Kanwar Maza Book 2 Page 23

 



Bashir ya ce "A'a, ba sai an kai ga amfani da ƙarfin tsiya ba, zata yi magana a hankali, ƙuriciya ke da


munta, amma duk da haka kamar akwai wata 'yar tsama tsakaninka da ita, yanayin abubuwan da take yi maka, kamar da gayyya take yi maka".


Adam ya É—an yi guntun tsaki ya ce "Manta da ita kawai, sai gobe in Allah ya kaimu, X-ray É—in na ta babu wata matsala?"


Bashir ya ce "Ai na gaya maka sai gobe in Allah ya kaimu likitan zai duba".


"Allah ya kaimu"


Bashir ya amsa da "Amin".


**

Nusaiba tun da ta ji abun da yake faruwa, ta rasa nutsuwarta, ko abincin kirki ba ta iya ci. Yanzu haka tana tsaka da tunanin da ta saba ta ji Iman ta dafata "Anty Nusaiba" Nusaiba ta É—an zabura sannan ta sauke numfashi ba tare da ta ce komai ba.


"Anty Nusaiba tunanin me ki ke yi haka ne?"


"Bari kawai Iman, tun da Ammi ta gaya mana zancen nan, na kasa nutsuwa ina tausaya mana idan zancen nan ya fita, kin san yadda aka samu a gaba da ma a masarautar nan, ƙiris ake jira wani abu ya faru, to ga wannan babbar magana gaba ɗaya na kasa nutsuwa, idan har ba Anty Aisha aka gano ba, wallahi muna cikin tashin hankali".


"Haka ne, amma babu abun da ya gagari addu'a anty nusaiba, kuma babu ta yadda muka isa mu kaucewa ƙaddara, in sha Allah babu abun da zai faru".


"Iman, na san kina dakewa ne kina ƙoƙarin kwantar mini da hankali, amma kar ki manta abun da aka gaya wa mutane a kan barinta ƙasar nan, kin san yadda aka sako yaya Adam a gaba, yanzu idan maganar nan ta fasu, babu irin sharrin da ba za ayi masa ba ba shi ba har Ammi da mu baki ɗaya. Shiyasa ni tun farko ban so hukuncin da ammi ta yanke ba, tun da komai muƙaddari ne" ta ƙarasa maganar tana kuka.


Iman ta rungumeta ita ma tana zubar da hawaye ta ce "Na sani Anty Nusaiba, amma Ammi uwa ce, duk abun da zata yi, tana yi ne dan bamu kariya da wanzuwar farincikinmu, kuma in sha Allah ƙoƙarin ta ba zai tafi a banza ba, komai zai zo ƙarshe da yardar Allah, ki daina damuwa, komai zsi zo da sauƙi, ai babu abun da ya gagari Allah" suka cigaba da kuka iman na rarrashin Nusaiba.


Baba uwani ce ta shigo tana sallama, tare da zuro kai. Da sauri suka gyara iman ta amsa mata.


Ta dubi iman ta ce "Uwar É—akina lafiya kuwa?".


Iman ta ƙaƙalo murmushi ta ce "Lafiya lau baba uwani, akwai wani abu ne?"


"Ni fa na kasa gane muku gaba É—aya, giwa ta daina walwala, mai gida ma haka, kuma gashi na tarar kuna kuka, dan Allah me kuke É“oyewa ne meyake faruwa haka? Gaba daya gidan babu daÉ—i, babu wata walwala saboda yanayin nan da ku ke ciki" Ta yi maganar tana neman fashewa da kuka.


Nusaiba ta ce "Baba Uwani babu wani abu kar ki damu".


Cikin damuwa iman ta ce 'Dan Allah kar ki yi kuka baba uwani, komai zai daidaita ba wani abun bane ba, Ammi jikinta ne ya ɗan tashi shiyasa bata walwala, kuma kin san walwalarta ce ta mu, kar ki yi kuka Please" baba Uwani ta matse ƙwalla ta ce "To shikenan, Allah ya bata lafiya, ya sanya komai lafiya, ya jishe mu alkhairi" tana gama maganar ta juya ta fice.


