Kanwar Maza Book 1 Page 12
12
Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce "Sata ki ka koma yi kenan ko?"
Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.
"Ba zaki buÉ—e baki ki yi mini magana ba?"
"A'a Yaya wallahi ba sata nake yi ba"
"To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?" Ta girgiza masa kai.
Ya ce "Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki"
Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce "Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo"
Gwaggo ta ce "Ku dai din ga haƙuri yarinya ce, ƙuruciya ce kawai take damunta"
Huzaifa ya yi ƙwafa ya ce "Ba ƙuriciya da yarinta ba, Allah ya sa ɗanyar ƙwaƙwalwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali"
Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murguÉ—awa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.
Daga shiga banÉ—aki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta É“ata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta É—au hijjabi ta tayar da salla.
Ita kanta ba ta san adadin raka'ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar ƙarshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu ɗaya nazari kawai take.
Haka ta idar ta saka addu'a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta faÉ—a sannan take zaman yin addu'a.
Ganin taƙi sallame addu'a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu'a ta tashi.
Ya ce "Oya, kamun kunne"
Cikin marairaicewa ta ce "Dan girman Allah Yaya.....
"Shut up! Zaki abin da na ce ko kuwa?"
Jiki a sanyaye, ta durƙusa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.
Gwaggo ta ce "Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne? Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?"
Ruma ta ce "A'a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi haƙuri"
Mai sunan Baba yayi shiru, ya ƙi kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce "Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?"
Mama ta ce "Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam" ƙarshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba ɗaya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi haƙuri ya ce in tashi"
"Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani waÉ—anda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana"
"Wayyo Allahna na shiga uku, wallahi mama zan iya rasuwa, kaina da wuyana ciwo suke yi mini, bana son na mutu yanzu, bana nafila karatun Alqur'ani ba kullum nake yi ba, gashi ina yi miki abin da ba kya so, bana son na mutu yanzu ban tuba ba, wallahi mama zan iya rasuwa a wurin nan"
Yasir ya ce "Ba ki jigata bane ba, da ki ke iya wannan surutun"
Gwaggo ta ce"Ji min kafirar yarinya, ba nace ki tashi ba kin ƙi, ni babu abin da ya ƙular da ni, irin wannan goho da ya saki kina 'ya mace, kema da azababben taurin kai na ce ki tashi kin ƙi".
Ruma ba ta kula Gwaggo ba, sai cigaba da rusa kuka da tayi, tana magiya da neman taimako.
Cike da ƙuluwa Yaya Aliyu ya ce"Ki yi mana shiru dan ubanki, tun da ba wani ne ya aike ki ki aikata abin da ki ka yi ba" haka ruma ta ja bakinta ta tsuke, tana kuka ƙasa-ƙasa dan wasu lokutan yaya Aliyu ma ba daga nan ba wuri8iya tsare gida da hukunci, dan daga yaya Umar sai shi a zafi.
Har mai sunan Baba ya dawo ruma tana nan tana aikin kamun kunne, tana yi tana faÉ—uwa tana tashi.
Sai da ya dawo sannan ya ce ta tashi, kuma ya ce mata washegari za su gauraya.
Tana miƙewa tsaye jiri ya kwasheta sai amai, Gwaggo ta fito da sauri ta kama ruma, kanta sai juyawa yake saboda azabar wahala.
A zaune ta yi alwala tayi sallar isha'i, ko abinci ba ta nema ba, ta kwanta saboda galabaita, cinyoyinta sai azabar ciwo suke yi mata, dama da fari suna ciwo saboda hawan keke, gwiwoyinta na raɗaɗi saboda duk ta ƙuje su saboda keke, yanzu kuma ga kamun kunne, jikinta kamar an mata duka haka take jin ta, a take wani irin wahalallen bacci ya kwasheta.
Sai dai kwana ta yi da wani irin zazzafan zazzaɓi, wanda ita kanta ba ta san ya hau ta ba, jin surutan ta ya yi yawa a baccin ne ya sanya mama zuwa ta taɓa jikinta, ta ji da zafi sosai.
