Kanwar Maza Book 2 Page 6
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228,
Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*
Tsuru-tsuru suka yi suna kallon umar, sai dai yanayinsu ya nuna a razane suke, kuma aka rasa wanda zai yi magana.
Ƙarasawa yayi gabansu, ya karɓi wayar daga hannun Aliyu, ya yi dialing lambar ɗanlami, yana kira ya ɗaga tare da yin sallama. Sai dai ɗanlami na jin muryar mai sunan baba cikinsa ya kaɗa, dan ba ƙaramin tsoron tijarar mai sunan Baba suke ba.
Cikin kakkausar murya Umar ya ce "Me ka gaya musu? Ina ruma take?"
Ɗanlami ya ɗan rikice sannan ya ce "Malam umar a saka addu'a, amma Akwai damuwa, ka san shi lamarin ƙaddarar Ubangiji ba ayi mata shamaki".
Cikin hasala ya kuma cewa"Ba nasiha na ce kayi mini ba, tambayata zaka amsa mini, damuwar me, ka yi mini bayani ina rumaisa take?"
Tamkar an ritsa ɗan lami da bindiga ya ce "Umar wallahi 'yan bindiga sun tafi da rumaisa, kuma ba da ita kaɗai suka tafi ba, amma an sanar da jami'an tsaro za su yi ƙoƙari a kai, za abi bayansu"
Cikin tashin hankali ya ce "Ya isa haka ɗanlami, amma kun san garin nan babu cikakken tsaro kuka tura yarinyar nan? Babu yadda ba ayi ba a kan gwaggo ta bayar da yarinyar nan a dawo da ita gida amma taƙi, ta turata in da ta san babu tsaro, duk yadda ake ciki ku san yadda zaku yi, ni ban san wata magana ba kawai an haɗa baki da ku an yi garkuwa da yarinya ku san yadda zaku yi".
Ɗanlami zai yi magana, mai sunan Baba ya kashe wayar ya cillar ya fice a fusace dan gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun miƙe saboda ɓacin rai da tashin hankali.
Mama ce ta fito tsakar gida ta na faÉ—in "Wai babana shi da wa yake É—aga murya, me kuka yi masa ne yake ta magana sama-sama?"
Cikin sanyin jiki Usman ya ce "Saɓani ne aka samu, kin san halinsa da zuciya da saurin fushi"
Mama ta ce "A'a ai kuwa bai fiye yin magana ba, sai an ƙure shi, wani abun dai ku ka yi masa, ko kuma faɗa kuke a tsakanin ku" gani tayi sun jeru basu ce mata komai ba, sai dai fuskokinsu ɗauke da damuwa, kamar a firgice suke.
Ta dubi Aliyu da kyau ta ce "Gadanga wai menene, na ganku duk wani iri me yake faruwa ne, ko akwai wata matsala ne?"
Aliyu ya dake ya ce "Babu komai mama, ni bari na fita zan sayo omo na yi wanki".
"Ban da omon da babana ya sayo shekaranjiya ya shigo da shi kaya guda, kusan kayan, wane omon kuma ka ke nema ko ka manta ne?"
Ya dafe kai ya ce "Ohh na manta, aski zani, ai na manta shaf da Oman ne, idan na dawo daga askin sai na yi wankin" yana yin maganar yayi waje, Usman ya rufa masa baya.
Gaba É—aya mama ta kasa gane kansu, kuma ba wanda yayi mata bayanin wani abu. Kawai ta share ta cigaba da sabgoginta.
Duk yadda usman ya so dakewa abu ya gagara, a soro ya durƙusa ya fashe da kuka, shi ya riga ya karaya ya san ubangijin da ya halicci ruma ne kawai zai fitar da ita.
Aliyu ya rungumo shi ya ce "Haba usyy so ka ke sai mama ta gane ne? Dan Allah ka jure kan mu san abin yi, kar mu bari ta gano akwai matsala idam ta gane, ka san tana da hawan jini, yanzu zai iya tashi"
Usman ya ce "Wane abun yi da me zamu karɓota? Me muke da shi? Mutanen da ba imani ne da su ba, 'ya mace ce fa, Allah kaɗai ya san me zasu yi mata, gara ace mutuwa ta yi ga gawarta da wannan tashin hankalin, wa zai kula da ita?".
Aliyu da tasa zuciyar ma ke daf da karyewa ya ce "Na sani, amma addu'a ba ta bar komai ba Usman ita zamu dagewa, kayi haƙuri tashi ka daina kuka kar mama ta zo ta samemu" haka yayi ta rarrashin Usman.
Mai sunan baba kuwa ji yayi duniyar ta yi masa zafi, ina ma shi aka É—auka aka bar ruma. Yaya mama za ta ji idan ta samu labarin an yi garkuwa da rumaisa?.
