Hamshakiya 9

 




*🌸HAMSHAƘIYA*🌸



Na

_Jiddah S Mapi_



*Chapter 9*




               "Washe garin ranan aka sanar mata an samu mansion me kyau a cikin gari, hamdala tayi ba É“ata lokaci ta ciro maÆ™udan kuÉ—aÉ—e ta biya bayan taje da kanta ta duba, gidane me kyau na masu kuÉ—i, kuÉ—i dayawa ya rage mata ba kaÉ—an ba, manyan kuÉ—aÉ—e.


tana daga zaune a cikin gidan marayu tana kallon mutanen ciki, tunani takeyi a cikin kwakwalwan kanta, saida ta gama tsara komai kafin ta tashi taje É—aki, shiri tayi cikin wani riga da skirt wanda yaji jiki, hijabi tasa pink ya koÉ—e shima ya zama fari, saide ya mata kyau sosai kasancewarta farar fata  gashi tana glowing kamar ba daga cikin wahala ta taso ba, fita tayi daga gidan bayan ta yiwa unty Sadiya sallama cewar zataje ta É—auko yara a school, tana fita bakin kofa taga wata galleliyar mota ta tsaya a kofan gidan, da alama meshi yana kallon shige da ficen waÉ—anda suke gidan ne, a ranta tace "shine"


yara ne suka taso daga school sukazo da gudu ganin untynsu me kula dasu a wurin, rungumeta sukayi itama tana dariya har gefen kumatunta yana lotsawa ta durkusa kasa, faÉ—awa sukayi jikinta yaran maza ne da mata kanana, É—agowa tayi tana murmushi tace "Ahmad kun dawo?"

"eh anty mun dawo"


ciro minti tayi daga jakanta ta raba musu, karɓa sukayi kowa ya ɓare, bakinta suka kai saida ta tsotsi na kowa kafin suka sa a baki suna sha suna tsalle kallonsu tayi tana murmushi, a hankali tace "ku shiga ciki yanzu zanje in dawo ko?"


shiga sukayi kowa yana jin daÉ—i an bashi minti, binsu tayi da kallo idanunta yana cika da hawaye, a hankali tasa bayan hannu ta share hawayen ta mike ta fara tafiya cikin nutsuwa.


yana daga cikin mota yana ganin duk abinda ya faru, shima hawaye ne ya gangaro daga idonshi zuwa fuskanshi, hannu yasa ya share domin sun bashi tausayi ba kaÉ—an ba, kullum sai yazo nan ya tsaya domin bincike yanason yaga ko akwai bakon fuska da zaizo gidan, saide baiga kowa ba, jingina kanshi yayi da jikin kujeran motan yanajin ranshi ba daÉ—i, marayu suna wani irin rayuwa wanda babu daÉ—i, suna cikin yunwa wannan yarinyar data samu kulawa da datafi haka kyau amma kana ganinta kaga wacce take cikin matsin rayuwa ba yau kaÉ—ai ya fara ganinta ba, ya jima da ganinta idan ya kawo tallafin abinci gidan, itace kawai bata ganinshi, abinda yasa ta kara birgeshi ta bashi tausayi shine yadda take kula da yaran, yana wurin har taje ta siyo omo ta dawo, kallon bayanta yayi yadda take tafiya cikin nutsuwa, lumshe manyan idanunshi yayi yana jin wani abu a cikin ranshi.


yaje barack ya É—anyi aiki saida ya gama ya mika file na mutuwan a hannun general kafin ya fita ya shiga motanshi, bai tsaya ko ina ba sai wurin shan coffee kamar yadda ya saba kullum sai yaje, zama yayi aka kawo mishi ya fara sha yauma hankalinshi akan waya.


Cup ne ya faÉ—i a wurin ji kake tasss ya tarwatse, da sauri ta mike ta wanke ma'aikaciyar wacce ta yadda cup É—in a kasa gashi coffee da zafi ya kona mata kafa, cikin É“arin jiki tace "sorry madam"


"sorry for your self"


hankalin mutane ya dawo kansu ganin yadda take huci ta cire bakin glass na fuskanta tana aikawa yarinyar kallon rashin mutunci, a hankali ya É—ago kanshi jin hayaniya a gefe, da sauri ya mike ganin yarinyar daya bari a gidan marayu yanzu.


cikin mamaki ya zuba mata ido yana kallon kayan jikinta, wando ne ya kamata sosai da riga baƙi, kanta wani karamin mayafi ne na gucci, takalmin kafarta me tsinin gaske baki, ga jaka da glass a hannunta.


taka kafarshi ya fara yana kara kallonta sosai, saida ya iso wurin mutane suka matsa domin sunsan matsayinshi, da hannu ya nunata "ba kece a can ba?"


harara ta watsa mishi cikin tsiwa tace "aina?"


shiru yayi ganin wannan tana da tsiwa saɓanin wancan kuma batama fiye magana ba, kare mata kallo yayi wannan tafi wancan tsayi saide wancan tafi wannan haske, to amma kama ɗaya komai iri ɗaya, kallon kayan jikinta yayi zai kai miliyan ɗaya duka da jakan gucci, wancan tana gidan marayu ta yaya zata samu kayan miliyan ɗaya?


ji yayi tace "stay away from here, banza useless baki iya kula da customer ba?"


kallonta ya kumayi bayan tasa eyeglass a idonta, ɗaukan jakarta tayi da makullin mota tabar wurin, bayanta yabi da kallo har yanzu bai daina mamaki ba, wannan tafi wancan kiɓa.


saida ta bar wurin ya daina kallonta zuciyarshi cike da mamaki, mutane sun watse a wurin a hankali cikin sanyin jiki da mamakin abin al'ajabin daya gani yaje wurin masu aikin yace "sannunku wannan data tafi anan yaushe tazo ne?"


"yallaɓai ta kai awa uku anan"

tunawa yayi da barinshi gidan marayu bai wuce awa É—aya bane, kara tambaya yayi "dama tana zuwa nan ne?"



"eh yallaɓai tana zuwa kullum"


biyansu kuÉ—insu yayi kafin ya fita daga wurin ya shiga motanshi ya fara tuki yana tunani haÉ—e da mamaki, a kofan gidan yayi parking ya ciro facemask yasa kafin ya fito, kai tsaye cikin gidan ya shiga bayan ya nuna id card nashi, yana shiga ya tsaya a bakin kofan yana kallon mutanen gidan, masu aiki sunayi masu kitso sunayi, daga can ya hangota da kayan jikinta na É—azu ta É—aura bokitin ruwa a kanta tana tafiya tana murmushi kamar yadda ta saba, innocent ce sosai fuskarta baya rabo da murmushi, da sauri ya juya baya baison ta ganshi.


abin mamaki ya tuno wancan kuma bata dariya gata da tsiwa da rashin kunya, wannan kuma Innocent ce, to ya akayi suke kama? ko dai twins ne? kamar shi da Umar, fita yayi daga gidan ya shiga mota yana dafe kanshi tunani ya kasa barin ƙwaƙwalwarshi.


murmushi tayi lokacin data ganshi ya juya baya, a ranta tace "mugu azzalumi ya dawo domin ya samu wata ya kara lalatawa, kafin yayi haka saina kashe shi da hannuna, juye ruwan tayi a cikin randa tana kara kallon kofa, ganin baya nan ta saki ajiyan zuciya.


da wannan tunanin ya koma gida, jikinshi a mace ya kwanta a falo ya zubawa Tv Ido, yau yaga abin al'ajabi, Ammi da Elham sun shirya zasuje karɓawa Elham maganin gargajiya domin cibiyanta yana ciwo, sun shirya tsab cikin riga da skirt anko sukayi yayi musu kyau, hannun Elham a cikin na Ammi tana ganinshi a kwance ta saki hannun Ammi taje da gudu ta faɗa jikinshi tana murna tace "yah Umar ina chocolate ɗin?"


lumshe ido yayi yanajin yadda ta dafa cikinshi har wani zafi yake mishi, É—agata yayi daga jikinshi yace "tashi da Allah bakya girma"


a take ta gane ba Umar bane Faruk ne, barin jikinshi tayi taje wurin Ammi, kallonshi Ammi tayi tace "lafiya babana?"