Duk da mama a ƙule take da ruma, haka ta fita ta ɗebo ruwa ta sanya ɗan ƙaramin towel, ta din ga shafawa ruma ruwa a jikinta.
Tun asubar fari kuwa, ruma amai ne ya tasheta, saboda har a lokacin jiri take yi.
Yanzu ma a zaune ta yi sallar asuba, ta nemi wuri ta kwanta.
Tun mama na basar da ita, har kuma ta fara damuwa, Gwaggo kuwa ta samu wuri É—aya ta zauna sai mita take na masifa a kan mama tana gani aka bawa ruma gwale-gwale amma ba ta ce komai ba.
Bayan gari ya gama wayewa, Gwaggo ta karya ta yi haramar tafiya, sai dai a lokacin ruma ta samu bacci, dan a galabaice take. Gwaggo ta ce kar a tasheta, Abdallah ya tafi rakata tasha, suna ta murna zasu huta, dan dama Gwaggon ta ishe su, ruma ce kawai take son zamanta a gidan.
Mama ta tashi ruma, ta matsa mata a kan lallai ta ci Abinci, ta na ci tana kuka ta É—an sha tea kaÉ—an ta kuma kwanciya, sai dai ko mintuna goma ba ayi da cin Abincin na ta ba, ta tashi ta cigaba da amai.
Ba shiri mama ta ce Aliyu ya zo ya kai ruma chemist a dubata.
Da ƙyar take iya tafiya, suna tafe tana kuka, har sai da ran Aliyu ya fara ɓaci, amma ya shareta suka cigaba da tafiya a hankali. Cikin sa'a kuwa suka tarar ya fito, kasancewar asabar ce, ranar ba ya zuwa aiki.
Ya na ganinsu cikin kulawa ya ce "Subhanallah, 'yar gidan mama yau ke ce ba lafiya?" Ita dai ba ta iya magana ba ta nemi wuri ta zauna. Aliyu ya zauna ya rungumeta, saboda ƙoƙarin faɗuwa take yi.
"Meya sameta haka?"
Aliyu ya ce "Ina ga zazzaɓi ne dai, da amai ta fara jiya"
Bakinta bai mutu ba, ta ce "Kamun kunne aka sakani, kusan awa goma shine ya sani rashin lafiya"
"Subhanallah, waye ya saki kamun kunne kuma?"
"Mai sunan Baba ne"
"To ki yi haƙuri, yanzu dai zan ɗibi jininki na yi miki gwaji, in duba meye ya haddasa zazzaɓin"
Ɗiban jinin da za'a yiwa ruma, tamkar za a cire mata ido, ta dinga kurma ihu, tana fizge-fizge, ga ta da shegen ƙarfi, da ƙyar Aliyu ya riƙeta aka ɗebi jinin nan.
Kuka har da majina, Aliyu ya dinga dungure mata kai yana zaginta.
Ya gama gwaje-gwajen da zai yi mata, ya ce "Malaria ce ke damunta, dan haka akwai buƙatar ayi mata allurai, da kuma magunguna"
Ruma ta yi masa zuru da ido, tana jiran ta ga a ina za ayi allaurar.
Ya haɗa alluransa ya nufo ta, ta miƙe tsaye.
"Ke malama ki tsaya, dan ba zaki sake wahalar da ni ba"
"To a ina za ayi mini allurar?"
Mai chemist ya ce "Ai a baya ake yin ta"
"Wai bayana" tayi maganar tana nuna bayanta.
Nasiru mai chemist ta ce "A'a a mazaunai"
"Suwaye mazaunan?"
Aliyu ya haÉ—e rai ya ce "Ke juya ki tsaya ayi miki allurar nan mu tafi, kin san sarai a in da za ayi".
