Furar Danko 67
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣7️⃣
.......Da sallama ya shiga falon, tana kwance a 3sitter idanunta a lumshe tamkar mai barci, sanye take da doguwar riga mara nauyi milk color data bi jikinta ta fidda ainahin surarta, sai dai bawai ta matseta bane ba, kanta babu ɗan kwali sai gashin data ɗaure a tsakkiya. Buɗe ƙofar da jin shiru kuma ya sata jiyowa tana buɗe luluu idanunta a kansa. Numfashi ya sauke a hankali da ɗan janye idanunsa batare da yace mata komai ba ya wuce ta, itama baki ta taɓe tare da maida idanunta ta lumshe. Minti kamar biyu sai gashi ya dawo riƙe da Hijjab a hannu, cikin motsa lips ɗinsa kaɗan kamar bayaso ya furta, “Ina tare da su Ahmad tashi kisa hijjab”.
Idanunta ta buɗe fuskarta a tsuke matuƙa da damuwar kaɗaicin da take ciki ita kaɗai a gida ba waya ba wani abin ɗebe kewa dan ba'a haɗa musu ba, kamar zata ɗauke kai sai kuma ta sake yamutse fuska cikin izzar nan tata ta furta, “Dan kawai kana tare da wasu sai na kama saka hijjab. Wai mi kake nufi da ni ne? Ko dan kaga na saka a waccan ranar kake tunanin cigaba da jin kanka sama can”.
“Mawaddat Umarni ne tashi ki saka hijjab ko nayi abinda bazai mana daɗi ba mu duka”. Ya faɗa shima cikin deep voice ɗinsa da dakewa yana tsatstsareta da idanun da take kira na macizai babu alamar wasa tattare da shi. Kanta ta ɗauke gefe a gatsine ta ce, “To yi ɗin mana”.
“Okay haka kikafi buƙata?”. Ya faɗa shima a dakensa yana ƙoƙarin kai hannu kanta. Tashi tai zaune tana watsa masa harara, dan babu abinda yazo a zuciyarta sai abinda ya faru tsakaninsu ɗazun, ita kuma abinda bazata iya ɗaukaba kenan taɓa mata jiki balle har yay tunanin sake maimaita abinda yay matan.
“Au ashe tsiwar taki iya baki ne? Da ki ƙi tashi ɗin mana kiga yanda zan tabbatar miki kan nawa a saman yake.” ya ƙarasa maganar yana jefa mata hijjab ɗin a jikinta ya juya ya fice. Wani irin kallon takaici ya riƙe maka maƙoshin nan ta bisa da shi, a zuciyarta tana ayyana (Mi wannan mutumin ke nufi da ni ne wai shin? Ƙoƙarin takani ko mi? Yimin gadara da nuna zafin kai ko mi? Humm aiko gidan ya tarar in dai nice, zan bashi mamaki a gidan nan mu zuba) ta yunƙura da nufin barin falon batare da saka hijjab ɗin ba. Sai dai tana miƙewar su Ahmad nayin sallama, ƙofar ta zubama ido kawai tama rasa miya kamata tayi har Smart ya shigo a farko, ja yay ya tsaya murmushin fuskarsa na ɓacewa ɓat, sai kuma ya rumtse ido da masifar ƙarfi zuciyarsa na dokawa da sauri-sauri, dan da gaske fa yanada kishi mai zafi, bai fahimci hakan ba kuwa sai a yanzu ɗin nan dan idanunsa har ji yake suna masa wani yaji-yaji. Koda ya buɗesu a kanta ita kanta sai da taji razani ya shigeta, dan cikin ƙanƙanin lokaci sun yi wani irin kaɗawa da canja launi, baice komai ba ya tako inda taken tsaye ya duƙa ya ɗauka hijjab ɗin ya warware ya saka mata. Su dai su Ahmad da sun riga da sun shigo basarwa sukayi, sai kuma ita Lulu a wautarta ganin ran Smart ya ɓaci sai tai niyyar sake ƙular da shi. Sai da ta saci kallonsa ta gefen ido sannan ta juya gasu Ahmad tana sakin wani sassanyan murmushi da faɗin, “Sannunku da zuwa, ni ai da har zan fara fushi”. Ahmad bai kawo komai a ransa ba tunda dama sun san juna da jimawa sai dai bawani mu'amala ke tsakaninsu ba mai ƙarfi dan Lulu fa ita da maza zira'i maitan ne. Shima murmushi yayi yana kaiwa zaune da faɗin, “Yauwa amarya. Ya kuke ya gajiyar biki? Duk da dai naga angon naki shi tun ɗazun”. Sai da ta sake satar kallon Smart ta ga yanda yay kicin-kicin da fuska ya kuma ƙi zama sai ta sake sakin murmushin da bama Ahmad amsa da “Gajiya kam tabi jiki, kuma ya taku gajiyar? Ya su Uncle Hameed”.
“Alhmdllh, Yaya kuma shima lafiya ƙalau yake”.
Kanta kawai ta jinjina, ta juya ga Faisal shima ta gaishesa sannan ta nufi kitchen tana dariya a ƙasan ranta. Ruwa da lemo ta ɗibo da kayan cin-cin, babu jimawa sai gata ta dawo ta ajiye gabansu. Yanzu kam Smart ya zauna, sai dai kansa a duƙe yana latsa waya. Komawa tai ta zauna itama tana ɗan murmushin santin da su Ahmad keyi na dubulan. Shi dai gogan kamar ruwa ya cinyesa a falon. Sai da ƙyar yay controlling kansa kodan Faisal dan ta Ahmad mai sauƙi ne zai iya fahimtarsa. Sai dai murmushin Lulu sukar masa zuciya yake kishi na sake riƙe masa maƙoshi. Haka dai ya danne har suka miƙe, kayayyakinta suka shigo mata da su sannan sukai mata sallama ita kuma ta basu kayan garar data juye musu a leda kowa da nasa ta ƙaro ma sannan ta zuba wanda za'a kaima Aunty Khadijah matar Abdull-Hameed (Coach) dan suna ɗasawa sosai itama kasancewar akwai ƙawance mai ƙarfi tsakaninta da Aunty Saliha. Suna fita ta koma ta zauna tana dariyar jin daɗin ƙular da Smart da tayi. Jinta take rai fess ita kam. A haka ya dawo ya sameta. Zama kawai yay baice mata komai ba dan a yanzu idan har yay magana ɓacin ransa ne zai bayyana a fili, dan haka yafi zaɓar zama shiru har zuciyarsa ta ɗan sassauta masa sannan ya tura mata ledar da wayoyinta ke ciki ya miƙe yabar wajen. Nanma da kallo ta bisa cikin taɓe baki kafin taja ledar ta buɗe. Sosai taji farin cikin ganin wayoyinta da laptop, cike da jin daɗi ta ɗauka tai bedroom domin saka caji dan duk sun mutu ba caji. Ga cajojin duk suna hanunta.....
Kiran sallar magrib ya fiddosa a ɗakinsa, ya ɗan zubama kayan da su Ahmad suka shigo da shi ido dan suna nan a inda suka ajiye, iska ya furzar batare da yace komai ba ya kwashe su ya fara shiga da su bedroom ɗin nata. Zaune take da laptop data jona a caji gabanta, tun ɗagowar farko da tai suka haɗa ido ta maida bata sake ɗagowa ba har ya kammala shigowa da kayan. Babu alamar wasa tattare da shi ya ce, “Bakiji an kira salla bane?”.
Tsayawa tai da ga danna laptop ɗin sai dai bata ɗago ta kallesa ba. Amma ta tsuke fuska alamar jira take yace kule tace cass. Takowa yay gabanta a hankali ya rufe laptop ɗin ya tura gefe. Dole ta ɗago yanzun kam ta dubesa da iyakar duk wani ƙarfi dan nuna masa yana shiga mata hanci fa. Kallon tsakkiyar ido sukema juna kowa da abinda zuciyarsa ke ayyana masa, dan ta gagara faɗar abinda tai niyyar da farko. Ita ta fara janyewa cikin taɓe baki. Sai kuma ta miƙe batare data tanka masa ba ta nufi toilet. Bayanta yabi dan yanzun ma yana son tai al'ala a gabansa kamar ɗazun, kasancewar shi yana da ita sai ya tsaya yana kallonta, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ganin tayi kamar yanda ya nuna matan ɗazun, sai yaji kuma nauyin da zuciyarsa yayi ya ragu, dan har cikin ransa yaji ta burgesa, in dai har haka take da saurin fahimta da ɗaukar abu komai zai zo da sauƙi kenan, kafin dai tayin ne yake ganin zasu dinga kai ruwa rana.
A karan farko ya ja musu jam'i yau, abi mafi sakata sake nutsuwa a wannan jam'i yanda Smart ke raira karatun Alkur'ani a nutse da fitar sauti nagartacce. Bayan sun idar cikin fuskewa tai yunƙurin miƙewa domin bar masa wajen amma sai ya hana hakan ta hanyar riƙo mata hannu. Hannun ta kalla sannan ta ɗago fararen idanunta ta zuba masa. Shima ɗin dai ita yake kallo dan haka suka zubama juna ido kowanne najin idon ɗan uwansa na ratsashi har tsakkiyar ruhinsa. Da ƙyar Smart ya iya aro jarumta da ga cikin ɗunbin ƙwarin gwiwar sa cikin fitar sauti ƙasa-ƙasa ya furta, “Inada kishi! Inada kishi mai zafi! Inada kishi mai tsanani Mawaddat. Wannan gaskiya ce da nake gaya miki ita danki haddace a cikin muhimman abubuwanki ki kuma kiyaye saboda gudun randa zaki iya tabbatar da ainahina akan wannan kalmar. Komai zan iya ɗauka, idan nace komai ina nufin komai amma banda kasa riƙe kanki ko killace kanki ga wanina koda kuwa uwa ɗaya uba ɗaya suka haifemu da shi. Ki cigaba da sanin *_SMART_* kawai, idan kika ce *_ALIYU HYDAR_* ki ke son gani a zahirance, to fa tabbas wasan zai iya canjawa da ga duk yanda kike iya tunanin ko kwallonsa a tsarin zuciyarki. Duk abinda kikaji nace bana so to da gaske bana sonsa, idan kuma bana son abu bana iya dogon kawaici a kansa game da ɗaukar hukunci mai tsauri. Idan har kina son cigaba da gudanar da duk abinda kika fara da ga gidanku cikin salama to ki kiyaye....”
Rikitaccen abinda ta hango a tsakkiyar idanunsa mai kama da guguwar hayaƙin turnuƙun yaƙi ya sata kasa iya maida murtani. Ba wai ta fahimci ainahin curarrun kalamansa bane ba a yanda shi yake son ta fahimta ɗin, a salon da yay maganar ne kawai ke son tilasta fassara mata su. Ba'a komai take garaje ba musamman maida murtani, dan haka ta shanye kamar komai bai mata zafi ba dan tana buƙatar fashin baƙi kafin ta maida raddi, dan haka kanta tsaye batare data janye idanunta da ga cikin nasa ba duk da hakan na cutar da ita ta ce, “Ka gama?”.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments