Nailah 7

 




*🌸NAILAH🌸*


   ~*(The abandoned flower🌹)*~




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*



*PAGE 7*



Nailah ta ɗago da sauri tana kallon Mommy tace "Mommy kenan da nayi aure shikenan zai kaini naga mama nah? Mommy idan nayi aure mamana zata yi farin cikin gani na fiye da idan na koma babu aure"



Mommy ta ɗaga mata kai tana murmushi tace eh mana ai ko ni sai nafi yin farin ciki idan na haɗe ku ke da Khairat lokaci ɗaya, amma ke naga kamar ma babu mai zuwa gurinki Nailah ya aka yi haka.




Nailah ta ɗaga kai sama kamar mai tunanin sai kuma tace "eh wlh Mommy nima dai bansan mi ke faruwa ba ƙila sai an taya ni da Addu'a"




Mommy ta murɗe kunnen Nailah da ɗan ƙarfi tana faɗin wato rainan hankali zaki yi ko, ina waɗanda ke mana zarya ba dare ba rana kina ƙin fita, idan an kira kuma ki ƙi ɗauka, ki fita idanuna fa na gaya maki.



Nailah ta shagwaɓe fuska tana faɗin Mommy da zafi fa, kuma ni wlh bana son ko ɗaya daga cikinsu, su zo su wani ishi mutum da surutu, kuma kinga ai ni bana son yawan surutu ko?




Mommy ta ɗago kan Nailah dake bisa kafaɗarta tana kallonta yanxu cikin yanayin serious tace "kin tabbata babu wanda kike so har yanzu? 



Itama da yanayi na sanyinta tace Mommy bani da ra'ayin soyayya, ban fara tunanin yin aure a nan kusa ba, ina fafutukar samun daraja dan na komai ga mahaifiya ta shiyasa na maida hankali a kan karatu kaɗai, na ɗauka idan na kammala karatun na samu aiki mai kyau ina samun kuɗi shine darajar amma ashe abin a kusa yake ni kuma nake ta kaishi nesa, Mommy da ace na san haka da tuni na saurari koda mutum ɗaya ne na bashi dama.



Mommy ta ƙure Nailah da kallo yadda ta saki jiki karon farko tana fitar mata da sirrin zuciyar ta, mutum ce mai zurfin ciki sosai amma ta iya buɗe mata sirrinta a yanxu, lallai Nailah ta ɗauki lamarin mahaifiyarta da girma, lokaci ɗaya ta canja akalar tunaninta saboda ita.


Ta kamo hannunta tana cigaba da kallon cikin idanunta tace " ba auren ne kaɗai daraja ba, sannan mahaifiyarki ma ba auren kaɗai take nufi kiyi ba, kina kan daidai, ilimin shine farkon abinda yake bama mutum daraja da daukaka a rayuwa kamar yadda Allah Subhanahu wa Ta'ala ya ɗaukaka Annabi Adam akan Mala'iku da ilimin da ya bashi.




Nailah ko ba mune al'ummar da farkon abinda aka saukarwa da Annabin mu, farkon abinda aka umurcesa shine “Yi karatu?


Idan har ance Masa haka (Manzon Allah SAW) yayi karatu, to mu miye muke jira? Miye zamuyi wanda ya wuce karatu? 


Kuma da hikimar Allah tunda bai bayyana wane karatu ne zaka yi ba, sai ya kasance yana ɗaukar duk wani karatu da zaka yi wanda zai amfani rayuwarka ta duniya da kuma ta lahira, ba wai ilimin da zai cutar da duniyarka ko lahirarka ba, dukda shima ba laifi bane ka sanshi dan ka guje mashi.



Ko a cikin maƙasƙacinciyar dabba (kare) akwai banbanci tsakanin mai ilimi da mara ilimi, domin idan aka koyar da kare ilimin farauta sai ya farauci dabba ya kashe ta, wannan dabbar ya halatta ka ci ta, amma idan ka samu ga dabba an kashe sai kaga karnuka biyu a kanta wato mai ilimi da kuma jahili, to tsayuwar wannan jahilin a kanta kaɗai ya haramta maka cin wannan dabbar dan gudun kokonto.