Ta riƙe skirt ɗin ta gam ta ce "Ni wallahi ba zai ganni ba"
Aliyu ya fizgota, ya riƙeta da ƙyar suka danneta suka yi mata, Aikuwa ta din ga zunduma ihu, kamar sun mata wani abu.
Haka aka gama yi mata treatment, suka taho gida, ban da uban kuka babu abin da take yi.
"To subhanallah, ko me aka yi mata kuma take wannan uban kukan haka oho" mama ta yi maganar tana fitowa tsakar gida.
Aikuwa suna shigowa, ta nufi mama tana kuka.
"Meye haka, kukan me ki ke haka,ki ke É“are baki?"
"Mama yaya Aliyu ne da Nasiru mai chemist"
"Suka yi miki me?"
"Bayan ya É—ibar mini jini, kuma suka buÉ—e mini tsiraici na aka yi mini allura"
Mama ta ce "Subhanallah"
"Mama ba ke ki ka ce ɗuwawu tsiraici bane ba, amma har da Yaya Aliyu ya riƙe ni, Nasiru mai chemist ya ganni, wallahi ban yafe ba"
Mama ta girgiza kai, ta ƙiftawa Aliyu ido sannan ta ce "Haba Haidara, ya zaka yi mini haka, dan me za'a buɗe mata jiki ayi mata allura?"
Aliyu ya ce "To mama ai larura ce, ko a addinance ba haramun bane".
Cikin masifa ta ce "To shi yayana ne da zai ganni? Har da taɓani ya yi mini allura a wurin"
Aliyu ya ce "Sa'anki ne ni, uban me za a kalla a jikin naki?"
"Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, Allah ya jijjigo bala'in duniya da lahira ya ɗora masa, tun da ya ganan mini tsiraici na"
Mama ta ce"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin Addu'a ce haka, kar in kuma ji, baki san larura ba?"
Aliyu ya ce "Sakarya, kamar ba tsairaicin ki ka je kina kaÉ—awa a gaban mutane ba jiya"
Umar ya shigo É—akin mama, suna magana, bai kula ruma ba amma dan ya duba jikinta ya shigo.
Tana kwance ga zafin ciwo, ga na takaicin allurar da aka yi mata, zafin allaurar bai dameta kamar ganinta da mai chemist ya yi.
Sai da yamma mama ta sakata ta yi wanka, ta canza kaya ta ɗan ji ƙwarin jikinta.
Sai da ta kwana uku tana fama, sannan ta ware gaba ɗaya, sai dai rashin lafiyar da tayi ya sanya aka mance da laifin da ta tafka, kowa sai lallaɓata yake, ban da Huzaifa.
Ta ware sarai har ta koma makaranta, kullum mama cikin nasiha take yi mata, tare da yi mata addu'a da fatan shiriya.
Tun daga ranar ruma ta daina bi ta hanyar chemist É—in Nasiru, idan kuwa ta ganshi ko kallonsa ba ta yi, balle ta gaishe shi, a cewarta É—an iska ne tsairaicin ta ya kalla.
"Mama wai yaushe zaki haihu ne, babannin 'yan ajinmu sai haihuwa suke yi, amma ke ban taɓa ganin kin haihu ba"
Mama ta ce "Ikon Allah, ba gaki na haife ki ba, ai ke ce auta ha zan kuma haihuwa ba, sai dai in kin girma kin haifa na É—auka"
"To ni yaushe zan haihun?"
"Sai kin girma kin yi aure"
Ruma ta ɗan yi jimm sannan ta ce "To ni so nake na haihu, ina son ƙani ko ƙanwa da zan din ga wasa da su"
"Ruma ki ka haihu yanzu ai a nemi tsari, sai an yi aure ake haihuwa"
"To gaskiya mama ni so nake na haihu yanzu"
Usman da yake jin hirar ta su ya ce "Ke, idan ki ka haihu ba aure tsanarki za ayi, a kore ki daga gidan nan da unguwar ma gaba ɗaya, shi ya sa ba a wasa da maza, ki ka bari namiji ya taɓa ki to ciki zaki ki haihu, kuma korar ki za mu yi"
Waro ido ruma tayi ta ce "Amma ku kuke taɓani?"
