Hamshakiya 5
*🌸HAMSHAƘIYA*🌸
Na
Jiddah S Mapi
*Chapter 5*
~Babban wurin shan coffee dake cikin garin wanda manyan mutane suke zuwa domin shan coffee, ƴammata da samari suma ba'a rasa su a wurin domin shaƙatawa da samun daman tattaunawa tsakanin masoya.
Tafiya yake cikin nutsuwa da kwarjini, duk inda ya gifta Æ´ammata kallonshi suke domin Faruk ba karamin kyakkyawa bane ga kuma jan aji, akan wani kujera wanda aka tanada domin customers acan ya zauna ya ciro waya, kanshi kasa ya fara latsa wayan dan baison idon mutane gashi ya lura shi kawai suke kallo musamman Æ´ammatan.
bai jima da zama ba wata waiter tazo tace "yallaɓai a kawo maka coffee ko tea? ko green tea?"
bai É—ago kai ba yace "coffee one cup"
"Okay sir"
tafiya tayi daga wurin bata jima ba sai gashi ta dawo da karamin plate wanda aka É—aura cup cike da coffee a ciki.
a gabanshi ta ajiye a hankali ya É—ago kai yana kallon coffee wanda yake tururi yana fitar da hayaki, saida ya bari ya É—an huce kafin ya É—aga ya fara sipping kaÉ—an-kaÉ—an, har yanzu hankalinshi yana kan waya, Æ´ammata sai kallonshi suke saide babu fuskan yin magana domin yanada kwarjini.
saida ya shanye coffee ya tashi bayan yayi payment ya fita daga wurin, driver É—inshi ya É—agawa hannu da sauri yaje ya buÉ—e mishi marfin mota, shiga yayi suka É—au hanyan zuwa gida.
suna isa gida getman ya buɗe musu suka cusa hancin motan izuwa ciki, saida sukayi Parking driver ya zagayo ya buɗe mishi marfin motan, a hankali yasa kafanshi ya fito, miƙa yayi yana bin cikin gidan da kallo, komai tsaf-tsaf kamar yadda yake so, baison ganin cikin gida ba tsari, ga kuma gefe guda masu kula da harkokin gidan suna aikinsu, yawancinsu sojoji ne domin shi ɗin babban soja ne hakan yasa aka bashi masu tsaro na gida da kuma na wajen aiki, takawa ya fara cikin nutsuwa har ya isa kofan da zai sadashi da babban falo, sallama yayi kafin ya shiga yana shaƙan ƙamshin daya bugi hancinshi, lumshe ido yayi shiyasa yake son Amminshi sabida tana son turare, kullum idan ya dawo gida ƙamshin turarenta shi yake fara yimishi marhaba.
Bai ganta a falo ba yanada tabbacin tana cikin É—akinta, tafiya ya fara yana taka matattakalar cikin nutsuwa har ya isa É—akin Ammi, knocking yayi tareda sallama, amsawa tayi tareda cewa "shigo"
tura kofan yayi ya shiga É—akin, komai a kimtse sai kashi yake tashi ga kuma sanyin Ac, akan sofa ya zauna yana kallonta, tasa riga dogo na atamfa da hijabi ruwan kasa, tace "Babana ka dawo lafiya?"
giÉ—a kai yayi kafin cikin miskilanci yace "na dawo Ammi, ina Umar?"
taɓe baki Ammi tayi sannan tace "kaima kasan halinshi ai bai dawo ba, yana dawowa kuma zaice aiki ne ya ajeshi, gashi kuma na san ba haka bane, daban ma inda yaje"
"sorry Ammi may be yana hospital ne bari na kirashi"
waya ya ciro yayi dialing numbern da yayi saving da dude love, bugu kusan uku bai É—aga ba, fuskarshi ne ya canja alaman baiji daÉ—in rashin É—agawan da Umar yayi ba, a hankali ya kuma dialing numbern"
ɓangaren Umar kuma yana can hotel shida teema suna aikata ba daidai ba, bayan ya gama biyan buƙatarshi ya kwanta lub a kan bed ya rufa jikinshi da lallausan bedsheet ya rungume teema a kirjinshi bacci me daɗi ya ɗauke su, kasancewar yasa wayarshi a silent hakan yasa baiji kiran da Faruk yake mishi ba"
miss calls kusan shida bai É—aga ba, Ammi tace "kyaleshi ba zai É—aga ba na tabbata wani abinda babu kyau yake aikatawa, na rasa yadda zanyi da Umar"
"Ammi may be Yana tsaka da aikine shiyasa bai É—aga ba amma bari na kira kamal naji ko yana hospital"
kiran Kamal yayi ya sanar mishi da Umar yabar hospital da jimawa"
kashe wayan kawai yayi ya kwanta akan sofan yana kallon slin É—in É—akin, Ammi ma bata kara magana ba taci gaba da abinda take yi.
