Kanwar Maza Book 1 Page 21

 


Jabir ya É—an yi gyaran murya ya ce "Ka ga dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka san ba a rasa irin waÉ—an nan a social media yaran talakawa ne kawai marasa tarbiyya amma dan Allah kawai ka share"



Takawa ya kalli Jabir ya ce "Ka kira mini Sidi na ce"


Jabir ya girgiza kai, wasu lokutan takawa akwai kafiya da gardama, da ga ganin comment É—in mace ce, kuma koma menene ba zai huce ba tun da ta riga ta yi.


Ya lalubo lambar sidi, ya kira masa shi, ya bashi wayar.


Cikin zafin zuciya ya karɓi wayar, ya yi wa sidi bayanin abin da yake son ayi masa.

Yana gama wayar, ya jefa wa Jabir wayar, ya fice daga É—akin gaba É—aya.



Sosai samha ta ɓata lokaci wurin yin kwalliya, kasancewarta 'yar ƙwalisa, sai dai babbar matsalarta ta ƙware a iya shigar banza, tun da garin Allah ya waye, bayan sun kammala waya da khalifa ta ji ta na son ganin takawa, dan haka da la'asar ta shirya ta tafi gidan, domin ganinsa.


Sai dai cikin sa'a, da ta shigo kan ta kai sashin Ammi, ta ga takawa ya taho fiuuu. Yanayinsa na rashin walwala bai sanya ta damu ba, balle ta saurara da abin da ta yi niyya.


Kai tsaye ta tunkari in da yake, ta fara yi masa magana, ko kallon in da take bai yi ba, yayi gaba abin sa, mamaki ne ya cikata, amma ba ta haƙura ba ta bi bayansa zuwa sashin Ammi, sai dai a sashin Ammi ma bai tsaya a falo ba, ya wuce ciki. Gaba ɗaya zuciyarsa a cunkushe take, an daɗe ba a gaya masa abin da ya ƙona masa rai kamar wannan comment ɗin ba, danganta shi da sata ba.

Samha kuwa gani tayi da kunya ta bi bayan takawa.

Nusaiba ce ta fito cikin shiri, da alama fita za ta yi, tayi arba da Samha a falo a tsaye.


"Ya dai na ganki a nan a tsaye, ko zama baki yi ba?" 'yan kame-kame Samha ta hau yi "Amm, dama takawa yana nan ne?"


"Ban sani ba, amma meyasa ki ke nemansa?"


Tsuke fuska Samha ta yi ta ce "Ina ruwanki da dalilin da ya sanya nake nemansa, ba abin da ya shafe ki bane"


"Haka ne, amma kamar yayi banbarakwai da yawa, ko kin manta waye shi a wurinki, Anty Samha ai ana barin halak dan kunya"


"Shut up! Na ce miki akwai wani abu ne a tsakaninmu, kin san bana son raini ko? Kuma ko ba komai ai takawa É—an uwana ne" Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya taimaka" ta wuce ta bar Samha a falon.


Samha ta damu ta ga Adam sosai da sosai, domin samun ƙwarin gwiwar yanke hukunci a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi.


Fitar Nusaiba babu daɗewa, Samha na tsaye na ta tunani, ma'aikatan sashin Ammi babu wanda ya tanka mata tun bayan gaisuwa, saboda sun san halinta na dizgi da wulaƙanta mutane da cin zarafi.


Iman ce tayi sallama a cikin falon, kamar kullum tana ganin Samha gabanta ya faÉ—i.

Salo-salo kamar mara lafiya iman ta ƙaraso cikin falon, ta kalli Samha ta ce "Anty Samha ina wuni?"


Samha ta ɗago kai ta kalli iman, ta yamutsa fuska, ta tsani iman fiye da yadda ta tsani 'yar uwatta. Ta ko ina iman kyakywar ce, ko da kwalliya babu, ko a wani yanayi yarinyar kyau ne da ita, ko kuka ko dariya, ko fushi ko fara'a komai kyau yake mata, ga tsananin kusanci da yake tsakaninta da takawa, bayan ɗaya katangar da ta yi mata shamaki da cimma burinta da take ta ƙoƙarin rusheta, iman ma wata babbar matsala ce a gare ta, dan duk tsanani akwai aure a tsakanin ta da takawa. Ba ta sake tabattar da Iman matsala ce a gare ta ba, sai da samarin 'yan matan gidan suke zamewa su ce suna son iman, sai da su Fauziyya suka yi da gaske, wurin damɓara mata mummunan fenti, da yayi mugun taka rawa wurin rusa farincikin rayuwar iman sannan suka samu sauƙi, ga yarinyar sumi-sumi kamar munafuka, tana da sanyin hali, nutsuwa da kuma girmama mutane, shiya sanya kowa yake sonta, ban da yanzu ma da ake janye jiki daga gare ta.


"Anty Samha, wai ya na ga kina ta kallona? Me na yi kuma?"


Wani mugun kallo ta yiwa iman ta ce "Zan yi maganinki ne, magani na har abada, idan har baki bar sabgar takawa ba" iman na shirin magana, Ammi ta fito da sauri daga sashenta tana ƙwalawa iman kira.


Ganin Ammi a ruÉ—e ya sanya iman bin Ammi da sauri, ba tare da tunnin komai ba, Samha ma ta rufa musu baya.


A ɗakin Ammi suka tarar da takawa a sheme a ƙasa.


Cikin ruÉ—u Ammi ta ce "Iman ina maganin sa"


Cikin rawar jiki iman ta ce "Ammi me aka yi masa kuma ciwon ya tashi?"


"Ban sani ba, kawai yana shigowa ya faÉ—i yi sauri ki É—auko".


"Kin san ya daÉ—e ciwon bai tashi ba, sai na binciko shi a in da na É“oye, bari na É—auko"


Samha ta ce "Ammi meya same shi ne?"


"Bashi da lafiya ne" Ammi ta bata amsa a taƙaice.


Iman ta ɗan jima sannan ta kawo maganin, wani mai ne a doguwar kwalba ta zo da shi, ta buɗe tana shafawa takawa a goshinsa, jikinsa sai wani irin rawa yake yana ƙamewa kamar mai farfaɗiya.


Iman ta dinga shafa masa tana karanto adduoi daban-daban, kusan mintuna goma sannan ya daina abin da yake yi, da kansa ya tashi ba tare da ya cewa kowa komai ba, ya je ya hau kan gadon Ammi ya kwanta ya rufe idonsa.


Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ammi bari na tafi, dama mama ce ta aiko ni wurin Mummy, na biyo na gaishe ki, bari na tafi Allah ya ƙara lafiya".


Har samha zata fita, Ammi ta kirata, Samha ta dawo gaban Ammi.

Ammi ta riƙo hannun Samha ta ce "Dan Allah Samha kar ki gayawa kowa takawa bashi da lafiya, waɗanda suka san yana da wannan rashin lafiyar sun zata tuni ya warke, dan Allah ki rufa mini asiri, ki yi shiru da bakinki" Ammi tayi maganar kamar zata yi kuka.


Cikin kulawa Samha ta ce "Ammina, kar ki damu, babu wanda zan gayawa in sha Allah, rufin asirinki ai namu ne, ba wanda zai ji in sha Allah "


Ammi ta jinjina kai, ta yiwa Samha godiya, iman kuwa tausayin Ammi yakamata, ammi haryanzu ba ta san halin samha ba, ko da yake ba wanda zai yadda da samha fuska biyu ce da ita.


Jiki a sanyaye Samha ta wuce sashin Mummy, sai dai sashin na ta shiru babu kowa. Kai tsaye ta nufi É—akin Mummy.

Ta tarar da mummyn na waya, ta samu wuri ta zauna tana jiran ta kammala wayar.

Mummy ta kammala wayar ta dubi Samha ta ce "Samha 'yar ƙwalisa, ya aka yi ne, na ga duk jikinki a sanyaye?"


Samha ta dubeta ta ce "Mummy, wai dan Allah baki da masaniya a kan rashin lafiyar Adam?"


"Wace rashin lafiya kuma?"


"Rashin lafiyar da ake cewa yana da ita, yau na gani da idona"


Mummy ta waro ido waje ta ce "Ki na nufin bai warke ba dama?"


"Eh, mahaifiyarsa ta nemi na yi shiru da bakina, amma na kasa jurewa, sai da na ga iman tana ta shafa masa wani abu a fuska, sannan ya tashi, anya Mummy babu hannunki a ciki?"