Iman ta ce "Allah sarki baba uwani, tana sonmu da yawa, bana son in ga masu shiga damuwar nan suna ƙara yawa, Allah ya bamu mafita, ina shirin gaya miki wani abu, wannan maganar ta kunno kai".


Nusaiba ta dubeta ta ce "Wane abun?"


"Ki bari wannan matter ta yi settling, zan gaya miki".


"No, kin san ba zan jure ba, ba zan iya jira ba, ki gaya mini yanzu kawai".


Iman ta ja numfashi ta ce "Kin san me uncle J ya ce mini?"


Nusaiba ta girgiza kai ta ce "Sai kin faÉ—a".


"Wai so na yake yi, kuma ko ban amince ba zai bi ta in da ya san za a bashi ni"


Nusaiba ta yi murmushi ta ce "Ni na san a rina ai, take-takensa duk ya gama nunawa, amma ke mai ya sa na ga kamar ba kya son shi ne? Mai uncle J É—in ya yi?"


Iman ta É—an murza zoben hannunta ta yi shiru.


"Do you still loves him?" Nusaiba ta yi maganar tana kallon fuskar Iman.


Iman ta É—an waro ido ta ce "Who?".


"Your recent ex, É—an......"


"Shhhhh" iman ta katseta.


"Kar mu kai ga nan Please, mu bar maganar ma kawai"


Baba uwani kuwa da ke laɓe a ƙofar ɗakin, jin sun sauya hira ya sanya ta tafi tana tsaki "Aikin banza jarababbu, sun ƙi yin maganar gaba ɗaya, zancen da suka yi kuma, idan na kai mata ba so take yi ba, aikin kawai".


***

Adam yana kwance ya ƙura wa roofing ido, sai ya tuna Jabir, abun da yayi masa ɗazu ya tuna, sai ya ji bai kyauta ba, jabir a komai yana tsaye a kan lamuransa, bai kamata ya yi masa haka ba, kuma jabir mutum ne mai kaifin tunani da hangen nesa, sanin ko ya so ko bai so ba zancen zai fit6, ya yanke shawarar ya yi wa jabir zancen, mussaman da suna tare Ruma ta yi masa abun da ta yi masa da farko, tare da saka ran Jabir zai iya samo masa mafita.

Da sauri ya tashi ya fita, ya É—au mota ya tafi gidan Galadima mai ci.


Sai dai tun a hanya yake kiran wayar Jabir ya ƙi ɗagawa, ya je gida ya tarar Jabir baya nan, sarai ya san in da zai same shi, dan haka bai tsaya ko ina ba sai can.


Ko da Jabir ya ga Adam, ƙoƙarin share Adam ɗin ya yi amma ya kasa.


"Wurinka na zo" Adam yayi maganar yana duban idon Jabir.


"Ina jin ka" jabir yayi maganar yana basarwa.


Adam ya sanya hannu ya É—ago Jabir da kwalar rigarsa, ya ja shi suka fita waje.


"Wai meye haka ka ke yi?".


Adam ya tsuke fuska ya ce "Yaya na zo wurinka in ce wurinka na zo, ka shareni ba ka fini mulki da jin kai ba, na san ka sani".


Jabir ya kalli Adam ya ce "Har ka manta few hours ago abun da ka yi mini?".


"Forget about it, just feel like to share it you"


"Ka riƙe sirrinka, tun da bai kamata na sani ba".


Adam ya dafa kafaÉ—ar Jabir ya ce "Kar ka yi mini yawa mana, yakamata ka saurareni".


"Ina jin ka"


Adam ya É—an yi shiru, sannan ya gaya wa Jabir abun da yake faruwa.

