Furar Danko 66




 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣6️⃣




........Ya samu su Ahmad na jiransa a ƙofar gida shi da wani cousin brother ɗinsa babban fan ɗin Smart akan ball, da yake kusan sa'ansu ne shima sai suke zumunci sosai duk da shi Smart ɗin yana jajja baya kamar yanda halayyarsa take na rashin sakewa da mutane. Ko Faisal yayi fushi sai kuma ya dawo dan matuƙa Smart ke burgesa a filin ƙwallo, damma ƙaddara ta hana komai gudu ai da yasan yanzu Smart na cikin manyan ƴan ƙwallo da Nigeria ke alfahari da su. Sun gaisa tare da zolayarsa irin na abokai musamman ma Ahmad da ya tasashi gaba sosai kafin su wuce Smart na roƙama Ahmad shiriya. Gidan Daddy suka fara zuwa. Inda suka sami tarba ta musamman da ga Mommy da su twins da basu koma ba. Bayan sun gaisa da Mommy sukai godiya tai musu iso falon Daddy da ya riga yasan da zuwansu. Ya ɗan sake musu fuska harda jansu da hira duk da sunata faman sinne kai musamman ma Smart. Dan koda aka kawo musu abin sha da ruwa da kayan motsa baki Faisal da Ahmad ne kawai suka sha ruwa. Shiko babu abinda ya taɓa. Wasa-wasa sun share kusan awa ɗaya da rabi kafin su baro gidan da wasu kayayyakin Lulu da Mommy ta saka Mubeen kai musu akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kimu za'a kai mata sauran kayan. Da ga nan gidan Uncle Yousuf suka nufa. Anan ɗin ma dai tarba suka samu ta girmamawa ga Aunty Saliha. Uncle Yousuf kuwa babu ruwansa zama yay cikinsu tamkar aboki tunda su duka ukun babu baƙonsa, gara garama Smart ɗin, amma su Ahmad ai tun suna dajinen majina ya sansu. Anan ma sun jima dan har sai da aka kira sallar la'asar sannan suka fito tare da Uncle Yousuf ɗin zuwa massalaci. Bayan sun dawo basu shiga ciki ba sai mota tunda dama sunyi sallama da Aunty Saliha. Anan ma dai an bada wasu kayan Lulu da wayoyinta da laptop da Uncle Yousuf ya amshe. Bayan sun baro nan Smart yace ma Ahmad yana son zaije yaga Malam tunda zuwa gidan Baba da sukai niyya ya rushe sakamakon sanar dasu Baba yayi tafiya Legos da Uncle Yousuf yayi. Ahmad yace babu damuwa. Sun nufi Yakasai wajen Malam Nasirudden. Sunyi sa'ar samunsa kuwa a gida bai fita ba. Bayan sun gaisa Ahmad ya janyo Faisal cikin dabara suka fito suka bar Smart tare da malam ɗin.

          Malam Nasirudden da ya fahimci akwai magana ya dubi Smart cikin murmushi da kulawa ya ce, “Idon Aliyu ango ne haka a waje, kai da ya kamata ace kana can gida sai bayan wata ɗaya ka fito”.

       Murmushi mai bayyana hakwara Smart ya saki a karo na farko, cikin sinne kai ya ce, “ALLAH ya gafarta malam idan hakan ta kasance ai kwa zaneni matsayinku na iyaye”. Dariya shima malam yayi da faɗin, “Ina ai idan hakan ta faru mun san lafiya ce ta ɓoye ka ai Malam Aliyu. Ya amarya da gajiyar biki?”.

            “Alhamdullah Malam”.

       “To Masha ALLAH, ince dai ba jikin bane ba ko?”.

“A'a malam jiki kam Alhmdllh, dan duk yau banji ciwon kan nan ba. Wani abu ne mai muhimmanci ya kawo ni dan ina buƙatar ƙarin haske da shawara”.

     “To Alhmdllh ALLAH ya ƙara lafiya mai albarka. Ina saurarenka mike tafe da kai?”.

    Zama Smart ya gyara yana sauke ajiyar zuciya da furzar da iskar bakinsa. “Malam akan ita matar tawa ne nake neman shawara. Kasan yanda al'amuran rayuwar nan suke tafiya a wannan lokaci musamman tarbiyya da ke neman zama wani babban ginshiƙi mai wahalar aiwatarwa ga iyaye ko riƙewa ga mu ƴaƴan, wasu zakaga iyayen nata iya bakin ƙoƙarinsu amma sai su fuskanci jarabawa a cikin ƴaƴan wasu su fanɗare, ko kaga tun fil'azal iyayen ne ma basu bi hanyoyin isar da tarbiyyar yanda ya kamata ba saboda soyayyar yaran. Wannan matsalar tana matuƙar tasiri akan addini da wasu ɗabi'un da takai a yanzu hatta ɗiyanmu mata na shaye-shayen abubuwan mayen nan a cikin gidajen iyayensu ko a gidan aure. Wasu sanadin abokai, wasu samari, wasu kuwa wani daliline kan jasu zuwa hakan. Karna jaka da nisa, ita matar tawa ta tsinta kanta a irin wannan halinne, sannan ba shaye-shaye ne kawai matsalar ba, hatta a ɓangaren ibada tana da matuƙar raunin da zan iya cemaka komai ma bata sani ba, saboda koda tasan wani to babban dalilai ya shafesu da ɓoye abinda ta sani ɗin. Kaina gaba ɗaya a cikinkushe yake yinin yau ka bani shawara dan ALLAH, dan ko mahaifana bana son su fuskanci wannan matsalar game da ita balle sauran ahalina saboda bana son mutuncinta ya samu rauni ko yaya a zukatansu”.

