Fin Karfi Book 2 Complete

    



     *FIN ƘARFI BOOK 2*



                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 1



Sulaiman sun yi iya nasu ƙoƙarin dan ganin uban amarya ya sauka amma abin ya ci tura domin har ya kai da faɗin wallahi baza a ɗaura auran ba,in dai shine ya haifi Ruƙayya ba zata auri Yusuf ba.


Gefen Dad shima ya ce "ban da ɗan yau da ƙaƙule-ƙaƙule ɗan shi yafi ƙarfin ƴar talaka. Kuma in ƴan mata huɗu yake so yau ɗin nan zaya aura masa don haka ya jiƙa ƴar tashi yasha.


Jami'an tsaro sun so damƙar Affa amma sai Dad  ya hana su ya ce "ku bar shi yaji da hasarar da yajawa ƴar tasa tunda yai mata baƙin cikin hutawa da cin tuwon dawa."


Gurin ya kaure gami da ya mutsewa  jama'a sai surutu suke yi wasu na ƙorafin an ɓata musu lokaci ya yin da dangin amarya suka rasa dalili da yasa Affa ya aikata haka,su ko dangin ango nasu ganin su aka wulaƙanta don haka sun shaƙa matuƙa.


Dad tsaye jikin motarshi yana waya Momy yake mawa inda yake ce mata "In son be fito ba Hajiya kada ki barshi ya fito."


Gaban Momy ya faɗi ta ce "saboda me?"


Ya ce "Akwai matsala ne shi yasa dan auran ma an fasa ɗaurawa."


Ta ce cikin faɗuwar gaba "akan me?"


Ya ce wulaƙanci mana mahaifin yarinyar ba dattijo bane ki tare son kada ya fito fa."


Jikin Momy yayi sanyi ta ce "ai tuni sun fita shi da abokinsa sai dai gyaran Allah."


Cikin shadda galila ƴar gaske blue takalmi da hula duk sun amshi angon yayi ƙyau, har ya gaji suna ta ratsa jama'a cikin motocin su da suka jero shi da abokinshi guda goma kowacce cike take da ɗan adam.


Yayan Dad shi ne ya tsaida su tare da faɗin su fito, ya dubi Dady ya ce "To Dady sai ka daina rawar kai tunda an fasa ɗaura auran." Jin maganar Dady ya yi kamar saukar aradu ya dubi wan mahaifin shi, ya ce "In dai da gaske kake yi kodai kana tsokana ta ne?"


Ya ce "Kai abokin wasa na ne da zan tsokane ka? Don haka ku juya gamu nan zuwa," ido Dady ya tsurawa Uncle ɗin nashi tamkar yau ya soma ganin shi tun yana ganin shi tar-tar har ya soma ganin wasu taurari suna zagaya kan Uncle ɗin,kai har ya zamana duhu ya mamaye baya ganin komai da kowa. Su Sadiƙ da suma suna cikin ruɗani suka juya domin su lallashi Dady ya zo su wuce,sai ganin shi suka yi ya kusan kaiwa ƙasa,da sauri suka kama shi suka saka shi a mota, Dad cikin ruɗewa shi ma isa da gudu ya shiga mota, girgiza shi yake yana faɗin My son! My son!! Kai innalillahi,wai wama ya sanar da shi wannan abin.


Ita ma Ruƙayya lokacin da labarin ya iso mata nan take ta faɗi sai dai ita hankalin ta be gushe ba,ta dai shiga ruɗu mara misaltuwa,kuka har muryar ta ta dushe. Yaya Murja da Yaya Fati su ne suka sa ta tsakiya suna lallashinta gami da nuna mata kada ta damu in har Dady mijinta ne babu makawa sai ta aure shi sai dai in ba mijinta ba ne.


Cikin kuka Ruƙayya ta ce "nasan zaya yi wuya in auri Dady kuna fa jin yanda me nan gidan ya ce, cewa fa yayi Affa ya cewa mahaifin Dady,ko Dady ne autan maza ba zaya bashi ni ba ya fasa,kun fi kowa sanin halin Affa mutum ne shi wanda baya magana biyu.


Yaya Murja ta ce "haka ne to amma abin mamaki menene dalilin Affa na ƙin amincewa da auran, alhalin da farko ya yarda? Bugu da ƙari sai da ya bari mutane sun taru, wannan abin sam be min daɗi ba don za'a zage shi a gari.


Fati ta gyara zama sannan ta dubi Murja ta ce "amma fa ina ganin aƙwai dalili mai ƙarfi."


Ruƙayya ta ɗaga ido ta dubi Yaya Fati "shin wane dalili  yasa Affa yayi min ƙwalele haka."


Yaya Fati ta ƙwantar da ita a jikinta,ta ce "Auta kiyi haƙuri, Affa shi ne ƙaɗai yake da amsar wannan tambayar,ki jure wata rana sai labari."


Lamo tayi tana sauraron Yaya Fati,tasan dole ne ma ta jure amma yanzun tana tunanin da wane ido zata dubi Dady?


Shin yanzun wane hali ma yake ciki? Duk da yake ma yanzu tasan baya tare da hankalinsa tafi kowa sanin irin son da Dady yake mata.


Sabon kuka ta saki tana cewa "nasan Dady yana cikin wani hali."


Su kansu sun rasa yanda zasuyi, basu kuma yi mata magana ba har tayi ta gaji, kafin wani lokaci tuni zazzaɓi ya rufe ta.


Ƴan biki jin anfasa tuni kowa ya kama gaban shi, sai dangi na jiki suma da gari ya waye gaban su zasu kama. Hafsi kam ji tayi tamkar sallah dan Yusra har da rawa tana jin daɗi.


Har zuwa wayewar gari Dady be farfaɗo ba, tashin hankali na ƙarshe iyayen shi sun shiga, don haka duk ilahirin likitocin dake asibitin, sun taru akan Dady, Momy kam kuka take da addu'o'in Allah yasa kada ɗan tilon ɗan nata kada ya tafi ya barta, shi kam Dad cewa yake in har yaron shi ya mutu bazaya yarda ba, to ko wanene zaya biya shi? Oho.


Kusan sha biyu saura na rana Dady ya farka, ruwan da ake ƙara masa ya bi da kallo shiru yayi yana tuna komai dalla-dalla, kanshi ya soma tambaya shin menene yasa Affa ya fasa bashi Pretty? Yasan yanda yake tsananin son ta kuwa,? Bama zai yiwu bane ace bazai auri Pretty ba,shin yanzu Pretty ɗin ma cikin wane hali take?


Tuni su Dad sun san cewa ya farfaɗo,sai dai likitan ya hana su suyi mashi magana, cewar likitan wai su barshi ya tuno abin da ya faru cikin sauƙi Dady ya juya ya dubi Dad ido ya zuba mishi kamar ya warke makanta, sannan ya mai da duban shi ga Momy,a ƙarshe ya koma ga likitan dukkan su suma shi suke kallo,a hankali likitan ya taka ya isa bakin gadon, yasa hannu ya shafa gefen fuskar Dady ya ce.


"Yusuf Son ya jikin? Kuma ina ne yake damun ka yanzun?


Shiru Dady ya yi tamkar kada ya tanka dan shi yanzu haushin kowa ma yake ji, amma daya tuna yana son yaje yaga Pretty ɗin sa sai ya tattara ɗan sauran ƙarfin halin ya yunƙura za ya tashi zaune likitanne ya taimaka masa, da sauri Dad da Momy suma suka iso bakin gadon ya dubi likitan ya ce "Doctor ni fa ina son a sallame ni dan ba inda yake min ciwo."


Dad ya riga  likitan magana, My son kayi haƙuri kaɗan ƙara jin sauƙi mana, cikin sigar lallashi Dad ke magana, likitan ya ɗora kan batun Dad, "ko nan da ƙwana uku, sannan ka zama normal."


Dady ya ce gaskiya fa ko awa uku bana jin zan ƙara a nan,dan ina son naga Pretty na kuma san halin da take ciki.


Idon Momy ya cika da hawaye dole ne ma tasan abin yi game da wannan lamarin, Dad ya soma mishi faɗa.


"Ka kashe kanka saboda wata ƴar matsiyata duk da irin wulaƙancin da ubanta ya yi mana,da zagin da yayi min cikin bainar jama'a,na tara mutane manyan ƙasa da Sarakuna ya bani kunya gabansu,ai dole ne ma na nunama mutumin nan kuskuren sa."


Dady ya ji zuciyarshi ta na mishi ƙuna saboda irin zagin da Dad ke ma Affa,yana da tabbacin cewa aƙwai wani babban dalilin da yasa Affa ya aikata wannan abun, kuma yana zargin cewa Dad ko ɗan'uwanshi ne sila,wato Uncle.


Ɗaya hannun shi yasa ya zare allurar da aka sa mishi cikin hannu,dama shi ne ƙarin ruwan, ya miƙe tsaye da sauri.


Ganin haka likita ya riƙe shi "Ina zaka Yusuf?" Da sauri itama Momy miƙe ta riƙe shi tana faɗin.


"Dady ina zaka ne?"


Ya ce yana haki "Bar ni na tafi koma ina ne kina jin irin faɗan da Dad yake yi bana son ji, zuciyata na min zafi, kamar ta faso ta fito waje."


Momy ta ce "to kaji,in ɓacin ran da yake ciki be kashe shi ba, to kuwa kai faɗan ka ya kashe shi,kabar shi mana yaji daɗi."


Tsaki yayi sannan ya ce "Na rasa menene Son ya gani gurin yarinyar nan ga mata ma nan ƙyawawa ƴaƴan manyan mutane, amma ya ƙi ya tsaya gurin wannan ƴar matsiyatan."


Da sauri likitan ya ja Dad ɗin Office ɗin shi bayan sun zauna Doctor ya dubi Dad da ke ta cika yana batsewa, ya ce "Alhaji ba abin da ya dace kayi kenan ba,ya kamata ka kula da yaron nan dan kuwa yana cikin wani hali,so ba ƙarya bane,ko kasan jinin ɗan ka ya hau?"


Da sauri Dad ya miƙe cikin tashin hankali,ya ɗaga murya ya ce "Doctor ka ce jinin Son ɗina ya hau?"


Doctor ya ce "Of Course,bayan haka ma zuciyarshi zata iya bugawa a kowane lokaci matsawar zaya dinga shi ga irin wannan halin da yake yanzu,ko kuma a dinga sanyashi cikin tashin hankali.


Matuƙar tashin hankali Dad ya shiga ya dubi likita "to yanzu menene mafita?"


Doctor ya ce "Yauwa,da farko sai ayi ƙoƙarin ƙwantar mishi da hankali ta hanyar nuna mishi za'a san yadda za'ayi a mallaka mishi yarinyar."


Dad ya ce"zaya yi wuya ya samu yarinyar nan saboda wani ƙwaƙwƙwaran dalili mahaifinta ba zai yarda ba, shi yasa nike so Son ya haƙura da yarinyar dan tun farko ma bata dace da shi ba, ƙaramar yarinya ce sosai fa,ban san me yake ganin gurin yarinyar nan ba."


Murmushi likitan ya yi sannan ya ce "Alhaji ka taɓa jin ciwon so kuwa? Koda yake ƙila baka taɓa ɗanɗana raɗaɗin so ba haƙiƙa saboda duk wanda ya taɓa ɗanɗana raɗaɗin so dole zai tausayawa yaronka so ba ruwan shi da talaka ko mai kuɗi,so ba ruwan shi da yarinta ko tsufa,ƙyau ko muni, duk mai yin so ba waɗannan bane damuwar shi,damuwar shi ya samu abin da yake so,don haka yaron ka damuwar shi ya samu yarinyar da yake so, yanzu a ƙwantar mishi da hankali mu samu jininshi ya sauka in yaso kai kuma sai ka je kayi shawara ka sama mishi mafita, don Allah kada kai mishi FIN ƘARFI."


Sai da suka koma ɗakin Dady yana zaune Momy ta na kusa da shi duk suna bakin gadone, kanshi na kan ƙafar Momy baki take bashi da cewa "Dady ka zama musulmi na ƙwarai mai yarda da ƙaddara mai ƙyau ko mara ƙyau a duk sanda ta same ka, komai zaya zo maka da sauƙi nasan kana son Ruƙayya amma in Allah bai yi matarka ba ce babu yanda zaka yi."


Wata ajiyar zuciya yayi sannan ya ce "Momy ni ban halicci kaina ba,bare na hana kaina son Pretty,ban san yanda akayi na faɗa son ta ba, haka nan jikina yana bani zan auri Pretty,ki tausaya mini ki taimaka mini Momy,I love Pretty to much,I need her,zan iya mutuwa domin ta ko kin musu?"


Ta tsura mishi ido kalaman sa suna matuƙar bata tsoro ta san shi tasan wanene shi,tasan halinshi, Dad da suka jima a tsaye suna sauraron ya ƙara shiga cikin tashin hankali ya dubi Doctor "Kana jin shi ko?".


Doctor ya ce "Come down Alhaji kar ka damu."


Suka isa gurin shi Dad cikin fara'a ya ce "Come on My Son dole ne ma ka auri Pretty ɗin ka kaifa ɗan gata ne gaba da baya, ya kamo hannun shi ka taɓa neman wani abu ka rasa? Dady ya girgiza kai.


"To ka ƙaddara ka auri Pretty ɗinka ina nufin koma ta halin yaya ɗin nan da nace ka gane?"


Ido Dady ya tsurama mahaifin nashi,yasan tunda ya furta haka da gaske hakan nan ne zaya aikata, Dad zaya iya nuna ƙarfin kuɗi kona mulki dan ganin ya cika masa burinsa, amma kash shi kam baya buƙatar samun ta ta wannan hanyar dan haka sai ya dubi mahaifin nashi ya ce "Dad duk da tsananin son da nake ma Pretty ba zan so in mallake ta ta hanyar FIN ƘARFI ba zan fi son in sameta cikin yarda da amincewar mahaifinta.


Kafin Dad ya yi magana likitan ya riga shi da cewa "Oh lover boy dama ai sai da yardar mahaifinta za'ayi ba dole za'a yi mishi ba, yanzu me kaɗan sa a cikin ka ne don ina son mu baka magani tare da maka wasu ƴan gwaje-gwaje.


Dady ya ce "Momy ni fa a sallame ni dan nasamu sauƙi sosai ina son in je in ga halin da Pretty take ciki."


Dad ya ce "haba my son ka bari mana ka kara samun sauƙi."


Momy ta ƙara da cewa "zan je na kawo maka ita in dai kayi ƙoƙarin ƙwantar da hankalinka."


A hankali ya sulale ya ƙwanta akan gadon yana faɗin "Momy don Allah je ki kawo min ita yanzu."


Doctor ya ce "to zata je" yana magana yana ɗaura mishi abin gwada jini."


Ita kam Ruƙayya daidai wannan lokacin tana ƙwance rigib cikin zazzaɓi lokacin tuni ana sallama da baƙinsu ƴan biki wasu abokan wasan ta suna ta mata tsiya,yarinya taga samu taga rashi kiyi haƙuri sai kuma Allah ya kawo sabon ƙwastoma in ji Jummai.


Yaya Murja ce ta amshe da cewa "Bakomai ai dai ba shine ya ce ya fasa ba mune muka ce."


Binta ta amshe "to ita amaryar menene na zazzaɓi ki tashi mun dai gane dama ganin tsoro ya yi miki,sai ranar ɗaurin auren ya ganki ashe ƙarama ki ke ga muni."


Yaya Fati ta ce "don Allah mu dai ku tattara ku nufi ƙauyenku har kina cewa Ruƙayya ƙarama ke san da muka je bikin ki kinfi shekara tara ne?" Duk ƴan biki suka ƙwashe da dariya.


Ƙanwar Babansu ta ce "amma Fatsima banga abokin ƙaryar ki ba,san da aka yi bikin Binta ai ko haihuwar ki ba'a yi ba.


Ruƙayya kam tana sauraren su ta ƙosa su tafi dan bata son wasan da suke mata bayan sun tafi ne Murja ta fita dan samo mata magani ita dai a son ta da ciwon zaya taimaka mata ya ɗauki ranta da taso,dubi ƴan'uwanta suna mata dariya saurayin ta ya gudu ina ga mutanen gari dama kuma ba son ta da Dady suke yi ba,kai zama ta iya ratsa layinsu? Domin wasu ma daga cikin ƙawayenta har cewa suke yi tana musu yanga dan zata auri ɗan masu dashi gaba da gaba wata Zina a layinsu tayi mata wannan batun. Hawaye suka zubo mata masu zafi yanzu ya ya zatayi da ƴan makarantar su da mutanen gari? Shin in wani ya yarda mahaifinta ne ya fasa bada ita wasu zasu yarda?


Kai ita da yaya ma zatayi ne? Gaskiya inda tasan inda zata je da ta tafi yau ƙwana uku da faruwar abun amma Affa baice da Umma ga matsalar da tasa ya aikata hakan ba, ita ma bata tambayeshi ba dan tasan tsarin shi, shi mutum ne da sam baya son raini ko wasa da mutuncinshi ta tabbata yana da wata hujja mai ƙwari kuma tasan da zaran hankalinshi ya dawo jikinshi sosai zaya mata bayani, ita dai fatan ta Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.


Dare ya tsala misalin ƙarfe biyu da rabi,shiru garin bakajin ƙarar komai Ruƙayya tana zaune kan katifa kanta yana bisa guiyoyinta,a ranta tana faɗin anya ko gaske ne da hausawa suke cewa dare mahutar bawa? A da kam ta yarda amma yanzu tana da ja,dan duk ƙwanakin nan da abin ya faru sam bata ko da gyangyaɗi,duk yarda ake labarin iya satar bacci baya iya satar ta, tsabar tunani ne kawai yake ɗawainiya da ita, kullum tunaninta yanda rayuwar ta zata kaya ba tare da Dady ba,bata ƙara tsinkewa da al'amarin ba sai da ta tuna yau da yamma Affa ya turo su Umma da su Yaya Fati suka shiga ɗakin su inda Ruƙayya ta ke ƙwance cikin zazzaɓi.


Ya ce ki sani Ruƙayya ada ni ne na yarda miki auran Yusufa, amma a yau na janye,a bisa abin da mahaifinsa ya yi min, Allah ya sani da tun farko nasan, Alhaji Mansur shi ne mahaifin Yusufa da bazan taɓa amincewa da zancen aurenku ba, ga ƴar'uwarki ga mahaifiyar ki na kira sune zasu zama shaida bani son ƙara jin labarin Yusufa anyi shi a gidan nan ballantana har ma yazo gurin ki,ki sani nayi rantsuwa wallahi koda Yusufa ne kaɗai ya rage ɗa namiji a doran duniya na raba ki dashi,sai dai ki mutu gwauruwa ma,kar ki yarda na samu labarin ko a hanya kin saurare shi, lokacin da Affa yake wannan bayanin ɗakin shiru dan kowa kasa gane menene ainihin dalilin da yasa Affa haka tamkar ya karancesu sai ya ce inna samu zama zaku san dalili ya nuna Umma sannan ya ce ke Maimuna kin manta Alhaji Mansur Yusuf da Yaran shi Alhaji Aminu jega? Faɗin Jega yasa Umma tayi saurin duban Affa.


"Me kake nufi Yusuf ɗan su Jega ne?"


Ya ce"ƙwarai kuwa tunda ɗan uban gidan Jega ne."


Umma ta ce "Tabɗi,an so tabka kuskure gwara da Allah yasa aka farga.


Affa ya miƙe in mun samu lokaci kun san wanene Alhaji Mansur da kuma Aminu jega."


Umma ta fita ta hau aiyukanta tana cewa "aiko da an ɗaura a ƙwance Allah ya tsare mu da azzalumai."


Shi ko Affa waje yayi suka bar yaran cikin tunanin shin wanene Jega?


Ta kuma duban su Fati sai faman bacci suke yi ita kam tananan tana ƙoƙarin lallashin zuciyarta dan ta yarda ta rabu da Dady, kuka sosai take yi da ta gano ba zaya yiwu  ta cire son Dady a ranta ba da tasan auran nasu ba me yiwuwa bane ta kuma rushewa da sabon kuka.


Kamar a mafarki Murja ta ji kuka dan haka sai tayi ƙoƙarin juyawa dan ta gyara ƙwanciya,sai ta gane ba mafarki take yi ba, gaske ne, ta tashi zaune ta ce "Ruƙayya me ya faru? Kiyi shiru kin san a yanzu dare ne,nasan kina cikin wani hali ki yi haƙuri ki daure komai me wucewa ne,Yaya Fati ta farka nan suka haɗu sunata lallashin ta. Ta dai yi shiru ta ƙwanta tasan dai badan bacci sai dai dan kada ƴan'uwanta su ga taƙi ji,tana ji har aka kira sallah.


Tamkar Dady da shima aka yi mishi allurar bacci,tun misalin takwas na dare likitan ya ma su Momy zai yi bacci sosai dan sai zuwa shida na safe zaya farka dan yana buƙatar hutu, amma abin al'ajabi daƙyar ya samu awa huɗu yana bacci misalin sha ɗaya da ran ya farko,lamo kawai yayi dan yana jin sanda abokan Dad suka zo duba shi, Momy ta ce ai da sauƙi allurar bacci akai mai dan likitan ya ce yana buƙatar hutu,jin haka yasa yayi lamo.


Saƙe-saƙe kawai yake yi yana ƙwance ma, tunanin shi a wane hali Pretty ɗin shi take shin ta wane hali ne ma Dad zaya aura mishi Pretty?.



🖊️🖊️🖊️

[7/25, 21:01] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 2



Shi fa baya son kota halin ƙaƙa ɗin nan da Dad ke faɗa,ya dai fi so ta tsarin addinin Musulunci yanda Ruƙayya ta ga tsawon dare haka ma Dady. (So manya).


Saboda rashin bacci da Dady bai samu damar yi ba, shi ne dalilin da ya kai sha ɗaya na safe bai tashi ba, tun da ya ɗan daure yayi Sallar asuba ya koma ya ƙwanta sai ko gwanin iya sata ya sace shi (wato bacci) kenan.


Likita ma shigowar shi biyu yana dubawa ko ya tashi dan yaɗan ƙara duba shi amma bai tashi ba. Mamakin shi tun shida na safe yakamata allurar ta sake shi, amma shiru.


Sai Momy ta ce "Doctor tun misalin sha biyu na lura idonshi biyu,na daren jiya tunanin nan dai daya sa kanshi, in yaga nace Dady sai ya rufe ido tamkar yana yin bacci.


Likitan ya ce "Ai sai a hankali,kin san fa kowa da akwai irin yanda so yake shigar shi.


Sha ɗaya daidai yayi miƙa gami da yin sallati da kuma ƴar gajeruwar miƙa, Momy ta je kasa dashi ta ce "ka tashi Babana ya jikin naka.?


Ya kai hannunsa ya shafa fuskarshi "da sauƙi Momy," ta ce likita ya shigo har sau biyu kana bacci sannan kuma abokan Dad ɗin ka ma sun zo su Alhaji Sabitu.


Ya ce "To nagode, Dad fa yazo?."


Ta ce "a'a ya dai kira phone ɗina yanzu ya ce suna tare da Uncle ɗin ku may be ko tare ɗin zasu zo,don ya ce daga wani guri suke."


Dady ya ce "Allah yasa daga gidan su Pretty suke,"Momy ta miƙo mishi Cup cike da tea ta ce to,sarki mai Pretty gashi ka shanye duka kafin ka sha magani.


Ya amsa ya soma sha yana cewa "Wai don Allah Momy me ya hana Hajja zuwa gurina."


Ta soma dariya tana cewa "Hajja tana fushi da mu wai zamu kashe mata jika, zuwan ta biyu lokacin baka cikin hankalin ka."


Kuka sosai ta yi mana ta ce duk laifin Dadyn kane don dama yayi mata ƙorafin bai son ka da Ruƙayya, shi ne tace duk laifin shi ne yaje ne ya yi musu wulaƙanci irin na masu sukuni dan tasa an bincika mata game mahaifin Ruƙayya, kuma ta samu labarin dattijon ƙwarai ne mai wadatar zuci, kuma shi ne mai gidan ba wai irin mazan da mata suke da gida ba, haka dai Hajja ta dinga faɗa akan haka in gaya maka sannan ta tafi ta ce ta daina ɓata ranta a banza in ma ka mutu ɗan mu ne mu ƙarata."


Dariya Dady yayi sannan ya ce "Hajja tawa kenan,bari ki gani bazata iya haƙura ba sai tazo, don yanzu nasan dai hankalinta yana nan."


Kafin Momy ta ce wani abu sai suka ga anturo ƙofa Abokan Dady sun kai su tara ganin shi zaune suka soma mishi dariya, Faisal ya ce "Son Guy,ka fara ramewa."


Sadiƙ ya ce "a'a lover boy zamu sa masa yanzu, ya tashi daga Son Guy."


Daddy ya ce "babu komai,ina Hussain?"


Kafin su bashi amsa Hussain ya shigo yana dariya,ya ce "Kafa samu Son Guy na zata ba zaka gane ba guda ɗaya ba."


Momy ta miƙe dan ta basu guri suka ce "Oh Momy sorry bamu kula dake ba, ina ƙwana? Ya me jiki?


Ta ce "Da sauƙi"


Sannan ta basu guri, Amir ya ce Son Guy yaushe ne wai zasu sallame ka?"


Ya ce ni fa ɗin nan nike so na bar gurin nan, don hankalina yana gurin yarinyar nan ko bacci bana samu ina son in san halin da take ciki."


Hussain ya ce "Ina phone ɗin ka ne,ba tana da phone ba?"


Dady ya ce "Tana dashi,Ok ku tambayi Momy phone ɗin nawa ban san ina take ba."


Sadiƙ ya ce "Ga tawa kira number ɗin muji."


Dady ya ce "a'a bani na kira ta da kaina" duk suka sa mishi dariya.


Sai da ya kira wayar anci sa'a gidan ba kowa sai Umma tana ɗaki.



Su Yaya Murja ma basu nan ta je makaranta.


Yaya Fati kuma tana gidan Yaya Amina,sai ta ji kukan waya cikin kayan Yaya Fati.


Da sauri ta ɗauka,sai da ta ɗan leƙa tsakar gidan babu kowa sannan ta ɗauki wayar tare da faɗin "Dady."



Ya amsa "Pretty na kina ina ne?"


Ta soma kuka ƙasa-ƙasa, zuciyarshi ta dugunzuma hankalinshi ya yi mugun tashi, ya ce "ki bar kukan ban son ji Pretty me yake faruwa ne me yasa Affa yayi min haka? Affa be san muna son juna ba ne?"


Cikin kuka ta ce "Ban san dalili ba Dady ina jin ka same shi nasan ƙila kai zaya sanar da kai komai kenan."


Ya ce "Zan zo yanzu ina asibiti ne, amma yau ne nike sa ran za'a sallame ni, don Allah ki taimaka min da kanki ki ƙwantar da hankalinki kin ji mata ta?.


Ta ce "To Dady kaima ka daina damuwa."


Ya ce "To kice min kina son zan fi jin daɗi."


Sam sai Ruƙayya ta ji yanzu zata iya yin duk abin da Dady ya ce tayi, cikin yanayin tausaya ma kansu ta ce "Yusuf ina son ka ina tsananin son ka zan cigaba da son ka har ƙarshen rayuwa ta. I love You so much," ta kashe wayar ta faɗa kan katifa taji daɗin jin muryar Dady tana sa ran in ya samu Affa komai zaya zo da sauƙi tunda Affa yana son shi.


Shi kam Dady ai mutuwa zaune yayi sanda Ruƙayya ta soma furta mishi kalmomi daya daɗe yana son ji daga gare ta,ganin yanda ya buɗe baki riƙe da waya,yasa abokanshi suka ƙwashe mishi da dariya. Al'amin ya zungure shi gami da cewa "yaya Son Guy irin wannan hangame baki kamar ka suma."


Cikin murna shima ya soma cewa "ni ma Ruƙayya ina son ki ina tsananin buƙatar ki I love You too." Tsalle sosai ya miƙe yana yi su kuma sai dariya suke masa.


Wanka Dady ya fito shadda fara ɗin kin 3-ƙwata, takalmi fari ya dubi fuskarshi a madubi,ya yi rama sosai idon shi ya ɗan ƙara haske ya ɗauki phone ɗin sa da key ɗin mota,ya sauka Momy tana gaban computer ya isa gurin ta "Momy na zan fita."


Da sauri ta dube shi "Dady ina zaka?" ( Bata jira amsa ba ta ci gaba) kasan fa Doctor ya ce ka natsu ka samu hutu yanda yakamata kuma ban da ka dage da fa ba zaya sallame ka ba."


Ya dafa ta "Kada ki damu Momy zan shiga Kabala ne naje naga Pretty sannan na je nayi bikon Hajja."


Ido Momy ta zuba mishi sannan ta ce "An ya kuwa zaka je gidan su Ruƙayya,ka san fa akwai ƴar hatsaniya da aka yi a ranar ɗaurin auren naku tsakanin Dad ɗin ka da mahaifinta,da ka bari ya huce sosai."


Shiru Dady ya yi na wani ɗan lokaci sannan ya ce "Kada ki damu Momy zan ga Affan ne nasan komai kenan zan sani shine kaɗai zaya fiddani daga duhun da na shiga.


Ta ce "Ok, to amma kada ka daɗe dan kasan Dad ɗin ka zaya yi faɗa,in ya dawo baka gida."


Ya ce"ki ce masa na je gidan Hajja kawai.


Ta ce "a'a kasan dai bazan mara maka baya kayi ƙarya ba ko?


Yayi murmushi yana tafiya ya ce " Ba ƙarya bane Momy kin san har can fa zanje, tayi murmushi ta maida dubanta ga computer.


Umma ta dubi Ruƙayya wacce sai jiya ta ɗan soma sakin ranta har tana fitowa tsakar gida ta ce "To ni zan je gaida ɗan gidan Lamin Ado mai karaya,a Kabala wastin kinga Murja suna biki bata nan ki ɗora min tuwo kafin Fati ta shigo, Ita ma daga kai wa Amina saƙo ta je tayi zaman ta.


Ruƙayya ta ce "To Umma anyo cefanan ne?"


Umma ta dube ta "To waye ya yo daga dai ni sai ke,a ciki ni ce nayo?.


Ta ce "Ni dama Umma wallahi bana son fita ne sai mutane su yi ta nuna ni."


Umma ta saka hijabinta tana faɗin "To nidai ga kuɗin nan ƙasan filo kada ki je don kar a nuna ki,ki aje in Yayar ku Fati ta shigo ko Affan ku ko kuma ni in na dawo sai naje na yo cefanan." (Ta faɗa cikin gatse).


Ta tafi,ɗaki Ruƙayya ta koma tana cewa kai nidai na shiga uku!!! Banda dole babu abin da zaya fitar da ni gidan nan,ƙwanciya tayi tana tunanin gun da yafi kusa da zata je cefanan,a jikinta ta ji wai Dady ya shigo unguwar su,ta tashi ta fito tsakar gida,a duk sanda jikinta ya bata cewa Dady yana unguwar su to abin ya kan kasance,ta dubi jikinta riga ce da siket na wakas ƴar Nigeriya,ta ɗauko hijabinta na islamiyya tasa,ta ɗauki kuɗin cefanan ta fita.