Sak jabir yayi, gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, wani irin gumi ya shiga tsatsfo masa ya ce "Takawa, wannan fa ba ƙaramar magana ba ce, case ne mai girman gaske, ni gaba ɗaya sarƙaƙiyar nan ta yi yawa, na kasa ganewa gaba ɗaya, an ce Aisha zata tafi ƙaro karatu, kuma tana Saudiyya rainon ciki, ta dawo ba wanda ya sani an yi garkuwa da ita, ta haihu jariri ya kuɓuta ita ba a san in da take ba, wannan zancen kamar film ko almara ni ban gane ba".


Cikin matsananciyar damuwa Adam ya ce "Bar shi a baka gane É—in ba, ka san wacece ta zo da yaron?"


Jabir ya girgiza kai, Adam ya ce "Wannan yarinyar da ta zageni a social media, da na yi niyyar hukuntawa ka hanani".


Jabir ya waro ido kamar su faÉ—o ya ce "Again? Ita a ina ta samu jaririn naka?"


"Wai kai Jabir anya ka ci waec kuwa? Duk bayanin da nake baka ganewa, amma ni babban mamakina bai wuce yadda yarinyar nan take manne da ƙaddarata ba, ita ma an yi garkuwa da ita watannin baya, Bashir ne ya tsinceta a Katsina, a hanyar kai kuɗin fansar aisha, ta zo da ɗankwalin aisha wanda ya ƙara tabattar mini ba ƙarya take yi ba, sai dai duk yadda muka kaɗa muka raya taƙi faɗar komai a kak aisha, kamar tana amfani da hakan ta rama abun da na yi mata ne".


Zamewa jabir yayi ya tsuguna yana maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Adam kuma yana tsaye yana murza yatsunsa ya na jin yadda hawaye ke cika masa ido.


Sai da Jabir ya gama salallaminsa, sannan ya tashi tsaye, ya dubi Adam ya ce "Yanzu ba lokacin tattauna wata magana ba ce, babu isasshen lokaci, dole a nemo in da aisha take kan kowa ya ji wannan zancen, gashi ka ce sun daina kiranka a kan kuÉ—in fansarta".


Adam ya jinjina masa kai alamar eh.


"Ka ga, maza mu je mota, muje Asibitin".


Haka Adam ya É—auki Jabir suka tafi wurin rumaisa.


A can unguwa kuwa, mama na nan suna ta fama da jinyar rumaisa, amma maganar jaririn nan ta cika gari, kasancewar mama babu wanda suka yi wa bayanin in da rumaisa ta samo jariri, ko a 'yan uwa ba kowane ya sani ba.

Wasu suka din ga cewa ciki rumaisa ta yi, shi ne aka kaita wani wurin ta haihu, dama wannan shegiyar fitinarta ta da rawar kai ta yi yawa, tsaf zata aikata, ba su yi la'akari da irin raunukan da suke jikinta ba, wasu ma cewa suke yi, ba wani saceta da aka yi, rainon ciki ta yi. Ya yin da wani sashen suke cewa gaba É—aya rumaisa ba ta yi kama da wadda ta É—au ciki ta haihu ba, dan a yadda take É—in nan, idan ma cikin ne, abu ne mai wahalar gaske ace ta iya haihuwa da kanta, haka unguwa ta É—auka, wasu suna sukarta, wasu suna bata kariya, sai dai su mama sam basu sani ba, dan ko a gari babu wanda ya iya tarar zaratan samarin nan ya yi musu zancen.


Yanzu ma mama na ta shirin su kwanta, ruma ta sha magungunan ta, tana ta shafa dogon gashin jaririnta, tana kallon dogon hancinsa.


"Meyasa ka yi kama da babanka, dama babarka ka yi kama, da ka fi haka kyau boy na" ta yi maganar tana kissing É—in sa a goshinsa, tana murmushi da jin soyayyar Sabir na shiga zuciyarta.


Yaya Abubakar ya dubeta ya ce "Mama boy, zan tafi gida, gobe in Allah ya kaimu zan biyo mu yi sallama, zan koma school zamu fara exams".