Mummy ta yi wani murmushi sannan ta ce "Samha kenan, ke idan da hannuna a ciki zan kasa gaya miki ne, ai da ko a wurin mahaifiyarku zaki ji, babu ruwana a cikin lamarin nan, ni ban ma san haryanzu yana da wannan ciwon ba, a zatona tuni ya warke"


Samha ta rausayar da kai, sannan ta miƙe tsaye ta ce "Na tafi, dama sauri nake" bayanta mummy ta bi da kallo, sannan tayi wani irin murmushi ta ce

"Yarinya man kaza, wannan labari yayi mini daÉ—i da ki ka zo mini da shi, dama na daÉ—e ban ji labari mai daÉ—in wannan ba. Zan cigaba da amfani da wawancinki ina ruftaki, dole in je gidan Galadima, sai Hajiya Luba ta ji wannan zancen"


****

Ruma kuwa tuni ta manta abin da ta yi, dan ba ta ɗauki abin da tayin wani abu mai muhimmanci ba, sabgoginta ta cigaba da yi, sai dai tana iya ƙoƙarinta yanzu a kan kar ta yi wani abun da zai kuma haɗata da mai sunan Baba, dan karonsu babu daɗi sam.


***

Kamar ko yaushe, haka yanzu ma muryarta ta yake ji a kunnuwansa, a hankali ya buÉ—e idonsa, yana son tabattar da a ina yake, abin da ya iya tunawa shine ya shigo cikin gidan sashin Ammi, amma daga haka bai iya tuna komai ba.

A hankali kunnuwansa suka jiyo masa muryar Ammi tana karatun Alqur'ani.

Ya juya, ya kalli Ammi, ta na sanye da hijjabi, iman kuma ta ziro masa ido tana kallonsa.


Da sauri iman ta ce "Ammi ya farka"


Cikin kulawa Ammi ta dube shi, ta É—ora hannunta a goshinsa tana yi masa sannu.

Ya jinjina kai, Iman ma ta shiga jero masa sannu yana jinjina kai.


"Takawa, duk da na san ba ka so, amma ya zama dole ka yi haƙuri mu cigaba da neman magani, a baya abu ya lafa amma Kwatsam yau sai gashi ka faɗi, dole mu yi wani abu a kai kafin a farga a samu abin faɗa.


Shiruu Adam ya yi yana sauraron Ammi, ba tare da ya iya cewa komai ba.

Ammi ta kalli iman ta ce "Auta, duk da bani da matsala da ke, amma ke ma ki yi shiru, ko waccan ruÉ—aÉ—É—iyar Nusaiba kar ki gayawa"


Iman ta ce "In sha Allah Ammi, bari na je na mayar da maganin".


Zuwa washegari takawa ya ware, kamar ba shi ba,  ya cigaba da azalzala a kan a nemo masa mamallakin account É—in nan da aka ce masa É“arawo da shi.


A washegari Mummy ta shirya ta tafi gidan Galadima mai ci a yanzu, wato gidan su Jabir.

Hajiya Lubabatu na ganinta suka yi wata shewa, tare da gaisawa da junansu.

Hajiya Lubabatu ta ce "Ya akwai labari ne?"


"Da É—umi-É—uminsa ma kuwa, mu shiga daga bedroom.


Cikin É—aki suka shiga, Mummy ta ce "Ya jikin Galadima ne?"


Hajiya Lubabatu ta ce "To ni me ma zance miki ne, a ƙarshen watan nan dai nake son ko ni ko jabir wani ya je, ance dai da sauƙi"


"To Allah ya ƙara afuwa, amma gaskiya Yakamata ki miƙe ki ɓata alaƙar da ke tsakanin Adam da Jabir, kin san idan babansu ya rasu sarauta gidanmu za ta dawo, ke sai ki zuba ido shikenan babu makoma, idan sarauta ta dawo hannun Adam waya san lokacin da zai mutu balle Jabir ɗin ma yayi sarautar, duk da ina ta ƙoƙarin ƙara rura wutar gaba tsakaninsa da Mahmud, sai dai Mahmud wawa ne, ya ƙi mayar da hankali a kan Sarautar, ba ta gabansa ".


Hajiya Lubabatu ta yi murmushi ta ce "Jamila kenan, ai kema kin san ba a zaune nake ba, kuma da sannu dukkaninmu zamu yi nasara, ai ke dama ba kya burin sarautar ta dawo gidanku"


"Ƙwarai kuwa, shiyasa nake ta son komai ya ɓaci, ko kin san ashe Adam bai warke daga wannan larurar da yayi ba yana yaro, mai kamar farfaɗiyae nan ba?"


"Haba dai, ya aka yi ki ka sani?"