"Ammi lafiya lau inaso na tambayeki wani abu please"


zama tayi a gefe tana ganin yanayinshi, tace "ina jinka"


matsowa yayi yace "Ammi dama mutane biyu suna iya yin kama kuma basuda alaqa?"

murmushi tayi kafin ta shafa kanshi tace "tabbas mutane biyu suna iya kama bakaji Allah yace yayi mutum da kamanninshi bakwai ba?"


"amma Ammi kaman fa Æ´an biyu suke"


"kwarai ikon Allah ko kuma ya kasance su Æ´an biyu ne wani abin yasa suka rabu suma basu sani ba, ko kuma kama ne kawai yazo É—aya"

lumshe ido yayi yace "na gode Ammi" 


Kallonshi tayi "lafiya dai kam?"

"lafiya kalau"


Umar da yake bakin kofa yace "kamar ni da kaine sai wani ƙaddara ya rabamu kai kaje kayi kuɗi fiye da wanda muke dashi ni kuma inje in talauce a wani gari"


shagwaɓe fuska Faruk yayi yace "Ammi kin ganshi ko? kinji irin maganan da yake yi"


"gaskiya na faɗa ƙaddara zai iya rabamu"

tashi yayi ya bishi da gudu yanaso ya kai mishi duka dan ya tsani ace zasu rabu da Umar, Elham ta É“oye kanta a bayan Ammi tana dariya tasan idan Faruk ya ganta sai tasha mari, Ammi dariya kawai takeyi ganin suna zagaye falon, hakan ya tuno mata da mahaifinsu wanda yake biye musu lokacin da suke yara suyita guje-guje a falon, É—auke kai tayi jin hawaye yana shirin wanke mata fuska a hankali tace "muje"

hannun Elham ta rike suka fita daga falon, driver ta É—agawa hannu da sauri ya buÉ—e musu mota suka shiga, driving ya fara suka bar gidan, kwantar da kai Elham tayi a cinyan ammi tace "ammi? Æ´an biyu suna iya rabuwa su girma a wuri daban-daban?"


"kwarai hakan yana iya faruwa wasu ƙaddara ne take faɗawa kansu har su rabu"


"yah Umar da yah Faruk sukam Allah ya taimaka basu girma daban-daban ba"


shafa kwantaccen gashin kanta Ammi tayi tace "kwarai kuma hakan abin jin daÉ—i ne, saimu kara godewa Allah a duk halin da muke ciki"



saida ya gaji da binshi kafin ya faÉ—i akan kafarshi ya rike yana cewa "wayyo kafata"

da gudu Umar yazo yana cewa "meya samu kafarka?"

janyoshi yayi ya fara bugunshi a baya, saida ya barshi kafin yace "kada ka kara magana akan rabuwarmu tare zamu mutu har karshen rayuwa"


murmushi yayi "nima da wasa nake amma kasan akwai ƙaddara me raba mutum da wanda yake so, kamar aure zai iya rabamu"


hannu yasa a bakinshi yana girgiza kai yace "zamu auri mata Æ´an biyu masu kama É—aya kamar mu, sannan mu zauna anan gidan muyi rayuwa me daÉ—i tareda Ammi"


"bakasan kalan macen da nakeso ba, kaima bansan kalan wacce take ranka ba, to idan ra'ayinmu baizo É—aya bafa?"


Umar yayi magana yana gyara zama a gefen Faruk, murmushi Faruk yayi yace "wace irin mace kake son aura?"


"inason mace classy kyakkyawa fara doguwa me ɗan kiɓa ba sosai ba, ya kasance tana son yin turanci a cikin magananta, me gashi, me tsiwa kuma wacce batada nuƙu-nuƙu ma'ana a fili take.


wani irin murmushi yayi a cikin ranshi jin irin matar da Umar ya lissafo zai aura, lumshe ido yayi nan ya hango wannan me faÉ—an a coffee shop, Umar ya É—an bugeshi kaÉ—an yace "kaifa wace kala kake so?"


"Inason mace shiru-shiru wacce bata fiye magana ba kamar ni, kuma marainiya me kula da marayu yara ƙanana, wacce take son murmushi a koda yaushe, inason wacce bata ɗauki duniya da faɗi ba"


lumshe ido yayi yana tuno yadda take bawa yara kulawa tana dariya a cikin ƴan uwanta marayu yace "kyakkyawa fara doguwa batada kiɓa, batada kayan sawa na kirki"

bugeshi Umar yayi "ka fara wautan naka ko?"


tashi yayi yana tafiya yace "kai ka sani idan kaga dama kaje ka É—au gidan marayun gaba É—aya ka kawo gidannan"


dariya kawai yayi shima ya tashi yaje ya zauna akan kujara yana kallon Tv yace "watarana zanyi hakan"

tsaki kawai Umar yaja bai kuma ce mishi komai ba.



*Gidan Marayu*


Kallon unty sadiya tayi tace "zanje yanzu na dawo ba zan jima ba"

"tom saikin dawo amma kada ki jima fa"


"Tom insha Allah bazan jima ba"


fita tayi daga gidan yau tayi sa'a baya nan, bata tsaya ko ina ba sai kofan asibiti, shiga tayi tana kallon inda suka kwantar da zainab, ranta yana zafi taje ta yanki katin ganin likita fuskarta da facemask babu wanda ya ganeta, anyi mata iso ta shiga ciki tayi sallama tareda cire facemask É—in, yana zaune akan kujeranshi me juyawa yana shan vitamin c, kallonta yayi yadda ta tsaya a kanshi yana murmushi yace "zauna mana Æ´ammata"

a hankali ta zauna akan kujeran dake facing nashi, a goshinshi take kallon zainab tana mata murmushi, cikin sakin fuska yace "meke damunki?"


da hannu ta nuna mishi kirjinta tace "nan yana ciwo"

murmushi yayi yace "ko zan iya gani?"

É—aga hijabin jikinta tayi idanunta a kanshi tana kallon fuskarshi, ba abinda take tunawa sai lokacin data durkusa kasa ta rike kafafunshi tana rokonshi ya yiwa zainab aiki.


bata ankara ba taga yana shirin ɗaura hannu akan kirjinta wuƙan data ɓoye a bayan skirt nata ta ciro da karfi ta caka mishi a hannu.


Ihu ya buÉ—e baki zaiyi da karfi ta toshe bakinshi, wukan ta ciro ta yanka wuyanshi take jini ya É“alle a wurin, kwantar dashi tayi har yanzu hannunta a bakinshi bataso yayi ihu, a kunnenshi tace "kune kuka nunamin wannan hanyan, bakuda imani nima na cire nawa, dolene na É—au fansan ran Æ´an uwana, mu marayu ne bamu da kowa sai Allah, a goshinka nake ganin zainab É—ina tana min murmushi, kaima kaje inda taje kace ina gaisheta idan tace wace kace kawarta Amrish"


tana gama magana taji ya daina motsi, janshi tayi da kyar ta kwantar dashi a gefe, zama tayi ta fara kuka, wukan yana hannunta tana kuka sosai me cin rai, "mutane sune suke koyawa mutum mugun hali, gashi sun janyo ta zamo me kisan kai"

saida tayi kuka me isanta kafin ta mike tasa facemask ta fita ta a É—ingishi, kallonta mutanen wajen sukayi bayan ta fita bata tsaya ko ina ba sai cikin taxi, gidan data siya can taje, akwai masu gadi akwai masu kula da flowers gefe guda kuma mata ne tsoffi guda biyu suna tsabtace cikin gidan idan yayi kura, bata gaida kowa ba a cikinsu ta fara taka matattakalar stair da gudu, wani haÉ—aÉ—É—en É—aki ta shiga, kyau da komai yayi, shiga toilet tayi wanda shima kaÉ—ai abin kallo ne, wanka tayi ta fito ta shirya cikin kaya wanda yake a buÉ—e hannun a yanke ansa leshi a jikin, rigan black ne ba karamin kyau yayi mata ba, hula irin na maza picap shi tasa, bayan ta kame tulin gashinta da bakin ribbon, zama tayi akan stool ta shafa powder da lipbalm abinda ta jima batayi ba kenan shine kwalliya, saida ta gama ta kalli kanta a madubi, gel ta shafa a gaban kanta ya kwantar mata da gashin dake goshinta sosai, turare masu kamshi ta fesa sannan ta É—auko wani siririn mayafi É—an karami tayi rolling na kanta, bakin glass tasa a idonta kafin taje wurin takalma ta É—au wani dogo tasa a kafarta, makullin mota ta dauko da wani waya kiran Iphone 14 pro, fita tayi daga dakin.


"Masha Allah" shine abinda kowa yake faÉ—a idan ya ganta, da sauri ta shiga motan ta fara driving, bata tsaya ko ina ba sai gidan marayu, Office na manyan taje dama ta kirasu a waya, shiga tayi bayan sunyi mata iso, waje aka bata me kyau ta zauna tare dasu suna fuskantar juna, duk ta sansu kaÉ—an daga cikine bata sansu ba, sune sabbin fuska, kallonta sukayi babu wanda ya ganeta a cikinsu.


"barkanku da warhaka nice Ameera Ibrahim dikko Æ´a É—aya tilo ga alhaji Ibrahim dikko me rasuwa, inason in siye gidan marayun nan idan kun yadda kun bani haÉ—in kai akan kuÉ—i ninkin wanda kuka sashi a kasuwa"


kallon kallo suka fara a tsakaninsu, basu taɓa tsammanin zasu samu kuɗi har haka ba akan gidan, kallonsu tayi ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya bata cire glass ɗin ba tace "na kara kaso biyu akan wanda na kara da farko"


zaro ido sukayi a take sukace "ranki shi daÉ—e mun siyar"


murmushi tayi wanda ya fito da sihirtaccen kyaunta tace "ba ranki shi daɗe ba kuce HAMSHAƘIYA"


atare suka haɗa faɗan "HAMSHAƘIYA mun siyar"


wani irin murmushi ta kuma yi kafin ta mike taje cikin mota ta ciro wani bakin jaka babba, dawowa tayi tace "kuyi sign ku bani original takaddun gidan"

dukkansu saida sukayi sign kafin suka miƙa mata cikin girmamawa, karɓa tayi ta duba, ta ciro wani abu kaman waya ta auna taga lalle wannan shine original kafin ta buɗe jakan kuɗaɗe ne daloli wanda ta kwashe a gidan Alhaji hamza, mika musu tayi har rige rige suke wajen karɓa a ranta tace "kwaɗayayyu masu son abin duniya"


kallonsu tayi tace "wannan kuɗin idan kuka canja zai siye wannan gidan marayun sau shida, saboda haka daga yau gidannan yana karkashin ikon Ameera Ibrahim dikko, wato hamshaƙiya"


tashi tayi da takaddun a hannunta tace "gobe za'a fara aiki kuma zan É—ibo sabbin ma'aikata na barku lafiya"


tsaban murna basu wani kulata ba sukace "mun gode"

fita tayi ta shige cikin mota, kifa kanta tayi jikin sitiyari ta fara kuka, kuka take sosai tana jin wani irin daÉ—i a cikin ranta, yanzu zata fara taimakon Æ´an uwanta marayu da yaddan Allah, da sauri taja motan ta nufi shagon coffee dan tasan yanzu haka yana can.


parking tayi kafin ta fito tana taku tana kallon mutane a tsiyace, shiga cikin shagon tayi tana taunan cingum, hangoshi tayi yayi kyau cikin riga dark blue da wando baƙi, murmushi tayi kafin ta fara takawa har zuwa gabanshi, takalmin da yake kafarta me tsini shi tasa akan kafanshi ta taka da iya karfin da Allah ya bata har tana cije leɓen bakinta.


"Auuuuch"

ya faÉ—a yana rike kafa jin wani azaban zafi ya ziyarceshi, murmushi tayi domin ta juya mishi baya, a hankali ta juyo tace "sorry"

bayan haka bata kara cewa komai ba taje ta zauna, coffee da biskit aka kawo mata ta karɓa tana kallonshi ta cikin glass dake idonta.


tsananshi tayi sosai dan abinda ya janyo teema tayi, a fuskarshi take hango teema lokacin data rataye kanta, ajiye cup ɗin tayi tabar wurin dan ba karamin tsana tayi mishi ba, shima idan bata kasheshi ba ba zata taɓa jin daɗi ba.




*Ki biya kuÉ—in littafin kiyi karatu cikin salama, ₦400 ne ta account nawa 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, ko katin mtn ta nan 08144818849 harda masu vtu kuyi ba matsala sai ki turo katin shaidan biya ta nan 08144818849*

No comments