Kanwar Maza Book 2 Page 27

 Ayshercool.




paid book ne, ₦500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai shaidar biya ta 08081012143, masu buÆ™atar vip ko special kuma, suna iya garzayawa arewabooks ku searching sunan littafin*




Da fari bayan bayyanar rumaisa, mama ta zaci ruman nutsuwa ta ɗan ratsata, amma ina sai ta ga akasin abun da ta yi tsammani, halinta yana nan yadda yake, Aliyu na ƙwala mata kira amma ta rufawa takawa baya.

Murmushi ammi ta yi ta ce "Ƙyaleta, shi ma dai neman magana ne ya sanya ya ɗauke shi zai fice, da na san haka zai yi da ban bashi sabir ɗin ba".


Usman ya ce "Ai gara da ya hanata, ƙin gaishe shi ta yi, sai tambayarsa ina ɗan ta dan ba ta da kunya"


Mama ta girgiza kai ta ce "Rumaisa ai sai fatan Allah ya shirya. Hajiya ina wuni ina gajiya?" Ta yi maganar tana mayar da kallonta ga Ammi


Ammi ta ce "Lafiya lau Alhamdilillah, ya gida ya iyali?".


"Kowa lafiya ƙalau, ya kuma ƙarin haƙurinmu".


"Haƙuri mun gode Allah"


Mama ta ce "To Allah ya sa ta huta, Allah ya rahamsheta"


Ammi ta amsa da "amin ya rabb, ya jikin rumaisa kuwa ina fatan ta wartsake gaba É—aya"


Mama ta ce "Jikinta dai da sauƙi, amma taƙi sakin jiki kullum kuka ita sabir, yau ne ma ta ɗan saki jiki har da hira da ta ji an ce za a zo gaisuwa".


Ammi ta ce "Allah sarki rumaisa, Allah dai ya bata haÆ™uri" 


Hira suka ɗan shiga taɓawa da mama, har ammi take ɗan gutsura mata kaɗan daga cikin halin da take ciki, na dangane da ƙalubalen rasuwar aisha, daga ita har adam, haka nan ammi take jin yadda da mama a cikin ranta.


Rumaisa kuwa bin adam ta cigaba da yi, tana cewa ya bata É—an ta, amma yayi banza da ita ya cigaba da tafiya.


"Wallahi idan ba ka tsaya ka bani ɗana ba, sai na yi maka ihu na tara maka mutane" bai ko tsaya ba balle ta sanya ran zai kulata. Kan ta ankara tuni ya sulale ta wata ƙofar ta neme shi ta rasa.


Komawa ta yi falon da ta baro su mama tana kuka.


Duk suka bita da ido, ammi ta ce "Rumaisa lafiya? Menene?"


Cikin kuka ta ce "Ba guduwa yayi da sabir É—in ba, ina ta roÆ™onsa yaÆ™i kulani, ya bi ta wata Æ™ofa ya gudu" 


Ammi ta ce "Subhanallah, takawa fa wasu lokutan ba shi da girma sai na jikinsa, bari kan ku tafi zai zo har nan ya sameni"


Mama ta ce "Rabu da ita, yanzun nan zamu tafi, can gida ina ta baƙi, yan dubiya da jaje"


Ammi ta ce "Allah sarki, na zata zaku wunar mini, baku ci komai ba fa"


"Wallahi karki damu"


Rumaisa ta ce "Dan Allah mama mu É—an jira ko zai dawo ".


Aliyu ya ce "Ba in da zai dawo, ba dai ke fitsara ba, gara ayi maganinki ai"


Ammi ta yi murmushi ta ce "Yauwwa, dan Allah wata alfarma nake nema, idan Allah ya kaimu jibi, ina son a kawo mini rumaisa, za'a kaita wurin turaki, mahaifin aisha, abun da zai hana a kaita yanzu, haryanzu yana karɓar gaisuwa kuma yana cikin alhini, amma ya buƙaci ya ganta, ko zuwa jibi ne in Allah ya kaimu sai ko turowa na yi a ɗaukota".


Mama ta ce "Yayyenta za su rakota in Allah ya yarda, babu wata damuwa Allah ya yi mata rahama, ai ko bai nemeta ba ya ci taje ta yi masa gaisuwa "


Ammi ta yi ta yi wa mama godiya, da kanta ta raka su har harabar gidan, rumaisa kuwa sai kuka take yi, ammin tana bata haƙuri, tare da yi mata alwashin hukunta adam.


Ko da suka taho hanya, mita ta cigaba da yi tare da cewa da ta san ba zata ga Sabir ba da wallahi ba zata bi su ba, dan ita saboda sabir ta je.


Su Aliyu ne suka tanka mata, mama kuwa shiru ta yi mata, sai da suka je gida, ta dirar mata da faɗa, faɗan da tun da ta kuɓuta daga hannun yan ta'adda ba ta yi mata irinsa ba, sakamakon rashin hankalin da ta yi wa takawa yau.


Takawa kuwa ya kai awanni uku bai dawo ba, har wayarsa ammi ta din ga kira, yana É—akinsa ya kulle kansa da shi da sabir, sai da ya daidaici su ruma sun tafi, sannan ya mayarwa da su iman sabir, ya fice ba tare da ya bari ya haÉ—u da ammi ba dan kar ta yi masa faÉ—a a kan abun da ya yi.


Yana fita gidansa ya wuce, ya je ya kulle kansa, ya kashe wayoyinsa, dan baya ko son jin motsin wani a kusa da shi.

Rainin hankalin da rumaisa ta yi masa ne ya faɗo masa a rai, taƙi gaishe shi, amma ta biyo shi tana kiran ya bata ɗan ta, wani gajeren tsaki yayi ya nemi wuri ya kwanta tare da lumshe idonsa.


Da magariba mama take bawa su Abdallah labarin yadda suka yi a gidan su takawa da suka je gaisuwa, da abun da rumaisa ta yi, suka yi mata caa suna yi mata faɗa, ita gaba ɗaya faɗan da suka yi mata bai dameta ba kamar takaicin rashin ganin sabir, ji take da zata ga Adam ta shaƙe shi ta huta.

Mai sunan baba da yake jin hirar ta su bai ce komai ba, ya kalli in da rumaisa take ya ga sam hankalinta baya kan faÉ—an da suke yi mata, baya raba É—ayan biyu ya san ba zai wuce tunanin Sabir take ba.


Gyaran muryar da ya yi ne ya sanya su waiwayowa suna kallonsa.


Cikin kakkausar muryarsa ya ce wa rumaisa "Ki nemo uniform ɗin ki kafin ranar monday in Allah ya kaimu, zan je mu yi magana da shugaban makarantar ku zaki koma makaranta" turus rumaisa ta yi, dan har ga Allah ita ba ta ƙaunar makaranta a ganinta kawai salon uzzurawa rayuwarta ne.


Usman ya ce "Amma mai sunan baba bai yi wuri ba? Yakamata a bari ta gama warwarewa"


"Ba wata warwarewa da zata kuma yi, makaranta za ta koma, daga boko har islamiyya" yadda ya yi maganar very serious, ya sanya kowa jan bakinsa ya tsuke, rumaisa ji ta yi kamar ta fasa ihu, dan ba ta ƙaunar makaranta ko kaɗan.

Daga bisani ta ajiye tunanin komawa makaranta, ta sanya tunanin yadda za ta yi ta ga Sabir a gaba.


Samha ba irin tunanin da ba ta yi, a kan yadda za ta samu burinta ya cika a kan Adam, tun da yanzu dai wadda za ta zame mata matsalar ta kau, so take yi ta samu wata kafa da za ta sanya ace ta maye gurbin aisha a wurin Adam.

Ko da ta je ta yi wa mahaifinsu gaisuwa baya walwalar da zata sanya ta kawo masa zancen abun da yake ranta.

Rashin samun mafita ya sanya ta shirya ta tafi gidansu takawa, wurin babbar aminiyarta Fauziyya.


Bayan da Samha ta gama gaya mata abun da ke ranta, Fauziyya ta ce "Lallai Samha kina da matsala, a wannan yanayin da ake ciki, ana tsaka da jimamin mutuwar zaki ce ga buƙatar ki, ai wannan sai ace ma ke ki ka kasheta".


"Allah ko? Wallahi na rasa yadda zan yi ne Fauziyya, yadda ki ka san in É—aura mana auren da kaina, wata dama ce fa da na daÉ—e ina jira, kawai sonake na yi amfani da ita ko ta yaya".


Fauziyya ta ce "Aikuwa kwaɓarki za ta yi ruwa, ke kin san yadda mai girma turaki yake ƙaunarta, daga mutuwarta ki zo masa da kina son mijinta, ashe kuwa kin taro aradu da ka".


Samha ta yi wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta ce "Hmm ba dan idon mutane ba, ai mu mutuwarta abun farinciki ce a garemu, ko banza mayi 'yan ci mu samu ya din ga yi mana kallon 'ya'yansa mu ma. Yanzu dai ba wannan ba, fauzi meye abun yi?"


"Yanzu ai baki ga ta neman abun yi ba, har sai Allah ya sa an kammala zaman makokin nan, ki ga in da mai girma turaki zai sanya gaba"


"Zan iya jiran nan kuwa Fauziyya, kar na sake rasa wannan damar?"


"Aikuwa idan ba zaki jira ba, zaki jawa kanki magana"


Samha ta É—an yi shiru sannan ta ce "Haka ne, yanzu tashi mu je sashin su takawar na ga jaririn dai".


Fauziyya ta ce "Saboda me, da an so mu ganshi ai ba za a din ga É“oye shi ba".


Samha ta riƙo hannunta ta ce "No, kar ki yi mini haka mana, ai duk cikin salo ne shi ma, dan Allah taso".


Haka Samha ta lallaɓa Fauziyya suka tashi suka nufi part ɗin Ammi.


Hadiman ammin suka tarar suna ta aikace-aikace, Fauziyya ta yi musu umarnin da su yi musu iso a wurin ammi.


Mintuna biyar, sai ga hadimar ta dawo, ta ce su shiga.


Kamar na kirki haka suka shiga a kame, a falon sashin suka tarar da ammin a zaune, suka gaida ammi, suka sake yi mata gaisuwa sannan Fauziyya ta ce "Ammi, dama zuwa muka yi mu ga jaririn, tun da Allah ya sa aka yi rasuwar nan babu wanda ya ganshi"


Ammi ta É—an yi shiru sannan ta ce "Akwai dalili ne, bashi da cikakkiyar lafiya shiyasa ba a son kowa ya din ga É—aukar sa, amma bari in sa a kawo muku shi".


Wayarta ta É—auka ta kira iman a waya, ta ce mata ta zo da sabir falonta tana son ganinta.


Daga cikin bedroom É—in ammi iman ta fito, nusaiba na biye da ita, sai dai kallon da samha ta yi wa iman, ya sanya iman saurin kawar da kanta gefe.

Ta ƙarasa gaban ammi ta ce "Ammi gani".


"Ina sabir É—in? Su Fauziyya ne zasu ganshi".


Iman ta ce "Ammi bacci yake yi, kuma kin san likita ya hana É—aukarsa, sai dai mu shiga su ganshi a  net


Nusaiba ta ce "A net ɗin ma dan dai su ne, amma ba shi da cikakkiyar lafiya" da ƙyar samha ta danne fushinta, suka bi su iman ɗakin ammi, Sabir yana cikin net ɗin sa sai bacci yake yi, yayi ƙalau da shi.


Samha ta kwaɓe baki, dan haka kurum ta ji ta tsani ɗan, ta ce "Ammi bari mu je, idan ya ji sauƙi sai a bamu mu ɗauka".


Ammi ta ce "Ku yi haƙuri fa, likita ne ya saka wannan dokar"


Fauziyya ta ce "Bakomai ammi, Allah ya raya shi" da haka suka fito, suna fitowa Fauziyya ta ce "Aikin banza da ki ka takura mu je, gashi nan a wulaƙantamu a banza ai"


"Ke ni ba wannan ba, zuwa na yi da niyyar in nuna nafi kowa ƙaunar yaron, amma ina ganinsa na ji na tsaneshi wallahi, wai meya hana ya bi uwarsa ya mutu ne shi ma?"


"Aikuwa ki ka kuskura aka gane ba kya son yaron nan, ke da Adam har abada" Samha ta ja tsaki ta ce 'Dole zan daure zuwa lokacin da burina zai cika, shegen yaron kyau kamar ubansa, na so da wani yayi kama ace É—an shege ne ma, tunda ba wanda ya san ta na da ciki, duniya kowa ya san ciki baya zama a mahafairta kamar rariya haka take"


"To ni dai shawara nake baki, kar ki É“ata rawarki da tsalle, ki iya takunki"


"Ohhh Allah, to shikenan zan bi komai a sannu, amma a wannan karon adam ba zai kuɓuce mini ba"


Bayan fitar su Fauziyya kuwa, bin su iman da kallo ammi ta yi ta ce "Mai ya sa zaku hanasu É—aukar yaron nan, suma ai É—ansu ne"


Nusaiba ta ce "A'a ammi, ta idonka daban ta bayan idonka daban, dole ayi kaffa-kaffa da sabir, ba kowa ne ma yakamata ya din ga zuwa wai ya zo ganinsa ba, kin san komai ammi".


Ammi ta jinjina kai ta ce "Haka ne, Allah ya iya mana"


Suka amsa da Amin.


Rumaisa kusan tun da suka dawo daga asibiti, sai ta yi mafarki gata a wurin su sule, ta yi ta zabure-zabure, tana ihu, sai mama ta riƙeta tayi mata adduoi, gashi kullum ta zauna ba ta da zance sai na Sabir ɗin ta.

Duk tsananin surutu irin na rumaisa, ta ƙi sakin jikinta ta bayar da labarin abun da ya faru da ita a hannun 'yan bindiga, da an fara zancen kuma sai ta yi shiru taƙi magana.


Yau shine ranar da suka yi, za a kai rumaisa wurin turaki, dan tun da safe ammi ta kira wayar mama, maman ta tabattar mata da za a kawo rumaisan.

Da safe bayan ruma ta cakali abinci, mama ta sakata tayi wanka, dan da fari taurin kai ta fara, wai ba zata je ba, sai da mama ta yi da gaske sannan ta shirya.


Mama ta kalleta a tsanake ta ce "Rumaisa" ta É—ago ta kalli mama.


"Gaban babban mutum zaki je, kar ki je ki nuna masa halinki na rashin hankali, tsaf zai saka a zaneki, wurin mahaifin ita mai rasuwar za a kai ki, ya ce yana son ganawa da ke, saura ki je ki yi masa rashin hankalin naki da ki ka saba, ko kuma kina ji ana tambayarki abu, ki ƙi bayar da amsa, ki ka dawo mini gidan nan sai jikinki gaya miki, ki ka kuskura ki ka yi rashin ɗa'a zaki ga yadda zan yi da ke. Usman ka saka mini ido a kanta, duk abun da ta yi na rashin ɗa'a ka zaneta tun a can"


Ya jinjina kai ya ce "In sha Allah" ita dai ba ta ce komai ba, ta tashi ta É—auko facemask É—in ta ta saka, usman ya tasata a gaba suka fita.


Duk wanda ya gansu a hanya, sai ya tsaya ya sake jajanta abun da ya samu rumaisa, da masu son bugun cikinta su ji yadda aka yi, duk tayi mirsisi taƙi magana, kai ka ce shiriya ce ta zo mata.


Adam tun safe yana gida, yana jiran zuwansu rumaisa, dan ya kai su wurin turaki, amma ba su zo ba sai azahar.


Suna sanya ƙafa a cikin falon, ƙamshin turarensa ne ya fara dukan hancin rumaisa. A hankali ta ɗaga kai aikuwa ta hango shi a zaune, ya kashingiɗa ya lumshe idanunsa.


Ammi ta faÉ—aÉ—a murmushinta, tare da yi musu sannu da zuwa. Sam rumaisa hankalinta ba ya kan su, ko gaida ammi ba ta yi ba, sai waige-waige take yi.


Ammi ta ce "Rumaisa ai kya bari mu gaisa, kan ki fara neman ɗan naki ko?" Rumaisa ta durƙusa ta ce "Ina wuni?".


Ammi ta ce "Na ga dai hankalinki baya nan, bari yanzu zasu kawo miki shi".


Rumaisa na jin su suna cigaba da gaggaisawa, amma ta kasa zama, kawai jira take ta ga ta ina za a fito da sabir.


Usman suka gaisa da takawa, yake tambayarsa ya mama ya ce masa tana nan lafiya.

Kamar mai shirin zarewa, suka ga rumaisa ta tashi ta nufi Nusaiba, tana zuwa ta karɓe sabir daga hannunta, nusaiba ta bi rumaisa da kallo, dan ba ta san wacece ba.


Ta rungumo sabir ta zauna da shi a wurin, kawai ta saka kuka "Sabir ɗina, ka ganni, ka gane ni? Ka yi missing ɗina ko? Kullum sai na yi tunaninka, kullum sai na yi mafarkinka, bana iya cin abinci ma kullum ina tunaka mai sunan babana, wallahi ina sonka sosai, ƙwace mini kai aka yi" ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani irin kuka, da yake bayyanar da tsantsar damuwar da take ciki.

Abun ka da uwa, take jikin ammi ya yi sanyi, ta ji hawaye sun cika mata ido, tausayin rumaisa ya kamata, amma ta dake ta ce "Haba rumaisa, ai kowa ya san Sabir ɗanki ne, babu mai rabaki da shi, ki daina kuka kin ji, nusaiba saka a kawo musu ruwa ma, da abun taɓawa".


Nusaiba kuwa tsananin mamaki ne ya cikata, yanzu wannan 'yar yarinyar ce ta yo jigilar jariri har ta kuɓutar da shi, iko sai Allah.


Sabir kuwa ƙura wa rumaisa ido ya yi, ko ɗan ɗauke kai ta yi, sai ya bita da ido kamar zai yi mata magana. Murmushi take yi masa, hawayenta na ɗiga a kan kayansa ta ce "Ka gane ni? Na da muka taho tare daga dajin nan? To nice nan rumaisa mamanka, ka din ga ce mini ko mama, ko umma ka ji ɗan albarka".


ÆŠan lumshe ido sabir yayi kamar zai yi barci, sai kuma ya washe mata bakinsa gaba É—aya yayi dariya.


Cikin matuƙar farinciki ta ce "Yaya usy, yayi mini dariya wallahi, kalli ka ga ya gane ni".


Usman ya ce "A'a ba wani ganeki da yayi, bacci zai yi haka jarirai suke bacci".


Haka aka jere musu kayan abinci, ruma ta koma gefe taƙi cin komai, sai wasa da take yi wa sabir, shi kuwa takawa satar kallonta kawai yake yi, wata ajiyar zuciya da take yi, kai ba ka ce ba ɗan ta bane ba.


Adam ya numfasa ya ce "Ina ga mu tafi, rana na cigaba da yi".


"Ni dai ku je ku dawo, kan nan na ga sabir sosai".


Ammi ta ce "Rumaisa, ai zuwan naki ne, ke yake son gani, ki yi haƙuri in Allah ya yarda da kaina zan din ga sawa a kawo miki sabir kin ji".