"Samha ce ta zo ta titsiyeni, wai ta gani a sashin su, wai ko ina da hannu a rashin lafiyar ta sa, na ce mata ni babu ruwana, da ciwonsa na ganshi"


Hajiya Lubabatu ta ce "Kai samha ma akwai bin ƙwaƙwƙwafi, shareta kawai ai aiki yana kyau sosai"


"Haaa ke dai bari, idan har ina raye ko zan tafi tsirara sai Binta ta É—anÉ—ana kuÉ—arta in Allah ya yarda sai ciwon nan ya zame masa hauka tuburan, na kaÉ—a sauran yaran nata tare da wannan shegiyar yarinyar mai kama da larabawa"


Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Shi dai wannan É—a abu ya zame masa goma da ashirin, da hauka ko in ce farfaÉ—iya, ga kuma maita duk shikaÉ—ai"


"Hmm ke dai bari, ina jiran lokacin da zan kwatsa zancen nan a cikin masarautar Kano, É—an da suke ji da shi maye ne, da ya sha a nonon uwarsa, ta ta ba ta baiyyana ba sai ta shi"


Cike da rashin imani suke ƙyaƙyace dariya, kamar ba za su bar duniya ba.


Cikin dare da misalin ƙarfe biyu da rabi, Baba uwani ce ke sanɗa kamar 'yar fashi, ta buɗe babbar ƙofar sashen Ammi ta fita, kai tsaye ta nufi sashen Mummy, tana tura ƙofar sashin ta buɗe, ta kutsa tana waige-waige.

Hanyar kitchen ta bi, ta tarar da Mummy a wani É—aki a zaune tana jiranta.

Baba uwani ta duƙa ta gaida Mummy, Bata amsa ba ta dubeta ta ce "Kin san dalilin da ya sanya na nemekk?"


Ta girgiza kai alamar a'a.


"An ce mini É—an uwar É—akinki Adam, haryanzu bai warke ba, ciwon nan da yayi da yarinta yana nan yana fama, jiya ma ya tashi haka ne?"


Baba uwani ta ce "Wallahi ban sani ba uwar É—akina, jiya ta aikeni, kuma ina tunanin babu wanda ya sani, saboda da na dawo ban ji labari ba".


"Ba tambayarki nake dogon labari ba, ance mini akwai wani abu da aka shafa masa, ya tashi da wuri, wannan abin nake son ki sanya ido ki É—auko mini"


"Ranki ya daÉ—e, ai ban san a in sa suke ajiyewa ba, ba ta sanya ni a sabgar neman maganin sa ba"


"Bai shafeni ba uwani, ki aikata abin da na ce kawai, tashi ki bani wuri"


Haka baba uwani ta taso, tana tunanin ta in da zata fara aiwatar da wannan aiki mai mugun hatsari.


****

Yau ruma fakar idon Yasir ta yi, ta ɗauki wayar nan ta jefa a jakar makarantar ta, ta yiwa mama sallama ta tafi makaranta. Sai dai da ta je makarantar babu wanda ta iya nunawa wayar, gudun kar yaran su tona mata asiri a ƙwace wayar, sai dai ta na jin kanta riƙe wayar nan da take yi, duk da ba wayar kirki ba ce ba.

Yau mama ba ta nan, ta je cikin gari za su kai wani kayan lefe na wani ɗansu, dan haka ruma sai lissafi take a kan ba zata islamiyya ba, ƙulewa za ta yi a ɗaki ta yi kallo a waya, kuma ta sha baccinta.


Ta tsaya ta sai gyaÉ—a a hanya, tana tafe tana ci, kamar ba É—iya mace ba, dan ruma duk wani abu na jan aji na mata ruma ba ta iya ba, haka nan take rayuwarta kamar namiji.


Ƙarar mota ta ji a bayanta, sai dai kan ta kauce, ta ga an sha gabanta da motar, wasu ƙarti ne suka fito suka ce "Shiga mota"


"In shiga aje ina kamar a film É—in indiya"


Cikin tsawa É—ayan ya ce "Ki shiga mota na ce"


Ruma ta cake ta riÆ™e Æ™ugu  ta ce "Wai saboda me, in shiga ka kai ni ina?"


"Kai dalla dannota kawai, za ta ɓata mana lokaci" sau ɗaya ya tankaɗa ƙeyar ruma, ta hantsila cikin motar.

Aikuwa ta din ga kurma ihu "Al'ummar É—orayi an saceni, dan Allah ku kawo mini agaji" rufe motar suka yi, suka ja dama motar tint ce, sai dai ruma ta cika musu kunne da kururuwa.


