Nailah 5

 




🌸NAILAH🌸*


   ~*(The abandoned flower🌹)*~



                         *Na*


                    *Baebee* 


~*WRITER OF✍🏽*~


*MUSAYAR BURI*


*YAN DABA NE (The revenge)*


*ZUCIYARMU* *AND NOW.......*



*NAILAH* ~*(the abandoned flower🌹)*~



*Wannan labarin da duk abinda ya ƙunsa ƙirƙira ne, idan yaci karo da rayuwar wani ko wata arashi ne a gafarce ni*



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*



*PAGE 5*


Ta ɗan jima tsaye a bakin office ɗin tana ƙoƙarin saita nustuwarta kafin tayi knocking aka bata izinin shiga, ta tura ƙofar a hankali ta shiga bakinta ɗauke da sallama.



Kamar yadda tayi cikakkar sallama haka aka amsa mata da muryar da ta sakata saurin ɗagowa ta dubi direction ɗin da aka yi maganar jin wani abu ya tsarga tun daga kwanyarta har zuwa yatsun ƙafarta ta sauke dubanta a kanshi.



Yana tsaye ya bama ƙofar baya yana facing ɗin window da kofin ceramic a hannusa ya juyo ya ɗan kalle ta a fizge sai kuma ya taka ya koma bisa kujera ya zauna yana cigaba da sipping ɗin black tea ɗinsa ba tare da yace mata komai ba, haka yasa Nailah ƙarasowa ta tsaya ƙiƙam a gabansa ita bata zauna ba ita bata yi magana ba dan ita ai bata saba fara yiwa mutum magana ba gaskiya.



Ta daɗe haka sannan ta ƙara ɗagowa ta ga ko ya gama shan abinda yake sha dan ta san ƙila yana nufin sai ya gama zai dawo kanta, ta tsinci idanunsa a cikin nata tsamo tsamo ya kafe ta da ido yana mata kallon da ta kasa fasarawa.



Jikinta ne ya ɗauki rawa ta kai hannu  zata goge zufar data fara karyo mata taji glass ɗin dake fuskarta, babu shiri ta tunɓuke shi dan a ganinta ko shine yasa yaƙi tanka mata yana jira sai ta cire shi sannan, a rarrabe tace " Sir ni....ni..nice wadda kace na same ka idan nazo"




Still yana kallonta ya miƙa mata hannu alamar ta bashi takardun, babu musu ta miƙa mashi ta dawo ta sake tsayuwa a gurin.



Babu zato ta jiyo muryarshi yace "Uhmm, why are you late?



Ta ɗago taga yanzu hankalin shi a kan takardun yake yana dubawa, a sanyaye tace Sir a yimin afuwa, na tsaya rubuta jarabawa ne.



Tsayawa yayi da abinda yake yace " ki bani school ID da kuma exam card ɗinki, let me confirm"



Da sauri tace ohk Sir sannan ta juya ta fita bata jima ba ta dawo da su a hannunta ta bashi, ya amsa yana dubawa a nutse sai kuma taga ya ɗago yana mata irin kallon da ya gama yi mata ɗazu wanda saura kaɗan ya saka ta kuka yace "wannan naki ne?



Ta girgiza kai da sauri tare da fadin eh" sai ya miƙo mata ƙaramin katin da ta kawo mashi a zuwan ID card yace ki duba dai inaga ba wannan na tambaye ki ba.



Nailah ta amsa tana ƙanƙance ido tana wara su duk a ƙoƙarin ta na son karanta abinda ke jiki ba tare da glass ba amma ta kasa, dan haka sai ta fiddo glass dinta da ta saka a cikin aljihun doguwar rigarta ta maida kallonta kan katin.




Bata san lokacin data furta "A'uzubillahi, SubhaAllahi" tana dafe ƙirjinta.



Katin da Zee ta bata a lokacin da aka yi taron buɗe babban hotel ɗin kusa da University? Katin da aka gayyaci yan mata masu amsa sunansu ana masu tayin duk kwana ɗaya Naira dubu ɗari? Wannan yasa tun daga lokacin ta fita harkar Zee gaɓa ɗaya sai gaisawa kawai shima dan kar ayi zaman gaba ne, shine yanzu dan jaraba katin nan zai biyo ta har nan ya nemi yi mata sanadin aikinta na rufin asiri, ina ba zai yiyu ba.




A hargitse sannan da yanayin da mutum ke magana idan yana so a yarda dashi Nailah ta cigaba da faɗin "tsaya kaji Sir, na rantse da billahillazi La Ilaihailla Huwa banje ba, dan Allah karka kore ni wlh ni ba yar iska bace kuma idan kaji ƙarya a tambayi Fatimar gidanmu"




Zaro ido Eeyad yayi yana kallon ikon Allah, yau ya ɗakko ma kanshi abinda zai dame shi, wai yarinya tana zabga mashi harara sannan tana roƙonshi Allah da Annabi kar ya kore ta, to shi ina ruwanshi idan ma taje da har ake ce mashi ya tambayi Fatima ko wa?




A fili kuwa sai ya nuna mata ƙofa tare da faɗin" kije"



Kamar Nailah zata yi kuka ta juya tana tafiya tana waige irin tana so tayi magana amma bata ga fuska ba dan haka ta fice ta koma office ɗinta tana jin kanta na sara mata ta shiga karanto Addu'o'i babu ƙaƙƙautawa, tana tsaka da haka taji shigowar saƙo cikin wayarta, cike da sanyin jiki ta janyo ta duba sai dai abinda ta gani bata san lokacin data saki wayar ba ta shiga yarfe hannuwa tana faɗin na shiga ukku ni Nailah yar malan Sagir, ba komai ta gani ba sai kuɗin da suka shigo cikin account ta, gani take yi shikenan korarta za'a yi shiyasa aka tura mata irin kuɗin nan da ake ba masu ajiye aiki ko waɗanda aka sallama, to inba haka ba mi zaisa taga dubu ɗari biyu a matsayin albashi daga kawai tana rubuta wasu yan bayanai, kai gaskiya da sakal.




Tun daga ranar jininta a kan akaifa yake tana jiran ta ga anzo an bata takaddar sallama amma shiru dan tun daga ranar ma bata ƙara ganin zuwanshi ba har yau da aka kusan shafe sati biyu da faruwar abin dan haka sai ta ɗan fara kwantar da hankalinta.



Husnah

A hankali ta buɗe ido ta sauke a kan mahaifiyarta dake tsaye a gefen gado tana kiran sunanta, ta tashi zaune sai kuma ta kai hannu ta dafe kanta dake sara mata.



Hajiya Umma ta zauna kusa da ita tana faɗin "ke lafiyarki kwana biyu kin daina fita breakfast kwata kwata sai gurin ƙarfe ɗaya ki tura a damo maki kunun tsamiya, wani salon wasa da ciki kika gane Husnah ko dai baki da lafiya.



Ta ida maganar tana kai hannunta kan goshin Husnah da taji zafi rau.



"SubhaAllah" ta faɗi tana neman rikicewa Husnah ta riƙo hannunta tace Ummi ba wani abu bane fa, kawai kullum da dare ne sai zazzaɓi ya rufe ni har safe sannan nake samun bacci shiyasa kika ga bana fitowa da wuri.



Shine kike cewa ba wani abu bane, u are not serious, yanxu zan kira doctor ta duba ki sai ki ɗan ci wani abu kafin tazo InshaAllah.



Tayi maganar tare da ficewa da sauri tana kara wayar a kunnenta.



Tsawon 20 minutes doctor ta shigo ta dudduba ta sosai tayi mata yan tambayoyi sannan ta buƙaci ta bata fitsarin ta.



