke kallon Abbu sbd jin furucinsa wanda ya gigita ta ya sauya mata lissafi tunaninta ya tsaya, kalmar shego ta nemi tarwatsa mata zuciya da sanya wa ta jita kamar matacciyya. Mami ta ce "Alhaji kasan me kake cewa kowa? Kada ka jawa Majeederh masifa da bakinka" Abbu ya ɗagawa Mami hannu ya ce "Ki daina saka mini baki cikin maganata Asabe" Mami ta zaune tana rushewa da kuka. Abraham jijiyoyin kansa suka fito tare da yin raɗa raɗa saman goshinsa silently ya ce "Ohk, ka shirya ganin babies" Yana faɗin hakan ya juya tare da ficewa daga cikin gidan a hanya suka haɗu da Latifa dake shigowa Murmushi tayi masa ta ce "Our son kana ta girma abinka wajan Mamin taka ka je?" Ko inuwarta bai kalla ba balle ya bata amsa shi duk duniya da Majeederh kawai yake duguwar magana. Yana zuwa mota Taj ya buɗe masa ya shiga gidan baya, Salamon na gaba shi kuma Taj ya nufi mazaunin driver bayan sun fice daga cikin gidan Taj ya ce "Bad boy ya amince?" Abraham ya yi shiru Salamon dake danna waya ya ce "What did i miss?" Taj ya ce "Bad boy ya je neman auren Mami" Da wani irin sauri Salamon ya juya ya kalli Abraham dake bayan mota idanunsa rufe ya dunƙule hannayensa ya birkita sumar kansa ya dawo da ganinsa kan Taj ya ce "Shawarar wace wannan?"Taj ya ce "I, to me zai zauna jira kawai ya aureta" Salamon da wani irin yanayi yake kallon Taj kafin ya ce "Wai mene ruwanka da rayuwar Abraham ne? Me yasa kake sawa ya aikata abinda bashi kenan ba? Daman haka ake neman aure a musulunci? Kawai ya tunkari mahaifin Mami ya ce he wants to marry his daughter ko me?" Taj ya ɗaga shoulder ya ce "Is just a suggestion, kawai na duba yanayinsa baya bacci cikin kwanakin nan kullum kiran sunan Mami ni kuma i can't take it anymore" Salamon ya ce "U can't take it a matsayinka na ubansa ko uwarsa ko kuma me?" Taj ya ce "A'a kada ka zageni bafa fini son Bad boy kayi ba, ina yin komai sbd farin cikinsa da kwanciyar hankalin sa ai shi ya sani idan kai baka sani ba" Tuni zuciyar Salamon ta fara kaiwa ƙarshe ya ce "Farin cikinsa ko kuma ɓata shi? Ka bashi ƙwaya ya sha ka saka masa maganin felling da burin ya yi wa Maminsa Fyaɗe Allah ya taƙaita, ka kirata har gidansa ta da burin ta ganshi kwance da Debeka, ka haɗa plan da Engagement, yanzu ka sanya ya je wajan mahaifinta wai ya bashi aurenta are you mad....," Da ƙarfi suka ji Abraham ya ce "Stop the car" Taj ya tsaya bakin titi cikin ƙara ji Abraham ya ce "Salamon get out of the car, bana son ganin fuskarka har abada" Murmushi kawai Salamon ya yi yana kallon Taj ya ce "Wannan shi ne abinda kake buƙata?" Taj bai ce komai ba, Salamon ya buɗe ƙofa ya fita tare da matsawa can gefe da gudu kuma Taj ya ja motar sai Club. Wine yake tsiyayawa Abraham yana zubawa cikinsa sai da ya sha ya yi tatul kafin Taj ya ce "Bad boy ni zan tsaya maka ko kowa zai gujeka ka mini halacci a rayuwa, Salamon son Maminka yake" Sai a lokacin Abraham ya buɗe rinannun idanunsa ya kalli Taj wani irin kallo yake masa kafin can ƙasa ya ce "I'll kill you Salamon" Taj ya ce "Ganin yana son ta shi ya sa nace bari kawai mu fara da neman auren amma tunda Abbu yaƙi kawai ka tafi gidan Uncle Isma'il yanzu kafin Abbu ya bata auren wani a daren nan" Cak yaga Abraham ya miƙe yana tangaɗi daga shi da three quarter ya zari key ya nufi hanyar fita daga cikin Clun ɗin da ƙyar, murmushi Taj ya yi ya ce "Well-done Abraham Daniel David"
Uncle Isma'il da Uncle Bello sai Abbu na zaune a compound na gidan Uncle Isma'il su kaga an buɗe gate wata dalleliyar mota ta shigo, gabaɗaya suka kalli motar banda Abbu da kansa ke ƙasa, Abraham ya buɗe murfin motar da ƙyar ya fito yana layi da tangaɗi ko idanunsa baya iya buɗewa sbd wine ɗin da Taj ya bashi mai ƙarfi ce, bibbiyu haka yake ganin su Uncle Isma'il, Uncle B ya gyara zama ya dinga bin Abraham da kallo har ya ƙarasu ya zube akan qiwwoyinsa ya lumshe idanunsa. Uncle Isma'il ya ce "Khalil lafiya?" Abraham ya yi shiru, Abbu ya miƙe zai bar wajan Uncle Bello ya ce "Ka zauna plx" Ya koma ya zauna daman alrdy ya shaida musu everything daya faru. Dafa shoulder ɗin Abraham ya yi ya ce "Khalil me kake so?" Kansa a ƙasa a hankali ya ce "Mami" girgiza kai kawai Uncle Isma'il ya yi ya ce "Mamin take kake so yanzu kuma?" A hankali ya ce "Yes, ina so Mami" Ya ce "Khalil bana jin ko ka kasance Musulmi Majeederh zata amince ka aureta, ta raineka da hannunta ta kula da kai da ace tayi aure babu mamaki ta samu ɗa kamarka, addininmu da naku ba ɗaya bane, babu yadda za a yi ka auri Majeederh, yau da ace kai Musulmi ne ita Christa to da sauƙi, amma kana Christa tana Musulma kuma Malama? Ba zai taɓa yiyuwa ba, ka yi haƙuri Ibrahim" Abraham baya fahimta bai kuma san haƙuri ba ya ce "Uncle Mami, ina son zama da ita" Ganin kamar zai basu matsala ya sanya Uncle Bello cewa "Ohk, ka turo iyayenka sai a saka muku date na bikin" Da ƙyar suka lallaɓa shi ya shiga mota yabar gidan. Uncle Bello ya kalli Abbu ya ce "Wai lamarin Majeederh ke damunka ne Alhji Abdul'aziz?" Abbu ya ce "Me ya sa ba zai daman ba?" Uncle Bello ya ce "Gaskiya bai kamata ya dameka ba, sbd komai ya faru kai ka siya da hannunka, akwai ƙaddara amma tana zuwa da sanadi, tun Majeederh na da 20yrs a duniya ta nuna aure take so, amma kayi burus ka nuna kamar baka sani ba, kamar baka san meke damun ƴarka ba, Imran ya fito aurenta ta kure shi sbd kawai cikar burinka, bata san karatu amma haka ta daure ta maida kanta kamar namiji ta tafi wata ƙasar tsayin shekaru Takwas, ta dawo ka tilasta mata fara aiki, yanzu kuma ka samu abinda kake so shi ne zaka damu sbd ba tayi aure ba? Allah zaka ma wayo ko ka nuna masa dabara kenan? Muna rayuwa da ƙaddararmu wacce Ubangiji ya tsara mana, ƙaddarar jinkirin aure ta samu Majeederh sai ka tayata amsa kayi mata addu'a, kuma ka bar ƙaddara ta yi aikinta" Abbu kallon Uncle Bello kawai yake, Uncle B ya ɗora da faɗin "Yanzu da kake zargin Majeederh a matsayinki na mahaifinta mu kuma da jama'ar gari mu ce me? Da Majeederh zata lalace to da tun a Misira hakan zai faru, ka gode Allah ka masa mubaya'a akan yadda ya tsara lamuransa, komai ya sameta a rayuwa kai ne sila, sannan daza ka yi wannan lalataccen furucin akan Abraham shi me ya yi masa zafi? Mutumin da yake da zuciya na ci, da taurin kai ka zafin rai, baka tunanin kalamanka su haifar da wani abu? Kai fa uba ne komai ka faɗa akan ƴarka Immediately Mala'iku za su amsa su rubuta, idan Allah ya ƙaddara Abraham mijinta sai kaga ya musulunta kuma ya aure ta" Abbu ya ce "Har abada ba zan taɓa bawa lalataccen yaron can auren yarinyata ba" Uncle Isma'il ya ce "Idan da rabo mai zafi sai kaga ya kashe ka, rashinka a duniya babu abinda zai hana, ka karɓi ƙaddara a yadda tazo domin allon lauhil mahfuz baya rubuta abin da ba daidai ba, komai ta faru da sanin Ubangiji, zanen ƙaddararta kenan"
After 2 yrs. Lokacin Majeederh nada 33yrs a duniya Abraham kuma 18 Abubuwan sun faru, tashin hankali fiye dana baya, Majeederh ta gujewa Abraham ya haukace baya iya ci baya iya sha duk wani abu da ta hana shi baya yi amma ya fita daga hayyacinsa, ganin hakan yasa Abbu barinta tafiya aikin Hajji bayan an kammala Azumin Ramadan. Fitowarta kenan daga bathroom ɗaure da towel duk ta rame tana daga tsaye taga kamar gilmawar shadow da sauri ta ɗauki hijabi ta saka tana juya idanunta ya sauka cikin na Abraham wanda ya sauya mata ya ƙara yin wani girma na ban mamaki kamar ana ƙara shi kyansa na baƙin ɗan America ya sake fitowa a fili. A kallo ɗaya da tayi masa ta fahimci bashi da cikakken nutsuwa walking slowly ya nufeta da sauri ta ce "Karka zo nan" Ya yi mata banza kamar ana jansa haka ya nufeta kafin ya ƙarasa ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, to addinina ba irin naku bane, ɗabi'ata tasha bambam da taku kada ka sake mafarkin taɓa jikina, ni ba Maminka bace ok fine ni ma ban haifeka ba, ba zan taɓa haifarka ba ka fice mini daga....," Caraf ta ji ya cafke lip's ɗinsa da bakinsa tare da manneta da jikin bango ya shiga....Zare idanu tayi alamar ya haka? Banda bugawa kuma babu abinda zuciyarta take. He was kissing her passionately, the kiss coming from the land of his heart with all love and affection. Takaici ya sanya Majeederh runtse Idanunta wani irin hawaye mai zafi ya shiga gangaro mata ta gefen idanunta, jikinta ya saki ta kasa koda motsa hannunta, tunda ta zo duniya bata taɓa jin wani abu mai kama da wannan ba, ji tayi jikinta ya shiga rawa da ɓari kamar ana kaɗa mata gangi, wani abu ke tsarga mata tun daga kan babban yatsar ƙafarta har tsakiyar kanta. Tsigar jikinta ya shiga tashi yana zubewa ganin yadda jikinta ya ɗauki rawa da ɓari numfashinta na neman ɗaukewa sbd kawai yana kissing ɗinta ya sanya Abraham buɗe idanunsa da sukai jajur yana jin kansa na masifaffen sara masa sbd baƙon lamarin daya ziyarce shi ba tare daya shirya zuwansa ba.
This is the first time in his life that he kissed a woman and the woman he looked upon as his mother. A hankali ya zame bakinsa ganin tayi baya zata faɗi ƙasa ya yi saurin saka hannu ya dawo da ita saman chest ɗinsa hannunsa ɗaya a waist ɗinta, idanunsa ya ware sosai cikin mutuwar jiki ya kasa cewa komai yadda take sauke numfashi haka shi ma yake ganin babu mai ƙauri a cikinsu ya sanya ya ƙara riƙeta sosai a jikinsa yana riƙe kansa da ƙoƙarin ganin ya dawo cikin nutsuwarsa. A hankali ya zame daga inda take yana matsawa ta yi baya zata kifa sbd ta gama tunanin tana jikinsa ta gama sakin jiki bakiɗaya, cikin sauri ta riƙe kanta da kyau tana jan breathing ɗinta da saukewa a hankali, har lokacin jikinta kuma bai gama daidaituwa ba rawa yake still. Idanunta ta buɗe da son nuna masa ko a jikinta ta ce "Ka fita daga cikin bedroom ɗina" Ta faɗa ba tare daya kalli direction ɗinsa ba, shi kuma ya zubawa yatsun ƙafarta idanu yana karantar yanayin da kike ciki, a hargitse ta ƙara cewa "Khalil get out of my room,i Said" gently ya ɗaga kai ya kalleta da rikitattun idanunsa wanda sukai laushi calmly ya ce "Bayan kasancewata Christa mene hujjarki?" Wani irin murmushi ta yi ta ce "Waya faɗa maka sbd kai ba musulmi bane ya sa naƙi amincewa? Da ace ina sonka da na ja ra'ayinka kan musuluncin ai" Ta gyara tsaiwa ta ce
"Ba zan taɓa son ka, ba zan taɓa son yaron cikina ba, ba zan taɓa auren under age irinka ba, kayi mini ƙanƙantar da ba zan iya cewa kai mijina bane, infact i don't love you, wani gwanini da kai a gabana" Tunda ta fara maganar yake kallonta da wani irin yanayi wanda ba zaka iya tantance shi akan fuskarsa ba, ya nufeta da niyyar riƙe hannunta ta yi saurin matsawa ta ce
"Ya zama last time da zaka ƙara gigin riƙe wani sashi na jikina, addina da naka akwai tazara mai yawan gaske" Rai ɓace kamar Mahaukaci! ya ce "Wanne irin addini ne wannan for God sake? Komai ba kyau" ta fizge hannunta, kau! Ta ɗauke shi da mari ta ce "Mahaukaci, addinina ya fi ƙarfin cin mutuncinka sai a yanka wuyan wanda duk zai aibata Musulunci" idanun Abraham sukai jawur ya ce "Shi addinin ya haramta auren macen data girmeka kenan? Shekaruna 18 mene abun yarinta a jikina? Me ya sa ki ka raina ni? Kawai saboda ni yaro ne, saboda kin girmeni da shekaru goma sha biyar?" "Kai yaro ne"
"Zan wadataki da komai JEE, don kin rai ne ni a lokacin dana rasa iyayena bashi ke nuna ba zan iya zaman aure dake ba, ina soyayyar da kika nuna mini ina yaro? Okay fine, i have a solution! Your father doesn't like me kawai muyi auren Choci ko kuma wallahi mu haifi ƴa ƴan banza kuma shegu, ko kuma na wulaƙanta addinin Musuluncin naku" Yana faɗin hakan ya fice daga cikin bedroom ɗin. Zubewa tayi saman gado tana riƙe kanta wanda yake juyawa mata, tama rasa wanne irin tunani za ta yi da matakin da zata ɗauka, Abraham na neman zame mata ƙarfe ƙafa. A hankali ta lumshe idanunta da sauri ta buɗe jin tsigar jikinta na tashi har yanzu while bakinta na mata wani iri, Abraham ya bar mata wani irin moment da memory mai wahalar mantawa a zuciya, ya yi abinda babu wani namiji daya isa ya yi shi ya kafa tarihi a rayuwar Majeederh. Shuɗaɗɗan abinda ke damunta shekara da shekaru wanda tayi maganinsa ya dawo mata sabo fil. Gabaɗaya ta hargitse tare da yin luf saman gado ta rungume pillow addu'a take Allah ya kawo mata ko tsoho ne wanda ya girmi Abbu ta aura ku ta samu sauƙin maganganun jama'a ta kaucewa rashin kunyar ɗan cikin nata.. Uncle Isma'il ne zaune a parlourn baƙinsa ya dubi Pasto David kana ganinsa kaka cikakken Christa gaba da baya. Uncle Isma'il ya yi murmushi ya ce "Sir Please ga ruwa nan" Grandpa ya yi murmushi ya ce "My pleasure sir"
Uncle Isma'il ya gyara zama cikin nutsuwa da harshen turanci ya ce "Kafin na ce komai zan su nasan waye kai, kuma na yi maka some of questions akan Abraham" Grandpa ya jinjina kai yana yaba nutsuwar Uncle Isma'il kafin ya ce "David sunana, shugaban church, business man with experience, sai wani secret aikina, kuma Abraham's Grandfather" Uncle Isma'il ya watsa hannu ya ce "That's good and i like it, amma Sir daman can Abraham Christa ne?" Kallo Uncle Isma'il kawai Grandpa ke yi kafin ya ce "Maybe, Abraham gaba da baya Christa ne kamar yadda ka ganni ɗin nan, muna ganin kima da matar tabar addininmu kamar yadda kuke ganin naku, muna ƙarfafa al'adunmu mun san muhimmancin hakan sosai, sai dai Abraham rayuwarsa ta samu bambanci da tamu kasancewar a nan Naija aka haife shi tun yana da 3yrs baya ƙaunar zama cikin gidan iyayensa, akwai wasu Neighbor ɗin su da suke Musulmi kullum yana gidan, yana da masifar wayo na ci da taurin kai, idan su kai alwala haka shi ma zai yi, ko sallah sukai haka shi ma zai. Bayan mahaifinsa ya fahimci hakan ya fara dukansa san bai gwadawa Abraham tausayi ba, ya tashi cikin mugunta yau zai dake shi ya fasa masa jiki haka zai wayi gari babu shi ya koma gidan Musulman nan, daga bisa ni ya kulle shi a wani ɗakin duhu babu abinci ya gana masa azaba sbd kawai ya daina zuwan gidan mutanen, kai har farcen ƙafa dana hannu Denial ya cire Abraham yana ɗan ƙaraminsa, shi yasa zuciyarsa ta ƙeƙa shi bashi da tsoro ko kaɗan, watarana kawai aka wayi gari babu shi neman duniya, shi kuma Denial ya yi tafiyarsa tunda daman ba a ƙasar yake ba, bai damu da ɗan ba ya ce watarana dole zai dawo gare shi idan har yana raye shi kuma daya haifi musulmi gwara ya kashe ɗan da hannunsa ya wuta" Wani irin tashin hankali ya bayyana akan fuskar Uncle Isma'il, da wani irin Expression yake bin Grandpa da kallo kafin ya ce "To mahaifiyarsa fa?" Ya ce "Ta mutu tun yana ƙarami ai, amma bai san da hakan bai kuma taɓa tambayar wani abu daya danganci mahaifiyarsa, Abraham bai taɓa zama da mace na minti ɗaya da sunan kulawa da bashi tarbiyya ba, mace ɗaya ta fara ƙoƙarin saita shi da ganin ya dawo hanya ita ce wacce yake kira da Mami, ur daughter Malamar nan" Uncle Isma'il ya ce "To ya akai ya dawo gare ku bayan ya ɓata? Tunda mun zauna da shi shekaru 2" Grandpa ya ƙara yin murmushi ya ce "His father, shi zuba private Investigators everywhere domin hankalinsa ya dawo kan shi, cikin sa a kuma aka same shi daga nan ya ɗauke shi zuwa wata ƙasar" Mamaki fal ya cika Uncle Isma'il sbd yasan cikin dare aka nemi Abraham aka rasa. "Waye mahaifin nasa? Yanzu yana ina? Me yasa kuma basa tare" Grandpa ya ce "You can ask him by yourself" Uncle Isma'il ya jinjina kansa kana ya yi murmushi ya ce "Yanzu ga abinda jikan naka yake ƙoƙarin rikituwa, kana ganin zai iya musulunta" Grandpa ya jima yana kallon Uncle Isma'il kafin ya ce "Har abada, ku gaggauta yiwa yarinyarku aure, idan kuma zaku bashi aurenta haka to, kai ko zaku bashi mahaifinsa ba zai taɓa yarda y auri musulma ba kuma ba wacce ta girme masa ai tayi tsofa da yawa gsky" Ran Uncle Isma'il ya fara ɓaci sosai kafin ya ce "Kai kake ganin tsofanta, bamu zamu gaggauta mata aure ba ku ne zaku jawa naku ɗan kunne akan ya fita harkar yarinyarmu ko kuma duk abinda ya same shi shikenan, ko hukuma ta rabamu da shi" Miƙewa Grandpa ya yi da sanda a hannu irin tsofaffin attajiran nan masu arziƙin gaske ba muna kuɗi ba ya ce "Hukuma? Waya faɗa maka Abraham na tsoran hukuma bayan shi ne hukumar kansa? Abraham babu wanda ya taɓa zama ya ce masa wannan abinda kake ba daidai bane ga wanda ya kamata ka yi, Abraham ko yini guda ya yi bai kai abinci bakinsa ba babu wanda zai ce masa ɗauki abinci kaci, irin wannan wanda bai san bambancin fari da baƙi be kake tunanin zai fahimci wani ya daina kula muku ƴa?" Grandpa ya girgiza kai kawai kafin ya ce "Sbd karamcinta ya sa nace kuyi nesa da ita daga idanunsa, Abraham ne yaro ne mai naci da taurin kai, tun yana ƙarami idan yana son abu kansa yake bugawa a ƙasa ba zau taɓa bari ba sai an bashi, Have a good day!" Yana faɗin haka ya fice daga cikin Parlourn ya nufi compound da sauri driver ya buɗe masa bayan mota ya shiga.
Anti dake shirya Lunch ta kalli Uncle Isma'il ta ce
"Ya akai kai jarumin namiji?" Ya nemi waje ya zauna tare da rufe idanu ya yi shiru. Ganin yanayinsa ya sa ta nemi ruwa mai sanyi a cup ta miƙa masa tana zama kusa da shi, bai musa ba ya amshi ruwa ya sha sosai yana sauke numfashi. Ganin bai ce komai ba itama Anti ta yi shiru da bakinta, har ya je sallar Asr ya dawo ya zauna cikin iyalansa idanunsa akan Jawaad ya kasa cewa komai, tunani fal ya sa yana sanya Jawaad matsayin Abraham taya zan iya sanwaltar da rayuwar ɗan shi ya bawa duniya ajjiyar shi? Ba dole ya kan gare ba. "Abba" Jawaad ya kira sunan Uncle Isma'il ganin kallon da yake masa kafin ya ce "Abba ruwa zan baka?" Ya girgiza kai kawai ya ce "Allah ya yi maka albarka Jawaad" Ya ce "Amin Abba" Sona ta ce
"Jawaad kaɗai Abba?" Ya haɗe rai ya ce "Sona dake da Jawaad waye babba?" A hankali ta ce "Shi ne" Ya ce "To ya zama last day da zan ji bakin ki ya ce Jawaad ki bi bakin Majaufiarki na Fulanin Gombe ki ce Hamma, ko ki ce Brother da turanci ko Yaya da Hausa" A hankali ta ce "Am sorry Abba" Ya ce "Bashi haƙuri" Ta kalli Jawaad ta ce "Am sorry Yaya" Jawaad ya yi murmushi ya ce "No bad my dear" Bayan sun kammala cin abinci Uncle Isma'il ya zayyane wa Anti yadda sukai da Grandpa. Anti ta yi shiru zuciyarta fal tausayin rayuwar Abraham ta ce "No wonder sweetheart, ka duba Abraham sosai wallahi kallo ɗaya nayi masa nasan babu kulawar uwa a tare da shi ita kuma ya yi missing, duk lalacewar yaro idan har a gaban mahaifiyarsa yake wlh zai samu nutsuwa da sauƙi wani abu, shi yasa a kullum muke addu'a Ubangiji ya bamu tsayin rai mai amfani mu rayu tare da yaranmu" Ta girgiza kai ta ce "I felt sorry for the boy, his life is full of challenges, wallahi ya bani tausayi yanzu da babarsa na duniya taya zai dinga garari? Ba sai dai su shiga duniyar tare ba?" Uncle Isma'il ya ce "Ƙaddara" Wani irin kuka Anti ta rushe da shi ta ce "Wallahi tallahi na ji gwara ɗana ya mutu ya barni da ace na mutum na barshi ban san wacce kalar rayuwa zai yi ba, ban san waye zai kula da shi ba, Innalillahi wa'inna ilahir raji'un Ubangiji kayi mana tsayin rai mu rayuwa da yaranmu cikin kulawa da amincinka ya Rahamanu ya Rahimu" Uncle Isma'il ya ce "Ke fa daman haka kike babu dama ki ji abu sai kuka haba" Ta girgiza kai kawai wani kukan na kwace mata ta ce "Yallaɓai baza ka gane ba, don Allah ka jawo Abraham jikinka plx" Ya yi shiru for good 3 minutes kafin ya ce "I'll think about that dear" Abraham na kwance saman 3 sitter a haɗaɗɗan parlourn shi kwana uku kenan cif babu inda yaje, duk ya fita daga cikin hayyacinsa. Taj ya kalle shi ya ce "Wani ya yi mini maganar zanen gida da kukai da shi, gashi har time ya shige" Abraham ya yi shiru idanunsa buɗe yana kallon sama alama ya lula duniyar tunani. Taj ya ce "Ina ta magana?" Sai a lokacin ya ce "Ka tura masa kuɗin shi ba zan ba" Taj ya ce "Nawa ne kuɗin?" Shortly ya ce "3M" Joshua ya girgiza kai ya ce "A'a ba za a mayar ba, a bashi haƙuri zuwa wani week ɗin kafin nan sai ka yi" Taj ya ce "Ya ce a mayar kuma daman shi zai aiki tunda ba zai ba bashi kenan ba?" John ya ce "Taj kada a mayar plx mu yi tunanin wani abun" Duk sukai shiru. John ya ce "Kunga news guy's?" Taj ya ce "What news? What's happening in the world?" A hankali ya ce "Wai President ɗin Germany aka kaiwa hari za a kashe shi" Da wani irin Mamaki Taj ya ce "Kashe kuma? President ɗin guda? Kuma a hospital?" Join ya ce "Daman wai jinya yake fa bashi da cikakkiyar lafiya, to a hospital ɗin akai attempting kashe shi amma ya kuɓuta, irin haka dole akwai haɗin bakin wani na kusa shi" Taj ya saci kallon Abraham da idanunsa ke lumshe yana jin duk abubuwan da suke cewa ya ce "Ayya! Shi bashi da ɗa ne wai?" A hankali Abraham ya miƙe ba tare daya kalli kowa ba ya nufi cikin part ɗinsa ya kwanta saman bed, haka kawai ya ji bashi da nutsuwa gabansa sai faɗuwa yake, ya runtse idanunsa sosai a hankali ya ce "Daddy"
Majeederh ta kalli Latifa a sanyaye ta ce "Yanzu Latifa ya zan yi? Wanne irin baƙin jini ne irin wannan? Kamar wata mujiya" Latifa ta girgiza kai ta ce "Ki daina cewa haka komai lokaci ne, ƙaddara ce kuma tana da nata lokacin" Ta goge hawayenta tare da yin shiru a hankali ta ce "Surutun jama'a ya fara damuna ana son mini sharri" Cike da tausayawa Latifa ta ce "Duk yadda kake kare kanka ba zaka taɓa hana jama'a faɗar abinda su kai niyya ba, wani ma bai san waye kai ba labari kawai zai ji yaje ya ɗorar ba zaki taɓa yiwa kowa daidai ba rayuwa kawai ki tsarkake zuciyarki" Latifa ta ce "To yanzu da Uncle ya kira Abraham gidan nan parlourn Abbu me zai masa?" Ta girgiza ta kasa cewa komai. Uncle Isma'il ya kalli Abraham ya ce "Khalil me ya kawo ka bedroom ɗin Mamin take few days ago?" A hankali ya ce "Matata dai not Mami" Uncle Isma'il ya jinjina kai ya ce "Ohk me ya kawo ka?" Ba tare da damuwar komai ba ya ce "Just to see her, sai kissing ɗinta da na yi" Uncle Isma'il ya saki baki dan ya san da gaske anyi hakan tunda har ya faɗa don baya ƙarya. Abbu ya runtse idanunsa sosai yana jin kamar zuciyarsa ta fita. Uncle Isma'il ya ce "kiss fa kace Ibrahim?" Abraham ya ɗan kalli Uncle I sai kuma ya kwaɓe fuska ya ce "A small kiss, kaɗan na yi fa" Uncle Isma'il ya ce "Tab ɗin" Uncle Bello shi abin dry ya bashi yana kallon Abraham cike da birgewa ganin baya ƙarya ko kaɗan kuma hakan alamar mutum mai nagarta ce wanda zai iya riƙe amana ta komai. Uncle Isma'il ya ce "Khalil ka san me kake cewa?" Ya ɗan watsa kafaɗa cikin turanci ya ce "Exlty, kwana biyu bata kulani Uncle I ka barni naje ko ɗan hugging nata na yi da kiss ɗin sai nayi ta ganinta a baccina" Kallonsa kawai suke, Abbu kuma ji yake kamar ya shaƙe Abraham Uncle Isma'il ya lura magana ce sosai a bakin Abraham wacce ya jima bai ba dan haka ya ce "Ya akai to yanzu?" Abraham ya gyara zama idanunsa sun yi jajur yana riƙe hannun Uncle Isma'il ya ce "Uncle I Mamina muguwa ce, bata so na ta hana ni sakat a bacci sai na dinga jin kamar gani kwance da ita" Wani irin hawaye ya zubu masa a cikin idanunsa masu zafi wanda rabon da ya yi kuka har ya manta ya ce "Uncle ka aura mini Mami idan na mata ciki zai sanya sunanka ka barni naje wajanta yanzu na yi mata small kiss.......
