Nailah 3

 




🌸NAILAH🌸*


   ~*(The abandoned flower🌹)*~



                         *Na*


                    *Baebee* 


~*WRITER OF✍🏽*~


*MUSAYAR BURI*


*YAN DABA NE (The revenge)*


*ZUCIYARMU* *AND NOW.......*



*NAILAH* ~*(the abandoned flower🌹)*~



*Wannan labarin da duk abinda ya ƙunsa ƙirƙira ne, idan yaci karo da rayuwar wani ko wata arashi ne a gafarce ni*



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAY*



*PAGE 3*



Washe gari da kanshi ya miƙa Ikhlas gida, wacce ke ta narke fuska ita bata son komawa gida saboda a nan ta samu Arif abokin wasa, a gida kuwa ita kaɗai ke kai kawonta ko wane da aikin dake gabansa.





Shugaban ƙasa yayi mamkin inda Eayad ɗin ya samo ta har ya kasa ɓoye hakan ya tambaye shi.



"Zuwa nayi muka tattauna dasu" shine kaɗai abinda ya fito daga bakin Eeyad dan ba mutum ne da zai buɗe baki ya dinga koro maka zance ba.




Shugaban ƙasa ya tabbata Eeyad ba zai ƙara cewa komai ba daga haka, sai shima ya kauda maganar ya kawo wata, sun ɗan jima suna zantawa sannan Eeyad ya miƙe dan tafiya Abban Husnah yayi saurin faɗin "ba zaku gaisa da iyalinka bane, ni na rasa irin wannan aure naku kamar dashi kamar babu, daga kai har ita kowa ya doge a kan matsayar sa.




Komawa yayi ya zauna bai ce komai ba, shugaban ƙasa ya miƙe ya fita dan turo mashi Husnah.




Tsawon minti goma ta shigo a nutse cikin shigar dakakken leshi maroon color da ya haska farar fatar jikinta, kujerar da yake zaune ta nufa ta zauna a kusa dashi daf ta ɗora kanta a damtsen hannunsa a shagwaɓe tace baby ka manta dani ko?




Gyara zama Eeyad yayi sosai ya ɗago fuskarta yana kallonta na yan seconds, a ranshi ya ayyana ga mace har mace yana da ita amma shine yake rayuwa irin ta wanda bashi da aure kwata kwata, saboda tashi macen an gama shagwaɓa ta sai abinda take so kawai take yi, duk irin son shin da take ta kasa jure ma yanayinsa ta gudo gida wai ba zata iya ba ita dai a nemi mafita, shine iyayen ta da basu son ɓacin ranta suka zuba mata ido basu fahimtar da ita haƙuri ake yi har a saba ba, suka barta a gida kamar ma sun mance tana da aure a kanta, shima sai ya kawo ido ya zuba masu dan shi dai ba zai ce ta dawo ba tunda ba shi yace ta tafi ba, sannan ba zai taɓa sakinta ba dan hakan baya cikin tsarinsa, ba zai juri ganin ya saki mace wani ya aureta ya ratsa gonar da shi ya ratsa ba sai idan mutuwa ce ta ɗauke shi ko kuma ƙaddara mai ƙarfi, babu yadda zai yi da ƙaddarar Ubangijinsa.




A nutse yace "ai kin baro inda za'a dinga tunawa dake ɗin ne, sannan miyasa idan kika kira na ɗauka sai ki kashe waya, bana son haka fa Husnah"




Husnah ta kifa kanta a ƙirjinsa tana sakin shagwaɓaɓɓen kuka ƙasa ƙasa, tabbas tana masifar son mijinta, tana son komawa ɗakinta amma ba zata iya jurar shi ba, ba zata iya misalta yanayin shi ba sam.





Rumtse ido yayi jin kukan nata na neman saka masa ciwon kai yace ya isa haka Husnah tashi ki rakani muje gurin mota ta.




Babu musu ta raka shi suka fito ya shige tana tsaye tana kallon shi yayi mata alamar ta shigo da hannunsa, da sauri ta girgiza masa kai alamar a'a.



Eayad bai ƙara ce mata komai ba ya rufo ƙofar yaja mota ya tafi, saida taga fitar shi sannan ta ɗaga ƙafafunta a hankali ta koma ciki.




🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸

Estate ce madaidaiciya mai ɗauke da gidaje iri ɗaya wadda gwamnati ta tanadarwa ɗaliban da ta ɗauki nauyinsu, duk gida ɗaya mutum ukku ne suke zama a cikinsa, kamar haka ya kasance su ukku ne a gidan nasu kowa da ɗakinta sai babban falo da ya haɗa su dan hatta bathroom kowace tanada shi a ɗakinta wannan ya ƙara kwantar ma Nailah da hankali dan bata son duk wani abu da zai dinga haɗa ta da shirgin mutane, tunda tazo bata sake fita ko ƙofa ba sai yau da ya kasance zasu fara lectures mai suna lecture tana idar da  sallar Asubah ta ɗan kwanta a sallayar da nufin gurin ƙarfe bakwai ta tashi tayi shirin tafiya.



Sama sama take jin knocking ɗin ƙofar ɗakinta, ta buɗe ido bakinta ɗauke da Addu'ar tashi daga bacci tana laluben glass dinta ta saka sannan ta tashi ta nufi ƙofar ta buɗe.




Fatima ce, ɗaya daga cikin yan gidan nasu da itama ba zata gaza shekarun Nailar ba tana cikin shirin fita tace "barka da safiya dama gani nayi baki fito ba shiyasa nazo inji ko baki da lectures ne naga wancan satin ma baki je ba ko sau ɗaya?



Nailah ta ɗan shafa goshin ta cikin abin baccin da bai sake ta duka ba tace inada lecture mana fatima karfe nawa ne yanxu?



Fatima ta nuna mata agogon dake jikin bango lokaci daya kuma tace ƙarfe takwas da rabi fa, sai kuma ta juya tayi hanyar fita tana faɗin kinga nima nayi late kawai ya kamata ki dinga saka alarm tunda naga kinada nauyin bacci babu laifi.



Nailah da tunda ta kalli agogo ta zaro ido tana faɗin na shiga ukku ta juya da sauri tayi nan tayi nan tama rasa ta ina zata fara dan bama zata kira haka latti ba, ta tabbata duka lecture din farko sai ta rasa ta dan haka sai ta ja numfashi a hankali dan neman nutsuwa sannan ta dauke sallayar ta ninke ta cire kayan baccin jikinta ta faɗa toilet.



Bata wani jima ba ta fito ta shirya cikin doguwar rigar material wadda bata kama mata jiki ba ta ɗora hijab ɗinta coffe brown tayi tsaye tana tunanin shin ta tsaya ta karya ko ta tafi, to ai ita bama yunwa take ji ba gaskiya dan haka sai kawai ta rufo ɗakinta ta fito gaba ɗaya tana tafiya cikin tafiyarta mai dan sauri dan batada yanga a tafiya sam.



Babu nisa tsakanin University da Estate din da suke dan haka Naira hamsin ta ba mai napep cikin kudin da hakimi ya bata da zasu taho yace kuma duk abinda take buƙata ta kira shi kai tsaye.




A hankali ta ƙaraso lecture hole ɗinsu dake tsit sai muryar lecturer dake ta ɓaɓatu cikin harshen turanci, ba tare da wani tsaye tsaye ba ta sa kai ta shiga hole ɗin kanta a ƙasa tana Addu'ar Allah ya taimaketa kar a samu wata matsala.




Ai kuwa Addu'ar sai dai ta samu ladar ta dan wata tsawa da ya daka mata yace "hey who are you" ya saka ta ƙamewa a gurin tana rumtse idanunta sai kuma ta buɗe labɓanta masu maiƙo dake rawa rawa tace "nan nike Sir".



"Get out" ya faɗa a taƙaice yana sake ƙure fuskarta da kallon mamaki ganin ta ƙi cire glass din idonta sannan sai wani kauda kai take tana nuna kamar maganar shi hau mata kai take.



A sanyaye ta juya ta fice ta zauna a ƙarƙashin bishiyoyin dake gefe inda aka yi wasu kujeru irin na siminti masu kyau dan hutawa ko kuma karatu.




Ba shi ya fito ba sai 11:30am sannan ta samu ta shiga ta nemi guri can baya ta zauna tana sauraron uban surutun da yan ajin ke zubawa, tunani ta shiga yi wai ya haka ne, duk ajin da take sai a haɗa masu shegen surutu gashi ita bata surutu ko a secondary sai su ja a bige ajin tass a haɗe harda ita bayan kuma bata yi laifin komai ba, jama'a wannan ai ba adalci bane.





A gajiye ta dawo dan sai 6pm aka tado su ga wata yunwa dake waftar hanjinta gaba daya tayi nadamar fita ba tare da ta yi breakfast ba, babu ɓata lokaci ta ɗebo garin kwaki wanda shi yafi mata komai sauƙin sarrafawa a halin yanxu ta jiƙo shi ta xuba dakakken ƙulinta da mai da magi ta hau bisa kanshi saida taji tayi nak sannan ta sha ruwa tare da gode ma Allah ta shiga tunannin rayuwa.



Ita dai macece wadda rayuwarta ke buƙatar abubuwa da yawa gashi yanxu tayi nesa da duk wani wanda zai kalle ta yaga tanada wata buƙata ta kuɗi ya biya mata, ita kuma ba mutum ce mai son tambayar mutane ba har Hakimi yake faɗin duk abinda take so ta tuntube shi, itako ai ba zata iya ba, koma tayi ɗin shi da kanshi akwai lokacin da zai gaji da bani banin ta, sai kawai ta yanke shawarar da taga zata fishe ta sannan ta daura niyyar yin sallar istihara dan neman zaɓin Allah.




Washe gari tun shidda da rabi ta tashi sakamakon alarm ɗin da ta sa, yau kam a nutse tayi duk wani shirin ta har tayi breakfast sannan ta fito daidai lokacin da fatima itama ta fito suka wuce gaba daya, suna tafe cikin napep Nailah ke tambayar ta ɗayar maƙwabciyarsu dan tun ganin farko bata ƙara saka ta a ido ba.



Fatima ta taɓe baki tana kaɗa ƙafarta tace ina zan sani? Ai yadda kika ganta nima haka na ganta.




Nailah tace Allah ya kyauta kawai ba tare da ta ƙara furta komai ba.



Da aka tashi bata wuce gida ba, shiga tayi cikin gari abinda bata taɓa yi ba kenan tun zuwanta aikau taga gari gari ya ganta dan kale kalle ba'a magana sai dai ainahin abinda ya fidda ita din bata samu ba, dama ta san ba abu ne mai sauƙi ba samun aiki amma zata cigaba da Addu'a ta san zata dace InshaAllah.




Tun daga ranar kullum sai ta fita cikin gari taje companies da sauran guraren da ta san za'a iya daukar mutum aiki ba na gwamnati ba amma sai dai ace ta rubuta application ta bada har dai ta gaji ta zuba ma sarautar Allah ido, gefe guda kuwa ta cigaba da karatu ba kama hannun yaro.





Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har semester din farko ta kusa ƙarewa suna ta shire shiren fara jarabawa, tuni malamai da sauran ɗalibai suka farga da irin yadda kanta ke ja a department ɗinsu dukda bata miƙewa ta bada amsa a aji sai idan anyi test, presentations da sauransu, wannan ya saka da yawan yan ajin suke maƙale mata maza da mata musamman a lokacin test ko idan aka bada assignment, sai dai wasu mazan da biyu suke zuwa ba dan komai ba sai dan su samu kusancin da zasu ƙare ma kakkyawar fuskarta kallo, wasu kuwa yanayin zubin halittarta kawai suke wa mayata, ɓangare ɗaya kuwa wasu ke jin haushin ta a cikin ajin suna gani girman kai ne da ita, kuma ba komai yasa suke ganin haka ba sai yadda bata magana da kowa sai idan kaine ka tanka mata, idan ma ka mata maganar sai ta kama maka wani shegen kallo shi ba harara ba shi ba kallon ƙasan ido ba, sannan ta baka amsa tana kauda kai kamar an mata dole, a gurin Nailah kuwa sam ba haka bane, har yanxu dai bata jin zata iya buɗe idanuwanta duka ta kalli mutane, tafi gane ma ta dinga kallonsu ta ƙasa-ƙasa gaskiya.



Mutum ɗaya ce Nailah ta aminta da ita a matsayin ƙawa kuma aminiya wadda suke kashewa tare su rufe tare a department ɗinsu, a hankali kuma Nailah ta fahimci Khairat daga gidan manyan mutane take amma bata da girman kai ko kaɗan hasali ma kullum da niƙaf take zuwa har a tashi bata shiga harkar kowa shiyasa tasu tazo ɗaya, sai dai matsalar ita Khairat ɗan banzan surutu ne da ita wanda ba zaka fahimci haka ba sai kun zauna na yan mintina kun zanta, wani lokaci har takan bi Nailah gidansu idan sunada interval da yawa tsakanin lectures su ci abinci su huta sannan su dawo, sosai Khairat ke mata kyaututtuka na ban mamaki tun tana ƙin amsa tana baya baya har ta dawo ta saki jikinta ganin yadda Khairat ɗin ke ɓata rai idan ta nunaa ba zata karɓa ba, taga damar ma ta kwana biyu bata zo ba dan tasan hakan ba ƙaramin taɓa zuciyar Nailah zai yi ba har sai ta dinga kiranta tana faɗin dan Allah ita dai tazo ta kawo mata koma miye zata karɓa sannan ta samu nutsuwar zuciya............✍🏽

No comments