Kanwar Maza Book 1 Page 16
Page 16
Kallon-kallo suka shiga yi wa juna, aka rasa wanda zai bawa wani hanya, Mahmud ne ya fara janye nasa idon ya wuce yana wani irin taku cike da rainin hankali, ya bawa Adam hanya.
Cikin hanzari Adam ya bar falon, yana jin wani abu yana tsikarar zuciyarsa.
Adam na fita, Mummy ta taso ta na faÉ—in "Mahmud ya haka, meyasa ba zaka tsaya ku gaisa ba, kamar ba É—an uwanka ba?"
Mahmud ya ce "Mummy, ni baki ga abin da ya yi mini ba? Lokacin da ya sauke girman kai ya duƙa mini, wataƙila na fara saurarasa"
"Haba Mahmud, shi ne fa gaba da kai, ya zaka ce haka? ni fa bana son ace ina ziga ka, kuma ko ba komai ya ci sunan mai martaba, ya cancanci ka girmama shi, kuma idan Allah ya sanya sarautarmu ta dawo gidan nan, ka san shi ne magajin babanku, shi zai zama galadima tun da shi ne babba"
Ya dubi Mummy ya ce "Ni wata sarauta ko wani abu makamancin haka bai dameni ba, a naɗashi sarki ma gaba ɗaya, wannan shi ta shafa, look Mummy, a bar wannan zancen ni bani da lokacinsa, bari na je na karya" yana gama maganar ya wuceta, ya na bada baya, Mummy ta yi murmushi ta ce "Haryanzu ina wasana yadda nake so, Mahmud dole na ɗarsa maka zaƙin mulki da ƙaunar sarauta, sannan kuma azo a rasa sarautar gaba ɗaya mu je zuwa".
****
Aliyu suna tafe a hanya, yana ta yiwa ruma faÉ—a.
"Dan ubanki kuɗin makaranta na, na registration na fara tarawa, yanzu kin saka na kwashe na bayar a banza, ban ci ba ban sha ba, dan ma Allah ya sanya DPO ya biya mafi yawa daga kuɗin. Saboda ba ki da mutunci ina kareki ki na ƙaryata ni, ni dama na ƙyaleta ta yi miki shegen duka".
Ta waro ido ta ce "Kaii, idan ta sumar da ni fa?"
"Ai gara ta sumar da ke É—in, tun da ke dai har abada ba kya hankali, wai ki ka karya 'yar mutane saboda tsabar kanki ba daÉ—i"
"To ba kai ne ka ce mini mahaukaciya ba, wai ana kai ni asibiti"
"To meye marabarki da mara hankalin? Zaki gane kurenki ne, bari mu je gidan sai na daki kuÉ—ina" har suka isa gida, ruma ba ta sake cewa komai ba.
Mama na ganin Aliyu tare da ruma sun dawo, ta fito daga É—aki ta na tambayar ko lafiya?
Ruma ta É—an sosa kai tana kallon Aliyu.
"Zaki dai na kallona ko sai na tsokane idon? Sai ki yi mata bayanin abin da ki ka yi ai".
Ruma ta kalli mama, kamar zata yi kuka ta ce "Wallahi mama tsautsayi ne"
"Tsautsayin me? Me ki ka aikata kuma?" Ruma ta yi tsilla-tsilla da ido.
"Ba zaki gaya mata ba"
"Mama, da wasa fa na gwada irin na wrestling É—in nan, shi ne wata ta karye"
A É—an hasale mama ta ce "Kai ka gaya mini abin da ta yi mana, ka tsaya ka na mini wasa da hankali".
Aliyu ya yiwa mama bayanin abin da ruma ta aikata, da yadda suka yi, zuwansu police station yanzu.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ka shiga lamarina, Allah ka dubeni a kan halin wannan yarinyar".
"Mama dan Allah ki yi haƙuri ba zan sake ba, ita ta fara tsokanata na rama, ban san zata karye ba wallahi"
Mama ta dube ta ta ce "In dai kece, ba zaki canza hali ba, yanzu ruma har ta kai ki ga zuwa police station ruma, kaf yaran nan yayyenki babu wanda ya taɓa zuwa wurin 'yan sanda, sai ke ruma ko? Allah ya yi miki magani, ki je ki yi ta yi kar ki fasa" mama na gama maganar ta shige ɗaki ta bar ruma a wurin.