Jama'a ya Ibada? Allah ya bada lada ayi addu'a sosai Allah ya hurewa kowa kuɗi ya biya Mijin Malama ya sauke nauyi..... Hakƙi ba wasa bane. 08119237616
*Aunty Zee MOM MUJAHID KATSINA*
*08162859027*
*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYIN KASHI CIWON BAYA CIWON KAFA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA WARIN GABA KURAJEN GABA KURAJEN JIKI KAIKAYIN JIKI RASHIN HAIHUWA BASUR MAI TSIRO CIKIN IKON ALLAH ZAIMAGANCE MAKI/MAKA ZAKIJI DADIN MAGANIN SANYINNAN SOSAI A BANGAREN GYARAN AURE BA A MAGANA DAN ZAI SAUKAR MAKI DA NI IMA ZAKI JI SHA AWA KODA SHA AWARKI TA DAUKE ZATA DAWO KIJI KE KIKE MARMARIN ABAR KEDAI KINEMI AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
4k
*MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA* *JIKINKI NONUWA ZASU CIKO SOSAI ANMA BANCE ZASU TSAYABA WANNAN MAGANI ANGWADA ANDACE HANZARTA KI MALLAKI NAKI YAR UWA 8K*
*TAREDA MAGANIN CIRE TUMBI DUK INDA KIKAI KAMAR KIN KUSA HAIHUWA AITA TAMBAYAR KI WATA NAWA IDAN KINSHIGA MATE KIZAMA KAMAR BABARSU DAN ALLAH KIZO KIJARABA 7k *INA AIKAYA KOWANI GARI DA YARDAR ALLAH INBAKI SHIRYA BA KIBARI KI SHIRYA SAI KUNZO NAGODE KAYAN* *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
*KI TUNTUBENI A WANNAN LAYIN*
*08162859027*Wani lafiyayyen mari Abbu ya sauke Abraham a fuska yana huci tare da cewa "Who the hell do you think you are? Akan idanuna kake cewa a barka kaje ka sumbaci ƴar cikina? Sbd ka tabbatar mana kai mahaukaci ne baka san addini ba ko? Yanzu kai ko musulunci ne How do you think I will welcome you to marry my daughter, I will never let you marry Majeederh as long as I am alive in this world even if you are a Muslim, balle kuma ƙaton arne wanda babu ɗigon imani tunani a ransa" Uncle Isma'il ya ce
"Alhaji Abdul'aziz wannan ba mafita bace, kamar kana ƙara tunzura shi ne wlh,This is not the way to solve this problem, take heart please" Abbu ya girgiza kai ya ce
"Ba zan iya zama takaici ya tarwatsa mini zuciyata ba Isma'ila, Majeederh ta zame mini masifa da bala'i a cikin zuri'a kamar ita kaɗai na haifa? Ina sane fa time to time yake hauro mini gida kamar ɓaraho ya shigewa ɗakinta, tunaninta itama ban sani ba" Uncle Bello ya buɗe baki da mamaki bai ce komai ba ya juya ya kalli Abraham ya ce "Khalil, Majeederh kake so? Zaka iya kula da ita? Zaka iya musulunta?...," Abbu ya yanke maganar Uncle Bello da faɗin "Me ya sa kuke mini haka ne wai? To idan baku yarda ba, bari na ƙara maimaitawa wlh wlh wlh tallahi ko wannan shegen yaron zai musulunta ba zan taɓa lamumce masa auren Majeederh ba, kai na rantse da Allah da Majeederh ta auri yaron nan gwara ta zama duk abinda take son zama, gwara ta dauma babu aure har ƙarshen rayuwarta, gwara ta zubar mini da shegu na dinga ganinsu da dai ace wannan yaron ya aureta, i hate him for no reason, don Allah ku saka shi ya fice mini daga cikin parlour" A hankali Uncle Isma'il ya ce "Khalil" Abraham bai ɗago kai ba, balle ya kalli Uncle Isma'il bai ma san me suke tattaunawa ba tunda da Hausa suke magana, yadda yake jin ihun Abbu ya san faɗa yake, zuciyarsa kawai yake kaiwa nesa da tuna al'ƙawarin da ya yiwa Majeederh. Uncle Isma'il ya ƙara cewa "Khalil je waje ka jira ni" Ya ɗaga kansa ya kalle shi calmly ya ce "Na je gun je?"
"A'a, ka je waje ka jirani itama tana can gidana ai" Miƙewa kawai ya yi jiki a sanyaye ya fice daga cikin parlourn ya jima tsaye yana kallon part ɗinta da yake a rufe yana jin kamar tana ciki musamman da ya ji zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, tuna Uncle Isma'il kuma ya ce bata nan yasa ya nufi compound na gidan. Yana tsaye jingine da motarshi idanunsa rufe ya ji ance "Aa yau Little ne a gidan namu?" Jin muryar Aaliyyah ya sanya ya buɗe idanunsa tare da zuba mata a hankali ya ce "Baki iya gaisuwa ba?" Aaliyyah ta zare ido tana riƙe haɓa ta ce "Wa zan gaisar? Kai? Tab ka tuna sanda muke goyaka ne a baya muke maka wanka" Ya haɗe fuska tamau idanunsa ya ƙara yin ja kamar ba zai magana ba sai kuma ya ce "Kee!" Aaliyyah ta ce "A'a ba wani batun kee, sbd kaga ka zama ƙato kamar samudawan farko? Daga yau Anti zaka dinga ce mini" Bai kulata ba sai kuma da sauri ya ce "Ko jee ba taɓa ganin jikina ba, balle ke yarinya" Ta riƙe haɓa ta ce "Yarinya?" Ya yi mata banza yana kallon motar Uncle Isma'il ta ce "Bari na ƙarasa na gaji sosai" Ya jinjina kai ta ce "Ka gama secondary school?" Ya wani irin kallonta sai kuma ya ce "A'a" Ta yi Murmushi ta ce "Ka dage ka gama sai ka fara zuwa University school ɗin da nake Yusuf Mai tama" Silently ya ce "Ohk" Sbd at this time bai ma san me zai ce mata ba, kuma darajar jinin Majeederh dake yawo a jikinta ya sanya yake conversing da ita. Yana kallo ta shige ciki. Uncle Bello ya kalli Abbu ya ce "Amma har ranka baka ji kunya da ka ce wai kana kallo Khalil yake shigewa part ɗin Majeederh? Ba tare da taking any action ba, kuma kana ji a ranka kai uba na gari ne ko? Ka bada gudunmawa mai tarin yawa a rayuwar Majeederh yanzu kuma kana son bawa ƴar cikinka laifi?" Ya girgiza kai Uncle Isma'il ya ce "Alhji Abdul'aziz Please faɗa mini tun daga kan haihuwar Majeederh kawo yanzu da tayi growing up ta mallaki tunaninta sau nawa cikin dare ka taɓa tashi ka duba ɗakinta kaga yadda take kwana, ka duba kaga akwai problem da zamanta ita ɗaya a ɗaki ko babu? To mace bata taɓa girma a gaban iyayenta muddin ba aure tayi ta nufi gidan mijinta ba, yadda duniya ta lalace Majeederh ko maza take kawowa cikin gidanka take kwana da su ba zaka taɓa sani ba, tunda baka bincike yanzu ma da Khalil ke zuwa dalili ne ya sanya ka fahimci yana zuwa sbd ka saka idanunka akan shi, haka son shi. Yadda zamani ya lalace da waya ma kadai zai iya sawa yarinya ta lalace ta dinga aikata ba daidai ba a ɗakinta tunda tana ganin ita kaɗai take kwana take tashi, waya kuma babu mai binka mata balle asan me take, Alhj Abdul'aziz till now da kake wannan harbin iskar baka taɓa zama ka ji mene problem ɗin ƴarka ba, baka taɓa zama ka ji wanne hali take ciki ba, babu mai bata shawara akan rayuwarta kama gdy Allah ya baka yarinya ta gari wlh, amma ka iya zama ka buɗe baki kace wai yaro yana shiga cikin bedroom ɗin Majeederh bayan baka taɓa tsawatar masa ba, idan zaka tashi ka kula da rayuwar yaranka fine" Uncle Bello ya sauke numfashi ya ce "Muma fata muke mu rabu da Abraham lafiya a samu Majeederh tayi aure shikenan dole ya haƙura, amma kana surutun banza da iska kasan kaifin bakin uba akan yaransa? Baka gudun bakinka ya kamata haka kurum kaja mata masifa? Bama wannan ba kana da wanda zaka bawa aurenta ne?" Calmly Abbu ya ce "Still searching" Ya ce "Allah ya kyauta ni zan shige" Uncle Isma'il ya miƙe ya ce tafiya zan ni ma. Fitowa sukai a tare suka bar Abbu zaune dafe da kansa dake juya masa. Suna fitowa Compound Raihana na shigowa ita da wani yaƙunannen mutum jikinsa duk dauɗa talakan ƙarshe mai fama da halin rayuwa. Bayan ta gaishe su Uncle Bello ya ce "Wannan fa?"
Ta ɗan shafa kanta ta ce "Tasi'u sunansa" Ya ƙara cewa "Who's he?" Ta ce "Shi ne wanda mukai magana ya amince zai auri Majeederh, na kawo shi Abbu ya gansa" Uncle's ɗin suka dinga kallon Tasi'u kafin Uncle B ya ce "Ok neman kai aka ce miki ake da ita?" Ta ɗan shafa kai ta ce "Daman naga har yanzu ba tayi aure bane, kuma tana ta yawo a gari har ana mana gori wai iskanci take....," Wani ba hangon mari ta ji an sauke mata nan take hancinta ya fashe, aka ƙara sauke mata wani. Da sauri Uncle Isma'il ya ce "Khalil mene haka?" Huci kawai Abraham yake bai ma san akan me ake magana ba, sunan Majeederh kawai ya fahimta. Ya juya kan Tasi'u sai gashi ya saki fitsari a wando yana cewa "Wallahi ƙarya take ni Mahaukaci ne ba wani aure da za a mini" Sai kuma ya kwasa da gudu ya fice daga cikin gidan. Raihana ma ta miƙe tai waje da gudu tuni gefen fuskarta ya kumbura bata taɓa jin zafin mari irin wannan ba wanda ya gigita ta lokaci ɗaya. Abraham ya shiga motarshi ya fice da gudu tare da nufar gidan Grandpa. "Wannan yaron zuciya ne dashi" Uncle Bello ya ce "I like him, da musulmi ne babu abinda zai hana ni aura masa Majeederh wlh, ko zata dinga goya shi a baya dan ƙanƙantar shekarunsa" Uncle Isma'il ya ce "Ko waye ya faɗa mata namiji na yin kaɗan? Kuma ma age is just a number sanda zata fara ƙaunar mijinta ba wanda ya sani" Murmushi kawai Uncle Bello ya yi ya ce "Exlty, kaga a 9mnts ka samu jika" Ya ce "Ko shakka babu a wannan zafin naman na shi".... Bayan kwana biyar Majeederh na zaune duk ta rame ta kalli Latifa sai ta ji kamar ta faɗa mata Abraham na shigo mata bedroom cikin dare amma ta ji tsoron kada tayi mata wata fassarar Kullum abin na damunta ta rasa yadda za ta yi, bata da ƙarfin qiwwar tunkarar Abbu da wannan maganar hakan ya sanya bata da wani mafita kullum addu'a take Ubangiji ya ɗauki ranta ta huta da wannan halin da take ciki. "Ni laifinki nake gani, ga Aliyu ki aura wlh da tuni kin haihu da shi a sanda na yi miki wannan maganar amma kin ƙi" Majeederh ta girgiza kai ta ce "Ina jin kamar bani da rabon farin ciki a wannan duniyar Latifa, bani da gata na ko wacce mace na sare banda na san hukuncin wanda ya kashe kansa wlh da rataye kai na zan yi na huta, an kasa fahimta ba babu wanda ya gane halin da