Kanwar Maza Book 2 Page 4

 Ayshercool.




*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*







Abin da gwaggo ta yi ba ƙaramin ɓatawa Aliyu rai yayi ba, da ya san haka ne da ba zai taɓa bari ta saka a kai ruma ko ina ba, daga zuwa ziyara kawai ta riƙe 'ya wai sai wani lokaci.


Ya sake duban gwaggo ya ce "Gwaggo, ruma fa ba zata yarda ta zauna a garin nan ba, rigima za ta yi miki idan ta dawo ta tarar na tafi na barta".


Gwaggo ta ce "Babu komai, na san yadda zan shawo kan kayata, amma a yanzu dai ba in da zata".


Takaici ya ishi Aliyu, ya bi gwaggo da kallo.


"Gadanga ko dukana zaka yi ne? Na gama yanke hukunci, idan kuma kaima zaka zauna ne ni haka nake so, sai mu zauna idan lokacin yayi sai ku tafi duka".


Tabbas ba dan gobe yana da test mai muhimmanci a makaranta ba zama zai yi, ya saka lawalli a gaba sai ya kai shi ya É—auko ruma, amma ba yadda iya ya É—auki jakarsa ya fice.


****

Har Adam yayi kwanakinsa uku a birnin tarayya, bai iya aikata komai ba, saboda da ya fita da niyyar zuwa wani wuri, sai jiki ya hau rawa kai ya hau ciwo, ga ruma da ta addabawa rayuwarsa ya kasa mantawa da ita, komai yake yi sai ya din ga ganinta.

Bayan ya cika kwanaki huɗu, ya kira Ammi yayi mata ƙaryar bai gama abin da yake yi bane, sai dai tattaunawar haka aka yi ta babu shi, duk da halartarsa tattaunawar na da matuƙar muhimmanci.

A kwana na biyar ya kira direbansa a waya, ya ce ya zo da mota ya same shi a hotel É—in da yake.

Ƙarfe biyu direban ya sameshi, sai dai a wannan karon cikin ikon Allah tun da ya fito sau É—aya kan ya sara, jiri ya É—an É—ebe shi, amma  ya tattara nutsuwartsa, yana addu'a, ya nufi motar.

Suka gaisa da direban nasa, yayi masa ya hanya, daga nan ya ce ya gaya masa in da zai kai shi.

Mintuna ashirin ce ta kaisu, a harabar wata plaza suka yi parking, Adam ya buÉ—e motar ya fita.


Wani matashi ne zaune wanda zai yi sa'an Adam, yana danna computer, yana ganin Adam ya miƙe cikin girmamawa yana murmushi ya ce "Barka da zuwa"


Adam ya ƙarasa yana murmushi, ya miƙa masa hannu suka gaisa, sannan ya zauna.


Matashin ya kalli Adam ya ce "Adam, ya aka yi an shirya zama da kai, amma ba ka yi attending ba?, na din ga kiran wayarka ba ka É—agawa, har wayar ma ta daina shiga gaba É—aya?"


Adam ya ɗan taune lips ɗinsa na ƙasa ya ce "Am sorry Habib, wata matsala aka samu, amma komai normal yanzu in sha Allah".


Cikin kulawa Habib ya ce "Are you safe?"


Adam ya jinjina kai sannan ya ce "Me aka tattauna, wace matsaya aka cimma?"


Habib ya ɗan rausayar da kai ya ce "To, mun tattauna yadda yakamata, amma dai kamar yadda na yi maka bayani da farko, ko da ka fito ƙarara ka bayyana lamarin nan, ko an je kotu za a sake su, saboda haryanzu baka da wata cikakkiyar hujja ta zahiri da zaka kafa, yanzu ko kun yi wani abu a kai, ya riga ya gama shiri, da tattaunawa da lawyoyinsa, ya shirya tsaf da ka yi attacking zai yi depending, yanzu abin da yafi shine ka sake mayar da hankali sosai da kai da abokan aikinka, ku samo hujja ta gaske, ta zahiri da za ayi amfani da ita, nima zan shirya tsaf domin cimma nasara ni da tawagarmu"