        Numfashi mai nauyi Malam ya sauke yana mai jinjina kansa. “Tabbas kai ɗan halak ne Aliyu, sannan ka matuƙar birgeni na kuma sake ganin kimarka a cikin idanuna. Domin ba kowa ALLAH ke azurtawa da irin zuciyarka ba a wannan ƙarnin. A koda yaushe, a ko wane irin kuskure mutanenmu sukan dubi mai wannan akin abin ƙyama, abin hantara, abin gudu, abin zinɗe, abin shune, a tunaninsu suma wayonsu ne ya hanesu da aikatawar ko ya hani nasu zuri'ar. Muna mantawa itafa rayuwar tamu gaba ɗayanta ma jarabawace, ba kuma lallai ne abinda ya kasance jarabawar waninka kai ya kasance taka ba. A duk sanda kaga gazawa ga wanin ka ba dandalin gulmarsa ya dace ka buɗe ba, da zunɗensa ko shunensa ya dace kayi ba idan zai gifta, ba ƙyamatarsa ya dace kayi ba ko hantara. Nema masa shiriyar UBANGIJI ya cancanta da tausasa masa a duk lokacin da rayuwarsa ta raɓi taka ko wani dalili. Wlhy Aliyu mutane da yawa sukan kasa gane cewar bakunansu ko ayyukansu ke jefa musu ƴaƴa cikin wata musifar. Zakaga kana iya bakin ƙoƙarin ka akan tarbiyyar yaranka, ALLAH kuma ya baka su nutsatstsu da ilimi yanda ya kamata, amma dare ɗaya yaro ya canja alƙiblarsa ka rasa daga ina matsalar take. Matsalar tana a tare da kai, bakinka shine matsalarka, ayyukanka sune matsalarka. Ɗan wancan dake famɗare ya gitta ka zunɗeshi da bama abokan zamanka labarin ai wancan yaron da kuke gani gagararrene, watsatstsene fanɗararre, baida aiki sai shaye-shaye, baida aiki sai bin ɗiyan mutane, baida aiki sai ɗauke-ɗauke. Ciki ta zubar babu adadi bar ganinta a cikin hijjab ɗin can karuwar gida ce, jibi yarinyar can babu abinda ta iya sai shigar banza, ta kwaile fata da bilicin ƴar isaka tafi ƙarfin iyayenta. Laifin uwarne ko ubanne basu bashi ko bata tarbiyya ba..... Waya gaya maka tsaiwarka akan tarbiyyar yaro ce kawai ke tsare maka shi ɗan uwana ko ƴar uwata? Muna mantawa akwai jarabawa, muna mantawa akwai ƙaddara, muna mantawa ƙyaƙyƙyawan furucinmu ga ɗiyan wasu kanyi tasiri ga namu ɗiyan, mummuna kanyi tasiri ga namu ɗiyan suma. A duk fa lokacin da ka ambaci ALLAH yayima wane albarka, ya shiryar da shi, sai kaima mala'iku suce Amin tare da kai da zuri'arka baki ɗaya. Idan kace ALLAH ya wadaran wane fanɗararre taƙadari ɗan iska, sai mala'iku su amsa da Amin tare da kai da zuri'arka baki ɗaya. To ashema yima wani ƙyaƙyƙyawar addu'a ko furuci tamkar kanka kayimawa kenan ko, shiyyasa nace maka harsunanmu sune manyan linzaman da suka zame mana masifu a wannan zamanin bakwai tarbiyyar bace kawai ta suɓuce mana. Da an taɓamu muce zamani, babu babban zamani sama da harsunanmu. Iyayenmu na baya da wahala kaga majalisar aibanta ɗiyan mutane, da wahala kaga wani ya zauna zinɗen yara marasa ji, idan yaga yaro yayi ba daidaiba zai hukuntashi batare da sanin iyayensa ba koya tsawatar masa ko ya masa nasiha. Amma a wannan ƙarnin sai dai mu koma gefe muna dariya ko yin ALLAH wadarai akan abinda munada damar gyarawa ko ambaton shiriyar ALLAH wa wannan yaron kuma tai tasiri garesa. Wani kuma zakaga a gefe sana'arsa itace saida kayan laifi ko wani mummunan abu dake ɓata tarbiyyar yara, shiyyasa sai UBANGIJI ya dawo da mummunan aikinsa wa zuri'ar tasa danta zame masa izina idan zai gane. Abinda kayi na yarda da auren yarinyar nan da ƙudurta gyara mata rayuwa batare da ƙyamata ba da ace haka muka dageyi a cikin al'ummar mu da an samu sauƙin yawaitar lalacewar yaranmu matuƙa. Domin duk wanda ya taimaki wani domin tsamosa daga wata halakar rayuwar duniya data lahira, shima UBANGIJI zai tsamesa da ga wasu masifu ya kuma tsame zuri'arsa ta inda bai zato ko tsammani ba. ALLAH yay maka albarka, ya ƙara mana yawaitar irinku acikin al'ummar mu. Dan irin waɗan nan yaran jawosu a jiki da haƙuri da yanayinsu ya dace muyi mu kuma maida hankali wajen fuskantar minene matsalolinsu. Kaifa abinda kake kallo ba dalili ba, wani a wajensa gagarumin dalilaine da zai iya tarwatsa masa rayuwa. In sha ALLAHU zakai nasara, wataran ba al'umma ba kai kanka sai kayi alfahari da jihadin da kayi da kuma kasancewarta iyalinka. Abu na farko da zakayi shine janta a jiki, karka ƙyamaci halin da take ciki, ka fuskanceta da ƙyau wajen gano minene ainahin abinda ya jefa rayuwarta a wannan yanayin dan na tabbata tanada ƙyawawan halaye itama da fuskantar ta ne zai bayyanar da su, sannan ka dage da addu'a, yin sadaka da ƙyautata mata, ka fuskanci abinda tafi so ka dinga jan ra'ayinta ga shi. Sai kuma ka ɗan dinga yin zafi kaɗan a wasu al'amuran dan irinsu zaka samesu da taurin zuciya da ƙin gane al'amura da wuri, dole idan ka hura wataran sai ka tauna, dan sai ka ɗauki matsayin miji ne wataran, wataran uba, wataran yaya, wataran abokin, wataran ƙani, wataran ma ɗa, haka zaka dinga canja mata kamar hawainiya dan yanda mata kance maza kamar yarane yanda ka renesu haka suke kasancewa, itama mace kamar gold ce, idan ka iya zama da ita ta yanda kaso kake sarrafata da adon da kake buƙata a idon duk wanda zai kalleta. Na ƙarshe shine haƙuri, dole sai kayi matuƙar haƙuri da zama mai juriya, dan wani lokacin zakaga kana tufkane kamar tana warwarewa, kada ka damu sai a hankali ɗabi'ar zata barta dan ta riga ta shigeta sosai ta yanda wannan abunne kawai ke sakata farin ciki da ƙarfafa ta saboda shi take kallo a matsayin dai-dai tunda a haka ta tashi taga kanta. Dolene kasa ido sosai a dukkan motsinta, ma'ana ka zama mai ankarewa akan ƙawayenta da abokan huɗɗarta danka janyeta daga irinta a cikinsu. Sannan fa saika shirya kawo mata wani abu mai ƙyau da idan kana yaƙin rabata da wancan ya zam kana cusa mata wannan, kasan kuskuren da mutanenmu keyi shine, kaita yaƙin cirema mutum halayen gurɓatattu amma baka bashi madadin abinda zai maye gurbinsa da shi ba, tayaya kake tunanin bazai koma ruwa ba. Sai kuma fahimtar da ita addininta, shine babban abinda zai iya tankwara maka ita cikin sauƙi ma fiye da komai. ALLAH yay riƙo da hannayenka kai da ire-iren ka game da irin wannan sadaukarwar. ALLAH ya sakakanka muku da sakamakon alkairi ku da zuri'arku a duniya da lahira da duk ma wanda zai iya koda tausasa harshene akan kuskuren wani.”