nake ciki, Abraham ya takura ni duk inda zani ya sani da ace na san ina ne dangin mahaifiyata wlh da can zan tafi maybe su za su iya fahimtar yadda nake ji a zuciyata, akwai mutanen da Ubangiji yake ƙaddara musu abubuwa wanda basu da rabo a duniya sai a lahira jikina yana bani ina ɗaya daga cikinsu" Hawaye ne ya kawo a idanun Latifa ta ce "Stop saying that dear, Ubangiji ya fi kowa sanin halin da kike ciki, In sha Allah watarana sai labari zaki zama abar kwatance, zaki farin ciki, zaki dariya sooner or later" Majeederh ta runtse Idanunta ba tare da ta ce komai ba. Gabaɗaya ƙaddara ce ke zagaye da rayuwarta tasan idan ta cika mumina dole tayi accepting na destiny ɗinta har zuwa lokacin mutuwar ta. Ƙilan rabonta na Aljanna yana jiranta. Aliyu dake sauraran su tun ɗazo ya sakko daga upstairs da sauri Majeederh ta rufe fuskarta da liƙab. Ya nemi waje ya zauna Latifa ta ce "Sweetheart ya zazzaɓi?" A hankali ya ce "Allhamd" Majeederh ta ce "Sannu Aliyu" Ya buɗe idanunsa zuciyarsa na harabawa jin ta kira sunansa ya dai kalleta bai ce komai ba. Can ya ce "Ki yi haƙuri da rayuwa, kada ki sare kuma ki yarda Allah ke yi shi kuma zai miki, ki tsarkake zuciyarki, ki miƙa lamuranki ga Ubangiji ki ci-gaba da addu'a watarana zai amsa, babu ɗan adam ɗin da bashi da damuwa ko ƙalubale Hawwa'u naki ne kawai ya fito fili" Miƙewa tayi tsaye ta ce "Thank you" Ya ɗauke idanunsa duk suka bita da kallo harta fice daga cikin Parlourn. Latifa ta ce "Sweetheart dan ka auri Majeederh" Da wani kalar yanayi ya kalleta ya ce "how many times zan ce miki bana son wannan maganar? Eh? Ni na taɓa ce miki ina son ta ne?" Ta ce "Sbd Allah, watarana zaka so ta, she's a darling ita abar so ce" Ya ce "Bana son ta" Da sauri Majeederh ta bar wajan tana rufe Idanunta domin daman tsaye tayi tana mai da numfashi sai kuma ta ji suna maganar. Latifa ta miƙe tsaye tare da barin wajan, Aliyu ya riƙe saitin zuciyarsa a hankali ya ce "Hauwwau, u're my destiny"
Majeederh na zaune zuru ita ɗaya lokaci lokaci take kallon ƙofa, a hankali ta miƙe ta zura hijabi ko wanka ba tayi ba ta nufi part ɗin Mami ta sameta ta shirya zata nufi part ɗin Abbu "Majeederh ya dai?" Kanta a ƙasa ta ce "Mami zan kwanta part ɗinki" Da mamaki ta ce "Me ya sa samu naki?" Ta ce "Tsoro nake ji" Ta dinga kallonta kafin ta ce "Ok ni zani wajan Abbunku ki kwanta ki zare key ɗin, kin ci abinci?" Ta ce "Bana jin yunwa" Mami ta ce "Wanne irin bakya jin yunwa? Da safe na haka kika ce fa, ki tabbatar ko tea kin sha kafin ki kwanta" Ta jinjina kai kana ta shige part ɗin Mami, da mamaki take kallon Ruma sai bata kulata ba Ruma ta ce "Ki ce yau mai kwanan gida ne, ana ta tsofa a gida dai" Majeederh bata ce komai ba. Ruma ta ce "Allah sarki ɗan haɗa mini tea plx ban jin daɗi" Majeederh ta juya ta kalleta ta ce "Ashe ba zaki sha ba" Ruma ta miƙe tana kallon Majeederh ta ce "Ina magana kina magana? Wake ja da matar aure baki san yanzu gaba nake dake...." Wasu tagwayen maruka Majeederh ta saukewa Ruma har sai da taga wuta ta nunata da yatsa ta ce "Ki iya bakin ki, stay in your limit da aure irin naki gwara ban ba, idan iskanci zan yi kinsan me lasisi zan yi" Ruma ta buɗe baki za ta yi magana ta ce "Uffan kika ce sai na haɗa miki jini da majina a nan" Ta yi tsit tana zare idanunta. Duguwar Majeederh ta zauna tana duba wayarta Dm ta gani domin tuni ta goge number Abraham amma ƙarshen Digits kawai ta gani ta san shi ne. Kamar zata share sai kuma ta buɗe ɗan short note ne mara yawa ta fara karantawa.
“Ina inviting naki zuwa bikin Easter Monday, gobe 4:30 no african time, ko kizo ko na zo na ɗauke ki....Ur Better half Bad boy”
Kashe wayar tayi tana jan tsaki domin bata bawa abun serious ba. Raya daren tayi ta kasa bacci gabanta sai faɗuwa yake daga ƙarshe tayi alwala tayi sallah daman bata jima da gama al'ada ba. Bikin Easter Monday. Mabiya addinin Kirisita a faɗin duniya kan gudanar da bukukuwan Easter duk shekara domin tunawa da gicciyewa da kuma tashin Yesu Almasihu daga cikin matattu.
Bikin dai a kan fara shi ne tun daga dare irin na Alhamis zuwa wayewar garin Juma'a a kuma kammala a ranar Litinin ta gaba. A faɗar David shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar Kano ya ce bukukuwan Easter sun kasu kashi biyu; akwai wanda ake kira Juma'a mai Tsarki wato ''Good Friday'' da kuma Easter Monday..
The day!. Majeederh na zaune a office ɗinta sbd kiran gaggawar da akai mata, bayan da a sallami jama'a ta miƙe tare da ɗaukan komai nata har waya ta rufe office ɗin sbd P.a bata nan, tana fitowa zata shiga mota taji an shaƙa mata abu hanci tare da caka mata allura a wuyanta, ganinta ya ɗauke komai nata ya tsaya bata ƙara sanin meke faruwa ba. Da sauri Taj ya sakata a mota shi da John suka ja motar da gudu suka bar wajan. Abraham na kwance a Main parlour na gidansa yana duba X-ray ɗin da akai masa sosai tsoro ya bayyana akan fuskarsa a karo na farko, ya dinga kallon X-ray ɗin da sauri kuma ya miƙe ganin Taj ɗauke da Majeederh a kafaɗa a hargitse ya nufe shi yana tallafo Majeederh zuwa saman ƙirjinsa idanunsa akan Taj ya ce "Me ka yi mata?" Ya ɗaga kafaɗa ya ce "Me kowa zan mata? Mafita na kawo maka sai ka gwada ka tabbatar" Yana faɗin hakan ya fice daga parlourn Abraham ya dinga kallon fuskar Majeederh kamar bai taɓa ganinta ba, abinda ke bashi mamaki sam ya daina jin yanayin da yake ji ya kwantar da ita tare da mikewa ya ɗauki Cork yana sha sam bai san Taj ya zuba ƙwaya a ciki ba, ya shanye tas yana rufe idanu, ko good 3 minutes ba a dauka ba jikinsa ya fara tsoma ya ƙarasa kusa da Majeederh ya zauna ya kifa kansa, idan ya ɗago ya kalleta sai kuma ya bayar da kansa kansa, rawar da jikinsa yake ya tsananta hankalinsa ya fara gujeshewa sbd wani irin mahaukatan ƙwayoyi Taj ya haɗa masa, kala daban-daban dana saka felling dana gusar da hankali. Bai san mene ya faru ba sai kawai ganinsa ya yi rungume da Majeederh ya mirginata gefe zuwa ƙasa daga nan ta fara loosing control ɗinsa wani kalar sauti yake fitarwa tare da neman hanyar ratsa jikinta amma ina! Jikinsa yaƙi bashi dama ɗan sauti yaƙi motsawa kamar lagwani a kalanzir, bashi da guzari ta wannan ɓangaren shi kansa kuma ya san ba haka yake ba ai amma cike da hope ya ci-gaba da ƙoƙarin ya ratsa ya shige kamar daga sama kuma suka fara jin ruwan bindigo, wanda ya ratsa cikin gidan Abraham kamar ana yaƙi, sosai Abraham yaji ƙara amma bashi da zarafin kare Majeederh balle kansa bai san inda hankalinsa yake ba a lokacin. Da gudu Taj ya shigo yana zuwa bai damu da yadda yaga Abraham ba ya saka hannu ya fisge Abraham daga kan Majeederh ya ce "Bad boy get up where's ur gun an kawo mana hari" Abraham ya yi shiru a lokacin kamar matacce idanunsa na zubar wani irin hawaye mai zafin gaske. Jin ƙarar bindigar na ƙara yawa ya sanya Taj ficewa ya ci karo da John da Joshua ko wanne riƙe da bindiga wasu manyan mutane ne fuska rufe hannunsu riƙe da manyan bindigo John ya nufi wani wanda ke ƙoƙarin shiga parlour cikin rashin sa a mutumin ya sakarwa John harsashi a ƙirji nan take ya faɗi matacce. Taj ya zare idanu kai tsaye kuma suka shige babu jimawa suka fito hannunsu ɗauke da Majeederh, mota suka shiga tare da barin gidan da gudu... Gudu mutanen suke sosai har suka isa wani haɗaɗɗan gida suna zuwa suka shimfiɗe Majeederh a ƙasa wani ya ce "Sir gata nan" Wanda aka kira da Sir ya juya ya saki wata mahaukaciyar dariya. Alhaji Bashir kenan dariya yake kamar zai kifa kafin ya ce "Well-done, Alhji Abdul'aziz Khan yau zaka biya bashin daka ɗauka, ka karɓe miliyoyin kuɗina da nufin zaka bani auren Ƴarka sbd son zuciya amma kaƙi ka ɗauka na manta?" Alhaji Bashir ya ƙara yin wata dariya kamar Mahaukaci cike da zallar rashin Imani ya ce "Zunubinka zai shafi Ƴarka, ki yi haƙuri Malama Majeederh Abdul'aziz Khan! Ubanki ya ja miki ba zan taɓa yafe masa kuɗina ba, a yanzu kuma ba kuɗin nake buƙata ba, ni bana yafiya ke na ce ina so kuma dole na samu, ya yi arziƙi ya mance da deal ɗinmu" Ya juya ya kalli wani ya ce "Dr wannan alurar ya ka ce aikinta?" Ya ce "Idan akai mata ita ba zata taɓa farkawa ba har tsayin kwana uku, sannan za a kashe mata dukkan jiyoyin jikinta, idan akai mata ki wuƙa aka saka za a cire mata ƙafa ba zata taɓa sani ba, ba zata jin wani abu wai shi zafi ba" Alhaji Bashir ya ƙara sakin dry ya ce "Well-done Dr" Dr ɗin ya ce "Amma Alhj na faɗa maka kazarinka ya saki ba zaka iya taɓuka abin arziƙi ba" Alhj Bashir ya ce "Dr tell me something, zan iya amsar virgin na mace?" Ya ce "Why not? Amma baifi kai 3mns ba, kuma duk wacce zakai virgin nata ba zata wahala ba" Alhji Bashir ya ce "I don't care ko ta sha wahala ko kada ta sha, idan har zan iya amsar budurcinta shikenan that's what i want" Murmushi Dr ya yi ya ce "Ok, amma daga kanta ba lallai ka sake kusantar kowa ba sbd jikinka ya gaji gabaɗaya, bari na yi mata alurar" Alhji Bashir ya ce "Go ahead, ka faɗa mata biyu" Dr ya girgiza kai yana jinjina rashin imanin Alhaji Bashir amma ko mene Ubanta ya ja mata ai. Allurai a kaiwa Majeederh aka kaita wani ɗaki, idanu rufe kamar maye cike da rashin tausayi da imani haka ya yi dis virgin na Majeederh ya yi mata Fyaɗe wanda ko shi da kansa bai zai ce ya ji daɗin abun ba.....
MIJIN MALAMA.... na kuɗi ne pay before you read 08119237616.
*Aunty Zee MOM MUJAHID KATSINA*
*08162859027*
*INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK WANI DATTIN MARA SANYIN KASHI CIWON BAYA CIWON KAFA JIN ZAFI YAYIN MU AMALAR AURATAYYA FITAR FARIN RUWA MAI WARI KAIKAYIN GABA TUSAR GABA WARIN GABA KURAJEN GABA KURAJEN JIKI KAIKAYIN JIKI RASHIN HAIHUWA BASUR MAI TSIRO CIKIN IKON ALLAH ZAIMAGANCE MAKI/MAKA ZAKIJI DADIN MAGANIN SANYINNAN SOSAI A BANGAREN GYARAN AURE BA A MAGANA DAN ZAI SAUKAR MAKI DA NI IMA ZAKI JI SHA AWA KODA SHA AWARKI TA DAUKE ZATA DAWO KIJI KE KIKE MARMARIN ABAR KEDAI KINEMI AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
4k
*MAGANIN GYARAN NONO MAI TADA KOMADAR NONO DA DUK WATA TAMOWA TA* *JIKINKI NONUWA ZASU CIKO SOSAI ANMA BANCE ZASU TSAYABA WANNAN MAGANI ANGWADA ANDACE HANZARTA KI MALLAKI NAKI YAR UWA 8K*
*TAREDA MAGANIN CIRE TUMBI DUK INDA KIKAI KAMAR KIN KUSA HAIHUWA AITA TAMBAYAR KI WATA NAWA IDAN KINSHIGA MATE KIZAMA KAMAR BABARSU DAN ALLAH KIZO KIJARABA 7k *INA AIKAYA KOWANI GARI DA YARDAR ALLAH INBAKI SHIRYA BA KIBARI KI SHIRYA SAI KUNZO NAGODE KAYAN* *AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA*
*KI TUNTUBENI A WANNAN LAYIN*
*08162859027*MIJIN MALAMA 50
End of book1
The begen of the beginning... Continuation
*AUTHOR'S NOTE*
_*This information is for those who do not understand this book.. Ni ban wani niyyar cewa komai ba, to na ce me? Kowa ya yi ta kansa da haka nasu na barku, to ganin ana ta yagalgala nama na yasa nace bari na tofa tawa. I have a question for you guys! Kunga na gama labarin nan na sauke? No??? Me ya sa aka bawa littafin suna MIJIN MALAMA?babu mamaki mijin nata ke shan wahala, babu mamaki masu neman aurenta suke da yawa shi ya sanya aka ce Mijin Malama Ko kuma ƙaddara aurarraki ta faɗa kanta duk wanda ta aura ya zama MIJIN MALAMA babu mamaki wannan Christa ɗin shi ne mijinta kasancewarta Christa sai a fara kiransa da MIJIN MALAMA.... Idan ƙaddara zata faɗawa mutum daman Ubangiji na neman shawarar shi? Ko kuma idan Allah ya jarabce ka da abu sai kace kada ya sake jarabtarka tunda ya taɓa? Ashe ɗan adam a karan kansa zai iya tunanin Ubangiji bai kyauta masa ba tunda yana ta jarabtar shi da abubuwa kala-kala? Abinda baku sani ba shi ne wannan labarin full of density ne cike yake da zanen ƙaddara, shaidar zur na mutane, ƙalubaleln da masu jinkirin aure suke samu, son zuciya da mugun baki na Iyaye, rashin kulawar su ga yaran su.... Saboda Majeederh ta kasance malama shike nan bai dace ayi ta ayi ta jarabtar ta ba? Ai cikakken mumini wanda ya yarda da Allah da Manzonsa shi, ya yarda da ƙaddara ya yi imani da ita shi kaɗai Ubangiji ke jarabta sbd nuna masa soyayyar shi, mutane wagairawun Ubangiji ba fiya shiga al'amarin su ba. Cewa akai ko wata guda kayi bakai ciwon kai ba, to ka tuntuɓi imaninka😞 Ga misalin Annabawa nan wanne irin ƙalubale ne basu fuskanta ba, suka jure ya zame musu tarihi. Taya zaki haɗa su da Ƙaruna wanda Ubangiji ya zuba musu idanu suna tunanin sun fi kowa Sa'a a duniya? Kuna ganin Fir'auna wacce tsiya ce bai shuka ba? Ga su hamana to haka al'amarin Ubangiji yake, ku bar ƙaddara tayi aikinta plx..... Sannan azana cewa wai ina barin ana taɓa jikinta wanne yaƙunannen kuga ya taɓa ta? Abraham bad boy? To a rayuwa duk abinda kake so Ubangiji ya fi jarabtarka da shi, babu mamaki zunubin hakan ya sameta nan gaba kuma har zuciyarta kallon ɗa wanda ta raina take masa bata taɓa bari ya riƙeta hannunta da nufin wani abu ba. Sai mema matar ta ce ne? Ni Afujajen na karanta write up ɗin nata, wai ina nuna masu liƙab basu da gaskiya? To ban ce komai ba idan kin karantar posting na yau zaki fahimta ni duk takaicina bana biya tayi ba, a wata ƙasar taci karo da shi... A ƙaddarorin Malama Majeederh babu sa hannunta a faruwar komai ni dai bari kawai na yi shiru a nan kada bakina ya yi tsayi ana zama lafiya.... Zamu fara BOOK2 ban yi kuma al'ƙawarin farin ciki har ƙarshe ba, tunda rayuwa bata taɓa tabbata da farin ciki amma nayi muku tanadin wata kalar tsaftacciyyar soyayya mai narkar da zuciyar mai karatu, In sha Allah wacce tayi write up ɗin nan ina zaune zata sake yin wani na yabon bama ita kaɗai ba. THANK YOU I LOVES YOU SO MUCH GUY'S😞🤓🥰*_
50
Tunda suka shiga cikin jirgin Abraham ya rasa tunaninsa idanunsa jajur kansa a kife yana jin gabaɗaya kamar bashi ba, jikinsa ne kawai cikin jirgin amma tunaninsa da ruhinsa ya barsu a nan Nigeria, babu kuma wanda ya yi attempting kula shi daga Escorts ɗin Dad ɗinsa har Grandpa. 5 hours 42 minutes, ya kai su Germany, jirkinsu ya sauka a airport ɗin Berlin Brandenburg Airport (BER). Ya ɗauki wajan minutes kafin gently ya fito dan kansa, da sauri ya shiga taka matattakalar benen zuwa ƙasa, tun kafin ya ƙarasa wata black ɗin Mercedes-Benz S600 ta tsaya a gabansa, aka buɗe masa back seat ya shiga yana sauke numfashi motar Escorts a gaba ta Abraham a tsakiya sai ta Grandpa na bin baya, sai wasu Escorts ɗin a bayansu. Tafiya sukai sosai sun ɗauki hanyar zuwa Hammerschmidt Villa in Bonn, sai suka samu saƙon gaggawa akan su shige da shi President's Palace. Suka juya kan motar tare da nufar Bellevue Palace in Berlin. Tun daga bakin shiga Federal President's Palace ɗin zaka dinga cin karo da wasu manyan manyan sojoji ga wasu Escorts na musamman. Hakan zai tabbatar da yadda shugaban ƙasar yake da ƙarfin iko sosai. Kai tsaye motocin ciki suka shiga tun kafin a gama parking Abraham ya fito da sauri kamar zai tashi sama. Ko'ina na gidan fari ne tas idan ka ɗauke green grass ɗin dake waje, kai tsaye part ɗin daya tabbatar sai samu Dad ɗin nasa ya nufa, cikin sa a ya same shi tsaye ya juya baya da ƙofar shigowa cikin parlourn nasa, hucin da ya ji yasan stubborn boy ɗinsa ya ƙarasu babu mai zarrar shigowa part ɗin nasa kai tsaye dole sai shi. Gently ya juya idanunsa ya sauka akan Abraham dake tsaye jikinsa na rawa sosai ya ce "Wlcm back my dear"
Wani ihu Abraham ya yi yana nuna Dad ɗin nasa ya ce "Who the hell do you think you are? Eh?" Dad ɗin ya ce "Son i need u" A hargitse ya ce "I hate you Dad, i hate you, i don't want see your face" Dad ya ƙarasa wajan Abraham zai taɓa shi ya ce "Faɗa mini wani abu, daɗin me kake ji a zaman Nigeria? Ko sbd kana son babbar mace Musulma?" Abraham ya yi shiru.
