Furar Danko 84
84
.......Sai da ya kai kwance duk tana kallonsa sannan ya cigaba da faÉ—in, “Zan kwana anan dan karma yaran can su fahimci wani abu daban har su faÉ—a a gida. Bazan so Ammah taji abinda bashi take fata ba a rayuwar gidana”.
Duk da maganar tasa ta É—an zabureta a zuciya sai ta kanne da tureta gefe ta É—auke kanta. Sai kuma ta juyo da tura masa bargo ta ce, “To ga duvet nan koma sofa. Dan wlhy ban iya kwana da mutum biyu a gado ba, a cikin É—aki ma kowa da makwancinsa ko yara ne takura nakeyi. Balle ma kai Æ™ato da kai ai saika sakani firgita”.
Dariya maganar tata ta bashi, amma sai ya kanne baiyi ba yay É—an murmushi kawai da kai hannunsa kan tarin fillos dake a gadon ya jawosu. Ita ya kalla da faÉ—in, “Kinga É—an matsa gaba”. Matsawar tai shi kuma ya shiga jera fillos É—in a tsakkiyarsu. “Gashi nan nikam an raba basai kin korani saman sofa ba dan bazan iya barci acan ba nima.”
Harararsa tai da sake faÉ—in, “To nifa wlhy zan iya tsorata?”.
“Saboda mi? Bayan kin san dai ni ne kuma bazan kawo wani hari ba inma yaÆ™in Æ™asa da Æ™asa kike tsoro”.
Ba fahimtarsa tai ba ita kam. Dan haka kai tsaye ta ce, “Kawai dai bana son namiji kusa dani, dan yana tuna min abinda bana son na tuna?”.
(Anzo wajen) ya faÉ—a a zuciyarsa. A zahiri kam sai yace, “Ai komai nada dalili. Miyasa hakan?”.
“Humm manta kawai”.
Ta bashi amsa tana maida hankali ga laptop ɗin tata. Shiru yay dan baya son nuna mata zaƙuwarsa na son ji. Sai ma ya lumshe idanunsa kamar wanda yay barci. Itama aikin ta cigaba da yi zuciyarta dai na wasuwasi akan kwanansa a ɗakin, wata kuma na ƙoƙarin nusar da ita na yau ne ai kawai. Bashi da wata manufa kuma tunda bai taɓa gwada makamancin hakan ba sai yau da yaran nan ke a gidan. Haka dai ta cigaba da saƙawarta da kwancewa har aikin ya nema gagararta, da ga ƙarshe dole ta kashe system ɗin da tattare takardun data baza. Juyawa tai tana kallon Smart da ke sauke numfashi a hankali, da gaske yanzu kam yayi barci dan a gajiye yake matuƙa. Sai ta samu kanta da sauke numfashi mai nauyi itama. Sauka tai a gadon ta nufi bayi, bata jima sosai ba ta dawo. Kasancewar dama wutar ɗakin ba wata mai haske bace can sosai ya sata ɗan tsayawa tana kallonsa da alama dai har yanzu zuciyarta na rawa, dan kallon da take masa bawai kallone irin na ka ɗauki hankalina ba, a'a kallone irin na nazari akan son yanke hukuncin na yarda ko kar na yarda?. Ta jima a wajen tsaye har ƙafafunta suka fara mata dayi sannan ta jasu da ƙyar ta koma saman gadon dai ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya a jere. Addu'ar barci da yakan gargaɗeta ta dinga yi wanda Alhmdllh ta yi nisa kaɗan a koyansu ta fara, sai dai bata zaton takai ko rabi ba barci ya kwasheta. Dan itama ɗin dai akwai gajiya tattare da ita, sannan da rana bayan dawowarsu ta sha syrup kwalba ɗaya. Gaba ɗayansu kamar wasa duk sai barcin yay musu nauyi sosai, kusan gabannin asuba Smart ya farka, jin abu a jikinsa da ɗumin da baiyi kama dana bargo ba ya sashi buɗe idanunsa da ke cike da nauyin barci da ƙyar. Akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta ya sauke cikin ɗan hasken ɗakin, barcinta take hankali kwance lafe a jikinsa kamar wata ƴar mage. Sai da ya ɗan waro ido na mamakin yaya akai hakan ya faru? Juyawa yay ya kallesu su da gadon, sai yaga tabbas shine ya ture filos ɗin tsakkiyarsu da ya jera ya dawo inda take. (Ɗan Ammah kaika fara kawo wannan harin na tsakanin ƙasa-da-ƙasa fa kenan) ya ayyana a zuciyarsa. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yay ɗan luuu da idanu yana maida kansa ga filonta da ya dawo kai. Kamata yay ace ya koma inda yaken kafin ta farka dan kuwa dai yasan zai sha cara, to amma yana yin wani motsi fa zata iya farkawa matsalar da yake gudun ta afku saboda a jikinsa take sosai, sai kawai ya zaɓi zubama sarautar ALLAH ido tunda akwai sauran daren, shima sabo da tashi yin nafilfilin daren ne ya sashi farkawar. Gashinta da duk ya zazzame da ga cikin ribbon da aka ɗauresa yasa hannu ya gyara mata, sai ƙyaƙyƙyawar fuskar tata ta sake fitowa fes da ƙyau. Kwanciyarta tai ƙoƙarin gyarawa da sake mamuƙesa a cikin barci batare data sani ba, dan ta kasance mai ɗabi'ar rungume filos idan tana barci, a yanzun ma dai da alama hakan take tunanin tayi, batasan baban filos bane gaba ɗaya😂. Ba shiri Smart ya rumtse idanun da ƙarfi yana cije lips, (Wayyo ɗan Ammah itamafa ta kawo hari wlhy, shike nan ƴan tada zaune tsaye sun fara tattaro makamai) ya sake faɗa a zuciyarsa yana matse jikinsa a waje guda sai dai ina a jikin nasa take ma gaba ɗaya, ta kuma cigaba da barcinta hankali kwance. Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da buɗe idanun da ƙyar a kanta. Wannan fa shi ake kira siye da kuɗi yafi siye da bashi, dan fuskarta ta sake matsowa kusa da tashi sosai ga numfashinta da ke sauka masa a kan fuska na sake rikita masa lissafi. Maida idanun kawai yay ya rumtse, sai dai zuciyarsa da gangar jikinsa sunki yarda da wannan lallashin, har takai baima gama yanke hukuncin abinyi ba kawai ya sauke lips ɗinsa akan nata, tun yanayi cikin shakka-shakkar karta farka har ya dake kawai abinsa yama ɗaura hannunsa sosai a jikinta ya sake turata ciki. Sam Lulu bata da nauyin barci, dan haka ta farka kuwa jin baƙon al'amari a gareta, sai dai nauyin da idanunta sukai da ma jikin nata ya sata jan sakanni kafin ta fahimci mike faruwa. Wannan ma wata dama ce ga Smart dake shagulgulansa batare da yasan ƙasar da ya kaima harin ta farka ba. Lokacin da ya kamata ta ɗauki mataki itama jikin nata ya fara amsar harin nasa, sai ta samu kanta da ƙoƙarin maida murtani. Rikicewa Smart ya sake yi illahirin jikinsa ya shiga rawa, sai ya nema canja salo akan fiye da abinda yake yin. Anan ne fa Lulu ta dawo hayyacinta, jikinta daya fara rawa ta fisge taja baya, sai kuma ta shiga kallon gadon da sauri, cikin ƙarfin hali da dafe kai shima Smart ya tashi zaunen. Masifa take son masa, amma bata da wani ƙarfin yinta, sai kawai ta sakar masa kuka.
(Ya ALLAH) ya ambata a zuciyarsa da janye hannunsa da ya dafe goshi ya É—ago idanunsa da sukai matuÆ™ar kaÉ—awa ya zuba a kanta. Lips É—insa na É—an rawa ya ce, “Mawaddat...” yama kasa Æ™arasa abinda yake son faÉ—ar, sai kawai ya sake dafe kan tare da komawa ya kwanta..