Kallonsa ta cigaba da yi tana kuka, Adam kuwa ya taso, yazo kanta ya durƙusa zai ɗau sabir.

Riƙe shi ta yi gam tana kuka, ya saka hannu ya ɗauke sabir ɗin ya bar ta da towel.


Riƙe towel ɗin tayi ta cigaba da kuka, ammi gaba ɗaya ta rasa me zata cewa rumaisa, sai da a ranta ta ji tsoron kar su shiga hakkinta wani ciwon ya kamata saboda ƙwace yaron nan.


Haka nan sai ammi ta ji nauyin rumaisa, ta ma rasa me zata gaya mata ta rarrasheta.


Nusaiba kanta wani irin tausayin ruman ne ya kamata, ta tashi ta bi bayan Adam bedroom É—in ammi.


Ya dubi nusaiba ya ce "Ku kula da kyau, kar a sake fito da shi, ina iman take?"


Jiki ba ƙwari Nusaiba ta ce "Ta sha maganin mura ne, tana ɗakinta tana bacci"


Ya miƙe mata sabir, sannan ya fito ya dubi usman ya ce "Mu je ko".


Ammi ta kasa cewa komai, sai riƙo hannun rumaisa, zuwa babban falo, ta ce "Rumaisa, ni dai ina kuma baki haƙuri, na san mu masu laifi ne a wurinki, amma ki yi haƙuri ki mayar da hankali a kan makaranta, in dai sabir ne bamu isa mu rabaki da shi ba, tunda ɗanki ne"


Baba Uwani ce riƙe da tsintsiya a hannunta, ta biyo bayan ammi, ta washe baki ta ce "Uwar ɗakina baƙi ki ka yi haka ne?"


Ammi ta waiwaya ta ce "Eh, dama ina nemanki" ta mayar da idonta kan rumaisa ta ce "Rumaisa, ki gaida mini da mamanki, akwai saƙonki a wurin takawa, ki yi haƙuri ki yi ta addu'a kin ji yarinyar kirki" rumaisa kawai jinjina kai ta kasa, ta bi bayansu takawa.


Usman har cikin ransa yake jin babu daɗi kukan da rumaisan ke yi, adam kuwa jinjinawa azababben ƙarfin halin rumaisa yake yi.


Ba wanda ya kuma juyowa tsakanin shi da usman, sai dai suka fita haraba wurin motar da za su hau, sannan suka waiwaya ba su ganta ba.


Usman ya ce "Kaii, ina yarinyar nan ta tsaya kuma?".


Adam ya ce "Bari na je na duba, ina zuwa "


Ya ja da baya ya koma in da suka biyo.


A zaune ya tarar da ita, bayan wasu bishiyu, ta cukuikuye a cikin hijjabinta, tana kuka mai É—an sauti kaÉ—an.


"Ke!" Ya yi maganar cikin tsawa. Ta zabura ta É—ago ta kalleshi, da sauri ta tashi tsaye.


A ɗan ƙufule ya ce "Meye haka muna tafiya zaki ja ki tsaya? Sauri fa nake bani da lokaci".


Wani mugun kallo ta yi masa ta ce "To ina ruwana da rashin lokacinka, ni fa ba a son raina na zo ba in gaya maka, kuma wallahi babarku tana son bani sabir, kai ne ka dage ka ƙwace mini ɗa, kuma sai ka bani ɗana ko ba ka so, ko kuma ka ga matakin da zan ɗauka".


Adam ya ƙare mata kallo ya ce "Idan aka baki shi, gaya mini da me zaki shayar da shi? Kalleki fa".


"To ai dai na ga ba shayar da shi ake yi ba, madara ake bashi, kuma idan na girma na zama babba sosai zan dinga shayar da shi".


Ya girgiza kai ya ce "An daina ba shi madara yanzu ai, ni nake shayar da shi, tunda na san nesa ba kusa ba, na fiki abun bashi, tashi ki wuce mu tafi".


No comments