"Ke, kin ishemu, zamu yanka ki da da wuƙa a motar nan"


"Wallahi ba zan yi shiru ba, kun satoni kun sakani a tsakiyarku bayan ku ba muharramaina bane ba".


Wanda yake tuƙa motar, ya dubi na kusa da shi, cikin harshen turanci ya ce "Anya kana ganin wannan yarinyar ce kuwa?"


"Oho, mu kai masa ita dai, shi zai tantance ".


"To ai gani na yi yarinya ce sosai, yaushe wannan zata iya wannan abu?"


"Kai wannan sai ta aikata, ji yadda take wa mutane ihu, dan ya ce ban da cin zarafi da sai na sakata a silent yanzun nan".


"Wallahi idan baku buɗe mini motar nan na fita ba, sai na tara muku jama'a, ashe ma ku ƙananan 'yan kidnapping ne, da kuka sace ni, to wallahi ni ƙanwar maza ce, idan yayyena suka gano ku, sai kun raina kanku" babu wanda ya kulata cikinsu, har suka isa in da zasu je, ba ta yi shiru ba ko na mintuna. Haka zalika idan za a kasheta ba ta san ta in da aka bi ba, saboda baƙin glass ne a motar.


Ita dai ta ji an tsaya, aka buÉ—e mota aka ce ta fito. Fitowa ta yi tana kallon harabar da aka paker motar.


Ingiza ruma suka yi, ta ƙanƙame jakarta tana kalle-kalle.

Wani falo aka shiga da ita, suna shiga wani irin sanyi ya daketa, ta ce "Wayyo sanyi" duk sai da suka kalleta kamar wata 'yar ƙauye.


Ita ba kawotan ne ya dameta ba, tsaruwar gidan da yadda aka narka masa dukiya ne ya burgeta take ta kallo.


Sanyin Ac ne ya fara damunta, saboda haryanzu babu wanda ya ce mata komai, tunani ta fara yi, idan mama ta dawo ta tarar bata nan fa, gaba É—aya hankalinta ya tashi yayi gida, a yadda take jin labarin kidnapping dai ba haka ake yin sa ba, ko da yake dai ai babu maraba.

Miƙewa tayi ta dubi mutumin da yake zaune a bakin ƙofa ta ce "Bawan Allah dan Allah ku zo ku sallameni, kar babata ta dawo ta ga bana gida"


"Wuce ki zauna, kafin na fasa kanki da harsashi"


"A'a da bom zaka fasa mini kai, ni me na yi muku ne?"


"Wallahi ki ka cigaba da yi mana hayaniya, sai na saka igiya na É—aureki"


"Kamar ya ya ka É—aureni da igiya, sai ka ce ragon layya? Dan Allah ku zo ku mayar da ni"


Cikin tsawa ya ce "Ki koma ki zauna na ce".


Tsaki ta ja ta koma ta zauna, bin ruma ya yi da kallo jin yadda ta yi masa tsaki.


Zama ta yi ta É—auko gyaÉ—arta ta cigaba da ci, tana É“ata wurin, mai gadin na ta kallonta yake, ita kamar ma ba ta damu da É—aukotan nan da suka yi ba, gaba É—aya ba ta da wata damuwa.


Ta gama cin gyÉ—arta, ta buÉ—e jakarta ta É—auko rake. Duk ta É“ata wurin, ta gama ta gaji tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Surutan mutane suka ji, alamar za a shigo. A cikin mutanen da suka shigo su uku, tana yiwa É—aya kallon sani, sai dai ta manta a ina ma ta sanshi.


"Tana ina?" Ya faɗa a taƙaice.


"Gata nan a gabanka sir, ita muka samo, kuma ta faÉ—i wasu abubuwa da ya sake tabattar da ita ce" cewar É—aya daga cikin wanda suka kawo ruma.


Mamaki ne ya kama shi, ta ina ƙaramar yarinya kamar wannan, ta samu waya, har ta iya yi masa wannan comment ɗin.


Ya zauna ya na ƙare mata kallo, sai wani haɗe rai take tana basarwa, tana harare-harare ta gefen ido.


Jabir ya ce "ka bi komai a sannu Please, ka ga ƙarshen abin ma ashe yarinya ce, dama haƙura kai kamar yadda na gaya maka da farko".


"Me na yi miki ki ka kirani da É“arawo?" Yayi maganar yana tsareta da ido.


