Nailah 4
*🌸NAILAH🌸*
~*(The abandoned flower🌹)*~
*Na*
*Baebee*
~*WRITER OF✍🏽*~.
*MUSAYAR BURI*
*YAN DABA NE (The revenge)*
*ZUCIYARMU* *AND NOW.......*
*NAILAH* ~*(the abandoned flower🌹)*~
*Wannan labarin da duk abinda ya ƙunsa ƙirƙira ne, idan yaci karo da rayuwar wani ko wata arashi ne a gafarce ni*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*
*(Hey, zaku ga labarin a taƙaice yake, eh haka salon shi yake, gajeren labari ne da gaba ɗayanshi ba zai wuce 15 pages ba InshaAllah)*
*PAGE 4*
Yau da ya kasance ranar Litinin bayan an tashi daga lectures drivern Khairat yazo ya ɗauke su kamar kullum ya ajiye ta a bakin Estate suka wuce ita kuma ta shige ciki.
Kayan jikinta ta cire tayo wanka tana jiyo motsin maƙwabtan ɗakin ta dan ɗayar ma tuni ta dawo sai dai abinda Nailah ta fahimta akwai yar matsala a halayyar Zee, haka kawai yadda take yawan ƙura ma ƙirjinta da bayanta ido yasaka Nailah taji sam bata wani ra'ayin Zee gaskiya, gashi lokuta da dama bata kwana a gidan sai asubar fari take dawowa ta dasa bacci har rana ta fito.
Tana tsaka da dafa indomie dan saka ma cikinta taji ƙarar yar wayarta me malatsai alamar kira na shigowa, ta duba taga number ce, tsaki taja dan ana yawan kiranta da numbers ace ana sonta waye waye sai dai kawai ta katse dan mutum ce da bata ra'ayin soyayya a nan kusa, so take ta samu darajar da zata komawa Ommi da ita sannan komai ya biyo baya, saida ta kusa tsinkewa sannan ta ɗauka a cikin muryarta mai sanyi tayi cikakkiyar sallama.
Daga can ɓangaren amsawa aka yi tare da tambayar ko ana magana da Nailah Sagir wadda ta kawo application a Unigold Company?
Wani irin wantsalowa tayi daga kan kujerar da take cikin sauri tace eh..eh nice" can ɓangaren aka cigaba da faɗin idan kinada dama kizo interview gobe da misalin bakwai na safe InshaAllah, daga haka aka katse kiran.
Hafeez na ajiye wayar ya maida kallonshi kan abokin aikin shi yana faɗin kai malam kaji murya a gurin mace tamkar sarewar da aka ƙera da zinari, wannan ai ba za'a taɓa gajiya da jin muryarta ba.
Baki Hassan ya taɓe tare da faɗin kai ko akwai na mamajo wlh, yanzu abu na gaba nasan cewa zakayi kana sonta, ai kuwa kaji jiki.
Nailah wani irin farin ciki ya mamaye duniyarta ta shiga gode ma Allah ba ƙakkautawa, Companyn da ko lokacin da ta bada application ta bada ne kawai amma bada tunanin za'a bi ta kanta bama balle a waiwaye ta, Companyn da kaɗan ya rage ta cire takalma ta shiga dan gurin bai yi mata kama da inda ake takawa da takalmi ba, kafin ma tace zata shiga sojan dake tsaye a get ɗin shiga ya tsayar da ita a waje ta rubuta komai ta bashi ta wuce, shine suka gayyace ta interview ita Nailah? Kai jama'a Allah me Alheri, ai wlh yau kwana zata yi Sallah tana roƙon Allah ya bata Sa'a ta ci wannan Interview, ai idan aka ɗauke ta aiki a gurin nan ta haye.
Tun daren ranar ta fitar da kayanta masu kyau na zuwa gurin Interview dan kankaro ma kanta mutunci kar taje gatanan dai a raina mata.
Washe gari koda tayi sallar Asuba bata koma bacci ba, ta cigaba da azdkar har gari yayi haske sannan ta miƙe ta gyara dakinta fes ta ɗora ruwan zafi ta faɗa wanka, tana fitowa ta shafa mai da kwalli sannan ta haɗa tea ɗin ta mai kauri ta sha da biscuit lokacin 6:45am.
Da sauri ta saka daguwar rigar atamfarta ash color da taji stones tun daga sama har ƙasa, ta matuƙar karɓi surar jikinta, ta saka hijab wadda tazo mata har guiwa ta fito.
Knocking ɗin ƙofar fatima tayi tana kiran sunanta, fatima da itama ke shirin fita lecture ta buɗe tana fadin kar dai kin shirya yau tun kafin bakwai.
Nailah tace a'a ai bama zan je school ba yau gaskiya, dama zuwa nayi in faɗa maki idan kin gama shiryawa ki tafi kawai.
Daga haka ta juya da nufin tafiya sai kuma ta sake dawowa tace "Fatima ki taya ni da Addu'a Allah ya bani Sa'a cikin abinda nake nema"
Fatima tace InshaAllah sai kin dawo.
Ɗakin Zee ta ƙwanƙwasa itama ta nemi ta taya ta da addu'a sannan ta fito ta wuce.
7:30am
"Arif ka tsaya mana miyasa kake son wahalar dani kullum rana ta Allah sai kasa nayi motsa jikin da banyi niyya ba" Khairat ke magana tana biye da Arif dake ta zagaye a cikin babban falon ƙasa yana faɗin ni nace maki bana so, bana so fa.
Khairat da kaɗan ya rage ta fashe dan haushi saboda tun daga ɗakinshi take biye dashi yana gudu ta shiga hawan matattakala tana kiran Mommy.
Ganin haka sai Arif yayi kwanciyarsa a saman kujera yana kallonshi hankali kwance kamar ba shirin school ake mashi ba, sai dai ganin Mommy na sakkowa ya sakashi ƙara tashi ya zuba a guje ya nufi compound ɗin gidan yana dariya.
Mommy data ƙarasa sakkowa ta fito ta saka ɗaya daga cikin soldiers ɗin dake kai kawo a compound ɗin ya saɓo mata shi sai zillewa yake shi ala dole fa ba za'a shirya shi a kaishi makaranta ba.
Da kanta ta saka mashi Uniform dan Khairat ma shirin makarantar take yi amma yake nema ya ɓata mata lokaci, tana tsaka da saka mashi socks taji ya ƙwala kiran Daddy haka yasa tayi saurin ɗagowa ta sauke idonta kan Eeyad dake tsaye bakin ƙofa hannuwanshi a harɗe a samar ƙirjinsa ya jingina bayanshi da ƙofar yana kallon cakusawar da ake yi da Arif kan makaranta, shi bai san waye yaron can ya gado rashin son school ba dan shi ai ba haka yayi ba da yana yari gaskiya, amma zai zauna dashi yaji abinda ke mashi yawo a cikin kai.
Ƙarasowa yayi ya zauna yana gaida Mommy cikin ladabi irin yadda zaka gaidar da mahaifiyarka, ta amsa tana tambayar iyalinsa kamar yadda take yi kullum kuma ba wai dan bata san iyalin tashi bata nan ba, shi dai bai san abinda take nufi da haka ba.
Bai bata amsa ba sai relaxing da yayi ya ɗan lumshe ido yace "Uhmm"
Itama bata ƙara cewa komai ba ta miƙe janye hannun Arif ta kaishi saman dining ta zuba mashi breakfast tana faɗin "kafa ci abincin nan na gaya maka ko in haɗa ka da Daddyn ka gashi can kuma ka san sauran babu ruwana ni"
Jin haka ya saka Arif kai dubanshi kan Eeyad sai kuma ya kama haɓa yana kallon Mommy ƙasa ƙasa kamar mai raɗa yace "Mommy karki faɗa mashi zanci wlh"
Murmushi Mommy tayi tare da jan kumatunsa tace good boy kayi sauri karka tsayar da Auntynka dama ka gama ƙuleta kuje can cikin mota ta jibgar min kai, ya girgiza kai sannan yayi Bismillah ya cigaba da ci.
Ba su suka bar gidan ba sai 8:15am, sai a lokacin Mommy ta dawo ta zauna a kujerar dake kallon wadda Eeyad ke zaune har yanxu yana kallon labaran safe.
Yana ganin ta zauna ya rage volume din gaba ɗaya ya maida hankalishi kanta dan tunda yaga tazo ta zauna to magana ce a bakinta.
Mommy data tsattsare shi da idanu ta cigaba da faɗin "yanxu kai kaji ka gani da irin rayuwar wannan rayuwar da kake yi mara alƙibla? Kaine zuwa yin breakfast, Kaine zuwa cikin abincin rana da na dare, ga mace kana da ita amma kake rayuwa kamar wanda bai taɓa sanin miye aure ba, rayuwar fa tafiya take, shekaru ƙaruwa suke dan yanxu ko babu komai ka bama shekara talatin da huɗu baya, kana tunanin wannan da kake gani ya isheka rayuwar duniya ne? Ai kai kanka babban misali ne ga kanka, ka kalli responsibilities ɗin dake kanka na kamfanonin da mahaifinka ya tarkato ya ɗora su a kanka dan shi yana so ya zauna ya huta sannan ga aikin ka, ka faɗa min inda kanada yan uwa da baka samu sauƙin wasu abubuwan ba, to ya isa haka nan, wlh daga kai har matarka ku shiga hankalin ku dan bana son tsohon iskanci, kodai kaje ka maido ta ko kuma ka ƙara aure na gaya maka.
Tana gama faɗin haka ta miƙe tayi tafiyarta ba tare da ta jira jin ta bakin shi ba, to mi ma zai faɗa mata, in ba rashin kishin kai irin na Eeyad ba yadda basu da yawa a family ɗinsu in shi wani ne ai sai ya auro mata kamar ukku ko huɗu su zo suyi ta haifa masa, ita ba zata gaji da jikoki ba wlh.
Nailah
Ƙarfe bakwai daidai ta isa Companyn inda ta tarar da abinda bata yi tsammani ba, tayi zaton zata ga cinkoson mutane yan zuwa Interview sai taga saɓanin haka dan gaba ɗaya su goma ne sannan ita kaɗai ce mai ƙananan shekaru a cikinsu, tunda suka zazzauna ba su aka bi ta kansu ba sai gabatowar goma na safe sannan aka fara kiransu ɗaya bayan ɗaya.
Tana zaune har aka zo kanta bayan ta gama amsa kiran Khairat har ba adadi tana tambayar ta miyasa bata zo lecture ba kuma bata faɗa mata cewa ba zata zo ba, inda ta san haka ne ai da itama tayi xamanta a gida, haka kawai Nailah taji ba sai ta faɗa mata abinda ya hanata zuwa ba dan haka tace mata " a'a gara dai da taje ita din dan ko babu komai zata jiye masu lectures din da akayi, daga haka suka yi sallama.
Ta miƙe ta shiga bakinta ɗauke da sallama, Hafeez dake ta zuba idon ganin mamallakiyar voice ɗin da suka yi waya da ita a jiya dan wasa wasa kusan kasa barci yayi babu abinda yake masa gizo sai muryata, ya amsa yana wani maƙe murya kamar an shaƙe mage yana ƙura mata ido a ranshi yace "Tabarakallah MashaAllah" sai kuma ya nuna mata gurin zama yana faɗin zauna mana.
Babu musu ta zauna ya shiga yi mata tambayoyin da har mamakin wasu takeyi, to a ganinta ita da tazo neman aiki na miye kuma za'a tambaye ta tanada aure ko bata dashi, tanada saurayi ko bata dashi, har dai aka gama ta miƙe ta fita dan zuwa office ɗin da ya kwatanta mata.
Nan ma tana shiga ta samu guri ta zauna matar dake office ɗin ta duba bayanan Nailah da aka tura mata a system sannan ta ɗago ta kalle ta tace "congratulation Miss Sagir zaki fara aiki damu daga gobe InshaAllah"
A hankali Nailah ta lumshe ido sai kuma ta saki sassanyan murmushin da ya saka matar ƙure ta da kallo itama murmushin kwance a kan fuskarta, ta faɗa mata bayanai masu muhimmanci game da Companyn da kuma yadda tsarinsu yake sannan ta bata damar tafiya.
Faɗin farin cikin Nailah a wannan ranar ba zai yiyu ba sai dai a hankali damuwa ta so lulluɓe komai ganin batada wanda zata kira ya taya ta murna, ba zata kira hakimi ko Mlm Abubakar tace ta nemi aiki ta samu ba dan zasu ɗauka bata gode ma hidimar da suka yi da ita kuma suke kan yi da ita ba.
Cike da ƙwarin guiwa ta faɗa ma Khairat inda ta samu aiki, Khairat tayi ɗan jim sai kuma tace "kin tabbatar a Unigold Company aka ɗauke ki aiki? Amma taya? Lallai kinada sa'a Nailah dan basu ɗaukar wanda matakin karatunsa bai kai matsayin degree ba.