        “Amin malam nagode sosai ALLAH ya saka da alkairi ya ƙara tsahon rai mai albarka. In sha ALLAH zanyi aiki da shawarar ka dan naji daɗinsu na kuma sake samun hasken da nake buƙata.”

       Murmushi malam ya sake yi yana tattaro littatafai daga cikin tarin wanda ke a ɗakin nasa. Sai da ya kammala ya juyi ga Smart. “Ga waɗan nan kaje da su ka fara koyar da ita, ina dai fatan kanada karatu mai zurfi game da addininka?”.

           “Alhmdllh akwai gwargwadon iko, a yanzu haka ma kuma ban daina nan ilimi ba ina zuwa islamiyya Sheikh Aliyu Abdur-ra'uff Maina (MUTUM DA DUNIYARSA) kafin abubuwa su taɓarɓare ne na dakata gaskiya, amma in sha ALLAH ina kan shirye-shiryen komawa na cigaba”.

      “Masha ALLAH kayi ƙyan kai kuwa, Ai Sheikh Aliyu Maina mutumin kirki kuma aminina ne sosai, kaga idan kunyi nisa ka fahimci ta fara tankwaruwa zaka iya sakata Islamiyyar da matansa ke jagoranta suma Malam Jiddah da Malam Maimunatu”.

          “In sha ALLAHU zanyi hakan malam”.

     Sun ɗan ƙara tattaunawa sannan Smart yay masa sallama ya fito saboda su Ahmad dake jiransa. Ya samu sunata hirarsu da ɗaliban malam, amma duk da haka saida ya basu haƙuri sannan suka wuce yana jin zuciyarsa sakayau ba kamar daren jiya zuwa safiyar yau da yake cikin damuwa ba akan lamarin Lulu. Sai kusan shida suka iso Sharaɗa, Smart ya fita ya buɗe musu gate suka shiga har ciki. Suna sauke kayanta da suka taho da shi ya zare jikinsa ya shiga ciki dan fara duba yanayin shigarta kafin su Ahmad ɗin su shiga........✍️


     


_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments