Furar Danko 63

 




𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲


  🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗




           𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻



𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 6️⃣3️⃣




.......A ɓangaren Smart kam suna isa gidan sashen Abba ya nufa domin gaidasa, yayinda Huwaila ta shige ciki fuuu tana ƙunƙuni. A falo ta iske Umma zaune suna karin kumallo da sauran ƴan uwanta da ƴaƴansu da duk ke shirin wucewa gida a yau tunda biki dai ya tashi. Umma ta bita da kallo kamar a firgice, sai dai kasancewar bata son tace wani abu a gaban sauran yaran ya sata ƙyafta mata ido ta cigaba da cin abincinta. Amma Huwaila sai ta dinga ƙunƙuni, da ga ƙarshe dai ta fara bama ƴan uwanta labarin ƙarya da gaskiya akan wai an mata wulaƙanci a gidan Smart, sun shige ɗaki sun barta, yanzu kuma yace Asma'u ta zauna can ita kuma ya taso ƙeyarta sun dawo. Da yawansu sun hau sun zauna. Sai Ismaha ce dai ta ce, “Humm Huwaila gaskiya ban yarda ba. Koda ace hakan da kika faɗa ma ta faru sai dai idan yanada manufarsa, kowa dai yasan Yaya Hydar a gidan nan kan rashin nuna bambanci a tsakaninmu da ƴan ɗakinsu. Da dai Yaya Salim kikace yayi hakan ko musa miki bazanyi ba...” tana gama faɗa ta tashi tai ficewarta. Cikin ƙanƙanin lokaci falon ya kaure da ka-ce-na-ce, kowa na faɗin albarkacin bakinsa. Da wannan damar Umma da hankalinta sam ba'a jikinta yake ba ta miƙe tana kama hannun Huwaila suka shige uwar ɗaka.

        “K lafiya? Ina abinda na aikeki yi na ganki hannu rabbana”.

    “To Umma ya kike so ki ganni, a gabanki fa na faɗi irin wulaƙanci da akai min a gidan can”.

    “Ke tafi can wawuyar banza da wofi, kin ko san muhimmancin abinda na turaki yi da zaki dawo min da wani shirmenki na banza. Wai ke ko Huwaila yaushe ne zakiyi hankali a rayuwarki. Ƙanwar-ƙanwarki Asma'u har ta fiki wayo amma ke gallaƙeƙiyar budurwa da ake shirinma aure baki son ciwon uwarki ba....”

           “To wai ni Umma ya kike so nayi dan ALLAH. Ni Wlhy ko ƙyallin wani kayan da suka saka jiya suka cire ban wani gani ba a gidan. Tunda kina ganin banyi miki ƙoƙari ba sai kije da kanki ai”. Tana gama faɗa tai waje abinta. Duk irin kiran da Umman ke ƙwala mata ko waiwayenta batai ba. Sai ma jiyo muryar Smart da tai alamar ya shigo gaishe ta. Sai dai yanda taji ƴaƴan nata na gaishesa a gatsine ya sata fita wuff dan taga suna neman ɓata mata shiri, saboda Malam Na-zuru ya jaddada mata a waya ɗazun da safe sai fa ta rage nuna abinda ke ranta a garesu, musamman ma matar tasa tai duk yanda zatayi ta shiga jikin yarinyar hakanne zai sakasu cin nasara cikin sauƙi. Cike da fara'a ta amsa gaisuwar da Smart ke mata tana tambayar ya baƙuntar sabon waje da amarya. Kansa a ƙasa cikin jin nauyi da girmamawa ya ce “Lafiya Lau tana gaishe ku”. 

      “To madalla ALLAH yay muku albarka. Kamayi ƙoƙari ai da ka fito tunda safe haka banyi zaton yau zamuga idonka ba a gidan nan kwata-kwata.”

     Shi dai murmushi kawai yay yana miƙewa batare da ya bata amsa ba ya fice abinsa. Sashen Ammah ya shiga dan ya gaisa da mama da Aunty Amarya. Nan ma dai zama yay suna gaisawa da dangin mahaifiyarsa da ke ta jansa da kiransa babansu babansu. Daga haka suka sake ɗora masa da nasiha mai ratsa jiki tare da addu'oin zaman lafiya mai ɗorawa da zuri'a mai albarka. Bai jima ba sosai Adda Suwaiba tace ya tashi yaje yabar matarsa dan ma Asma'u nacan. Daga haka yay musu sallama ya fito bayan sun ɗanyi magana da Ammah a gefe ya kawo kuɗin jikinsa na gudunmawa da ya ɗan sassamu ya bata akan ta basu suyi kuɗin mota. Daga haka ya juya ya tafi akan zuwa anjima zai dawo kafin su tafi gidan su Lulu godiya ta al'ada da ango kanje da abokansa gidan dangin amarya washe garin tashin biki.....


      Har lokacin da ya shigo gidan Lulu na zaune tana tsakurar abincin nan, yayinda Asma'u ke ƙarasa saka turaren ruwa a carpet ɗin falon da labuloli. Ɗaga kai kawai tai ta kallesa ta maida kan abincinta batare data amsa masa sallamar ba. Sai Asma'u ce ta amsa tana masa sannu da zuwa cikin girmamawa. Amsa mata yay da kansa kawai. Da yake hankalinta ba'a kansu yake ba ita bama ta lura Lulu bata amsa masa sallama ba. Ta kammala ta maida turaren a inda ta ɗauka Lulun na mata sannu cikin murmushi. Ta gefen ido yake kallonta da mamakin yanda take sakema Asma'un. Baki ya ɗan taɓe batare da ya kalla Asma'un ba ya ce, “K zoki bani abincin nan na karya”. Amsa masa tai da to Yaya, sannan ta nufi kitchen ɗin ɗakko masa plate kamar yanda ta ɗakkoma Lulu ɗazun. Sai lokacin ya dubi Lulun a kaikaice, cikin deep voice ɗin nan tashi a dakensa ya ce, “Ke baki iya amsa sallama ba balle sannu da zuwa ko, amma kin iya tasa abinci kina ci”.

       “Sauƙin ma bakai ka bani ba balle kamun gori shishshigi master”. Ta faɗa tana balla masa harara. Lips ɗin ta dake motsawa a hankali yabi da kallo, sai kuma ya ɗan cije nasa da ɗauke kansa yana jin wata irin kasala na sake saukar masa fiye data barcin da yake ji. Bai sake magana ba saboda fitowar Asma'u, ta jawo basket ɗin gabansa tana buɗe kulolin da faɗin, “Yaya mizan zuba maka bayan kunu dan nasan dai shikam ba canji”. Ƙaramar hararar data sata saki siririyar dariya ya sakamar mata, sai kuma ya nuna mata yam balls ɗin da faɗin, “Karki sakama kunun komai”. Da to ta amsa masa, sannan ta zuba komai yanda ya kamata kuma dai-dai adadin da tasan zai cinye dan shima yam balls ɗin ma masoyinsa ne. Lulu da ke satar kallon abincin ta gefen ido ta ce, “Hu'umm kuma duk cinyesa zakayi?”. Yanda tai maganar da ɗan waro Luluu eyes ɗinta waje tana riƙe haɓa ya bama Asma'u dariya, sai dai ta danneta da ƙyar ta tashi ta fice da ga falon gaba ɗaya taje waje tai abarta son rai.  

       Smart ya ɗan laɓe baki batare da ya kalleta ba ya fara cin abincinsa da faɗin, “Mi kike tsoro ne a cikin cin abincin nawa? Kina gudun kar ki gagara ɗaukata ne?” ya ƙare maganar da ɗago idanunsa da take kira na macizai ya zuba mata su. Baki ta taɓe cikin masa kallo mai kama da harara ta ce, “Kamar ya? Miya shafen da nauyinka?”.