Tana fita ƙarshen lungunsu motarshi tana tsayawa kamar mutuwar Soja haka Ruƙayya ta tsaya kyam tana dubanshi,ya fito shi ma gurinta ya nufo fuskarshi ɗauke da fara'a ta dubi fuskar tashi ya yi matuƙar ramewa,ga idanunshi masu birgeta suka ƙara haske, ɗan ƙyakkyawan gashin bakin shi daya zagaye ilahirin fuskarshi har zuwa haɓar shi da gefen fuskarshi ya ƙara fitowa,ƙyau ya yi masa sosai sannan ta ji ta ƙara son shi mai tsanani ji take kamar ta je ta rungume shi.


Daf da ita ya tsaya Pretty na,ta ɗago ido ta dube shi,tuni ƙwalla sun soma taruwa a cikin ƙwarmin idonta, ta juya cikin lungun ta nufi gida, da sauri ya biyo ta yana cewa "Pretty don son Manzon Allah ki tsaya kada kisa kaina ya sara Please tsaya." Ta tsaya daidai ƙofar gidan su ya iso "Haba Pretty menene na guduwa dan na zo?"


Ta sunkuyar da kai tana tunanin Affa, ya ce ko labari yaji an gansu tare to zata sani,tana tsoro kada a gaya mishi ko kuma Yaya Fati ta dawo ta gansu tare, tunda suma basu bata goyon bayan tsayawa da Dadyn ba, sun ce mata dole ne ta bi maganar Affa duk da basu san dalilin shi ba, gashi mutane sun tsura musu ido. Hannunshi yasa ya ɗago fuskarta, ta zuba mishi ido ya ce "Gaya min Pretty, me yake faruwa?"


Muryarta tana sarƙewa, ta ce "sai dai ka tambayi Affa,ni dai ya kafa min dokar cewa kada mu kuma tsayawa ni da kai."


Ya ce "What? Da gaske ki ke yi? Ya saki fuskarta, hankalinshi ya yi mugun tashi har tayi da na sanin gaya masa, hannu yasa ya riƙe kanshi, da sauri Ruƙayya ta ce.


"Dady ka sani ne,ka shiga mota ka gangara ƙasannan layi na uku zan zo sai muyi maganar yanda komai zaya kaya.


Ya dube ta ya ce "ba mutane ne a gurin? Kar su faɗa mishi."


Ta ce "Kai dai ka je ka jirani kada Yaya Fati ta zo ta ganmu,za ta ce ban ji maganar da Affa ya faɗa min ba."


Da sauri ya ja motar mutanen bakin lungun da zauna gari gulma dama ji suke kamar su shiga lungun su ga meke faruwa,sai suka ganshi ya fito ya ja motar yayi ƙasa, wasu suka ce kai yaron nan yana tsakanin son yarinyar nan,ji bi duk ya damu.


Wasu kuma suka ce,in sune me zasuyi da wata Ruƙayya,dama dai Yayartace don kaf ƴan'uwanta sun fi ta ƙyau, wani kuma dake can gefe ya ce "Kai itama fa yarinyar akwai ta fa,kai mata uzuri nan da ƴan shekaru,ai ƙaramar yarinya ce shi yasa" shi ko wani cewa ya yi tsohonta ai ya mata buƙulu, wannan yaron fa ɗan gidan former I.G ne fa ubanshi har Gwamna ya yi a Katsina. Kuma shi ne ɗan daya mallaka ɗaya tilo. Ruƙayya ta fito dan kada sa'idawan bakin lungun su sa mata ido,sai tayi sama don tayi zagaye ta wani lungu, da ido suka bi ta suna ci gaba da sharhi akan fasa auran nata,yana tsaye jikin motar gefen direba, kanshi ya kifa a saman murfin motar da yake a buɗe,sam bai san zuwan ta gurin ba,sai dai ji yayi ta ce "Dady."


Da sauri ya juyo,motar ya shige sannan ya buɗe mata ɗaya ƙofar ta shiga ta rufe duk da akwai ƙarancin mutane sai da ya rufe gilasan motar sannan ya kunna (A.C) ya juya yana mai da dukkan hankalinshi akan ta "Pretty to yau menene abin yi?"


Ta ce "To nidai ka samu Affa ko yaya ka ce?


Ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce "kamar yaushe kenan?"


Ta ce "ko yau da dare ne."


Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce "Ya Allah na ma rasa gane kan wannan matsalar,na rasa wanda ya yi mana wannan sanadin tsiyar don wannan, domin bala'i ne."


Ruƙayya ta ce "Bakomai, akwai Allah."


Ya ce "haka ne Pretty, ina son yanzu mu yiwa juna wani alƙawari."


 Ta dube shi kamar yaya?


Ya ce "yauwa ina son ki min alƙawarin duk rintsi duk tsanani duk wahala ba zaki rabu dani ba,nima zan miki wannan alƙawarin." Ya miƙo mata ƴar ƙaramar batta kamar aƙwati ya ciro zobuna guda biyu masu shegen ƙyau,


Ta dube shi "Dady ai munyi alƙawarin."


Ya ce "Wannan da zamuyi na musamman ne, kuma yana nufin ba rabuwa."


Ta dube shi sam fuskarshi babu wasa don haka ita ma ta nutsu.


Ya ce "bani yatsan alƙawarin ki." Ta miƙa mishi ya kama dogon yatsan nata mai ɗauke da ƙyakƙyawar ƙumba ya lallatsa ya ciro zoben sai faman ƙyalli yake yi Stone ɗin jiki green.


Ya ce "na ɗauki alƙawari ni Yusuf bazan rabu dake  Ruƙayya ba, rana ko dare, ciwo ko tsufa,nakasa ko wahala, Allah kai ne shaida, ya zura mata zoban, jikinta yayi matuƙar sanyi,lallai Dady,ya shiga sosai ya miƙo mata zoben da zata sa mishi gami da yatsan shi,jiki ba ƙarfi ta amsa gami da kama lallausan yatsan shi tamkar bana namiji ba.


Ta ce "To me zan ce?"


Ya ce "abin da ki ka ji nace."


Itama ta maimaita irin kalaman da ya faɗa na alƙawari tana gamawa tasa mishi,gaba ɗaya sai taji wani abu ya ratsa ta kamar tsawa ta dube shi ta ce "kaji abin da ya ratsani kuwa?" Ya ce "kamar yaya?"


Ta ce "ina gama ɗaukar alƙawarin sai naji tamkarr an yi tsawa.


Ya yi murmushi dan ya tsoratar da ita sai ya ce "kin san girman alƙawari kuwa?"


Ta ce, Eh.


Ya ce "To sai ki kiyaye in kuma ki ka karya to wannan tsawar sai ta ci ki."


Ta ce "to bazan karya ba."


Ya ce "Ina phone ɗin ki?"


Ta dube shi"tana gida."


Ya ce "to ta zama tana kusa da ke zan dinga kiran ki ko cikin dare ne, sannan yau zan ga Affa bayan magriba."


Ta ce "kasan fa su Yaya Murja dasu muke ƙwana zasu sani kuma zasu saɓamin tun da Affa dasu ya kafa shaida kuma in ya sani suma zata shafe su tunda zai ce sune ya kamata su san halin da nake ciki,su sani hanya mai ƙyau, tare da bin dokar shi.


Ya ce "ki bari zan san yaya zamu yi sai dai in naga Affan yau."


Ta ce zan tafi kada Yaya Fati ta dawo bana nan."


Ya ce "to sai kin jini yarda muka yi anjima dashi zaki ji."


Ta ce "to" ya buɗe mata ƙofa ta fito, sai da yaga ƙulewarta sannan shi ma ya tada motar. Tana isa cikin gida bayan tayi cefane sai ta samu Yaya Fati har taji tsoro ya kamata,dan bata san yamma tayi sosai ba haka."


Harara Yaya Fati ta sakar mata sannan ta ce "Ya yi miki ƙyau, ina kika tafi haka? Cikin faɗuwar gaba ta ce "Cefane fa na je."


Yaya Fati ta ce "Cefane amma ai ba'a nan unguwar ki kayo ba ko? Kusan awa biyu da rabi nima nayi a gidan da dawowa,  ƙila satabakin dogo ki ka je?


Ruƙayya dai tayi shiru,Fati ta ce "Ni bani in kin ga dama kije kiyi sallar la'asar,ga wanke-wanke nan. Ruƙayya ta wuce Fati tana ta faɗa tana ci gaba da aiki.


Dady cikin ƴar damuwa ya isa gidan Hajja yana yin sallama, Hajja ta fito daga ɗaki tana faɗin Muryar wa nike ji ne ya yi ƴar fara'a ya ce "Ni ne dai mai gidan , ta ce mai sunan mai gidan dai ashe kana da sauran shan ruwa ɗan nan? Aini fushi nayi da iyayen ka tunda sun ƙi ƴar talaka sai ƴar masu hali, mutumin nan dattijon kirki amma sai da ubanka ya yi sanadin fasa auran."


Ta ce "To sai ka bincika ai shi ba mahaukaci bane da zai sa a tara jama'a sannan kuma ya ce ya fasa."


Dady ya ce "Da aƙwai dalili kam."


"Kinsan ni dashi mahaifin nata aƙwai fahimtar juna,in anjima zan je gunsa nasan zaya fiddani daga duhu."


Ta ce "to Allah ya taimaka yaya ƙarfin jikin?"

Ya ce "Alhmdllh."


Ta ce "ja'iri in anzo nan ayi ta cika min baki sai gashi zaka mutu kan ƙaramar yarinya."


Ya ce "Eh, bakomai duk a cikin sone,so ba ƙarya bane."


Ta ce "Ai fa gashi nan na gani ku so ya dama,shi yasa kullum kuna cikin wahala,mu zamanin mu ina ruwan mu da wani so."


Ya juyo ya fuskance ta cikin dariya ya ce "kenan auren dole ake maku."


Ta ce "Ba wani dole kinsan mijinki bare mu gidan mu tsohonmu sadaka yake bada ƴaƴansa bai taɓa amsar sadakinmu ba."


🖊️🖊️🖊️

[7/26, 18:11] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 3



Dady yana dariya ya miƙe ya buɗe fridge ya ɗauko Hollandia ya ce "Ina Baba Saude?"


Ta ce "ta je ɗauko mana markaɗen waina."


Ya ce "To wai Hajja shima tsohon mijin naki haka aka ce miki ga miji?".


Ta ce "ƙwarai kuwa to mu ko kinada ƴan samarin ki na dandali ba lallai bane ki auri ɗayan su dan ni kakan ka ko ganinshi ban taɓa yi ba sai da aka kaini gidan su."


Ya ce "Shi fa ya taɓa ganin ki?"


Ta ce a ina zai ganni? Mahaifinshi aminin tsohon mu ne ba ma a Katsina ya ke ba yana gurin yar mahaifinsu a Huntuwa sai da aka yi auranmu sannan ya dawo nan gidan su."


Dady ya ce "Da kenan ni yanzun ya ma za'a yi na yarda."


Ta ce "To bama kai ba mahaifinka ma soyayya yayi da uwar ka kan ayi auren shi ka biyo ai da yake ance magaji ma fiyi taka take murika tashi."


Dady yayi shiru ya ce "Zan kam bar tarihi dan ni nasan tawa ta ƙare."


Hajja ta ce"kai dai baka da fatan arziƙi mu can za labari."


Ya ce "wa ne canza labari Hajja aini banida labari mafi soyuwa a raina kamar na Pretty na."


Ta ce "Kai ni ja can ga sunan yarinya Ruƙayya mai daɗi amma kaƙi kiranta dashi sai wani kiristine  ko pristine ma Oho."


Yayi dariya ya ce "Hajja tawa ni na Ruƙayya gashi kina son sunan ta amma baki iya faɗa ba wai Rukayya."


Ta ce "Aifa ku ƴan bokon nan komai aka ce ba'a iya ba sai ku."Haka sukayi ta hira har zuwa sallar magriba.


Dady yana zaune gaban Affa bayan sun gaisa sai ya ce "Yusufa sai kuma ka ji yanda Ubangiji ya yi ikon sa ko?"


Dady kanshi a ƙasa ya ce "na ji Affa sai dai har ya zuwa yanzu kaina yana duhu Affa ban san laifi na ba kai min irin wannan horon duk da nasan kai uba ne na gari mai hangen ƙwarai nasan bisa ga babban dalili ka aikata wannan abu zan so nasan dalili inda hali.


Jikin Affa ya yi sanyi ƙwarai da jin lafazin Yusuf kuma har ma yaji kunya, ya gyara zama sannan ya ce "Yusufa da farko dai kai min afuwa har ga Allah da nasan cewa Alhaji Mansur Yusuf Katsina shine mahaifin ka da babu dalilin da zan baka ƴata da sauri Dady ya dubi Affa bakin shi yana rawa ya ce "Affa saboda me?"


Affa ya ce "kafin haka ina son kayi haƙuri ka bar Ruƙayya,ga kayan ku nan da kuɗin ku kai hatta ƙyautar farko da kayi mata duk da na kashe,na samo na harhaɗa na maida na fasa baka Ruƙayya mahaifinka shi ne yakamata ya baka labarin dalilin da yasa na fasa aura maka ƴata, kuma nima dole ne na hana aurenta koda hakan yana nufin zaku rasa rankune kai da ita zan so ka gane, yanzu bari na shiga in sa a haɗo maka kayan ku. Zan cigaba da yi maka fatan alheri dan kaifa ɗa ne Yusuf."


Ɓari jikin Dady ya soma yi ya kasa magana har sanda Affa ya shigo ya zube mishi kuɗi a gabansa,ko takan kuɗin Dady bai bi ba, ya ce "Ka ce na tambayi Dad ɗina ko?"


Affa ya ce "Ƙwarai ka ce masa wanene koda yake ai kasan Jega ko?


Ya ce "Alhaji Aminu Jega?"


Affa ya ce "Shi"


Dady ya ce "nasan shi, shi ne mai kula da harkokin gine ginen Dad ɗina."


Affa ya ce "yauwa ka ko san shi, to ka je kace da mahaifin naka na ce ya sanar da kai me ke tsakanina dashi da Jega?"


Ikon Allah ne ya kai Dady gida ya fito a mota hankalin nan nashi a tashe yana shiga cikin falon su ya hangi Momy ita da Dad wajen daning Dad yana tsaye da alama ma faɗa yake yi, ya isa gurinsu Dad ya dube shi da sauri ina ka shigane Son tunda na dawo nike neman ka a phone ka kashe ka shiga gari kaji dai abin da Doctor ya ce kana buƙatar hutu shi ne amma zaka tashi kalar neman damuwa ai gashi nan kana yaronka jininka ya soma hawa nida girmana nawa be hau ba sai naka dan kaine kasa kanka, Momy ta miƙe ta ce "Haba Alhaji yaya zaka sanar dashi halin da yake ciki in kuma yaji ya ƙara tada hankalinsa fa."


Dad ya ce "ai gara yaji in zayayi mentain ɗin lafiyar sa yayi in bazai yi ba shi ya sani."


Tunda Dad yake ta faɗa Dady ko ajikinsa sai da ya gama ya zauna sannan Dady ya dube shi ,kayi haƙuri Dad nima dole ce tasa na fita ya cigaba. Ya ce "Dad wai dan Allah meke tsakanin ka da Affan Ruƙayya da kuma Alhaji Aminu Jega?" Ido Dad ya tsura mishi na ɗan lokaci sannan ya ce me kake son sani ne? Wannan ba damuwar ka bane,kana ji na ko Son?"


Dady ya ce "Damuwa ta ce domin akan ta zan rasa Ruƙayya wanda hakan zaya iya haifar da komai mahaifin Ruƙayya shi ne ya turo ni gurinka dan naji daga gareka,dan ya ce kaine kafi cancanta ka sanar dani dalili kuma ya ce na yarda duk abin da ka gaya min."


(Dad ya katse shi) "Son ka kiyaye ni fa zanyi fushi da kai banason kana zuwa gurin wannan ɓarawon mutumin ka koma shi ya gaya maka da kansa tunda kai ya zama dole sai ka auri ƴarsa." Da faɗar haka yayi saman shi cikin ɓacin rai.


Kai Dady ya kifa akan daning table zufa ce ƙwarai ke zubo masa ya yin da kansa ya soma sarawa ya sa hannu ya riƙe kan.


Momy ta tashi ta kamoshi ta ce "Dady zo muje ɗaki zo ka sanar da ni yanda kukayi."


Ko gani sosai bayayi suka shiga ɗaki bakin gado suka zauna ta dafashi "Yaya kuka yi da Affan Ruƙayya? A hankali ya sanar da ita komai."


Ta ce"ka ƙwantar da hankalinka gobe zamuje ni da kai dan ya sanar damu komai kenan daga nan sai naga abin zanyi akai."


Duban Momy Dady ya yi ya ce "Nagode Uwata mai maganin damuwata Allah ya bar min ke" ta ce to kayi bacci bana son hirar dare ka ji." Ya ce "insha Allah " ya miƙe cikin ƙarfin gwiwa.


Talatainin dare tunda ya ƙoƙarta ya yi wanka sai ya zama ya kasa bacci sai faman sintiri yake a tsakar ɗaki,ƙarfe biyu da minti ashirin sannan ne ya samu ya faɗa kan gado, hannu yasa ya janyo filo ya rungume shi tsam,ban da muryar Pretty dinshi babu abin da yake muradi hannun shi yasa ya ɗauko wayar sa ya soma neman ta nan take ya tuna cewa ta ce suna ƙwana tare da Yayyanta. Amma duk da haka sai yaji zuciyarsa tana matsa masa, don haka sai ya ci gaba da neman layin ta, ringing ɗin farko Ruƙayya ta miƙe ta ɗauko wayar da sauri ta koma can bayan jakunkunan kayan su,a hankali take magana "Dady ya ya ne?" Ya yi ajiyar zuciya gami da juyi rigingine ya kuma ƙara rungume filon tsam ji yake tamkar ita ce a ƙirjinsa ya ce "Oh my sweet heart,ina cikin damuwa na kasa bacci."


Ta ce, nima haka ya ce "Allah sarki, yanzun dama ɗaya ta rage mana don haka gobe zamu zo da Momy ƙila ya yarda."


Ta ce "Allah yasa haka."


Ya ce "Amin,ki dinga zama koda yaushe da wannan wayar zan dinga kira."


Ta ce "To, amma kada ka kirani kuma lokacin da mutane.


Ya ce "Zan gaya miki yanda zaki maida ta a silent in na kira sai dai tayi vibrating ba mai ji sai ke kinga sai ki kauce daga gurin mutane."


Ta ce "To."


Ya ce "Yanzu gaya min kina zaune ne ko kina ƙwance?"


Ta ce "A'a ina ma raɓe ne bayan kayan sawar mu,kai fa?"


Ya ce "Allah Sarki,Ni kam yanzu ina ƙwance a ɗaki na kan gado rungume da filo a ƙirjina,sai ina ji tamkar Pretty ɗina ce na mannata." Ta yi ƴar dariya ta ce


"Kai ko."


Shima ya ce "Ke ko." Suka yi dariya tare.


Ya ce "I love You."


Ta ce "me too"


Sai kawai taji ya yi kiss ɗin ta a wayar a kunnanta taji ya ratsata har tafin ƙafarta,da sauri ta kashe wayar tayi ajiyar zuciya gami da ɗan murmushi cikin jakar kayan ta ta tura wayar ta koma tayi ƙwanciyar ta.


Shima dariya ya yi har da wuntsilawa zuciyarshi ta yi fes ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya shiga miƙama Ubangiji matsalar sa.


Ruƙayya tana sharan tsakar gida Umma ta na ɗaki lokacin dai dai ƙarfe biyar sun gama abincin dare sun sa a kula Fati da Murja suna ɗaki suna labari Momy ta yi sallama da sauri Ruƙayya ta miƙe suka dubi juna murmushi Momy ta saki ta ce "Ruƙayya ƴata kina shara ne."


Ruƙayya ta sunkuyar da kai sannan ta ce "Momy sannu da zuwa."


Momy ta ce "yauwa ƴata ina Umman taki?"Ruƙayya ta shiga ɗakin Umma ta ce "kinyi baƙuwa." Ta fito ta shiga ɗakin su,Yaya Fati anyi baƙuwa fa.


Suka dube ta "Wacece."


Ta ce "Momyn Dady ce." Da sauri suka tashi suka fita sun samu Umma ta fito mata da tabarma ta shinfiɗa mata a tsakar gidan dake share ƙal. Dan Umma ta ce mata ta shiga ɗaki amma sai ta ce nan yayi ma, Yaya Fati ta kawo mata ruwa mai sanyi na randa sai ƙamshin saiwar da ake sawa cikin ruwa ta zuba shi ne cikin sabon jug irin na kayan auran Ruƙayya Yaya Murja kam tuwon Affa ta kawo mata cikin sabuwar kula da yake ance baƙon ka annabin ka.


Momy ta ce "Agaishe ku ƴaƴana." Suka russuna suka gaishe ta.


Ta ce "ina ƴata shi ne ta shige ɗaki."


Suka yi dariya sun yabawa Momy mace mai sauƙin kai da rashin ƙyamar talaka, ita ma sun burge ta sosai.


Ta yaba da tarbiyyar su ta girmama na gaba,sun gaisa da Umma, Umma ta ce to baki ci tuwon ba.


Momy ta ce Alhamdulillahi na sha ruwan,dan dama nazo gurin Affan nasu Ruƙayya dan Dady ya ce min ƙarfe biyar zamu sameshi."


Umma ta ce "ƙwarai ya kan dawo biyar ɗin, to yau dai gashi har shida saura nasan dai yana hanya."


Momy ta ce "Allah ya kawo shi lafiya."


Umma ta ce "Amin." Phone ɗin ta ta soma kuka ta ɗauka.


Ta ce "Yaya ne Dady?"


Yayi muryar tausayi "Please Momy ki turo min Pretty mana."


Momy ta ce "A'a ka shigo mana kaima ai gidanku ne."


Ya ce "Ina jin kunyar Umma,dama dai Affa ne zan iya shigowa."


Ta ce "to sai ka jirashi don be ƙaraso ba." Ta kashe wayar.


Affa tare suka shigo da Dady,yana riƙe da ledar da Affa ya ruƙo daga kasuwa mai ɗauke da lemu da yalo da kuma gautan ɗaci, Umma ta tashi tana sannu da dawowa Malam, ta buɗe mishi ɗakinsa Momy ma ta mai sannu ya amsa sannan ya shiga ɗakin Dady ya ɗan russuna ya miƙa ma Umma ledar bayan ta fito daga ɗakin Affa inda ta kai masa ruwan sha, ya ce "Yusuf shigo mana."


Shi kam yana ta waiwayen inda zai hango Pretty ɗin sa.


Momy ta ce "kaifa yake kira." Sannan ya bar leƙen windon ɗakin su Ruƙayya inda ya hango ta,tai mishi gwalo ta tsugunne shi ne yake ta faman leƙen windon.


Ya shiga suka gaisa sannan ya ce "Na kawo Momyna tana son ganin ka."


Affa ya ce "to ai babu damuwa,sai ku shigo."


Momy ta nemi guri ta zauna a cikin ɗakin, Affa ya dubi Momy "sannu da zuwa Hajiya."


Momy ta amsa sosai suka gaisa, sannan ta ce "Dama dalilin zuwa na shi ne, ina neman alfarma da kayi haƙuri ka yarjewa yaran nan da su auri juna, musamman ma ita Ruƙayya dake fama da matsala,ni na rasa menene ainihin matsalar.


Affa ya gyara zama ya ce "shi maigidan naki bai sanar dake komai a kai ba?"


Ta ce "Wallahi bai gaya min komai ba."


Ya ce "Ni dai nafi son kuji daga gareshi."


Momy ta ce "Babu komai,in kaima ka sanar damu."


Ya ɗan ɗaga murya ya ce "Ke Fati." Ta amsa, ya ce "Kira min Ruƙayya ku zo harda Murja.."


Suka shigo da sallama ciki suka wuce suka zauna, Dady kam ko kunya ya tsurawa Ruƙayya ido, ita kam sunkuyar da kai tayi tana tunanin Allah yasa Affa ya amince su auri juna.


Ya dube su duka, sannan ya ce "Hajiya ina son ki bani aron hankalinki har da naku ku ma,ki min adalci shin ya dace na bada ƴata ga ɗan wanda ya yi min wannan aikin.?


Wata sansayar yamma ce ta ranar Laraba ina aiki cikin gonar gadon mu da mahaifina ya rasu ya bar mana ni da ƙannena mu goma sha ɗaya mu biyar mazane shida kuma mata,mu huɗu da ƙannena uku muna aikin noman rani da damina sai ga wani mai gadi nan kusa damu mai suna Isa ina aiki ya shigo muna gaisawar zumunci da Isa shi yana gadin filin former I.G Alhaji Mansur Yusuf ƙaton fili ne kuma an zagaye shi da katanga, shi wannan filin rabin shi na mahaifinmu ne, former I.G ya karɓa ya bashi dubu sha biyar amma can lokacin,ya nemi gwamnati ta mallaka mishi filin wanda a yanzu zai kai miliyan hamsin.


Malam Isa ya ce dani "Malam Sani an aikoni gurinka." bayan mun zauna sai yake min bayanin Alhaji Mansur mai gidan shi yana son gani na,na ce to ko lafiya? Ya ce lafiya lau ina ga dai alheri ne dan mai gidan namu mutumin kirki ne,na je na kira ƙanina Sulaiman na ce yazo mu je.


Affa ya dubi Momy ya ce "Kina ji na?"

Ta ce "ina jin ka."


Ya ce "wannan abun fa da nike sanar dake duk a can gida Katsina ya faru.


Momy ta ce "Tunda na ji ka kira ƙaton fili na gane  can gida abin ya faru."


Ya ci gaba "Koda muka je gaban Alhaji Mansur shi da Alhaji Aminu Jega muka sameshi wani dallali kuma mai Kula da gine-ginen Alhaji Mansur da filayenshi muka zauna ƙasa muka gaisa dasu cikin girmamawa Alhaji Mansur ya dubeni "Kaine Sani."


Na ce "Eh,ni ne ranka yaɗaɗe."


Ya ce "muna tare da ku amma ban san ku ba?" Muka yi shiru.


Ya ci gaba "Ni nasan mahaifinku sosai dattijon arziƙi mai son jama'a sam shi abin shi be rufe mai ido ba,kun san fili na na kusa da ku gurinshi na amsa,naima filin kuɗin gwamnati, kuma na bada ma wasu kuɗin daga baya akai mishi ashe saƙon bai same shi ba." Mu kace ya wuce ba komai." Ya ce "yanzu ya labarin wannan gurin naku? Ni ina son gurin zan siya.


Na ce "To bari muje muyi shawara da sauran ƴan'uwanmu, mahaifiyarmu tana nan da rai dan haka sai mun shawarta.


Ya ce "To hakan ya yi."


Jega dake gefe ya ce "Kuna da takardar gurin ta gwamnati?"


Na ce "Muna da ita."


Alhaji ya ce "Ku nawa ne gurin mahaifinku."


Na ce "mu sha ɗaya ne sai mahaifiyarmu."


Ya ce "amma ai kuna da gidan kan ku ko?"


Na ce "ƙwarai gidan mu muke ciki."


Ya ce "Ni ku ɗauke ni tamkar ɗan'uwa don bazan cuceku ba, kuyi shawara nawa zaka saida min da gurin dan ba zan ci haƙƙin marayu ba."


Muka ce "To." Muka tashi muna godiya.


Bayan munyi shawara mu saida mishi sai muka sake dawowa da ƙanina. Miliyan uku da rabi muka ce su bamu.


Jega har yana cewa wai shima tunda shi ne yazo ya yi ma Alhaji tallar gurin sai mun bashi wani abu,sai muka ce babu komai.


Dubu ɗari biyar muka ce zamu bashi in an biya mu, duk da ba tallah muka yi ba.


Bayan wasu ƙwanaki suka bamu miliyan biyu saura ɗaya da rabi,da shike muna cikin buƙatar kuɗin ne sai muka ce mu raba.


Malamai ne ma dai suka raba mana kowa aka bashi nashi,muna jiran sauran kuɗin, rannan sai ga saƙo daga Jega,wai fili gwamnati ta riga ta ba wani, kuma wanda aka ba yaron Alhaji Mansur ne, don haka takardun mu na ƙarya ne mu dawo da kuɗi,ki na ji?


Momy ta ce "Ina sauraron ka." Ya ci gaba "Koda na ji sai naje na ce to muje land and sobe ɗin ai fayil ɗinmu na can a taƙaice dai Hajiya haka wannan Jega ɗin suka yo takardun bogi suka ce na gurin ne sai mu dawo da kuɗi. Bayan duk unguwarmu kowa yasan tsohonmu da gurin ga takardu ga komai, haka suka sa ƴan sanda suka kamamu suka tafi damu (State C.I.D) aka tsare mu da har ma ance gidan yari za'a kaimu tunda mu rasa wanda zamu cuta sai (former I.G).


Munsha wuya,don ma ƴan'uwanmu da Abokaina sun yi ta ƙoƙarin ganin haɗa kuɗin an basu, tunda sun ce sai mun basu kuɗin su sannan zasu sake mu, wasu suka ce duk sharrin Jega ne aje a samu (Former I.G) shi zai sa a fito damu dan mutumin kirki ne, ana zuwa ya ce magana tana gurin Jega, anyi-anyi amma yaƙi ya ce a sake mu, tunda shi ne mai kuɗin, Hajiya lokacin ƴan'uwana da mahaifiyarmu sun shiga tashin hankali, mata ta......


🖊️🖊️🖊️

[7/28, 08:27] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 4



Mata ta da yarana, lokacin su waɗannan ya nuna su (Ruƙayya)suna ƙanana haka ƴan'uwa da Abokaina suka dinga samun manyan mutane don su sa baki, amma kowa ya ji da (Former I.G)ne Alhaji Mansur,sai suce gaskiya sai dai kayi haƙuri  ba zamu iya tunkarar shi ba, don ubanmu ne, to Hajiya ƙarewa ma ƙwamishinan ƴan sanda na jihar Katsina a wancan zamanin shi ne da kanshi ya zo ya tafi damu, kuma don tsohon wulaƙanci.


Bayan mun saida sauran kadarorinmu mun haɗa miliyan biyun su mun basu sai da muka ƙara ƙwana uku sannan suka sake mu,bugu da ƙari sun sa ƙwamishina ya amsa mana takardar gurin. Kinga sun amshe mana guri ga ɗauri ga kuma asarar sauran kadarorinmu, baƙin cikin wannan abun shi ne yasa ni nabar Katsina na dawo nan Kaduna da zama, kayan koli nike saidawa kuma ba laifi dashi ne na samu na sai wannan tsohon gidan nawa kuma nike biyawa yara kuɗin makaranta nake ci dasu.


Sannan yanzu duk mutumin da ya yi min wannan aikin na ɗan shi ƴata,ai ko ƴan sanda ka kira min ka gama da ni bare har kasa a tsare ni saboda haka kayi haƙuri ba zan iya bada ƴata gare ka ba, kayi haƙuri.


Gwiwa biyu Dady ya durƙusa a gaban Affa ya ce "don Allah Affa ka taimake ni kada kaimin haka."


"Ni ban maka komai ba." Yusufa ba ƙaramin ɓakin cikin rashin wannan auran nayi ba,don har ga Allah zuciyata tana tsananin son ka har yanzu,sai dai in har na baka ƴata Yusufa ban ma san abin da nake yi ba kenan."


Momy ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Tabbas nasan sanda abin nan ya faru domin kusan mata uku a wancan lokacin sun zo dan neman nayi ma Alhaji magana, koda nai masa sai ya ce min maganar ta mutu."


Affa ya ce "To kin ji ma kinsan lokacin."


Ta ce "To don Allah Affan Ruƙayya kada ka biyewa halin shi, kayi haƙuri don Allah."


Ya ce "Hajiya na gama magana, hawaye Dady yake sosai amma Affa ya ce "ina."


Itama Ruƙayya sai ta samu da jin zafin abinda Dad ya yi wa Affan ta.


Amma duk da haka sai ya zamo bata ga laifin Dady ba, tunda shi ba shine ya yi ma Affa ba, ta dubi Dady ya ruɗe ya fita haiyacin shi.


Ta dube shi ta ce"Kayi haƙuri Allah zai baka wadda ta fini."


Cikin ruɗewa ya ce "Kina nufin kin haƙura dani? Kada kiyi min haka Pretty ni mai sonki ne har abada."


Kuka sosai Ruƙayya ta saki cikin kukan ta ce "Bayan da zan yi ne."


Fati da Murja suka dube ta cikin ƙulewa,dan sukam sun matuƙar jin zafin abinda Dad ya yi ma Affa dan haka sai suka ce "ke kima mutane shiru, tashi mu je tunda ke baki kishin ubanki."


Ruƙayya ta ce "Ku tausaya min rabani da Dady ba ƙaramin abu bane." Suka yi tsaki suka fita.


Momy ta kasa magana dan tasan lallai an ma Affa FIN ƘARFI, yanzu tana jin nauyin ta matsa mishi,miƙewa tayi ta kama hannun Dady ta ce "To zo muje mu bar komai a hannun Allah."


Affa ya ce "Ga kuɗin ku nan bari a fita da jakunkunan kayan."


Momy ta ce "Kar kayi haka Affan Ruƙayya,ai Ruƙayya ƴata ce,dan haka daga kayan har kuɗin na bar mata."


Affa ya ce "a'a sam." Momy ta ce,in har kace haka to tabbas akwai wani abu a ranka,ba mahaifin Dady ya baka ba,ni ce nan kuma ko ɗaya ban ga laifin ka ba sai na mahaifinshi, domin ko ni akai ma haka, tsakani da Allah ba zan bayar da ƴata ba."


Ganin zasu fita Affa ya ce "To shikenan."


Ruƙayya ta duƙar da kai tana kuka mai tsuma rai, sauraron ta Affa yake tayi, tayi har muryar ta ta dushe, ya ce"ki yi haƙuri Ruƙayya ban maku FIN ƘARFI ba,bana son mahaifinshi ya raina min wayo,ko ba komai zai san cewa shima talaka yana da rana da kuma baiwa, wacce zayayi iko da ita, ina son ki nutsu ki bar zancen aure, karatun ki shi zaki sa gaba,ki manta da Yusufa dan ki samu zaman lafiya a cikin gidan nan, tunda matsawar kika bijiremin ko ƴan'uwanki ba zaki samu ƙwanciyar hankali da su ba."


Ta ce "To."


Ya ce "Maza tashi kije kiyi sallah."


Ta miƙe ta fita. Koda ta shiga ɗakinsu su Murja suna sallah, bayan sun idar itama ta idar ta tashi taje ta kawo musu abinci, ta koma kan katifa ta ƙwanta saboda tsabar ciwon kai,da yake damun ta suka bita da kallo, basu ce ƙala ba suka cigaba da cin abincin su suna hira,taji tausayin kanta wato ma fushi suke yi da ita,tasan da dane taƙi cin abinci zasu yi ta lallashin ta ne har sai taci. Isha'i ma sai a zaune tayi ta ƙwanta cikin tunanin Dady. Shikenan yanzu soyayyarsu ta zama tarihi, tsarin da Dady ya yi musu na zaman aure yasha ruwa,ta tuna wata rana da suke hira da Dady game da bikin su,ya ce "Pretty." Ta dube shi ya ce in mukayi aure nifa kinsan ina son haihuwa da wuri, ina son yarinya ta mace ƙyaƙƙyawa, Ruƙayya tayi dariya ta ce, Ni bana son na haihu da wuri, ya ce "Saboda me?" Ta ce "don na tsufa kai ka auro wata ya yi dariya ya ce "Ai Pretty duniya da lahira ke kaɗai ce mata ta kuma uwar ƴaƴana kullum in ta tattalin ku ina shagwaɓa ku, komai ni zan miki kamar bawa zan koma miki abinci a baki,in miki wanka,in miki wanki,in ki ka ce be miki ba sai na sake miki wani,in zamu fita ni ne mai ɗaukar miki jaka, hannu tasa a bakin ta tana dariya tana faɗin kada kasa ace na mallake ka, ya ce na nawa aini yanzu sai yanda kika ce,kin san Momy zata so mu taso yaranmu.


Ruƙayya ta ƙara fara sabon kuka, Fati ta dubi Murja ta ce , Murja ki ji min ikon Allah zata cika mana kunne.


Murja ta je ta jawo ta ta zauna,bazaki mana shiru ba ko?


Cikin sarƙewar murya da shashshekar kuka ta ce "Yanzu ba zaku tausayawa halin da na shiga ba."


Fati ta ce "Ba fa zancen tausayi a cikin sa kai dan wannan sa kaine, kuma ki mana shiru ko ki ci duka."


Tasan tsaf zasu dake ta,dan haka sai tayi shiru tare da yin kukan zuci.


Shi kam Dady ai akan shi aka ƙwana asubar fari sai asibiti,ƙwananshi sha ɗaya abu ba sauƙi sai na Allah. Dad da kanshi ya yi ma wanshi waya yana neman shi, bayan ya zo suka yi shawara Dad ya so suje su roƙi Affa ya yi haƙuri ya ba Dady Ruƙayya, amma sai ɗan'uwanshi ya ce, a'a ba haka za ayi ba, abin da zaya fi shi ne haɗa Dady da Yusra, tunda ai Ruƙayya ba fin Yusran zatayi ba, bayan haka ma tunda Yusra tafi Ruƙayya girma zata mantar dashi Ruƙayya tare da tattalinshi,ka ga tunda an gama komai game da wannan Company shi sai a haɗa da bikin buɗe Company dana auransu.


Dad ya amince amma Momy ta ƙi yarda, ta ce "Sam a bar mata yaronta ya samu lafiya kafin ayi mishi shawara in ya yarda,fa ni'im in bai amince ba sai a fasa."


Shi ma likitan ya ba Dad shawara, suka bari yaji sauƙi kuma kada ai mishi dole, wannan ne dalilin da yasa Dad duk ya fita daga haiyacin sa,koda ya tuntuɓi amininshi mahaifin Hafsi sai ya ce mishi "baya goyon baya mutum kamar shi ya je yana roƙo ga talaka, don haka ya barshi kawai."


Kan Dad ya yi zafi yama rasa yadda zayayi, Momy ce ta zaunar da shi ta ce "Ya ƙwantar da kai ya je ya samu su Alhaji Sabitu su dafa mishi baya ya je ya ba Affan Ruƙayya haƙuri.


Hakan ce kuwa ta kasance amma Affa ya ce "Sam."


Zuwan su Dad uku saboda kowa yaga Dady sai ya tausaya mishi in dai kana da zuciyar imani. Shima Affa duk da baiga Dady ba ya tausaya mishi,sai dai yana son Alhaji Mansur yaji yanda ya ji shima san da aka tsare shi akai ta zuwa ana roƙon shi amma yaƙi.


Ita ma Ruƙayya duk da tana ƙoƙarin nuna cewa ta haƙura babu daran da bazatayi kuka ba, kuma su Murja sun san tana yi, suna nuna mata basu sani bane, kuma suna tausayin ta sai dai basu so su nuna mata ne dan kada ta samu ƙofar kawo musu zancen Dady duk ta rame karatun tama ya yi rauni tun daga boko har islamiyya.


Germany su Dad suka yanke shawarar kai Dady dukansu suka tafi har ma da ƴan rakiya. Su Ruƙayya suna tsaka da zana jarabawa ciwon cikin ta ya motsa, kasancewar wancan watan batayi ba sai yazo mata da muguwar matsala tasha wahala sosai, ita ason ranta ma Allah ya ɗauki ƙwananta ta huta saura paper ɗin ta uku batayi ba,dan ma tayi masu muhimmanci.


Haka lokaci ya cigaba da tafiya sai ki ga da gari ya waye har yamma tayi sai ki ga dare ya shigo gari ya ƙara waye wa,ba wuya ace juma'a ta zago gashi har Dady ya samu wata uku a can Germany ya warke sarai sai dai zuciyarshi ce bata warke ba har yanzu son Pretty ɗin shi yana nan daram ƙauna zalla daga Allah, ya yi ƙyau ga wani haske da idonshi ya ƙara sai dai bai gama maida jikinshi ba. A wannan lokacin Ruƙayya tuni ta soma karatun ta a makarantar ƙwana dake Bakori a jihar Katsina. Affa ya yi hakane dan ya nisanta ta daga gida, duk da labari ya sameshi an fita da Dady (Germany)ta soma (S.S.1) ɗin ta ne cikin haƙuri da juriya.


Suna makaranta aka yi bikin su Fati,taso ace tana nan amma ina,taji haushi sosai ƙawayanta Safiya Umar da Walida da Amira sune suka yi ta bata baki. Safiya ƴar Katsina ce a Tudun Wada ita ko Walida ƴar Funtuwa ce ya yin da Amira ta zama ƴar Zariya.


Su huɗun nan koda yaushe suna tare. Suna mata labarin samarin su,Amira auran zumunci zasuyi ita da Mansur, ɗan kawun ta, ita ko Walida yaron Ogan Babanta zata aura na gurin aiki, Safiya kuwa ɗan layin su ne Usman, dukkansu Ruƙayya ta san su saboda sun zo lokacin ziyara.


In sun ce tana da saurayi,sai ta ce a'a, wata rana suna ƙwanarsu suna ta hira sai Walida ta ce "Ruƙayya don Allah zan tambaye ki wani abu zaki bani?."


Ruƙayya ta ce "Faɗa ko menene."


Ta ce "wannan zoben nake so."


Ruƙayya ta ce "Kash,aikuwa Walida sai dai ki amshi ɗayan nan amma ban da wannan don mutuwa ce kaɗai zata raba ni da zobannan."


Amira ta ce "Zoban alƙawari ne."


Ruƙayya ta yi murmushi ta ce "Ko masu bincike makarantar nan sun bar ni da zobannan, Zoban Dady Allah sarki Dady mai sona da gaskiya." Sai hawaye kuka sosai tayi da ƙyar su Amira suka lallasheta suka kaita har gadonta suka zauna.


Safiya ta ce "Ruƙayya Dadyn ya rasu ne?"


Murmushin ɓacin rai tayi ta ce "Dady yana nan sai dai yanzu ban san inda yake ba." Nan ta basu labarin Dady har ta nuna musu wayar ta daya bata sun sha mamaki, tare da tausaya musu sannan suka ɗauki alwashin sa ta a cikin addu'arsu kullum suka yi sallah biyar.


Walida ta ce "Ba zaki kirashi a wayar ba ne?"


Ruƙayya ta ce "bazaya yiwu ba tunda bazan same shi ba,gara nayi ƙoƙarin nesanta kaina dashi."


Su kam su Walida sun so ace wayar da chaji su ga yanda ake amfani da waya kasancewar wayar a wancan lokacin sai wane da wane ko a masu kuɗin. Suna cikin haka har lokacin hutu ya zo sun yi murna da ɗoki sosai na zuwa gida, Umma ta ce "Auta har yanzu kina nan kina ƙulafucin Dady ko?."


Ruƙayya ta yi yaƙe sannan ta ce "Haba dai Umma ai ni nama mance da wani Dady me kika gani?.


Ta ce "har yanzu baki maida jikinki ba, gashi kin samu ɗan wake sai Allah."


Ruƙayya ta ce "munyi ciye-ciye ne a mota (ta sako wata maganar) Umma lokacin dana samu labarin auran su Yaya Fati sai da nayi kuka nace shin Affa yasa lokaci kusa dan kada naga bikin ko?"


Umma tana dariya ta ce "Ke da Affan naki in yazo sai ku ƙarata."


Ruƙayya ta ce "ina aka kaisu?"


Ta ce "Fati tana Kakuri, ita kuma Murja N.N.P.C ƙwatas."


Na ce "Eh,anan Yaya Ahmad yake aiki."


Umma ta ce "Eh, suna ta labari har Affa ya shigo duk da ya kula har yanzu Ruƙayya bata maida jikinta ba,ya ji daɗin ganinta tana ƴar walwala suna aiki tare da Ummanta.


Ruƙayya ta durƙusa ta gaishe shi cikin fara'a,ya amsa mata tare da nuna mata murnar shi na ganinta. Cikin hirar da suke yi da daddare take ƙorafin anyi biki bata, Affa lokacin da aka aiko min da wasiƙar nan sai da nayi kuka."


Ya yi dariya ya ce "Neman ilimin kenan,kema gashi makarantar Islamiyyarku da kuka yi sauka anyi walima ba ƙyanan,sai dai ke an aiko miki da ƙyautukan ki 


Ta ƙara turo baki "kai gaskiya ni dai ban so haka ba."


Affa ya ce "To ai shikenan ya wuce ai ko?."


Ta je gidan Fati ta wuni washegari ta je gidan Murja,sun ji daɗin ganinta sai dai dukkansu sun mata ƙorafin rashin maida jikinta, cewa ta yi karatu ne, tayi sha'awar yanda mahaifin nasu yayi matuƙar ƙoƙari ya tsarawa ƴan'uwanta ɗaki ta je gidan su Yaya Amina Yaya Suwaiba da Sadiya, duk sun yi murnar ganin Auta ta ƙwantar da hankalinta.


Bayan sun koma makaranta sun haɗu da ƙawayenta suka ci gaba da karatu.


Ƙwanci tashi gurin Allah ba wuya sai gashi sun shiga S.S.2, ciwon cikin ta kam yana nan tana shan wuya,malaman su har sun gane ta, saboda duk wata sai tayi wani sa'in kuma tana yin wata biyu ko uku,in ta dawo hutu samari kamar me amma bata fita ko Umma ta ce tashi ki je tunda ai ba danki zamuyi dake ba kina gamawa aure zakiyi,sai ta tura baki tana fita zata korashi,in ko a hanya ne sai ta ce tana da miji.


A haka dai har suka shiga S.S.3 ance aski in yazo gaban goshi tafi zafi to haka suma karatun nasu yafi zafi yanzu,dan haka suna ƙoƙari kuma har zuwa wannan lokacin Ruƙayya tana kukan Dady da yawa tana ganin shi cikin mafarkin ta,yana faɗi mata kar ta karya alƙawari.


Sun samu hutun zango na biyu a shekarar su ta ƙarshe bakin titi suka tsaya suna ta banƙwana Ruƙayya da Amira hanyarsu guda dan haka tare suka taho a Zaria Amira ta sauka ita kuma ta nufo Kaduna.


Girma da cika Ruƙayya tayi ga ƙyanta ya bayyana fatar ta tamkar Black America wasu kuma su ce kamar ƴan matan Ethiopia duk saurayin da ya ganta sai ya sake dubanta.


Cikin shadda pink kayan ya yi matuƙar amsar ta gidan Yaya Murja zata. Bayan ta miƙa ɗinkinta gurin Nasir,a hankali cikin natsuwa take tafiya ƙwarai tana birge mutane, shagon Nasir ta tsaya ƙyaƙƙyawan saurayi mai son neman na kansa ya yi matuƙar iya ɗinki da aikin surfani na mata,dan haka ma shine ke ma mata manya da ƴan mata masu son a birgewa,yana ganinta ya ce "manya Ruƙayya saukar yaushe?"


Tayi murmushi ta ce "shekaran jiya na dawo ya aiki?."


Ya ce "Alhamdulillah,"ta zube mishi zannuwan ta "kin san kuɗin zannuwan nan kuwa."


Ta ce "Nasir kenan, nima ban sani ba."


Ya ce "ai naga alama daga yanayin riƙon da kikai musu. Dariya ta saki tana cewa "lallai Nasir to wane irin riƙo nayi musu?."


Ya ce "Oga ne ya siya miki ko?"


Ta ce "wane Oga aini banida wani Oga."


Ya gyara tsayuwa dan ya daɗe yana son ta sai dai yana shakka dan yasan dole tana da samari "Ban yarda ba, domin ke son kowane." Ta ɗan rage fara'a.


Ta ce "To nagode, yanzu kana da style a ƙasa."


Ya ce "Ko babu dole na nemo shi."


Ta ce "ayimin landin full a riguna,sun fi zama."


Ya ce "An gama."


Ta ce "Bill ɗin kuɗina naji."


Ya ce "Ki je sai angama."


Gidan Yaya Murja ta wuce ta sameta tana dafa abinci a kitchen,kicin ɗin suka shiga tare,alalanwake da hanta da ƙwai take yi Ruƙayya ta ce "ina mama ne?"


Murja ta ce "tana bacci yanzun nan ta ƙwanta bayan ta gama rigima zata bi babanta."


Ruƙayya ta ce "Ai dama mama ƴar dan ja ce aƙwai rigima, Muhsin ɗin Yaya Fati yafi ta haƙuri."


Murja ta ce "Jiya ko can gidan su muka wuni,sai faman labarin auren ki muke yi sai kace bikin ya zo."


Ruƙayya ta taɓe baki ta ce "Ni fa shiyasa bana son muyi hutu saboda zancen auren nan."


Murja ta na dariya ta ce "Ka ji yarinya ba dole ai miki zancen aure ba tunda kin isa."


Ruƙayya ta ce "To ai banida saurayi."


Murja ta ce "Aƙwai wani faruk ƙanin Baban Mama yasha min zancen ki,yana da kirki, gashi yana da aikin shi."



🖊️🖊️🖊️

[7/28, 18:44] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 5



Ruƙayya ta ce "A ina ya ganni kin da mishi tallata." Ta ce "a'a zuwan ki da sallah ya ganki kin ma san shi wanda yazo na ce ki kawo mishi abinci har ma yace ya ƙoshi sai dai a bashi drink mai sanyi."


Ta ce "Ok na tuno shi gaskiya nidai be min ba."


Murja ta ce "Eye,ƙyau kika fishi ko iya ado ka jiki dan ma yace yana sonki."


Ruƙayya ta ce "Ya je da ƙyaunsa  na yafe." Nan ta yi sannan ta dawo gida."


Washegari gidan Yaya Fati ta yi, Yayyanta kamar haɗin baki duk wanda ta je gurinshi sai ya yi mata zancen aure, takaici ni dai karatu zanyi tunda ku duk an rasa me yin sa kowacce daga secondary ta sare,sai su ce aiko badai a gidan Affa ba dan ba zaya yarda ba, ta ce to shikenan zaku gani.


Umma ta dubi Ruƙayya ta ce, "Auta ina ji kusan minti goma kenan da shigowar yaro ya ce ana sallama dake,ko kin manta ne."


Ta ce "Ƙyale su Umma samarin unguwar nan ƴan rainin wayo ne, ƙanana dasu ba a gama wanke musu kashi ba,sai ki gansu wai sun zo taɗi."


Umma ta harare ta "Dalla ni ki tashi ki fita,wato ke kin fi son kiyi ta zama damu gashi kin kusan gama makaranta, Allah ya baki sa'a kin san dai Affanku,ya iya wanke ki ya ba wani."


Cikin tura baki da fushi ta fita,Nasir ta gani tsaye da laida ranta ya ɓaci ta dube shi "Yaya ne Nasir na ganka a gidan mu.?"


Ya yi murmushi "Nasan dole ki tambaya zahirin gaskiya na jima ina son ki so na haƙiƙa na aure shiyasa na ce bari in zo dan hausawa suna cewa da zafi-zafi akan bigi ƙarfe."


Haushi ya kama Ruƙayya ta ce "Nasir ina matuƙar ganin girman ka kada muyi haka da kai dan zahiri zamu ɓata,ka kama kanka danni ba aure a kaina."


Da sauri ya dubeta "Saboda me?"


Ta ce "Wannan ba damuwar ka bane kai dai ka janye."


Ya ce "Ni kam sai naga ƙal uwar daka."


Ta ce "shikenan,ta juya tayi gida."


Shiru yayi na ɗan lokaci sannan ya wuce yana saƙa yanda zai ɓullowa abin.


Duk irin korar da tayi ma Nasir bai ji ba haka ya liƙe mata tamkar cingam, gashi in yazo ko taƙi fita sai Umma ta kora ta ya yo mata ɗin kunanta tsala-tsala sai ma taji ta tsani zannuwan,ban da ma zannuwan na cikin kayan da Dady yabar mata ne, Allah da bazata sa su ba,dan dai tana matuƙar son kayan dan suna sa ta cikin begen Dady tana alfahari da kayan ba dan kasancewar su masu tsada ba,sai dan kasancewar su daga Dady.


Dama ta ƙosa su koma makaranta dan haka hutun su na ƙarewa ko yini bata ƙara ba,ta koma ita da in sun koma sai tayi kusan ƙwana uku, ta ce ba'a komai. Nasir ma bata sanar dashi ba sai dai ya shafa ya ji bata nan, sai da ta koma a group ɗin su ita kaɗai ce tazo, amma duk da haka sai taji gara haka tunda ba mai damun ta da zancen aure bayan ƙwana biyu sauran suka iso. Matuƙa Ruƙayya tasa kai ga karatu sosai ba wasa don haka koda jarabawa sai taji mata sauƙi, ta kuma sa kai sosai, saboda tana son cigaba da karatu.


Ranar yayesu sun sha kukan rabuwa ita da ƙawayenta, bayan an watse daga taron na bada ƙyaututtuka,a mafiya yawan ƙyautukan Ruƙayya Sani ta amsa mutane da wasu iyayen sun yi sha'awar ta. Affa da Fati da Murja da Yaya Amina da yaran Yaya Sadiya duk sun je, mota guda suka yi,mijin Fati ya kai su,dan haka Affa ya yi alfahari da Ruƙayya, haka Yayyanta. Wasu kusa dashi suna faɗin "Kai Iyayen yarinyar nan sun ji daɗi ina ma su barta ta ci gaba da karatun da wannan ƙasa zata ƙaru da ita,ga tsafta ga tarbiyya duk itace ta amsa,Ɗayan ya ce gaskiya da sun ƙyauta,in sun barta aima duk ƙyautukan masu mahimmanci duk ta amshe, gashi shi kanshi mai bada ƙyautukan sai da ya bata tashi,ko menene ciki Oho. Ɗayan ya ce kuɗi ne na sani.


Hotuna dai sun ɗauka kamar me, sun yi kuka sosai sun rabu da alƙawarin za su zo Kaduna kawo mata hotunan bikinsu. Da Amira suka taho suka sauke ta Zaria, ta ce zata zo Kaduna very soon don aƙwai Yarta a unguwar Rimi zata nemi Ruƙayya.


Suka yi sallama, mijin Yaya Fati Baban Muhsin sai tsokanar Ruƙayya yake yi, ya ce "Ruƙy yanzu sai maganar aure ko?"


Ta ce "Allah shi ƙyauta sabon karatu zan dasa ko baka ji abin da mai raba mana ƙyautuka ya ce ba.?"


Ya ce "Naji yana ba iyayen ki shawara akan su barki ki ci gaba da karatu, har ma ya ce gata shi gudunmuwar nan ki sai form.".


Ta ce "To shi ne zaka kira min aure? To ni mijina koma ƙeroshi ba'ayi ba."


Ya ce "Kedai ki faɗa in baki dashi ne ki faɗa sai in fito duk da dai matata tafi ki ƙyau in rufa miki asiri."


Ta harare shi "Kama faɗa ka ce matarka tafi ni ƙyau,sai dai ta nuna min fari,farin me,ga kala ta ƴar yayi,jikina golding ne kasan ko ba kowa ke da wannan kalar ba,sai ɗan baiwa. Ni one in town ce a garin Kaduna ba ta biyu na,da fatan ka gane."


Duk dariya suka saki dama Affa ta haya ya biyo ya ce in zauna a gurin shi haka muka iso ana raha, don haka sai na manta da tunanin ƙawayena.


A gida mun samu Umma ta tsara mana ɗan wake da mai da yaji harda ƴar miya ga mai so,Nasan tayi ne donni, don haka ban bata kunya ba,gurin ci ina santi na ce "Allah ya bar min ke Umma, ta ce "au to, Allah ko bazai barni ba, sai dai in lokaci na baiyi ba.


Ruƙayya ta ce "Umma bar faɗi, Umma sai kinga jikokina da tattaɓa kunne na." Suka sa dariya.


Umma ta ce "Allah ya tsare ni."


Haka suka yi ta raha da ƴan'uwanta da Umma, sun kuma duba ƙyautukan suna ta murna har zuwa kan ƙyautar mai bada ƙyautuka,wato ƙwamishinan ilimin jihar Katsina.


Check ne na zunzurutun kaɗi har naira dubu ɗari biyu da hamsin inda ya bada check ɗin bankin arewa.


Suna ta murna, Affa ya shigo ya samu gidan tamkar sallah, Umma ta tashi ta ce "kun ga bari naje gurin tsohon mijina." Ta fita suna mata dariya, suka ce kije ki duba shi muma munfi son haka ."


Cikin sa'a Affa ya yarda Ruƙayya ta ci gaba da karatu, don haka sai ta siyo jam form dama da result ɗin ta ya fito taga yanda tayi tsammani, don duk set ɗin su ba mai yawan credit ɗin ta.


Sun yi jarabawar jam bayan ta fito suka duba, cikin sa'a ta samu Bayero Kano kuma sun bata Course ɗin da take so wato law.


Kuɗin ta da ƙwamishina ya yi mata ƙyauta gaba ɗaya ta amso su, kuma ga kuɗin da Dady ya bar mata ko taro Affa bai ci ba, don haka aka soma shige da fice inda kuma ta je tayo registration, sannan ta zo ta kammala komai sai makaranta, kafin tafiyar ta tasha nasiha gurin Affa da Umma,sun kuma hore ta data tsaya tsayin daka tayi karatu dan shi ya kaita,ta kame kanta tare da maida kai gurin ibadarta. Tai musu alƙawarin bin yadda suka ce tare da tsare dokar Ubangiji.


Ta soma karatu cikin nasara ba wani problem hutun farko da ta dawo sun yi bikin Safiya dana Walida,sati ɗaya tsakanin su sun sha zirga-zirga tsakanin Katsina da Funtuwa, samarin Katsina sun sha kai hari ta ce no way.


Bayan sun koma hutu nan suka ci gaba da karatu, samarin makaranta sun sha cuso kai ba fuska, don haka sai su haƙura wasu su ci gaba da naci, fannin ƙawaye ma sai da ta tantance sannan ta zaɓi Munira M Bash da kuma Sadiya Armaya'u, dukkansu law suke karanta ƴaƴan masu kuɗi ne sosai sun zata Ruƙayya ma ƴar masu dashi ne, amma da kanta ta gaya musu iyayen ta talakawa ne. Sun sha mamakin jin haka don sunyi la'akari da shigar ta da kuma yanda take koman ta zuwa shopping ɗin ta,ta ce Affanta da Yayinta sune rufin asirin ta don haka take karatun ta yanda yakamata saboda kar suyi asara Sadiya Armaya'u ƴar Kano ce ita ko Munira M Bash ƴar Abuja ce mahaifinta minista ne, amma ƴan asalin Gombe ne, yanda take basu labari baima daɗe da samun muƙamin ba suka koma Abuja, Sukan je gidan su Armaya'u sunan da suke kiran Sadiya kenan Munira ma M Bash suke ce mata yayin da suke cewa Ruƙayya Muhammadu Sani, Hajiyarsu Armaya'u ta yarje ma Armaya'u da taje musu suma, Kaduna suka sauka gidan su Ruƙayya suka yi ƙwana uku Umma ta yaba da yanda suke tafiyar da rayuwar su haka ma Affa, Armaya'u da M Bash sun sha mamakin ganin gidan su Ruƙy M basu zata gaske ne su Ruƙy talakawa ne ba sai yau,dan ma Murja da Fati da Amina sun haɗu sun gyara gidan tare gyara ma Ruƙayya ɗaki sutura kam har yau tana ɗin ka na aƙwatin Dady gashi ta danka su gwanin sha'awa sai da ma su M Bash suka yi mata tsiyar aƙwatunan, ta ce son sune yasa na siya da yawa dan bata basu labarin Dady ba, sun kuma sha mata tsiya aka zoban hannunta wai ta cire tunda ya yi mata kaɗan ta ce tana son shi bazata taɓa iya rabuwa da zoban ba.


Sai dai sun yaba da tsaftar Umma tare da abincinta kalolin gargajiya masu shegen daɗi,ƙwana uku suka yi a Kaduna Affa ya yarje mata zuwa Abuja. Sun sha mamakin ganin gidan su Munira M Bash masu kuɗi ne na gaske,su huɗu ne ƴaƴan gidan,Yayanta Zuyad M Bash,sai ƙannan ta guda biyu Mom mahaifiyar su tayi murna da ganin Ruƙy da Armaya'u dan tana shan labarin su gurin Munira an musu sauka mai ƙyau tare da basu girma.


Tun gurin cin abinci Ziyad M Bash ya ƙyallo Ruƙy, don haka sai ya shiga mika mata saƙonni cikin gaggawa, ta ganoshi, sai dai ta basar, amma ya ɗan birgeta saboda ɗan sajenshi ya tuno mata da Dady, ya ce "Munira kin taɓa faɗa ma Ruƙy tana da ƙyau kuwa?"


Munira ta yi dariya ta ce "Itama ta sani bros zayid ni kaina ina son yanayin Ruƙy kaf B.U.K babu mai ƙyaun Ruƙayya dan ƙyaun ta dabanne.


Cikin dariya Ruƙy ta ce kai M Bash kina so sharri  fa."


Armaya'u ta ce "wane sharri ke ba fara bace ba kuma baƙa ba kina da yanayi da Black American ko Etopia."


Ya ce gaskiya kuke faɗa tama wuce nan,ni dai zan so ku mini compain dan mu samu iri a Abuja tunda babu a nan ɗin." Duk suka saki dariya.


Ya shagala yana kallon yanda take dariya, komai nata birgeshi yake yi.


Munira ta ce "Zan so haka bros Zayid ko dan mu samu golding Baby gidan nan."


Ruƙy ta tashi ta wuce tana cewa "Har na ƙoshi saboda zagin yayi yawa."


Kallo Zayid ya bita dashi kafin ya ce Mom, sister Munira komai na yarinyar nan eto ne,ina sonta."


Munira ta ce "To aƙwai aiki fa dan Ruƙy bata son samari kaga yanda yarinyar nan take gara maza? Sorry kaine ma naga tai maka dariya.


Ya ce "Ƙila rabo na ne."


Suka ce "Allah yasa."


Munira ta ce "To bros ya zamuyi da jalala kasan fa angama komai."


Ya ce "Ni miji mace nawa ne?"


Ta ce "a'a bamason kishiya." Ya ce "Yes zan iya barin jalila."suka sa dariya.


Armaya'u ta ce "Shikenan kabar komai a hannun mu."


Ƙwanansu uku suka yo sallama da Abuja cike da begen juna da kuma kaya niƙi-niƙi na tsaraba surutu da kayan shafa ciye-ciye da kuma lashe-lashe, musamman Bros ya zagaya dasu gurare  suka sha yawo,kai sun ji daɗin zuwa Abujan nan. Bayan sun koma daga hutu sun haɗe sun cigaba da gudanar da karatun su cikin tsari suna matuƙar son junansu da gaskiya. Saurayin Munira dake England Mustapha Ƙasim ɗan Alhaji Ƙasim ne abokin M Bash course ya je na shekara biyu kuma saura ƴan watanni ya gama.


Ita ko Sadiya Armaya'u coursing ɗin ta ne zata aura Shitu M.D suna zaune Fatakot,can ma yake aiki, cikin su Ruƙayya ce bata da dahir gashi Affa ya ce ita ma tasan me take ciki kafin ta gama.


Dad ya dubi ɗan nasa wanda ya cika har ya batse da ƙyau ga ƙoshin lafiya baya ga hawan jini dake damunsa baya da wata matsala. Ya ce "Son wannan satin za'a kawo sababbin injinan da kake magana akai, ina so ka isa Legos akan kari da zaran sun iso bana son ɓata lokaci."


Ya ce "To Dad da nima ina da zuwa Germany a wannan satin sai dai zan ɗaga sai next week na je."


Ya ce "kuma Momy ɗin ka tana son ganin ka."


Ya yi murmushi "Zan zo very soon aiki ne yayi yawa kuma ga costomers muna samu."


Dad ya yi murmushi "Son  ai kai komai naka akwai sa'a a cikin shi,you are very lucky akan komai, gashi yanzu Companynka yafi kawo riba, duk da daɗe war nawa naka fa baifi shekara biyar ba,niko nawa ya kai goma kuma ina ƙoƙari gurin aiki mai ƙyau."


Yayi dariya ya ce "Dad ai kowa da lokacin sa, kafin nasa yayin ya wuce shiyasa nike son tsiro wasu abubuwan kafin zuwan ƙurewar lokacin sa na dasa sabon zamani."


Dad ya ce "Kayi tunani Son."


Dad Ya miƙe "Ni zan tafi sai kazo,Dad ai ita Momy nasan damuwarta zan kirata a phone insha Allah kuma zan zo mata da labari mai daɗi. Ya yi dariya.


Zan kira phone naka Dad sai in komai ya yi normal.


To shikenan na wuce.


Ya ce "Ka gaida min da Hajja zan zo kada ta damu."


Bayan sallamar su da Dad ɗin ya koma ya zauna shiru ya yi yana tunanin sam ya manta ya yi ma Dad maganar bikin cikar Company shekara biyar da yake son yayi a watan gobe,ba komai dole ma yaje Kadunan kodan ya duba babban Companyn shi da za'a canza ma injina.


A gida bayan ya fito daga wanka yaronsa Sunday ya gabatar da dinner akan table,ya zauna ya soma ci white rice da miyar chiken sai kayan shaye-shaye musamman Hollandia wanda har Office akwai ta cikin fridge ɗin shi, don haka ne ma yasa a other ɗin shi da yawa don shi yake son ya sha lokacin partyn Companyn shi.


Bayan ya gama ya wanko baki,a bakin gado ya zauna shi kanshi yasan suna shirye-shiryen bikin Hussain,ya ɗan yi tsaki son ranshi ya huta amma yasan dole ne su je gurin ƙawayen amarya don suyi musu lissafin abubuwan da suke shiryawa. Gayu sosai ya yi don shi tun dama aƙwai Gayu shiyasa abokanshi suke kiran shi Son Guy.


Yasa turarenshi special Gold ya ɗauki key ɗin Hummer ya yi gidan Sagir.


Zina matar Sagir tana musu tsiya ba wani sallamar ƴan matan amarya taɗi zasu, Dady ya ce "To muda muke da right ɗin huɗu har zakiyi wani abu." Ta jawo Sagir  "gaskiya bazan yarda ba gara shi, yanzu zainab bata shiga gidan shi ba."


Dady ya ce "Ai na gaya mata tanada kishiya."


Zina ta ce "To ni banida ita,kai je ka." Dariya suka shiga yi mata ganin da gaske take.


Dady ya ce "Kaima sai ka ce ba namiji ba sai wani lallashin ta kake ka zo muje kawai."


Ta tura baki ta ce "To ku tafi ɗin."


Sagir ya ce "Ban isa ba,yama zan tafi bada iznin ki ba, salon in dawo ba wajen hutu, kiyi haƙuri tawan ƙarfe nawa zan dawo."


Dady ya fita yana cewa "Kai amma fa ba namiji bane, ka zama zauna nan mijin ta ce ni na fita inta barka to,in ko baka fito ba nan da minti uku to ni zan tafiya ta, kada inyi biyu babu gashi ance mata tantsa tantsa.


Sagir ya dubi Zina ya ce "Zinarin zuciyata na je? Allah bazan jima ba,kin ji tawan?"


Ta ce "To ka je amma minti ashirin."


Ya ce "Nagode." Ya yi waje.


Sannan ya ce "sai na dawo."


Sun isa gidan su amarya dake can Asokoro bayan sun shiga sun yi parking ƴan matan amarya da suke zaune a falo suna hira suna jiran zuwan abokan ango.Gogaggun ƴan mata ne ƴan jami'ar Abuja, ɗaya mai suna Bintu ta ɗan ɗaga labule ta ce "Kai gasu nan ku zo mu fita."


Wasu suka ce "a'a mu bari su iso."


Ƴan matan su goma ne cif, phone ɗin amarya Dady ya kira, ta ɗauka ya gamu, sun fito dukkansu, Sagir ya soma rawar jiki, "Kai kaga babys kuwa?.


Dady ya ce "Kama kanka fa," Dady yasha kunu, fuska ba walwala shi dama in yana gaban mata magana ma yinta yake kamar zasu siya,yana matuƙar kama ajinshi, kai ko Zainab da zai kai maganarta ga iyayenshi baya sakar mata fuska sosai, ita ko son shi take kamar me.


Suna isowa da yawan su Dady suke kaima hari,shi kam yasha kunu tamkar jinin sarauta, ya ce "Nawa ku kayi lissafi.?"


Bintu ta yi tsalle ta ce "Kasan fa abubuwan da zamuyi suna da yawa fa,ga dinner ga....." 


Ya katse ta "Kar kisa dinner don namu ne, kuma da zaki sauwaƙa ma kanki da kun faɗi kuɗin kawai don sauri muke yi."



🖊️🖊️🖊️

[7/29, 12:56] Ummi Tandama😇: *FIN ƘARFI BOOK 2*




                   *LITTAFIN*

*HALIMA ABDULLAHI K MASHI*



                        Page 6



Wata a cikin su mai suna Mina ta ce "Kai ko yanzu zaka tafi da wuri bawan Allah ka bari mu gaisa." Tayi tana fari.


Ya yatsina baki ya ce "No ma gaisa next time,nawa ne kuɗin?."


Suka ce "One million."


Ya ce "Ok, ya buɗe mota ya ciro check ya rubuta musu ya miƙa ya ce "Sagir zo muje."


Sai ga Sagir can da wata ya girgiza kai ya shige mota, ya faɗa ya yi mishi horn,don yasan Dady zaya iya tafiya yabar shi, shi yasa yayi sauri ya shiga motar.


Dady ya dubeshi "Kaidai sakaraine mata ne ajalin ka,ga mata a gida ka baro ka zo nan kana shirme."


Ya yi dariya ya ce "Tun da kai ka kasa bar mu muyi."


Dady ya ce "dole mata su garaka."


Bayan ya sauke Sagir sai ya nufi gida, shirin ƙwanciya yayi ya ɗauko Hollandia mai sanyi ya zuba a kofi, ya dubi cikin shi,a ranshi ya raya gobe zaya tashi da wuri don ya motsa jiki, tumbin nan nashi yana son ya zauna shi kuma ya tsani tumbi, ya ɗaga kai yana duban zaman yarinyar daya jima yana ƙishirwar gani hoton ta ya bada aka zana ta, tayi murmushi cikin ƙanana kaya ranar birthday ɗin shi akai mata hotunan,da shike me zanen ya ƙware sai ma tafi ƙyau a zanen fitilu yasa ja da blue in wannan ta kawo wannan ta ɗauke yayi addu'a ya shafa sannan ya tsura ma hoton ido ya raya ance tuni an mata aure ƙauyen Katsina yasan yanzu tana da yara tana kuma rayuwa cikin wahala.


Ya lumshe ido wasu ƴan hawaye suka zubo mishi shi kam daya san inda Pretty take daya taimaki rayuwarta da ya ba mijinta amanar ta daya taimaka mishi cikin waɗannan tunanin ya yi bacci.


Bikin Hussain ya kan kama, ƴan mata sai son Dady suke shi kam yaƙi bada fuska,dan ko Zainab taso zuwa bikin ya ce mata "A'a sai ranar dinner."


Zainab Umar ƴar wani minista ce Ƙawar Zina ce matar Sagir, ya shareta, ya shareta amma ta nace ta kuma liƙe,ya yarda zaya aure ta ne saboda dalilai guda biyu, na farko dan idonta yana mishi yanayi dana Pretty, sannan dan ya kare kanshi daga sha'awa tun da shi bai kasance mazinaci ba,in ya ji zaya matsu sai ya yi ta azuminshi shi yasa ya ce zaiyi ta kare sha'awa tunda an dace tana tsananin son shi, sai dai ya ce mata ba ita kaɗai ba ce, yanzu ma yana son su gama da bikin Hussain sannan ya je Kaduna dan kai zancan Zainab.


Sun sha biki taro ya tashi ankai amarya gidan ta dake nan Abuja. Dan su Hussain sun taso bayan ƙarin girman da mahaifinshi ya samu Dady ya je Legos daga can Kaduna ya wuce gurinsu Momy da farko tayi fushi amma yana bata labarin Zainab sai ta hau murna da sanya albarka ita ma Hajja taji daɗin jin labarin Zainab har tana cewa sai asa da wuri indai ana son in ci tuwon Zainabu Abun.


Ya ce "Babu gaggawa Hajja gaggawa daga shaiɗan ne.


Ta ce "Allah yasa mu dace, gashi Saude bata nan taje ganin gida da tayi murna sosai."


Ya yi ma Hajja alherin da ya sama, sannan ya fito,yana fitowa nan ma ya shiga yi wa mutanen dake maƙwafta da Hajja alheri, bakin wanda Allah yasa yana wajen kowa ya samu rabon shi haka Dady yake da ƙyauta.


Yana zuwa bus stop ɗin daya shiga unguwar su Pretty sai kawai ya tuna da, nan ya samu kanshi da shiga unguwar ya tsaya bakin shagon mutumin nan, bayan sun gaisa ya da mai shagon "Ka kuwa gane ni?."


Mai shagon ya ce "a'a."


Dady yayi murmushi yana mamakin yanda mutane basa gane shi da sauri. "Yanzu to me ya ƙara ne?"


Ya dubi mutumin  ya ce "don Allah ko har yanzu Malam Sani yana gidan shi na nan?"


Mai shagon ya ce "yana nan."


Dady ya koma mota ya rubuto check na dubu ɗari biyu ya ba mai shagon ya ce "Ka bashi ka ce Zakka ce nima an aiko ni ne."


Mai shago ya amsa jiki na rawa duk da bai san ko nawa bane tunda bashi da boko.


Shi ma dubu ashirin Dady ya bashi, ya tafi cike da tausayin Affa kasancewar Allah bai bashi namiji ba bare ya taimaka mishi.


Wannan hutun ma Mom ɗin su Munira ta matsa sai su Ruƙy sun zo mata musamman ma da za'ayi bikin ƙaninta kuma itace Uwar biki, Ruƙy daƙyar Affa ya barta, suna isa suka ci karo da Zayid dama tunda Munira ta ce mishi zasu zo shikenan ya shiga rawar jiki,ko yarinyan da zaya aura yasha bata labarin Ruƙy, tun tana fushi, har ta daina ƙwana ɗaya da zuwan su aka soma biki Munira ta kai su gyaran gashi da lalle, Uncle Jamil ƙanin Mom shine mai auran babban ɗan ƙwangila ne yana da kuɗi sosai ƴar Maiduguri zaya aura.


Sun halarci guraren bikin, har zuwa ranar dinner inda Ruƙayya tayi ƙwanciyar ta tace ta gaji ba zata ba,sukai ta naci taƙi, Mom ta ce "tashi kuje Ruƙy ai daga yau shikenan.


Ado sosai suka yi domin tunda suka zo sabon kaya suke sawa duk Mom tai musu har da jakunkuna da takalma, tare da Bros Zayid suka tafi dan ya ce ba zai je da Jalila ba.


Suna shiga gaban Ruƙayya ya yi wani irin mummunan faɗuwa nan take ta soma jin wata alama da ta jima har ma ta soma manta yanda abun yake,sai yau gurin dinner,tabbas ko shakka batayi matsawar ta ji wannan abin to Dady yana gurin,dan haka sai taji duk jikinta yayi sanyi daƙyar ta shiga, suna zaune a table ɗaya dasu Munira M Bash da Sadiya Armaya'u da kuma Bros,ido kawai Ruƙy take rabawa taga ta inda Dady zaya fito bata gani ba,ta na kai ganin ta ga ango da amarya, sun yi ƙyau sun kuma dace suna zaune,sai kusa da su ga wani table ɗin Ruƙy ta ce "Bros wancan kujerun na wanene?."


Ya ce "na abokinshi ne." Kafin tayi magana sai taga Dady sun shigo da Zainab jerowa suka yi sun sha ado tamkar amarya da ango,nan taji abin magana ya ɗauka "Ga babban aminin ango ya iso Yusuf Mansur, Yusuf wanda aka fi sani da Son Guy."


Tsigar jikin Ruƙy ya tashi yar musamman da taji ance tare da amaryar shi Zainab nan da nan kanta ya sara ta soma jin sanyi.


Tana jin su Munira suna cewa kan uba wannan haɗaɗden Guy ɗin fa? Bros Zayid ya ce "Yaro da kuɗi kenan, abokin Uncle Jamil ne, amma ya dama Uncle a kuɗi, wannan babban yaro ne sai a hankali Guy ɗin nan.


Tuni zazzaɓi ya rufe ta haka haƙoranta sai haɗuwa suke yi ta ce cikin makyarkyata,Bros Zi...,Bros Ziyad zo ka kaini gida bani da lafiya shi yasa nace ba zan zo ba."


Ta bayan mutane ta bi dan kada ya ganta, Bros ya kaita gida, shi ma Dady a nashi ɓangaren gaban shi ya faɗi kuma jikinshi ya bashi Pretty tana nan, sai dai shi tunanin shi mai zai kawo ta nan ita da aka ce mishi tana aure ƙauyen Katsina, sai dai fa koma menene tana nan gurin dan har ma ƙamshinta ya shiga ji,dube-dube da ƴan waige-waige har Zainab tana tambayar shi ko lafiya, ya ce mata babu komai.


Kuka sosai Ruƙy ta yi cikin dare har zuwa wayewar gari, shikenan Dady ya ci amana ya karya alƙawari ya yi aure ya manta da ita, ashe Dady zaya daina sonta? Lallai namiji a gaida maza basu da tabbas haka ta ƙwana da safe dole Mom ɗin su Munira ta yi ma Doctor ya zo ya duba Ruƙayya bayan tasha allurai ta samu bacci.


Shi ma Dady a daddafe ya bari aka gama dan dai yana matsayin babban abokin ango shiyasa ya haƙura ya na sauke Zainab bai saurari sallamar da zatai mishi ba, ya yi gaba,bin motar tayi da ido har ya ƙule ta ce "kai mutumin nan halin shi daban ne."


Washegari Ruƙy ta ce gida zata je amma sai Mom ta hanata ta ce sai gobe haka suka kuma ƙwana duk sun kasa gane kanta sai kuka take yi, koda ta koma gida ma Umma ta kasa gane kanta, sai dai cewa tayi kin san Umma ƙarshen wata shi yasa jikina ya soma mutuwa, Umma ta ce "To ai sai azo a siyo maganin da ki ke sha."


Ruƙayya ta yi tsaki ta ce "Magungunan nan masu shegen tsada haushi suke bani."


Umma ta ce "Aiko kina jin daɗi tun da baya yi miki mugun ciwon nan."


Ta ce "Sai dai kuma haka."


Umma ta ce "Au na manta na gaya miki ranan nan wani ya bada check a ba Affanku,wai zakka har dubu ɗari biyu ne,ko nawa ne, kuma ba'a gane ko wanene ba,dan Mai shago ya ba shi kuma mai shago ya ce bai gane ko wanene ba,dan shima ya bashi dubu ashirin."


Ruƙayya ta ce "To ko wanene Allah ya bashi lada haka dama ake son zakka.


Karatu babu kama hannun yaro su Ruƙayya Allah ya kawo su shekarar ƙarshe, sai dai inda da hali suna gamawa su je law school wata tara sai dai taji Munira ta ce mata da tsada amma ai komai yana gurin Ubangiji tunda da farko ma bata zaci zata gama karatun ba.


A ƙwana a tashi babu gurin a wajen Allah sun cikin sa'a wata biyu bayan nan aka soma shirye-shiryen bikin Munira su Ruƙayya manyan ƙawaye an soma yawo ba zama, ango Mustapha ya yi murna da ganin Ruƙayya,daya ke yana jin labarin ta gurin Munira, sun gama da abokan ango sun yi maganar komai bikin zaya kasance ne ranar sati saboda aiki, don haka tun Monday zasu soma bikinsu.


Ranar Lahadi kayan da zasu sa na musamman ne,dubu ashirin Affa ya ba Ruƙayya ta sai ma Munira gudunmawa suka haɗa da Sadiya Armaya'u suka buga zannuwa,Bros Zayid ma ya bata kuɗi duka ta haɗa.


Suna saloon ranar Monday sai ga wata yarinya ta shigo, Ruƙy tana ta satar kallon yarinyar domin tana ganin kamar ta santa, ta ce sannunku suka amsa.


Ta zauna ita ma gyaran kai tazo, haka komai yasa sai Ruƙayya taji bata son yarinyar, can sai yarinyar ta dubi kan Ruƙayya ta ce "Kai amma gaskiya kina da gashi,ga cika ga tsawo."


Ruƙy ta ce "To nagode,kema ai ba laifi."


Ta cire ɗanƙwalin ta, "kin ganshi dai.


Nata gashin tsawo ne dashi babu cika. Ruƙayya ta ce "Ga naki kina son na wani "


Suna cikin hira sai wayar yarinyar ta soma ringing,ta ciro ta ce "wanene zaya dameni?"


Tana dubawa taga sunan, cikin sauri ta ce "Oh My husband ya ya ne?."


Ko me yace? Sun dai ji tace "Ok, yau? Sai kuma suka ji ta ce "bikin ya zo ne? "Oh wannan satin lallai biki ya zo,to sai iso." Ta kashe waya.


Da yake mayyar surutu ce, sai ta dubi Ruƙayya ta ce "wanda zan aura ne ya je Holand shi ne yake gaya min zaya dawo don bai gama abin da ya kaishi ba, kuma ga bikin friend ɗin shi "


Sadiya ta ce "karatu ya je ne ko?"


"A'a harkokin kasuwanci shi ne ya kaishi sati biyu za yayi da,yau ƙwanan shi taƙwas kenan."


Ruƙy ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya."


Sun gama sun barta nan, Munira ta ce,"Kai wannan ta cika surutu tamkar an tambaye ta."


Ruƙayya ta ce "Ni fa haka nan batai min ba."


Sun iso gida suka samu sauran ƙawayen amarya na nan cikin garin Abuja sun iso, don haka sai suka haɗu suna labarin yanda kowanne program zaya kasance.


Sadiya Armaya'u ita ce tafi sauran damuwa ta ce "Gaskiya Munira abokan angon nan sun cika ƙwauro, gaskiya su ƙaro kuɗi ba zamu yi yanda muke buƙata ba.


Munira ta ce "nima naga haka shiyasa na ce ma Al-Mustapha sun mana ƙwauro,ɗari da hamsin ya yi kaɗan." Sauran suka ce gaskiya.


Munira ta ce "Ya ce in kuɗin be isa ba zaya ƙara mana yace dan ɗayan abokin baya nan ne shi yana da kirki yafi sauran,yana da zumunci."


Ruƙy ta ce "Kada dai mu nuna musu maitarmu a fili fa."


Ruƙy tana wanka ta ji ana "ga ɗayan abokin da ake labari ya zo, sai kawai ta ji gabanta ya yi mugun faɗuwa ta soma jin alamar Dady yana gurin, jikinta yayi sanyi Sadiya ta zo tace, "Ruƙy kiyi sauri ki zo ga wannan Guy ɗin da ake labari Allah ya kawo mana shi."


Ruƙy ta ce "Ku je kawai Armaya'u yanzu ma na soma wankan." Ta ce don Allah kiyi sauri ganin ki zai sa ya bamu ko nawa muka buƙata tunda waɗancan masu maƙon ma ganin kine suka ƙara."


Ta ce "To jeki zan zo." Guri ta samu cikin toilet ɗin tayi zamanta, hawaye suka ƙwace mata,ta tabbata ko kaffara ba zata yi ba, Dady ne ya zo,su shida suka fita duk da amarya, abokan kuwa su biyar ne banda ango Dady tun shigowar su unguwar nan jikinshi ya bashi Pretty tana nan. Suna tsayawa ƙofar gidan ya soma tunanin ko dai ita ma tazo bikin,to dalilin wa? shi ne bai sani ba.


Bayan sun gaisa sam fuskarshi babu walwala, Master ɗaya daga cikin abokan shine ya ce "Gafa ɗayan abokin mu ya iso kema amarya nasan baki san shi ba ko?.


Munira ta ce "Kaman dai na taɓa ganin shi, ina wuni?."


Ya ce "Lafiya,ya gida?"


Ta ce "lafiya."


Master ya ce "Ai ku ma ƙawayen amarya sai a gaisa ko?." Suka gaisa da Dady Sadiya ma ta gane shi.


Ya dubi Master ya ce "Kun gama komai ko?"


Master ya ce "Ƙwarai."


Ummi cikin ƙawayen ta ce "A'a suna son ƙarin kuɗi.


Master ya ce "Kun cika rainuwa mune fa zamu kama hull mu kawo drinks.


Sauran ƙawayen suka haɗa baki "Gaskiya ɗari da hamsin yayi mana kaɗan."


Sadiya ta ce "Ok Ruky M ko to tana wanka gaskiya ba zamu kira ta ba, komai Ruky sai ta ce kada mu matsa muku shiyasa ku kafi son magana da ita."


Dady yana jin su kuma duk da yasan ba Pretty ɗin shi ba ce sai ya samu kanshi da son ganin Ruky M ya dubi amarya, to Ruky ɗin tazo muji ta bakinta.


Wasu daga cikin ƴan matan sun ji haushi yana ta share mutane daga jin ance Ruƙy ya yi tsagal ya ce a kira ta.


Munira da kanta ta je ƙofar toilet ta ce "To sai ki fito ya ce dake zaya yi magana.


Ta ƙoƙarta ta ce "Bazan fito ba ku ce dashi kome ya ƙara ko nawa ne shikenan."


Yanda Munira ta ji muryar Ruky sai bata matsa mata ba ta juya. Ya na jiran ganin Ruky ta ɓullo sai ya ji Munira tana cewa har yanzu bata fito ba,dama fa ita in tashi ga wanka sai Allah.


Ta ce dai wai kuyi mana ƙari, ya ce "Check zan baku ko cash."


Suka ce "Cash don kasuwa zamu shiga."


Ya ce "To sai naji gida,dan ban fito da kuɗi ba,zan ba Master ya kawo."


Suka haɗa baki "A'a mudai gaskiya kada ka bashi."


Ya ce "To wa zan ba?"


Suka ce "Mudai kowa zaka ba ka ba amma ban da Master."


Master ya yi dariya ya ce "Kun min muguwar shaida ko?"


Suka sa dariya suka ce "Mun san zaka iya ragewa." Nan dai suka yi sallama.


Yaron shi Sunday ya yi ma ƙwatance ya kawo kuɗin, bayan an gama musu zanan dayis da suka yi gidan Aunty Farida sai suka wuce kasuwa.


Washegari Mom tayi mother day an cashe sai ranar Laraba suka yi Sister Day nan ma ba maza sannan sai Launching, Dady bai samu zuwa launching ba don yana Kaduna duk da zuciyarshi tana matuƙar son taga Ruƙayya ɗin nan, gashi ba zaya dawo ba sai ranar ɗaurin aure, kuma zasu halarci dinner yana jin shi da Zainab.


Yau ne ɗaurin auren Munira M Bash bayan gama ɗaurin aure an gabatar da walima anan cikin gidan su inda Malama Rukiya ta yi musu wa'azi mai shiga jiki tayi tsokaci kan zaman aure da kuma ƴan mata waɗanda basa son aure,ba dan sun rasa masu son su ba sai don wani dalili nasu na daban, gaba ɗaya Ruky sai tama ji tamkar dan ita akayi wa'azin,tayi tunanin wanda take wannan kanshi ya ma yi auren shi ya manta da ita don haka ita ma zata san abin yi don tunda ya karya mata alƙawari ta haƙura dashi garama da matsalar ta fito ta gurinshi, hawaye ya zubo mata,sam bazata iya zama da kishiya gidan Dady ba garama in wani ne amma ban da Dady,shi ɗin na daban ne a zuciyarta.


An kai Munira gidan ta dake Maitama, za'a je dinner ita kam ta yanke shawarar bazata je ba saboda ta san zaya yi wuya Dady bai je gurin ba kuma ita bata son su haɗu, tafi son koda zasu haɗun itama tayi aure ko kuma ta kama mijin auren a hannu.


Dan haka duk ƙawayen sun zube akan gadon amarya suna ta labari yawanci batsa tafi yawa a cikin hirar tasu. Ruƙayya wadda tayi shiru tana dubansu ta dubi Sadiya Armaya'u da ke ta faman zuba labarin yanda daren farkon ta zai kasance in anyi auren su da Shitun ta tace "Ke Armaya'u baki fa kida mutunci dan na kula da ace Hajiya zata ƙyale ki tsaf zaki kai kanki gidan shitun.


Sadiya ta ce "Ba dai ke kin tsaya yanga ba,dubi haɗaɗɗun Guys a B.U.K yadda suka mutu a kanki amma ki kai ta wulaƙanci."


Munira ta ce "Har kin tuna min da Faruk yaron nan ya mutu kan Ruky."


Sadiya tana dariya ta ce "Kai munci kuɗin Guy ɗin nan,sai muce zamu shawo masa kanta,kin ga yanda yake mana ƙyauta da a alƙawaruruka in mun shawo masa kanta zaya bamu."


Ruƙy ta ce "Ai ku dama ƴan iska ne."


Kafin wata ta ce wani abu phone ɗin Munira ta soma ringing Ango Al-Mustapha ne yake sanar da ita su shirya ga motoci nan zuwa,wai zo kiga shiri gurin amare ko ince ƴan matan amarya.


Ruƙy kam tana ƙwance lakadan tana duban su ɗaiɗai, Munira ta ɗaɗa mata duka "Ki tashi ki shirya Malama kin wani min ɗai ɗai a gado."


Armaya'u ta ce "Kin san ta gurin ƙwaliya ba dama, kallon mu kawai take yi,a ranta tana cewa kuyi ku gama zan baku assignment."


Su Ummi suka ce "Gaskiya Ruky aƙwai ta da tsara gay,in tana guri sai kiga duk ƙwalliyar ka ta zama dusu-dusu."


Na tashi zaune ina faɗin "Dukkanku nagode da zagi ke M Bash har da gorin gado ko? Ni ma ki jira nawa gadon very soon."


Armaya'u ta ce "Um kamar da gaske mu dai kawai ki shirya Malama."

Ta koma ta sake ƙwanciya tare da jawo filo "Ni fa ba zan je ba,Gara ma kun daina damuna da wani batun shiri."


Munira ta ce "Kina ƙarya ne." Ta soma ja mata hannu.


Ta ce Allah da gaske nake yi, babu inda zan je.


Suna ga kamar wasa ne amma sai Ruky tayi ƙiri-ƙiri ta ce bata zuwa.


Ran Armaya'u ya ɓaci ta ce "Haba Ruƙy M yama zaki ce wai ke bazaki je dinner ba, Ruky ta ce "To ai sai kiyi, tunda na ce baza ni ba,ba sai ku barni ba,ko dole ne? Ta ci gaba da ƙwanciyar ta ƙafa ɗaya kan ɗaya tana taunar cingam.


Munira ta ce "Shikenan nima na fasa zuwa tunda haka ne."


Sauran ƙawayen da wasu ƴan'uwanta suka ce don bazata ba,sai ki fasa lallai ma Munira.


Munira ta cire rigar da ta soma sakawa tare da nunkewa tana faɗin "Wallahi matsawar baza ta je ba,nima na fasa."


Mamakin ta ne ya cika sauran ƙawayen yayin da Ruky abin ya bata dariya, ta ce "M Bash kina hauka ne zaku tara mutane kice ba zaki je ba? Ashe kuma zaki bawa angon ki kunya kenan ko?"


Tsaki Munira ta ja, sannan kuma ta haye kan gadon itama, Armaya'u ta zauna bakin gadon tana cewa "Bani phone ɗin ki."


M Bash ta ce "To ba ga ta nan kusa dake ba."


Armaya'u ta ɗauka kai tsaye number angon ta nema.


Ga zaton shi amarya ce har ya ce "Sweet Darling kun gama shiryawa ne."


Armaya'u ta ce "a'a ba ita bace ni ce Sadiya Armaya'u dama zan sanar da kai ne cewa,wai Ruky da Munira sun fasa zuwa gurin dinner ɗin don haka sun ce ka sallami jama'an daka tara."


Ya ce "What,Me ya faru ne? Munira ta me? Sadiya ta ce "ban san me ya faru ba kuma ga Muniran nan."


Ya ce "Bata phone ɗin Please."


Sadiya tana dariya ta miƙa ma M Bash wayar. Cikin shagwaɓa ta ce "Hello Babyna." Ya ce "Sweet Darling me yake faruwa ne, ance kin fasa zuwa dinner ɗin.?"


Cikin shagwaɓa tamkar zata rushe da kuka ta ce "Ba Ruky M bace tace wai ta fasa zuwa nima shi ne kawai na fasa Please ka zo da kanka in kana son na je sai mu lallashe ta ko?"


Ya ce "four mint gani nan."


Shi da Master suka zo har cikin bedroom ɗin suka shigo yanda suka ƙwanta tuni suka tashi suka sake, Munira tana ta ɗan danne-danne a waya kanta na saman cikin Ruky, Al-Mustapha dariya suka bashi ya ce "Haba Ruƙy ke kuma da zaki gyara wasa sai kuma ki ɓata."


Ta tashi tana dariya ta ce "Ban ɓata ba Al-Mustapha na ce bazan samu zuwa bane shi ne wannan shagwaɓaɓɓiyar amaryar taka tace ta fasa sai ka ce kaine kace ba zaka je ba."


Ya ce "To ke me yasa bazaki bane?"


Ta ce "Wani dalili ne kawai."


Master yasa baki "Haba baby a gurin nan na boby kin gane?"


Al-Mustapha ya ce "Kai kuma malam kai mana shiru."


Ruƙy ta harari Master, ya ce "Allah ya huci zuciyarki Baby gani nayi kin fi sauran aji ko baki san aji ba?"


Al-Mustapha ya dube ta "don Allah Ruky saboda menene?"


Ta ce "Gaskiyar magana aƙwai wanda bana son mu haɗu da shi.


Ya ce "Kada ki damu ba zaku haɗu ba."Nan dai ta yarda zata daƙyar........




Ku ɗan ƙaramin haƙuri zuwa na uku dan jin yadda zata kaya..


Taku Halima Abdullahi K/Mashi

No comments