"Buɗe kunne ka ji da kyau, kai da Nigeria har abada, zaka zauna dani a nan, ka je can uban yarinya na wulaƙantan ka bayan ka fi shi komai na rayuwa? You're my darling, President's son, kana da komai ka zauna wajan wanda basu da ko sisi" Abraham ya ture hannun Dad ɗinsa daga kafaɗarshi yana huci ya ce "Su ɗin sun fiye mini kai" Dad ya yi murmushi kawai yana ƙara jinjina ƙuruciyar ɗan nasa
"Sbd wacce kake kira Mami? Ta faɗi nawa za a bata da rainon da tayi maka shi kenan?" Abraham ya ce "Aurenta zan yi, ina son ta" Dad ya koma ya zauna saman wata ƙatuwar kujera mai kyau yana girgiza ƙafa ya ce "Ba zaka sauya ba, my child is still young" Abraham ya sa ƙafa ya tar watsa Glasses ɗin dake kusa da shi ya ce
"Young? To ka jira zan kawo maka ɗan da zanwa Jee ciki ta haihu, stay away from my life ka manta kana da ɗa kamar yadda na manta ina da uba, me ka taɓa mini na kyautatawa daga haihuwa zuwa yanzu eh? Sau ɗaya baka taɓa kwana tare dani ba, ban taɓa jin ɗumin jikin ba, ban taɓa ganin soyayyarka ba, cutarwarka kawai na sani, azabarka kawai na sani you're the reason behind anything duk abinda na aikata kai ne sila, ka zaɓi karuwarka fiye dani" Dad ɗin kallon yaron nasa kawai yake, yana mamakin yadda ya kasa mance lokacin daya same shi tare da Kiristi akan gado, memory na nan a kansa moment ɗin ba zai taɓa goshewa a wajansa ba, wannan ya riga a ransa wanda ya sa ya yi masa tsana mai muni. A hankali ya ce
"Listen Son, zo nan I'll explain everything to you" Abraham ya ce "Everything?" Ya girgiza kai kawai ya rasa me zai ce tunda ya fara maganar yaƙi yadda ya kalli cikin idanun mahaifin nasa. Ya juya zai fice Dad ya ce "Ina zaka?" Ya ce "Nigeria" Dad ya miƙe ya ce "Kai ba zaka kaji wani iri ba? Ka zauna a inda ake wulaƙanta ka? Kuma waccar yarinyar kake son lalata ƙungiyarka a wajanta? Me ka gani a wajanta?" A hargitse Abraham ya ce "Abinda ka gani a wajan Kiristi, Jee da kake gani tafi mini komai na duniya, mulkin ka ɗin me? Kaga taɓa ji na nemi sisi wajaka Dad? Duk abinda na mallaka kuɗi na ne, halak ɗina ne kamar yadda Jee ta faɗa mini na nemi halak duk wahalarsa, to yanzu na girma baka isa ka faɗa mini yadda zan da rayuwata ba am maturel enough Dad" Dad ɗin masifar ɗan nasa da zafin ransa har mmki yake basa daman can haka yake? Shi ba zai ɗorar da komai akan rayuwar Abraham ba yana sawa dai ana bincika masa. Private Investigators.
"Sweetheart na tara maka dukiya, na ajjiye maka komai na jin daɗi Debeka na jiranka hatta gidan da kake son rayuwa sai ka zaɓa, I am the president of Germany, I am your father, I have the power to choose what is right for you, I will decide, wancan Musulmin old woman ɗin ta maka ƙatuwa kaje ka nemi wacce zaka ji daɗi tare da ita, ba zaka taɓa komawa Nigeria ba" Wani irin dariyar takaici Abraham ya yi har yana durƙoshewa a ƙasa idanunsa na zubar da hawaye ya ce "Exlty, that's exactly who you are" Ya girgiza kai yana jan numfashi tare da riƙe ƙirjinsa ya ce "I need love and care not money, soyayyar ma dana nema a baya a wajanka ka wulaƙanta ni yanzu ban so ban so" Yana faɗin hakan ya miƙe zai fice daga cikin Parlourn Dad ya ce "Come in"
Wasu sabbin Escorts ne wanda Abraham bai sani ba, suka damƙe shi "Take him out" Abraham ya ce "Don't do this to me, ina son Malumana i love jee i love Mamina ka sanya su cika ni na mata al'ƙawarin zan koma" Ya fara abu kamar hauka hauka hakan yasa Dad tunanin ya samu matsala few minutes ya saka akai masa wata mahaukaciyar Injection ta bacci akai kai sa wani part can ƙarshen Palace ɗin aka garƙame.. Har wajan sati uku Abraham sunan Majeederh a bakinsa ya yi ta surutu shi kaɗai damuwa ta samu gurbi a zuciyarsa tayi daram, ya daina cin abinci ya daina magana daman dariya bata dame shi ba zai ma iya irga sanda ya yi ta. Haka aka dinga masa allura ana saka masa drip sbd rashin cin abinci. Dad ɗin ya ce da dai Abraham ya auri Musulma kuma older gwara kawai yaga gawar ɗan shi duk da irin son da yake masa. He will never allow him to be MIJIN MALAMA ba. Ba zai taɓa barinsa ya zama MIJIN MALAMA ba, wannan babban abin kunya ne ga mabiya addinin su na Kirista magoya bayan Yesu su ji labarin ɗan shi yana auran Malama, ba zai taɓa faruwa ba hakan zai iya sawa ya samu matsala da kujerarsa ta shugaban ƙasa,He doesn't want that to happen hakan ba zai taɓa faruwa...
After 1 mnt. Majeederh na zaune a dining room tayi shiru tun ranar data dawo daga hospital ta koma shiru shiru. Yau kuma ta tashi bata jin daɗin gabaɗaya tayi tunanin ko al'ada za ta yi? Tana wannan tunanin Latifa ta yi sallama Mami ta ce "Latifa da sanyin safiya?" Latifa ta ce "Wlh Mami, an tashi lafiya?" Ta ce "Allahamdulillah" Latifa ta zauna tana kallon Majeederh ta ce "Lafiya kike?" Ta ɗan lumshe jiƙaƙƙun idanunta tana girjiza kai can a hankali ta ce "Headache" Mami ta ce "Gashi bamu da paracetamol a gidan nan" Latifa ta buɗe jakarta ta ce "Ga wani maganin ciwon kai mai kyau ne, tun sanda Aliyu ya ce waje da bashi da lafiya maganin yake yana da kyau sosai" Majeederh ta kalli maganin sai kuma ta jawo gorar ruwa tare da zubawa cikin cup maganin kala biyu ne ta haɗa ta watsa a baki, ta haɗiye da ƙyar dan ba zata iya kallo ai mata wata allura ba. Ji tayi amai na zuwar mata ta kifa kanta ta kifa saman dining tana mai da numfashi. Mami ta ce "Latifa ki rufawa kan ki asiri kina zama ɗakin mijinki, ki daina biyewa yawon majeederh kada azo ayi haihuwar guzuma dake da ita, ita ba aure ke kuma ki kashe naki" Lafita ta ce "Haba Mami, wai ba zaku yadda da ƙaddara bane? Mene laifin Majeederh a rashin aurenta bafa yin kanta bane itama da zaɓi za a bata wlh da tuni tana gidan mijinta da yaranta, amma miji bai zo ba zata auri kanta ne?" Mami ta ce "Ke wane ya ce miki miji ne bai zo ba? Bata niyyar aure ne amma a yawon da take na Ngo da faɗar kar da matan da take kaɗai ya isa wani ya ganta ya ƙyasa, ba lissafin aure a cikin lissafin rayuwarta" Latifa ta girgiza kai ta ce "Jinkirin aure ne kawai ta samu, Ubangiji kaɗai ya san manufar hakan itama ba da ra'ayinta ba, nasan Majeederh nasan halinta da wani yace yana sonta da aure tabbas zata faɗa mini, Mami da aure da haihuwa duk na Allah ne, amma duk kun bi kun juya mata baya sbd kawai ba tayi aure ba? Idan iyaye basu jawoka jiki a irin wannan condition ɗin da take ciki ba, bai ci ace sun juya mata baya ba, suna bawa jama'ar gari damar d su faɗi duk abinda sukai niyya akan Majeederh, Mami cikar imanin mutum shi ne yadda da ƙaddara cikakken mumini shi Ubangiji yake jarabta ko dan tabbatar da imaninsa, wallahi ba gama garin mutane Ubangiji yake nunawa jarrabawa da ƙuddirarsa akan su ba, mu yarda ne bai kawowa Majeederh mijin aure ba, mu yarda jinkirin aure ta samu" Mami ta ce "Idan mu mun yarda jama'ar gari fa?" Latifa tayi shiru can kuma ta ce "Mami mutum tara yake bai cika goma ba, a jikin ko wanne mai rai akwai zuciya ita take saƙa masa komai, to at this point ba zaka taɓa hana mutane abinda sukai niyyar faɗa ba, haka halin ɗan adam yake, baka da gadonsa yana da gadon maganarka, wani ma bai sanka ba bai san ya kake gudanar da rayuwarka baz bai san komai game da kai ba, ji kaiwa zai yi mutane suna magana ya ara ya yafa ya ɗora nashi akai, sbd kawai baya ƙaunarka ko yana baƙin ciki da abinda kake ko yadda yake gudanar da rayuwarka, wani kuma haka halinsa yake da haɗa ƙanzon kurege haka mutum yake, The world is big, the challenges in it are many, the people in it each have their own character" Latifa tayi shiru tana goge hawayen idanunta ta ce "Human nature is difficult to deal with, whether you do well or not, you will never stop a person from saying what he intends, kinga kenan babu yadda za mu yi, let them says lokacin su ne watarana za su daina, Mami banga aibun auren yaron daka raina ba, tunda bakai ka haife shi ba, ba kuma na nufin rainon yaran da ba kai ka haifa ba illa ne ko haramun ne, amma da Abbu ya bawa Abraham dama nasan dole zai musulunta" Cak Majeederh ta miƙe jiri na ɗaukarta. Washegari gari ta yiwa asibiti tsinke ta nufi wajan Dr Jamal ya gudata ya shaida mata kawai stress ne na gari ya bata magani. Bayan ta koma gida ta samu Abbu da Mami a parlour Mami ta ce "Me Dr ya ce? Akan zazzaɓin?" Majeederh ta ce "Wai stress ne" Mami ta ce "Oh Allah ya ƙara sauƙi" Abbu daman tuni ya zame hannunsa daga kan Majeederh ko gaisuwarta baya amsawa Family ta daina shiga kowa iyaye yake mata akan yana da aure gorin aure ake mata babu ji babu gani, ji take kamar ta mutu ta huta da sauri kuma take Asstagafirullah. Shiru tayi haka kurum tunanin Abraham ya faɗo mata gani take tafi kowa laifi, mai yasa idanunta ya rufe a lokacin ta kasa fahimtar da gaske ba ita ta haife shi ba? Me ya sa take sake masa har yake taɓa jikinta? Bayan tasan ya haramta a gareta, kenan ita ce wacce ta bashi da dama har ya ji ya fara sha'awarta. "Innalillahi wa'inna ilahir raji'un, na shiga uku, Allah na tuba Ubangiji ka yafe mini, ban taɓa tunani hakan ba" Tun daga ranar take neman yafitar Ubangiji da yardar shi, tana jin kamar ta ci amanar addinin musulunci ne, Tunanin Alpha ya faɗo mata haka nan taji tana son saka shi cikin addu'a, shi ma ya riƙe hannunta amma gwara shi yayanta ne, Sai Ajlaal kuma bashi da kunya dama daga gani yafi ƙarfinta ko wanne a riƙe hannunta mistake ne bada gangan ba Abraham kai ta sakewa yanzu kuma tayi ladama kullum cikin neman yafiyar Ubangiji take tana hora kanta da raya dare tana sallah da azumi.....
After a year da ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal nan ma ya shaida mata lafiya take. Lokacin tana da shekaru 34 ta jingine komai a gefe, ta ƙaddara Abraham baya ƙasar ba labarinsa babu na Gang team. Lokacin data shiga shekaru 35 farkon shekarar sai ta ji kamar gilamar abu a cikinta ta ɗauka kawai irin abin nan ne da ake kira macijin ciki. Nan ma ta ƙara zuwa wajan Dr Jamal ya dubeta yana murmushi ya ce "Wai mai Malama Majeederh ke tunani ne? Gashi dai har scanning da X-ray duk nayi amma ba komai lafiya lou kike" Ta ɗan yatsuna fuska ta cikin liƙab ta ce "Kawai ban san yin ciwo" Ya jinjina kai ya ce "You're right, ni kam na tambayeki mana" Ta jinjina masa kai ya ce "Me muhimmancin saka liƙab da hijabi ga mace ne?" Ta kalle shi ta ɗauke kai ya ce "Wlh masu saka liƙab da hijabi na mugun birgeni, na taɓa ganin wata ina sonta amma tayi mini kwarjini" Sai a lokacin Majeederh ta ce "A duk sanda kaga mace ka ji sha'awa to ba kai ne mai laifi ba ita ce zata ɗauki zunubi, ita ta baka damar ganin abinda zai sanya ka ji sha'awarta, to me liƙab sirri ne, hijabi mai taraba ne ga ko wacce mace, abu uku zuwa huɗu yake fara jan hankalin namiji ga ƴa mace, na farko da namiji yaga mace idanunta yake fara kalla, a wannan kallon wani zai iya samun matsala, daga nan sai baki, daga nan sai wuya, abu na gana kuma murya, daga nan kuma bayan mace namiji yake gani, to idan zaka saka hijabi ka saka liƙab ka rufe jikinka babu wani ɗa namiji da zai sha'awarka balle ita macen ta ɗauki zunubi, liƙab da hijabi alama ne da tarbiyyr mutum, masu sakawa a fassara mu su da Allah, idan ka duba larabawa za kaga ko wacce da liƙab ɗinta, me ya sa ƴan izala suke sawa matansu suna sakawa? Ka yi tunanin su ɗin suna da kishi kuma sun san amfaninsa" Zai yi magana ta miƙe ta ce "Thank you Dr Jamal" kwanci tashi Majeederh ta ji cikinta ya fara girma tsoro ya kamata har aka ɗauki wata biyar Mami kallonta kawai take. Tana zaune kamar daga sama taga Uncle Isma'il da Uncle Bello "Saka hijabi hospital zamu" Bata ce komai ba ta miƙe suna zuwa asibiti a gabansu akai mata komai da komai Dr ya ce "Lafiya lou take, gaskiya ko da wata cutar mu dai bamu gani ba, ga photon komai na cikinta ai kuna gani" Uncle Bello ya sauke numfashi Uncle I ya ce "Mu je wani hospital ɗin" suna zuwa wani the same abinda aka faɗa musu shi ne suka sake ji, Uncle Isma'il ya saka akai mata medical check up nan ma the results is good dole suka dawo gida. Latifa ta dinga bawa Aliyu labarin halin da ake ciki akan Majeederh shiru kawai yake mata ta ce "Don Allah don Annabi ba danni ba ka duba girnan Allah dana mahaifiyarka Hajia ka amince da auran Malama Majeederh" A hankali yana miƙewa tsaye ya ce "Accepted" ta kurma ihu ta rungume shi. Lokacin data jewa Majeederh da maganar fata fata sukai ta ɗauke mata huta. Tafiya tayi tafiya har Majeederh tayi wata tara cikin shekarar data shiga na 35 haka kurum ta ji hankalinta yaƙi kwanciya, musamman da cikinta ya yi wani irin mahaukacin girma ƙafarta ya kumbura sosai ta buɗe tai wata ƙiba, hijabi ta saka ta ɗauki waya da jaka ta fito, Mami na zaune a a parlour tare da Raihana da Ruma da Aaliyah hadda Sahar data zo ta fito da ƙyar, tunda ta fito Mami ke kallonta ta ce "Wai kinga ganki kuwa? Anya likita ba ƙarya ya yi miki ba? Ji bi ciki kamar wacce akaiwa ajjiya? Majeederh ta ce "Mami ko jiya sai da Uncle Isma'il ya tisani a gaba wajan likita asibiti biyar muka je Mami ki tambaya ki ji" Ta ce "To Likitocin me suke cewa?" Kanta a ƙasa ta ce "Cewa suke lafiya ta lau, ba su ga komai ba" Ta jinjina kai ta ce "Allah ya kyauta" Ta ce "Zani wajan Dr Jamal na kirasa yanzu ya ce yana cikin asibiti kawai zuwa zan" Mami ta ce "To Allah ya kiyaye" Raihana dai kallon Majeederh take tun daga sama har ƙasa tana tuntsirewa da dariya, da ƙyar Majeederh ta ja ƙafarta zuwa waje ta nufi gidan Latifa ta sameta zaune ta ce "Plx ki yi dropping nawa hospital Latifa i can't drive myself" Ta ce "Ok, amma yau kin fi bani tsoro akan kullum wannan kamar wata mai cikin tagwaye?" Ta miƙe ta ɗauki key ta mayafi ta ce "Sweetheart ya fita zan masa yawa idan mun je" Mota suka shiga Latifa na driving Majeederh a gefe idanunta rufe ta cure waje guda sbd wani irin sanyi da aka tashi da shi yau ga wani masifaffan hazo na tashin hankali, tunda suke tafiya kuma bata ce komai ba rawar sanyi take Latifa ta ɗaga Glasses ɗin motar ta kashe komai na sanyi, amma duk da haka sanyin shiga jikin Majeederh yake tun kuma data shiga motar kanta ke sunkuye, Latifa na lura da damuwar da Majeederh ke ciki, kuma ta yau tafi da ko yaushe, ta ƙara sauri domin su yi su ƙarasa Aminu Kano hospital ɗin amma ina daidai by pass na first bank go-slow ya riƙe su...... _*(A page 1 za a ga ci-gaba daga nan)*_
Continuation..
Shassheƙar kukanta His Excellency Abu-turab yake ji har tsakiyar kansa ya ɗauka kukan farin ciki ne, da Allah ya bata shi a matsayin mijin aure, wanda ya ji tausayinta na ƙaddarar daya faɗa mata ya aura, amma sai ya ga kukan tsananin baƙin ciki da damuwa ne a hankali ya ce "Ya isa haka Jiddo"
Ta zame jikinta daga na shi da sauri duk da babu hijabi a tsakaninsa yanzu mijinta ne shi kuma matarsa ce, amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. His Excellency ya watsa mata rinannun idanunsa cike da zallar so ya ce "Mene na kuka?" Ta yi masa shiru ya miƙa hannu zai riƙo nata tayi saurin barin parlourn ya bita da sauri ta shige bedroom ta banko ƙofa tare da murza key tana sulalewa jikin ƙofar tare da rushewa da wani irin raunataccen kuka. *END OF BOOK 1*
Allahamdulillah! A nan na kawo ƙarshen BOOK1 wanda suka labari ne, akan yadda aka samu cikin Khalil da kowa ke cewa ɗan shi. I hope yanzu zaku fahimci labarin daidai idan mun ɗora... Da yawa za kuga kamar Malama Majeederh ba ta yi achieving komai a rayuwarta ba sai baƙin da ƙaddarori da suke ta rige-rigen faɗa mata. Ba zan iya cewa kun ji daɗin BOOK1 ko aka asin hakan ba... Abu ɗaya na tsani tsagwaron labarin yana BOOK2. Akwai wasu ƙalubalen tunda mutum a karan kansa bai taɓa dauwama da farin ciki ba, to rayuwa haka take yau fari gobe baƙi, yau zuma gobe maɗaci. Duk macen da zata buɗe baki ta ce tunda tayi aure da mijinta zaman daɗi suke basu taɓa samun matsala ko saɓani ba, tuni na bugi ƙirji na ce ƘARYA TAKE. Allah ya taɓa zuciyata na fahimci komai na gane komai kuma ina fatan zaku biyoni domin kuma ku fahimta...
1. Wacce rayuwa Majeederh za ta yi a gidan Abuturab?
2. His Excellency zai yarda ya saketa ko ya ya? Zata haihu da shi ko ya ya?
3. Abraham zai dawo kamar yadda ya yi al'ƙawari? Idan ya dawo ya samu labarin Majeederh na gidan mijinta me zai faru? Zai haƙura ya barta tayi rayuwa da mijinta ko ya?
4. Ina fatan baku manta da General Alpha Bello khan ba? Shin bayan ya gudu sbd baya son auren haɗi tsakaninsa da Majeederh ina yaje? Yana raye ko ya mutu ne? Yana cikin hankalinsa ko hauka yake? Zai bar Majeederh ko ya?
5. Aliyu ya ce idan har bai auri Majeederh ba to mutuwa ya yi, shin ya zata kaya? Zai haɗa su kishi da Latifa ne?
6. Kuna ganin Abbu zai yi aman shi ya lashe? Wacce magana Fulani zata faɗawa Majeederh amma bata samu dama ba sai Abbu ta faɗawa.
7. EHEM🤓 WAYE AJLAAL SULTAAN Mr ji dakai masu taƙama da rawani, kuna ganin zai dawo Nigeria a karo na biyu? Waye zai yi SACRIFICE a cikin zataran mazan? Su waye zasu haƙura da Majeederh wa kuma kuke ganin ya dace da ita matsayin miji na gari?.
WANNE IRIN ZAMA ZA A YI TSAKANIN MAMI DA ƊAN RAINONTA?🤣 BILLAHI DRAMA CE BABBA WANDA BAI BIYONI A BOOK2 BA BABU RUWANA... KUN TAƁA GANIN INDA MATA TAKE GUDUN MIJINTA?😂DUK MAI SON SHIGA GROUP 2 ZAI BIYA #500 BABU YAWA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER6850917335
Na'ima Shu'aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616 ayi maza a cika group wanda bashi da 500 kada ya karanta na sata yazo na yi masa Discount sbd Allah shi ya taɓa zuciyata ba ruwana. Ina ƙaunar masoyana na amana da gaskiya da duk mai karanta littafina. Ubangiji yabar zumunci da ƙauna Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira ya sadaku da dukkan alheri yayi muku albarka🥰Ya hure muku kuɗin siyan MIJIN MALAMA 2 thanks for the love and cares thanks for patronize me 🤞🏽kune ni da bazarku nake taƙama kune kuke sawa asan da zamana 😘😘😘😘 Nimcyluv sarauta's love you👑💋❣️
No comments