Adam yayi ajiyar zuciya tare da dafe goshinsa, ya sake ɗagowa ya kalli Habib ya ce "Duk wata hanya da zan bi domin neman hujjar kama mutumin nan an tosheta, kuma kullum kallon mutunci ake masa, ana sake bashi girma tare da shigar da shi cikin al'amuran ƙasar nan, bayan su ne babbar matsalar mu"


"Adam, tun da ka ga haka, ba shi kaÉ—ai bane, ko dai an san me yake yi ake rufa masa asiri, ko kuma akwai wasu manyan da suke aikin tare "


"Haka ne, abin da nake tunani kenan nima, amma babu komai in sha Allah zamu yi nasara, zan cigaba da ƙoƙari, ina son magana da saifu ma, zan zauna a garin nan sai Allah ya kaimu monday zan koma kano".


Habib ya ce "To shikenan, Allah ya yi jagora, gashi ko shayi ban baka ba"


Adam ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu"


Daga haka Adam ya tashi ya fita, ya saka direbansa ya mayar da shi masauki. Sam ya ƙi yadda yaje gidan sa, saboda wani Dalili nasa.


***


Ƙauye ne sosai in da aka kai ruma, sai dai mutane masu matuƙar karamci da girmama ɗan Adam, tamkar za su goya ruma, dan wasunsu duk basu santa ba, sai dai sun san mahaifinta sosai tunda ɗa ne a wurinsu.

Garin sun yi noma sosai, sai dai an girbe an tare shi a cikin gonaki, ba a kwashe an kai gida ba, ga yanayin garin kamar yanayin garin da aka yi wata annoba.

Wani wurin a ƙone, wani wurin dai gashi nan.

Tun da safe ruma ta fara cewa ita azo a mayar da ita gidan gwaggo, yau zasu koma gida ita da yaya Aliyu, amma dattijon da ya kasance ƙanin kakanta ne ya ce "Ai jikata ba ke ba tafiya, sai hutun makarantar bokonku ya ƙare, kina nan tare da mu"


A É—an razane ruma ta ce "Saboda me?"


"Haka gwaggonki ta ce"


"Ni gaskiya ba zan iya zama a garin nan ba, gida nake so na koma na ga mama, na gaji, ni ku mayar da ni gida" ta yi maganar tana kuka.


Matarsa da ake kira da iya ta ce "Haba rumaisa, muma fa duk iyayenki ne, muna ƙaunarki sosai, ki kwantar da hankalinki kin ji, za a mayar da ke, idan ki ka matsa zasu iya ƙwaceki gaba ɗaya, 'yan kwanaki zaki yi a mayar da ke"


"Ni mama nake son na gani".


"Ki yi haƙuri, za a mayar da ke in dai wurin mama ne" An kai ruwa rana sosai da ruma, kan ta daina koke-koke, sai dai ita ma ta haɗa musu aiki, ba komai take ci ba, tsirfar yau daban ta gobe daban.


In da ta ɗan ƙara samun sassauci, shine tana tare da lawisa, kuma a gidan akwai wata sa'ar tata zaliha, dan haka sukan ɗebe mata kewa.


***

Ba ƙaramin ɓacin rai 'yan mazan mama suka shiga ba, tun bayan da Aliyu ya dawo musu babu ruma, tare da sanar da su hukuncin da gwaggo ta yanke ba.

Abdallah ya ce "Wallahi gwaggon nan tana da matsala, tsabar mugunta ta yi garkuwa da yarinya dan son zuciya daga kai mata ita a sada zumunci".


Sai da suka yi dariya jin abin da ya ce, wai tayi garkuwa da ita.


Usman ya ce "Wane irin garkuwa kuma?".


"To idan ba garkuwa ba, ta yaya zata saka a kai yarinya wani ƙauye a ɓoyeta, wai ba zata dawo yanzu ba, amma idan ta cika musu ciki da rashin ji, ai sa dawo da ita da kansu"


Suna cikin tattaunawar mai sunan Baba ya dawo, suka gaisa da Aliyu, ya tambaye shi ina ruma? Ya sanar masa da yadda suka yi da gwaggo.


