Furar Danko 85

 85





.........Lulu duk da ranta a dagule yake tayi dauriyar dannewa saboda yaran, kasancewar Maryam akwai hankali tunda daddare ta tsara musu su tafi yau suba ma'auratan waje, sai kuma akai sa'a har su Amrah suka fahimceta. Koda gari ya waye sukaga basu fito ba basu damu ba suka gyara gidan tsaf sukai break fast. Nasu sukaci suka shirya musu nasu a table. Sun kammala kenan Lulu ta fito. Gaisheta sukai su duka cikin haɗa baki, ta amsa musu tana murmushin ƙarfin hali, dan girmamawa na ɗaya da ga cikin abinda Lulu keso gana ƙasa da ita. Wannan kuma shine mataki na farko da dangin Smart suka kama mata zuciya da shi, yau gashi har ƙannenta sun kwatanta abinda bata taɓa gani ba. Kamar yanda suka tsara Maryam ce ta sanar mata zasuje gidan ƙunshi su taho da mai ƙunshi da tace tana so. Lulu bata kawo komai a ranta ba ta ce, “Da sassafen nan kuma Maryam. Ku bari sai anjima ni ƙunshin ma kamar na fasa kuma”.


    “Kai aunty dan ALLAH karki fasa. Ai zamuje ne dan ta sani inma tanada wani aiki kinga ta kammala da wuri bawai yanzu zata zo ba”.


   “To shike nan, amma har ku duka zakije?”.


  A tare suka amsa mata da eh. Key ɗin motar ta dake a falon ta miƙama Amrah dan sun iya driving duk da dai ba basu mota ake ba sai ta kama. Cikin gargaɗi tare, “Banda ganganci Please”. Dariya kawai su Afrah sukai dan sun san dai aunty Lu.. ɗin su indai tuƙin ganganci ne ita ɗin master ce. Sallama sukai mata suka fice, dama sun fidda kayansu tun ɗazun..


   Kwanciya tai a falon batare da neman abincin da zata ci ba duk da kusan goma ne yanzun. Tana a wajen kwance ba barci take ba har sha biyu, tunanin abubuwa kawai take daban-daban, babu alamar su Maryam dan haka ta ɗaga waya tai kiran su Amrah. Cikin dariya suke sanar mata ai su suna ma gida, sai da suka fara ajiye su Asma'u ma sannan. Shiru kawai tai da mamakin wai ita yaran nan zasu yaudara, sai kawai tai ƙwafa ta yanke kiran. Ɗan jimm tai saboda abinda take jiyowa kamar ƙaƙarin amai, kamar zata share sai kuma ta miƙe da sauri jin abin na ƙaruwa. Sam batai tunanin Smart na gidan ba, ɗakin nasa ta shiga dan anan take jiyowa, nan ɗinne kuwa a cikin toilet, mamaki ya kamata duk da matsanancin haushinsa da take ji na abinda ya faru sai ta nufi bayin. Sosai gabanta ya faɗi, har bata ma san sanda ta afka bayin ba inda yake.


    “Lafiya kake kuwa?”.


  Bai iya bata amsa ba dan ya gama galabaita da aman, dole ta ajiye komai da ke ranta kuma ta shiga taimaka masa ya wanke bakinsa da fuska, da taimakonta ya fito ya sake hawa gadon ya kwanta. 


      “Please lulluɓe ni”.


    Ya faɗa da ƙyar. Lulluɓe san tai hankalinta a tashe, dai-dai nan kiran Ahmad ya shigo wayarsa, har ya lumshe idanunsa ya buɗe, ita ya kalla yayinda ita kuma take kallon wayar. “Waye?”. Ya faɗa a hankali. Wayar ta miƙo masa da faɗin, “Besty kasa”. Sake maida idanun nasa yay ya lumshe da faɗin, “Ahmad ne ɗaga”. Kafin ta ɗaga ɗin wayar ta yanke, tana ƙoƙarin kira Ahmad ɗin ya sake kira. Ɗagawa tai ta saka a Hansfree da faɗin “Hello”. Daga can Ahmad ya amsa mata duk da yayi mamakin jin wayar a hannunta. Gaisheshi tai da sanar masa bai da lafiya. 


     Hankali tashe Ahmad ya ce, “Ya ALLAH gani a ƙofar gate ai”. 


  “Okay to bara ina zuwa”.


Tai maganar tana yanke kiran. Wayar ta ajiye ta miƙe, Smart da ke saurarensu ya buɗe idanunsa a kanta, a hankali ya furta “Please kar ki fita a haka kisa hijjab”. Harararsa tai batare da tace komai ba ta fice. Samun kanta tai da shiga ɗakinta ta ɗauka hijjab ɗin ta saka sannan taje ta buɗema Ahmad ɗin. Ita tai masa rakkiya har ɗakin Smart ɗin ta fito ta barsu. 


     Bayan Ahmad yay masa sannu ya ce, “Tashi zakai mu tafi asibiti”.


Kai Smart ya girgiza masa yana ɗan buɗe idanunsa, “Basai naje asibiti ba zai bari da kansa in sha ALLAH. Tunda ma na samu nayi aman shike nan”.


   Ahmad ya riga da yasan miye matsalar Smart ɗin. Dan haka yay shiru kawai. Dai-dai nan Lulu ta shigo ɗakin da sallama. Amsa mata Ahmad yayi. Ta ajiye tray data haɗo abincin tana faɗin “Ya sanar maka abinda ke damun nasa kai ko?”. Murmushi Ahmad yay da bata amsa. “Kin san mutumin naki ai, yanzu ma fama nake da shi muje asibiti yaƙi”.


     Kallonta takai kan Smart, ganin shima ita yake kallo ƙasa-ƙasa saita janye nata da ɗan taɓe baki. Shi Ahmad ma sai suka bashi dariya. Dan haka ya miƙe. “Inaga bashi abincin ni bari naje na samo masa magani, dan tunda yace bazaije asibitin ba to bazai je ba”. Bai jira cewarta ba ya fice. Ɗan hararar Smart Lulu tayi, a taƙaice ta ce, “Ka tashi”. Sake buɗe idanun nasa yay ya zuba mata su na kusan minti ɗaya, ita kuma ta kauda nata dan tun ɗazun yanda idanun nasa launinsu ya sake canjawa suka fito a sak na macizan da take kiransu taji bata son ya kalleta. Hannu ya miƙa mata alamar ta kamashi. Kamar zata share sai kuma dai ta kama dan ya ɗan bata tausayi kuma. Harya faɗa kamar wanda ya kwana biyu yana ciwon. Shayin data haɗo masa ta miƙa masa, babu musu ya amsa tare da motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Thanks”. Koda ta miƙa masa soyayyan doyan sai ya girgiza mata kai alamar bazai ci ba. Kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta maida doyar ta ajiye. Tana zaune ta ɗan juya masa baya tana latsa wayarta har ya kammala, kofin ya miƙa mata ya koma ya kwanta, ta tattare kayan ta fita da su, a lokacin kuma Ahmad ya dawo, ruwan da ya buƙata da Smart ɗin zai sha magani ta ɗakko masa, da ga haka ta koma falo tai zamanta...


   Ahmad bai bar gidan ba sai da Smart ya samu barci, bayan wucewarsa Lulu ta leƙasa, ganin yay barci ta ɗan sauke ajiyar zuciya da hararsa kamar yasan tanayi. Ɗakinta ta nufa ta ɗan kwanta itama dan shirun gidan kuma duk sai yay mata babu daɗi. Kusan a tare suka tashi bayan la'asar, tai wanka tai salla dan yanzu kam Alhamdullah, idan ma tai kamar zatai sakaci lokaci ya wuce sai taji duk babu daɗi har sai ta tashi tayi sallar take samun nutsuwa. Cikin skert dogo baƙi da ƙaramar top baƙa itama datai mata ɗas a jiki ta fito, kanta babu ɗankwali sai gashin da ya sha gyara yanata walƙiya. Wayar da take dannawa tana charting da aunty Naja'atu yasa bata lura da shi ba har sai da takai zaune. Shiko tun fitowarta ya zuba mata idanu, murmushin da take yi ya matuƙar ƙawata ƙyawunta da motsa rauninsa. Hakama kwalliyar tata ta ɗauki hankalinsa duk da ita hakan normal ne a gareta badan wani birge miji ko wani abu ta saka ba tunda dai sune kayanta na koyaushe fiye da atamfa. Ƙaramin gyaran murya da yay ya sata farga da shi, dariyar da takeyi a hankali ta haɗiye ta ɗago idanunta da sukai wani tar-tar da su da haske mai ɗaukar hankali kasancewar duk yau da ba'asha komai ba. 