Ruma ta kalli Aliyu ta ce "Kai baka da rufin asiri, wallahi da yaya usy ne zai rufa mini asiri, amma na fuskanci da kai da Yasir, da Huzaifa baku taɓa rufa mini asiri ba, ƙiris ku ke jira .....
"Dalla rufe mini baki, tun ban daki kuɗina a jikinki ba, dubu gomar nan ta tsaye mini, ni Wallahi da ma ƙyaleki na yi su yi miki duk abin da suka ga dama" ɓata fuska ta yi, ta bi bayan mama, sai dai mama sam taƙi kulata, wanda hakan ba ƙaramin tayar wa ruma hankali yake ba.
Wunin yau gaba É—aya aka rasa mai saurara ruma, duk wanda ta yiwa magana sai ya hantareta gaba É—aya haushin abin da ta yi suke ji.
"Hmm huzaifa ni fa Allah ne ya taimake ni, da matar cewa ta yi sai ta dakeni, ka ganta kuwa, ƙatuwace sosai da sosai fa, a kan benci ta zauna, kaga hannun ta a cure da nama, idan ta dakeni ai ji zan kamar an buga mini guduma"
Usman ya ce "Sai na zubar da haƙoranki, ba zaki nutsu ba ko?, ki ke cigaba sa kwatanta yadda take, ina ma Alin ya bar ta ci ubanki, ke ban da rashin kan gado, kawai ki je ki karya 'yar mutane saboda tsabar wauta ta yi miki yawa, sai ka ce wata rainon gaɓa-gaɓa?"
Aliyu ya ce "Kai ba ka san abin takaicin ba ma, har da wani cewa ai aljanunta ne suka tashi, ba a hayyacinta ta daki yarinyar ba, tsabar cin kai"
Mama ta ce "Ba ku ne ku ke zigata ta É—auko magana, ku ka ce kun tsaya mata, dole ta yi abin da ta ga dama ai, kuma daga yau duk wasu tashoshi na wrestling a gidan nan sai an sauke mini su, an daina kallon sa a gidan nan, kai kallon ma sai an daina"
Ruma ta waro ido ta ce "Mama, shikenan sai na daina ganin saurayina na wrestling"
Usman ya ce "Au ke har wani saurayi ne da ke a wrestling É—in?"
"Eh mana, ba ka san shi bane, Huzaifa ya ma sunan sa, É—an tuna mini, idan na ganshi har wani daÉ—i nake ji".
Huzaifa ya ce "Ke ki ka san shi ni ban san shi ba"
Yasir yayi tsaki ya ce "Wallahi Mama mi bamu go ahead, mu yi wa yarinyar nan ruƙiyya ni da Huzaifa, mu samo tsumangiya in cuɗa mata jikinta in haɗa da ayar Allah wallahi dolen aljanun na ta su magantu"
"Wallahi ni ba ni da aljanu sai raina ya ɓaci, kuma na sha tabara da ayatul kursiyyu, na fi ƙarfin aljani da makiri ko tsunburbura na fi ƙarfinta"
"Ke dalla ware, ai ke kin fi tsunburburar ma rashin ji" suka din ga caccakar ruka kamar zasu daketa.
Ita damuwarta a kan mai sunana Baba ne, hukuncin da zai É—auka a kan ta, na abin da ta aikata, sai ta ji bai ce komai ba ma, yayi shiru kamar bai san me aka yi ba.
***
Tsaye yake a bakin wardrobe ɗin, yana ƙarewa kayan ciki kallo kamar ba nasa ba, ya saka hannu da nufin ya ɗauko kaya, hannunsa a sauka a kan koriyar alkyabbarsa.
Kamar ya na jin tsoron Alkyabbar, ya zarota ya na kallonta.
*Sarki mai koriyar alkyabba a dawo lafiya, ka É—anani a kan dokinka ko ka bani kyautar doki*
Shiru ya É—an yi ya na tunani, ta yaya zai ji murya É—aya a mabanbantan wurare, kuma haryanzu bai kai ga ganin fuskar wacece ba, gashi a duk lokacin da zai ji muryar, sai ta kira shi da sarki!.