Mamaki ne ya kama ruma, ita a ina ta sanshi da zata kira shi da ɓarawo. Ya sake maimaita maganar amma tayi banza taƙi magana.


Jabir ya ɗauko wayarsa, ya shiga account ɗin da ruma tayi comment da shi ya nuna mata, ya ce "ke ki ka yi wannan comment ɗin?" Ta zubawa Jabir ido, shima ta ƙi kulashi, sai dai a yanzu ta gane in da ta taɓa ganin Adam, a Instagram taga hotonsa tayi comment.


"Wai kurma ce ne?"


"Sir wallahi ba kurma bace, yanzu ta gama magana iskanci ne, ka bari a casata kawai".


"Am talking to you, me na yi miki ki ka ci mutuncina, wai na saci kuÉ—in talakawa, ance miki ni É—an siyasa ne?"


Jabir ya ce "Easy Adam, yarinya ce ƙarama, ki na ji ki san abin da zaki din ga rubutawa a social media, wanda ya baki waya ma shi ne babban mai laifi, da ya bawa under age waya. Babban mutum ne sannane, ɗan gidan marigayi Galadiman Kano ne, bashi da alaƙa da siyasa, amma kin yi masa ƙazafi shi mahaifinsa basarake ne, kuma ɗan kasuwa ba kuɗin tal.....


"Shut up Jabir, na meye zaka din ga yi mata wani bayani"


"A'a ka yi haƙuri, kin ga bashi haƙuri komai ya wuce" wani kallon zaka bushe ruma tayi masa, ta ƙara gyara jakarta ta ɗauke kanta gefe guda.


Mamaki ne ya cika Adam, shi da yake dodo ko a cikin manyan mutane, amma shi wannan 'yar shilar ke rainawa hankali, yana yi mata magana amma ta mayar da shi É—an iska.


Jabir ya jinjina kai ya ce "Lallai gaba da gabanta, anya wannan yarinyar ba mahaukaciya bace ba?"

Kallon Jabir tayi ta galla masa harara, haka kawai tana ganinsa ta ji ta tsaneshi, wani mugun haushinsa ya kamata, ya fiye shishshigi.


Adam rasa abin yi ma yayi, dama wata babbace he knows how to deals with her, amma wannan ya hukunta ta ya ce ya yiwa wa?.


Ruma ta miƙe tsaye da jakarta, tana kallon wanda suka kawota, jinjina kai kawai suke, da ganin namijin ƙoƙarin da ubangidansu yayi.


Cikin ƙunƙuni ta ce "Ni a mayar da ni in da aka ɗauko ni" tayi maganar tana nufar ƙofar fita.


"Ku kamata ku É—aure mini ita, sannan a nemo mini waye ubanta, in nuna wa babanta banbancin arziki da tsiya, shine dai-dai yi na, dan na fuskanci bayan talauci har da rashin tarbiyya a tare da ita.


Ba tare da ta waiwayo ba ta tsaya, dan ma kar ta kalleshi ya yi mata kwarjini ta ce "Shi baban nawa sai ka bishi kabari ka nuna masa ka fishi kuÉ—i, kuma Alhamdilillah ni dai an yi mini tarbiyya dai-dai gwargwado, kuma wallahi sai na saka yayyena sun yi maka bugun sakwara, har DPO na unguwarmu sai na gaya masa, ba sunanka Adam ba É—an galadima ko wambai to wallahi sai na faÉ—a ka saceni ka kawoni cikin maza" tuni ya daskare a wurin, jikinsa ya hau tsuma, ga zafin maganganu da fitsarar Ruma, ga razani na jin muryar da take ta addabar kunnuwansa.


Cikin azama ya fizgota, ya juyo da ita gabansa, ya riƙe hijjabinta tare da rigar uniform ɗin ta. Kallon hannun takawa tayi, da ya sanya wani agogo mai kyawun gaske, amma babban abin da ya razana ruma, yadda ya riƙota ta wuya hannun ƙaton namiji a jikinta kan ƙirjinta, abin da aka ce ta ɓoye ta tattala, kar wani ya kai hannu wurin, idan ba haka ba za tayi ciki, amma hannun wani ƙato a wurin !!!



(Saura page É—aya mu kammala book1, wanda za su sai book 2, an fara payment 500 ne, in sai an gama document 800.


0009450228

Aisha Adam

Jaiz bank.

Sai a turo shedar biya ta 08081012143)



Ayshercool

08081012143

ƘANWAR MAZA

                 


Na Aisha Adam (Ayshercool)


MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES


No comments