Tsuke fuska yayi ya ce "Wane irin abu ne haka? Idan na gama exams ranar lahadi zan je na taho da ita, akan me zasu riƙe ta?"


Mama ta ce "A'a babana, tun da na haƙura dan Allah kuma ku yi haƙuri ku ƙyalesu, yanzu sai ace zigaku nake yi, su je su ƙarata, sati biyu ai kamar yau ne"


"Duk da haka, bai kamata ruma ta zauna a wurin nan ba, babu tsaro gaba É—aya dole zan je na taho da ita, dan ba ta zuwa makarantar boko yanzu, islamiyya fa?" Sosai ya É—au zafi, mama dai ta ce ba ta yadda wani yaje ya ce zai taho da ruma ba.


***

Gaba daya ta tattara hankalinta da nutsuwarta a kan litattafanta, gefe kuma ga calculator tana dannawa, tayi ɗai ɗai a ƙasan carfet, ta saki dogwayen kalbar da aka yi mata, ta zubo har kafaɗarta, duk da kalbar ta tsufa amma ta yi kyau sosai.

Nusaiba ta turo ƙofar ɗakin ta shigo da sallama.

Iman ta amsa mata, ta zuba mata ido tana kallonta.


"Sarkin littafi, me kuma ake yi?" Iman ta kalli litattafan ta yi murmushi ta ce "Boko nake ci masoyiyya, ta samu ne?"


Nusaiba ta zaune ta ce "Eh to, ba nace ba, uncle J ne ya zo, kuma da alama ke yake son gani, sai tmbayata yake kina ina?"

Tsaki iman tayi, ta gyara zamanta tana ƙoƙarin mayar da kanta kan litattafanta.


"Kai, uncle J É—in ki ke yi wa tsaki, ya zo ya sakani a gaba sai tambayata yake kina ina?"


"Anty Nusaiba dan Allah ki ƙyaleni da sabgar mutumin nan, wai me zan yi masa ne dan Allah?"


"Nifa na kasa gane abin da kuke É“oyewa, anya ba sonki yake yi ba?"


Da sauri iman ta girgiza kai ta ce "Dan Allah Anty Nusaiba kar ki ɗaga maganar nan, idan har Ammi ta ji za ta bayar goyon bayan hakan, ni kuma ba zan watsa mata ƙasa a ido ba, amma ni bana sha'awar duk wani wanda ya fito daga masarautar na, ke kin san me nake nufi".


Nusaiba ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, na daina cigaba da aikin ki, zan je na ce masa bacci ki ke kawai"


Iman ta jinjina kai alamar to.


****

Tafe suke su uku, ruma na ta shan tsamiyar biri tana zubarwa a hanya, mayafinta a kafaÉ—a. Su fuskarsu duk da hoda da kwalli, ruma kuwa tata yadda take haka take kamar namiji, kunneta babu ko É—an kunne.


"Kai ku tsaya" ruma tayi maganar tana kallon wata bishiyar mangwaro, 'yar gajeriya amma tayi 'ya'ya fal.


Suka kalli ruma suna son jin dalilin tsayar da su É—in.


"Mangwaro zan tsinka".


A ɗan razane Zaliha ta ce "A'a ruma, a garin nan fa bakomai ake taɓawa ba, baki ga gonaki duk an yi girbi ba, amma ba a ɗauka ba,masu garin ake jira su zo su yanke harajin da za a biya sannan a ɗebi amfanin gona, yanzu idan suka zo wucewa suka ganki, zaki saka mu a matsala.


"Suwaye masu garin?" Ta yi maganar cikin ko in kula.


Lawisa ta ce "Ke dai ki bari kawai ruma, ki bari idan muka je gida sai a saka a samo miki"


Ruma ta cire mayafinta, ta ɗorawa lawisa a kafaɗarta, ta nufi bishiyar nan, suna ƙwala mata kira, amma ba ta tsaya ba, ta kama bishiya ta haye kamar buranya, hawan katanga da bishiya ba abu ne mai wahala a wurin ruma ba.


Ta naɗe doguwar rigarta, ta tara mangwaron sannan ta saukko, su kuma suna ƙasa suna jiranta cikin tsoro suna cewa ta sauko.


Bayan ta sauko ta karɓi mayafinta ta zuba a ciki, ta saɓo abunta tayi gaba ta ƙyalesu.

Bin ruma suka yi da kallo, ta ci uwar ubansu a rashin ji, haka suka rufa mata baya suna kallonta.


Suna cikin tafiya suka ga ta saki hanya ta shiga wata gona, tarin masarar da aka jingine ta je ta fara É—auka.


"Innalillahi, dan Allah ruma kar ki janyo mana masifa, dan Allah ki fito mu tafi, duk wanda aka gani a gona bayan girbi ba a biya haraji ba kashe shi za ayi".


"Kisa kuma sai ka ce cinnaka, guda biyar kawai zan É—auka gasawa  zan yi na ci"


Zaliha ta ce "Dan Allah ki fito kar su ganki".


"Wai suwaye ne? In sun ganni ba ruwanku ni kaÉ—ai na É—auka" ta zuba masarar a mayafinta ta fito. Kamar suna tsoron ruma suka sake rufa mata baya suna zazzare ido.


Sun yi tafiya mai nisa sun kusa gida, suka ji ana musu magana "Ke daga ina ku ke?" Gaba É—aya suka tsaya suka waiwaya, wani dogon mutum ne a tsaye, sanye da rawani hannunsa saye a cikin tsummar rigarsa, ya ma dai fi kama da mahaukaci.


Ruma ta ƙare masa kallo za ta yi gaba abinta.


"Ke ina magana zaki tafi?" Ya daka mata tsawa.


Cikin tsiwa da rainin hankali ruma ta ce "Haba babana ke fa ka ce mana, kuma na ga dai ba aikenmu ka yi..."


Da sauri zaliha ta riƙe hannun ruma ta ce wa mutumin "Dan Allah ka yi haƙuri, baƙuwa ce ne a garin".


"Baƙuwa amma mara tarbiyya ko? Ba ta san nan ina ne ba? Kuma ba ta iya ladabin yin magana da manya ba, Meye wannan ta riƙo?"


Ruma ta ja da baya ta ce "Nifa ban gane ba, me na yi maka zaka ce mini mara tarbiyya? Mangwaro ne da masara" tayi maganar tana buÉ—e masa mayafin.


"Waye ya baki izinin É—aukar masarar?"


Ruma da haushi ya fara kamata ta dake ta ce "Yi haƙuri ban san gonarka bace, idan yayana ya zo ɗaukata daga birni zai baka kuɗin masararka, ni na tafi sai kun taho" ta ɗau kayanta tayi gaba.


Su kuwa jiki na rawa suka tsaya suna sauraren mutumin.


"Lallai dagaci, wato har da kawo baƙi marasa ɗa'a ba tare da ya nemi izini ba, har su zo su karya mana doka, to zai gane kuskurensa da mu yake zancen, ku wuce ku tafi".


Da gudu suka tafi gida domin sanar da abin da yake faruwa.


Suka tarar da iya na tuhumar ruma ina ta samo wannan kayan, amma tayi shiru ta ƙi magana.

Su zaliha ne suka kwashe komai suka gaya wa iya.


"Mun shiga uku ruma, ai mu garin nan ba a mana haka, a zaune muke ƙarƙashin umarnin 'yan bindiga, suke da garin, ki daina haka ba ruwanki da kowa, duk wanda ki ka gani a garin nan girmamashi to ba ruwansu da ke, amma idan ki ka yi musu rashin kunya sai su yi miki illa".


"To ku mayar da ni gidanmu mana, ni ba wanda ya isa yayi mini wani abu, dan ni ƙanwar maza ce zane mutum yayyena za su yi. Kawai sai ya ce mini mara tarbiyya shi tarbiyyar ce ta saka yake yi wa mutane magana a haka, ni a kano kowa ya san ina girmama mutane raini ne ban so, ni na zata ma mahaukaci ne".


Iya ta kwantar da murya ta ce "To na ji, amma dai dan Allah ki kula, bari Alhaji ya shigo zai je ya basu haƙuri, 'yan bindiga ne sai su illataki, muma bin umarninsu ne ya sanya muke zaune lafiya"


Ruma ta É—an yi shiru sannan ta ce "Wai iya su waye 'yan bindigar nan?"


"'yan tayar da ƙayar baya ne, Allah ne kawai ya san meye aƙidarsu"


Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Meye ƙayar baya kuma, sai ka ce wasu kifaye?"


"Ba zaki gane ba ko na yi miki bayani, amma dai bisa umarnin su muke zaune, sai abin da suka ce muke yi"


"To suma shugabanni ne zaɓarsu ake yi, na ji kin ce ba kwa komai sai da izininsu, ko 'yan sanda ne su?"


"Babu É—aya ruma, kawai dai ku yi ta mana addu'a, muna zaune ne dan kawai mun san ko mun bar nan ba in da zamu je, bamu da wurin zuwa"


Ƙwaƙwalwa ruma ta shiga wani tunanin na daban, ba ta kuma cewa komai ba, ta shiga wata sabgar.


Tana missing É—in gida sosai, ga wayarta ta mutu ba caji tama barota cikin kaya a gidan gwaggo.


Kullum da safe cikin bata rubutu da banka mata hayaƙi ake a gidan, wai maganin tsarin jiki na baki maita da aljanu.

Ruma kuwa ta ce ita ba zata sha wani rubutu ba, warin tawadar nan amai zai sakata. A kwanaki biyu kacal ruma ta fara buwayarsu, saboda sai ƙoƙari take sai ta aikata wani abu da zata tsokano mutanen nan.


Yau da yamma kasuwar ƙauyen take ci, dan haka suka shirya su uku zasu tafi kasuwa, iya tayi ta jawa ruma kunne a kan rashin ji da kuma yi wa mutane tsiwa, sannan ta basu kuɗi suka fita suka tafi.


Kasuwar ƙauye ce dai, amma ta burge ruma sosai da sosai, ga kayan gargajiya nan kala-kala.

Sai dai abin da ya bata mamaki, yadda ta kan ga wasu mutane masu rufaffiyar fuska suna kaiwa suna komowa, hannayensu saye a cikin rigunan su.


Shagon wani mai awo suka shiga suka zauna, za su sai wake, da alama su lawisa sun san shi, sai hira suke. Suna cikin hirar wani mutum yayi sallama suka amsa masa, ya shigo ya zauna, bai ce musu komai ba, suma kuma ba wanda ya tanka masa.


Ruma ta ce "Ni fa hausar nan taku dariya take bani".


Mai awo ya ce "to  hausar mu tafi daÉ—i ai, na ji kamar hausar kanawa ki ke yi ko?"


"Eh mana, ni 'yar kano ce, hausarmu mai daÉ—i, garinmu ma yafi naku kyau sosai da sosai"


Mai awon ya ce "Ai mu ma dan nan ƙauye ne, amma garinmu yana da daɗi da kyau".


Ruma ta yi dariya ta ce "Ba wani nan, garin naku da baku da iko da komai, wai sai an baku umarni mutum da kayansa, kano kuwa ba haka bane, abu idan naka ne naka ne kawai. Kuma ku ba damar baƙo ya zo sai a din ga tuhuma waye wannan, kano kuwa ba a haka?. Haka wani zanƙalelen mutum kamar mahaukaci ya tsayar da mu yana tambaya wai wacece ni?"


Zaliha ta ɗan daki cinyar ruma tana ƙifta mata ido, amma ruma taƙi shiru.


"Wai me awo suwaye masu yawon nan da rufaffiyar fuska kamar munafukai" a tare suka kalli ruma, sannan suka kalli mutumin nan na zaune.


"Ya naga kuna kallona kamar an ritsa mara gaskiya? Bawan Allah ko kai ka san su?" Ta yi maganar tana kallon mutumin


Ya girgiza kai ya ce "A'a, amma ina ga ko sune masu garin da ake faÉ—a".


"Wai sune 'yan ta'addan?"


Ya rausayar da kai ya ce "Wataƙila"


Ruma ta ce "Amma kuwa ba su kyauta ba, ba su yi wa kansu adalci ba, su dinga ƙwacewa mutane kaya, nima fa da zamu zo garin nan a kan bindigogi na zo, ina 'yan ta'addan ne a mota ɗaya muka hau da su"


Ya É—an waro ido ya ce "Haba dai, baki ji tsoro ba?"


Kamar ya kunna ruma, ta gyatta zama ta ce "Ni ban ji tsoro ba, a cikinsu fa wani har kaza ya sai mini, yayi kalar masu kirki, amma ban san meyasa suke kashe mutane ba, kullum a rediyon mama sai an ce sun kashe mutane, abun tausayi, ku yi ta Addu'a kuna musu nasiha, ko zasu daina".


Mutumin yayi murmushi ya ce "To shikenan, kuma kanawa ku tayamu da Addu'a, amma na yi mamaki da ki ka ce a kan bindigogi ki ka zo, kuma ba ki ji tsoro ba"


Ruma ta yi wani irin murmushi ta ce "Baka sanni bane ba, yayyena maza bakwai" ta yi maganar tana nuna masa da yatsunta.


Sannan ta ɗora da cewa "Ni ba komai ne yake bani tsoro ba, na ce musu dan Allah su buɗe mini in gani ko da gaske suke bindiga ce, kai ka ga yawan bindigar? Allah ya kyauta kawai" ta miƙe tsaye ta ce "Bari na je na sayo gyaɗa" tayi waje.


Lawisa ta yi ƙasa da murya ta ce "Zaliha tashi mu gudu kar yarinyar nan ta ja a harbemu a tsakiyar kasuwar nan".


"Ya ya za ayi mu gudu mu barta?".


Mai awo ya ce "Ranka ya daɗe ayi mata haƙuri baƙuwace kuma yarinya ce, ayi haƙuri dan Allah" mutumin bai ce komai ba ya cigaba da danna wata waya mai madannai.


Gaban mai gyaɗa marau ruma ta duƙa, tana saya wani mutum ya wuce tare da bigeta da wani abu, kuma ko waiwayowa bai yi ba yayi gaba abunsa.


Da gudu ta tashi ta bishi "Malam ka bugeni, ba ka ji ba na ce ka bugeni fa"


Ya waiwayo yana kallon ruma.


"Ba ka ji ka buga mini wani abu a bayana, kuma ba ka bani haƙuri ba"


Ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce "Ni ne zan baki haƙurin?"


"Eh mana, wani abu fa ka bugeni da shi a bayana, ai ka waiwayo ka bani haƙuri ko?"


Zai yinƙura kenan ya ji an danƙi hannunsa an ja shi. Wani mutum ne shima mai rufaffiyar fuska ya riƙe shi.


Cikin tsiwa ta ce "Bana yi wa manya Allah ya isa, amma wallahi ban yafe ba, Allah ya haɗaka da wanda yafi ƙarfinka kaima ya ci zalinka"


Idon kowa ya dawo kan ruma, ita kuwa ko a jikinta, ta koma ta sai gyaÉ—arta da ruwan leda, ta koma shagon mai awo.

Ko da ta koma, ta bi su ta  bawa kowa leda É—aya ta gyÉ—a, har da wannan mutumin da ya shigo ya zauna.


Ta kalli mutumin ta ce "ÆŠan uwanmu kana da 'ya'ya?" Ya jinjina mata kai alamar eh.


Ta kuma bashi É—auri biyu ta ce "To ka kai musu wannan, ga ruwa ma na baka. Ku kuma ku tashi mu tafi, 'yan garin nan ba su da mutunci, wani ya bugeni da wani abu a baya, kuma yaÆ™i bani haÆ™uri ni kuwa na masa Allah ya isa, kuma wallahi na koma gida sai na je na gaya wa 'yan sanda, abin da ske a  garin nan da abin da na gani ana yi! Sai na faÉ—i komai"


No comments