Ruma ta É“ata fuska ta ce "Dan Allah kar ka tafi, bana son ka tafi".


"Ki hi haÆ™uri, exams É—in nan ce zata saka na koma, ba dan haka ba a kusa da ke zan kasance in ta kallonki gudan jinina" 

Ta yi murmushi ta ce "Allah ya bayar da sa'a" 


Mama ta ce "Ka zo ka tafi kar ka yi dare" 


"To mama, ban gaji da ganinku bane" kan mama ta yi magana Adam suka shigo.


Ruma ta kawar da kai tana faÉ—in "Innalillahi wa Innalillahi raji'un" domin ta gaji da ganin takawa, da kullum sai ya zo sau biyu, kuma duk zuwa sai ya É—aga mata hankali a kan ta gaya masa in da Aisha take.

Ba ta ƙara haɗe rai ba sai da ta ga Jabir, sarai ta gane shi, da shi aka haɗa baki Adam ya ɗaukota yayi mata wulaƙanci.


Cikin girmamawa suka gaisa da ammi, yayin da jabir ya ƙurawa rumaisa ido, da ta haɗe rai.


Suka gaisa da Abubakar ma, da yake tsaye yana shirin tafiya.


Mama ta ce "Ana ta ɗawainiya da rumaisa fa, mun gode sosai Allah ya yi albarka, ya shiga lamarin ka ya kareka da ga sharrin maƙiya".


Adam ya ce "Bakomai mama, yi wa kai ne, ki daina godiya ma, addu'a muka fi buƙata"


Rumaisa a ranta ta ce "Ji shi, wai mama sai ka ce babarsu, dan tsabar kuturun iyayi, wallahi mamanmu ce kawai" ta yi maganar a zuciyarta.


Abubakar ya ce "Ruma baki iya gaisuwa bane?"


Ta ɗago ta ce 'Au wai baƙi mama ta yi, sannunku"


"Ya jiki kuwa?" Jabir yayi maganar yana kallon ruma.


"Da sauƙi".


"Ai da yake ban san meyafaru ba, sai yau, shiyasa bamu zo da shi na dubaki ba, mu ga jaririn"


Maimakon ta miƙo shi, sai saka hannu ta dafe shi, tana harare-harare.


Abubakar ya matsa ya ɗauko masa jaririn, ya bashi sannan ya fara yi wa ruma mita "Wai ke wace irin yarinya ce ne? Ke shikenan ba wanda zai taɓa yaron nan sai ke, ke da kece uwassa ban san yadda za'ayi ba".


"To ai nice mamansa, ai dai bar mini shi ta yi".


Ya ce "Ke tafi can, ke ma É—in ai Haryanzu rainonki ake yi, mama bari na wuce na je gida na haÉ—a kayana"


"Yaya Sadik, sai da safe ka gaishe da su"


"Ba yanzu duk suka tafi ba, duk kuna tare sai da safe, ban da yi wa mama rigima dan Allah, a bari sai mun zo mu ayi mana" murmushi ta yi Abubakar ya kama hanya ya fita.


Jabir ya zubawa yaron ido, Adam da ke zaune a gefensa ma, ya zuba masa ido yana saƙa abubuwa daban daban a ransa.


Mama ta juya tana amsa waya, ruma ta lallaɓa a hankali ta sauko daga kan gadonta, ta saka hannu ta ɗauke jaririn daga hannun jabir, a gabansa ta ce "A'uzubi kalaimatillahi tammat" ta ƙarasa gadonta ta kwantar da jaririnta, ta hau gadon tana ta haɗe fuska.


Adam ya É—an kalli jabir, kallon irin ka gani ko?.


Jabir ya girgiza kai ya ce "Rumaisa, na ji duk abun da ya faru, ina fatan Allah ya tsare gaba, amma yakamata ki bayar da haɗin kai wurin kuɓutar da maman yaron nan in dai kina ƙaunar ɗan ta da gaske, da haka zaki tabattar mana son gaskiya ki ke wa ɗan ta".


A wulaƙance rumaisa ta kalli Jabir ta ce "An gaya maka ina abu dan na burge mutane ne? To kar Allah ya sa ku yadda ɗin mana ina ruwana, wataƙila shi sai in gaya masa kai ban gaya maka ba, mugwaye kawai, kuma ni ba dan ta bar mini jaririn nan ba, ba abun da zan yi da ɗan ku, dan ni bana ko ɗaukar yara, idan aka bani riƙon ɗa ma, mintsini yake sha da cizo, wannan kuwa ɗana ne, ba wanda ya isa ya ƙwace mini shi ehe" ta yi maganar tana fari da murguɗa baki".


Jabir ya ce "Kan uba, haka ki ke?"


"Ai na fi haka ma, idan kun gama zaman kwa tafi, ko ku cigaba da zaman jirana in gaya muku in da take,  tun da ni na saceta" tana gama maganar ta juya ta kwanta.


Jabir ya riƙe haɓa yana jinjina kai, Adam kuwa tuni ya fusata ya tashi fuuuu ya bar ɗakin, a waje ya tarar da mama yayi mata sallama suka wuce.


A mota Jabir yake cewa Adam "Ban taɓa zaton azabar taurin kan yarinyar nan ya kai haka ba, ji yarinya ƙarama da iya shege".


"Shawarar da bashir ya bayar, ita ce last option ɗina, idan taƙi ba da haɗin kai, zan yi abun da ba ta zato" a haka suka tafi gida suna tattaunawa.


Washegari da safe Ammi ta shirya, zata asibiti Nusaiba da Iman sun so bin ta, amma ta ce a'a su yi haƙuri ba yanzu ba, ta saka aka sheƙa girki, ta saka a mota, tana shirin shiga motar su tafi, ta ji yo muryar Mummy "Giwa, waye Babu lafiya ne na ganki da kulolin abinci da safiyar nan? Ko wani ne a cikin yaran amma ki ke ɓoye mini?"


Ammi mamaki ne ma yakamata, ya aka yi ta fito da sassafe haka, har ta ganta.


'Ba É—aya yara duk suna lafiya, wani abu ne mai muhimmanci" daga haka Ammi ta shige motar, ba tare da sake tanka Mummy ba.

Mummy ta riƙe ƙugu ta jinjina kai ta ce "Lallai ta tabbata akwai abun da ki ke ɓoyewa giwa, kuma da alama yana da muhimmanci a wurinki, bari mu ga idan na bankaɗo ko menene in da zaki saka kanki, zan saka a bi bayanki, domin ganin in da ki ke zuwa"


Rumaisa tana jin zuwan Ammi, suna ta hira ita da mama, amma ta yi bakam kamar bacci take yi, alhalin idonta biyu maganar ce kawai ba ta son yi.

Sai da likita ya shigo, sannan ta tashi suka gaisa da Ammi, likita ya duba X-ray ɗin ta ya ce babu wata matsala, haƙararin nata ma buguwa ce kawai, zai rubuta mata magani.


Mai sunan baba ma tuni sun zo, tare da Abubakar ya biyo yayi musu sallama zai koma makaranta.

Ammi take tambayar mama ko 'yan biyu ne saboda kamanin da suke yi, ba ta gane su, kawai dai ta lura da É—aya yana da fara'a É—aya baya yi.

Mama ta ce "Eh 'yan biyu ne, Abubakar da mai sunan babana, shi ne sa, ba ka dariya sai hamma".


Ammi ta yi murmushi ta ce "Tubarkallah Allah ya ray miki, familynki sun burgeni sosai da sosai, rumaisa a yayyen nan naki ki bani biyu mana, na je na ƙara da nawa yaran mana, ni nawa duk rasuwa suke yi, saura uku a raye"


Mama ta ce "Allah sarki, Allah ya raya wanda suka rage, ya jiƙan wanda suka rasu".


Ammi ta amsa da Amin.


Aka zubawa ruma abinci, Abubakar yana bata a baki, tana ta shagwaɓa.


Bashir yayi sallama, da shi da 'yan sanda huÉ—u cikin uniform.


Ruma ta tsaya cak tana bin su da ido, nan suka gaggaisa da kowa, Ammi ta bi bashir da kallon ko lafiya.


"Maman Boy, ya jiki? Yau zaki ganni da police, su ne case É—in binciken aisha yake hannunsu, dan haka za su yi miki tambayoyi ne" a take rumaisa ta haÉ—e rai, ta kawar da kanta gefe.


Ɗaya daga cikin 'yan sandan ya ce "Baby girl, ki amsa mana tambayoyinmu, zai taimaka mana ƙwarai wurin binciko wanda suka yi garkuwa da ku".


Ruma ta zumÉ“ura baki ta ce "Ni fa bana riÆ™e abubuwa, na manta komai, likita ya hana ayi mini zancensu" 


"Ki yi haƙuri ki bamu haɗin kai, ba zancen su zamu yi miki ba, yaya aka yi aka sace ki? Yaya aka yi ki ka haɗu da aisha har ta baki jaririnta da ɗankwalinta?".


"Ni kawai sace ni aka yi, muka gamu da ita, ta bani yaron, na taho" yanayin yadda ta yi maganar zaka san ƙarya take yi.


Ɗan sandan ya sake nutsuwa ya ce "Ki yi haƙuri ki kwantar da hankalinki, a ina kuka haɗun da ita?"


Kawar da kanta gefe ta yi, irin idan ka gaji ka tashi É—in nan.

Duk yadda ya so lallaɓa rumaisa sai da ta fara hasala shi, rarrashin duniya amma fafur ta ce ba ta san komai ba.

Mama ta yi kanta da zagi, Abubakar yana lallaɓata amma ta yi mursisi tana hawaye, ta ce ba ta san komai ba ita ta manta.


Mai sunan baba da tun ɗazu yake jin su bai yi magana ba, sai yanzu ya tashi ya nufi gadonta, ya ture Abubakar shi ya zauna ya kalleta, ta sunkuyar da kai ƙasa, cikin muryarsa mai razanar da ita ya ce "Kalleni" ta ɗago da ƙyar ta kalleshi.


"Gaya musu abun da suka tambayeki" ta kallesu É—aya bayan É—aya sannan ta mayar da idonta kansa  ta shiga girgiza masa kai.


Idonta ne ya cika da hawaye, amma ta kasa magana.


Mama ta ce "Ruma ba kya ji ana yi miki magana ne?".


Ammi ta ce "Ku bita a hankali, kar ku tsoratata".


"Ba zaki faɗa ba sai na saka sun saka miki sarƙa sun tafi da ke, ana magana kina kallon mutane" yadda mai sunan baba yayi mata maganar cikin hargowa sai da ta tsorata, jikinta ya hau rawa, tana girgiza masa kai.


Ya sake kafeta da ido ya ce "FaÉ—i, komai É—acinsa da muninsa faÉ—i"


Cikin rauni idonta na zubar da hawaye ta ce "Bana son faɗa, bana son tunawa ne, labarin babu daɗin ji, kuma babu daɗin tunawa. Ta mutu!ta mutu! Ko sin ce sun kasheta? Ta mutu ne ba ta raye, kuma sun zo da mota sun ɗauke ta tun a can, bana son tunawa, mutuwar anty aisha abu ne da ba zan manta ba, ta mutu! Ta mutu!! Ta mutu ku rabu da ni dan Allah tun da na gaya muku" ta yi maganar cikin hargowa tare da watso piliown kan gadon tana wani irin kuka, da sai da mai sunan baba ya rungumeta jikinsa a matuƙar sanyaye.


Takawa ta gani a tsaye a ƙofar ɗakin, ya zuba mata ido da dukkanin nutsuwarsa, yana jin abun da take faɗa tamkar zubar dalma a tsakiyar zuciyarsa.


No comments