Furar Danko 50
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
🫗 𝙁𝙐𝙍𝘼𝙍 𝘿𝘼𝙉𝙆'𝙊.....!!🫗
𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻
𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 5️⃣0️⃣
........Idanunsa da ke lumshe ya buɗe a hankali ya saukesu akan wayarsa da ke ruri. Har wayar ta kusa tsinkewa yana kallon number da ake kiran nasa da ita, sai kuma yay murmushi yana mai cije gefen lip ɗinsa da ɗaukar wayar ya sa a hansfree tare da maida idanunsa ya lumshe, cikin nutsuwarsa da deep voice ɗin nan ya ce, “Assalamu alaikum. Ina magana da waye?”.
Alh. Sulaiman da ke huci da ga can ya ji wani irin takaici ya sake maƙure masa maƙoshi. A kausashe ya ce, “Da ubanka ne. Kai har kai ne zan kira ka ce min da waye?”.
Murmushi Smart ya saki mai bayyana sautin da har ya shiga cikin kunnen Alh. Sulaiman. Babu alamar ɗar a tare da shi ya ce, “Yes kaima uba ne kam. Dan koba komai na auri ɗiyar Sister ɗin ka. Uncle ina yini. Nafa gode da ƙyauta ALLAH ya saka da alkairinsa, insha ALLAH nan da wata tara zakuga tukuycin jika maybe ma sunanka zai ci. Sai dai bazanyi fatan ya gadoka ba, mai asalin sunan nake son ya gada da ƙyawawan halayensa nagartattu....”
“Yaro baka san wuta ba sai ka taka. Kana tunanin kai har karanka ya kai tsaiko kenan? Da har zan baka aiki ka koma gefe da tunanin cin dunduniyata! Wlhy ba kai ba hatta ahalinka sai sunyi nadamar kasancewarka a cikinsu. Ni Alh. Sulaiman Sufi Ado Garko sai na maida rayuwarka abar kwatancen da ko faɗar sunanka akai sai an tofar da yawu....”
Wata shashashar dariyar rainin wayo Smart ya saki cikin katsesa ya ce, “Da ace alƙalamin ƙaddarata a hannunka ya ke da tun kafin yau na kasance a ƙarƙashin inuwar tsoron cika bakinka. Sai dai kash kai baka isa ko dakatar da kaɗawar daƙiƙa ba na cikin ƙaddarata. Aliyu M. Idris Mawashi UBANGIJINSA kaɗai yake tsoro ba ɗan adam irinsa mai kashi da barci ba. Amma zan baka shawara idan ka shirya ka koma ka canja shiri, idan kuma baka fara ba ka ƙaro matakan shirin naka dan da kura kawai ake wasa a cikin kasuwa ZAKI sai kallo da ga nesa dan ko shafar jikinsa sai da dabara. Kamar yanda na faɗa maka nafi ƙarfinka kuma ni ba'amun barazana. Dan haka shawara ɗaya da zan baka ka goge tarihin alaƙar data taɓa alaƙantani da kai a baya, ka ɗauki sabuwar alaƙar zamantowarka suruki na sai mu amfana da tagomashi mutunta juna. Idan kuma ka ce a'a lallai zan cigaba da gara rayuwarka a tsakkiyar harabar gidan Alhaji Sufi Ado Garko fiye da yanda yara ke gara katantawar wasa a saman suminti. A yanzu bana buƙatar cewarka anan kaje kayi nazari. Na Barka lafiya sai nazo gasheka tare da AMARYAR ƘAMSHI bye Kawu”. Ya yanke wayar ƙittt. Kansa ya dafe yana wani irin furzar da huci a jajjere na ɓacin rai. Hannunsa ya kai saman goshinsa yana murzawa. Shi kam wace irin masifa ce wannan kuma ya shiga. Da ga wannan sai wancan. Sake furzar da iskar yay saboda abinda zuciyarsa ta ayyana masa cewar (Jarabawa ce).
Haukacewa Alhaji Sulaiman ya nema yi jin Smart ya yanke masa waya bayan ya gama yaɓa masa maganganu masu zafi. Cikin wani irin bahagon ɓacin rai ya shiga ƙoƙarin sake kiransa amma ana nuna masa busy alamar yayi blocking ɗinsa ma kenan. Dai-dai nan kiran Hajiya Turai mahaifiyar Tajuddeen ya shigo masa a ɗayar waya. Ɗagawa yay da sauri yana mai kaiwa kunnensa. Sai dai jin kukan data fashe da shi ya sashi zabura har da bugewa “Ke lafiya kuwa zaki ɗagamin hankali haka da kuka?”.
Cikin kuka ta ce Alhaji babu lafiya. Tajuddeen ya farka gashi nan yana aman jini, shike nan zamu rasas......” ai kusan da gudu ma ya fito da ga sashen nasa har yana neman faɗuwa. Ba ƙaramar tsorata maigadi yayi ba. Hakama drivern sa da yaronsa Malami. Da ƙyar ya iya sanar musu “Muje asibiti” ya buɗe gaban motar ta shiga batare da ya jira an buɗe masa ba. Dole suma suka shiga da hanzarinsu....
Tofa Tajuddeen yaya dai? Karfa ciwon son Lulun mu ya kasheka😔🚶.
___________________★★
A ɓangaren su Umma da aminiyarta masu tafiya garin Zuru da ƙyar ta samu Abba ya barta bayan ta lafta masa ƙaryar zuwa garin su duba Innarta, acewarta ƙanwarta tai kiranta da dare ta sanar mata jikin Innarsu ya motsa. Bai kawo komai a ransa ba tunda yasan Innar tasu dama jiyya take kusan shekara huɗu kenan. Ya jajanta mata da bata izninin tafiya dan haka ana sallame sallar asuba taima ƴan gidan sallama ta wuce. Duk da asubancin tafiyar da sukai basu iso garin Zuru ba sai bayan sallar azhar. Burinsu su kammala komai su koma garinsu Umma ɗin a yau su kwana. Sun koyi sa'ar samun Malam Na-zuru a gidan kamar ma su yay zaman jira kasancewar tun kan su taso sunyi kiransa sun sanar masa. Bayan gaisuwa da tambayar juna bayan rabuwa ya dubi Hajiya Naqiba dan ita kam bata rabo da zuwa inda yake har ma ta saba dan ta riga ta gama kama mijinta a hannu a sake take kamar akuyar fulani. Umma kam Abba bai kasance a ƙarƙashin ikon nata ba ɗari bisa ɗari shiyyasa zuwan ke mata wahala kai tsaye sai idan gagarumin abu ne ya faru.
“Hajjaju yau Aminiyar ki ta tuna damu kenan ko? Idan ban manta ba rabonta da nan kusan shekara uku kenan fa”. Cikin ƴar dariya Hajiya Naqiba ta ce, “Gaskiya za'ayi kam malam. Kasan ita akuyar ɗaure ce ganinta sai anyi sake ko tsautsayi ya gifta ta kufce”. Ta ƙare maganar tana kallon Umma. Dariya sukayi gaba ɗaya. Kafin Malam Na-zuru ya tsagaita da maida hankalinsa ga Umma yace, “Hajiya Yaha mike tafe da ke?”.
“Abubuwane da yawa kashi-kashi malam. Sai dai mafi girma a cikinsu aikin yaron nan ne mai shegen taurin kai ya ke neman buɗe min wlhy....”
“Tofa badai yaro mai tamaula ba ko?”.
“Wlhy shi kuwa malam. Dan jiya-jiya aka ɗaura masa aure da ƴar wani hamshaƙin attajiri”.
“Aure kuma? Ya akai haka ta faru Hajiya? Kina ina akai wannan babbar ta'asa bayan kin san da ƙyar muka samu yaron nan ya shiga hannun mu? Wannan kuma yana a cikin babban abinda muka ƙullesa da shi fa”.
“Wlhy malam nima ban san yaya akai hakan ta faru ba. Sai dai na lura tsabar munafunci ne na ubansu ya sa aka rufe mana komai sai ɗaurin aure kawai mukaji bayan an riga an ɗauro. Malam ka taimakeni dan ALLAH. Kai kanka ka sanar min yaron nan yanada taurari masu ƙarfin gaske da zasu iya disashe kaf ƴaƴan gidan nan ya zam babu hasken wanda ake gani sai shi, bayan kai malamai kusan huɗu sun sanar min hakan wasu ma sun kasa aiki a kansa sai kai ne da kayi akaci nasara. Gashi kuwa na fara gani dan aure fa akai masa, kuma da ƴar Alhaji Isma'il Jiƙamshi, wannan abu ya hanani samun barci sam a daren jiya”.
“Tirƙashi! Dolene ki kasa barci. Dan aurensa na ɗaya da ga cikin abinda muka ƙulle masa har sai ya tsufa a haka ta yanda babu mai ɗaukar ƴa ya bashi. Ba ƙaramin duka a ciki mijin nan yay mana ba gaskiya. Dan yaron nan yanada ƙarfin nacin ibada shiyyasa muka jima muna aiki yana tafiya a iska, na ƙarshen nan ma da ƙyar kina gani muka samu ya haushi da taimakon anfani da gashin mahaifansa da nashi.....”
“Na sani Malam, dan ALLAH ka taimakeni wannan aure ya watse kafin ma cikar sati ɗaya na tarewar wannan yarinya. Sannan a matse minsu waje guda su rasa gabas su rasa yamma akan wajen da zai zauna da abinda zasuyi hidimar biki. A sakama duk danginta tsanarsa a zuciya hatta da jaririn yaro. A birkitamin lissafin yarinyar ta ce bata son sa”.
“Aikin nan yana da wahala Yahanasu. Amma dai zaɓi ɗaya anan mu gwada mu gani”. Ya ƙare maganar da ajiye mata tazbaharsa gabanta. Da ƙyar ta iya tsaida nutsuwarta wajen ɗaukar ɗiyan tazbahar ɗaya ta miƙa masa. Amsa yay ya duba ya sake ajiye mata yace ta ɗauka. Sai da sukai haka sau uku sannan ya kalleta cikin jinjina kansa. “Gaskiya akwai babban aiki a gareki. Dan gaba ɗaya fa an riga an lalata aikin sai kaɗan ne bai bar jikinsa ba. Wanda kuma ya ƙulla wannan auren mutum ne mai nasibi matuƙa shima, dan komai yayisa ne da hikima kasancewar ya fahimci akwai ɓoyayyen al'amari akan rayuwar yaron......”
“Kenan babu yanda za'ai malam? Sannan waye shi wannan matsiyacin da ke tare da shi haka ba sani ba tun da wuri?”. Umma ta faɗa kamar zatayi kuka. Malam Na-zuru yay gyaran murya yana gyara zama. “Baza'a rasa yanda za'aiba kam. Sai dai dole za'a canja taku kuma. Shi wannan mutumin da kike tambaya yanada alaƙa da yarinyar matuƙa, sannan yana ƙaunar yaron da zuciya ɗaya, mutum ne kuma mai wayo da hikima gaskiya. Samun nasara a kansa kuma shima sai munyi yaƙi na gaske. Amma ita matar da aka ɗaura masa auren da ita mu maida akalar aikin namu ta hanyarta kawai inaga hakan zai taimaka mana”.
“To amma malam matar da ba'a bukatar ma ta tare miye amfanin kafa harsashin aiki kanta?”. Hajiya Naqiba ce yanzu tai masa tambayar dan Umma dai damuwar jin labarin waye Uncle Yousuf ya hanata magana ma. Amsa ya bata da faɗin, “Gaskiya in har kuna son cimma burinku akan yaron nan dole sai anbi ta hanyar ita wannan yarinya. Hakan na nufin kuma dole sai ta tare da shi sannan komai mu bisa a sannu.....”
Da sauri Umma ta ce, “Malam kana nufin ma har sai ya kusanceta a shimfiɗa kenan?”.
“A'a ba wannan nake nufi ba. Ko tarewa a gidansa tai matsayin mata to ya wadatar damu. Dan muna buƙatar kayan da aka kawota gidansa da shi a ranar, da wanda shi kuma zai shiga gareta da su. Sauran aikin ya rage namu mukuma”.
Jimmm Umma tai alamar tunani kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya da faɗin, “Shike nan malam zanyi wannan ƙoƙarin. Sai kuma akan kishiyoyin nawa ina son a sabunta min aiki musamman uwar yaron nan. Dan na tsaneta fiye da kowa a gidan nan. Bana son koda ganinta matsiyaciyar. Yanda ta saka katanga tsakanina da masoyina har sai da ta fara zama matsayin matarsa na tsawon shekaru kafin ya kalleni bisa tirsasawar iyaye, wlhy itama sai na gunzuga mata baƙin cikin da har ta mutu bazata fita a cikinsa ba.”
“Burinki zai cika kuwa. Mudai je zuwa mataki-mataki zaki sha mamaki”.
Sosai farin ciki ya mamaye Umma, ta cigaba da zayyano ma Malam Na-zuru duk yanda take buƙata akan Ammah da zuri'arta. Suma sauran matan kowacce da kalar nata shirin da take so ai mata. Sai matar ɗanta Salim da itama ke neman zame mata ƙarfen ƙafa akan janye mata ra'ayin Salim ɗin. Basu dai baro garin Zuru ba sai bayan la'asar, a hakan ma ɗan basu tsaya yin koma ba. Sun jigatu kam gwargwadon iko sai kusan goma sha ɗaya na dare suka iso garin su Umma da nufin duba mahaifiyar Tata su kwana.......✍️
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
VIP🔥💯
Zafin kai 3k
Furar danko 3k
Tabarmar kashi 3k
Bakon munafuki 3k
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏_*
No comments