*UNIGOLD COMPANY*
Office ne aka bata madaidaici da ya haɗa komai na more rayuwa, aikin ta kuma na rubuta bayanin duk wani gold da ya shiga Companyn ne, babu ruwan ta da wanda ya fita, cikin Sa'a kuma dutyn maraice aka saka ta permanently.
Tun daga lokacin ta zama busy idan aka tashi daga school ta koma gida sallah kawai take yi tayi wanka ta wuce gurin aiki ba tare da ta tsaya dafa abinci ba, dan a can Company duk idan lokacin cin abinci yayi za'a zo a bama kowa takeaway kullum rana ta Allah, yanxu ne ma da suke exam take samun ɗan lokacin zama a gida saboda tunda suka fara exam ta safe zuwa sha ɗaya suke yi.
Thursday
Da sauri ta ƙarasa rubuta abinda ya rage cikin answersheet ta miƙa ma supervisor ta fice bata ko tsaya jiran Khairat ba saboda makarar da tayi a yau da suka yi exam ɗin rana, ita da ke zuwa aiki tun ƙarfe biyu da rabi yau gata har 4pm tana kan hanya.
Babu abinda yake ƙara ɗaga mata hankali irin tunda satin nan ya kama aka sanar dasu mamallakin Companyn zai zo yau, abinda kuma take ji a bakin mutane dangane dashi shine baya son wasa da shirme a cikin aiki sam sannan baya amsar uzurin mai yawan makara, idan ya samu mutum da laifin zai dakatar da shi na watanni ukku yace yaje ya maida hankali a kan abinda yake makarar dashi, raba hankali gida biyu ai ba abun yi bane, wannan yasa take kafa kafa duk ranar Alhamis take zuwa da wuri koda sunada sauran lecture saidai ta baro ta tafi, amma yau da ya kasance jarabawa ce babu yadda za'a yi ta baro school ba tare da ta gama ba.
Tunda ta shiga napep take Addu'a har ta sauka ta shiga cikin farfajiyar gurin kunnuwanta suka jiyo mata Sallar la'asar da ake yi a masallacin dake cikin Companyn haka yasa ta lallaɓa ta shige ba tare da kowa ya ganta ba.
Turus tayi ganin office ɗin a kulle alamar wadda zata amsa ta tafi a fili ta furta, Innalillahi, na bani shikenan aunty Safiya ta jiƙa min aiki, Allah ka taimakeni babu wanda ya neme ni balle a fahimci bana nan" tayi maganar tana jin kewar Hafeez da cikin ƙanƙanin lokaci ta saba dashi a farkon zuwanta, duk irin yadda tayi wani ba daidai ba a cikin aikinta zai tsaya yaga bata shiga matsala ba, har ya kan zo office ɗinta suyi fira wani lokaci, amma a'a kawai rana tsaka taji wai an ɗauke shi daga Companyn an maida shi wanda ake sayar da jewelries ɗin da aka ƙera a wannan Companyn.
Tana shiga ta ɗauro alwala a cikin bathroom ɗin dake office ɗin ta dawo tayi sallar la'asar ta zauna tana azkar dan yau azumi take shiyasa ma bata nemi abinci ba.
Knocking ɗin da aka yi ya saka ta ɗago kanta ta kalli ƙofar sannan tace shigo"
Mai office ɗin dake kusa da nata ya shigo da sallama yana mata kallon yau kin kaɗe a taƙaice yace "Sir yace idan kin zo ki same shi a office ɗinsa.
Gaban Nailah ya yanke ya faɗi ta miƙe tsaye da sauri tana faɗin tsaya kaji dan Allah, wai da gaske kake, kar kace min yazo ya iske bana nan.
Musa da ya buɗe ƙofa zai fita ya tsaya yace " aff na nawa kuma, ai duk lokacin da ya zo mutum biyu yake fara nema, wanda yake da bayanan shigar gold da wanda yake da bayanan fitar su, kuma wlh tun 3pm yazo yasa a kira masa ke baki nan har gashi yanxu huɗu da rabi, gaskiya fa kina cikin matsala sai kiyi ta Addu'a ba kama hannun yaro.
Yana gama faɗin haka yayi ficewarshi ya bar Nailah tsaye tana zarar ido sai kuma ta shiga harhaɗa takardun dake tattare da bayanan komai ta haɗa su guri guda ta fice daga office ɗin..........✍🏽
No comments