"Ai mu yayyenki ne, muharramanki ne mu"
Ruma ta dafe ƙirji ta ce "Allah ya rufa mini asiri, ai da ban sani ba, taɓ idan aka koreni ina zani?"
"Oho miki dai, wannan damben da ki ke da maza ma, idan ba ki daina ba, sai dai ki ga kin haihu, kuma sai kin bar mana gida"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "In sha Allah hakan ma ba zata faru ba, ai ni ban san hakan abin yake ba, Allah ya sa na yi tsawo na auri kyakykyawa mai kuÉ—i".
Mama ta ce "Ke zan ci ubanki ke da kyakykyawa mai kuɗin nan, miji na gari ake roƙon Allah, fitsararriya"
"Ni dai gaskiya bana son mummuna, mai kyau nake so"
"Ke dalla ware, da wannan munin za ki auri kyakykyawa?"
"Ni dai yaya Ussy, ka yi mini Addu'a, ka san wa zan aura a cikin 'yan ball".
Miƙewa ya yi ya ce "Ba ni da lokacin jij wannan shirmen na ki".
Tun daga wannan lokacin, ruma take kaffa-kaffa, da gudun kar wani namiji ya taɓa ta, saboda kar ta haihu a koreta ta shiga uku, kuma ta san idan aka koreta ba kuɗin mota za a bata ba, balle ta tafi ko ƙauye ne wurin Gwaggo.
Yau gaba É—aya mama ta kasa gane kan ruma, tun da ta dawo daga makaranta yanayinta ya nuna kamar tana cikin damuwa.
Ba irin tambayar da mama ba ta yi mata ba, amma ta ƙi gayawa maman dalilin damuwarta ta, ta ce cikinta ne yake yi mata ciwo kawai
Mama ta aiki ruma sayen maganin sauro, ta je ta sayo, ta dawo ta tsaya a soro tana kuka.
Huzaifa ne ya sameta a soron tana kuka, dan sai da ya É—an tsorota.
"Ke me ki ke yi a nan?"
Cikin kuka ta kira sunansa "Huzaifa"
"Na'am" ya amsa.
"Ka san wani abu?"
"A'a sai kin faÉ—a"
"Yaya Usyy ne ya ce mini idan namiji ya taɓani, zan yi ciki in haihu, kuma korata za ayi daga gidan nan, sai malam ya aikeni karɓo masa chalk, da na kawo masa hannunsa ya taɓa nawa. Na tambayi 'yan babban aji na gaya musu abin da yaya ussy ya gaya mini, suka ce eh haka ne wai ciki ne da ni, ka ga cikina ma ya fara kumbura yanzu ya zan yi bana son a koreni dan Allah ya zan yi" ta yi maganar har cikin zuciyarta tana rushewa da kuka.
Huzaifa a ransa ya ce 'Alhamdilillah, na samo maganinki'
"Tabbas Deluwa kin kwaso mana abin kunya, yanzu abin da zai faru shi ne, ki haÉ—a kayanki a É“oye, cikin dare na kai ki tasha ki bar gidan nan, dan idan mai sunan Baba ya sani sai ya jefa ki a rijiya"
Sake rushewa ta yi da kuka har da majina, ya yi saurin cewa "Sai mama ta jiyo kina kuka asirinki ya tonu ko?"
Ta goge hawanyeta ta ce "To ya zan yi?"
"Shikenan, zan rufa miki asiri, amma zaki din ga yi mini wankin uniform".
"Eh na yadda, amma dan Allah kar ka faÉ—awa mama, bana son a koreni dan Allah"
Huzaifa ya yi wani murmushi cikin mugunta ya ce "To na ji, goge hawayen ba zan tona miki asiri ba"
Abu kamar wasa, ruma ko abinci ba ta iya ci, gashi kullum sai ta wanke wa Huzaifa kayan uniform.
Mama ta gaji ta ritsa ruma, har da bulala sannan ta zauna ta yiwa mama bayanin abin da yake damunta.
Mama ta yi salati ta sanar da Ubangiji, gaba ɗaya ruma ba ta da wayo, ga shegiyar tambaya idan kuma ka yi mata bayani yadda za ta fahimta, nan ma ta yi wata kwaɓar.
Sai da mama ta yi da gaske, sannan Ruma ta yadda ba ta da ciki, dan har da nunawa mama cikinta wai ya kumbura É—a ne a ciki.
******
Ta na zaune a kan sallaya ta idar da salla, sai dai ta lula duniyar tunani, ba lazamin take yi ba.
Kamar daga sama ta ji ana kiran sunanta, ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.
"Ohh Nusaiba, an gama girkin daren ne?"
Nusaiba cikin damuwa ta dubi Ammi sannan ta ce, "Ammi, tunanin me ki ke yi haka ne? kin san fa ba ki da cikakkiyar lafiya"
Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Nusaiba tunanin nan na dole ne, shi yake yin kansa, abubuwa sun yi mini yawa, bana son na nuna gazawata amma ni na san na gaza na kasa shawo kan komai, al'amura na ta ƙara dagule mini"
"Me kuma ya faru ne?"
"Mahmud, lamarinsa yana damuna, ga kuma yadda aka addabawa yarinyar nan a cikin gidan nan, haƙurina ya fara ƙarewa, duk wanda ya taɓa Iman ni ya taɓa raina ya na ɓaci fiye da tunaninki"
Nusaiba ta gyara zamanta ta ce "Ammi, kin san wannan duk shirin Mummy ne, so take ki magantu ku raba abin faɗa a cikin garin nan, ita take buga miki wannan wasan, ki ƙyaketa kuma ki yi haƙuri ki ɗauke kan ki daga Mahmud, ba ga takawa nan ba, mu da shi mun isheki rayuwa su je su ƙarata mana"
Ammi ta girgiza kai ta ce "Nusaiba kenan, ba zaki gane ba, tashi maza ki je ki tabattar an gama komai, sannan ki kira mini Iman, ba na son zamanta ita kaÉ—ai"
Nusaiba ta ce "To shikenan Ammi, bari na je".
Sannu a hankali yake tafiya, tamkar ya na tausayawa ƙasar da yake takawa, har wani rangaji yake kamar wanda ake yiwa kiɗa.
Fuskar nan a murtuke babu annuri, in da ya sa a gaba kawai yake kallo, yake burin cinmma. Babu tsammani suka yi kiciɓis a baranda, ba tare da ɗaya ya san ɗaya ya taho ba, kuma aka rasa wanda zai bawa wani hanya ya wuce.
Kallon-kallo suka yi na wani É—an lokaci, sannan ya lumshe idonsa a hankali ya buÉ—e. "Banihanya"
Kallonsa ya yi irin kallon ba ka isa ba ya ce "Ni da kai waye ya tarewa wani hanya?"
Cikin tsawa da zafin zuciya ya ce "Ka bani hanya na ce"
Murmushin gefen baki yayi, tare da rausayar da kai, yayi taku biyu ya koma gefe ya bashi hanya.
Sai da ya ƙare masa kallo, kamar ba zai wuce ba, sannan ya cigaba da takawa sannu a hankali ya wuce.
Ya waiwaya ya bi bayansa da kallo, yayi wani murmushi sannan ya ce "Zamu ga wanda ya fi iya buga wasan sa"
(A mini afuwa ban editing ba)
AYSHERCOOL
08081012143
[19/07, 8:42 am] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
Na Aisha Adam (Ayshercool)
MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES
https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
Ku yi subscribing YouTube channel É—in
@Cool Hausa Novels, domin samun daÉ—aÉ—an litattafan hausa na sauraro.
No comments