Sannan a cikin aljannu ma munji a tarihin Annabi Sulaiman A.S tsakanin aljani da yace zai kawo masa gado kafin ya tashi daga fada, da kuma aljani mai  ilimi daga cikin littafi da yace zai kawo masa kafin ya ƙyfta idanunsa kuma sai gashi ya kawo ɗin, to ina ga mu yan Adam.



Jahilin mutum komai kuɗinsa idan ka zanta da shi na wani lokaci a hankali sai ya tona kanshi, haka mai ilimi komai talaucinsa idan kayi zama dashi sai ka fahimci eh lallai wannan mai ilimi ne, sai dai kuma mai ilimi ne kaɗai zai iya gane haka.



Nailah ki cigaba da neman iliminki, ba'a daina neman ilimi sai idan ƙasa ce ta birni idon mutum, amma aure, kar kice ba shine a gabanki ba, domin babbar sunnah ce ta fiyayyen halitta SAW kuma da shine ake samun ɗa' na halal, akwai nutsuwa a ciki sannan akwai jijircewa dan cika dokokin Allah sai rayuwar ta kasance cikin salama, idan har kin fahimci maganaganu na zan roƙe ki alfarma guda ɗaya.



*Ƙauyen Dosan*


Ommi dake zaune gaban murhu tana ƙoƙarin tuƙa tuwo ta dubi Asma dake tsaye tana jijjiga ƙafarta tace " kin kyauta Asma yanzu dai haka kika ga ya dace ki dinga yiwa mahaifinku kan maganar aure ko? To ki maida hankali kiyi.



Asma ta zunɓuro baki gaba tana wani haɗe fuska tace nifa gaskiya Ommi sai dai ayi haƙuri dan wlh ba zanyi auren nan ba, kuma kawai sai ya wani dinga kawo min mutane kala kala wai su duba ni sai kace wata kayan saidawa shi ga mai ɗiyar da ta wuce munzalin aure amma bata yi ba, to mi ake da mazan, ki faɗa mashi ya fa shafa min lafiya gaskiya, ki faɗa mashi ya barni in yi rayuwa ta yadda nake so"



Ommi da ba yau ta fara jin irin waɗannan kalaman daga bakin Asma kan mahaifinsu ba, tayi faɗan, ta gibga, ta yi nasiha amma abin Asma kullum gaba yake ƙarawa, zata yi magana suka ji an banko ƙofar gidan an shigo.




Saratu ce maƙwabciyarsu janye da hannun yaronta yana kuka da jini a bakin shi alamar ciwo ya ji a bakin ta ƙaraso gaban Ommi tana huci ta cigaba da faɗin "kin ga abinda wannan baƙar yar taki fitinanniya ta yiwa Anas ko, to ki san abin yi wlh kafin in ɗauki mataki da kaina"




"Ommi ta lumshe ido a ranta tana fadin Ya Salaam, Fatiya kuma dai" sai kuma ta buɗe ido tana shirin magana fatiya ta shigo gidan da gudu kamar an wurgo ta, dan tunda ta ga mamarsu Anas ta janyo shi ta san ƙararta za'a sai dan haka ta biyo su ayi komai a gabanta.




Gaba daya shekarunta takwas ne da ɗan wani abu, kalar fatar jikinta baƙa ce amma ba can sosai ba sai uban gashin da har ya kusa tardo ɗuwawunta, tana shigowa Ommi tace Anas ya je ya rama dukan shi, haka ya saka Asma saurin kallon Ommi tana rarraba idanu sai kuma ta maida dubanta kan yaran, ta ga Anas na rama dukan shi fatiya ta ƙara dagewa ta wanka mashi marin da har saida yayi baya ya faɗa jikin Saratu.




A hargitse Saratu ta nufi fatiya zata dake ta Asma tace "ke tsaya min dan Allah, ke baki da kunyar idon mahaifi, kin wani zo buguzun buguzun zaki daki yarinya gaban uwarta, ki barsu mana suyi abinsu a tsakaninsu tunda na san shine ya tsokane ta, duk uban da yaji ba zai juri a dinga dakar mashi ɗa ba to ku ja masu kunne su daina shiga harkar ta sai idan wasa ne za'a yi ko harkar arziƙi, yan iska kai, a ganinku yadda kuka ja ra'ayin mu tun muna jin yar uwarmu a rai har kuka sa muka ji eh lallai bata dace da mu ba a ranmu, kuka sa muka barta a rayuwar kaɗaici a lokacin da tafi buƙatar mu, zamu zuba ido ne ku yiwa wannan? Baku isa ba wlh, duk girman mutum ni sai in saka shi kwana kuka babu abinda ya min zafi, yanxu ki kama tarkacen ɗanki ku wuce kafin na ƙara mai.