      A karan farko ya saki wani makirin murmushin da aduk sanda yayisa yake tunzurata dan tafi kwallonsa a murmushin rainin hankali ya cigaba da cin abincinsa. Siririn tsaki taja da ɗauke kanta itama ta cigaba da shan romon farfesun da yaci ace tama manta ta gama ci. Amma ina gayu da yanayinta yasa anata tsakurarsa, ga shi yamata daɗi matuƙa ta yanda ta gagara ajiyesa. Duk da yaji tsakin nata bai sake yin magana ba ya maida hankalinsa ga cin abincin harya kammala zai tashi, sai lokacinne itama take kammalawar. Asma'u ya ƙwalama kira, ta amsa da ga waje dan ta gama zagaye gidan ne tana jin daɗin kallon flowers ɗin da aka ƙawatashi da su. “Zoki wuce gida” ya faɗa yana miƙa mata ɗari biyu. Lulu Asma'u ta kalla cikin shagwaɓe fuska, itama Lulun shi take kallo, ta ce, “Kamarya tazo ta tafi? Nan fa zata kwana”. Yanda take maganar itama kamar a shagwaɓa-shagwaɓa ya sashi kallonta. Sai kuma ya ce, “A ina ɗin zata kwana? No karma ku fara abinda bazaku iya ƙara sawa ba, common Malama ɗakko hijjab ɗinki ki wuce gida, wannan abincin ki tafi da shi a bama wani dan nan dai bacinsa za'ai ba”. Da ga haka yay wucewarsa hanyar bedroom. Sum-sum Asma'u ta nufi kwanikan da suka kammala cin abincin ta tattara zata kai kitchen sannan tazo ta wuce dan tasan shifa baya magana sau biyu. Takaicin wannan nuna isar tasa ya saka Lulu miƙewa a fusace tabi bayansa. Burumm ta shigo ɗakin dai-dai ya zare rigarsa zai cire wandon, amma sai ya dakata ya tsaya kallonta.

      “Malam wai kai miyasa kake son dinga juya mutanene kamar wasu ƴaƴanka?”.

      Kallonta kawai yake yi batare da yace komai ba. Aiko sai ta sake fusata da takaicinsa ta ce, “To babu inda zataje”.

         “Idan kece sama da ni kenan”. 

      Ya faɗa yana ƙara tsatstsareta da idanu. Itama a tsiwace ta ce, “Oh da mika ɗauki kanka?”. Karo na biyu ya saki murmushi, dan shi kam ƙarfin halinta tunba yanzu ba dariya ma yake bashi. A hankali ya tako zuwa gabanta daf, ta wani yamutsa fuska tare da matsawa baya tana hararsa, sake matsawa yay shima ta matsa itama, shima ya bitan dai, a masife ta ce, “Miye haka wai?”. 

      “Ina son nuna miki abinda na ɗauki kaina ɗin ne Madam” yay maganar dai-dai suna danganewa da bango idanunsa cikin nata. Yanda suke daf-daf ga hannunsa da ya tokare a bangon ya bashi damar dabaibaye ta da ƙyau har tanajin numfashi na neman mata wahalar shaƙa dan in ma ta shaƙa ɗin ƙamshinsa ne iskar da kawai take iya zuƙowa ya sata faɗin, “Aliyu bana son iskanci da raini fa. Dalla matsa min”..

            “Haba Madam! K bakiji kunyar faɗar sunan ba haka gatsal sunan mijinki ne fa”. Yay maganar da sake ranƙwafowa yay mata rumfa ta yanda jikinta ke neman fara rawa. Amma sai ta dake dan bata yarda itafa yaga gazawarta ba. Hannu tasa ta turashi amma ko gezau, sai ma wani lumshe idanun da yay ya sauke akan hannayen nata da ke a saman jikinsa. Da sauri ta janye tana jan tsaki da faɗin, “In ma abinda banzan zuciyarka ke faɗa maka kenan to ka goge, dan tamkar kana mafarki ne a gaɓar da ake gab da tashinka da ruwan sanyi, wannan auren baida maraba da wasan drama ɗan son banza phone store”.

      Idanunsa ya lumshe da buɗewa a lokaci guda yana cafko hanunta dan shirin duƙewa take tabar wajen. “Haba Madam ya kuma zaki wuce ban nuna miki abinda na ɗauki kan nawa ba?”.

          “Aliyu!!”.

     Ta sake faɗa da ƴar tsawar takaicin kiranta Madam da yake yi dana goga jikinsa a nata. 

       “Uhmm Madam”.

   Ya amsa mata da wata irin kasalalliyar muryar son sake ƙular da ita yana sake kusanta fuskarsa gab-gab.........✍️




_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_


*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*


FURAR DANKO

Billyn Abdul


-ZAFIN KAI

Mamuhgee


-TABARMAR ‘KASHI

Safiyya Huguma


-BAKON MUNAFIKI

Miss xoxo


Duka hudu 1k

Uku 800

Biyu 600

Daya 400


Pay at👇


1487616276 

Access Bank

Bilkisa Ibrahim Musa

Sai katura shedar biyanka anan👇


09032345899


Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇

09033181070



*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


*THANKS FOR CHOOSING US*🥰


Zafafa🫶🔥




*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*

No comments