Ajiye Alkyabbar ya yi, ya É—auko wata dark blue É—in suit, ya shirya a cikinsu ya É—auki jakarsa ya fita.
A É—aki ya tarar da Ammi tana sallar walaha, ya zauna ya jira ta idar.
Ta idar ta kammala Adduointa, sannan ta kalli Adam ta ce "Barka da wannan lokaci takawa".
Yayi murmushi ya ce "Barkanki Ammi, zan wuce ne"
Cikin tausayawa ta kalleshi ta ce "Ka na ganin babu matsala, zaka iya zuwa aikin?"
"Babu wata matsala in sha Allah"
"To matso na yi maka addu'a" ba musu ya matsa kusa sa Ammi, ya durƙuso mata da kansa, ta ɗora hannunta na dama a kan nasa, ta dinga kwararo masa Adduoi.
Wata irin nutsuwa ya din ga ji ta na ratsa shi, ya lumshe idonsa, sai da ta idar, sannan ya riƙe hannun ya sumbaci hannun ya ce "Allah ya ja zamanin giwar Galadima, ya baki yawan rai, Allah ya jiƙan Galadima"
Murmushi ta yi, tare da jin maganar har cikin ran ta ta ce "Amin takawa, Ubangiji Allah ya tsare" ya miƙe yana faɗin Amin, ya bar ɗakin.
***
Tun da abin nan ya faru, an kai ruwa rana sosai, kan malaman su ruma su yarda ta cigaba da zuwa makarantar, bisa sharuÉ—ai sannan ruma ta cigaba da zuwa makarantar.
Tun baya da aka yi sulhu a police station, duk ranar juma'a sai mama ta aika wani ya tasa ruma a gaba sun je duba Asiya, sun kai wani abu, amma kullum babar Asiya babu godiyar Allah, kullum suka je sai ta yi complain, ita kuma ruma kan su taho, sai ta aikata wani abun da za ta sake tunzarata tayi ta masifa.
A haka duk suka ce sun daina zuwa, yau mama ta ce dan Allah mai sunan Baba ya saka ruma a gaba su je.
Tun da Allah ya sa babar Asiya ta yi arba da fuskar mai sunan baba, ta shiga hankalinta, ko maganar kirki ta kasa sai kame-kame.
Tun da suka gaisa, ya bata abin da zai bata, ya ce ruma ta tashi su tafi, ko yaya mai jiki bai ce ba balle ya ce Allah ya kyauta.
suka taho hanya, ruma a nutse take babu tsokana da hauma-hauma, saboda kura ta san gidan mai babban sanda.
da suka zo bakin layin su, cikin girmamawa ruma ta kalli mai sunan Baba ta ce "Mai sunan Baba, mama ta ce na taho mata da kayan miya a wurin Hudu"
Ya kalleta ya ce "Idan kin ga dama, ki tsaya hauma-hauma da neman magana a hanya, zaki zo ki sameni".
"In sha Allah ba zan yi ba"
Ganin da mutane a wurin Hudu, ya sanya ruma ta tsaya ta na jira, sai dai kan ya kawo kanta, ta ɗau wuƙa ta din ga daddatsa masa kabewa bai sani ba.
Da ta gaji ta ce "Malam hudu ka sallameni mana"
Ya ce "Yi haƙuri na fara sallamar matan aure, su da zasu ɗora girki"
Ruma ta yamutsa fuska ta ce "To da me matan auren suka fini? Nima fa watarana matar auren nan ce"
Yayi murmushi ya ce "Eh, amma dai yanzu ƙwaila ce, Allah ya nuna mana kin zama matar aure ruma"
Ta haɗe rai ta ce "Gaskiya malam Hudu ka daina gaya mini wannan kalmar ta watsewa, ƙwaila fa iskanci ne"
Ɗan buɗe baki yayi ya na kallonta, sai kuma ya ce "To Allah ya baki haƙuri" sai da ta bawa mutanen wurin dariya.
Can ta kalli Hudu, ta kalli lafcecen billensa kamar an yi masa da gatari ta ce "Malam Hudu, na daÉ—e da tambayar nan a zuciyata wai meyasa aka yi maka bille?"
Yayi murmushi ya ce "Delu billen mahauta ne"
"To amma dai da wuƙa aka yi maka ko?"
Ya ce "A'a, aska ce, billen gado ne na mahauta"
"To kai baka gaji kuÉ—i ba sai bille, da babanku ya mutu sai aka raba muku billen?"
"Ke na gaji da wannan wulaƙancin naki, mai zan baki?" Ruma ta miƙa masa kuɗi, ta yi masa bayanin abun da zai bata, ya sallameta ta tafi gida.
Da ta je gida, ta haÉ—a kayan miyan, ta gyara su ta tafi kai markaÉ—e.
****
Tsaye take a harabar Hotel, tana sanye da doguwar riga ja, ta naÉ—e kanta da jan mayafi, fuskarta sanye da tabarau da kuma takunkumin fuska, dan haka idan ba wanda yayi mata cikakken sani ba, ba yadda za ayi ka ganeta.
Wayarta ta É—auko ta kira wata lamba, ta kara a kunnenta, a É—an hasake ta ce "Gani nazo ka na ina?"
"Room A7, Vip" ta ajiye wayara, ta shiga cikin hotel ɗin, babu wanda ta tambaya da kanta ta gano ɗakin, ta tsaya a bakin ƙofa, ta kuma kiran wayar "Gani a ƙofar ɗakin" ta faɗa a taƙaice.
Wani mutum ne ya buɗe ƙofar ɗakin ya leƙo ya ce "Ke ce baƙuwar yallaɓai?"
"Kai ka san wani Yallaɓai, ka je ka gaya masa gani na zo"
"Ok, to dama cewa ya yi a shigo da ke"
"Ba zan shigo ba, idan ya matsu ya fito idan kuma ba a matse yake ba zan yi tafiyata, bana son jira".
Ya É—an yi jimm ya ce "Amma kamar maganar ki ta yi tsauri"
A fusace ta ce "Kai ka san wacece ni kuwa? Na yi mai wuyar ai da na zo nan, idan ba zai fito ba zan tafi"
Juyawa mutumin ya yi ya koma cikin É—akin, babu daÉ—ewa sai ga wani mutumin ya fito, shi ma fuskarsa rufe da takunkumi.
"Ki shigo mana, zuwa bai yi miki wahala ba sai shigowa?"
"Ba zan shigo ba, ka gaya mini koma menene a nan ina jin ka"
Ya ce "Well, mu je ƙasa to, sai mu yi magana"
Tare suka sauka ƙasa, suka samu wuri suka zauna, ya dubeta ya ce "To sauke takunkumin mana"
"Ba zan sauke ba, wai tukuna kai wayene naga kamar ka na ƙoƙarin raina mini hankali"
Murmushi ya yi, ya sauke takunkumin fuskarsa ya ce "Khalifa senator usman, na san kin sanni kuma kina jin sunana, kuma kin san me nake nema"
Ajiyar zuciya ta yi, ta sauke na ta takunkumin ta ce "Dama kai ne? To Meyasa ka ke nema na?"
"Samha kenan, kin san ita kasuwar muradi babu in da ba ta kai mutum, ba wani abu ne ya sa nake neman ki ba, sai dan mu haɗa hannu na taimake ki, ki taimake ni. Ban sani ba ko baki sani ba, amma na san kin san Adam, Adam ya na barazana ga mutunci da rayuwar mahaifina, da kuma ni kaina da career ta, dan haka nake son ki taimakeni na kai shi ƙasa, zan baki kuɗi ko nawa ki ke bukata" yayi maganar yana tsareta da ido.
Ta cire gilashin fuskarta, ta dube shi ta ce "Da ka tashi binciken ba ka binciko da cewa, Adam ba É—an uwana ne ba kawai, shi ne mutumin da nake so, kuma nake muradin aure"
ÆŠan waro ido ya yi ya ce "Kuma!"
"Ƙwarai kuwa, sannan kar ka manta, ni 'ya ce da na fito daga gidan sarauta mafi daraja a nahiyar Afirka, sarautar Kano, dan haka kar ka yi zaton zaka ruɗeni da kuɗi, kuma kar ka sake nemana"
Khalifa ya ce "A'a Samha, kar ki yi gaggawa, ki yi tunani dai"
"Babu wani tunani da zan yi" ta tashi ta mayar da tabaranta, ta na ƙoƙarin tafiya, Khalifa ya sha gabanta ya ce"Samha ki na abu kamar ba wayayyiya ba, ki rubuta ki ajiye, za ki neme ni da kanki a nan gaba"
Ba ta kuma tanka masa ba, ta raɓa shi ta wuce.