Hakan da yay sai ya sa wani irin takaici sake mamaye zuciyar Lulu wato ma kenan yayi hakanne dama da shiri. Tattaro dukkan ɓacin ranta take a maƙoshi, amma ta kasa furtawa, sai kawai ta tura kanta cikin ƙafafunta ta sake sakin kuka. Har cikin tsakkiyar ransa yake jin kukan nata, ga bala'in daya ƙulle masa ciki ya sashi kasa koda iya motsawa, jin ta sauka a gadon ya sashi buɗe idanun nasa da ƙyar, dai-dai nan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fita tare ba banging nata da ƙarfi har sai da ya rumtse idanunsa. Har aka kira asuba ya kasa tashi saboda halin da yake ciki, ita kuma bata dawo ba, addu'a kawai yake ALLAH yasa ba ɗakin yaran ta tafi ba, duk da baya jin zatai hakan. Duk da halin da yake ciki shi ya cancanci tausayi amma shi ita yake tausayawan, dan yau ya sake tabbatar da akwai wani abu a ranta da yasa take ma tsanar maza da ƙara ƙaimi wajen son ɗaukar mataki akan masu fyaɗe. Hakan kuma nada alaƙa da cin kashin da takema ƴan aikin gidansu, dan tun a wancan karon dama ya lura tafi taka mazan fiye da matan. Da ƙyar yay dauriyar sakkowa ya nufi bathroom ɗin ɗakin, ko kayan bai cire ba ya sakar ma kansa ruwan sanyi, ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jajjere, yafi mintina goma kafin ya kashe shower ɗin ya zame kayan jikinsa, dole ya tsaftace jikinsa sannan ya fito, har yanzu dai da alama cikin nasa bai saki ba, a haka yay dauriyar fita a ɗakin ɗaure da towel ɗinta. Falo ya fara dubawa ko tana nan, amma bai ganta ba, sai kawai ya yarda wajen yaran taje. Lips ɗinsa kawai ya cije ya koma bedroom ɗinsa, sai kuma a mamakinsa ya ganta kwance anan. Dan yana buɗe ƙofar tana miƙewa zumbur cikin ɗan barcin da ya figeta bayan ta gama shan kukanta a dalilin abubuwa da yawa na rayuwarta da suka shiga dawo mata wanda bazata taɓa mantawa da su ba.
“Nan ma biyo ni kayi? Aliyu ni zaka shiryama tuggu kamin fyaÉ—e! Wlhy ka sani nafi Æ™arfinka kai da ma duk ire-iren ka, kuma da ga yau idan ka sake tunanin raÉ“ata sai na É—auki mataki a kanka dan zan iya maka illa, dan haka ka kama kanka kwanakin nan su cika batare da ka rasa wani sashe na jikinka ba!”.
Sororo Smart yay kawai yana kallonta, yanda take maganar da dukkan gaskiyarta ga hawaye tanayi kuma, kalmar “Zan iya illataka Aliyu! Wlhy zan iya illata ka kamar yanda na kashe wancan tsinannen” ta sashi dawo hayyacinsa. Sai kuma Æ™irjinsa ya shiga bugawa, amma sai yay jarumtar dannewa wajen faÉ—in, “Mawaddat relax ni fa mijinki ne, ki sani ni ba irin waÉ—ancan da kike tunani bane, ALLAH ya halatta min ke duk abinda zan miki bada nufin cutarwa bane. Mawaddat aure yanada tarin abubuwa da suka banbanta da abinda zuciyarki ke iya hasaso miki. Dan ALLAH ki bar kukan nan haka ki nutsu bayan munyi salla muyi magana”.
“Bazanyi magana da kai ba Aliyu, bakuma zan sake ganin mutuncinka ba wlhy, ban san haka kake ba ai kaina da ban É—auke ka a yanda na fara ba....” fuuu ta fice a É—akin nan ma tai banging Æ™ofar da Æ™arfi har sai da ya É—an zabura. Ya jima shiru abubuwa da yawa na masa kai da kawo a zuciya har aka fara Æ™oÆ™arin shiga salla. A gaggauce ya shirya sai dai bazai iya fita massalaci ba dan cikinsa yay masifar Æ™ullewa dole a gidan yay salla. Bayan ya idar yana son zuwa inda take amma yana gudun kar yaran can su fahimci mike faruwa. Dole ya haÆ™uri akan har sai sun wuce, dan haka ya hau gado ya kwanta. Abu kamar wasa sai ga Æ™aramar magana ta zama babba, dan kuwa dai zazzaÉ“i ne mai zafin gaske ya lulluÉ“e Smart harda su rawar sanyi.........✍️
No comments