Zuciyarsa ta din ga zafi yana jin da zai ga gwaggo sai yayi mata rashin mutuncin da bata taɓa tunani ba, dan yana jin zai iya mangareta dan duk ita ta janyo wannan masifar, duk da tana ƙanwar mahaifinsu, cewar da aka yi tana gadon asibiti jininta ya hau bai dameshi ba, dan da jinin tasa uwar ya hau ko wani abu ya samu ruma, gara duk abin da zai faru ya faru.
***
Zuwan takawa a Abuja a wannan karon ya sanya ya samu abubuwa masu muhimmanci da bincikensa bai kai masa ba a baya, sai dai zuciyarsa na ta azalzalarsa a kan lallai ya koma gida, jinsa yake tamkar a kan wuta, idan bai bar garin ba kamar wani mummunan abu zai faru da shi, dan haka babu shiri, ya tattara kayansa ya taho Kano, dama ga Ammi na ta waya dan duk a tsorace take, saboda yanayin jikinsa, Jabir ma duk ya addabeshi a kan nan kano ma akwai aiki, dan haka ya haÉ—a kayansa ya koma kano.
Sai ka ce a wannan karon ya fara tafiye-tafiye, Ammi sai hamdala take a kan dawowarsa gida lafiya, dan ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, da yayi tafiyar nan dan sam ji ta yi ba ta son tafiyar ta sa.
A gidan Turaki suka haÉ—u, da takawa, da Jabir da kuma Jamil da ya kasance wa ga Samha kuma cousin É—in sa.
Hira suke yi sosai, suna tattaunawa a kan rayuwa.
Jamil ya zunguri Takawa ya ce "Kai, wai me kake nufi da ni ne, ba fa ka taka gidana ba, ranar da na tare ma ko rakiya ba ka yi mini ba, kuma ba ka zo ba sai harkokinka kawai kake"
Ɗan shiru Adam yayi, tun daga lokacin da ya ji muryar ruma a ranar ya rasa nutsuwarsa, kilisar ma da ƙyar aka ƙarasata da shi, tunani ya fara yi ko zuwa unguwar su zai yi.
'Ka je ka yi mata me?' wata zuciyar ta tambayeshi.
Tsaki yayi wanda ya fito fili bai sani ba.
"Tsakin me kake kuma?" Adam ya tambaye shi.
Girgiza kai yayi bai ce komai ba.
Jabir ya ce "Yauwwa Takawa, ina mutuniyarka kuwa wannan yarinyar?"
Haɗe rai Adam yayi tare da basarwa, Jamil ya ce "Wace yarinyar, budurwa yayi ne? Kai ka isa ka yi wa ƙanwata kishiya?"
Jabir ya ce "To bana ce ba, wata 'yar figigiyar yarinya ce mai kama da bainu, ban taɓa ganin yarinya mara mutunci da rashin tsoro irinta ba".
Adam a ransa ya ce "Ai ba ka san mara mutunci ba, sai ka ga wasiƙar da ta rubuta mini' amma a zahiri yayi shiru kamar ba da shi suke hirar ba.
***
"Ina sonka Adam, so bana wasa ba, so mai tsananin gaske son da nake jin zan iya komai domin na mallake ka, duk da na rasa dalilin da ya sanya bana gabanka, ko da yake ba rasa dalili na yi ba, nafi kowa sanin dalilin da yasa bana gabanka, kuma ina daf da magance komai domin in samu miƙaƙƙiyar hanya ɗoɗar ta cimma muradina na rayuwa da kai, ko baka aureni ba ina son kasancewa da kai na rayu ƙarƙashin kulawarka. Ban sani ba ko zuwa nan gaba asirina ya tonu duk da bana tunanin faruwar hakan, amma idan ma ya farun ka yi mini uzuri soyayyar ka ce ta janyo mini hakan" tamkar taɓaɓɓiya haka samha ta saka hoton Adam a gaba ta na surutu, hoton yana sanye da kaya ne na sarauta, ya ɗan sauke rawaninsa yana murmushi, wanda aka ɗauka da hawan wata salla.
Sai da ta gama soki burutsunta, ta mayar da hoton ma'ajiyarsa, ta tashi ta ƙarasa shirinta ta fice.
Mummy ce tare da aminiyarta zaune a ƙuryar ɗakin Mummy suna tattaunawa.
"Wai hajiya Lubabatu babu wani zazzafan malami ne, abubuwa kamar sun tsaya mini, sun ƙi cigaba kamar yadda nake so".
"Haba Jamila, ke kin san an daɗe muna haƙa rijiya, rijiyar da muke saka ran samun ruwa a kowane lokaci, mun shirin da idan balli ya tashi akwai rikici, ke dai mu cigaba da haƙuri".
Mummy ta girgiza kai ta ce "Ya ci ace burina ya gama cika, nifa da dai da mintuna biyar bana son ruhin Binta ya kasance cikin kwanciyar hankali da farinciki, so nake ta dauwwama a baƙin ciki har ƙarshen rayuwarta".
Dariya Hajiya Lubabatu ta yi ta ce "Haba Jamila, ai ko a haka kika barta wallahi ta yabawa aya zaƙinta, kuma ta ɗanɗana kuɗarta, amma ki cigaba da haƙuri ai mun ɗana tarko daban-daban".
Mummy ta jinjina kai ta ce "Shikenan, bari mu ga zuwa yaushe, na cigaba da sanya musu ido, duk wani motsinsu uwani na gaya mini, kuma na ce lallai ta kawo mini maganin da waccan 'yar tsintuwar ke shafa masa".
"To shikenan, to bari mu ga yadda abubuwa zasu kaya".
***
Har azahar babu wanda ya kula su ruma, masu kuka na yi masu addu'a na yi, ga yunwa ta addabeta a gida wataran ƙarfe bakwai ta karya, amma har bayan azahar babu wanda ya kulasu balle ya basu wani abu.
Tashi ruma ta yi ta samu É—aya daga cikin 'yan bindigar ta ce "Bawan Allah yunwa nake ji, ku bani abinci na ci"
Wani mugun kallo ya yi wa ruma ya ce "Zo ki cinyeni, an gaya miki nan wurin hutu ne da jin daÉ—i?".
"Ai ni ba mayya bace da zan cinyeka, idan ma cin ne ban ga abin ci a nan ba, idan ba za a bamu abinci ba meyasa zaku kawo mu nan?" Ta na rufe baki yana hankaɗeta sai dai faɗi ƙasa ya saita ta da bindiga "Idan ki ka yi mini hauka, yanzu na lahira zasu yi maraba da ke".
Ruma ta kalli yadda ta faɗi ƙasa, wata irin zuciya ta harziƙota ta miƙe tsaye ta sake kallonsa ta ce "Na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, ai daɗinta idan ka kasheni ba a wuta zaka sakani ko aljanna ba, hisabi na Allah ne, to na faɗa a bani abinci yunwa nake ji, harbeni maza kai kuma a ƙara maka kwanakinka a duniya"
Babu alamar tsoro ko shakka a tare da ruma, kowa sai da ya Zubo mata ido, saboda ƙarfin halinta.
A fusace ya tashi yayi kan ruma, amma wani ya riƙe shi, ya ce kar ka kuskura, ƙyaleta idan ka yi mata wani abun za'a iya samun matsala, ka bari oga ya zo ya faɗi ya za ayi".
Huci ya din ga yi yaso ya tattaka ruma, ko ya keta mata haddi a gaban mutanen wurin, ya kawo ƙarshen harshenta.
"Ni baka kyauta mini ba da baka bari ya kasheni na huta ba"
"Wato ke dai bakinki ba zai mutu ba ko?"
"Idan har so ku ke na yi shiru, to ku kasheni ko ku mayar da ni gidanmu, wannan ai zalunci ne ni yunwa nake ji" tayi maganar tana share hawaye.
Dattijon nan ne dai na jiya ya ce "Yarinya ki yi shiru da bakinki, kar su citar da ke, wannan mutanen ba ayi musu haka".
"To ni yunwa nake ji" tayi maganar har cikin zuciyarta.
Duk wani kurari da zare ido ruma taƙi yin shiru, kamar ma da gayya take yi dan ta tunzurasu su yi mata abin da za su yi mata.
***
Har dare mama ba ta san abin da ya faru ba, kuma an rasa wanda zai gaya mata, sai mita take musu cewar ita fa ta kasa haƙuri ta kira gwaggo idan an dawo da ruma ta haɗata da ita, amma wayar gwaggon ba ta shiga. Sun yi mamaki da duk jin rediyon mama ba ta ji batun kai harin ba.
Ganin tana ta surutu ita kaɗai ba wanda ya tanka mata, ya sanya ta magantu "Wai ba zaku gaya mini meke faruwa ba ne? Duk cikinku fa yau babu wanda ya ci abinci, kun ƙi walwala kun ƙi magana, kuma kun ƙi gaya mini menene?"
Usman ne ya tashi ya ce "Mama sai da safe, ni dai bana jin daÉ—i ne".
Babu wanda ya bawa mama amsa, a hankali duk suka watse daga tsakar gidan, mama ta sha jinin jikinta ta fara tunanin menene ya faru haka, da basa son gaya mata?.
Babu wanda ya saurari su ruma sai bayan la'asar, aka zo da wasu kuloli a kan babur, aka rarraba musu wata busashshiyar gurasa, gaya guda É—ai-É—ai, sai pure water É—aya tamkar mabarata.
Ruma ta kalli gurasar nan, duk uwar yunwar da take ji, amma a rasa me za a bata sai wannan takurarriyar abar a bushe, babu mai babu komai a jiki.
Gashi duk ta bushe kamar ƙanzo.
Ruma ta gasta ta fara ƙoƙarin haɗiya, amma ta kasa haɗiyewa, da ƙyar ta dannata da ruwa, daga gutsura ɗayar nan ba ta ƙara ba ta shanye ruwanta ta yar da ledar, sauran kuwa tuni kowa ya kama gurasar nan suka cinye.
***
Duk wata tattaunawa su Usman da sauran 'yan uwansa sun yi, amma sun rasa ta ina zasu É“ullowa lamarin, duk in da zasu buga sun yi, amma babu wani labari game da in da su ruma suke, gashi da wani ya ce zai je katsinan mama za ta gano akwai abin da yake faruwa, dan a yanzu haka ma duk ta tsargu, mussaman yadda suka daina walwala ga kuma ta fara shiga damuwa rashin shigar wayar gwaggo.
Su huzaifa ma sun gano abin da yake faruwa, sai dai yanayin ruÉ—ewa da Huzaifa da Yasir suka yi, ya sanya mama cigaba da jefa musu zargi da kuma kokwanto.
Yau ƙarfe tara na safe taga duk sun fito daga ɗakinsu sun jeru a tsakar gida, kamae kullum babu wanda yake walwala a cikinsu, kuma babu mai sunan Baba a cikinsu.
Mama ta girgiza kai ta ce "Koma menene Allah yayi muku maganinss, tunda ni dai ina tsakaninku ba zaku gaya mini ba".
Ta fito daga banÉ—aki kenan, Abubakar yayi sallama ya shigo da jakarsa ta makaranta, sai dai kallo É—aya tayi masa shima ta ga tsananin tashin hankali a fuskarsa.
Mama tayi saroro tana kallonsa, cikin ƙarfin hali ta ce masa "Kai kuma me ya dawo da kai yanzu?"
Suka haÉ—a ido da Aliyu, Aliyu ya sunkuyar da kai, Yasir kuma ya hau goge hawaye.
"Saddiƙu, dan Allah kai ka gaya mini menene? Ku daina ɓoye mini koma menene, na kasa nutsuwa sun ƙi su gaya mini abin da yake faruwa, na rasa gane kansu, dama har akwai abin da ban cancanci in sani ba?"
Abubakar ya ajiye jakarsa ya kamo hannun mama ya ce "Mu je É—aki mama sai mu yi magana"
Mama ta buge hannunsa ta ce "Ba in da zani, ku yi ta riƙe abin ku a cikinku nima bana son ji, idan abin da bana ƙauna a rayuwata bai wuce ganin fuskokin da ba sa son damuwata in gansu cikin damuwa ba, ko ba zan maganta muku ba ai na yi addu'a" ta juya za ta wuce ɗakinta.
"Mama ruma ce" ya furta a hankali, cak mama ta tsaya ta kasa gaba ta kasa baya, ta ji maganar ta sa kamar bai faÉ—eta dai-dai ba.
Ba tare da ta waiwayo ba ta ce "Mutuwa ta yi?"
"An yi garkuwa da ita, a garin su Iya, a cikin harin da aka kai ƙauyen har da ita aka ɗauka".
Innalillahi wa Innalillahi raji'un, mama za ta iya cewa ko mutuwar iyayenta ba ta girgizata kamar wannan abu da ta ji yanzu ba, ji ta yi kamar ba a hayyacinta ta ji maganar ba, tamkar an mata yayyafin wuta, Rumaisa a hannun 'yan biniga, gara ace kashe mata ita suka yi, ta tura a ɗauko mata gawarta, amma ruma 'ya mace ƙarama a hannunsu a tsakiyar dajin Allah, Allah kaɗai ya san me za su yi mata, ga halin ruma da ta sani na rashin kunya da surutun tsiya, tsaf za su illata ta.
Jikin mama ne ya hau rawa, ta sake ƙare musu kallo, Huzaifa da Yasir suna ta kuka, Aliyu kuma ya sunkuyar da kai, haka Abdallah, Usmsn kuwa barin tsakar gidan ya yi, babu mai sunan Baba ko ba a gaya mata ba ya tafi katsinan ne.
Ta yinƙura da niyyar ɗaga ƙafarta, ta tafi luuu gaba ɗaya suka yi kanta suna kiran sunanta
No comments