***
Abdallah ya na ta wanke kayan mama tare da na ruma, mama kuma tana aikace-aikacenta, ruma tana ta yanka salak, sai ta ajiye wuƙar ta riƙe haɓa ta ce "Mama, kin san wani abu?"
"A'a"
"Ba kin ce mini mutane ta baki suke haihuwa ba?"
Mama ta ce "Eh"
"To wallahi akuyoyi ta É—uwawu suke haihuwa, ta wurin kashinsu in gaya miki, É—azu da na kai markaÉ—e na gani a gidan"
Abdallah ya ce "An zo wurin"
Mama ta yi tsuru ta rasa me zata gaya wa ruma.
"Wallahi mama da gaske nake, ta wurin kashi suke haihuwa, akuyar ta din ga kuka, baki ga abin ƙyama ba, na tsura mata ido, ta bani tausayi, Allah ya taimaki mutane ta baki suke haihuwa, idan ka haihu ta wurin kashi, ai idan ka na ji kashi sai dai ya zubo, dan wurin ba zai rufu ba"
Mama ta share ruma, ba ta ce mata uffan ba, hakan bai sanya ruman ta gaji ba ta kuma cewa "Mama kaji ma fa ta wurin kashinsu suke yin ƙwai, to Meyasa mutane suke haihuwa ta baki, na ga dai baki ƙarami ne".
A ƙule mama ta ce "Ke ki ƙyaleni, idan na kuma aiken ki kai markaɗe, ki ka kai gidan sai na zane miki jikinki, ita ma saboda wauta ta bari ki ke kallon haihuwar akuya"
Ruma ta yi shiru ta sunkuyar da kai, Abdallah kuwa kamar ya bushe da dariya, ganin yadda mama ta hasala, gashi ba abin kayi wa ruma bayani ba, ka na gaya mata abin da kan ta bai É—auka ba, zata kuma gangamo maka wata maganar.
Ko da dare yayi, ruma ta na shirin kwanciya barci, ta ce "Mama, dan Allah ki tasheni na yi sallar dare, zan roƙi Allah abubuwa da yawa"
Mama ta ce "To, Allah ya sa silar shiriyar kenan"
Ruma ta kwanta ta ji daɗin katifar, bacci ya fara ɗaukarta, ta ce "Mama ko na baki sallahun Addu'ar ne, ina ga ba yau ba, ba zan iya tashi ba, ki yi mini addu'a Allah ya sa na samu saurayi nima na din ga zance, 'yan ajinmu na islamiyya su yi ta bayar da labari, ni kuma ban san me ake ji a zancen nan ba, amma dan Allah kar ki roƙo mini mummuna mama"
Mama kawai ta cigaba da abin da take, ruma ta gama surutanta, bacci yayi awon gaba da ita.
Da safe kowa yana ta azamar ya kammala abin da zai yi da wuri ya fita, ruma kuwa sai cin abinci take sannu a hankali ta na murmushi.
Abdallah ya kalleta ya ce "Ke lafiyarki kuwa?"
Ta yi murmushi ta ce "Mama jiya kin yi mini addu'ar da na baki sallahu kuwa?"
"Ruma addu'a, ai kullum cikin yi muku nake"
Ruma ta sake murmushi ta ce "Abdallah ka san mafarkin me na yi yau?"
"A'a"
"Mafarki na yi wai ana bikina, kai ka ga angon mai kyau, kai Allah dai ya sa na yi tsayi ayi mini aure, dama Hudu mai kayan miya jiya yaƙi sallamata, wai ni ba matar aure bace ba, ba ka ga angon ba, sai so nake na ɗago na kalleshi ina ta irin sunkuyar da kan nan na amare, ina...... Shiru ta yi da idonta ya sauka a cikin na mai sunan Baba a tsaye, ya naɗe hnnayensa ya na kallonta.
AYSHERCOOL
08081012143
[26/07, 9:03 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*
Ku yi subscribing YouTube channel É—in
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
No comments