   “Dama haka ake jiyyar mara lafiya Madam?”.


   Hararsa ta ɗanyi da taɓe baki. “Ka dai san mai jiyyarka ba dai Mawaddat ba”.


     “Uhm hakane ashe Ahmad ne kuma fa”. 


    Ya faɗa yana danne dariyarsa. 


  Sake taɓe bakin tai taƙi cewa komai. Da ga haka shiru ya ratsa falon, yana tunanin faɗa mata zancen tafiyarsa da ya taso ne, dan abinda ma ya kawo Ahmad kenan, amma sai yaga bari dai ya bari ta sake nutsuwa ko zuwa gobe in sha ALLAHU. Kusan mintuna goma ya sake takalota da faɗin, “Ba abinci gidan ne? Ina kuma yaran nan banji motsinsu ba?”.


      Yanzu kam kai tsaye ta bashi amsa da “Sun wuce”.


   “Abincin fa?”.


“Na daina girki a gidan nan”.


“Miyasa?”.


   “Ba sai da dalili ba, dama can ra'ayi nayi, yanzu kuma na daina sai ka bari sai ka auro matar da zata maka”.


      “Kishiya kike sha'awa kenan?”.


   Kamar bazata tanka masa ba sai kuma tai murmushi. “Sai dai idan yau zaka aurota ko gobe kafin cikar jibi da zan ƙara gaba maybe wasu su kalleta a matsayin hakan”.


    Murmushi kawai ya saki, maimakon cewa wani abu akan batun nata sai cewa yay “Bani furar da Ahmad ya kawo Please dan yunwa nake ji”. Kamar bazata je ɗin ba sai kuma ta miƙe. Babu jimawa ta dawo da furan da kofi ta ajiye masa ta koma inda ta tashi. Television ta kunna shi kuma ya zuba furar ya fara sha. 


  “K mi kika ci?”.


 “Ba buƙata”.


Ta faɗa a takaice. 


   “Okay amma da kinsha furan da ga gidan Ammah ya amso ta”.


   Ɗagowa tai ta kallesa. Sai ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa. 


      “Gama ka bani kofin bana jin sake tashi”. Ta faɗa tana maida kanta ga wayarta. Bai sake magana ba har ya gama ɗin ya zuba mata, sai dai bata da yawa dan haka ya miƙe da kansa yaje kitchen ya sake ɗakko wata ya ƙarasa cika kofin ya miƙa mata. Hankalinta nakan waya take shan furar harta shanye, sake ƙarawa tai. Sai da ta shanye ta biyun yay ƙaramar dariya da faɗin, “Babu wata furar Ammah da kika sha yarinya a titi ya sayota”. Da sauri ta kallesa tana yamutsa fuska, ya sake sakin dariya da nuna mata 8-10. Filo ta ɗauka ta jefa masa da yin ƙwafa tana harararsa, sai kuma ta fara ƙaƙarin amai shiko ya cigaba da dariyarsa. Kofin takai kitchen ta wanke dan bata ƙaunar ƙazanta, duk da kuwa aikin na cimata rai dan ma yana ƙoƙarin taya ta ne, tun tana ƙorafin mai aiki har ma ta bari tunda dai taga kwanakin sun ƙare mata a gidan. Falon ta dawo ta cigaba da ɗan kallon abubuwa a TikTok. Shiko yana kwance shiru ya zuba mata ido ta ƙasa kawai yana kallonta. Kiran sallar magrib ne ya tadasu su duka. Smart ya wuce massalaci ita kuma ta tafi ɗaki. Bai jimaba ya dawo gidan saboda abinda ke damunsa ba wai ya gama sakinsa bane gaba ɗaya, jarumtar da ya saba ce kawai ta dannewa. Bai samu Lulu a ɗakin ba dan itama tana nata ɗakin a cikin makamancin irin nasa yanayin koma ace wanda yafi nasan. Dan wani abu ne ke faman ratsa mata jiki mai ban mamaki. Ga tsigar jikinta sai faman tashi take kamar mai jin sanyi. Al'amarin kamar wasa sai ya fara neman fin ƙarfin Lulu, dan da ƙyar ta iya tashi tai sallar isha'i........✍️


   😵‍💫Lulun mu muya hwaru kuma🥲?

No comments