sai kusan karfe 10 na dare Umar yasa Teema a mota suka nufi gidan marayu, a inda ya saba ajeta anan yauma ya ajeta bayan ya bata kuÉ—aÉ—e masu yawa, juyawa yayi ya kama hanyan gida, kusan karfe 10:30 ya isa gida, getman ya buÉ—e mishi kofa ya shiga, fitowa yayi ya shiga ciki, Ammi da Faruk ya gani suna zaune a falo suna kallo sai hira suke jifa-jifa domin Faruk bai fiye surutu ba, rarraba ido yayi kafin ya samu waje ya zauna jikinshi a mace ganin babu wanda ya mishi magana, gyaran murya yayi cikin rashin gaskiya yace "Ammi ina Elham?"
fuskanta ba yabo ba fallasa tace "tayi bacci" daga wannan bata kara yin magana ba, kallon Faruk yayi wanda yake sanye da jensy ya zubawa Tv Ido baiko kalli inda yake ba, saida ya keɓe baki alaman yasan yayi laifi kafin yace "Dude? ya kake ya gida?"
bai kalli inda yake ba yace "lafiya"
tashi yayi cikin rashin gaskiya ya haura sama, É—akinsu ya shiga wanda mallakinsu ne shida Faruk, wanka yayi kafin shima yasa jesy irin na Faruk ya fito, zama yayi a gefen Faruk shima ya zubawa Tv Ido, Ammi da bata lura da zuwanshi ba hankalinta yana kan Tv ta É—ago kai zata yiwa Faruk magana taga su biyu ne a wurin, kasa gane wannene Faruk a cikinsu tayi, dama watarana idan sukayi dressing iri É—aya bata iya bambance waye Umar kuma waye faruk?.
nunawa tayi kaman ta ganesu tace "faruk bani maganina a cikin frij"
a tare suka amsa da "to"
da sauri Faruk ya kalleshi, sakin bai Ammi tayi ganin sun mike a tare, cikin É“acin rai tace "Faruk nace ba Umar ba"
kin zama yayi saima kallon Faruk da yayi, shima Faruk kallonshi kawai yayi, atare sukaje bakin frij, Umar ne ya É—au maganin ya kaiwa Ammi.
kallonshi tayi sosai atake ta gane wannan ne Umar kin karɓan maganin tayi tace "ka bawa Faruk shi nace ya ɗaukomin ba kaiba"
murmushi yayi ganin ta ganeshi ya durkusa kasa yace "kiyi hakuri Ammi wallahi wani aiki nakeyi shiyasa ban dawo da wuri ba, but am sorry"
kallonshi tayi, ba zata iya fushi da yaranta ba, a hankali tace "amma kasan mahaifinku kafin ya rasu ya bani amanarku? kada na bari ku aikata wani abinda ba kyau? gashi naga kai Umar sam hakan baka É—aukeshi a bakin komai ba, case uku yanzu aka kawomin a kanka daga naji kayi faÉ—a da wannan sai naji kana tare da wannan yarinyar sai yau kana wannan club É—in gobe kana wancan, hakan yana maka daÉ—i ne?"
girgiza kai yayi kanshi a kasa, "kayi koyi da É—an uwanka mana"
"Sorry Ammi"
"ba komai ka canja hali"
tashi yayi ya haura sama kwanciya yayi akan bed domin bacci yakeji, Faruk ne ya turo kofa ya shigo, hawa gadon yayi shima yaja blanket ya kwanta, kallon bayanshi Umar yayi da alama yana fushi dashi ne, murmushi kawai yayi ya lumshe ido dan yasan gobe da safe shi zai fara yimishi magana.