Sosai Husnah taso yin tutsu sai dai yadda Umma ta buɗe mata wuta ya saka ta miƙewa ta shiga bathroom tayo ta kawo mata, doctor ta amsa ta fice bayan ta buƙaci su bata 2 hours zata je tayi awon fitsarin.



Umma da tuni ta gama fahimtar rashin lafiyar Husnah sai dai tana so ta tabbatar ne ta matso ta zauna kusa da ita tana shafa kanta a hankali.


Nailah

Tun kafin su yi hutun semester ta kira hakimi ta sanar dashi hutun da zasu samu, ga mamakin ta sai yace mata tayi zamanta ba sai tazo ba saboda hutun ba yawa ne dashi ba, kuma tafiya ce a gabanta ba kaɗan ba, zata wahalar da kanta tunda ita kanta ta san ko taje ba zai barta taje ƙauyen Dosan ba.



Cikin ladabi ta amsa shi sannan ya katse kiran, ta shiga tunannin ita kam ina zata zauna idan yan gidan suka tafi gida? Bama yan gidansu kawai ba, gaba ɗaya estate ɗin ta san kowa zai nufi gidan ubansa ne ita kuma ba zata iya zama ita kaɗai ba gaskiya, dole ta nemi mafita.



Bata da abokin shawarar da ya wuce Khairat, haka yasa ana jibi zasu gama jarabawa ta tuntuɓe ta da maganar dan jin shawarar da zata bata.



Murmushi Khairat tayi tace ina kike dashi bayan gidan mu? Dole can zaki koma ki zauna, kuma wlh karki sake kimin gardama dan zan ɗauka bani da matsayi a gurinki kamar yadda na baki matsayi mai girma a duniya ta.



Shiru Nailah tayi tana hango gidan su Khairat dan ta taɓa zuwa sau ɗaya, gidan da wai idan ba'a sanka ba sai ka ba ƙartin sojojin da suke tsaitsaye ƙiƙam wani kati kafin su barka ka shiga, gidan da ta shiga saida tayi da gaske ta taro kanta daga zuba ƙauyancin kalle kalle dan kar a raina ta, shine Khairat ke so taje ta zauna salon ta saba da rayuwar jin daɗi lokacin komawa ƙauye yayi ido ya raina fata? To amma ba zata iya mata jayayya ba dan haka tace shikenan.




Haka ya kasance yau bayan sun gama jarabawa bata ɗauki komai daga gidan estate ba dan Khairat tace ba sai ta zo da komai ba, daga ita sai babbar wayarta da ta siya cikin albashinta wanda take tarawa a cewarta idan ta koma zata gina masu sabon gida tayi ɗakinta mai girma ba irin wanda ta baro ba, ta sayi katifa da ledar ƙasa sannan ta saka ma Ommi gado, abubuwan dai da yawa wanda zatayi gaskiya.



Koda suka isa a babban falon ƙasa suka iske Mommy tana aiki da system, Khairat na gaba Nailah tana biye da ita a baya suka zauna kujera ɗaya.



Mommy tana murmushi ta amsa gaisuwar da Nailah tayi mata tana tambayar su jarabawa, suka amsa da Alhamdulillah sannan Khairat ta cigaba da fadin "amma fa Mommy gaskiya jarabawar yau tayi zafi, questions sai kace na zuwa ƙiyama, da yake lecturers biyu suke ɗaukar course din kuma kowane saida yayi tambaya a ƙalla talatin cikin ɓangaren shi, ai ba sauƙi kam sai a gurin Allah.




Tana tsaka da zubar nan kamar kanyar da babu daɗi taji Nailah ta ƙanƙame ta da sauri can ƙasa ƙasa yadda Mommy bata ji ba ta furta "Innalillahi Sir!!!" sai kuma ta shiga ƙoƙarin janyo hijab ɗin Khairat tana so ta rufe fuskarta.




Khairat ta ɗago da sauri ganin abinda Nailah kema wannan abin idonta ya sauka a kan yayanta dake shigowa falon da waya maƙale a kunnensa yana amsa kira.............✍🏽

No comments