Sanin halin Asma ya saka Saratu jan dogon tsaki ta juya bayan ta sauke wa Ommi wata muguwar harara.




Ommi ta juyo ta sauke idonta kan Asma dake ta jijjiga tana huci sai kuma ta dawo ta sauke kan fatiya da tunda ta mari Anas take tsaye tana ta haɗiyar zuciya irin a fusacen nan fa take, sai ta cire kanta ta maida hankalinta kan tuƙin tuwonta, to mi zata ce? Yadda bata bi gidan kowa ta kai ƙara lokacin da ake cutar da Nailar ta ba, haka ba zata je gidan kowa bada haƙurin abinda fatiya ke yi ba, bayan haka ai yarinyar sai an jata ne ake jin ta babu daɗi, tabbas Allah ne ya nuna masu iyakarsu ya haɗa su da fatiya, bata da haƙuri sam, duk wanda ya jata ta kan rama a take, babba ko yaro kowa ta san da irin abinda zata sosa masa zuciya wannan ya saka ita bata tashi a halin ƙunci ba, take rayuwarta cikin walwala ba tare da takurar kowa ba.




Tun bayan tafiyar Nailah da yan watanni Ommi ta haifi fatiya, sai dai a wannan karon sosai Ommi tayi mamakin yadda Abbansu ya amshi yarinyar ya bata kyakkyawar runguma ƙwalla ta gangarowa a gurbin idonsa, shi kaɗai ya san halin da ya shiga bayan tafiyar Nailah, shi kaɗai ya san darasin da ya ɗauka bayan nuna ko in kula ga yar cikin shi, amma waye zai fahimce shi bayan irin rashin darajar da ya tafka a baya, ya tabbata Allah ne ya jarabce shi ya ƙara bashi wata baƙar dan ya nuna masa ba shine ke da iko ba, sai ya amshe ta hannu bibbiyu yake nuna mata son da bai nunawa kowa cikin yaransa ba, so ƙarara a fili dan kullum zaman da yake a ƙofar gida da ita yake fita ya zaunar a gefen shi tana gwarancin ta yana dariya.




Tun abokansa suna jefa masa habaici kan abinda yayi a baya har suka gaji dan baya tanka maka ko mai zaka ce, to mi zai ce bayan duk abinda suke faɗa yayi ba ƙarya suka yi masa ba, wannan jan ta a jikin da yake yi, wannan son nata da yake yi shine yayi tasiri ga yan uwanta da manyan mutanen garin suma suka ɗauke ta tamkar kowa, suka manta da yanayin fatarta sai waɗanda ba za'a rasa ba da kuma yara, a nan ya gane kuskuren sa kamar yadda bahaushe ya faɗa a karin maganar sa "*NAKA SHI YAKE BADA KAI*" duk irin halinka, duk rayuwar da kake cikin, duk rauninka, idan naka bai bada ƙofar da za'a wulaƙanta ka ko a maka kallon ƙaskanci ba, babu wanda zai kawo yi maka hakan a rai, koda anyi sai dai a ɓoye amma ba a fili ba.




A hankali damuwa take yiwa Abba yawa wanda har yanzu babu wanda ya taɓa buɗe baki ya sanar ma damuwarshi sai dai tuni matar shi wadda tafi kowa kusanci da shi a fahimci komai baya daukar lokaci bai kwanta ciwo ba, haka yasa ta sanar da Mlm. Abubakar duk abinda ke faruwa ta kuma roke shi alfarma ganin ciwon Abban sai ƙaruwa yake har ya kai ya kwantar dashi, da yake kuma ƙauye babu zuwa asibiti sai jiƙe jiƙe kawai ake banka masa..........✍🏽

No comments