"Karatun kur'ani take koyawa yara ƴan kanana duk bayan sallan isha, yanzu ma haka har sun fara, saide yau bata cikin yanayi me daɗi domin an tafi da Feenah kuma tana da tabbacin saudiyya zasuje da ita su rinƙa bara suna tara makudan kuɗaɗe da ita, bini-bini hawaye yana wanke mata fuska tana gogewa ba tareda ta bari sun gani ba, rayuwar yaran yana cikin haɗari ita kanta bata tsira ba, domin suna kwasan ƴammata su bawa masu kuɗi suyi amfani dasu, wasu ayi amfani dasu ta baya wasu kuma maza sun kai uku a kansu, suna cikin karatu Zainab ta shigo da katon leda a hannunta, idanu ta zuba mata har ta iso ta ajiye a gaban yaran tana kallon Amrish tasan akwai tambaya a bakinta amma ta share ta fara raba musu juice irin na yara ɗinnan, da biskit sai minti me tsinke, saida ta rabawa kowa suna murna suna godiya sukace "mun gode Unty zainab"
cikin sakin fuska tace "ku tashi kuje ɗaki kuci, amma banda faɗa duk wanda yayi faɗa zan karɓe nashi"
tashi sukayi suna murna harda tsalle domin basu taɓa samun irin wannan abin ba, da kallo ta bisu idanunta suna cika da kwalla, itama Amrish hawayene ya cika mata ido, a hankali ta juya ba tareda ta bari zainab ta gani ba ta share hawayen, kafin cikin danne kukan tausayin kansu da yaran tace "ina kika samo kuɗi dayawa haka?"
shiru zainab tayi bata amsa mata ba, gaban Amrish ne ya faÉ—i, matsowa tayi kusa da ita ta dafa kafaÉ—arta tace "tambayanki nake zainab ina kika samu kuÉ—i?"
ganin ta kuma yin shiru sai hawaye da suke wanke mata fuska tace "ba dai mutuncinki kika siyar ba?"
kallon Amrish tayi wacce ta tsareta da manyan idanunta tace "mutunci kuma na nawa Amrish? Ai mutunci na jima da rabuwa dashi, ko kin manta a asibiti da MUTUNCINA aka yiwa su Na'eem me rasuwa aiki?"
sakinta Amrish tayi a hankali ta koma baya ta zauna, fashewa tayi da kuka me tsuma zuciya tace "zainab hakan ba shine zai baki daman aikata saɓon Allah ba, idan mukayi hakuri Allah zai bamu mafita, bazan iya juran ganinki kina wannan halin ba, tare muka tashi dake keɗin ƴar uwata ce kuma kawata bazan iya ganinki haka ba, bazan iya ba zainab"
ta faÉ—a cikin kuka sosai, rungumarta zainab tayi suka fara kuka sosai babu me lallashinsu, saida sukayi me isansu kafin suka saki juna kowacce ta samu guri ta zauna tayi tagumi, suna tunanin halin da Æ´an uwansu zasu tashi a ciki, basa fatan su tashi cikin kunci kamar yadda su suka tashi a ciki.
shugaba ta kula da zainab ta fara fita tana bin maza hakan ba karamin daÉ—i yayi mata ba, taci gaba da sa mata ido tana ganin duk wani shige da fice da yarinyar takeyi a gidan, ganin sawu galla gallan motoci ne suke sauketa yasa ta fara jan yarinyar a jiki.
kullum sai tayi musu karatu kuma suna ɗauka zainab tana cigaba da kawo musu abinci da kayan abinci masu yawa, gashi kowani dare saita rabawa yaran minti da juice harma da biskit, suna jin dadi hakan yasa suke zuwa islamiyyan daren har rige-rigen zuwa suke, Amrish batajin daɗin abinda zainab takeyi saide ba yadda ta iya suna cikin talauci da matsin rayuwa dolene take karɓan abin tana ci badan taso ba.
Umman manal tace "Amrish!!" firgigit ta juyo tana kallonta tayi nisa cikin tunani ko magana bata ji, zama tayi a gefenta hannunta rike da jaririyar da take kuka tace "kefa yarinya ce karama irin wannan tunanin zai iya jefa rayuwarki cikin haɗari zaki iya kamuwa da low BP kizo kina shan wahalan jinya, kina fa gani a idonki aka rabani da ƴata manal aka kaita wa maza matsafa sukayi amfani da ita, gawanta aka dawomin dashi gidannan, Amrish ni kuma hauka kikeso nayi? ai wannan yafi karfin nayi tunani saide karamin hauka, amma haka na miƙa komai wa ubangiji na hakura na rungumi ƙaddara naci gaba da rayuwa a nan gidan domin babu inda zanje, kun zame min kamar kannena, bazan iya rayuwa babu ku ba, keda zainab da sauran ƴammatan gidannan kune gata na ku nake gani naji sanyi, wannan yaran kuma kamar ƴaƴan cikina nake ganinsu dan Allah ki rage tunani kinji?"
itama kuka take yayinda take bata labarin, murmushin takaici Amrish tayi kafin tace "kema dauriya kawai kike yi, ba zaki iya tafiya ki barmu bane shiyasa kika zauna, amma ba komai zan rage tunani"
karɓan jaririyan tayi wacce take tsala ihu kamar ana dukanta, a hankali tace "shikenan Najma shikenan ki daina kuka"
girgiza takeyi a bayanta har tayi shiru, karɓan zani tayi ta goyata kafin ummanta wacce take da suna Sadiya tace "ku daina cemin Umman manal ku rinƙa kirana da sunana Unty sadiya domin sunan manal yana kara tunomin da ita"
murmushi tayi tace "tom unty Sadiya"
É—aukan bokiti tayi da yarinyan a bayanta ta nufi bakin bohold, buga ruwan tayi domin tanaso tayiwa yaran wanka kafin itama tayi, saida ta cika ta É—aura a kanta, kaiwa tayi cikin wani katon roba ta juye, kiransu ta fara É—aya bayan É—aya tana wankesu, saida ta tabbatar sun wanku kafin itama taje ta cika roba tazo ta shiga bayi, sauke Najma tayi daga bayanta tayi mata wanka itama kafin ta mikata wa anty sadiya, komawa tayi tayi wanka, tareda wanke gashin kanta me tsayin gaske, kallon jikinta tayi ita kanta tasan Allah ya bata farantaka da kyaun sura saide baya samun gyara, gashinta ma Allah ya yishi da tsayi da tsantsi amma tasan da yana samun gyara da zaifi haka kyau, ga kuma fatanta dake shining duk da bata wanka da sabulu sai omo, É—aura zani tayi a kirji ta zura katon hijabi da silifas ta É—au bokitin ta fito.
babu man shafawa shiyasa kowa yasa riganshi itama wani dogon rigan material red tasa wanda yaji jiki sosai ta zauna a gefe tayi tagumi tana jin jikinta yana janta, dama haka wanka da Omo yake idan baka shafa mai ba sai jikinka yayi ta kanka.
Allah dai ya kawo musu mafita, zainab ce ta shigo da dogon hijabi da babban leda a hannu, kallonta anty sadiya tayi tace "daga ina kike?"
zama tayi tana buÉ—e ledan abinci ne masu kyau harda kaji da drinks tace "Unty Sadiya kuzo muci nasan kuna jin yunwa bakuci komai ba, ku yafeni ban dawo da wuri ba, kuma na haÉ—aku da Allah kada ku tambayeni inda na samu"
suna kin yunwa tabbas amma ba zasu iya zuba ido suna ganin tana wannan rayuwan ba, cikin faÉ—a da nasiha anty sadiya ta rinka nuna mata abinda takeyi ba daidai bane, tayi shiru kawai, matsowa sukayi sukaci kadan badan sun koshi ba suka bawa yaran sauran har kokawa sukeyi akai, saida Amrish ta rabasu kafin ta bawa kowa nashi.
_domin neman karin bayani a tuntuɓi wannan number 08144818849_
No comments